Language: Hausa

Book: 3 John

3 John

Chapter 1

1 Daga dattijon zuwa ga Gayus, wanda nake kauna da gaske. 2 Ya kaunatace na, ina addu'a domin ka samu albarka cikin kowanne al'amari, da kuma koshin lafiya, kamar yadda ruhun ka yake lafiya. 3 Na yi farin ciki kwarai sa'adda wadansu 'yan'uwa suka zo suka ba da shaida a kan bangaskiyar ka, kamar yadda ka ke bin gaskiya. 4 Ba abin da ya fi faranta mani rai kamar in ji yayana suna tafiya cikin gaskiya. 5 Ya kaunatace na, kana aiki da aminci zuwa ga 'yan'uwa da baki, 6 wadanda suka shaida kaunar ka a gaban ikilisiya. Zai yi kyau ka yi masu taimako da kyakkyawar salama, ta hanyar da ta dace da masu ibada, 7 domin sabili da sunan nan ne suka fito, ba su kuma karbar kome a hannun al'ummai. 8 Don haka ya kamata mu karbi irin wadannan mutane, domin mu zama abokan aiki tare da su a kan gaskiya. 9 Na rubuta wasika zuwa ga ikilisiya, amma Diyotariffis, wanda ya fi kowa son girma a cikinsu, bai karbe mu ba. 10 Saboda haka, idan na zo, zan tuna masa da irin ayukkan sa, da kuma yadda yake babbata sunayen mu a wurin jama'a da miyagun kalmomi. Wannan ma bai ishe shi ba, har ma yana kin karbar 'yan'uwa. Ya kuma hana wadanda suke son su yin hakan, harma ya kan kore su daga ikilisiya. 11 Ya kaunatace na, kada ka yi koyi da mugun abu, sai dai abu mai kyau. Dukan wanda yake yin abu mai kyau na Allah ne; mai aikata mugunta kuma bai san Allah ba. 12 Dimitiriyas yana da kyakkyawar shaida a gun kowa har a wurin gaskiyar da kanta. Mu ma mun shaida shi, ka kuma san shaidar mu gaskiya ce. 13 Ina da abubuwa dayawa da zan rubuta maka, amma ban so in rubuta maka su da alkalami da tawada ba. 14 Ina sa zuciya mu sadu ba da dadewa ba, sa'annan mu yi magana ido da ido. 15 Bari salama ta kasance tare da kai. Abokanmu suna gaishe ka, kuma ka isadda sakon gaisuwar mu ga sauran abokai da sunayen su.



3 John 1:1

Mahaɗin Zance:

Wannan wasiƙa ce daga Yahaya zuwa ga Gayus. Dukan inda aka mori "ka" ana nufin Gayus ne.

dattijon

Wannan ya na nufin Yahaya, manzo da kuma almajirin Yesu. Watakila ya kira kansa "dattijo" saboda shekarunsa ko kuma domin shi shugaba ne a ikillisiya. Ana iya sa sunan marubucin a bayyane. "Ni, Yahaya dattijo, ina rubutu."

Gayus

Wannan ɗan'uwa mai bi ne wadda Yahaya ya rubuto masa wannan wasiƙan.

wanda nake ƙauna da gaske

"wadda na ke ƙauna ta gaskiya"

domin ka samu albarka cikin kowanne al'amari, da kuma ƙoshin lafiya

"ku kasance da nasara cikin kowanne al'amari, ka kuma kasance da ƙoshin lafiya"

kamar yadda ruhun ka yake lafiya

"kamar yadda kake lafiya a ruha"

'yan'uwa suka zo

"yan'uwa masubi sun zo." Da alama waɗannan mutanen maza ne duka.

ka yi tafiya cikin gaskiya

Tafiya a hanya, na nufin yadda mutum yake rayuwarsa. AT: "Ku na rayuwar ku a bisa gaskiyar Allah"

'ya'yana

Yahaya yana magana game da wadda ya koyar da su game da bangaskiya cikin Yesu kamar su 'ya'yansa ne. Wannan ya na nanata ƙaunarsa garesu da kulawa da yake da shi dominsu. Yana kuma iya zama cewa shi ne ya kai su ga sanin Ubangiji. AT: " 'ya'yana na ruhu"

3 John 1:5

Mahaɗin Zance:

Yahaya ya rubuta wannan wasiƙa ne domin ya yaba wa Gayus da yadda ya riƙe mallamai na Littafi masu tafiye tafiye; sai ya yi magana game da mutane biyu , ɗaya mai halin kirki da kuma ɗaya mai hali marar kirki.

Ya ƙaunatace

A nan ana amfani da kalmar ƙauna domin yan'uwa masubi.

kana aiki da aminci zuwa ga 'yan'uwa da baƙi

"kana aiki da aminci ga Allah" ko kuma "ka na biyayya da Allah"

yi wa 'yan'uwa da kuma baƙi

"taimaki 'yan'uwa masubi da waɗanda ba ku sansu ba"

baƙi, waɗanda suka shaida ƙaunar ka a gaban ikilisiya

"baƙi waɗanda suka faɗa wa masubi a cikin ikilisiya game da yadda ka ƙaunace su"

Zai yi kyau ka sallame su

Yahaya ya na gode wa Gayus domin taimako da ya saba yi wa waɗannan masubi.

domin sabili da sunan nan ne suka fito

A nan "sunan" na nufin Yesu. AT: "saboda sun fita domin su gayawa mutane game da Yesu"

karɓa kome

babu karɓar kyauta ko kuma taimako

Al'umman

A nan "Al'umman" ba yana nufin mutane da ba Yahudawa kaɗai ba. Ya na nufin mutane da ba su dogara da Yesu ba.

domin mu zama abokan aiki tare da su a kan gaskiya

"domin mu hada kai da su a sanar da gaskiyar Allah ga mutane"

3 John 1:9

taro

Wannan ya na nufin Gayus da kungiyar masubi waɗanda sukan haɗu domin su bauta wa Allah.

Diyotarifis

Shi ɗan taron ne.

wanda ya fi kowa son girma a cikinsu

"wanda ya fi son kasancewa da muhimminci a tsakaninsu" ko kuma "wanda ya na son yi kamar shi ne shugabansu"

yadda yake ɓaɓɓata sunayen mu a wurin jama'a da miyagun kalmomi

"da kuma yadda ya ke faɗin mugayen abubuwa game da mu da ba gaskiya ba"

yana kin karbar 'yan'uwa

"bai karɓi 'yan'uwa masubi ba"

hana waɗanda suke so su karɓe su

"hana waɗanda suke so su karɓi masubi"

ya ƙore su daga ikilisiya

"ya tilasa masu su bar taron"

3 John 1:11

kada ka yi koyi da mugun abu

"kada ka yi koyi da mugayen abubuwa da mutane suke yi"

sai dai abu mai kyau

AT: "Amma ka yi koyi da abubuwa masu kyau da mutane su ke yi"

na Allah ne

"ya zama na Allah ne"

bai ga Allah ba

"ba na Allah ba ne" ko kuma "bai gaskata da Allah ba"

Dimitiriyas yana da kyakkyawar shaida a gun kowa

AT: "Dukan waɗanda sun san Dimitiriyas suna shaida shi" ko kuma "Kowane mai bi da ya san Dimitiriyas ya na magana mai kyau game da shi"

Dimitiriyas

Mai yiwuwa wannan mutumin ne Yahaya ya ke so Gayus tare da taron masubi su marabce shi a lokacin da zai ziyarce su.

a wurin gaskiyar da kanta

"gaskiya da kanta tana shaidar shi." A nan an kwatanta "gaskiya" kamar mutum ne da ke magana. AT: "Dukan wadda ya san gaskiyan ya san cewa shi mutumin kirki ne"

Mu ma mun shaida shi

Wannan ya na tabbatar da abin da Yahaya yake nufi a nan. AT: "Mun kuma yi magana da kyau game da Dimitiriyas"

3 John 1:13

ba na so in rubuta maka su da alƙalami da tawada

Yahaya ba ya so ya rubuta waɗannan abubuwa ko kaɗan. Ba wai ya na ce wa zai rubuta masu wasiƙa da wani abu dabam da alƙalami da kuma tawada ba.

ido da ido

"ido da ido" na nufin "da kansa." AT: "da kansa"

Bari salama ta kasance tare da kai

"Bari Allah ya ba ku salama"

Abokanmu suna gaishe ka

"Abokai a nan suna gaishe ka"

ka isadda sakon gaisuwar mu ga sauran abokai da sunayen su

"ka isadda sakon gaisuwa na ga masubi a can"


Translation Questions

3 John 1:1

Da wane suna ne marubuci Yahaya ya gabatar da kansa a wannan wasiƙar?

Yahaya ya gabatar da kansa a sunan datijjo.

Wane dangataka ne Yahaya ya ke da shi da Gayus, wanda shine mai karɓan wannan wasiƙar?

Yahaya ya na kaunar Gayus a cikin gaskiya.

Don menene Yahaya ya ke adu'a game da Gayus?

Yahaya yayi adu'a cewa Gayus ya ɓunkasa a cikin kowane abu ya kuma zama da lafiya, kamar yadda ruhunsa ya ke ɓunkasa.

Menene babban farin cikin Yahaya?

Babban farin cikin Yahaya shine y ji cewa yaranshi suna tafiya cikin gaskiya.

3 John 1:5

Su wanene Gayus ya marabta ya kuma aike su a tafiyarsu?

Gayus ya yi marabci ya kuma aika su a tafiyarsu wasu waɗanda ke fita saboda Sunan.

Me ya sa Yahaya ya ce ya kammata masubi su yi ta marabtar yan'uwa kamar waɗannan?

Yahaya ya ce masubi su marabce so domin su zama yan'uwa ma'aikata domin gaskiya.

3 John 1:9

Menene Diyotarifis ke kauna?

Diyotarifis ya na kaunar ya zama shine farko a cikin ikklisiya.

Menene halin Diyotarifis zuwa ga Yahaya?

Diyotarifis bai karɓi Yahaya ba.

Menene Yahaya zai yi idan ya zo wurin Gayus da kuma ikklisiyar?

Idan Yahaya ya zo zai yi tuna da mugun halayen Diyotarifis

Menene Diyotarifis ya ke yi da yan'uwan da suke fita domin Sunan?

Diyotarifis ba ya karɓan yan'uwan.

Menene Diyotarifis ya ke yi da waɗanda suka karbi yan'uwa da ke fita domin Sunan?

Diyotarifis ya na hana su karɓan yan'uwan, ya na kuma korar su da ga ikkklisiya.

3 John 1:11

Menene Yahaya ya gaya wa Gayus ya kwaikwaya?

Yahaya ya gaya wa Gayus ya kwaikwayi mai kyau.

3 John 1:13

Menene yahaya yake begen yi a nan gaba?

Yahaya na begen zuwa ya kuma yi magana tare da Gayus fuska da fuska.


Translation Words

Allah

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

aiki, cikin naƙuda, ciwon naƙuda, zafin haihuwa, zafin haihuwar ɗa

Ma'ana

Macen dake "cikin naƙuda" tana fuskantar zafin dake kaiwa ga haihuwar ɗanta. Ana kiran waɗannan "ciwon naƙuda."

(Hakanan duba: naƙuda, kawakin ƙarshe)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

aiki, aikace-aikace, aikin ƙarfi, ma'aikaci, ma'aikata, aiki tuƙuru

Ma'ana

Kalmar aikin ƙarfi na nufin kowanne irin aiki tuƙuru.

(Hakanan duba: tuƙuru, zafin naƙuda)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

al'umma, al'ummai

Ma'ana

Al'umma babbar ƙungiyar mutane ce da suke da wasu sharuɗɗan mulki. Yawancin lokaci mutanen da suka zama al'umma sun fito ne daga zuriya ɗaya da kuma yare ɗaya.

Shawarwarin Fassara:

Wannan kalma da ta nuna yawa "al'ummai" za a iya fassara ta a ce "ƙungiyar mutane."

(Hakanan duba: Asiriya, Babila, Kan'ana, Al'ummai, Girik, ƙungiyar mutane, Filistiyawa, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Taski:

alama, alamomi, tabbaci, tunatarwa

Ma'ana

Alama abu ne, ko aiki da kan yaɗa abu mai ma'ana.

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: mu'ujiza, manzanni, Almasihu, alƙawari, kaciya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

albarka, mai albarka, sa albarka

Ma'ana

A sã wa wani mutum ko wani abu "albarka" ma'anar shi ne a sã abu mai kyau da abubuwan amfani su faru ga mutumin nan ko wannan abin da ake săwa albarka.

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: yabo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

amin, hakika, gaskiya

Ma'ana

Wannan furci "amin" kalma ce da ake amfani da ita a nanata ko a jawo hankali ga abin da wani ya faɗa. Yawancin lokaci ana amfani da ita a ƙarshen addu'a. Wani lokaci ana fassara shi ya zama "gaskiya."

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: cikawa, gaskiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

bangaskiya

Ma'ana

A faiyace, kalmar nan "bangaskiya" tana magana ne akan imani, dogoro, ko amincewa da wani, ko wani abu.

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: gaskata, amintacce)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

dattijo, dattawa, tsoho

Ma'ana

Dattawa sune waɗanda suka manyanta a ruhaniya waɗanda aka danƙawa sha'anin gudanar ayukan Ikkilisiya da kuma ayuka na ruhaniya a cikin mutanen Allah.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

fara, fari

Ma'ana

Wannan kalma "fãri" na nufin wasu manyan ƙwari ne masu tashi cikin cincirindonsu su yi ɓarnar cinye dukkan ganyaye da suka tarar.

(Hakanan duba: bawa, Masar, Isra'ila, Yahaya (mai Baftisma))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

gaskiya, gaskiyar, gaskiyoyi

Ma'ana

Kalmar "gaskiyar" na ma'anar abu ɗaya ko fiye da haka da yake tabbatacce, al'amuran da suka ainihin faru, kuma maganganun da ainihin an faɗe su. Waɗannan abubuwa ana ce masu "gaskiya."

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: gaskatawa, aminci, cikawa, biyayya, anabci, fahimta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

ikilisiya, Ikilisiya

Ma'ana

A cikin Sabon Alƙawari, wannan kalma "ikilisiya" na nufin karamar ƙungiyar masu bada gaskiya ga Yesu waɗanda suke tattaruwa kullum su yi addu'a su kuma ji wa'azin maganar Allah. Wannnan kalma "Ikilisiya" kuma ana nufin dukkan Kristoci.

Shawarwarin Fassara

(Hakanan duba: taruwa, gaskatawa, kirista)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

iri, maniyi

Ma'ana

Iri sashe ne na dashe da ake shukawa a cikin ƙasa domin ya bãda 'ya'ya dashe kamarsa. Yana kuma da wasu ma'ana na misalai da yawa.

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: zuriya, 'ya'ya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

kai, kawuna, goshi, goshi fiye da ɗaya, saiƙo, farkon kai, iyakokin kai, kogonnin kai, hallakarwa

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "kai" an more ta sosai cikn salon magana da ma'anoni masu yawa.

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: hatsi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

kala, yin kala, kalatacce, aikin kala

Ma'ana

Kalmar nan "kala" tana nufin a zagaya fili ko gidan gona a tsince duk sauran hatsi ko 'ya'yan hatsi da masu girbi suka rage a baya.

(Hakanan duba: Bo'aza, hatsi, gibi, Rut)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

kamar, ra'ayi ɗaya, kamalta, kamamni, kama da yawa, haka ma, sun yi kama, ba kamar, sai ka ce

Ma'ana

Wannan furci "kamar" da "kamanni" ana nufin wani abu ya yi dai-dai da, ko ya yi kusan kama, da wani abu.

Kalmar nan "kamar" ana amfani da ita cikin maganar da ake ceda ita "kamaltawa" idan za a gwada wani abu da wani abun da ban, tare da faɗin inda suka yi kama musamman. Misali, "tufafinsa suka yi walƙiya kamar rana" da "muryar ta yi ƙara kamar aradu."

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: dabbobi, nama, surrar Allah, sura, lalacewa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

koyi da, mai koyi da, masu koyi da

Ma'ana

Kalmar nan "koyi da" da "mai koyi da" na nufin kwaikwayon wani abu da bam ko wani abin da wani ke yi.

Shawarwarin Fassara:

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

mai

Ma'ana

Mai wani abu ne mai kauri, ruwa-ruwa da za a iya samunsa daga wasu tsire-tsire. A lokacin Littafi Mai Tsarki

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

mai kyau, hali mai kyau

Ma'ana

Kalmar nan "kyau" tana da ma'ana iri-iri bisa ga wurin. harsuna da yawa za su mori mabambantan kalmomi domin fassara waɗanan mabambantan ma'anoni.

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: mugunta, tsarki, riba, adalci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

mugunta, mugu, aikin mugunta, abu na mugunta

Ma'ana

Kalmomin nan "mugu" da "mugunta duk suns magana ne akan duk wani abu da ya yi saɓani da nufin Allah mai tsarki.

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: rashin biyyaya, zunubi, nagarta, adalci, aljani)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

rai, rayuka

Ma'ana

Rai shine abin da ba a gani, na cikin mutum, yana nufin ɓangaren da ba jiki ba na cikin mutum.

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

ruhu, ruhohi, ruhaniya

Ma'ana

Kalmar "ruhu" na nufin ɓangaren da ba na jiki ba a cikin mutum wanda ba a iya gani. Idan mutum ya mutu, ruhunsa na barin jikinsa. "Ruhu" akan iya danganta shi da halaiya ko lamiri.

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: mala'ika, aljani, Ruhu Mai Tsarki, rai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

sa'a, sa'o'i, lokaci, nan da nan, har wani lokaci

Ma'ana

Wannan kalma "sa'a" ana amfani da ita a Littafi Mai Tsarki yawancin lokaci domin a faɗi wane lokaci ne a ranar abin nan ya faru. Ana kuma amfani da ita da ma'anar "lokaci" ko "yanzun nan."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

sa'a, sa'o'i

Ma'ana

Buga da ƙari ana magana ne don a nuna yadda da kuma tsawon lokacin da wani abu ya faru "sa'a" an more ta ta hanyoyin salon magana:

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: sa'a)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

salama, masu sulhu

Ma'ana

Wannan kalma "salama" na nufin yanayi ne na jin babu wata matsala, damuwa ko tsoratarwa. Mutum mai "salama" yana da natsuwa kuma yana da tabbacin yana tsare babu abin cutarwa.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

shaida, bada shaida, mashaidi, masu shaida, mashaidi da ido, shaidu da ido

Ma'ana

Sa'ad da wani ya bada "shaida" yana bada bayani game da wani abu wanda ya sani, da jaddada cewa bayanin gaskiya ne. A "bada shaida" shi ne ayi "shaida."

Kalmar "mashaidi" na nufin wani wanda ya fuskanci wani abu da ya faru kai tsaye. Yawanci mashaidi kuma wani ne ko wasu dake shaida kan abin da sukka sani cewa gaskiya ne. Kalmar "mashaidi da ido" na jaddada cewa wannan taliki na wurin kuma yaga abin da ya faru.

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: akwatin alƙawari, laifi, hukunci, annabi, shaida, gaskiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

shaida, ɗauka, yadda

Ma'ana

Wanan kalma "shaida" ma'anarta shi ne bada cikakken nuna sani ga wani abu ko wani mutum.

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: biyayya, ɗaukaka, ceto)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

suna, sunaye, sa suna

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki kalmar nan "suna" an yi amfani da ita domin misali.

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: kira)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

tafiya, yi tafiya

Ma'ana

Kalmar "tafiya" ana amfani da ita a misali da nuna ma'anar "rayuwa."

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: Ruhu Mai Tsarki, girmamawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

yadda, an yadda, abin yadda, isar yadda

Ma'ana

A "yadda" da wani abu ko wani mutum shi ne a gsakata cewa abin ko mutumin gaskiya ne ko abin dogaro ne. Wannan gaskatawar ita ma ana kiranta "yadda." Mutum "abin yadda" shi ne talikin da zaka yadda da shi cewa zai yi kuma zai faɗi abin da ke dai-dai da gaskiya kuma, saboda haka wannan shi ne keda halin "isar yadda."

Shawarwarin Fassara:

(Hakanan duba: bangaskiya, gabagaɗi, gaskatawa, amincewa, gaskiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

zuciya, zukata

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki kalmar nan "zuciya" akan fi yawan moron salon magana a ambaci tunani, lamiri, marmarin, ko abin da mutum ke so.

Shawarwarin Fassara:

̇(Hakanan duba: wuya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki: