Language: Hausa

Book: Mark

Mark

Chapter 1

1 Wannan itace farkon bisharar Yesu Almasihu, Dan Allah. 2 kamar yadda aka rubuta cikin littafin annabi Ishaya. Duba, ina aika manzona, a gabanka, wanda zai shirya maka hanya. 3 Akwai murya mai kira a jeji, tana cewa ka shirya hanyar Ubangiji. ka daidaita ta. 4 Yahaya ya zo, yana baptisma acikin jeji yana wa'azin tuba, domin gafarar zunubai. 5 Dukan kasar Yahudiya da mutanen Urshalima suka zo wurin sa, a ka kuma yi masu baptisma a kogin urdun. suna furta zunubansu. 6 Yahaya yana saye da tufa ta gashin rakumi, yana kuma da damara ta fata a kugunsa, abincinsa fara ce da zuma. 7 Yana wa'azi, ya ce "akwai mai zuwa a bayana wanda ya ke da iko fiye da ni. wanda ko maballin takalminsa ban isa in kwance ba. 8 Ni ina yi maku baptisma da ruwa, amma mai zuwa a bayana zai yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki". 9 Sai ya kasance a kwanakin nan Yesu ya zo daga Nazarat ta Galili, sai Yahaya ya yi masa baptisma a kogin urdun. 10 Sa'adda Yesu ya fito daga ruwan, sai sama ta bude, sai Ruhu ya sauko a bisansa da kamanin kurciya. 11 Sai wata murya ta zo daga sama, tana cewa, "Kai kaunataccen Dana ne. zuciyata ta na murna da kai kwarai". 12 Sai Ruhu ya iza shi zuwa jeji. 13 Yana a jeji kwana arba'in, Shaidan yana jarabtar sa. Yana cikin jeji da dabobi, sai malaiku su ka yi masa hidima. 14 Bayan da aka kama Yahaya, Yesu ya shiga kasar Galili yana wa'azin bisharar Allah. 15 Yana cewa, "Lokaci ya yi, gama mulkin Allah ya kusato. Ku tuba ku bada gaskiya ga bishara". 16 Sa'adda ya ke wucewa a gefen takun Galili, sai ya ga Saminu da Andarawus, dan'uwansa suna jefa taru a teku, domin su masunta ne. 17 Yesu ya ce masu ku zo, ku biyo ni, ni kuwa sai in maisheku masuntan mutane". 18 Nan da nan suka bar tarun su, suka bi shi. 19 Sa'adda Yesu ya yi tafiya kadan, sai ya ga Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan'uwansa; suna gyaran tarunsu a jirgin ruwa. 20 Sai ya kira su, su kuwa suka bar mahaifinsu Zabadi a jirgin ruwan da ma'aikatansu, sai su ka bi shi. 21 Da su ka shigo cikin kafanahum, a ranar asabar, Yesu ya shiga majami'a ya koya masu. 22 Su ka yi mamakin koyarwarsa, domin ya na koya masu da iko ba kamar marubuta ba. 23 A nan cikin majami'a akwai wani mutum mai kazamin ruhu, sai ya yi ihu da karfi. 24 Yana cewa Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo ne domin ka halakar da mu? Na san wanene kai. Kai ne Mai Tsarki na Allah". 25 Sai Yesu ya tsauta wa kazamin ruhun ya ce, "Ka yi shiru ka fita daga cikinsa". 26 Bayan da kazamin ruhun ya buga shi kasa, sai kazamin ruhun ya yi ihu sa'annan ya fita daga jikinsa. 27 Sai dukan mutanen su ka yi mamaki kwarai, suna tambayar junansu menene wannan? wace sabuwar koyarwa ce da iko haka? har yana umartar kazaman ruhohi suna kuwa yi masa biyayya!" 28 Nan da nan labarinsa ya bazu ko'ina a dukkan kewayen kasar Galili. 29 Bayan da suka bar majami'a, sai su ka shiga gidan Saminu da Andarawus, suna kuma tare da Yakubu da Yahaya. 30 Surikar Saminu tana kwance ba lafiya tana fama da zazzabi. Sai suka gaya wa Yesu game da ita. 31 Sai ya zo, ya kama hannunta, ya daga ta, sai zazzabin ya sake ta, ta fara yi masu hidima. 32 Da yamman nan, bayan da rana ta fadi, sai su ka kawo masa dukan marasa lafiya da masu fama da aljanu. 33 Dukan mutanen garin su ka taru a bakin kofa. 34 ya warkar da masu ciwo da yawa da masu chututtuka iri-iri, ya kuma fitar da bakaken aljanu, amma bai yarda aljanun su yi magana ba domin sun san shi. 35 Ya tashi da sassafe, tun da sauran dare, ya tafi wurin da ba kowa, a can ya yi add'ua. 36 Saminu da wandanda suke tare da shi suka neme shi. 37 Suka sa me shi, sai su ka ce masa, "kowa yana nemanka". 38 Ya ce, bari mu tafi wani wuri, zuwa wadansu garuruwan da ke kewaye, Saboda in yi wa'azi a can kuma. Wannan shi yasa na zo nan". 39 Ya tafi dukan kasar Galili, yana wa'azi a majimi'un su yana kuma fitar da aljanu. 40 Wani kuturu ya zo wurinsa. Yana rokonsa, ya durkusa. Ya ce masa, "in ka yarda kana iya warkar da ni. 41 Sai ya yi juyayi, Yesu ya mi ka hannun sa ya ta ba shi ya na ce masa "Na yarda. Ka sarkaka". 42 Nan da nan kuturtar ta barshi, ya kuma sa mu tsarkakewa. 43 Yesu ya yi masa gargadi sosai, ya salame shi. 44 Ya ce masa "ka tabbata fa kada ka gayawa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, sai ka je ka yi hadaya domin tsarkakewa kamar yadda Musa ya umurta, domin shaida. 45 Amma da ya fita sai ya fara gaya wa kowa, ya baza maganar a ko'ina, har Yesu bai iya tafiya a sake a garin ba. Ya tafi ya tsaya a wuraren da ba kowa, mutane kuwa su ka zo wurinsa daga ko'ina.

Mark 1:1

Muhumin Bayani:

littafin Markus ta fara the anabcin annabi Ishaya game da zuwan Yahaya mai baftisma, wanda ya yi wa Yesu baftisma.

Ɗan Allah

Wannan laƙani ne mai mahimanci na Yesu.

a fuskarku

Wannan karin magana ce wanda ke nufin "a gabanku"

fuskarka... hanyarka

A nan, kalman nan "ka"

wanda

Wannan na nufin mai sakon.

zai shirya hanyarka

Yin haka na nufin shirya mutane domin zuwan Ubangiji. AT: "zai shirya mutanen domin zuwanka"

Muryar wani na kira a jeji

Wannan za a iya bayyanata a jimla kamar haka. AT: "an ji muryar wani na kira a jeji" ko kuwa "Sun ji karar wani na kira a jeji"

Shirya hanyar ubangiji ... daidaita hanyarsa

wadannan maganganu suna nufin abu daya ne.

Shirya hanyar Ubangiji

"sa hanyar Ubangiji ta shiryu." yin haka na madadin yin shiri domin sakon Ubangiji in ta zo. mutane na yi haka tawurin tuba daga zunubansu. AT: "shirya domin sakon Ubangiji a sa'ada ta zo" ko kuwa "Tuba da kuma shiri domin zuwan ubangiji"

Mark 1:4

Yahaya ya zo

Ku tabbatar cewa masu karatu sun fahimci cewa Yahaya ne mai saƙon da anabi Ishaya ya yi maganarsa a ayan da ta rigaya.

Dukan kasar Yahudiya da dukan mutanen Urushalima

Kalmomin nan "dukan kasar" misalin ne ta mutanen da ke zama a kasar da kuma wanda ake nufin mafi yawan mutane, ba kowane mutum ba. AT: "Mutane daga Yahudiya da Urushelima"

ya ka kuma yi masu baftisma a Kogin Urdun. suna furta zunubansu.

Sun yi wannan a lokaci ɗaya be. An yi wa mutanen baftisma domin sun tuba daga zunubansu. AT: A sa'ada suka tuba da zunubansu, Yahaya ya yi musu baftisma a Kogin Urdun"

abincinsa kuwa fara ce da zuma

Fara da zuma irin abinci biyu ne da Yahaya saba ci a sa'anda ya ke jeji. Wannan bai nuna cewa Yahaya ya cin waɗannan abinci a sa'ada yana yi wa mutanen baftisma ba.

Mark 1:7

ya shaida

"Yahaya ya shaida"

wanda ko maballin takalminsa ban isa in durkusa in kwance ba

Yahaya ya kwatanta kansa da bawa don ya nuna yadda girman Yesu yake. AT: "ban isa in kaskantarciyar aikin cire takalminsa ba" (Dubi: )

maballin takalminsa

A lwancan oƙacin da Yesu ke cikin duniya, mutane sun cika sa takalma wanda aka yi da fata suna kuma ɗaure ƙafafunsu da igiyar fata.

sunƙuya

"sunƙuya"

amma mai zuwa a bayana zai yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki'

Wannan na kwatanta baftisman Yahaya da ruwa da kuma baftisma mai zuwan nan gaba da Ruhu Mai Tsarki. Wannan na nufin cewa baftisman Yahaya alama ce ta share zunuban mutane. Baftisma ta wurin Ruhu Mai Tsarki lallai zai wanke mutane daga zunubansu. In ya yiwu, yi amfani da kalma ɗaya ta "baftisma" anan kamar yadda kun yi amfani da shi ga "Yahaya mai baftisma" don kwatanci tsakanin biyun.

Mark 1:9

ta faru a zamanin can

Wannan alama ce na farkon wani abu da ya faru a labarin.

An yi masa baftisma ta wurin Yahaya

AT: "Yahaya ya yi masa baftisma"

Ruhun ya sauko a bisan sa kamar kurciya

Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) wannan wa salon magana ne, wato Ruhun ya sako bisa Yesu kamar tsuntsu dake saukowa daga sarari zuwa kasa ko kuwa 2) Ruhun daidai kamar kurciya ya sauko bisa Yesu.

Murya daga sama

Wannan na wakilcin Allah na magana. Wani loƙaci mutane na ƙin kiran sunan Allah domin suna girmama shi. AT: "Allah ya yi magana daga sama"

ƙaunataccen ɗa

Wannan lakabi ne mai muhimmanci na Yesu. Uban ya kira Yesu "ƙaunatacciyar ɗa" sa saboda madawammiyar ƙaunarsa gare shi.

Mark 1:12

Mahaɗin Zance:

Bayan Baftisman Yesu, yana cikin jeje kwanaki arba'in, ya kuma tafi Galilee don ya koyar ya kuma kira almajiransa.

iza shi ya fita zuwa

"tilasta Yesu ya fita zuwa"

Yana a jeji

"Ya zauna a jeji"

kwanaki hamsi

"kwanaki 40"

Yana tare da

"Yana tsakanin"

Mark 1:14

bayan an kama Yahaya

"bayan an sa Yahaya a kurkuku." AT: "bayan su kama Yahaya"

shalar bishara

"gayawa mutane da yawa game da bisharar"

Lokacin ya yi

"Yanzu ne lokacin"

Mulkin Allah ya kusa

"Lokaci ya kusa da Allah zai fara mulki mutanensa"

Mark 1:16

ya ga Siman da Andarawas

"Yesu ya ga Siman da Andarawas"

suna jefa taru a teku

A nan iya bayyana ma'anar wannan magana a fili. AT: "jefa taru cikin ruwa don su kama kifi"

Zo, ku bi ni

"Ku bi ni" ko kuwa "Ku zo tare da ni"

Zan mai da ku masuntan mutane

Wannan na nufin cewa Siman Andarawas za su koya wa mutane gaskiyar saƙon Allah don wasu ma su bi Yesu. AT: "Zan koya muku yadda za ku tara mutane zuwa gare ni kamar yadda kuna tara kifi"

Mark 1:19

cikin jirgin

Ana iy tsammani cewa jirgin na Yakubu da Yahaya ne. AT: "cikin jirginsu"

ɗinkin taruna

"gyaran taruna"

kira su

Zai zama da taimako sosai in ab faɗa dalilin da ya sa Yesu ya kira Yakubu da Yahaya. AT: "kira su su zo gare shi"

ma'aikata da aka yi hayar

"bayin da ke yi musu aiki"

sun bi shi

Yakubu da Yahaya sun tafi tare da Yesu.

Mark 1:21

zo cikin Kafarnahum

"shiga Kafarnahum"

don yana koyar da su kamar wanda ke da iko ba kamar marubutan ba

Ra'ayin "koyarwa" ana iya bayana ta a fili in ana magana game da "wani wanda ke da iko" da kuma "marubutan." AT: "domin yana koyar da su kamar yadda wanda ke da ikon ke koyarwa ba kamar yadda marubutan ke koywarwa ba"

Mark 1:23

Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazare?

Aljanu sun yi wannan tambaya da ma'anan cewa ba bu wata dalilin da Yesu zai shiga tsakani su kuma suna so ya bar su. AT: "Yesu Banazare, ka bar mu! Babu wata dalilin da zai sa ka shiga tsakanin mu."

Ka zo ne ka hallaka mu?

Ajanun sun yi wannan tambaya don su cewa Yesu kada ya yi musu lahani. AT: "Kada ka hallaka mu!"

wurgar da shi

A nan kalman nan "shi na nufin mutumin nan mai aljanin.

Sa'ad da ya yi kuka da murya mai karfi

Aljan ne ke kuka ba mutumin ba.

Mark 1:27

sun tambaye juna, "Me cece wannan?" Tabɗi! sabuwar koyarwa da iko? ... suka kuma yi masa biyayya!"

Mutanen sun yi amfani da tambayoyi biyu don su nuna mamakin su. Ana iya bayana tambayoyin kamar maganar motsin rai. AT: "suka cewa juna, "wannan da mamaki! Ya bada sabuwar koyarwa kuma ya yi magana da iko! ... suka kuma yi masa biyayya!'"

Ya umurce

Kalman nan "ya" na nufin Yesu.

Mark 1:29

Yanzu kuwa surukuwar Bitrus na kwanciye ba lafiya, zazzaɓi na damun ta

Kalman nan "yanzu" na gabatar da surukuwar Siman a labarin da kuma ƙarin haske ga labari game da ita.

tashe ta

"sa ta ta tashi tseye" ko kuwa "ya sa ta ta iya saukowa daga gado"

zazzaɓin ya bar ta

Ana iya nuna wa a fili wanda ya warkar da ita. AT: " Yesu ya warkar da ita daga zazzaɓi"

ta yi musu hidima

Ana nufin cewa an ba su abinci. AT: "ta ba su abinci da ruwan sha"

Mark 1:32

duk marasa lafiya ko kuwa masu aljan

Kalman nan "duk" zuguiguci ne da ke nanata gaggaruman lisafin mutanen da suka zo. AT: "yawanci wanda ke rashin lafiya ko kuwa masu aljan"

Dukkan 'yan birnin sun taru a ƙofar

Kalman nan "birni" na nufin mutanen da ke birnin. A nan kalman nan "dukka" mai yiwuwa na nanata cewa yawancin mutane daga birnin sun taru. AT: "Mutane da yawa daga birnin sun taru a bakin ƙofar"

Mark 1:35

inda ba kowa

"wurin da zai iya zama shi kaɗai"

Siman da waɗanda ke tare da shi

A nan "shi" na nufin Siman. Waɗanda suke tare da shi kuma sune Andarawas, Yakub, Yahaya, mayiwuwa da wasu mutane.

Kowa na neman shi

Kalman nan "kowa" zuguiguci ne da ke nanata cewa mutane da yawa suna neman Yesu. AT: "Mutane da yawa suna neman ka"

Mark 1:38

Mu tafi wani wuri

"Ya kamata mu je wasu wurare." A nan Yesu ya yi amfani da kalman nan "mu" don yana nufin kansa da kuma Siman, Andarawas, Yakub da Yahaya.

Ya gama dukkan ƙasar Galili

Kalman nan "gama dukkan" zuguiguci ne aka yi amfani da ita don a nanata cewa Yesu ya tafi wurare da yawa lokacin da yake aikinsa. AT: "Ya tafi wurare da yawa a ƙasar Galili"

Mark 1:40

Wani kuturu ya zo wurinsa, yana roƙonsa, ya durƙusa yana cewa

"Wani kuturu ya zo wurin Yesu, ya durƙusa yana roƙon Yesu yana cewa"

In ka yarda, ka tsarkake ni

Cikin jimla ta farko, kalman nan "a tsarkake ni", an fahimce ta saboda jimla ta biyu ne. AT: "In ka yarda ka tsarkake ni, to, za ka iya tsarkake ni"

yarda

"so" ko kuwa "muradi"

za ka iya tsarkake ni

A lokacin littafi Mai Tsarki, mutum da ke da wani cuta da ta shafi fata, ana dubansa mara tsarki, sai ya warke gabakiɗaya . AT: "za ka iya warkar da ni"

Sai ya yi juyayi, Yesu

A nan kalman nan "ya yi" na nufin a ji tausayi game da bukatan wani. AT: "Da tausayi domin sa, Yesu" ko kuwa "Yesu ya ji tausayi domin mutumin, sai ya"

Na yarda

Zai yi taimako in an ambata abin da Yesu ya yarda ya yi. AT: "Na yarda in tsarkake ka"

Mark 1:43

Ka tabbata ba ka gaya wa kowa ba

"Ka tabbata ba ka gaya wa kowa kome ba"

nu na kanka ga firist

Yesu ya ce wa mutumin ya nuna kansa ga firist domin firist ya duba fatansa ko kuturtan ya barshi da gaske. An bukaci wannan cikin dokar Musa, mutum ya kai kansa gaban firist in an tsarkake shi.

nuna kanka

Kalman nan "kanka" na wakilcin fatan kuturun. AT: "Nuna fatanka"

shiada a gare su

Zai fi kyau a yi amfani da "su" in mai yiwuwa ne a harshen ku. Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) "shaida ga firist" ko kuwa 2) "shaida ga mutanen."

Mark 1:45

Amma ya tafi

Kalman nan "ya" na nufin mutumin da Yesu ya warkar.

ya shiga yada labarin a ko'ina

A nan "yada labarin a ko'ina" na nufin cewa ya yi shaida wa mutane a wurare daban dabam game da abin da ya faru. AT: "fara gaya wa mutane a wurare da yawa game da abin da Yesu ya yi"

har ya kai

Mutumin ya yada labarin har ya kai

cewa Yesu bai iya shiga wani gari a sarari ba

Wannan ita ce sakamakon yada labarin da mutumin ya yi so sai. Anan "sarari" na nufin "a fili."Yesu bai ba iya shigan farin ba domin mutane da yawa sun taru a gefensa. AT; "cewa Yesu bai iya shigar a fili ba" ko kuwa "cewa Yesu bai iya shigar garin ta hanyar da mutane za su iya ganinsa ba"

wuraren da ba kowa

"wuraren kaɗaici" ko kuwa "wuraren da babu kowa"

daga ko'ina

Kalman nan "ko'ina" an yi amfani da ita don a nanata cewa mutane daga wurare da yawa ne suka zo. AT: "daga dukkan yankin"

Chapter 2

1 Da ya dawo Kafarnahum bayan yan kwanaki kadan, aka ji cewa yana gida. 2 Da yawa suka taru a can, ba wuri har kofa, sai Yesu ya yi masu magana. 3 Sai wadansu mutane su ka zo wurinsa dauke da wuni mutum shanyayye, mutane hudu na dauke da shi. 4 Lokacin da ba su iya zuwa kusa da shi ba domin yawan jama'a, sai su ka daye jinkar dakin daidai da inda ya ke. Bayan da suka huda ramin suka saukar da gado wanda shanyayyen ke kwance a kai. 5 Da ganin bangaskiyarsu, Yesu ya ce wa shanyayyen mutumin, "Da, an gafarta maka zunuban ka". 6 Amma wadansu marubuta da ke zaune a nan, suka yi tunani aransu. 7 Yaya wannan mutum zai yi magana haka? Ya yi sabo! wa ke iya gafarta zunubi "sai Allah kadai?" 8 Nan da nan Yesu ya sani a ruhunsa, abinda suke tunani a tsakaninsu. Ya ce masu, "Me ya sa kuke tunanin wannan a zuciyarku? 9 Me yafi sauki a cewa shanyayyen mutumin, 'An gafarta maka zunuban ka' ko kwa a ce masa, 'tashi, ka dauki shinfidarka, ka yi tafiyarka'? 10 Amma domin ku san cewa Dan mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya, ya ce wa shanyayyen, 11 "Na ce maka, tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidan ka." 12 Sai nan da nan ya tashi ya dauki tabarmarsa, ya fita gidan a gabansu, dukansu su ka yi mamaki, su ka girmama Allah, "suka ce ba mu taba ganin abu irin wannan ba." 13 Ya sake fita gefen tafki, dukan taron jama'a suka zo wurinsa, sai ya koya masu. 14 Sa'adda ya na wucewa, ya ga Levi dan Halfa yana zaune a wurin karbar haraji, sai ya ce masa, "Ka biyo ni." Ya tashi, ya bi shi. 15 Sa'adda Yesu ya shiga gidan Levi yana cin abinci, masu karbar haraji da masu zunubi da yawa su ka zo wurinsa da almajiransa, jama'a masu yawan gaske suka ka bi shi. 16 Da Marubuta wadanda su ke Farisawa, sun ga cewa Yesu na cin abinci da masu zunubi da masu karbar haraji, sai su ka ce wa almajiransa, "Me ya sa ya ke ci da masu karbar haraji da mutane masu zunubi?" 17 Da Yesu ya ji wannan ya ce masu, "Mutane wadanda ke da lafiya a jiki ba su bukatar likita; sai dai ko marasa lafiya ke bukatarsa. Ban zo domin in kira mutane masu a dalci ba, amma mutane masu zunubi." 18 Almajiran Yahaya da Farisawa suna azumi, sai wadansu mutane suka zo suka ce, "Don me almajiran Yahaya da almajiran Farisawa na azumi amma na ka almajiran ba su yi?" 19 Sai Yesu yace masu, "Abokan ango, za su yi azumi sa'adda ango yake tare da su? muddin suna tare da ango ba za su yi azumi ba. 20 Amma kwanaki za su zo da za a dauki angon daga gare su, a wadancan kwanakin ne, za su yi azumi. 21 Babu wanda zai dinka sabuwar riga ya hada ta da tsohuwar riga, sai rigar ta yage, kuma ta yi mummunar yagewa. 22 Babu wanda zai sa sabon ruwan inabi a cikin tsohuwar salka, ai sai salkar ta fashe kuma ruwan inabin ya zube. duka biyu ruwan inabin da salkar arasa su. A maimakon haka, sai ka sanya sabon ruwan inabi cikin sabuwar salka." 23 A ranar asabar Yesu ya tafi cikin gonakin hatsi, sai almajiransa su ka fara zagar hatsi, 24 Sai Farisawa su ka ce masa, "Duba, don me suke yin abin da bai dace a yi ranar Asabar ba?" 25 Yace masu, Ba ku karanta ba abinda Dauda ya yi sa'adda yake jin yunwa, shi da mutanen da ke tare da shi? 26 Yadda ya shiga gidan Ubangiji, sa'adda Abiyata ya ke babban firist, ya ci gurasa da ke ta firist wadda bai dace wani ya ci ba sai Firistoci. Har kuma ya ba wadanda ke tare da shi?" 27 Yesu yace, "Asabar an yi ta don mutum ne, ba a yi mutum don Asabar ba. 28 Saboda haka, Dan Mutum Ubangiji ne, har da na Asabar."

Mark 2:1

Mahaɗin Zance:

Bayan wa'azinsa da kuma warkar da mutane da Yesu ya yi a yankin kasar Galili, ya koma kafarnahum inda ya warkar da wani shanyayye mutum ya kuma yafe masa zunubansa.

sai suka ji labarin yana gida

AT: "Mutanen da da ke a wurin sun ji cewa yana zama a gida"

da yawa suka taru a wurin

Kalman nan "a wurin" na nufin in da Yesu ke zama a kafarnahum. AT: "Mutane da yawa sun taru a wurin" ko kuwa "Mutane da yawa sun zo gidan"

har ba sauran wuri

Wannan na nufi babu wurin a cikin gidan. AT: "har babu ɗaki domin su a ciki"

Yesu ya yi magana game da kalman zuwa gare su

"Yesu ya yi wa'azin saƙon zuwa a gare su"

Mark 2:3

mutum huɗu na ɗauke da shi

"su huɗu suna ɗauke da shi." Mai yiwuwa akwai mutane fiye da huɗu cikin mutanen da suka kawo mutumin wurin Yesu.

na kawo shanyeyyen mutum

"na kawo mutumin wanda ba iya tafiya ba ko kuwa bai iya amfani da hannayensa ba"

kăsa kusa da shi

"kăsa zuwa kusa da inda Yesu yake"

suka cire rugin ... suka sauƙar

Gidajen da Yesu ya zauna na da shimfiɗaɗɗen rufi da aka yi da yumɓu aka kuma rufe da fale-falen abu. Ana iya bayana a fili yadda ake yin rami a rufi ko kuwa ana iya bayana ta ga yadda kowa zai gane ya harshen ku. AT: "suka cire fale-falen abin da aka sa a saman rufi daidai in da Yesu yake. Bayan sun tona rufin yumɓun, sai suka sauƙar" ko kuwa "sun yi rami cikin rufin daidai ta inda Yesu yake, sai suka suaƙar da

Mark 2:5

da ganin bangaskiyarsu

"da ganin bangaskiyar mutanen." Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) cewa mutanen da suka ɗauke shanyeyyen mutumin ne kawai ke da bangaskiya. ko 2) cewa shanyeyyen mutumin da mutanen da suka kawo shi wurin Yesu, dukkan su su na da bangaskiya.

Ɗa

Kalman nan "Ɗa" a nan na nuna cewa Yesu ya kula da shi kamar yadda uba ke kula da ɗa. AT: "Ɗa na"

an yafe maka zunubanka

In mai yiwuwa ne a juya wannan yadda zai nuna cewa Yesu bai faɗi wanda ya yafe zunuban mutumin ba. AT: "zunubanka sun tafi" ko kuwa "ba ka bukatan ka biya domin zunubanka na" ko kuwa "ba a lisafta zunubanka a kanka ba"

tunani a zuciyarsu

A nan "zuciyarsu" na nufin tunanin mutane. AT: "suna tunani da kansu"

Yaya wannan mutu zai yi magana haka?

Marubutan sun yi amfani da wannan tambayar don su nuna fushin su cewa Yesu ya ce "An gafarta maka zunubanka" AT" "Bai kamata wannan mutum ya yi magana haka ba!"

Wa zai iya gafarta zunubi in ba Allah ba?

Marubuta sun yi amfani da wannan tambayar cewa dashike Allah ne kaɗai ke iya yafe zunubai, to ba kamata Yesu ya ce "An yafe maka zunubanka" ba. AT: " Allah ne kaɗai ke da iya yafe zunubai!"

Mark 2:8

a ruhunsa

"cikin ransa" ko kuwa "a cikinsa"

suna tunani a junansu

Kowane malamin attaura na tunani da kansa; ba su magana ga juna.

Me yasa kuna tunanin wannan a zuciyarku?

Yesu ya yi amfani da wannan tambayar don ya gaya wa malaman attauran cewa abin nana da suke tunani ba daidai ba ne. AT: "Abin da kuke tunani ba daidai ba ne." ko kuwa "Kada ku yi tunanin cewa ina saɓo"

wannan a zuciyarku

Kalman nan "zuciya" na nufin tunaninsu da kuma sha'awace sha'awacensu. AT: "wannan a cikin ku" ko "waɗannan abubuwa"

Wanne ya fi sauƙi ga shanyeyyen mutumin ... ɗauki gadonka ka yi tafiyar'?

Yesu ya yi amfani da wannan tambayar don ya sa malaman attauran tuna game da abin da zai tabbatar cewa lallai zai iya yafe zunubai ko ba zai iya ba. AT: "Na dai cewa wa shanyeyyen mutumin, 'An yafe maka zunubanka.' Mai yiwuwa kuna tunanin cewa yana da wuya a ce 'Tashi, ɗauki gadonka ka yi tafiya,' saboda tabbacin cewa zan iya ko ba zan iya warkar da shi, ba za a nuna ta tawurin tashinsa ya yi tafiya ko kuwa bai tashi ya yi tafiya ba." ko kuwa "Mai yiwuwa kuna tunanin cewa ya fi sauƙi a ce ma shanyeyyen mutumin 'An yafe maka zunubanka' fiye da a ce 'Tashi, ɗauki gadonka ka yi tafiya.'"

Mark 2:10

Amma don ku sani cewa

"Amma don ku sani." Kalman nan "ku" na nufin marubutan da kuma taron jama'an.

cewa Ɗan Mutum na da ikon

Yesu ya dubi kansa a matsayin "Ɗan Mutum." AT: "cewa ni Ɗan Mutum ne kuma ina da iko"

a gaban kowa

"a sa'ad da dukkan mutanen ke kallo"

Mark 2:13

tafki

Wannan tekun Galilli ne wanda ake kiran ta tafkin Janisarata.

taron jama'an sun zo wurinsa

"mutanen sun je in da ya ke"

Lawi ɗan Halfa

Halfa uban Lawi ne.

Mark 2:15

gidan Lawi

"gidan Lawi"

Mutane masu zunubi

Farisiyawan sun yi amfani da jimlar nan "mutane masu zunubi" don suna nufi mutanen da ba sa bin doka kamar yadda Farisiyawan na nuna su yi.

masu yawan gaske suka bi shi

Ma'ana mai yiwuwa na kamar haka 1) "don akwai masu karɓar haraji masu yawan gaske da mutane masu zunubi wanda suka bi shi" ko kuwa 2)"gama Yesu yana da almajirai masu yawa sun kuma bi shi."

Me ya sa ya ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?

Malaman attauran da Farisiyawan sun yi wannan tambayar don su nuna cewa ba su yarda da kirkin da Yesu ya nuna ba. Ana iya sa wannan cikin magana. AT: "Bai kamata ya ci da masu zunubi da masu karɓar haraji ba!"

Mark 2:17

Ya ce musu

"ya ce wa malaman attauran"

Mutane masu karfi cikin jiki ba su bukatan likita' sai dai mutane wanda ba su da lafiya

Yesu ya yi amfani da wannan karin magana game da mutane marasa lafiya da likita don ya koya musu cewa mutanen da sun san cewa suna cike da zunubi sun gane cewa suna bukatan Yesu.

masu karfi cikin jiki

"lafiyayyu"

Ba domin in kira masu adalci na zo ba, amma mutane masu zunubi

Yesu na tsammanin masu sauraronsa su fahimci cewa ya zo ne domin waɗanda ke bukatan taimako. AT: "Na zo domin mutanen da sun fahimci cewa su masu zunubi ne, ba domin mutane da sun gaskanta cewa su masu adalci ne ba"

amma mutane masu zunubi

Kalmomin nan "na zo in kira", an fahimci ta ne daga maganar da ke kafin wannan. AT: "amma na zo domin in kira mutane masu zunubi"

Mark 2:18

Farisiyawan na azumi ... almajiran Farisiyawan

Wannan maganganu biyun na nufin ƙungiyan mutane ɗaya ne, amma an tabbatar da na biyun. Duka biyun na nufin mabiyan ɗarikar Farisiyawan, amma ba su mayar da hankali ga shugabannen Farisiyawan ba. AT: "almajiran Farisiyawan na azumi ... almajiran Farisiyawan"

Wasu mutane

"Wasu mutane." Zai fi kyau in an juya wannan magana ba tare da an tantance wanene waɗanan mutanen ba. Idan a harshen ku lallai ne a tantance, to ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) waɗannan mutanen ba sa cikin almajiran Yahaya ko kuwa almajiran Farisiyawa ba ko kuwa 2) waɗannan mutanen na cikin almajiran Yahaya.

zo sun ce masa

"zo sun ce wa Yesu"

Abokan ango, za su yi azumi sa'adda ango yake tare da su?

Yesu ya yi amfani da wannan tambayar don ya tunashe mutanen abin da sun riga sun sani don kuma ya karfafa su yi amfani da ita da shi da almajiransa. AT: "Abokan ango, ba sa azumi a sa'ad da ango na tare da su. Maimakon haka suna shagali da taya shi murna."

Mark 2:20

za a ɗauki angon

AT: "angon zai tafi"

daga wurinsu ... za su yi azumi

Kalman nan "su" na nufin abokan ango.

Babu mutum zai ɗinka sabuwar riga ya hada ta da tsohuwar tufa

Ɗinkin riga a kan tsohuwar tufa na sa ramin tsohuwar tufan ta zama mafi ɓaci in gutsuren sabon rigan bai tauye ba. Sabon rigar da tsohon tufan duk za su ɓaci.

Babu mutum.

"Babu mutum." Wannan maganar na nufin dukkan mutane, ba mazaje kawai ba.

Mark 2:22

sabuwan ruwan inabi

"ruwan 'ya'yan itacen inabi." Wannan na nufin ruwan inabi da bai riga ya tashi ba. Inda ba a san inabi a yanki ku ba to a yi amfani da kalman da kowa ya sani na ruwan 'ya'yan itace.

tsofaffin salkuna

Wannan na nufin salkunan da aka yi amfani da su sau da dama.

salkuna

Waɗanan jakuna ne da aka yi da fatan dabba. Ana iya kiran su "jakunan inabi" ko "jakunan fata."

ruwan inabi zai fasa fatan

Sabuwar inabi na buduwa a sa'ad da yake tashiwa, saboda da haka zai sa tsohon salkunan fata ta yage.

za a rasa

"zai ɓaci"

sabon salkuna

"sabon salkuna" ko "sabuwar jakunan fata." Wannan na nufin salkunan fatan da ba taba amfani da ita ba.

Mark 2:23

sai almajiransa su ka fara zagar kan hatsi ... yin abin da bai dace a yi ranar Asabar

zagar hatsi cikin gonakin wasu, kuma cin wannan ba a duban ta kamar sata. Tambayar ita ce ko daidai be bisa ga doka a yi wannan ranar Asabar.

zagar kan hatsi

Almajiran na zagar kan hatsi don su ci sabar, ko kwayar da ke cikin su. Ana iya sa wannan cikin kalma don nuna ma'anar gabaki ɗaya. AT: "zagar hatsi suna kuma cin kwayar"

kan hatsi

"kan" saman tsiren alkama wanda ke kamar ciyawa mai tsayi. Kan na rike hatsi ko iri tsiren da ta balaga.

Duba, don me suke yin abin da bai dace a yi ranar Asabar ba?

Farisiyawa sun yi wa Yesu tambaya don su kayar da shi. Ana iya juya wannan kamar magana. AT: "Duba! Su na karya dokar Yahudawa game da ranar Asabar."

Dubi

"Duba wannan" ko "Kassa kunne." Wannan kalma ne da an yi amfani da shi don kama hankalin wani don a nuna musu wani abu. In akwai wata kalm a harshen ku da ake amfani da ita don a jawo hankalin mutu, to ana iya amfani da ita anan.

Mark 2:25

Ba ku karanta ba abinda Dauda ... waɗanda ke tare da shi?

Yesu ya yi wannan tambayar don ya tunashe malaman attauran da Farisiyawa wani abin da Dauda ya yi a ranar Asabar.Tambayar ta yi dogo sosai, don haka ana iya raba shi zuwa jimla biyu.

Ba ku karanta ba abinda Dauda ya yi sa'adda yake jin yunwa, shi da mutanen da ke tare da shi? Yadda ya ... shi?"

Ana iya faɗin wannan kamar umurni. AT: "Ku Tuna abin da kin karanta game da abin da Dauda ... shi."

karanta abin da Dauda

Yesu na nufin karanta game da Dauda cikin Tsohon Alkawari. Wannan ana iya juya shi ta wurin nuna ainihin zancen a fili. AT: "karanta cikin nassosin abin da Dauda"

Yadda ya shiga gidan Allah ... waɗanda ke tare da shi.?

A nan iya bayana wannan a matsayin furuci dabam da aya 25. AT: "Ya shiga gida Allah ... waɗanda ke tare da shi."

yadda ya shiga

Kalman "ya" na nufin Dauda.

gurasa da ke ta

Wannan na nufin gurasa shabiyun wanda aka ajiye kan taburin zinariya wanda ke cikin alfarwa ko ginin haikali, hadaya ga Allah lokacin Tsohuwar Alkawari.

Mark 2:27

Ai Asabar domin mutum aka yi

Yesu ya bayana a fili dalilin da Allah ya yi Asabar. AT: "Allah ya yi Asabar don mutum"

mutum

"mutum" ko "mutane" ko kuwa "bukatun mutane." Wannan kalma na nufin mazaje da mataye dukka.

ba mutum domin Asabar ba

Kalmomin nan "aka yi" an fahimci ta daga maganar da ke a baya. Ana iya sake faɗin ta ana. AT: "ba a yi mutum domin Asabar ba" ko kuwa "Allah bai yi mutum domin Asabar ba"

Chapter 3

1 Sai kuma ya sake tafiya cikin Majami'a sai ga wani Mutum mai shanyayyen hannu. 2 Wadansu mutane suna kallonsa sosai, su gani ko zai warkar da shi a ranar Asabar. don su zarge shi. 3 Yesu ya ce wa mai shanyayyen hanun " Ka tashi ka tsaya a tsakiyar kowa." 4 Sai ya ce wa mutane, "Ya dace a yi abu mai kyau aranar Asabar ko a yi mugunta; a ceci rai, ko a yi kisa? "Amma suka yi shiru. 5 Sai ya dube su cikin fushi, yana bakin ciki da taurin zuciyar su, ya ce wa mutumin ka mikar da hanunka, sai ya mikar da hanunsa Yesu kuwa ya warkar da shi. 6 Sai Farisiyawa suka fita da sauri zuwa wurin mutanen Hirudus suka shirya yadda za su kashe shi. 7 Sai Yesu da almajiransa, suka tafi bakin teku. sai mutane dayawa suka bi shi, daga Galili da Yahudiya 8 Daga Urushalima da Edom gaba da Urdun da kewayan Taya da Sidon, da baban taro, ya ji abinda yake yi. suka zo wurinsa. 9 Ya tambayi almajiransa su shirya masa karamin jirgin ruwa domin yawan mutane, domin kada su murkushe shi. 10 Ya warkar da mutane da yawa, yadda duk wadanda suke da cuttutuka suna kokari su taba shi. 11 Duk sa'adda kazaman ruhohin suka ganshi, sai su durkusa a gabansa su yi ihu da karfi su ce, kai Dan Allah ne." 12 Ya umarce su da karfi kada su sa a san shi. 13 Ya hau saman dutsen, ya kira wadanda yake bukar su, su zo wurinsa. 14 Ya zabi guda goma sha biyu (ya kira su manzanni). Wadanda zasu kasance tare da shi, ya kuma aike su, su yi wa, azi, 15 Ya kuma basu Ikon fitar da aljanu. 16 Ya zabi guda goma sha biyu wato Saminu kuma yaba shi suna Bitrus. 17 Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan-uwan Yakubu wanda ya basu sunan Buwanarjis watau 'ya'yan tsawa, 18 da Andarawus da Filibus da Bartalamawus da Matta da Toma da Yakubu dan Halfa, da Taddawus da Saminu Ba-kananiye, 19 da Yahuza Iskariyoti wanda zai bashe shi. 20 Sa'adda ya shiga gida, Taron kuwa ya sake haduwa, har ya hana su cin abinci, 21 Da iyalansa suka ji haka, sai suka fito sun kamo shi, saboda sun ce, "Ai, baya cikin hankalinsa " 22 Marubutan da suka zo daga Urushalima suka ce "Ai Ba'alzabuba ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu." 23 Yesu ya kirawo su wurinsa ya ce da su cikin misalai, "Yaya shaidan zai iya fitar da shaidan? 24 idan mulki ya rabu gida biyu ba zai tsayawa ba. 25 Haka in gida ya rabu kashi biyu, gaba da kansa bai zai tsaya ba. 26 Shaidan kuma in ya tayar wa kansa ya rabu, ba zai iya tsayawa ba, gama karshen sa ya zo kenan. 27 Amma ba mai iya shiga gidan kakkarfan mutum ya kwace kayansa, ba tare da ya fara daure kakkarfan mutumin ba, sa'an nan kuma ya kwashe kayan gidansa. 28 Hakika, ina gaya maku, dukan zunuban da mutane suka yi za a gafarta masu, da kowane irin sabon da suka furta, 29 amma fa duk wanda yayi sabon Ruhun Mai Tsarki baza a gafarta masa ba ko kadan, ya zama mai zunubi har abada." 30 "Yesu ya fadi wadannan abubuwa domin suna cewa yana da ba kazamin ruhu," 31 Sa'an nan uwatasa, da "Yan'uwansa suka zo suna tsaye a waje. sai suka aika masa, suna kuma umurtar sa ya zo. 32 Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka yi magana da shi da cewa, ga uwarka da yan-uwanka suna nan a waje, suna nemanka." 33 Ya amsa masu, "Dacewa su wanene uwa-ta da "yan'uwa na?" 34 Sai ya waiwayi wadanda suke zaune kewaye da shi, yace, "Ga uwa-ta da yan-uwana anan! 35 Gama duk wanda ke yin abin da Allah yake so, shine dan'uwana da yar, uwata, da kuma uwa-ta."

Mark 3:1

Mahaɗin Zance:

Yesu ya wakar da wani mutum ranar Asabar a cikin majami'a ya kuma nuna yadda ya ji game da abin da Farisiyawa sun yi da umurni game da Asabar. Farisiyawan da mutanen Hirudus su fara shirin yadda za su kashe Yesu.

wani mutum mai shanyayyen hannu

"wani mutum wanda gurgu ne a hannu"

Waɗansu mutane suna kallonsa sosai, su gani ko zai warkar da shi

"Wasu mutane na kallonsa Yesu sosai, su gani ko zai warkar da mutumin wanda ke da shanyayyen hannu"

Wasu mutane

Wasu Farisiyawa." Nan gaba, cikin [Markus: 3:6] waɗannan mutanen an gane su Farisiyawa ne.

don su zarge shi

Ida Yesu ya warkar da mutumin a ranar, Farisiyawan za su zarge shi cewa ya karya doka ta wurin yin aiki ranar Asabar. AT: "domin su iya zarginsa cewa bai yi daidai ba" ko "domin su iya zarginsa cewa ya karya dokan"

Mark 3:3

a tsakiyar kowa

"a tsakiyar wannan taron jama'a"

Ya dace a yi abu mai kyau aranar Asabar ... ko a yi kisa?

Yesu ya faɗi wannan domin ya kalubalance su. Ya na so su amince cewa ya halatta a warkar da mutane ranar Asabar.

a yi abu mai kyau aranar Asabar ko a yi mugunta ... a ceci rai, ko a yi kisa

Waɗannan magana biyun suna da ma'ana kusan iri ɗaya, sai dai na biyun matsananci ne sosai.

a cece rai ko a yi kisa

Mai yiwuwa zai yi taimako in an nanata "ya halatta" kamar ita ce tambayar da Yesu ya yi kuma a wata hanya. AT: "ya halatta a cece rai ko a yi kisa"

rai

Wannan na nufi rai na wannan jiki. Ya na kuma nufin mutum. AT: "wani daga mutuwa" ko "ran wani"

Amma suka yi shiru

"Amma sun ki su amsa masa"

Mark 3:5

Ya dube kewaye

"Yesu ya dube kewaye"

ya na baƙin ciki

"ya yi fushi sosai"

da taurin zuciyar su

Wannan ya bayyana yadda Farisiyawa ba sa shirye su ji tausayin mutum mai shanyayyen hannu da tausayi. AT: "domin ba sa shirye su ji tausayin mutumin"

miƙar da hannunka

"Mika hannunka"

hannunsa kuwa ya koma lafiyayye

AT: "Yesu ya komar masa da hannunsa lafiyayye" ko "Yesu ya sa hannunsa ya zama daidai yadda yake a dă"

fara shirya măkirci

"fara yin dabara"

mutanen Hirudus

Wannan suna ne na yau da kullum na wata kungiyan siyasa da ke goyon bayan Hirudus Antibas.

yadda za su kashe shi

"yadda za su kashe Yesu"

Mark 3:7

takun

Wannan na nufin Tekun Galili.

Idumiya

Wannan yankin ne wanda a baya an san ta da suna Edom, wanda ya kunshi rabin lardin kudacin Yahudiya.

abubuwa da yake yi

Wannan na nufin al'ajiban da Yesu ke yi. AT: "babbar abin al'ajiban da Yesu ke yi"

zo wurinsa

"zo wurin da Yesu yake"

Mark 3:9

Muhimman Bayani:

Aya 9 ta faɗi abin da Yesu ya ce wa almajiransa su yi saboda gaggaruman taron mutane da ke kewaye da shi. Aya 10 ta faɗi dalilin da ya sa gagaruman tarons suna kewaye da Yesu. Bayanin da ke a waɗannan ayoyi sake kasa su don a bayana labarun daidai yadda sun faru, kamar yadda yake cikin UDB.

Ya ce wa almajiransa su shirya masa karamin jirgin ruwa ... kada su murkushe shi

A sa'ad da gaggaruman taron na kara matsowa kusa da Yesu, yana cikin hatsarin da za su iya murkushe shi. Ba da saninsu za su murkushe shi ba. Amma domin dai kawai akwai mutane da yawa.

Ya ce wa almajiransa

"Yesu ya gaya wa almajiransa"

Ya warkar da mutane da yawa, yadda duk waɗanda ... taba shi

Wannan ta gaya mana dalilin da ya sa mutane masu yawa suna kewaye da Yesu har sai da ya yi tunani cewa za su murkushe shi. AT: "Gama, saboda Yesu ya warkar da mutane da yawa, duk waɗanda ... taba shi"

Gama ya warkar da ... da yawa

Kalman nan "yawa" na nufin gaggaruman mutanen da Yesu ya warkar da su. AT: "Gama ya wakr da mutane da yawa"

duk waɗanda suke da cuta suna koƙarin su zo wurin sa don su taɓa shi

Sun yi wannan ne saboda sun gaskanta cewa in sun taba Yesu za su warke. A nan iya bayana wannan a fili. AT: " dukkan mutane marasa lafiya sun nace zuwa suna kokarin sun taɓa shi domin su warke"

Mark 3:11

gan shi

"gan Yesu"

suka fãɗi a kasa ... yi ihu da ƙarfi, suka ce

A nan "su" na nufin aljannun. Sune suke sa mutanen da suka shige su su yi waɗannan abubuwa. Anan iya bayana wannan a fili. AT: "Sun sa mutanen da suka shige su su fãɗi kasa a gaban shi, su yi kuka a gare shi"

sun fãɗi a gaban shi

Aljannun ba su fãɗi a gaban Yesu saboda suna kaunar shi ba ko suna so su yi masa sujada ba. Sun fãɗi a gabansa domin sun ji tsoronsa ne.

Kai Ɗan Allah ne

Yesu yana da iko a kan aljannun domin shi "Ɗan Allah" ne.

Ɗan Allah

Wannan laƙani ne mai muhimmanci na Yesu.

Ya umurcesu kwarai da gaske

"Yesu ya umurce aljannun"

kada su bayana shi

"kada su bayana ko shi wanene"

Mark 3:13

don su kasance tare da shi, ya kuma aike su, su yi wa, azi, sakon

"don su kasance tare da shi, shi kuma zai aike su, su yi wa'azi sakon"

Saminu, wanda yaba shi suna Bitrus

Marubucin ya fara lisafta sunayen manzane goma sha biyun. Saminu shi ne na farko da aka ambata.

Mark 3:17

wanda ya ba shi

Maganan nan "wanda" na nufin Yakubu ɗan Zabadi da ɗan'uwansa Yahaya.

suna Buwanarjis, wato 'ya'yan tsawa

Yesu ya kira su da wannan suna domin suna kamar tsawa ne. AT: "suna Buwanarjis, wanda ke nufin mutane da ke kamar tsawa" ko "suna Buwarnarjis, wanda ke nufin mutanen tsawa"

Yahuza

Wannan sunan na miji ne.

wanda zai bãshe shi

"wanda zai bãshe da Yesu" Kalman nan "wanda" na nufin Yahuda Iskariyoti.

Mark 3:20

Sai ya tafi gida

"Sai Yesu ya tafi gidan da yake zama."

har ya hana su cin gurasa

Kalman nan "gurasa" na wakilcin abinci. AT: "Yesu da almajiransa ba su iya cin abinci ba ko kaɗan" ko "ba su iya cin komai ba"

sun fito don su kama shi

'Yan iyalinsa sun shiga cikin gidan don su kama shi su sha shi dole ya je gida tare da su.

don ya ce

Ma'ana mai yiwuwa na kalman nan "su" na kamar haka 1) danginsa ko 2) wasu mutane da cikin taron.

ba ya cikin hankalinsa

iyalin Yesu sun yi amfani da wannan karin magana don su bayana yadda suke tunani yake yi. AT: "haukace"

ta wurin sarkin aljannu yake fitar da aljannu

"Ta wurin ikon Ba'alzabul, wanda shine sarkin aljannu, Yesu ke fid da aljannu"

Mark 3:23

Yesu ya kira su wurinsa

"Yesu ya kira mutanen wurinsa"

Yaya shaiɗan zai iya fitar da shaiɗan?

Yesu ya yi wannan tambaya don ya amsa maganar malaman attaura da cewa yana fid da aljan ta wurin ikon Ba'alzabul. AT: "Shaiɗan ba zai iya fid da kansa ba!" ko "Shaiɗan baya gãba da mugayen ruhohinsa!"

Idan mulki ya rabu gida biyu

Kalman nan "mulkin" na nufin mutane da ke wannan mulkin. AT: "Idan mutanen da ke zama cikin mulki sun rabu suna gãba da juna"

bai zai tsaya ba

Wannan na nufin cewa mutane ba za su haɗu kuma ba kuma za su faɗi. AT: "ba zai iya jimrewa ba" ko "zai faɗi"

gida

Wannan na nufin mutane da ke zama a gidan. AT: "iyali"

Mark 3:26

Idan Shaiɗan kuma in ya tayar wa kansa ya rabu

Kalman nan "kansa" na nufin Shaiɗan, yana kuma nufin mugayen ruhohi. AT: "Idan Shaiɗan da mugayen ruhohinsa suna faɗa da juna." ko "Idan Shaiɗan da mugayen ruhohinsa na gãba da juna kuma sun rabu"

ba zai iya tsayawa ba

Wannan na nufin cewa zai fãɗi kuma ba zai jimre ba. AT: "ba zai haɗu ba" ko "ba zai jima ba kuma ta zo ga ƙarshe kenan" ko "zai fãɗi kuma ta zo ga ƙarshe kenan"

kwashe

a sata kayan mutum da kuma mallaka

Mark 3:28

Hakika ina gaya maku

Wannan na nuna cewa maganar da za a iya mai muhimmanci ne kuma gaskiya ne.

'ya'yan mutane

"waɗanda mutum ne ya haifa." Wannan na nanata cewa 'yan adam ne. AT: "mutane"

magana

magana

suna cewa

"mutane suna cewa"

na da baƙin aljan

Wannan karin magana da ke nufin aljan ya yi mulkin wani. AT: "na da baƙin aljani"

Mark 3:31

Sai uwa tasa da 'yan'uwansa suka zo

"Sai uwar Yesu da 'yan'uwansa suka zo"

Sun aika a kira shi, suna kuma umurata ya zo

"Sun aiki wani a ciki ya gaya masa da cewa suna a waje kuma suna so ya zo wurin su"

na neman ka

"na tambaya game da kai"

Mark 3:33

wanene uwa-ta da 'yan'uwa na?

Yesu ya yi amfani da wannan tambaya don ya koya wa mutanen. AT: "Zan gaya maki ko wanene uwata da 'yan'uwana"

Duk wanda ke ... wannan mutum shine

"waɗanda ke aikata ... sune"

shine ɗan'uwana da yar, uwata

Wannan na nufin almajirans Yesu sune iyalinsa na ruhaniya. Wannan ya fi muhimmanci fiye da zama cikin iyalinsa na jiki. AT: "wannan mutum shi kamar ɗan'uwana, da 'yar'uwata, ko uwa a gare ni"

Chapter 4

1 Ya kuma fara koyarwa a bakin teku. Akwai babban taro kewaye da shi, sai ya shiga cikin jirgin ruwa a cikin tekun, ya kuwa zauna. Duk taron kuwa na kan tudu a bakin tekun. 2 Ya koya masu abubuwa da yawa da misalai, a cikin koyawarsa ya ce masu, 3 "ku saurara! wani mai shuka ya tafi shuka. 4 Yana cikin yafa iri, sai wadansu iri suka fadi a kan hanya, tsuntsaye kuma suka zo suka tsince su. 5 Wadansu kuma suka fadi a kan dutse inda ba kasa dayawa. Nan da nan kuwa suka tsiro saboda rashin zurfin kasa. 6 Da rana fa ta daga, sai suka yankwane da yake ba su da saiwa sosai, sai suka bushe. 7 Wadansu kuma suka fadi cikin kayayuwa su ka yi girma sai kayayuwan suka shake su, ba su yi tsaba ba. 8 Wadansu kuma suka fadi a kasa mai kyau, suka yi yabanya, suka yi tsaba, suka yi girma, wadansu ribi talattin wadansu sittin, wadansu kuma dari". 9 Sai ya ce, Duk mai kunnen ji, ya ji," 10 Sa'adda Yesu yake shi kadai, wadanda suke kusa dashi tare da sha biyun suka tambaye shi ma'anar misalan. 11 Sai ya ce masu, "ku an yardar maku, ku san asirin mulkin Allah, amma ga wadanda ba su cikinku, komai sai a cikin Misalai, 12 don gani da ido sun gani, amma ba su gane ba. ji kuma, sun ji, amma ba su fahimta ba, don kada su juyo a gafarta masu," 13 Ya ce masu, "Ashe, ba ku fahimci wannan misalin ba? yaushe za ku fahimci sauran? 14 Mai shukan nan fa maganar Allah yake shukawa. 15 Wadanda suka fadi a hanyar kuwa, su ne kwatancin wadanda. a aka shuka mganar a zuciyarsu, Da suka ji, nan da nan sai shaidan ya zo ya dauke Maganar da aka shuka a zuciyarsu. 16 Haka kuma wadanda aka shuka a wuri mai duwatsu, sune wadanda da zarar sun ji Maganar sai su karba da farin ciki. 17 Su kuwa basu da tushe, ba su da karfi, idan kunci ko tsanani ya zo saboda kalmar, nan da nan sai su yi tuntube. 18 Wadansu kuma su ne kwatacin wadanda suka fadi cikin kayayuwa, sune wadanda suka ji Maganar, 19 amma abubuwan duniya, da rudin dukiya da kuma kwadayin wadansu abubuwa, sukan shiga su shake Maganar, har ta zama marar amfani. 20 Wadanda aka shuka a kasa mai kyau kuwa, sune kwatancin wadanda suke jin Maganar, su karba, su kuma yin amfani da ita wadansu ribi talatin, wadansu sittin, wadansu dari." 21 ya ce masu, "Shin, ana kawo fitila a cikin gida don a rufe ta da kwando ko a ajiye ta a karkashin gado? ku kan kawo ta ne don ku dora ta a kan madorinta. 22 Ba abin da yake boye, da baza a sani ba ko kuma ba abinda ke asirce da bazaya bayyana a fili ba. 23 Bari mai kunnen ji, ya ji!" 24 Sai ya ce masu, ku mai da hankali a kan abin da kuka ji, Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a kara maka. 25 Domin mai abu akan karawa, marar abu kuma za a karba daga wurinsa a kuma karawa mai shi." 26 Sai ya ce, "Mulkin Allah kamar mutum yake mai yafa iri a kasa. 27 A kwana a tashi har irin ya tsiro, ya girma bai kuwa san ta yaya aka yi ba. 28 Kasa da kanta, takan ba da amfani, tsiro shine ne na farko, 29 Sai kai, sa'anan sai kwaya mai kwari. Sa, adda amfani ya nuna, sai ya sa lauje ya yanke nan da nan, wato kaka ta yi kenan." 30 Ya kuma ce, "Da me za mu kwatanta Mulki Allah? ko kuwa da wane misali za mu misalta shi? 31 Kamar kwayar zarra yake wadda, in an shuka ta, ko da yake ita ce mafi kankanta cikin kwayoyi a duniya. 32 Duk da haka in an shuka ta, sai ta yi girma fiye da duk sauran ita-tuwan da ke a jeji tayi manyan rassa, har tsuntsaye su iya yin sheka arassanta." 33 Da misalai da yawa, irin wadannan ya yi masu Magana, dadai gwargwadon ganewarsu, 34 ba ya fada masu kome sai da misali, amma a kebe, yakan bayyana wa almajiransa dukan abu. 35 A ranan nan da yama ta yi yace masu "Mu haye wancan ketaren." 36 Sai suka bar taron, suka tafi tare da shi acikin cikin jirgin. wadansu jirage kuma na tare da shi. 37 Sai babban hadari da iska mai karfi ya taso, rakuman ruwa kuma na ta girgizawa cikin jirgin, har jirgin ya cika. 38 Yesu kuwa na daga karshen bayan jirgin a kan kujera, yana barci, sai suka tashe shi, suka ce masa "Malam za mu hallaka ba ka kula ba?" 39 Sai ya farka, ya tsawata wa Iskar. Ya kuma ce wa ruwan tekun, "Ka natsu! ka yi shiru!" Sai Iskar ta kwanta, wurin duk ya yi shiru. 40 Ya ce masu, "Don me kuka firgita haka? Har yanzu baku da bangaskiya ne?" 41 Sai suka tsorata kwarai suka ce wa juna, "wanene wannan kuma, wanda har Iska da teku ma suke yi masa biyayya?"

Mark 4:1

Mahaɗin Zance:

A sa'ada Yesu ya koya masu daga cikin jirgin ruwa a bakin teku, ya basu misalin kasa.

tekun

Wannan Tekun Galili ne.

Mark 4:3

ku kassa kunne! wani manomi

"Ku saurara! Wani manomi"

iri ... waɗansu iri ... tsince su ...Waɗansu kuma ... inda ba kasa dayawa ...suka tsiro ... rashin zurfin kasa

An yia maganar dukkan irin da manomin ya shuka kamar iri guda ɗaya ne. "irin ... waɗansu ... tsince su ... Wasu iri ... ba su sami ... suka tsiro ... ba su sami"

Yana cikin yafa iri, sai waɗansu iri suka faɗi a kan hanya

"A sa'ad da ya wasa iri a ƙasa." A al'adu daban-dabam mutane suna da hanyoyin shukin iri daban-dabam. A wannan misalin an shuka iri ta wurin wasa wa a ginar da aka shirya.

ta tsiro

"irin da aka shuka a gonar da ke da duwasu sun fara girma da sauri"

ƙasa

Wannan na nufin datti da ke kasa wanda za a iya shuka iri.

Mark 4:6

sai suka yankwane

Wannan na nufin shukin da basu kosa ba. AT: "ta yankwane shukin da basu kosa ba"

da yake ba su da saiwa sosai, sai suka bushe

"domin shuki ba ta da saiwa sosai, sai suka bushe"

Waɗansu iri ... suka shake su ... ba su bada amfani

A nan an yi magana game da duk irin da manomin ya shuka kamar iri guda ɗaya ne. Dubi yadda ka juya wannan cikin [Markus 4:3]. "Wasu iri ... suka shake su ... ba su bada amfani ba"

Mark 4:8

riɓi talattin wadansu sittin, wadansu kuma ɗari

Yawan tsaban da shukin ta bayar an kwatanta shi da iri guda da ya yi girma. AT: "Waɗansu shukin sun bada amfani fiye da irin da mutumin ya shuka sau talatin, waɗansu iiri sun bada tsaba sau sittin, waɗansu kuma sun bada amfanin tsaba sau dari"

talatin ... sittin ... ɗari

"30 ... 60 ... 100." Za a iya rubuta waɗannan cikin adadi.

Duk ma kunnen ji

Wannan wata hanya ce da ake nufin duk wanda ke wurin wanda kuma na jin abin da Yesu yake faɗa. AT: "Kowa wanda zai iya ji na" ko "Duk wanda zai iya ji na"

yă ji

A nan kalman nan "ji" na nufin saurara. AT: "yă saurara da kyau" ko "lalle ne ya suarari abin da ina faɗa da kyau"

Mark 4:10

Sa'adda Yesu yake shi kadai

Ba wai wannan na nufin cewa Yesu yana nan gabaɗaya shi kaɗai ba; maimakon haka, abin nufi shine, lokacin da taron sun tafi, Yesu kuma na tare da sha biyun da wasu masubinsa.

an ba ku

AT: "Allah ya ba ku" ko "Na ba ku"

waɗanda ba su cikinku

"amma waɗanda ba sa cikin ku." Wannan na nufin dukkan mutanen da ba sa cikin sha-biyun ko sauran masubi Yesu na kusa.

komai sai a cikin Misalai

Ana iya faɗin cewa Yesu ya ba wa mutanen misalai. AT: "Kowane abin da na faɗa, na yi shi cikin misali"

don gani da ido ... sun ji

Ana ɗaukan cewa Yesu yana magana game da mutane suna ganin abubuwan da ya nuna masu suna kuma jin abin da ya gaya masu. AT: "sa'ad da suna ganin abin da nake yi ... sa'ad da suna jin abin da nake faɗa

sun gani, amma ba su gane ba

Yesu yana magana game da fahimtar mutane ga abin da suka gani kamar a zahiri suna gani ne. AT: "sun gani ba su kuma gane ba"

za su juyo

"juyo wurin Allah." Anan "juyo" na nufin "tuba," AT: "za su tuba"

Mark 4:13

Sa'an nan ya ce masu

"Sai Yesu ya ce wa almajiransa"

Ashe, ba ku fahimci wannan misalin ba? Ta yaya za ku fahimci sauran?

Yesu ya yi amfani da waɗannan tambayoyi don ya nuna fushin sa cewa almajiransa ba su fahimci misalinsa ba. AT: "Idan ba ku iya fahimtar wannan misalin ba, yi tunani game da zai yi maku wahala ku fahimci sauran misalen."

Manomin da ya shuka irinsa

"Manomi wanda ya shuka irinsa na wakilcin"

Mai shukan nan fa maganar

"maganar" na nufin saƙon Allah. Bada sakon na nufin koyar da ita. AT: "wanda yake koyawa mutane saƙon Allah"

Waɗannan sune suka fadi a hanyar

"wasu mutane suna kamar iri da suka faɗi a gefen hanya" ko "wasu mutane suna kamar hanyan da wasu iri suka faɗi"

hanya

"tafarki"

da suka ji ta

A nan "ta" na nufin "maganan" ko "saƙon Allah"

Mark 4:16

sune waɗanda

"wasu kuma suna kamar irin." Yesu ya fara bayana yadda wasu mutane suna kamar iri da ta faɗi a kan ƙasa ma duwatsu.

ba su da karfi

Wannan kwatanci ne da shuki da jijiyoyin sa ba su yi zurfi ba. Wannan na nufin cewa mutanen sun yi murna sa'ada suka karɓi magana, amma basu dukufa ga maganar ba. AT: "suna kuma kamar shuki da ba shi da jijiya"

ba jijiya

Wannan na nanata rashin zurfin jijiyoyin.

jimre

A wannan misali, "jimre" na nufin "bada gaskiya." AT: "cigaba cikin bangaskiyarsu"

kunci ko tsanani ya zo saboda kalmar

Zai zama da taimako in an bayana cewa kunci na zuwa domin mutane sun bada gaskiya ga saƙon Allah. AT: "kunci ko tsanani na zuwa domin sun bada gaskiya ga saƙon Allah"

sun yi tuntuɓe

A wannan misalin, "tuntuɓe" na nufin "sun daina bada gaskiya ba saƙon Allah"

Mark 4:18

Waɗansu kuma su ne kwatacin waɗanda suka fadi cikin ƙaya

Yesu ya fara bayana yadda wasu mutane suke kamar iri da ya faɗi cikin ƙaya. AT: "wasu mutane kuma suna kamar irin da aka shuka cikin ƙaya"

amma abubuwan duniya

"damuwoyin wannan rayuwa" ko "damuwan rayuwan yanzu"

da rudin dukiya

"sha'awace sha'awacen dukiya"

suka shiga su shake Maganar

Sa'anda Yesu ya cigaba da magana game da mutane wanda suke kamar irin da ta fadi cikin ƙaya, ya bayana ainihin mecece sha'awace sha'awace da damuwo'in ke yi wa kalmar a rayuwansu. AT: "sun shiga sun shake saƙon Allah cikin rayuwar su kamar yadda ƙaya ke shake shuki"

ba ta bada amfanin gona ba

"maganan ba ta bada amfani gona a cikinsu ba"

Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa

Yesu ya fara bayana cewa wasu mutanen suna kamar iri da aka shuka a ƙasa mai kyau. AT: "kamar iri da aka shuka a ƙasa mai kyau"

talatin, wadansu sittin, wadansu dari fiye da abin da aka shuka

Wannan na nufin tsaba da aka shukin ta bada amfanin ta. AT: " wasu sun yi tsaba talatin, wasu tsaba sittin, wasu kuma tsaba ɗari" ko "wasu sun bada tsaba fiye da abinda aka shuka sau 30, wasu sun bada tsaba fiye da abin da aka shuka sau 60, wasu kuma sun bada tsaba fiye da abin da aka shuka sau 100"

Mark 4:21

Yesu ya ce masu

"Yesu ya cewa taron"

Shin, ana kawo fitila a cikin gida don a rufe ta da kwando ko a ajiye ta a ƙarƙashin gado?

A nan iya rubuta wannan tambaya kamar ba tambaya ba. AT: "Haƙika ba a kawo fitila cikin gida don a rufe ta da kwando, ko a ajiye ta a ƙarƙashin gado!"

Ba abin da yake ɓoye, da baza a sani ba ... da bazaya bayyana a fili ba

AT: "Gama duka abin da yake a ɓoye za a bayyana shi, kuma kowane abin da ke a asirce za a bayyana a fili"

ba abin da ke a ɓoye ... ba abin da ke a asirce

"babu wani abin da ke a ɓoye ... babu wani abin da ke a asirce" Maganganu biyun nan na nufin abu ɗaya. Yesu yana nanata cewa kowane abu da ke a asirce za ta zama sanannen.

Duk mai kunnen ji, ya ji

Dubi yadda ka juya wannan cikin [Markus 4:9]

Mark 4:24

Ya ce masu

"Yesu ya ce wa taron"

da abin da ka auna

Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) Yesu yana magana game auwu da kuma bayarwa a yalwace ga wasu ko 2) wannan na nufin Yesu yana magana game da "fahimta" sai ka ce "auwu."

za a auna maka, za a kuma kara maka

AT: "Allah zai auna maka, zai kuma kara maka"

ga shi za a kara ... ko abin da yake da shi ma za a karɓe

AT: "Allah zai kara masa ... Allah zai karɓe" ko "Allah zai kara masa ...Allah zai karɓe daga wurinsa"

Mark 4:26

kamar mutumin da ya shika irinsa

Yesu ya kwatanta mulkin Allah da manomi wand aya shika irinsa. AT: "kamar manomin da ya shuka irinsa"

A kwana a tashi

Wannan abu ne da mutumin ya saba yi. AT: "Yana barci kowane dare, yana kuma tashiwa kowane rana" ko "Yana barci kowane dare ya kuma tashi kashegari"

tashi da rana

"ya tashi da rana" ko "ya fara aiki da rana"

kodashike bai san ya aka yi ba

"kodashike mutumin bai san ya aka yi irin ya toho ya kuma yi girma ba"

ganye

kara ko toho

kai

kan kara ko bangare shuke da ke rike 'ya'yan

sai ya sa lauje ya yanke nan da nan

A nan "lauje" na nufin manomin ko mutanen da manomin ya aike su girbin hatsin. AT: "nan da nan ya tafi gonar da lauje do ya yi girbin hatsi" ko "nan da nan ya aiki mutane da lauje zuwa cikin gonar su yi girbin hatsin"

lauje

wani wuka da ke a lanƙwashe ko wani kugiya mai kaifi da ana amfani da ita a girbe hatsi

domin lokacin girbi ta yi

A nan maganan nan "ta yi" na nufin hatsin ta yi don girbi. AT: "domin hatsi ta yi domin girbi"

Mark 4:30

Da me za mu kwatanta Mulki Allah? ko kuwa da wane misali za mu misalta shi?

Yesu ya yi wannan tambaya domin masu karatun su yi tunani game macece mulkin Allah. AT: "Da wannan misalin zan iya kwatanta mulkin sama."

wadda, in an shuka

AT: "sa'ad da wani ya shuka ta"

tayi manyan rassa

An bayana bishiyan mustad kamar an sa rassan tayi manya. AT: "da manyan rassa"

Mark 4:33

ya yi masu Magana

"Magana" anan na nufin "saƙon Allah." Kalman nan "su" na nufin taron. AT: "ya koyawa masu sakon Allah"

daidai gwargwadon ganewarsu

"kuma ida sun iya fahimtar wasu, sai ya cigaba da gaya masu"

sa'ad da ya zama shi kaɗai

Wannan na nufin cewa ba ya tare da taron, amma almajiransa suna tare da shi.

yakan bayana wa almajiransa kowane abu

A nan "kowane abu" daɗaɗawa ne. Ya bayana masu duk misalinsa. AT: "Ya bayana masu duk misalinsa"

Mark 4:35

wancan ƙetaren

"wancan ƙetaren Tekun Galili" ko "wancan ƙetaren takun"

Sai babban hadari mai iska ya taso

A nan "taso" na nufin "fara." AT: "sai babban hadari mai iska ya fara"

har jirgin ya kusan cika da ruwa.

Zai yi taimako in an bayana cewa jirgin yana cika da ruwa. AT: "jirgin na hatsarin cika da ruwa"

Mark 4:38

Yesu kansa

A nan "kansa" na nanata cewa Yesu shi kaɗai ya kasan jirgin. AT: "Yesu kansa na nan shi kaɗai"

kasan jirgin

Wannan ita ce bayan jirgin. "bayan jirgin"

sun tashe shi

Kalman nan "su" na nufin almajiransa. Kwatanta zance dake kusan ɗaya da wanda ke a aya 39, "Ya tashi." "Ya" na nufin Yesu.

ba ka damu ko mun kusan mutuwa ba?

Almajiran sun yi wannan tambaya don su nuna soron su. A nan iya rubuta wannan tambaya a matsayin magana. AT: "ya kamata ka jawo hankalin ka ga abin da yake faruwa; mun kusa mu mutu dukkan mu!"

mun kusan mutuwa

Kalman nan "mu" na nufin almajiran da Yesu kansa.

Natsu! Ka yia shiru!

Waɗannan maganganu biyun suna nan kusan iri ɗaya ne kuma suna nanata abin da Yesu ya son iska da tekun su yi.

Iskar ta kwanta

"an sami matuƙar kwantawar iska a tekun"

Mark 4:40

Don me kuka firgita? Har yanzu baku da bangaskiya ne?

Yesu ya yi waɗannan tambayoyi don ya jawo hankalin almajiransa su duba dalilin da ya sa suka firgita a sa'ad da yake tare da su. AT: "Bai kamata ku ji tsoro ba. kuna bukatan ku sami bangaskiya sosai."

wanene wannan kuma, wanda har Iska da teku ma suke yi masa biyayya?

Almajiran sun yi wannan tamaya cikin mamaki saboda abin da Yesu ya yi. AT: "Wannan mutum ba kamar sauran mutane bane; har iska da teku sun yi masa biyayya!"

Chapter 5

1 Da su ka zo daya ketaren tekun, wanda ya ke cikin yankin Garasinawa. 2 Sa'adda Yesu ya sauko daga cikin jirgin ruwan sai wani mutum mai aljanu ya fito daga cikin kaburbura ya tarbe shi. 3 Mutumin yana zama a cikin kaburbura. An daure shi da sarkoki da mari 4 An daure shi da sarkoki da mari sau da yawa, amma ya tsuntsunke sarkoki da marin. har ma ba wanda zai iya daure shi kuma. 5 Dare da rana a cikin kabarbarun da duwatsu mutumin ya na ihu ya na yaiyage jikinsa da duwatsu masu kaifi. 6 Sa'adda ya hango Yesu daga nesa, sai ya tarbi Yesu ya durkusa a gabansa. 7 Ya tada muryarsa da karfi ya ce, ina ruwa na da kai? Yesu Dan Allah Madaukaki Ina rokon ka da sunan Allah kada ka bani wahala, 8 Gama Yesu ya ce masa kai aljani ka fito daga cikinsa." 9 Ya tambaye shi, "Yaya sunanka? Ya ce suna na tari gama muna da yawa. 10 Ya yi ta rokonsa kada ya raba su da wannan yankin kasar. 11 Akwai babban garken aladu a wurin suna kiwo a gindin tsauni. 12 Sai suka roke shi ya bar su su shiga cikin wadannan aladun. 13 Shi kuma ya yardar masu. Aljanun suka fita suka shiga cikin aladun su kimanin dubu biyu. Aladun dubu biyu suka gangaro daga gindin tsaunin suka fada cikin ruwa. 14 Mutanen da ke kiwon aladun su ka shiga cikin gari da kewaye suka bada labarin abin da ya faru. Mutane da yawa suka je su ga abin da ya faru 15 Sai suka zo wurin Yesu suka ga mutumin mai aljanun a zaune, cikin hankalinsa, saye da tufafi, sai suka tsorata. 16 Wadanda suka zo su ka ga abin da ya faru da mutumin mai aljanun, suka je suka fada wa mutane abin da suka gani game da aladun. 17 Mutanen suka roke shi ya fita daga yankin kasarsu. 18 Shi mutumin da aljanu ke iko da shi, sa'adda ya ga Yesu zai shiga cikin jirgin ruwa ya tafi, ya roki Yesu da ya bi shi. 19 Amma Yesu bai yarda masa ba. Ya ce masa ka tafi gidanku, wurin mutanenka ka gaya ma su alherin da Ubangiji ya yi maka. 20 Mutumin ya shiga cikin Dikafolis yana shaidar babban abin da Yesu ya yi masa, dukansu suka cika da mamaki. 21 Sa'adda Yesu ya sake ketaren kogin zuwa daya gefen, acikin jirgin, sai taron jama'a suka keweye shi, a gefen tekun. 22 Sai wani daya daga cikin shugabannin Majami'a mai suna Yayirus, ya zo, wurinsa sa'adda ya ganshi ya durkusa a gabansa. 23 Ya yi ta rokonsa, yana cewa, "Diya ta ba ta da lafiya har ma ta kusa mutuwa. Ina rokonka mu je gida na ka dora ma ta hannu domin ta warke. ta rayu." 24 Sai ya tafi tare da shi, babban taro suka biyo shi har ma suna matse shi. 25 Akwai wata mace wadda ta ke zubar jini ta kai tsawon shekara goma sha biyu. 26 Ta sha wahala kwarai da gaske ta je wurin likitoci da yawa ta kashe kudi sosai, amma ba ta warke ba abin ma sai karuwa ya ke yi. 27 Ta ji labarin Yesu. Sai ta biyo bayansa yana tafiya cikin taro, ta taba habar rigarsa. 28 Domin ta ce "Idan dai na taba ko da habar rigarsa zan warke." 29 Da dai ta taba shi sai zubar jinin ta ta tsaya, ta ji a jikin ta ta warke, daga damuwarta. 30 Nan da nan, Yesu ya ji iko ya fita daga gare shi sai ya ce "wanene ya taba rigata?" 31 Almajiransa suka ce, "a cikin wannan taron mutane da yawa ka ce wanene ya taba ni?" 32 Amma Yesu ya waiga ya ga ko wanene ya taba shi. 33 Matar ta san abin da ya faru sai ta zo cikin tsoro da rawar jiki ta durkusa a gaban Yesu ta fada masa gaskiya. 34 Sai ya ce da ita, "Diya bangaskiyarki ta warkar da ke, ki tafi lafiya kin sami warkewa daga cutarki". 35 Sa'adda ya ke magana da ita sai ga mutane daga gidan shugaban majami'a suka ce "Diyarka ta mutu me ya sa za ka dami malam?" 36 Amma sa'adda Yesu ya ji abin da suka ce, sai ya ce da shugaban majami'ar, "kada ka ji tsoro ka ba da gaskiya kawai." 37 Bai bari kowa ya kasance tare da shi ba sai Bitrus da Yakubu da Yahaya dan'uwan Yakubu. 38 Suka zo gidan shugaban majami'ar ya ga mutane suna bakin ciki, suna kuka sosai. 39 Sa'adda ya shiga gidan ya ce da mutane "Me ya sa kuke damuwa da kuka?" Yarinyar ba ta mutu ba barci ta ke yi. 40 Sai su kayi masa dariya. Amma ya fitar da su waje su duka. Ya kira baban yarinyar da mamar ta da wadansu da ke tare da shi su ka shiga wurin da yarinyar ta ke. 41 Ya kama hannun yarinyar ya ce da ita "Tilatha koum" wato yarinya na ce ki tashi" 42 Nan da nan yarinyar ta tashi ta yi tafiya (gama shekarun ta sun kai goma sha biyu). Nan da nan mutanen suka yi mamaki kwarai da gaske. 43 Ya ummurce su da gaske kada kowa ya sani. Ya ce da su su ba ta abinci ta ci.

Mark 5:1

Mahaɗin Zance:

Bayan Yesu ya kwantar da iska, ya wakar da wani mutum da ke da aljannu, amma Garasinawan ba su yi murna domin ya yi warkarwa ba, saboda haka sun roƙe Yesu ya tafi.

sun zo

Kalman nan "Su" na nufin Yesu da Almajiransa.

tekun

Wannan na nufin Tekun Galili.

Garasinawa

Wannan suna na nufi mutanen da zama cikin Garasa.

mai baƙin aljan

Wannan karin magana ne da ke nufin cewa baƙin ajan na "mulki" ko "ya haukatar da shi". AT: "baƙin aljan na mulkinsa" ko "baƙin aljan ya haukatar da shi"

Mark 5:3

An ɗaure shi da sarkoki da mari sau da yawa

AT: "Mutane sun ɗaure shi da sarkoki sau da yawa"

sarkokin sa sun tsintsinke

AT: "ya tsintsinke sarkokinsa"

sarkoki

karafuna da mutan sukan kewa hannu da kafafun ɗan sarka su kuma haɗa shi da sarka da kuma wani abu da ba ya motsi don kada fursunan ya yi motsi

ba wanda zai iya ɗaure shi kuma

Mutumin na da ƙarfi har ma ba wanda zai iya ɗaure shi. AT: "Ya na da ƙarfi sosai har ma ba wanda ke da ƙarfin ɗaure shi"

ɗaure shi

"mulke shi"

Mark 5:5

ya na yaiyage jikinsa da duwatsu masu kaifi

Sa'ad da aljan ya mallake mutumin, so da dama aljan zai sa mutumin ya yi munanan abubuwa da zai hallakas da shi, wato abu kamar, yaiyanke kansa.

Sa'adda ya hango Yesu daga nesa

Da ganin Yesu, mai yiwuwa Yesu na koƙarin fitawa da jigin ruwa kenan.

rusuna

Wannan na nufin cewa ya durkusa a gaban Yesu don ya girmama ya kuma daraja shi, ba ya na masa sujada ba.

Mark 5:7

Muhimman Bayani:

Bayanin da ke waɗannan ayoyi biyun ana iya săke shirya shi don a iya ba da labarin daidai yadda ya faru, kamar yadda yake a UDB.

Ya tada murya

"Baƙin aljanin ya tada murya"

ina ruwa na da kai, Yesu Ɗan Allah Maɗaukaki?

Baƙin aljanin ya yi wannan tambayar don ya ji tsoro ne. AT: "Rabu da ni, Yesu, Ɗan Allah Maɗaukaki! Babu wata dalili da zai sa ka sami sabani da ni."

Yesu ... kada ka bani azăba

Yesu na da ikon ba wa baƙin aljanin azăba.

Ɗan Allah Maɗaukaki

Wannan lakani ne mai muhimmanci na Yesu.

Ina rokon ka da sunan Allah

A nan baƙin aljanin na ransuwa da Allah a sa'ada yana roƙo Yesu. Dubi yadda ake irin wannan roƙo a harshen ku. AT: "a gaban Allah ina roƙon ka" ko "na rantse da sunan Allah, ina roƙon ka"

Mark 5:9

Ya tambaye shi

"Sai Yesu ya tambaye baƙin ajan"

Ya amsa masa ya ce, "Sunana Tuli, don muna da yawa."

Ɗaya daga ciki aljanun na magana a maɗaɗɗin sauran. Ya yi magana game da su sai ka ce su rundunan, rundunar sojojin Romawa da ke kusan sojoji 6,000. AT: "Sai aljan ya ce masa, 'ka kira mu rundunan, domin dayawan mu muna cikin mutumin nan."

Mark 5:11

sun roke shi

"bakin aljanun sun roke Yesu"

ya bar su

Zai iya zama da taimako in an bayana a fili abin da Yesu ya bar su su yi. AT: "Yesu ya bar baƙin aljanun su yi abin da suka roƙa"

suka ruga a guje

"aladun suka ruga a guje"

zuwa cikin tekun, su kusan dubu biyu suka hallaka a cikin tekun

Ka na iya raba wannan zuwa jimla daban dabam: "zuwa cikin teku. Aladun kusan dubu biyu ne, sun kuma hallaka a cikin tekun"

aladu kusan dubu biyu

"aladu kusan 2,000"

Mark 5:14

cikin gari da kewaye

Ana iya bayana a fili cewa mutanen sun ba da rohoto abin da ya faru ga mutanen da ke cikin gari da kewaye. AT: "ga mutanen cikin gari da kewaye"

Tuli

Wannan sunan aljanun da dã suna cikin mutumin. Dubi yadda ka juya wannan cikin [Markus 5:9].

daidai cikin hankalinsa

Wannan na nufin cewa yana tunani da kyau. AT: "hankalinsa daidai" ko "tunani da kyau"

sai suka tsorata

Kalman nan "su" na nufin mutanen da suka je su ga abin da ya faru.

Mark 5:16

Waɗanda sun ga abin da ya fari

"Mutanen da sun ga abin da ya faru"

Mark 5:18

mutum mai aljan

Kodashike a yanzu mutumin ba shi da aljan, akan bayana shi a haka. AT: "mutumin da dã ke da aljan"

Amma Yesu bai ba shi dama ba

Ana iya bayana a fili abin da Yesu bai ba shi daman yi ba. AT: "Amma bai bar mutumin ya bi su ba"

Dikafolis

Wannan suna wani yanki ne da ke nufin Birane Goma. Ya na a kudu-gabacin Tekun Galili.

dukkansu suka yi mamaki

Zai zama da taimakon in an bayana dalilin da ya sa mutanen suka yi mamaki. AT: "dukkan mutanen da suka ji abin da mutumin ya faɗa sun yi mamaki"

Mark 5:21

ɗayan bangaren

Zai zama da amfani in an kara bayani a wannan magana. AT: "ɗayan bangaren teku"

gefen takun

"a bakin tekun" ko "gaɓar teku"

Yayirus

Wannan sunan mutum.

sai ya tafi tare da shi

"sai Yesu ya tafi tare da Yayirus." Almajiran Yesu ma sun tafi tare da shi. AT: "Sai Yesu da Almajiran sun tafi tare da Yayirus"

sa hannun ka

"Sa hannu" na nufin annabi ko malami ya sa hannunsa a kan wani, yana kuma warkar da shi ko sa masa albarka. A wannan al'amari, Yayiru yana tambayar Yesu ya warkar da 'yarsa.

don ta sami lafiya ta rayu

AT: "ya kuma warkar da ita da sa ta ta rayu"

har ma suna matse shi

Wannan na nufin sun taru kewaye da Yesu sun matse kansu don su yi kusa da Yesu.

Mark 5:25

Yanzu akwai wata mace

"yanzu" na bada alaman cewa an gabatar da wannan macen a labarin. Dubi yadda kuna gabatar da abon mutum cikin labarin a harshen ku.

wadda ta ke zub da jini na tsawon shekara goma sha biyu

Macen ba ta da wani ciwon da ke a buɗe; maimakon haka, hailar ta bai tsaya ba. Mai yiwuwa harshen ku na da wata hanya mai da'a da ana iya faɗin wannan yanayi.

tsawon shekara goma sha biyu

"tsawon shekara 12"

abin ma sai karuwa ya ke yi

"rashin lafiyar sai karuwa ya ke yi" ko "zub da jinin sai karuwa ya ke yi"

Ta ji labarin Yesu

Ta ji labari game da Yesu yadda ya warkar da mutane. AT: "cewa Yesu ya warkar da mutane"

rigarsa

rigar da ake sa a waje ko kwat

Mark 5:28

Zan warke

AT: "zai warkar da ni" ko "ikonsa za ta warkar da ni"

an warkar da ita daga cutar ta

AT: "cutar ya bar ta" ko "ta sami lafiya"

Mark 5:30

iko ya fita daga gare shi

Sa'ad da macen ta taɓa Yesu, Yesu ya ji ikon warkar da ita.Yesu kansa bai rasa ikonsa na warkar da mutane ba sa'ad da ya warkar da ita. AT: "cewa ikonsa na warkarwa ya warkar da macen"

wannan taron mutane da yawa ka

Wannan na nufin sun taru kewa da Yesu, sun matse junansu don su yi kusa da Yesu. Dubi yadda ka juya wannan cikin [Markus 5: 24]

Mark 5:33

făɗi a gabansa

"durkusa a gabansa." Ta durkusa a gaban Yesu a matsayin girmamawa da mika kai.

faɗa masa gaskiyar gabaki ɗaya

Maganan nan "gaskiyar gabakiɗaya" na nufin yadda ta taɓa shi har ta warke. AT: "faɗa masa gaskiyar gabakiɗaya game da yadda ta taɓa shi"

Diya

Yesu ya yi amfani da wannan kalma don yana duban macen a matsayin maibi.

bangaskiyar ki

"bangaskiyar ki a ciki na"

Mark 5:35

Sa'ad da yake magana

"Sa'ad da Yesu ke magana"

wasu mutane daga gidan shugaban majami'a

Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) waɗannan mutane sun zo daga gidan Yayirus ko 2) Yayiru ya riga ya umurce waɗannan mutane su zo su ga Yesu ko 3) mutumin da ke shugaban majami'a a sa'ad da Yayiru ba ya nan, shine ya turo waɗannan mutane.

shugaban majami'a

"shugaban majamia" shine Yayirus.

majami'a, cewa

"majami'a, cewa wa Yayirus"

Me ya sa kuna damun malamin kuma?

AT: "Ba shi da amfani a dame malamin kuma." ko "Ba ku bukata ku dame malamin kuma."

malamin

Wannan na nufin Yesu.

Mark 5:36

ka ba da gaskiya kawai

In lallei ne, to ana iya faɗin abin da Yesu yake umurtan Jarus ga bada gaskiya ga shi. AT: "Ka dai gaskanta cewa zan ta da 'yar ka"

Bai bari ... ya ga

Cikin waɗannan ayoyi kalman nan "Ya" na nufin Yesu.

Bai bari kowa ya kasance tare da shi ba

"ya bi shi ba." Zai zama da taimakon in an faɗa wurin da za suna koƙarin zuwa. AT: "ya bi shi zuwa gida Shugaban majami'a"

Mark 5:39

Ya ce masu

"Yesu ya cewa mutenen da suke kuka"

Me ya sa kuke damuwa me ya sa kuma kuna kuka?

Yesu ya yi wannan tambaya don ya taimake su su ga reashin bangaskiyarsu. AT: "Wannan ba lokacin damuwa da kuka ba ne."

Yarinyar ba ta mutu ba barci ta ke yi." Sai suka yi masa dariya

Yesu ya yi amfani da kalman da an saba amfani da ita na barci, haka kuma sai a yi amfani da shi a juyin. Ya kamata masu karatun su fahimta cewa mutanen da ke sauraron Yesu sun yi masa dariya domin ba su san bambanci tsakanin mutumin da ya mutu da wanda ya ke barci ba, suna kuma tunanin cewa shi bai sani ba.

Amma ya fitar da su dukka waje

"ya fitar da sauran mutanen da ke cikin gidan zuwa waje"

waɗanda suke tare da shi

Wannan na nufin Bitrus, Yakub da Yahaya.

shiga wurin da yarinyar ta ke

Zai zama da taimakon in an bayana inda yarinyar take. AT: "shiga cikin ɗakin da yarinyar take kwanciye"

Mark 5:41

Talita kumi

Wannan jimlar da harshe Yahudanci ne, wanda Yesu ya yi magana da karamar yarinyar cikin harshen ta. Ku rubuta waɗannan kalmomin kamar yadda yake da haruffan ku.

shakarun ta goma sha biyu ne

"shakarun ta 12 ne"

Ya ummurce su da gaske kada kowa ya san wannan. Sa'annan

AT: "Ya umurce su da gaske, 'kada kowa ya san game da wannan!' Sa'annan" ko "Ya umurce da gaske, 'Kada ku gaya wa kowa game da abin da na yi!' Sa'annan"

Ya umurcie su da gaske

"Ya ba su umurni da gaske"

Sa'annan ya ce masu su ba ta abinci ta ci

AT: "Sai ya ce masu, 'Bata abinci ta ci"

Chapter 6

1 Ya bar su ya zo garinsu, almajiransa su ka biyo shi. 2 Sa'adda ranar Asabar tazo ya shiga cikin masujada ya yi koyarwa. Mutane da yawa da su ka ji koyarwarsa su ka yi mamaki, suka ce daga ina ya sami irin wannan koyarwar? Wacce irin hikima ce Allah ya ba shi haka? Wadanne irin ayyukan al'ajibi ya ke yi da hannuwansa? 3 Wannan ba kafintan nan ba ne dan Maryamu, dan'uwan Yakubu da Yosi da Yahuza da Saminu? Ba ga 'yan'uwan sa 'yan mata mu na tare da su ba? Ba su ji dadi ba a ransu saboda Yesu. 4 Yesu ya ce, "Annabi ba ya rasa daraja sai a gidansa da garinsa da cikin danginsa." 5 Bai iya yin wani aikin al'ajibi a wurin ba sai dai mutane kadan marasa lafiya ya dorawa hannu ya warkar da su. 6 Rashin bangaskiyarsu ya ba shi mamaki. Sai ya tafi cikin kauyuka na kewaye da su ya yi ta koyarwa. 7 Ya kira almajiransa su goma sha biyu, ya aike su biyu-biyu, ya ba su iko a kan aljanu, 8 ya dokace su kada su dauki komai tare da su domin wannan tafiya, sai dai sanda kadai. Kada su dauki abinci ko jaka ko kudi a cikin aljihunsu, 9 sai dai su sa takalmi kadai, kada su sa taguwa biyu a jikinsu. 10 Ya ce da su, idan ku ka shiga wani gida sai ku zauna a gidan har lokacin da za ku tashi. 11 Idan ku ka je wani gari aka ki karbar ku, ku karkabe kurar da ke kafufunku ta zama shaida kan mutanen garin. 12 Sai suka tafi suka yi ta shela ga mutane cewa su tuba daga zunubansu. 13 Sun fitar da aljanu da yawa, suka shafawa mutane da yawa mai suka warkar da su. 14 Sarki Hirudus ya ji wannan, gama sunan Yesu ya zama sananne a wurin kowa da kowa. Wadansu suna cewa Yahaya mai yin baftisma ne ya tashi daga matattu shi ya sa ake yin wadannan ayyukan al'ajibi ta wurinsa. 15 Wadansu kuma suna cewa, "Iliya," Har yanzu wadansu suna cewa daya "daga cikin annabawa ne na da can." 16 Sa'adda Hirudus ya ji wannan sai ya ce, "Yahaya wanda na fillewa kai shine ya tashi." 17 Saboda Hirudus ne ya sa aka kama Yahaya aka kulle shi a kurkuku saboda Hirodiya( matar Filibus dan'uwansa), domin ya aure ta. 18 Saboda Yahaya ya gaya wa Hirudus cewa bai halarta ya auri matar dan'uwansa ba. 19 Sai ita Hirodiya ta yi kudurin ta kashe Yahaya amma bai yiwu ba. 20 Domin Hirudus yana jin tsoron Yahaya, domin ya sani shi mai adalci ce, mai tsarki kuma. Domin haka Hirudus bai so wani abu ya faru da Yahaya ba, amma ya kan fusata idan ya ji wa'azin yahaya. Duk da haka da fari ciki yakan saurare shi. 21 Amma sai dama ta samu inda Hirodiya za ta iya yin abin da ta ke so ta yi. A lokacin kewayowar ranar haihuwar sa, sai Hirudus ya shirya liyafa domin manyan da ke aiki tare da shi a cikin gwamnatin sa, da shugabannin da ke cikin Galili. 22 Diyar Hirodiya ta zo ta yi masu rawa, rawarta kuwa tagamshi Hirudus da bakinsa. Sarki ya ce da yarinyar, "ki tambayi duk abin da ki ke so ni kuwa zan ba ki shi". 23 Ya rantse mata da cewa"Ko menene ki ka ce ki na so, ko da rabin mulkina ne" 24 Sai ta fita ta je ta tambayi mamarta, "me zan ce ya bani?" Sai ta ce kan Yahaya Mai Yin Baftisma. 25 Sai ta dawo da sauri cikin dakin taro wurin sarki ta ce da shi, "Ina so ka ba ni kan Yahaya Mai Yin Baftisma a cikin tire." 26 Sarki ya damu kwarai, amma saboda ya yi alkawari ga kuma ofisoshinsa, ba dama ya ce a'a. 27 Sai sarki ya aiki wani soja ya ba shi ummurni ya je ya kawo kan Yahaya. Sojan ya je ya fillo kan sa daga cikin kurkuku. 28 Ya kawo kan a cikin tire ya ba yarinyar, yarinyar kuma ta kai wa mamarta. 29 Da almajiran su ka ji labari, suka zo suka dauki gawarsa suka rufe a cikin kabari. 30 Almajiran suka zo wurin Yesu, suka fada masa dukkan abin da suka yi da abin da suka koyar. 31 Sai ya ce da su "ku je cikin kebabben wuri domin ku huta kadan," domin mutane suna ta kaiwa da komowa, ba su sami damar hutawa ba balle su ci abinci 32 Sai suka tafi kebabben wuri a cikin jirgin ruwa su kadai. 33 Amma mutane da yawa sun gansu suna tafiya sun kuma gane su, sai suka fito daga cikin dukan garuruwa da gudu har su ka kai wurin kafin su zo. 34 Sa'adda suka zo bakin gaba Yesu ya ga taron mutane da yawa sai ya ji tausayinsu domin sun yi kamar tumakin da ba da mai kiwo. Sai ya cigaba da koya masu abubuwa da yawa. 35 Sa'adda yamma ta yi, almajiran sa suka zo suka ce da shi, "wurinnan kebabben wuri ne kuma ga lokaci ya tafi. 36 Ka sallami mutanen nan domin su shiga cikin garuruwa da kauyuka da ke kusa domin su sayi abin da zasu ci. 37 Amma sai ya ba su amsa ya ce,"Ku ku basu abinci su ci mana". Sai suka ce da shi, "ma iya zuwa mu sawo gurasa ta sule dari biyu mu basu su ci?" 38 Sai ya ce dasu, "Dunkulen gurasa guda nawa kuke dasu? Kuje ku gani." Dasuka gano sai suka ce da shi, dunkule biyar ne da kifi guda biyu." 39 Sai ya ba da umarni mutanen su dukka su zauna a kan danyar ciyawa. 40 Suka zauna kungiya kungiya wadansu su dari wadansu hamsin. 41 Sai ya dauki dunkulen gurasa guda biyar da kifi guda biyu, ya ta da kansa sama, yasa albarka, ya kakkarya dunkulen gurasan, ya ba almajiran domin su rabawa taron jama'a duka. 42 Dukansu suka ci suka koshi. 43 Suka tattara gutsattsarin gurasar suka cika kwanduna guda goma sha biyu da gutsattsarin da kuma gutsattsarin kifin. 44 Mutanen da suka ci gurasar sun kai mutum dubu biyar. 45 Nan da nan ya ce almajiran sa su hau jirgin ruwa su yi gaba kafin ya zo, su je Baitsaida. Shi kuma ya tsaya domin ya sallami taron mutanen. 46 Bayan da suka tafi shi kuma ya hau kan dutse domin ya yi addu'a. 47 Har yamma ta yi jirgin ruwan ya na tsakiyar rafi shi kuma yana kan tudu shi kadai. 48 Ya gansu suna wahala gama iska ta hana su tafiya. Wajan karfe hudu na asuba sai ya tawo wurin su yana tafiya a kan ruwa, yana so ya wuce gaban su. 49 Sa'adda suka gan shi ya na tafiya a kan ruwa suka yi tsammani fatalwa ce, suka yi ihu, 50 gama su duka sun gan shi, tsoro ya kama su. Sai nan da nan ya yi magana dasu ya ce, "Ku karfafa ni ne! kada ku ji tsoro!" 51 Ya shiga cikin jirgin ruwan tare dasu, sai iska ta dena bugawa. Sai suka yi mamaki kwarai. 52 Gama basu gane batun dunkulen ba. Maimakon haka, sai zukatansu suka taurare. 53 Sa'adda suka haye su zo kasar Janisarita suka sa wa jirgin sarka. 54 Su na fitowa daga cikin jirgin kenan, mutane suka gane cewa Yesu ne. 55 Mutane suka ruga cikin yankin su, suka kawo marasa lafiya a bisa shinfidun su zuwa wurinsa, dukan inda suka ji yana zuwa. 56 Ko ina ya shiga birni da kauye, ko a cikin kasar sukan kawo marasa lafiya a kasuwanni suna rokonsa su taba ko da habar rigarsa, dukan wadanda suka taba kuwa suka warke.

Mark 6:1

Mahaɗin Zance:

Yesu ya komo garinsa, inda ba a karɓarsa.

garinsa

Wannan na nufin garin Nazarat, inda Yesu ya yi girma da inda iyalinsa suke zama. Wannan ba ya nufin cewa yana da nasa fili a wurin.

Wacce irin hikima ce Allah ya ba shi haka?

AT: "Macece wannan hikima da ya samu?"

ya ke yi da hannuwansa

Wannan magana na nanata cewa Yesu kansa yana yin abin al'ajibin. AT: "wanda shi kansa ya yi"

Shin wannan ba kafintan nan ba ne ɗan Maryamu, ɗan'uwan Yakubu da Yosi da Yahuza da Saminu? Ba ga 'yan'uwan sa 'yan mata mu na tare da su ba?

Waɗannan tambayoyin ana iya rubuta su cikin jimlar da ba tambaya ba. AT: "Wannan kafinta ne kawai! Mun san shi da iyalinsa. Mun san uwa tasa Maryamu. Mun san 'yan'uwansa Yakubu, Yosi, Yahuza da kuma Saminu. 'yan'uwansa mata kuma suna tare da mu."

Mark 6:4

masu

"wa taron"

Annabi ba ya rasa daraja sai

AT: "Ana daraja Annabi a koyaushe, sai" ko "Wurin da ba a daraja annabi shine"

sai dai mutane kaɗan marasa lafiya ya dorawa hannu

Annabi da malami na iya sa hannu a kan mutane don ya warkar da su ko albarkace su. Wannan yanayi, Yesu yana warkar da mutane ne.

Mark 6:7

Muhimman Bayani:

Umurnin Yesu a aya 8 da 9, ana iya sake kasafa shi ta wurin raba abin da ya gaya wa almajiransa su yi daga abin da ya ce masu kada su yi, kamar yadda yake a UDB.

ya kira goma sha biyun

A nan kalman nan "kira" na nufin cewa ya urmuce sha biyun su zo wurinsa.

biyu-biyu

"2 da 2" ko "cikin biyu"

kada ... gurasa

A nan "gurasa" na nufin abinci. AT: "ba abinci"

kuɗi a cikin damaransu

A wancan al'ada, mazaje na ɗauka kuɗi su ajiye a cikin damararsu. AT: "ba kuɗi a cikin jakunan kuɗinsu" ko "ba kuɗi"

Mark 6:10

Ya ce masu

"Yesu ya cewa sha biyun"

sai ku zauna a gidan har lokacin da za ku tashi

A nan "zauna" na nufin komowa zuwa gidan ko wani ranar don su ci su kuma yi barci a wurin. AT: "ku ci, ku kuma kwanta a wannan gida har sai lokacin da za ku bar wannan wuri"

ta zama shaida a gare su

"ta zama shaidan a kansu." Zai zama da taimako a bayana yadda wannan ya zama shaida a gare su. "ta zama shaida a gare su. Tawurin yin haka, za ku shaidi cewa ba su marabce ku ba"

Mark 6:12

Sai suka tafi

Kalman nan "su" na nufin sha biyun, ban da Yesu. Zai zama da taimako kuma a bayana cewa sun tafi garuruwa daban dabam. AT: "Sun shiga garuruwa daban dabam"

juyo daga zunubansu

A nan "juyo daga" na nufin a daina yi wani abu. AT: "bar yin zunubi" ko "tuba daga zunubansu"

Sun fitar da aljanu da yawa

Zai iya zama da taimako a faɗa cewa sun fitar da aljanu daga cikin mutane. AT: "Sun fid da aljanu da yawa daga cikin mutane"

Mark 6:14

Sarki Hirudus ya ji wannan

Kalman nan "wannan" na nufin dukkan abin da Yesi da almajiransa sun yi ta yi a garuruwa daban dabam, duk da fid da aljannu da kuma warkar da mutane.

Waɗansu suna cewa, "Yahaya Mai baftisma ne

Wasu suna cewa Yesu, shine Yahaya Mai Baftisma. Wannan ana iya bayana shi a fili. AT: "Waɗansu suna cewa, "Shine Yahaya Mai Baftisma ne wanda aka"

Yahaya Mai Baftisma ne ya tashi daga matattu

"Tashi daga mattattu" anan wata karin magana ne na "sa mutum ya rayu kuma." AT: "Ana tashe Yahaya Mai Baftisma kuma" ko "Allah ya sa Yahaya Mai Baftisma ya rayu kuma"

Waɗansu kuma suna cewa, "Shi Iliya ne,"

Zai zama da taimakon in an bayana cewa wasu mutane suna tunanin cewa shine Iliya. AT: "Waɗansu sun ce, 'Iliya ne wanda Allah ya yi alkawari zai aika kuma.'"

Mark 6:16

wanda na fillewa kai

A nan Hirudus ya yi amfani da kalman nan "na" don yana nufin kansa ne. Kalman nan "na" na nufin sojijin Hirudus. AT: "wanda na umurci sojoji na su fille kansa"

shine ya tashi

AT: "yana raye kuma"

Hirudus ne ya sa aka kama Yahaya aka kulle shi a kurkuku

AT: "Hirudus ya aiki sojojinsa su kama Yahaya su kulle shi a kurkuku"

aika a

"umurta a"

saboda Hirodiya

"ta dalili Hirodiya"

matar Filibus ɗan'uwansa

"matar ɗan'uwansa Filibus." Filibus ɗan'uwan Hirudus ba ɗaya ne da Filibus wanda an ambata cikin littafin Ayukan Manzani ko Filibus ɗaya daga cikin almajiran sha biyu na Yesu.

domin ya aure ta

"domin Hirudus ya aure ta"

Mark 6:18

ta yi kudurin ta kashe shi amma bai yiwu ba

Hirodiya shine kan maganan wannan magana "ta" na nufin cewa ta na so wani ya kashe Yahaya. AT: "ta na so wani ya kashe shi amma ba ta iya kashe shi ba"

Domin Hirudus yana jin tsoron Yahaya, ya sani

Waɗannan magana biyu ana iya haɗa don ya nuna a fili dalilin da ya sa Hirudus yana jin tsoron Yahaya. AT: "domin Hirudus yana jin tsoron Yahaya domin ya sani"

domin ya sani shi mai adalci ce

"Hirudus ya sani cewa Yahaya mutum ne mai adalci"

yakan saurare shi

yakan saurare Yahaya"

Mark 6:21

ya shirya liyafa domin manyan da ke aiki tare da shi a cikin gwamnatin sa ... Galili

A nan kalman nan "ya" na nufin Hirudus, yana kuma na nufin bawansa wanda ya bada umurni a shirya liyafa. AT: "ya shirya liyafa domin manyan ma'aikatansa ... Galili" ko "ya gayaci manyan ma'aikatansa ... Galili ci su kuma yi murna tare da shi"

liyafa

wata abinci ta musamman ko liyafa

Hirudiya kanta

Kalman nan "kanta" an yi amfani da ita don nanata cewa yana da muhimmanci cewa 'yar Hirudiya ne wanda ta yi rawa a lokacin liyafa.

shigo cikin

"shigo cikin dakin"

Mark 6:23

Ko menene ki ka ce ... mulkina

"zan ba ki har rabin abin da nake da shi da mulkina, in kin roƙa"

fita

"fita daga dakin"

a cikin tire

"kan katako" ko "a kan babban kwano da aka yi da itace"

Mark 6:26

saboda ya yi alkawari ga kuma baƙi da sun zo liyafa

Ana iya bayana abin da ke cikin alkawarin, da kuma dangantaka tsakanin alkawarin da bakin da sun zo liyafa, a fili. AT: "domin baƙin sun ji ya yi alkawarin cewa zai ba ta kowane abin da ta roƙa"

a cikin tire

"a kan tire"

Sa'ad da almajiransa

"Sa'ad da almajiran Yahaya"

Mark 6:30

keɓaɓɓen wuri

wurin da ba kowa

mutane da yawa suna ta kaiwa da komowa

Wannan na nufin cewa mutane suna zuwa wurin manzanin su kuma koma.

ba su sami

Kalman nan "su" na nufin manzanen.

Sai suka tafi

A nan kalman nan "su" na nufin manzanen da Yesu.

Mark 6:33

sun gansu suna tafiya

"mutanen sun ga Yesu da manzanen suna tafiya"

s kafa

Mutanen suna tafiya a kafa, wannan kuwa ya zama da bambanci da tafiyar almajiran a kwalekwale.

ya ga taron

"Yesu ya ga gaggaruman taro"

suna kamar tumakin da ba makiyayi

Yesu ya kwatanta mutane da tumakin da sun rikice a sa'ad da ba su da makiyayi da ke shugabantansu.

Mark 6:35

Sa'adda yamma ta yi

Wannan na nufin can da yamma. AT: "Sa'adda yamma ya fara yi" ko "Can da rana"

Mark 6:37

Amma ya amsa ya ce

"Amma Yesu ya amsa ya cewa almajiransa"

ma iya zuwa mu sayo gurasa ta dinari dari biyu mu ba su su ci?

Almajiran sun yi wannan tambaya don su bayana cewa babu wata hanya da za su iya sayan abinci da zai ishe taron. AT: "Ba za mu iya sayan gurasa wanda zai isa ciyad da wannan taron ba, ko muna da denari ɗari biyu!"

denari ɗari biyu

"denari 200." Mufuradin wannan kalman "denari" shine "denarus." Denarus guda kuɗi ne na azurfa wanda Romawa ke amfani da shi a wancan lokaci don biyan hakin ma'aikata a rana ɗaya.

gurasa

dunƙulallen gurasa da aka yi.

Mark 6:39

danyar ciyawa

Ku bayana ciyawan da kalman kalan da ake amfani da shi a harshen ku na ciyawa mai kyau, wanda maiyiwuwa ba kore ba.

kungiya kungiya waɗansu su ɗari waɗansu hamsin

Wannan na nufin mutane da ke kowane kungiya. AT: "mutane kunsan hamsin a wasu kungiya, wasu kuma mutane kusan ɗari wa wasu kungiyan"

dubi sama

Wannan na nufin cewa ya daga kansa ya dubi cikin sama, wanda ake kamata shi da inda Allah yake.

ya sa albarka

"ya albarkaci" ko "ya mika godiya"

Ya kuma raba kifi biyun a tsakaninsu dukka

"ya raba kifi biyun don kowa ya samu"

Mark 6:42

Suka tattara

Ma'ana ma yiwuwa na kamar haka 1) "Almajiran sun tattara" ko 2) "Mutanen sun tattara."

gutsattsarin gurasar suka cika kwanduna guda goma sha biyu

"gursarin gurasar sun cika kwanduna goma sha biyu"

kwanduna goma sha biyu

"kwanduna 12"

maza dubu biyar

"maza 5,000"

Mutanen da suka ci gurasar sun kai mutum dubu biyar

Ba a lisafta yawan mata da 'ya'ya ba. Idan ba za a iya fahimtar cewa ba a ambata yawan mata da 'ya'ya ba, to za a oya bayana a fili. AT: "mutum dubu biyar sun ci gurasan. Ba ma kirga mata da yara ba"

Mark 6:45

zuwa wata bangaren

Wannan na nufin Tekun Galili. Anan iya bayana wanna a fili. AT: "zuwa wata bangaren Teku Galili" (Dubi: gs_ellipsis)

Baitsaida

Wannan gari ne a arewacin Tekun Galili.

Sa'ad da sun tafi

"Sa'ad da mutanen sun tafi"

Mark 6:48

Wajen karfe

Wannan lokaci ne tsakanin 3 a.m.

fatalwa ce

ruhu matatcen mutum ko kuwa wasu irin ruhu

Ku karfafa ni ne! ... kada ku ji tsoro!

Waɗannan jimla biyun suna da ma'ana kusan iri ɗaya, suna kuma nanata cewa almajiran ba sa bukatan su ji tsoroI. In ta zama wajibi, ana iya haɗa su su zama ɗaya. AT: "Kada ku ji tsoro!"

Mark 6:51

Sun yi mamaki

In kuna bukatan ku bayana a fili abin da ya sa su mamaki za ku iya yi. AT: "Sun yi mamakin abin da ya yi"

abin da dunƙule ke nufi

A nan maganan nan "gurasan" na nufin sa'ad da Yesu ya ninka dunƙunlen gurasa. AT: "abin da ake nufi da cewa Yesu ya ninka gurasan" ko "abin da ake nufin sa'ada Yesu ya sa dunkulen gurasa ta karu ta yi yawa"

zukatansu ta taurare

Taurin zuciya na nufin kin ji don a fahimta. AT: "sun taurare zuciyar har sun kãsa fahimta"

Mark 6:53

Janisarata

Wannan sunan yankin arewa maso yammacin Tekun Galili.

suka ruga cikin duk yankin

Zai zama da taimako in an bayana dalili da ya sa sun ruga zuwa cikin yankin. AT: "sun ruga zuwa cikin yankin don ya gayawa sauran mutane cewa Yesu yana wurin"

sun ruga ... sun ji

Kalman nan "su" na nufin mutane sun gane Yesu, ba almajiran ba.

marsa lafiya

Wannan magana na nufin mutane. AT: "mutane marasa lafiya"

Mark 6:56

Duk inda ya shiga

"Duk inda Yesu ya shiga"

za su sa

A nan "su" na nufin mutanen. Ba ya nufin almajiran Yesu.

Sun roƙe shi

Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) "Marasa lafiyan sun roƙe shi" ko 2) Mutanen sun roƙe shi."

ya bari su taɓa

Kalman nan "su" na nufin marasa lafiyan.

habar rigarsa

"bakin tufafinsa" ko "gefen rigarsa"

da yawa da

"dukkan waɗanda"

Chapter 7

1 Farisawa suka taru wurin Yesu tare da wadansu marubuta wadda suka zo daga Urushalima. 2 Sun ga cewa wasu daga cikin almajiransa sun ci gurasa da hannuwa marasa tsabta, wato, basu wanke hannu ba, 3 (Domin Farisawa da dukan Yahudawa ba su cin abinci sai dole sun wanke hannu da kyau domin suna kiyaye al'adun dattawa. 4 Idan Farisawa suka dawo daga kasuwa, wajibi ne su yi wanka kamin su ci abinci. Akwai sauran al'adun da suke kiyayewa, kamar wanke moda, tukwane, da wasu santula na dalma, har da dakin cin abinci.) 5 Farisawa da Marubuta suka tambaye Yesu, "Don me almajiran ka basu kiyaye al'adun dattawa, domin suna cin abinci ba tare da sun wanke hannu ba?" 6 Amma ya amsa masu cewa, "Ishaya ya yi anabci akan ku masu bautan ganin ido, da ya rubuta cewa 'wadanan mutane suna girmama ni a baka amma zuciyar su tana nesa da ni. 7 Sujadar wofi suke mani suna koyar da ka'idodi na mutane a matsayin rukunansu'". 8 Kun watsar da dokar Allah sai kuka rungumi al'adun mutane. 9 Sai yace masu, kun yi nasara wurin kau da dokokin Allah domin ku kiyaye al'adun ku na mutane. 10 Koda shike Musa ya rubuta cewa, "ka girmama Ubanka da Uwarka", kuma, "duk wanda ya zagi Ubansa ko Uwatasa, ya cancanci mutuwa nan take". 11 Amma kun ce, 'idan mutum ya ce wa iyayensa, "duk taimakon da ya cacanci ku samu daga guna ya zama kebabbe (wato, 'na mika wa Allah)"'. 12 Sabo da haka, kun ba shi izini kada ya yi wa Ubansa ko Uwatasa wani abu. 13 Kuna mayar da dokan Allah abin banza, sabili da al'adun ku da kuka mika masu. Wannan, da wasu abubuwa kamar haka kuke yi." 14 Ya kara kiran taron jama'ar yace masu, "ku kasa kunne gareni, kuma ku gane. 15 Babu wani abu daga wajen mutum da zai iya gurbatar da shi har idan ya shiga cikinsa. Amma, abinda ya fita daga cikinsa shike gurbatar da shi" 16 Bari mai kunnen ji, ya ji. 17 Da Yesu ya bar taron jama'ar, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma'anar wannan misali. 18 Sai Yesu yace, 'ashe baku da ganewa? ko baku sani cewa abin da ya shiga cikin mutum daga waje ba zai iya gurbatar da shi ba, 19 domin ba zai iya kai wa cikin zuciyarsa ba, sai dai ya shiga cikin sa ya kuma fita a matsayin bayan gari a salga". Da wannan magana, Yesu ya mayar da dukan abinci ya zama da tsabta. 20 Ya ce, abinda ke cikin mutum shike gurbatar da shi 21 Domin daga cikin mutum, kuma daga cikin zuciyarsa ne, mugun tunani, lalata, sata, kisa, 22 zina, kwadayi, mugunta, hai'inci, mugun guri, kishi, zargi, girmankai, wawanci. 23 Duk wadannan miyagun abubuwa suna fitowa ne daga cikin mutum, kuma suke gurbatar da shi." 24 Ya tashi daga nan ya tafi shiyyar Sur da Sida. Ya shiga wani gida don baya son wani ya sani cewa yana nan, amma bai iya boyuwa ba. 25 Amma nan da nan wata mace, wadda diyarta ke da mugun ruhu-wannan mace kuwa ta ji game da Yesu sai ta zo ta durkusa a gabansa. 26 Matar yar kasar Girka ce, kuma asalinta daga Fonishiya take. Ta roke shi da ya fitar da mugun ruhun nan daga diyarta. 27 Sai ya ce mata, "Bari a ciyar da 'ya'ya tukuna. Domin bai kamata a dauki abincin yaya a ba karnuka ba". 28 Sai ta amsa masa cewa, "I, Ubangiji, Karnukan ma sukan ci abincin da ke fadowa daga teburin 'ya'yan." 29 Ya ce mata, "domin kin fadi haka, kina iya ki tafi domin aljani ya fita daga diyarki." 30 Ta koma gida sai ta iske diyarta na kwance akan gado, aljanin ya fice daga jikinta. 31 Ya sake fita daga shiyar Sur, ya biyo ta Sidon, har zuwa tekun Galili a shiyar Dikafolis. 32 Sun kawo masa wani kurma, kuma bebe ne shi, suna rokansa ya dora hanuwansa a bisansa. 33 Sai ya jawo shi daga taron jama'ar, zuwa gefe, sai ya sa hanunsa a kunuwan beben bayan ya tufa yawunsa, sannan ya taba harshensa. 34 Ya dubi sama, ya ja numfashi ya ce masa, "Ifatha", wato, "bude!" 35 Nan da nan ya mayar masa da jinsa. abinda ya daure harshensa ya sake shi, sai ya fara magana da kyau. 36 Ya umarce su da kada su gaya wa wani. Amma duk da umarnin da yake basu, suna ta shaida shi ko'ina. 37 kuma suna ta mamaki cewa, "Yayi kowanne abu da kyau, har ya sa kurame suna jin magana, da kuma bebaye na magana."

Mark 7:1

Mahaɗin Zance:

Yesu ya kwaɓe Farisiyawa da kuma mallaman attaura.

taru wurinsa

"taru a wurin Yesu"

Mark 7:2

Muhinmin Bayyani:

A aya ta 3 da 4, marubucin ya ba da shahararen bayani game da al'adu na wankin Farisawan domin ya nuna dalilin da ya sa Farisawan suka damu da cewa almajaren Yesu basu wanke hannayen su kafin su fara cin abinci ba. Za a iya kara juya wannan bayanin domin a samu ganewa me kyau, kamar yadda take a UDB.

Sun gani

"Farisawan da mallamen attauran suka gani"

wato, basu wanke hannu ba,

Kalman nan "basu wanke hannu ba" ya yi bayanin dalilin rashin tsabtan hannayen almajaren. AT: "cewa, da hannayen da basu wanke ba" ko "cewa, basu wanke hannayen su ba"

dattawa

Dattawan Yahudawan shugabane ne a wurin su, kuma su Mahukunta ne ga mutanen.

santula na dalma

"butan dalma" ko "tukunyan karfe"

har da dakin cin abinci

"benci" ko "gado." A wancan lokacin, Yahudawan zasu jingina a kai iɗan suna cin abinci.

Mark 7:5

Don me almajiran ka basu kiyaye al'adun dattawa, domin suna cin abinci ba tare da sun wanke hannu ba?

"kiyaye" kalma ce na yin "biyayya." Farisawan da mallaman attaturan sun yi tambayan nan domin su tsokane ikon Yesu. AT: "Almajaren ka sun rashin biyayya ga ala'dun dattawan mu! Su wanke hannayen su ta wurin anfani da hanyan al'adun mu."

gurasa

Wannan kalma ce da take nufin abinci gabadaya. AT: "abinci"

Mark 7:6

da bakin su

A nan "baki" kalma ce na magana. AT: "ta wurin abin da suka ce"

amma zuciyar su tana nesa da ni

A nan "zuciya" ya nufin shauƙi ko tunanin mutum. Wannan hanya ce da take cewa mutane basu ba da lokacin su da gaske ga Allah ba. "amma ba su ƙaunace ni da gaske ba"

Sujadar wofi suke mani

"Sujadar wofi suke mani" ko "A banza suka bauta mani"

Mark 7:8

watsar

ki yin biyayya

rungumi al'adun

"rike da ƙarfi" ko "kadai kuka ajiye"

kun yi nasara wurin kau da dokokin ... kiyaye al'adun ku

Yesu ya yi anfani da kalman nan domin ya kwaɓe masu jin sa domin sun rabu da Umurnin Allah. AT: "Ku na tunanin kun yi adalci ta wurin kau da dokokin Allah domin ku iya kiyaye al'adun ku, ko kadan, abun da kuka yi ba shi da kyau"

kammar yadda kuka ki

"Kamar yadda kuka yi fasaha ta wurin kin"

duk wanda ya faɗi mugun abu

"duk wanda ya zagi"

ya cancanci mutuwa

"lalle a kashe shi"

Duk wanda ya zagi ubansa da uwarsa, ya cancanci mutuwa

" AT: "Lallei ne hukuma ta zartadda kisa ga wanda ya zagi ubansa ko uwarsa"

Mark 7:11

duk taimakon da ya cacanci ku samu daga guna ya zama kebabbe

Al'adan mallaman attaura sun zartadda da cewa da zaran an yi kautan kuɗi ko wani abu wa haikali, ba za a yi anfani da su wa waɗansu abubuwa ba.

zama keɓaɓɓe

"keɓaɓɓe" kalmar Yahudawa ne da yake nufin abubuwan da mutane suka yi alkawali cewa zasu mika wa Allah. AT: "kauta ce ga Allah" ko "na Allah ne"

Mika wa Allah

Kalman nan ya ba da ma'anan kalman Yahudawan nan "keɓaɓɓe." AT: "Na rigaya na mika wa Allah"

Sabo da haka, kun ba shi izini kada ya yi wa Ubansa ko Uwatasa wani abu

Ta wurin yin haka, Farisawan suna hana mutane tanaɗa wa iyaye, iɗan suka mika wa Allah abun da suka yarda zasu mika masa.

abin banza

abin da aka share ko aka manta da shi

da wasu abubuwa kamar haka kuke yi

"wasu abubuwan da kuke yi suna nan ƙamar haka ne"

Mark 7:14

Ya kira

"Yesu ya kira"

ku kasa kunne gareni, kuma ku gane

Kalman nan "Kasa kunne" da kuma "gane" suna kama. Yesu yayi anfani da su domin ya nanata wa masu jin sa cewa su kassa kunne ga abin da yake faɗi.

ku gane

Zai zama da taimako a faɗa masu abin da Yesu yake so su gane. AT: "ku gane abin da nake so kokarin in gaya maku"

Babu wani abu daga wajen mutum

Yesu yana magana akan abin da mutum yake ci ne. Wannan ya bambanta da "abin da yake fita daga mutum." "babu wanu abu daga wajen mutu da zai iya ci"

abin da yake fitowa daga cikin mutum ne

Wannan na nufin abin da mutum yake yi ne ko kuma yana faɗa. Wannan ya bambanta da "abin da yake wajen mutum da yake kai ciki." AT: "abin da yake fitowa da cikin mutum ne yake faɗa ko ya aikata"

Mark 7:17

Yanzu

Ana anfani da wannan kalman anan domin a nuna alamar dakatawa a cikin ainihin labarin. Yanzu Yesu ya yi nesa da jama'a, a wani gida tare da almajarensa.

Ashe, har yanzu baku da ganewa?

Yesu yayi anfani da tambayan nan domin ya nuna rashin jin daɗin sa cewa basu gane ba. AT: "Bayan abubuwan da na fada, na kuma aikata, ina gani kaman kun gane."

ba zai shi zuciyar shi ba

A nan "zuciya" kalma ce da take nuna cikin mutum ko zukatar sa. Anan Yesu na nufin cewa abinci bashi da anfani ga hallin mutum. AT: " ba zai taba shiga cikin zukatar s ba"

ko baku sani cewa abin da ya shiga ... salga

Yesu yayi anfani da tambayan nan domin ya koya wa almajaren sa abin da yakamata da daɗewa su sani. AT: "abin da ya shisga ... salga."

da shike

A nan "shi" na nufin abin da yake shigo cikin mutum; abin da mutum yake ci kenan.

dukan abinci ya zama da tsabta

Zai iya zama da taimako a bayyana ma'anan kalman nan a fili. AT: "duƙan abinci ya zama da tsabta, na ma'anan cewa mutum zai iya cin kowane abinci ba tare da Allah ya sabtace mai ci din ba"

Mark 7:20

Ya ce

"Yesu ya ce"

abinda ke cikin mutum shike gurbatar da shi

"abinda ke gubatar da mutum, shi ke a cikin sa"

mugun guri

rashin ƙame kai ga sha'awa

suna fitowa ne daga cikin

A nan kalman "cikin" na bayyana zuciyar mutum. AT: "na fitowa daga cikin zuciyar mutum" ko "na fitowa daga cikin tunanin mutum"

kuma daga cikin zuciyarsa ne, mugun tunani

A nan "zuciya" kalma ce da yake nuna cikin zukatar mutum. AT: "daga cikin mutum ne, mugun tunani ke fitowa" ko "daga zukata ne, mugun tunani ke ftiowa"

Mark 7:24

ke da mugun ruhu

Wannan ƙarin magana ne wande yake nufin ta kamu da mugun ruhu. AT: "kamu da mugun ruhu"

faɗi

"durkusa." Wannan ayukan ba da girma ne da kuma mika kai.

Matar yar kasar Girka ce, kuma asalinta daga Fonishiya take

Kalman nan "Yanzu" na nuna alamar dakatawa a cikin ainihin labarin, wannan maganan kuma na bamu shahararen bayani game da matan.

Fonishiya

Wannan suna ne na inda matar ta fito. An haife ta ne a Phoenician yankin Syria.

Mark 7:27

Bari a ciyar da 'ya'ya tukuna. Domin bai kamata ... a ba karnuka ba

A nan Yesu yana magana akan Yahudawa kaman su 'ya'ya ne, Al'ummai kuma kaman ƙarnuka ne. AT: "Bari a fara ciyar da 'ya'yan Isra'ila tukuna. Domin ba daidai bane a dauki gurasar 'ya'ya a ba wa Al'ummai, wanda suke kaman karnuka"

Bari a ciyar da 'ya'ya tukuna

AT: "Lalle ne mu fara ciyes da 'ya'ya Isra'ila tukuna"

karnuka

Wannan na nufin kananan karnuka wanda ake ajiyewa a matsayin abin wasa.

Mark 7:29

kina iya tafiya

Yesu na nufin cewa ba dalilin ta saya ta tambaye shi cewa ya taimaki 'yar ta. Zai yi mata. AT: "za ki iya tafiya yanzu" ko "za ki iya tafiya gida da salama"

Aljanin ya fita daga diyarki

Yesu ya saka mugun ruhun ya ar jikin diyar matar. AT: "Na saka mugun ruhun ya bar jikin 'yar ki"

Mark 7:31

fita daga jihar Sur

"bar jihar Sur"

zuwa jihar

AT:1) "a jihar" Da Yesu yake tekun a jihar Dikafolis ko 2) "ta jihar" da Yesu ya bi ta jihar Dikafolis domin ya iso tekun.

Dikafolis

Wannan sunan wata jiha ce da take ma'anar Gariruwa Goma. Ana samun ta ne a ..................Galili

Suka kawo

"Sai mutane suka kawo"

wanda shi kurma ne

"wanda ba ya ji"

suka roke shi ya mika hannun sa a kansa

Annabai da mallamai suna saka hannuwan su akan mutane domin su wanrkas da su ko kuma su saka masu albarka. A wannan hali, mutane na roƙon Yesu ya warkas da wani mutum. AT: "sun roƙe Yesu ya saka hannun sa akan mutumin domin ya warkas da shi"

Mark 7:33

Ya dauke shi

"Yesu ya dauki mutumin"

ya saka yatsosinsa a kunnen mutumin

Yesu yana saka yatsosinsa a kunnen mutumin.

bayan ya tufa yawunsa, ya taba harshen sa

Yesu ya tofa wa mutumin yau, ya kuma taba harshen sa.

bayan ya tufa

Zai iya zama da taimako a fadi cewa Yesu ya tofa yau a yatsosin sa ne. AT: "bayan da ya tofad da yau a yatsosin sa"

ya duba sama

Wannan yana nufin cewa ya daga idanunsa zuwa sama, wanda ake zatto inda Allah yake.

Iffata

A nan marubucin na nufin kalman da kalmar Aramaic. rubuta wannan kalma da sifar rubutu na ƙabilar ka. .........

ya ja numfashi

Wannan na nufin cewa yayi nishi ko ya ja dogon numfashi da za a iya ji. Mai yiwuwa yana nuna tausayi d Yesu yake nuna wa mutum.

ya ce masa

"faɗa wa mtumin"

kunnuwan sa ya buɗu

Wannan na nufin cewa ya fara ji. AT: "kunnuwansa sun buɗu sai ya fara ji" ko "ya fara ji"

harshensa ya sake shi,

AT: "Yesu ya dauke abin da yake tsare harshen sa daga magana" ko "Yesu ya kwance harshen sa"

Mark 7:36

duk da umarnin da yake basu

Wannan na nufin shi yake ba su umurni kada su fada wa kowa game da abin da yayi. AT: "duk da umarnin da yake basu kada su fada wa kowa"

suna ta shaida shi ko'ina

"suna ta shaida shi ko'ina" ko "a yalwace"

suka yi mamaki gaba da kima

"suka yi mamaki sosai" ko "suka yi mamaki kwarai" ko "suka yi mamaki gaba da kima"

kurma ... bebe

Wannan na nufin mutane ne. AT: "kurmaye ... bebbe mutane" ko "mutanen da baswa iya ji ... mutanen da baswa iya magana"

Chapter 8

1 A kwanakin nan, akwai wani gagaruman taron mutane, kuma basu da abincin ci. Yesu ya kirawo almajiransa yace masu, 2 "Ina tausayin taron mutanen nan domin kwana uku kenan suna nan tare da ni babu abinci. 3 Idan na salame su su koma gidajensu ba tare da sun ci abinci ba, za su galabaita a hanya domin gidajensu na da nisa." 4 Almajiransa suka amsa masa cewa, "A ina za mu iya samu gurasa a wannan jeji da zai ishi wadannan mutane haka?" 5 Ya tambaye su, "gurasa nawa kuke da su?" Sai suka ce, "Bakwai." 6 Ya umarci mutanen da su zauna. Ya dauki gurasar bakwai, bayan da ya yi godiya, ya kakarya gurasar, sa'annan ya umarci almajiransa da su raba wa mutanen. Su kuwa suka raba masu. 7 Suna kuma da kananan kifaye kadan. Bayan da ya yi godiya akan su, ya umurci almajiran su rabawa mutanen. 8 Sun ci sun koshi. Suka tattara ragowar, har sun cika kwanduna bakwai. 9 Akwai maza kimanin dubu hudu a wurin. Yesu ya sallame su. 10 Nan take, ya shiga jirgin ruwa da almajiransa zuwa shiyyar Dalmanuta. 11 Sai Farisawa suka zo suka fara gardama da shi. Suna nema ya nuna masu alama daga sama, domin su gwada shi. 12 Ya ja numfashi a ruhunsa yana cewa, "Don me wannan tsarar tana neman alama. Hakika ina gaya maku, babu wata alama da za a ba wannan tsarar." 13 Sai ya bar su ya sake shiga jirgin zuwa hayin tafkin. 14 A lokacin nan, almajiransa sun manta su dauki gurasa. Domin gurasa daya ce tak a garesu cikin jirgin ruwan. 15 Ya gargade su, "ku yi hattara da yisti na Farisawa da Yisti na Hirudus." 16 Almajiran suka fara tattaunawa a tsakaninsu, "Saboda ba mu da gurasa ne." 17 Yesu yana sane da wannan, sa'annan ya ce masu, "Don me kuke tattaunawa akan rashin gurasa? Har yanzu baku gane ba? Har yanzu ba ku da sane? Ko zuciyar ku ta duhunta ne?" 18 Kuna da idanu, ba ku gani? Kuna da kunnuwa, ba ku ji? Ba ku tuna ba? 19 Da na kakkarya gurasar a cikin mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka samu ragowa? Suka ce masa, "Goma sha biyu." 20 Kuma da na kakarya gurasa bakwai a cikin mutane dubu hudu, kwanduna nawa kuka dauka cike da ragowar? Suka ce masa, "bakwai." 21 Ya ce masu, "har yanzu baku gane ba?" 22 Sun zo Baitsaida. Mutanen wurin suka kawo masa wani makaho, sai suka roke shi ya taba shi. 23 Yesu ya rike hanun makahon, ya jagorance shi zuwa bayan kauyen. Da ya tofa yawunsa a idon mutumin, kuma ya dora hanunsa akan mutumin, sai ya tambaye shi "kana ganin wani abu kuwa?" 24 Ya daga ido sai ya ce, "ina ganin mutane na tafiya kamar itatuwa." 25 Ya sake dora masa hannu a idanuwansa, mutumin ya bude idanuwansa, sai ya fara ganin gari da kyau. 26 Yesu ya sallame shi zuwa gidansa nan take, ya ce masa, "kada ka shiga cikin garin" 27 Yesu da almajiransa sun shiga kauyukan kaisariya ta Filibi. Da suke kan hanya, sai ya tambaye su, "Shin wanene mutane ke ce da ni?" 28 Suka amsa masa suka ce, Yahaya mai Baftisma. Wasu suka ce, "Iliya". wadansu kuma, 'Daya daga cikin anabawa". 29 Ya tambaye su, "Amma me ku ke ce da ni?" Bitrus ya ce, "Kai ne Almasihu." 30 Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa game da shi. 31 Sai ya fara koya masu cewa, dole ne Dan Mutum ya sha wahala, dattawa da marubuta da manyan Firistoci zasu ki shi, a kuma kashe shi. Bayan kwana uku, zai tashi daga matattu. 32 Ya fadi wannan afili. Sai Birus ya ja shi gefe ya fara tsauta masa. 33 Amma Yesu ya juya ya dubi almajiransa sa'annan ya tsautawa Bitrus yana cewa, "Ka koma bayana Shaidan, domin kana kula da abubuwan mutane ne kawai, ba na Allah ba." 34 Sai ya kira taron jama'ar da almajiransa a wuri daya, ya ce masu, "Duk wanda yake so ya bini, dole ne ya musunci kansa, ya dauki giciyensa ya biyo ni. 35 Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi, amma duk wadda ya rasa ransa domina da kuma bishara zai cece shi. 36 Me zai amfani mutum idan ya sami dukan duniya sannan ya rasa ransa. 37 Me mutum zai bayar amaimakon ransa? 38 Duk wanda ke jin kunyata ko maganata a wannan mazinaciyar tsara mai zunubi, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa a lokacin da ya dawo cikin daukakar Ubansa da Malaiku masu tsarki."

Mark 8:1

Mahaɗin Zance:

Babban taron jama'an mutane da suke tare da Yesu suna jin yunwa. Yesu ya ciyes da su da gurasa biyer da kiman kifaye kafin shi da almajarensa suka shiga jirgi domin su je wani guri.

A lokacin can

Ana anfani da wannan kalman domin a gabatar da sabon abu a cikin labarin.

domin kwana uku kenan suna nan tare da ni babu abinci

"kwana uku kenan mutanen nan suna tare da ni, amma basu samu komai sun ci ba"

za su iya suma

AT: 1) zahiri, " za su iya rasa hankulan su nan da nan" ko 2) misalin mangana "za su iya rasa ƙarfin su."

A ina za mu iya samu gurasa a wannan jeji da zai ishi wadannan mutane haka?

Almajaren suna mamaki cewa Yesu yana tsamanin cewa zasu sami ishashen abinci. AT: "Wannan wurin yayi shuru harma babu wurin da zamu samu ishashen gurasa da zai kosher da mutane!"

gurasa

Gurasa dunkulen kunle ce da aka shirya ta a wata sifa sai a gasa shi.

Mark 8:5

Ya tambaye su

"Yesu ta ya tambaye almajarensa"

Ya umarci mutanen su zauna

Za a iya rubuta wannan kai saye a nassin. "Yesu ya umurci jama'an, 'Zauna a kasa'"

zauna

Yi anfani da kalmar kabilar ku domin nuna yadda mutane gargajiya suke cin abinci idan babu tabur, ko ta zama ko kwanciya.

Mark 8:7

Suna kuma da

Kalman nan "su" ana nufin Yesu da almajaren sa ne.

ya yi godiya akan su

"Yesu ya yi godiya akan ƙifin"

Suka ci

"Mutanen suka ci"

suka tara

"Almajaren suka tara"

ragowar, har sun cika kwanduna bakwai

Wannan na nufin raguwar ƙifi da gurasar bayan da mutane suka ci. AT: "raguwar gurasa da kuma ƙifin, wanda suka cika kwanduna baƙwai"

Ya sallame su

Zai zama da taimako a bayyana lokacin da ya sallame su. AT: " Bayan da suka ci, Yesu ya sallame su"

ya shiga jirgin ruwa da almajiransa zuwa shiyyar Dalmanuta

Zai zama da taimako a bayyana yadda suka kai Dalmanuta. AT: "suka yi ta yawo a tekun Galili a yankin Dalmanuta"

Dalmanuta

Wannan sunan wuri ne a kusa da arewa - kuɗu na tekun Galili.

Mark 8:11

Sun neme shi

"Suka tambaye shi akan"

alama daga sama

Suna neman alama da zai tabbatar masu cewa iko Yesu daga Allah ne. 1) Kalman nan "sama" kalma ce da ke nufin Allah. AT: "alama daga Allah" ko 2) kalman nan "sama" na nufin sarari. AT: "alama daga sarari"

a gwada shi

Farisiyawan sun yi kokari su gwada Yesu domin ya nuna masu ko shi daga Allah ne. AT: "ya tabbatar masu cewa Allah ne ya turo shi"

Ya ja numfashi da zurfi a ruhun sa

Wannan na nufin ya yi gardama ko ya ja numfashi da zurfi da mutane zasu iya ji. Mai yiwuwa ya nuna bacin ransa kwarai da Farisiyawan domin sunki su yarda da shi AT: [7:4]

cikin ruhun sa

"cikin sa"

Don menene wannan zamanin suna neman alama

Yesu yana masu faɗa. AT: "Kada wannan zamanin su nema alama"

wannan zamani

A lokacin da Yesu yayi magana game da "wannan zamani," ya nufin mutane da suke rayuwa a lokacin ne. A wurin Farisiyawan ma an haɗa da su. AT: "ku da mutanen zamanin nan"

ba alaman da za a nuna

AT: "ba zan nuna alama ba"

ya bar su, a shigo cikin ya kuma kwalekwalen

Almajaren Yesu sun tafi tare da shi. Za a iya bayyana wasu bayanin a fili. AT: "ya bar su, ya shiga jirgin tare da almajaren sa"

ɗayan gefen

Wannan ya yi bayanin tekun Galilin, wanda za a iya bayyana a fili. AT: a ɗayan gefe na tekun"

Mark 8:14

Yanzu

Ana amfani da wannan kalma domin a nuna alamar dakatawa a cikin ainhin labarin. Anan marubucin na ba da shahararen bayani game mantuwar da almajaren su ka yi su kawo gurasar.

kar ya fi gurasa daya

Kalma mara amfanin nan "kar ya fi" ana anfani da shi a nuna kalilar yawan gurasar da suke da shi. AT: "gurasa ɗaya kawai"

ku yi hattara da yisti

Waɗanan kala

yisti na Farisawa da Yisti na Hirudus.

A nan Yesu yana magana da almajarensa a hanyan da zasu gane ne. Yesu yana kwatanta koyaswan Farisawa da kuma Hiridus game da yistin.

Mark 8:16

domin bamu da gurasa ne

Za'a iya bayanin yanayin nan a fili. AT: "Idan sararin ta yi ja da asuba" ko "Idan sarari ta yi ja alokacin da rana tana tashiwa"

ba gurasa

"Kun san yadda ake kallon sarari kun kuma gane wace irin yanayi ce za ku samu"

Don me ku ke tunanin cewa ba za ku sami gurasa ba?

"Yesu yana magana game dazamanin sa ne. AT: "Ku muguye zamani maciya amana ne, wanda kuke neman alamu daga ni ... da za a baku" [12:39]

Har yanzu baku gane ba? Har yanzu ba ku da sane?

"saidai wancan alamar da aka ba wa annabi Yunusa."

Ko zuciyar ku ta duhunta ne?"

A nan "yisti" magana ce da take nufin mugun shawara da kuma koyeswar ƙarya. Za a yi bayanin maganar nan gaba [16:12].

Mark 8:18

Kuna da idanu, ba ku gani? Kuna da kunnuwa, ba ku ji? Ba ku tuna ba?

A nan "idanu" na nufin iko. AT: "inda dattawa, manyan firistoci da malaman attaura zasu ba shi wahala"

mutane dubu biyar

Wannan ƙarin magana ne da ke nufin "kada wannan ya faru." AT: "A' a" ko "Allah ya kiyaye wannan"

kwanduna nawa kuka samu ragowa

"sai ya guje wa sha'awan jikinsa" ko "sai ya bar sha'awar jikinsa"

Mark 8:20

Mutane dubu huɗu

Wannan na nufin mutane 4,000 da suka Yesu ya ciyes. AT: "mutane 4,000"

kwanduna nawa ne kuka dauka

"Ina gaya maku gaskiya." Wannan kalmomin ƙari ce ga abin da Yesu ya fada a gaba.

baku gane ba?

Dukkan maganganun nan na nufin mala'ikun ne.

Mark 8:22

Baitsaida

Wata gari ce wanda take kusa da Galili. [6:45]

don su taba shi

Idan ya zama dole, za'a iya faɗin wannan maganan a wani juyi. AT: "Domin Yahaya ya faɗa wa Hiridus cewa bai kama Hiridus ya ɗauki Hirudiya a matsayin matar sa ba."

da ya tufa yau a idanunsa ... ya tambaye shi

AT: "Bayan da mahaifuwarta ta umurce ta"

Mark 8:24

Ya kalli sama

"Mutumin ya kalle sama"

na gan mutane wanda suke tafiya kaman ittatuwa

A nan marubucin ya fara faɗa yadda Hiridus ya kashe Yahaya mai Baftisma. Waɗannan abubuwan sun faru a wasu lokatai kafin abun da ya faru a ayoyin da suka wuce.

Sai ya kuma

"Sai Yesu ya kuma"

sai mutumin ya buɗe idanunsa, sai idanun sa ya buɗe

Idon akwai bukata, za ka iya mika yadda abubuwan suka faru a 14:3-4, yadda take a UDB

Mark 8:27

Suka amsa shi suka ce

"Suka amsa shi, suna cewa"

Yahaya mai Baftisma

Almajarensa suka amsa shi suka ce ga abin da mutane na cewa game da kai. AT: "Wasu sun ce kai Yahaya mai Baftisma ne"

Sauran jama'a sun ce ... suaran jama'a

Suka ce kai ne Yahaya mai Baftisma.

Mark 8:29

Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa game da shi

Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa cewa shi Almasihu ne. AT: Yesu ya umurce su, kada ku gaya wa kowa cewa ni Almasihu ne'"

Mark 8:31

Ɗan Mutum

Wannan lakani ne mai muhinminci na Yesu.

dattawa da marubuta da manyan Firistoci zasu ki shi, Bayan kwana uku, zai tashi daga matattu

Wannan na faɗi cewa Hiridus yayi haka ne, domin ya umurce wasu ne suyi mashi. AT: "Hiridus ya umurce sojojin sa su kamo Yahaya mai Baftisma, su ɗaure shi, su kuma jefa shi a kurkuku"

Ya faɗa a fili

Filibus dan'uwan Hiridus ne. Hiridus ya ɗauki matar Filibus ta zama matar sa.

Ya fara kwaɓe su

AT: "a tsakanin baƙi da suka je bukin aihuwar"

Mark 8:33

Ka komo baya na Shaidan! Baka da huja

AT: "Bayan da mahaifuwarta ta umurce ta"

Ka komo baya na

"Ka yi nesa da ni"

ka biyo ni

Bin Yesu a nan na nufin zama ɗaya daga ciikin almajeren sa, AT: "zama almajerina " zama ɗaya daga ciikin almajerina"

sai ya musunci kansa

AT: " Rokon da tayi ya saka Sarki bakin ciki sosai"

daga giciyensa, ya biyo ni

AT: "ya umurce mutanen sa su yi abin da ta faɗa"

Mark 8:35

Domin duk wanda yake so

"Ga duk wanda yake so"

ransa

Wannan na nnufin rayuwa ta jiki da na ruhaniya.

domina da kuma bishara

"domina da kuma bishara." Yesu yana magana game da mutanen da suka rasa ransu domin sun bi shi da kuma bisharar sa. AT: "domin ya bi ni ya kuma yi wa waɗansu bishara"

Me zai amfani mutum idan ya sami dukkan duniya sannan ya rasa ransa

AT: "Idan ma mutum ya samu dukan duniya, ba riɓa bane idan ya rasa ransa."

ya sami dukkan duniya sannan ya rasa ransa

AT: "idan ya samu dukkan duniya ya kuma rasa ransa"

ya samu dukkan duniya

Kalman nan "dikkan duniya" wannan magana ne da yake nuna arziki. AT: ya samu dukkan abin da yake bukata"

rasa

A rasa abu ko a bar wani ya kwashe ta.

Me mutum zai bayar amaimakon ransa?

AT: "Babu wani abu da mutum zai iya bayar a maimakon rayuwar sa" ko "Ba wanda zai bayar da komai a maimakon rayuwar sa."

Me mutum zai bayar

A kabilar ka "bayarwa" na bukatar wani ya karbi abin da aka ba shi "Me mutum zai ba wa Allah"

Mark 8:38

kunya ta da kalmomi na

"kunya ta da sako ta"

a wannan mazinaciyar tsara mai zunubi

Yesu yayi magana game da wannan zamanin kamar "mazinaci ne," na nufin cewa ba suwa yin gaskiya cikin dagartakar su da Allah. AT: "a wannan zamanin mutane da suka yi zina suna kuma yin zunubi wa Allah" ko "a wannan zamani da mutane ba su da gaskiya suna kuma yin zunubi ga Allah"

a lokacin da ya dawo

"a lokacin da ya dawo"

ɗaukakar Ubansa

Idon Yesu ya dawo, zai samu ɗaukaka daya da Ubansa.

tare da mala'iku masu tsarki

"tare da mala'iku masu tsarki"

Chapter 9

1 Sai ya ce masu, "Hakika, ina gaya maku, akwai wasun ku anan da ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko." 2 Bayan kwana shida Yesu ya dauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kadai. Sai kamaninsa ya sake a gabansu. 3 Sai tufafinsa ya zama fari fat, yadda ba mai rinin da zai iya rininsa haka a duniya. 4 Sai Iliya da Musa suka bayyana gare su, suna magana da Yesu. 5 Sai Bitrus ya amsa ya ce, malam, bari mu da muke anan mu kafa bukka uku, daya ta ka, daya ta Musa, da ta Iliya, 6 Ya rasa abin da zai fada ne, don sun tsorota kwarai.) 7 Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga gajimaren, "ta ce Wannan shine kaunataccen Dana, Ku saurare shi. 8 Nan take da suka duba, ba su ga kowa ba, sai Yesu shi kadai. 9 Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai ya kwabe su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan da Dan Mutum ya tashi daga mattatu. 10 Sai suka bar zancen a tsakaninsu, amma suka tamabayi junansu "mene ne tashin matattu" ke nufi. 11 Suka tambaye shi yaya malaman attaura suka ce Iliya zai fara zuwa?" 12 Ya ce masu, laile ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwan. Don me a ka rubuta cewa Dan Mutum, zai sha wuya iri iri a kuma ki shi? 13 Amma ina gaya muku Iliya ya riga, ya zo, amma sun yi masa abin da suke so su yi kamar yadda littatafai suka yi magana a kansa." 14 Sa'adda suka dawo wurin sauran almajiran, suka ga taron jama'a masu yawa suna ta muhawara tare da manyan malaman attaura. 15 Da ganin sa, sai dukan taron yayi mamaki kwarai da gaske, suka dungumo wurinsa a guje, suna gaishe shi. 16 Ya tambayi almajiransa, "Wacce muhawara ce kuke yi da su?" 17 Daya daga cikin taron ya amsa masa"malam, ga shi na kawo maka dana don yana da beben aljani. 18 Duk lokacin da ya tasar masa yakan buga shi har kasa, na kuma yi wa almajiranka magana su fitar sun kasa. 19 Ya amsa masu ya ce ya ku mutanen zamaninnan marasa bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku ina jimrewa? ku dai kawo mini shi. 20 Sai suka kawo masa yaron. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan ya buge yaron jikinsa na rawa. Sai yaron ya fadi yana ta birgima, bakinsa yana kumfa. 21 Yesu ya tambayi mahaifin yaron, Tun yaushe wannan abu ya same shi? Mahaifin yaron ya ce tun yana karami. 22 Ya kuwa sha jefa shi a ruwa da wuta, don ya halakar da shi. Idan zaka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimakemu. 23 Yesu ya ce masa, "In zan iya? Ai dukan abu mai yiwuwa ne, ga duk wanda ya gaskata. 24 Nan da nan mahaifin yaron ya daga murya ya ce, Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata. 25 Da Yesu ya ga taron na dungumowa a guje, sai ya tsawata wa bakin aljanin ya ce masa, "kai, beben aljani na umarce ka, ka fita daga wannan yaron kar ka sake shigar sa. 26 Sai wannan aljanin ya daga murya ya fita ya rabu da wannan yaron. Sai yaro ya zama kamar mattacce, sai sauran mutanen suka ce, "Ai, yaron ya mutu. 27 Yesu ya kama hannunsa, ya daga shi, sai yaron ya mike tsaye. 28 Da Yesu ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi a kadaice, me ya sa muka kasa fitar da shi?" 29 Ya ce masu, "Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a." 30 Sai suka ratsa cikin Galili, amma ba ya son kowa ya san inda suke. 31 Da yake koyar da almajiransa, ya ce masu lokaci na zuwa da za'a ba da Dan mutum a hannun mutane, za su kuwa kashe shi, sa'adda aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi. 32 Amma fa ba su fahimci maganar ba, suna kuma jin tsoron tambayarsa. 33 Sai suka zo kafarnahum. A lokacin da ya ke cikin gida, ya tambayi Al'majiransa, Menene ku ke magana a kansa a hanya? 34 Amma suka yi shiru. don suna gardama da junansu akan hanya, a kan wane ne mafi girma. 35 Sai ya zauna, ya kira al'majiransa goma sha biyu, yace masu duk wanda ya ke so ya zama na fari, dole ya kankantar da kansa, sa'annan ya bautawa sauran duka. 36 Sai ya dauko karamin yaro a hannunsa ya sa shi a tsakiyarsu. Ya rumgome shi a kafadarsa ya ce masu. 37 Dukan wanda ya karbi dan karamin yaron nan a cikin sunana ni ya karba, kuma dukan wanda ya karbi wani, ni ya karba, bai kuma karbeni ni kadai ba, duk da wanda ya aiko ni." 38 Sai Yahaya ya ce masa, Malam mun ga wani yana fitar da aljanu da sunanka mun yi kokari mu hana shi domin ba ya tare da mu. 39 Sai Yesu ya ce masu ku kyale shi domin babu wanda zai yi irin wannan babban aikin, sa'annan ya fadi wasu maganganu mara sa kyau a kanmu. 40 Duk wanda ba ya gaba da mu, na mu ne. 41 Duk wanda ya ba ku ruwa ku sha domin kuna na Almasihu, gaskiya nake fada maku ba za ya rasa ladansa ba. 42 Amma duk wanda ya sa kananan nan tuntube, ya fi kyau a rataya masa dutsen nika a jefa shi a cikin teku. 43 Idan har hannun ka zai sa ka yi tuntube, zai fi kyau ka yanke shi. Domin zai fi kyau ka shiga aljanna da hannu daya da ka shiga jahannama da hannu biyu. 44 (Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa). 45 Idan kafarka za ta sa ka yi tuntube, ka yanke ta ka yar. Zai fi kyau ka shiga aljanna da kafa daya da ka shiga jahannama da kafa biyu. 46 (Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa). 47 Idan idonka zai sa ka yi tuntube, ka kwakule shi ka yar, domin gwamma ka shiga mulkin Allah da ido daya, da a jefa ka cikin wuta da idanu biyu. 48 Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa. 49 Domin da wuta za a tsarkake kowa. 50 Gishiri yana da kyau, amma idan ya rasa zakinsa, ta ya ya za ka sa shi yayi zaki kuma? Ku kasance da zaki, kuma ku yi zaman lafiya da kowa.

Mark 9:1

Mahaɗin Zance:

Yesu yana magana da mutane kuma almajaren sa suna ta kokarin bin sa. Bayan kwana ta shida, Yesu ya tafi tudu tare da almajarensa guda uku, inda watarana kamanin sa zai canza ba da daɗewa ba zuwa yanda zai zama a mulkin Allah.

Ya ce masu

"Yesu ya ce wa almajarensa"

mulkin Allah na zuwa da iko

Mulkin Allah da ke zuwa na nuna Allah da kansa a matsayin sarki. AT: "Yesu ya bayyana kansa a matsayin sarki da matukar iko"

su kadai

Marubucin ya yi amfani da kalmar aiki ne anan "da kansu" domin ya nanata cewa da Yesu, da Bitrus, daYakubu, da Yahaya da kansu ne suka hau tudun.

kamaninsa ya sake a gabansu

Da suka kalle shi, kamanin sa ya canza dabam kamar yadda yake da farko.

kamaninsa ya sake

AT: "Kamanin sa ya canza" ko "kamanin sa ya zama dabam"

a gaban su...

"a gaban su" ko "domin su gan shi a fili"

fari fat

"da haske." Tufafin Yesu yayi haske sosai har yana fitar da haske.

sosai

sosai ko fiye da take

yadda ba mai rinin da zai iya rininsa haka a duniya

AT: "yadda ba mai rinin da zai iya rininsa haka a duniya"

Mark 9:4

Iliya da Musa suka bayyana

Za iya zama da taimako a fadi ko wanene mutanen nan suke. AT: "annabi guda biyu da suka yi rayuwa a tun zamanin da suka wuce, Iliya da Musa suka bayyana"

Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu

"Bitru ya ce wa Yesu." Kalman nan "amsa" an yi amfani da shi domin a gabatar da Bitrus cikin labarin. Bitrus bai amsa tambaya ba.

bari mu da muke anan...

Kalman nan "mu" ba tabatar ba ko yana nufin Bitrus, ko Yakubu, da Yahaya ba ne, ko yana nufin duk wanda suke wurin wanda ya shafi Yesu, Iliya da Musa...

bukka

dan bukka da aka gyara domin a zauna ko a yi barci

Ya rasa abin da zai fada ne, don sun tsorota kwarai

Maganan nan ya ba da shahararen bayani game da Bitrus, Yakubu da kuma Yahaya.

sun tsorata

"sun tsorata kwarai" ko "sun ji tsoro sosai"

Mark 9:7

ya zo ya rufe

"ya bayana ya rufe"

aka kuma ji wata murya daga gajimaren

A nan "murya ta fito daga" kalma ce da take nuna wani na magana. Za a iya kuma bayana a filli wa ya yi maganan. AT: "Sai wani ya yi magana daga gajimaren" ko "Sai Allah ya yi magana daga gajimaren"

Wannan shine kaunataccen Dana, Ku saurare shi

Allah Uba y nuna kaunar sa wa "kaunataccen Ɗan sa" Ɗan Allah.

kaunataccen Ɗa

Wannan lakaɓi ce mai muhinminci na Yesu. Ɗan Allah.

da suka duba

A nan "suka" na nufin Bitrus, Yakubu da kuma Yahaya ne.

Mark 9:9

ya umurci su kada su gaya wa kowa ... sai bayan da Dan Mutum ya tashi

Wannan na nufin cewa ya na basu izini su faɗa wa mutane abin da suka gani bayan da ya tashi daga mattatu.

tashi daga mattatu ... tashiwa daga mattatu

"tashi daga cikin mattatu ... a tashi daga cikin mattatu." Wannan na magana game da zama rayayye kuma. Maganan nan "mattatu" na nufin "mattatun mutane" kuma magana ce na mutuwa. AT: "tashi daga mattatu ... tashiwa daga mattartu"

Sai suka bar zancen a tsakaninsu

A nan "suka bar zancen a tsakaninsu" karin magana ne da yake nufin basu faɗa wa kowa ba abin da suka gani. AT: "Sai basu faɗa wa kowa ba abin da suka gani"

Mark 9:11

Suka tambaye shi

"Kalman nan "su" na nufin Bitrus, Yakubu da kuma Yahaha.

don me malaman attaura suka ce Iliya zai fara zuwa?

Anabci ya faɗi cewa Iliya zai sake zuwa daga sama. Sai Mai ceto, wanda shine Ɗan Mutum, zai zo domin yayi mulki. Almajaren suka rikice cewa ta yaya Ɗan Mutum zai mutu ya kuma tashi. AT: "don me malaman attaura suka ce Iliya zai fara zuwa kafin Mai ceton ya zo? "Dubi:

Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwan

Bayan da faɗa haka, Yesu ya tabbatar da cewa Iliya zai fara zuwa.

Don me a ka rubuta ... a kuma ki shi?

Yesu yayi amfani da tambayan nan domin ya tunashe almajarensa cewa littafin ya koyas da cewa Ɗan Mutum zai sha wahala kafin a kashe shi. AT: "amma ina son ku duba abin da aka rubuta game da Ɗan Mutum.mlittafin ya faɗa cewa zai sha wahala sosai a kuma ki shi."

ki shi

AT: "mutane zasu ki shi"

suka yi duk abi da suke so su yi da shi

Zai zama da taimako a faɗi abiin da mutane suka yi wa Iliya. AT "dattawan mu sun yi mashi mugunta, kamar yadda suke so su yi"

Mark 9:14

Sa'adda suka dawo wurin almajaren

Yesu, Bitrus, Yakubu da Yahaya sun dawo wurin sauran almajaren wanda basu tafi tare da su zuwa tuɗun ba.

suka gan babban taro kewaye da su

"Yesu da almajaren nan guda uku sun ga babban taro kewaye da sauran almajaren"

mallaman attauran suna musu da su

Mallaman attaura suna musu da sauran almajaren da basu tafi tare da Yesu ba.

suka yi mamaki

Zai zama da amfani a faɗi dalilin da suka yi mamaki. AT: "suka yi mamaki cewa Yesu ya zo"

Mark 9:17

Yana da aljani

Wannan na nufin aljani ya shige yaron. "Yana da aljani" ko "aljani ya shige shi"

ya fito da kunfa a bakin sa

ɗaukar ruwa daga baki, ko figar ruwa yan kan iya saka damuwa wa mutum ta wurin numfashi ko haɗiye abu. Wannan na saka farin kumfa ya fita daga baki. Idan harshen ka tana da wata hanyar bayyana wannan, ka yi amfani da ita. "kunfa ya fito daga bakin sa"

ya kan zama da ƙauri

"ya kan zama da ƙauri" ko "jikin sa ya zama da ƙauri"

basu iya ba

Wannan na nufin almajaren basu iya fitad aljanin daga yaron ba. AT: "basu iya fitad da shi daga jikin sa ba"

Ya amsa masu

Kodashike, uban yaron ne ya tambaye Yesu, Yesu ya amsa wa dukkan jama'an"

Zamaninnan marasa bangaskiya

" ku zamaninnan marasa bangaskiya." Yesu ya kira taron haka, da ya fara amsa masu.

har yaushe zan kasance tare da ku? ... in yi hakkuri da ku?

Yesu yayi amfani da tambayoyin nan domin ya nuna damuwar sa. Tambayoyin nan suna da amsa iri daya. AT: "Na zama da damuwa kwarai domin rashin bangaskiyar ka!" ko "Rashin bangaskiyar ku ya ishe ni! Na rasa har yaushe ne zan hakkura da ku."

hakkura da ku

"jimre da ku" ko "hakkuri da ku"

Kawo mani shi

"Kawo mani yaron"

Mark 9:20

aljani

Wannan na nufin aljani AT: [Markus 9:17]

ɗaukar ruwa

Wannan yanayi ne da yake saka mutum ya rasa iko ga jikin sa, kuma jikin sa na kaɗewa da ƙarfi.

tun yana yaro

"Tun yana karamin yaro." AT: "Haka yake tun yana karamin yaro"

ji tausayi

"ji tausayi"

Mark 9:23

In zaka iya?

Yesu ya sake maimaita abin da mutumin ya faɗa masa. AT: "Ka ce mani "Idan zan iya'?" ko "Don me ka ce 'Idan zan iya'?"

Komai mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskanta

"Allah kan iya yin komai ga duk mutumin da ya ba da gaskiya gare shi"

ga wanda

"ga mutumin" ko "ma kowa"

ba da gaskiya

Wannan na nufi ba da gaskiya ga Allah. AT: "ba da gaskiya ga Allah"

A kore mini rashin bangaskiyata

Mutumin na rokon Yesu ya taiake shi ƙoran rashi bangaskiyar shi ya kuma inganta bangaskiyar sa. AT: "Ka taimake ni idan ban gaskanta ba" ko "Ka taimake ni in samu bangaskiya"

taron suna zuwa wurinsu a guje

Wannan na nufin mutanen suna zuwa inda Yesu yake a guje kuma taron na karuwa sosai.

Kai, beben da kuma kurman aljani

Kalman nan "bebbe" da kuma "kurma" za a iya bayyana ta. AT: "Kai aljani, kai da kake hana yaron yin magana da kuma ji"

Mark 9:26

ya daga murya

"aljanin ya daga murya"

ya tamke yaron da ƙarfi

"ya girgiza yaron da ƙarfi"

ya fito

Wannan na nufin cewa aljani ya fita daga yaron. AT: "fita daga yaron"

Yaron ya yi kaman wanda ya mutu

An kwatanta fuskar yaron da mattatcen mutum. AT: "Yaron ya yi kaman ya mutu" ko "Yaron ya yi kama da mattacen mutum"

sai yawancin mutane

AT: [9:26]

kama hannunsa

Wannan na nufin Yesu ya kama hannun yaron da hannuwansa. AT: "ya kama yaron a hannu"

daga shi sama

"ya taimake shi ya mike sama"

Mark 9:28

a kadaice

Wannan na nufin su kadai ne.

fitar da shi

"fitar da aljanin." Wannan na nufin fitar da aljanin daga jikin yaron. AT: "fitar da aljanin daga jikin yaron"

Irin wannan ba ya fita sai da addu'a

Kalman nan "ba ya" da kuma "sai da" kalmomi mara amfani ne. zai fi kyau ayi amfani da kalmomi masu amfani a wasu harshen. AT: "sai ta wurin addu'a ne kawai za a iya fitad da su"

Irin wannan

Wannan ya fasara aljanin. AT: "Irin wannan aljanin"

Mark 9:30

Suka fita daga wurin

"Yesu da almajaren sa sun bar wancan yankin"

suka ratsa

"suka bi ta" ko "suka wuce ta"

Da yake koyar da almajiransa

Yesu yana koyar da almajarensa a asirce, a nesa da jama'a. AT: "da yake koyar da almajaren sa a asirce"

Za a ba da Ɗan Mutum

AT: "Wani zai ba da Ɗan Mutum"

Ɗan Mutum

A nan Yesu yana kansa ne a matsayin Ɗan Mutum. Wannan laƙani ne mai muhinminci na Yesu. "Ni. Ɗan Mutum,"

a hannun mutane

A nan "hannu" kalma ce na iko na mutane. AT: "zuwa ga ikon mutane" ko "saboda mutane su iya samun iko a akan sa"

Idan aka kashe shi, bayan kwana ta uku zai

AT: "Bayan da aka kashe shi, kwana ta uku kuma ta wuce, ya"

suna jin tsoron tambayarsa.

Suna jin tsoro su tambaye Yesu mai nufin Maganar sa. AT: "suna jin tsoro sun tambaye shi mai yake nufi"

Mark 9:33

suka zo

"suka iso." Kalman nan "su" na nufin Yesu da almajaren sa ne.

ku ke magana a kai

"kuna magana da junan ku ne"

suka yi shiru

Sun yi shiru domin suna kunyan faɗa wa Yesu abin da suke magana akai. AT: "sun yi shiru domin sun ji kunya"

wanene mafi girma

A nan "mafi girma" na nufin "mai girma" a sakanin almajaren ne. AT: "wanene mafi girma a sakanin su"

Idan akwai wanda yake so ya zama na farko, sai dai ya zama na karshe duka

A nan, kalmomin nan "farko" do "karshe" ƙishiyar junan su ne. Yesu yayi magana game da zama "mafi girman" kaman na "farkon ne" sai kuma "mara muhinminci" kaman na "karshen ne." AT: " idan akwai wanda yake son Allah ya duba shi a matsayin babba a sakanin su, sai ya mayar da kansa mara muhinminci a duka"

a duka ... a duka

"a dukka mutane ... a dukkan mutane"

Mark 9:36

a sakanin su

" a cikin su." Kalman nan "su" na nufin jama'a ne.

Ya ɗauko su a hannuwar sa

Wannan na nufin ya ɗauko yaron ya kuma ajiye shi a cinyar sa.

ɗan yaron nan

"irin yaron nan"

a suna na

Wannan na nufin a yi abu domin kaunar Yesu. AT: "domin yana ƙauna ta" ko "domina"

wanda ya aiko ni

Wannan nufin Allah ne, wanda ya turo shi zuwa duniya. AT: "Allah, da ya turo ni"

Mark 9:38

Yahaya ya ce masa

"Yahaya ya ce wa Yesu"

fitar da aljani

"korar aljani." Wannan na nufin cire aljani daga jikin mutane. AT: "fitar da aljani daga jikin mutane"

a sunan ka

A nan "suna" ya shafe ikon Yesu da karfin sa. AT: "tawurin ikon sunan ka" ko "tawurin karfin sunan ka"

ba ya tare da mu

Wannan na nufin ba ya tare da almajaren. AT: "ba ya cikin mu" ko "ba ya tafiya tare da mu"

Mark 9:40

ba ya gaba da mu

"ba ya gaba da mu"

namu ne

AT: "yana kokarin yin nasara da mu ke"

Duk wanda ya ba ku ruwa ku sha domin kuna na Almasihu ne

Yesu yana magana akan ba wa wani ruwa, misali ne da yadda mutum ɗaya zai taimaki ɗan'uwan sa. Wannan magana ne na taimakon juna ta kowace hanya.

bai rasa ba

A wasu harshe, zai zama da tamako a yi amfani da kalmomi masu amfani. AT: "hakika, zai ƙarbi"

Mark 9:42

dutsen nika

babbar, mulmulin dutse da ake yin amfani a niƙa kwayar hatsi zuwa gari

Idan hannuwar ka zasu saka ka tuntuɓe

A nan "hannu"magana ne da yake nuna yin sha'awa ne da zai saka ka yin zunubi da hannun ka" AT: "Idan kana son ka yi zunubi da wani hannun ka"

ka shiga aljanna

"ka zama dungu sai ka shiga rai" ko "ka zama dungu kafin ka shiga rai"

ka shiga rai

A nan magana game da mutuwa sa'annan a fara rayuwan har'abada kammar shigar rai ne. AT: "ka shiga rai na har'abada" ko "ka mutu sa'annan ka fara rayuwa na har'anada"

aljanna

Rasa wani gaba na jiki domin an cire ta ko ta wurin jin ciwo. Anan na nufin rasa hannu ne. AT: "ba hannu" ko "hannun da babu"

zuwa cikin wuta mara kasuwa kuwa

"inda ba za a iya kashe wutan ba"

Mark 9:45

Idan ƙafan ka ya saka ka tuntuɓe

A nan kalman nan "kafa" magana ne da yake nuna yin sha'awa ne da zai saka ka yin zunubi da ƙafafun ka, kamar inda bai kamata ka je ba. AT: "Idan kana son ka yi zunubi da wani ƙafafun ka"

ka shiga da gurgunta

"ka zama gurgu sa'a nan ka shiga rayuwa" ko "ka zama gurgu kafin ka shiga rai"

gurgu

"rashin iya tafiya da kyau." A nan na nufin rashin iya tafiya domin babu wani ƙafa. AT: "babu ƙafa" ko "babu wani ƙafa"

wurga cikin wuta

AT: "da Allah ya wurga ka cikin wuta"

Mark 9:47

Idan idon ka na sa ka tuntuɓe, ka ƙwaƙule shi

A nan kalmar "ido" 1) kalma ce da yake saka mutum sha'awar zunubi na kallo. AT: "Idan kana so ka yi wani abun zunubi ta wurin kallo, ka ƙwaƙule idanun ka" ko 2) sha'awar yin zunubi domin abin da ka kalla. AT" Idan kana so ka yi zunubi domin abin da ka kalla, ka ƙwaƙule idanun ka"

ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya da idon ka biyu

Wannan na nufin kamanin jikin mutum idan ya mutu. Mutum ba ya ɗaukan jikin sa tare da shi zuwa aljanna. AT: "ka shiga zuwa mulkin Allah bayan da ka yi rayuwa a duniya da ido ɗaya da ka yi rayuwa a duniya da idanu biyu"

a wurga cikin wuta

AT: "da Allah ya wurga ka cikin wuta"

inda tsutsotsi basu mutuwa

AT: "inda tsutsotsi masu cin mutane basu mutuwa"

Mark 9:49

Da wuta za a tsarkake kowa

AT: "Allah zai tsarkake kowa da wuta" ko "Kamar yadda wuta na tsarkake haɗaya, Allah zai tarkake kowa tawurin barin su su sha wuya"

za a tsarkake da wuta

A nan "wuta" magana ce na shan wuya, kuma saka wa mutane gishiri kalma ce na tsarkakewa. Hakannan "za a tsarkake su da wuta" magana ce na tsarkakewa ta wurin shan wuya. AT: "za a mayad da shi da tsabta cikin wutar mai wahala" ko "za a sha wuya domin a tsarkake a matsayin hadaya shine tsarkakewa da gishiri"

zakinsa

"zakinsa"

ta yaya za a samu ɗanɗanon ta kuma

AT: "ba za ka iya samu ɗanɗanon ta kuma ba"

ɗanɗanon ku

"ɗanɗanon kuma ba"

Ku ksance da gishiri a zuciyar ku

Yesu yana magana akan yi wa juna abubuwa masu kyau kamar abubuwa masu kyau gishiri ne da mutane ke gada. AT: Ku yi wa kowa kirki, kamar gishiri da yake kara ɗanɗano wa abinci"

Chapter 10

1 Yesu ya bar wannan wurin, ya tafi yankin Yahudiya, wajen hayin kogin Urdun. Sai jama'a suka je wurinsa. Ya ci gaba da koya masu, kamar yadda ya zama al'adarsa. 2 Sai Farisawa su ka zo wurinsa, su ka ce, "dai dai ne mutum ya saki matarsa?" Wannan tambaya sun yi ta ne domin su gwada shi. 3 Ya amsa ya ce, menene Musa ya umarce ku? 4 Suka ce, "Musa ya yarda mutum ya rubuta takardar saki ga matarsa, ya sallameta ta fita." 5 "Domin taurin zuciyarku ne ya rubuta maku wannan dokar," Yesu ya ce masu. 6 Amman tun daga farkon halitta, 'Allah ya halicci namiji da ta mata.' 7 Domin wannan dalilin ne mutum zai rabu mahaifinsa da mahaifiyarsa ya mannewa matarsa. 8 Su biyu kuwa sun zama jiki daya, ba biyu ba, 9 Saboda haka abinda Allah ya hada kada mutum ya raba." 10 Lokacin da suke cikin gida, sai almajiransa suka sake tambayarsa akan wannan magana. 11 Ya ce da su. Dukan wanda ya saki matarsa ya kuma auro wata matar yayi zina da ita kenan. 12 Haka nan duk matar da ta saki mijinta ta auri wani ta yi zina da shi kenan." 13 Mutane suka kawo masa 'ya'yansu kanana don ya taba su, sai almajiransa suka kwabe su. 14 Da Yesu ya gani, ya ji haushi, ya ce masu. Ku bar yara kanana su zo wurina, kada ku hana su domin mulkin Allah na irinsu ne. 15 Gaskiya na ke fada maku duk mutumin da bai karbi mulkin Allah kamar karamin yaro ba, babu shakka ba zai shiga mulkin Allah ba. 16 Sai ya rungume su ya sa masu albarka. 17 Lokacin da ya fara tafiya, sai wani mutum ya rugo wurinsa, ya durkusa a gabansa. Ya tambaye shi, yace ya "Malam managarci, me zan yi domin in sami rai na har abada?" 18 Amma Yesu ya ce masa. Don me ka ke kira na managarci? Babu wani managarci sai dai Allah kadai. 19 Kasan dokokin. Kada ka yi kisan kai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar zur, kada ka yi zamba, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka." 20 Sai mutumin ya ce masa Malam ai na kiyayye duk wadannan abubuwa tun ina yaro. 21 Yesu ya dube shi duban kauna ya ce masa. Abu daya ka rasa. Shi ne ka je ka sayar da duk mallakarka ka ba mabukata, za ka sami wadata a sama. Sa'annan ka zo ka bi ni. 22 Da ya ji haka sai ransa ya baci, ya tafi yana bakin ciki, don shi mai arziki ne kwarai. 23 Yesu ya dubi almajiransa ya ce. "Yana da wuya masu arziki su shiga mulkin Allah!" 24 Almajiransa suka yi mamakin maganarsa. Sai Yesu ce masu, ya ku ya'ya'na yana da wuya kamar me a shiga mulkin Allah. 25 Zai zama da sauki ga rakumi yabi ta kafar allura da mai arziki ya shiga mulkin Allah. 26 Sai suka cika da mamaki sosai, su kace wa juna, "to idan haka ne wanene zai iya tsira kenan?" 27 Yesu ya dube su ya ce masu. Ga mutane a bu ne mai wuyar gaske, amma a wurin Allah komai yiwuwa ne. 28 Bitrus ya ce masa, "to gashi mu mun bar kome, mun bika". 29 Yesu ya ce. Gaskiya na ke fada maku, babu wanda zai bar gidansa, da yan'uwansa maza da mata, da mahaifiya ko mahaifi, ko 'ya'ya ko gona, saboda da ni da kuma bishara, 30 sa'annan ya rasa samun nikinsu dari a zamanin yanzu, na gidaje, da yan'uwa mata da maza' da iyaye mata da 'ya'ya da gonaki, game da tsanani, a duniya mai zuw kuma ya sami rai madawwami. 31 Da yawa wadanda suke na farko za su koma na karshe, na karshe kuma za su zama na farko. 32 Suna tafiya Urushalima, Yesu kuwa na gabansu. Almajiransa sun yi mamaki, mutane da ke biye da su kuwa sun tsorata. Yesu kuwa ya sake kebe sha biyun nan, ya fara fada masu abin da zai same shi. 33 "Kun ga, za mu Urushalima za a bada Dan mutum ga manyan Firistoci da malan Attaura, za su kuma yi masa hukuncin kisa su kuma bada shi ga al'ummai. 34 Za su yi masa ba a, su tofa masa yau, su yi masa bulala, su kashe shi, bayan kwana uku kuwa zai tashi." 35 Yakubu da Yahaya, 'ya'yan Zabadi, suka zo wurin sa, suka ce, "Malam muna so kayi mana duk abin da mu ka roke ka" 36 Ya ce masu. "Me ku ke so in yi maku?" 37 Suka ce, "ka yardar mana, a ranar daukakarka, mu zauna daya a damanka, daya kuma a hagunka." 38 Yesu ya ce masu. "Ba ku san abinda ku ke roka ba. Kwa iya sha daga kokon da zan sha? Ko kuma za a yi maku baftismar da za a yi mani?" 39 Suka fada masa, "Zamu iya." Yesu ya ce masu, "kokon da zan sha, da shi zaku sha, baftismar da za ayi mani kuma da ita za a yi maku." 40 Amma zama a damata, ko a haguna, ba na wa ba ne da zan bayar, ai na wadanda a ka shiryawa ne." 41 Da sauran almajiran nan goma suka ji, suka fara jin haushin Yakubu da Yahaya. 42 Yesu kuma ya kira su wurinsa ya ce masu, "kun sani wadanda aka san su da mulkin al'ummai sukan nuna masu iko, hakimansu kuma sukan gasa masu iko. 43 Amma ba haka zai kasance a tsakaninku ba. Duk wanda ya ke son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku. 44 Duk wanda ya ke so ya shugabance ku lalle ne ya zama bawan kowa. 45 Saboda haka ne Dan mutum ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi yayi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda da mutane da yawa." 46 Sa'adda suka iso Yariko, yana fita daga Yariko kenan, shi da almajiransa, da wani babban taro, sai ga wani makaho mai bara, mai suna Bartimawas dan Timawas yana zaune a gefen hanya. 47 Da ya ji Yesu Banazare ne, ya fara daga murya yana cewa, "Ya Yesu, Dan Dauda, kaji tausayina" 48 Mutane da yawa suka kwabe shi, cewa yayi shiru. Sai ya kara daga murya kwarai da gaske, yana cewa, Ya Dan Dauda ka yi mani jinkai, ka ji tausayina!" 49 Yesu ya tsaya ya ce, ku kirawo shi. Su kuwa suka kirawo makahon suka ce masa. "Albishrinka, ta so! Yana kiranka." 50 Makahon ya yar da mayafinsa, ya zaburo wurin Yesu. 51 Yesu ya tambaye shi, ya ce, "me ka ke so in yi maka?" Makahon ya ce, "Malam in sami gani." 52 Yesu ya ce masa. "Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai." Nan take idanunsa suka bude, ya bi Yesu, suka tafi tare.

Mark 10:1

Mahaɗin Zance:

Bayan da Yesu da almajiransa sunka bar Kafarnahum, Yesu ya tunashe Farisiyawan da kuma almajiransa, abin da Allah ke bukata a cikin aire da kuma kashe aure.

Yesu ya bar wannan wurin

Almajiran Yesu suna cikin tafi tare da shi. Suna koƙarin barin Kafarnahum. AT: "Yesu da almajiransa sun bar Kafarnahum"

wajen hayin Kogin Urdun

"zuwa kasar da ke wajen hayin Kogin Urdun" ko "zuwa gabacin Kogin Urdun"

Ya cigaba da koya masu

Kalman nan "su" na nufin taron.

kamar yadda ya zama al'adarsa

"zama al'adarsa" ko "ya saba yi"

me Musa ya umarce ku

Musa ya ba wa kakaninsu doka wanda yakamata su bi. AT: "Me Musa ya umuce kakaninku game da wannan"

takarda na kisan aure

Wannan wata takardar da ta bayana cewa macen ba matan shi bane kuma.

Mark 10:5

"Domin ... wannan dokar," Yesu ya ce masu. Amman

A wasu harsuna, mai magana ba ya katse maganar da aka ruwaito don a faɗa ko wa yake magana. Maimakon haka su kan faɗi wanda ke magana da farko ko a karshe maganar da aka ruwaita. AT: "Yesu ya ce masu, 'domin ... wannan dokar. Amma"

"Domin taurin zuciyarku ne ya rubuta maku wannan dokar

Tun da, Musa ya rubuta wannan dokar ga Yahudawa da zuriyarsu saboda sun taurare zukatansu. Yahudawan a lokacin Yesu su ma sun taurare zukatansu, saboda haka Yesu haɗa da su ta wurin yin amfani da kalman"ku." AT: "domin kakaninku da ku duk kuna da taurin zuciya shi ya sa ya rubuta wannan dokar"

taurare zukatanku

A nan "zukatan" na nufin cikin mutum ko runaninsa. Maganan nan "taurare zukatan" na nufin "taurin kai." AT: "taurin kanku"

Allah ya halicci su namiji da ta mata

Yesu ya ruwaito wannan daga abin da Allah ya faɗa cikin littafin Farawa.

Allah ya halici su

"Allah ya halicci mutane"

Mark 10:7

Saboda wannan dalili ... jiki ɗaya

Yesu ya cigaba da ruwaito da abin da Allah ya faɗa a cikin littafin Farawa.

Saboda wannan dalili

"Saboda haka" ko "saboda wannan"

ya mannewa matarsa

"haɗuwa da mata tasa"

sun zama jiki ɗaya, ba biyu ba

Wannan na misalta ɗayantakan su a matsayin miji da mata. AT: "mutane biyun suna kamar mutum ɗaya" ko "yanzu kam su ba biyu bane amma tare sun zama jiki ɗaya"

Saboda haka abinda Allah ya haɗa kada mutum ya raba

Maganan nan "abin da Allah ya haɗa" na nufin masu aure. AT: "Saboda haka, dashike Allah ya haɗa miji da mace, to, kada wani ya raba"

Mark 10:10

Lokacin da suke

"Sa'adda Yesu da almajiransa suke"

suke cikin gidan

Almajiran Yesu suna magana da shi a ɓoye. AT: "suke su kaɗai a cikin gidan"

sake tambayarsa game wannan

Kalman nan "wannan" na nufin magnan da Yesu ya yi da Farisiyawan game da kashe aure.

Duka wanda

"kowa"

yayi zina da ita kenan

A nan "ita" na nufin macen da ya aure ta da farko.

ta yi zina

A wannan yanayi ta yi zina ga mijinta na dă. AT: "ta yi zina ga shi" ko "ta yi zina ga mutum na farkon"

Mark 10:13

Sai suka kawo

"Mutane suna kawo." Wannan abin da ya faru nan gaba a labarin ne.

don ya taɓa su

Wannan na nufin cewa Yesu zai taɓa su da hannunsa ya sa masu albarka. AT: "don ya taɓa su da hannunsa ya kuma sa masu albarka. ko "ya sa hannunsa a kansu ya albarkace su"

sauta masu

"sauta wa mutane"

Yesu ya gan su

Kalman nan "su" na nufin almajiran suna kwaɓen mutane wanda suke kawo 'ya'yan wurin Yesu.

ba ji daɗi ba

"ya yi fushi"

Bar 'ya'ya kanana su zo wurina, kada ku hana su

Waɗannan maganganu biyu suna da ma'ana kusan iri ɗaya, an maimaita ta don nanaci. A wasu harsuna ba abune mai yiwuwa ba a nanata wannan a wanta hanya. AT: "Ku tabbata kun bar 'ya'ya kanana su zo wurina"

kada ku hana su

A wasu harsuna ba abune mai yiwuwa ba a yi amfani da magana da ke bada tabbaci. AT: "bar"

gama mulkin Allah na mutane ne kamarsu

Mulkin ba mutane ne, na nufin mulkin har da su ma. AT: "mulkin Allah na haɗe da mutane kamar su" ko "domin mutane kamarsu sune kaɗai ke na mulkin Allah"

Mark 10:15

duk wanda bai karɓi ... yaro ba babu shakka ba zai shiga

"duk wanda bai karɓi ... yaro, babu shakka ba zai shiga ba

kamar karamin yaro

Yesu ya kwatanta yadda ta zama tilas mutane su karɓi mulkin Allah da yadda kananan yara sun karɓi ta. AT: "daidai kamar yadda yaro zai yi"

ba zai karɓi mulkin Allah

"ba zai yi na'am da Allah a matsayin sarki ba"

babu shakka ba zai shiga ta

Kalman nan "ta" na nufin mulkin Allah.

Sai ya ɗauki yara a hannunsa

"ya rungume yara"

Mark 10:17

găji rai madawwami

A nan mutumin ya yi maganar "karɓi" sai kace "gădo." Wannan na nanata muhimmancin karɓar. Haka kuma, "găji" anan ba ta nufin cewa dole wani ya mutu tukuna. AT: "karɓi rai madawwami"

Don me ka ke kira na managarci?

Yesu ya yi wannan tambayar don ya tunashe mutumin cewa ba wani mutum da ke nagari kamar yadda Allah yake. AT: "Ba ka fahimci abin da kake faɗi ba a sa'adda ka kirani managarci."

managarci sai dai Allah kaɗai

"managarci. Allah kaɗai shine managarci"

kada ka yi shaidar zur

"kada ka yi wa wani shaidar zur" ko "kada ka yi ƙarya game da wani a kotu"

Mark 10:20

Abu daya ka rasa

"Akwai abu ɗaya da ka rasa." A nan "rasa" na nufin bukatan yin wani abu. AT: "Abu ɗaya kana bukata ka yi" ko "Akwai abu ɗaya da ba ka yi ba"

ka ba da ita ga matalauta

A nan kalman nan "ita" na nufin abubuwan da ya sayar. Wannan na nufin kuɗin da ya karɓa a sa'ad da ya sayar da su. AT: "ba da kuɗin ga matalauta"

matalauta

Wannan na nufn mutane matalauta. AT: "mutane matalauta"

mallakarka

arziki, abubuwa masu daraja

don shi mai arziki ne

"na da abubuwa masu yawa"

Mark 10:23

Yana da wuya

"Yana da matuƙar wahala"

Yesu ya ce masu kuma

"Yesu ya ce wa almajiransa kuma"

'ya'ya, yana da

"'ya'yana, yana da." Yesu yana koya masu daidai kamar yadda uba zai koyawa 'ya'yansa. AT: "Abokaina, yana da"

zai zama da wuya

"yana da matuƙar wuya"

zai zama da sauki ... mulkin Allah

Yesu ya yi amfani da wannan don ya nanata yadda yake da matuƙar wahala mutane masu arziki su shiga mulkin Allah.

yana da sauki rãƙumi

Wannan na maganar yanayi da ba zai taba yiwuwa ba. In ba za ku iya bayana wanna a harshenku ba, to, to ana iya rubuta shi a matsayin misali. AT: "zai zama da sauki rãƙumi"

kafar allura

"ramin allura." wannan na nufin wata karamar rami a ƙarshen alluran dinki wanda zare ka wuce ta ciki.

Mark 10:26

suka cika

"Almajiran sun yi"

wanene zai iya tsira kenan?

AT: "In haka ne, to ba wanda zai tsira!"

Ga mutane abu ne mai wuyar gaske, amma ba a wurin Allah ba

Ana iya bayana abin da aka fahimta. AT: "Ba shi yiwuwa mutane su cece kansu, amma Allah zai iya ceton su"

duba, mun bar kowane abu, mun bi ka

A nan kalman nan "duba" an yi amfani da ita don a jawo hankali ga kalmomin da ke zuwa nan gaba. Abu makamancin haka ana iya bayana shi a wata hanya. AT: "Mun bar kowane abu, mun bi ka"

bar duk abubuwa

bar kowane abu a baya"

Mark 10:29

babu wanda zai bar ... sa'annan ya rasa samun

AT: "duk wanda ya bar ... zai sami"

ko gona

"ko fili" ko "ko gonar da ke nasa"

saboda da ni

"sabili da ni" ko "don ni"

da kuma bishara

"don shelar bishara"

wannan duniya

"wannan rayuwa" ko "wannan zamani"

da yan'uwa mata da maza' da iyaye mata da 'ya'ya

Daidai kamar jeri abubuwan da ke cikin aya 29, wannan na bayana iyali gabakiɗaya. Kalman nan "uba" ba a ambata shi a aya 30 ba , amma wannan bai canza ma'anar ba.

game da tsanani, a duniya mai zuwa kuma ya sami rai madawwami

Ana iya sake rubuta wannan domin zance da ke wannan suna "tsanani" a bayana shi cikin aikatau "tsanantawa." Saboda jimlar ta yi tsayi kuma da wuyar fahimta, maganan nan"zai sami" ana iya maimaita shi. AT: "kuma ko mutane sun tsananta masu, a duniyan nan mai zuwa, za su sami rai madawwami"

duniyan nan mai zuwa

"a duniyan da ke nan gaba" ko "a nan gaba"

na farko za su zama na karshe, na karshe kuma za su zama na farko

A nan kalmomin nan "farko" da "ƙarshe" sun sha bam-bam da juna. Yesu yana magana game da zama "muhimmanci" a matsayin "farko" da kuma zama "marasa muhimmanci" a matsayin "ƙarshe." AT: "da ke da muhimmanci za su zama marasa muhimmanci, waɗanda basu da muhimmanci za su zama masu muhimmanci"

na karshe kuma farko

Maganan nan "na ƙarshe" na nufin mutanen da ke na "ƙarshe." Kuma, ana iya sa kalman aikatau da an fahimce ta a wannan magana. AT: "waɗanda ke ƙarshe za su zama farko"

Mark 10:32

Suna tafiya ... Yesu kuwa ya tafi gaba kafin su

"Yesu da almajiransa suna tafiya kan yanyan ... Yesu kuma na can gaban almajiransa"

waɗanda ke biye

"waɗanda ke biye da su." Wasu mutane suna tafiya biye da Yesu da almajiransa.

Gani

"Duba" ko "kassa kunne" ko "sa hankalin ku ga abin da zan gaya maku"

za a bada Ɗan Mutum

Yesu na magana game da kansa. Ana iya bayana wannan a fili. AT: "Ni, Ɗan Mutum, za a"

za a bada Dan mutum ga

AT: "wani zai bashe Ɗan Mutum ga" ko "za su mika Ɗan Mutum ga"

za su kuma yi masa hukuncin kisa

kalman nan "su" na nufin firistoci da malaman attaura.

bada shi ga Al'ummai

"sa shi karƙashin mulkin Al'ummai"

Za su yi masa ba'a

"Mutane za su yi masa ba'a"

su kashe shi

"kashe shi"

zai tashi

Wannan na nufin tashiwa daga mattattu. AT: "zai tashi daga mattattu"

Mark 10:35

mu ... mu

Waɗannan kalmomi na nufin Yakub da Yahaya ne kawai.

cikin ɗaukakarka

"sa'adda an ɗaukaka ka." Maganan nan "cikin ɗaukakarka" na nufin sa'adda an ɗaukaka Yesu a kuma yi mulki bisa mulkinsa. AT: "sa'adda kana mulki a bisa mulkin ka"

Mark 10:38

Ba ku san

"Ba ku fahimci"

Kwa iya sha daga ƙoƙon da zan sha

A nan "koko" na nufin wahalar da Yesu za sha. An yi maganar shan wahala sau da dama kamar sha daga ƙoƙo. AT: "sha ƙoƙon wahala da zan sha" ko "sha daga cikin ƙoƙon wahala da zan sha daga ciki"

za ku jimre baftismar da za a yi mani

A nan "baftisma" da kuma yin baftisma na wakilcin wahala. Kamar yadda ruwa ke rufe mutum a lokacin baftisma, wahala za ta shafe Yesu. AT: "jimre baftismar wahalar da zan sha"

Ma iya

Amsawarsu ta wannan hanya na nufin cewa sun za su iya sha da cikin ƙoƙon ɗaya su kuma jimre baftisma ɗayan.

za ku sha

"ku ma za ku sha"

Amma zama a damata, ... ba na wa ba ne da zan bayar

"Amma ba ni bane zan bar mutane su zauna a hannu dama na ko kuwa hagu na"

amma ga waɗanda aka shirya ta

"Amma waɗannan wurare ga waɗanda aka shirya wa ne." Kalman nan "ta" na nufin wurare a hannun damansa da hagunsa.

aka shirya

AT: "Allah ya shiya ta" ko "Allah ya shirya su"

Mark 10:41

suka ji wannan

Kalman nan "wannan" na nufin Yakub da Yahaya suna roƙo su zaun a hannun dama da hagun Yesu.

Yesu ya kira su

"Yesu ya kira almajiransa"

waɗanda aka san su da mulkin al'ummai

Ma'ana mai yiwuwa na kamar haka 1) mutane a takaice na duban waɗanda mutane a matsayin masu mulkin al'ummai. AT: "waɗanda mutane ke duba a matsayin masu mulkin Al'ummai" ko 2) Al'ummai na duban waɗannan mutane a matsayin masu mulkinsu. AT: "waɗanda Al'ummai na tunanin cewa sune masu mulkinsu"

nuna iko

mulki ko iko bisa

gasa masu iko

"nuna masu iko." Wannan na nufin cewa suna nuna ko amfani da ikonsu a yadda bai kamata ba.

Mark 10:43

Amma ba haka zai kasance a tsakaninku ba

Wannan na kai ga aya da ke a baya game da masu mulkin Al'ummai. Anan iya bayana wannan a fili. AT: "Amma kada ku zama kamar su"

zama babba

"a girmama shi"

zama farko

Wannan na nufin zama mafi muhimmanci. AT: "zama mafi muhimmanci"

Gama Ɗan Mutum bai zo domin a bauta masa ba

AT: "Gama Ɗan Mutum bai zo don ya sa mutane su bauta masa ba"

bauta masa ba, amma don ya bauta

"mutane su bauta masa ba, amma ya bauta wa mutane"

gama dayawa

"gama mutane dayawa"

Mark 10:46

Bartimawas ɗan Timawas, makaho ne shi mai bara

"makaho mai bara mai suna Bartimawas ɗan Timawas." Bartimawas shien sunan mutumin. Timawas kuma sunan mahaifinsa ne.

Da ya ji Yesu

Bartimawas ya ji mutane suna cewa Yesu ne. AT: "Sa'adda ya ji mutane suna cewa ai Yesu ne"

Ɗan Dauda

An kira Yesu Ɗan Dauda saboda shi daga zuriyar Sarki Dauda ne. AT: "Kai da kake Mai Ceto daga zuriyar Sarki Dauda"

da yawa sun sauta

"Mutane da ya sun sauta"

kwarai da gaske

"sosai"

Mark 10:49

umurta a kirawo shi

AT: "umurci sauran su kira shi" ko "umurce su, 'ku kira shi ya zo nan.'"

Sun kira

Kalman nan "su" na nufin taron.

kada ka ji tsoro

"Ka karfafa" ko "Kada ka firgita"

Yana kiranka

"Yesu yana kiranka"

tashi tsaye

"ya zabura"

Mark 10:51

amsa masa

"makahon ya amsa"

in sami gani

"in iya gani"

bangaskiyarka ta warkar da kai

An rubuta wannan magana haka don a nanata bangaskiyar mutumin. Yesu ya warkar da mutumin don ya gaskanta cewa Yesu zai iya warkar da shi. Anan iya bayana wannan a fili. AT: "Ina warkar da kai don ka bada gaskiya a gare ni"

ya bi shi

"ya bi Yesu"

Chapter 11

1 Da suka kusa Urushalima, kusa da Betafaji, da Betanya, wajen dutsen zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu 2 ya ce masu, "ku shiga kauyen can kusa da mu. Da zarar kun shiga za ku ga aholaki a daure, wanda ba a taba hawa ba. Ku kwance shi, ku kawo mani. 3 In wani ya ce maku, "Don me kuke haka? ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsa, zai kuma komo da shi nan da nan."' 4 Sai suka tafi, suka tadda aholakin a daure a kofar gida a bakin hanya, suka kwance shi. 5 sai wadanda suke tsaye a gun suka ce masu, "Don me kuke kwance aholakin nan? 6 Suka fada masu abinda Yesu yace, sai suka kyale su suka tafi. 7 Almajiran nan biyu suka kawo wa Yesu aholakin, suka shimfida mayafansu a kai, sai ya hau. 8 Sai mutane da yawa suka shimfida mayafansu a hanya, wadansu kuma suka baza ganyen da suka yanko daga filayen. 9 Wadanda suke gaba da shi da wadanda ke bin bayansa suka yi sowa suna cewa, "Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji. 10 Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na Ubanmu Dawuda! Dukaka a cikin sama!" 11 San nan Yesu ya shiga Urushalima, ya shiga Haikalin. Sai ya dudduba komai, da magariba ta yi, ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyu nan. 12 Kashe gari, suka tashi daga Betanya, sai ya ji yunwa. 13 Da ya hango itacen baure mai ganye daga nesa sai ya je ya ga ko za sami 'ya'ya. Da ya iso wurinsa bai ga komai ba sai ganye, don ba lokacin 'ya'yan baure ba ne. 14 Sai ya ce wa bauren, "Kada kowa ya kara cin "ya'yanka har abada!" Almajiransa kuwa sun ji maganar. 15 Suka iso Urushalima, da shigar su, ya kori masu saye da sayarwa, ya watsar da taburan 'yan canjin kudi, da kujerun masu sayar da tantabaru. 16 Ya hana kowa ya dauki wani abu da za a i ya sayarwa a cikin haikalin. 17 Sai ya koyar da su cewa, "Ashe ba rubuce yake ba, "Za a kira gidana gidan addu'a na dukan al'ummai? Amma ku kun mayar da shi kogon yan fashi". 18 Da mayan Faristoci da marubutan attaura suka ji maganar da ya yi, sai suka nami hanyar da za su kashe shi. Amma suka ji tsoronsa domin dukkan taron na mamakin koyarwarsa. 19 Kowace yamma kuma, sukan fita gari. 20 Da safe suna wucewa, sai suka ga bauren nan ya bushe. 21 Bitrus kuwa ya tuna ya ce "Malam, dubi! Baurenan da ka la'anta ya bushe." 22 Yesu ya amsa masu ya ce, "ku gaskata da Allah." 23 Hakika, ina gaya maku, duk wanda ya ce wa dutsen nan tashi ka fada cikin tekun', bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata haka kuwa zai faru, haka kuwa Allah zai yi. 24 Saboda haka ina dai gaya maku, komai kuka yi addu'a kuka roka, ku gaskata cewa samamme ne, zai kuma zama naku. 25 Duk sa'add da kuke addu'a ku gafarta wa wadanda suka yi maku laifi, domin Ubanku shima zai gafarta maku naku laifi." 26 (Amma in baku gafartawa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma da ke sama ba zai gafarta maku ba.) 27 Da suka sake dawowa Urushalima. Yasu na tafiya cikin haikali, sai manyan firistoci, da marubuta, da dattawa suka zo wurinsa, 28 suka ce masa, "Da wanne iko kake yin wadanan abubuwa? Ko kuwa wa ya ba ka ikon yinsu?" 29 Sai Yesu ya ce masu, "Zan yi maku wata tambaya. ku ba ni amsa, ni kuwa zan gaya maku ko da wanne iko ne nake yin wadannan abubuwan. 30 Baftismar da Yahaya yayi, daga sama take ko kuwa daga mutum take? ku bani amsa". 31 Sai suka yi mahuwara da juna, suka ce, "in kuwa muka ce, 'daga sama take,' za ya ce, "To, don me ba ku gaskata shi ba? 32 In kuwa muka ce, "amma in muka ce ta mutum ce zasu jejjefemu domi suna jin tsoron jama'a, don duk kowa ya tabbata, cewa Yahaya annabi ne. 33 Sai suka amsa wa Yesu suka ce, "Ba mu sani ba" Yesu ya ce masu, "Haka ni kuma ba zan fada muku ko da wanne iko nake yin abubuwan nan ba."

Mark 11:1

Da suka shiga Urushalima ... Betafaji, da Betanya, wajen Dutsen Zaitun

"Sa'ad da Yesu da almajiransa sun yi kusa da Urushalima, sun shiga Betafaji da Betanya kusa da Dutsen Zaitun" Sun zo Betafaji da Betanya cikin yankin Urushalima.

Betafaji

Wannan sunan kauye ne.

can kusa da mu

"gaba da mu"

aholaki

Wannan na nufin karamin jaki da zai iya ɗaukan mutum.

wanda ba a taba hawa ba

AT: "wanda ba wanda ya taba hawa"

Don me kuke wannan

Za a iya rubuta abin da kalman nan "wannan" ke nufin. AT: "Me ya sa kuke kunce, da kuma tafiya da aholakin"

na bukatarsa

"bukatar ta"

zai kuma komo da shi nan da nan

Yesu zai mayar da ita bayan ya gama amfani da ita. AT: "zai mayar da ita da wuri a lokacin da baya bukatan shi"

Mark 11:4

Sun tafi

"Almajiran biyun sun tafi"

aholaki

Wannan na nufin karamin jaki da zai iya ɗaukan mutum. Dubi yadda ka juya wannan cikin [Mark 11:2].

Sun yi magana

"Sun amsa"

Yesu ya faɗa masu

"kamar yadda Yesu ya ce masu su amsa." Wannan na nufin yadda Yesu ya gaya masu amsa tambayar mutanen game da ɗaukan aholakin.

bar su su tafi

Wannan na nufin cewa sun bar su su cigaba da yin abin da suke yi. AT: "bar su su tafi da jakin"

Mark 11:7

suka shimfiɗa mayafinsu a kai don Yesu ya hau

"shimfiɗa mayafinsu a bayan ta don Yesu ya iya hawa." Ya fi sauki a tuka aholaki ko doki a sa'ad da akwai bargo ko wani abu makamancinsa a bayan. A wannan yanayi, almajiran sun shimfiɗa mayafinsu a kan ta.

mayafi

"riga" ko "tufafi"

mutane da yawa sun shimfiɗa mayafinsu a kan hanya

Al'ada ce a shimfiɗa mayafi a kan hanya daidai gaban mutane masu muhimmanci don a daraja su. Za a iya bayana wannan a fili. AT: "Mutane da yawa sun shimfiɗa mayafinsu

waɗansu kuma suka baza ganyen da suka yanka daga filayen

Al'ada ce a shimfiɗa ganyayen dabino a hanya gaban mutane masu muhimmancin don a martaba su. AT: "wasu suka baza ganyayen a da suka yanka daga fili, a kan hanya, don su martaba su"

wanda suka bi baya

"wanda suka bi bayansa"

Hosanna

Wannan kalma na nufin "Ka cece mu," amma mutane sun yi iihun kira da farinci a sa'adda suke so su yi wa Allah yabo. Za ku iya juya ta bisa ga yadda aka yi amfani da kalman, ko kuwa ku rubuta "Hosanna" ta wurin yin amfani da harshen ku bayana kalma. AT: "Yabi Allah"

Albarka ta tabbata ga

Wannan na nufin Yesu. Ana iya bayana wannan a fili. AT: "Albarka ta tabbata a gare ka, kai wanda"

cikin sunan Ubangiji

Wannan na nufin ikon Ubangiji. AT: "ikon Ubangiji"

Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na ubanmu Dauda

"Albarka ta tabbata ga mulkin ubanmu Dauda." Wannan na nufin zuwan Yesu ya yi mulkin a matsayin sarki. AT: "Albarka ta tabbata ga zuwan mulkin ka" ko "Bari Allah ya albarkace ka a sa'adda kake mulkin ka mai zuwa"

Albarka ta

"Allah ya albarkace"

na ubanmu Dauda

A nan ana duban zuriyan Dauda da za su yi mulki kamar Dauda ne da kansa. AT: "na mafi girma cikin zuriyar ubanmu Dauda" ko "wanda mafi girma cikin zuriyar Dauda zai yi mulki"

Ɗukaka a cikin sama

Ma'ana mai yiwuwa 1) "Yabo ga Allah na sama" ko 2) "Bari wanda suke cikin sama su yi sowa su ce 'Hosanna'."

cikin sama

AT: "sama" ko "sama"

Mark 11:11

lokacin ya kure

"saboda can da rana"

ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyun

"shi da almajiransa goma sha biyun sun bar Urushalima sun tafi Betanya"

sa'anda suka dawo daga Betanaya

"sa'adda suke komowa zuwa Urushalima daga Betanya"

Mark 11:13

Mahaɗin Zance:

Wannan ya faru ne a sa'adda Yesu da almajiransa suna tafiya zuwa Urushalima.

ko zai sami wani 'ya'yan itace a kan ta

"ko akwai wani 'ya'ya a"

bai sami komai ba sai dai ganyaye

Wannan na nufin cewa bai sami wani ɓaure. AT: "ya sami ganyaye ne kawai babu ɓaure a itacen"

lokacin

"lokaci na shekara"

Sai ya ce ma ta, "Ba wanda zai kara ci daga 'ya'yanka kuma

Yesu yana magana da itacen ɓaure ya kuma la'anta ta. Ya yi magana da itacen don almajiransa su ji shi.

Ya yi magana da ita

"Ya yi magana da itacen"

almajiransa sun ji ta

Kalman nan "ta" na nufin cewa Yesu yana magana da itacen ɓauren.

Mark 11:15

Sun zo

"Yesu da almajiransa sun zo"

fara korin masu saya da sayarwa a cikin haikali

Yesu yana korin waɗannan mutane daga cikin haikali. Ana iya rubuta wannan a fili. AT: "ya fara fid da masu sayarwa da saya daga haikalin"

masu sayarwar da bayarwa

"mutanen da ke siya da sayarwa"

Mark 11:17

Muhimman Bayani:

Allah ya faɗa a cikin maganarsa tawurin annabi Ishaya, cewa, haikalinsa zai zama gidan addu'a ga dukkan alummai.

An rubuta, 'Za a ce da gida na ... al'ummai'?

Yesu ya sautawa shugabannen Yahudawan don sun yi amfani da haikalin ta hanyar da bai dace ba. AT: "An rubuta cikin nassosin cewa Allah ya ce, 'Ina so a kira gida na gidan da al'umma dukka za su yi addu'a."

kun maishe shi kogon 'yan fashi

Yesu ya kwatanta mutanen da 'yan fashi, haikali kuma da kogon 'yan fashi. AT: "Amma ku kamar 'yan fashi ne wanda suka maishe gida kogon 'yan fashi"

kogon 'yan fashi

"kogon da 'yan fashi ke ɓoyewa"

sun nemi hanyar

"suna neman hanyar"

da yamma

"da yammaci"

sun bar birnin

"Yesu da almajiransa sun bar birnin"

Mark 11:20

wucewa

"suna tafiya a kan hanya"

itacen ɓauren ya yi yaushi har zuwa jijiyoyin

Ka juya wannan magana yadda zai bayana da cewa itacen ya mutu. AT: "itacen ɓauren ya yi yaushi har zuwa jijiyoyin sa sai ya mutu"

yaushi

"bushe"

Bitrus ya tuna

Zai zama da taimako a bayana abin da Bitrus ya tuna. AT: "Bitrus ya tuna abin da Yesu ya faɗa wa itacen ɓauren"

Mark 11:22

Yesu ya amsa masu

"Yesu ya amsa wa almajiransa"

Hakiƙa, ina gaya maku

"Ina gaya maku gaskiya." Wannan magana na nanata abin da Yesu ya faɗa nan gaba.

duk wanda ya ce

"in wani ya ce"

in bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata

A nan "zuciya" na nufin tunanin mutumin da kuma rayuwarsa na ciki. AT: "hakika in ya bada gaskiya a zuciyarsa" ko "in bai yi shakka ba amma ya bada gaskiya"

Allah zai yi

"Allah zai sa abin ya faru"

Mark 11:24

Saboda haka ina gaya maku

"Don haka ina gaya maku"

zai zama naku

An fahimta cewa wannan zai faru saboda Allah zai tanada abin da kuka roƙa. Ana iya bayana wannan a fili. AT: "Allah zai ba ku"

sa'add da kuke addu'a

Al'ada ce a yahudanci a tsaya a tsaye sa'adda ana addu'a ga Allah. AT: "Sa'adda kuke addu'a"

kowane abu da kuke da shi game da wani

"kowane ƙiyayya da kuke da shi game da wani." Anan kalman nan "kowane" na nufin kowane ƙiyayya da kuke da shi game da wani do ya yi maku laifi ko wani fushi da kuke da shi game da wani.

Mark 11:27

sun zo wurin

"Yesu da almajiransa sun zo"

Yesu yana tafiya a cikin haikali

Wannan na nufin cewa Yesu yana tafiya a cikin haikalin; ba wai yana koƙarin shiga haikalin ba.

Suka ce masa

Kalman nan "su" na nufin firistocin, malaman attaura da kuma shugabanin jama'a.

Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa, kuma wa ya ba ka ikon aikata su?

Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) Duk waɗannan tambayoyin suna da ma'ana iri ɗaya, an kuma yi su don a yi tambaya mai karfi game da ikon Yesu, saboda haka za a iya haɗa su. AT: "Wa ya ba ka ikon aikata waɗannan abubuwa?" 2) Tambayoyi biyu ne daban dabam, na farko na tambaya game da yanayin ikon, na biyun kuma na game da wanda ya ba shi ikon.

kake yin waɗanan abubuwa

Kalmomin nan "waɗannan abubuwa" na nufin kife tabur na masu sayarwa da cikin haikali da Yesu ya yi, da kuma maganarsa da ke gãba da abinda firistocin da malaman attaura suke tunani. AT: "abubuwa kamar waɗanda ka yi anan jiya"

Mark 11:29

Gaya mani

"ku ba ni amsa"

Baftismar Yahaya

"baftismar da Yahaya ke yi"

shin daga sama ne ko daga wurin mutane

"an ba shi ikon daga sama ne ko daga wurin mutane"

daga sama

A nan "sama" na nufin Allah. AT: "daga Allah"

daga mutane

"daga mutane"

Mark 11:31

In mun ce, 'Daga sama',

Wannan na nufin inda baftisman Yahaya ya fito.

gaskanta da shi ba

Kalman nan "shi" na nufin Yahaya mai baftisma.

Amma in mun ce, 'Daga wurin mutane,

Wannan na nufin inda baftismar Yahaya ya fito.

Amma in mun ce, 'Daga wurin mutane,' ...

Shugabannin addinin suna nufin cewa za su sha wahala daga wurin mutane in sun bada wannan amsar. AT: "Amma in mun ce 'daga mutum,' wannan ba zai zama da kyau ba." ko "Amma ba ma so mu ce, daga mutum ne."

suna jin tsoron mutanen

Marubucin, Markus, ya bayana dalilin da ya sa shigabannin addinin ba sa son su ce cewa baftismar Yahaya daga mutum ne. Anan iya bayana wannan a fili. "Suka ce wa junansu don suna tsoron mutanen" ko "Ba sa so su ce cewa Baftismar Yahaya daga mutum ne domin suna tsoron mutane"

Ba mu sani ba

Wannan na nufin baftismar Yahaya. Abin da aka fahimta anan ana iya bayana shi. AT: "Ba mu san inda baftismar Yahaya ya fito ba"

Chapter 12

1 Sai Yesu ya fara koyar da su da misalai. "Wani mutum ne ya yi gonar inabi ya shingen ta, ya haka ramin matse inabin, ya kuwa gina hasumayar tsaro. Ya ba wandansu manoma jinginar gonar, sa'an nan ya tafi wata kasa mai nisa. 2 Da lokaci ya yi, sai ya aika masu wani bawansa domin ya karbi wadansu daga cikin amfanin gonar. 3 Amma manoman suka kama shi, suka yin masa duka, suka kore shi hannu banza. 4 Ya sake aikar wani bawan. Shi kuma suka raunata shi aka, suka wulakanta shi. 5 Ya sake aiken wani. Shi kam, suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da wadansu da yawa, sun dodoki wadansu, suka kuma kashe wadansu. 6 Yanzu dai yana da sauran daya tak, shine kaunatacen dansa. Daga karshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, ai za su bashi girma. 7 Amma manoman nan suka ce wa juna, "ai, wannan shine magajinsa, 'ku zo mu kashe shi, gadon ya zama namu." 8 Sai suka kamo shi, suka kashe shi, suka jefar da shi bayan shinge. 9 To, me mai gonar inabin zai yi? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba wadansu gonar. 10 Ashe, ba ku karanta wannan nassi ba? cewa, ' Dutsen da magina suka ki, shi ne ya zama mafi mahmimanci. 11 Wannan daga Ubangiji ne, kuma ya yi dai dai a idanunmu."' 12 Sai suka nemi su kama shi, don sun lura a kansu ne ya yi masalin, amma suka ji tsoron jama'a. Don haka suka kyele shi, suka tafi. 13 Suka aika masa da wadansu farisiyawa da Heridiyawa, don su sa masa tarko da kalamai cikin maganarsa. 14 Da suka zo, suka ce masa, "Malam, gaskiya kana koyar da maganar Allah sosai, ba ka nuna bambanci tsakani mutane, sai koyar da tafarkin Allah kake yi sosai. "Shin, mu biya haraji ga Kaisar, ko a a?" 15 AmmaYesu ya gane munafuncinsu, ya ce masu, "Don me kuke gwada ni? ku kawo mani dinarin in gani." 16 Suka kawowa Yesu daya. Ya ce masu, "Kamar waye da kuma rubutun wanene? suka ce masa, "Na Kaisar ne." 17 Yesu ya ce, "to, ku ba Kaisar abinda yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah. Sai suka yi mamakinsa kwarai. 18 Sai Sadukiyawa suka zo wurinsa, su dake cewa babu tashin matattu. Suka tambaya shi suka ce, 19 "Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan dan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba da, lallai ne dan'uwan mutumin ya auri matar, ya haifa wa dan'uwansa 'ya'ya.' 20 To an yi wadansu 'yan'uwa maza guda bakwai, na farko ya yi aure, ya mutu bai bar 'ya'ya ba. 21 Na biyu kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba 'ya'ya. Na ukun ma haka. 22 Haka dai duk bakwai din, ba wanda ya bar 'ya'ya. A karshe kuma ita matar ta mutu. 23 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai din nan sun aure ta". 24 Sai Yesu ya ce, "Ba saboda wannan dalili ne kuka yi kuskure ba, wato don ba ku san littafin ba, kuma ba ku san ikon Allah ba? 25 Domin in an tashin daga matattu, ba a aure, ba a auraswa, amma sun zama kamar malaiku a sama. 26 Amma game da mattattun da suka tashi, ashe, ba ku taba karantawa a littafin Musa ba, yadda Allah ya ce masa? "Ni ne Allah na Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu'? 27 Ai, shi ba Allahn mattatu bane, amma na rayyayu ne. Hakika kun yi kuskure ". 28 Sai wani malamin attuara ya zo ya ji suna muhawara da juna. Da dai ya ga Yesu yana ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, "Wanne Umarni ne mafi girma dukka?" 29 Yesu ya amsa yace, "mafi girma shine, 'ku saurara ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji daya ne. 30 Sai ka kaunaci Ubangiji Allah da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka da dukkan tunaninka, da dukkan karfinka. 31 ta biyu itace, 'ka kaunaci makwabcinka kamar kanka, Ba wata doka da ta fi wadannan." 32 Sai malamin attaura ya ce masa, "Hakika gaskiyarka malam, Allah daya ne, ba kuma wani sai shi. 33 A kaunace shi kuma da dukkan zuciya, da dukkan hankali, da dukkan karfi, a kuma kaunaci makwabci kamar kanka, ai ya fi dukkan hadayu na konawa." 34 Da Yesu ya ga ya yi masa magana da hikima, sai ya ce masa, "Ba ka nesa da mulkin Allah." Bayan wannan kuma ba wanda ya sake tambayarsa wani abu. 35 Yesu ya amsa a lokacin da yake koyarwa a Haikali, ya ce "Yaya malaman attaura suke ce wa Kristi dan Dauda ne? 36 Domin Dauda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce, "Ubangiji ya ce wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na kaskantar da makiyanka'. 37 Dauda da kansa ya kira shi 'Ubangiji; To, ta yaya ya Almasihu zai zama Dan Dauda?" Babban taron jama'ar suka saurare shi da murna. 38 A koyarwa sa Yasu ya ce, "ku yi hankali da malaman attaura, masu son yawo da manyan riguna, suna so a gaishesu a kasuwa, 39 da kuma son wuraren zama masu daraja a haikali, da wurin bukukuwa. 40 Sun kuma kwace gidajen gwauraye, da yin doguwar addu'a, don mutane su gani. Wadanan mutanen zasu sami hukunci mai tsanani." 41 Sai ya zauna a gaban akwatin baiko a Haikalin, yana duban yadda jama'a suke zuba kudi a ciki. 42 Wadansu masu arziki da yawa suna zuba kudi masu tsoka. Sai gwauruwa mara abin hanu ta saka anini biyu a ciki akwatin baikon. 43 Ya kira almajiransa, ya ce masu, "Hakika, ina gaya maku, abinda gwauruwa nan ta saka a akwatin baikon nan ya fi na sauran dukka. 44 Su duk sun bayar daga yalwa tasu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta bada duk abinda take da shi."

Mark 12:1

Mahaɗin Zance:

Yesu ya yi wannan misalin saboda firistoci da malaman attaura da kuma shugabannin jama'a.

Sai Yesu ya fara koya masu

Kalman "su" a nan na nufin firistoci da malaman attaura da kuma shugabannin jama'a wanda Yesu ke magana da su a sura da ke a baya.

ya shingen ta

Ya sa abin toshe hanya kewaye da ita. zai iya zama kananan itatuwa da aka jera, shinge ko kuwa shingen da aka yi da duwatsu.

haka ramin matse inabin

Wannan na nufin cewa ya sassaka rami a kan dutse wanda zai zama kasan wurin matse inabin wand da za a yi amfani da shi don tare ruwan 'ya'yan itacen inabin da aka matse. AT: "ramin da aka sassaka a dutse don matse inabi. ko "ya yi wata rami don tara ruwan inabi daga wurin matse inabi"

Ya ba wandansu manoma jinginar gonar

Har yanzu gonar na mai shi ne, amma ya ba bar manoman su lura da ita. A sa'anda inabin ya nuna, suna bukatan su ba wa mai gonar wasu sai su ajiya sauran.

A daidai lokacin

Wanna na nufin lokacin girbi. Anan iya bayana wannan a fili. AT: "Sa'anda lokaci ya yi na girbin inabin"

Amma suka kama shi

"Amma manoman sun kama bawan"

hannu wofi

Wannan na nufin cewa ba su ba shi wani 'ya'yan itacen ba. AT: "babu wani inabi"

Mark 12:4

ya aika masu

"mai gonar ya aika wa manoman"

sun ji masa ciwo a kai

Ana iya rubuta wannan a fili. AT: "sun yi masa duka a kai, sun ji masa ciwo kwarai da gaske"

Ya sake aikan wani ... waɗansu da yawa

Waɗannan maganganu na nufin sauran barorin. AT: "aikan wani bawan ... waɗansu barorin"

Haka fa suka yi ta yi da waɗansu da yawa

Wannan na nufin barorin da mai gonar ya aika. Maganan nan "haka suka yi" na nufin cewa an wulakanta. Ana iya rubuta wannan a fili. AT: "Sun kuma wulakanta waɗansu barori wanda ya aika"

Mark 12:6

ƙaunataccen ɗa

Na nufin cewa wannan ɗan mai gonar ne. AT: "ƙaunataccen ɗansa"

magajin

Wannan na nufin magaji mai gonar, wato wanda zai gaji gonar bayan mutuwar mahaifinsa. AT: "magajin mai gonar"

gãdon

'Yan hayan na duban gonar a matsayin "gãdon." AT: "wannan gonar"

Mark 12:8

Suka kamo shi

"Manoman suka kamo ɗan"

Saboda haka, me mai gonar inabin zai yi?

Yesu ya yi tambaya sai kuma ya bada amsan don ya koya wa mutanen. Ana iya rubuta tambayan ba a matsayin tambaya ba. AT: "Saboda haka ina gaya maku abin da mai gonar zai yi."

Saboda haka

Yesu ya gama bada misalin, yanzu kuwa yana tambayan mutanen abin da suke tunani zai faru nan gaba.

hallaka

kashe

zai ba waɗansu gonar

Kalman nan "waɗansu" na nufin waɗansu manoma wanda za su lura da gonar. AT: "zai bada gonar ga manoma don su lura da ita"

Mark 12:10

Muhimman Bayani:

Ana rubuta wannan nassi tun dã a cikin maganar Allah.

Ashe, ba ku karanta wannan nassi ba?

Yesu ya tunashe mutanen game da wata nassi cikin Littafi Mai Tsarki. Ya yi amfani da tambaya don ya sauta masu. AT: "Hakiƙa ba ku karanta wannan Nassi ba." ko "Ya kamata ku tuna da wannan Nassi."

shi ne ya zama mafificin dutsen gini

AT: "Ubangiji ya maishe shi mafificin dutsen gini"

Wannan daga Ubangiji ne

"Ubangiji ne ya yi wannan"

ya yi daidai a idanunmu

A nan "a idanunmu" na maɗaɗɗin gani, wanda ke nufin ra'ayin mutane. AT: "mun gani, mu kuma yi tunanin cewa ta yi daidai" ko "muna tunanin cewa abun ban mamaki ne"

Sai suka nemi su kama shi

"Su" na nufin firisitocin da malaman attaura da shugabannin jama'a. Waɗannan kungiya za a iya dubansu a matsayin "shugabannen Yahudawa."

nemi

"so"

amma sun ji tsoron taron

Sun ji tsoron abin taron za su yi masu in sun kama Yesu. Ana iya bayana wannan a fili. AT: "amma sun ji tsoron abin da taron za su yi masu in sun kama shi:

a kansu ne

"zarge su"

Mark 12:13

Sai suka aiki

"Sai shugabannen Yahudawan suka aiki"

Heridiyawan

Wannan suna ce na jami'yan siyasa da ta yi goyon bayan Hiridus Antibas.

sa masa tarko

A nan marubucin ya bayana zambar da ake yi wa Yesu a matsayin "sa masa tarko." AT: "zambace shi"

Da suka zo, suka ce

A nan "su" na nufin waɗanda aka aika daga cikin Farisiyawan da mutanen Hiridus.

ba ka damu da ra'ayin wani ba

Wannan na nufin cewa Yesu ba damu ba. AT: "Ba ka damu da ra'ayin mutane ba" ko "ba ka damu da samun tagomashi a wurin mutane ba"

AmmaYesu ya gane munafuncinsu

Riya suke yi. Anan iya bayana wannan a fili. AT: "Yesu ya san cewa ba so suke su san abin da Allah yana so su yi ba"

Don me kuke gwada ni?

Yesu ya sautawa shugabannen Yahudawan don zambarsa suke koƙarin yi. AT: "Na san da cewa kuna so ku sa ni in faɗi wani abu da ba daidai ba don ku zarge ni."

dinarin

Wannan kuɖin ya kai hakin ma'akaci na rana ɗaya.

Mark 12:16

Suka kawo ɗaya

Farisiyawan da Hiridiyawan sun kawo dinari ɗaya"

Kamar waye da kuma rubutun wanene

"hoto da suna"

Suka ce, "Kaisar"

A nan "Kaisar" na nufin kamaninsa da rubutunsa. AT: "Suka ce, 'Kamanin Kaisar da rubutunsa'"

ku ba Kaisar abinda yake na Kaisar

Yesu yana koyar da cewa mutanensa su girmama gwamnati ta wurin biyan haraji. Anan iya bayana wannan a fili ta wurin canza sunan Kaisar zuwa gwamnatin Roma. AT: "Ba wa gwamnatin Roma abubuwan da ke na gwamnatin Roma"

kuma ga Allah

Ana iya sa aikatau da aka fahimta . AT: "kuma ba wa Allah"

suka yi mamakinsa ƙwarai

Sun yi mamakin abin da Yesu ya faɗa. Ana iya bayana wannan a fili. AT: "Sun yi mamakinsa da kuma abin da ya faɗa"

Mark 12:18

waɗanda suka ce cewa babu tashin matattu

Wannan maganan ya bayana ko su wanene Sadukiyawa. Anan iya rubuta wannan a fili. AT: "wanda sun ce babu tashiwa daga cikin matattu"

Musa dai ya rubuta mana cewa idan ɗan'uwan mutum ya mutu

Sadukiyawan suna ruwaita abin da Musa ya rubuta a attauran. Ana iya rubuta abin da musa ya rubuta kamar haka. AT: "Musa ya rubuta mana cewa ida ɗan'uwan mutum ya mutu"

rubuto mana

"rubuto wa Yahudawa." Sadukiyawa wata kungiya ne na Yahudawa. Anan sun yi amfani da kalman nan "mu" don suna nufin kansu ne da kuma sauran Yahudawa.

ɗan'uwan mutumin ya auri matar

"mutumin ya auri matar ɗan'uwansa"

ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.'

"haifa wa ɗan'uwansa ɗa." Za a dubi ɗan farin mutumin a matsayin ɗan ɗan'uwan da ya mutu, zuriyar ɗan kuma za a dube su a matsayin zuriyar ɗan'uwan da ya mutu. Ana iya bayana wannan a fili. AT: "haifi ɗa wanda za a dube shi a matsayin ɗan ɗan'uwan da ya mutu"

Mark 12:20

To an yi waɗansu 'yan'uwa maza guda bakwai

Sadukiyawan sun yi magana game da yanayin da bai faru ba domin suna son Yesu ya faɗa masu abin da yake tunani daidai ne ko ba daidai ba. AT: "A misali akwai 'yan'uwa maza bakwai"

na farko ... Na biyu ... Na ukun

Waɗannan lambobin na nufin kowane ɗan'uwan kuma ana iya bayana shi a hakan. AT: "ɗan'uwan na farko ... ɗan'uwan na biyu ... ɗan'uwa na biyu"

Bakwain

Wannan na nufin dukka 'yan'uwan. AT: "'yan'uwa bakwain"

na farko ya ɗauke mata ... Na biyu ya ɗauke ta

"na farkon ya aure matan ... na biyun ya aure ta." An yi maganar auren mace kamar an "ɗauke" ta.

haka kuma na ukun

Zai zama da taimako a bayana abin nufin da "haka kuma". AT: "ɗan'uwa na ukun ya aure ta kamar yadda ɗan'uwansa ya yi, sai shi ma ya mutu bai bar 'ya'ya ba"

Na bakwain bai bar 'ya'ya ba

Kowane daga cikin 'yan'uwan ya aure matan sai ya mutu kafin ya sami 'ya'ya da ita. Anan iya bayana wannan a fili. AT: "A ƙarshe dukka 'yan'uwa bakwai din sun aure wannan macen ɗaya bayan ɗaya, amma ba wanda ya sami 'ya'ya da ita, kuma ɗaya bayan ɗaya suka mutu"

To, a tashin matattu, sa'adda sun tashi kuma, matar wa za ta zama a cikinsu?

Sadukiyawan suna gwada Yesu tawurin yin masa wannan tambayan. Idan masu karatunka za fahimci wannan a matsayin roƙo domin bayani, to ana iya rubuta wannan a matsayin magana. AT: "To, gaya mana ko matar wa za ta zama a ranar tashin matattu, a sa'adda sun tashi kuma."

Mark 12:24

Ba saboda wannan dalili ne kuka yi kuskure ba ... ikon Allah ba?

Yesu ya sauta wa Sadukiyawan domin sun yi kuskure game da shari'ar Allah. Anan iya bayana wannan cikin magana. AT: "Kun yi kuskure domin ... ikon Allah."

don ba ku san Nassin ba

Wannan na nufin cewa ba su fahimci abin da aka rubuta a cikin Nassosin Tsohon Alkawari ba.

ikon Allah

"yadda Allah ke da iko"

Domin in sun tashi

A nan kalman nan "su" na nufin 'yan'uwan da macen da cikin misalin.

tashi

Tashiwa daga barci wata karin magana ne da ke nufin sake rayuwa kuma bayana an mutu.

daga matattu

Daga cikin duk waɗanda suka mutu. Wannan na bayana dukkan mutane da suka mutu a ƙarkashin ƙasa. Tashi daga cikin su na nufin sake rayuwa kuma.

ba a aure, ba a auraswa

"ba sa aure, kuma ba sa auraswa"

ba sa auraswa

AT: "kuma ba wanda auras da su"

sama

Wannan na nufin inda Allah ya ke.

Mark 12:26

da aka tashe su

AT: "wanda sun tashi" ko "wanda sun tashi don su rayu kuma"

Littafin Musa

"littafin da Musa ya rubuta"

labari game da jejin

Wannan na nufin bangaren Littafin Musa da ta yi bayani game da sa'adda Allah ya yi magana da Musa daga cikin jeji dake konewa amma bata kone ba. AT: "nassin game da jeji me konewa" ko "kalmomi game da jeji mai konewa"

jejin

Wannan na nufin kananan itace, wanda bai kai bishiya ba.

yadda Allah ya yi masa magana

"game da sa'adda Allah ya yi wa Musa magana"

Ni ne Allah na Ibrahim ... Ishaku ... Yakubu'

Wannan na nufin cewa Ibrahim da Ishaku da kuma Yakubu sun yi wa Allah sujada. Waɗannan mutane sun mutu, amma a ruhuniya suna a raye kuma suna yi wa Allah sujada.

ba Allahn mattatu bane, amma na rayyayu ne

A nan "mattattu" na nufin mutanen da suka mutu, "rayayyu" kuma na nufin mutanen da ke raye. Haka kuma, kalman nan "Allahn" ana iya bayana shi a fili cikin magana na biyu. AT: "ba Allah mattattun mutane ba, amma Allahn rayayyun mutane"

rayayyu

Wannan mutane ne wanda ke raye cikin jiki da kuma ruhaniya a haɗe.

Hakika kun yi kuskure

Zai zama da taimakon a bayana abin da sun yin kuskure game da shi. AT: "In kun ce cewa mattattu ba za su rayu kuma ba, hakika kun yi kuskire"

yi kuskure

"matuƙar kuskure" ko "ba daidai ba kwarai"

Mark 12:28

Ya tambaye shi

"Malamin attauran ya tambaye Yesu"

mafi muhimmanci dukka ... mafi muhimmanci shine

"Mafi muhimmanci" na nufin umurni mafi muhimmanci. AT: "umurni mafi muhimmanci dukka ... umurni mafi muhimmanci ta ce"

ku saurara ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne

"Kassa kunne ya Isra'ila! Ubangiji Allahmu, Ubangiji ɗaya ne"

da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka da dukkan tunaninka, da dukkan karfinka

A nan "zuciya" da "rai" na nufin cikin mutum. Waɗannan maganganu huɗun na nufin "gabakiɗaya" ko "da naciya."

ka ƙaunaci makwabcinka kamar kanka

Yesu ya yi amfani da wannan don ya kwatantan yadda ya kyautu mutane su ƙaunaci juna da ƙuana iri ɗaya kamar yadda suke ƙaunar kansu. AT: "ƙaunaci makwabcinka kamar yadda kake ƙaunar kanka"

ta fi waɗannan.''

A nan kalman nan "waɗannan" na nufin dokoki biyun da Yesu ya gayawa mutanen.

Mark 12:32

Da kyau, Malam

"Amsa mai kyau, Malam" ko "Magana mai kyau, Malam"

Allah ɗaya ne

Wannan na nufin cewa akwai Allah ɗaya ne kawai. AT: "Allah ɗaya ne kawai"

babu wani kuma

Kalman nan "Allah" an fahimce shi daga magana da ke a baya. AT: "babu wani Allah"

da dukkan zuciya ... dukkan hankali ... dukkan karfi

A nan "ziciya na nufin tunanin, ji ko kuwa cikin mutumin. Waɗanna maganganu uku an yi amfani da su tare ne kuma suna nufin "gabakiɗaya" ko "da naciya."

ƙaunaci makwabci kamar kanka

Wannan na kwatantan yadda ya kamata mutane su ƙaunaci juna da irin ƙaunar sa suke yi wa kansu. AT: "a ƙaunaci makwabci kamar yadda kake ƙaunar kanka"

ai ya fi dukkan

Wannan na nufin cewa wani abu ya fi wani muhimmanci. A wannan yanayi, waɗannan dokoki biyun sun fi faranta wa Allah rai fiye da haɗayu. Anan iya bayana wannan a fili. AT: "ya fi muhimmanci fiye da" ko "ya fi faranta wan Allah rai fiye da"

Ba ku yi nesa da mulkin Allah ba

A nan Yesu ya yi magana game da mutumin da ya shirya ya mika kansa ga Allah a matsayin sarki kamar yin kusa da mulkin Allah, sai ka ce wani wuri ne da ana gani. AT: "Kun yi kusa ku mika kanku ga Allah a matsayin sarki"

ba wanda ya kalubalance

AT: "duk sun ji tsoro"

Mark 12:35

Yesu ya amsa a lokacin da yake koyarwa a Haikali, ya ce

Bayan dan lokacin kaɗan, Yesu ya shi haikali. Wannan ba ya cikin hiran da ke a baya. AT: "Bayan haka, sa'anda Yesu yana koyaswa a cikin haikali, ya ce wa mutanen"

Yaya malaman attaura suke ce da Almasihu ɗan Dauda ne?

Yesu ya yi amfani da wannan tambaya don ya sa mutanen su yi zurfin tunani game da Zaburan da zai ruwaita. AT: "Dubi dalilin da ya sa malaman attaura sun ce Almasihu shi Ɗan Dauda ne."

Ɗan Dauda

"zuriyan Dauda"

Dauda kansa

Kalman nan "kansa" na nufin Dauda, an yi amfani da

cikin Ruhu Mai Tsarki

Wannan na nufin cewa Ruhu Mai Tsarki ya iza shi. Wato, Ruhu Mai Tsarki ya shugabance Dauda cikin abin da ya făɗa. AT: "Ruhu Mai Tsarki ya iza shi"

ya ce, 'Ubangiji ya ce wa Ubangijina

A nan Dauda ya kira Allah "Ubangiji", ya kira Almasihu kuma "Ubangijina." Anan iya bayana wannan a fili. AT: "faɗa game da Almasihun, 'Ubangiji Allah ya ce wa Ubangijina"

Zauna a hannun dama na

Yesu ya ruwaita daga ckin Zabura. Anan Allah na magana da Almasihu ne. Zama a "hannun daman Allah" alama ce na samun martaba da iko daga Allah. AT: "zauna a wuri mai daraja tare da ni"

har sai na ɗora ka a kan makiyanka

A wannan da aka ambata, Allah ya yi magana game da cin nasara ga abokn găba kamar ɗora ka a kansu. AT: " har sai na yi nasara da makiyin ka gabakiɗaya"

kira shi 'Ubangiji.'

A nan kalman nan "shi" na nufin Almasihu.

to ta yaya Almasihu zai za ɗan Dauda?

AT: "to dubi yadda Almasihu zai iya zama daga zuriyar Dauda"

Mark 12:38

gaisuwar da suka karɓa daga cikin kasuwa

Sunan nan "gaisuwa" za a bayana shi da aikatau nan "gaishe." Waɗannan gaisuwar na nufin cewa mutanen sun martaba malaman attaura. AT: "a gaishe su da martaba a cikin kasuwa" ko "mutane su gaishe su da martaba a cikin kasuwa"

Sun kuma kwace gidajen gwamraye

A nan Yesu ya bayana magudi da malaman attaura ke yi wa gwamraye da sata gidajen su a matsayin "kwace" gidajensu. AT: "sun kuma yi wa gwamraye magudi don su sata gidajensu"

Gidajen gwamraye

Kalman nan "gwamraye" da "gidaje" na nufin mutanen da ba su samu mai taimakon ba, da kuma mallakar masu muhimmanci na mutumin. AT: "kowane abu daga wurin mutanen da basu da mai taimako"

Wadanan mutanen za a yi masu hukunci mai tsanani

AT: "Hakiƙa Allah za hukunta su da hukunci mai tsanani" ko "Hakiƙa Allah zai yi masu hukunci mai tsanani"

a yi masu hukunci mai tsanani

Kalman nan "tsanani" na nufin kwatanci. Anan kwatanci an yi shi ne da sauran mutane wanda aka hunkunta. AT: "za a yi masu hukunci fiye da sauran mutane"

Mark 12:41

akwatin baiko

Wannan akwatin da kowa zai iya amfani da shi akan sa baikon haikali a ciki.

anini biyu

"kananan tsabar kuɗi biyu." Waɗannan sune tsabar kuɗi masu daraja da akwai.

farashin ta kusan dinari guɗa

"farashin ta kaɗan ne." Farashin dinari kaɗan ne. A juya "dinari" da sunan kuɗi mai karami farashin a harshenku in kuna da wanda farashin ta kaɗan.

Mark 12:43

Ya kira

"Yesu ya kira"

Hakiƙa ina gaya maku

Wannan na nuna cewa maganar da ya bi baya gaskiya ne kuma na da muhimmanci. Dubi yadda ka juya wannan cikin [Markus 3: 28]

na dukka waɗanda suka ba da gudummawa

"na dukka sauran mutanen da suka sa kuɗi a ciki"

yalwa

yawan dukiya, yawan abubuwa masu daraja

talaucin ta

"rashin" ko "kaɗan da take da shi"

da za ta rayu da shi

"rayu da shi"

Chapter 13

1 da Yesu ke fita daga Haikalin, sai daya daga cikin almajirnsa ya ce masa "malam, dubi kyawawan duwatsunnan da kyawawan gine-ginnenan!" 2 Ya ce masa, ka ga wadannan kyawawan gine- ginen? babu wani dutsen da za a bar shi akan dan'uwansa, da ba za a rushe shi ba." 3 Yana zaune a kan dutsen zaitun wanda yake kusa da Haikali, sai Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, da Andarawus suka tambaye shi a asirce, suka ce. 4 Gaya mana yaushe za a yi wadannan abubuwa? mecece zata zama alamar faruwar wadanna abubuwa da zasu faru?" 5 Yesu ya ce masu, "ku kula, kada kowa ya rudeku. 6 Da yawa za su zo da sunana, suna cewa nine shi, har su bad da mutane da yawa. 7 In kuka ji labarin yake- yake, da jita-jitarsu kada ku damu, wannan zai faru, amma karshen duniya bai gabato ba. 8 Al'umma za ta tasarwa al'umma, mulki ya tasarwa mulki. Za a yi girgizar kasa awurare dabam-dabam, da kuma yunwa, amma fa dukkan wadanna abubuwan mafarin azaba ne. 9 Amma, ku zauna a fadake. Don za su kai ku gaban majalisa. za a yi maku duka a cikin majami'u. Su kuma kai ku gaban masu mulki da sarakuna, saboda sunana, domin ku ba da shaida a gare su. 10 Amma lallai sai an fara yi wa dukkan al, ummai bishara. 11 Sa'ad da suka kai ku gaban shari'a suka mika ku, kada ku damu a wannan lokacin, za a baku abin da zaku fada, Amma duk abin da aka yi muku a wannn lokacin, shi za ku fada, domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhu mai tsarki ne. 12 Dan'uwa zai bada dan'uwarsa akashe shi, uba kuwa dansa. Yara kuma zasu tayar wa iyayensu har su sa akashe su. 13 Za a ki ku saboda sunana, amma duk wanda ya jumre har karshe zai cetu. 14 Sa'adda kuka ga an kafa mummunan aikin sabo mai ban kyama a wurin da bai kamata ba (bari mai karatu ya fahimta), to, bari wadanda suke kasar Yahudiya, su gudu zuwa dutse. 15 Wanda yake tudu kuma kada ya sauko ya shiga gida garin daukar wani abu. 16 Wanda yake gona kuma kada ya koma garin daukar mayafinsa. 17 Amma, kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokacin. 18 Ku yi addu, a kada abin ya faru da damina. 19 A lokacin za ayi wata matsanaciyar wahala, wadda bata taba faruwa ba, tun farkon halittar da Allah ya yi har zuwa yau, ba kuwa za a taba yi ba har abada. 20 In da ba ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba Dan adam din zai tsira. Amma saboda zabbabunan da ya zaba, ya rage kwanakin. 21 To, in wani ya ce maku, kun ga Almasihu nan!' ko, 'kun gan shi can, kada ku gaskata. 22 Gama almasihan karya, da annabawan karya zasu bayyana kuma, zasu yi abubuwan al'ajibai masu ban mamaki. 23 Amma ku zauna a fadake, Na dai fada maku wadannan abubuwan kafin lokacin. 24 Amma, bayan matsanaciyar wahalannan, rana zata duhunta, wata kuma ba zai bada haske ba. 25 Taurari za su fado daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama. 26 Sa' annan zasu ga Dan mutum na zuwa a cikin gajimare, da iko mai girma da daukaka. 27 Zai aiko da mala'ikunsa su tattaro zabbabunsa daga kusuwoyi hudu na duniya(watau Gabas da Yamma, kudu da Arewa) har zuwa karshen sama. 28 "Ku yi koyi da itacen baure. Da zarar rassansa sun fara taushi yana kuma fitar da toho, kun san damina ta yi kusa ke nan. 29 Sa'adda kuka ga wadannan abubuwa suna faruwa, ku dai sani ya kusato, a bakin kofa ma ya ke. 30 Hakika ina gaya maku, zamanin nan ba zai shude ba sai dukan abubuwan nan sun faru. 31 Sararin sama da kasa za su shude, amma maganata ba za ta shude ba. 32 Amma wannan rana ko sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun sama, ko Dan, sai dai Uban kadai. 33 Ku kula, ku zauna a fadake, kuna addu'a don baku san ranar da lokacin zai yi ba. 34 Kamar yadda mutum mai tafiya, in ya bar gida ya wakilta bayinsa kan gidansa, kowanne da aikinsa, ya kuma umarci mai gadi ya zauna a fadake. 35 To, ku zauna a fadake don ba ku san lokacin da maigidan zai zo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko da carar zakara ne, ko da safe ne. 36 Kada ya zo ba zato, ya samu kuna barci. 37 Abinda na gaya maku, ina gaya wa kowa, shine ku zauna a fadake!"

Mark 13:1

Muhimmin Bayani:

Sa'adda sun bar haikalin, Yesu ya gaya wa almajiransa game da abin da zai faru da kyawawan haikalin da Hiridus ya gina a nan gaba.

kyawawan duwatsunnan da kyawawan gine-ginnenan

Su "duwatsun" na nufin duwatsun da an yi su gine-ginnen da su. AT: "kyawawan gine-ginnen da kyawawan duwatsun da an yi da"

ka ga wadannan kyawawan gine- ginen? Babu wani dutsen

An yi amfani da wannan tambaya domin a jawo hankali ga gine- ginen. AT: "Dubi wannan gine- ginen! Babu wani ɗutsen" ko "Kun gan waɗannan gine- ginen masu girma yanzu, Amma babu wani dutsen"

babu wani dutsen da za a bar shi akan ɗan'uwansa, da ba za a rushe shi ba

Ana nufin cewa makiyan sojoji za su rushe duwatsun. AT: "babu wani dutsen da zai kasance a kan ɗan'uwansa, don makiyan sojoji za su zo su rushe waɗannan gine- ginen"

Mark 13:3

Mahadin Zance:

Yesu ya gaya masu abin da zai faru nan gaba, a cikin amsan tambayoyin almajran game da rushewan haikalin da abin da zai faru.

Sa'adda yana zaune a kan Dutsen Zaitun wanda yake akasi da Haikalin, Bitrus

Ana iya bayyana cewa Yesu da almajiransa sun yi tafiya zuwa Dutsen Zaitun. AT: "Bayan da sun isa Dutsen Zaitun, da yake akasi da haikalin, Yesu ya zauna. Sai Bitrus"

asirce

lokacin da suke su kadai

wadannan abubuwa sun faru ... sun yi kusan faruwa

Wannan na nufin abin da Yesu ya ce zai faru da dutsunan haikalin. AT: "waddannan abubuwan sun faru da gine- ginen haikalin ... ya yi kusan faruwa da gine- ginen haikalin"

lokacin da dukka wadannan abubuwa

"da dukka wadannan abubuwa"

Mark 13:5

masu

"wa almajiransa"

rudeku ... za su rudeku

A nan "ruɗu misaline na canza wa wani ra'ayi ya yarda da abin da ba gaskiya bane. AT: "ruɗe ka ... za su ruɗe mutane dayawa" (Dubi: [[rc://*/ta//man/translate/figs-metaphor]])

a cikin sunana

AT: 1)" riya iko na" ko 2) "cewa Allah ya aiko su."

Ni ne shi

"Ni ne Almasihun"

Mark 13:7

ji game da yake- yake, da jita-jitarsu

"ji game da yake-yake da labarin yake-yake." AT: 1) "ji karan yake-yake a krukusa da labarin yake-yake da nisa" ko 2) "ji game da yake-yaken da sun fara kai ruhotu game da yake-yake da sun yi kusan faruwa"

amma karshen duniya bai gabato ba

"amma ba karshen ba ne" ko "amma karshen ba za ta faru ba sai anjuma" ko "amma karshen zai zama anjuma"

a karshen

Mai yiwuwa wannan na nufin karshen duniya.

za ta tasarwa

Wannan ƙarin magana na nufin yin faɗa da juna. AT: "za ta yi faɗa da juna"

mulki za ta tasarwa mulk

An fahimci kalmomin "za ta tasarwa" daga jumla da ta wuce. AT: "mulki za ta tasarwa mulk" ko "mutanen wani mulki za su yi faɗa da mutanen wani mulki"

Waɗannan abubuwan mafarin azaba ne

Yesu ya yi maganar waɗannan abubuwa kamar farkon azabar haifuwa domin mafi matsanancin abubuwa za su faru bayan su. AT: "Waɗannan abubuwa zasu zama kamar azaba na farko da mace take sha a loƙacin da ta yi kusan haifuwa"

Mark 13:9

Ku zauna a faɗake

"Ku shirya da abin da mutane za su

za su kai ku gaban majalisa

"ɗauke ku a sa ku cikin mulkin majalisa"

za a yi maku duka

AT: "mutane za su yi maku duka"

Za ku tsaya a gaban

Wannan na nufin hukunta ku. AT: "Za a sharanta ku a gaban" ko Za a sharanta a kuma hukunta ku ta wurin"

ta dalili na

"saboda ni" ko "bisa labari na"

shaida a gare su

Wannan na nufin za su shaida game da Yesu. AT: "ku kuma shaida masu game da ni" ko "za ku kuma gaya masu game da ni"

Amma dole sai an fara yi wa dukkan al'ummai bishara

Yesu ya na magana game da abubuwan da ɗole za su faru kafin karshen ya zo. AT: "Amma ɗole sai an fara yi wa dukkan al'ummai bishara kafin karshen ya zo"

Mark 13:11

kai ku gaban

Wannan anan na nufin sa mutane a ikon hukuma. AT: "kai ku gaban hukuma"

amma Ruhu mai Tsarki

An fahimci kalmomin "zai yi magana" a jumla da ta wuce. AT: "amma Ruhu mai Tsarki zai yi magana ta wurinku"

Dan'uwa zai bada dan'uwarsa ga mutuwa

"Wani ɗan'uwa zai sa wani ɗan'uwa cikin ikon mutanen da za su kashe shi" ko "Yan'uwane za su sa yan'uwanensu cikin ikon mutanen da za su kashe su." Wannan zai faru da sosai wa mutane dayawa. Yesu ba ya maganan mutum ɗaya da ɗan'uwansa.

Ɗan'uwa ... ɗan'uwa

Wannan na nufin 'yan'uwa mata da maza. AT: "Mutane ... yan'uwani"

uba kuwa ɗansa

An fahimci kalmomin "zai mika wa mutuwa" daga jumla da ta wuce. Wannan na nufin cewa waɗansu ubanne za su bashe yaransu, kuma wannan bashewan zai sa a kashe yaransun. AT: "ubanne za su ba da yaransu ga mutuwa" ko "ubanne za su bashe yaransu, mika su don a kashea su"

Yara kuma zasu tayar wa iyayensu

Wannan na nufin cewa yara za su yi hamayya da iyayensu su kuma bashe su. AT: "Yara za su yi hamayya da iyayensu"

sa a kashe su

Wannan na nufin cewa hukuma za su hukunta iyayen ga mutuwa. AT: "sa hukuma su hukunta iyayen ga mutuwa" ko "hukuman za su kashe iyayen"

kowa zai ki ku

AT: "Kowa zai ki ku"

saboda sunana

Yesu ya yi amfani da "sunana" don ya na nufin kansa. AT: "saboda ni" ko "saboda kun gaskanta da ni"

duk wanda ya jumre har karshe zai sami ceto

AT: "duk wanda ya jumre har karshe, Allah zai ceci wannan mutum" ko "Allah zai ceci duk wanda ya jumre har karshe"

duk wanda ya jumre har karshe

A nan "jumre" na wakilcin cingaba da aminci da Allah ko a wahala. AT: "duk wanda ya sha wahala ya kuma saya har karshe da aminci ga Allah"

har karshe

AT: 1) "har ga karshen rayuwarsa" ko 2) har ga karshen loƙacin wahala"

Mark 13:14

mummunan aikin sabo mai ban kyama

Wannan jumla na daga littafin Daniel. Ya kamata masu saurarans

na tsaya a inda bai kamata ya tsaya ba

Masu sauraron Yesu na iya gani cewa wannan na nufin haikali ne. AT: "na tsaye a cikin haikalin, inda bai kamata ya tsaya ba"

bari mai karatu ya fahimta

Wannan ba Yesu ba ne ke magana. Matiyu ya kara wannan domin ya sami hankalin masu karatun, domin su ji wannan gargadi. AT: "bari duk wanda ya na karanta wannan ya kasa kunne ga wannan gargadin"

kan tudu

Kan tudu da Yesu ya yi zama na nan shimfiɗaɗɗe, kuma mutane na iya sayawa akansu.

kada ya koma

Wannan na nufin koma zuwa gidansa. AT: "kada ya koma gidansa"

ɗauki mayafinsa

"ɗaukar mayafinsa"

Mark 13:17

masu goyo

Wannan wata hanya ne na ce wani na da juna biyu. AT: "na da ciki"

Ku yi addu'a

"Ku yi addu'a wannan kwanakin" ko "Ku yi addu'a waɗannan abubuwa"

damina

"loƙacin sanyi" ko "sanyi, loƙacin damin." Wannan na nufin loƙacin da ke da sanyi kuma babu dadi da kuma wuyan tafiya.

wadda bata taba faruwa ba

"ba za a sake samin mafi yawa kuma ba." Wannan ya nuna irin muni da wuya da azaban zai zama. Ba a taba yin irin azaba mai muni kamar irin wannan ba.

ba kuwa za a sake yinta ba

"ba za a sake samin mafi yawa kuma ba" ko "kuma bayan azaban, ba za a sake wani azaba kamar haka ba"

ya rage kwanakin

"ya rage loƙacin." Zai yi kyau a takaita wane "kwanakin" ne ana nufi. AT: "ya rage kwanakin wahala" ko "ya rage loƙacin wahala"

ba Ɗan Adam da zai tsira

Kalmar "Ɗan Adam" na nufin mutane, kuma "tsira" na nufin ceton jiki. AT: "babu wanda zai tsira" ko "kowa zai mutu"

saboda zabbabun

"don a taimake zabbabun"

zabbabunan, waɗanda ya zaba

Jumlar "waɗanda ya zaba" na nufin abu ɗaya da "zabbabun." An nanata cewa Allah ya zabi waɗannan mutanen.

Mark 13:21

Almasihan karya

"mutanen da suke ce su Almasihu ne"

don su ruɗe

"begen a ruɗe" ko "niyar ruɗe"

in ya yiwu, don su ruɗe, har zabbabun

Jumlar "har zabbabun" na nufin cewa Almasihan karya da annabawan karya za su so su ruɗe mutane, amma ba za su san ko za su iya rudin zabbabun ba. AT: "don a ruɗe mutane, a kuma rude zabbabun, in ya yiwu"

zabbabun

"mutanen da Allah ya zaba"

ku zauna a fadake

"ku zauna da shiri"

Na dai faɗa maku waɗannan abubuwan kafin loƙacin

Yesu ya gaya masu waɗannan abubuwa domin ya ƙwabe su. AT: "Na dai faɗa maku waɗannan abubuwa kafin loƙaci don in ƙwabe ku"

Mark 13:24

rana zata duhunta

AT: "rana zata zama da duhu"

wata kuma ba zai bada haskensa ba

An yi maganar wata anan kamar na da rai kuma na iya ba wa wani abu. AT: "watan ba za ta haskaka ba" ko "watan za ta yi duhu"

Tauraro za su fado daga sararin sama

Wannan ba ya nufin cewa za su fado kasa ba amma za su faɗi daga inda suke. AT: "tauraron za su fadi daga inda suke a sararin sama"

za a kuma girgiza ikon da suke a sararin sama

AT: "za a kuma girgiza ikon da suke a sararin sama" ko "Allah zai girgiza ikon da suke a sararin sama"

ikon da suke a sammai

"abubuwa masu iko a cikin sammai." AT: 1) "wannan na nufin rana, wata, da tauraro ko 2) wannan na nufin ruhuhi masu iko.

a cikin sammai

"sararin sama"

Sai za su gan

"Sai mutane za su gan"

da iko mai girma da ɗaukaka

"da iko da ɗaukaka"

zai tattaro

Kalmar "zai" na nufin Allah kuma ƙarin magana ne wa mala'ikunsa, don su ne waɗanda za su tara zabbabun. AT: "za su tara" ko "mala'ikunsa za su tara"

kusuwoyi hudu

An yi maganar dukka duniya kamar "kusuwoyi hudu," wanda na nufin jihohi: Gabas, Yamma, kudu da Arewa" ko "dukka yankin duniya"

daga karshen duniya zuwa karshen sararin sama

An ba da waɗannan matsananci biyun don a nanata cewa za a tara zabbabun daga dukka duniya. AT: "daga kowane wuri a duniya"

Mark 13:28

reshen sun fara taushi su na kuma fitar da ganye

Jumlar "reshe" na nufin reshen itacen bauren. AT: "reshensa sun fara taushi su na kuma fitar da ganyensu"

taushi

"kore da laushi"

fitar da ganye

An yi maganar itacen baure anan kamar ya na da rai kuma na iya sa ganyensa su yi girma. AT: "ganyensa sun fara tohowa"

damina

sashin shekara mai dumi ko loƙacin shuki

waɗannan abubuwa

Wannan na nufin loƙacin azaba. AT: "waɗannan abubuwa da na ƙwatanta"

ya yi kusa

"Ɗan Mutumin ya yi kusa"

kusa da kofan

Wannan ƙarin magana na nufin cewa ya yi kusa kuma yi kusan zuwa, na nufin mai tafiya ya yi kusan isan kofan garin. AT: "kuma ya yi kusa"

Mark 13:30

Hakika ina gaya maku

Wannan ya nuna cewa magana da ke biye na da muhimminci. Dubi yanda kun juya wanna a cikin 3:28.

ba zai shude ba

Wannan hanya ne mai kyau na magana game da mutum da ke mutuwa. AT: "ba zan mutu ba" ko "ba zai kare ba"

sai dukan waɗannan abubuwan

Jumlar "waɗannan abubuwan" na nufin lokacin azaba.

Sama da kasa

An ba da matsananci biyu domin a bayyana dukka sarari, tare da rana,wata, tauraro, da tauraro masu kewayan rana da dukkan kasan. AT: "Sararin, da kasan, da komai a cikinsu"

za ta shuɗe

"daina kasance." Wannan jumla anan na nufin karshen duniya.

maganata ba za ta shuɗe ba

Yesu ya yi maganar rasa ikon magana kamar abu ne da ba zai taba mutuwa ba. AT: "maganata ba za su taba rasa ikonsa ba"

wannan rana ko sa'a

Wannan na nufin loƙacin da Ɗan Mutum zai dawo. AT: "wannan rana ko sa'a da Ɗan Mutum zai dawo" ko "ranar ko sa'a da zan dawo"

ba wanda ya sani, ko mala'ikun sama, ko Ɗan, sai dai Uban

Waɗannan kalmomin sun nuna waɗansun da ba su san loƙacin da Ɗan Mutum zai dawo ba, dabam ne daga Uban, wanda ya sani. AT: "ba wanda ya san-ko mala'ikun a sama ko Ɗan-amma Uban" ko "ko mala'ikun a sama ko Ɗan sun sani; ba wanda ya sani sadai Uban"

mala'ikun a sama

A nan "sama" na nufin wurin da Allah yake zama.

amma Uban

Zai yi kyau ku fasara "Uba" da irin kalma da harshenku na amfani a kirin uba na mutuntaka. Wannan kuma ƙarin magana ne da na bayyana cewa Uban ya san loƙacin da Dan zai dawo. AT: "amma Uban ne kadai ya sani"

Mark 13:33

menene loƙacin

Za a iya bayyana da kyau abin da "loƙacin" na nufi anan. AT: "loƙacin da dukka abubuwan nan zasu faru"

kowanne da aikinsa

"gaya wa kowanne aikin da zai yi"

Mark 13:35

zai iya zama da yamma ne

"zai iya dawo da yamma"

carar zakara

Zakaran tsuntsu ne da na "cara" da sammako ta wurin kira mai karfi.

samu kuna barci

A nan Yesu ya yi maganar rashin zama da shiri kamar "barci." AT: "same ku da rashin shirin dawowarsa"

Chapter 14

1 Idin Ketarewa da bukin gurasa mara yisti sauran kwana biyu kenan, sai shugabanin firistoci da malaman attaura suka nemi yadda zasu kama Yesu a asirce domin su kashe shi. 2 Suna cewa amma "Ba a lokacin idin ba, domin kada su haddasa hargitsi a tsakanin mutane". 3 Yesu yana Betanya a gidan Saminu kuturu, yana shirin liyafa kenan sai ga wata mace dauke da kwalbar turare mai tamanin kwarai, ta shafa masa a kansa. 4 wasu dake tare da Yesu suka husata, suna kwalbarta da cewa 5 "Ai wannan turare ne mai tsada, ina laifin a sayar a raba wa talakawa kudin? ina dalilin wannan almubazaranci? 6 Sai Yesu yace masu "Ku kyaleta, don me kuke tsauta mata, 7 ai Idan kuna da niyyar taimakon talakawa ko matalauta, suna nan tare da ku ko a yaushe amma ni bazan kasance da ku kullum ba. 8 Macen nan tayi aiki nagari domin shirya jikina ga jana'iza. 9 hakika, Ina gaya maku, duk inda za'a yi bishara a duniya baza a mance da matan nan da hidimar da ta tayi mini ba." 10 Da jin haka sai Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin manzannin ya ruga zuwa wurin baban firist domin ya bashe shi a garesu, 11 Da mayan firistoci suka ji haka suka yi murna matuka tare da alkawarin kudi ga Yahuza, shi kuwa sai ya fara neman zarafin da zai mika Yesu a gare su. 12 A ranar farko ta bukin gurasa marar yisti da kuma hadayar ragon Idin ketarewa, almajiransa suka ce masa "Ina zamu shirya liyafar domin idin ketarewa? 13 Ya aiki biyu daga cikin almajiransa da cewa "Ku shiga cikin birnin, zaku tarar da wani mutum dauke da tullun ruwa. 14 Duk gidan da ya shiga ku bishi, sai ku cewa mai gidan, malam yace "ina bukatar masauki domin hidimar idin ketarewa tare da almajiraina?"' 15 Zai kuwa nuna maku babban bene gyararre. Sai ku yi mana shiri a can." 16 Da shigar almajiran cikin birnin, sai kome ya kasance yadda ya fada, su kuwa suka yi shirye shiryen idin ketarewar. 17 Da maraice ta yi, sai ya tare da sha biyun. 18 Yayin da suke zazzaune a teburin suna cin abincin, sai Yesu ya ce "Hakika ina gaya maku wani da ke ci tare da ni a nan zai bashe ni". 19 Sai suka damu suka tambaye shi daya bayan daya suna cewa "Hakika bani bane ko?" 20 Yesu ya amsa masu da cewa "Daya daga cikin sha biyu ne, wanda ke sa hannu tare da ni yanzu cikin tasar". 21 Dan Mutum zai tafi ne yadda nassi ya umarta game da shi amma kaiton wanda zai bashe shi! "zai, fiye masa, dama ba a haife shi ba". 22 Lokacin da suke cin abincin, Yesu ya dauki gurasa ya sa albarka, ya gutsuttsura ta, sai ya basu yana cewa "Wannan jikinana ne". 23 Ya kuma dauki koko, yayi godiya, ya basu, su kuwa suka sha daga kokon. 24 Ya ce "Wannan jinina ne na alkawari da an zubar ga yawancin mutane". 25 Hakika, bazan kara sha daga wannan ruwan inabi ba sai a ranar da zan sha sabo cikin mulkin Allah." 26 Bayan sun raira wakar yabo ga Allah, sai suka tafi wurin dutsen zaitun. 27 Yesu ya ce masu dukkan ku zaku yi tuntube harma ku fadi saboda ni gama rubuce take cewa "Zan buge makiyayin, tumakin kuwa za su watse; 28 Amma bayan tashina, zai yi gaba in riga ku zuwa Galili. 29 Bitrus ya ce masa "ko dukkansu sun fadi, faufau banda ni". 30 Yesu yace masa "Hakika ina gaya maka, cikin wannan dare kafin carar zakara ta biyu zaka yi musun sani na sau uku". 31 Amma Bitrus ya sake cewa "Koda za'a kasheni tare da kai ba zan yi musun sanin ka ba". Dukkan su kuwa suka yi wannan Alkawari. 32 Suka isa wani wuri da ake kira Getsamani, sai Yesu ya ce wa almajiransa "Ku dakata anan domin zan je inyi addu'a". 33 Sai ya dauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya. Ya fara jin wahala mutuka tare da damuwa kwarai. 34 Sai ya ce masu "Raina na shan wahala harma kamar in mutu. Ku dakata a nan, ku zauna a fadake". 35 Da Yesu yayi gaba kadan, sai ya fadi kasa yayi addu'a yana cewa idan mai yiwuwa ne "A dauke masa wannan sa'a daga gare shi. 36 Ya ce "Ya Abba Uba, kome mai yuwane gare ka, ka dauke mini kokon wahalan nan, duk da haka ba nufina ba sai dai naka". 37 Da komowarsa ya same su suna barci, sai ya ce wa Bitrus, Siman barci kake? Ashe, ba za ka iya zama a fadake ko da sa'a daya ba? 38 Ku zauna a fadake, kuyi addu'a kada ku fada cikin jaraba. Lalle ruhu na da niyya amma jiki raunana ne. 39 Sai ya sake komawa, yayi addu'a, yana maimaita kalmominsa na farko. 40 Har wa yau kuma ya sake dawowa, ya same su suna barci don barci ya cika masu idanu kwarai, sun kuwa kasa ce masa kome. 41 Ya sake komowa karo na uku yace masu "har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Ya isa haka! Lokaci yayi, an bada Dan Mutum ga masu zunubi". 42 Ku tashi mutafi kun ga, ga mai bashe ni nan ya kusato." 43 Nan da nan, kafin ya rufe baki sai ga Yahuza, daya daga cikin sha biyun da taron jama'a rike da takkuba da kulake. Manyan firistoci da malaman attaura da shugabanni suka turo su. 44 Mai bashe shi din nan ya riga ya kulla da su cewa "Wanda zan yi wa sumba shine mutumin, ku kama shi ku tafi da shi a tsare. 45 Da isowarsa kuwa, sai ya zo wurin Yesu ya ce "Ya malam!". Sai ya sumbace shi. 46 Su kuwa suka kama shi, suka tafi da shi. 47 Amma daya daga cikin na tsaye ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya yanke masa kunne. 48 Sai Yesu ya ce "kun fito kamar masu kama yan fashi da takkuba da kulake, domin ku kama ni? 49 Lokacin da nake koyarwa a Haikali, kowace rana da ku, baku kama ni ba. Amma anyi haka ne domin a cika abinda Nassi ya fada." 50 Daga nan duk wadanda suke tare da Yesu suka yashe shi, suka tsere. 51 Wani saurayi, daga shi sai mayafi ya bi shi, suka kai masa cafka. 52 Shi kuwa ya bar masu mayafin ya gudu tsirara. 53 Daga nan suka tafi da Yesu wurin babban firist. a can suka tara dattawa duk da manyan firistoci da shugabanni da marubuta, suka taru a wurinsa. 54 Bitrus kuwa ya bi shi daga nesa har cikin gidan babban firist. Ya zauna tare da dogaran Haikalin, yana jin dumin wuta. 55 Sai, manyan firistoci da duk 'yan majalisa Yahudawa suka nemi shaidar da za a tabbatar a kan Yesu, don su samu su kashe shi. Amma basu samu ba. 56 Da yawa kuma suka yi masa shaidar Zur (Karya), amma bakin su bai zama daya ba. 57 Sai wadansu kuma suka taso suka yi masa shaidar zur (karya) suka ce. 58 "Mun ji ya ce, wai zai rushe haikalin nan da mutane suka gina, ya sake gina wani cikin kwana uku, ba kuwa ginin mutum ba". 59 Duk da haka, sai shaidar tasu bata zo daya ba. 60 Sai babban firist ya mike a tsakanin su, ya tambayi Yesu yace "Ba ka da wata amsa game da shaidar da mutanen nan suke yi a kanka? 61 Amma yayi shiru abinsa, bai ce kome ba. Sai babban firist din ya sake tambayarsa "To, ashe kai ne Allmasihu Dan Madaukaki? 62 Yesu ya ce "Nine. Za ku kuwa ga Dan Mutum zaune dama ga mai iko, yana kuma zuwa cikin gajimare". 63 Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa yace "Wacce shaida kuma zamu nema? 64 Kun dai ji sabon da yayi! Me kuka gani? Duk suka yanke masa hukunci akan ya cancanci kisa. 65 Wadansu ma suka fara tottofa masa yau, suka daure masa idanu, suka bubbuge shi suna cewa "Yi annabci" Dogaran kuma suka yi ta marinsa. 66 Bitrus kuwa na kasa a filin gida, sai wata baranyar babban firist ta zo. 67 Da ta ga Bitrus na jin dumi, ta yi masa kallon gaske ta ce "Kaima ai tare kake da banazaren nan Yesu". 68 Amma ya musa ya ce "Ni ban ma san abinda kike fada ba balle in fahimta". Sai ya fito zaure. Sai zakara yayi cara. 69 Sai baranyar ta ganshi, ta sake ce wa wadanda ke tsaitsaye a wurin, "Wannan ma daya daga cikinsu ne". 70 Amma ya sake musawa, jim kadan sai na tsaitsayen suka ce wa Bitrus "Lalle kai ma dayansu ne don ba Galile ne kai". 71 Sai ya fara la'anta kansa yana ta rantsuwa yana ce wa "Ban ma san mutumin nan da kuke fada ba". 72 Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu, Bitrus kuwa ya tuna da maganar Yesu a gare shi cewa "Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sani na sau uku". Da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.

Mark 14:1

Mahaɗin Zance:

Kwana biyu kafin idin ketarewa, shugabanin firistoci da malaman attaura suna yin shiri a boye don su kashe Yesu.

a sace

ba tare da mutuane su gane ba

domin su na cewa

Kalmar "su" na nufin shugabanin firistoci da malaman attaura.

Ba a lokacin idin ba

Wannan na nufin ba su kama Yesu a loƙacin idin ba. AT: "Kada mu yi a loƙacin idin"

Mark 14:3

Saminu kuturu

Dama wannan mutumin na da kuturta amma yanzu babu. Wannan mutum dabam ne da Saminu Bitrus da kuma Saminu Zilot.

ya na kwanciye a teburin

A al'adan Yesu, loƙacin da mutane sun taru don cin abinci, su na kwanciye da gefensu, jinginar da kansu akan pillo a gefen tuburin.

ƙwalbar alabaster

Wannan ƙwalba ne da an yi shi daga alabaster. Alabaster wata kore-farin dutse mai sada. AT: "kyaukyauwar farin ƙwalba"

turare mai tsada da tamanin kwarai da ke ainahin nard

"da ya ƙunsa turare mai tsada da ake kira nard." Nard na da tsada, kuma mai ne da kamshi da ana amfani don yin turare.

a kansa

"a kan Yesu"

ina dalilin wannan almubazaranci?

Sun yi wannan tambaya domin su nuna cewa sun ki yadda matan ta na zuba turaren akan Yesu. AT: "Abin tsoro ne cewa ta na batar da turaren!"

Da an sayad da wannan turaren

Markus na so ya nuna wa masu karatunsa cewa waɗanda suke a loƙacin sun damu da ƙudi. AT: "Da mun sayad da wannan turaren" ko "Da ta sayad da wannan turaren"

dinari ɗari uku

"dinari ɗari uku." Dinari sulen azurfa ne na Roma.

ba wa talakawa

Jumlar "talakawa"na nufin mutane masu talauci. Wannan na nufin ba da ƙudin wa talakawa daga sayad da turare. AT: "a ba wa talakawa ƙudin"

Mark 14:6

Don me kuke damin ta?

Yesu ya tsauta wa mutanen don maganganu akan abin da matannan ta yi. AT: "Kar ku dame ta!"

talakawa

Wannan na nufin mutane masu talauci. AT: "talakawa"

Hakika, Ina gaya maku

Wannan na nuna cewa magana da na biye gaskiya ne kuma ya na da muhimminci. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 3:28.

duk inda za'a yi bishara

AT: " duk inda masubi na sun yi bishara"

za a yi shilar hidimar da matan nan ta tayi

"za a kuma yi shilar hidimar da matan nan ta tayi"

Mark 14:10

domin ya bashe shi a garesu

Yahuza bai rigaya bashe Yesu ba, ya je ya yi shiri da su. AT: "don ya shirya da su cewa zai ba su Yesu"

ya bashe shi a garesu

"kowa masu Yesu don su iya kama shi"

Da mayan firistoci suka ji haka

Zai yi kyau ku bayyana abin da mayan firistoci sun ji. AT: "Da mayan firistoci suka ji abin da ya ke da niyar yin masu"

Mark 14:12

da suka yi hadayar ragon Idin ketarewa

A ranar farko ta bukin gurasa marar yisti, al'ada ne a yi hadayar rago. AT: "da loƙacin da al'adan su ya kai na yin hadayar ragon idin ketarewa"

ɗauke da tullun ruwa

"ɗauke da babban tullu cike da ruwa"

Malam yace "Ina ne masauki na ... da almajiraina?"

AT: "Malamman mu su na so su san inda masuakin yake, inda zai iya cin abincin idin ketarewa tare da almajiransa."

masauki

dakin baki

ci idin ketarewa

A nan "ketarewa" na nufin abincin idin ketarewa. AT: "ci abincin idin ketarewa"

Mark 14:15

Ku yi mana shiri a can

Za su shirya abinci wa Yesu da almajiransa don su ci. AT: "Shirya mana abincin a can"

Almajiran suka tafi

"Almajirai biyun suka tafi"

kamar yadda ya faɗa

"kamar yadda Yesu ya faɗa"

Mark 14:17

ya zo da sha biyun

Zai yi kyau ku faɗa inda sun zo. AT: "ya zo gidan da sha biyun"

kwanciye a teburin

A al'adan Yesu, loƙacin da mutane sun taru don cin abinci, su na kwanciye da gefensu, su kuma jinginar da kansu akan pillo a gefen tuburin.

ɗaya bayan ɗaya

Wannan na nufin cewa almajiran sun tambaye juna "ɗaya bayan ɗaya."

Hakika bani bane ko?

AT: 1) wannan tambaya ne da almajiran sun zata amsan ya zama babu ko 2) wannan tambaya ne da bai bukaci amsa ba. AT: "Hakika ba ni ne zan bashe ka ba!"

Mark 14:20

Ɗaya daga cikin sha biyun ne, wanda yanzu

"Shi ne ɗaya daga cikin sha biyun, wanda yanzu"

tsoma gurasa tare da ni yanzu cikin tasar

A al'adan Yesu, mutane na yawan cin gurasa, tsomawa a cikin tasar miya ko mai da an hada da ganyen itace.

Gama Ɗan Mutum zai tafi ne yadda nassi ya umarta game da shi

A nan Yesu ya na nufin annabcin nassi game da mutuwarsa. Idan ku na da wata hanya mai kyau na magana akan mutuwa a harshenku, ku yi amfani da shi. AT: "Gama Ɗan Mutum zai mutu kamar yadda nassi ya ce"

ta wurin wanda ya bashe Ɗan Mutum

AT: "wanda ya bashe da Ɗan Mutum"

Mark 14:22

gurasa

Wannan shimfiɗaɗɗer gurasa marar yisti. wanda an ci a abincin ketarewa.

ya karya ta

Wannan na nufin cewa ya gutsuttsura gurasa wa mutanen su ci. AT: "ya gutsuttsura ta"

Karba wannan. Wannan jikinana ne

"Karba wannan gurasa. Jikina ne." Ko da shike yawanci sun fahimci wannan da cewa gurasa alama ne na jikin Yesu kuma ba ainahin jiki ba ne, zai yi kyau a fasara wannan magana a zahiri.

Ya ɗauki koko

A nan "koko" ƙarin magana ne na ruwan inabi. AT: "Ya ɗauki kokon ruwan inabi"

Wannan jinina ne na alkawari da an zubar ga yawancin

Alkawarin na gafarta zunubai ne. Ana iya sa wannan a bayyane. AT: "Wannan jinina ne da ya tabbatar da alkawarin, jinin da an zub da domin yawancin su iya samin gafarar zunubai"

Wannan jinina ne

"Wannan ruwan inabin jinina ne." Ko da shike yawanci sun fahimci wannan da cewa ruwan inabin alama ne na jinin Yesu kuma ba ainahin jini ba ne, zai yi kyau a fasara wannan magana a zahiri.

'ya'yan inabin

"ruwan inabi." Wannan kwatanci ne na ce ruwan inabi.

sabo

AT: ) "kuma" ko 2) "a wata sabuwar hanya"

Mark 14:26

wakar wakoki

Wakar yabo wata irin waka ce. Al'ada ne masu su yi wakar zabura ta Tsohon Alkawari.

Yesu ya ce masu

"Yesu ya ce wa almajiransa"

faɗi

Wannan ƙarin magana ne da na nufin bari. AT: "bar ni"

Zan buga

"Ƙashe." "Zan" na nufin Allah.

tumakin kuwa za su watsu

AT: "Zan watsar da tumakin"

Mark 14:28

tashina

Wannan ƙarin magana na nufin cewa Allah zai sa Yesu ya tashi kuma bayan ya mutu. AT: "Allah ya ta da ni daga mattatu" ko "Allah ya sa ni rayuwa kuma"

zai yi gaba in riga ku

"Zan tafi kafinku"

ko dukkansu sun faɗi, ba zan

Ana iya bayyana "Ba zan" kamar "Ba zan faɗi ba." Jumlar "zai faɗi ba"na ɗauke da ma'ana mai yaƙini. AT: "ko da dukkansu sun bar ku, Zan zauna da ku"

Mark 14:30

carar zakara

Zakara tsutsu ne da na kirari

sau biyu

sau biyu

zaka musunta ni

"za ka ce ba ka san ni ba"

Ko zan mutu

"ko da ɗole ne in mutu"

Dukkan su kuwa suka yi alkawari iri ɗaya

Wannan na nufin cewa dukka almajiran su faɗa abin da Bitrus ya ce.

Mark 14:32

Sun zo wurin

Kalmar "sun" na nufin Yesu da almajiransa.

wuya

cike da baƙin ciki

damuwa kwarai

Kalmar "kwarai" na nufin Yesu ya damu sosai a rainsa. AT: "damuwa mai tsanani"

Raina na

Yesu ya yi maganar kansa kamar "rain sa." AT: "Zan"

har ma ga mutuwa

Yesu ya na zuguiguitawa domin ya na jin wuya da baƙin ciki har ya na ji kamar zai mutu, ko da shike ya san cewa ba zai mutu ba sai rana ya tashi.

duba

Almajiran za su zauna a fadake sa'adda Yesu na addu'a. Wannan ba ya nufin cewa yakamata su kali Yesu sa'adda ya na addu'a.

Mark 14:35

idan na yiwuwa

Wannan na nufin cewa idan Allah zai bari ya faru. AT: "Idan Allah zai bari"

sa'an ya wuce

A nan "sa'an" na nufin loƙacin wahalar Yesu, yanzu da anjuma a lambun. AT: "ba sai ya yi wannan wahala ba"

Abba

kalma ne da 'ya'yan Yahudawa ke amfani da shi a yin magana da ubansu. Tun da ya na biye da "Uba," zai yi kyau a fasara wannan kalma.

Uba

Wannan muhimmin laƙabi ne wa Allah.

ka ɗauke mini kokonnan

Yesu ya yi maganar wahala da zai sha kamar koko ne.

ba nufina ba sai dai naka

Yesu ya na rokon Allah ya yi abin da ya ke so a yi ba kuma abin da Yesu ya na so ba. AT: "Amma kada ka yi abin da nake so, yi abin da kake so"

Mark 14:37

same su suna barci

Kalmar "su" na nufin Bitrus, Yakub da Yahaya.

Siman barci kake? Ashe, ba za ka iya zama a fadake ko da sa'a ɗaya ba?

Yesu ya ƙwabe Siman Bitrus domin barci. AT: "Siman, Kana barci bayan na gaya maka ka zauna a fadake. Ba ka iya zama a fadake ko na dan sa'a ɗaya ba."

kada ku faɗi cikin jaraba

Yesu ya yi maganar faɗi cikin jaraba kamar shigan cikin bayyananniyar wuri. AT: "kada a jarabta ku"

Lalle ruhu na da niyya amma jiki na raunana

Yesu ya ƙwabe Siman Bitrus da cewa ba shi da ƙarfin yin abin da yake so ya yi a ƙarfinsa. AT: "Ka na da niyya a ruhunka, amma ka na raunana sosai a yin abin da ka ke so ka yi" ko "Ka na so ka yi abin da na ce, amma ka raunana"

Ruhun ... jikin

Wannan na nufin kamani biyu na Bitrus. "Ruhun" shi ne bege na ciki. "Jikin" shi ne iyawa da ƙarfi na mutuntaka.

yi amfani da kalmomi ɗaya

"maimaita addu'an da ya yi"

Mark 14:40

don barci ya cika masu idanu kwarai

A nan marubucin ya yi maganar wuya da mutum mai jin barci ya ke ji a barin idannunsa a buɗe kamar "idannu masu nauyi." AT: "don sun ji barci sosai sun kasa barin idannunsu a buɗe"

Ya sake zuwa sau na uku

Yesu ya je ya yi addu'a kuma. Sai ya kuma sau uku. AT: "Sai ya je ya yi addu'a kuma. Ya komo karo na uku"

Barci kuke yi har yanzu kuna kuma hutawa?

Yesu ya ƙwabe almajiransa don rashin zama da fadake da kuma yin addu'a. AT: "Ku na nan ku na barci da hutawa!"

Lokaci yayi

Loƙacin wahala da bada Yesu ya yi kusan faruwa.

Duba!

"saurara!"

an bada Ɗan Mutum

Yesu ya ƙwabe almajiransa cewa mai bashe shi ya yi kusa da su. AT: "Ni, Ɗan Mutum, an bashe ni"

Mark 14:43

Muhimmin Bayani:

Aya arba'in da hudu ya ba da tushen bayani game da yadda Yahuza ya shirya da shugabanin Yahudawa don ya bashe Yesu.

Yanzu mai bashe shi

Wannan na nufin Yahuza.

shi ne

A nan "ne" na nufin mutumin da Yahuza zai nuna. AT: "shi ne wanda ku ke so"

sumbace shi

"Yahuza ya sumbace shi"

sa hannu a kansa, suka tafi da shi

Waɗannan jumloli biyun na da ma'ana iri ɗaya don nanata cewa sun kama Yesu. AT: "rarume da kuma kama Yesu" ko "kama shi"

Mark 14:47

wanda na tsaye

"wanda na tsaye a kusa"

kun fito kamar masu kama yan fashi da takkuba da kulake, domin ku kama ni?

Yesu ya na tsauta wa taron. AT: "abin ba'a ne cewa kun zo nan don ku kama ni da takkuba da kulake kamar na zama mai fashi!"

Amma anyi haka ne domin

"Amma wannan ya faru domin"

Duk waɗanda suke tare da Yesu

Wannan ya na nufin almajiran.

Mark 14:51

mayafi

kayan da an yi daga abin da ake tufkewa.

da ya yafa

AT: "da ya yafa akansa"

Da mutanen suka kama shi

"Da mutanen suka kama wannan mutumin"

ya bar masu mayafin

Sa'adda mutumin ya na kokarin guduwa, sauran na iya kama kayansa, da kokarin hana shi.

Mark 14:53

A can suka tara dattawa duk da manyan firistoci da shugabanni da marubuta

Ana iya sakewa domin fahimta. "Dukka manyan firistoci, dattawa, da kuma marubuta sun taru a can"

Yanzu

An yi amfani da wannan kalma anan domin a sa alama a labarin sa'adda marubucin ya fara gaya mana game da Bitrus.

daga nesa har cikin fadar babban firist

Sa'adda Bitrus ya bi Yesu, ya tsaya a fadar babban firist. AT: "kuma ya tafi da nisa har fadar babban firist"

Ya zauna tare da dogaran

Bitrus ya zauna tare da dogaran da suke aiki a fadan. AT: "ya zauna a cikin fadan tare da dogaran"

Mark 14:55

za su iya kashe shi

Basu ba ne za su kashe Yesu; maimakon haka, za su sa wani ya aikata. AT: "za su iya sa a kashe Yesu" ko "za su iya sa wani ya kashe Yesu"

Amma basu samu komai

Basu sami wani shaida akan Yesu da za su iya hukunta shi su kuma kashe shi ba. AT: "Amma basu samu wani shaida wanda za su iya hukunta shi ba"

yi masa shaidar zur

A nan an kwatanta yin shaidar zur kamar abu ne da ana iya gani da wani na iya ɗauke. AT: "sun zarge shi ta wurin yin masa shaidar zur"

amma bakin su bai zama ɗaya ba

AT: "amma shaidarsu ya bambanta da juna"

Mark 14:57

Mun ji ya ce

"Mun ji Yesu ya ce." Kalmar "mun" na nufin mutanen da suna kawo shaidar zur akan Yesu, bai hada da mutanen da suke magana ba.

da an ya da hannaye

A nan "hannaye" na nufin mutane. AT: "da mutane sun yi ... ba tare da taimakon mutum ba" ko "da mutane sun gina ... ba tare da taimakon mutum ba"

a kwana uku

"a cikin kwana uku." Wannan na nufin cewa za a gina haikalin a cikin kwana uku.

zai gina wani

An fahimci kalmar "haikali" a jumla da ta wuce. AT: " zai gina wani haikali"

bata zo ɗaya ba

"bambanta da juna."

Mark 14:60

mike a tsakanin su

Yesu ya tashi a tsakiyar jama'a masu fushi don ya yi masu magana. Fasara wannan don ya nuna wanda ya na nan a loƙacin da Yesu ya tashi yin magana. AT: "mike a tsakanin manyan firistoci, marubuta, da dattawa"

Ba ka da wata amsa? Menene shaidar da mutanen nan suke yi a kanka?

Babban firist din bai tambayi Yesu akan bayanin game da abin da shaidun suka ce ba. Ya na tambayan Yesu don ya nuna cewa abin da shaidun sun ce ba daidai ba ne. AT: "Ba za ka amsa ba? Menene ka ce a amsa game da shaidan da waɗannan mutanen ke fada akan ka?"

Ɗan Maɗaukaki

A nan an kira Allah "Madaukaki." Zai fi kyau a fasara "Ɗan" da irin kalma da harshenku za su yi amfani a kiran "ɗan" uban mutum. AT: "Ɗan Maɗaukaki" ko "Ɗan Allah"

Nine

AT: 1) don amsa tambayar babban firist da kuma 2) don ya kira kansa "Nine," wanda shi ne yake abin da Allah ya kira kansa a cikin Tsohon Alkawari.

ya na zaune a hannun damar mai iko

A nan "iko" ƙarin magana ne da na wakilcin Allah. Zama a "hannun damar Allah" alama ne na karban babban ɗaukaka da iko daga Allah. AT: "ya na zaune a wurin girma a gefen Allah mai iko dukka"

zuwa cikin gajimaren sama

An ƙwatanta gajimaren a nan kamar su na rakiyar Yesu a dawowarsa. AT: "Indan ya soko a gajimaren a sararin sama"

Mark 14:63

kyakketa tufafinsa

Babban firist din ya kyakketa tufafinsa don ya nuna fushinsa da ƙyamarsa a abin da Yesu ya ce. AT: " kyakketa tufafinsa a cikin fushi"

Wacce shaida kuma zamu nema?

AT: "Ba lallai ne muna son mutane kuma wanda za su shaida akan wannan mutum ba!"

Kun dai ji sabon

Wannan na nufin abin da Yesu ya ce, wanda babban firist ya kira sabo. AT: "Kun dai ji sabon da ya ce"

Duk suka ... Waɗansu ma suka fara

Waɗannan jumlolin na nufin mutanen cikin taron.

rufe masa idanunsa

Sun rufe masa idanunsa da ƙyalle ko abin ɗaure ido, don kada ya iya gani. AT: "don a rufe masa idanunsa da abin ɗaure ido"

Yi annabci

Sun yi mashi ba'a, da ce masa ya yi annabcin wanda yake buga shi. AT: "Yi annabcin wanda ya buga ka"

Dogaran

mazajen da suke tsaron gidan gumna

Mark 14:66

kasa a filin gida

"a waje a filin gida"

wata baranyar babban firist

Baranyar yanmatan su na aiki wa babban firist. AT: "wata baranyar wanda su na yi wa babban firist aiki"

musanta

Wannan na nufin amince cewa wani abu ba gaskiya ba ne. Wannan lamarin, Bitrus na faɗa cewa abin da baranyar ta faɗa game da shi ba gaskiya ba ne"

ban ma san ko gane abinda kike fada ba

Dukka "sani" da "gane" na da ma'ana iri ɗaya anan. An nanata ma'anar domin a nuna abin da Bitrus na ce. AT: "Ban gane abin da kike magana akai ba"

Mark 14:69

baranyar

Wannan ne baranyar da ta nuna Bitrus a farko.

ɗaya daga cikin su

Mutanen suna nuna cewa Bitrus ɗaya ne daga cikin almajiran Yesu. AT: "ɗaya daga cikin almajiran Yesu" ko "ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da wannan mutumin da an kama"

Mark 14:71

la'anta kansa

Idan ɗole ne ya kamata ku ba da sunan mutumin da ya la'anta wani a harshenku, ku ce Allah. AT: "ce don Allah ya la'anta shi"

Nan da nan sai zakara ya yi cara

Zakara tsuntsu ne da ke kira da samako. Karar da yake yi ne "cara."

sau biyu

"Biyu" lamba ne.

ya fashe

Wannan ƙarin magana na nufin cewa ya cika da damuwa ya kuma rasa ikon shaukinsa. AT: "ya cika da bakin ciki" ko "ya rasa ikon shaukinsa"

Chapter 15

1 Da sassafe, sai manyan firistoci suka hadu da dattawa da manyan malamai, da majalisa suka daure Yesu, suka sa shi gaba suka mika shi ga Bilatus. 2 Bilatus ya tambaye shi, kaine sarkin Yahudawa? ya amsa ya ce "haka ka ce" 3 Sai manyan firistochi suka kawo zargi iri iri a kan Yesu. 4 Bilatus ya sake tambayarsa, ba ka da abin cewa? ka lura da yawan zargi da ake yi maka. 5 Amma Yesu baya sake yi masa magana ba. wannan ya ba shi mamaki. 6 A lokacin idi, Bilatus ya kan sakar masu da dan bursuna wanda jama'a suka bukaci a saka, 7 A cikin gidan yari, in da aka tsare wadansu yan tawaye, da masu kisan kai, akwai wani mai kisan kai, ana ce da shi Barrabbas. 8 Sai Jama'a suka zo wurin Bilatus ya yi masu kamar yadda ya saba yi. 9 Bilatus ya amsa masu ya ce, kuna so in sakar maku sarkin Yahudawa? 10 Yayi wannan domin ya sani cewa Firistoci sun bada shi ne domin suna kishin sa, 11 Sai Firistochi suka zuga jama'a, sai suka yi kuwwa suna cewa, a sakar masu Barrabbas amaimakon Yesu. 12 Bilatus ya sake yi masu tambaya "Yaya zan yi da Sarkin Yahudawa?" 13 sai suka amsa da kuwwa" a "giciye shi!" 14 Bilatus ya ce masu menene laifinsa sai suka kara ihu, "a giciye shi." 15 Bilatus don yana son ya farantawa jama'a zuciya sai ya sakar masu da Barrabbas sai ya yi wa Yesu bulala, sannan ya mika shi a giciye shi. 16 Sojoji suka kai shi cikin kagara, suka tara rundunan soja, 17 Suka sa masa tufafin shulaiya suka nada masa rawanin kaya, 18 Suna masa kirari na ba'a suna cewa, "A gaida sarkin Yahudawa!" 19 Sai suka buge shi a kai da kulki suka kuma tofa masa yau a fuska, suka kuma durkusa suna yi masa sujadar ba'a. 20 Bayan sun gama yi masa ba'a sai suka cire masa tufafin shunnaiya, sai suka maida masa tasa tufafinsa, sai suka fitar dashi don su giciye shi. 21 Suna cikin tafiya sai suka hadu da wani, mai suna Saminu Bakairawani (wato uban Alizanda da Rufus); suka tillasta shi ya dauki gijiyen Yesu. 22 Sojojin suka kawo Yesu wurin da ake kira Golgota (wato kokon kai) 23 Suka bashi ruwan inabi hade da mur, amma ya ki ya sha. 24 Sai suka giciye shi, suka kuma raba tufafinsa suka kuma jefa kuri'a domin kowanne soja ya sami rabonsa. 25 A sa'a ta uku aka giciye shi. 26 Sai aka rubuta alamar zargi da take cewa "Ga Sarkin Yahudawa" 27 Suka kuma giciye shi tare da wadansu yan fashi guda biyu. 28 Daya a hannun damansa daya a hannun hagunsa. Domin a cika abinda nassi ya fada. 29 suke wucewa suna zaginsa suna kada kai suna cewa, "Aha! kai da zaka rushe haikali ka kuma gina shi cikin kwana uku, 30 ka ceci kanka mana, ka sauka daga giciye!" 31 Haka ma manyan firistoci da malamai, suka yi masa ba'a suna cewa "Ya ceci wadansu amma bai iya ceci kansa ba" 32 Bari Almasihu Sarkin Yahudawa ya sauka daga giciye. Domin mu gaskata shi, sai wadanda aka giciye shi tare dasu, suma suka yi masa ba'a. 33 sa'a ta shida zuwa sa'a ta tara, duhu ya rufe ko'ina, 34 A sa'a ta tara, Yesu ya tada murya da karfi ya ce Eloi, Eloi lamathsabathani?" Ma'ana Ya Allahna Ya Allahna, me ya sa ka yashe ni?" 35 Wasu daga cikin na tsaye, da suka ji shi, sai suka ce, "Duba, yana kiran Iliya." 36 Sai wani ya hanzarta, ya dauki soso ya tsoma a ruwan inabi mai tsami, ya soka agora ya mika masa don yasha. Mutumin yace bari mu gani ko Iliya zai zo ya saukar da shi. 37 Sai Yesu yayi kuka da babban murya da karfi sannan ya rasu. 38 Sai labulen haikalin ya rabu kashi biyu daga sama har kasa. 39 Sa'adda da jarumin sojan da ke tsaye yana fuskantar Yesu ya ga yadda ya mutum, Sai ya ce "hakika, wannan mutum Dan Allah ne." 40 Akwai kuma mata wadanda ke dubawa daga nesa. Daga cikinsu akwai Maryamu Magadala, da Maryamu( Uwar Yakubu da Yusufu) da Salome. 41 Wadannan matan sune suka bishi sa'adda da yake Galilee suna yi masa hidima. Da wadansu mata da yawa suka zo Urushalima tare da shi. 42 Da maraice an shiga shirye shirye domin kashe gari asabbaci ce. 43 Sai Yusufu daga garin Arimatiya ya zo, mutumin kirki, mai girma kuma dan majalisar dattawa, mai sauraron mulkin Allah, da gaba gadi ya tafi wurin Bilatus ya bukaci a bashi jikin Yesu. 44 Bilatus ya yi mamakin mutuwar Yesu cikin lokaci kadan, sai ya kira jarumin ya tabbattar koYesu ya mutu. 45 Bayan ya tabbattar daga wurin jarumin soja cewa Yesu ya mutu, sai ya bada jikin ga Yusufu. 46 Yusufu ya sayo likafani. ya saukar da shi daga giciye, ya kawo likafanin nan ya lulube jikin Yesu dashi. Ya kai shi kabarin da aka sassaka da dutse, wadda ya shirya shi domin kansa. Ya kawo dutse ya rufe bakin kabarin da shi. 47 Maryamu Magadaliya da Maryamu Uwar Yusufu sun ga wurin da aka yi jana'izar Yesu.

Mark 15:1

Mahaɗin Zance:

Da manyan firistoci, da shugabanni, da malaman Attaura, da dukkan 'yan majalisa suka Yesu wurin Bilatus, sai suka zarge shi da aikata munanan abubuwa. Da Bilatus ya tambaya ko karan da suka kawo gaskiya ne, Yesu bai amsa shi ba.

suka ɗaure Yesu, suka sa shi gaba

Sun umurta a ɗaure yesu, amma yana iya zama cewa masu tsaro ne suka ɗaure shi suka sa shi gaba. AT: "suka umarta a ɗaure Yesu, sa'annan aka yi gaba da shi" ko kuma "suka umarce masu tsaron su ɗaura Yesu, sa'annan suke sa shi gaba"

suka miƙa shi ga Bilatus

Suka sa aka kai Yesu ga Bilatus, sa'annan suka bar shi yă bi da Yesu.

haka ka ce

Wannan na iya nufin 1) ta wurin faɗin haka, Yesu yana cewa Bilatus ne ke ce da shi Sarkin Yahudawa ba Yesu ba. AT: "Ai kai da kanka ne ke ce haka" ko kuma 2) ta wurin faɗin haka, Yesu na nufin cewa shi ne Sarkin Yahudawa. AT: "I, yadda ka faɗa, Ni ne" ko kuma "I, haka ne yadda ka faɗa"

suka kawo zargi iri iri a kan Yesu

"suna zargen Yesu da laifuffuka iri iri" ko kuma "suna cewa Yesu ya aikata munanan abubuwa masu yawa"

Mark 15:4

Bilatus ya sake tambayarsa

"Bilatus ya sake tambayar Yesu kuma"

ba ka da abin cewa

AT: "Kana da abin faɗi"

ka lura

"Duba" ko kuma "ka Saurara" ko kuma "Ka mai da hankali ga abinda za faɗa maka"

wannan ya ba shi mamaki

Bilatus ya yi mamaki cewa Yesu bai tanka shi ko ma ya kare kansa ba.

Mark 15:6

Yanzu

A nan amfani ne da wannan kalmar don a nuna kaucewa daga ainihin labarin yayin da marubucin yana ba da tarihin al'adan Bilatus na saka wani ɗan kurkuku a bukukkuwa da kuma game da Barrabas.

A cikin gidan yari, in da aka tsare wadansu yan tawaye, ... mai kisan kai, ana ce da shi Barrabbas

"A wancan lokacin akwai wani mutum mai suna Barrabbas, yana kurkuku tare da wasu mutane. Sun yi kisankai yayin da suka yi tawaye da gwamnatin Roma"

ya yi masu kamar yadda ya saba yi

Wato sakie ɗan kukuku a bukukkuwa. AT: "ya sake masu wani ɗan kurkuku kamar yadda ya saba yi"

Mark 15:9

Yayi wannan domin ... kishin sa... masa Yesu

Wannan na ba da tarihin dalilin da yasa aka ɗanka Yesu wa Bilatus.

domin ya sani cewa Firistoci sun bada shi ne domin suna kishin sa

Suna kishin Yesu, mai yiwuwa domin da yawa a cikinsu suna binsa suna kuma zama almajiransa. AT: "manyan firistocin suna kishin Yesu. Shi yasa suna" ko kuma "manyan firistocin suna kishin farin jini da Yesu ke da shi ne a cikin mutane. Shi ya sa suna"

suka zuga jama'a

AT: "ta da hankulan jama'a" ko kuma "suka rinjaye jama'a"

a sakar ... amaimakon

Sun roƙa a sake masu barrabbas a maimakon Yesu. AT: "a sakar a maimakon Yesu"

Mark 15:12

Yaya zan yi da Sarkin Yahudawa

Bilatus yana tambayan abinda zai yi idan ya sake masu Barrabbas. Ana iya kara haske a wannan, AT: "Idan na sake maku Barrabbas, me zan yi da Sarkin Yahudawa"

Mark 15:14

Bilatus ya ce masu

"Bilatus ya ce wa taron"

ya farantawa jama'a zuciya

"ya sa taron su jo daɗi ta wurin yin abinda shi yake son su yi"

ya yi wa Yesu bulala

Sojojin Bilatus ne sun bulale Yesu, ba Bilatus dai da kansa ba.

bulala

"duka." A "bulale" mutum na nufin a yi wa mutum duka mai za i da sumagiya.

sannan ya miƙa shi a giciye shi

Bilatus ya umarci sojoji su tafi da Yesu don su giciye shi. AT: "ya ce wa sojojin su tafi da Yesu su giciye shi"

Mark 15:16

kagara (wato fadar rundunar sojoji)

A nan ne sojojin Roma da ke Urushalima su ke zama, kuma gwamna ma yakan zama anan ne idan yana Urushalima. AT: "fadar rundunan sojoji da ke bariki" ko kuma "kagarar gidan gwamna"

rundunan soja

"iyakar sojojin da ke wurin gabaɗaya"

Suka sa masa tufafin shulaiya

shulaiya kala ce da 'yan sarauta ke sakawa. Sojojin ba su yarda cewa Yesu sarki ba ne. Sun saka masa waɗannan tufafun ne domin su yi masa ba'a domin akwai masu cewa shi ne sarkin Yahudawa.

rawanin ƙaya

"rawani da aka yi da rasan ƙaya"

A gaida sarkin Yahudawa

Akan yin irin wannan gaisuwar da hannu a sama ne musamman domin a kaishe Sarkin Roma. Sojojin basu gaskata cewa Yesu sarkin Yahudawa bane. A maimakon haka, suna faɗin haka ne domin su yi masa ba'a'.

Mark 15:19

kulki

"sanda" ko kuma "itace"

suka kuma durkusa

Mutumin da ya durkusa ya lankwasa guiwar sa, ana iya cewa duk wanda ya durkusa ya lankwasa guiwarsa kenan." AT: "durkusawa" ko " durkusa"

suka tillasta shi ya ɗauki gijiyen Yesu

Dokan Roma ya ba wa sojoin Roma izini su tilasta duk mutumin da suka samu a hanya ya ɗauki masu kaya. A wannan hali, sun tilasta Saminu yă ɗauki giciyen Yesu.

daga ƙasar

"daga bayan garin"

wani, ... Rufus),

Wannan na ba da tarihin mutumin da sojojin sun tilasta shi ya ɗauki giciyen

Saminu ... Alizanda ... Rufus

Waɗannan sunayen mutane ne maza.

Bakairawani

Wannan sunan wani wuri ne.

Mark 15:22

wato koƙon kai

"wurin koƙon kai" ko kuma "wurin koƙon." Wannan shi ne sunan wurin. Ba wai yana nufin cewa akwai su koƙon kai da yawa a wurin ba.

koƙon kai

koƙon kai shi ne ƙwaƙwalwan kai, ko kuma kan da babu soka ko nama a jikinta.

ruwan inabi haɗe da mur

Zai zama da taimako idan an yi bayani cewa mur wata mai ce mai rage zafi. AT: "ruwa inabi a haɗe za wata magani mai suna mur" ko kuma "ruwan inabi a haɗe da magani mai rage zafi da ake kira mur"

Mark 15:25

sa'a ta uku

"uku" anan yana daidai jerin kirge. Wannan na nufin ƙarfe tara na safe. AT: "a ƙarfe tara na safe"

alamar

Sojojin sun manna wata alama a jikin jiciyen a bisa Yesu. AT: "Sun manna a giciyen a sama da kan Yesu wata alama da ke"

zargi da take cewa

"laifin da suke zargin sa"

Ɗaya a hannun damansa ɗaya a hannun hagunsa

Ana iya kara haske a wannan. AT: "ɗaya a bisa giciye a hannun damansa sannan ɗaya kuma a bisa giciye a hannun hagu"

Mark 15:29

suna kada kai

Wannan alama ce da ke nuna cewa mutane ke yi don su nuna cewa basu amice da Yesu ba.

Aha!

Wannan alama ce na ba'a. Ku yi amfani da daidai yadda ake yin ba'a a harshen ku.

kai da zaka rushe haikali ka kuma gina shi cikin kwana uku

Mutanen suna tunashe Yesu da abinda ya anabta zai yi ne dama. AT: "kai da ka ce za ka rushe haikali ka ka sake gina shi a kwana uku"

Mark 15:31

Haka ma

Wato yadda mutanen da ke tare da Yesu ma suna masa ba'a.

suka yi masa ba'a suna

"suna faɗin maganganun ba'a a kan Yesu a junansu"

Bari Almasihu Sarkin Yahudawa ya sauka

Shugabannin basu gaskata cewa Yesu shi ne Almasihu, Sarkin Isra'ila. AT: "Yana ce da kansa Almasihu da kuma Sarkin Isra'ila. To ya sauka" ko kuma "Idan shi ne Almasihu na gaskiya da Sarkin Isra'ila kuma, sai yă sauka"

gaskata

Wato a gaskata da Yesu. AT: "gaskata shi"

suka yi masa ba'a

suka zazzage shi.

Mark 15:33

sa'a ta shida

Wato tsakar rana kenan ko kuma 12 p.m.

duhu ya rufe ko'ina

A nan Marubucin yana bayanin yadda wuri yake yin duhu ne kamar wani kaɗi ne da ke masowa a bisa ƙasar. AT: "ƙasar gabaɗaya ya zama baki"

A sa'a ta tara

Wato ƙarfe uku na rana kenan. AT: "A ƙarfe uku na rana kenan. ko kuma "a sakar yini kenan"

Eloi, Eloi lamathsabathani

Waɗannan kalamun Yahudnci ne da ake iya ɗauko so zuwa harshenke yadda muryar su suka fito anan.

an fasara

"ma'ana"

Wasu daga cikin na tsaye, da suka ji shi, sai suka ce,

Ana iya fada a fili cewa basu fahimci abinda Yesu ke cewa ba. AT: "Wasu da ke tsaye a wurin sun ji kalamunsa, amma basu fahimci abinda yake cewa ba"

Mark 15:36

ruwan inabi mai tsami

"ruwan inabi mai tsami da gaske"

a gora

"sanda."

ya miƙa masa

"ya ba wa Yesu." Mutumin nan ya daga sandar sama ne domin Yesu ya samu yă iya shan ruwan inabin daga soson. AT: "ya riƙe shi sama wa Yesu"

Sai labulen haikalin ya raɓu kashi biyu

Markus yana nuna cewa Allah ne da kansa ya raɓa labulen haikalin. AT: "Allah ya raɓa labulen haikalin kashi biyu"

Mark 15:39

jarumin

Wannan shi ne jarumin da ya kula da sojojin da suka giciye Yesu.

da ke tsaye yana fuskantar Yesu

Anan "fuskanta" wata karin magana ne da ke nufin a kalli mutum. AT: "ya tsaya a gaban Yesu"

yadda ya mutu,

"yadda Yesu ya mutu"

Ɗan Allah ne

Wannan wata lakaɓi ne mai muhimmanci na Yesu.

ke dubawa daga nesa

"suna kallo daga nesa"

(Uwar Yakubu da Yusufu)

A nan iya rubuta wannan a baka ba.

Yakubu kanin

kanin Yakubu Ana ce da wannan "kani" mai yiwuwa domin a banbanta shi da wani mutum mai kuma mai suna Yakubu ne.

Yosis

Wannan Yosis ba shi ne kanin Yesu ba. Duba yadda kun juya wannan a [Markus 6:3]

Salome

Salome sunan mace ce.

suka biyo shi, sa'ad da yake ƙasar Galili ... tare da shi zuwa Urushalima

" Waɗannna matan sun bi Yesu, sa'ad da Yesu yake galili ... da shi zuwa Urushalima." Wannan shi ne ɗan tarihi game da matan da suke kallon yadda a ka giciye shi daga nesa.

biyo shi zuwa Urushalima

Urushalima na sama da kowani gari a Isra'ila, shi yasa mutane sun saba cewa suna haurowa zuwa Urushalima da kuma saukowa.

Mark 15:42

maraice an shiga

A nan ana maganar yamma kama wani abu ne da ke iya sa wa a wani wuri. AT: "yamma ya yi" ko kuma "yamma ne ko"

Sai Yusufu daga garin Arimatiya ya zo, mutumin kirki, mai girma kuma

Jimlar nan "ya zo" na nufin Zuwan Yusufu zuw wurin Bilatus, wadda aka yi bayaninsa bayan tarihin da aka bayar, amma ana maganar zuwansa ne domin a nanata, ya kuma taimaka a gabatar da labarin. Ana iya samun wata hanya daban na yin haka a harshenku. AT: "Yusugu ɗan garin Arimatiya, mutum ne mai girma"

Yusufu daga garin Arimatiya

Yusufu shi ne sunan mutumin, Arimatiya shi ne sunan inda ya fito.

shi mutumin kirki ne, mai girma kuma ɗan majalisar... mulkin Allah

Wannan shi ne tarihin Ysusfu.

ya tafi wurin Bilatus

"ya tafi inda Bilatus yake"

ya bukaci a bashi jikin Yesu

Kuna iya karin bayani cewa yana bukatan jikin Yesu ne domin ya bizne shi. AT: "ya bukaci izinin ɗaukan jikin Yesu ne domin ya bizne shi"

Bilatus ya yi mamakin mutuwar Yesu cikin lokaci kadan, sai ya kira jarumin

Bilatus ya ji mutane suna cewa Yesu ya mutu. Wannan ya ba shi mamaki, don haka, ya tambayi jarumin ko hakan gaskiya ne. AT: "Bilatu ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu, don haka, ya kira jarumin"

Mark 15:45

sai ya bada jikin ga Yusufu

"sai ya ba wa Yusufu Izini ya tafi da jikin Yesu.

likafani

likafini wani yadi ne da aka yi shi daga zaren wani itace. Duba yaka kuka juya wannan a [Markus 14:51]

ya saukar da shi ... Ya kawo dutse sun rufe

Kuna iya bayani cewa Yesufu ya nema wasu mutane su taya shi daukan jikin Yesu da ya saukar da shi daga giciye, ya shirya shi domin ya sa shi a kabari, ya kuma rufe kabarin. AT: "Sai shi da wasu mutane sun saukar da shi ... Sun kawo dutsen sun rufe"

kabarin da aka sassaka da dutse

AT: "kabarin da wani ya sassaka da sutse

dutse ya rufe

"babban dutse da aka fafe aka sa a gaban"

inda aka binne shi

AT: "inda Yusufu da sauran suka binne jikin Yesu"

Chapter 16

1 Bayan ranar assabaci, Maryamu Magadaliya da Maryamu uwar Yakubu da Salomi, suka sayo man shafawa mai kamshi domin shafe jikin Yesu saboda jana'iza. 2 Da safiyar ranar farko ta mako sai suka tafi kabarin a dai dai fitowar rana. 3 Suna magana a tsakaninsu suna cewa, wanene zai gangarar da dutsen da aka rufe bakin kabarin da shi?" 4 Da suka daga ido, sai suka ga an riga an gangarar da dutsen, domin yana da girma. 5 Da suka shiga cikin kabarin sai ga wani saurayi saye da farar tufa, yana zaune a hannun dama, suna mamaki. 6 Sai ya ce masu, "Kada ku ji tsoro. Kuna neman Yesu banazare, wanda aka giciye. Ya tashi! Baya nan. Ku duba wurin da aka kwantar dashi. 7 Sai ku je, ku gaya wa almajiransa da Bitrus cewa ya rigaya ya yi gabanku zuwa Galili. A can zaku ganshi, kamar yadda ya fada maku." 8 Suka fita daga cikin kabarin da gudu suna rawar jiki da mamaki, ba su cewa kowa komai ba domin suna jin tsoro. 9 Da safiyar ranar farko ta mako ya fara bayyana kansa ga Maryamu Magadaliya wadda ya kori aljannu guda bakwai daga cikinta. 10 Sai ta tafi ta shaida wadanda suke tare da shi suke makoki da kuka. 11 Sai suka ji cewa ya tashi kuma ta ganshi, amma basu gaskata ba. 12 Bayan wadannan al'amura ya bayana kansa ta wata siffa ga mutum biyu sa'ilin da suke tafiya akan hanya. 13 Sai suka tafi suka gaya wa sauran almajiransa, duk da haka basu gaskata ba. 14 Bayan wani lokaci, Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa su goma sha daya, ya tsauta masu saboda rashin gaskatawa da taurin zuciya, bayansun ji daga wadanda suka ganshi bayan ya tashi daga matattu. 15 Sai ya umarcesu cewa "Ku tafi cikin duniya ku yi bishara ga dukan halitta. 16 Wanda ya ba da gaskiya aka kuma yi masa baftisma, zaya sami ceto, wanda baya bada gaskiya ba za ya hallaka. 17 Wadannan alamu za su kasance da wadanda suka gaskata; a cikin sunana, za su fidda aljannu, za su yi magana da sabbin harsuna. 18 Za su dauki macizai da hannayesu, idan sun sha guba ba ta cutar dasu ba, za su dibiya hannayensu ga marasa lafiya, za su sami warkaswa." 19 Bayan Ubangiji ya gama magana da su, sai aka dauke shi zuwa sama in da zai zauna a hannun dama na Allah. 20 Almajiransa kuma suka tafi ko'ina suna sheilar bishara. Ubangiji kuma yayi aiki tare da su, yana tabbatar da kalma ta wurin ayukan al'ajiba tare da su.

Mark 16:1

Mahaɗin Zance:

A rana ta farko na mako, sa matan suka yi sammako domin su shafe jikin Yesu da man kamshi. Sun yi mamaki ƙwarai da sukn ga wani saurayi yana faɗi masu cewa Yesu yana da rai, amma sun ji tsoro kuma basu gaya wa kowa hakan ba.

Bayan ranar assabaci

Wato, bayan Asabar, rana ta bakwai na mako, ta kare sa'annan rana ta farko ta fara.

Mark 16:3

an riga an gangarar da dutsen

AT: "wani ya riga ya gangarar da dutsen"

Mark 16:5

Ya tashi!

Mala'ikan yana magana ne da tabbaci cewa yesu ya tashi daga matattu. AT: "Allah ya ta da shi daga matattu!" ko kuma "Ya ta da kansa daga matattu!"

Mark 16:9

ranar farko ta mako

"ranar Lahadi"

Sai suka ji

"Sai suka ji Maryamu Magadaliya tana cewa"

Mark 16:12

ya bayana kansa ta wata siffa

"su biyun" sun gan Yesu, amma ya yi daban da yadda yake dama.

mutum biyu

mutum biyu "waɗanda ke tare da shi" ([Markus 16:10])

basu gaskata da su ba

Sauran almajiran basu gaskata da abinda mutum biyun da ke ke tafiya cikin ƙasar ke cewa ba.

Mark 16:14

goma sha ɗaya

Waɗannan su ne manzanni goma sha ɗaya da suka rage bayan da Yahuza ya bar su.

sa'ad da suke cin abinci

Wannan misali ne na cin abinci, wanna haye ne na kullum wanɗa mutane suke cin abinci. AT: "suna cin abinci"

cin abinci

A al'adan Yesu, mutane suka taru ne a waje ɗaya lokacin cin abinci.

taurin zuciya

Yesu yana sauta wa almajiransa ne domin basu gaskanta da shi ba. A juya wannan karin maganar yadda za a fahimci cewa almajiran basu gaskata da Yesu ba ne. AT: "ƙi gaskatawa"

Ku tafi cikin duniya

A nan "duniya" karin magana ne da ke nufin mutanen da ke cikin duniya. AT: "Ku je duk wurin da akwai mutane"

dukkan halitta

Wannan ƙari ne a maganar kuma ya na nufin mutane a ko'ina. AT: "kowa da kowa gabakiɗaya"

Wanda ya ba da gaskiya aka kuma yi masa baftisma, zaya sami ceto

Kalmar nan "wanda" na nufin ko ma wa. AT: "Allah za cece dukkan mutanen da sun ba da gaskiya sun kuma yarda a ku yi masu baftisma"

wanda baya bada gaskiya ba za ya hallaka

Kalmar nan "wanda" na nufin ko ma wa. AT: "Allah zai hallaka dukkan mutanen da basu ba da gaskiya ba"

Mark 16:17

Waɗannan alamu za su kasance da waɗanda suka gaskata

Markus yana maganar mu'ajizai kamar su mutane ne da ke tafiya tare da masubi. AT: "Mutanen da ke kallon waɗannan sun gaskata za su ga waɗannan abubuwan suna faruwa, za su kuma sani cewa Ina tare da masubi"

a cikin sunana, za su

Wannan na iya nufi 1) Yesu yana ba da jerin abubuwa: "A cikin suna na za su yi abubuwa kamar haka: Za su" 2) Yesu yana ba da daidai jerin abubuwa: "Ga abubuwan da za su yi a cikin sunana: Za su."

a cikin sunana

A nan "suna" yana haɗe ne da Iko ko kuma karfin ikon Yesu. Duba yadda kuka juya "a cikin sunar ka" a [Markus 9:38]. AT: "Ta wurin ikon sunana" ko kuma "Ta wurin karfin ikon sunana"

Mark 16:19

sai aka ɗauke shi zuwa sama in da zai zauna

AT: "Allah ya ɗauke shi zuwa sama, ya kuma zaunar da shi"

zauna a hannun dama na Allah

A zauna a "hannun dama na Allah" alama ce na samun wata babban girma da iƙo daga gun Allah. AT: "zaune a wuri mai girma a gefen Allah"

yana tabbatar da kalma

Wanna karin magana na nufin yana nuna cewa jawabin su gaskiya. AT: "yaya nuna cewa jawabin nan da suke yi gaskiya"