1 Littafin asalin Yesu Almasihu Dan Dauda, Dan Ibrahim. 2 Ibrahim shine mahaifin Ishaku, Ishaku shine mahaifin Yakubu, Yakubu shine mahaifin Yahuza da 'yan'uwansa. 3 Yahuza shine mahaifin Farisa da Zera, ta wurin Tamar. Farisa kuma shine mahaifin Hasruna, Hasruna kuma shine mahaifin Aram. 4 Aram shine mahaifin Amminadab, Amminadab shine mahaifin Nashon, Nashon shine mahaifin Salmon. 5 Salmon shine mahaifin Bo'aza ta wurin Rahab, Bo'aza shine mahaifin Obida ta wurin Rut. Obida shine mahaifin Yesse, 6 Yesse shine mahaifin sarki Dauda. Sarki Dauda shine mahaifin Sulaimanu ta wurin matar Uriya. 7 Sulaimanu shine mahaifin Rehobo'am, Rehobo'am shine mahaifin Abija, Abija shine mahaifin Asa. 8 Asa shine mahaifin Yehoshafat, Yehoshafat shine mahaifin Yoram, Yoram kuma shine mahaifin Uziya. 9 Uziya shine mahaifin Yotam, Yotam shine mahaifin Ahaz, Ahaz shine mahaifin Hezekiya. 10 Hezekiya shine mahaifin Manassa, Manassa shine mahaifin Amon, sannan Amon shine mahaifin Yosiya. 11 Yosiya shine mahaifin Yekoniya da 'yan'uwansa, dai dai locacin da aka kwashe su zuwa kasar Babila. 12 Bayan kwasar su zuwa kasar Babila, Yekoniya shine mahaifin Sheyaltiyel, Sheyaltiyel shine mahaifin Zarubabel. 13 Zarubabel shine mahaifin Abihudu, Abihudu shine mahaifin Eliyakim, sannan Eliyakim shine mahaifin Azuru. 14 Azuru shine mahaifin Saduku. Saduku shine mahaifin Akimu, sannan Akimu shine mahaifin Aliyudu 15 Aliyudu shine mahaifin Ali'azara, Ali'azara shine mahaifin Matana, sannan Matana shine mahaifin Yakubu. 16 Yakubu shine mahaifin Yusufu maigidan Maryamu, wadda ta wurin ta ne aka haifi Yesu, wanda ake ce da shi Almasihu. 17 Tun daga Ibrahim zuwa Dauda, an yi tsara goma sha hudu ne, daga Dauda zuwa lokacin da aka kwashe su zuwa Babila, tsara goma sha hudu ne, sannan daga lokacin da aka kwashe su zuwa Babila zuwa Almasihu tsara goma sha hudu ne 18 Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu ta kasance. Mahaifiyarsa, Maryamu, tana tashi da Yusufu, amma kafin su yi aure, sai aka same ta da juna biyu ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 19 Mijinta, Yusufu, adalin mutum ne, amma ba ya so ya kunyatar da ita a sarari. Sai ya yi shawara ya sake ta a asirce. 20 Yana cikin tunanin wadannan al'amura, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gareshi a mafarki, ya ce masa, "Yusufu, dan Dauda, kada ka ji tsoron daukar Maryamu a matsayin matarka. Gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi. 21 Za ta haifi Da, za ka kira sunansa Yesu, domin za ya ceci mutanensa daga zunubansu." 22 Duk wannan ya faru ne domin a cika abinda aka fada ta bakin annabin, cewa, 23 "Duba, budurwa za ta sami juna biyu sannan za ta haifi da, za su kira sunansa Immanuel"-ma'ana, "Allah tare da mu." 24 Yusufu ya farka daga barci, ya yi kamar yadda mala'ikan Ubangiji ya umarce shi, sai ya dauke ta a matsayin matarsa. 25 Amma Yusufu bai sadu da ita ba sai bayan da ta haifi da. Ya kira sunansa Yesu.
Marubucin ya fara da asalin Yesu domin ya nuna cewa Yesu daga zuriyar Sarki Dauda ne da kuma na Ibrahim. An cigaba da asalin har zuwa 1:1-17 .
Za a iya fassara wannan kamar cikakken zance. AT: "Wannan ita ce jerin sunayen kakanin Yesu Almasihu"
Akwai zuriya da yawa tsakanin Yesu, Dauda, da Ibrahim. Anan "ɗa" na nufin "ɗan zuriya". AT: "Yesu Almasihu, zuriyar Dauda, wanda shi zuriyar Ibrahim ne"
A wani lokacin ana amfani da kalmar "ɗan Dauda" kamar laƙani, amma a nan kamar ana amfani da shi a gano zuriyar Yesu.
Akwai hanyoyi dabam dabam da za a iya fassara wannan. A yadda ka fara fassara anan sai a ci gaba har karshen jerin sunayen kakanin Yesu. AT: "Ishaku ɗan Ibrahim"
A nan an riga an fahimci kalmar "shine". AT: "Ishaku shine mahaifin ... Yakubu shine mahaifin"
Wadannan sunayen maza ne.
A nan an riga an fahimci kalmar "shine". AT: "Feresa shine mahaifin ... Hesruna shine mahaifin"
A nan an riga an fahimci kalmar "shine". AT: "Aminadab shine mahaifin ... Nashon shine mahaifin"
Akwai hanyoyi dabam dabam da za a iya fassarar wannan. AT: "Salmon shine mahaifin Bo'aza, Uwar Bo'aza kuwa Rahab ce" ko kuma "Salmon da Rahab sune iyayen Bo'aza"
A nan an riga an fahimci kalmar "shine". AT: "Bo'aza shine mahaifin ... Obida shine mahaifin"
Akwai hanyoyi dabam dabam da za a iya fassarar wannan. AT:"Bo'aza shine mahaifin Obida, Uwar Obida kuma Rut ce" ko kuma "Bo'aza da Rut sune iyayen Obida"
A nan an riga an fahimci kalmar "shine". Akwai hanyoyi dabam dabam da za a iya fassarar wannan. AT: "Dauda shine mahaifin Sulaimanu, Uwar Sulaimanu kuwa matar Uriya ce" ko kuma "Dauda da matar Uriya sune iyayen Sulaimanu "
"gwauruwar Uriya." An haifi Sulaimanu bayar mutuwar Uriya.
A nan an riga an fahimci kamar "shine" a dukka maganar. AT: "Rehobo'am shine mahaifin Abija, Abija shine mahaifin Asa"
Wani lokaci ana fassara wannan haka "Amos"
ana iya amfani da wani kalma dabam da "kakani" idan ana amfani da wannan a nufin iyayen mahaifi ne kadai. AT: "Yosiya kakan Yekoniya ne"
lokacin da aka tilasta su tafiya zuwa Babila" ko kuma "lokacin da mutanen Babila suka Kwace yancin su a yaƙi, suka kuma sa su zama a Babila." idan harshe ku na bukatar a bayyana su wanene suke tafi Babila, za ku iya ce "Isra'ilawa" ko kuma "Isra'ilawan da suke zama a ƙasar Yahuza."
A nan wannan na nifin ƙasar Babila da al'ummar ta, ba birnin kawai ba.
yi amfani da kalmomin da ka mora a Matiyu 1:11.
Sheyaltiyel kakan Zarubabel ne.
Marubucin ya kumshi zuriyar Yesu, da ya fara cikin Matiyu 1:1.
Ana iya faɗin wannan cikin sifar aiki. AT: "Maryamu, wanda ta haifi Yesu"
Ana iya faɗin wannan cikin sifar aiki. AT: "wanda mutane ke kira Almasihu"
"14"
yi amfani da kalmomin da ka mora a Matiyu 1:11.
"Mahaifiyarsa, Maryamu, za ta auri Yusufu." Iyaye su ke shirya auren 'ya'yan su. AT: "Iyayen Maryamu, Mahaifiyar Yesu, sun yi alkawarin auren ta da Yusufu"
fassara wannan ta hanyar da zai nuna cewa ba a haifi Yesu ba a lokacin da Yusufu yake tashin Maryamu. AT: "ana tashin Maryamu, wanda za ta zama Uwar Yesu.
"kafin suyi aure." wannan na iya nufin kafin Maryamu da Yusufu su san juna. AT.: "kafin su san juna"
Ana iya bayyana wannan a sifar aiki. AT: "sai aka gane cewa za ta sami jariri" ko kuma "ya kassance cewa tana da juna biyu"
ikon Ruhu Mai Tsarki ya bata daman sami jariri kafin ta kwana da namiji.
Yusufu bai aure Maryamu ba tukunna, amma a sa'ada namiji da mace sun yi alkawarin aure ga juna, Yahudawa suna ganin su miji da mata, koda yake basu zama tare. AT: " Yusufu, wanda ke tsammani auren Maryamu" ko kuma "Yusufu"
"sokar da shirye shiryen auren su"
"Sa'ada Yusufu na tunani"
"zuwa ma sa a sa'ada Yusufu ke mafarki"
ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. "Ruhu Mai Tsarki ya sa ta kassance da juna biyu"
domin Allah ne ya aiki mala'ikan, shi yasa mala'ika ya san jaririn namiji ne.
"lalle za a ce da sunan sa" ko kuma "lalle za a sa masa suna." Wannan umurni ne.
mai fassara na iya kara matuni a kasa cewa "sunan 'Yesu' na nufin 'Ubangiji yana ceto.'"
wannan na nufin Yahudawa ne.
ba mala'ikan ne ke magana ba yanzu. Matiyu ne ke bayyana muhimmancin abin the mala'ikan ya ce.
ana iya ambata wannan cikin sifar aiki: AT: "abin da Ubangiji ya gaya wa annabin ya rubuta a zammanin da"
Akwai annabawa da yawa. Matiyu na magana game da annabi Ishaya ne. AT: "annabi Ishaya"
Anan Matiyu na ambata rubutun annabi Ishaya,
kula da kyau, domin abin da zan faɗa muhimmin gaskiyane: Budurwan"
Wannan sunan namiji ne.
Wannan baya cikin littafin Ishaya. Matiyu ne ke bayyana ma'anar sunan "Immanuwel." ana iya fassara wannan cikin wani jimla dabam. AT: "sunan na nufin 'Allah tare da mu.'"
Mala'ikan ya gaya wa Yusufu ya dauki Maryamu ta zama matarsa ya kuma kira sunan ɗan Yesu.
"ya aure Maryamu"
"jariri namiji" ko kuma "ɗan ta." tabata ce wa Yusufu bai fito a matsayin ainahin mahaifinsa ba.
"Yusufu ya sa sunan jaririn Yesu"
Magabata biyu da aka lisafta a farko su ne Dauda da Ibrahim.
Maryamu, matar Yusufu aka lisafta, domin ta wurin ta ne aka haifi Yesu.
Maryamu ta sami juna biyu ta wurin Ruhu mai Tsarki kafin su yi aure da Yusufu.
Yusufu, mutum mai dalci ne.
Yusufu ya yi shawara ya sake Maryamu a asirce.
Mala'ika ya faɗa wa Yusufu a mafarki cewa ya ɗauki Maryamu a matsayin matarshi, gama abinda ke cikinta, ta wurin Ruhu Mai Tsarki aka same shi.
An faɗa ya ba wa ɗan suna Yesu saboda zai ceci mutanensa daga zunubansu.
Annabcin Tsohon Alkawari ya faɗa cewa budurwa za ta haifi ɗa, kuma za su kira shi Immanuel, wanda na nufin "Allah tare da mu."
Yusufu ya kula har bai kwana da Maryamu ba sai da ta haifi Yesu.
1 Bayanda aka haifi Yesu a Baitalami ta kasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga wadansu masana daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa, 2 "Ina wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Mun ga tauraronsa a gabas mun kuma zo mu yi masa sujada." 3 Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu kwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima. 4 Hirudus ya tara dukan manyan firistoci da marubuta na jama'a, ya tambaye su, "Ina za a haifi Almasihun?" 5 Suka ce masa, "A Baitalami ne ta kasar Yahudiya, domin haka annabin ya rubuta, 6 'Ke kuma, Baitalami, ta kasar Yahudiya, ba ke ce mafi kankanta ba a cikin shugabanin Yahudiya, domin daga cikin ki mai mulki zai fito wanda zai zama makiyayin jama'a ta Isra'ila.'" 7 Sai Hirudus ya kira masanan a asirce ya tambaye su aininhin lokacin da tauraron ya bayyana. 8 Ya aike su Baitalami, ya ce, "Ku je ku binciko mani dan yaron da kyau. Idan kun same shi, ku kawo mani labari, don ni ma in je in yi masa sujada." 9 Bayan sun ji maganar sarkin, sai suka yi tafiyar su, ga shi kuwa, tauraron da suka gani a gabas yana tafe a gaban su, har ya zo ya tsaya bisa inda dan yaron nan yake. 10 Da suka ga tauraron, sai suka yi matukar farin ciki. 11 Sai suka shiga gidan, suka ga dan yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka rusuna gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka mika masa kyautar su ta zinariya da lubban, da mur. 12 Allah kuma ya gargade su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma kasarsu ta wata hanya dabam. 13 Bayan sun tashi, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki, ya ce, "Tashi, ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka gudu zuwa kasar Masar, ka zauna a can sai na fada maka, don Hirudus yana shirin binciko dan yaron ya hallaka shi." 14 A wannan dare fa Yusufu ya tashi ya dauki dan yaron da mahafiyarsa ya tafi Masar. 15 Ya zauna a can har mutuwar Hirudus. Wannan kuwa domin a cika abin da Ubangiji ya fada ne ta bakin annabin, "Daga Masar na kirawo Da na." 16 Da Hirudus ya ga masanan nan sun shashantar da shi, sai ya hasala kwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa kasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan. 17 A lokacin ne aka cika fadar Annabi Irmiya, 18 "An ji wata murya a Rama, tana kuka da bakin ciki mai zafi, Rahila ce take kuka saboda 'ya'yanta, kuma ta ki ta ta'azantu, domin ba su. 19 Sa'adda Hirudus ya mutu, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusufu a mafarki a Masar ya ce, 20 "Tashi ka dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ka tafi kasar Isra'ila, domin masu neman ran dan yaron sun mutu." 21 Yusufu ya tashi, ya dauki dan yaron da mahaifiyarsa, ya zo kasar Isra'ila. 22 Amma da ya ji Arkilayus ya gaji mahaifinsa Hirudus, yana mulkin kasar Yahudiya, sai ya ji tsoron isa can. Bayan da Allah ya yi masa gargadi a mafarki, sai ya ratse zuwa kasar Galili 23 sai ya je ya zauna a wani gari da ake kira Nazarat. Wannan ya cika abin da aka fada ta bakin annabawa, cewa, za a kira shi Banazare.
A wannan aya an gabatar da sabon labari wanda aka cigaba har karshen ayan nan. Matiyu ya ba da labarin yunkurin Hiridus domin kisan sabon Sarkin Yahudawa.
"ƙasar Baitalami ta yankin Yahudiya"
"a lokacin da Hiridus ke sarki"
Ana nufin Hiridus mai girma ne
"masu Ilimin nazartan sararin sama daga gabas"
"daga wata ƙasa mai nesa a gabarcin Yahudiya
daga ilimin nazarin masanan, tauraron da suka gani na bayyana cewa an haife wanda zai zama sarki. Suna neman inda aka haife jaririn. AT: "Ina jariri da aka haifa wanda zai zama sarkin Yahudawa?"
ba su nufin cewa jaririn ne da tauraron. "tauraron da ya bayyana game da shi" ko kuma "tauraron da ke wakilce haifuwarsa"
"tasowa daga gabas" ko kuma "a lokacin da muke kasarmu"
AT: "suna da niyyar yi wa jaririn sujada a matsayin Ubangiji", ko kuma "suna so su daraja shi kamar sarkin wata ƙasa". Idan a harshen ku akwai wata hanyar bayyana wannan a yi amfani da shi.
" ya damu." Hiridus ya damu cewa wannan jaririn zai maye gurbinsa ta sarauta.
A nan "Urushalima na nufin mutanen ne. kuma "dukka" na nufin "da yawa." Matiyu ya yi magana haka domin ya nanata yadda mutane da yawa sun damu. AT: "Yawancin mutane da ke cikin Urushalima"
Cikin kasar Baitalami ta yanki Yahudiya
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "hakanan ne annabawa suka rubuta da dadewa"
Annabi Mika na magana da mutanen Baitalami kamar suna tare da shi a lokacin da yake magana amma ba haka ba. ana iya fassara "ba ke ce mafi kankanta ba" ta wani hanya. AT: ku mutanen Baitalami, ... kasar ku na cikin muhimman wurare a kasashen da ke Yahudiya"
Annabi Mika na magana game da wannan mai mulkin kamar wani makiyayi. wannan na nufin zai shugabanci, ya kuma kula da jama'an. AT: "wanda zai shugabanci jama'a ta Isra'ila kamar yadda makiyayi ke kiwon tumakinsa"
wannan na nufin Hiridus yayi magana da Masanan ba tare da sanin sauran mutane ba.
Za a iya fassara wannan ta wannan hanyan. AT: "Ya tambaye mazan, wani lokaci ne tauraron ya bayyana? Ya"
Yana nuna cewa Masanan sun faɗa masa lokacin da tauraron ya bayyana. AT: "wani lokaci ne tauraron ya bayyana. Masanan sun gaya wa Hiridus farkon bayyanuwar tauraron"
Wannan na nufin Yesu ne.
"bari in sani" ko kuma "gaya mani" ko "kawo mun rahoto"
dubi yadda aka fassara wannan cikin 2:2.
"Bayan Masanan"
"suka gani ya taso daga gabas" ko kuma " suka gani a kasar su"
"shirye su" ko kuma "jagorance su"
"tsaya bisa"
"wurin da dan jaririn ya ke zama"
zancen anan ya koma gidan da Yusufu, Maryamu, da Yesu suke zama.
"Masanan suka tafi"
AT: "Suka rusuna gabansa suka yi masa sujada" ko kuma "Suka rusuna da fuskansu a ƙasa." Sun yi haka ne domin su darajanta Yesu.
"taska" anan na nufin jakan da suke dauke da dukiyarsu a ciki. AT: "jaka ko akwatin da dukiyarsu ke dauke"
"daga baya kuma, Allah ya gargaɗe Masanan." Allah ya sani cewa Hiridus yana so ya yi lahani ga jaririn.
Ana iya fassara wannan haka. AT: a mafarki cewa, "kada ku koma wurin Sarki Hiridus, sai"
"Masanan sun tashi"
"ya zo wa Yusufu a lokacin da yake mafarki"
Allah na magana da Yusufu ne shi kadai.
ana iya bayyana wannan a sarari kamar haka. AT: har sai na faɗa maka cewa yayi kyau ka dawo"
A nan Allah ne ke magana. Malaika na magana a madadin Allah
ana nufin Yusufu, Maryamu, da Yesu ne suka kasance a Masar. AT: "suka kasance"
Hiridus baya mutu ba sai a 2:19. Wannan maganar na bayyana sawon kasancewarsu a Masar, amma ayan baya faɗa cewa Hiridus ya mutu a lokacin ba..
"na kira ɗa na daga Masar"
A littafin Yusha'u wannan na nufin dukka mutanen Isra'ila ne. Matiyu ya yi irin wannan maganar domin ya nuna gaskiyar cewa Yesu, Ɗan Allah ne. fassara wannan ta hanyar da zaya nuna cewa shine kadai ɗan ko kuma ɗan fari.
AT: "masanan sun kunyatar da shi ta wurin yin masa zamba"
Hiridus bai kashe yaran da hanunsa ba. AT: "Ya umurce sojoji su karkashe 'ya'ya maza" ko kuma " Ya aike sojoji wurin, su karkashe dukka 'ya'ya maza"
"shekaru biyu da wanda ba ya kai ba"
"a bisa lokacin"
ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: Wannan cikar" ko kuma "ayyukan Hiridus ya cika"
ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "abin da Ubangiji ya faɗa da dadewa ta wurin annabi Irimiya"
Matiyu na faɗin maganar annabi Irimiya.
ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "mutane suka ji murya" ko kuma "akwai wata ƙara mai ƙarfi"
Rahila ta yi rayuwa shekaru da yawa kafin wannan lokacin. wannan annabcin ya nuna Rahila, wanda ta mutu tana kuka domin zuriyarta.
ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "ba wanda ya iya ta'azantar da ita"
"domin ta rasa 'ya'yan kuma basu komo ba. Anan "an rasa" wata taushin hanyar cewa sun mutu ne. AT: "domin sun mutu"
Wannan alama ce ta fara fadan wani abu da ya faru cikin babban labari. ana iya samun mutane dabam da wanda suke abin da faru a baya. harshe ku na iya samun da yadda ake fadin wannan.
A nan "neman ran ɗan jaririn" hanyar nuna cewa suna so su kashe jaririn ne. AT: "wanda suke neman jaririn domin so kashe shi"
Wannan na nufin Sarki Hiridus da mashawarcinsa.
"Amma da Yusufu ya ji"
Wannan sunnan ɗan Hiridus ne.
"Yusufu ya ji tsoro"
ana iya faɗin wannan cikin sifar aiki. AT: "abin da Ubangiji ya faɗa da dadewa ta bakin annabawa"
"shi" anan na nufin Yesu. kafin lokacin zuwan Yesu annabawa sun ce da shi Mai ceto ko kuma Almasihu. AT: "mutuna za su ce Almasihu Banazare ne"
An haifi Yesu a Baitalami ta Yahudiya.
Masana daga gabas suka ba wa Yesu laƙamin "Sarkin Yahudawa."
Masanan sun ga tauraron Sarkin Yahudawa a gabas.
Da sarki Hirudus ya ji labarin, sai ya damu kwarai.
Sun san annabcin da ya faɗa cewa za a haifi Almasihu a Baitalami
Tauraro a gabas ya tafi a gabansu, har ya zo ya tsaya bisa inda Yesu yake.
Yesu ƙaramin yaro ne a loƙacin da masanan sun zo su gan shi.
Masanan sun ba wa Yesu ƙyautar zinariya, turare, da mur.
Masanan sun koma gida ta wata hanya domin Allaha ya gargade su a mafaiki cewa kada su koma wurin Hirudus.
An umarce Yusufu a mafarki cewa ya ɗauki Yesu da Maryamu ya gudu zuwa Masar, domin Hirudus na so ya ƙashe Yesu.
Annabcin, ''Daga Masar na kirawo Ɗa na'' ya cika a loƙacin da Yesu ya dawo daga Masar.
Hirudus ya ƙarkashe dukan 'yan maza da yankin Baitalami wanda suke shekara biyu zuwa kasa.
An umarce Yusufu a mafarki cewa ya dawo ƙasar Isra'ila.
Yusufu ya zauna da Maryamu da Yesu a Nazaret a Galili.
Annabcin cewa za a kira Almasihun Banazare.
1 A kwanakin nan Yahaya Mai baftisma ya zo, yana wa'azi a jejin Yahudiya yana cewa, 2 "Ku tuba, domin mulkin sama ya kusa." 3 Wannan shine wanda annabi Ishaya ya yi maganarsa, ya ce, "Muryar wani mai kira a jeji yana cewa, 'Ku shirya wa Ubangiji hanyarsa, ku daidaita tafarkunsa." 4 Yahaya kuwa yana sanye da tufa ta gashin rakumi, yana kuma daure da damarar fata, abincinsa kuwa fara ne da zuman jeji. 5 Sai mutanen Urushalima, da na dukan Yahudiya, da na duk kasashen bakin Kogin Urdun, suka yi ta zuwa wurin sa. 6 Ya yi masu baftisma a Kogin Urdun, yayinda suke furta zunubansu. 7 Amma da ya ga Farisawa da Sadukiyawa da yawa, suna fitowa domin a yi masu baftisma, sai ya ce masu, "Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargade ku ku guje wa fushi mai zuwa? 8 Ku ba da 'ya'ya da za su nuna tubanku. 9 Kada kuwa ku dauka a ranku cewa, 'Ibrahim ne ubanmu.' Domin ina gaya maku, Allah yana da iko ya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin duwatsun nan. 10 Ko yanzu ma an sa gatari a gindin bishiyoyin. Saboda haka duk bishiyar da ba ta ba da 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta. 11 Na yi maku baftisma da ruwa, zuwa tuba. Amma mai zuwa baya na, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in dauka ba. Shi ne zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta. 12 Kwaryar shikarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai, ya tara alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma zai kona buntun da wutar da ba za a iya kashewa ba." 13 Sai Yesu ya zo daga kasar Galili, ya je Kogin Urdun wurin Yahaya, domin ya yi masa baftisma. 14 Amma Yahaya ya yi ta kokarin ya hana shi, yana cewa, "Ni da nake bukatar ka yi mani baftisma, ka zo gare ni?" 15 Yesu ya amsa masa ya ce, "Bari ya zama haka a yanzu, domin a cika dukan adalci." Sai Yahaya ya yarje masa. 16 Bayan da aka yi masa baftisma, Yesu ya fito nan da nan daga cikin ruwan, sai kuma sammai suka bude masa. Ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya, ya sauko a kansa. 17 Duba, wata murya daga sammai tana cewa, "Wannan shi ne kaunataccen Da na. Wanda ya gamshe ni sosai."
A Wannan sashin Matiyu ya fara ba da sabon labari game da hidimar bishara na Yahaya mai Baftisma. A aya Uku ta (3), Matiyu ya ambata maganar annabi Ishaya domin ya nuna cewa Yahaya mai Baftisma shine zabaɓen dan saƙon da zai shirya hidimar bisharar Yesu.
Wannan wasu shekaru ne bayan Yusufu ya bar Masar zuwa Nazarat. Wannan na yiyuwa kusa da lokacin da Yesu zai fara hidimar bishararsa. AT: " A bayan wasu lokaci" ko kuma "Bayan wasu shekaru"
Yahaya na magana da taro ne.
"mulkin sama" na nufin Allah na mulki kamar sarki. AT: "Allahnmu na sama zai nuna kansa a matsayin sarki bada jimawa ba"
ga wata hanyar faɗin wannan. AT: Gama annabi Ishaya yayi magana game da Yahaya mai Baftisma lokacin da ya ce"
Ana iya faɗin wannan cikin wata jimla kuma. AT: "An ji muryan wani na kira daga cikin jeji" ko kuma "Sun ji ƙarar wani da ke kira daga cikin jeji"
wannan jimlu biyun na nufin abu daya ne.
"Shirya hanyar Ubangiji"." Yin haka na nuna shirin jin sakon Ubangiji lokacin da ya zo. Mutane na yin haka tawurin tuba daga zunubansa. AT: "shirya domin jin sakon Ubangiji lokacin da ya zo" ko kuma "Tuba da kuma shiri domin zuwan Ubangiji"
A nan Matiyu na ba da wani muhimmin bayyani game da Yahaya mai Baftisma, shiyasa ya amfani da kalman "Yanzu kuwa" domin ya ba da wannan ƙarin hasken.
Irin wannan tufafi na ba da hoton cewa Yahaya mai Baftisma annabi ne kamar annabawan da, musamman annabi Iliya.
"Urushalima", "Yahudiya", da "kasashen da ke yankin" na nufin mutanen da ke cikin kasashen ne. kalman "dukka" na nuna cewa yawacin mutanen sun fito. AT: Sai mutane da yawa daga Urushalima, Yahudiya, da kasashen yankin"
Ana iya faɗin wannan ta wata hanya. AT: "Yahaya yayi masu Baftisma"
Wannan na nufin mutane daga Urushalima, Yahudiya, da kasashen da ke yankin kogin Urdu.
A nan " 'ya'ya" na nufin "yanayin halayya kamar." Macizai masu dafi na ba hoton miyagu ko mugunta. AT: "Ku mugayen macizai masu dafi! wa ya" ko kuma "Ku mugaye kamar macizai masu dafi! Wa ya"
Yahaya ya yi amfani da tambaya domin ya tsautawa farisawa da sadukiyawa wanda suna so ya yi masu baftisma domin su gujewa hukuncin Allah, amma ba su so su daina aikata zunubi. AT: "ba za ku iya guje wa fushin Allah haka ba." ko kuma "kada ku yi tunani cewa za ku gujewa fushin Allah wai domin na yi maku baftisma."
kalmar "fushi" na nufin hukuncin Allah domin fushinsa na zuwa kafin hukuncin. AT:"guje wa hukunci da ke zuwa " ko kuma "kuɓuta daga hukucin Allah a gare ku"
maganar "ba da 'ya'ya" na nufin halayyan mutum. AT: "Bari ayukkan ku su nuna cewa tũbanku na gaskiya ne"
"Ibrahim kakanmu ne" ko kuma "mu zuriyar Ibrahim ne." Shugabanin Yahudawa na tunani cewa Allah ba zai hukuntasu ba domin su zuriyar Ibrahim ne.
Wannan na kara karfin maganar da Yahaya zai yi.
Allah yana da iko ya wa Ibrahim zuriyar ta jiki daga duwatsun nan"
Yahaya mai Baftisma ya cigaba da tsautawa Farisawa da Sadukiyawa.
Wannan na nufin Allah na shirye ya hukunta masu zunubi. Za a iya bayana wannan ta wata hanya. AT: "Allah na shirye da gatarinsa ya sare duk itãcen da ta ke ba da mumunan 'ya'ya ya kuma kona ta" ko kuma "Kamar yadda mutum ke shirya gatarinsa domin ya sare itãcen da ke ba da 'ya'ya marasa kyau domin ya kone ta, haka Allah ke shirye domin ya hukunta ku sabili da zunubanku"
"nuna cewa an tũba"
Yesu shine mutumin da ke zuwa bayan Yahaya.
"yana da muhimmanci fiye da ni"
Ana kamanta baftisman da Yahaya ke yi da ruwa da kuma baftisma da ke zuwa na wuta. Wannan na nuna cewa baftisma Yahaya alama ce na tsaftace mutane daga zunuban su. Baftismar Ruhu mai Tsarki da wuta kuma shine ke da gaskiyar ikon wanke mutane daga zunubansu.
Wannan na kwatanta yadda Almasihu zai ware adalai da marasa adalci kamar yadda mutum ke ware alkama da ɓuntu. AT: "Almasihu na kamar mutumin da kwaryar shiƙarsa na hannunsa"
Anan "na hannunsa" na nufin mutum da ke shirye domin aiki. AT: "Almasihu na rike da Kwaryar shiƙarsa domin yana shirye"
Wannan kayan aikin sheke alkama ne domin a ware alkaman da ɓuntu. Ana jefa su sama amma alkaman na saukowa, sai iska ya kwaso ɓuntun zuwa wata gefe.
Almasihu na kamar mutumin da ke rike da Kwaryar shiƙarsa domin ya share masussukarsa.
"filinsa" ko kuma "filin ƙasa inda yake ware hatsin daga ɓutun"
Wannan na nuna yadda Allah zai ware adalai daga miyagu mutane. Adalai kuwa za su sama kamar yadda manomi ke tãra alkama a rumbu, sai Allah ya ƙone mutanen da ke kamar ɓuntu da wutan da ba za a iya kashewa ba.
AT: "ba za ta taba karewa ba"
AT: "don Yahaya ya iya masa baftisma"
Yahaya ya yi amfani da tambaya ya nuna mamakinsa game da buƙatan da Yesu ke yi. AT: " Kafini muhimmanci. baikamata in yi maka baftisma ba. Kai yakamata kayi mani baftisma."
A nan "mu" na nufin Yesu da Yahaya.
AT: "Bayan da Yahaya yi wa Yesu baftisma"
kalmar "gashi" anan na jan hankalimu zuwa ga sako mai ban mamaki da ke zuwa.
ga wata hanyar sa wannan. AT: "Yesu ya ga sama ta bude" ko kuma "Allah ya bude samai wa Yesu"
AT: "wannan magana na nufin cewa Ruhun na kamar kurciya or "Ruhun ya sauko akan Yesu a hankali kamar yadda kurciya ke yi.
"Yesu ya ji murya daga sama." Anan "murya" na nufin Allah ne ke magana. AT: "Allah ya yi magana daga sama"
Wannan muhimmin laƙani ne na Yesu da ke bayyana dangantakarsa da Allah.
Ku tuba, domin mulkin sama ya kusa.
Annabcin ya faɗi cewa Yahaya mai baftisma zai shirya hanyar Ubangiji.
Sa'ad da an yi masu baftisma, mutanen suka furta zunubansu.
Yahaya mai baftisma ya gaya wa Farisawa da Sadukiyawa cewa su ba da 'ya'ya da ya cancanci tubarsu.
Yahaya ya kwaɓe Farisawa da Sadukiyawa cewa kada kuwa su ɗauka a ransu wai, Ibrahim ne ubansu.
Yahaya ya ce duk itacen da ba ta ba da 'ya'ya masu kyau ana sare ta a jefa a wuta.
Wanda na zuwa a bayan Yahaya zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.
Yesu ya ce daidai ne Yahaya ya yi masa baftisma domin a cika dukan adalci.
A loƙacin da ya fita daga ruwa, Yesu ya gan Ruhun Allah ya na saukowa kamar kurciya, ya kuma na bayyana a kansa.
Murya daga sama ya ce, "Wannan shi ne ƙaunataccen Ɗa na, wanda ya gamshe ni sosai.''
1 Sa'an nan Ruhu ya bi da Yesu zuwa cikin jeji, domin Ibilis ya gwada shi. 2 Da ya yi azumi kwana arba'in dare da rana, daga baya yunwa ta kama shi. 3 Sai mai jarabtar nan ya zo, ya ce masa, "Idan kai Dan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa." 4 Amma Yesu ya amsa ya ce masa, "A rubuce yake cewa, 'Ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace magana da ta ke fitowa daga wurin Allah.'" 5 Sa'an nan Ibilis ya kai shi tsattsarkan birni ya dora shi can kan kololuwar ginin haikali, 6 ya ce masa, "In kai Dan Allah ne, to dira kasa. Domin a rubuce yake cewa, 'Zai ba mala'ikunsa umarni game da kai,' kuma, 'Za su daga ka da hannuwansu, domin kada ka yi tuntube da dutse.'" 7 Yesu ya ce masa, "kuma a rubuce yake, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.'" 8 Kuma, sai Ibilis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo kwarai, ya nuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. 9 Ya ce masa, "Dukan wadannan zan baka idan ka rusuna ka yi mani sujada." 10 Sai Yesu ya ce masa, "Tafi daga nan, Shaidan! Domin a rubuce yake, 'Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.'" 11 Sa'an nan Ibilis ya rabu da shi, sai kuma mala'iku suka zo suka yi masa hidima. 12 To, da Yesu ya ji an kama Yahaya, sai ya tashi zuwa kasar Galili. 13 Ya bar Nazarat, ya koma Kafarnahum da zama, can bakin tekun Galili, kan iyakar kasar Zabaluna da Naftali. 14 Wannan ya faru domin a cika fadar annabi Ishaya cewa, 15 "Kasar Zabaluna da kasar Naftali, ta bakin teku, da hayin Kogin Urdun, Galili ta al'ummai! 16 Mutane mazauna duhu suka ga babban haske, sannan ga wadanda ke zaune a yankin da inuwar mutuwa, haske ya keto masu." 17 Daga lokacin nan, Yesu ya fara wa'azi, yana cewa, "Ku tuba domin mulkin sama ya kusa." 18 Yana tafiya a bakin tekun Galili, sai ya ga wadansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, domin su masunta ne. 19 Yesu ya ce masu, "Ku zo, ku biyo ni, zan mai da ku masuntan mutane." 20 Nan da nan sai suka bar tarunsu, suka bi shi. 21 Da Yesu ya ci gaba da tafiya, sai ya ga wadansu mutum biyu, su kuma 'yan'uwa ne, Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya, suna cikin jirgi tare da mahaifinsu Zabadi, suna gyaran tarunsu. Sai ya kira su. 22 Nan take suka bar mahaifinsu da jirgin, suka bi shi. 23 Yesu ya zazzaga dukan kasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar mulkin, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya a cikin mutane. 24 Labarinsa ya bazu a cikin dukan kasar Suriya, kuma mutanen suka kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farfadiya, da shanyayyu. Yesu ya warkar da su. 25 Taro masu yawa suka bi shi daga kasar Galili, da Dikafolis, da Urushalima, da kasar Yahudiya, har ma daga hayin Urdun.
A nan Matiyu ya fara ba da sabowar labari game da yadda Yesu yayi kwanaki arba'in a cikin jeji, anan ne Shaidan ya jarabce shi. a aya 4, Yesu ya tsuata wa Shaidan ta ruwaito magana a Maimaitawar Shariya.
AT: "Ruhun ya kai Yesu"
AT: "domin Iblis ya jarabci Yesu"
Wannan na nufin mutun ɗaya ne. Ya yiwu lalle ka yi amfani da dukka kalmomin domin fasara.
A magana game da Yesu ne.
"rana 40 da dare 40." Wannan na nufin sa'an lokaci 24. AT: "kwanaki 40"
Ya fi kyau a yi tsamanin cewa Shaidan ya san wai Yesu Ɗan Allah ne. Ya yiwu ana nufin 1) Wannan jaraba ne domin Yesu ya yi al'ajabi domin amfanin kansa. AT: "Domin kai Ɗan Allah ne, za ka iya umurci" ko 2) Wannan tuhuma ne ko zargi. AT: "ka hakikanta kai Ɗan Allah ne ta wurin umurtan"
Wannan muhimmin laƙani ne na Yesu ne da ke nuna dangantakar sa da Allah.
kana iya fasarar wannan ta wurin ruwaito maganar. AT: "ce da waɗannan duwatsun, 'Ku zama gurasa.'"
A nan "gurasa" na nufin kowani irin abinci. AT: "abinci"
AT: "Musa ya rubuto wannan a cikin nassosi tun da daɗewa"
Wannan na nuna cewa akwai wani abu game da ruwa da ya fi gurasa muhimminci.
Anan "magana" da "baki" na nufin abun da Allah ya ce. AT: "amma sai ta wurin sauraron dukka abun da Allah ya ce"
Ya fi kyau a yi tsamanin cewa Shaiɗan ya san wai Yesu Ɗan Allah ne. Ya yiwu ana nufin 1)Wannan jaraba ne domin Yesu ya yi al'ajabi domin amfanin kansa. AT: "Tun da shike da gaske kai Ɗan Allah ne, ka dira ƙasa" ko 2) Wannan tuhuma ne ko zargi. AT: "ka hakikanta gaskiyar cewa kai Ɗan Allah ne ta wurin dirowa da kanka ƙasa"
"bar kai da kanka ka dira zuwa ƙasa" ko "yi tsalle zuwa ƙasa"
AT: "gama ma rubucin ya rubuto a cikin nassosin" ko "domin nassosin ya ce"
"Allah zai umurce malai'ikunsa su lura da kai, kuma "Ana iya fasarar wannan ta wurin ruwaito magana. AT: "Allah zai ce da malai'ikunsa, "ku lura da shi", kuma"
" malai'ikunsa zasu riƙe ka"
An gane cewa Yesu na ruwaito nassi ne kuma. AT: Kuma, zan gaya maka abun da Musa ya rubuto a cikin nassosin"
Anan "ka" na nufin kowani mutum. AT: "kada wani ya gwada" ko "kar wani mutum ya gwada"
"daga nan, Iblis"
"Iblis ya ce wa Yesu"
"zan ba ka duk waɗannan abubuwan." majarabcin na jadada cewa zai bayar da "dukka waɗannan abubuwan," ba wai wasu ba.
"sa fuskar ka a ƙasa". An saba yin wannan domin nuna cewa mutum na sujada ne.
Wannan shine karshen sashin labari game da yadda Shaiɗan ya jarabce Yesu.
wannan umurni ne ga kowa da ke ji.
Kalmar "gashi" na jawo hankalin mu ne ga wani sabon bayani mai muhimmanci da ke zuwa.
Ana amfani da wannan kalma domin a dakatar da asalin labari da ake bayarwa. Matiyu ya fara bayar da wani sabon sashin labarin.
AT: "Tsarkin ya tsare Yahaya"
"Zabaluna da Naftali" sunayen zuriyar da suke zama a waɗannan yankuna ne shekaru da yawa da suka wuce kafin baƙi suka ɗauki iko akan ƙasar Isra'ila.
Wannan na nufin tafiyar Yesu zuwa Kafarnahum ya zauna.
AT: "Abun da Allah ya faɗa"
Waɗannan yankunan su na bayana wuri daya ne. Za a iya ambata waɗannan yankunan a cikin jimla. AT: "Cikin yankinZabaluna da Naftali ... cikin yankin Galili inda al'ummai ke zama, Mutanen da ke zama"
Wannan tekun Galili ne.
A nan "duhu" na nufin rashin sanin gaskiyar game da Allah. "haske" kuma na nufin gaskiyar maganar Allah da ke ceton mutane daga zunuban su.
Wannan na nufin abu daya ne da farkon sashin jimlar. Anan "waɗanda ke zaune a yankin, da inuwar mutuwa" ƙarin magane. yana nufin waɗanda basu san Allah ba. Waɗannan mutane na haɗari mutuwa da rabuwa da Allah har abada.
maganar "mulkin sama" na nufin shugabanci Allah a matsayin Tsarki. Wannan maganar na littafin Matiyu ne kadai. Dubi yadda aka fasara wannan a Matiyu 3:2. AT: "Allahnmu na cikin sama zai nuna kansa a matsayin Tsarki"
Ana iya bayana cikakiyar ma'anar wannan maganar a fili. AT: "jefan taru a cikin ruwa domin su kama kifi"
Yesu ya gayyato Saminu da Andrawus su biyo shi, su yi rayuwa da shi, su kuma kasance almajiransa. AT: "zama almajirai na"
Wannan ƙarin magana ne da ke nufin Saminu da Andrawus za su zama masu koyar da gaskiyar maganar Allah ga mutane, domin wasu ma su bi Yesu. AT: "Zan koyar da ku yadda za ku taro mutane wurina kamar yadda kuke taro kifi"
"Yesu ya kira Yahaya da Yakub." Wannan maganar na nufin cewa Yesu ya gayyace su, su biyo shi, su yi rayuwa da shi, su kuma zama almajiransa.
"nan da nan suka bar"
Yakamata ya zama a fili cewa wannan canjin rayuwa ne. Waɗannan mutanen baza su cigaba zama masunta ba, kuma za su bar kasuwanci iyalinsu su kuma bi Yesu dukka rayuwarsu.
"koyarwa a cikin majami'un Galilawa" ko "koyarwa a cikin majami'un waɗancan mutanen"
A nan "Mulki" na nufin shugabancin Allah a matsayin sarki. AT: "shelar bishara game da yadda Allah zai nuna kansa a matsayin tsarki"
kalmomin nan "cuta" da "ciwo" na da danganta sosai, amma a fasara su a matsayin kalmomi dabam dabam in ya yiwu. "cuta" shi ya ke sa mutum ya yi ciwo.
wannan rauni ne ko annoba ta jiki da ke samuwa daga cuta.
AT: "waɗanda suke karkashin mulkin aljannu"
Wannan na nufin kuwanene da ke da farfaɗiya a wurin, ba wai akwai wani da ake nufi ba na musammanda ke da farfaɗiya. AT: "waɗanda suke figar ruwa loto-loto" ko "waɗanda suke suma loto-loto da wanda baza a iya shawo kansa ba"
Wannan na nufin kuwanene da ke shanyayye a wurin, ba wai akwai wani da ake nufi ba na musamman da ke shanyayye. AT: "da kuma duk wanda ke shanyayye" ko "da waɗanda ba su iya tafiya ba"
Wannan sunan na nufin "garuruwa goma." Wannan sunan wani yanki ne kudu maso gabas da tekun Galili.
Ruhu mai Tsarki ya bi da Yesu zuwa cikin jeji, domin Ibilis ya gwada shi.
Yesu ya yi azumi kwana arba'in dare da rana a cijin jeji.
Ibilis ya jarabci Yesu da cewa Yesu ya mayar da duwatsu su zama gurasa.
Yesu ya faɗa cewa ba da gurasa kadai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace magana da ta ke fitowa daga wurin Allah.''
Ibilis ya gwada Yesu da cewa ya jefa kansa daga haikalin.
Yesu ya faɗa cewa kada ka gwada Ubangiji Allahnka.
Ibilis ya gwada Yesu da cewa Yesu ya bauta masa sai ya ba shi dukka mulkin duniya.
Yesu ya faɗa cewa ɗole ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kadai za ka bauta wa.
Annabcin Ishaya ya cika wanda ya faɗa cewa mutanen Galili za su gan babban haske.
Yesu ya yi wa'azi, "Ku tuba domin mulkin sama ya yi kusa".
Bitrus da Andarawas masu masunta ne.
Yesu ya faɗa cewa zai sa Bitrus da Andarawas su zama masu masuntan mutane.
Yakubu da Yahaya masu masunta ne.
Yesu ya yi koyarwa a majami'un Galili.
An kawo wa Yesu dukan marasa lafiya da masu aljannu, kuma Yesu ya warkar da su.
Taro masu yawa suka bin Yesu a wannan loƙaci.
1 Da Yesu ya ga taron jama'ar, sai ya hau saman dutse. Sa'adda ya zauna, almajiransa suka zo wurinsa. 2 Ya bude bakinsa kuma ya koyar da su, yana cewa, 3 "Albarka ta tabbata ga masu talauci a ruhu, domin mulkin sama nasu ne. 4 Albarka ta tabbata ga masu makoki, domin za a ta'azantar da su. 5 Albarka ta tabbata ga masu tawali'u, domin za su gaji duniya. 6 Albarka ta tabbata ga masu yunwa da kishin adalci, domin za a kosar da su. 7 Albarka ta tabbata ga masu jinkai, domin za su samu jinkai. 8 Albarka ta tabbata ga masu tsabtar zuciya, domin za su ga Allah. 9 Albarka ta tabbata ga masu kawo salama, domin za a ce da su 'ya'yan Allah. 10 Albarka ta tabbata ga wadanda ake tsananta masu saboda adalci, domin mulkin sama nasu ne. 11 Masu albarka ne ku sa'adda mutane suka zage ku, suka kuma tsananta maku, ko kuwa suka zarge ku da dukan miyagun abubuwa iri iri na karya, saboda ni. 12 Ku yi murna da matukar farin ciki, domin sakamakonku mai yawan gaske ne a sama. Ta haka ne mutane suka tsananta wa annabawa da suka yi rayuwa kafin ku. 13 Ku ne gishirin duniya, amma idan gishiri ya sane yaya za a mai da dandanonsa? Ba zai kara anfani ga komai ba, sai ko a zubar da shi, a tattake a karkashin kafafun mutane. 14 Ku ne hasken duniya, birnin da ke kan tudu ba shi boyuwa. 15 Mutane ba za su kunna fitila su sa ta karkashin kwando ba, sai ko a dora ta a mazaunin ta, domin ta ba da haske ga kowa da ke gidan. 16 Bari hasken ku ya haskaka gaban mutane yadda za su ga kyawawan ayyukanku su kuma yabi Ubanku da ke cikin sama. 17 Kada ku yi tsammanin na zo ne domin in rushe shari'a ko annabawa. Ban zo domin in rushe su ba, amma domin in cika su. 18 Domin gaskiya ina gaya maku, har sama da kasa su shude, amma digo ko wasali daya ba za ya shude ba a cikin shari'ar, sai an cika dukan al'amura. 19 Saboda haka duk wanda ya karya mafi kankanta daga cikin dokokin nan ko kuwa ya koya wa wasu su yi haka, za a kira shi mafi kankanta a cikin mulkin sama. Amma dukan wanda ya kiyaye su ko kuwa ya koyar da su, za a kira shi mafi girma a cikin mulkin sama. 20 Gama ina gaya maku cewa idan adalcin ku bai zarce adalcin marubuta da Farisawa ba, babu yadda za ku shiga mulkin sama. 21 Kun ji dai an ce wa mutanen da, 'Kada ka yi kisan kai,' kuma 'Duk wanda ya yi kisan kai yana cikin hatsarin hukunci.' 22 Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da dan'uwansa, yana cikin hatsarin hukunci. Kuma duk wanda ya ce da dan'uwansa, 'Kai mutumin banza!' yana cikin hatsarin tsayawa gaban majalisa, kowa kuma ya ce da dan'uwan sa 'Kai wawa!' yana cikin hatsarin shiga wutar jahannama. 23 Saboda haka idan za ka yi baiko a bagadi sai ka tuna cewa dan'uwanka yana da damuwa da kai, 24 ka bar baikon ka a gaban bagadin, ka yi tafiyarka. Da farko dai, ka sasanta da dan'uwanka kafin ka zo ka mika baikon. 25 Ka yi sulhu da mai karar ka tun kana hanyar zuwa gaban shari'a, domin kada mai karar ka ya mika ka ga alkali, alkali kuwa ya mika ka ga dogarai, za a kuwa jefa ka a kurkuku. 26 Gaskiya ina gaya maka, ba za ka taba fita daga can ba sai ko ka biya dukan kudin da ya ke binka. 27 Kun dai ji an ce, 'Kada ka yi zina'. 28 Amma ina gaya maku, duk wanda ya dubi mace, da muguwar sha'awa, ya riga ya yi zina da ita a zuciyarsa. 29 Idan idonka na dama zai sa ka tuntube, kwakule shi ka jefar daga gareka. Don gara daya daga cikin gabobinka ya halaka, da a jefa dukan jikin ka a jahannama. 30 Ko kuwa idan hannunka na dama zai sa ka tuntube, ka yanke shi ka jefar daga gare ka. Domin gara daya daga cikin gabobin ka ya halaka, da a jefa dukan jikinka a jahannama. 31 An sake fada, 'Duk wanda ya kori matarsa, sai ya ba ta takaddar saki.' 32 Amma ina gaya maku ko wa ya saki matarsa, idan ba a kan laifin lalata ba, ya mai da ita mazinaciya kenan. Kuma duk wanda ya aure ta bayan sakin, ya yi zina kenan. 33 Kun sake ji an ce wa wadan da suke a zamanin da, 'Kada ku yi rantsuwar karya, amma ku yi rantsuwar ku ga Ubangiji.' 34 Amma ina gaya maku, kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama domin kursuyin Allah ne; 35 ko kuwa da duniya, domin mazaunin kafafunsa ne, ko da Urushalima, domin birnin babban sarki ne. 36 Ko ma ace ku yi rantsuwa da kanku, domin ba za ku iya mai da gashin kanku baki ko fari ba. 37 Amma bari maganarku ta zama 'I, I', ko kuwa 'A'a, a'a.' Duk abin da ya wuce wannan, daga mugun yake. 38 Kun dai ji an ce, "Ido a maimakon ido, hakori kuma a maimakon hakori.' 39 Amma ina gaya maku, kada ku yi jayayya da wanda ke mugu, a maimakon haka, ko wa ya mare ku a kuncin dama, ku juya masa dayan ma. 40 Idan wani yana da niyyar kai kararku gaban shari'a saboda ya karbi rigarku, ku ba wannan mutumin mayafinku ma. 41 Duk wanda ya tilasta ku ga tafiyar mil daya, ku je da shi biyu. 42 Ku ba kowa da ya tambaye ku, kuma kada ku hana kowa da ke neman rance a wurinku. 43 Kun ji abin da aka fada, 'Za ka kaunaci makwabcin ka ka ki magabcin ka.' 44 Amma ina gaya maku, ku kaunaci magabtan ku, ku yi addu'a domin masu tsananta maku, ku albarkaci wadanda suka la'ance ku, ku yi alheri ga wadanda suke kin ku, 45 domin ku zama 'ya'yan Ubanku da ke cikin sama. Domin yakan sa rana ta haskaka wa mugu da mutumin kirki, kuma yakan aiko da ruwan sama ga adali da azzalumi. 46 Domin idan kuna kaunar wadanda suke kaunarku, wanne lada kuka samu? Ba haka masu karban haraji ma suke yi ba? 47 Kuma in kun gaida 'yan'uwanku kadai, me kuke yi fiye da sauran? Ba hakanan al'ummai ma suke yi ba? 48 Saboda haka, lalle ne ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na sama yake cikakke.
Wannan farkon sabuwar sashin labari ne da Yesu ya fara koyad da almajiran sa. Wannan sashin ya cigaba har zuwa karshen sura 7, an saba ce da wannan sashin huɗuba akan dutse.
Yesu ya fara bayana halayen mutane da suke da albarka a aya 3.
AT: "Yesu ya fara magana"
Kalmar "su" na nufin almajiransa.
Wannan na nufin wanda yake da tawali'u. AT: "waɗanda sun san bukatan su na Allah"
A nan "mulkin sama" na nufin Allah na mulki a matsayin sarki. A littafin Matiyu ne kadai aka ambata wannan. In ya yiwu, a sa "sama" a cikin fasara. AT: " gama Allah na sama zai zama tsarkin su"
Mai yiwuwa dalilin baƙin cikinsu su ne 1) yadda duniya ke cike da zunubi, ko 2) zunubansu, 3) mutuwar wani. kada a ba da takameme dalili nadămar, saidai harshan ku na bukatar wannan.
AT: "Allah zai sanyaya musu rai"
"mai kyakkyawan dabi'a" ko kuma "waɗanda basu dogara da karfin su"
"Allah zai ba su dukkan duniya"
Wannan na bayana mutanen da suke marmarin aikata abun da ke daidai. AT: "waɗanda suke marmarin aikata abun da ke daidai kamar yadda suke marmarin abinci da ruwan sha"
AT: "Allah zai cika muradinsu" ko "Allah zai gamsad da su"
"mutanen da zuciyar su na da tsarki." A nan "zuciya" na nufin asalin cikin mutum ko niyyar sa. AT: "waɗanda marmarin su kadai shine su bauta wa Allah"
A nan "ga" na nufin za su iya kasancewa tare da Allah. AT: Allah zai yardar musu su kasance tare da shi"
waɗannan mutane ne masu taimaka daidaita zaman salama tsakanin wasu.
AT: "gama Allah zai kira su 'ya'yan sa" ko "zasu kasance 'ya'yan Allah"
Ya fi kyau a fasara " 'ya'ya" yadda ake ce da yaran mutum a harshen ku.
AT: "mutane wanda ba a yi musu kirki ba"
"domin suna aikata abun da Allah ke so su yi"
A nan "mulkin sama" na nufin shugabancin Allah a matsayin sarki. Wannan maganar na littafin Matiyu ne kadai. In ya yiwu a sa kalmar "sama" a fassara. Duba yadda ku ka fassara wannan a 5:3. AT: "gama Allah na sama zai zama tsarkin su"
"faɗa kowace irin muguwar karya game da ku" ko "faɗin mumunar abubuwa game da ku da ba gaskiya ba"
"domin ku mabiya na ne" ko "domin kun gaskanta a gare ni"
"Murna" da "farin ciki matuƙa" na nufin kusan abu ɗaya. Yesu na so masu sauraron sa su kasance ba da murna kadai, in akwai abun da ya fi murna shi ya ke so su yi.
Mai yiwuwa ana nufi 1) kamar yadda gishiri ke sa abinci dadi, haka almajiran Yesu ke rinjayar mutane duniya domin su zama mutanen kirki. AT: " Kuna kamar gishiri ne ga mutanen duniya" ko 2) kamar yadda gishiri ke adana abinci haka almajiran Yesu ma suke kiyaye mutane daga ɓace wa. AT: "Kamar yadda gishiri ke a abinci, haka ku ke a duniya"
Mai yiwuwa ana nufi 1) "idan gishiri ya rasa ikon yin aikin sa na matsayin gishiri" ko 2) "in gishiri ya rasa ɗanɗano shi."
"yaya za a mayar da shi mai amfani kuma?" Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya koyad da almajiran sa. AT: "ba yadda za a iya amfani da shi kuma ba."
AT: "sai dai mutane su zubar da shi a kan yanya su kuma taka akai"
Wannan na nufi cewa mabiyen Yesu ke kawo saƙon gaskiyar maganar Allah ga mutane da basu san Allah ba. AT: "Ku na kamar haske ne ga mutanen duniya"
Da dare mutane na iya ganin hasken birnin na haskakawa. AT: "Da dare, ba mai iya ɓoye hasken da ke haskakawa a birnin da ke kan tudu" "Kowa na ganin hasken birnin da ke kan tudu"
"mutane ba su kunna fitila"
"sa fitilar a karkashin kwando." Wannan na nufi cewa wauta ne a kunna haske sa'anan a ɓoye ta domin kar mutane su ga hasken fitilar.
Wannan na nufin cewa ya kammata almajirin Yesu ya yi rayuwa ta hanyar da wasu zasu koyi game da gaskiyar Allah. AT: "Bari rayuwar ku ta zama kamar hasken da ke haskakawa ga mutane"
Zai fi kyau a fasara kalmar "Uba" yadda harshe ku ke kiran mahaifi.
Wannan na nufi abubuwan da annabawa suka rubuto a nassosin.
"Ina gaya muku gaskiya." Wannan maganar na nuna muhimmancin abun da Yesu zai faɗa nan gaba.
A nan "sama" da "ƙasa" na nufin duniya gaba daya. AT: "muddin duniya nan na nan"
ɗigo ne karamin haruffa na Yahudawa, wasali kuma wani dan alama da ke raba haruffa biyu. AT: "ba ko ɗigo ko wasali a haruffa ba"
AT: " dukka abubuwa sun faru" ko "Allah ya sa dukka abubuwa su auku"
"duk wanda ki biyayya" ko "duk wanda ya yi watsi"
"kowane daga waɗannan umurnai, ko mafi ƙanƙantan muhimmanci"
AT: "idan wani ... koyar wa wasu su yi haka, Allah zai ce da wannan mutum"
Wannnan magana "mulkin sama" na nufin sarautar Allah a matsayin sarki. A littafi Matiyu ne kadai aka faɗa wannan. In ya yiwu yi amfani da kalman "sama" a fasara ka. AT: "mafi ƙanƙanta a cikin mulkinsa na samaniya" ko "mafi ƙanƙancin muhimmanci a karkashin mulkin Allahnmu a sama"
"yi biyayya da dukka waɗannan umurnai, da kuma koyar wa wasu su yi haka"
mafi muhimmanci
Wannan na nuna muhimmancin abun da Yesu zai faɗa nan gaba.
AT: " cewa dole adalcinku ya fi ... malaman attaura domin ka shiga"
Ana iya faɗin wannan cikin sifar aiki. AT: "Allah ya ce wa mutane tun da daɗewa" ko "Musa ya ce wa kakaninku da daɗewa"
Anan "hukunci" na nufi alƙalin zai hukunta mutumin zuwa mutuwa. AT: "Alƙali zai hukunta duk wanda ya kashe wani mutum"
Wannan kalman na nufi kisan kai, ba kowani irin kisa ba.
Yesu ya yarda da maganar Allah, amma bai yarda da yadda malaman addini ke fasara maganar Allah. Kalmar "Ni" na bayyananniya. Wannan na nufin cewa abun da Yesu ke faɗi na na muhimmanci ɗaya da asalin umurnin da Allah ya bayar. Yi kokari fasara wannan maganar ta hanyar da zai nuna wannan bayyani.
Wannan na nufi ɗan'uwa mai bi, ba ɗan ciki ɗaya ba ko maƙwabci.
kamar wannan na ba da alamar cewa ba mutum ne alƙalin da Yesu ke nufi ba, amma Allah ne zai hukunta mutumin da ke fushi da ɗan'uwarsa.
Wannan zagi ga mutanen da ba su tunani da kyau. " wawa mutum" na kamar "mara ƙwaƙwalwa," "wofi" na ba da ra'ayin rashin biyyaya ga Allah.
Wannan na iya yiwuwa cewa ana nufi karamin majalisa ne ba babban majalisan firistoci na Urshalima ba.
Yesu na magana da jama'a game da abun da ya kamata su yi ko kar su yi a matsayinsu na mutane. An yi amfani da "ka" ko "naka", amma a wasu harshuna zai yiwu lalle a yi amfani da su a matsayin jam'i.
"bayar da sadakarka" ko "kawo sadakarka"
Wannan na nufin bagadin Allah a cikin haikali a Urshalima. AT: "ga Allah a kan bagadi a cikin haikali"
"a sa'ad da kana tsaye a bagadi ka tuna"
"wani mutum na fushi da kai domin wani abu da ka yi"
AT: "da farko ka samu salama da mutumin"
Yesu na magana da jama'a game da abun da ya kamata su yi ko kar su yi a matsayinsu na mutane. An yi amfani da "ka" ko "naka", amma a wasu harshuna zai yiwu lalle a yi amfani da su a matsayin jam'i.
Wannan na nufi mutum wanda ya zargi wani a kan aikata wani laifi. Ya kai mai laifin kotu domin ya dore masa laifi a wurin alƙali.
A nan "bashewa" na nufin bayar da yancin wani a hannun wani dabam. AT: "bar wa alƙali ya hukanta ka"
A nan "miƙa ka" na nufi bayar da yancin wani a hannun wani dabam. AT: "alƙali kuwa zai miƙa ka a wurin dogari"
mutum da ke da yancin ɗaukan umurnin alƙali
AT: "dogarin na iya jefa ka a cikin kurkuku"
"daga kurkuku"
AT: "wai Allah ce" ko "wai Musa ya ce"
Wannan kalmar na nufi aikata abu ko yin wani abu.
Wannan na nufin cewa mutumin da ya yi sha'awar mace na da alhakin laifin zina kamar mutum wanda ya aikata zinar kanta.
"kuma sha'awar ta" ko "kuma ya yi marmarin kwana da ita"
A nan "zuciya" na nufin tunanin mutum. AT: "cikin tunanin sa"
Yesu na magana da jama'a game da abun da ya kamata su yi ko kar su yi a matsayinsu na mutane. An yi amfani da "ka" ko "naka", amma a wasu harshuna zai yiwu lalle a yi amfani da su a matsayin jam'i.
A nan "ido" na nufin abun da mutum ke gani. "tuntuɓe" kuma na a matsayin "zunubi." AT: "in abun da ka ke gani na sa ka yi tuntuɓe" ko "in kana so ka yi zunubi domin abun da ka ke gani"
Wannan na nufin ido ko hannu mafi muhimmanci. Ya yiwu za a bukaci a fasara "dama" a matsayin "mafi inganci" ko "mafi karfi."
Wannan umurni ne da ke nufi mutum ya yi duk abun da ya ke bukata ya yi domin ya daina zunubi.
"cire shi a dole" ko "hallakar da shi." Idan ba a ambaci idon dama ba, za a bukaci a fasara wannan haka "hallakar da idanun ka." amma in an ambaci idanu, to ya yiwu a fasara shi "hallakar da su."
"kawar da shi"
"ka rasa ɗaya daga gaɓoɓin jikinka"
AT: "da Allah ya jefa dukka jikinka a gidan wuta"
hannun na a matsayin duk aikin da jikin mutum ke yi.
AT: "Allah ya kuma ce" ko "Musa ya kuma faɗa"
Wannan na nufin sakin mata.
"dole ya bayar"
mutumin da ya saki matarsa ba a hanyar da ta dace ba shi ne ya "mai da ita mazinaciya." A al'adu da yawa, ba damuwa ta sa ke aure, amma idan sakin ba a hanyar da ta dace ba to wannan auren zina ce.
AT: "bayan mai gidan ta ya sake ta" ko "sakakkiya matar"
"ku kuma" ko "ga wani misali. ku"
AT: "Allah ya faɗa wa mutanen zamanin da ya wuce" ko "Musa ya faɗa wa kakani tun da daɗewa"
"kada ka ɗauka alkawarin yin abu sa'an anan ka ki yi. Amaimako sai ka aikata abu da ka ɗau alkawari ga Ubangiji cewa za ka yi"
A nan Yesu na nufin cewa kada wanda suke ɗaukan alkawari ko faɗin gaskiya su rantse da wani abu. Wasu suna koyar cewa idan mutum ya rantse da Allah to wajibi ne ya cika, amma idan rantsuwar ga wani abu ne kamar samaniya ko ƙasa, to ba shi da wani illa sosai idan bai cika ba. Yesu na cewa rantsuwa da samaniya ko ƙasa ko Urshalima na da muhimminci ɗaya da rantsuwa da Allah, domin Allah ne ke da dukka abubuwa.
"kada ku ɗauki rantsuwa ko kadan" ko "kada ku rantse da kowani abu"
Domin Allah na mulki da ga sama. Yesu na maganar sama kamar sama kursiyi ne. AT: "da ga nan ne Allah ke mulki"
Wannan maganar na nufin cewa ƙasa ma na Allah ne. AT: "ta na kamar matashi ne da sarki ke sa ƙafarsa"
"domin ita ce birnin Allah, babban Sarki"
Yesu na magana da tarin mutane game da abun da yakamata su yi a matsayinsu na mutane. Duk wurin da wannan kalmar ya fito a matsayin mutum daya ne, amma za a iya fasara su a matsayin mutane dayawa.
Wannan na nufin ɗaukan alkawari. duba yadda aka fasara wannan a 5:34.
"Idan kana nufi I, ce I, idan kuma kana nufi a'a, ce a'a."
shariyar Musa ya yardar wa mutum ya yi lahani ga mutum ta hanyar da wancan mutumin ya cũtar da shi, amma ba fiye ba.
"mugun mutum" ko "wanda ke cũtar ka"
zagi ne a al'adar garin Yesu a mare mutum a kuncisa. Kamar yadda ido da hannu ke da muhimminci haka kunci dama ke da muhimminci, babbban zagi ne a mare mutum a kuncinsa.
mari da bayan hannu
"yardar masa ya mari ɗayan kuncin kuma"
Ana sa "tuguwa" a jiki ne, kamar riga mai nauyi. "mayafi" kuwa ya fi taguwa daraja, ana sa wannan akan taguwa ne domin dumi, kua akan yi amfani da shi kamar bargo wajen barci.
"ka kuma ba mutumin"
"Ko wanene." mahalin wannan maganar na nuna cewa ya na magana ne game da sojojin Roma.
Wannan na nufin takawa dubu, domin wannan ne iyakar tafiyar da sojan Roma ke da ikon tilasta wani ɗauka masa abu bisa ga doka. Idan ba a gane kalmar "mil" sosai ba, ana iya fasara wannan kamar "kilomita" ko "bisa nisa."
wannan na nufin ga wanda ya tilasta ka yin tafiya.
"yi tafiyar da ya tilasta maka, ka kuma kara wani mil." Idanba a gane kalmar "mil" ba, yi amfani da fasarar "kilomita biyu" ko kuma "hada nisar tafiyar sau biyu."
"kada ka hana ba da rance." AT: "rantar wa"
Anan ba wani makwabci ta musamman ne kalmar nan "makwabci" ke nufi ba, amma ko ma wani ɗan al'umma ko mutane. Waɗannan mutanen ne yawanci mutum yakan yi marmarin yin masu alheri ko a kalla ya yarda ya bi da su da kyau. AT: "'yangarinka" ko kuma "waɗanda suke mutanenka"
Ya fi kyau a fasara " 'ya'ya" a yadda harshe ku ke amfani da kalmar a kiran 'ya'yan wani mutum.
Wannan muhimmin laƙani ne na Allah.
Yesu yayi amfani da tambaya dommin ya koyad da mutanen cewa idan masoyansu kadai suke ƙauna, ai ba wani muhimmin abu ne da Allah zai saka musu ba. AT: "Gama in kuna ƙaunar iyakar wanɗanda ... ba ku samu ko wani lada ba."
Yahudawa na duban masu karɓar haraji a matsayin masu zunubi ƙwarai. Yesu yayi amfani da wannan tambaya ya tunashe su cewa ai ko masu karɓar haraji ma suna ƙaunar masoyansu.
Yesu yayi amfani da tambaya dommin ya koyad da mutanen cewa idan 'ya'uwansu kaɗai suke gayarwa, ai ba wani muhimmin abu ne da Allah zai saka musu akai ba. AT: "Idan 'ya'uwanku kaɗai kuke gayarwa, ba kuwa yin komai fiye da waɗansu."
Wannan hanyar nuna marmari ne domin lafiyar mai jin.
Yahudawa na duban al'ummai a matsayin masu zunubi sosai. Yesu ya yi tambaya ya tunashe su cewa ai al'ummai ma suna gai da 'yan'uwansu. AT: "ai ko al'ummai suna gai da mutanensu." Dubi:
Matalauta a ruhu su na da albarka, domin mulkin sama nasu ne.
Masu makoki su na da albarka, domin za a ta'azantar da su.
Masu tawali'u su na da albarka, domin za su gaji duniya.
Masu yunwa da kishin adalci su na da albarka, domin za a kosar da su.
Waɗanda mutane na zagin su, ana kuma tsananta masu don Yesu masu albarka ne, domin sakamakonsu mai yawan na sama.
Masubi suke haskaka haske a gaban mutane ta wurin kyauwawar ayyuka.
Yesu ya zo domin ya cika doka da kuma annabawar Tsohon Alkawari.
Waɗanda sun kiyaye umarnen Allah da wanda ya koyar da su wa wasu, za a kira shi mafi girma a cikin mulkin sama.
Yesu ya koyar da cewa ba waɗanda sun yi kisa kadai ba, amma wanda na fushi da dan'uwansa, na cikin hatsarin hukunci.
Yesu ya koyar da cewa mu je mu sasanta da ɗan'uwanmu idan ya na da damuwa da mu.
Yesu ya koyar cewa mu yi sulhu da mai karar mu tun mu na hanyar zuwa kotu.
Yesu ya koyar cewa ba yin zina ne kadai zunubi ba, amm da duban mace da muguwar sha'awa.
Yesu ya ce mu watsar da komai da ke sa mu yin zunubi.
A kan dalilin zina ne Yesu ya yarda da saki.
Mijin ya sa matarsa ta zama mazinaciya idan ya sake ta ba tare da laifi ba ta kuma yi wani aure.
Yesu ya ce a maimakon yin rantsuwa da dukka waɗannan abubuwa, maganarmu ta zama 'I, I', ko kuwa 'A'a, a'a.'
Yesu ya koyar cewa mu guje mai yi mana mugunta.
Yesu ya koyar cewa mu ƙaunace maƙiyanmu da masu tsananta mana, mu kuma yi masu addu'a.
Yesu ya faɗa cewa idan mun ƙaunace waɗanda suke ƙaunar mu kadai, ba za mu karbi lada ba domin mu na yin abin da al'ummai sun yi.
1 Ku yi hankali kada ku yi ayyukan adalcinku gaban mutane domin su ganku, idan kun yi haka, ba za ku sami sakamako a wurin Ubanku da yake sama ba. 2 Saboda haka, in za ku yi sadaka, kada ku busa kaho yadda munafukai suke yi a majami'u da kuma akan tituna domin mutane su yabesu. Gaskiya ina gaya maku, sun samu ladansu. 3 Amma in za ku yi sadaka, kada hannunku na hagu ya san abin da hannunku na dama yake yi, 4 domin sadakarku ta zama a asirce. Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai saka maku. 5 Sa'adda za ku yi addu'a kuma, kada ku zama kamar munafukai, domin sun cika son yin addu'a a tsaye a majami'unsu da kuma a gefen tituna, domin mutane su gansu. Gaskiya ina gaya maku, sun sami ladarsu kenan. 6 Amma ku, idan za ku yi addu'a, sai ku shiga cikin daki. Ku rufe kofa, ku yi addu'a ga Ubanku wanda yake a asirce, Ubanku kuwa da ke ganin abin da ake yi a asirce, zai saka maku. 7 Idan za ku yi addu'a, kada ku yi ta maimaici marar anfani, kamar yadda al'ummai suke yi, domin a tunanin su za a saurare su saboda yawan maganganunsu. 8 Domin haka, kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatar ku tun kafin ku roke shi. 9 Saboda haka sai ku yi addu'a kamar haka: 'Ubanmu da ke sama, bari a tsarkake sunanka. 10 Bari mulkinka shi zo. Bari nufinka ya yiwu a duniya kamar yadda ake yi a sama. 11 Ka ba mu yau abincinmu na kullum. 12 Ka gafarta mana basussukanmu, kamar yadda mu ma muke gafarta ma wadanda muke bi bashi. 13 Kuma kada ka kawo mu cikin jaraba, amma ka kubutar da mu daga Mugun.' [1]14 Domin in kun yafe wa mutane laifuffukansu, Ubanku na Sama shima zai yafe maku. 15 In kuwa ba ku yafe wa mutane laifuffukansu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku laifuffukanku ba." 16 Haka kuma, in za ku yi azumi, kada ku zama da fuska kamar masu makoki yadda munafukai ke yi, domin sukan yankwane fuskokinsu, domin su bayyana ga mutane kamar suna azumi. Gaskiya, ina gaya maku, sun sami ladansu ke nan. 17 Amma in kuna azumi, ku shafa mai a ka, ku kuma wanke fuska, 18 don kada mutane su gane kuna azumi, sai dai Ubanku da yake a asirce. Kuma Ubanku da ke ganin abinda ke a asirce, zai saka maku." 19 "Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa ke batawa, inda barayi kuma ke fasawa su yi sata. 20 Maimakon haka, ku tara wa kanku dukiya a sama, inda babu asu da tsatsa da za su bata, inda kuma ba barayi da za su fasa su yi sata. 21 Domin inda dukiyar ka take, a nan zuciyar ka ma take. 22 Ido shi ne fitilar jiki. Saboda haka, idan idonka na da kyau, dukan jiki na cike da haske. 23 Amma in idonka na da lahani, dukan jiki na cike da duhu. Saboda haka, in hasken da yake cikinka duhu ne, ina misalin yawan duhun! 24 Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ki daya, ya so daya, ko kuma ya amince wa dayan ya raina dayan. Ba dama ku bauta wa Allah da kuma dukiya. 25 Saboda haka ina gaya maku, kada ku damu a kan rayuwarku, game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha- ko kuwa jikinku, abin da za ku yi tufafi da shi. Ashe rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? 26 Ku dubi tsuntsayen da ke sararin sama. Ai, ba su shuka, balle girbi, ba su kuma tarawa a cikin rumbuna, amma Ubanku na Sama na ciyar da su. Ashe, ba ku fi su martaba ba? 27 Kuma wanene a cikinku, don damuwarsa, zai iya kara ko taki ga tsawon rayuwarsa? 28 To, don me kuke damuwa a kan tufafi? Ku dubi furannin jeji, yadda suke girma. Ba su aiki, kuma ba su sakar kaya. 29 Duk da haka ina gaya maku, ko Sulaimanu ma, cikin dukan daukakar sa bai yi ado kamar daya daga cikin wadannan ba. 30 Idan Allah yayi wa ciyawar jeji ado, wadda yau tana wanzuwa, gobe kuwa a jefa ta cikin murhu, ina misalin adon da za ya yi maku, ya ku masu karancin bangaskiya? 31 Don haka kada ku damu, kuna cewa, 'Me za mu ci? ko, Me za mu sha?' ko kuwa, 'Wadanne tufafi za mu sa?' 32 Ai, al'ummai ma suna neman dukan irin wadannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu. 33 Amma ku nemi mulkinsa da farko da adalcinsa, kuma dukan wadannan abubuwa za a baku. 34 "Saboda haka kada ku damu don gobe, ai, gobe za ta damu da kanta. Kowace rana ta na cike da wahalarta".
Yesu ya ci da koyar da almajiransa a cikin wa'azinsa akan dutse, wadda ya fara a Matiyu 5:3. A wannan sashi, Yesu na magana game da "ayyukan adalci" na, sadaka, addu'a, da yin azumi.
Yesu na magana da taron jama'a game da abun da yakamata su yi a matsayinsu na mutane. Duk wurin da wannan kalmar ya fito a matsayin mutum daya ne, amma za a iya fasara su a matsayin mutane dayawa.
Wannan na nuna cewa waɗanda suka ga wannan mutumin za su girmama shi. AT: a gaban mutane domin su girmama ka akan abun da ka yi"
Wannan muhimmin laƙani ne na Allah.
Wannan maganar na nufin aikata abu da niyyar jawo hankalin mutane. AT: "kada ka jawo hankalin mutane a gare ka kamar wani mai busa ƙaho da ƙarfi a cikin jama'a"
"Ina faɗi muku gaskiya." Wannan maganar na nuna muhimmanci abun da Yesu zai faɗa nan gaba.
Wannan maganar na nufin "asiri gaba ɗaya." Kamar yadda yawanci loƙaci hannaye suna aiki tare, ɗayan hannun na sanin me ɗayan hannun ke yi, kada ma ka yarda mafi kusa da kai su sani a sa'ad da kana bayarwa ga matalauta.
AT: "kana iya bayar wa matalauta ba tare da sanin mutane ba"
Wannan na nuna cewa waɗanda suka gan su girmama su. AT: "domin mutane su gan su, su kuma girmama su"
"ka kebe wani wuri ka je" ko "ka je inda ka ke kai kadai"
Mai yiwuwa ana nufi 1)ba wanda ke iya ganin Allah. AT: " Uba, wanda baya ganuwa" ko 2) Allah na tare da mai yin addu'ar a kebeben wuri. AT: " Uban, wanda ke tare da ku a asirce"
"Ubanku zai ga abun da ku ke yi a asirce da"
Mai yiwuwa ana nufi 1) maimaitawar ba amfani. AT: "kada ku yi tsayuwar banza kuna ta maimaitawa" ko 2) kalmomin ko maganar ba su da ma'ana. AT: kada ku tsaya kuna ta maimaita kalmomi marasa ma'ana"
AT: "allolin karyarsu za su ji su"
Wannan shi ne farkon addu'ar, Yesu kuma ya na koyar wa mutanen yadda za su kira Allah.
Anan "sunanka" na nufi Allah da kansa. AT: "bari kowa ya daraja ka"
A nan "mulki" na nufi shugabancin Allah a matsayin tsarki. AT: "Bari mulkin ka akan kowa da komai ya cika"
AT: "Bari duk abun da zai faru a duniya ya zama bisa ga nufinka, kamar yadda komai a sama ke faruwa"
A nan "abinci" na nufin kowani irin abinci.
A nan laifi na nufi zunubi.
Wannan na nufin wanda suka yi mana laifi.
AT: kada ba kar wani abu ya jarabce mu" ko "kada ka bar wani abu ya sa mu sha'awar zunubi"
AT: "in su yi muku laifi ...in ku yi wa Allah laifi" ko "in sun illatar da ku ...in kun aikata abun da zai sa Ubanku fushi"
munafukai ba sa wanke fuskar su, ko tsefe gashi. Suna yin haka ne da niyyar jawo hanklin mutane a kansu domin a ga cewa suna azumi, sai a daraja su.
"sa mai a gashin ka." Anan "shafe" kai na nufi yadda aka saba lura da gashi. Bai shafe komai game da "Almasihu" "shafafen" ba. Yesu na nufi cewa mutane kar su canja ko da suna azumi ko ba sa yi.
"wanda ke ganin abun da ka ke yi a ɓoye."Dubi yadda aka fasara wannan a 6:6.
arziki, abubuwan da mutum ke ba da dukka daraja
"inda asu da tsatsa ke lalatar da dukiya"
karamin ƙwaro ne da ke ɓata tufafi
abune mai launin ruwar ƙasa da ke fitowa akan ƙarfe
Wannan maganar na nufin aikata abu mai kyau a duniya domin Allah ya ba ka lada a sama.
Wannan na kwatanta idanu masu lafiya da ke sa mutum gani, da kuma idanu ma masu lahani da ke sa makanta. Wannan na nufi lafiyar ruhaniya. Yayudawa na amfani da kalmar "mumunar ido" a nufin haɗama. Ma'anar ita ce idan mutum ya mika kai gaba ɗaya ga Allah, kuma yana duban abubuwa yadda Allah ke yi, to yana yin abun da ke daidai. Idan mutum na haɗama, to ya na aikata abun da ba dai dai ba.
Wannan maganar na nufin cewa ido ne ke sa mutum gani kamar yadda fitila na taimakon mutum kallo a duhu. AT: kamar fitila, ido na sa ku ganin abubuwa da kyau"
Ya yiwu zai fi a fasara wannan cikin jam'i, "Idanu."
Wannan ba ya nufin sihiri. Yahudawa sun saba amfani da wannan a nufi wanda ke da haɗama.
"idan abun da yakamata ya kawo haske ga jiki ka ke sa duhu, to jikinka na cikin duhu baki ɗaya"
dukka waɗannan maganar na nufin abu ɗaya ne. Suna jaddada cewa mutum ba zai iya so Allah ba ya kuma amince masa ba sanan kuma yaso kudi a lokaci ɗaya ba.
"ba za ka iya ƙaunar Allah da kudi a lokaci guda ba"
Wannan na nuna muhimmanci abun da Yesu zai faɗa a nan gaba.
Yesu na magana da taron jama'a game da abubuwan da yakamata a matsayin su na mutune su yi da wanda bai kamata su yi ba.
Yesu yayi amfani da tambaya don ya koyar da mutanen. AT: " A fili ya ke cewa rayuwa ya fi abun da kuke ci, jiki kuma ya fi abun da za ku sa." ko "A sarari ya ke, akwai abubuwa game da rayuwa fiye da abinci, kuma akwai abubuwa game da jiki da sun fi sa tufafi."
wurin ma'ajiyan abinci
Yesu yayi amfani da tambaya domin ya koyar da mutanen. AT: "A fili ya ke, kun fi tsunsaye martaba."
Yesu yayi amfani da tambaya domin ya koyar da mutanen. Anan "ƙara taƙi ɗaya ga tsawon rayuwarsa" na nufin ƙarin lokaci na zaman rayuwar mutum. AT: "Babu ko ɗayanku, ta wurin damuwarsa, zai iya ƙara shekaru ga rayuwarsa. ba za ka iya ƙara ko minti ɗaya a rayuwarka ba! don haka kada ka damu game da abubuwan da ka ke bukata."
taƙi ɗaya auni ne kasa da rabin mita.
Yesu yayi amfani da tambaya domin ya koyar wa mutanen. AT: "kada ku damu game da abun da zaku sa."
"dubi"
Yesu na magana game da tsire-tsire jeji kamar su mutane ne masu sa tufafi. Adon tsire-tsire jeji na nufi tsire-tsiren na da kyau da launin furanne.
wannann wani irin fure ne a jeji.
AT: "ba sa ado kamar yadda tsire-tsiren ke da kyau"
Yesu ya cigaba da magana game da tsire-tsire jeji kamar su mutane ne da ke sa tufafi. Adon tsire-tsiren jeji na nufin furanni masu kyau da launi da ke fitowa tsire-tsire.
Idan harshen ku na da sunan "ciyawa" dabam da "tsire-tsire jeji" da aka ambata a ayan baya, a yi amfani da shi anan.
Yahudawa a wacan zamani suna amfani da ciyawa a hura wutar dafa abinci. AT: "wani na jefa shi a cikin wuta" ko "wani na ƙona shi"
Yesu yayi amfani da tambaya ya koyar da mutane cewa Allah zai tanada musu abun da suke bukata. AT: "lalle ne ya tanada muku tufafi ... bangaskiya?
"ku da kuke da karamin bangaskiya." Yesu ya yi magana da mutanen haka domin suna ta da hankalin su game da tufafi, wannan ya nuna cewa suna da ƙaranci bangaskiya.
"domin dukka wannan"
A wannan jimla, "tufafi" na a matsayin mallakar dũkiya. AT: "Wani mallaka za mu samu"
"domin Al'ummai sun damu da abun da za su ci, su sha, da su kuma sa"
Yesu na nufin cewa Allah zai sa su samu duk abun da suke bukata.
A nan "mulki" na nufin shugabanci Allah a matsayin tsarki. AT: "ku dame kanku da bautar Allah, wanda shi ne tsarkin ku da kuma aikata abun da ke daidai"
AT: "Allah zai tanadar muku dukkan waɗannan abubuwa"
Yesu na managa game da "gobe" kamar wani mutum ne da zai iya damuwa. Yesu na nufin cewa mutum zai samu iyakar abubuwa da zai damu da su sa'ad da goben ta kai.
Waɗanda su ke yin ayyukar adalcinsu don mutane su gani sun karba ladar yaɓon daga mutane.
Mu yi ayyukan adalcinmu a ɓoye.
Waɗanda suke yin addu'a domin mutane su gansu su na karban ladansu daga mutane.
Waɗanda suke yin addu'a a asirce su na karban ladansu daga Uba.
Yesu ya ce kaɗa mu yi addu'a da maimaici marar amfani domin Uban ya san abin da muke bukata kafin mu roke shi.
mu roki Uban cewa nufinsa ya tabata a duniya kamar yadda yake a sama.
Idan ba mu gafarta ma wasu basusukansu ba, Uban ba zai gafarta mana basusukanmu ba.
Mu yi azumi ba tare da nuna wa mutane ba, kuma Uba zai ba mu lada.
Mu tara dukiya a sama, domin ba zata lalace ko a sace ba.
Zuciyarmu za ta kasance a inda dukiyarmu yake.
Ɗole mu zaɓa sakanin Allah da kuma dukiya a matsayin iyayengijinmu.
Kada mu damu da abinci, ruwa, da sutura domin Uba na lura da tsuntsaye, kuma mun fi su daraja.
Yesu ya tuna mana da cewa ba za mu iya kara tsawon ranmu ta wurin taraddadi ba.
Ɗole mu nemi mulkinsa da farko da adalcin Uba, za a tanada mana dukan bukatu na duniya.
1 Kada ku yi hukunci, domin ku ma kada a hukunta ku. Domin da irin hukuncin da ku kan hukunta da shi za a hukunta ku. 2 Mudun da kukan auna, da shi za a auna maku. 3 Don me kake duban dan hakin da ke idon dan'uwanka, amma ba ka kula da gungumen da ke naka idon ba? 4 Ko kuwa yaya za ka iya ce wa dan'uwanka, 'Bari in cire maka dan hakin da ke idon ka,' alhali ga gungume a cikin naka idon? 5 Kai munafiki! Ka fara cire gungumen da ke idonka, sa'annan za ka iya gani sosai yadda za ka cire dan hakin da ke idon dan'uwanka. 6 Kada ku ba karnuka abin da ke tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa aladu, lu'u lu'anku. Idan ba haka ba za su tattake su a karkashin sawunsu, su kuma juyo su kekketa ku. 7 Roka, kuma za a ba ku. Nema, kuma za ku samu. Kwankwasa kuma za a bude maku. 8 Ai duk wanda ya roka, zai karba, kuma duk wanda ya nema zai samu, wanda ya kwankwasa kuma za a bude masa. 9 Ko, kuwa wane mutum ne a cikin ku, dan sa zai roke shi gurasa, ya ba shi dutse? 10 Ko kuwa in ya roke shi kifi, zai ba shi maciji? 11 Saboda haka, idan ku da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga 'ya'yanku, ina kimanin yadda Ubanku na sama zai ba da abubuwa masu kyau ga duk wadanda suke rokon sa? 12 Saboda haka, duk abinda ku ke so mutane su yi maku, ku ma sai ku yi masu, domin wannan shi ne dukan shari'a da koyarwar annabawa. 13 Ku shiga ta matsattsiyar kofa, don kofar zuwa hallaka na da fadi, hanyar ta mai saukin bi ce, masu shiga ta cikin ta suna da yawa. 14 Domin kofar zuwa rai matsattsiya ce, hanyar ta mai wuyar bi ce, masu samun ta kuwa kadan ne. 15 Ku kula da annabawan karya, wadanda su kan zo maku da siffar tumaki, amma a gaskiya kyarketai ne masu warwashewa. 16 Za ku gane su ta irin "ya'yansu. Mutane na cirar inabi a jikin kaya, ko kuwa baure a jikin sarkakkiya? 17 Haka kowanne itace mai kyau yakan haifi kyawawan 'ya'ya, amma mummunan itace kuwa yakan haifi munanan 'ya'ya. 18 Kyakkyawan itace ba zai taba haifar da munanan 'ya'ya ba, haka kuma mummunan itace ba zai taba haifar da kyawawan 'ya'ya ba. 19 Duk itacen da ba ya ba da 'ya'ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta. 20 Domin haka, ta irin 'ya'yansu za a gane su. 21 Ba duk mai ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ne, zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda ya yi nufin Ubana da yake cikin sama. 22 A ranar nan da yawa za su ce mani, 'Ubangiji, Ubangiji,' ashe ba mu yi annabci da sunanka ba, ba mu fitar da aljanu da sunanka ba, ba mu kuma yi manyan ayyuka masu yawa da sunanka ba?' 23 Sa'annan zan ce masu 'Ni ban taba saninku ba! Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!' 24 Saboda haka, dukan wanda yake jin maganata, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidan sa a bisa dutse. 25 Da ruwa ya sauko, ambaliyar ruwa ta zo, iska ta taso ta buga gidan, amma bai fadi ba, domin an gina shi bisa dutse. 26 Amma duk wanda ya ji maganar nan tawa, bai aikata ta ba, za a misalta shi da wawan mutum da ya gina gidansa a kan rairayi. 27 Ruwa ya sauko, ambaliyar ruwa ta zo, sai iska ta taso ta buga gidan. Sai kuma ya rushe, ya kuwa yi cikakkiyar ragargajewa." 28 Ya zama sa'adda Yesu ya gama fadin wadannan maganganu, sai taro suka yi mamakin koyarwarsa, 29 Domin yana koya masu da iko, ba kamar marubuta ba.
Yesu ya cigaba da koyar da almajiran sa cikin huɗuban da ya fara a 5:3 akan Dutse.
Yesu na magana da taron jama'a game da abubuwan da yakamata a matsayin su na mutune su yi da wanda bai kamata su yi ba.
An nuna cewa "hukunci" anan na ba da ma'anar "mummunar kushewa" ko "ɗore laifi." AT: "kada ku yi wa mutane mummunar kushewa"
AT: "Allah ba zai yi muku mummunar kushewa ba"
tabbata cewa mai karatu ya gane maganar 7:2 na bisa abun da Yesu ya faɗa a 7:1.
AT: "Allah zai hukunta ku ta hanyar da kuka hukunta wasu"
Mai yiwuwa ana nufi 1) wannan ita ce yawan hukuncin da aka bayar ko 2) wannan shi ne ma'auni da ake amfani da shi wajen hukunci.
AT: "Allah zai auna muku"
Yesu ya yi amfani da tambaya ya tsautawa mutanen domin suna mai da hankali a zunubin wasu, ba sa kula da nasu zunubin. AT: kuna duban ... idon ɗan'uwa, amma ba ku lura da gungumen da yake a naku idon." ko "kada ku dubi ... idon ɗan'uwa, kuma kula da gungumen da yake naka idon."
Wannan na nufin ɗan laifi da ɗan'uwa maibi ya aikata mara muhimmanci.
"yayi" ko "sartse" ko "ɗan ƙura." Yi amfani da sunan ɗan karamin abu da ya saba fadi a idonun mutum.
duk inda aka yi amfani da kalmar "ɗan'uwa" a 7:3-5, ana nufin ɗan'uwa maibi ne ba ɗan'uwan haifuwa ko maƙwabci ba.
Wannan na nufin babban laifin da mutum a aikata. Gungume ba iya shigan idon mutum, Yesu ya yi amfani da wannan domin ya jaddada cewa mutum ya mayar da hankalinsa akan babban laifinsa kafin ya shiga harkar kananar laifofin wani.
sashi ne mafi girma a itacen da aka yanka
Yesu yayi amfani da wannan tambaya domin ya kalubalence mutane su sa hankalinsu a nasu zunuben kafin su sa hankalin su a zunuben wani. AT: "kada ka ce ... idon ka."
Yahudawa suna duban waɗannan dabobi da rashin tsabta, kuma Allah ya ce dasu kada su ci waɗannan dabobin. Suna a matsayin mugayen mutane wanda ba sa daraja tsarkakan abubuwa. Zai fi kyau a fasara waɗannan kalmomi yadda suke.
waɗannan suna kamar duwatsune ne masu daraja ko dusten ado. Suna a matsayin sanin Allah ko kuma kowani abu mai daraja.
"aladun kuwa su tattaka"
"karnukan kuwa su juyo su kyakketa"
Waɗannan na nufin addu'a ga Allah. A sifar aikatau, wannan jimlar na nuna cewa mu cigaba da addu'a har sai ya amsa. In a harshenku akwai kalmar da ke bayyana cigaba da yin abu akai-akai to ayi amfani da shi.
tambaye abu daga wurin wani, a wannan yanayi kuwa Allah ne
AT: "Allah zai baku abun da ku ke bukata"
neman wani, a wannan yanayi kuwa Allah ne
ƙwanƙwasa ƙofa rokone cikin kaskanci domin wadda yake cikin gida ya bude ƙofa. In ƙwanƙwasa ƙofa ba hanyar nuna kaskanci bane ko ma ba ayi a harshen ku, to ayi amfani da hanyar da mutane suke roƙa a buɗe musu ƙofa cikin kaskanci. AT: "gaya wa Allah kana so ya buɗe ƙofa"
AT: "Allah zai buɗe muku"
Yesu na amfani tambaya ya koyar da mutanen. AT: "Ba bu kowa a cikin ku ... dutse."
Wannan na nufi kowani irin abinci. AT: "abinci"
A fasara waɗannan sunaye yadda suke.
Yesu ya sake yin tambaya domin ya koyar da mutanen. A gane cewa har yanzu Yesu na magana game da Uba ne da ɗansa. AT: "Kuma ba bu ko ɗayan ku wanda in ɗansa ya roke shi kifi sai ya bashi maciji."
Yesu na amfani da tambaya ya koyar da the mutanen. AT: "ai lalle ne Ubanku na sama zai ba ... shi."
Wannan muhimmin laƙani ne na Allah.
kowace hanya kuke biɗar mutane su aikata muku"
Anan "attaura" da "annabawa" na nufin abun da Musa da annabawa suka rubuta. AT: "domin wannan shi ne Musa da annabawa suka koyar a cikin Nassi"
Wannan na ba da hoton masu tafiya akan hanya kuma suna shige wani kofa zuwa masarauta. wani masarautar na da saukin shiga, ɗayan na da wahalar shiga.
Ya yiwu zai bukaci a mayar da wannan zuwa ƙashen aya 14. "Saboda haka, ku shiga ta ƙunƙuntar ƙofa."
Mai yiwuwa ana nufi 1) "hanyar" na nufin in da za a bi zowa ƙofar masrautar, ko 2) "ƙofar" da "hanyar" duk na nufin ƙofar shiga masarautar.
Ana iya fasarar waɗannan sunayen da aikatau. AT: "zuwa wurin da mutane ke mutuwa ...zuwa wurin da mutane ke rayuwa"
"tsare kanku daga"
Wannan maganar na nufin cewa annabawan ƙarya na zuwa kamar masu gaskiya ne kuma suna so su taimake mutane, amma asilinsu miyagu ne kuma za su illatar da mutane.
Wannan na nufin ayyukan mutum. AT: "Kamar yadda akan gane itace ta irin 'ya'yan da take bayar, haka ma ta irin ayyukansu ake gane su annabawan ƙarya ne"
Yesu na amfani da tambaya ya koyar da mutanen. Yakamata mutanen su san amsa a'a ne. AT: "Mutane ba sa ciran ... kaya."
Yesu ya cigaba da misalta annabawa gaske ta wurin kyawawa ayyukansu da kalmominsu da 'ya'yan itace.
Yesu ya cigaba da misalta annabawa ƙarya ta wurin munanan ayyukansu da 'ya'yan itace.
Yesu ya cigaba da amfani da 'ya'yan itace a misalin annabawan ƙarya. Anan, yana faɗin iyakan abun da zai faru da munanan itace ne. Ana nufin cewa haka nan ma zai faru da annabawan ƙarya.
AT: "mutane na sare su kuma ƙona"
Kalmar "su" na iya zama annabawan ko itacen. Wannan na nuna cewa 'ya'yan itace da ayyukan annabawa ke bayyana ko su na da kyau ko babu. In ya yiwu, a fasara wannan ta hanyar da zai nuna cewa ana magana game da itace da annabawa.
A nan, "mulkin sama" na nufin sarautar Allah a matsayin tsarki. A littafin Matiyu ne kadai aka faɗi wannan maganar. in ya yiwu, a sa kalmar "sama" a fasarar, AT: "zai kasance tarw da Allah a sama a sa'ad da ya nuna kansa a matsayin tsarki"
"wanda yake aikata abun da Ubana na cikin sama yake so"
Yesu ya ce "ranar nan" domin ya san masu sauraronsa za zu gane yana magana game da ranar shariya. Za ka iya fasara shi haka "ranar shariya" inda masu karatu ba za su gane wace rana ne ba.
Mutanen suna amfani da tambaya domin su jaddada cewa sun aikata waɗannan abubuwa. AT: " mun yi annabci ... mun fitar da aljannu ... mun yi ayyukan al'ajabi masu girma da yawa."
Kalmar "mu" anan bai shafi Yesu a ciki ba.
ai yiwuwa ana nufi 1) "ta wurin ikon ka" ko "ta wurin karfin ka" ko 2) domin muna aikata abun da kake so mu aikata" ko 3) "domin mun roƙe ka ikon mu aikata su"
"al'ajibai"
Wannan na nufin mutumin baya tare da Yesu. AT: "Kai ba mabiyi na ba ne" ko "ba ni da wata harka da kai"
"Domin wannan"
A nan "kalmomi" na nufin abun da Yesu ya faɗa.
Yesu ya kwatanta masu jin maganarsa kamar mutumin da ya gina gidansa inda ba wanda zai iya hallakar.
Wannan dutse ne da shumfide a ƙasa, ba babban dutse mai tudu ba ko.
AT: "ya gina ta"
Yesu ya cigaba da kwatanci da yayi a ayan baya. Ya misalta waɗanda ba sa biyyaya da maganarsa da wawayen magina. Wawa ne kadai zai gina gida akan rairayi, inda ruwan sama, ambaliya, da iska na iya share wa.
Yi amfani da kalmar da akan kira a harshenku idan ana so a ce gida ya rushe.
Ruwar sama, da ambaliya, da kuma iskan sun hallakar da gidan gaba ɗaya.
Wannan maganar ya canja labarin daga koyar Yesu zuwa abun da ya faru na gaba. AT: "sa'adda" kon "bayan haka"
A fili ya ke cewa a 7:29 ba mamakin abun da Yesu ya koyar kadai suke yi ba amma har da yadda yake koyarwar ma. AT: "mamakin yadda yake koyarwa"
Ɗole mu fara hukunta kanmu, mu kuma cire gungumen da ke idonmu kafin mu iya taimake 'yan'uwanmu.
Idan kun ba wa karnuka abin da ke da tsarki, za su tattake su su kuma juyo su kekketa ku.
Ɗole ne mu roka, mu nema, mu kuma kwankwasa domin mu samu daga Uba.
Uba na ba da kyauwawar abubuwa wa waɗanda sun roke shi.
Shari'a da annabawa suka koya mana cewa mu yi wa wasu abin da mu na son mutane su yi mana.
Fadddiyar kofa na kai ga hallaka.
matsattsiyar kofa na kai ga hallaka.
Za mu iya gane annabawan karya ta wurin 'ya'yansu da rayuwarsu.
Waɗanda su na yin nufin Uba ne za su shiga mulkin sama.
Yesu zai ce masu 'Ni ban taba saninku ba! Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!'
Wanda ya ji maganar Yesu kuma ya yi biyayya da su na nan kamar mutum mai hikima.
Duk wanda ya ji maganar Yesu kuma bai yi biyayya da su na nan kamar mutum mai wauta.
Yesu ya koya wa mutanen kamar wanin da ke da iko, ba kamar yadda marubuta suke yi ba.
1 Da Yesu ya sauko daga dutsen, sai taro masu yawa suka bi shi. 2 Sai wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, "Ubangiji, in dai ka yarda, za ka iya tsarkake ni." 3 Yesu ya mika hannunsa ya taba shi, ya ce, "Na yarda, ka tsarkaka." Nan da nan aka tsarkake shi daga kuturtarsa. 4 Yesu ya ce masa, 'Ka tabbata, ba ka gaya wa kowa komai ba. Sai dai ka je ka nuna kan ka ga firist, ka kuma bayar da baiko da Musa ya umarta domin shaida garesu? 5 Da Yesu ya shiga kafarnahum, sai wani hafsa ya zo gunsa ya roke shi, 6 Ya ce, Ubangiji, bawana na kwance shanyayye a gida, yana shan azaba kwarai." 7 Yesu ya ce masa, "Zan zo in warkar da shi." 8 Sai hafsan, ya ce, "Ubangiji, ban isa har ka zo gida na ba, amma sai ka yi magana kawai, bawana kuwa zai warke. 9 Domin ni ma ina karkashin ikon wani ne, ina kuma da sojoji a karkashina, sai in ce wa wannan, 'je ka,' sai ya je, wani kuma in ce masa, 'zo,' sai ya zo, in ce wa bawa na, 'yi abu kaza,' sai ya yi," 10 Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, "Gaskiya, ina gaya maku, ko a cikin isra'ila ban taba samun bangaskiya mai karfi irin wannan ba. 11 Na gaya maku, da yawa za su zo daga gabas da yamma, su zauna cin abinci tare da Ibrahim da Ishaku, da Yakubu a cikin mulkin sama. 12 Amma 'ya'yan mulkin kuwa sai a jefa su cikin matsanancin duhu. Can za su yi kuka da cizon hakora." 13 Yesu ya ce wa hafsan, "Je ka! Bari ya zamar maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi," A daidai wannan sa'a bawansa ya warke. 14 Da Yesu ya shiga gidan Btrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance da zazzabi. 15 Yesu ya taba hannunta, zazzabin ya sake ta, ta kuma tashi ta fara yi masa hidima. 16 Da maraice ya yi, sai mutanen suka kakkawo wa Yesu masu aljanu da yawa. Da magana kawai ya fitar da aljanun, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. 17 Ta haka kuwa maganar annabi Ishaya ta samu cika cewa, "Shi da kansa ya debe rashin lafiyar mu, ya dauke cututtukan mu." 18 Sa'adda Yesu ya ga taro masu yawa kewaye da shi, sai ya ba da umarni su tafi su koma wancan hayi na tekun Galili. 19 Sai wani marubuci ya zo ya ce masa, "Malam, zan bi ka duk inda za ka je." 20 Yesu ya ce masa, "Yanyawa suna da ramukansu, tsuntsayen sama kuma da shekunan su, amma Dan mutum ba shi da wurin da zai kwanta." 21 Wani cikin almajiran ya ce masa, "Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne mahaifina." 22 Amma Yesu ya ce masa, "Bari matattu su binne matattunsu." 23 Da Yesu ya shiga jirgi, almajiransa suka bi shi. 24 Sai ga wata babbar iska ta taso a tekun, har rakuman ruwa suka fara shan kan jirgin. Amma Yesu yana barci. 25 Sai almajiran sa suka je suka tashe shi, suka ce, "Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!" 26 Yesu ya ce masu, "Don me kuka firgita haka, ya ku masu karancin bangaskiya?" Sa'annan ya tashi, ya tsauta wa iskar da tekun. Sai wurin gaba daya ya yi tsit. 27 Mutanen suka yi al'ajibi, suka ce, "Wanne irin mutum ne wannan, wanda har iska da teku ma suke masa biyayya?". 28 Da Yesu ya zo daga wancan hayin a kasar Garasinawa, mutane biyu masu al'janu suka fito suka same shi. Suna fitowa daga makabarta kuma suna da fada sosai, har ma ba mai iya bin ta wannan hanya. 29 Sai suka kwala ihu suka ce, "Ina ruwanka da mu, kai dan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?" 30 To akwai wani garken aladu masu yawa na kiwo, babu nisa da su. 31 Sai al'janun suka roki Yesu suka ce, "In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan." 32 "Yesu ya ce masu, "To, ku je." Sai aljanun suka fita, suka shiga cikin aladun. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka fada cikin tekun, suka hallaka a ruwa. 33 Mutanen masu kiwon aladun suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin komai da komai, musamman abin da ya faru da masu al'janun. 34 Sai duk jama'ar gari suka fito su sami Yesu. Da suka gan shi, suka roke shi ya bar kasarsu.
Wannan ne farkon sabon sashin labarin da ya kunsa labaran Yesu da ya warkad da mutane. Wannan kan magana ya cigaba har zuwa 9: 35.
"Bayan da Yesu ya sauko daga dutsen, taro masu yawa suka bi shi." Mai yiwuwa taron su na tare da mutanen da suke tare da shi a kan dutsen da kuma mutanen da ba sua tare da shi.
Kalmar "gani" na shirya mu ga sabon mutum a labarin. Harshenku na iya samin wata hanyar yin wannan.
"wani mutum da ke da kuturta" ko "wani mutum da ke da cuta"
Wannan alama ne na tawali'u da ladabi a gaban Yesu.
"idan ka na so." Kuturun ya san cewa Yesu ya na da ikon warkad da shi, amma bai san ko Yesu zai so ya taba shi ba.
A nan "tsarkake" na nufin warkewa da kuma iya yin rayuwa a cikin jama'a kuma. AT: "za ka iya warkad da ni" ko "don Allah ka warkad da ni"
Ta wurin fadan haka, Yesu ya warkad da mutumin.
"A wannan loƙacin aka tsarkake shi"
Sakamakon da Yesu ya ce "ka tsarkake" na nufin cewa mutumin ya warke. AT: "ya na da lafiya" ko "kuturtan ya bar shi" ko "kuturtan ya kare"
Wannan ya na nufin mutumin da Yesu ya warkad da shi.
"kada ka ce komai wa kowa" ko kada ka gaya wa wani cewa ni ne na warkad da kai"
Dokan Yahudawa ya bukaci mutumin ya nuna jikinsa da ya warke ga firist, wanda zai yarda mashi ya koma cikin gari, don ya yi zama da mutane.
Dokar Musa ya bukaci cewa duk wanda ya warke daga kuturta ya ba da baikon shaidan godiya ga firist. Mutane za su san cewa mutumin ya warke a loƙacin da firist ya karbi kyautan. A na tura kutare daga cikin gari, sai sun nuna cewa sun warke.
AT: 1) firistoci ko 2) dukka mutane ko 3) masu sokanan Yesu. Idan zai yiwu, yi amfani da wakilin suna da zai iya nufin kowane abu na wannan taron.
A nan sashin ya maso zuwa wani wuri da loƙaci dabam ya kuma faɗa game da yadda Yesu ya warkad da wani mutum.
A nan "shi" ya na nufin Yesu.
rashin iya motsi saboda cuta ko rashin motsi
"Yesu ya ce wa hafsan"
"Zan zo gidan ka in warkad da bawan ka"
Wannan ƙarin magana ne da na nufin cikin gidan. AT: "cikin gida na"
Anan "magana" na wakilcin umurni. AT: "ba da umurnin"
AT: "zai warke"
AT: "wanda ya na ƙarƙashin ikon wani dabam"
Zama a "ƙarƙashin" wani na nufin zama da ƙanƙancin muhimminci da kuma bin umurnin wani mai mafi muhimminci.
"Ina gaya maku gaskiyan." Wannan jumla na kara nanaci ga abin da Yesu ya faɗa.
Masu sauraran Yesu na iya yin tunani cewa Yahudawa a cikin Isra'ila, wadda sun ce su ne ''ya'yan Allah, za su sami babban bangaskiya fiye da kowa. Yesu ya na cewa ba daidai ba ne kuma bangaskiyar hafsan din ne ya fi.
A nan "ku" jam'i ce kuma ya na nufin "waɗanda suke bin shi" a cikin 8:10.
Yin amfani da "gabas" da "yamma" wata hanya ne na ce "ko ina." AT: "daga ko ina" ko "daga nesa a kowane jiha"
Mutane a wannan al'ada su na ƙwanciye sa'ad da su na cin abinci. Wannan jumla ya nuna cewa dukka waɗanda suke teburin yan iyali ne da abokai. Ana yawan maganan murna a cikin mulkin Allah kamar mutanen a wuri suna biki ne. AT: "zauna kamar iyali da abokai"
A nan "mulkin sama" na nufin mulkin Allah a matsayin sarki. An yi amfani da jumlar "mulkin sama" a cikin littafin Mata. In ya yiwu, bar "sama" a cikin juyinku. AT: "a lokacin da Allahn mu a sama ya nuna cewa shi sarki ne"
AT: "Allah zai jefar da 'ya'yan mulkin"
Jumlar " 'ya'yan" ƙarin magana ne da na nufin Yahudawa marasa bangaskiya na mulkin Yahudia. Akwai habaici anan domin za a jefar da "'ya'yan" a wuje sai a marabshe baki. AT: "waɗanda ya kamata sun yarda Allah ya yi mulki da su"
A nan "matsanancin duhu" ƙarin magana ne na wurin da Allah zai tura waɗanda sun ki shi. Wannan wuri ne da ya rabu daga Allah har abada. AT: "duhun wuri mai nesa daga Allah"
"cizon hakora" ayuka ne na alama, da na wakilcin tsananin bakin ciki da azaba. AT: "yin kuka da nuna tsananin azabarsu"
AT: "don haka zan yi maka"
AT: "Yesu ya warkad da bawan"
"a daidan loƙacin da Yesu ya ce zai warkad da bawan"
Mai yiwuwa almajiran su na tare da Yesu, abin duba a labarin na akan abin da Yesu ya faɗa da kuma yi, don haka za ku iya gabatar da almajiran idan ya kamata don hankali da ma'anar da ba daidai ba.
"mahaifiyar matar Bitrus"
Idan harshenku za su fahimci wannan ƙarin maganan da cewa zazzabi na iya tunani da kuma aikatuwa, za a iya juya wannan kamar "ta yi sauki" ko "Yesu ya warkad da ita."
"tashi daga gado"
Domin Yahudawa ba su yi tafiya ba ko su yi tafiya a ranar Asabar, "maraice" wannan na iya nufin bayan Asabar. Sun jira sai maraice don su kawo mutane wa Yesu. Ba sai kun ambaci Asabar ba sai dai ku yi hankali da ma'ana da ba daidai ba.
AT: "mutane dayawa da suke da aljanun" ko "mutane dayawa da aljanun su na mulki da su"
Anan "kalma" na matsayin umurni. AT: "Ya umurci aljanun su tafi"
AT: "Yesu ya cika annabcin da annabi Ishaya ya faɗa wa mutanen Israi'la"
Mata ya na faɗan abin da annabi Ishaya a faɗa. Waɗannan jumla biyu a takaice na nufin abu ɗaya kuma ya na nanata cewa ya warkad da dukka cututtukanmu. AT: "warkad da waɗanda suke da rashin lafiya"
An yi amfani da wannan kalma anan domin a sa alama a ainahin labarin. Anan Mata ya fara ba da sabon sashin labarin.
"ya gaya wa almajiransa"
Wannan na nufin bayan Yesu "ya ba da umarni" amma kafin ya shiga cikin kwalekwalen.
zuwa kowane wuri
Yesu ya amsa da wannan magana. Wannan na nufin cewa har dabban daji na da wurin hutawa.
Yanyawa dabba ne kaman karnuka. Suna cin tsuntsaye masu gida da kuma kananun dabbobi. Idan yanyawa ba sananne ne a garin ku ba, ku yi amfani da kalmar dabba kamar kare ko wani irin dabba mai fushi.
Yanyawa su na yin ramuka a kasa don su zauna a ciki. Yi amfani da kalma da ta dace a inda dabban da kun yi amfani a "yanyawa" suke zama.
Yesu ya na maganar kanshi.
Wannan na nufin wurin barci. AT: "ba wurin dake nasa da zai yi barci"
ba a bayyane ne ya ke ko mahaifin mutumin ya mutu kuma zai binne shi nan da nan ba, ko mutumin ya na so ya tsaya na dan tsawon loƙaci sai mahaifinshi ya mutu don ya iya binne shi. Ainahin maganan shi ne mutumin ya so ya yi wani abu dabam kafin ya bi Yesu.
Yesu ba ya nufin cewa matattu za su binne sauran matattu, "matattu." AT: 1) ƙarin magana ne ga waɗanda sun yi ƙusan mutuwa, ko 2) ƙarin magana ne na waɗanda ba su bin Yesu kuma matattu a ruhaniya. Ainahin maganan shi ne kada almajiri ya bar wani abu ya jinkirtad da shi daga bin Yesu.
"shiga kwalekwalan"
Yi ƙoƙari ku yi amfani da kalmomi ɗaya a "almajiri" da kuma "bi" da kuka yi amfani a cikin 8:21-22.
AT: "babbar hadari ta taso a tekun"
AT: "har rakuman ruwa suka sha kan jirgin"
AT: 1) da farko sun tashe Yesu sai suka ce, "Cece mu" ko 2) sa'adda sun ta da Yesu, su na cewa "Cece mu."
Zai yi kyau ku juya waɗannan tare. Mai yiwuwa almajiran su na nufin sun so Yesu ya cece su da kuma kansa daga nutsewa.
"za mu mutu"
Yesu ya na tsawta almajiransa da wannan tambaya mai zurfi. AT: "Kaɗa ku ji tsoro ... bangaskiya!" ko "Babu abin jin tsoro ... bangaskiya!"
"ku da kuke da karancin bangaskiya."Yesu ya yi wa almajiransa magana haka domin taraddadinsu akan hadarin ya nuna cewa suna da ƙarancin bangaskiya akanshi. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 6:30.
"Har iska da teku su na yi masa biyayya! Wanne irin mutum ne wannan?" Wannan tambaya ya nuna cewa almajiransa sun yi mamaki. AT: "Wannan mutum ba kamar kowane mutum ne da mun taba gani ba! Har iska da teku su na yi masa biyayya!
Ba abin mamaki ne mutum ko dabba ya yi biyayya ko rashin biyayya ba, amma abin mamaki ne iska da ruwa su yi biyayya. Wannan ƙarin magana ne da ke ƙwatanta abin halitta da na iya ji kamar mutane.
"ta hayin tekun Galili
An lakaɓa sunan kasar da sunar garin da ae kira da suna Gadara. (Dubi: Transalated names)
Aljannun da ke cikin waɗannan mutane biyu ɗin suna da zafi kwarai da gaske har da mutane kan guji ratsewa ta hanyar.
Aljannun sun yi amfani da tambaya amma sun haura wa Yesu kwarai da gaske. AT: "Kar ka damu da mu, ya "Ɗan Allah!"
wannan muhimmin laƙanin Yesu ne, wanda ya nuna dangantakarsa da Allah. (Dubi: duidelines_sonofgodprinciples)
A nan kuma, aljannun sun yi amfani da tambaya a cikin fushi. AT: "Kaɗa ka ketare dokar Allah tawurin tsananta mana kamin lokacin da Allah ya ayana mana!"
Ana nufin cewa al'janun sun san cewa Yesu zai fitar da su. AT: "Domin za ka fitar da mu"
Wannan dabam ne, ya na nufin al'janun kadai.
"Al'janun suka bar mutumin sai suka shiga cikin aladun"
"gangarawa da sauri"
"suka faɗi a cikin ruwan sun kuma nutse"
"kula da aladun"
AT: "abin da Yesu ya yi don ya taimake mutanen da al'janu sun mallaka"
Kalmar "gari" ƙarin magana ne na mutanen garin. Mai yiwuwa kalmar "duk" zuguici ne domin a nanata yadda mutane dayawa suka fito. Ba lallai ne kowane mutum ya fita ba.
"kasarsu"
Yesu ya ce wa kuturun da ya warke cewa ya tafi wurin firist domin shaidar godiya.
Yesu ya ce zai je gidan jarumin ya warkad da bawan.
Jarumin ya faɗa cewa bai cancanci Yesu ya zo gidan shi ba, kuma Yesu zai iya faɗa kalma don ya warkad da bawan.
Yesu ya faɗa cewa ko a cikin isra'ila bai taba samun mutum mai bangaskiya irin wannan kamar na jarumin ba.
Yesu ya faɗa cewa dayawa za su zo daga gabas da yamma su kuma zauna a tebur a mulkin sama.
Yesu ya ce za a jefar da 'ya'yan mulkin a cikin duhu.
Yesu ya warkad da surukar Bitrus a loƙacin da ya shiga gidan Bitrus.
Annabcin Ishaya, "Shi da kansa ya ɗauki rashin lafiyar mu, ya dauke cututtukan mu," ya cika.
Yesu ya ce ba shi da takamamman gida.
Yesu ya ce wa almajirin ya bi shi, ya kuma bar matattu su binne matattunsu.
Yesu yana barci a loƙacin da babbar iska ta taso a tekun?
Yesu ya ce wa almajiran, "Don me ku na tsoro, ya ku masu karancin bangaskiya?"
Almajiran sun yi mamakin Yesu domin iska da teku sun yi masa biyayya.
Yesu ya hadu da mutane biyu masu al'janu da kuma ƙarfin gaskiye.
Al'janun sun damu cewa Yesu ya zo ne don ya tsananta masu kafin loƙacin da ya kamata?
A loƙacin da Yesu ya fitar da al'janun, sun shiga cikin garken aladu sai aladun suka rugungunta cikin teku suka kuma hallaka.
Mutanen sun roke Yesu ya bar yankinsu.
1 Yesu ya shiga jirgi ya haye ya je birninsa. 2 Sai gashi, sun kawo masa wani mutum shanyayye kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, "Da, ka yi farin ciki. An gafarta maka zunuban ka." 3 Sai wadansu marubuta suka ce a tsakaninsu, "Wannan mutum sabo yake yi." 4 Yesu kuwa da yake ya san tunaninsu, yace, "Don me kuke mugun tunani a zuciyarku? 5 Wanne ya fi sauki, a ce, 'An gafarta maka zunubanka,' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya'? 6 Amma domin ku sani Dan mutum yana da ikon gafarta zunubai a duniya,..." Sai ya ce wa shanyayyen, "Tashi, ka dauki shimfidarka ka tafi gida." 7 Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida. 8 Da taron suka ga haka sai suka yi mamaki, suka daukaka Allah, wanda ya ba mutane irin wannan iko. 9 Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karbar haraji. Yace masa, "Ka biyo ni." Ya tashi ya bi shi. 10 Sa'adda kuma Yesu yake cin abinci a gida, sai ga masu karbar haraji da masu zunubi da yawa sun zo, sun zauna tare da shi da almajiransa. 11 Da Farisawa suka ga haka, sai suka ce wa almajiransa, "Don me malamin ku ya ke ci tare da masu karbar haraji da masu zunubi?" 12 Amma da Yesu ya ji haka ya ce, "Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya. 13 Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, 'Ni kam, ina bukatar jinkai ba hadaya ba.' Ba domin in kira masu adalci su tuba na zo ba, sai dai masu zunubi. 14 Sai almajiran Yahaya suka zo wurinsa, suka ce, "Don me mu da Farisawa mu kan yi azumi a kai a kai, amma naka almajiran ba su yi?" 15 Sai Yesu ya ce masu, "Masu hidimar buki za su yi bakin ciki tun ango yana tare da su? Ai, lokaci yana zuwa da za a dauke masu angon. A sa'annan ne fa za su yi azumi." 16 Babu mutumin da zai sa sabon kyalle a kan tsohuwar tufa, domin kyallen zai yage daga tufar, har ma yagewar ta fi ta da. 17 Mutane kuma ba su dura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. Idan sun yi haka, sai salkunan kuma su fashe inabin ya tsiyaye, sai salkunan su lalace. A maimakon haka, ana sa sabon inabi cikin sababbin salkuna, ta haka an tsirar da duka biyun kenan." 18 Yesu kuwa yana cikin yi masu magana sai ga wani shugaban jama'a ya zo ya yi masa sujada, ya ce, "Yanzun nan 'yata ta rasu, amma ka zo ka dora mata hannu, za ta rayu." 19 Sai Yesu ya tashi ya bi shi tare da almajiransa. 20 Sai ga kuma wata mace wadda ta yi shakaru goma sha biyu tana zubar da jini sosai, ta rabo ta bayan Yesu, ta taba gezar mayafinsa. 21 Domin ta ce a ran ta, "Ko da mayafinsa ma na taba, sai in warke." 22 Sai Yesu ya juya, ya gan ta ya ce, '"Yata, ki karfafa. Bangaskiyarki ta warkar da ke." Nan take matar ta warke. 23 Da Yesu ya isa gidan shugaban jama'ar, ya kuma ga masu busar sarewa da taro suna ta hayaniya sosai. 24 Sai ya ce, "Ku ba da wuri, ai, yarinyar ba matacciya take ba, barci ta ke yi." Sai suka yi masa dariyar raini. 25 Sa'adda aka fitar da taron waje, ya shiga ya kama hannunta, sai kuwa yarinyar ta shi. 26 Labarin kuwa ya bazu a duk yankin. 27 Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai wadansu makafi biyu suka bi shi, suna daga murya suna cewa, "Ya Dan Dauda, ka ji tausayinmu." 28 Da Yesu ya shiga wani gida sai makafin suka zo gareshi. Yesu ya ce masu, "Kun gaskata ina da ikon yin haka?" Sai suka ce masa. "I, ya Ubangiji." 29 Sai Yesu ya taba idanunsu, ya ce, "Ya zama maku gwargwadon bangaskiyarku." 30 Sai idanunsu suka bude. Amma Yesu ya umarce su kwarai, ya ce, "Kada fa kowa ya ji labarin nan." 31 Amma suka tafi suka yi ta baza labarinsa a duk yankin. 32 Da makafin biyu suka tafi, sai aka kawo wa Yesu wani bebe mai aljani. 33 Bayan da an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, su ka ce, "Kai, ba a taba ganin irin wannan a cikin Isra'ila ba!" 34 Amma sai Farisawa suka ce, "Ai, da ikon sarkin aljanu ya ke fitar da aljanu." 35 Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da kauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. 36 Amma da ya ga taro masu yawa sai ya ji tausayinsu, domin suna shan wahala kuma sun karaya. Suna nan kamar tumaki da babu makiyayi. 37 Sai ya ce wa almajiransa, "Girbin yana da yawa, amma ma'aikatan kadan ne. 38 Saboda haka sai ku yi sauri ku roki Ubangijin girbin ya turo ma'aikata cikin girbinsa."
Matta ya komo zuwa ga maganan da ya fara a cikin 8:1, na Yesu da ya na warkad da mutane. Wannan ya fara ba da labarin Yesu da ya na warkad da shanyayyer mutum.
Ana nufin cewa almajiran su na tare da Yesu.
Mai yiwuwa wannan irin jirgin ne a Matta 8:23. Za ku iya ba da takamaiman wannan a inda ya kamata domin yin hankali da gardama.
"zuwa garin da ya na zama." Wannan na nufin Karfanahum.
Wannan ya ba da alama a farkon wani abu a babban labarin. Na iya ƙunshi mutane dabam dabam fiye da abin da ya faru a baya. Harshenku na iya samin wata hanyar nuna wannan.
"waɗansu mutane daga garin"
Wannan na nufin mazan kuma ya shafi bangaskiyar shanyayye mutumin .
Mutumin ba ainahin ɗan Allah ba ne. Yesu ya na yi masa magana da ladabi. Za a iya juya zuwa "Abokina" ko "ƙaramin mutum" ko kuma a cire idan zai kawo gardama.
AT: "Na gafarta maka zunuban ka"
AT: 1) kowanne na tunani wa kansa, ko 2) su na magana a sakaninsu.
Yesu ya na cewa zai iya yin abubuwan da marubatan su na tunani Allah ne kadai zai iya yi.
Yesu ya san abin da suke tunanin ko da ya wuce ikon ɗan Adam ko domin ya iya gani cewa suna magana da juna.
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya domin ya ƙwabe marubutan.
Wannanmugunta ne da ba daidai ba, ba kuskure ba ne.
A nan "zuciya" na nufin hankalinsu ko tunaninsu.
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya don ya sa marubuta su yi tunani game da abin da zai iya nuna cewa zai gafarta zunubai. AT: "Na ce 'An gafarta maka zunubanka.' Za ku iya tunani cewa ya na da wuya a ce 'Tashi ka yi tafiya,' domin tabacin cewa zan iya warkad da mutumin zai nuna ta wurin tashiwarsa ya yi tafiya." ko "Za ku iya tunani cewa mafi sauki ne a ce 'An gafarta maka zunubanka' da a ce 'Tashi ka yi tafiya."
Ana iya juya maganan a kaikace. AT: "wanne ne ya fi sauki, a ce wa wani cewa an gafarta masa zunubansa, ko a ce masa ya tashi ya yi tafiya?" ko "za ku iya tunani cewa mafi sauki ne a gaya wa wani cewa an gafarta masa zunubansa da ce masa ya tashi ya yi tafiya."
AT: "Na gafarta maka zunubanka"
"Zan nuna maku." "ku" jam'i ne.
Ba wai Yesu ya na haramta mutumin cewa ya tafi wani wuri ba ne. Ya na ba wa mutumin dama ya je gida.
"domin ya ba da"
Wannan na nufin irin iko da na furta gafartawar zunubi.
Wannan jumla ya sa alama a farkon sabon sashin labarin. Idan harshenku na wata hanyar yin haka, za ku iya amfani da shi anan.
"na tafiya"
Al'adan Ikilisiya ya ce Matiyu ne marubucin wannan bishara, amma littafin bai ba da dalilin canza wakilin sunaye daga "sa" da "Shi" zuwa "ni" ba.
"Yesu ya ce wa Matiyu"
"Matiyu ya tashi ya bi Yesu." Wannan na nufin cewa Matiyu ya zama almajirin Yesu.
Wannan abin ya faru a gidan Matiyu mai karban haraji.
Mai yiwuwa wannan gidan Matiyu ne, amma zai iya zama gidan Yesu ne. Ba da cikakken bayani don hankali da hargitsawa.
"Da Farisawa suka gan cewa Yesu ya na cin abinci tare da masu ƙarban haraji da mutane masu zunubi"
Farisawan sun yi amfani da wannan tambaya don su yi zargin abin da Yesu ya na yi.
A nan "haka" na nufin tambayan da Farisawan sun yi game da yadda Yesu ya na cin abinci da masu ƙarban haraji da masu zunubi.
Yesu ya amsa da magana. Ya na nufin cewa ya na cin abinci da irin waɗannan mutane domin ya zo don ya taimake masu zunubi ne.
"Mutane masu lafiya"
likita
An fahimci jumlar "na bukatan likita." AT: "mutane masu rashin lafiya na bukatan likita"
Yesu ya yi kusan magana daga nassin. AT: "Ku koya ma'anar abin da Allah ya ce a cikin nassin"
A nan "ku" jam'i ne kuma ya na nufin Farisawan.
Yesu ya na faɗan abin da annabi Hosiah ya rubuta a cikin nassi. Anan "Ina" na nufin Allah.
A nan "Na" na nufin Yesu.
Yesu ya na yin amfani da ƙarin magana. Ba ya tunanin cewa akwai mutanen da suke da adalci da ba su neman tuba. AT: "waɗanda su na tunanin cewa su masu adaci ne"
"shigaba da ci kullum"
Yesu ya yi amfani da tambaya don ya amsa almajiran Yahaya. Sun san cewa mutane ba su makoki da azumi a bukin aure. Yesu ya yi amfani da wannan magana don ya nuna cewa almajiransa ba su makoki domin ya na nan tare da su.
Wannan wata hanya ne na nuna loƙacin nan gaba. AT: "loƙacin na zuwa da" ko "wani rana"
AT: "angon ba zai iya kasance da su kuma ba" ko "wani zai ɗauke masu angon"
Mai yiwuwa Yesu ya na nufin mutuwarsa ne, amma kada a sa wannan a bayyane a wannan juyin. Zai yi kyau ku faɗa cewa angon ba zai kasance a wurin kuma ba don a tsare ƙarin maganan.
"Babu wani da na ɗinka sabon ƙyalle a kan tsohon tufa" ko "Mutane ba su ɗinka sabon ƙyalle kamar faci a kan tsohon tufa ba"
"tsohuwar ƙyalle ... ƙyalle"
In da wani zai wanke tufar, facin sabon kayan zai tauye, amma tsohon tufar ba zai tauye ba. Wannan zai yage facin daga tufar ya kuma bar babban rami.
"kyallen sabon kaya." Wannan kyalle ne da ana amfani don a rufe rami a tsohon tufa.
AT: "wannan zai sa yagewar mafi muni"
Yesu ya yi amfani da wani ƙarin magana don ya amsa almajiran Yahaya. Wannan na nufin abu ɗaya da ƙarin maganan a cikin 9:16.
"Ba wani da na ɗura" ko "Mutane ba su ɗura"
Wannan na nufin inabin da bai rigaya tashi ba. Idan ba a san inabi a yankin ku ba, ku yi amfani da kalmar 'ya'ya. AT: "ruwan inabi"
Wannan na nufin salkunan da sun yage domin an riga an yi amfani da su don ta da inabi.
Waɗannan jakuna ne da an yi shi daga fatan dabba.
AT: "kuma wannan zai ɓata salkunan ya kuma tsiyaye inabin"
Loƙacin da sabon inabin ya tashi ya kuma kumbura, fatan na yagewa domin ba za su iya miƙewa ba.
"sabon jakunan inabi." Wannan na nufin salkunan da ba a yi amfani da shi ba.
AT: "wannan zai ajiye salkunan da inabin"
Wannan na nufin amsa da Yesu ya ba wa almajiran Yahaya game da azumi.
Wannan hanya ne da mutum na nuna ladabi a al'adan Yahudawa.
Wannan ya nuna cewa shugaban Yahudawan ya gaskanta cewa Yesu na da ikon sa yarshi ta rayu kuma.
"Almajiran Yesu"
"wadda ta na jini" ko "wadda ta na yawan jini." Mai yiwuwa ta na jini daga mahaifarta ko loƙacin bai kai ba. Waɗansu al'adu na iya samin wata hanya mai kyau na kiran wannan yanayin.
"ma ɗaurinsa" ko "abin da ya sa"
Ta faɗa wa kanta wannan kafin ta taɓa mayafin Yesu. Wannan ya ba da dalilin da ta taɓa mayafin Yesu.
Bisa dokar Yahudawa, bai kamata ta taɓa kowa ba domin ta na yin jini. Ta taɓa mayafinsa domin ikon Yesu ya warkad da ita kuma
"Matan ta na bagen cewa za ta iya taɓa shi a ɓoye, amma Yesu"
Matan ba ainahin yar Yesu ba ne. Yesu ya na magana da ita da ladabi ne. Za a iya juya wannan kamar "ƙaramin mace" ko a cire idan zai zama da gardama.
"domin kin gaskanta da ni, zan warkad da ke"
AT: "Yesu ya warkad da ita a loƙacin"
Wannan yadda ana makokin wanin da ya mutu.
"mutane masu busar sarewa"
Yesu ya na magana da mutane dayawa, don haka ku yi amfani da umurni na jam'i idan harshenku na da shi.
Yesu ya na amfani da magana a cikin magana. Sanannen abu ne a zamanin Yesu a kira mataccen mutum wanda yake "barci." Amma anan matacciya yar za ta tashi, kamar dama ta na barci ne.
AT: "Bayan da Yesu ya fitar da taron waje" ko Bayan da iyalin suke fitar da mutanen waje"
"ta shi daga gado." Wannan ma'ana ɗaya ne a cikin 8:15.
"Mutanen dukka yankin su ji game da shi" ko "Mutanen da sun gan cewa yarinyar ta na da rai sun fara gaya wa kowa a cikin dukka garin"
Wannan na nufin cewa su na tafiya a bayan Yesu, ba lallai ne cewa sun zama almajiransa ba.
Ya na nufin cewa sun so Yesu ya warkad da su.
Yesu ba Ɗan Dauda na zahiri ba, do haka za a iya juya wannan kamar "Zuriyar Dauda." Ko da shike, "Ɗan Dauda" laƙabi ne wa Mai ceto, kuma mai yiwuwa mutanen su na kiran Yesu da wannan laƙabin.
Wannan zai iya zama gidan Yesu ko gidan a cikin 9:10.
Ba a rubuta cikkaken amsarsu ba, amma an gane. AT: "I, Ubangiji, mun gaskanta cewa za ka iya warkad da mu"
Ba a bayyane ne yake ko ya taba idanun maza biyun a loƙaci ɗaya ne ko ya yi amfani da hanunsa na dama don ya taba su ɗaya bayan ɗaya ba. Kamar yadda ana amfani da hanun hagu don ayuka mara tsarki a al'adan, mai yiwuwa ya yi amfani da hanun damansa ne. Ba a bayyane ne yake ko ya yi magana a yayin da yake taba su ba ko ya tabasu kafin ya yi masu magana ba.
AT: "Zan yi kamar yadda kun gaskanta" ko "Domin kun gaskanta, zan warkad da ku"
Wannan na nufin cewa sun iya gani. AT: "Allah ya warkad da idanunsu" ko "makafi biyun sun iya gani"
A nan "gan" na nufin "tabbaci." AT: "Ku tabbata cewa wani bai san game da wannan ba" ko "Kada ku faɗa wa wani cewa ni ne na warkad da ku"
"Mutane biyun ba su yi abin da Yesu ya gaya masu su yi ba. Su"
"gaya wa mutane dayawa game da abin da ya faru da su"
AT: "wani ya kawo beben mutum ... wa Yesu"
rashin iya magana
AT: "wanda na da aljani" ko "wanda aljani na iko da shi"
AT: "Bayan da Yesu ya fitar aljanin da ƙarfi" ko "Bayan da Yesu ya umurci aljanin ya tafi"
"beben ya ya fara yin magana" ko "mutumin da da shi bebe ne ya fara magana" ko "mutumin da yanzu ba bebe ba, ya yi magana"
"Mutanen sun yi mamaki"
AT: "Wannan bai taba faruwa ba" ko "Babu wanda ya taba yin abu irin wannan"
"ya na tilasa aljanun su tafi"
Wakilin suna "ya" na nufin Yesu.
Kalmar "dukka" zugwaigwaitawa ne da na nanata yawan garuruwa da Yesu ya je. Ba lalai ba ne ya je kowannensu ba. AT: "yawancin garuruwa "
"babban kauyuka ... kananun kauyuka" ko "babban birni ... kananun birni"
A nan "mulki" na nufin mulkin Allah kamar sarki. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 4:23.
"kowace irin cuta da rashin lafiya." Kalmomin "cuta" da "rashin lafiya" suna kusa amma za a iya juya su kamar kalmomi dabam dabam. "Cuta" abu ne da ke sa mutum rashin lafiya. "Rashin lafiya" rashin ƙarfin jiki ne ko rashin ɗadi daga samin cuta.
Wannan ƙarin magana na nufin ba su da shugaba da zai kula da su. AT: "Mutanen ba su da shugaba"
Yesu ya yi amfani da ƙarin magana don ya amsa abin da ya na gani. Yesu ya na nufin cewa akwai mutane dayawa da sun shirya su gaskanta da Allah amma mutane kaɗan ne akwai don su koya masu gaskiyar Allah.
"Akwai abinci da sun nuna don wani ya tara"
"ma'aikata"
"ku yi addu'a ga Allah, domin shi ne shugaban girbin"
Wasu marubuta sunsun yi tunani cewa Yesu ya yi wa Allah saɓo domin faɗa wa shanyeyyen mutumin cewa an gafarta masa zunubansa.
Yesu ya gaya wa shanyeyyen mutumin cewa an gafarta masa zunubansa domin ya bayyana cewa ya na da ikon gafarta zunubai a duniya.
Sun yi mamaki suka kuma girmama Allah, wanda ya ba da irin wannan iko wa mutane.
Matiyu mai karbar haraji kafin ya bi Yesu.
Yesu da almajiransa sun ci abinci da masu ƙarbar haraji da mutane masu zunubi.
Yesu ya ce ya zo ne don ya kira masu zunubi ga tuba.
Yesu ya ce almajiransa ba su azumi domin ya na nan da su.
Yesu ya ce almajiransa za su yi azumi a loƙacin da an ɗauke da shi.
Mace mai zub da jini sosai ta taba gezar mayafin Yesu da tunani cewa idan ta taba mayafinsa, za ta warke.
Yesu ya faɗa cewa mace mai zub da jini sosai ta warke ta wurin bangaskiyar ta.
Mutanen sun yi wa Yesu dariya don Yesu ya faɗa cewa 'yar ba ta mutu ba amma ta na barci.
Labarai game da yadda Yesu ya ta da 'yar daga matattu ya bazu zuwa dukka yankin.
Makafi biyu suka yi ta daga murya suna cewa, ''Dan Dauda, ka ji tausayinmu.''!
Yesu ya warkad da makafi biyun bisa ga bangaskiyarsu.
Farisawa suka yi zargin Yesu ta wurin fitar da aljanu ta sarkin aljanu.
Yesu ya ji tausayin taron saboda sun damu, sun kuma karaya su na nan kamar tumakin da babu makiya.
Yesu ya ce wa almajiransa su yi addu'a da sauri don Ubangijin girbi ya aiko da ma'aikata zuwa cikin girbinsa.
1 Yesu ya kira almajiransa goma sha biyu, ya kuma ba su ikon fitar da kazaman ruhohi, su warkar da kowacce irin cuta da rashin lafiya. 2 To yanzu ga sunayen manzanin nan goma sha biyu. Na farkon shine, Saminu, wanda ake kira Bitrus, da dan'uwansa Andarawas, da Yakubu dan Zabadi, da dan'uwansa Yahaya; 3 Filibus, da Bartalamawus, da Toma da Matiyu mai karbar haraji da Yakubu dan Halfa, da Taddawus; 4 Saminu Bakairawane, da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bashe shi. 5 Sha biyun nan su ne Yesu ya aika, ya yi masu umarni ya ce, "Kada ku shiga wajen al'ummai, ko kuma kowane garin Samariyawa. 6 Sai dai ku je wurin batattun tumaki na gidan Isra'ila. 7 Sa'adda kuna tafiya, kuna wa'azi, kuna cewa, 'Mulkin Sama ya kusato'. 8 Ku warkar da marasa lafiya, ku tada matattu, ku tsarkake kutare, ku kuma fitar da aljanu. Kyauta kuka samu ku ma ku bayar kyauta. 9 Kada ku rike zinariya, ko azurfa, ko tagulla a jakarku. 10 Kada kuma ku dauki zabira a tafiyarku, ko taguwa biyu, ko takalma, ko sanda, don ma'aikaci ya cancanci abincin sa. 11 Kowanne birni, ko kauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a cikinsa, ku kuma zauna a wurin har lokacin da za ku tashi. 12 In za ku shiga gida ku ce, salama a gareku. 13 Idan gidan akwai dan salama, salamarku za ta ta tabbata a gare shi. Idan kuwa babu, salamarku za ta komo maku. 14 Ga wadanda su ka ki karbar ku ko sauraron ku, idan za ku fita garin ko gidan, sai ku karkade kurar kafafunku. 15 Hakika, ina gaya maku, a ranar shari'a za a fi rangwanta wa kasar Saduma da ta Gwamrata a kan wannan birni. 16 "Duba, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai, don haka sai ku zama masu wayo kamar macizai, da kuma marasa barna kamar kurciyoyi. 17 Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi maku bulala a majami'unsu. 18 Za su kuma kai ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku bada shaida a gabansu, da kuma gaban al'ummai. 19 Idan har sun bada ku, kada ku damu da yadda za ku yi magana, ko kuwa abin da za ku fada, domin za a ba ku abin da za ku fada a lokacin. 20 Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku. 21 Dan'uwa zai ba da dan'uwansa a kashe shi, uba kuwa dansa. 'Ya'ya kuma za su tayarwa iyayensu, har su sa a kashe su. 22 Kowa kuma zai ki ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har karshe, zai tsira. 23 In sun tsananta maku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Hakika ina gaya maku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Dan Mutum zai zo. 24 Almajiri ba ya fin malaminsa, bawa kuma ba yafin ubangijinsa. 25 Dai dai ne almajiri ya zama kamar malaminsa, bawa kuma kamar ubangijinsa. In har sun kira mai gida Ba'alzabuba, za su kuma bata mutanen gidansa! 26 Don haka kada kuji tsoron su, domin ba abin da yake boye da ba za a bayyana ba. 27 Abin da nake fada maku a asirce, ku fada a sarari. Abin da kuma kuka ji a cikin rada, ku yi shelarsa daga kan soraye. 28 Kada ku ji tsoron masu kisan jikin mutum, amma ba sa iya kashe rai. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon kashe jiki ya kuma jefa rai cikin jahannama. 29 Ba 'yan tsuntsaye biyu ake sayarwa akan kobo ba? Ba ko daya a cikin su da zai fadi kasa ba tare da yardar Ubanku ba. 30 Ai, ko da gashin kan ku ma duk a kidaye yake. 31 Kada ku ji tsoro. Gama darajarku ta fi ta tsuntsaye masu yawa. 32 "Saboda haka duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, ni ma zan yi shaidar sa a gaban Ubana wanda ya ke cikin Sama. 33 Amma duk wanda ya yi musun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi musun sanin sa a gaban Ubana da yake cikin Sama." 34 "Kada ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. Ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi. 35 Domin na zo ne in hada mutum da ubansa gaba, 'ya da uwatarta, mata da kuma surukarta. 36 Zai zama na kuma magabtan mutum su ne mutanen gidansa. 37 Dukan wanda ya fi son mahaifinsa ko mahaifayarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son dansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. 38 Wanda kuma bai dauki gicciyensa ya biyo ni ba, bai cancanci zama nawa ba. 39 Dukan mai son ya ceci ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, yana ceton sa ne. 40 "Wanda ya marabce ku, ya marabce ni ke nan. 41 Wanda ya marabce ni kuwa, ya marabci wanda ya aiko ni. Wanda ya marabci annabi domin shi annabi ne, zai karbi lada kamar na annabi. Wanda kuma ya marabci mai adalci saboda shi mai adalci ne, zai sami lada kamar na mai adalci. 42 Kowa ya ba daya daga cikin 'yan kananan nan, ko da kofin ruwan sanyi ya sha, domin shi almajirina ne, hakika, Ina gaya maku, ba zai rasa ladarsa ba."
Wannan ya fara labarin da Yesu ya turo almajiransa goma sha biyu don su yi aiki.
"kirawo almajiransa goma sha biyu"
Ku tabata cewa wannan matanin ya bayyana cewa wannan iko 1) don fitar da kazaman ruhohi da kuma 2) don warkad da cuta da rashin lafiya.
"ya sa kazaman ruhohi su tafi"
"kowane irin cuta da kowane rashin lafiya." Kalmomin "cuta" da "rashin lafiya" su na kusa amma in ya yiwu a juya su kamar kalmomi biyu dabam dabam. "Rashin lafiya" rashin ƙarfin jiki ne ko wahala daga wani cuta.
Marubucin anan ya ba da sunayen manzane goma sha biyu a matsayin tushen bayanin.
An yi amfani da wannan kalma anan don a sa alama a ainahin labarin. Anan Matiyu ya ba da tushen bayani game da manzane goma sha biyu.
Wannan kungiya ɗaya ne da "almajirai goma sha biyu" a cikin 10:1.
Wannan farko ne bisa shiri ba a jeri ba.
AT: 1) "Bakairawane" laƙabi ne da na nuna cewa ya na cikin kungiyan mutane da sun so su ceci mutanen Yahudawa daga mulkin Romawa. AT: "mai kishin kasarsa" ƙwatanci ne da na nuna cewa shi bakairawane don Allah ya sami ɗaukaka.
"Matiyu, wanda da mai ƙarban haraji ne"
"wanda zai bashe Yesu"
"Yesu ya aika waɗannan mutane sha biyu" ko "waɗannan mutane sha biyun nan ne Yesu ya aiko":
Yesu ya aike su don wata dalili.
"Ya gaya masu abin da za su yi" ko "ya umurce su"
Wannan ƙarin magana ne da na ƙwatanta dukka al'umman Isra'ila da tumakin da sun bazu daga makiyayinsu.
Wannan na nufin al'umman Isra'ila. AT: "mutanen Isra'ila" ko "zuriyar Isra'ila"
A nan "kun" jam'i ne kuma na nufin manzane goma sha biyu.
Jumlar "Mulkin Sama" na nufin mulkin Allah kamar sarki. Wannan jumla na cikin littafin Matiyu ne kadai. Idan ya yiwu, yi amfani da kalmar "sama" a cikin juyinku. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 3:2. AT: "Allahn mu a sama ya yi kusa ya nuna kansa a matsayin sarki"
Waɗannan jam'i ne kuma na nufin manzane goma sha biyu.
Wannan ƙarin magana ne. AT: "sa matattu su rayu kuma"
Yesu bai bayyana abin da almajiran sun ƙarba ko za su bayar ba. Wasu harshen na iya bukaci wannan bayani a cikin jimlan. Anan "Kyauta" na nufin babu biya. AT: "A kyauta kuka ƙarba waɗannan abubuwa, ku bayar da su kyauta wa waɗansu" ko "Kun ƙarba waɗannan abubuwa ba tare da biya ba, don haka, ku ba wa waɗansu ba tare da sa su biya ba"
Waɗannan ƙarafuna ne da ake yin ƙerarren kuɗi. Wannan ƙarin magana ne na kuɗi, idan ba a san irin ƙarfen a garin ku ba, juya su kamar "kuɗi."
Wannan na nufin "ɗamara" ko "ɗamaran kuɗi" amma ya na iya nufin kowane abu da ana iya amfani da shi don ɗaukan kuɗi. Ɗamara wata dogon igiyan ƙyalle ne ko fata da an sa a ƙugu. Ya nan da faɗi da ana iya nadewa a kuma yi amfani don ɗaukan kuɗi.
Wannan na iya zama kowane irin jaka da ana ɗaukan kaya a tafiya, ko jakar da wani ke amfani da shi don ƙarban abinci ko kuɗi.
Yi amfani da irin kalma da kun yi amfani ma "taguwa" a cikin 5:40.
ma'aikaci
A nan "abinci" na nufin kowane abu da mutum na yi. AT: "abin da ya na bukata"
"Duk loƙacin da kun shiga birni ko ƙauye" ko "Loƙacin da kun shiga kowane birni ko ƙauye"
"babban ƙauye ... ƙaramin ƙauye" ko babban gari ... ƙaramin gari." Dubi yadda kun juya wannan a cikin 9:35.
A cikin 10:11-13 mutum da ya "dace" na nufin mutumin da ya yarda ya ƙarbi almajiran. Yesu ya ƙwatanta wannan mutum da wanda "bai dace ba," mutumin da ba ya ƙarban su almajiran.
Ana iya sa a bayyane cikakken ma'anar bayanin. AT: "ku zauna a cikin gidan wannan mutumin har sai kun bar garin ko ƙauyen"
Jumlar "yi masa gaisuwa" na nufin gai da gidan. Sanannen gaisuwa a waɗannan zamanin shi ne "salama a gareku!" Anan "gida" na wakilcin mutanen da suna zama a gidan. AT: "Sa'adda kun shiga cikin gidan, ku gai da mutanen da suke zama a ciki"
A nan "gida" na wakilcin waɗanda su na zama a cikin gidan. AT: "mutanen da suke zama a cikin wannan gidan sun ƙarbe ku da kyau" ko mutanen da suke wannan gidan sun nuna maku hali mai kyau"
Kalmar "shi" na nufin gidan, wadda na wakilcin mutanen da suke zama a cikin gidan. AT: "bari su ƙarbi salamarku" ko "bari su ƙarbi salamarku da kun gaishe su da shi"
Kalmar "bata" na nufin gidan. Anan "gida" na nufin mutanen da suke zama a cikin gidan. AT: "idan ba su ƙarbe ku da kyau ba" ko "idan ba su nuna maku hali mai kyau ba"
AT: 1) idan iyalin ba ta dace ba, Allah zai rike salama ko albarku daga wannan iyali ko 2) idan iyalin ba ta dace ba, yakamata manzanen su yi wani abu, kamar rokon Allah kada ya ƙarbi gaisuwar salamarsu. Idan harshenku na da irin ma'anar komar da gaisuwa, a yi amfani da shi anan.
"Idan babu mutane a cikin gidan ko birnin da za su ƙarbe ku ko saurara"
A nan "magana" na nufin abin da almajiran sun ce. AT: "saurare sakonku" ko "saurare abin da za ku ce"
Ku juya wannan kamar yadda kun yi a cikin 10:11.
"ku karkade kurar kafafunku sa'adda kun tafi." Wannan alama ne cewa Allah ya ki mutanen wannan gidan ko garin.
"Ina gaya maku gaskiyan." Wannan jumla ya kara bayani ga abin da Yesu ya faɗa a gaba.
"azaban zai yi sauki"
Wannan na nufin mutanen da suka yi zama a Saduma da Gwamrata. AT: "mutanen da sun yi zama a garurukan Saduma da Gwamrata"
Wannan na nufin mutanen cikin birnin da basu ƙarbi manzanin ko ji sakonsu ba. AT: "mutanen garin da basu ƙarbe ku ba"
Kalmar "Dubi" anan ya kara bayani a abin da ke a gaba. AT: "Ga, na aike" ko "Sauraro, aiko" ko "Ku yi hankali da abin da zan gaya maku. Na aiko"
Yesu ya na aikan su don wata dalili ta musamman.
Tumaki dabba ne da ba ya iya kariya kuma kyarketai sun ciki binsu. Yesu ya na bayyana cewa mutane na iya cutar da almajiran. AT: "kamar tumaki a cikin mutanen da suke kamar mugayen kyarketai" ko "kamar tumaki a cikin mutanen da su ke yi kamar yadda mugayen dabbobi suke yi"
Yesu ya na gaya wa almajiransa cewa dole ne su zama da hankali da rashin cuta a cikin mutane. Idan kwatanta almajiran da macizai ko kurciyoyi zai kawo rikicewa, Zai fi dama in kun fade shi tamka. AT: "aikata da fahimta da hankali, da kuma rashin laifi da kirki"
Za ku iya juya da "domin" don a nuna yadda waɗannan bayyanen sun shafi juna. AT: "Ku yi hankali da mutane domin za su"
"za su sa ku cikin ikon"
Shugabanin addini na wuri ɗaya ko dattibai wanda suke sadar da salama a cikin mutane
"duke ku da bulala"
AT: "za su kawoku" ko "za su jawoku"
"domin ku nawane" domin kun bi ni"
Jam'in "ku" na nufin "gwamna da sarakuna" ko Yahudawa masu kushewa.
"Idan mutane sun kai ku wa majalisa." "Mutanen" anan ɗaya ne da "mutanen" cikin 10:17.
"kada ku damu"
"yadda za ku yi magana ko abin da za ku ce." Ana iya hada ra'ayi biyun. "abin da za ku ce"
AT: "domin Ruhu mai Tsarki zai gaya maku abin da za ku fada"
Anan "loƙaci" na nufin "nan da nan." AT: "a wannan loƙacin"
Idan wajibi ne, Za a iya juya wannan kamar "Ruhun Allah Ubanku na samaniya" ko ana iya sa karin bayani don a bayyana cewa wannan na nufin Allah Ruhu mai Tsarki ba kuwa ruhun uba na duniya ba.
Wannan muhimmin laƙabi ne wa Allah.
"ta wurin ku"
"Wani ɗan'uwa zai ba da ɗan'uwansa ga mutuwa" ko "Yan'uwa za su ba da yan'uwansu ga mutuwa." Yesu ya yi maganar abin da zai faru sasai.
Ana iya bayyana kalmar "mutuwa." AT: "mika ɗan'uwa ga hukuma wanda za su ƙashe shi"
Ana iya fasara wannan kalmomin kamar ciƙaƙƙen jimla. AT: "Ubanni za su ba da 'ya'yansu ga mutuwa"
"yi tawaye"
AT: "sa a ƙashe su" ko "sa hukuma su ƙashe su"
AT: "Kowa zai tsane ku" ko "Dukka mutane za su tsane ku"
Wannan jam'i ne kuma ya na nufin almajirai goma sha biyun.
A nan "suna" na nufin dukkan mutum. AT: "saboda ni" ko "saboda kun gaskanta da ni"
"duk wanda ya tsaya da aminci"
Ba a bayyane ne yake ko "ƙarshen" na nufin loƙacin da mutum ya mutu, loƙacin da tsanantawan zai kare, ko ƙarshen zamani da Allah zai nuna kansa ma matsayin sarki. Ainahin maganan shi ne sun jure yanda ya kamata.
AT: "Allah zai ceci wannan mutumin"
A nan "wannan" ba ya nufin takamaiman gari. AT: "a gari ɗaya"
"gudu zuwa gari na gaba"
Yesu ya na magana game da kansa.
"isa"
Yesu ya na amfani da ƙarin magana ne anan domin ya koya wa almajiransa gaskiya ta musamman. Yesu ya na nanata cewa kaɗa almajiran su zaci mutane su yi masu da kyau fiye da yanda mutane suka yi wa Yesu.
"Almajiri na da mafi ƙanƙancin daraja fiye da ubangijinsa" ko "Malami na da mafi daraja fiye da almajirinsa"
"kuma bawa na da mafi ƙanƙancin daraja fiye da ubangijinsa" ko "kuma ubangiji na da mafi daraja fiye da bawarsa"
"Almajirin ya ji dadin zama kamar malaminsa"
In ya yiwu, za ku iya sa a bayyane yadda bawan ya zama kamar mallamin. AT: "san sosai kamar yadda mallamin ya sani"
In ya yiwu, za ku iya sa a bayyane yadda bawan ya zama kamar ubangijin. AT: "ya kamata bawan ya ji dadin zama da daraja kamar ubangijinsa"
Yesu ya na kuma nanata cewa tun da mutane sun wullakanta shi, almajiransa su yi zaci cewa mutane za su yi masu haka ko mafi muni.
"sunayen da ake kiran mutanen gidansa za su zama da mafi muni" ko "hakika za a kira mutanen gidansa da sunaye mafi muni"
"Tun da mutane sun kira"
Yesu ya na amfani da wannan ƙarin magana wa kansa.
Ana iya fasara wannan sunan kamar 1) "Beelzebul" ko 2) juya shi da ainahin ma'anarsa na "Shaidan."
Wannan ƙarin magana ne wa almajiran Yesu.
A nan "su" na nufin mutanen da su na wullakanta masubin Yesu.
Dukka waɗannan magana na nufin abu ɗaya ne. Zama da rufe ko ɓoye na wakilcin ajiye a asirce, kuma bayyana na wakilcin zama sananne. Yesu ya na nanata cewa Allah zai sa komai sananne. AT: "Allah zai bayyana abubuwan da mutane na ɓoyewa"
Dukka waɗannan magana na nufin abu ɗaya ne. Yesu ya na nanata cewa almajiran su gaya wa kowa abin da ya faɗa masu a asirce. AT: "Gaya wa mutane a haske abin da na faɗa maku a duhu, ku kuma yi shela akan soraye abin da kun ji a cikin kunnenku"
A nan "duhu" magana ne na "dare" wanda magana ne kuma na "asirce." Anan "haske" magana ne na "sarari." AT: "Abin da nake fada maku a asirce da dare, ku fada a sarari da haske"
Wannan wata hanya ne da na nufin raɗarwa. AT: "abin da na raɗar maku"
Sorayen inda Yesu na zama shimfiɗaɗɗe ne, kuma mutanen da su na da nisa na iya jin duk wanda ke magana da babban murya. Anan "soraye" na nufin wurin da dukka mutane na iya ji. AT: "yi magana da ƙarfi a sararin wuri domin kowa ya ji"
Wannan ba ya bambanta sakanin mutanen da ba su iya ƙashe rai da mutane da sun iya ƙashe rai ba. Babu mutum da zai iya ƙashe rai. AT: "Kada ku ji tsoron mutum. Za su iya ƙashe jikin, amma ba za su iya ƙashe rai ba"
Wannan na nufin sa mutuwa. Idan waɗannan kalmomin basu da kangado, za ku iya juya wannan kamar "ƙashe ka" ko "ƙashe wasu mutane."
sashin mutum da ana iya tabawa, da ke hamayya da jiki ko ruhu
Wannan na nufin lahanta mutane bayan sun mutu.
sashin mutum da ba a iya taba kuma na nan da rai har bayan jikin ya mutu
Za ku iya kara "domin" don ku bayyana dalilin da ya kamata mutane su ji tsoron Allah. AT: "Ji tsoron Allah domin na iya"
Yesu ya bayyana wannan magana kamar tambaya domin ya koyar da almajiransa. AT: "Yi tunani game da tsuntsaye. Su na da daraja kadan da ku na iya saya biyu a dan kobo kadan."
Waɗannan kananun, tsuntsaye masu cin ƙwaya. AT: "kananun tsuntsaye"
Ana juya wannan kamar ƙaramin kobo mai daraja da akawai a kasarku. Na nufin kobon ƙarfe da ya kai ɗayan-sha shida na ƙudin ma'aikaci na kwana ɗaya. AT: "ƙudi kadan sosai"
AT: "Ubanku ya san loƙacin da tsuntsu ɗaya yake mutuwa ya kuma faɗi a kasa"
AT: "Allah ya san yawan gashin dake kanku"
"ƙirga"
"Allah ya na daraja ku fiye da tsuntsaye masu yawa"
"duk wanda ya shaida ni ... Zan kuma shaida a gaban Ubana" ko "Idan wani ya shaida ni ... Zan kuma shaida a gaban Ubana"
"gaya wa waɗansu cewa shi almajiri na ne" ko "amince a gaban waɗansu mutane cewa ya na yi mani biyayya"
Za ku iya sa a bayyane bayanin da kun fahimta. AT: "Zan kuma amince a gaban Ubana wanda ya na cikin sama cewa wannan mutumin nawa ne"
"Ubana na samaniya"
"duk wanda ya musunta ni ... Zan kuwa musunta a gaban Ubana" ko "Idan wani ya musunta ni ... Zan kuwa musunta shi a gaban Ubana"
"musunta ga sauran mutane cewa ya na yi ma ni biyayya" ko "kin ya amince wa waɗansu cewa shi almajiri na ne"
Za ku iya sa a bayyane bayanin da kun fahimta. AT: "Zan musanta a gaban Ubana wanda na sama cewa wannan mutumin nawa ne"
"Kada ku zata" ko "Kada ku yi tunani"
Wannan na nufin mutanen da su na zama a duniya. AT: "ga mutanen duniya" ko "ga mutane"
Wannan na nufin rabawa, faɗa, da kisa a sakanin mutane.
"sa ... yi faɗa da"
" hada ɗa da ubansa gaba"
"mafi munin maƙiyan mutum"
"mutanen gidansa"
A nan "shi" na nufin kowane mutum. AT: "Waɗanda na ƙaunar ... bai cancanci" ko "Idan ku na ƙaunar ... ba ku cancanci"
Kalmar "ƙauna" a nan na nufin "ƙauna na 'yanwantaka" ko "ƙauna daga aboki." AT: "damu da" ko "ba da kai"
"ya cancanci ya zama nawa" ko "cancanci ya zama almajiri na"
"ɗauka gicciyensa ya biyo ni." Gicciyen na wakilcin azaba da mutuwa. Daukan gicciye na wakilcin yarda ka sha azaba ka kuma mutu. AT: "yi mun biyayya har ga azaba da mutuwa"
"ɗauka" ko "ɗauka da ɗauki"
Yesu ya yi amfani da ƙarin magana don ya koyar da almajiransa. AT: "Waɗanda sun so ransu za su rasa su. Amma waɗanda sun rasa ransu ... za su samu" ko "Idan kun sami ranku za ku rasa shi. Amma idan kun rasa ranku ... za ku same shi"
Wannan ƙarin magana ne na "ajiye" ko "ceci." AT: "na yin kokari ya ajiye" ko "na yin kokari ya cece"
Wannan ba ya nufin cewa mutumin zai mutu. Karin magana ne da na nufin cewa mutumin ba zai yi rayuwa ta ruhaniya da Allah ba. AT: "ba zai sami rayuwa ta gaskiya ba"
Wannan ba ya nufin mutuwa. Karin magana ne da na nufin mutum ya zaba cewa yin biyayya da Yesu ya fi muhimminci fiye da ransa. AT: "wanda ya hanakansa"
Wannan ƙarin magana na nufin cewa mutumin zai yi rayuwa ta ruhaniya da Allah. AT: "zai sami rai ta gaskiya"
Kalmar "Shi" na nufin kowanene. AT: "Duk wanda" ko "duk wanda ya" ko "Wanda ya"
Wannan na nufin ƙarban wani kamar bako.
Yesu ya na nufin cewa idan wani ya marabce ku, na nan kamar marabtan shi ne. AT: "Idan wani ya marabce ku, ya na nan kamar ya na marabta na ne"
Wannan na nufin duk loƙacin da wani ya marabci Yesu, Na nan kamar marabtan Allah ne. AT: "In wani ya marabce ni, na nan ne kamar ya na marabtan Allah Uba wanda ya aiko ni" ko "Idan wani ya marace ni, ya na nan kamar ya na marabtan Allah Uba wanda ya aiko ni"
A nan "shi" ba ya nufin mutumin da ke yin marabta. Ya na nufin mutumin da an yi masa maraba.
Wannan na nufin lada da Allah na ba wa annabin, ba lada da annabi ke ba wa wani mutum ba.
A nan "shi" ba ya nufin mutumin da ke yin marabta. Ya na nufin mutumin da an yi masa maraba.
Wannan na nufin lada da Allah na ba wa mai adalci, ba lada da mai adalci ke ba wa wani ba.
"Duk wanda ya bayar"
"daya daga cikin 'yan ƙanƙantan nan." Jumlar "ɗaya daga cikin waɗannan" na nufin ɗaya daga cikin almajiran Yesu.
"domin shi almajirina ne." Anan "shi" ba ya nufin wanda an ba shi amma ga mafi ƙanƙanci.
A nan "zai" da "sa" na nufin wanda an ba shi.
"Allah ba zai hana shi ba." wannan bai kunsa ƙwace dukiya ba. AT: "Allah zai ba shi"
Yesu ya ba wa almajiransa goma sha biyu ikon fitar da kazamar ruhohi, su kuma warkar da kowacce irin cuta da rashin lafiya.
Sunar almajirin da zai bashe Yesu shi ne Yahuza Iskariyoti.
Yesu ya aike almajiransa zuwa wurin batattun tumaki na gidan Isra'ila kadai.
A'a, almajiran ba za su ɗauki kuɗi ko ƙarin tufafi ba.
Almajiran za su nemi wani mai mutunci a cikin kauyen sai su zauna a wurin har lokacin da za su tashi.
Hukunci a kan biranen da ba su karbi almajiran ko saurare magangarsu ba zai fi hukuncin Sadoma da Gomrata.
Yesu ya ce mutanen za su ba da almajiran wa majalisa, a duke su, a kuma kawo su gaban gwamnoni da sarakuna.
Ruhun Uba zai yi magana ta wurin almajiran a loƙacin da an bada su.
Yesu ya ce waɗanda sun jimre har karshe za su tsira.
Waɗanda sun ƙi Yesu za su kuma ƙi almajiransa.
Mu ji tsoron shi wanda ke da ikon hallaka jiki da rai a jahannama.
Kada mu ji tsoron masu kisan jikin, amma ba sa iya ƙashe rai ba.
Yesu zai shaida shi a gaban Uba a sama.
Yesu zai musanta shi a gaban Uba a sama.
Yesu ya ce ya zo ya kowa rabuwa har cikin gigaje.
Wanda ya rasa ransa ta dalilin Yesu zai sami ransa.
Wanin da ya ba da kofin ruwa mai tsanyi wa almajiri mai mara daraja zai ƙarbi ladar sa?
1 Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa gargadi, sai ya bar wannan wuri, ya tafi biranensu domin yayi koyorwa, da wa'azi. 2 Da Yahaya mai baftisma ya ji daga kurkuku irin ayyukan da Yesu ke yi, sai ya aika sako ta wurin almajiransa. 3 Ya ce masa. "Kai ne mai zuwa"? ko mu sa ido ga wani. 4 Yesu ya amsa ya ce masu, "Ku je ku gaya wa Yahaya abin da ku ka gani da abin da ku ka ji. 5 Makafi suna samun ganin gari, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na jin magana kuma, ana tada matattu, mabukata kuma ana ba su bishara. 6 Kuma mai albarka ne wanda baya tuntube sabili da ni. 7 Bayan wadannan sun tafi, sai Yesu ya fara wa jama'a jawabi game da Yahaya mai baftisma, yana cewa, "Me ake zuwa gani a jeji - ciyawa ce da iska ke busawa? 8 Shin menene kuke zuwa gani a jeji - mutum mai sanye da tufafi masu laushi? Hakika, masu sa tufafi masu laushi suna zaune ne a fadar sarakuna. 9 Amma me ku ke zuwa gani, annabi? Hakika ina fada maku, fiye ma da annabi. 10 Wannan shine wanda aka rubuta game da shi, 'Duba, ina aika manzona, wanda za ya tafi gabanka domin ya shirya maka hanya inda za ka bi'. 11 Ina gaya maku gaskiya, cikin wadanda mata suka haifa, babu mai girma kamar Yahaya mai baftisma. Amma mafi kankanta a mulkin sama ya fi shi girma. 12 Tun daga kwanakin Yahaya mai baftisma zuwa yanzu, mulkin sama yana shan gwagwarmaya, masu husuma kuma su kan kwace shi da karfi. 13 Gama dukan annabawa da shari'a sun yi annabci har zuwa lokacin Yahaya. 14 kuma in zaku karba, wannan shine Iliya wanda za ya zo. 15 Wanda ke da kunnuwan ji, ya ji. 16 Da me zan kwatanta wannan zamani? Ya na kamar yara masu wasa a kasuwa, sun zauna suna kiran juna 17 suna cewa mun busa maku sarewa baku yi rawa ba, mun yi makoki, baku yi kuka ba. 18 Gama Yahaya ya zo, baya cin gurasa ko shan ruwan inabi, sai aka ce, "Yana da aljannu". 19 Dan mutum ya zo yana ci yana sha, sai aka ce, 'Duba, ga mai hadama, mashayi kuma, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!' Amma hikima, ta wurin aikin ta ake tabbatar da ita. 20 Sannan Yesu ya fara tsautawa biranen nan inda ya yi yawancin ayukansa, domin ba su tuba ba. 21 "Kaiton ki Korasinu, kaiton ki Batsaida! In da an yi irin ayuka masu ban mamaki a Taya da Sidon! Yadda aka yi a cikinku, da tuni sun tuba suna sanye da tsumma da yafa toka. 22 Amma zai zama da sauki a kan Taya da Sidon a ranar shari'a fiye da ku. 23 Ke kafarnahum, kina tsammani za a daukaka ki har zuwa sama? A'a za a saukar da ke kasa zuwa hades. Gama in da an yi irin al'ajiban da aka yi a cikin ki a Sodom, da tana nan har yanzu. 24 Amma ina ce maku, za a saukaka wa Sodom a ranar shari'a fiye da ku." 25 A wannan lokaci Yesu ya ce, "Ina yabon ka, ya Uba, Ubangijin sama da kasa, domin ka boye wa masu hikima da fahimta wadannan abubuwa, ka bayyana wa marasa sani, kamar kananan yara. 26 I, ya Uba gama wannan shine ya yi daidai a gare ka. 27 An mallaka mani dukan abu daga wurin Ubana. Sannan babu wanda ya san Dan, sai Uban, babu kuma wanda ya san Uban, sai Dan, da duk wanda ya so ya bayyana masa. 28 Ku zo gare ni, dukanku masu wahala da fama da nauyin kaya, ni kuma zan ba ku hutawa. 29 Ku dauki karkiya ta ku koya daga gare ni, gama ni mai tawali'u ne da saukin hali a zuciya, sannan zaku sami hutawa ga rayukanku. 30 Gama karkiyata mai sauki ce, kaya na kuma ba shi da nauyi."
Wannan wani bangare ne daga cikin farkon labarin da Matiyu ya bayana yadda Yesu ya yi magana game da Yahaya Mai Baftisma ga almajiransa.
Wannan magana ya kai mu daga koyaswar Yesu zuwa ga abin da ya faru a gaba. AT: "Sa'anan kuma" " ko "Bayan haka"
"ya gama koyar" ko "ya gama bada umurnin"
Wannan na nufin mazanai goma sha biyun da Yesu ya zaɓa.
A nan "su" na nufin Yahudawa gabakiɗaya.
Wannan kalman alama ce ta kaucewa daga ainihin kan labarin. Anan Matiyu ya fara bada sabuwar gangaren labarin.
"Lokacin da Yahaya, wanda ke cikin kurkuku, ya ji game da" ko kuwa "Sa'ad da wani ya gaya wa Yahaya, wanda ke a kurkuku, game da." Kodashike, Matiyu bai gaya wa masu karatunsa cewa Sarki Hiridus ya kulle Yahaya a kurkuku ba, ainihin wanda ya rubuta masu suna sane da labarin sun kuma san ainihin zance anan. Matiyu zai kara yin bayani nan gaba game da Yahaya Mai Baftisma, saboda haka, zai fi kyau kada a bayana shi anan.
Yahaya Mai Baftisma ya aike almajiransa da sako zuwa ga Yesu.
"sa" na nufin Yesu.
"Kai ne wanda muke sa sammanin zuwansa." Wannan a wani hanya, na nufin Mai Ceto ko Almasihu.
"Mu yi sammanin wani dabam" Kalman nan "mu" na nufin dukkan Yahudawa ba almajiran Yahaya ba.
"gaya wa Yahaya"
AT: "Ina warkar da Kutare"
A nan a ta da na nufin a sa wanda ya mutu ya rayu kuma. AT: "Mutanen da suka mutu an sa su su rayu kuma" ko "Ina sa waɗanda suka mutu su rayu kuma" and idiom)
AT: "Ina gaya wa mutane mabukata"
Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yahaya Mai Baftisma.
Yesu ya yi amfani da tambaya don ya sa mutane su yi tunani ko wani irin mutum ne Yahaya Mai Baftisma. AT: "Haƙiƙa ba a zuwa jeji a ga ciyawa ...iska...!"
Ma'ana suna kamar haka 1) Yesu na nufin shuke-shuke da ke a Kogin Urdun ko 2) Yesu na amfani da wannan don ya na nufin wane irin mutum. AT: "mutum wanda ke iya canza ra'ayinsa, shi kuma kamar ciyawa ne da isake busawa nan da nan"
AT: "tafi cikin iska" ko "iska ke busawa"
Yesu ya yi amfani da tambaya don ya sa mutanen su yi tunani ko wani irin mutum ne Yahaya Mai Baftisma. AT: "Haƙiƙa ba ku zuwa jeji don ku ga mutum ...tufafin...!"
"Sanya tufafi masu tsada." Masu arziki na sa irin wannan tufafin.
Wannan kalman na kara nanata abin da ke biye. AT: "lalle"
"fădar sarakuna"
Yesu ya yi amfani da tambaya don ya sa mutane tunani ko wani irin mutum ne Yahaya Mai Baftisma. AT: "Amma kuwa kun tafi jeji don ku ga annabi!"
Ina gaya maku, hakika"
AT: "she ba annabi ne kawai ba" ko "yana da muhimmanci fiye annabi"
AT: "Wannan shine abin da annabi Malachi ya rubuta game da Yahaya Mai Baftisma tun dă"
kalman nan "na" na nufin Allah. Malachi ya ambata abin da Allah ya faɗa ne.
A nan "ka" na nuna cewa Allah na magana ne da Mai Ceton. AT: "ya zo a gabanka"
Wannan na nufin cewa manzon zai shirya mutane don su karɓi sakon Mai Ceton.
"gaskiya ina gaya maku." Wannan magana na kara nanata abin da Yesu ya faɗa a nan gaba.
Kodashike Adamu ba mace ce ta haife shi ba, amma wannan wata hanya ce na yin magana game da dukkan 'yan Adam. AT: "cikin dukkan mutane da suka taba rayuwa"
AT: "Yahaya Mai Baftisma ya fi kowa girma" ko "Yahaya Mai Baftisma shine mafi muhimanci"
A nan "Mulkin sama" na nufin mulkin Allah a matsayin Sarki. Maganan nan "mulkin sama" Matiyu ne kawai ya yi amfani da shi. In mai yiwuwa ne, to sai ku cigaba da amfani da "sama" a juyin ku. AT: "mafi kankanata a karƙashin mulkin Allahmu a cikin sama"
"ya fi Yahaya muhimanci"
Tun daga lokacin da Yahaya Mai Baftisma ya fara wa'azi sakonsa." Kalman nan "lokaci" mai yiwuwa na nufin watanni ko shekaru.
Akwai fasarar wannan aya daban dabam. UDB na ɗaukan cewa wasu mutane na so su yi amfani da mulkin Allah don son ransu, saboda da haka suna shirye su musguna wa sauran mutane don su cikata wannan. Wasu juyin suna ɗaukan cewa kira don shiga mulkin Allah ta zama cikin gaggawa, saboda haka lallai ne mutane su yi kowace abin da za su iya yi don su amsa wannan kira, su kuma guje wa gwaji ta cigaba da yin zunubi. Fasara ta uku shine cewa mutane masu kawo hargitsi na yi wa mutanen Allah lahani don haka suna koƙarin hana Allah mulki.
A nan "annabawa da shari'a" na nufin abubuwan da annabawa da Musa suka rubuta a nassi. AT: "Waɗannan sune abubuwan da annabawa da Musa suka yi annabcinsa tawurin nassosin har zuwa lokacin Yahaya Mai Baftisma"
"ku" na nufin taron mutane.
Kalman nan "shi" na nufin Yahaya Mai Baftisma. Ba wai wannan na nufin cewa Yahaya Mai Baftisma shine Iliya ba. Yesu yana nufin cewa Yahaya Mai Baftisma ya cika annabcin da aka yi game da "Iliya wanda zai zo" ko Iliya mai zuwa. AT: "sa'ad da annabi Malachi ya ce cewa Iliya zai dawo, yana magana ne game da Yahaya Mai Baftisma."
Wannan wata hanya ce da ake nufin kowane mutum da ke jin abin da Yesu ke faɗa. AT: "Duk wanda zai iya ji na"
A nan "kassa kunne" na nufin sa hankali ga abinda ake faɗa. AT: "kassa kunne ga abin da nake faɗa"
Yasu ya yi amfani da wannan tambaya don ya gabatar da kwatancinsa da mutane a lokacinsa da da kuma abin da 'ya'ya sa su ce a cikin kasuwa. AT: "Wannan shine kamanin wannan zamani"
"mutanen da ke rayuwa a yanzu" ko "waɗannan mutane" ko "ku mutanen wannan zamani"
Yesu ya yi amfani da wannan misălin don bayana irin mutanen da ke rayuwa a lokacinsa. Ya kwatanta su da 'ya'yan da ke koƙarin sa sauran 'ya'ya su yi wasa tare da su. Amma duk koƙarin da suka yi, sauran 'ya'yan ba za su haɗa kai da su ba. Yesu na nufin cewa ba lallai ne a ce in Allah ya aiko da wani kamar Yahaya Mai Baftisma, wanda ya yi rayuwa a jeji ya kuma yi azumi, ko wani kamar Yesu wanda ya yi murna a wurin biki da masu zunubi bai kuma yi azumi ba. Mutanen nan, musamman Farisiyawa da kuma shugabannen adini su taurare sun kuma ƙi su karɓi gaskiyar Allah.
wani babban wuri wanda mutane ke sayar da siyan abubuwa.
"mu" na nufin 'ya'ya da ke a kasuwa. Anan "ku" na nufin rukuni sauran 'ya'yan.
"amma ba ku yi rawa ba ga kiɗa ta murna ba"
Wannan na nufin cewa sin yi wakar baƙin ciki kamar wand mataye ke yi a wurin jana'iza.
"amma ba ku yi kuka tare da mu ba"
A nan "gurasa" na nufin abinci. Wannan ba ya nufin cewa Yahaya bai taba cin abince ba. Yana nufin cewa sau da dăma yana azumi, kuma a lokacin da ya ci abinci, bai ci abinci mai kyau ko mai tsada ba. AT: "Sau da dama yana azumi kuma ba ya shan barasa" ko "ba ya cin abinci mai kyau ba ya kuma shan ruwan inabi"
AT: sun ce wai yana da aljannu" ko "sun zargi shi cewa yana da aljannu"
Dukkan bayyanuwar kalman nan "su" na nufin mutane a wancan zamani musamman Farisiyawa da shugabannen adini.
Yesu yana nufin kansa. AT: "Ni, Ɗan Mutum na zo"
Wannan ya sha banbam da halin Yahaya. Wannan nufin ci fiye da sha fiye da yadda ya kamata. Yana nufin cewa Yesu ya yi biki ya kuma ci abinci mai kyau ya kuma sha daidai kamar sauran mutane.
AT: "sun ce wai shi mutum mai handama ne mashayi kuma ...masu zunubi." ko "sun zargi shi cewa yana ci yana kuma sha fiye da yadda ya kamata kuma shi... masu zunubi."
"shi mai handama ne" ko "a kodayaushe yana ci fiye da yadda ya kamata"
"bugagge" ko "ya cigaba da shan barasa so sai"
wannan wani karin magana ne da Yesu ya yi amfani da wannan a yanayin saboda mutanene da su ƙi shi da Yahaya su maras hikima ne. Yesu da Yahaya Mai Baftisma su masu hikima ne, kuma sakamakon ayyukansu ta tabbatar da ita.
A nan "hikima" an bayyana ta kamar mace da an tabbatar cewa ayyukan nagari ne. Yesu yana nufin cewa sakamakon ayyukan mutum mai hikima na nuna tabbacin cewa lallai shi mai hikima ne. AT: "sakamakom ayyukan mutum mai hikima yana ba da tabbacin cewa shi mai hikima ne"
Anan "biranen" na nufin mutanen da ke rayuwa a cikin ta. AT: "tsautawa mutane birane"
"gari"
"manya-manyan aiki" ko "aiki iko" ko "mu'ujizai"
Yesu ya yi magana kamar mutanen biranen Korasinu da Betsaida suna wurin kuma suna jin shi, amma ba sa ji
"Zai zama maki da muni." Anan "ki" na nufin birnin. In zai fi sauki a yi amfani da kalman nan "ku" a sa'ad da ake nufin mutane maimakon birni, to sai ku yi amfani da shi a juyin ku.
Sunayen waɗannan biranen na nufin mutanen da ke zama cikin waɗannan birane.
Yesu yana bayana wata yanayi ta musamman da zai iya faruwa a dă amma bai faru ba.
AT: "In da a ce na yi ayuka masu ban mamaki a tsakanin mutanen Taya da Sidon wanda na yi a tsakaninku"
A nan "ku" na nufin Korazinu da Betsaida. In ya fi sauki a harshenku, za ku iya yin amfani da "ku" a maɗaɗɗin birane biyun ko "ku" a maɗaɗɗin mutanen biranen.
"su" na nufin mutanen Taya da Sidon.
"da sun nuna cewa sun damu saboda zunubansu"
A nan "Taya da Sidon" na nufin mutanen da ke zama a wurin. AT: "Allah zai nuna jinkai ga mutanen da ke Taya da Sidon a ranar shari'a fiye da ku" ko "Allah zai yi muku hunkucin mai tsanani a ranar shari'a fiye da mutanen Taya da Sidon"
A nan iya bayana abin nufin anan a fili. AT: "fiye da ku domin ba ku tuba kun bada gasikiya a gare ni ba, kodashike kun ga mu'ujizan da na yi"
Yesu na magana da mutanen birnin Kafarnahum kamar suna jin shi, amma ba sa kuwa ji. Kalman nan "ke" na nufin Kafarnahum a gabaɗayan waɗannan ayoyi biyun.
In ya fi sauki ayi amfani da "ku" a sa'ad da ana nufin mutanen birnin, to za ku iya yi amfani da shi a juyin ku.
Sunayen waɗannan biranen na nufin mutane da ke zama a Kafarnahum da Saduma.
"kina tsammanin za a ɗauke ki zuwa sama?" Yesu ya yi tambayar ganganci don ya tsautawa matanen da ke Kafarnahum saboda girman kan su. AT: "ba za ki iya ɗauke kan ku zuwa sama ba!" ko "yabon da wasu ke yi miki ba za ta kai ki sama ba!" ko "Allah ba zai kai ki sama ba kamar yadda ki ke tunani zai yi!"
AT: "Allah zai kai ku zuwa Hades"
Yesu ya bayana wata misalin yanayin da dă zai iya aukuwa amma bai auku ba.
AT: "In da a ce na yi manyan ayuka a tsakanin mutanen Saduma irin wanda na yi a tsakanin ku"
Kalman nan "ta" na nufin birnin Saduma.
Wannan magana na kara nanata abin da Yesu ya faɗa a gaba.
A nan "ƙasar Saduma" na nufin mutane mutanen dake zama a wurin. AT: "Allah zai nuna jinkansa ga mutanen Saduma a ranar shari'a fiye da ku" ko "Allah zai yi maku hukunci mai tsanani fiye da mutanen Saduma a ranar shari'a"
Wannan lakabi mai muhimmanci ne na Allah.
"Ubangiji mai mulkin sama da duniya." "sama da duniya" na nufin dukkan mutane da abubuwan da ke cikin duniya gabakiɗaya. AT: "Ubangiji mai mulkin dukkan duniya"
Ma'anar kalmomin "waɗannan abubuwa." ba ya a fili. In harshen ku na bukatan bayana abin nufi, to wannan juyin zai zama mafi kyau a yi amfani da shi. AT: "ka ɓoye waɗannan gaskiyar ... ka bayyana su"
"ba ka sa waɗannan abubuwa su zama sanane ga." Wannan aikatau sabo ne da "bayyana"
AT: "ga mutanen masu hikima da fahimta"
Yesu ba ya tunanin cewa mutanen nan suna da hikima. AT: "mutanen da ke tunanin cewa suna da hikima da fahimta"
"sa su zama sananne." Kalman nan "su" na nufin "waɗannan abubuwa" a baya cikin wannan aya.
Yesu ya kwatanta mutane jãhilai da 'ya'ya kanana. Yesu ya nanata cewa mutane da yawa da suka gaskanta da shi ba a koyar da su da kyau ba ko kuwa ba sa tunanin kansu a matsayin masu hikima.
Maganan nan "a gare ka" na nufin yadda mutane ke duban wani abu. AT: "gama ka ga ya kyautu ka yi wannan"
AT: "Ubana ya mallaka mani dukkan kome" ko "Ubana ya mika mini dukkan kome
Ma'anar mai yiwuwa na kamar haka 1) Allah Uba ya bayyana dukkan abubuwa game da kansa da mulkinsa ga Yesu ko 2) Allah ya mika dukkan iko ga Yesu.
Wannan lakabi ne mai muhimmanci na Allah da ke bayana dangantakan Allah da Yesu.
"Uban kaɗai ne ya san Ɗan"
Kalman nan "san" anan na nufin fiye da idan sani wani. Yana nufin sani wani na kwarai saboda dangantaka ta musamman da shi.
Yesu na duban kansa a matsayin na uku.
Wannan lakabi ne mai muhimmanci na Yesu, Ɗan Allah.
"Ɗan kaɗai ya san Uban"
Yesu ya yi magana game da mutanen da sun raunana cikin koƙarinsu su yi biyayya ga dukkan dokoki kamar dokokin kaya ne mai nauyi kuma mutane da shan wahalan ɗaukansu. AT: "wanda ya raunana daga koƙarin" ko "waɗanda suka raunana daga koƙarin yi matuƙar biyayya da dokokin"
"Zan bar ku ku huta daga wahala da nauyi"
Yesu yana kiran mutane su zo su zama almajiransa da masubin sa.
A nan "tawali'u" da "saukin halin zuciya" a takaice na nufin abu ɗaya. Yesu ya haɗa su don ya nanata cewa shi zai yi kirki fiye da shugabannen adini. AT: "Ni mai saukin kai ne da kuma tawali'u" ko "Ni mai matuƙar saukin kai ne"
A nan "zuciya" na nufin cikin mutum. Maganan nan "saukin halin zuciya" na nufin "kaskanci" AT: "Kaskanci"
kalman "rayuka" na nufin mutum gabaɗaya. AT: "za ku sami hutawa" ko "za ku iya hutawa"
Duk waɗannan maganganu na nufin abu ɗaya. Yesu na nanata cewa ya fi sauki a yi masa biyayya fiye da shari'ar Yahudawa. AT: "Gama abin da na sa a kanku, za ku iya ɗauka wa domin ba shi da nauyi.
Kalman "ba shi da nauyi" anan dabam ne da nauyi ba kuma duhu.
Yesu ya gama yi wa almajiransa goma sha biyu gargadi kafin ya tafi.
Yahaya mai Baftisma ya aika sakon, "Kai ne Mai Zuwa, ko mu sa ido ga wani"?
Makafi suna samun ganin gari, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na jin magana kuma, ana tada matattu, mabukata kuma ana ba su bishara.
Yesu ya yi alkawarin albarka ga waɗanda basu yi tuntuɓe sabili da shi ba.
Yesu ya faɗa cewa Yahaya mai Baftisma shi ne mai sakon da an yi annabci, wanda zai shirya hanya kafin Mai Zuwa.
Yesu ya ce Yahaya mai Baftisma ne Iliya.
Wancan zamanin sun ce Yahaya mai baftisma na da aljanu.
Wancan zamanin sun faɗa cewa Yesu mai hadama ne, mashayi kuma, kuma abokin masu karbar haraji da masu zunubi.
Yesu ya tsautawa biranen da ya yi yawancin ayukansa, amma ba su tuba ba.
Yesu ya girmama Uba domin bayyana mulkin sama ga waɗanda ba a koyar masu ba, kamar kananar 'ya'ya.
Yesu ya girmama Uba domin rufe mulkin sama wa masu hikima da fahimta.
Yesu ya ce ya san Uba, da kuma duk wanda ya so ya bayyana shi.
Yesu ya yi alkawarin hutu wa masu wahala da nauyin kaya.
1 A wannan lokaci, Yesu ya tafi a ranar Asabaci, ya bi cikin gonar hatsi. Almajiransa na jin yunwa, sai suka fara zagar hatsi suna ci. 2 Amma da Farisawa suka gan su, sai su ka ce wa Yesu. "Duba, almajiranka su na yin abin da doka ta haramta a ranar Asabaci." 3 Amma Yesu ya ce masu, "Baku karanta abin da Dauda ya yi ba, lokacin da ya ke jin yunwa, tare da mazan da ke tare da shi? 4 Yadda ya shiga gidan Allah, ya ci gurasar alfarwa da doka ta hana shi ko mazan da ke tare da shi su ci, sai dai Firistoci ne kawai doka ta basu damar ci? 5 Sa'annan ba ku karanta cikin shari'a cewa, a ranar Asabaci, Firistoci da ke cikin haikali na sabawa ranar Asabaci, amma kamar ba su yi laifi ba? 6 Amma ina tabbatar maku da cewa, wani wanda ya fi haikali girma yana nan. 7 In da kun san ma'anar wannan 'Na fi son jinkai fiye da hadaya,' da baku shari'anta wa marar laifi ba. 8 Gama Dan mutum shine Ubangijin Asabaci." 9 Sa'annan Yesu ya bar wannan wuri, ya shiga majami'ar su. 10 Sai ga wani mutum wanda hannun sa ya shanye, sai Farisawa suka tambayi Yesu, cewa, "Doka ta halarta a yi warkarwa a ranar Asabaci?" Domin su zarge shi a kan zunubi. 11 Yesu ya ce masu, "Wanene a cikin ku, wanda idan ya na da tunkiya guda, sa'annan tunkiyar nan ta fada a rami mai zurfi a ranar Asabaci ba zai kamo ta ya fitar da ita ba? 12 Yaya za a kwatanta darajar mutum da tunkiya! Saboda haka ya halarta a yi alheri ranar Asabaci." 13 Sai Yesu ya ce wa mutumin nan "Mika hannun ka." Ya mike hannunsa, sai hannun nan ya dawo lafiyaye kamar dayan hannunsa. 14 Amma Farisawa su ka fita waje su ka fara mugun shiri domin sa. Su na neman hanyar da za su kashe shi. 15 Da Yesu ya fahimci wannan, sai ya janye kan sa daga nan. Mutane da dama su ka bi shi, ya warkar da su duka. 16 Ya dokace su da kada su bayyana shi ga kowa, 17 domin ya zama gaskiyar abin da aka fada ta wurin annabi Ishaya, cewa, 18 "Dubi, bawa na zababbe; kaunatacce na, wanda ya ke faranta mani raina sosai. Zan sa Ruhu na bisan sa, za ya furta hukunci zuwa al'ummai. 19 Ba za ya yi jayayya ko tada murya ba, babu wanda za ya ji muryar sa a karabku. 20 Ba zai karya kara da ya tankwashe ba; ba zai kashe fitilar da ta kusa mutuwa ba; sai ya kawo hukunci ga nasara. 21 Sa'annan al'ummai za su dogara a ga sunansa. 22 Sa'annan wani mutum, makaho ne, kurma kuma, aljannu kuma na cikinsa, an kawo shi wurin Yesu. Ya warkar da shi, ya sami ganin gari ya kuma yi magana. 23 Jama'a su ka yi mamaki kwarai, su na cewa, "Ko wannan ne Dan Dawuda?" 24 Amma da Farisawa su ka ji wannan al'ajibi, sai su ka ce, "Mutumin nan yana fitar da aljannu ta wurin Bahalzabuba sarkin aljannu ne." 25 Amma Yesu ya san tunanin su, sai ya ce. "Duk mulkin da ya rabu gaba da kan sa, ba zaya tsaya ba, duk wani birni da ya rabu ba zai tsaya ba, ko gida da ya tsage, za ya rushe. 26 Idan Shaidan ya fitar da Shaidan, ya rabu gaba da kansa. Yaya mulkin sa za ya tsaya? 27 Idan Ina fitar da aljannu da ikon Ba'alzabuba, ta wurin wa masu bin ku su ke fitar da su? Saboda haka, su za su shari'anta ku. 28 Amma idan ina fitar da aljannu da Ruhun Allah ne, hakika mulkin Allah ya zo gare ku. 29 Kuma ta yaya mutum za ya shiga gidan mai karfi ya kwashe masa kaya ba tare da ya fara daure shi ba? Sa'annan ne za ya iya satar masa kaya daga gidansa. 30 Wanda baya tare da ni yana gaba da ni ke nan, wanda kuma baya tarawa tare da ni, yana watsarwa ne. 31 Saboda haka ina ce maku, kowanne zunubi da sabo, za a gafarta wa mutum, amma sabon Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta shi ba. 32 Duk wanda yayi batanci ga Dan Mutum, za a gafarta masa. Amma duk wanda yayi batanci game da Ruhu Mai Tsarki ba za a gafarta masa ba, a nan duniya da har abada. 33 Ko dai a mai da itace mai kyau 'ya'yansa kuma su yi kyau, ko a mai da itace marar kyau 'ya'yansa kuma marasa kyau, gama ana sanin itace ta wurin 'ya'yansa. 34 Ku 'ya'yan macizai, tun da ku miyagu ne, yaya za ku iya fadin abubuwa nagari? Gama daga cikar zuciya baki ke magana. 35 Mutumin kirki daga ajiyar zuciyarsa ya kan fitar da abubuwa masu kyau, mugun mutum kuma daga mummunar ajiyar zuciyarsa ya kan fitar da abubuwan mugunta. 36 Sa'annan ina ce maku a ranar shari'a, mutane za su bada lissafin abubuwan banza da su ka fadi. 37 Gama ta wurin maganganun ku, za a 'yantar da ku, ta wurin maganganun ku kuma za a kashe ku." 38 Sa'annan wadansu Malaman Attaura, da Farisawa suka amsa suka ce wa Yesu, "Mallam, muna so mu ga wata alama daga gare ka." 39 Amma Yesu ya amsa ya ce masu, "Mugun zamani da mazinaciyar tsara, su na bukutar alama. Amma babu alamar da za a ba su, sai dai alamar annabi Yunusa. 40 Gama yadda Yunusa ya yi kwana uku da dare uku a cikin babban kifi, haka ma Dan Mutum zaya yi kwana uku da dare uku a cikin zuciyar kasa. 41 Mutanen Nineba za su tsaya a ranar shari'a da wannan zamani sannan su kashe su. Domin sun tuba da suka ji wa'azin Yunusa, amma duba wanda ya fi Yunusa yana nan. 42 Sarauniyar Kudu za ta tashi da mutanen wannan zamani ta kuma kashe su. Ta zo daga karshen duniya domin ta ji hikimar Sulaimanu, kuma duba, wanda ya fi Sulaimanu yana nan. 43 Idan kazamin ruhu ya rabu da mutum, ya kan wuce ya nemi wuraren da ruwa yake domin ya huta, amma bai samu ba. 44 Sai ya ce, 'zan koma gidana inda na fito'. Bayan ya dawo, sai ya tarar da gidan nan an share shi ya zama da tsabta. 45 Sai ya koma ya kawo wadansu ruhohi guda bakwai, wadanda su ka fi shi mugunta, sa'annan dukan su su zo su zauna a nan. Sa'annan yanayin mutumin nan na karshe ya fi na farko muni. Haka zaya kasance ga wannan mugun zamani. 46 Sa'adda Yesu ya ke yi wa Jama'a jawabi, sai mahaifiyarsa da 'yan'uwansa su ka zo su ka tsaya a waje, suna neman su yi magana da shi. 47 Sai wani ya ce masa, "Duba, mahaifiyarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai". 48 Amma Yesu ya amsa ya ce wa shi wanda ya gaya masa, "Wacece mahaifiyata? Kuma su wanene 'yan'uwana?" 49 Sai ya mika hannu ya nuna almajiransa ya ce, "Duba, ga mahaifiyata da 'yan'uwana! 50 Gama duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda ya ke cikin sama, shine dan'uwana, da 'yar'uwata da mahaifiyata."
Wannan farkon sashin labarin inda Matiyu ya bayana gãbã mutane domin aikin Yesu. Anan, Farisawa suna zargin almajiransa don suna tsine kwayar hatsi a ranar Asabar.
Wannan alama ce na sabuwar bangaren labarin. AT: "jim kaɗan"
wurin shukin hatsi. In ba a san alkama ba kuma kowa ya san "hatsi" to za ku iya amfani da "gonar tsire tsire da suke amfani da shi su yi gurasa"
Zagar hatsi a gonar wasu a ci ba a dubansa a matsayin sata. Tambayar ita ce ko mutum zai iya yin wannan abin da doka ta haramta a ranar Asabar.
"zagar wasu alkama suna ci" ko "zagar wasu hatsin suna ci"
Wannan na nufin saman alkama. Ta na rike hatsi da sun nuna ko iri.
Wannan ba ta nufin cewa dukkan Farisawan. AT: "wasu Farisiyawa"
Farisawan sun yi amfani da wannan kalman don su jawo hankalin mutane zuwa ga abin da almajiran suke yi.
Yesu ya amsa zargin da Farisiyawan.
"ga Farisawan"
Yesu ya yi amfani da tambaya don ya amsa zargin Farisawan. Yesu us kalubalance su su yi tunani game da ma'anar nassosin da suka karanta. AT: "Na san cewa kin karanta game da ... tare da shi"
ba bu haikali a zamanin sarki Dauda. AT: "alfarwa" ko "wurin yi wa Allah sujada"
Wannan gurasa ce mai tsarki da Firist ke ajiyewa a gaban Allah cikin alfarwa. AT: "gurasar da Firist ya ajiye a gaban Allah" ko "gurasa mai tsarki"
"mazan da ke tare da Dauda"
"amma, bisa ga doka, Firist zai iya ci"
Yesu ya yi amfani da tambaya don ya amsa zarginsa da Farisawa ke yi. Yesu ya kalubalance su, su yi tunani game da ma'anar abin da suka karanta a nassosin. AT: "Na tabbata kun karanta a cikin shariyar Musa cewa ... amma ba su da." ko "yakamata kun san cewa shariya ta koyar ... amma ba ku amince da laifinku."
"yi abin da za su iya yi a kowace ranar, a ranar Asabar"
"Allah ba zai hukunta su ba" ko "Allah ba ya duban su a matsayin masu laifi"
Wannan ya kara nanata abin da Yesu ya faɗa a gaba.
"wani wanda ya fi haikali muhimmanci." Yesu na nufin cewa shine wanda ya fi girma.
Yesu ya ɗauka daga nassi. AT: "Annabi Yusha'u ya rubuta wannan a dă: 'jinkai nake biɗa ba hadaya ba.' Da a ce kun fahimci ma'anar wannan, da baku shara'anta marasa laifi ba"
A cikin shariyar Musa, Allah ya umurci Isra'ilawa su mika hadaya. Wannan na nufin cewa Allah ya fi duban jinkai a matsayin mafi muhimmancin fiye da hadayu.
Kalman "nake" na nufin Allah.
AT: "waɗanda ba su da laifi"
Yesu na nufin kansa ne.
"mai mulkin Asabaci" ko "sa dokoki game da abin da mutane za su iya yi a ranar Asabar"
"Yesu ya bar gonar hatsin" ko "Sai yesu ya tafi"
Ma'ana mai yiwuwa 1) kalman nan "su" na nufin Yahudawan wannan gari. AT: "majami'an" ko 2) kalman nan "su" na nufin Farisawan da Yesu ya yi magana da su da sauran Yahudawan da suka zo garin. Kalman nan "su" baya nufin cewa majami'an na Farisawa ne. AT: "majami'an da suka shiga"
Kalman "sai ga" jawo hankalin mu zuwa ga sabon mutum a cikin labarin. Mai yiwuwa harshen ku na da wata hanyan yin wannan.
"mutum wanda hannunsa a gurgunce"
"Farisawan suna so su zargi Yesu a kan zunubi, sai suka tambaye shi, "ya kyautu a yi warkarwa a ranar Asabar?"
"Bisa ga shariyar Musa, a iya warkar da wani a ranar Asabar"
Ba wai kawai suna so su zarge Yesu a gaban mutane ba. Farisawan suna so Yesu ya ba su amsar da bai yi daidai da shariyar Musa ba don su kai shi gaban alkali nan kuma su dora masa laifin karye doka.
Yesu ya yi amfani da tambaya don ya bada amsa ga Farisawan. Ya kalubalance su su yi tunani game da irin aiki da suke yi a ranar Asabar. AT: "Kowannen ku, In a ce kuna da tunkiya ɗaya ... zai kama tinkiyan ya fitar da ita."
Maganan nan "yaya za a" na kara nanata maganan ne. AT: "Lallai hakika, mutum ya fi tunkiya daraja!" ko "Yi tunani game da muhimmancin mutum fiye da tunkiya"
"waɗanda suka yi ayuka nagari suna biyayya da dokar ranar Asabar"
AT: "Sai Yesu ya umurce mutumin ya mika hannunsa"
"mutumin da ke da shanyayyen hannu"
"Rike hannunka"
"Mutumin ya mika"
AT: "ya warke" ko "ya zama lafiyayye kuma"
"shiri su yi wa Yesu lahani"
"na tattauna yadda za su yi su kashe Yesu"
"Yesu na sane da abin da Farisiyawan na shirin yi , sai ya"
"bar wurin" ko "bar"
"kada ya gaya wa wani game da shi"
Maganan nan "domin ya zama gaskiyar" ana iya juya shi a farkon jimlar. AT: "kada ya sa wasu su san shi. wannan don a cika abin da"
AT: "Abin da Allah ya faɗa tun dă ta wurin annabi Ishaya"
"Duba" ko kassa kunne" ko "kassa kunne ga abin da zan faɗa maku"
Duk aukuwar wannan kalman na nufin Allah. Ishaya faɗi abin da Allah ya gaya masa.
"shi ƙaunatacce na ne, kuma ina farinciki da shi"
A nan "rai" na nufin mutum gabaɗayansa. AT: wanda nake farinciki da shi"
Hanyar da bawan Allah zai faɗa wa al'ummai cewa akwai hukunci. Ana iya bayana a fili cewa Allah shine wanda zai kawo hukunci, ana iya bayana "hukunci" a matsayin "abin da ke daidai." AT: "zai shaida wa al'ummai cewa Allah zai yi masu abin da ke daidai"
A nan rashin jin muryar na wakilcin rashin magana da karfi. AT: "ba zai yi magana da karfi ba"
Duk aukuwar waɗannnan kalmomin na nufin zaɓaɓɓen bawan Allah.
Wannan na nufin "a fili." AT: "a birane da garuruwa"
Duk magana biyu nan na nufin abu ɗaya. Suna kuma nanata cewa bawan Allah zai zama mai saukin kai da alheri. "karya kara da ya tanƙwashe" da "kusa mutuwa" na nufin mutane marasa karfin da an yi masu rauni. idan wannan na rikitar da ku, za ku iya juya zahirin ma'anan. AT: "zai yi kirki ga mutane marasa karfi, zai kuma zama mai saukin kai ga waɗanda aka yi wa rauni"
"tsiren da ya lalace"
"ba zai hana wata wuta ci ba"
Wannan na nufin fitilar da ta mutu an bar hayakin ne kaɗai.
Ana iya juya wanna cikin sabuwar jimla: "... Wannan shine abin da zai yi har"
Kai wani ga nasara na nufin a sa shi ya yi nasara. Sa hukunci ta yi nasara na nufin daidai abubuwa da sun lalace. AT: "ya na daidai kowane abu"
A nan "suna" na nufin mutum gabakiɗaya. AT: "cikin sa"
AT: "Sai wani ya kawo wa Yesu wani mutum wanda makaho ne kuma kurma ne domin aljannu na shugabncinsa"
"wani wanda baya gani bai iya magana ba kuma"
Dukkan mutanen da suka gan lokacin da Yesu ya warkar da mutumin sun yi mamaki ƙwarai da gaske"
Wannan lakabi ne na Almasihu ko Mai Ceto.
A nan na nufin "daga zuriyan"
Wannan na nufin al'ajibin na warkar da makaho, kurma, da mutum mai ajan.
AT: "Wannan mutum ya iya fid a ajan saboda shi bawan Ba'alzabul"
Farisiyawan sun ƙi kiran Yesu da sunansa don su nuna cewa sun ƙi.
"shugaban aljannu"
Yesu ya yi amfani da karin magana don ya amsa wa Farisiyawan. Maganganun nan biyu na nufin abu ɗaya ne. Sun nanata cewa zai zama da ma'ana ba Ba'alzabul ya yi amfani da ikonsa ya yi yaki da ajannu.
A nan "mulki" na nufin waɗanda ke zaman a mulkin. AT: "mulkin ba zai jima ba in har mutanen na yaki tsakaninsu"
A nan "birni" na nufin mutane dake zama a wurin, "gida" kuma na nufin iyali. "rabu" na nufin mutanen na fada da juna. AT: "yana rushe birni ko iyali in mutanen na fada da juna"
Yin amfani da Shaiɗan na biyun na nufin ajannu da ke bautawa Shaiɗan. AT: "Idan Shaiɗan ya găba da aljannunsa"
Duka biyun suna nufin mutum ɗaya.
Yesu ya yi amfani da tambaya don ya nuna wa Farisawan cewa abin da suke faɗi ba shi da ma'ana. AT: "Idan Shaiɗan ya rabu găba da kansa, mulkinsa ba zai tsaya ba!" ko "Idan Shaiɗan na yaki da aljannunsa, mulkinsa ba zai jima ba!"
Yesu ya yi amfani da wani tambaya don ya kalubalanci Farisawa. AT: "to sai ku ce masu bin ma na fitar da ajannu ta wurin ikon Ba'alzabul. Amma kun san cewa wannan ba gaskiya ba ne."
Yesu yana magana da Farisawan. Kalmomin nan "'ya'yan ku" na nufin masubinsu. Wannan wata hanya ce da aka saba amfani da ita sa'ad da ake nufin masubin malamai ko kuwa shugabanne. AT: "masubin ku"
"domin masubin ku na fitar da aljannu ta wurin ikon Allah, sun nuna cewa ba ku yi daidai game da ni ba."
A nan "idan" ba ta nufin cewa Yesu na shakkan yadda yake cire Aljannu. Anan Yesu ya yi amfani da kalman nan don ya gabatar da gaskiyar maganarsa. AT: "Amma domin ina"
"hakika mulkin Allah ya zo tsakanin ku." Anan "mulkin" na nufin mulkin Allah a matsayin sarki. AT: "wannan na nufin Allah ya kafa mulkinsa a tsakanin ku"
A nan "ku" na nufin mutanen Isra'ila
Yesu ya yi amfani da misali don ya cigaba da ba wa Farisawan amsa. Yesu na nufin cewa zai iya cire ajannu saboda ya fi Shaɗan Iko.
Yesu ya yi amfani da tambaya don ya koya wa Farisawan da kuma taron. AT: "Babu wanda zai iya shiga ... ba tare da ya fara ɗaure mutum mai karfin ba" ko "In wani yana so ya shiga ... dole ne ya fara ɗaure mutumin nan mai karfi."
"ba tare da ya fara mulkin mutum mai ƙarfin ba"
"Sa'annan zai yi sata" ko "to zai iya sata"
"wanda ba ya goyon baya na" ko "wanda ba ya aiki tare da ni"
"na hamayya da ni" ko "aiki găba da ni"
Yesu ya yi amfani da karin magana da ke nufin mutane na tattara garkin tumaki zuwa ga makiyayi ko kuwa suna sa su su yi nesa da makiyayin. Yesu yana nufin cewa mutum na koƙarin sa mutane su zama almajiran Yesu ko yana sa mutane su ƙi Yesu.
Yesu na magana ne da Farisiyawa, yana kuma koyawa taron.
AT: "Allah zai gafarta kowane zunubi da mutane suka yi da kowane mugun abu da sun faɗa" ko "Allah zai gafarta wa kowane mutum da ya yi zunubi ko faɗa mugun abubuwa"
AT: "Allah ba zai yafe wa mutumin da ya faɗi mugun abubuwa game da Ruhu Mai Tsarki ba"
Anan "kalma" na nufin abin da mutum ya faɗa. AT: "In wani mutum ya faɗi wani mugun abu game da Ɗan Mutum"
Yesu yana magana ne game da kansa.
AT: "Allah zai gafarta wa mutumin wannan"
AT: "Allah ba zai gafarta wa mutumin nan ba"
A nan "wannan duniya" da "wanda ke zuwa" na nufin rayuwa ta yanzu da nan gaba. AT: "a wannan rayuwa ko kuwa rayuwa a nan gaba" ko "yanzu ko har abada"
Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) "in kun sa itace ta yi kyau, to 'ya'yan ta ma sai ta yi kyau, un kuma kun sa itace ta zama mara kyau to 'ya'yanta ma sai ta zama mara kyau" ko 2) "in kun dubi itace a matsayin mai kyau, yana yiwuwa saboda 'ya'yan ta masu kyau ne, in kuwa kun dubi itace a matsayin mara kyau, to mai yiwuwa saboda 'ya'yan ta mara kyau ne." Wannan karin magana ne. Mutanen da za su yi amfani da gaskiyar ta don sani yadda za su san ko mutum nagari ne ko mugu.
"lafiyayye ... mai cuta"
"'ya'ya" anan na nufin ayyukan mutum. AT: "mutane suna sanin ko itace mai kyau ne ko mara kyau ta wurin duban 'ya'yan ta" ko "mutane sun san ko mutum nagari ne ko mugu ta wurin duban sakamakon ayyukan wannan mutum"
Anan "'ya'yan" na nufin " samu halayyan." Macizai anan na nufin macizai masu dafi kuma mugaye, macizai kuma na wakilkcin mugu. Dubi yadda kuka juya magana makamanci haka cikin [Matiyu 3:7]
Wannan na nufin Farisiyawa.
Yesu ya yi amfani da tambaya don ya sauta wa Farisiyawan. AT: "ba za ku iya faɗi abubuwa nagari ba." ko "kun iya faɗi miyagun abubuwa ne kawai."
A nan "zuciya" na nufin tunanin zuciyar mutum. Anan "baki" na nufin mutum gabakiɗayansa. AT: "abin da mutum ya faɗa da bakinsa na bayyana abin da ke zuciyarsa"
Yesu yana magana game da "zuciya" kamar wata bokiti ne da mutum ya cika ta da abubuwa masu kyau ko mummuna. Wannan magana ce da ke nufin abin da mutum ya faɗa na bayyana yadda mutumin yake. In kuna so ku iya amfani da wannan siffar, to ku dubi UDB. Kuna kuma iya juya zahirin ma'anan wannan. AT: "Mutum dake nagari zai yi maganan abubuwa masu kyau, mugun mutum kuwa zai yi maganan miyagun abubuwa"
"Allah zai tambaye mutane game da" ko "Lalle ne mutane su bayana wa Allah"
A nan "kalma" na nufin abin da wani ya faɗa. AT: "kowane abin cutaswa da suka faɗa"
AT: "Allah zai kuɓutar da ku ... Allah zai hukunta ka"
"muna buƙata"
Za ku iya bayyana a fili dalilin da ya sa suna so su ga alama. AT: "mu ga alama daga gare da ta tabbatar cewa abin da ka faɗa gaskiya ne"
Yesu na magana da mutanen zamaninsa. AT: "Ku muguwar zamani da mazinaciyar tsara wanda ke neman alama a gare ni ... za a ba ku"
A nan "mazinaciyar" na nufin mutanen da ba su da aminci a gaban Allah. AT: "tsara marasa aminci" ko "tsara marasa bin Allah"
Yesu ba zai nuna masu wata alama ba domin kodashike ya riga ya yi mu'ujiza masu yawa duk da haka sun ƙi su gaskanta da shi. AT: "ba zan ba ta wata alama ba" ko "Allah ba zai ba ku wata alama ba"
"sai dai irin alama da Allah ya ba wa annabi Yunusa"
A nan "kwana" da "dare" na nufin sa'a 24. AT: "kwanaki uku"
"'yan kasar Nineba"
"sa'ad da Allah zai shara'anta mutane"
Wannan na nufin mutane da ke rayuwa a lokacin da Yesu na wa'azi.
Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) "kayas" anan na nufin zargi. AT: " za si kuma zargi wannan tsara" ko 2) Allah zai kayas da wannan tsara domin ba su tuba kamar yadda mutanen Nineba suka tuba ba. AT: "Allah kuma zai kayas da wannan tsara"
"duba." Wannan na nanata abin da Yesu ya faɗa a nan gaba.
"wani wanda ya fi muhimmanci"
Yesu na magana game da kansa.
Za ku iya bayana a fili abun da Yesu ke nufi a maganarsa. AT: "fiye da Yunusa na nan, duk da haka ba ku tuba ba, wannan ita ce dalilin da Allah zai kayar da ku"
Wannan na nufin Sarauniya Sheba. Sheba wata kasa ce a kudunci Isra'ila.
za ta tsaya a ranar shari'a"
Wannan na nufin mutanen da ke rayuwa a lokacin da Yesu ke wa'azi.
Dubi yadda ka juya magana makamancin haka cikin [Matiyu 12:41]. Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) "kayas" anan na nufin zargi. AT: " za si kuma zargi wannan tsara" ko 2) Allah zai kayas da wannan tsara domin ba su kassa kunne ga hikima kamar yadda Sarauniyar Kudu t ayi ba. AT: "Allah kuma zai kayas da wannan tsara"
A nan "karshen duniya" na nufin "nesa". AT: "Ta zo daga wuri mai nisa"
Wannan magana ta bayana dalilin da Sarauniyar Kudu ta kayas da mutane a zamanin Yesu. AT: "Gama ta zo"
Za ku iya bayana abin da maganar Yesu ke nufin a fili. AT: " fi Sulemanu yana nan, duk da haka ba ku kassa kunne ba. Shi ya sa Allah zai kayas da ku"
Yesu ya bada wannan misalin don ya yi wa mutane kashedi game da hasarin rashin bada gaskiya a gare shi.
"wuraren da sun bushe" ko "wuraren da mutane ba sa zama"
A nan "ba" na nufin hutu.
AT: "Don haka, baƙin aljan ya shirya ya koma gidan da ya fito"
Wannan wata karin magana ne na mutumin da baƙin aljan ke rayuwa a dă. AT: "wurin da na bari"
AT: "baƙin aljan ya tarar wani ya share gidan ya kuma addana ta"
A nan kuma "gida" na nufin mutum wanda baƙin aljan ke rayuwa a dă. Anan "share shi ya zama da tsabta" na nufin cewa ba wani wanda ke rayuwa a ciki. Yesu yana nufin cewa a sa'ad da baƙin aljan ya bar mutum, lalle ne mutumin ya gayaci Ruhu Mai Tsarki ya yi rayuwa cikin sa ko kuwa aljanun ya dawo.
Wannan na nufin cewa idan mutanen zamani Yesu ba su bada gaskiya a gare shi su kuma zama almajiransa ba, za su samu kansu a mummunan yanayi fiye da yanayin su na dă kafin ya zo.
Maryamu ce, Uwar Yesu a jiki.
Waɗannan mai yiwuwa wasu 'ya'ya ne da Maryamu ta haifa, amma yana iya yiwuwa wannan kalma "'yan'uwa" anan na nufin ɗan'uwa Yesu.
"so su yi magana"
AT: "Wani ya gaya wa Yesu cewa uwa tasa da 'yan'uwansa na waje kuma suna so su yi magana da shi"
Bayanin saƙon da mutumin ya gaya wa Yesu an fahimice ta filla-filla ba a kuwa maimiata ta anan ba. AT: "wanda ya gaya wa Yesu cewa uwa tasa da 'yan'uwansa sun so su yi magana da shi"
Yesu ya yi amfani da waɗannan tambayoyin don ya koyar mutanen. AT: "Zan gaya maku waɗanda suke uwa ta da 'yan'uwan na"
Wannan na nufin almajiran Yesu iyalin Yesu ne a ruhaniya. Wannan ya fi muhimmanci fiye da zama cikin iyalinsa a jiki.
...
Wannan lakabi ne ma muhimmancin na Allah.
Wannan na nufin cewa duk waɗanda ke biyayya ga Allah su 'yan iyali Yesu ne a ruhaniya. Wannan ya fi muhimmanci fiye da zama cikin iyalinsa a jiki.
Farisawan sun kai ƙarar cewa almajiran Yesu suna tsara hatsi suna ci, wanda sun amince cewa ba daidai ba ne a yi a ranar Asabar.
Yesu ya faɗa cewa shi ya fi haikalin.
Ɗan Mutum, Yesu, shi ne Ubangijin Asabar.
Farisawan sun tambaye Yesu, "Doka ta halarta a yi warkarwa a ranar Asabaci?"
Yesu ya ce daidai ne a yi alheri a ranar Asabar.
Farisawa su ka fita waje su ka fara mugun shiri akan shi, su na neman hanyar da za su hallaka shi.
Al'ummai za su ji hukuncin Allah kuma za su amince da Yesu.
Yesu ba zai ƙoƙarta, tada murya, karya kara da ya tankwashe, ko kashe fitilar da ta kusa mutuwa ba.
Yesu ya ce idan Shaidan ya fitar da Shaidan, to ya ya mulkin Shaidan zai tsaya?
Yesu ya ce mulkin Allah ya sauko masu idan ya fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah.
Yesu ya faɗa cewa ba za a gafarta saɓo wa Ruhu Mai Tsarki ba.
A na sanin itace ta 'ya'yansa.
Yesu ya ce za a 'yantar da Farisawan a kuma hukunta su ta wurin maganganunsu.
Yesu ya ce zai ba wa zamaninsa alamar Yunusa, da kasancewa kwana uku da dare uku a cikin zuciyar ƙasa.
Yesu ya faɗa cewa ya fi Yunusa.
Mutanen Nineba sun hukunta mutanen zamanin Yesu domin sun saurari maganar Allah ta wurin Yunusa, amma zamanin Yesu ba su saurari Ɗan Mutum wanda ya fi Yunusa ba.
Yesu ya faɗa cewa ya fi Sulaimanu.
Zamanin Yesu zai zama kamar mutum da ke da ruhu mai kazanta da ya rabu da shi, domin kazamin ruhun ya dawo da ruhohi guda bakwai sa'annan yanayin mutumin nan a karshe ya fi na farko muni.
Yesu ya ce waɗanda su na yin nufin Uba su ne 'yan'uwansa maza, 'yan'uwansa mata, da kuma mahaifiyarsa.
1 A waccan rana Yesu ya fito daga gida ya zauna a gefen teku. 2 Taro mai yawan gaske kuwa suka kewaye shi, sai ya shiga cikin kwalekwale ya zauna. Dukan taron kuwa na tsaye a bakin tekun. 3 Sai Yesu ya fada masu abubuwa da yawa cikin misalai. Ya ce, "Wani mai shuka, ya tafi yayi shuka. 4 Da yayi shukar, wadansu irin suka fadi a kan hanya, sai tsunsaye suka zo suka cinye su. 5 Wadansu irin kuwa suka fadi a kan duwatsu, wurin da babu kasa. Nan da nan sai suka tsira, domin kasar babu zurfi. 6 Amma da rana ta taso, sai suka yankwane domin ba su yi saiwa ba, suka kuwa bushe suka zube. 7 Wasu irin kuwa suka fada a cikin kayayuwa. Kayayuwan kuwa suka shake su. 8 Wasu irin kuwa suka fada a wuri mai kyau suka ba da tsaba, wani ya ba da dari, wasu sitin, wasu kuma talatin. 9 Duk mai kunnen ji, bari ya ji. 10 Almajiran suka zo suka ce ma Yesu, "Don me ka ke yi wa taron magana da misali?" 11 Yesu ya amsa ya ce masu, "An baku 'yanci ku fahimci asiran mulkin sama, amma gare su ba a bayar ba. 12 Domin wanda yake da shi, za a kara masa, zai kuma samu dayawan gaske. Amma duk wanda ba shi da shi, sai a dauke har ma abin da yake dashi. 13 Saboda haka na yi masu magana cikin misalai, amma ko da ya ke sun gani, duk da haka ba su gani ba. Kuma ko da yake sun ji, hakika ba su ji ba, balle ma su fahimta. 14 A gare su ne annabcin Ishaya ya cika, wanda yake cewa, "Game da sauraro zaku saurara, amma ba za ku fahimta ba. Game da gani kuma za ku kalla, amma ba za ku gane ba. 15 Domin zuciyar mutanen nan ta duhunta, sun taurare ga saurare, kuma sun rufe idanunsu domin kada su gani da idanunsu, ko kuwa su ji da kunnuwansu, ko kuwa su fahimta da zukatansu, saboda su juyo kuma in warkar da su'. 16 Amma idanunku masu albarka ne, domin sun gani, haka ma kunnuwanku, domin sun ji. 17 Hakika ina gaya muku, annabawa da mutane dayawa masu aldalci sun yi marmarin ganin abin da kuka gani, amma ba su sami ganin su ba. Sun yi marmarin jin abin da kuka ji, ba su kuwa ji su ba. 18 Ku saurari misalin nan na mai shuka. 19 Idan wani ya ji maganar mulkin sama amma bai fahimce ta ba, sai mugun nan ya zo ya kwace abinda aka shuka a zuciyarsa. Wannan shine irin da aka shuka a kan hanya. 20 Shi wanda aka shuka akan duwatsu, shine wanda ya ji maganar ya kuma karbe ta da murna nan da nan. 21 Duk da haka, bai yi karfi cikin ta ba kuma nan ba da dadaiwa ba. Da wahala da tsanani suka taso saboda maganar, sai ya yi tuntube nan da nan. 22 Shi wanda aka shuka a cikin kayayuwa wannan shine wanda ya ji maganar, amma dawainiyar duniya da kuma yaudarar dukiya suka shake maganar, sai ya kasa ba da 'ya'ya. 23 Shi wanda aka shuka a kasa mai kyau, wannan shine wanda ya ji maganar, ya kuma fahimce ta. Wannan shine wanda ba da 'ya'ya da gaske; wadansu ribi dari, wadansu sittin, wasu kuma talatin." 24 Yesu ya sake ba su wani misali, yana cewa "Za a kwatanta mulkin sama da wani mutum wanda ya shuka iri mai kyau a gona. 25 Amma da mutane suka yi barci, magabcin sa ya zo ya shuka ciyayi a cikin alkamar, ya kuwa yi tafiyarsa. 26 Sa'adda suka yi toho suka kuma ba da tsaba, sai ciyayin suka bayyana. 27 Bayin mai gonar kuwa suka zo suka ce masa, maigida, ashe ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? ya ya aka yi ta kasance da ciyayi? 28 Ya ce masu, "Magabci ne ya yi wannan". Sai bayin suka ce masa, 'kana so mu je mu tuge su ne?' 29 Mai gonar ya ce, 'A'a, kada a garin tuge ciyayin, ku tuge tare da alkamar. 30 Bari dukan su su girma tare har lokacin girbi, a lokacin girbin zan gaya wa masu girbin, "Ku tuge ciyayin da farko a daura su dami dami sai a kona su, amma a tara alkamar a kai rumbunana.'" 31 Sai Yesu ya sake yin magana da su cikin misalai, yana cewa "Za a kwatanta mulkin sama da kwayar mustad, wanda wani mutum ya shuka a lambunsa. 32 Wannan iri shine mafi kankanta cikin dukan iri. Amma bayan ya yi girma, sai ya fi dukan ganyaye dake lambun. Ya zama itace, har ma tsuntsayen sama su yi sheka a rassansa." 33 Yesu ya sake fada masu wani misali. "Za a kwatanta mulkin sama da yisti da mace takan dauka ta kwaba gari da shi mudu uku har sai ya yi kumburi." 34 Duk wadannan abubuwa Yesu ya fada wa taron cikin misalai. Babu abinda ya fada masu da ba a cikin misali ba. 35 Wannan ya kasance ne domin abinda annabin ya fada ya zama gaskiya, da ya ce, "Zan buda bakina da misali. In fadi abubuwan da ke boye tun daga halittar duniya." 36 Sai Yesu ya bar taron ya shiga cikin gida. Amajiransa suka zo wurin sa suka ce, "Ka fasarta mana misalan nan a kan ciyayin da ke gonar" 37 Yesu ya amsa kuma ya ce, "Shi wanda ya shuka iri mai kyau Dan Mutum ne. 38 Gonar kuwa duniya ce; iri mai kyau kuma sune 'ya'yan mulkin. Ciyayin kuma sune 'ya'yan mugun, 39 magabcin da ya shuka su kuma shaidan ne. Girbin shine karshen duniya, kuma masu girbin sune mala'iku. 40 Saboda haka, kamar yadda aka tara ciyayin aka kona su da wuta, haka ma zai faru a karshen duniya. 41 Dan Mutum zai aiki mala'ikunsa, kuma su tara dukan abubuwan da ke sa zunubi daga cikin mulkinsa, da kuma wadanda su ka yi aikin mugunta. 42 Za su jefa su cikin korama ta wuta, inda za a yi kuka da cizon hakora. 43 Sa'an nan ne mutane masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Bari mai kunnen ji, ya ji. 44 Mulkin sama kamar dukiya ce da ke boye a gona. Mutum ya samu sai ya boye ta, ya tafi cikin murna, ya sayar da mallakarsa kuma ya sayi filin. 45 Haka ma za a kwatanta mulkin sama da wani attajiri mai neman Lu'ulu'ai masu daraja. 46 Da ya sami lu'ulu'u daya mai darajar gaske, ya je ya sayar da dukan mallakarsa ya kuma saye shi. 47 Haka kuma, za a kwatanta mulkin sama da taru da aka jefa cikin teku, ya kuwa tara hallitu iri-iri. 48 Da ya cika, sai masuntan suka jawo shi bakin tekun. Sai suka zauna suka tara kyawawan abubuwan a taska, amma munanan abubuwan, suka watsar da su. 49 Haka zai kasance a karshen duniya. Mala'iku za su zo su ware miyagu daga cikin masu adalci. 50 Za su jefa su cikin korama ta wuta, inda za a yi kuka da cizon hakora. 51 Kun fahimci dukan wadannan abubuwa? Amajiran suka ce da shi, "I". 52 Sai Yesu ya ce masu, "Saboda haka kowane malamin attaura da ya zama almajirin mulkin sama, yana kamar mutum mai gida wanda ya zaro tsoho da sobon abu daga taskarsa." 53 Daga nan, sa'adda Yesu ya kammala ba da wadanan misalai, sai ya tafi ya bar wurin. 54 Sai Yesu ya shiga yankinsa ya koyar da mutane a masujadarsu. Saboda haka suka yi mamaki suna cewa, "Daga ina wannan mutumin ya sami hikimarsa da al'ajibai? 55 Wannan mutumin ba dan masassakin nan ba ne? Ba kuma sunan mahaifiyarsa Maryamu ba? Ba Kuma 'yan'uwansa sune, Yakubu da Yusufu da Saminu da kuma Yahuza ba? 56 Ba 'yan'uwansa mata na tare da mu ba? To daga ina wannan mutumin ya sami dukan wadannnan abubuwa? 57 Suka bata rai saboda shi. Amma Yesu ya ce masu, "Ai annabi bai rasa daraja sai dai ko a garinsa da kuma cikin iyalinsa. 58 Kuma bai yi al'ajibai dayawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.
Wannan farko ne a bangaren labarin wanda Yesu ya fara koya wa taron ta wurin amfani da misali game da mulkin sama.
Waɗannan sun faru ne a rana ɗaya da waɗanda ke a sura da ke a baya.
Ba a faɗa ko a gidan wa Yesu ke zama ba.
Na nufin cewa ya zauna don ya koyar da mutanen.
Na nufin cewa Yesu ya shiga cikin kwalekwale domin zai zama da sauki ya koyar mutanen.
Wannan mai yiwuwa wani kwalkwale da ke a bude, na itace kuma wanda ake kaman kifi.
Yesu ya bayana mulkin sama ta wurin ba da misali game da wani mutum da ke sukin iri.
...
"wa mutanen cikin taron"
"Kassa kunne." Wannan kalma na jan hankali zuwa ga abin da za a faɗa nan gaba. AT: "Kassa kunne ga abin da zan faɗa maku"
"manumi ya tafi gona don ya yafa iri"
"a yayinda manumin na cikin yafa iri"
Wabbab ba nufin "hanya" da ke gefen gonar. kasar ta yi tauri domin mutane suna tafiya a kai.
"cinye dukka irin"
Wannan wuri ne cike da duwatsu. kasa kuwa kaɗan ne a saman duwatsun.
"Irin nan da nan suka tsira suka yi girma"
AT: "rana ta sa shukin sun yankwane, sun yi zafin kuma"
"shukin ta bushe ta kuma mutu"
"faɗa cikin wurin da ƙaya ke girma"
"shaƙe sabbin da suka toho." Yi amfani da kalman da ke nuna yadda ciyayi ke hana tsire-tsire girma da kyau.
"bada iri da yawa" ko "bada 'ya'ya"
kalmomin nan "iri" "amfani" da "amfanin gona" an fahimce su ne daga magana da ke a baya. Ana iya bayana wannan a fili. AT: "wasu irin sun ba da amfani dari dari bisa ga yawan amfanin gona, wasu irin sun bada amfani sittin sittin bisa ga amfanin gona, wasu irin kuma sun bada talatin talin bisa ga yawan amfani"
"100 ... 60 ... 30"
Wannan wata hanya ce da ake nufin kowa da ke a wurin wanda ke jin abin da Yesu ke faɗa. Dubi yadda ka juya wannan cikin [Matiyu 11: 15] AT: "Duk wanda zai iya ji na"
A nan "kassa kunne" na nufin sa hankalin ga abin da ake faɗa. Dubi yadda ka juya wannan cikin [Matiyu 11: 15]. AT: "sa hankalin ga abin da nake faɗa"
Ana iya bayana abin nufin a fili. AT: "Allah ya ba ku 'yancin fahimtar asiran mulkin sama, amma Allah bai ba wa waɗannan mutane ba" ko "Allah ya sa ku ku iya fahimtar asiran mulkin sama, amma ba sa waɗannan mutane su fahimta ba"
Kalman nan "ku" na nufin almajiran.
A nan "mulkin sama" na nufin mulkin Allah. "mulkin sama" ta auku a littafin Matiyu ne kaɗai. In mai yiwuwa ne, ku yi iyakacin koƙarin ku ku juya shi yadda ta ke. AT: "asirai game da Allahnmu a cikin sama da mulkin sa"
"duk wand ke da fahimta" ko "duk wanda ya karɓi abin da na koyar"
AT: "Allah zai kara masa fahimta"
"duk wanda ba shi da fahimta" ko "duk wanda bai karɓi abin da na koyar ba"
AT: "Allah zai karɓi abin da yake da shi"
Duk aukuwar "su" na nufin mutanen taron.
Yesu ya nanata wa almajiransa cewa taron sun ƙi su fahimci gaskiyar Allah.
Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) wannan na nufin sun ga abin da Yesu ya yi. AT: "ko da ya ke sun ga abin da na yi" ko 2) wannan na nufin sun iya gani. AT: "ko da ya ke sun iya ganin"
A nan "gani" na nufin fahimta. AT: "ba su fahimta ba"
Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) wannan na nufin cewa suna ji abin da Yesu ya koyar. AT: "Ko da ya ke sun ji abin da na faɗa" ko 2) wannan na nufin sun iya ji. AT: "ko da ya ke sun iya jin"
A nan "ji" na nufin kassa kunne da kyau. AT: "ba su kassa kunne da kyau ba" ko "ba su ba da hankalin su ba"
AT: "Suna cika abin da Allah ya faɗa tun dă ta wurin annabi Ishaya"
Wannan annabci ne daga annabi Ishaya da aka ambato game da rashin bada gaskiya na mutanen zamaninsa. Yesu ya yi amfani da wannan don ya bayana yadda taron da ke kassa kunne a gare shi suke. Wannan magana na nanata cewa mutanen sun ƙi sun fahimci gaskiyar Allah.
"Za ku ji abubuwa, amma ba za ku fahimce su ba." Za ka iya bayana a fili abin da mutanen za su ji. AT: "Za ku ji abin da Allah ya ce ta wurin annabawa amma ba za ku fahimci gaskiyar ma'anan ta ba"
Za ka iya bayana a fili abin da mutanen za su gani. AT: "za ku ga abin da Allah ya yi ta wurin annabawan, amma ba za ku fahimta ba"
Cikin 13:15 Allah ya kamanta mutane Isra'ila kamar suna da wata cuta ne cikin jiki da ke sa su su kăsa iya koya, gani, da ji. Allah yana so su zo gare shi don ya warkar da su. Wannan na bayana yanayi na ruhaniyan mutanen. Ta na nufin mutanen sun taurare sun kuma ƙi su sami fahimta daga gaskiyar Allah. In za su karɓi gaskiyar, to za su tuba, Allah kuma zai yafe masu, zai kuma marabce su a matsayin mutanensa. Idan ma'anan na a fili, to a yi amfani da karin magana cikin juyin ku.
Anan "zuciya" na nufin tunani. AT: "tunani waɗannan mutanen ba ta saurin koyo"
Su ba kurma ba ne a jiki. Anan "wuyan ji" na nufin sun ƙi su kassa kunne su koya gaskiyar Allah. AT: "sun ƙi su yi amfani da kunnuwan su su kassa kunne" (Dubi:
Ba su rufe idanun a zahiri ba. Wannan na nufin cewa su ƙi su fahimta. AT: " sun ƙi su yi amfani da idanun su don su gani"
"domin kada su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, ko kuwa su fahimta da zuciyarsu, kuma saboda haka su juyo kuma"
A nan "zukata" na nufin tunanin mutanen. AT: "fahimta daga tunanin su"
"juyo wurina" ko "tuba"
"in warkar da su." Wannan na nufin Allah zai warkar da su a cikin ruhaniya ta wurin yafe masu zunubansu ya kuma karɓe su a matsayin mutanen. AT: "in warkar da su kuma"
Maganganun na biyu na nufin abu ɗaya. Yesu ya nanata cewa sun faranta wa Allah rai domin sun bada gasikiya ga abin da Yesu ya faɗa da aikata.
A nan "idanu" na nufin mutum gabaɗayansa. AT: "Ku masu albarka ne domin idanun ku sun iya ganin"
Duk aukuwar wannan kalma na nufin almajiran ne.
A nan "kunnuwa" na nufin mutum gabaɗayansa. Za ka iya sa a fili zancen da aka fahimta anan. AT: "ku masu albarka ne domin kunnuwanku sun iya ji"
"Gaskiya ina gaya maku." Wannan na kara nanata abin da Yesu ya faɗa a nan gaba.
Kuna iya bayana abin da suka gani a fili. AT: "abubuwan da kun ga na yi"
Kuna iya bayana abin da suka ji a fili. AT: "abubuwan da ku ka ji na faɗa"
"sakon game da mulkin Allah a matsayin sarki"
Yesu ya yi magana game da Shaiɗan ya sa mutum ya manta abin da ya ji sai ka ce Shaiɗan tsuntsune da ke tsine iri daga ƙasa. AT: "Mugun ya sa shi ya manta da sakon da ya ji daidai kamar yadda tsuntsun ke tsine iri daga ƙasa"
Wanna na nufin Shaiɗan.
A yi ƙoƙari a yi amfani da kalman da ke nufin kwace wani abu daga wurin wani mai shi.
AT: "sakon da Allah ya shuka a zuciyarsa" ko "sakon da ya ji"
A nan "zuciya" na nufin tunanin mai sauraro.
"Wannan shine abin da irin da ya fadi a gegen hanya yake nufi" ko "Hanyar da an shuka irin na a maɗaɗɗin mutumin"
Maganan nan "abin da aka shuka" na nufin iri da ya făɗi. AT: "Irin da ya făɗi a duwastsu"
"Duwatsun da aka yi shuki na wakilcin" ko "Duwatsun da irin ya făɗi na wakilcin"
A misalin, irin na nufin maganar.
Wannan na nufin sakon Allah. AT: "sakon" ko "Koyaswar Allah"
An yi maganar gaskantawa da maganar kamar karɓan ta. AT: "gaskanta da farin ciki"
duk da haka jijiyoyin sa ba su yi nisa ba kuma suna jimawa na dan lokacin kaɗan ne. "Jijiya na nufin abin da ke sa mutum ya cigaba da bada gsakiya ga sakon Allah. AT: "Amma kamar shukin da jijiyoyin sa ba su yi nisa ba, yana jimawa na dan lokacin kaɗan ne"
A nan "tuntunɓe" na nufin ƙi gaskantawa. AT: "nan da nan ya faɗi" ko "nan da nan sai ya ƙi bada gaskiya ga sakon"
Wannan na nufin irin da an shuka ko kuwa ta faɗi. AT: "Irin da aka shuka" ko "Irin da ta faɗi"
"filin da akwai ƙaya, inda aka shuka irin"
"wannan na wakilcin mutumin"
Yesu yana magana game da dawainiyar duniya da jarabar dukiya a
"abubuwa da mutanen wannan duniya ke damuwa game da su"
Yesu ya yi bayani akan "dukiya" kamar dukiya mutum ne wanda zai iya yauɗarar wani. Wannan na nufin cewa mutane suna tunanin cewa samun kudi za ta sa su farin ciki, amma ba za ta sa su farin ciki ba. AT: "ƙaunar kuɗi"
An yi maganar mutmin kamar shi shuki. Rashin bada 'ya'ya na nufin rashin yin amfani. AT: "zama mara bada amfani" ko " ba ya yin abin da Allah yake so"
"Ƙasa mai kyau da aka shuka irin"
An yi maganar mutumin sai ka ce shuki. AT: "Kamar shuki da bata da cuta da ke bada amfanin gona, yana bada 'ya'ya"
Mangana nan "fiya da wanda aka shuka" an fahimce ta bisa ga waɗannan lambobin. Dubi yadda ka juya wannan cikin [Matiyu 13:8] AT: "Wasu mutane sun bada amfani fiye da abin da aka shuka sau 100 wasu sau 60, wasu kuma sau 30"
Kada a daidaita mulkin sama da mutum, amma sai dai mulkin sama na kamar yanayin da aka bayana a misalin.
A nan "mulkin sama" na nufin mulkin Allah a matsayin sarki. "An yi amfani da "mulkin sama" a Matiyu ne kaɗai. In mai yiwuwa ne, ku yi amfani da "sama" a juyin ku. AT: "Sa'ad da Allahnmu na sama ya bayana kansa a matsayin sarki, zai zama kamar"
"irin abinci mai kyau" ko "irin hatsi mai kyau." Mai yiwuwa masu sauraro suna tunanin cewa Yesu na magana game da alkama.
"magabcin sa ya zo gonar"
Waɗannan ciyayin suna kamar wata shuki ne da za a iya ci, a sa'ad da bai yi girma ba, amma hatsi su guba ce. AT: "iri mara kyau" ko "irin ciyayi"
Sa'ad da irin alkaman ta toho" ko "Sa'ad da shuki ta yi girma"
"bada tsaba" ko "bada tsaban alkama"
Sa'annan mutane za su iya ganin cewa lalle akwai ciyayi a gonar"
Wannan mutum ɖaya ne da wanda ya shuka iri mai kyau a gonarsa.
Barorin sun yi amfani da tambaya don su nanata yadda sun ji mamaki. AT: "ka shuka iri mai kyau a gonar ka!"
Mai yiwuwa mai gonar ya sa barorinsa ne sun shuka irin. AT: "ashe ba mu shuka"
"Mai gonar ya ce wa barorin"
Kalman nan "mu" na nufin barorin.
"Mai gonar ya ce wa barorinsa"
AT: "Zan gaya wa masu girbin su tara ciyayin da farko su ɗaure su dami dami su kona su, sai kuma su tara alkaman a cikin rumbu na"
ginin da ana iya amfani da shi a ajiye hatsi
wata ƙanƙanin iri da ke girma ya zama babbar itace
Ga masu sauraro na farko, iri mustad ita ce mafi ƙanƙanta cikin iri da suka sani.
"Amma bayan shukin ta girma"
"ta yi babba fiye da"
Itacen mustad na iya girma daga mita 2 zuwa 4 a tsayi.
"tsuntsaye"
Mulkin na kamar yisti, amma yaduwar mulkin na kamar yaduwar yisti.
Sai a ce "auwu mai yawa na gari" ko kuwa a yi amfani da kalman da ake amfani da shi a al'adan ku na auna gari mai yawa.
Abin nufin shine yisti da auwu uku na gari an yi kullun shi don a yi burodi.
Jimla biyun na nufin abu ɗaya. An haɗa su don a nanata cewa Yesu ya koyawa taron da misalai ne kaɗai.
Wannan na nufin abin da Yesu ya koyar da farko a [Matiyu 13:1]
"ba gaya masu komai ba sai dai ta wurin misalai." AT: "duk abin da ya koya masu ya faɗa cikin misalai ne"
AT: "Abinda Allah ya gaya wa ɗaya daga cikin annabawan ya rubuta tun dã zai zama gaskiya"
"sa'ad da annabin ya ce"
Wannan na nufin a yi magana. AT: "zan yi magana"
AT: "abubuwan da Allah ya ɓoye"
"tun daga farkon halittar duniya" ko "tun da Allah ya halici duniya"
"shiga cikin gida" ko "shiga cikin gidan da yake zama"
"Wanda ya shika iri mai kyau" ko "Mai shukin iri mai kyau"
Yesu na nufin shi da kansa.
Karin maganan nan "'ya'yan" na nufin waɗanda ke na mulkin ko suna da hali kamar na wani ko wani abu. AT: "mutanen da ke na mulkin"
A nan "mulki" na nufin Allah a matsayin sarki. AT: "na Allah"
Karin maganan nan "'ya'yan" na nufin waɗanda ke na mugun ko suna da hali kamar na wani ko wani abu. AT: "mutanen da ke na mugun"
"mugun wanda ya shuka ciyayi"
AT: "Saboda haka, kamar yadda mutane suna tara ciyayi su kona da wuta"
A nan Yesu na magana game da kansa. AT: "Ni Ɗan Mutum, zan aiko da mala'ikuna"
"waɗanda ba su bin doka" ko "mutane masu mugunta"
Wannan na nufin jahannama. In ba a san "korama" ba, to, ana iya amfani da "wuri mai zafi da ke da murfi " AT: "tafki ta wuta a ruruwa"
"Cizon haƙora" anan alama ce da ke wakilcin matuƙar bakinciki da wahala. Dubi yadda ka juya wannan cikin [Matiyu 8:12]. AT: "kuka suna nuna cewa lallai suna shan matuƙar wahala "
In ba a fahimci wannan a harshen ku ba, kana iya amfani da: "da saukin gani kamar rana."
Wannan lakani mai muhimmanci na Allah.
AT: "dukiya ce da wani ya ɓoye a gona"
abu mai daraja ko kuwa tarin abubuwa.
"rufe shi"
Abin nufin anan shine mutumin ya sayi filin don abin da aka ɓoye ya zama nasa.
Abin nufin shine mutumin da neman lu'ulu'ai masu daraja don ya saya.
mai ciniki ko 'yan sari wanda saya kaya yawanci lokatai dagar wurare masu nisa
"lu'ulu'ai" na da santsi, na da tauri, na walkiya kuma, fari ne ko kuma kamar dutsen ado mai haske wanda ke cikin teku ana kuma sayan shi da tsada kamar wani dutse mai daraja ko kuwa ana maida shi kamar kayan ado masu daraja. AT: "lu'ulu'ai mai tsabta" ko "lu'ulu'ai masu kyau"
Mulkin ba kamar tarun ba ne, amma mulkin na jawo kowane irin mutane kamar yadda taru ke kama kowane irin kifi.
AT: "kamar taru ne da masunta suka jefa a cikin teku"
"an wurga cikin teku"
"kama kowane iri kifi"
"jawo tarun suza bakin tekun" ko "jawo gaɓan teku"
"masu kyau"
"munanan kifin" ko "kifin da ba za a iya ci ba"
"za su fito" ko "za su fita" ko "za su zo daga sama"
AT: "mayagun mutane daga cikin mutane masu adalci"
"mala'iku za su jefa mugayen mutanen"
AT: "Yesu ya tambaya su ya ce in da sun fahimci duk wannan, sai suka ce sun fahimta."
A nan "mulkin sama" na nufin mulkin Allah a matsayin sarki. Maganan nan "mulkin sama" an yi amfani da shine a littafin Matthew ne kaɗai. In ma yiwuwa ne a yi "amfani" da juyinku. AT: "sun koyi gaskiya game da Allah na sama, wanda shine sarki" ko "ya mika kansa don Allah ya yi mulkinsa"
Yesu ya bada wani misali kuma. Ya kwatanta malaman attauran da sun san nassosin da Musa da annabawa sun rubuta kuma wanda sun karɓi koyaswar Yesu da magidanta wanda ya yi amfani da tsoho da kuma sabon taska.
Wannan magan na kai labarin daga koyaswar Yesu zuwa ga abin da ya faru nan gaba. AT: "Sai" ko "Bayan"
"birninsa." Wannan na nufin birnin Nazarat inda Yesu ya yi girma.
Kalman "su" na nufin mutanen yankin.
...
Mutanen sun gaskantan cewa Yesu shi kamar sauran mutane yake. Sun yi amfani da wannan tambayan don su nuna yadda suka ji mamaki cewa yana da hikima har ya iya yin aikin al'ajibi. AT: "Ta yaya mutum kamar wannan zai zama da hikima har ya yi manyan abin al'ajibi?" ko "Bakon abu ne cewa ya iya magana da hikima da kuma aikata abin al'ajibi!"
Taron sun yi amfani da wannan tambayar don su nuna cewa lalle sun san ko wanene Yesu, shi kuwa mutum na kamar mu. AT: "Shi ɗan masassaki ne. Mun san mahaifiyarsa Maryamu, da 'ya'uwansa Yakubu, Yusufu, Saminu da kuma Yahuza. Kuma duk 'yan'uwansa mata na tare da mu"
Masassaki mutum ne wanda ke yin abubuwa da katako ko dutse. In ba a san "masassaki" ba do za a iya amfani da "magina".
Taron sun yi amfani da wannan tambayan don su nuna fahimtarsu cewa lalle Yesu ya samin iyawarsa daga wanin wuri. Mai yiwuwa suna nuna shakkar su cewa ya sami wannan iya daga wurin Allah. AT: "Lalle iyawarsa na yin waɗannan abubuwa ya sami ta daga wani wuri!" ko "Ba mu san inda ya sami waɗannan iyawar ba!"
AT: "Mutanen garin Yesu sun yi fushi da shi" ko "Mutanen sun ƙi Yesu"
AT: "Annabi na samu daraja a ko'ina" ko "Mutane a ko'ina na daraja annabi"
"a yankin sa" ko "a garinsa"
"cikin gidansa"
"Yesu bai yi ala'jibai dayawa a garinsa ba"
Irin da ya faɗi a hanya tsuntsaye sun ci.
Irin da sun faɗi a kasa mai duwatsu sun tsira nan da nan, amma rana ta buga su sai suka zube.
Irin da sun faɗi a cikin kayoyi, kayayuwan kuwa suka shake su.
Irin da suka faɗa a wuri mai kyau suka ba da tsaba, wani ya ba da ɗari, wasu sitin, wasu kuma talatin.
Annabcin Ishaya ya faɗa cewa mutanen za su ji, amma ba za su fahimta ba, za su gani, amma ba za su gane ba.
Mutanen da sun saurari Yesu amma basu fahimta ba su na da zuciya mara tunani, da nauyin ji, sun kuma rufe idannunsu.
Irin da aka shuka a hanya mutum ne da ya ji maganar mulkin sama amma bai fahimce ta ba, sai mugun nan ya zo ya kwace abinda aka shuka a zuciyarsa.
Irin da aka shuka a kasa mai duwatsu mutum ne da ya ji maganar ya kuma karbe ta da murna nan da nan, amma ya yi tuntube nan da nan da wahala da tsanani suka taso.
Irin da aka shuka a cikin kayayuwa mutum ne da ya ji maganar, amma dawainiyar duniya da kuma yaudarar dukiya suka shake maganar, sai ya kasa ba da 'ya'ya.
Irin da aka shuka a kasa mai kyau mutum ne da ya ji maganar ya kuma fahimce ta na kuma ba da 'ya'ya.
Magabci ne ya shuka muguwar ciyayi a gonar.
Mai gonar ya ce wa bayin su bar dukan su su girma tare har lokacin girbi, a tara muguwar ciyayin a kona su, amma alkamar a kai rumbuna.
Kwayar mustad ya zama itace, sai ya fi dukan ganyaye dake lambun domin tsuntsayen sama su yi sheka a rassansa.
Yesu ya fada cewa mulkin sama na nan kamar yisti da aka kwaba gari mudu uku da shi har sai ya yi kumburi.
Mai shuka iri mai kyau shi ne Dan Mutum, gonar kuwa duniya ce, iri mai kyau kuma su ne 'ya'yan mulkin, muguwar ciyayin su ne 'ya'yan magacin, kuma shaidan ne mai shuka muguwar ciyayin.
Masu girbin sune mala'iku, kuma girbin shine karshen duniya.
A ƙarshen duniya, za a jefar da waɗanda suke yin aikin mugunta a korama ta wuta .
A ƙarshen duniya, masu adalci za su haskaka kamar rana.
Mutum da ya samu dukiya mai daraja na sayar da mallakarsa dukka ya sayi filin.
Mutum da ya sami lu'ulu'u ɗaya mai daraja na sayar da mallakarsa dukka ya saye shi.
Kamar yadda an raba abubuwar wofi da masu kyau daga taro, a karshen duniya za a raba mugaye da masu adalci a kuma jefar da su a wuta.
Mutanen sun yi tambaya cewa, "A ina ne wannan mutumin ya sami hikimarsa da waɗannan al'ajibai"?
Yesu ya faɗa cewa annabi ba shi da girma a ƙasarsa
Saboda rashin gaskantawar mutanen, Yesu bai yi abubuwar al'ajibi a yankinsa ba.
1 A lokacin nan ne, Hiridus mai mulki ya ji labarin Yesu. 2 Ya ce wa barorinsa, "Wannan Yahaya mai baftisma ne; ya tashi daga matattu. Saboda haka wadannan ikoki na aiki a cikinsa". 3 Domin Hiridus ya kama Yahaya, ya daure shi, kuma ya jefa shi a kurkuku saboda Hirudiya, matar dan'uwansa Filibus. 4 Ya ce masa, "Bai kamata ka dauke ta a matsayin matarka ba." 5 Da Hirudus ya kashe shi, amma yana tsoron jama'a, domin sun dauke shi a matsayin annabi. 6 Amma da ranar bikin haihuwar Hirudus ta kewayo, diyar Hirudiya tayi rawa a lokacin har ta burge Hirudus. 7 Sai ya yi mata alkawari har da rantsuwa cewa ta roki komenene ta ke so, zai ba ta. 8 Bayan ta amshi umurni daga wurin mahaifiyarta, ta ce, "Ka bani kan Yahaya mai baptisma a kan tire. 9 Sarki ya husata da rokonta, amma domin rantsuwar da ya yi kuma domin mutanen da ke a wurin bukin tare da shi, sai ya umurta a yi haka. 10 Ya aika aka yanke kan Yahaya acikin kurkuku. 11 Sai aka kawo kansa bisa tire, aka mika wa yarinyar, ta kuwa kai wa mahaifiyarta. 12 Sai almajiransa suka zo, su ka dauki gawar su ka je su ka yi jana'iza. Bayan haka, su ka je su ka fada wa Yesu. 13 Sa'adda da Yesu ya ji haka, ya fita daga cikin kwale-kwale zuwa wani kebabben wuri. Da taron suka ji haka, suka bi shi da kafa daga biranen. 14 Sai Yesu ya zo gabansu, ya kuma ga babban taron. Ya tausaya masu ya kuwa warkar da marasa lafiya dake cikinsu. 15 Da maraice ya yi, almajiransa su ka zo su ka ce masa, "Wannan wuri jeji ne, dare kuwa ya riga ya yi. Ka sallami taron domin su je cikin kauyukan nan, su sayo wa kansu abinci." 16 Amma Yesu ya ce masu, "Babu amfanin tafiyar su, ku basu abin da za su ci." 17 Suka ce masa, "Muna da gurasa guda biyar da kifi biyu ne kawai." 18 Yesu ya ce, "Ku kawo mani su." 19 Sai Yesu ya umarci taron su zauna akan ciyawa. Ya dauki gurasa biyar da kifi biyun. Ya dubi sama, ya sa albarka ya gutsuttsura ya kuma ba almajiran. Almajiran suka ba taron. 20 Dukansu suka ci suka koshi. Sai suka dauki gutsattsarin gurasa da kifin, kwanduna goma sha biyu cike. 21 Wadanda su ka ci kuwa kimanin maza dubu biyar ne, ban da mata da yara. 22 Nan take sai ya sa almajiran suka shiga kwale-kwalen su haye zuwa dayan gefen kafin shi, domin ya sallami taron. 23 Bayan ya sallami taron sun tafi, sai ya haura kan dutse domin yayi addu'a. Da dare yayi, yana can shi kadai. 24 Amma yanzu fa kwale-kwalen na tsakiyar tekun, kuma da wuyar sarrafawa saboda rakuman ruwa da iska na gaba da su. 25 Da asuba (wajen karfe uku na dare) Yesu ya nufo su yana tafiya akan teku. 26 Da almajiran suka ganshi yana tafiya akan tekun, sai suka firgita suna cewa, "Fatalwa ce," suka yi kururuwa cikin tsoro. 27 Amma Yesu yayi magana da su nan da nan yace, "Ku yi karfin hali! Ni ne! Kada ku ji tsoro." 28 Bitrus ya amsa masa cewa, "Ubangiji, idan kai ne, ka umarce ni in zo wurin ka bisa ruwan." 29 Yesu yace, "Zo" Sai Bitrus ya fita daga jirgin yana tafiya akan ruwan zuwa wurin Yesu. 30 Amma da Bitrus ya ga iska, sai ya tsorata. Yayin da ya fara nutsewa, sai ya tada murya ya ce, "Ubangiji, ka cece ni!" 31 Nan take Yesu ya mika hannunsa, ya kama Bitrus ya ce masa, "Kai mai karancin bangaskiya, meyasa ka yi shakka?" 32 Bayan da Yesu da Bitrus suka shiga cikin kwale-kwalen, sai iska ta daina kadawa. 33 Sai almajiran dake cikin kwale-kwalen su ka yi wa Yesu sujada suna cewa, "Hakika kai Dan Allah ne." 34 Da suka haye, sun iso kasar Janisarata. 35 Da mutanen wurin suka gane Yesu, sai suka aika da sako zuwa dukan yankin, kuma suka kawo masa dukan marasa lafiya. 36 Suka roke shi don su taba gezar rigarsa, kuma dukan wadanda suka taba shi sun warke.
Waɗannan ayoyi suna bayana yadda Hiridus ya yi, da ya ji labari game da Yesu. Wannan abun ya faru ne bayan wasu lokatai da suka wuce..
" A lokacin da suka wuce" ko "Da Yesu yake bishara a Galili"
"ya ji labari game da Yesu" ko "ya ji sunan da Yesu yayi"
"Hiridus ya ce"
Kalmomin nan "daga mattatu" na magana akan dukan mutanen da suka mutu na cikin karkashin kasa. Tashiwa daga mattatu na magana akan zama rayyeye kuma.
Wasu Yahudawa a lokacin can sun yadda cewa iɗan mutum ya dawo daga mattatu zai samu ikoki ya yi abubuwan al'ajibi.
A nan marubucin ya fara fada yadda Hiridus ya kashe Yahaya mai Baftisma. Waɗannan abubuwan sun faru a wasu lokatai kafin abun da ya faru a ayoyin da suka wuce.
Iɗan akawai bukata, za ka iya mika yadda abubuwan suka faru a 14:3-4, yadda take a UDB
Wannan na faɗi cewa Hiridus yayi haka ne, domin ya umurce wasu ne suyi mashi. AT: "Hiridus ya umurce sojojin sa su kamo Yahaya mai Baftisma, su ɗaure shi, su kuma jefa shi a kurkuku"
Filibus dan'uwan Hiridus ne. Hiridus ya ɗauki matar Filibus ta zama matar sa.
Iɗan ya zama dole, za'a iya fadin wannan maganan a wani juyi. AT: "Domin Yahaya ya fada wa Hiridus cewa bai kama Hiridus ya ɗauki Hirudiya a matsayin matar sa ba."
"Domin Yahaya ya cigaba da fada wa Hiridus"
Philibus yana nan a raye da Hiridus ya aure Hirudiya.
"Hiridus ya tsorata"
"sun ɗauka Yahaya"
AT: "a tsakanin baƙi da suka je bukin aihuwar"
AT: "Bayan da mahaifuwarta ta umurce ta"
"zuga" ko "gaya"
" 'yar Hirudiya ta ce wa Hiridus"
babban faranti
AT: " Roƙon da tayi ya saka Sarki bakin ciki sosai"
"Sarki Hiridus"
AT: "ya umurce mutanen sa su yi abin da ta faɗa"
AT: "wani ya kawo ƙansa a bisa tire, aka mika wa 'yarinyar"
Yi amfani da kalman wa 'ya, 'yarinya marasa aure.
"almajaren Yahaya"
"gangar jikin"
Za 'a iya bayyana ma'anar gabadaya a filli. AT: "almajaren Yahaya suka je suka kuma gaya wa Yesu abun da ya faru da Yahaya mai Baftisma"
An yi amfani da kalman nan domin a saka alamar burki acikin ainihin labarin. Anan, Mattiyu ya fara maganar sabuwar sashi a labarin.
"ji abun da ya faru da Yahaya mai Baftisma" ko "ji labari game da Yahaya"
"ya tafi" ko "ya bar wurin taron." Ana zaton cewa almajaren Yesu sun tafi tare da shi. AT: Yesu da almajarensa suka tafi"
"daga wancan wurin"
"Da taron suka ji inda Yesu ya je" ko "Da taron suka ji cewa ya tafi"
"taron jama'a" ko "babban taron jama'a"
Wannan na nufin cewa mutanen da suke cikin taron suna tafiya ne.
" Da Yesu ya je gaba, ya ga babban taro"
" almajaren Yesu suka je wurinsa"
"Ba llale ba ne mutanen da suke cikin taron"
Kalman nan "Ku" Jam'i ne, yana nufin almajaren ne.
"Almajaren suka ce wa Yesu"
Gurasa ɗunkulen ƙullu ne da aka shirya ta a wata tsifa aka kuma gasa ta.
"Ku kawo mini gurasan da kuma ƙifin"
"kwanta." Za ka iya yin amfani da wannan kalman tawurin nuna yadda mutanen kabilar ka suke cin abinci.
"Ya rike a hannayensa." Bai sato su ya yi ba.
" ya yage gurasar"
"gurasa" ko "gabadayar gurasar"
AT1): "Yayen da yake kallon sama" ko 2)"Bayan da ya kalla sama."
AT: "har sun koshi" ko "har suka daina jin yunwa"
"almajaren suka tattara" ko "wasu mutanen suka tattara"
"kwanduna 12 cike"
"Waɗanda suka ci gurasar da kuma ƙifin"
"maza 5,000"
"da Yesu ya gama ciyer da dukan mutanen, sai ya"
"har kurewar yammaci" ko "har guri tayi duhu"
"har ma almajaren basu iya tuka ƙwaleƙwalen ba saboda gaggarumin raƙumen ruwan"
Da asuba tsakanin ƙarfe uku na safiya da kuma rana. "dai kafin yammaci ta gabato"
"tafiya a bisa ruwa"
"suka ji tsoro sosai"
ruhun da ya rigaya ya bar gangan jikin mutum da ya mutu
"Bitrus ya amsa wa Yesu
Anan "gan iskan" na nufin yana sane da iskan. AT: "Da Bitrus ya ga iskan da ke koran raƙuman ruwan gaba da baya" ko "da ya gane karfin iskan"
"Kai da kake da ƙarancin bangaskiya." Yesu ya faɗa wa Bitrus haka domin Bitrus ya ji tsoro. AT: "Don me ka ke da ƙarancin bangaskiya haka!"
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya faɗa wa Bitrus kada yayi shakka. Za ka iya bayyana a fili dalilin da Bitrus zai yi shakka ba. AT: "bai kamata kayi shakka ba domin zan iya tsare ku daga nitsewa ba."
Wannan laƙabi ne mai muhinminci sosana Yesu da yake bayyana ɗangantakansa da Allah. (Dubi: )
"Da Yesu da kuma almajaren sa suka haye tekun"
Wannan ƙaramar gari ce da take...................................................................
"mazajen da suke wancan yankin suka aiko da sako"
"Mutane mara lafiya suka roƙe shi"
"tufafin sa" ko "abin da ya saka"
AT: "suka samu lafiya"
Hiridus ya zata cewa Yesu ne Yahaya mai Baftisma wanda ya tashi daga matattu.
Hiridus ya aure matar ɗan'uwarsa.
Hiridus bai kashe Yahaya mai Baftisma nan da nan ba domin ya ji tsoron mutanen da sun ɗauke shi a matsayin annabi.
Hiridus ya yi yi alkawari zai ba wa Hirudiya duk abin da ta roƙa.
Hirudiya ta roƙa kan Yahaya mai Baftisma a kan tire.
Hiridus ya ba Hirudiya roƙonta domin rantsuwar da ya yi kuma domin mutanen da ke a wurin bukin tare da shi.
Yesu ya ji tauwsayinsu sai ya warkad da marasa lafiya dake cikinsu.
Yesu ya ce wa almajiransa su ba wa jama'an wani abu su ci.
Yesu ya dubi sama, ya sa albarka ya gutsuttsura ya kuma ba almajiran don su ba taron.
Maza kusan dubu biyar suka ci tare da mata da yara, kuma an rage kwanduna goma sha biyu.
Yesu ya tafi kan dutse don ya yi addu'a da kan shi.
Kwale-kwaler almajiran ya kusan zama wanda ba za a iya bi da shi ba saboda rakuman ruwa da iska.
Yesu ya je wurin almajiran ta tafiya akan teku.
Yesu ya ce masu su yi karfin hali kuma kada su ji tsoro.
Yesu ya ce wa Bitrus ya zo ya yi tafiya a kan ruwa.
Bitrus ya fara nutsewa a cikin ruwa da ya ji tsoro.
Sa'ad da Yesu da Bitrus suka shiga cikin kwale-kwalen, sai iska ta daina kadawa.
Da almajiran suka gan wannan, su ka yi wa Yesu sujada suka kuma ce shi ne Dan Allah.
A loƙacin da Yesu da almajiran suka kai ɗayan gefen teku, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya.
1 Sai wadansu Farisawa da malamai suka zo wurin Yesu daga Urushalima. Su ka ce, 2 "Meyasa almajiranka suke karya al'adar dattawa? Don ba su wanke hannayen su kafin su ci abinci." 3 Yesu ya amsa masu ya ce, "Kuma don me ku ke karya dokar Allah saboda al'adunku? 4 Domin Allah ya ce, 'Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka; 'Shi wanda ya yi muguwar magana ga mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lallai zai mutu. 5 Amma kun ce, "Duk wanda ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, "Kowanne taimako da za ka samu daga gare ni yanzu baiko ne ga Allah,'" 6 wannan mutum ba ya bukatar ya girmama mahaifinsa. Ta wannan hanya kun maida maganar Allah wofi saboda al'adunku. 7 Ku munafukai, daidai ne Ishaya ya yi annabci akan ku da ya ce, 8 " Wadannan mutane girmama ni da baki kawai suke yi, amma zukatansu nesa suke da ni. 9 Suna mani sujada a banza, domin suna koyar da dokokin mutane a matsayin rukunansu." 10 Sai ya kira taron mutane zuwa gare shi ya ce masu, "Ku saurara ku fahimta, 11 ba abin da ke shiga baki ke kazantar da mutum ba. Sai dai, abin da ke fitowa daga baki, wannan shi ya ke kazantar da mutum." 12 Sai al'majiran suka zo suka ce masa, "Ka san Farisawa ba su ji dadi ba da suka ji maganan nan?" 13 Yesu ya amsa ya ce, "Kowace shuka wadda ba Ubana na sama ya shuka ba za a tuge ta. 14 Ku kyale su kawai, su makafin jagora ne. In makaho ya ja wa wani makaho gora dukan su za su fada rami." 15 Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, "Ka bayyana wannan misali a garemu," 16 Yesu ya ce, "Ku ma har yanzu ba ku da fahimta? 17 Ko baku gani ba duk abin da ke shiga baki zuwa ciki ta haka yake fita zuwa salga? 18 Amma abubuwan da ke fita daga baki suna fitowa ne daga zuciya. Su ne abubuwan da ke kazantar da mutum. 19 Domin daga zuciya mugayen tunani suke fitowa, kisan kai, zina, fasikanci, sata, shaidar zur, da zage-zage. 20 Wadannan su ne abubuwan da ke kazantar da mutum. Amma ci da rashin wanke hannu baya kazantar da mutum." 21 Sai Yesu ya tafi daga nan ya nufi yankin biranen Taya da Sidon. 22 Sai wata mace Bakan'aniya ta zo daga wannan yanki. Ta daga murya ta ce," Ka yi mani jinkai, Ubangiji, Dan Dauda; 'yata tana cikin bakar azaba da aljani." 23 Amma Yesu bai ce mata kome ba. Almajiransa suka zo suka roke shi, suna cewa, "Ka sallame ta, domin tana bin mu da ihu." 24 Amma Yesu ya amsa ya ce, "Ba a aike ni gun kowa ba sai dai ga batattun tumakin gidan Isra'ila." 25 Amma ta zo ta durkusa a gabansa, tana cewa, "Ubangiji ka taimake ni." 26 Ya amsa ya ce, "Ba daidai bane a dauki gurasar yara a jefa wa kananan karnuka. 27 Ta ce, "I, Ubangiji, amma ko kananan karnuka suna cin barbashin da ke fadowa daga teburin maigida." 28 Sai Yesu ya amsa ya ce mata, "Mace, bangaskiyarki tana da girma. Bari ya zamar maki yadda ki ke so." 'Yarta ta warke a lokacin. 29 Yesu ya bar wurin ya tafi kusa da tekun Galili. Sai ya hau tudu ya zauna a can. 30 Taro mai yawa suka zo gunsa. Suka kawo masa guragu, makafi, bebaye da nakasassun mutane da yawa, da wadansu marasa lafiya. Suka kawo su gaban Yesu, sai ya warkar da su. 31 Don haka mutane da yawa suka yi mamaki a lokacin da suka ga bebaye suna magana, nakasassu sun warke, guragu suna tafiya, makafi suna gani. Sai suka daukaka Allah na Isra'ila. 32 Yesu ya kira almajiransa zuwa gun sa sai ya ce, "Ina jin tausayin taron, sun kasance tare da ni kwana uku ke nan kuma ba su da abin da za su ci. Bana so in sallame su ba tare da sun ci abinci ba, domin kada su suma a hanya." 33 Almajiran suka ce masa, "A ina zamu sami isasshiyar gurasa a wannan wuri da babu kowa har ta ishi babban taron nan." 34 Yesu ya ce masu, "Gurasa nawa ku ke da ita?" Suka ce, "Bakwai da 'yan kifi marasa yawa." 35 Sai Yesu ya umarci taron su zauna a kasa. 36 Ya dauki gurasar nan bakwai da kifin, bayan ya yi godiya, ya kakkarya gurasar ya bada ita ga almajiran Sai almajiran suka ba taron. 37 Jama'a duka suka ci suka koshi. Suka tattara gutsattsarin abincin da ya rage, kwando bakwai cike. 38 Wadanda suka ci su dubu hudu ne maza, banda mata da yara. 39 Sai Yesu ya sallami taron ya shiga cikin jirgin ruwa ya tafi yankin Magadan.
Wannan wurin ya canza zuwa abin da ya faru a sashin suran da suka wuce. Anan Yesu ya amsa game da mummunan ra'ayin farisawan.
Farisiyawa da kuma Mallamen attaura suna amfani da wannan tambayan don su zarge Yesu da almajaren sa. AT: "Almajaren ka ba suwa biyyaya ga dokokin da kaƙanen mu suka bamu."
Wannan ba iri ɗaya bane da dokan Musa. Wannan na kai mu zuwa ga koyaswan da suka zo daga baya da kuma fasarar doka da shugabanen addini suka bayas bayan Musa.
Wannan wankin, ba na hannaye kawai ba. Wannan na nufin bukin wanki bisa ga al'adun dattawa. AT: "basu wanke hannayen su tsap ba"
Yesu ya amsa da tambaya domin ya zargi abin da shugabanen addini suke yi. AT: " Kuma na gani cewa kun ki ku yi biyyaya ga umurnin Allah domin ku iya bin abin da kakannen ku suka koyas maku!"
Yesu ya cigaba da amsa wa farisawa
hakika mutanen za su halaka shi
AT: "Amma kuna koyas da cewa mutum bashi da bukata ya girmama iyayensa ta wurin basu abin da zai taimake su idan mutmin ya gaya wa iyayensa cewa ya riga ya bada shi a matsayin kyauta wa Allah"
Anan "ku" jam'i ne kuma na nufin Farisawa da mallaman attaura.
Ya nuna da cewa "ubansa" na nufi "iyensa." Wannan yana nufi da cewa shugabannen adini sun koyas da cewa mutum bashi da bukatan nuna girmamawa ga iyayensa ta wurin kulawa da su.
"kun mai da al'adunku mafi muhinminci fiye da umurnin Allah"
"Ishaya ya faɗi gaskiya game da ku a wannan anabcin"
Ana nufin cewa Ishaya ya na faɗin abin da Allah ya gaya mashi ne. AT: "da ya faɗa abin da Allah ya ce"
A nan "baki" na nufin magana ne. AT: "Waɗannan mutane sun faɗi abubuwa masu kyau game da ni"
Duk abubuwan da suka faru a maganan ya shafi Allah.
A nan "zuciya" na nufin tunani ko yadda mutum yake ji. Wannan maganan hanya ce da za'a iya cewa, da gaske ne mutane basu ba da kan su ga Allah ba. AT: "amma ba so na da gaske suke ba"
"Sujadarsu a banza ne gare ni" ko "Nuna wa suke yi wai suna mani sujada"
"dokan da mutane suka ƙera"
Yesu yana nanata muhinmincin abun yake ƙoƙarin faɗa. Za'a iya bayyana nufin bayanin nan a fili. AT: "Ku saurara da kyau ga abun da zan ce domin ku fahimce manufan ta"
Yesu yana kwatanta abin da mutum ke ci da abin da yake faɗi. Yesu na nufin cewa Allah ya fi kula da abin da mutum yake faɗi fiye da abin da yake ci.
AT: "Farisawan sun yi fushi da wannan kalman" Farisawan basu ji daɗi da wannan maganan ba"
Wannan ƙarin magana ne. Yesu yana nufin cewa Farisawan ba na Allah ba ne, saboda haka Allah zai cire su.
Wannan laƙani ne mai muhinminci sosai ga Allah wanda yake bayyana dangantakan saƙanin Allah da Yesu.
AT: "Uba na zai tuge ta" ko "zai tuge kasan" ko "zai cire"
Kalman nan "su" na nufin Farisawan ne.
Yesu yayi amfani da wata kalma domin ya yi bayani game da Farisawa. Yesu na nufin cewa Farisawan basu fahimce umurnin Allah ba ko kuma yadda zasu faranta masa rai.
"wa mu almajaren"
Yesu yayi amfani da tambaya domin ya sauta wa almajaren domin basu fahimce misalin ba. Haka kuma, kalman nan "ku" ana nanata ta. Yesu ma bai yarda cewa almajaren basu fahimce shi ba. AT: "ina yanke buri na a gare ku almajare na, har yenzu baku fahimce abun da na koyas ba!"
Yesu yayi amfani da tambaya domin ya sauta wa almajaren game da rashin fahimtan misalin sa. "haƙika kun fahimta ... zuwa salga"
"shiga zuwa ciki"
Wannan kalma ce mai ladabi da ake nufin inda mutane na binne mattacen gangan jiki.
Wannan na nufin abin da mutum yake faɗa. AT: "kalmomin da mutum yake faɗa"
A nan "zuciya" na nufin zuciyar mutum ko cikin mutum. AT: "daga cikin mutum" ko "daga zuciyar mutum"
aikata kisa ga mutum mara laifi
Bisa ga al'adun dattawan, da farko wannan na nufin mutum ya ci kafin bukin wanke hannun. AT: "ci kafin mutum ya wanke hannu"
Ana nufin cewa almajaren sun tafi tare da Yesu. AT: "Yesu da almajarensa sun bar wurin" (Dubi:
Kalman nan "Sai" na jawo hankalin mu zuwa sabon mutum a cikin labarin. Za ka iya nemi hanyar yin haka da harshen ka. AT: "Akwai wata mace Baƙan'aniya wanda ta zo"
"wata mace wanda ta zo daga wancan yankin mutanen da ake kiransu Baƙa'nai......... "Ƙasan Kan'anam ba ta nan a yanzu. Tana cikin taron mutanen da suka yi rayuwa kusa da garin Tyre da Sidon.
Kalman nan na nufin cewa tana roƙon Yesu ya warkas da 'yar ta"
Yesu ba ainihin ɗan Dauda ba ne, haka kuma za'a iya juya wannan a matsayin "Zuriyar Dauda." Haƙannan kuma "Ɗan Dauda" laƙabi ne na mai Ceto, mai yiwuwa matan ta kiran Yesu da laƙabin sa.
AT: "Aljani na mummunar mulki ga 'ya ta" ko "yata tana cikin bakar azaba da aljani."
Anan "kalma" na nufin abun da mutum ke faɗi ne. AT: "bai faɗi komai ba"
AT: "Allah bai aike ni gun kowa ba"
Wannan ƙarin magana ce da ta ke kwatanta gabadayar jihar Isra'ila da tumakin da ya raɓa hanya da makiyayinsa. AT: [10:6]
"Baƙa'aniyar macen ta zo"
Wannan ya nuna cewa matar ta ƙaskantar da kanta a gaban Yesu.
Yesu ya amsa wa matar da ƙarin magana. Tushin ma'anan nan shine ba daidai bane a ɗauki abun da ke na Ba-yahuɗe a ba wanda shi ba Ba-yahuɗe ba.
A nan "gurasa" na nufin abinci ne. AT: "abincin yara"
Yahudawa suna ɗaukan karnuka a matsayin kazamtattcen dabba ne. Anan amfani da hoton bayanin nan wa waɗanda su ba Yahudawa ba ne.
Amsar matar yayi iri ɗaya ne da kwatancin da Yesu yayi amfani da shi a ƙarin maganan da ya fada. Tana ma'anar waɗanda ba su Yahuɗawa ba su yi koƙarin su samu kiman abubuwa masu kyau da Yahudawa suna banza da ita.
AT: [Matta 15:26]
AT: "Zan yi"
Wannan ƙarin magana ne. AT: "A daidai lokacin" ko "Nan da nan"
AT: "Yesu ya warkas da 'yar ta" ko " 'yarta ta warke"
"waɗanda ba suwa iya tafiya, waɗanda ba suwa iya gani, waɗanda ba suwa iya magana, da waɗanda hannayensu ko kafafunsu basuwa aiki"
Haka kuma wasu mara lifiya ko guragun mutane basu iya tashiwa ba, da abokanayen su suka kawo su a wurin Yesu, sun ajiye su a kasa a gaban shi. AT: "Taron suka ajiye mutane mara lafiyan a kasa a gaban Yesu"
AT: "guragun suka warke"
AT: "guragun mutane ... nakassasun mutane ... maƙafin mutane"
"ba tare da cin abinci ba domin zasu iya suma a hanya"
Almajaren suka yi amfani da tambaya don su fada cewa babu inda zasu samu abinci wa taron. AT: "Babu wuri kusa inda zamu iya samun isheshen gurasa wa irin wannan babban taron."
AT: "Gurasa guda bakwai da kuma kiman kananan ƙifaye"
Yi amfani da kalman kabilar ka domin nuna yadda mutane ke cin abinci a lokacin da babu tabur, ko ta wurin zama ko kwance.
" Yesu ya rike gurasa guda biyer da kuma ƙifin a hannayensa"
"ya yago gurasar"
"ya ba da gurasan da kuma ƙifin"
"almajaren suka tattara" ko "wasu mutane suka tattara"
"Mutanen da suka ci"
"maza 4,000"
"yankin"
Wasu lokaci ana kiran yankin " Magdala."
Farisawan sun hana 'ya'ya taimakon iyayensu ta wurin ɗauka kuɗin a matsayin "kyauta da an ba Allah".
Ishaya ya yi annabci cewa Farisawa za su girmama Allah da bakinsu, amma zukatansu za su nesa da shi.
Farisawan su na koyar a fanin adini dokokin mutane.
Yesu ya faɗa cewa abin da ke fitowa daga bakin mutum ne ke kazantar da mutum.
Yesu ya faɗa cewa abin da mutum ke ci ba ya kazantar da mutum.
Yesu ya kira Farisawan makafin jagora, kuma ya ce za su fadi rami.
Daga zuciya mugayen tunani suke fitowa, kisan kai, zina, fasikanci, sata, shaidar zur, da zage-zage.
Yesu bai ce mata kome ba.
Yesu ya bayyana cewa an aike shi ga batattun tumakin gidan Isra'ila kadai.
Yesu ya faɗa cewa matan ta na da babban bangaskiya, kuma ya biya mata bukatanta.
Yesu ya warkad da guragu, makafi, bebaye da nakasassu.
Almajiran su na da kifi bakwai da 'yan kifi marasa yawa.
Yesu ya ɗauki gurasar da kifin, ya yi godiya, ya kakkarya gurasar ya ba da su ga almajiransa.
kwando bakwai cike suka rage bayan kowa ya ci.
Maza dubu huɗu, tare da mata da yara suka ci har sun koshi.
1 Sai Farisawa da Sadukiyawa suka zo su gwada shi suka roke shi ya nuna masu alama daga sama. 2 Amma ya amsa ya ce masu, "Lokacin da yamma ta yi, sai ku ce, 'Za a yi yanayi mai kyau, domin sama ta yi ja,' 3 Kuma da safe ku ce, 'Zai zama yanayi mara kyau a yau, domin sama ta yi ja ta kuma gama gari, kun san yadda za ku bayyana kammanin sararin sama, amma ba ku iya bayyana alamun lokaci ba. 4 Mugun zamani, maciya amana suna neman alama, amma babu wata alama da za a nuna sai ta Yunusa." Daga nan sai Yesu ya tafi. 5 Almajiran suka zo daga wancan gefe, amma sun manta su dauki gurasa, 6 Yesu ya ce masu, "Ku kula ku kuma mai da hankali da yisti na Farisawa da Sadukiyawa." 7 Sai almajiran suka fara magana da junansu suka ce, "Ko saboda bamu kawo gurasa bane." 8 Yesu yana sane da wannan sai ya ce, "Ku masu karancin bangaskiya, don me ku ke magana a tsakaninku cewa ko don bamu kawo gurasa bane? 9 Ba ku gane ko tuna da gurasa guda biyar da aka ciyar da mutum dubu biyar, kuma kwando nawa kuka tara ba? 10 Ko gurasa bakwai ga mutum dubu hudu, da kuma kwanduna nawa kuka dauka ba? 11 Yaya kuka kasa fahimta cewa ba game da gurasa nake yi maku magana ba? Ku yi hankali ku kuma lura da yistin Farisawa da Sadukiyawa." 12 Sa'annan suka fahimta cewa ba yana gaya masu su yi hankali da yistin da ke cikin gurasa ba ne, amma sai dai su yi lura da koyarwar Farisawa da Sadukiyawa. 13 A lokacin da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, ya tambayi almajiransa, cewa, "Wa mutane ke cewa Dan Mutum yake? 14 Suka ce, "Wadansu suna cewa Yahaya mai baftisma; wadansu Iliya, saura suna cewa Irmiya, ko daya daga cikin annabawa." 15 Ya ce masu, "Amma ku wa kuke ce da ni?" 16 Sai Saminu Bitrus ya amsa ya ce, "Kai ne Almasihu, Dan Allah mai rai." 17 Yesu ya amsa ya ce masa, "Mai albarka ne kai, Saminu dan Yunusa, don ba nama da jini ba ne ya bayyana maka wannan, amma Ubana wanda ke cikin sama. 18 Ina kuma gaya maka cewa kai ne Bitrus, a kan wannan dutse zan gina ikilisiya ta. Kofofin hades ba za su yi nasara da ita ba. 19 Zan ba ka mabudan mulkin sama. Duk abin da ka kulla a duniya zai zama abin da an kulla a cikin sama, kuma duk abinda ka warware a duniya a warware yake cikin sama," 20 Sai Yesu ya umarci almajiransa kada su gaya wa kowa cewa shi ne Almasihu. 21 Daga lokacin nan Yesu ya fara gaya wa almajiransa cewa dole ne ya tafi Urushalima, ya sha wahala mai yawa a hannun dattawa, da manyan firistoci da malaman attaura, a kashe shi, a tashe shi zuwa rai a rana ta uku. 22 Sai Bitrus ya kai shi a gefe ya tsauta masa, cewa, "Wannan ya yi nesa da kai, Ubangiji; wannan ba zai taba faruwa da kai ba." 23 Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, "Ka koma bayana, Shaidan! Kai sanadin tuntube ne gare ni, domin ba ka damuwa da abubuwan da suke na Allah, amma sai abubuwan mutane." 24 Sa'annan Yesu ya ce wa almajiransa, "Duk wanda yake so ya bi ni, lallai ne ya ki kansa, ya dauki gicciyensa, ya bi ni. 25 Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi. Duk wanda ya rasa ransa domina zai same shi. 26 Domin wace riba mutum zai samu in ya sami dukan duniya ya rasa ransa? Me mutum zai iya bayarwa a maimakon ransa? 27 Domin Dan Mutum zai zo ne cikin daukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. Sa'annan ne zaya biya kowane mutum bisa ga ayyukansa. 28 Gaskiya ina gaya maku, akwai wadansun ku da ke tsaye a nan, da ba za su dandana mutuwa ba sai sun ga Dan Mutum na zuwa cikin mulkinsa."
Wannan sashi ya fara da saduwar Yesu da Farisiyawa da kuma Malamen attaura.
A nan "gwadawa" ana amfani da shi tawurin mummunar nufi. AT: "ƙallubale shi" ko "so su sa masa tarko"
Za'a iya bayanin yanayin nan a fili. AT: "Idan sarari tayi jawur da yammaci" ko "Idan sarari tayi jawur a lokacin da rana take sauka"
Wannan na nufin haske, sauki da kuma yanayi mai kyau.
Idan rana ta na sauka, Yahudawa sun san cewa idan sarari ta canza zuwa ja, alama ce cewa washegari zata yi sauki ta kuma yi haske.
Yesu ya cigaba da amsar shi zuwa ga Farisiyawa da kuma Mallamen attaura.
Za'a iya bayanin yanayin nan a fili. AT: "Idan sararin ta yi ja da asuba" ko "Idan sarari ta yi ja alokacin da rana tana tashiwa"
"gizagizai, yanayin ta yi haɗari"
"ta yi ja da kuma gizagizai"
"Kun san yadda ake kallon sarari kun kuma gane wace irin yanayi ce za ku samu"
"amma baku gane yadda zaku dubi abin da yake faruwa yanzu kuma ku gane ma'anar ta ba"
"Yesu yana magana game da zamanin sa ne. AT: "Ku muguye zamani maciya amana ne, wanda kuke neman alamu daga ni ... da za a baku" [12:39]
A nan "maciya amana" magana ce da ake amfani wa mutanen da ba suwa abubuwan gaskiya ga Allah. [12:39] AT: "Zamani mara gaskiya" ko "Zamani marasa tsoron-allah"
Yesu ba zai ba su alamu ba domin, da shike ya rigaya ya yi abubuwan al'ajibai dayawa amma, sun ki su yarda da shi. AT: [12:39] "Ba zan nuna wata alama ba" ko "Allah ba zai nuna maku wata alama ba"
"saidai wancan alamar da aka ba wa annabi Yunusa." [12:39]
Za ka iya yin bayyana maganan nan yadda za a gane ta. AT: "wancan gefen tekun" ko "wancan gefe na tekun Galili"
A nan "yisti" magana ce da take nufin mugun shawara da kuma koyaswar ƙarya. Za a yi bayanin maganar nan gaba [16:12].
"shawara da junansu" ko "tunani game da abun"
"Ku masu ƙarancin bangaskiyan nan." Yesu yayi haka wa almajarensa domin tunanin da suke yi akan rashin kawo gurasa, ya nuna cewa suna da ƙarancin bangaskiya da cewa Yesu zai tanaɗa masu. [6:30]
Yesu yayi anfani da tambaya, ya kwaɓe almajarensa domin rashin fahimtar abin da ya faɗa. AT: "ban ji daɗi ba domin kun yi tunanin cewa kun manta ku kawo gurasa ne ya sa na yi magana game da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa."
Yesu yayi amfani da tambaya domin ya kwaɓe almajiran. AT: "Haƙika, kun tuna ... kun tattara!"
" 5,000 ... 4,000"
"Ko kun tuna da gurasa bakwai ... kuka ɗauka ba? Yesu yayi anfani da tambaya domin ya kwaɓe almajaren. AT: "Haƙika kun tuna da gurasa bakawai ... da kuka ɗauka!"
Yesu yayi anfani da wannan tambaya domin ya kwaɓe almajaren. AT: "Da kun gane cewa ba gurasa nake magana akai ba."
Wannan nufin ga almajaren ne.
Ana amfani da kalman nan domin a nuna alamar birki cikin ainihin labarin ko kuwa a gabatar da sabon mutum cikin labarin. Anan Matiyu ya fara faɗa subuwar sashi a cikin labarin.
Yesu yana nufin ƙansa ne.
Wannan laƙaɓi ce mai muhinminci ne na Yesu da take nuna dangantakarsa da Allah.
A nan "rai" na kwatanta Allahn Isra'ila da dukkan allohlin ƙarya da kuma gumakai da mutane ke ɓauta wa. Allahn Isra'ila ne kadai yake raye, yana da iko kuma ya aikata.
"Saminu dan Yunusa"
A nan "nama da jini" na nufin mutum mai rai ne. AT: "mutum bai bayyana ba"
A nan "wannan" na nufin kalamun Bitrus ne, cewa Yesu shine Almasihu Ɗan Allah mai Rai.
AT: "amma Uba na wanda ke cikin sama ne ya bayyana maku wannan"
Wannan laƙani ce mai muhinminci ne na Yesu da take bayyana dangantaka sakanin Allah da kuma Yesu.
Wannan ya ƙara yin bayani akan abin da Yesu zai faɗa nan gaba.
"Ma'anar sunan Bitrus shine "dutse."
A nan "gina ikilisiya ta" wata irin magana ce da ake amfani domin a haɗa mutane da suka gaskanta da Yesu da jama'a. AT: 1) "wannan dutse" na nufin Bitrus ne, ko 2) "dutsen nan" na nufin gaskiya da Bitrus ya tashi fada a cikin [Matiyu 16:16]
Ana maganan "Hades" kamar gari ne da take kewaye da katanga da kofofi da take bambanta inda ake ajiye mattatu da kuma rayyayun mutane aciki da kuma waje. Anan "Hades" na nufin mutuwa ne, kuma "kofofin" na nufin ikon ta ne. AT: 1) "ikon mattatu ba za su yi nassara akan ikilisiya na ba" ko 2) "ikilisiya ta za ta yi nassara da ikon mattatu kamar yadda sojoji ke yin nassara da gari."
A nan "ka" na nufin Bitrus ne.
Mabuɗi abu ne da ake amfani a kulle ko a buɗe kofa. A nan suna walkilcin iko ne.
Wannan na nufin Mulkin Allah a matsayin Sarki. Kalman nan "mulkin sama" an yi anfani da shi kadai a littafin Matiyu. Idan zai yiwu, yi anfani da "sama" a fasarar ka.
Wannan maganan na nufin cewa Allah na sama zai amince da bin da Bitrus ya amince ko kuma ya ki amincewa a duniya.
AT: "Allah zai kulla ... Allah zai warware"
Yesu ya gaya masu na farko cewa ya kusan mutuwa. Zai kuma kara gaya masu bayan wannan na farkon. Bayan na farkon ne Bitrus ya kai yesu gefe.
A nan "hannu" na nufin iko. AT: "inda dattawa, manyan firistoci da malaman attaura zasu ba shi wahala"
A nan, a tasher zuwa rai kuma ƙarin magana ne da ya ke nufin saka wanda ya mutu ya zama rayyaye kuma. AT: Dattawa da manyan firistoci zasu kulla wa Yesu domin mutane su ƙashe shi. "mallaman attaura. Sai mutane zasu ƙashe shi, a rana ta uku zai zama rayayye kuma"
"Na uku" adadin jeranta siffa na "uku" ne."
"Bitrus ya yi wa Yesu magana yadda ba wanda zai iya jin su"
Wannan ƙarin magana ne da ke nufin "kada wannan ya faru." AT: "A' a" ko "Allah ya kiyaye wannan"
Yesu yana nufin Bitrus ya na yi kaman Shaidan domin Bitrus yana koƙarin hana Yesu cika nufin Allah game da abin da aka turo shi ya yi. AT: "Ka koma bayana, domin kana yi kaman Shaiɗan! kai sanadin tuntuɓe ne a gare ni" ko "Ka koma bayana, Shaiɗan! Na kira ka Shaiɗan domin kai sanaɗin tuntuɓe ne gare ni"
"Ka yi nesa da ni"
Bin Yesu anan na nufin zama ɗaya daga cikin almajarensa. AT: "zama almajiri na" ko "zama ɗaya daga cikin almajiri na"
"sai ya guje wa sha'awan jikinsa" ko "sai ya bar sha'awar jikinsa"
"ɗauka giciyensa, ya biyo ni." Giciyen na wakilce wahala da kuma mutuwa. Ɗaukan giciyen na nufin amincewa zaka sha wahala zaka kuma mutu. AT: "kuma yi biyyaya ga ni har ga wahala da kuma mutuwa" ko "sai kuma yayi biyyaya ga ni har ga wahala da kuma mutuwa"
Bin Yesu anan na nufin biyayya ga shi ne. AT: "ka kuma yi biyyaya ga ni"
"Ga duk wanda yake so"
Wannan bayanin na nufin cewa dolle ne mutumin zai mutu. Magana ne da yake ma'anan cewa mutumin zai duba yin biyayya ga Yesu a matsayi mafi muhinminci da rayuwarsa.
"domin ya gaskanta da ni" ko "akai na" ko "domina"
Wannan na nufin cewa mutumin zai fuskanci rayuwar ruhaniya da Allah. AT: "zai sami rai na gaskiya"
Yesu yayi anfani da tambaya domin ya koya wa almajarensa. AT: "ba zai kawo riba ga mutum ba ... ransa."
Kalmomin nan "dukan duniya" ƙãri ne ga babban arziki. AT: "idan ya samu duk abin da yake bukata"
"amma ya rasa ransa"
Yesu yayi amfani da tambaya domin ya koya wa almajarensa. AT: "Babu abin da mutum zai iya bayarwa domin ya samu ransa."
A nan Yesu na nufin kansa ne a matsayin mutum uku. AT: "Ni, Ɗan Mutum ... Ubana ... Sai na"
"zai zo, zai zama da iko daya da Ubansa"
"mala'ikun zasu zauna tare da ni." AT: "mala'ikun Ubana zasu zauna tare da ni."
Wannan laƙani ne mai muhinminci da yake bayyana dangantaka sakanin Allah da Ɗan Mutum, Yesu.
"bisa ga abin da kowane mutum ya yi"
"Ina gaya maku gaskiya." Wannan kalmomin ƙari ce ga abin da Yesu ya fada a gaba.
Dukkan maganganun nan na nufin mala'ikun ne.
A nan "ɗandana" na nufin a fuskanta. AT: "ba za su fuskanci mutuwa ba" ko "ba zai mutu ba"
A nan "mulkinsa" na wakilcin sa a mastayin Sarki. AT: "sai dai sun ga Ɗan Mutum zuwa a kamanin Sarki" ko "sai dai sun ga shaiɗa cewa Ɗan Mutum Sarki ne"
Farisawa da Sadukiyawa su na so su gan alama daga sama.
Yesu ya ce zai ba wa Farisawa da Sadukiyawa alama ta Yunusa.
Yesu ya ce wa almajiransa su yi lura da yisti na Farisawa da Sadukiyawa.
Yesu ya na faɗa wa almajiransa cewa su yi lura da koyarwar Farisawa da Sadukiyawa.
Yesu ya tambaye almajiransa cewa, "Wa mutane suke cewa Dan Mutum yake"?
Wadansu mutane sun zata ko Yesu Yahaya mai baftisma ne, ko Iliya, ko Irmiya, ko ɗaya daga cikin annabawa.
Bitrus ya amsa, "Kai ne Almasihu, Dan Allah mai rai."
Bitrus ya san amsar tamabayar Yesu domin Uba ne ya bayyana mashi.
Yesu ya ba wa Bitrus mabudan mulkin, domin ya iya kulla da kuma warware a duniya za a kuma kulla a kuma warware a sama.
Yesu ya fara gaya wa almajiransa cewa ɗole ne ya tafi Urushalima, ya sha wahala mai yawa, a kashe shi, ya kuma tashi a rana ta uku.
Yesu ya ce wa Bitrus "Ka koma bayana, Shaidan"!
Duk wanda yake so ya bi Yesu, lallai ne ya ki kansa, ya ɗauki gicciyensa.
Yesu ya ce babu riba wa mutum idan ya ya sami dukan duniya amma ya rasa ransa.
Dan Mutum zai biya kowane mutum bisa ga ayyukansa a loƙacin da zai zo.
Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa tare da mala'ikunsa.
Yesu ya faɗa cewa wasu a tsaye tare da shi za su gan Ɗan Mutum na zuwa cikin mulkisa.
1 Bayan kwana shida Yesu ya dauki Bitrus da Yakubu, da Yahaya dan'uwansa, ya kai su kan wani dutse mai tsawo su kadai. 2 Kamanninsa ya canja a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, kuma rigunansa suka yi kyalli fal. 3 Sai ga Musa da Iliya sun bayyana garesu suna magana da shi. 4 Bitrus ya amsa ya ce wa Yesu, "Ubangiji, ya yi kyau da muke a wurin nan. In kana so, zan yi bukkoki uku daya dominka, daya domin Musa, daya domin Iliya." 5 Sa'adda yake cikin magana, sai, girgije mai haske ya rufe su, sai murya daga girgijen, tana cewa, "Wannan kaunattacen Dana ne, shi ne wanda yake faranta mani zuciya. Ku saurare shi." 6 Da almajiran suka ji haka, suka fadi da fuskokinsu a kasa, saboda sun tsorata. 7 Sai Yesu ya zo ya taba su ya ce, "Ku tashi, kada ku ji tsoro." 8 Amma da suka daga kai ba su ga kowa ba sai Yesu kadai. 9 Yayin da suke saukowa daga dutsen, Yesu ya umarce su, ya ce, "Kada ku fadawa kowa wannan wahayin, sai Dan Mutum ya tashi daga matattu." 10 Almajiransa suka tambaye shi, suka ce, "Don me marubuta ke cewa lallai ne Iliya ya fara zuwa?" 11 Yesu ya amsa ya ce, "Hakika, Iliya zai zo ya maido da dukan abubuwa. 12 Amma ina gaya maku, Iliya ya riga ya zo, amma ba su gane shi ba. A maimakon haka, suka yi masa abin da suka ga dama. Ta irin wanan hanya, Dan Mutum kuma zai sha wuya a hannunsu. 13 Sa'annan almajiransa suka fahimci cewa yana yi masu magana a kan Yahaya mai Baftisma ne. 14 Da suka iso wurin taron, wani mutum ya zo gunsa, ya durkusa a gaban sa, ya ce, 15 "Ubangiji, ka ji tausayin yarona, domin yana da farfadiya, kuma yana shan wuya kwarai, domin sau da yawa yana fadawa cikin wuta ko ruwa. 16 Na kawo shi wurin almajiran ka, amma ba su iya su warkar da shi ba." 17 Yesu ya amsa ya ce, "Marasa bangaskiya da karkataccen zamani, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan jure da ku? Ku kawo shi nan a wurina." 18 Yesu ya tsauta masa, sai aljanin ya fita daga cikinsa. Yaron ya warke nan take. 19 Sai almajiran suka zo wurin Yesu a asirce suka ce, "Me ya sa muka kasa fitar da shi?" 20 Yesu ya ce masu, "Saboda karancin bangaskiyarku. Domin hakika, ina gaya maku, in kuna da bangaskiya ko da kamar kwayar mastad, za ku ce wa wannan dutse, 'Matsa daga nan ka koma can,' zai kuwa matsa kuma ba abin da zai gagare ku. 21[1]22 Suna zaune a Galili, Yesu ya ce wa almajiransa, "Za a bada Dan Mutum ga hannun mutane. 23 Kuma za su kashe shi, a rana ta uku zai tashi." Sai almajiransa suka yi bakin ciki kwarai. 24 Da suka iso Kafarnahum, mutane masu karbar haraji na rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, "Malaminku na ba da rabin shekel na haraji?" 25 Sai ya ce, "I." Amma da Bitrus ya shiga cikin gida, Yesu ya fara magana da shi yace, "Menene tunaninka Saminu? Sarakunan duniya, daga wurin wa suke karbar haraji ko kudin fito? Daga talakawansu ko daga wurin baki?" 26 Sai Bitrus ya ce, "Daga wurin baki," Yesu ya ce masa, "Wato an dauke wa talakawansu biya kenan. 27 Amma don kada mu sa masu karbar harajin su yi zunubi, ka je teku, ka jefa kugiya, ka cire kifin da ya fara zuwa. Idan ka bude bakinsa, za ka sami shekel. Ka dauke shi ka ba masu karbar harajin nawa da naka.
Wannan yana ba da farkon labarin canza kamanin Yesu kenan.
"Bitrus, Yahaya, da Yakubu ɗan'uwan Yahaya"
Da suka kalle shi, kamaninsa ya banbanta da yadda yake da.
AT: "bayyanuwarsa ya canza" ko kuma "bayyanuwarsa ya yi dabam"
"a idonsu" ko kuma "har sun iya ganinsa da kyau"
Waɗannan ƙãrin bayyani ne don a nanata irin hasken da bayyanuwar Yesu ya zama.
"kayakin jikinsa"
Wannan kalmar na jan hankalinmu ne zuwa ga abin mamaki da ya biyo baya.
Wato Bitrus, Yakubu, da Yahaya.
"da Yesu"
"cewa." Ba amsa tambaya Bitrus ke yi ba.
Babu wata taƙamammen bayani ko "mu" na nufin Bitrus, da Yakubu, da Yahaya ne kadai ko kuma idan yana nufin dukkan waɗanda ke wajen, a haɗe da Yesu, Iliya, da Musa. Idan za ku iya juya wannan don ya ba da dukkan ra'ayi biyun, to, sai ku yi hakan.
Wannan na iya nufin 1) wuraren da mutane za su iya zuwa don yin sujada ko kuma 2) wurare da mutane za su iya yi barci amma ba na dindindim ba.
"ya maimaye su"
A nan "murya" na nufin maganar da Allah ke yi. AT: "Sai Allah yayi magana da su daga girgijen"
"almajiran suka ji Allah na magana"
A nan "faɗi da fuskokinsu" karin magana ne. AT: "suka durkusa da fuskokinsu ƙasa"
Waɗannan abubuwan da suka biyo baya sun faru ne ba da jimawa ba bayan almajire ukun sun gan canjawar kamanin Yesu.
"Yayin da Yesu da almajiransa"
Yesu yana magana a kan shi da kansa ne.
Almajiran na magana ne game da wata sani na cewa Iliya zai dawo da rai ya kuma koma zuwa ga mutanen Isra'ila kafin Almasihu ya zo.
"yă sa abubuwa su yi daidai" ko kuma "yă shirya mutane domin marabtan Amasihu"
Wannan na ƙara nanata maganar Yesu da ke biyo baya ne.
Duk wuraren da waɗannan kalamun sun auku, sun iya nufin 1) shugabannin Yahudawa ko kuma 2) dukkan mutanen Yahudawa.
A nan "hannu" na nufin iko. AT: za su sa Ɗan Mutum yăsha wuya"
Yesu yana magana a kan shi da kansa ne.
Ana ɗaukan cewa mutumin yana so Yesu ya warkar da yaronsa ne. AT: "ka yi wa ɗa na jinkai ka warkar da shi"
Wato wani lokaci ya kan yi farfaɗiya. Hankalinsa ya kan fita, sai ya zama gagararre. AT: "yana da farfaɗiya"
"Wannan tsaran bata gaskanta da Allah ba kuma ba ta san abinda ke daidai da wanda ba daidai ba. Har"
Waɗannan tambayoyin suna nuna bakin cikin Yesu da mutanen. AT: "Na gaji da kasancewa tare da ku! Na gaji da rashin bangaskiyar ku da karkacewan ku!"
AT: "yaron ya sami warkaswa"
Wannan karin magana ne. AT: "nan da nan" ko kuma "a daidai lokacin"
A nan "mu" na nufin masu magana amma banda masu sauraro don haka, ba kowa da kowa bane.
"Me yasa ba mu iya fitar da aljannun daga jikin yaron ba?"
"Ina faɗa maku gaskiya." Wannan na ƙara nanata abin da Yesu zai faɗa ne.
Yesu yana kwatanta girrman kwayar mastad da iyakar bangankiyar da ake buƙata don a yi al'ajibi. Kwayar mastad karami ne sosai, amma yana girma ya zama wani babban bushiya. Yesus yana nufin cewa muna buƙatar bangaskiya kaɗan ne kawa mu iya yin babban al'ajibi.
AT: "za ku iya yin kowani abu"
Yesu da almajiransa suna zaune"
AT: "Wani zai ba da Ɗan mutum"
Yesu yana nufin shi kansa ne amma yan maganar kaman wani ne uku ne yake magan akai.
Kalmar "hannu" anan na nufin ikon da mutane ke moran hannun su su yi amfani da shi. AT: "ɗauke shi a sa shi a karkashi ikon mutane" ko kuma "ɗauke shi a ba da shi ga mutanen da za su yi da shi yadda suke so"
A nan "hannu" na nufin iko ko mulkin mutane"
"Uku" shi ne jerin kirge "uku"
Wato zai tashi daga matattu kenan. AT: Allah zai ta da shi kuma" ko kuma "Allah zai tashe shi da rai kuma"
Da Yesu da almajiransa"
Wannan harajjin ne mutanen Yahudawa ke biya don su tallafa wa haikalin da ke Urusahalima. AT: "haikalin haraji"
"wurin da Yesu ke zama"
Yesu yana wannan tambayan ne domin ya koya wa Saminu cewa, kada yă samu sanin don kansa kadai. AT: "Ka ji, Saminu. Mun san da cewa yayin da sarukuna sun karɓa haraji, suna karɓa ne daga wurin mutanen da ba 'yan gidansu ba"
Idan kun juya maganar a [17:25], kuna iya ba da wat hanya da za a iya juya ta anan. AT: "Da Bitrus ya ce, 'i, wannan gaskiya ne. Sarakuna suna karɓan haraji daga baƙi ne,' Yesu ya ce" ko kuma "Da Bitrus ya amince da maganar da Yesu ya yi, Yesu ya ce"
A zamanin yau, shugabanni sukan sa haraji wa nasu mazauna. Amma, a zamanin da, shigabanni suka sa haraji wa mutanen da su ci su da yaƙi ne ba mazaunan garinsu ba.
mutanen da mai mulki ko sarki ke mulki a bisansu
"Amma ba mu so mu sa masu karɓan haaji su yi fushi. Don haka, jeka"
Masu kaman kifi sukan ɗaura kugiyansu a ƙarshen igiya, sa'annan su jefa shi a ruwa don su kamo kifi.
"baƙin kifin"
kuɗi wanda ya isa ladan aiki na kwana huɗu
ka ɗauki kuɗin"
A nan "naka" na nufin Bitrus. Lalle ne kowanensu ya biya harajin rabin shekel. Don haka shekel ɗaya zai issa wa Yesu da Bitrus su biya harajinsu.
Bitrus, Yakubu, da Yahaya sun hau kan dutse tare da Yesu.
Yesu ya canza don fuskarsa ta haskaka kamar rana, kuma rigunansa suka yi kyalli kamar haske.
Musa da Iliya sun bayyana sun kuma yi magana da Yesu.
Bitrus ya so ya yi bukkoki uku domin mutane ukun.
Murya daga girgijen ya ce, "Wannan ne ƙaunattacen Ɗana, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi."
Yesu ya umarce almajiran cewa kada su fada wa kowa wahayinsu, sai Ɗan Mutum ya tashi daga matattu.
Yesu ya cewa hakika, Iliya zai zo ya maido da dukan abubuwa.
Yesu ya ce Yahaya mai Baftisma ne Iliya wanda ya rigaya zo, kuma sun yi masa abin da sun gadama.
Almajiran ba su iya sun warkad da yaro mai farfadiyan ba.
Yesu ya tsauta wa aljanin, sai Yaron ya warke nan take.
Yesu ya faɗa cewa saboda ƙanƙancin bangaskiyar su ne ya sa basu iya warkad da yaro mai farfadiyan ba.
Yesu ya gaya wa almajiransa cewa za a bada shi ga hannun mutanen da za su kashe shi, kuma zai tashi a rana ta uku.
Yesu ya ce wa Bitrus ya je teku, ya jefa taru, ya kuma jawo kifin da ta fara zuwa, wanda za ta zo da shekel a bakinta domin haraji.
1 Daidai wannan lokacin, almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, "Wanene mafi girma a mulkin sama?" 2 Sai Yesu ya kira karamin yaro gunsa, ya sa shi a tsakaninsu, 3 ya ce, "Hakika ina gaya maku, idan baku juya kun zama kamar kananan yara ba, babu yadda zaku shiga mulkin sama. 4 Saboda haka, duk wanda ya kaskantar da kansa kamar karamin yaron nan, shi ne mafi girma a mulkin sama. 5 Duk wanda ya karbi karamin yaro a suna na, ya karbe ni. 6 Amma duk wanda ya sa daya daga cikin 'yan yaran nan da suka gaskanta da ni zunubi, gwamma a rataya dutsen nika a wuyansa a jefa shi cikin zurfin teku. 7 Kaiton duniya saboda lokacin tuntube! Lallai ne wadannan lokuta su zo, amma kaiton mutumin da ta wurinsa ne wadannan lokutan za su zo! 8 Idan hannunka ko kafarka ce za ta sa ka tuntube, ka yanke ta, ka yar daga gare ka. Zai fi maka kyau ka shiga rai da nakasa ko gurguntaka, da a jefa ka cikin madawwamiyar wuta tare da hannayenka ko kafafunka. 9 Idan idonka zai sa ka tuntube, ka kwakule shi, ka yar. Zai fi maka kyau ka shiga rai da ido daya, da a jefa ka cikin madawwamiyar wuta da idanu biyu. 10 Ku kula fa kada ku rena kananan nan. Domin koyaushe a sama, mala'ikunsu na duban fuskar Ubana da ke sama. 11[1]12 Menene tunaninku? Idan mutum na da tumaki dari, sa'annan daya ta bata, ashe ba zai bar tassa'in da tara a gefen tudu ya tafi neman wadda ta bata ba? 13 In ya same ta, hakika ina gaya maku, farin cikinsa na samun dayan nan da ta bace, zai fi na tassa'in da taran nan da basu bata ba. 14 Hakanan fa, ba nufin Ubanku dake sama ba ne da ya daga cikin wadannan kananan ya hallaka. 15 Idan dan'uwanka yayi maka laifi, fada masa tsakaninku, kai da shi kadai. Idan ya saurare ka, ka maido da dan'uwanka kenan. 16 Amma in ya ki ya saurare ka, ka je da 'yan'uwa biyu ko uku su zama shaidu, don ta wurin shaidu biyu ko uku ake tabbatar da kowacce kalma. 17 In kuma ya ki ya saurare su, ka kai lamarin ga ikklisiya. Idan ya ki ya saurari ikklisiya, ka maishe shi ba'al'umme da mai karbar haraji. 18 Hakika ina gaya maku, duk abin da kuka daure a duniya, a daure yake a sama. Abin da kuka kwance kuma, a kwance yake a sama. 19 Kuma ina gaya maku, idan mutum ku biyu zaku yarda akan duk abin da zaku roka, Ubana wanda ke a sama zai yi maku shi. 20 Wurin da mutum biyu ko uku suka taru a cikin sunana, zan kasance tare da su." 21 Bitrus ya zo ya ce wa Yesu, "Ubangiji, sau nawa ne dan'uwana zai yi mani laifi in gafarta masa? Har sai ya kai sau bakwai?" 22 Yesu ya amsa ya ce masa, "Ban gaya maka sau bakwai ba, amma bakwai din ma har sau saba'in. 23 Saboda haka, za a kwatanta mulkin sama da wani sarki da yake so ya lisafta dukiyarsa dake a hannun barorinsa. 24 Da ya fara yin haka, sai aka kawo masa daya daga cikin barorinsa da yake binsa talanti dubu goma. 25 Amma tunda ba shi da abin biya, ubangidansa ya bada umurni a sayar da shi, tare da matarsa da 'ya'yansa da duk mallakarsa, domin a biya. 26 Sai baran ya fadi kasa, ya rusuna a gaban ubangidansa ya ce, "Maigida, kayi mani hakuri, zan biya duk abin da na karba." 27 Don haka ubangidansa yayi juyayi, sai ya ce, ya yafe bashin, a saki baran. 28 Amma bayan an saki wannan baran, ya je ya sami wani baran kamar sa da yake bi bashin dinari dari. Ya cafke shi, ya shake shi a wuya, ya ce, 'Ka biya bashin da nake bin ka.' 29 Amma dan'uwansa bara ya roke shi ya ce, kayi mani hakuri, zan biya ka duk abinda na karba.' 30 Amma baran nan na farko ya ki. A maimakon haka, ya sa aka jefa dan'uwansa bara a kurkuku sai ya biya bashin nan. 31 Da sauran barori suka ga abin da ya faru, suka damu kwarai. Sai suka je suka fada wa ubangidansu yadda abin ya faru duka. 32 Sai ubangidansa ya kirawo shi, ya ce masa, "Kai mugun bawa, na gafarta maka bashin nan duka, domin ka roke ni. 33 Ashe, bai kamata kaima ka nuna jinkai ga dan'uwanka bara kamar yadda na nuna maka jinkai ba?' 34 Ubangidansa yayi fushi, ya danka shi ga masu azabtarwa, har sai ya gama biyan dukan bashin da ake binsa. 35 Hakanan Ubana dake a sama zai yi maku, idan kowannenku bai gafarta wa dan'uwansa daga zuciya ba."
Wannan itace farkon labarin da ya maimaiye littafin Matta [18:35] inda Yesu yake koyarwa game da rayuwa a cikin mulkin sama. Anan, Yesu yana amfani ne da karamin Yaro a koyaswan shi ga almajiran.
"Wanene mafi muhimmanci" ko kuma "Wanene a cikinmu mafi muhimmanci"
Jimlar nan "mulkin ssama" na nufin sarautar Allah a matsayinsa na sarki. An yi amfani da wannan jimlar a littafin Matta ne kadai. In ya yiwu, ku bar "sama" a naku juyin. AT: "a mulkin Allah" ko kuma "yayin da Allahn mu na sama zai kafa mulkinsa a duniya"
"Ina gaya maku gaskiya." Wannan na kara nanata magan Yesu da ke biya baya ne.
AT: "sai kun canza ... kananan yara kamun ku shiga"
Yesu yana amfani ne da wannan karin magana ya koya wa almajiransa cewa kada su damu da zancen wanene mafi muhimmanci. Sai dai su damu da zancen wanene ke kaskatar da kansa kamar karamin yaro.
Jimlar nan "mulkin sama" na nufin sarautar Allah a matsayin sa na sarki. An yi amfani da wannan jimlar a littafin Matta ne kadai. In ya yiwu, ku bar "sama" a naku juyin. AT: "shiga mulkin Allah" ko kuma "zama da Allahn mu a sama yayin da ya kafa mulkinsa a nan duniya" (Dubi: )
Yesu ya cigaba da koya wa almajiransa muhimmancin zama da kaskanci kamar karamin yaro idan suna so su zama da girma a mulkin Allah.
"shi ne mafi muhimmanci" ko kuma "zai zama mafi muhimmanci"
A nan "suna na" na nufin mutum gabaɗaya. AT: "saboda ni" ko kuma "saboda shi almajiri na ne"
Yesu yana nufincewa daidai ne da marabtansa. AT: "Yayin da wani ... a suna na, yana daidai kamar yana marabta na ne" ko kuma "Yayin da wani ... a suna na, kamar yana marabta na ne"
AT: "in wani ya sa masa dutsen niƙa a wuyansa ya jefa shi cikin teku mai zurfi"
Wannan babban mulmulallen dutse ne, mai nauyi, da ake niƙa hatsi zuwa gari da ita. AT: "wata dutse mai nauyi"
A nan "duniya" na nufin mutane. AT: "mutanen duniya"
A nan "tuntuɓe" karin magana ne da ke nufin zunubi. AT: "abubuwan da ke sa mutane zunubi ... abubuwa za su zo da za su sa mutane su yi zunubi ... duk wanda ya sa wasu su yi zunubi"
Yesu ya yi wannan maganada karfi domin yă nanata cewa lallai ne mutane su yi komen da yakamata domin su kawas da zukatansu daga duk abinda ke sa su zunubi.
Yesu yana maganar mutane ne gabaɗaya. Zai fi ɗacewa harshenku ta juya wannan yadda za ta nuna cewa mutane masu yawa ne "ka" ɗin.
"cikin rai madawami"
AT: "da ka zama da hannayenka da kafafunka yayin da Allah ke jefa ka cikin madawwamiyar wuta"
Umarnin kwalkwale idon, wadda mai yiwuwa shi ne gabar jiki mafi muhimmanci, na iya zama kururuta magane ne kawai ga masu sauraronsa cewa su yi komai da yakamata domin su yi nesa da duk wani abu a rayuwarsu da ke sa su zunubi.
A nan "tuntuɓe" ƙarin magana ne da ke nufin zunubi. AT: "ke sa ka zunubi"
AT: "da ka kasance da idanuka biyu yayin da Allah ke jefa ka cikin madawwamiyar wuta"
"Ku yi hankali" ko kuma "Ku tabbatar cewa"
"kada ku ɗauki waɗannan kananan da rashin muhimmanci." AT: "ku ba waɗannan kananan nan girma"
Wannan na ƙara nanata maganar Yesu da ke biyo baya ne.
Malaman Yahudawa suna kayar da cewa mala'iku mafi muhimmanci ne kawai suna iya kasancewa a gaban Allah. Yesu kuma yana nufin cewa mala'iku mafi muhimmanci suna magana da Allah akan waɗannan kananan nan.
Wannan wata karain magana ne da ke nufin cewa suna gaban Allah. AT: "suna kusa da Ubana a kodayaushe" ko kuma "suna gaban Ubana a kodayaushe"
Wannan wata lakaɓi ne mai muhimmanci da ke bayyana ɗangartakan da ke tsakanin Allah da Yesu.
Yesu yana amfani da wannan tambayan ne domin ya jawo hankalin jama'a. AT: "Ku yi tunanin yadda mutane ke yin." ko kuma "Ku yi tunanin wannan"
...
Yesu yana amfani ne da misalai yă koya wa almajiransa.
"100 ... 99"
Yesu yana amfani ne da wannan tambayan ya koya wa almajiransa. AT: "zai riƙa barin ... băta ba"?
Ubanku da ke sama ba ya son ɗaya daga cikin waɗannan kananan nan ya mutu" ko kuma "Ubanku da ke sama ba ya son ko ɗaya daga cikin waɗannan kananan ya mutu"
Wannan wata lakaɓi ne mai muhimmanci na Allah.
Wato ɗan'uwanka a bin Allah kenan, ba wai na ciki ɗaya ba. AT: "ɗan'uwanka mai bi"
"ka sa ɗangartakanka da ɗan'uwanka ya yi kyau kenan kuma"
A nan "bãki" da "kalma" na nufin abinda mutum ya faɗa. AT: "don mutm biyu ko uku su tabbatar cewa abin nan da ka faɗa game da ɗan'uwanka gaskiya ne"
"In ɗan'uwanka mai bi ya ƙi yă saurare shaidun da suka zo tare da kai"
"taron masubi gabaɗaya"
"ka bi da shi kamar yadda za ka bi da Ba'alumme ko mai karɓar haraji." Wannan na nufin cewa a cire shi daga taron masubi.
...
Wannan wata karin magana ne da ke nufin cewa Allah na Sama zai amince da abinda almajiransa suka amince da shi ko sun haramta a duniya. Duba yadda kuka juya irin wannan jimlar a [16:19]
AT: "Allah zai ɗaure ... Allah zai kwance"
Wannan yana ƙara nanata maganar Yesu da zai biyo baya kenan.
Ana ɗaukan cewa Yesu na nufin "idan a kalla mutum biyu" ko kuma "in ku biyu ko fiye."
Wannan na nufin "ku biyu." AT: "ku ... ku"
Ana ɗaukan cewa Yesu na nufin "biyu ko fiye" ko kuma "a kalla mutum biyu"
"haɗu"
"sau 7"
Wannan na iya nufin 1) 70 sau 70" ko kuma 2) "sau 77." Idan amfani da lamba zai kawo rikicewa, kuna iya jya shi kamar "sau fiye da iya lisafin da kuka iya yi" ko kuma "lallai ne ku yi ta gafarta masa"
Wannan na gabatar da wata misali ne. Duba yadda kuka juya irin wannan gabatar da misalin a [13:24]
"barorinsa su biya bashin da ake binsu"
AT: "sai wani ya kawo ɗaya daga cikin barorin sarkin"
"talanti 10,000" ko kuma "kuɗi mai yawa da bawan ba zai iya biya ba"
AT: "saikin ya umarci barorinsa su sayar da mutumin ... domin a biya bashin da kuɗin da aka samu"
Wannan na nuna cewa baran ya zo gaban sarkin a wata hanya da ta fi nuna kaskanci.
"a gaban sarkin"
"ya ji tausayin baran"
"a bar shi ya tafi"
"dinari 100" ko kuma "ladan aikin kwana ɗari"
"Bara na farkon ya shaƙe ɗan'uwansa bara"
"ya cafke shi" jo kuma "ya riƙe shi"
Wannan na nuna cewa baran ya zo gaban sarkin a wata hanya da ta fi nuna kaskanci.Duba yadda kuka juya wannan a [18:26].
...
"bawa na farkon ya je ya sa aka jefa ɗan'uwansa bawa a kurkuku"
"sauran barorin"
"faɗa wa sarkin"
"Sai sarkin ya kirawo bara na farkon"
...
Sarkin yana amfani ne da wannan tambayan yana yi masa sawa. AT: "Ai da ka ...maka ...!"
"Sarkin"
"ya miƙa shi." Akwai sammani ko sarkin ne ya ɗauke bara na farin zuwa ga waɗanda za su azabce shi." AT: "ya umarci barorinsa su danka shi"
"ga waɗanda za su ba shi azaba"
AT: "da sarkin ke bin bara na farkon
Wannan wata laƙani ne mai muhimmanci da ke bayyana ɗangantakan da ke tsakanin Allah da Yesu.
Yesu yana magana ne da almajiransa, amma misalin sa yana koyar da gamammaiyar gaskiya da ya shafe dukkan masubi.
A nan "zuciya" na nufin tunanin da ke cikin mutum. Jimlar nan "daga zuciya" karin magana ne da ke nufin da "gaske." AT: "da gaske" ko kuma "gabaɗaya"
Yesu ya ce ɗole mu tuba mu kuma zama kamar ƙananan 'yara don mu shiga mulkin sama.
Yesu ya ce duk wanda ya kaskantar da kansa kamar karamin yaron, shi ne mafi girma a mulkin sama.
Duk wanda ya sa daya daga cikin 'yan yaran nan da suka gaskanta da Yesu yin zunubi zai gwammaci a rataya dutsen nika a wuyansa a jefa shi cikin teku.
Yesu ya ce ɗole mu jefar da duk abin da ke sa mu tuntube.
Kada mu rena kananan yara domin mala'ikunsu na duban fuskar Uba kullum.
Ba kuma nufin Uba ne wadannan kananan su hallaka ba.
Farko, ka je ka nuna masa laifinsa tsakaninka, da shi kadai.
Na biyu, ka je da 'yan'uwa biyu ko fiye don shaidu.
A karshe, idan ya ki ya saurari ikklisiya, ka maishe shi ba'al'umma da mai karbar haraji.
Na uku, ka kai lamarin ga ikklisiya.
Yesu ya yi alkawari cewa zai kasance tare da biyu ko uku da sun taru a sunarsa.
Yesu ya ce mu gafarta wa ɗan'uwarmu so bakwai har sau saba'in.
Maigidan na bin bawarsa talanti dubu goma, wanda bai iya biya ba.
Ubangidansa ya ji tausayinsa, sai ya yafe bashin bawan.
Bawan ya ƙi ya yi hankuri sai ya jefa dan'uwansa bara a kurkuku.
Maigidan ya ce wa bawan cewa da ya nuna jinkai ga dan'uwansa bara.
Maigidansa ya danka shi ga masu azabtarwa, har sai ya gama biyan dukan bashin da ake binsa.
Yesu ya ce Uba zai yi mana kamar yadda maigidan ya yi wa bawan idan ba mu gafarta wa ɗan'uwarmu daga zuciya ba?
1 Sai ya zama sa'adda Yesu ya gama wadannan maganganu, sai ya bar Galili ya zo kan iyakokin Yahudiya, ketaren kogin Urdun. 2 Taro mai yawa suka bi shi, ya kuma warkar da su a wurin. 3 Farisawa suka zo wurinsa, suna gwada shi, suka ce masa, "Ya hallata bisa ga doka mutum ya saki matarsa don kowanne dalili?" 4 Yesu ya amsa ya ce, "Baku karanta ba, cewa shi wanda ya yi su tun farko ya yi su miji da mace? 5 Shi wanda ya yi su kuma ya ce, "Saboda wannan dalilin, mutum zai rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya hade da matarsa, su biyun su zama jiki daya?" 6 Su ba biyu ba ne kuma, amma jiki daya. Don haka, duk abin da Allah ya hada, kada wani ya raba." 7 Sai suka ce masa, "To me yasa Musa ya umarcemu mu bada takardar saki, mu kuma kore ta?" 8 Sai ya ce masu, "Saboda taurin zuciyarku, shi yasa Musa ya yarda maku ku saki matanku, amma da farko ba haka yake ba. 9 Ina gaya maku, duk wanda ya saki matarsa in ba saboda zina ba, ya kuma auri wata, yana zina kenan. Wanda kuma ya auri macen da aka saka, yana aikata zina." 10 Almajiran suka ce wa Yesu, "Idan haka yake game da mutum da matarsa, ba kyau ayi aure ba." 11 Amma Yesu yace masu, "Ba kowa ne zai karbi wannan koyarwa ba, amma sai wadanda an yardar masu su karbe ta. 12 Akwai wadanda aka haife su babanni. Akwai wadanda mutane ne suka maida su babanni. Sa'annan akwai wadanda sun mayar da kansu babanni saboda mulkin sama. Duk wanda zai iya karbar wannan koyarwa, ya karba." 13 Sai aka kawo masa yara kanana don ya dibiya hannuwansa akansu, yayi masu addu'a, amma almajiran suka kwabe su. 14 Amma Yesu ya ce masu, "Ku bar yara kanana, kada ku hana su zuwa wuri na, domin mulkin sama na irinsu ne." 15 Ya sa hannuwa akan su, sa'annan ya bar wurin. 16 Sai wani mutum ya zo wurin Yesu, ya ce, "Malam, wanne ayyuka nagari ne zan yi domin in sami rai madawwami?" 17 Yesu ya ce masa, "Me yasa kake tambaya ta game da abin da ke nagari? Daya ne kawai ke nagari, amma idan kana so ka shiga cikin rai, ka kiyaye dokokin." 18 Mutumin ya ce masa, "Wadanne dokokin?" Yesu ya ce masa, "Kada kayi kisa, kada kayi zina, kada kayi sata, kada kayi shaidar zur, 19 ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma ka kaunaci makwabcinka kamar kanka." 20 Saurayin nan ya ce masa, "Ai na kiyaye duk wadannan. Me nake bukata kuma?" 21 Yesu ya ce masa, "Idan kana so ka zama cikakke, ka tafi ka sayar da mallakarka, ka kuma ba matalauta, zaka sami dukiya a sama. Sa'annan ka zo ka biyo ni." 22 Amma da saurayin nan ya ji abin da Yesu ya fada, ya koma da bakin ciki, domin shi mai arziki ne kwarai. 23 Yesu ya ce wa almajiransa, "Hakika ina gaya maku, zai zama da wuya mai arziki ya shiga mulkin sama. 24 Ina sake gaya maku, zai fi wa rakumi sauki ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah." 25 Da almajiran sun ji haka, suka yi mamaki kwarai da gaske, suka ce, "Wanene zai sami ceto?" 26 Yesu ya dube su, ya ce, "A wurin mutane wannan ba zai yiwu ba, amma a wurin Allah, kome mai yiwuwa ne." 27 Sai Bitrus ya amsa ya ce masa, "Duba, mun bar kome da kome mun bi ka. To me za mu samu?" 28 Yesu ya ce masu, "Hakika ina gaya maku, ku da kuka bi ni, a sabuwar haihuwa, lokacin da Dan Mutum ya zauna a kursiyin daukakarsa, ku ma zaku zauna a kursiyoyi goma sha biyu, kuna shari'anta kabilu goma sha biyu na Isra'ila. 29 Duk wanda ya bar gidaje, 'yan'uwa maza, 'yan'uwa mata, mahaifi, mahaifiya, 'ya'ya, ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkin su dari, ya kuma gaji rai madawwami. 30 Amma dayawa dake farko yanzu, za su zama na karshe, dayawa dake karshe kuma, su zama na farko.
Wannan ita ce farkon wata sabuwar sashin labarin da ta biyo [22:46] da ke maganar hidimar Yesu a Yahudiya.
Wannan jimlar yana canza labarin daga koyarwar Yesu zawa abinda ya faru nan gaba. AT: "Da" ko kuma "Bayan da"
A nan "maganganu" na nufin koyarwan da Yesu ya yi daga [18:1]. AT: "ya gama koyar da waɗannan abubuwa"
"ya tafi daga" ko kuma "ya tashi daga"
Yesu Ya fara koyarwa akan aure da saki.
"suka zo wurin Yesu"
A nan "gwada" ba domin alheri ba. AT: "sai suka sokane shi ta wurin tambayansa" ko kuma "suna son su yi masa tarko ta hanyar yi masa tambaya"
Yesu yana amfani ne da wannan tambayan don yă tunashe Farisiyawan da abinda nassosin suka ce game da miji, mace, da kuma aure. AT: "Hakika kun karanta, cewa tun farko da Allah ya hallici mutane, ya hallice su miji da mace."
Wannan shi ne abinda Yesu yana sammanin Farisawa sun fahimta daga nassi. AT: "kuna haƙĩƙa kun sani cewa Allah ma ya faɗi cewa don wannan dalilin ... jiki"
Wannan sashin labarin daga littafin Farawa ne dame da Adamu da Hauwa'u. A wannan wurin, dalilin da namiji zai bar Ubansa da Uwatasa shi ne domin Allah ya hallici mace ta zama abokiyan tarayyan sa.
"ya zama kusa da matarsa" ko kuma "ya zauna da matarsa"
Wannan wata karin magana ne da ke nanata ɗayantakar mai gida da uwargida. AT: "za su zama kamar mutum ɗaya"
Wannan wata ƙarin magana ne da ke nanata ɗayantakar mai gida da uwargida. AT: "Don haka maigida da uwargida ba mutum biyu kuma ba, ammam suna kamar mutu m ɗaya ne"
"Farisiyawan sun ce wa Yesu"
"umarce mu Yahudawa"
Wannan wata takardar shaida ne da ke yanke raba aure bisa ga ka'ida.
Jimlar nan "taurin zuciya" ƙarin magana ne da ke nufin "taurin kai" AT: "Saboda taurin kan ku" ko kuma "Domin kuna da taurin kai"
Yesu yana magana da Farisawa ne, ammam Musa ya ba da wannan umarnin a shekaru da dama ne tun kakanninsu. Umarnin Musa ya shafe dukkan mutanen Yahudawa ne gabaɗaya.
Anan "farko" na nufin lokacin da Allah ya fara hallitan na miji da mace.
Wannan na kara nanata maganar Yesu da ya biyo baya ne.
Kuna iya kara haske a bayanin. AT: "auri wata mata"
Wasu rubuce-rubuce na dã basu haɗa waɗannan kalmomin ba.
AT: "waɗanda Allah ya bar su" ko kuma "waɗanda Allah ya izasu"
Kuna iya kara haske a wannan bayyani. AT: "Akwai dalilai daban daban da ya sa mutane basu aure. Ana misali, akawai maza da yawa da aka haife su babanni"
AT: "akawai waɗanda wasu mutane ne suka mayar da su babanni"
Wannan na iya nufin 1) mutanen da sun mayar da kansu babanni ta wurin cire gabansu" ko kuma 2) "mutanen da sun zaɓa su zama a rashin aure da kuma tsarkinsu a sashin jima'i
A nan "mulkin sama" na nufin sarautar Allah a matsayin sarki. Ana samun wannan jimlar a littafin Mata ne kawai. In ya yiwu, ku ba "sama" a juyin ku. AT: "don su fi iya bauta wa Allahn mu a sama"
"karɓa wannan koyarwa ... karɓe shi"
AT: "wasu mutane sun kawo wa Yesu yara kanana"
...
"kada ku hana su zuwa wurin na"
A nan "mulkin sama" na nufin sarautar Allah a matsayin sarki. Ana samun wannan jimlar a littafin Matta ne kadai. In Ya yiwu, sai ku bar "sama" a naku juyin. AT: "gama idan Allahn mu a sama ya kafa nasa sarautar a duniya, a bisa irin waɗannan" ko kuma "gama Allah yana barin irin waɗannan a cikin mulkinsa"
"na irin waɗanada su na kamar yara kanana ne." Wannan wata karin magana ne da ke nufin cewa waɗanda suna da kaskanci kamar yara kanana za su shiga mulkin Allah.
Wannan kalmar "ga shi" yana jan hankulan mu ne zuwa ga wani sabon mutum a labarin. Mai yiwuwa harshen ku ma da wata hanyar yin haka.
wato abinda ke gamsar Allah.
Yesu yana amfani da wannan tambayan gangancin ne domin ya ƙarfafa mutumin game da dalilinsa na tambayan Yesu game da abinda ke nagari. AT: "ka tambaye ni game da abinda ke nagari" ko kuma "Yi tunanin dalilin da ya sa ka yi mani tambaya akan abinda ke nagari"
"Allah ne kaway ke nagari gabakiɗaya"
"karba rai madawammi"
Mutanen Yahudawa sun gaskanta cewa makwabtansu ne kawai sauran Yahudawa. Yesu kuma yana faɗada wannan bayyani ya haɗa da dukkan mutane.
"idan kana marmari
AT: "waɗanda ke talakawa ne"
Jimlar nan "dukiya a sama" karin magana ne da ke nufin lada daga Allah. AT: "Allah zai baku lada daga sama"
"Ina gaya maku gaskiya." Wannan jimlar yana kara nanata maganar Yesu da zai biyo baya ne.
A nan "mulkin sama" na nufin sarautar Allah a matsayin sa na sarki. Ana samu wannan jimlar a littafin Matta ne kadai. In ya yiwu, ku bar "sama" a juyin ku. AT: "yă karɓa Allahnmu a sama a matsayin sarkinsu"
Yesu yana amfani ne da wannan kururtan ya kwatanta yadda ya ke da wuya wa mutum mai arziki yă shiga mulkin Allah.
ramin da ke kusa da ƙarshen allura, ta wurin da zaren ke bi
"almajiran suka yi mamaki." Ana ɗaukan cewa suka yi mamaki ne domin sun gaskanta cewa arziki alama ce cewa Allah ya amince da mutum.
Almajiran suna amfani ne da wannan tambayan don su nuna mamakinsu. AT: "To ai ba mutumin da Allah zai cetas!" ko kuma "To ai ba wanda zai samu rai madawammi!"
"mun bar duk dukiyoyiimu" ko kuma "mun yafe dukkan mallakarmu"
Wane abu nagari ne Allah zai bamu?
"a sabuwar lokaci." Wannan na nufin yayin da ya mai gyara dukkan kome. AT: a lokacin da Allah ya sa kome ya zama sabo"
Yesu na magana game da kansa ne.
Zama a kursiyinsa na nufin sarautar sa a matsayin sa na sarki. Kursiyinsa kuma ya zama da ɗaukaka na nufin sarautar sa ya zama da ɗaukaka. AT: "Yana zaune a kursiyinsa na ɗauka" ko kuma "yana sarauta da ɗaukaka a matsayin sarki"
A nan zama a kursiyoyi na nufin sarauta a matasyin sarakuna. Almajiran ba za su zama daidai da Yesu da shi ma ke bisa kursiyin ba. Za su karɓi iƙo daga wurinsa. AT: "zauna a matsayin sarakuna a bisa kursiyoyi 12"
A nan "kabilu" na nufin mutanen waɗannan kabilun. AT: "mutanen kabilu 12 na Isra'ila"
A nan "suna" na nufin mutumin gabaɗaya. AT: "saboda ni" ko kuma "domin ya gaskanta da ni"
"zai karɓa daga wurin Allah ninki 100 kamar iyakan nagargarin abubuwan da suka bari"
Wannan wata karin magana ne da ke nufin "Allah zai albarkace su da rai madawwami" ko kuma "Allah zi sa su rayu har abada."
A nan "farko" da "ƙarshe" na nufin matsayi ko muhimmancin mutane. Yesu yana banbanta matasyin mutane a yanzu da kuma matasyinsu a mulkin sama. AT: "Amma ma su yawa da sun na yi kamar suna da muhimmanci a yanzu za zama da mafi ƙanƙantan muhimmanci, kuma da yawa da suke yi kamar ba su da muhimmanci a yanzu za su zama da muhimmanci ƙwarai"
Farisawa sun tambaye Yesu cewa, ''Ya hallata bisa ga doka mutum ya saki matarsa don kowanne dalili?''
Yesu ya ce tun farkon halitta, Allah ya yi su miji da mace.
Yesu ya faɗa cewa sa'ad da miji ya sadu da matarsa, biyun sun zama jiki ɗaya.
Yesu ya faɗa cewa mutum zai rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya haɗe da matarsa.
Yesu ya ce kada mutum ya raba abin da Allah ya hada.
Yesu ya ce Musa ya umarce takardar saki saboda taurin zuciyar Yahudawa.
Yesu ya ce duk wanda ya saki matarsa in ba saboda zina ba, ya kuma auri wata, ya yi zina. Kuma mutumin da ya auri macen da aka saka, yana aikata zina.
Yesu ya faɗa cewa waɗanda an yardar masu su amince da zama babanni.
A loƙacin da an kawo yara kanana wa Yesu, almajiran suka ƙwabe su.
Yesu ya ce su bar yara kanana su zo, gamma mulkin sama na irinsu ne.
Yesu ya ce wa mutumin ya kiyaye dokokin don ya shiga rai madawami.
Da saurayin ya ce ya kiyaye dokokin, Yesu ya ce mashi ya sayar da abin da yake da shi ya ba wa talakawa.
Saurayin ya tafi da bakin ciki domin ya na da dukiya sosai.
Yesu ya faɗa cewa da mutane ba mai yiwuwa ba ne, amma da Allah, kome mai yiwuwa ne.
Yesu ya yi wa almajiransa alkawari cewa a sabuwar haihuwa, za su zauna a kursiyi goma sha biyu, za su yi hukunci wa kabilu goma sha biyu na Isra'ila.
Yesu ya ce waɗanda suke farko yanzu za su zama karshe, kuma waɗanda suke karshe yanzu za su zama farko.
1 Gama mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da asuba ya nemi 'yan kwadago da za su yi aiki a gonarsa. 2 Bayan sun shirya kudin da zai biya ma'aikata kimanin dinari daya a kowanne yini, sai ya aike su gonarsa suyi aiki. 3 Misalin sa'a ta uku sai ya sake fita, sai ya ga wasu ma'aikata suna tsaye a bakin kasuwa, babu aiki. 4 Sai ya ce masu, 'Kuzo kuyi aiki a gonar, duk abinda ya wajaba, zan ba ku,' Sai suka tafi su yi aikin. 5 Sai ya sake fita a sa'a ta shida ya kuma sake fita a sa'a ta tara, ya sake yin hakan din. 6 Ya kuma sake yin haka a sa'a ta sha daya, da ya fita sai ya ga wasu a tsaye da ba sa yin kome. Sai ya ce masu, 'Me yasa kuke tsaye ba ku yin kome dukan yini?' 7 Sai suka ce masa, 'Ai babu wanda ya dauke mu aiki, shi yasa.' Sai ya ce masu, 'ku ma, kuje cikin gonar. 8 Da yamma ta yi, sai mai gonar ya ce wa manajansa, 'Ka kira ma'aikatan nan ka biya su hakkin su, amma ka fara da wadanda suka zo a karshe, zuwa na farkon.' 9 Sa'adda wadanda suka fara aiki da yamma suka zo, an biya su daidai yadda ake biya a yini. 10 Da wadanda suka fara aiki tun safe suka zo, suna tsammani za a ba su fiye da wadanda sun zo daga baya, amma aka ba kowannensu dinari daya. 11 Da suka karbi hakkinsu, suka yi gunaguni game da mai gonar. 12 Suka ce, 'Wadannan da suka zo a karshe, sa'a guda ce kadai suka yi aiki, amma ka ba su daidai da mu, mu da muka yi fama da aiki cikin zafin rana.' 13 Amma mai gonar ya amsa wa daya daga cikin su, ya ce, 'Aboki na, ban yi maku laifi ba. Ai mun shirya zan biya ku yadda ake biya a yini, ko ba haka ba? 14 Ku karbi abin da ke na ku, ku tafi. Ganin dama ta ne, in ba wadannan da suka zo a karshe daidai da ku. 15 Ashe, ba daidai bane a gare ni, in yi abin da na ga dama da mallaka ta? Ko kishi ne kuke yi saboda kirki na?' 16 Haka yake, na karshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na karshe." [1]17 Da Yesu zai tafi Urushalima, ya dauki sha-biyun nan a gefe, yayin da suke tafiya, sai ya ce masu, 18 "Ku duba fa, zamu tafi Urushalima, kuma za a bada Dan Mutum ga manyan firistoci da marubuta. Za su kuma yanke masa hukuncin kisa, 19 za su kuma bada shi ga al'ummai don suyi masa ba'a, su bulale shi, su kuma gicciye shi. Amma a rana ta uku, za a tada shi." 20 Sai uwar 'ya'yan Zabadi ta zo wurin Yesu tare da 'ya'yanta. Ta rusuna a gabansa tana neman alfarma a wurinsa. 21 Yesu ya ce mata, Me kike so in yi maki?" Sai ta ce masa, "Ina so ka ba 'ya'yana izinin zama a mulkinka, daya a hannun damanka, daya kuma a hannun hagunka. 22 Amma Yesu ya amsa, ya ce, "Baku san abin da kuke roko ba. Ko zaku iya sha daga cikin kokon da zan sha bada dadewa ba?" Sai suka ce masa, "Zamu iya." 23 Sai ya ce masu, "In dai kokon nan da zan sha ne, lallai zaku sha. Amma, zama a hannun dama na da kuma hannun hagu na, ba ni ne mai bayarwa ba, amma na wadanda Uba na ya shirya domin su ne." 24 Sa'anda sauran almajirai goma suka ji haka, sun yi bacin rai da 'yan'uwan nan biyu. 25 Amma Yesu ya kira su wurin sa, ya ce, "Kuna sane da cewa, sarakunan al'ummai suna gwada masu mulki, manyan-gari kuma na nuna masu iko. 26 Ba zai kasance haka a tsakanin ku ba. A maimakon haka, duk wanda ke da marmari ya zama da girma a tsakanin ku, ya zama baran ku. 27 Wanda kuma ke da marmari ya zama na farko a cikin ku, ya zama baran ku. 28 Kamar dai yadda Dan mutum bai zo don a bauta masa ba, amma yayi bauta, ya kuma bada ransa fansa domin mutane dayawa." 29 Da suka fita daga Yariko, babban taro suka bi shi. 30 Suka kuma ga makafi biyu zaune a bakin hanya. Da makafin suka ji cewa Yesu ne ke wucewa, sai suka tada murya suna cewa, "Ya Ubangiji, Dan Dauda, kayi mana jinkai." 31 Amma jama'ar suka tsauta masu, suka ce suyi shiru. Duk da haka, makafin suka kara tada murya fiye da na da, suka ce, "Ya Ubangiji, Dan Dauda, kayi mana jinkai." 32 Sai Yesu ya tsaya cik, ya sa aka kira su, sai ya ce masu, "Me kuke so in yi maku?" 33 Sai suka ce masa, Ya Ubangiji, muna so mu sami ganin gari." 34 Sai Yesu yayi juyayi a cikin sa, ya taba idanunsu. Nan da nan, suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.
Yesu ya ba da misalin wani mai gona da ya ɗauki ma'aikata. Ya yi haka ne don ya ƙwatanta yadda Allah za sãka wa waɗanda suke 'yan mulkin sama.
Wannan itace farkon misalin. Duba yadda aka juya gabatarwar misalin a [13:24]
"Bayan da mai gonar ya yarda"
Kuɗin aikin kowane yini kenan a wancan lokacin. AT: "kuɗin yini ɗaya"
"sai ya aike su gonarsa su yi aiki"
"Mai gonar ya sãke fita"
Sa'a ta ukun shi ne misalin ƙarfe tara na safe.
"suna tsaye a bakin kasuwa ba su yin aikin kome" ko kuma "suna tsaye a bakin kasuwa ba aikin yi"
"wata babbar wuri ne, a tsarari kuma da mutane suna siya da sayar da abinci da sauran abubuwa.
"Sai mai gonar ya sake fita"
sa'a ta shida shi ne misalin tsakar rana. Sa'a ta tara shi ne misalin ƙarfe uku na rana.
Wato mai gonar ya sake zuwa bakin kasuwa ya ɗauke ma'aikata.
Wato a misalin ƙarfe biyar na yamma.
"ba su aikin kome" ko kuma "ba su da aiki"
Kuna iya kara hasken abinda ake nufi. AT: "fara da ma'ikatan da suka fara aiki a baya, sa'annan ma'aikatan da suka fara da ɗan lokaci, sai kuma a ƙarshe ma'aikatan da sun fara aiki tun farko" ko kuma "fara biyan ma'aikatan da na ɗauka a ƙarshe, sa'annan waɗanda na ɗauka a tsakar rana, sai kuma a ƙarshe na biya waɗanda na ɗauka da farko"
AT: "waɗanda mai gonar ya ɗake su aiki"
"Da ma'aikatan da suka yi aiki na tsawon lokaci mafi yawa suka karɓi"
"mai gonar innabi"
"ka biya su daidai kimanin kuɗin da ka biya mu"
Jimlar nan "fama cikin zafin rana" karin magana ne da ke nufin "aiki dukkan yini." AT: "mu da muka yi aiki dukkan yini, a lokaci mafi zafi ma"
"ɗaya daga cikin ma'aikatan da suka yi aiki na lokaci mafi yawa"
Ku yi amfani da kalmar da mutum zai yi amfani da shi idan yana magana da mutum da yake tsauta masa a hankali.
Mai gonar yana amfani ne da wannan tambayan don ya tsauta wa ma'aikatan da suna gunaguni. AT: "Ai mun riga mun shirya cewa zan biya ku dinari ɗaya ba."
Mai gonar yana amfani ne da wannan tambayan ya daidaita ma'aikatan da ke gunaguni. AT: "Ai zan iya yin duk abinda na ke so da mallaka ta"
Mai gonar yana amfani ne da wannan tambayan do ya tsauta wa ma'aikatan da suke gunaguni. AT: "Kada ku yi kishi sa'adda nake yin halin kirki ga sauran mutane."
A nan "farko" na nufin "ƙarshe" na nufin matsayin mutane ko kuma "muhimmanci. Yesu yana banbanta matsayin mutane a yanzu da kuma matsayin su a mulkin sama. Duba yadda kuka juya irin wannan jimlar a [19:30]. AT" Don haka, waɗanda suna kamar mara muhimmanci yanzu za su zama mafi muhimmanci, kuma waɗanda suke kamaar su ne mafi muhimmanci yanzu za su zama da kalilar muhimmanci"
Misalin ya kare a nan, Yesu kuma yana kan magana. AT: "Sai Yesu ya ce, 'haka yake, na ƙarshe za su zama na farko.'"
Urushalima yana bisa duwatsu ne, don haka mutane sukan haurowa sama ne zuwa wurin.
Yesu yana amfani ne da kalmar nan "Ku duba" don ya ce wa almajiransa, lallai ne su sa hankalinsu ga abinda zai faɗa masu.
A nan "mu" na nufin Yesu da almajiransa.
AT: "wani zai bada Ɗan mutum"
Yesu yana maganar kansa ne kamar wani mai saurara na uku ne. In ya zama lallai, kuna iya juya waɗannan zuwa mutum na fari.
"Babban firist ɗin da shugabannin shari'a za su yanke masa hukunci su bada shi ga al'ummai, sa'annan al'umman kuma za su ya wa Yesu ba'a.
"su zane shi" ko kuma "su yi masa duka da bulala"
"uku" na daidai bisa jerin kirge ne.
Kalmomin nan "a ta da shi" karin magana ne da ke nufin "zai rayu kuma." AT: "Allah za ta da shi" ko kuma "Allah zai ba shi rai kuma"
Wato Yakubu da Yahaya kenan.
Wato a matsayi mai girma, iƙo, da kuma daraja.
A nan "mulki" na nufin sarautar Yesu a matsaying sarki. AT: "yayin da kake sarki"
A nan "ku" na nufin uwar da 'ya'yan.
A nan "ku" na nufin 'ya'ya biyun. Kuma a yanzu dai Yesu yana magana da 'ya'ya biyun ne kawai.
A "sha kokon" ko kuma "sha daga kokon" karin magana ne da ke nufin a ɗanɗana azaba" AT: "sha azaban da zan sha"
"'Sai ya'yan Zabadi suka ce masa" ko kuma "Yakubu da Yahaya suka ce masa"
A "sha kokon" ko kuma "sha daga kokon" karin magana ne da ke nufin a ɗanɗana azaba." AT: "Lallai fa za ka sha azaba kamar yadda zan sha azaba"
Wato a matsayi mai girma, iƙo, da kuma daraja. Duba yadda kuka juya wannan a [20:21]
AT: "Ubana ne ya shirya waɗannan wuraren, kuma shi ne za ba wa duk waɗanda ya zaɓa"
Wannan wata lakani ce mai muhimmanci da ke bayyana ɗangartakar da ke tsakanin Allah da Yesu.
"suka ji abinda Yakubu da Yahaya suke tambayan Yesu"
Idan ya zama lallai, kuna iya kara bayanin dalilin bacin rai na almajirai goma. AT: "suna bacin rai da 'yan'uwan nan biyu domin kowannensu ma na son su zauna a wuri mai dararja kusa da Yesu"
"ya kira almajirai sha biyun"
"sarakunan al'ummai suna mulki a bisa mutanensu da ƙarfi"
"manyan gari a cikin al'ummai"
"suna mulkin mutanen"
"duk mai so" ko kuma "duk wanda ke marmari"
"yă zama farko"
Yesu yana maganar kansa ne kamar da wani na uku yake yi. Idan ya zama lallai, kuna iya juya wannan zuwa mutum na farko
AT: "bai zo don sauran mutane su bauta masa ba" ko kuma "ban zo don sauran mutane su bauta mini ba"
Kuna iya karin bayyanin abinda aka fahimta da wannan maganan. AT: "amma ya bauta wa mutane"
Ran Yesu "domin mutane" karin magana ne da ke nufin hukuncinsa don ya ceci mutane daga hukuncin zunubansu. AT: "ya ba da ransa a maimakon na mutane" ko kuma "ya da da ransa domin ya ceci mutane masu yawa"
Mutum yă ba da ransa karin magana ne da ke nufin mutum yă zaba ya mutu, sau da dama ana haka ne domin a ceci mutane. AT: "ya mutu"
...
Wato almajiran da Yesu kenan.
"suka bi Yesu"
Akan iya juya wannan zuwa "Sai, da wasu makafai biyu a zaune." Matta na jan hankalin mu ne zuwa ga sabobin mutane a labarin. Mai yiwuwa harshen ku na da wata hanya ta musamman na yin haka.
"Da suka ji"
"ke wuce kusa da su"
Yesu ba ɗan Dauda bisa ga jiki ba ne, don haka, anan iya juya wannan zuwa "Ɗan zuriyar Sarki Dauda." Ko da shike, "Ɗan Dauda" ma wata lakaɓi ce da Almasihu, kuma mai yiwuwa mutanen suna kiran shi ne da wannan lakaɓin.
"aka kira makafin"
...
Saboda tambayan da Yesu ya yi dama, muna fahimtar cewa suna furta abinda suke so ne. AT: "muna so ka buɗe idanun mu" ko kuma "muna so mu iya gani"
"cike da tausayi" ko kuma "ya ji tausayinsu"
Mai gonar ya amince zai biya ma'aikatan da ya ɗauke su aiki da safiya dinarus ɗaya.
Mai gonar ya ce zai biya su duk abin da ya dace.
Ma'aikatan da an ɗauke su aiki a sa'a ta sha ɗaya sun karbi dinarus ɗaya.
Sun yi gunaguni cewa sun yi aikin duka rana amma sun karbi biya ɗaya da waɗanda sun yi aikin sa'a ɗaya.
Mai gonar ya ce bai yi masu laifi ba kuma ya ba su hakinsu.
Yesu ya faɗa wa almajiransa cewa za a bada Ɗan Mutum ga manyan firistoci da marubuta, za a kuma yanke masa hukuncin kisa, su kuma gicciye shi, kuma a rana ta uku, zai tashi.
Ta so Yesu ya umarta cewa 'ya'yan ta biyu su zauna a hannun dama da hagu a mulkin.
Yesu ya ce Uba ya shirya waɗannan wurare ga wanda ya zaɓa.
Yesu ya ce duk wanda ke son ya zama na farko ɗole ya zama bawa.
Yesu ya ce ya zo ne domin ya yi bauta ya kuma bada ransa fansa domin mutane dayawa.
Makafi biyun suka daga murya da cewa, Ya Ubangiji, Ɗan Dauda, kayi mana jinkai.''
Yesu ya warkad da makafi biyu domin ya ji tausayi.
1 Yayinda Yesu da almajiransa suka kusato Urushalima sai suka zo Betafaji wajen dutsen zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa guda biyu, 2 yace masu, "Ku shiga kauyen da yake gaban ku zaku iske wata jaka da aholaki tara da ita. Ku kwance su ku kawo mani su. 3 Idan wani ya gaya maku wani abu game da haka, sai ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsu,' mutumin kuwa zai aiko ku da su nan da nan." 4 Anyi wannan kuwa domin a cika annabcin anabin. Yace, 5 "Ku cewa diyar Sihiyona, duba, ga sarkinki na zuwa wurin ki, mai tawali'u ne, kuma akan jaki wanda aholaki ne." 6 Sai almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su. 7 Suka kawo jakar da dan aholakin, suka sa tufafinsu akai, Yesu kuwa ya zauna akan tufafin. 8 Yawancin jama'a kuwa suka baza tufafinsu akan hanya, wasu kuma suka yanko ganye daga bishiyoyi suka shimfida su a hanya. 9 Taron jama'a da suke gabansa da wadanda suke bayansa, suka ta da murya suna cewa, "Hossana ga dan Dauda! mai albarka ne shi wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Hossana ga Ubangiji!" 10 Sa'adda Yesu ya shiga Urushalima sai doki ya cika birnin ana cewa, "Wanene wannan?" 11 Sai jama'a suka amsa, "Wannan shine Yesu annabi, daga Nazaret ta Galili." 12 Sai Yesu ya shiga haikalin. Ya kori duk wadanda ke saye da sayarwa a cikin ikiilisiya. Ya birkice teburan masu canjin kudi da kujerun masu sayar da tantabaru. 13 Ya ce masu, "A rubuce yake, 'Za a kira gidana gidan addu'a,' amma kun mayar dashi kogon 'yan fashi." 14 Sai makafi da guragu suka zo wurin sa a haikalin, ya warkar da su. 15 Amma da manyan firistoci da malaman attaura suka ga abubuwan banmamaki da yayi, kuma sa'adda suka ji yara suna tada murya a cikin haikalin suna cewa, "Hossana ga dan Dauda," sai suka ji haushi. 16 Suka ce masa, kana jin abinda wadannan mutanen ke fadi?" Yesu ya ce masu, "I! Amma ba ku taba karantawa ba, 'daga bakin jarirai da masu shan mama ka sa yabo'?" 17 Sai Yesu ya bar su, ya fice daga birnin zuwa Betaniya ya kwana a wurin. 18 Washegari da safe yayin da yake komawa birnin, sai yaji yunwa. 19 Da ya ga bishiyar baure a bakin hanya, sai yaje wurin amma bai sami kome ba sai dai ganye. Sai ya ce mata, "Kada ki kara yin 'ya'ya har abada." Sai nan take bishiyar bauren ta bushe. 20 Da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suka ce, "Kaka bishiyar bauren ta bushe nan da nan?" 21 Yesu ya amsa yace masu, "Hakika ina ce maku, in dai kuna da bangaskiya ba ku yi shakka ba, ba abinda aka yi wa bauren nan kadai za kuyi ba har ma za ku cewa tsaunin nan, "Ka ciru ka fada teku,' sai kuwa haka ta kasance. 22 Kome kuka roka cikin addu'a, in dai kun gaskanta, za ku samu." 23 Sa'adda Yesu ya shiga haikalin, sai manyan fristocin da shugabannin jama'a suka zo suka same shi yayin da yake koyarwa, suka ce, "Da wane iko kake yin wadannan abubuwa?" 24 Yesu ya amsa yace masu, "Ni ma zan yi maku tambaya daya. In kun fada mani, ni ma zan fada maku ko da wane iko nake yin wadannan abubuwa. 25 Daga ina baftismar Yahaya ta fito, daga sama ko kuma daga mutune?" Sai suka yi shawara a tsakanin su, suka ce, "In munce, 'daga sama,' zai ce mana, 'don me bamu gaskanta dashi ba?' 26 Amma in munce, ' daga mutune,' muna tsoron jama'a, saboda sun san Yahaya annabi ne." 27 Sai suka amsa ma Yesu suka ce, "Bamu sani ba." Shi ma yace masu, "Nima bazan gaya maku ko da wane iko nake yin abubuwan nan ba. 28 Amma me kuke tunani? Wani mutum yana da 'ya'ya biyu. Ya je wurin na farkon yace, 'Da, je ka kayi aiki yau a cikin gona.' 29 Yaron ya amsa yace, 'bazan yi ba,' amma daga baya ya canza tunaninsa ya tafi. 30 Sai mutumin ya je wurin da na biyun ya fada masa abu guda. Wannan dan ya amsa ya ce, 'zanje, baba,' amma bai je ba. 31 Wanene a cikin 'ya'ya biyun nan yayi nufin ubansa?" Suka ce, "na farkon." Yesu ya ce masu, "Hakika ina gaya maku, masu karbar haraji da karuwai za su shiga mulkin Allah kafin ku. 32 Gama Yahaya ya zo maku a hanyar adalci, amma ba ku gaskata da shi ba, a yayinda masu karbar haraji da karuwai suka gaskata da shi. Ku kuwa, bayan kun ga abin da ya faru, baku ma tuba daga baya ba don ku gaskata da shi. 33 Ku saurari wani misalin. Anyi wani mutum, mai gona. Yayi shuka a gonar, ya shinge ta, ya gina ramin matse inabi a cikin gonar, ya kuma gina wata hasumiyar tsaro, sai ya bada hayar gonar ga wadansu manoma. Sai ya tafi wata kasa. 34 Da kakar inabi ta yi, sai ya aiki wadansu bayi su karbo masa amfanin gonar. 35 Amma manoman suka kama bayin, suka doddoki dayan, suka kashe dayan, suka jejjefe dayan da duwatsu. 36 Sai mai gonar ya sake aika wadansu bayinsa da suka fi na farko, amma manoman suka yi masu kamar yadda suka yi wa sauran. 37 Bayan wannnan, sai mai gonar ya aika da dansa wurin su yana cewa, 'za su yi wa dana biyayya.' 38 Amma da manoman suka ga dan, sai suka ce a tsakanin su, 'wannan shine magajin. Kuzo, mu kashe shi mu gaji gonar.' 39 Sai suka dauke shi, suka jefar da shi daga cikin gonar, suka kashe shi. 40 To idan me gonar ya zo, me zai yiwa manoman? 41 Suka ce masa, "Zai hallaka mugayen manoman nan ta hanya mai tsanani, zai kuma bada gonar haya ga wadansu manoman, mutanen da za su biya, lokacin da inabin ya nuna." 42 Yesu yace masu, "Baku taba karantawa a nassi ba," 'Dutsen da magina suka ki ya zama dutse mafi amfani. Wannan daga Ubangijine, kuma abin mamaki ne a idanunmu?' 43 Saboda haka ina gaya maku, za a karbe mulkin Allah daga wurin ku a ba wata al'umma da zata bada amfaninsa. 44 Duk wanda ya fadi akan dutsen nan zai ragargaje. Amma duk wanda dutsen ya fadawa, zai nike." 45 Da manyan firistocin da farisawan suka ji wannan misalin, sai suka gane da su yake. 46 Da suka nemi kama shi, sai suka ji tsoron taron, saboda mutanen sun dauke shi annabi.
Wannan ne mafarar labarin shigar Yesu a Urushalima. Anan ya ba wa almajiransa umurni game da abin da za su yi.
Wannan kawye ne da ke kusa da Urushalima.
AT: "jakin da wani ya ɗaura"
Za ku iya bayyana yadda an ɗaura jakin. AT: "a ɗaure a wurin, a kan itace"
ƙaramin jaki
A nan, marubucin ya faɗi abin da annabi Zechariah ya ce domin ya nuna cewa Yesu ya cika annabcin ta wurin hawan jaki zuwa Urushalima.
An yi amfani da wannan kalma anan domin a sa alama a ainahin labarin. Matthew ya bayyana yadda ayukan Yesu ya cika nassi.
AT: "wannan ya faru ne domin Yesu ya cika abin da Allah ya faɗa ta wurin annabi tun da daddewa"
Akwai annabawa dayawa. Matthew ya na maganar Zechariah ne. AT: "annabi Zechariah"
"diyar" garin na nufin mutanen garin. AT: "mutanen Sihiyona" ko "mutanen da su na zama a Sihiyona"
Wannan wani suna ne na Urushalima.
Jumlar "akan jaki, duƙushin jaki" na bayyana cewa jakin ƙaramin dabba ne. AT: "a kan ƙaramin jaki"
waɗannan tufa ne na waje.
Waɗannan hanyoyi ne na nuna girma ga Yesu sa'ad da ya na shigan Urushalima.
Wannan kalma na nufin "cece mu," amma ya na iya nufin "yabi Allah!"
Yesu ba ainahin ɗan Dauda ba ne, za a iya juya wannan kamar "ɗan zuriyar sarki Dauda." Ko da shike, "Ɗan Dauda" laƙani ne wa Mai ceto, mai yiwuwa taron su na kiran Yesu da wannan laƙanin.
A nan "a cikin sunan" na nufin "cikin iko" ko "kamar wakili." AT: "a cikin ikon Ubangiji" ko "kamar wakilin Ubangiji"
A nan "ma ɗaukaki" ya na nufin Allah da ke mulki daga sararin sama. AT: "Yabi Allah, wanda ya na cikin sama" ko "Yabo ga Allah"
A nan "garin" ya na nufin mutanen da suke zama a wurin. AT: "mutane dayawa daga garin sun yi ɗoki"
"murna"
Yesu bai shiga ainahin haikalin ba. Ya shiga ta fãdar haikalin.
Attajirai su na saya da sayar da dabbobi da waɗansu abubuwa da masu tafiye-tafiye sun saya don su mika hadaya da ta dace a haikalin.
"Yesu ya ce wa waɗanda su ke canza ƙudi da saya da sayar da abubuwa"
AT: "Annabawa sun rubuto tun da daddewa" ko "Allah ya faɗa da daddewa"
AT: "Gida na zai zama"
A nan "Na" ya na nufin Allah kuma "gida" na nufin haikali.
Wannan karin magana ne. AT: "wurin da mutane na addu'a"
Yesu ya yi amfani da ƙarin magana don ya tsawta wa mutanen don saya da sayar da abubuwa a cikin halkalin. AT: "kamar wurin da masu fashi suke ɓoye"
AT: "waɗanda su makafai ne da kuma waɗanda su guragu ne"
waɗanda su ke da ciwon ƙafa ko ƙafan da na sa tafiyawa wahala
"abubuwan banmamaki" ko "abin al'ajibi." Wannan ya na nufin warkaswa da Yesu ya yi wa makafi da guragu a cikin 21:14.
Ya na nufin cewa sun yi fushi domin ba su gaskanta cewa Yesu ne Almasihu ba kuma ba su son sauran mutanen su yabe shi. AT: "sun ji fushi sosai domin mutane su na yabon shi"
Manyan firistoci da malaman attaura suka yi wannan tambaya don su ƙwabe Yesu domin su na fushi da shi. AT: "Kada ka bar su sa faɗa waɗannan abubuwa game da kai!"
Yesu ya yi wannan tambaya domin ya tuna wa manyan firistoci da malaman attaura da abin da sun karanta a cikin nassi. AT: "I, Na ji su, amma ku tuna da abin da kun karanto a cikin nassi ... yabo."
Jumlar "daga bakin" na nufin magana. AT: "Ka sa ƙanannan 'ya'ya da masu shan mama su shirya don su yabi Allah"
" Yesu ya bar manyan firistoci da malaman attaura"
ya mutu ya kuma bushe
Almajiran su yi amfani da tambaya domin su nanata yadda suke mamaki. AT: "Mu na mamaki cewa bishiyar bauren ta bushe da sauri!"
"ya bushe ya kuma mutu"
"Ina gaya maku gaskiya." Wannan jimlar ya kara nanaci a abin da Yesu zai faɗa.
Yesu ya bayyana maganan don ya nanata cewa dole ne wannan bangaskiya ya zama na gaske. AT: "in kun gaskanta da gaskiya"
Za ku iya juya wannan magana kai tsaye. AT: "za ku iya ce wa wannan tsaunin nan ya tashi, ya jafa kansa a cikin teku"
AT: "zai faru"
Ya na nufin cewa Yesu bai shiga ainahin haikalin ba. Ya shiga fada a ta haikalin.
Wannan na nufin koyarswa da warkaswarYesu a cikin haikali. Mai yiwuwa ya na kuma nufin kora da Yesu ya yi wa masu saya da sayad a ranar da ta wuce.
"daga ina ne ya sami ikon yin wannan?
Wannan na da magana a cikin magana. za ku iya juya maganan. AT: "In mun ce mun gaskanta cewa yahaya ya karba ikonsa daga sama, Yesu zai tambaye dalilin da ba mu gaskanta da yahaya ba."
A nan "sama" na nufin Allah. AT: "daga Allah a sama"
Shugabanin addinai sun san cewa Yesu zai iya tsawta masu da wannan tambaya. AT: "Da kun gaskanta da Yahaya mai Baftisma"
Wannan magana ne cikin magana. Za ku iya juya maganan kai tsaye. AT: "Amma in mun faɗa cewa mun gaskanta Yahaya ya karba ikonsa daga mutane"
"muna tsoron abin da taron za su yi tunani ko su yi mana"
"sun gaskanta cewa Yahaya annabi ne"
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya tsokane shugabanin adini don su yi tunani da zurfi game da misalin da zai gaya masu. AT: "Faɗa mani game da abin da ku ke tunani a abin da zan gaya maku."
Wannan na nufin ɗan da ya sake duba tunaninsa ya kuma so ya aikata dabam daga yadda ya ce zai yi.
"Shugaban firistoci da dattawa su ka ce"
"Yesu ya ce wa shugaban firistoci da dattawa"
A nan "mulkin Allah" na nufin mulkin Allah kamar sarki. AT: "a loƙacin da Allah zai kafa mulkinsa a duniya, zai yarda ya albarkace masu karban haraji da karuwai ta wurin yin mulki da su kafin ya yarda ya yi maku wannan"
AT: 1) Allah zai karɓi masu karban haraji da karuwai ba da daddewa ba fiye da yadda zai karbi shugabanin Yahudawa, ko 2) Allah zai karbi masu karban haraji da karuwai a maimakon shugabanin addin yahudawa.
A nan "ku" ɗaya ne kuma ya na nufin dukka mutanen isra'ila ba shugabanin Yahudawa kadai ba. AT: "Yahaya ya zo wa mutanen isra'ila"
Wannan karin magana ne da na nufin cewa Yahaya ya nuna wa mutanen hanyar gaskiya da za su yi rayuwa. AT: "ya kuma gaya ma ku yadda Allah ya na so ku yi rayuwa"
A nan " ku" ɗaya ne kuma ya na nufin shugabanin Yahudawa.
"mutum da ke da dan dukiya"
"danga"
"gina rami a cikin gonan don matse inabi"
Mai shi ne ya ke da gonan, amma ya bar manoman su kula da shi. A loƙacin da inabin sun yi, za su ba wa mai shi sai su ajiye sauran.
Waɗannan mutane ne da sun san yadda ana kula da gona da kuma inabi.
"bayin mai gonan"
Matiyu bai bayyana wanda ya amsa Yesu ba. Idan ku na so ku ba da takamaiman mai sauraro, za ku iya juya ta kamar "Mutanen sun ce wa Yesu."
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya sa masu sauraransa su yi tunani da zurfi game da abin da wannan nassin na nufi. AT: "Yi tunanin abin da kun karanta ... idanu.?
Yesu ya na faɗa daga cikin zabura. Wannan magana ne da na nufin shugabanin Yahudawa, kamar masu gini, za su ki Yesu, amma Allah zai sa shi mafi muhimminci a cikin mulkinsa, kamar dutse mafi amfani a cikin gini.
AT: "ya zama dutse mafi amfani"
"Ubangiji ya sa wannan babban canji"
A nan "a idanunmu" na nufin gani. AT: "abin al'ajibi ne a gani"
Wannan na kara nanaci akan abin da Yesu zai ce.
A nan "ku" ɗaya ne. Yesu ya na magana da shugabanin addini da kuma mutanen Yahudawa ne a takaice.
A nan "mulkin Allah" ya na nufin mulkin Allah kamar sarki. AT: "Allah zai karbi mulkinsa daga wurin ku ya kuma ba wata al'umma" ko "Allah zai ki ku, Mutanen Yahudawa, kuma zai zama sarki ga mutane daga wasu al'ummai"
Ba bu wanda ya tabatar ko Yesu ya na nufin cewa Allah zai ba da mulkin wata rana ko kuwa ba zai ba da shi ba. Juyawarku ya ba da fahimta mai yiwuwa.
"amfanin" a nan magana ne na "sakamako." AT: "da na ba da sakamako masu kyau"
A nan, "wannan dutse" ɗaya ne a cikin 21:42. Wannan magana ne da na nufin cewa Almasihu zai hallakar da duk wanda ya yi masa tawaye. AT: "Dutsen zai ragargaje duk wanda ya faɗi akai"
A takaice wannan ya na nufin abu ɗaya ne a jumla da ta wuce. Magana ne da ya na nufin cewa Almasihu zai yi hukunci na ƙarshe kuma zai hallakar da duk wanda ya yi masa tawaye.
"misalan Yesu"
Yesu ya ce za su iske wata jaka a ɗaure da aholaki tara da ita.
Annabi ya yi annabcin cewa Sarkin zai zo a kan jaki, kuma a kan aholaki.
Taron kuwa suka baza tufafinsu akan hanya, suka kuma shimfida ganye a kan hanya.
Taron suka ta da murya suna cewa, "Hossana ga dan Dauda! mai albarka ne shi wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Hossana ga maɗaukaki."
Yesu ya kori duk waɗanda ke saye da sayarwa a cikin ikiilisiya, ya kuma birkice teburan masu canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tantabaru.
Yesu ya ce masu kasuwanci sun mayar da gidan Allah kogon 'yan fashi.
Yesu ya faɗa abin da annabi ya faɗa cewa daga bakin jarirai da masu shan mama ke yin yabo.
Yesu ya sa itacen bauren ya bushe domin ba ta da 'ya'ya.
Yesu ya koya wa almajiransa cewa idan sun roka a addu'a da gaskantawa, za su sama.
Manyan firistoci da dattawan sun so su san ta wane iko ne Yesu ya na yin wadannan abubuwa.
Sun san cewa Yesu zai tambaye su dalilin da ba su gaskanta da Yahaya ba.
Yesu ya tambaye su ko su na tunani cewa baftimar mai Baftisma daga sama ne ko daga mutane ne.
Sun ji tsoron jama'an da sun amince cewa Yahaya annabi ne.
Ɗa na farkon ya ce ba zai je ba, amma ya canza ra'ayinsa sai ya je.
Ɗa na biyun ya ce zai je amma bai je ba.
Yesu ya ce za su shiga mulkin domin sun gaskanta da Yahaya, amma manyan firistoci da marubbata ba su gaskanta da Yahaya ba.
Ɗa na farkon.
Manoman inabin suka doddoki ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jejjefe bayin.
Mai gonar a karshe ya aika dansa.
Manoman inabin suka ƙashe ɗan mai gonan.
Mutanen suka ce mai gonar ya hallaka manoman inabi na farko sai ya ba da haya ga wadansu manoman, wanda za su biya.
Dutsen da magina suka ki ya zama dutse mafi amfani.
Yesu ya faɗa cewa za a karba mulkin Allah daga wurin manyan firistoci da farisawa a ba wata al'umma da zata bada amfaninsa.
Sun ji tsoron taron, saboda mutanen sun ɗauke shi annabi.
1 Yesu ya sake yi masu magana da misalai, yace, 2 "Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya wa dansa liyafar aure. 3 Ya aiki bayinsa su kira wadanda aka gayyata su zo liyafar auren, amma suka ki zuwa. 4 Sai sarkin ya sake aiken wasu bayin, yace, "Ku gaya wa wadanda aka gayyata, "Duba, na shirya liyafata. An yanka bajimaina da kosassun 'yanmarukana, an gama shirya komai. Ku zo wurin bikin auren." 5 Amma mutanen ba su dauki sakon da mahimmanci ba kuma suka yi tafiyarsu. Wani ga gonarsa, wani ga kasuwancinsa. 6 Sauran kuma suka kama bayin sarkin, suka wulakanta su, suka kuma kashe su. 7 Amma sarkin ya ji haushi. Ya aika sojojinsa, ku kashe masu kisan kan nan, ku kuma kone birnin su. 8 Sai ya ce wa bayinsa, 'An gama shirya bikin, amma wadanda aka gayyata ba su cancanta ba. 9 Saboda haka ku je bakin hanya ku gayyaci iyakar yawan mutanen da za ku samu zuwa bukin auren.' 10 Bayin suka tafi hanya suka tattaro dukan mutanen da suka samu, da masu kyau da marassa kyau. Zauren auren kuwa ya cika makil da baki. 11 Amma da sarkin ya zo don ya ga bakin, sai ya ga wani wanda bai sa kayan aure ba. 12 Sai sarkin ya ce masa, 'Aboki, ta yaya ka shigo nan ba tare da kayan aure ba?' Mutumin kuwa ya rasa ta cewa. 13 Sai sarkin ya ce wa bayinsa, 'Ku daure mutumin nan hannu da kafa, ku jefa shi cikin duhun, inda za ayi kuka da cizon hakora.' 14 Gama mutane dayawa aka kira, amma kadan aka zaba."' 15 Sai Farisawan suka tafi suka shirya makirci akan yadda zasu kama shi ta maganarsa. 16 Suka tura masa almajiransu, da Hirudiyawa. Suka ce ma Yesu, "Mallam, mun san kai mai gaskiya ne, kuma kana koyar da hanyar Ubangiji da gaskiya. Ba ka damu da ra'ayin kowa ba, kuma ba ka nuna bambanci a tsakanin mutane. 17 To gaya mana, menene tunaninka? Ya halarta a biya haraji ga Kaisar ko a'a?" 18 Amma Yesu ya gane muguntarsu yace, "Don me kuke gwada ni, ku munafukai? 19 Ku nuna mani sulen harajin." Sai suka kawo masa sulen. 20 Yesu yace masu, "Hoto da sunan wanene wadannan?" 21 Suka ce masa, "Na Kaisar." Sai Yesu ya ce masu, "To ku ba Kaisar abubuwan dake na Kaisar, Allah kuma abubuwan dake na Allah." 22 Da suka ji haka, suka yi mamaki. Sai suka bar shi suka tafi. 23 A ran nan sai wadansu Sadukiyawa, wadanda suka ce ba tashin matattu, suka zo wurinsa. Suka tambaye shi, 24 cewa, "Mallam, Musa yace, 'Idan mutum ya mutu, bashi da 'ya'ya, dole dan'uwansa ya auri matarsa ya kuwa haifawa dan'uwansa 'ya'ya. 25 Akwai wasu 'yan'uwa bakwai. Na farkon yayi aure sai ya mutu. Da shike bai bar 'ya'ya ba. Ya bar wa dan'uwansa matarsa. 26 Sai dan'uwansa na biyu shi ma yayi haka, haka kuma na ukun, har zuwa dan'uwan na bakwai. 27 Bayan dukansu, sai matar ta mutu. 28 To a tashin matattu, matar wa zata zama a cikin su bakwai din? Don duk sun aure ta." 29 Amma Yesu ya amsa yace masu, "Kun bata, domin ba ku san litattafai ko ikon Allah ba. 30 Domin a tashin matattu basu aure, ba kuma a bada su aure. Maimaikon haka, suna kama da mala'ikun sama. 31 Amma game da tashin matattu, ba ku karanta abinda Allah ya fada maku ba, cewa, 32 'Nine Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu'? Allah ba Allah na matattu bane, amma na rayayyu." 33 Da taron suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa. 34 Amma da Farisawan suka ji cewa Yesu ya kure Sadukiyawa, sai suka tattara kansu. 35 Daya daga cikinsu, masanin shari'a, yayi masa tambaya, yana gwada shi- 36 "Mallam, wace doka ce mafi girma a cikin shari'a?" 37 Yesu yace masa, "Ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.' 38 Wannan itace babbar doka ta farko. 39 Doka ta biyu kuma kamar ta take- 'Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.' 40 Akan wadannan dokoki ne dukkan shari'a da annabawa suka rataya." 41 Yayin da Farisawa suke tattare wuri daya, Yesu yayi masu tambaya. 42 Yace, "Me kuke tunani game da Almasihu? Shi dan wanene?" Suka ce masa, "Dan Dauda ne." 43 Yesu yace masu, "To ta yaya kuma Dauda cikin Ruhu ya kira shi Ubangiji, yana cewa, 44 "Ubangiji ya cewa wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na mai da makiyanka matakin sawayenka." 45 Idan Dauda ya kira Almasihu 'Ubangiji,' ta yaya ya zama dan Dauda?" 46 Ba wanda ya iya bashi amsa, ba kuma wanda ya kara yi masa tambayoyi tun daga wannan rana.
Yesu ya ba da labari game da bikin auren, don ya tsawata shugabanin addini da kuma nuna rashin gaskantawarsu.
"wa mutanen"
Wannan ne farkon labari. dubi yadda kun juya wannan a cikin 13:24.
AT: "mutanen da sarkin ya gayyato"
Ana iya bayyana wannan magana kai tsaye. AT: "bayin, umurta su su gaya wa waɗanda ya gayyato"
"Duba" ko "ji" ko" saurara abin da zan gaya ma ku"
Ya na nufin cewa an dafa dabbobin kuma su na nan a shirye don ci. AT: "Bayi na sun kashe sun kuma dafa bajimaina da kosassun 'yanmarukana"
"Bajimaina mafi kyau da kosassun 'yanmarukana don ci"
"Amma waɗannan baƙi da sarkin ya gayyata sun ki gayyatan"
Ya na nufin cewa sojojin sarkin sun ƙashe masu kisa.
AT: "waɗanda na gayyato"
"inda ainahin hanyoyin haye suke." Sarkin ya na aikan bayin zuwa wurin da za a iya samin mutane.
"mutane masu kyau da marassa kyau"
AT: "Bakin sun cika da zauren auren"
babban ɗaki
Sarkin ya yi amfani da wannan tambaya domin ya tsawata bakon? AT: "ba ka sa kayan da ta dace da aure ba. Bai kamata ka na nan ba."
"mutumin ya yi shiru"
"ɗaure shi don kada ya iya motsa hannunsa ko kafa"
A nan "cikin duhu" magana ne na wurin da Allah na tura waɗanda sun ki su. Wannan wuri ne da an ƙebe daga Allah har abada. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 8:12. AT: "duhun wuri da nisa daga Allah"
"cizon hakora" alama ne na yin abu, da na wakilcin bakin ciki mai tsanani da wahala. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 8:12. AT: "kuka da bayyana wahala mai tsanani"
AT: "Gama Allah ya gayyace mutane dayawa, amma ya zabi kadan"
Wannan ya nuna wucewa. Yesu ya kalmasa labarin zai kuma bayyana ma'anar labarin yanzu.
"yadda za su sa Yesu ya faɗa wani abin da ba daidai ba don su iya kama shi"
Almajiran Farisawa sun amince da biyan haraji ga shugabanin Yahudawa. Hirudiyawan sun amince da biyan haraji ga shugabanin Romawa. Ana nufin cewa Farisawa sun yarda cewa duk abin da Yesu ya ce, zai saba wa ɗaya daga cikin taron.
Waɗannan ma'aikata ne da masu bin sarki Hiradus na Yahudawa. Shi abuta ne da shugabanin Romawa.
"ba ka nuna bambancin girma ga kowa" ko "ba ku ɗaukan wani da mafi muhimminci fiye da wani dabam ba"
Mutane ba su biyan haraji kai tsaye wa kaisar ba amma ga wani mai karɓan harajinsa. AT: "a biya harajin da Kaisar ya umurta"
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya domin ya tsawata waɗanda su na son su kama shi. AT: "Kada ku gwada ni, ku munafukai? ko "Na san cewa ku munafukai ku na so ku gwada ni ne!"
Wannan sulen Romawa ne da ya kai ƙudin aikin rana ɗaya.
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya domin ya sa mutanen su yi tunani sosai game da abin da ya na faɗa. AT: "Faɗa mani hoto da sunan wanene ku ke gani a kan wannan sulen."
Za ku iya bayyana bayanin da an fahimta a cikin amsansu. AT: "Sulen na da hoto da sunar Kaisar a kai"
"abubuwan dake na Kaisar"
"abubuwan dake na Allah"
Shugabanin addini su na tambayan Yesu game da abin da Musa ya rubuto a cikin nissi. Idan harshenku bai yarda da magana a cikin magana ba, za a iya bayyana maganan kai tsaye. AT: "Mallam, Musa ya faɗa cewa idan mutum ya mutu"
Anan "sa" ya na nufin mutumin da ya mutu.
"Babban ... mai bin babban ... ɗayan babbab ... ƙaramin" ko "Babban ... babban ƙaramin ɗan'uwansa ... wannan babban ƙaramin ɗan'uwan ... ƙaramin"
"Bayan kowane ɗan'uwa ya mutu"
A nan Saducees sun matsa daga labari game da 'yan'uwa bakwai zuwa ainahin tambayansu.
"lokacin da matattu za su rayu kuma"
Ana nufin cewa Yesu ya na nufin sun bata da abin da su ke tunani game da tashin matattu. AT: "kun bata da tashin matattu"
"abin da Allah na iya yi"
"mutane ba za su yi aure ba"
AT: "mutane ba za su kuma ba da 'ya'yansu a aure ba"
A cikin 22:32, Yesu ya faɗa daga Fitowa don ya nuna cewa mutane na rayuwa kuma bayan mutuwa.
Yesu ya yi wannan tambaya domin ya tuna wa shugabanin addini game da abin da sun sani daga nassi. AT: "Na san cewa kun karanta, amma ba ku fahimci abin da ... Yakubu."
AT: "abinda Allah ya faɗa maku"
Za ku iya juya wannan magana kai tsaye. AT: "Allah, wanda ya ce wa Musa cewa shi ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu."
AT: "na matattun mutane, amma shi Allah na rayayyun mutane"
"gwani a shari'a." Wannan ba-Farasi ne da ke da fasahar shari'ar Musa.
An yi amfani da waɗannan jimloli biyu don a nuna "cikakke" ko "mai himma." A nan "zuciya" da "rai" magana ne na cikin mutum.
A nan "babban" da "farko" na nufin abu ɗaya. Su na nanata cewa wannan ne doka mafi muhimminci.
AT: 1) "akwai wani doka dake biye a muhimminci" ko 2) "akwai doka ta biyu da ke da muhimminci." haka kuma, Yesu ya na nufin waɗannan dokoki biyu su na da muhimminci fiye da dukka sauran dokoki.
Wannan ya na nufin kamar doka a cikin 22:37.
A nan "makwabcinka" ya na nufin fiye da waɗanda su ke zama kusa. Yesu ya na nufin dole ne mutum ya kaunace dukka mutane.
A nan jumlar "dukkan shari'a da annabawa" na nufin dukka nassi. AT: "Komai da Musa da annabawan sun rubuto a cikin nissi su na bisa waɗannan dokoki biyu"
A cikin waɗannan "ɗan" ya na nufin "zuriya."
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya sa shugabanin addini su yi zurfin tunani game da zabura da ya na sa ya faɗa. AT: "To, faɗa mani dalilin da Dauda a cikin Ruhu ya kira shi Ubangiji"
"Dauda, wanda Ruhu mai Tsarki ke ƙarfafa." Wannan na nufin Ruhu mai Tsarki ne na albarkaci abin da Dauda na faɗa.
A nan "shi" ya na nufin Almasihu, wanda shi ma zuriyar Dauda ce.
A nan "Ubangiji" ya na nufin Allah Uba.
A nan "Ubangiji" ya na nufin Almasihu. Kuma, "na" ya na nufin Dauda. Wannan Almasihun ya fi Dauda.
Zauna a "hannun damanan Allah" alama ne na karban babban ɗaukaka da iko daga Allah. AT: " zauna a wurin girma a gefena"
Wannan ƙarin magana ne. AT: "sai na ci nasara da makiyanka" ko "sai na sa makiyanka su durkusa a gaban ka"
Yesu ya yi amfani da tambaya don ya sa shugabanin addini su yi zurfin tunani game da abin da ya na faɗa. AT: "Dauda ya na kiransa 'Almasihu,' don haka dole Almasihu zai fi zuriyar Dauda."
Dauda ya na kiran Yesu "Almasihu" domin Yesu ba zuriyan Dauda kadai ba, amma ya fi shi.
A nan "amsa" na nufin abin da mutane na na faɗa. AT: "ba shi amsan komai" ko "amsa shi"
Ana nufin cewa babu wanda ya yi masa irin tambayoyin da zai sa shi ya faɗa abin da bai dace ba don shugabanin addini su iya kama shi.
Wasu ba su ɗauki sakon da mahimmanci ba kuma suka yi tafiyar kasuwancinsu kuma sauran suka kama bayin sarkin suka ƙashe su.
Sarkin ya aika sojojinsa, ku kashe masu kisan kan nan, ku kuma kone birnin su.
Sarkin ya kuma gayyato iyakar yawan mutanen da za ku samu da masu kyau da marasa kyau.
sarkin ya sa aka ɗaure shi aka kuma jefa shi cikin duhu.
Farisawan su na kokarin yadda zasu kama Yesu ta maganarsa.
Sun tambaye Yesu ko halak ne a biya haraji ga Kaisar ko a'a.
Yesu ya ce su ba Kaisar abubuwan dake na Kaisar, Allah kuma abubuwan dake na Allah.
Sadukiyawan sun gaskanta cewa babu tashin matattu.
Macen ta na da mazaje bakwai.
Yesu ya ce Sadukiyawan ba su san nassi ko ikon Allah ba.
Yesu ya ce a tashin matattu, babu aure.
Yesu ya faɗa nassin da Allah ya ce shine Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu-Allah na matattu.
Mai shariyar ya tambaye Yesu wace doka ce mafi girma a cikin shari'a.
Yesu ya faɗa cewa ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka shi ne mafi girma da kuma doka ta farko?
Yesu ya ce ka ƙaunaci makwabcinka kamar kanka shi ne doka ta biyu.
Yesu ya tambaye su ɗan wane ne ne Almasihu.
Farisawan sun faɗa cewa Almasihu ne ɗan Dauda.
Yesu ya tambaya su yadda Dauda ya iya kiran ɗansa, Almasihun, Ubangiji.
Farisawan basu iya amsa Yesu ko kadan ba.
1 Sai Yesu yayi wa taron da alamajiransa magana. 2 Ya ce, "Marubuta da Farisawa suna zaune a mazaunin Musa. 3 Don haka, duk abinda suka umarceku kuyi, kuyi wadannan abubuwa ku kuma kiyaye su. Amma kada kuyi koyi da ayyukansu, gama suna fadar abubuwa amma kuma ba su aikata su. 4 I, sukan daura kaya masu nauyi, masu wuyar dauka, daga nan su dauka su jibga wa mutane a kafada. Amma su kan su baza su mika danyatsa ba su dauka. 5 Duk ayyukan su suna yi ne don mutane su gani, suna dinka aljihunan nassinsu da fadi, suna fadada iyakokin rigunansu. 6 Su na son mafifitan wuraren zama a gidan biki, da mafifitan wuraren zama a majami'u, 7 da kuma gaisuwar musamman a wuraren kasuwanci, a kuma rika ce da su 'mallam.' 8 Amma ba sai an kira ku 'mallam, ba' domin malami daya kuke da shi, ku duka kuwa 'yan'uwan juna ne. 9 Kada ku kira kowa 'Ubanku' a duniya, domin Uba daya ne ku ke da shi, kuma yana sama. 10 Kada kuma a kira ku malamai, saboda malamin ku daya ne, shi ne Almasihu. 11 Amma wanda yake babba a cikin ku zaya zama bawanku. 12 Duk wanda ya daukaka kansa za a kaskantar dashi. Duk wanda ya kaskantar da kansa kuma za a daukaka shi. 13 Amma kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kun toshewa mutane kofar mulkin sama. Baku shiga ba, kuma ba ku bar wadanda suke so su sami shiga ba. 14 kaiton ku marubuta da Farisawa, domin kuna hallaka gwauraya - 15 Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kuna tafiya ketaren tekuna da kasashe domin samun almajiri daya tak, in kwa kun samu kukan mai da shi biyunku danwuta. 16 Kaiton ku, makafin jagora, kuda kuke cewa, Kowa ya rantse da Haikali, ba komai. Amma duk wanda ya rantse da zinariyar Haikalin, rantsuwarsa ta daure shi.' 17 Ku wawayen makafi! wanene yafi girma, zinariyar ko kuwa Haikalin da yake tsarkake zinariyar? 18 Kuma, 'Kowa ya rantse da bagadi, ba komai bane. Amma duk wanda ya rantse da baikon da aka dora a kai, sai rantsuwarsa ta kama shi.' 19 Ku makafi! Wanene yafi girma, baikon ko kuwa bagadin da yake kebe baikon ga Allah? 20 Saboda haka, duk wanda ya rantse da bagadi, ya rantse da shi da duk abinda ke kansa. 21 Kuma duk wanda ya rantse da Haikali ya rantse dashi da kuma wanda yake cikin sa. 22 Kuma duk wanda ya rantse da sama, ya rantse da kursiyin Allah da kuma wanda yake zaune akai. 23 Kaiton ku Farisawa da marubuta, munafukai! Kukan fitar da zakkar doddoya, da karkashi, da lamsur, amma kun yar da al'amuran attaura mafi nauyi-, wato, hukunci, da jinkai da bangaskiya. Wadannan ne ya kamata kuyi, ba tare da kunyi watsi da sauran ba. 24 Makafin jagora, ku kan burtsar da kwaro dan mitsil, amma kukan hadiye rakumi! 25 Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! kuna wanke bayan moda da kwano, amma aciki cike suke da zalunci da keta. 26 Kai makahon Bafarise! Sai ka fara tsarkake cikin modar da kwanon domin bayansu ma su tsarkaka. 27 Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Kamar kaburburan da aka shafa wa farar kasa kuke, masu kyaun gani daga waje, daga ciki kuwa sai kasusuwan matattu da kazanta iri iri. 28 Haka nan kuke a idanun mutane ku adalai ne, amma a ciki sai munafunci da mugun aiki. 29 Kaiton ku marubuta da Farisawa, munafukai! Ku kan gina kaburburan annabawa, kuna kuma kawata kaburburan adalai. 30 Kuna cewa, 'Da muna nan a zamanin Ubanninmu, da bamu basu goyon baya ba wajen zubar da jinin annabawa.' 31 Domin haka kun shaida kanku ku ne 'ya'yan masu kisan annabawa. 32 Sai kuma kuka cika ma'aunin ubanninku! 33 macizai, Ku 'ya'yan ganshekai, Yaya zaku tsere wa hukuncin Gidan wuta? 34 Saboda haka, duba, ina aiko maku da annabawa, da masu hikima da marubuta. Za ku kashe wadansun su kuma ku gicciye su. Zaku yiwa wasu bulala a majami'un ku, kuna bin su gari gari. 35 Sakamakon hakan alhakin jinin dukkan adalai da aka zubar a duniya ya komo a kan ku, tun daga jinin Habila adali har ya zuwa na Zakariya dan Barakiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikali da bagadi. 36 Hakika, Ina gaya maku, duk wannan zai auko wa mutanen wannan zamani. 37 Urushalima, Urushalima, keda kika kashe annabawa kika kuma jejjefi wadanda aka turo maki da duwatsu! Sau nawa ne naso in tattaro ki kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta cikin fukafukanta, amma kin ki. 38 Ga shi an bar maku gidan ku a yashe! 39 Ina dai gaya maku, ba za ku kara gani na ba, sai ran da kuka ce, 'Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji."'
Wannan farkon sabon sashin labarin da ta bi 25:46, inda Yesu ya koyar game da ceto da kuma hukunci na karshe. A nan ya fara da tsawata wa mutanen game da Marubuta da Farisawa.
A nan "zauna" na wakilcin ikon yin mulki da kuma yin hukunci. AT: "na da iko kamar Musa" ko "na da ikon faɗan abin da dokan Musa ke nufi"
"dukkan abubuwa ... yi su ku kuma kiyaye su" ko "komai ... yi ku kuma kiyaye"
A nan "ɗaura kaya masu nauyi ... jibga wa mutane a kafada" magana ne na shugabanin addini da su ke sa dokoki masu wuya da kuma sa mutane su yi biyayya ga su. Kuma "baza su motsa danyatsa" ƙarin magana ne da ke nufin cewa shugabanin addin ba za su taimake mutanen ba. AT: "su na sa ku yi biyayya ga dokoki masu yawa da ke da wuyan bi. Amma basu yin komai don su taimake mutanen a bin dokan"
AT: "Su na yin dukka ayukansu domin mutane su iya ganin abin da suke yi"
Dukka waɗannan abubuwa ne da Farisawa suke don su bayyana kamar su na girmama Allah fiye da waɗansu mutane.
ƙaramin akwatin fata da ke ɗauke da takarda da an rubuto nassi a kai
Farisawan sun yi alakwayi a ƙasan tufafinsu musamman don su nuna biyayyar su ga Allah.
Yesu ya cigaba da magana da taron da kuma almajiran game da su Farisawan.
Dukka waɗannan wurare ne da mutane masu daraja suke zama.
babban, fili inda mutane suke saya da sayar da abubuwa
AT: "don mutane su kira su 'Mallam."'
AT: "Amma ba sai kun yarda wani ya kira ku"
Duk aukuwar "ku" ɗaya ne kuma na nfuin duka masubin Yesu.
A nan "'yan'uwa" na nufin "'yan'uwa masubi"
Yesu ya na amfani da ƙarin magana domin ya faɗa wa masu sauraransa cewa kaɗa su yarda mutane masu daraja su fi daraja a wurinsu fiye da Allah. AT: "kaɗa ku kira wani a duniya Ubanku" ko "kaɗa ku faɗa cewa kowane mutum a duniya ubanku ne"
"Uba" anan muhimmin laƙabi ne wa Allah.
AT: "Kuma, kaɗa ku bar wani ya ƙira ku"
A lokacin da Yesu ya ce "Almasihu," ya na maganan kansa a cikin mutum na uku. AT: "Ni, Almasihun, ni ne malaminku"
"mutumin da ke mafi daraja a cikinku"
A nan "ku" na nufin masubin Yesu."
"daraja kansa"
AT: "Allah zai kaskanta"
AT: "Allah zai sa daraja" ko "Allah zai girmama"
"yadda zai zama da ban tsora a Dubi yadda kun juya wannan a cikin 11:21.
Yesu ya na maganar mulkin sama, wadda Allah ya na mulki akan mutane, kamar gida ne, kofa wadda farisawan suka toshe daga waje domin kada su ko wani dabam ya shiga gidan. Ana samin jumlar "mulkin sama" a cikin littafin matthew. In ya yiwu, Yi amfani da kalmar harshenku na "sama" a juyinku. AT: "kun sa shi yiwuwa wa mutane su shiga mulkin sama ... ba ku shiga ba ... kuma ba ku bar waɗanda suke so su sami shiga ba" ko "Kun hana mutane daga karban Allah, wadda yake zama a sama, sarki ... ba ku ƙarbe shi kamar sarki ba ... kuma kun sa shi mara yiwuwa wa waɗanda su ke so ƙarbe shi sarki su yi haka"
Wannan ƙarin magana ne da na nufin su na tifiyan wurare masu nisa. AT: "ku na tafiya mai nisa sosai"
"domin ya sa wani ya ƙarba addininka"
A nan "ɗan" ƙarin magana ne da na nufin "zama na." AT: "mutum da ya zama na wuta" ko "mutum da ya kamata ya je wuta"
Dubi rubutan ƙasa. Kalmar "cinye" magana ne da ke nufin kwace da ƙarfi. Ma'ana mai yiwuwa 1) "gidaje" na nufin gidajensu. AT: "ku na sace gidajen gomraye daga wurinsu" 2) "gidaje" magana ne na dukka mallakarsu. AT: "ku na sata dukka mallakar gomraye"
Shugabanin Yahudawan makafi ne a ruhaniya. Ko da shike sun ɗauki kansa kamar malamai, ba su iya gane gaskiyar Allah ba. Dubi yadda kun juya "jagora makafin" a cikin 15:14.
"ta haikali ba sai ya ɗauka rantuwarsa ba"
"ɗaure da rantsuwarsa." Jumlar "ɗaure da rantuwarsa" magana ne da na bukata a yi abin da ya ce zai yi a cikin rantsuwa. AT: "dole ne ya yi abin da ya ce zai yi"
Yesu ya yi amfani da wannan tambayan domin ya ƙwabe Farisawan domin sun ɗaukake zinariyar kamar ya fi haikalin daraja. AT: "Haikalin da ya mika zinariyar ga Allah ya fi daraja fiye da zinariya!"
"Haikalin da yake sa zinariyar ya zama na Allah kadai"
Ana iya sa a bayyana bayanin da an fahimta. AT: "Kun kuma ce"
"ba sai ya yi abin da ya rantse zai yi ba" ko "ba sai ya tsaya a kan rantsuwarsa ba"
Wannan dabba ne ko hatsi da mutum zai kawo wa Allah ta wurin sakawa a kan bagadin Allah.
Shugabanin Yahudawan makafi ne a ruhaniya. Ko da shike sun ɗauki kansa kamar malamai, ba su iya gane gaskiyar Allah ba.
Yesu ya yi amfani da wannan tambayan domin ya ƙwabe Farisawan don yadda suke yi da kyautan kamar ya fi daraja fiye da bagadin. AT: "Bagadin da ya na tsarkake kyautan ya fi kyautan!"
"bagadin da yake ba kyautan daraja ga Allah" "
"ta dukkan kyautanne da mutane sun saka a kai"
Duk waɗannan na nufin Allah Uban.
yadda zai zama da ban tsora ... munafukai! Dubi yadda kun juya wannan a cikin 11:21.
Waɗannan itce da iri ne da mutane na amfani don su sa abinci ya yi dadi.
"ba ku yi biyyaya"
"al'amuran mafi daraja"
"ya kamata kun yi biyyaya da waɗannan dokoki masu daraja"
AT: "tare da bin dokoki masu dan daraja"
Yesu ya yi amfani da wannan magana domin ya kwatanta Farisawan. Yesu ya na nufin cewa Farisawan ba su fahimci umurnin Allah ko yadda za su faranta mashi rai ba. Don haka, ba za su iya koya wa waɗansu yadda za su faranta wa Allah rai ba. Dubi yadda kun juya wannan magana a cikin 15:14.
Mai da hankali a bin ƙananan dokoki masu dan daraja da kuma ƙyale dokoki mafi daraja na nan kamar hwaka ne kamar mai da hankali don ƙada ku haɗiye ƙaramin dabba mai datti amma cin namam babban dabba. AT: "ku na nan kamar wawaye kamar mutum da ya na butsar da ƙwaro da ya faɗi a cikin ruwansa amma ya haɗiye rakumi"
Wannan na nufin juye ruwa a tuffafi don a cire ƙwaro daga ruwan sha.
ƙaramin ƙwaro mai tashi sama
Wannan magana ne da ke nufin cewa marubuta da Farisawan sun bayyana da tsarki a waje ga waɗansu, amma a a ciki kuwa mugaye ne.
"su na son abin da waɗansu ke da shi, kuma sun yi son kai"
Farisawan sun makanta a ruhaniya. Ko da shike sun ɗauki kansu kamar mallamai, ba su iya fahimtar gaskiyar Allah.
Wannan magana ne da na nufin cewa idan za su zama da tsarki a cikinsu sakamokan shi ne za su zama da tsarki a wajen.
Wannan magana ne da ke nufin cewa Farisawa da marubuta
"kaburburan da wani ya shafa wa farar kasa." Yahudawa su na shafa wa kaburbura farar kasa domin mutane su iya gani su kuma daina taɓasu. Taɓa kaburi zai sa mutum ya zama da kazanta.
AT: "na mutane masu adalci"
"a loƙacin kakaninmu"
"da bamu hadu da su ba"
A nan "jini" na nufin rai. Zub da jini na nufin ƙashe. AT: "ƙashe" ko "yin kisa"
A nan "'ya'ya" na nufin "zuriya."
Yesu ya yi amfani da wannan domin ya nuna cewa Farisawan za su cika mugayen ayukan da kakaninsu su ka fara a loƙacin da sun ƙashe annabawan. AT: "Kun kuma gama zunuban da kakaninku sun fara"
Shaidan macizai ne, kuma ganshekai macizai ne masu dafi. Mugaye ne kuma su kullum alamu ne na mugu. AT: "Ku na nan muguye da mugunta kamar macizai masu dafi"
A nan "'ya'ya" na nufin "samin halin." Dubi yadda kun juya jumla irin wannan a cikin 3: 7.
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya don ƙwaba. "babu hanya da za ku tsere hukuncin gidan wuta!"
Ana magana wani loƙaci domin a nuna cewa wani zai yi wani abu nan ba da juma ba. AT: "Zan turo maku annabawa, masu hikima, da kuma marubuta"
Jumlar "A kan ku zai zo" ƙarin magana ne da ke nufin ƙarban hukunci. Zuba jini magana ne da na nufin ƙashe mutane, don haka "jinin adalci da an zuba a duniya" na wakilcin mutane masu adalci da an ƙashe su. AT: "Allah zai hukunta ku domin kisan dukka mutane masu adalci"
A nan kalmar "jini" na wakilcin ƙashen mutum. AT: "daga mai kisan ... zuwa mai kisan"
Habila ne farkon mai adalci wanda aka ƙashe shi, kuma Zakariya, wanda Yahudawa suka ƙashe shi a cikin haikali, ana zaton ku shi ne na ƙarshe. Waɗannan maza biyun su na wakilcin dukka mutane masu adalci da aka ƙashe.
Wannan Zakariya ba shi ne Uban Yahaya mai baftisma ba.
Yesu ba ya nufin cewa mutanen da ya ke magana da su ne suka ƙashe Zakariya. Ya na nufin kakaninsu ne su yi.
"Ina gaya maku gaskiyar." Wannan na kara nanaci a abin da Yesu zai faɗa nan gaba.
Yesu ya yi magana da mutanen Urushalima kamar su ne garin.
AT: "waɗanda Allah ya turo maki"
Yesu ya na magana da Urushalima kamar mace ne kuma mutanen 'ya'yanta ne. AT: "mutanen ki" ko "mazaunanki"
Wannan magana ne da ke nanata kaunar Yesu ga mutanen da kuma yadda ya so ya kula da su.
kaza na mace. Za ku iya juya da kowane tsuntsu da ke ƙare 'ya'yanta a cikin fiffikenta.
"Allah zai bar gidanku, kuma zai zama fanko"
AT: 1) "birnin Urushalima" ko 2) "haikalin."
Wannan na ƙara nanata abin da Yesu zai faɗa a gaba.
A nan "cikin sunan" ko "kamar wakili." Dubi yadda kun juya wannan a cikin 21:9. AT: "Mai albarka ne shi wanda ke zuwa a cikin ikon Ubangiji" ko "Shi wanda ke zuwa a matsayin wakilin Ubangiji zai zama da albarka"
Yesu ya faɗa wa mutanen cewa su yi abubuwan da Marubuta da Farisawa suka koyar daga mazaunin Musa.
Yesu ya ce kada su yi koyi da ayukansu domin su na fadar abubuwa amma kuma ba su aikata wa.
Marubuta da Farisawan suke yin dukka ayukarsu don mutane su gani.
Yesu ya ce shi ne Ubanmu ɗaya wanda yake sama, kuma malaminmu ɗaya shi ne Almasihu.
Allah zai kaskantar da wanda ya ɗaukaka kansa kuma ya ɗaukaki wanda ya kaskantar da kansa.
Yesu ya sake kiran marubuta da Farisawan munafukai.
A loƙacin da marubuta da Farisawa suka sami almajiri, ya na nan biyun ɗan wuta kamar yadda suke.
Yesu ya faɗa cewa marubuta da Farisawa makafin jagora ne da kuma wawaye.
Farisawa da marubuta sun kasa yin al'amuran attaura mafi nauyi-, wato, hukunci, jinkai da bangaskiya.
Marubuta da Farisawan sun kasa share cikin modarsu, domin wajen ya kuma zama da tsabta.
Marubuta da Farisawan suna cike da tilistawa a karbar kuɗi, rara, munafurci, da mugunta.
Ubannen marubuta da Farisawa sun ƙashe annabawan Allah.
Marubuta da Farisawa za su samu hukuncin Gidan wuta.
Yesu ya ce za su ƙashe wasu su kuma gicciye wasu, su bulale wasu, a kuma kore wasu daga gari zuwa gari.
Alhakin jinin dukkan adalai da aka zubar a duniya zai sauko kan marubuta da Farisawa.
Yesu ya faɗa cewa ga wannan zamani ne dukkan waɗannan abubuwa za su faru.
Yesu ya so ya tattaro 'ya'yan Urushalima tare amma ba za su yarda ba.
Za a bar gidan Urushalima a yashe.
1 Yesu ya fita daga cikin haikalin ya kama hanyar sa. Almajiran sa suka zo suna nuna masa ginin haikali. 2 Amma ya amsa masu yace, "kun ga dukkan wadannan abubuwan? Ina gaya maku gaskiya, ba ko dutse daya da za'a bari akan dan'uwansa wanda ba za'a rushe shi ba." 3 Yayin da ya zauna a kan dutsen zaitun, almajiran sa suka zo wurin sa a boye suka ce, "me zai zama alamar zuwanka da kuma na karshen duniya?" 4 Yesu ya amsa yace dasu, "Ku kula kada wani yasa ku kauce." 5 Gama da yawa za su zo da sunana. Za su ce, "ni ne almasihu," kuma za su sa da yawa su kauce. 6 Za ku ji labarin yake-yake da kuma shelar yake-yake. Ku kula kar ku tsorata, domin dole abubuwan nan su faru; amma karshen dai tukunna. 7 Gama al'umma zata tayarwa al'umma, kuma mulki zai tayarwa mulki. Za'a yi yunwa da girgizar kasa a wurare dabam dabam. 8 Amma dukkan wadannan farkon ciwon haihuwa ne kawai. 9 Bayan haka za'a bada ku ga tsanani a kuma kashe ku. Dukkan al'ummai za su tsane ku saboda sunana. 10 Daga nan da yawa za su yi tuntube, kuma su ci amanar juna, su kuma tsani juna. 11 Annabawan karya da yawa za su taso kuma susa da yawa su kauce. 12 Domin mugunta zata ribambanya, kaunar masu yawa zata yi sanyi. 13 Amma duk wanda ya jure har karshe, zai sami ceto. 14 Za'a yi wa'azin wannan bisharar mulkin a dukkan duniya don ya zama shaida akan dukkan al'ummai. Daganan karshen zai zo. 15 Don haka, idan kun ga abin kyama mai lalatarwa, wanda Annabi Daniyel ya yi maganar sa, Ya tsaya a wuri mai tsarki (bari mai karatu ya fahimta), 16 bari wadanda ke yahudiya su gudu zuwa kan duwatsu, 17 Bari wanda yake kan bene kada ya sauko don daukar wani abu a cikin gidansa, 18 kuma wanda yake gona kar ya dawo gida domin daukar babbar rigarsa. 19 Amma kaito ga wadanda suke dauke da yaro, ko masu shayarwa a wannan kwanakin! 20 Ku yi addu'a kada gudun ku ya zama lokacin hunturu, ko ranan asabaci. 21 Domin za'ayi tsanani mai girma, wanda ba'a taba yin irin shi ba, tun farkon duniya har ya zuwa yau, a'a ba za ayi irin shi ba kuma. 22 In ba don an rage kwanakin ba, da ba mahalukin da zai tsira. Amma albarkacin zababbun, za a rage kwanakin. 23 Sa'annan idan wani yace maku, duba, "ga Almasihu a nan!" ko, "ga Almasihu a can!" kar ku gaskata. 24 Gama annabawan karya da almasihan karya za su zo suna nuna alamu da al'ajibai, don su yaudari masu yawa zuwa ga bata, in ya yiwuma har da zababbun. 25 Kun gani, na gaya maku kafin lokacin ya zo. 26 Saboda haka, idan suka ce maku, "ga shi a jeji," kar ku je jejin. Ko, "ga shi a can cikin kuryar daki," kar ku gaskata. 27 Yadda walkiya ke haskakawa daga gabas zuwa yamma, haka nan zuwan Dan mutum zai zama. 28 Duk inda mushe yake, nan ungulai suke taruwa. 29 Amma nan da nan bayan kwanakin tsananin nan, rana za ta duhunta, wata kuma ba zai ba da haskensa ba, taurari kuma za su fado daga sama, ikokin sammai za su girgiza. 30 Sa'annan alamar Dan Mutum za ta bayyana a sararin sama, kuma dukkan kabilun duniya za su yi bakin ciki. Za su ga Dan Mutun na zuwa a gajimarai da iko da daukaka mai girma. 31 Zai aiki mala'ikunsa, da karar kaho mai karfi, kuma za su tattara dukkan zababbu daga dukkan kusurwoyi hudu, daga karshen sararin sama har zuwa wani karshen. 32 Kuyi koyi da itacen baure. Da zaran reshen sa ya yi toho ya fara bada ganye, za ku sani bazara ta kusa. 33 Haka kuma, idan kun ga dukkan wadannan abubuwa, ya kamata ku sani, Ya yi kusa, ya na bakin kofa. 34 Ina gaya maku gaskiya, wannan zamanin ba zai wuce ba, sai dukkan wadannan abubuwan sun faru. 35 Sama da kasa za su shude, amma kalmomina ba za su shude ba. 36 Amma game da ranan nan ko sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun sama, ko Dan, sai Uban kadai. 37 Kamar yadda kwanakin Nuhu suke, haka zai zama game da zuwan Dan Mutum. 38 A wadannan kwankin kafin zuwan ruwan tsufana suna ci suna sha, suna aure suna aurarwa har ranar da Nuhu ya shiga jirgin, 39 ba su san kome ba har ruwan ya zo ya cinye su_ haka ma zuwan Dan Mutun zai zama. 40 Sa'annan mutane biyu zasu kasance a gona za a dauke daya, a bar daya a baya. 41 Mata biyu na nika a manika za a dauke daya, za a bar dayar. 42 Don haka sai ku yi zaman tsaro, domin baku san ranar da Ubangijinku zai zo ba. 43 Amma ku san wannan, idan maigida ya san lokacin da barawo zai zo, zai zauna a shirye ba zai bar gidan sa har a balle a shiga ba. 44 Don haka sai ku shirya, domin Dan Mutum zai zo a sa'ar da ba ku yi zato ba. 45 To wanene amintaccen bawannan mai hikima, wanda maigidan sa ya sa ya kula mar da gida, domin ya ba su abinci a kan lokaci? 46 Mai albarka ne bawan, da mai gidan zai same shi a kan aikin sa a lokacin da ya dawo. 47 Ina gaya maku gaskiya mai gidan zai dora shi a kan dukkan a binda yake da shi. 48 Amma idan mugun bawa ya ce a zuciyarsa, "maigida na ya yi jinkiri," 49 sai ya fara dukan sauran barorin, ya yi ta ci da sha tare da mashaya, 50 uban gidan bawan zai dawo a ranar da bawan bai zata ba, a lokacin da bai sani ba. 51 Uban gidansa zai datsa shi biyu, karshen sa zai zama daidai da na munafukai, za a sashi inda a ke kuka da cizon hakora.
Yesu ya fara kwatanta abubuwan da zai faru kafin ya dawo kuma a zamanin ƙarshe.
Ya na nufin cewa Yesu da kansa ma ba ya cikin haikalin. Ya na cikin fadan haikalin.
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya sa almajiransa su yi tunani mai zurfi game da abin da zai gaya masu. AT: "Bari in gaya maku game da dukka waɗannan ginin."
"Na faɗa maku gaskiya." Wannan ya kara nanaci a abin da Yesu zai ce nan gaba.
Ya na nufin cewa makiya sojoji za su rushe duwatsun. AT: "loƙacin da makiya sojoji su ka zo, zo su rushe kowane dutse a cikin waɗannan gini"
Anan "zuwanka" na nufin loƙacin da Yesu zai zo a cikin iko, kafa mulkin Allah a duniya
A nan "sa ku kauce" magana ne na sa wani ya gaskanta da abin da ba gaskiya ba. AT: "Ku kula kada wani ya ruɗe ku ... kuma zai ruɗe mutane dayawa"
A nan "suna" na nufin "iko" ko "kamar wakilin" wani. AT: "da yawa za su amince cewa sun zo kamar wakili na" ko "da yawa za su ce su na yi mani magana"
AT: "Kaɗa ku bar wannan ya tsorata ku"
Dukka waɗannan na nufin abu ɗaya. Yesu ya na nanata cewa mutane a ko ina za su yi faɗa da juna.
Wannan na nufin zafin da mace ta ke ji kafin ta haife yaro. Wannan magana na nufin waɗannan yaƙe-yaƙe, yunwa, da girgizan kasa farkon abubuwan da zai kai ga ƙarshen duniya.
"mutane za su ba da ku ga masu iko, wadda za su za ku wahala a kuma ƙashe ku."
A nan "al'ummai" magana ne, da na nufin mutanen al'ummai. AT: "Mutane daga kowane al'umma za su tsane ku"
A nan "suna" na nufin cikakken mutum. AT: "domin kun gaskanta da ni"
"Taso" anan ƙarin magana ne na "zama tabbatacce." A: "zai zo"
A nan "sa ... ƙauce" magana ne na sa wani ya gaskanta da abin da ba gaskiya ba. AT: "kuma ruɗe mutane dayawa"
Za a iya fasara "rashin doka" da jumlar "rashin biyayya ga doka." AT: "rashin biyayya ga doka zai karu" ko "mutane za su ki bin dokan Allah da kuma fiye"
AT: 1) "mutane dayawa ba za su ƙaunaci sauran mutane ba" ko 2) "mutane dayawa ba za su ƙaunace Allah ba."
AT: "Allah zai cece mutumin da ya jure har ƙarshe"
"mutum da ya tsaya da aminci"
Ba a fahimci ko kalmar "ƙarshe" na nufin loƙacin da mutu ya mutu ko loƙacin da azaban ya kare ko ƙarshen zamani loƙacin da Allah zai nuna kansa a matsayin sarki. Ainahin maganan shi ne sun jure.
A nan "mulki" na nufin mulkin Allah kamar sarki. AT: "Mutane za su faɗa wannan sako game da mulkin Allah"
A nan, "alummai" na nufin mutane. AT: "dukka mutane a dukka wurare"
"ƙarshen duniya"
AT: "mara kunya wadda ya ƙazantad da abubuwan Allah, game da wadda Daniyel ya rubuto"
Ba Yesu ne na magana ba. Matthew ya ƙara wannan don ya shirya mai karatun da cewa Yesu ya na amfani da kalmomin da zai sa su yi tunani su kuma fasara.
Benen da Yesu ya yi zama na nan shimfiɗaɗɗe, kuma mutane na iya tsaya a kai.
Wannan wata hanya ne na ce "mata masu ciki."
"a wannan loƙacin"
"da ba sai kun gudu ba"
"loƙacin sanyi"
AT: "In Allah bai rage loƙacin wahalan ba, kowa zai mutu"
"mutane." Anan "mahaluki" hanya ne na ce dukka mutane.
AT: "Allah zai rage loƙacin wahalan"
"kada ku yarda da abubuwan karya da sun gaya maku"
A nan "yauɗare" magana ne na sa wani ya gaskanta wani abun da ba gaskiya ba. Ana iya juya wannan a jimloli biyu. AT: "don su ruɗi, in ya yiwu, har zababbun" ko "don su ruɗi mutane. In ya yiwu, za su ma ruɗi zababbun"
AT: "Idan wani ya ce faɗa maku cewa Almasihun na cikin jeji, kar"
AT: "Ko, idan wani ya gaya maku cewa Almasihun na cikin kuryar daka,"
"a cikin dakin ɓoye" ko "a cikin ɓoyeyyer wurare"
Wannan na nufin cewa Ɗan Mutum zai zo da sauri kuma za a iya ganin shi.
Yesu ya na maganar kansa a cikin na uku.
Mai yiwuwa wannan labari ne da mutanen zamanin Yesu sun fahimta. AT: 1) Loƙacin da Ɗan Mutum zai zo, kowa zai gan shi za su kuma san cewa ya zo, ko 2) duk inda matattun mutane a ruhaniya suke, annabawan karya za su kasance a wurin domin su gaya masu karya.
tsuntsaye da su ke cin jikin matattu ko matattun dabbobi
"sa'adda tsananin wannan loƙacin ya gama, ranan"
"loƙacin wahala"
AT: "Allah zai sa rana ta duhunta"
AT: "Allah zai girgiza abubuwa a cikin sarari da kuma saman sararin"
Yesu ya na maganar kansa a cikin na uku.
A nan "kabilu" na nufin mutane. AT: "dukka mutanen kabilun" ko "dukka mutane"
"Zai busa kaho ya kuma aiki mala'ikunsa" ko "zai sa mala'ika ya busa kahon, zai kuma aiki mala'ikunsa"
"mala'ikarsa za su tattara"
Waɗannan mutane ne da Ɗan Mutum ya zaba.
Dukka waɗannan na nufin abu ɗaya. Karin magana ne da ke nufin "daga koina." AT: "daga dukkan duniya"
Yesu ya na maganar kansa a cikin na uku. AT: "loƙacin zuwa na ya yi kusa"
"kusa da kofofin." Yesu ya yi amfani da misalin sarki ko mutum mai daraja da ke zuwa kusa da kofofin gari mai katanga. Magana ne da ke nufin loƙacin da Yesu zai shiga ba da daddewa ba.
A nan "wuce" hanya mai kyau ne a ce "mutu." AT: "wannan zamani ba za su mutu dukka ba"
AT: 1) "dukka mutane musa rai yau,"na nufin mutanen da suke rayayye a loƙacin da Yesu ya na magana, ko 2) "dukka mutane musa rai a loƙacin da waɗannan abubuwan da na faɗa maku ya faru." Yi kokari ku juya dukka don fasara ya iya yiwuwa.
"sai Allah ya sa dukka waɗannan abubuwa sun faru"
Kalmomin "sama" da "kasa" magana ne da ya kumshi komai da Allah ya hallita, musamman abubuwa da su na nan kamar dauwammamme. Yesu ya na ce wa kalmarsa, ba kamar waɗannan abubuwa ba, dauwammamme ne. AT: "Ko sama da kasa ma za su shude"
"ɓace"
A nan "kalmomi" na nufin abin da Yesu ya faɗa. AT: "abin da na faɗa zai zama gaskiya kulum"
A nan "rana" da "sa'a" na nufin daidan loƙacin da Ɗan Mutum zai dawo.
"ba ma Ɗan ba"
Wannan muhimmin laƙabi ne wa Yesu, Ɗan Allah.
Wannan muhimmin laƙabi ne wa Allah.
"A loƙacin da Ɗan Mutum zai zo, zai zama kamar loƙacin Nuhu."
Yesu ya na maganar kansa a na uku.
AT: " jirgin. Kuma mutanen ba su gane wani abu na faruwa ba"
AT: "ɗauke. haka ne zai zama a loƙacin da Ɗan Mutum zai zo"
Wannan ne loƙacin da Ɗan Mutum ya zo.
AT: 1)Ɗan Mutum zai ɗauki hanya ɗaya zuwa sama zai kuma bar ɗayan a duniya wa hukunci ko 2) mala'ikun za su ɗauki ɗaya don hukunci su kuma bar ɗayan wa albarka.
abin nika
"Domin abin da na faɗa gaskiya ne"
"yi hankali"
Yesu ya yi amfani da labarin maigida da bayi domin ya kwatanta wa almajiransa cewa su zauna a shirye domin zuwansa.
Yesu ya na faɗa cewa zai zo a loƙacin da mutane ba su zata ba, ba wai zai zo ya yi tsata ba.
"da ya tsare gidansa"
AT: "da bai bar wani ya shiga gidansa don ya saci abubuwa ba"
Yesu ya yi mafani da wannan tambaya domin ya sa almajiransa su yi tunani. AT: "To wanene amintaccen bawannan mai hikima wanda maigidansa ... lokaci."
"ba wa mutanen cikin gidan maigida abincinsu"
A nan "zuciya" na nufin hankali. AT: "na tunani a zuciyarsa"
AT: "Maigida ya ɗade da dawowa" ko "Maigida na ba zai dawo da sauri ba"
Dukka waɗannan maganganun na nufin abu ɗaya. Su na nanata cewa Uban gidan zai zo a loƙacin da bawan bai zata ba.
Wannan ƙarin magana ne da na nufin a sa mutum ya sha wuya sosai.
"sa shi da munafukai" ko "tura shi zuwa wurin da ana tura munafukai"
"cizon hakora" anan alama ne, da ke wakilcin wahala mai tsanani. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 8: 12. AT: "mutane za su yi kuka da cizon hakoransu saboda wahalarsu"
Yesu ya yi annabci cewa ba ko dutse ɗaya na haikalin da za'a bari akan ɗan'uwansa wanda ba za'a rushe shi ba.
Almajiran suka tambaye Yesu loƙacin da waɗannan abubuwan za su faru, da kuma abin da zai zama alamar zuwarsa da kuma karshen duniya?
Yesu ya ce da yawa za su zo su ce su ne almasihu, kuma za su sa da yawa su kauce.
Yesu ya ce yake-yake, yunwa da girgizar kasa za su zama farkon ciwon haihuwa.
Yesu ya faɗa cewa masubi za su sha azaba kuma wasu za su yi tuntuɓe su kuma bashe juna.
Duk wanda ya jure har karshe, zai sami ceto.
Za'a yi wa'azin bisharar mulkin a dukkan duniya kafin karshen ya zo.
Yesu ya ce masubi su gudu zuwa kan duwatsu.
A wannan loƙaci tsanani zai zama mai girma, fiye da wanda ba'a taba yin irin shi tun farkon duniya.
Annabawan karya za su nuna alamu da al'ajibai, don su yaudari masu yawa.
Zuwan Ɗan Mutum zai zama kamar walkiya mai haskakawa daga gabas zuwa yamma.
Rana da wata za ta duhunta kuma taurari za su fado daga sama.
Kabilun duniya za su buga ƙirazarsu.
Karar kaho mai ƙarfi ne za a ji a loƙacin da malai'kun sun tattara zababbu.
Yesu ya ce wannan zamanin ba zai wuce ba, sai dukkan wadannan abubuwan sun faru.
Yesu ya ce sama da kasa za su shude, amma kalmomisa ba za su shude ba.
Uban ne kadai ya san loƙacin da waɗannan abubuwa zasu faru
Mutanen za su ci su na sha, su na aure su na aurarwa ba tare da sanin komai na hukunci mai zuwa da zai kaushesu ba.
Yesu ya faɗa cewa masubi su yi zama da shiri, domin basu san ranar da Ubangiji zai zo ba.
Amintaccen bawanna mai hikima na kula da gidan maigidansa a loƙacin da magidansa ya yi tafiya.
A loƙacin da ya dawo, mai gidan zai dora amintaccen bawannan mai hikima a kan dukkan a binda yake da shi.
Mugun bawa na dukan 'yan'uwansa barori ya kuma ci ya sha da mashaya sa'ad da maigidansa ba ya nan.
Idan ya dawo, maigidan zai datsa mugun bawa so biyu ya kuma kai shi inda a ke kuka da cizon hakora.
1 Sa'annan mulkin sama zai zama kamar budurwai goma da suka dauki fitilunsu domin su taryi ango. 2 Biyar daga cikin su masu hikima ne biyar kuma wawaye. 3 Sa'adda wawayen budurwai suka dauki fitilunsu, ba su dauki karin mai ba. 4 Amma budurwai masu hikimar suka dauki gorar mai tare da fitilunsu. 5 To da angon ya makara, dukkan su sai suka fara gyangyadi sai barci ya dauke su. 6 Amma da tsakkar dare sai aka yi shela, 'Ga ango ya iso! Ku fito taryensa. 7 Sai dukka budurwan nan suka tashi suka gyaggyara fitilunsu. 8 Wawayen su ka ce da masu hikimar, 'Ku sammana kadan daga manku gama fitilunmu su na mutuwa.' 9 "Amma masu hikimar suka ce 'Tun da man ba zai ishe mu tare da ku ba, sai ku je gun ma su sayarwa ku sayo wa kanku. 10 Sa'adda suka tafi sayan man, sai angon ya shigo, kuma wadanda suke a shirye su ka shiga tare da shi bukin auren, sai aka rufe kofar. 11 Bayan dan lokaci kadan sauran budurwan suka dawo suna cewa, 'Mai gida, mai gida, bude mana kofar.' 12 Amma ya amsa ya ce, 'A gaskiya ina gaya maku, ni ban san ku ba.' 13 Don haka sai ku lura, don baku san rana ko sa'a ba. 14 Domin yana kama da wani mutum da zai tafi wata kasa. Ya kira barorinsa ya ba su dukiyar sa. 15 Ga wani ya ba shi talanti biyar, ga wani ya ba shi biyu, ga wani kuma ya ba shi talanti daya. kowa an bashi gwargwadon iyawarsa, sai wannan mutum ya yi tafiyar sa 16 nan da nan sai wanda ya karbi talanti biyar ya sa nasa a jari, ya sami ribar wasu talanti biyar. 17 Haka ma wanda ya karbi talanti biyu ya sami ribar wasu biyu. 18 Amma bawan da ya karbi talanti dayan ya yi tafiyar sa, ya haka rami, ya binne kudin mai gidansa. 19 To bayan tsawon lokaci sai ubangidan barorin nan ya dawo, domin yayi lissafin kudinsu. 20 Bawan da ya karbi talanti biyar, ya kawo nasa da ribar wasu biyar. Yace, 'Maigida, ka bani talanti biyar, gashi na samo ribar karin talanti biyar.' 21 Maigidansa yace masa, 'Madalla, bawa na gari mai aminci! Ka yi aminci akan abu kadan. Zan sa ka akan abubuwa masu yawa. Ka shiga cikin farincikin maigidanka.' 22 Bawan da ya karbi talanti biyun, ya zo yace, 'Maigida, ka ba ni talanti biyu. Gashi kuwa na sami karin ribar wasu biyun.' 23 Ubangidansa yace masa, 'Madalla, kai bawa na gari mai aminci! Ka yi aminci akan abubuwa kadan. Zan saka akan abubuwa masu yawa. Ka shiga cikin farincikin maigidanka.' 24 Sai bawan da ya karbi talanti daya ya zo yace, 'Maigida, na san kai mai tsanani ne. Kana girbi inda baka yi shuka ba, kuma kana tattarawa inda ba ka watsa ba. 25 Na ji tsoro, don haka sai na je na boye talantinka a rami. Duba, ga abinda yake naka.' 26 Amma ubangidansa ya amsa yace, kai mugu malalacin bawa, ka san cewa ni mai girbi ne inda ban shuka ba kuma ina tattarawa inda ban zuba ba. 27 To da ba sai ka kai kudina a banki ba, da bayan na dawo da sai in karbi abina da riba. 28 Saboda haka ku kwace talantin daga gare shi ku baiwa mai talanti goman nan. 29 Gama ga wanda yake da shi za'a kara masa har ma a yalwace za'a kara bashi. Amma ga wanda bashi da komai abinda ke nasa ma za'a kwace. 30 Ku jefa wannan mugun bawan marar amfani, cikin duhu mai zurfi, inda ake kuka da cizon hakora.' 31 Sa'adda Dan mutum zai zo cikin daukakarsa da dukan Mala'iku tare da shi, sa'annan zai zauna kursiyinsa na daukaka. 32 A gabansa za'a tattara dukkan al'ummai, zai rarraba mutanen daya'daya, kamar yadda makiyayi yake rarraba tumaki daga awaki. 33 Zai sa tumakin a hannunsa na dama, amma awakin a hannunsa na hagu. 34 Sa'annan sarkin zai ce wa na hannun damarsa, 'Ku zo ku da Ubana ya albarkata, ku gaji mulkin da aka shirya maku kafin a kafa duniya. 35 Gama na ji yunwa kuka bani abinci; Na ji kishi kuka bani ruwa; Na yi bakunci kun bani masauki; 36 Na yi huntanci kuka tufasar dani; Na yi ciwo kuka kula dani; Ina kurkuku kuka ziyarceni.' 37 Sa'annan masu adalcin za su amsa su ce, 'Ubangiji, yaushe muka ganka kana jin yunwa muka baka abinci? Ko kana jin kishi muka baka ruwan sha? 38 Kuma yaushe muka ganka kana bakunci har muka baka masauki? Ko kuma kana huntanci da muka tufatar da kai? 39 Yaushe kuma muka ganka kana ciwo ko a kurkuku har muka ziyarce ka?' 40 Sa'annan Sarkin zai amsa masu yace, 'Hakika Ina gaya maku, duk abinda kuka yi wa daya mafi kakanta daga cikin 'yan'uwana a nan ni kuka yi wa.' 41 Sa'annan zai cewa wadanda suke hannunsa na hagu, 'Ku rabu da ni, ku la'anannu, ku tafi cikin wutar jahannama da aka shirya wa Shaidan da aljannunsa, 42 domin ina jin yunwa baku bani abinci ba; ina jin kishi ba ku bani ruwa ba; 43 Ina bakunci amma baku bani masauki ba; ina huntanci, baku tufasar da ni ba; ina ciwo kuma ina kurkuku, baku kula da ni ba.' 44 Sa'annan suma zasu amsa su ce, 'Ubangiji, yaushe muka ganka kana jin yunwa, ko kishin ruwa, ko kana bakunci, ko kana huntanci, ko ciwo, kuma a kurkuku, da bamu yi maka hidima ba?' 45 Sa'annan zai amsa ya ce masu, 'Ina gaya maku hakika abin da baku iya yiwa mafi karanta daga cikin wadannan ba, ba ku yi mani ba.' 46 Wadannan kuwa zasu tafi cikin madawwamiyar azaba amma adalai zuwa rai madawwami."
Yesu ya ba da labarin budurwai masu hikima da wawaye don ya bayyana cewa almajiransa su shirya don dawowarsa.
A nan "mulkin sama" na nufin mulkin Allah kamar sarki. An yi amfani da jumlar "mulkin sama" a cikin Matthew ne kadai. In ya yiwu, yi amfani da "sama" a juyinku. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 13:24. AT: "Sa'ad da Allahn mu a sama ya nuna kansa sarki, zai zama kamar"
AT: 1) fitilu ko 2) jiniya da an yi su daga sa tufaffi a karshen itace da kuma jika tufaffun da mai.
"budurwai biyar"
"su na da mai na cikin fitilar su kadai"
An yi amfani da wannan kalma don a sa alama a ainahin labarin. Yesu anan ya fara faɗan sabon sashin labarin.
AT: "sa'ad da angon ya ɗauki tsawon lokaci kafin ya isa"
"gyangyadi ya ɗauke dukka budurwai goman"
"wani ya yi ihu"
"gyaggyara fitilinsu don ya ci da haske"
AT: "Wawayen budurwan su ka ce da budurwan masu hikimar"
Wannan ƙarin magana ne. AT: "wutan cikin fitilunmu sun yi kusan mutuwa"
"wawayen budurwai biyar suka tafi"
AT: "zuwa sayan mai"
Wannan budurwan ne da suke da sauran mai.
AT: "bayin suka rufe kofan"
Ana iya sa wannan bayyani a bayyane. AT: "buɗe ma na kofa don mu iya shiga ciki"
"Ina gaya maku gaskiyan." Wannan na kara nanata a abin da mai gidan zai ce.
"Ban san wanene kai ba." wannan ne ƙarshen labarin.
A nan "rana" da "sa'a" na nufin abu ɗaya. Ana iya sa bayanin a bayyane. AT: "ba ku san ainahin lokacin da Ɗan Mutum zai dawo ba"
"mulkin Allah na nan kamar " (Dubi: Matthew 13:24)
"ya shirya tafiya" ko "ya kusan tafiya"
"ya sa su kula da dukiyarsa"
"dukiyar sa"
"talanti biyar na zinariya." Daina juya wannan zuwa kuɗin zamani. "Talanti" na zinariya ya kan kai kuɗin shekaru ashirin. Labarin ya na bayyana irin kuɗin biyar, biyu, da ɗaya da kuma babban dukiya da ke ciki. AT: "jaka biyar na zinariya" ko "jaka biyar na zinariya, kowanne ya kai kuɗin shekaru ashirin"
An fahimci kalmar "talanti" daga jumla da ta wuce. AT: "ga wani ya ba shi talanti biyu na zinariya ... ba da talanti ɗaya na zinariya" ko "ga wani ya ba shi jakan zinariya biyu ... ba da jakan zinariya ɗaya"
Ana iya bayyana wannan bayanin. AT: "bisa iyawar kowane bawa a bi da dukiya"
"daga cikin jarinsa, ya sami ribar talanti biyar"
"sami wani talanti biyu"
"na samo ribar karin talanti biyar"
"Talanti" ya kai ƙudin shekaru ashirin. Daina juya wannan zuwa kuɗin zamani. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 25:15.
"Ka yi koƙari" ko "Ka yi daidai." Al'adan ku na iya samin bayyyani da maigida (ko wani a mulki) zai yi amfani don ya nuna cewa ya amince da abin da bawansa (ko wani a karkashinsa) ya yi.
Jumlar "shiga cikin farincikin" ƙarin magana ne. Kuma, maigidan ya na naganar kansa ne a cikinsa na uku. AT: "Zo ku yi murna da ni"
"na sami ribar talenti biyu"
Kalmomin "girbi inda baka yi shuka ba" da "tattarawa inda ba ka watsa ba" na nufin abu ɗaya ne. Su na nufin manomin da yake tattara amfanin gona da waɗansu mutane sun shuka. Bawan ya yi amfani da wannan magana don ya yi zargin maigidan da ɗaukan abubuwan waɗansu.
"watsa iri." Wannan na nufin shuka iri ta wurin jefawa a hankali cike da hanu a cikin ƙasa.
"Duba, ga abinda da ke naka"
"Kai mugun bawa ne wadda ba ya so ya yi aiki. Ka san"
Kalmomin "girba inda ban shuka ba" ko " tattarawa inda ban zuba ba" na nufin abu ɗaya ne. Su na nufin manomin da ya ke tattara amfanin gona da mutanen da sun yi masa aiki sun shuka. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 25: 24, inda bawan ya yi amfani da waɗannan kalmomi biyu don ya yi zargin manomin. Mai karatun ya gane cewa manomin na amince cewa ya na tattara abin da waɗansu sun shuka amma ya na cewa daidai ne ya yi haka.
AT: " ƙarbi ƙudi na"
biya daga banki domin yin amfani da ƙudin mai gidan na dan loƙaci.
Mai gidan na magana da sauran bayin.
"Talanti" ya kai ƙudin shekaru ashirin. Daina juya wannan zuwa kuɗin zamani. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 25:15.
Ya na nufin cewa wanda ke da wani abu na amfani da shi da hikima. AT: "wanda ya na amfani da abin da ya na da shi da kyau"
AT: "Allah zai ba da fiye" ko "Zan ba da fiye"
"har fiye da"
Ya na nufin cewa mutumin na da wani abu amma ba ya amfani da shi da hikima. AT: "ga wanda ba ya amfani da abin da ya ke da shi da kyau"
AT: "Allah zai kwace" ko "Zan ƙwace"
Anan "duhu mai zurfi" magana ne na inda da Allah na tura waɗanda sun ki shi. Wannan wuri ne da ke rabe daga Allah har abada. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 8:12. AT: "wuri mai duhu mai nisa daga Allah"
"cizon hakora" anan alama ne, da ke wakilcin wahala da bakin ciki mai tsanani. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 8: 12. AT: "kuka da nuna tsananin wahalarsu"
Yesu ya na magana game da kansa a cikin mutum na uku.
AT: "Zai tattara dukka al'ummai a ganbansa"
"A gabansa"
A nan "al'ummai" na nufin mutane. AT: "dukka mutane daga kowane ƙasa"
Yesu ya yi amfani da ƙarin magana don ya kwatanta yadda zai raɓa mutanen.
Wannan magana ne da na nufin cewa Ɗan Mutum zai raɓa dukka mutane. Zai sa mutane masu adalci a hannun damarsa, ya kuma sa masu zunubi a hannan hagunsa.
A nan, "sarkin" wani laƙabi ne wa Ɗan Mutum. Yesu ya na nufin kansa a mutum na uku. AT: "Ni, sarki, ... hannun damana"
AT: "Zo, ku da Ubana ya albarkance ku"
Wannan muhimmin laƙabi ne wa Allah da ke kwatanta ɗangartaka tsakanin Allah da Yesu.
AT: "ku gaji mulkin da Allah ya shirya maku"
"tun da ya halittce duniya"
AT: "mutane masu adalci"
AT: "Ko yaushe mun gan ka na kishi ... Ko yaushe mun gan ka na tsirara"
Wannan wani laƙabi ne wa Ɗan Mutum. Yesu ya na magana game da kansa a mutum na uku.
"gaya wa waɗanda suke hannun hagunsa"
" ɗaya mafi daraja"
A nan " 'yan'uwa" na nufin kowai, na miji ko mace, da na biyyaya da sarkin. AT: " 'yan'uwana maza da mata anan" ko "waɗannan da su na nan kamar 'yan'uwana maza da mata"
"Na duba cewa kun yi mani"
"Sa'annan Sarkin zai." Yesu ya na maganar kansa a cikin mutum na uku"
"ku mutanen da Allah ya la'ananta"
AT: "wutar jahannama da Allah ya shirya"
masu taimakonsa
An fahimci kalmomin "ina" riga "tsirara." AT: "ina tsirara, baku tufasar da ni ba"
An fahimci kalmomin "ina" riga "ciwo." AT: " ina ciwo kuma ina kurkuku"
Wannan ne ƙarshen sashin labarin da ya fara a cikin 23
"waɗanda suke hagunsa za su amsa"
"wa mafi ƙaƙantan mutane na"
"Na duba cewa ba ku yi mani ba" ko "Ni ne wanda ba ku taimake ni ba"
"Sarkin zai turo waɗannan zuwa inda za su ƙarbi azaba da ba ya karewa"
AT: "amma sarkin zai turo adalai zuwa inda za su zauna har abada tare da Allah"
Budurwai marasa hikima ba suka ɗauki gorar mai tare da fitilunsu ba.
Budurwai masu hikima suka ɗauki gorar mai tare da fitilunsu.
Angon ya zo da tsakkar dare wanda ba loƙacin da an zata ba.
Budurwai masu hikima sun tafi tare da angon bukin auren.
Budurwai marasa hikima sun je su saya mai, sai da suka dawo an rufe masu kofar bukin.
Yesu ya ce masubi su yi lura, lura, don basu san rana ko sa'a ba.
Bawa mai talanti biyar ya sake yin wani talanti biyar, kuma mai talanti biyu ya sake yin talanti biyu.
Bawa mai talanti ɗaya ya haka rami a kasa, sai ya binne kuɗin mai gidansa.
Mai gidan ya yi tafiya na tsawon lokaci.
Maigidansa yace, 'Madalla, bawa na gari mai aminci! sai ya sa su kula da abubuwa masu yawa.
Mai gidan ya ce "Kai mugu malalacin bawa," ya karbi talanti ɗayan daga wurinsa sai ya jefa shi cikin duhu.
Ɗan Mutum zai tattara dukkan al'ummai, zai kuma rarraba mutanen ɗaya'ɗaya.
Waɗanda suke hannun damar Sarki za suu gaji mulkin da aka shirya masu daga kafa duniya.
Waɗanda suke hannun damar Sarki sun ba masu jin yunwa abinci, ruwa wa masu jin kishi, ƙarbi baki, tufasar da marasa sutura, kula da marasa lafiya sun kuma ziyarce wanda su na kurkuku.
Waɗanda suke hannun hagun Sarki za su karbi wutar jahannama da aka shirya wa Shaidan da mala'ikunsa
Waɗanda suke hannun hagun Sarki ba su ba masu jin yunwa abinci ba, ruwa wa masu jin kishi, ƙarbi baki, tufasar da marasa sutura, kula da marasa lafiya ko ziyarce wanda su na kurkuku ba.
1 Yayin da Yesu ya gama fadi masu wadannan maganganu, sai ya cewa almajiransa, 2 "Kun sani sauran kwana biyu idin ketarewa ya zo, kuma za'a bada Dan mutum domin a gicciye shi. 3 Sa'annan manyan firistoci da dattawan jama'a suka taru a fadar babban firist, mai suna Kayafa. 4 Suka shirya yadda zasu kama Yesu a boye su kuma kashe shi. 5 Amma suna cewa, "Ba a lokacin idin ba, domin kada tarzoma ta tashi daga cikin mutane." 6 Sa'adda Yesu yake Baita'anya a gidan Saminu Kuturu, 7 daidai lokacin da ya zauna a gefen teburin cin abinci, sai wata mata ta shigo da kwalbar mai, mai tsada, ta zuba wa Yesu a kansa. 8 Amma da almajiransa suka ga haka, sai suka ji haushi suka ce, "Ina dalilin yin irin wannan asara? 9 Ai da an sayar da wannan mai da kudi mai yawa a rabawa talakawa." 10 Amma da yake Yesu ya san tunaninsu, sai yace masu, "Don me kuke damun matar nan? Ta yi abu mai kyau domina. 11 Kuna da talakawa tare da ku koyaushe, amma ni ba zan kasance da ku ba koyaushe. 12 Don a sa'adda ta zuba man nan a jikina, ta yi haka ne don jana'iza ta. 13 Hakika Ina gaya maku, duk inda za ayi wannan bishara a dukan duniya, abin da matar nan tayi za'a rika ambatar da shi don tunawa da ita." 14 Sai daya daga cikin sha biyun, mai suna Yahuza Iskariyoti, ya tafi wurin manyan firistocin, 15 yace, "Me kuke da niyyar bani idan na mika maku shi?" Suka auna masa azurfa talatin. 16 Daga wannan lokacin yayi ta neman zarafi da zai bada shi a wurinsu. 17 To a rana ta fari na idin ketarewa almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, "Ina kake so mu shirya maka da zaka ci abincin idin ketarewa?" 18 Yace, "Ku shiga cikin birnin zaku sami wani mutum sai kuce masa, 'Mallam yace, "lokaci na ya kusa. Zan ci idin ketarewa a gidanka, da almajiraina."'" 19 Almajiran suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su, suka shirya abincin idin ketarewar. 20 Da yamma ta yi, sai ya zauna domin ya ci tare da almajiransa goma sha biyu. 21 Sa'adda suke ci, yace, "Hakika ina gaya maku, daya daga cikin ku zai bada ni." 22 Suka yi bakin ciki, suka fara tambayarsa daya bayan daya, "Na tabbata ba ni bane ko, Ubangiji?" 23 Sai ya amsa, "Wanda ke sa hannu tare da ni cikin kwano daya shi ne zai bada ni. 24 Dan mutum zai tafi, kamar yadda aka rubuta akan sa. Amma kaiton mutumin da ta wurin sa za'a bada Dan mutum! Gwamma da ba'a haifi mutumin nan ba." 25 Yahuza da zai bada shi yace, "Mallam ko ni ne?" Yace masa, "Ka fada da kanka." 26 Yayin da suke ci, sai Yesu ya dauki gurasa, ya sa albarka, ya karya. Ya ba almajiran yace, "Ku karba, ku ci, wannan jiki nane." 27 Sai ya dauki kokon yayi godiya, Ya ba su yace, "Ku sha, dukanku. 28 "Gama wannan jinina ne na alkawari wanda aka zubar domin gafarar zunuban mutane da yawa. 29 Amma ina gaya maku, ba zan kara shan ruwan inabin nan ba, sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a cikin mulkin Ubana." 30 Da suka raira waka, sai suka ka tafi dutsen zaitun. 31 Sai Yesu yace masu, "Dukan ku zaku yi tuntube a wannan dare sabili da ni, gama a rubuce yake, "Zan bugi makiyayin, garken tumakin kuma za su watse.' 32 Amma bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa Galili." 33 Amma Bitrus yace masa, "Ko dama duka zasu fadi sabili da kai, ni kam bazan fadi ba." 34 Yesu yace masa, "Hakika ina gaya maka, a wannan daren kafin carar zakara, za ka yi musun sani na sau uku." 35 Bitrus yace masa, koda zan mutu tare da kai, bazan yi musunka ba." Sai sauran almajiran suma suka fadi haka. 36 Sa'anna Yesu ya tafi tare da su, wurin da ake kira Getsaimani sai yace wa almajiransa, "Ku zauna a nan ni kuma zan je gaba in yi addu'a." 37 Ya dauki Bitrus da kuma 'ya'ya biyu na Zabadi tare da shi, sai ya fara damuwa da juyayi. 38 Sai yace masu, "Raina na cikin damuwa sosai har ga mutuwa. Ku kasance anan kuna tsaro tare da ni." 39 Ya dan taka zuwa gaba kadan, sai ya fadi a fuskarsa, yayi addu'a. Yace, "Ya Ubana, in zai yiwu, bari kokon nan ya wuce ni. Duk da haka, ba nufina za'a bi ba, amma naka nufin." 40 Ya koma wurin almajiran ya same su suna barci, sai ya cewa Bitrus, "Kai, ba zaku yi tsaro tare da ni ba koda sa'a daya? 41 Ku yi tsaro kuma, kuyi addu'a domin kada ku fada cikin jaraba. Ruhu dai ya yarda amma, jiki ba karfi." 42 Sai ya koma karo na biyu yayi addu'a, Yace, "Ya Ubana, in wannan kokon ba zai wuce ba sai na sha shi, bari nufinka ya kasance." 43 Ya sake dawowa, ya same su suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi. 44 Sai ya sake barinsu ya tafi. Ya koma karo na uku yana addu'a yana fadin kalmomi iri daya. 45 Sai Yesu ya koma wurin almajiran yace masu, "Har yanzu barci kuke kuna hutawa? Duba, lokaci ya kusato, kuma an bada Dan mutum ga hannun masu zunubi. 46 Ku tashi mu tafi. Duba, wanda zai badani ya kusato." 47 Sa'adda yana cikin magana Yahuza, daya daga cikin sha biyun, ya zo. Babban taro ya zo tare da shi daga wurin manyan firistoci da dattawan jama'a. Suna rike da takubba da kulake. 48 To mutumin da zai bada Yesu ya rigaya ya basu alama, cewa, "Duk wanda na sumbata, shine. Ku kama shi." 49 Nan da nan ya kaiga Yesu ya ce, "Gaisuwa, Mallam!" sai ya sumbace shi. 50 Yesu kuwa yace masa, "Aboki, kayi abin da ya kawo ka." Sai suka iso suka sa hannuwansu kan Yesu suka kama shi. 51 Nan take, daya daga cikin wadanda suke tare da Yesu ya mika hannunsa, ya zare takobinsa, ya sare wa bawan babban firist din kunne. 52 Sai Yesu yace, masa, "Ka maida takobinka cikin kubensa, domin duk wadanda suka dauki takobi su ma ta wurin takobi za su hallaka. 53 Ko kana tunanin ba zan iya kiran Ubana ba, ya kuma aiko da rundunar Mala'iku fiye da goma sha biyu? 54 Amma to tayaya za'a cika nassi, cewa dole wannan ya faru?" 55 A wannan lokacin Yesu yace wa taron, "Kun zo da takubba da kulake ku kama ni kamar dan fashi? Ina zaune kowace rana a haikali ina koyarwa, amma baku kama ni ba. 56 Amma duk wannan ya faru ne don a cika abinda annabawa suka rubuta." Bayan haka sai dukkan almajiran suka bar shi suka gudu. 57 Wadanda suka kama Yesu, suka kai shi wurin Kayafa babban firist, inda marubuta da duttawan jama'a suka taru. 58 Amma Bitrus ya bi shi daga nesa, har zuwa farfajiyar babban firist din. Ya shiga ya zauna da masu tsaro domin ya ga abinda zai faru. 59 A wannan lokaci manyan firistoci da duk 'yan majalisar suka fara neman shaidar karya akan Yesu, domin su samu su kashe shi. 60 Amma ba su samu ko daya ba, ko dayake an samu shaidun karya dayawa da suka gabata. Amma daga baya sai wasu su biyu suka fito 61 sukace "Wannan mutum yace zan iya rushe haikalin Allah, in kuma gina shi cikin kwana uku.'" 62 Babban Firist din ya tashi tsaye yace masa, "Ba zaka ce komai ba? Wace irin shaida ce ake yi akanka?" 63 Amma Yesu yayi shiru. Babban Firist ya ce, "Na umarce ka da sunan Allah mai rai, ka gaya mana ko kai Almasihu ne, Dan Allah." 64 Yesu ya amsa masa, "Ka fada da bakin ka. Amma ina gaya maka, daga yanzu zaka ga Dan mutun na zaune a hannun dama na iko, ya na zuwa akan gizagizai na sama." 65 Sai babban firist din ya yayyaga rigarsa, yana cewa, "Yayi sabo! don me ku ke neman wata shaida kuma? Duba, yanzu kun ji sabon. 66 Menene tunaninku?" Suka amsa sukace, "Ya cancanci mutuwa." 67 Sai suka tofa masa yawu a fuska, suka kuma yi masa duka, suka kuma mammare shi da tafin hannuwansu, 68 sukace, "Ka yi mana anabci, kai Almasihu. Wanene wanda ya dokeka. 69 To Bitrus kuwa na zaune a farfajiyar, sai wata yarinya baiwa ta zo wurinsa tana cewa, "Kaima kana tare da Yesu na Galili." 70 Amma ya yi musun haka a gaban su duka, yace, "Ban ma san abinda kike magana akai ba." 71 Da ya fita zuwa bakin kofa, nan ma wata yarinyar baiwa ta gan shi tace wa wadanda suke wurin, "Wannan mutumin ma yana tare da Yesu Banazare." 72 Sai yayi musun haka kuma, har da rantsuwa, yace, "Ban san mutumin nan ba." 73 Bayan dan lokaci kadan wadanda suke a tsaye suka zo wurin Bitrus suka ce masa, "Hakika kai daya daga cikin su ne, gama harshen ka ya tonaka." 74 Sai ya fara rantsuwa irin ta la'ana, yana cewa, "Ban san wannan mutumin ba," nan da nan zakara yayi cara. 75 Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya fada, "Kafin carar zakara zaka yi musun sani na sau uku." Sai ya fita waje yayi kuka mai zafi."
Wannan ne farkon sabon sashin labari da ke faɗa labarin gicciyen Yesu, mutuwarsa, da kuma tashinsa. Anan ya gaya wa almajiransa yadda zai sha wahala ya kuma mutu.
"Bayan" ko "Sai, bayan." Wannan jumla ya canza labarin daga koyarwar Yesu zuwa abin da ya faru.
Wannan ya na nufin duk abin da Yesu ya koyar daga 24:3.
AT: "waɗansu mazaje za su kai Ɗan Mutum zawa wurin wasu mutanen da za su gicciye shi"
Yesu ya na maganar kansa a cikin mutum na uku.
Waɗannan ayoyin sun ba da tushin bayani game da shirin shugabannin Yahudawa don su kama Yesu su kuma ƙashe shi.
AT: "suka haɗu"
"Yesu a ɓoye"
Ana iya sa a bayyane abin da shugabannin ba su so su yi a lokacin idin. AT: "Kada mu ƙashe Yesu a lokacin idin"
Wannan idin ketarewa ne na kowane shekara.
An yi amfani da wannan kalma anan domin a sa alama a ainahin labarin. Anan Matiyu ya fara ba da sabon labari.
Ana nufin cewa wannan ne mutumin da Yesu ya warkar daga kuturta.
"Yesu ya na ƙwanciye a gefensa." Za ku iya yin amfani da kalmar harshen ku a zaman da mutane su ke yi a loƙacin da su na cin abinci.
"mace ta zo wurin Yesu"
Wannan ƙwalba ne mai tsada da an yi shi daga dutse mai laushi.
mai da ke da kamshi mai kyau
Matan ta yi wannan don ta girmama Yesu.
Almajiran sun yi wannan tambaya don fushinsu akan ayyukan matan. AT: "Wannan matan ta yi mumunan abu ta wurin yin asaran wannan mai!"
AT: "Da ta sayar da wannan da ƙudi mai yawa a kuma ba da ƙudin"
Ana iya bayyana "talakawa." AT: "wa mutane talakawa"
Yesu ya yi wannan tambaya don ya ƙwabe almajiransa. AT: "Kaɗa ku dame wannan matan!"
"ku" na nufin almajiran.
AT: "mutane talakawa"
"Ina gaya maku gaskiyan." Wannan ya kara nanata abin da Yesu ya faɗa ne.
AT: "duk inda mutane sun yi wannan wa'azin bishara"
AT: "za su tuna da abin da wannan matan ta yi za su kuma gaya wa wasu game da ita" ko "mutane za su tuna da abin da matan ta yi za su kuma gaya wa wasu game da ita"
"don in kawo maku Yesu"
Tun da waɗannan kalmomi ɗaya ne da waɗanda su na cikin annabcin Tsohon Alkawari, bar wannan a maimakon canzawa zuwa ƙudin zamani.
"guda talatin"
"don a mika shi masu"
Wannan na da magana a cikin magana. AT: "Ya faɗa wa almajiransa cewa su je cikin gari zuwa wurin wani mutum su kuma faɗa mashi cewa Mallam ya ce masa, 'Lokaci na ya kusa. Zan ci idin ketarewa a gidanka, da almajiraina."' ko "Ya gaya wa almajiransa su je cikin gari zuwa wurin wani mutum sai su faɗa mashi cewa lokacin Mallam ya yi kusa kuma zai ci idin ketarewa a gidan wannan mutumin tare da almajiraina."
AT: 1) "lokacin da na gaya maku" ko 2) "Lokacin da Allah ya shirya mani."
AT: 1) "ya yi kusa" ko 2) "ya zo."
"ci abincin idin ketarewa" ko "yi bikin idin ketarewa ta wurin cin abinci"
Yi amfani da kalman zama da mutane a al'adan ku ke amfani da shi a lokacin cin abinci.
"Na tabbata cewa ba ni bane, ni ne, Ubangiji?" Wannan na iya nufin 1) wannan tambayar ganganci ne da shike almajiran sun tabbata cewa ba za su ba da Yesu ba. AT: "Ubangiji, Ba zan taba ba da kai ba!" ko 2) wannan tambaya ne na gaskiya tun da mai yiwuwa maganar Yesu ya dame su.
A nan "tafi" wata hanya ne na nufin mutuwa. AT: "zai tafi mutuwarsa" ko "zai mutu"
AT: "kamar yadda annabawa sun rubuto game da shi a cikin nassi"
AT: "mutumin da ya ba da Ɗan mutum"
"Mallam, ni ne zan ba da kai?" Mai yiwuwa Yahuza ya na amfani da wata tambaya ne don ya musanta cewa shi ne wadda zai ba da Yesu. AT: "Mallam, hakika ba ni zan ba da kai ba"
Wannan ƙarin magana ne da Yesu na amafini da shi kuma yana nufin "i". AT: Ka na faɗin haka" ko "Ka na amincewa da haka"
Dubi yadda kun juya waɗannan kalmomi a 14:19.
Juya "ɗauki" kamar yadda kun yi a cikin 14:19.
A nan "koko" na nufin kokon da ke da ruwan inabin a cikinta.
"ya ba wa almajiransa"
"Sha ruwan inabi daga wannan kokon"
"Gama wannan ruwan inabin jini na ne"
"jinin da ya sa alkawarin yiwuwa"
AT: "zai fito daga jikina" ko "zai fito daga jikina loƙacin da na mutu"
Wannan na kara nanaci akan abin da Yesu zai faɗa.
Wannan karin magana ne. AT: "ruwan inabi"
A nan "mulki" na nufin mulkin Allah kamar sarki. AT: "a lokacin da Ubana ya ƙafa mulkinsa a duniya"
Wannan muhimmin laƙabi ne wa Allah da ke ƙwatanta ɗangartaka da ke tsakanin Allah da Yesu.
wakar yabo ga Allah
"bar ni"
AT: "gama annabi Zakariya ya rubuto da daɗewa a cikin nassin"
A nan "zan" na nufin Allah. Ana nufin cewa Allah zai sa ko zai bar mutane su yi wa Yesu illa, su kuma ƙashe shi.
Waɗannan karin magana ne da ke nufin Yesu da almajiransa.
AT: "za su watsar da garken tumakin" ko "garken tumakin za su gudu a kowane lungu"
A nan tashi ƙarin magana ne na sa wani da ya mutu ya rayu kuma. AT: "bayan Allah ya tashe ni" ko "bayan Allah ya sa na rayu kuma"
Zakaru sun saba cara a lokacin da rana ta fito, don haka mai yiwuwa masu sauraron sun fahimci waɗannan kalmomi akan karin magana ne na fitan rana. Ko da shike, ainahin carar zakara muhimmin sashi ne a labarin nan gaba, don haka ku bar kalmar "zakara" a juyin.
kaza na miji, tsuntsun da ke kira da ƙarfi a ta lokacin da rana ta fito
Wannan sanannen kalmar nasara ce na abin da zakara ya ke yi don ya yi babban kiransa.
"za ka faɗa sau uku cewa kai ba mai bi na ba ne"
"ya yi bakin ciki sosai"
Anan "rai" ya na nufin dukkan mutum. AT: "Ina bakin ciki sosai"
Wannan karin magana ne. AT: "kuma na ji kamar zan iya mutuwa"
Ya ƙwanta da da fuska a ƙasa don ya yi addu'a.
Wannan muhimmin laƙabi ne wa Allah da ke nuna ɗangartaka sakanin Allah da Yesu.
Yesu ya na maganar aikin da dole ne ya yi, tar da mutuwa a kan gicciye, kamar ruwa mai ɗaci da Allah ya umurce ci ya sha daga kokon. Kalmar "koko" muhimmin kalma ce a cikin Tsabon Alkawari, ku yi koƙari ku yi amfani da shi a juyin ku.
A nan "koko" magana ne da na wakilcin koko da abin cikin. Abin cikin kokon magana ne na wahala da Yesu zai sha. Yesu ya na rokan Uban da cewa idan zai yiwu ma shi kada ya mutu, ya kuma sha wahala da Yesu ya san zai faru ba da juma ba.
Za a iya bayyana wannan kamar jimla. AT: "Amma kada ku yi abin da ina so; a maimako, yi abin da ku na so"
Yesu ya na magana da Bitrus, amma "ku" ɗaya ne, ya na nufin Bitrus, Yakub, da kuma Yahaya.
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya ƙwabe Bitrus, Yakub da Yahaya. AT: "Ina mamaki da cewa ba ku iya zama da ni na sa'a ɗaya ba!"
A nan ana iya bayyana "jaraba." AT: "kada wani ya jarabce ku cikin zunubi"
A nan "ruhu" magana ne da ke matsayin begen mutum ya yi abu mai kyau. "Jiki" na matsayin sha'awar jikin mutum. Yesu ya na nufin cewa almajiran za su iya samin sha'awar yin abin da Allah na so, amma bas u da ƙarfi a mutuntaka kuma su na kasawa. (Dubi: and
"Yesu ya tafi"
"idan wannan ne hanya kadai da wannan zai wuce shi ne idan na sha shi." Yesu ya yi maganar aikin da ɗole zai yi kamar ruwa ne mai ɗaci da Allah ya umurce shi ya sha.
A nan "wannan" na nufin kokon da abin da ke ciki, magana ne na wahala, kamar a cikin 26:39.
"sai dai na sha daga shi" ko "sai dai na sha daga wannan kokon wahala." Anan "shi" na nufin kokon da abin da na cikinsa, magana ne na wahala, kamar a cikin 26:39.
AT: "bari abin da ka ke so ya faru" ko "yi abin da ka na so"
Wannan ƙarin magana ne. AT: "su na jin barci"
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya ƙwabe almajiransa don yin barci. AT: "Ina mamaki da cewa har yanzu ku na barci da kuma hutawa!"
Wannan ƙarin magana ne. AT: "lokaci ya kai"
AT: "wani ya na bada Ɗan Mutum"
A nan "hannu" na nufin iko ko mulki. AT: "bada ga ikon masu zunubi" ko "bada domin masu zunubi su sami iko akansa"
"kasa kunne game da abin da zan gaya maku"
"Sa'adda Yesu ya na magana"
babban itce mai ƙarfi na buga mutane
A nan an yi amfani da "Yanzu" don a sa alama a ainahin labarin. Anan Matthew ya ba da tushen bayani game da Yahuza da kuma alama da ya shirya ya yi amfani don ya bada Yesu.
AT: "cewa duk wanda ya sumbuta shi ne wadda za su kama."
"Wanda na sumbata" ko "Mutumin da na sumbata"
Wannan amintacen hanya ne na gai da Mallam.
"Yahuza ya zo wurin Yesu"
"same shi da sumbata." Abokai masu hali za su sumbace juna a tsaurin ido, amma mai yiwuwa almajira zai sumbace mallaminsa a hannu don ya nuna ladabi. Ba bu wadda da ya san yadda Yahuza ya sumbace Yesu.
A nan "su" na nufin mutane masu takubba da kulake du su ka zo tare da Yahuza da shugabanin Yahudawa.
"riƙe Yesu, kuma kama shi"
Kalmar "Nan take" na sa mu ba da hankali akan bayani mai mamaki da ke biye.
Kalmar "takobi" magana ne na ƙashe wani da takobi. Ana iya sa a bayyane bayanin. AT: "wanda na ɗaukan takobi don ya ƙashe waɗansu" ko "wadda ya na so ya ƙashe waɗansu mutane"
"takobi za su mutu ta wurin takobin" ko "takobi-takobin ne wani zai ƙashe su"
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya tunawa mutumin da ke da takobin cewa Yesu zai iya hana waɗanda suke kama shi. AT: "Hakika ka san cewa zan iya kiran ... mala'uku"
A nan "ka" na nufin mutum mai takobin.
Kalmar "runduna" kalmace soja da ke nufin taron sojoji kusan dubu shida. Yesu na nufin cewa Allah zai turo da mala'iku dayawa don su iya hana waɗanda suke kama Yesu. Ainahin lambar mala'ikun ba su da muhimminci. AT: "fiye da ainahin babban taron mala'iku goma sha biyu"
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya bayyana dalilin da ya bar waɗannan mutane su kama shi. AT: "Amma idan ba yi ba, ba zan iya cika abin da Allah ya fada cewa dole ya faru a cikin nassi"
Yesu ya na amfani da wannan tambaya domin ya nuna mumunan ayukan masu kama shi. AT: "Kun san cewa ni ba mai fashi ba ne, ba daidai ba ne ku zo mani da takubba da kulake"
A nan nufin cewa Yesu ba ya cikin ainahin haikalin. Ya na ta farfajiyar haikalin.
AT: "Zan cika dukka abin da annabawa sun rubuto a cikin nassi"
Idan harshen ku na da kalma da na nufin sun bar shi a lokacin da ya kamata su kasance tare da shi, ku yi amfani da shi anan.
"Bitrus ya bi Yesu"
filli ne kusa da gidan babban firist
"Bitrus ya shiga ciki"
A nan "su" na nufin babban firistoci da membobin majalisa.
"iya samin dalilin ƙashe shi"
"maza biyu suka zo gaba" ko "shaiɗu biyu suka zo gaba"
Idan harshenku ba ta yarda da magana a cikin magana ba, za ku iya sake rubuta shi kamar magana ɗaya. AT: "Wannan mutum yace zai iya rushe ... kwanaki.'
"Wannan mutum Yesu ya ce"
"cikin kwana uku," kafin rana ta sauka sau uku, ba "bayan kwana uku ba," bayan rana ta sauka sau uku
Babban firist din ba ya tambayan Yesu game da abin da shaiɗun sun ce. Ya na tambayar Yesu don ya nuna cewa abin da shaidun sun ce ba daidai ba ne. AT: "Menene amsar ka game da abin da shaidun su na faɗa akanka?"
Wannan muhimmin laƙabi ne wa Allah da na ƙwatanta ɗangartaka sakanin Almasihu da Allah.
A nan "rai" na bambanta Allahn Isra'ila da allolin karya da gunki da mutane suke bauta. Allahn Isra'ila ne kadai na da rai kuma na da ikon aikatu. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 16:16.
Yesu ya na magana da babban firist da kuma sauran mutane a wurin.
AT: 1) jimlar "daga yanzu" magana ne da na nufin za su gan Ɗan Mutum a cikin ikonsa a wani lokaci gaba. ko 2) jumlar "daga yanzu" na nufin cewa daga lokacin shari'ar Yesu kuma nan gaba, Yesu ya na nuna kansa cewa shi ne Mai Ceto wadda na da iko da cin nasara.
A nan "Iko" magana ne da na wakilcin Allah. Zama a "hannun damar Allah" alama ne na karban babban daraja da iko daga Allah. AT: "a zaune a wurin daraja a gefen Allah mai iko dukka"
"zuwa duniya akan gizagizai na sama"
Yage tufafi alama ne na fushi da bakin ciki.
Dalilin da babban firist din ya kira maganar Yesu sabo shi ne wata kila ya fahimci kalmomin Yesu a cikin 26:64 da cewa shi daidai ne da Allah.
Babban firist ya yi amfani da wannan tambaya domin yă nanata cewa shi da membobin majalisa ba sau so su ji daga wasu shaiɗu. AT: "Ba mu so mu ji daga wani shaiɗu kuma ba!"
A nan "ku" na nufin mutanen majalisa.
AT: 1) Sai wasu mazajen" ko 2) "Sai sojojin."
An yi wannan kamar zagi ne.
A nan "yi mana anabci" na nufin faɗan ikon Allah. Ba ya nufin faɗan abin da zai faru a gaba.
Waɗanda suka buga Yesu ba su san cewa shi ne Almasihu ba. Sun kira shi haka don su yi masa ba'a.
Bitrus ya iya gane abin da yarinya baiwan ta na faɗa. Ya yi amfani da wannan kalmomi don ya musanta cewa ya na tare da Yesu.
"Loƙacin da Bitrus ya fita"
hanya a katangar farfajiyar
"faɗa wa mutanen da su na zaune a wurin"
"ya musanta kuma ta rantsuwa, 'Ban san mutumin ba!'"
"ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu"
AT: "Za mu iya ce kai daga Galili domin ya na magan kamar ɗan Galili"
"ya kira rantsuwa a kansa"
Zakara tsuntsu ne da na kira da ƙarfi a lokacin da rana ta fito. A na kiran karan da zakara na yi "carar." Dubi yadda kun juya wannan a cikin 26:34.
AT: "Bitrus ya tuna cewa Yesu ya faɗa ma shi cewa kafin zakara ya yi cara, zai musanta shi sau uku"
Yesu ya faɗa cewa idin ketarewa na zuwa a kwana biyu.
Su na shirin kama Yesu a ɓoye su kuma ƙashe shi.
Su na tsoro cewa idan sun ƙashe Yesu a ranar idin, mutane za su yi faɗa.
Almajiran sun yi fushi sun kuma so su san dalilin da ba a sayar a kuma ba wa matalauta ba.
Yesu ya faɗa cewa matan ta zuba man a kansa domin bison shi.
An biya Yahuza Iskariyoti azurfa talatin domin ya mika Yesu a hannun manyan firistoci.
Yesu ya faɗa cewa ɗaya daga cikin almajiransa zai bashe shi.
Yesu ya faɗa cewa zai zama gwamma wa mutumin da ya bashe shi da ba'a haifi shi ba.
Yesu ya amsa cewa, "Ka fada da kanka."
Yesu yace, "Ku karba, ku ci, wannan jiki na ne."
Yesu ya ce kokon jinisa ne na alkawari wanda aka zubar domin gafarar zunuban mutane da yawa.
Yesu ya faɗa wa almajiransa cewa za su watse a wannan daren sabili da shi.
Yesu ya faɗa cewa Bitrus zai musunta shi so uku a daren kafin zakarar ya yi cara.
Yesu ya ce masu su kasance anan suna tsaro tare da shi.
Yesu ya roka cewa in zai yiwu kokon nan ya wuce shi.
Almajiran suna barci a loƙacin da Yesu ya dawo daga addu'a.
Yesu ya bar almajiran so uku don ya je ya yi addu'a.
Yesu ya yi addu'a cewa nufin Uban ya yiwu, komin nufinsa.
Yahuza ya sumbaci Yesu a matsayin alama wa taron da cewa Yesu ne za su kama.
Daya daga cikin almajiran Yesu ya zare takobinsa, sai ya yanka kunnen bawan babban firist.
Yesu ya faɗa cewa zai iya kiran Uban, wanda zai aiko da rundunar Mala'iku.
Yesu ya faɗa cewa nassin na cikawa ta waɗannan abubuwa.
Dukka almajiran sun gudu sun bar shi.
Suna neman shaidar karya akan Yesu, domin su samu su kashe shi.
Babban Firist ya umarce Yesu ya gaya masu ko shi ne Almasihu, Dan Allah.
Yesu ya ce, "Ka fada da kanka".
Yesu ya ce babban firist zai gan Dan mutun a zaune a hannun dama na iko, ya na kuma zuwa akan gizagizai na sama.
Babban firist ya yi wa Yesu zargin yin saɓo.
Sun tofa wa Yesu yawu a fuska, suka kuma yi masa duka, suka kuma mammare shi da tafin hannuwansu.
Bitrus ya amsa cewa bai san Yesu ba.
Nan da nan da Bitrus ya amsa na uku, zakara yayi cara.
Bitrus ya tuna cewa Yesu ya faɗa cewa kafin zakarar ya yi cara, zai masunce shi so uku.
1 Da gari ya waye, duk manyan firistoci da dattawan jama'a suka shirya yadda zasu kulla makirci domin su kashe shi. 2 Suka daure shi, suka mika shi ga gwamna Bilatus. 3 Sa'adda Yahuza, wanda ya bashe shi, ya ga an zartarwa Yesu hukuncin kisa, ya nemi tuba ya kuma mayar da azurfar talatin ga manyan firistocin da dattawan, 4 yace, "Na yi zunubi ta wurin cin amanar mara laifi." Amma sukace, "Ina ruwan mu? Ka ji da shi da kanka?" 5 Sai ya jefar da kwandalolin azurfar a kasa cikin haikalin ya kuma bar su, ya tafi ya rataye kansa. 6 Sai babban firist ya dauki kwandalolin azurfar ya ce, "Ba daidai bane bisa ga shari'a musa wannan cikin ma'aji, saboda kudin jini ne." 7 Sai suka tattauna al'amarin a tsakanin su, kudin kuma suka sayi filin maginin tukwane domin makabatar baki. 8 Dalilin wannan ne ake kiran wurin, "Filin jini" har yau. 9 Sai abin da aka fada ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa, "Suka dauki tsabar azurfa talatin na farashin da mutanen Isra'ila suka sa a kansa, 10 suka bayar domin sayen filin mai tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni." 11 Sai Yesu ya tsaya a gaban gwamna, gwamna ya kuma tambaye shi, "Kai sarkin Yahudawa ne?" Yesu ya amsa, "Haka ka fada." 12 Amma da manyan firistocin da dattawan suka zarge shi, bai ce komai ba. 13 Sai Bilatus yace masa, "Baka ji dukan zarge-zargen da ake yi maka ba?" 14 Amma bai ce masa ko kalma guda ba, sai gwamna yayi matukar mamaki. 15 To lokacin bikin idi, al'adar gwamna ne ya saki mutum guda wanda jama'a suka zaba. 16 A wannan lokacin suna da wani sanannen dan kurkuku mai suna Barabbas. 17 To da suka tattaru, sai Bilatus yace masu, "Wa kuke so a sakar maku? Barabbas, ko Yesu wanda ake kira Almasihu?" 18 Saboda ya san sun kawo shi ne domin kishi. 19 Da yake zaune a kujerar shari'a, matarsa ta aika masa cewa, "Ka fita sha'anin mutumin nan marar laifi. Saboda na sha wahala sosai a yau cikin mafarki saboda shi." 20 A lokacin nan manyan firistoci da dattawa suka rinjayi ra'ayin jama'a suce a sakar masu da Barabbas, a kashe Yesu. 21 Sai gwamna ya tambayesu, "Wa kuke so a sakar maku?" Sukace, "Barabbas." 22 Bilatus yace masu, "Me zan yi da Yesu wanda ake kira Almasihu?" Sai duka suka amsa, "A gicciye shi." 23 Sai yace, "Don me, wane laifi ya aikata?" Amma suka amsa da babbar murya, "A gicciye shi" 24 Amma da Bilatus ya ga ba zai iya komai ba don hargitsi zai iya barkewa, ya dauki ruwa ya wanke hannuwansa a gaban jama'a, yace, "Ba ni da laifi ga jinin mutumin nan marar laifi. Ku yi abin da kuka ga dama." 25 Duka mutanen sukace, "Bari jininsa ya kasance a kan mu da 'ya'yan mu." 26 Sai ya sakar masu da Barabbas amma yayi wa Yesu bulala ya mika shi garesu domin su gicciye shi. 27 Sai sojojin gwamna suka dauki Yesu zuwa farfajiya suka kuma tara dukan rundunar sojoji. 28 Suka yi masa tumbur sa'annan suka sa masa jar alkyabba. 29 Sai suka yi masa rawanin kaya suka sa a kansa, suka kuma bashi sanda a hannunsa na dama. Suka rusuna a gabansa suna masa ba'a, suna cewa, "Ranka ya dade, Sarkin Yahudawa!" 30 Suka kuma tofa masa yawu, suka kwace sandar suka buga masa a ka. 31 Bayan sun gama masa ba'a, suka cire masa alkyabbar suka sa masa kayansa, suka jagorance shi zuwa wurin da za a gicciye shi. 32 Da suka fito waje, sai suka iske wani Bakurame mai suna Saminu, wanda suka tilasta ya tafi tare dasu domin ya dauki gicciyen. 33 Suka iso wani wuri da ake kira Golgotta, wanda ke nufin,"Wurin kwalluwa." 34 Suka bashi ruwan inabi da aka gauraya da wani abu mai daci. Amma da ya 'dan-'dana shi sai ya ki sha. 35 Bayan da suka gicciye shi, suka kada kuri'a a kan rigarsa. 36 Suka kuma zauna suna kallonsa. 37 A sama da kansa suka sa abinda ake tuhumarsa da ita a rubuce, "Wannan shine sarkin Yahudawa." 38 An gicciye shi da 'yanfashi guda biyu, daya ta damansa dayan kuma ta hagunsa. 39 Wadanda suke wucewa suna zaginsa, suna girgiza kai, 40 suna kuma cewa, "Kai da kace zaka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku, ka ceci kanka mana! In dai kai Dan Allah ne, ka sauko daga gicciyen!" 41 Ta haka ma manyan firistocin suka rika yi masa ba'a, tare da marubuta da shugabannin, suna cewa, 42 "Ya ceci wasu amma ya kasa ceton kansa. Shi ne sarkin Isra'ila. Ya sauko mana daga kan gicciyen, sai mu ba da gaskiya gareshi. 43 Tun da ya yarda da Allah. Bari Allahn ya cece shi mana, saboda yace, "Ni dan Allah ne." 44 Hakan nan ma 'yanfashin guda biyu da aka gicciye su tare suka zage shi. 45 To tun da tsakar rana sai duhu ya rufe kasar gaba daya har karfe uku na yamma. 46 Wajen karfe uku, Yesu ya tada murya mai karfi yace, "Eli, Eli lama sabaktani?" wanda ke nufin, "Allahna, Allahna, don me ka yashe ni?" 47 Da wadanda suke tsaye kusa suka ji haka, sai sukace, "Yana kiran Iliya." 48 Nan take wani ya ruga da gudu ya dauki soso ya tsoma cikin ruwan inabi mai tsami ya soka kan sandar kara ya mika masa ya sha. 49 Sai sauran sukace, "Rabu da shi mu gani ko Iliya zai zo ya cece shi." 50 Sai Yesu ya ta da murya mai karfi yayi kuka sai ya saki ruhunsa. 51 Sai labullen haikali ya yage gida biyu daga sama zuwa kasa. Kasa kuma ta girgiza, duwatsu suka farfashe. 52 Kaburbura suka bude, tsarkaka kuwa wadanda suke barci da yawa suka tashi. 53 Suka fito daga kaburbura bayan tashinsa, suka shiga birni mai tsarki suka bayyana ga mutane da yawa. 54 Da hafsan sojan da wadanda suke kallon Yesu suka ga girgizar kasar da abinda ya faru, suka ji tsoro kwarai sukace, "Hakika wannan Dan Allah ne" 55 Mata dayawa da suka bi Yesu daga Galili domin su lura da shi suka tsaya suna kallo daga nesa. 56 A cikin su akwai Maryamu Magadaliya, Maryamu uwar Yesu da Yusufu, da uwar 'ya'yan Zabadi. 57 Da yamma sai wani attajiri mutumin Armatiya ya zo, mai suna Yusufu wanda shi ma almajirin Yesu ne. 58 Ya je wurin Bilatus ya roka a bashi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a bashi. 59 Yusufu ya dauki jikin, ya rufe shi da likafani mai tsabta, 60 sai ya sa shi a cikin sabon kabarinsa da ya sassaka cikin dutse. Sai ya mirgina babban dutse a bakin kofar kabarin ya tafi. 61 Maryamu Magadaliya da dayan Maryamun suna nan zaune akasin kabarin. 62 Washegari, wato bayan ranar Shiri, Sai manyan firistoci da Farisawa suka taru tare da Bilatus. 63 Sukace, "Mai gida, mun tuna lokacin da mayaudarin nan yake da rai, yace, "Bayan kwana uku zan tashi." 64 Saboda haka, ka bada umarni a tsare kabarin na kwana uku. In ba haka ba almajiransa zasu zo su sace shi, kuma su ce wa mutane, "Ya tashi daga mattatu." Kuma yaudarar karshe zata fi ta farko muni." 65 Bilatus yace masu, "Ku dauki masu tsaro. Kuyi tsaro iyakar karfin ku." 66 Sai suka tafi suka tsare kabarin, suka hatimce dutsen, suka sa masu tsaro.
Wannan ne farkon labarin shari'ar Yesu a gaban Bilatus.
An yi amfani da wannan kalma domin a sa alamar fashi a ainahin labarin. Anan Matiyu ya fara faɗan sabon labari.
Shugabanin Yahudawa suna shirya yadda za su iya sa shugabannin Romawa su ƙashe Yesu.
Wannan abin ya faru a bayan shari'ar Yesu a gaban majalisar shugabannin adinin Yahudawa, amma ba mu san ko ya faru kafin shari'a ko lokacin shari'ar Yesu a gaban Bilatus ba.
Idan harshenku na da wata hanyar nuna cewa an fara sabon labari, za ku so ku iya amfani da shi a nan.
AT: "cewa shugabannin Yahudawa sun hukunta Yesu"
Wannan ne ƙudin da firistoci suka ba wa Yahuza don ya bashe Yesu. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 26:15.
Wannan ƙarin magana ne da na nufin mutuwar mai mara laifi. AT: "mutumin da bai cancanci mutuwa ba"
Shugabannin Yahudawa sun yi amfani da wannan tambaya domin su nanata cewa ba su damu da abin da Yahuza ya faɗa ba. AT: "Wannan ba damuwar mu bane!" ko "Wannan damuwar ku ne!"
AT: 1) ya jefar da kandalolin azurfar a cikin farfajiyar haikalin, ko 2) ya na tsaye a cikin farfajiyar haikalin, sai ya jefar da kwandalolin azurfar a cikin haikalin.
"Shari'ar mu ba ta yarda mana mu sa wannan"
"sa wannan azurfa"
Wannan ne wurin da sun ajiye ƙudin ne da suke amfani da shi don su tanada abubuwan da ake bukata a haikali da kuma firistoci.
Wannan karin magana ne da na nufin ƙudin da an biya mutumin da ya taimaka a ƙashen wani. AT: "ƙudin da an biya don mutum yă mutu"
Wannan fili ne da aka saya domin a binne baki da suka mutu a cikin Urushalima.
AT: "mutane suke kiran wannan filin"
Wannan na nufin har lokacin da Matiyu ya na rubuta wannan littafi.
AT: "Wannan ya cika abin da annabi Irimiya ya faɗa"
AT: "farashin da mutanen Isra'ila suka sa a kansa"
Wannan na nufin waɗanda su na cikin mutanen Isra'ila wadda sun biya don a ƙashe Yesu. AT: "waɗansu mutanen Isra'ila" ko "shugabanin Isra'ila"
A nan "ni" na nufin Irmiya.
"Bilatus"
Wannan na iya nufin 1) ta wurin faɗin haka, Yesu ya na nufin cewa shi ne Sarkin Yahudawa. AT : "I, kamar yadda ka faɗa, haka ne" ko "I, haka ne yadda ka ce" ko 2) ta faɗin haka, Yesu ya na faɗin cewa Bilatus, ba Yesu ba, ne na kiran sa Sarkin Yahudawa. AT: "Kai da kanka ne ka faɗi haka"
AT: "Amma lokacin da manyan firistocin da dattawan suka zarge shi"
Bilatus ya yi wannan tambaya domin ya na mamaki da yadda Yesu ya yi shiru. AT: "Ina mamakin cewa ba ka amsa waɗannan mutanen da sun yi zargin ka da yin abubuwan da ba daidai ba!"
"bai ce ko kalma ɗaya ba; wannan ya ba wa gwamna mamaki sosai." Wannan wata hanyar nanaci ne na faɗa cewa Yesu ya yi shiru.
Wannan ne bikin idin ketarewa.
AT: "ɗan kurkuku wadda jama'a za su zaba"
"akwai wani sanannen ɗan kurkuku"
sananne a yin mugun abu
AT: "taron sun tattaru"
AT: "wanda wasu mutane ke kira Almasihu"
"shugabannin Yahudawa sun kawo masa Yesu." Sun yi wannan domin Bilatus ya hukunta Yesu.
"Da Bilatus yake zaune"
"zaune a kujerar mai shari'a." Wannan ne wurin da mai shari'a zai zauna a yayin da ya na yanke hukunci.
" aika sako"
"na damu sosai yau"
An yi amfani da "yanzu" a nan don a sa alama a ainahin labarin. Matiyu ya ba da tushen bayani game da dalilin da ya sa taron suka zabi Barabbas.
AT: "sa sojojin Romawa su ƙashe Yesu"
"tambaye taron"
AT: "wanda waɗansu mutane suke kira Almasihu"
"Yesu ya aikata"
"taron suka amsa da babbar murya"
Bilatus ya yi wannan domin ya nuna cewa ba shi da hakin mutuwar Yesu.
A nan "jini" na nufin mutuwar wani. AT: "mattatu"
"wannan hakinku ne"
A nan "jini" magana ne da na matsayin mutuwar mutum. Jumlar "kasance a kan mu da 'ya'yan mu" ƙarin magana ne da na nufin cewa sun amince da hakin abin da na faruwa. AT: "I! Mu da zuriyarmu mun ɗauki hakin zartadda shi"
"Sai Bilatus ya sakar masu da Barabbas"
Ana nufin cewa Bilatus ya umurci sojojin don su bulali Yesu. Mika Yesu domin a gicciye shi ƙarin magana ne na sa sojojinsa su gicciye Yesu. AT: "ya umurci sojojinsa don su bulali Yesu su kuma gicciye shi" (Dubi: and )
"bulali Yesu"
"taron sojoji"
"cire tufafinsa"
jar walƙiya
"rawanin da an yi daga reshen kaya" ko "rawanin da an yi daga reshe masu kaya"
Sun ba Yesu sanda ya rike don ya wakilci sandar sarauta da sarki ke rikewa. Sun yi haka don su yi wa Yesu ba'a.
Su na faɗa haka domin su yi wa Yesu ba'a. Su na kiran Yesu Sarkin Yahudawa," amma ba su gaskanta cewa shi sarki ba ne. Kuma abin da suna faɗa gaskiya ne.
"Mun girmamaka" ko "Bari ka yi rayuwar tsawon lokaci"
"da yawunsu, sojojin suka tofa wa Yesu yawu"
Wannan na nufin Yesu da sojojin sun fita daga garin. AT: "Sa'adda suka fito daga Urushalima"
"sojojin sun gan wani mutum"
"wanda sojojin suka tilasta ya tafi tare dasu domin ya ɗauki gicciyen Yesu"
AT: "wuri da mutane na kira Golgotta"
AT: "shi ruwan inabi da suka gauraya da wani abu mai ɗaci"
ruwan 'yarani mai ɗaci da jiki na amfani da shi a narkewar abinci
Waɗannan tufafi ne da Yesu na sakawa.
"rubutaccen bayani na dalilin da aka gacciye shi"
AT: "Sojojin suka gicciye 'yan fashi biyu tare da Yesu"
Sun yi haka ne don su yi wa Yesu ba'a.
Ba su gaskanta cewa Yesu Ɗan Allah ba ne, sun so ya nuna har idan gaskiya ne. AT: "Idan kai ne Ɗan Allah, ka nuna ta wurin saukowa daga gicciyen"
Wannan muhimmin laƙabi ne wa Almasihu da ke nuna ɗangartakarsa da Allah.
AT: ) Shugabannin Yahudawa ba su gaskanta cewa Yesu ya ceci wasu ba ko ma zai iya ceton kansa ba, ko 2) sun gaskanta cewa ya ceci wasu amma suna dariyarsa domin bai iya ceton kansa yanzu ba.
Shugabannin na yi wa Yesu ba'a. Sun kira shi "Sarkin Isra'ila," amma ba su gaskanta cewa shi sarki ba ne. AT: "Ya faɗa cewa shi ne Sarkin Isra'ila"
AT: "Don Yesu ya faɗa cewa shi ne Ɗan Allah."
Ɗan Allah Wannan muhimmin laƙabi ne wa Yesu da ke ƙwatanta dangartakarsa da Allah.
AT: "'yan fashin da sojojin suka gicciye su tare da Yesu"
"daga rana ... na sa'a uku" ko "daga ƙarfe sha biyu na tsakar dare ... sai ƙarfe uku na rana"
Kalmar "duhu" mai zuzzurfar ma'ana ne. AT:
"Yesu ya yi ihu"
Waɗannan ne kalmomin da Yesu ya yi kira a cikin harshensa. Masu juyi su na kan bar waɗannan kalmomin a yadda suke.
AT: 1) ɗaya daga cikin sojojin ko 2) ɗaya daga cikin masu kallo.
Wannan wani abu ne da ake samunta a teku, ana kuma amfani da shi don a daga a kuma riƙe abu ruwa-ruwa. Ana iya matse waɗannan abubuwa ruwa-ruwan.
"mika wa Yesu"
A nan "ruhu" na nufin abin da na ba da rai wa mutum. Wannan jimlar wata hanya ne na cewa Yesu ya mutu. AT: "ya mutu, ya ba da ruhunsa wa Allah" ko "ya ja numfashinsa na ƙarshe"
Kalmar "gashi" anan ya shiryamu mu ne mu ba da hankali ga bayani na mamaki da na biye.
AT: "labullen haikali ya yage gida biyu" ko "Allah ya sa labullen haikali ya yage gida biyu"
AT: "Allah ya buɗe kaburburan ya tashi da tsarkakun mutane dayawa da suka mutu"
Tashi anan ƙarin magana ne na sa mutum da ya mutu ya kuma rayu. AT: "Allah ya sa rai a tsarkakun mutane da suka yi barci"
Wannan wata hanya ce na ce mutuwa. AT: "mutu"
Jerin abubuwa da suka faru ba su a bayane. Bayan girgizan ƙasa a lokacin da Yesu ya mutu kaburbura kuma suka buɗe 1) tsarkakun mutanen suka rayu kuma, sai kuma, Yesu ya rayu kuma, tsarkakun mutanen suka shiga Urushalima, inda mutane dayawa suka gan su, ko 2) Yesu ya rayu kuma, sai kuma tsarkakun sun rayu, sun kuma shiga cikin garin, inda mutane dayawa sun gan su.
"waɗanda suke tsaron Yesu." Wannan na nufin sojojin da ke tsaron Yesu tare da jarumin. AT: "sojojin tare da shi wanda suke tsaron Yesu"
"mahaifiyar Yakub da Yahaya" ko "matar Zabadi"
Wannan sunan wata gari ne a Isra'ila.
AT: " Sai Bilatus ya umarci sojojin su ba wa Yusufu jikin Yesu"
tufafi mai kyau da kuma tsada
Ana nufin cewa Yusufu na da ma'aikata da sun yanka kabarin a cikin dutsen.
Mai yiwuwa Yusufu na da waɗansu mutane a wurin da sun taimake shi mirgina dutsen.
"a ƙetare daga kabarin"
Wannan rana ce da mutane na sa komai a shirye domin Asabar.
"sadu da Bilatus"
"lokacin da Yesu, mayaudarin, yake da rai"
Wannan na da magana a cikin magana. AT: "ya ce bayan kwana uku zai tashi kuma."
AT: "umurce sojojinka su tsare kabarin"
"almajiransa zasu iya zuwa su sace jikin shi"
AT: "almajiransa zasu iya ... ce wa mutane ya tashi daga mattatu, kuma"
Daga dukka waɗanda sun mutu. Wannan magana ya nuna dukka mattatu a cikin duniya. Tashi daga sakaninsu na nufin zama rayeyye kuma.
AT: "kuma idan sun yaudare mutane ta faɗa cewa, zai zama da muni fiye da yadda ya yaudare mutane a da lokacin da ya ce shi ne Almasihu"
Wannan ya ƙunshi sojoji huɗu zuwa sha shida na Romawa.
Wannan na iya nufin 1) suka sa igiya a kewaye da dutsen sun kuma haɗa shi da bangon dutsen a dukka gafen kofan kabarin ko 2) sun sa hatimi a sakanin dutsen da bangon.
"gayawa sojojin su tsaya a inda za su iya hana mutane daga yin karambani da kabari"
Da gari ya waye, manyan firistoci da dattawan suka kai shi ga gwamna Bilatus.
Yahuza ya nemi tuban bashe jinin mara laifi, ya kuma mayar da azurfar talatin din, sai ya tafi, ya rataye kansa.
Suka sayi filin maginin tukwane domin makabatar baki.
Waɗannan abubuwan sun cika annabcin Irmiya.
Bilatus tambaye Yesu ko shi ne Sarkin Yahudawa, sai Yesu ya amsa cewa, "Haka ka fada."
Yesu bai amsa ko kalma ɗaya ba.
Bilatus ya so ya sake Yesu, bisa ga al'adun bikin idin ketarewa.
Ta gaya mashi cewa ya fita sha'anin wannan mutum mai mara laifi.
Manyan firistoci da dattawa suka rinjayi ra'ayin jama'a suce a sakar masu da Barabbas, a maimakon Yesu.
Jama'an sun ta da murya da cewa su na so a giciye Yesu.
Bilatus ya wanke hannuwansa, yace, ba shi da laifi ga jinin mutumin nan marar laifi, sai ya mika wa jama'an Yesu.
Mutanen sukace, "Bari jininsa ya kasance a kan mu da 'ya'yan mu."
Sojojin sun sa masa jar alkyabba da kuma rawanin kaya a kansa.
An tilasta Saminu da cewa ya ɗauki gicciyen Yesu.
Sun je Golgotta, wanda ke nufin, "Wurin kwalluwa."
Sojojin suka kada kuri'a a kan rigarsa suka kuma zauna suna kallonsa.
Sun rubuto, "Wannan shine sarkin Yahudawa."
An gicciye Yesu tare da 'yanfashi guda biyu, ɗaya ta damansa ɗayan kuma ta hagunsa.
Su yi ma Yesu ba'a cewa ya ceci kansa, ya kuma sauko daga kan gicciye.
Duhu ya rufe ƙasar gaba ɗaya har karfe uku na yamma.
Yesu ya tada murya mai ƙarfi yace, "Eli, Eli lama sabaktani?"
Yesu ya saki ruhunsa.
Labullen haikali ya yage gida biyu daga sama zuwa kasa bayan da Yesu ya mutu.
Tsarkaka dayawa kuwa waɗanda suke barci da yawa suka tashi sun kuma bayyana ga mutane bayan Yesu ya mutu.
Hafsan ya shaida cewa, "Hakika wannan Ɗan Allah ne"
Wani attajirin almajirin Yesu, Yusufu, ya roki Bilatus don a bashi jikin, ya rufe shi da likafani, ya kuma shimfiɗa shi a sabon kabari.
An mirgina babban dutse a bakin kofar kabarin da jikin Yesu yake.
Manyan firistoci da Farisawa sun so su tabatar cewa an tsare kabarin Yesu don kada wani ya iya tsata jikinsa.
Bilatus ya yarda masu su hatimce dutsen, su kuma sa masu tsaro.
1 Da daddare ranar Asabaci, rana ta fari ga mako ta fara gabatowa, Maryamu Magadaliya da daya Maryamun suka zo don su ziyarci kabarin. 2 Sai aka yi girgizar kasa mai karfi, saboda mala'ikan Ubangiji ya sauko daga sama ya kuma murgine dutsen ya zauna a kai. 3 Kamanninsa kamar walkiya, tufafinsa kuma fari fat kamar suno. 4 Masu tsaron suka razana don tsoro suka zama kamar matattun mutane. 5 Mala'ikan ya yi wa matan magana cewa, "Kada ku ji tsoro, nasan kuna neman Yesu wanda aka gicciye. 6 Baya nan, amma ya tashi kamar yadda ya fada. Ku zo ku ga wurin da aka kwantar da shi. 7 Ku hanzarta ku gaya wa almajiransa, 'Ya tashi daga matattu. Duba, ya tafi Galili, can zaku same shi.' Gashi ni kuwa na fada maku." 8 Matan suka yi hanzari suka bar kabarin da tsoro da murna, suka ruga domin su sanar wa almajiransa. 9 Sai ga Yesu ya tare su, yace masu, "A gaishe ku." Sai matan suka kama kafar sa, suka kuma yi masa sujada. 10 Sai Yesu yace masu, "Kada ku ji tsoro. Ku je ku fada wa 'yan'uwana su je Galili. Can zasu ganni." 11 Sa'adda matan suke tafiya, sai wadansu masu tsaro suka shiga gari suka fada wa Shugabanin Firistoci dukan abin da ya faru. 12 Firistocin suka hadu da dattawa suka tattauna al'amarin, sai suka bada kudi masu yawa ga sojojin 13 Sukace masu, "Ku gaya wa sauran cewa, "Almajiran Yesu sun zo da daddare sun sace gangar jikinsa lokacin da muke barci." 14 Idan wannan rahoto ya isa wurin gwamna, za mu lallashe shi mu ja hankalinsa mu raba ku da damuwa." 15 Sai sojojin suka karbi kudin suka yi abinda aka umarcesu. Wannan rahoto ya bazu a tsakanin Yahudawa, ya ci gaba har zuwa yau. 16 Amma almajiran sha daya suka tafi Galili, kan dutsen da Yesu ya umarcesu. 17 Da suka gan shi, suka yi masa sujada, amma wadansu suka yi shakka. 18 Yesu ya zo wurin su ya yi masu magana, yace, "Dukan iko dake sama da kasa an ba ni. 19 Sai kuje ku almajirantar da dukan al'ummai. Kuna yi masu baftisma cikin sunan Uba da na Da da na Ruhu Mai Tsarki. 20 Ku koya masu su kiyaye dukan abin da na umarce ku. Duba, ni kuma kullum ina tare da ku har karshen zamani."
Wannan ya fara labarin tashiwar Yesu daga matattu.
"Da Asabar ya wuce, daidai haurowar rana da safe ran Lahadi"
An yi amfani da wannan kalma anan ne don a sa alama a ainahin labarin. Anan Matiyu ya fara maganar wata sabuwar sashin labarin kenan.
"ɗayan matan mai suna Maryamu." Wannan Maryamu uwar Yakubu da Yusufu. (Dubi: [Matthew 27:56])
Kalmar "ku ga" a nan yana sa mu mu sa hankali ne ga bayanin ban mamaki da ke biye. Harshenku na iya samun wata hanyar yin haka.
AT: 1) girgizan kasan ya faru domin mala'ikan ya sauko ya kuma murgine dutsen ko 2) dukka abubuwannan ya faru a lokaci ɗaya.
wata girgizan ƙasa mai ƙarfi
"Bayanuwar mala'ikan"
Wannan magana ne da ke nanata yadda hasken kamannin mala'ikan yake. AT: "na da haske kamar walkiya"
Wannan magana ne da ke nanata yadda tufafin mala'ikan yake da fari da kuma haske. AT: "tufafinsa fari ne sosai, kamar suno"
Wannan magana ne da ke nufin cewa sojojin sun faɗi kuma ba su motsa ba. AT: "sun faɗi a ƙasa sun kuma kwanta kamar matattun mutane"
"Maryamu Magadaliya da kuma wata mata mai suna Maryamu"
AT: "wanda mutane da sojoji suka gicciye" ko "wanda suka gicciye"
Wannan magana ne a cikin magana. AT: "gaya wa almajiransa cewa ya tashi daga matattu kuma Yesu ya tafi Galili inda za ku gan shi."
"Ya rayu kuma"
Daga cikin dukka waɗanda sun mutu. Wannan magana ya kwatanta dukka matattu a cikin karkashin duniya. Tashi a cikinsu na nufin rayuwa kuma.
A nan "ku" ɗaya. Ya na nufin matan da almajiran.
Anan "ku" na nufin matan.
Wannan gaisuwa ne irin ta yau da kullum, kamar "barka" a turanci.
"durkusa da gwiwarsu suka kuma kama kafarsa"
Wannan na nufin almajiran Yesu.
"daidaita shiri a sakaninsu." Firistoci da dattawa sun yarda su ba sojoji kuɗin.
AT: "Gaya wa waɗansu cewa almajiran Yesu sun zo ... lokacin da kuke barci"
"Idan gwamna ya ji cewa kuna barci ne lokacin da almajiran Yesu sun ɗauke jikinsa"
"Bilatus" 27:2
"kad ku damu. Za mu ɗauke shi don ka da ya hukunta ku."
AT: "yi abin da firistoci sun ce masu su yi"
"Yahudawa dayawa sun ji wannan rahoto sun kuma cigaba da faɗa wa waɗansu har zuwa yau"
Wannan na nufin lokacin da Matthew ya rubuto littafin.
AT: 1) sukka yi wa Yesu sujada ko da shike waɗansu sun yi shakka, ko 2) waɗansu sun yi wa Yesu sujada, amma waɗansu ba su yi masa sujada ba domin sun yi shakka.
Ana iya bayyana abin da almajiran sun yi shakka. AT: "waɗansu sun yi shakka cewa shi ne Yesu kuma wai ya rayu kuma"
AT: "Ubana ya ba ni dukkan iko"
An yi amfani da "sama" da "ƙasa" anan don a bayyana kowa da komai a cikin sama da ƙasa.
A nan "al'ummai" na nufin mutane. AT: "na dukkan mutanen duniya"
A nan "suna" ya na nufin iko. AT: "ta wurin ikon"
Waɗannan muhimmin laƙabi ne da ke kwatanta ɗangantaka sakanin Allah da Yesu.
"Duba" ko "ji" ko "ba da hankulanku ga abin da zan gaya maku"
"sai ƙarshen zamani" ko "sai ƙarshen duniya"
Da ya kusa zuwa rana ta farko na satin, suka tafi zuwa kabarin Yesu.
Mala'ikar Ubangiji ya sauko ya kuma murgine dutsen.
Masu tsaron sun razana da tsoro sun kuma zama kamar matattun mutane a loƙacin da suka gan mala'ikan.
Mala'ikar ya faɗa cewa Yesu ya tashi kuma ya na tafiya a gaban su zuwa Galili.
Matan sun sadu da Yesu, sai suka rike ƙafansa suka yi masa sujada.
Shugabanin Firistoci suka bada kuɗi masu yawa ga sojojin sai suka ce masu su faɗa cewa, almajiran Yesu sun zo sun sace jikin.
Almajiran sun yi wa Yesu sujada, amma waɗansu suka yi shakka.
Yesu ya ce an ba shi dukkan iko a sama da ƙasa.
Yesu ya umarce almajiransa cewa su je su yi almajiranci, su kuma yi masu baftisma.
Yesu ya gaya wa almajiransa cewa su yi baftisma a cikin sunar Uba, da na Ɗa, da kuma Ruhu mai Starki.
Yesu ya yi alkawari zai kasance tare da su, har karshen duniya.
Yesu ya umarce almajiransa su koya masu su kiyaye dukan abin da ya umarta.
1 Wannan itace farkon bisharar Yesu Almasihu, Dan Allah. 2 kamar yadda aka rubuta cikin littafin annabi Ishaya. Duba, ina aika manzona, a gabanka, wanda zai shirya maka hanya. 3 Akwai murya mai kira a jeji, tana cewa ka shirya hanyar Ubangiji. ka daidaita ta. 4 Yahaya ya zo, yana baptisma acikin jeji yana wa'azin tuba, domin gafarar zunubai. 5 Dukan kasar Yahudiya da mutanen Urshalima suka zo wurin sa, a ka kuma yi masu baptisma a kogin urdun. suna furta zunubansu. 6 Yahaya yana saye da tufa ta gashin rakumi, yana kuma da damara ta fata a kugunsa, abincinsa fara ce da zuma. 7 Yana wa'azi, ya ce "akwai mai zuwa a bayana wanda ya ke da iko fiye da ni. wanda ko maballin takalminsa ban isa in kwance ba. 8 Ni ina yi maku baptisma da ruwa, amma mai zuwa a bayana zai yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki". 9 Sai ya kasance a kwanakin nan Yesu ya zo daga Nazarat ta Galili, sai Yahaya ya yi masa baptisma a kogin urdun. 10 Sa'adda Yesu ya fito daga ruwan, sai sama ta bude, sai Ruhu ya sauko a bisansa da kamanin kurciya. 11 Sai wata murya ta zo daga sama, tana cewa, "Kai kaunataccen Dana ne. zuciyata ta na murna da kai kwarai". 12 Sai Ruhu ya iza shi zuwa jeji. 13 Yana a jeji kwana arba'in, Shaidan yana jarabtar sa. Yana cikin jeji da dabobi, sai malaiku su ka yi masa hidima. 14 Bayan da aka kama Yahaya, Yesu ya shiga kasar Galili yana wa'azin bisharar Allah. 15 Yana cewa, "Lokaci ya yi, gama mulkin Allah ya kusato. Ku tuba ku bada gaskiya ga bishara". 16 Sa'adda ya ke wucewa a gefen takun Galili, sai ya ga Saminu da Andarawus, dan'uwansa suna jefa taru a teku, domin su masunta ne. 17 Yesu ya ce masu ku zo, ku biyo ni, ni kuwa sai in maisheku masuntan mutane". 18 Nan da nan suka bar tarun su, suka bi shi. 19 Sa'adda Yesu ya yi tafiya kadan, sai ya ga Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan'uwansa; suna gyaran tarunsu a jirgin ruwa. 20 Sai ya kira su, su kuwa suka bar mahaifinsu Zabadi a jirgin ruwan da ma'aikatansu, sai su ka bi shi. 21 Da su ka shigo cikin kafanahum, a ranar asabar, Yesu ya shiga majami'a ya koya masu. 22 Su ka yi mamakin koyarwarsa, domin ya na koya masu da iko ba kamar marubuta ba. 23 A nan cikin majami'a akwai wani mutum mai kazamin ruhu, sai ya yi ihu da karfi. 24 Yana cewa Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo ne domin ka halakar da mu? Na san wanene kai. Kai ne Mai Tsarki na Allah". 25 Sai Yesu ya tsauta wa kazamin ruhun ya ce, "Ka yi shiru ka fita daga cikinsa". 26 Bayan da kazamin ruhun ya buga shi kasa, sai kazamin ruhun ya yi ihu sa'annan ya fita daga jikinsa. 27 Sai dukan mutanen su ka yi mamaki kwarai, suna tambayar junansu menene wannan? wace sabuwar koyarwa ce da iko haka? har yana umartar kazaman ruhohi suna kuwa yi masa biyayya!" 28 Nan da nan labarinsa ya bazu ko'ina a dukkan kewayen kasar Galili. 29 Bayan da suka bar majami'a, sai su ka shiga gidan Saminu da Andarawus, suna kuma tare da Yakubu da Yahaya. 30 Surikar Saminu tana kwance ba lafiya tana fama da zazzabi. Sai suka gaya wa Yesu game da ita. 31 Sai ya zo, ya kama hannunta, ya daga ta, sai zazzabin ya sake ta, ta fara yi masu hidima. 32 Da yamman nan, bayan da rana ta fadi, sai su ka kawo masa dukan marasa lafiya da masu fama da aljanu. 33 Dukan mutanen garin su ka taru a bakin kofa. 34 ya warkar da masu ciwo da yawa da masu chututtuka iri-iri, ya kuma fitar da bakaken aljanu, amma bai yarda aljanun su yi magana ba domin sun san shi. 35 Ya tashi da sassafe, tun da sauran dare, ya tafi wurin da ba kowa, a can ya yi add'ua. 36 Saminu da wandanda suke tare da shi suka neme shi. 37 Suka sa me shi, sai su ka ce masa, "kowa yana nemanka". 38 Ya ce, bari mu tafi wani wuri, zuwa wadansu garuruwan da ke kewaye, Saboda in yi wa'azi a can kuma. Wannan shi yasa na zo nan". 39 Ya tafi dukan kasar Galili, yana wa'azi a majimi'un su yana kuma fitar da aljanu. 40 Wani kuturu ya zo wurinsa. Yana rokonsa, ya durkusa. Ya ce masa, "in ka yarda kana iya warkar da ni. 41 Sai ya yi juyayi, Yesu ya mi ka hannun sa ya ta ba shi ya na ce masa "Na yarda. Ka sarkaka". 42 Nan da nan kuturtar ta barshi, ya kuma sa mu tsarkakewa. 43 Yesu ya yi masa gargadi sosai, ya salame shi. 44 Ya ce masa "ka tabbata fa kada ka gayawa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, sai ka je ka yi hadaya domin tsarkakewa kamar yadda Musa ya umurta, domin shaida. 45 Amma da ya fita sai ya fara gaya wa kowa, ya baza maganar a ko'ina, har Yesu bai iya tafiya a sake a garin ba. Ya tafi ya tsaya a wuraren da ba kowa, mutane kuwa su ka zo wurinsa daga ko'ina.
littafin Markus ta fara the anabcin annabi Ishaya game da zuwan Yahaya mai baftisma, wanda ya yi wa Yesu baftisma.
Wannan laƙani ne mai mahimanci na Yesu.
Wannan karin magana ce wanda ke nufin "a gabanku"
A nan, kalman nan "ka"
Wannan na nufin mai sakon.
Yin haka na nufin shirya mutane domin zuwan Ubangiji. AT: "zai shirya mutanen domin zuwanka"
Wannan za a iya bayyanata a jimla kamar haka. AT: "an ji muryar wani na kira a jeji" ko kuwa "Sun ji karar wani na kira a jeji"
wadannan maganganu suna nufin abu daya ne.
"sa hanyar Ubangiji ta shiryu." yin haka na madadin yin shiri domin sakon Ubangiji in ta zo. mutane na yi haka tawurin tuba daga zunubansu. AT: "shirya domin sakon Ubangiji a sa'ada ta zo" ko kuwa "Tuba da kuma shiri domin zuwan ubangiji"
Ku tabbatar cewa masu karatu sun fahimci cewa Yahaya ne mai saƙon da anabi Ishaya ya yi maganarsa a ayan da ta rigaya.
Kalmomin nan "dukan kasar" misalin ne ta mutanen da ke zama a kasar da kuma wanda ake nufin mafi yawan mutane, ba kowane mutum ba. AT: "Mutane daga Yahudiya da Urushelima"
Sun yi wannan a lokaci ɗaya be. An yi wa mutanen baftisma domin sun tuba daga zunubansu. AT: A sa'ada suka tuba da zunubansu, Yahaya ya yi musu baftisma a Kogin Urdun"
Fara da zuma irin abinci biyu ne da Yahaya saba ci a sa'anda ya ke jeji. Wannan bai nuna cewa Yahaya ya cin waɗannan abinci a sa'ada yana yi wa mutanen baftisma ba.
"Yahaya ya shaida"
Yahaya ya kwatanta kansa da bawa don ya nuna yadda girman Yesu yake. AT: "ban isa in kaskantarciyar aikin cire takalminsa ba" (Dubi: )
A lwancan oƙacin da Yesu ke cikin duniya, mutane sun cika sa takalma wanda aka yi da fata suna kuma ɗaure ƙafafunsu da igiyar fata.
"sunƙuya"
Wannan na kwatanta baftisman Yahaya da ruwa da kuma baftisma mai zuwan nan gaba da Ruhu Mai Tsarki. Wannan na nufin cewa baftisman Yahaya alama ce ta share zunuban mutane. Baftisma ta wurin Ruhu Mai Tsarki lallai zai wanke mutane daga zunubansu. In ya yiwu, yi amfani da kalma ɗaya ta "baftisma" anan kamar yadda kun yi amfani da shi ga "Yahaya mai baftisma" don kwatanci tsakanin biyun.
Wannan alama ce na farkon wani abu da ya faru a labarin.
AT: "Yahaya ya yi masa baftisma"
Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) wannan wa salon magana ne, wato Ruhun ya sako bisa Yesu kamar tsuntsu dake saukowa daga sarari zuwa kasa ko kuwa 2) Ruhun daidai kamar kurciya ya sauko bisa Yesu.
Wannan na wakilcin Allah na magana. Wani loƙaci mutane na ƙin kiran sunan Allah domin suna girmama shi. AT: "Allah ya yi magana daga sama"
Wannan lakabi ne mai muhimmanci na Yesu. Uban ya kira Yesu "ƙaunatacciyar ɗa" sa saboda madawammiyar ƙaunarsa gare shi.
Bayan Baftisman Yesu, yana cikin jeje kwanaki arba'in, ya kuma tafi Galilee don ya koyar ya kuma kira almajiransa.
"tilasta Yesu ya fita zuwa"
"Ya zauna a jeji"
"kwanaki 40"
"Yana tsakanin"
"bayan an sa Yahaya a kurkuku." AT: "bayan su kama Yahaya"
"gayawa mutane da yawa game da bisharar"
"Yanzu ne lokacin"
"Lokaci ya kusa da Allah zai fara mulki mutanensa"
"Yesu ya ga Siman da Andarawas"
A nan iya bayyana ma'anar wannan magana a fili. AT: "jefa taru cikin ruwa don su kama kifi"
"Ku bi ni" ko kuwa "Ku zo tare da ni"
Wannan na nufin cewa Siman Andarawas za su koya wa mutane gaskiyar saƙon Allah don wasu ma su bi Yesu. AT: "Zan koya muku yadda za ku tara mutane zuwa gare ni kamar yadda kuna tara kifi"
Ana iy tsammani cewa jirgin na Yakubu da Yahaya ne. AT: "cikin jirginsu"
"gyaran taruna"
Zai zama da taimako sosai in ab faɗa dalilin da ya sa Yesu ya kira Yakubu da Yahaya. AT: "kira su su zo gare shi"
"bayin da ke yi musu aiki"
Yakubu da Yahaya sun tafi tare da Yesu.
"shiga Kafarnahum"
Ra'ayin "koyarwa" ana iya bayana ta a fili in ana magana game da "wani wanda ke da iko" da kuma "marubutan." AT: "domin yana koyar da su kamar yadda wanda ke da ikon ke koyarwa ba kamar yadda marubutan ke koywarwa ba"
Aljanu sun yi wannan tambaya da ma'anan cewa ba bu wata dalilin da Yesu zai shiga tsakani su kuma suna so ya bar su. AT: "Yesu Banazare, ka bar mu! Babu wata dalilin da zai sa ka shiga tsakanin mu."
Ajanun sun yi wannan tambaya don su cewa Yesu kada ya yi musu lahani. AT: "Kada ka hallaka mu!"
A nan kalman nan "shi na nufin mutumin nan mai aljanin.
Aljan ne ke kuka ba mutumin ba.
Mutanen sun yi amfani da tambayoyi biyu don su nuna mamakin su. Ana iya bayana tambayoyin kamar maganar motsin rai. AT: "suka cewa juna, "wannan da mamaki! Ya bada sabuwar koyarwa kuma ya yi magana da iko! ... suka kuma yi masa biyayya!'"
Kalman nan "ya" na nufin Yesu.
Kalman nan "yanzu" na gabatar da surukuwar Siman a labarin da kuma ƙarin haske ga labari game da ita.
"sa ta ta tashi tseye" ko kuwa "ya sa ta ta iya saukowa daga gado"
Ana iya nuna wa a fili wanda ya warkar da ita. AT: " Yesu ya warkar da ita daga zazzaɓi"
Ana nufin cewa an ba su abinci. AT: "ta ba su abinci da ruwan sha"
Kalman nan "duk" zuguiguci ne da ke nanata gaggaruman lisafin mutanen da suka zo. AT: "yawanci wanda ke rashin lafiya ko kuwa masu aljan"
Kalman nan "birni" na nufin mutanen da ke birnin. A nan kalman nan "dukka" mai yiwuwa na nanata cewa yawancin mutane daga birnin sun taru. AT: "Mutane da yawa daga birnin sun taru a bakin ƙofar"
"wurin da zai iya zama shi kaɗai"
A nan "shi" na nufin Siman. Waɗanda suke tare da shi kuma sune Andarawas, Yakub, Yahaya, mayiwuwa da wasu mutane.
Kalman nan "kowa" zuguiguci ne da ke nanata cewa mutane da yawa suna neman Yesu. AT: "Mutane da yawa suna neman ka"
"Ya kamata mu je wasu wurare." A nan Yesu ya yi amfani da kalman nan "mu" don yana nufin kansa da kuma Siman, Andarawas, Yakub da Yahaya.
Kalman nan "gama dukkan" zuguiguci ne aka yi amfani da ita don a nanata cewa Yesu ya tafi wurare da yawa lokacin da yake aikinsa. AT: "Ya tafi wurare da yawa a ƙasar Galili"
"Wani kuturu ya zo wurin Yesu, ya durƙusa yana roƙon Yesu yana cewa"
Cikin jimla ta farko, kalman nan "a tsarkake ni", an fahimce ta saboda jimla ta biyu ne. AT: "In ka yarda ka tsarkake ni, to, za ka iya tsarkake ni"
"so" ko kuwa "muradi"
A lokacin littafi Mai Tsarki, mutum da ke da wani cuta da ta shafi fata, ana dubansa mara tsarki, sai ya warke gabakiɗaya . AT: "za ka iya warkar da ni"
A nan kalman nan "ya yi" na nufin a ji tausayi game da bukatan wani. AT: "Da tausayi domin sa, Yesu" ko kuwa "Yesu ya ji tausayi domin mutumin, sai ya"
Zai yi taimako in an ambata abin da Yesu ya yarda ya yi. AT: "Na yarda in tsarkake ka"
"Ka tabbata ba ka gaya wa kowa kome ba"
Yesu ya ce wa mutumin ya nuna kansa ga firist domin firist ya duba fatansa ko kuturtan ya barshi da gaske. An bukaci wannan cikin dokar Musa, mutum ya kai kansa gaban firist in an tsarkake shi.
Kalman nan "kanka" na wakilcin fatan kuturun. AT: "Nuna fatanka"
Zai fi kyau a yi amfani da "su" in mai yiwuwa ne a harshen ku. Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) "shaida ga firist" ko kuwa 2) "shaida ga mutanen."
Kalman nan "ya" na nufin mutumin da Yesu ya warkar.
A nan "yada labarin a ko'ina" na nufin cewa ya yi shaida wa mutane a wurare daban dabam game da abin da ya faru. AT: "fara gaya wa mutane a wurare da yawa game da abin da Yesu ya yi"
Mutumin ya yada labarin har ya kai
Wannan ita ce sakamakon yada labarin da mutumin ya yi so sai. Anan "sarari" na nufin "a fili."Yesu bai ba iya shigan farin ba domin mutane da yawa sun taru a gefensa. AT; "cewa Yesu bai iya shigar a fili ba" ko kuwa "cewa Yesu bai iya shigar garin ta hanyar da mutane za su iya ganinsa ba"
"wuraren kaɗaici" ko kuwa "wuraren da babu kowa"
Kalman nan "ko'ina" an yi amfani da ita don a nanata cewa mutane daga wurare da yawa ne suka zo. AT: "daga dukkan yankin"
Ishaya ya fadi cewa Allah zai aiko wani manzo, muryar wani mai kira da cikin jeji, saboda ya shirya hanyar Ubangiji.
Yahaya ya zo yana wa'azin baftisman tuba domin yafewan zunubai.
Mutanen su ka furta zunuban su sa'ad da Yahaya ya ke yi masu baftisma.
Yahaya ya ci fari da zuman daji.
Yahaya ya ce ma zuwa a bayan shi za ya yi baftisma da ruhu mai tsarki.
Bayan baftisman sa, Yesu ya ga sama ta bude sai ruhu ta sauko a kansa kamar kurciya.
Murya daga sama ta ce, ''kai ne Ɗa na kaunatacce, ina jin dadin ka kwarai.
Ruhun ne ya koro Yesu cikin jeji.
Yesu ya na cikin jeji har tsawon kwanaki arba'in, shaidan kuma ya yi ta jarabtan shi a wurin.
Yesu ya yi wa'azi cewa mulkin Allaha ya yi kusa, kuma ya zama tilas ma mutane su tuba su kuma yi ĩmãni da bishara.
Saminu da Andarawus masunta ne.
Yesu ya ce zai zamar da Saminu da Andarawus masuntan mutane.
Yakubu da Yahaya masunta ne.
Koyarwan Yesu ya ba ma mutane mamaki domin Yesu ya yi koyarwa kamar wanda ya ke da izni.
Ruhohi marasa tsabtan cikin majami'a sun bawa Yesu sunan mai tsarki na Allah.
Labari game da Yesu ya fita zuwa ko'ina.
A lokacin da suka je gidan Saminu, Yesu ya warkar da surikar Saminu
A lokacin da yamma ya yi, mutanen suka kawo dukka wadandan ba su da lafiya, wadanda suke da aljanu sai kuma Yesu ya warkar da su.
Kafin rana ta tashi, Yesu ya fita zuwa wuri makadaice ya yi adu'a a wurin.
Yesu ya ce ya zo ne ya yi wa'azi a cikin garuruwan da suke a kewaye.
Yesu ya yi tausayin sa ya warkar da shi.
Yesu ya gaya wa kuturun ya je ya mika hadaya bisa ga abubuwan da Musa ya ke umurtawa a kan ba da shaida.
1 Da ya dawo Kafarnahum bayan yan kwanaki kadan, aka ji cewa yana gida. 2 Da yawa suka taru a can, ba wuri har kofa, sai Yesu ya yi masu magana. 3 Sai wadansu mutane su ka zo wurinsa dauke da wuni mutum shanyayye, mutane hudu na dauke da shi. 4 Lokacin da ba su iya zuwa kusa da shi ba domin yawan jama'a, sai su ka daye jinkar dakin daidai da inda ya ke. Bayan da suka huda ramin suka saukar da gado wanda shanyayyen ke kwance a kai. 5 Da ganin bangaskiyarsu, Yesu ya ce wa shanyayyen mutumin, "Da, an gafarta maka zunuban ka". 6 Amma wadansu marubuta da ke zaune a nan, suka yi tunani aransu. 7 Yaya wannan mutum zai yi magana haka? Ya yi sabo! wa ke iya gafarta zunubi "sai Allah kadai?" 8 Nan da nan Yesu ya sani a ruhunsa, abinda suke tunani a tsakaninsu. Ya ce masu, "Me ya sa kuke tunanin wannan a zuciyarku? 9 Me yafi sauki a cewa shanyayyen mutumin, 'An gafarta maka zunuban ka' ko kwa a ce masa, 'tashi, ka dauki shinfidarka, ka yi tafiyarka'? 10 Amma domin ku san cewa Dan mutum na da ikon gafarta zunubi a duniya, ya ce wa shanyayyen, 11 "Na ce maka, tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidan ka." 12 Sai nan da nan ya tashi ya dauki tabarmarsa, ya fita gidan a gabansu, dukansu su ka yi mamaki, su ka girmama Allah, "suka ce ba mu taba ganin abu irin wannan ba." 13 Ya sake fita gefen tafki, dukan taron jama'a suka zo wurinsa, sai ya koya masu. 14 Sa'adda ya na wucewa, ya ga Levi dan Halfa yana zaune a wurin karbar haraji, sai ya ce masa, "Ka biyo ni." Ya tashi, ya bi shi. 15 Sa'adda Yesu ya shiga gidan Levi yana cin abinci, masu karbar haraji da masu zunubi da yawa su ka zo wurinsa da almajiransa, jama'a masu yawan gaske suka ka bi shi. 16 Da Marubuta wadanda su ke Farisawa, sun ga cewa Yesu na cin abinci da masu zunubi da masu karbar haraji, sai su ka ce wa almajiransa, "Me ya sa ya ke ci da masu karbar haraji da mutane masu zunubi?" 17 Da Yesu ya ji wannan ya ce masu, "Mutane wadanda ke da lafiya a jiki ba su bukatar likita; sai dai ko marasa lafiya ke bukatarsa. Ban zo domin in kira mutane masu a dalci ba, amma mutane masu zunubi." 18 Almajiran Yahaya da Farisawa suna azumi, sai wadansu mutane suka zo suka ce, "Don me almajiran Yahaya da almajiran Farisawa na azumi amma na ka almajiran ba su yi?" 19 Sai Yesu yace masu, "Abokan ango, za su yi azumi sa'adda ango yake tare da su? muddin suna tare da ango ba za su yi azumi ba. 20 Amma kwanaki za su zo da za a dauki angon daga gare su, a wadancan kwanakin ne, za su yi azumi. 21 Babu wanda zai dinka sabuwar riga ya hada ta da tsohuwar riga, sai rigar ta yage, kuma ta yi mummunar yagewa. 22 Babu wanda zai sa sabon ruwan inabi a cikin tsohuwar salka, ai sai salkar ta fashe kuma ruwan inabin ya zube. duka biyu ruwan inabin da salkar arasa su. A maimakon haka, sai ka sanya sabon ruwan inabi cikin sabuwar salka." 23 A ranar asabar Yesu ya tafi cikin gonakin hatsi, sai almajiransa su ka fara zagar hatsi, 24 Sai Farisawa su ka ce masa, "Duba, don me suke yin abin da bai dace a yi ranar Asabar ba?" 25 Yace masu, Ba ku karanta ba abinda Dauda ya yi sa'adda yake jin yunwa, shi da mutanen da ke tare da shi? 26 Yadda ya shiga gidan Ubangiji, sa'adda Abiyata ya ke babban firist, ya ci gurasa da ke ta firist wadda bai dace wani ya ci ba sai Firistoci. Har kuma ya ba wadanda ke tare da shi?" 27 Yesu yace, "Asabar an yi ta don mutum ne, ba a yi mutum don Asabar ba. 28 Saboda haka, Dan Mutum Ubangiji ne, har da na Asabar."
Bayan wa'azinsa da kuma warkar da mutane da Yesu ya yi a yankin kasar Galili, ya koma kafarnahum inda ya warkar da wani shanyayye mutum ya kuma yafe masa zunubansa.
AT: "Mutanen da da ke a wurin sun ji cewa yana zama a gida"
Kalman nan "a wurin" na nufin in da Yesu ke zama a kafarnahum. AT: "Mutane da yawa sun taru a wurin" ko kuwa "Mutane da yawa sun zo gidan"
Wannan na nufi babu wurin a cikin gidan. AT: "har babu ɗaki domin su a ciki"
"Yesu ya yi wa'azin saƙon zuwa a gare su"
"su huɗu suna ɗauke da shi." Mai yiwuwa akwai mutane fiye da huɗu cikin mutanen da suka kawo mutumin wurin Yesu.
"na kawo mutumin wanda ba iya tafiya ba ko kuwa bai iya amfani da hannayensa ba"
"kăsa zuwa kusa da inda Yesu yake"
Gidajen da Yesu ya zauna na da shimfiɗaɗɗen rufi da aka yi da yumɓu aka kuma rufe da fale-falen abu. Ana iya bayana a fili yadda ake yin rami a rufi ko kuwa ana iya bayana ta ga yadda kowa zai gane ya harshen ku. AT: "suka cire fale-falen abin da aka sa a saman rufi daidai in da Yesu yake. Bayan sun tona rufin yumɓun, sai suka sauƙar" ko kuwa "sun yi rami cikin rufin daidai ta inda Yesu yake, sai suka suaƙar da
"da ganin bangaskiyar mutanen." Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) cewa mutanen da suka ɗauke shanyeyyen mutumin ne kawai ke da bangaskiya. ko 2) cewa shanyeyyen mutumin da mutanen da suka kawo shi wurin Yesu, dukkan su su na da bangaskiya.
Kalman nan "Ɗa" a nan na nuna cewa Yesu ya kula da shi kamar yadda uba ke kula da ɗa. AT: "Ɗa na"
In mai yiwuwa ne a juya wannan yadda zai nuna cewa Yesu bai faɗi wanda ya yafe zunuban mutumin ba. AT: "zunubanka sun tafi" ko kuwa "ba ka bukatan ka biya domin zunubanka na" ko kuwa "ba a lisafta zunubanka a kanka ba"
A nan "zuciyarsu" na nufin tunanin mutane. AT: "suna tunani da kansu"
Marubutan sun yi amfani da wannan tambayar don su nuna fushin su cewa Yesu ya ce "An gafarta maka zunubanka" AT" "Bai kamata wannan mutum ya yi magana haka ba!"
Marubuta sun yi amfani da wannan tambayar cewa dashike Allah ne kaɗai ke iya yafe zunubai, to ba kamata Yesu ya ce "An yafe maka zunubanka" ba. AT: " Allah ne kaɗai ke da iya yafe zunubai!"
"cikin ransa" ko kuwa "a cikinsa"
Kowane malamin attaura na tunani da kansa; ba su magana ga juna.
Yesu ya yi amfani da wannan tambayar don ya gaya wa malaman attauran cewa abin nana da suke tunani ba daidai ba ne. AT: "Abin da kuke tunani ba daidai ba ne." ko kuwa "Kada ku yi tunanin cewa ina saɓo"
Kalman nan "zuciya" na nufin tunaninsu da kuma sha'awace sha'awacensu. AT: "wannan a cikin ku" ko "waɗannan abubuwa"
Yesu ya yi amfani da wannan tambayar don ya sa malaman attauran tuna game da abin da zai tabbatar cewa lallai zai iya yafe zunubai ko ba zai iya ba. AT: "Na dai cewa wa shanyeyyen mutumin, 'An yafe maka zunubanka.' Mai yiwuwa kuna tunanin cewa yana da wuya a ce 'Tashi, ɗauki gadonka ka yi tafiya,' saboda tabbacin cewa zan iya ko ba zan iya warkar da shi, ba za a nuna ta tawurin tashinsa ya yi tafiya ko kuwa bai tashi ya yi tafiya ba." ko kuwa "Mai yiwuwa kuna tunanin cewa ya fi sauƙi a ce ma shanyeyyen mutumin 'An yafe maka zunubanka' fiye da a ce 'Tashi, ɗauki gadonka ka yi tafiya.'"
"Amma don ku sani." Kalman nan "ku" na nufin marubutan da kuma taron jama'an.
Yesu ya dubi kansa a matsayin "Ɗan Mutum." AT: "cewa ni Ɗan Mutum ne kuma ina da iko"
"a sa'ad da dukkan mutanen ke kallo"
Wannan tekun Galilli ne wanda ake kiran ta tafkin Janisarata.
"mutanen sun je in da ya ke"
Halfa uban Lawi ne.
"gidan Lawi"
Farisiyawan sun yi amfani da jimlar nan "mutane masu zunubi" don suna nufi mutanen da ba sa bin doka kamar yadda Farisiyawan na nuna su yi.
Ma'ana mai yiwuwa na kamar haka 1) "don akwai masu karɓar haraji masu yawan gaske da mutane masu zunubi wanda suka bi shi" ko kuwa 2)"gama Yesu yana da almajirai masu yawa sun kuma bi shi."
Malaman attauran da Farisiyawan sun yi wannan tambayar don su nuna cewa ba su yarda da kirkin da Yesu ya nuna ba. Ana iya sa wannan cikin magana. AT: "Bai kamata ya ci da masu zunubi da masu karɓar haraji ba!"
"ya ce wa malaman attauran"
Yesu ya yi amfani da wannan karin magana game da mutane marasa lafiya da likita don ya koya musu cewa mutanen da sun san cewa suna cike da zunubi sun gane cewa suna bukatan Yesu.
"lafiyayyu"
Yesu na tsammanin masu sauraronsa su fahimci cewa ya zo ne domin waɗanda ke bukatan taimako. AT: "Na zo domin mutanen da sun fahimci cewa su masu zunubi ne, ba domin mutane da sun gaskanta cewa su masu adalci ne ba"
Kalmomin nan "na zo in kira", an fahimci ta ne daga maganar da ke kafin wannan. AT: "amma na zo domin in kira mutane masu zunubi"
Wannan maganganu biyun na nufin ƙungiyan mutane ɗaya ne, amma an tabbatar da na biyun. Duka biyun na nufin mabiyan ɗarikar Farisiyawan, amma ba su mayar da hankali ga shugabannen Farisiyawan ba. AT: "almajiran Farisiyawan na azumi ... almajiran Farisiyawan"
"Wasu mutane." Zai fi kyau in an juya wannan magana ba tare da an tantance wanene waɗanan mutanen ba. Idan a harshen ku lallai ne a tantance, to ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) waɗannan mutanen ba sa cikin almajiran Yahaya ko kuwa almajiran Farisiyawa ba ko kuwa 2) waɗannan mutanen na cikin almajiran Yahaya.
"zo sun ce wa Yesu"
Yesu ya yi amfani da wannan tambayar don ya tunashe mutanen abin da sun riga sun sani don kuma ya karfafa su yi amfani da ita da shi da almajiransa. AT: "Abokan ango, ba sa azumi a sa'ad da ango na tare da su. Maimakon haka suna shagali da taya shi murna."
AT: "angon zai tafi"
Kalman nan "su" na nufin abokan ango.
Ɗinkin riga a kan tsohuwar tufa na sa ramin tsohuwar tufan ta zama mafi ɓaci in gutsuren sabon rigan bai tauye ba. Sabon rigar da tsohon tufan duk za su ɓaci.
"Babu mutum." Wannan maganar na nufin dukkan mutane, ba mazaje kawai ba.
"ruwan 'ya'yan itacen inabi." Wannan na nufin ruwan inabi da bai riga ya tashi ba. Inda ba a san inabi a yanki ku ba to a yi amfani da kalman da kowa ya sani na ruwan 'ya'yan itace.
Wannan na nufin salkunan da aka yi amfani da su sau da dama.
Waɗanan jakuna ne da aka yi da fatan dabba. Ana iya kiran su "jakunan inabi" ko "jakunan fata."
Sabuwar inabi na buduwa a sa'ad da yake tashiwa, saboda da haka zai sa tsohon salkunan fata ta yage.
"zai ɓaci"
"sabon salkuna" ko "sabuwar jakunan fata." Wannan na nufin salkunan fatan da ba taba amfani da ita ba.
zagar hatsi cikin gonakin wasu, kuma cin wannan ba a duban ta kamar sata. Tambayar ita ce ko daidai be bisa ga doka a yi wannan ranar Asabar.
Almajiran na zagar kan hatsi don su ci sabar, ko kwayar da ke cikin su. Ana iya sa wannan cikin kalma don nuna ma'anar gabaki ɗaya. AT: "zagar hatsi suna kuma cin kwayar"
"kan" saman tsiren alkama wanda ke kamar ciyawa mai tsayi. Kan na rike hatsi ko iri tsiren da ta balaga.
Farisiyawa sun yi wa Yesu tambaya don su kayar da shi. Ana iya juya wannan kamar magana. AT: "Duba! Su na karya dokar Yahudawa game da ranar Asabar."
"Duba wannan" ko "Kassa kunne." Wannan kalma ne da an yi amfani da shi don kama hankalin wani don a nuna musu wani abu. In akwai wata kalm a harshen ku da ake amfani da ita don a jawo hankalin mutu, to ana iya amfani da ita anan.
Yesu ya yi wannan tambayar don ya tunashe malaman attauran da Farisiyawa wani abin da Dauda ya yi a ranar Asabar.Tambayar ta yi dogo sosai, don haka ana iya raba shi zuwa jimla biyu.
Ana iya faɗin wannan kamar umurni. AT: "Ku Tuna abin da kin karanta game da abin da Dauda ... shi."
Yesu na nufin karanta game da Dauda cikin Tsohon Alkawari. Wannan ana iya juya shi ta wurin nuna ainihin zancen a fili. AT: "karanta cikin nassosin abin da Dauda"
A nan iya bayana wannan a matsayin furuci dabam da aya 25. AT: "Ya shiga gida Allah ... waɗanda ke tare da shi."
Kalman "ya" na nufin Dauda.
Wannan na nufin gurasa shabiyun wanda aka ajiye kan taburin zinariya wanda ke cikin alfarwa ko ginin haikali, hadaya ga Allah lokacin Tsohuwar Alkawari.
Yesu ya bayana a fili dalilin da Allah ya yi Asabar. AT: "Allah ya yi Asabar don mutum"
"mutum" ko "mutane" ko kuwa "bukatun mutane." Wannan kalma na nufin mazaje da mataye dukka.
Kalmomin nan "aka yi" an fahimci ta daga maganar da ke a baya. Ana iya sake faɗin ta ana. AT: "ba a yi mutum domin Asabar ba" ko kuwa "Allah bai yi mutum domin Asabar ba"
Mazajen sun cire jinkan gidan suka kuma saukar da gurgun zuwa ga Yesu.
Yesu ya ce, ''ɗa, an yafe maka zunuban ka''.
Wasu malaman Attauran sun yi tunani cewa Yesu ya yi sabo domin Allah ne kadai ya na iya gafarta zunubai.
Yesu ya gaya wa gurgun ya tashi ya dauki gadon sa ya tafi gidansa, kuma haka mutumin ya yi.
Levi yana zaune a wurin karban haraji a lokacin da Yesu ya kira shi.
Yesu ya na cin abinci da masu zunubi da kuma masu karban haraji.
Yesu ya ce ya zo ya kira duka mutane ma su zunubi
Sun tambaye shi me ya sa almajiransa ba su yi azumi a lokacin da almajiran Yohanna da kuma almajiran farisiyawa suka yi ba.
Yesu ya ce a lokacin da ango yana tare da abokkansa ba za su iya yin azumi ba.
Almajiran Yesu sun sama hatsi suka kuma ci a ranar asabar.
Yesu ya ba da misalin Dauda wanda ya ci daga gurasan da ke kasancewa wanda a ka keɓe wa firistoci.
Yesu ya ce an yi ranar asabar domin mutane ne.
Yesu ya ce shi ne Ubangiji kuma na ranar asabar.
1 Sai kuma ya sake tafiya cikin Majami'a sai ga wani Mutum mai shanyayyen hannu. 2 Wadansu mutane suna kallonsa sosai, su gani ko zai warkar da shi a ranar Asabar. don su zarge shi. 3 Yesu ya ce wa mai shanyayyen hanun " Ka tashi ka tsaya a tsakiyar kowa." 4 Sai ya ce wa mutane, "Ya dace a yi abu mai kyau aranar Asabar ko a yi mugunta; a ceci rai, ko a yi kisa? "Amma suka yi shiru. 5 Sai ya dube su cikin fushi, yana bakin ciki da taurin zuciyar su, ya ce wa mutumin ka mikar da hanunka, sai ya mikar da hanunsa Yesu kuwa ya warkar da shi. 6 Sai Farisiyawa suka fita da sauri zuwa wurin mutanen Hirudus suka shirya yadda za su kashe shi. 7 Sai Yesu da almajiransa, suka tafi bakin teku. sai mutane dayawa suka bi shi, daga Galili da Yahudiya 8 Daga Urushalima da Edom gaba da Urdun da kewayan Taya da Sidon, da baban taro, ya ji abinda yake yi. suka zo wurinsa. 9 Ya tambayi almajiransa su shirya masa karamin jirgin ruwa domin yawan mutane, domin kada su murkushe shi. 10 Ya warkar da mutane da yawa, yadda duk wadanda suke da cuttutuka suna kokari su taba shi. 11 Duk sa'adda kazaman ruhohin suka ganshi, sai su durkusa a gabansa su yi ihu da karfi su ce, kai Dan Allah ne." 12 Ya umarce su da karfi kada su sa a san shi. 13 Ya hau saman dutsen, ya kira wadanda yake bukar su, su zo wurinsa. 14 Ya zabi guda goma sha biyu (ya kira su manzanni). Wadanda zasu kasance tare da shi, ya kuma aike su, su yi wa, azi, 15 Ya kuma basu Ikon fitar da aljanu. 16 Ya zabi guda goma sha biyu wato Saminu kuma yaba shi suna Bitrus. 17 Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan-uwan Yakubu wanda ya basu sunan Buwanarjis watau 'ya'yan tsawa, 18 da Andarawus da Filibus da Bartalamawus da Matta da Toma da Yakubu dan Halfa, da Taddawus da Saminu Ba-kananiye, 19 da Yahuza Iskariyoti wanda zai bashe shi. 20 Sa'adda ya shiga gida, Taron kuwa ya sake haduwa, har ya hana su cin abinci, 21 Da iyalansa suka ji haka, sai suka fito sun kamo shi, saboda sun ce, "Ai, baya cikin hankalinsa " 22 Marubutan da suka zo daga Urushalima suka ce "Ai Ba'alzabuba ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu." 23 Yesu ya kirawo su wurinsa ya ce da su cikin misalai, "Yaya shaidan zai iya fitar da shaidan? 24 idan mulki ya rabu gida biyu ba zai tsayawa ba. 25 Haka in gida ya rabu kashi biyu, gaba da kansa bai zai tsaya ba. 26 Shaidan kuma in ya tayar wa kansa ya rabu, ba zai iya tsayawa ba, gama karshen sa ya zo kenan. 27 Amma ba mai iya shiga gidan kakkarfan mutum ya kwace kayansa, ba tare da ya fara daure kakkarfan mutumin ba, sa'an nan kuma ya kwashe kayan gidansa. 28 Hakika, ina gaya maku, dukan zunuban da mutane suka yi za a gafarta masu, da kowane irin sabon da suka furta, 29 amma fa duk wanda yayi sabon Ruhun Mai Tsarki baza a gafarta masa ba ko kadan, ya zama mai zunubi har abada." 30 "Yesu ya fadi wadannan abubuwa domin suna cewa yana da ba kazamin ruhu," 31 Sa'an nan uwatasa, da "Yan'uwansa suka zo suna tsaye a waje. sai suka aika masa, suna kuma umurtar sa ya zo. 32 Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka yi magana da shi da cewa, ga uwarka da yan-uwanka suna nan a waje, suna nemanka." 33 Ya amsa masu, "Dacewa su wanene uwa-ta da "yan'uwa na?" 34 Sai ya waiwayi wadanda suke zaune kewaye da shi, yace, "Ga uwa-ta da yan-uwana anan! 35 Gama duk wanda ke yin abin da Allah yake so, shine dan'uwana da yar, uwata, da kuma uwa-ta."
Yesu ya wakar da wani mutum ranar Asabar a cikin majami'a ya kuma nuna yadda ya ji game da abin da Farisiyawa sun yi da umurni game da Asabar. Farisiyawan da mutanen Hirudus su fara shirin yadda za su kashe Yesu.
"wani mutum wanda gurgu ne a hannu"
"Wasu mutane na kallonsa Yesu sosai, su gani ko zai warkar da mutumin wanda ke da shanyayyen hannu"
Wasu Farisiyawa." Nan gaba, cikin [Markus: 3:6] waɗannan mutanen an gane su Farisiyawa ne.
Ida Yesu ya warkar da mutumin a ranar, Farisiyawan za su zarge shi cewa ya karya doka ta wurin yin aiki ranar Asabar. AT: "domin su iya zarginsa cewa bai yi daidai ba" ko "domin su iya zarginsa cewa ya karya dokan"
"a tsakiyar wannan taron jama'a"
Yesu ya faɗi wannan domin ya kalubalance su. Ya na so su amince cewa ya halatta a warkar da mutane ranar Asabar.
Waɗannan magana biyun suna da ma'ana kusan iri ɗaya, sai dai na biyun matsananci ne sosai.
Mai yiwuwa zai yi taimako in an nanata "ya halatta" kamar ita ce tambayar da Yesu ya yi kuma a wata hanya. AT: "ya halatta a cece rai ko a yi kisa"
Wannan na nufi rai na wannan jiki. Ya na kuma nufin mutum. AT: "wani daga mutuwa" ko "ran wani"
"Amma sun ki su amsa masa"
"Yesu ya dube kewaye"
"ya yi fushi sosai"
Wannan ya bayyana yadda Farisiyawa ba sa shirye su ji tausayin mutum mai shanyayyen hannu da tausayi. AT: "domin ba sa shirye su ji tausayin mutumin"
"Mika hannunka"
AT: "Yesu ya komar masa da hannunsa lafiyayye" ko "Yesu ya sa hannunsa ya zama daidai yadda yake a dă"
"fara yin dabara"
Wannan suna ne na yau da kullum na wata kungiyan siyasa da ke goyon bayan Hirudus Antibas.
"yadda za su kashe Yesu"
Wannan na nufin Tekun Galili.
Wannan yankin ne wanda a baya an san ta da suna Edom, wanda ya kunshi rabin lardin kudacin Yahudiya.
Wannan na nufin al'ajiban da Yesu ke yi. AT: "babbar abin al'ajiban da Yesu ke yi"
"zo wurin da Yesu yake"
Aya 9 ta faɗi abin da Yesu ya ce wa almajiransa su yi saboda gaggaruman taron mutane da ke kewaye da shi. Aya 10 ta faɗi dalilin da ya sa gagaruman tarons suna kewaye da Yesu. Bayanin da ke a waɗannan ayoyi sake kasa su don a bayana labarun daidai yadda sun faru, kamar yadda yake cikin UDB.
A sa'ad da gaggaruman taron na kara matsowa kusa da Yesu, yana cikin hatsarin da za su iya murkushe shi. Ba da saninsu za su murkushe shi ba. Amma domin dai kawai akwai mutane da yawa.
"Yesu ya gaya wa almajiransa"
Wannan ta gaya mana dalilin da ya sa mutane masu yawa suna kewaye da Yesu har sai da ya yi tunani cewa za su murkushe shi. AT: "Gama, saboda Yesu ya warkar da mutane da yawa, duk waɗanda ... taba shi"
Kalman nan "yawa" na nufin gaggaruman mutanen da Yesu ya warkar da su. AT: "Gama ya wakr da mutane da yawa"
Sun yi wannan ne saboda sun gaskanta cewa in sun taba Yesu za su warke. A nan iya bayana wannan a fili. AT: " dukkan mutane marasa lafiya sun nace zuwa suna kokarin sun taɓa shi domin su warke"
"gan Yesu"
A nan "su" na nufin aljannun. Sune suke sa mutanen da suka shige su su yi waɗannan abubuwa. Anan iya bayana wannan a fili. AT: "Sun sa mutanen da suka shige su su fãɗi kasa a gaban shi, su yi kuka a gare shi"
Aljannun ba su fãɗi a gaban Yesu saboda suna kaunar shi ba ko suna so su yi masa sujada ba. Sun fãɗi a gabansa domin sun ji tsoronsa ne.
Yesu yana da iko a kan aljannun domin shi "Ɗan Allah" ne.
Wannan laƙani ne mai muhimmanci na Yesu.
"Yesu ya umurce aljannun"
"kada su bayana ko shi wanene"
"don su kasance tare da shi, shi kuma zai aike su, su yi wa'azi sakon"
Marubucin ya fara lisafta sunayen manzane goma sha biyun. Saminu shi ne na farko da aka ambata.
Maganan nan "wanda" na nufin Yakubu ɗan Zabadi da ɗan'uwansa Yahaya.
Yesu ya kira su da wannan suna domin suna kamar tsawa ne. AT: "suna Buwanarjis, wanda ke nufin mutane da ke kamar tsawa" ko "suna Buwarnarjis, wanda ke nufin mutanen tsawa"
Wannan sunan na miji ne.
"wanda zai bãshe da Yesu" Kalman nan "wanda" na nufin Yahuda Iskariyoti.
"Sai Yesu ya tafi gidan da yake zama."
Kalman nan "gurasa" na wakilcin abinci. AT: "Yesu da almajiransa ba su iya cin abinci ba ko kaɗan" ko "ba su iya cin komai ba"
'Yan iyalinsa sun shiga cikin gidan don su kama shi su sha shi dole ya je gida tare da su.
Ma'ana mai yiwuwa na kalman nan "su" na kamar haka 1) danginsa ko 2) wasu mutane da cikin taron.
iyalin Yesu sun yi amfani da wannan karin magana don su bayana yadda suke tunani yake yi. AT: "haukace"
"Ta wurin ikon Ba'alzabul, wanda shine sarkin aljannu, Yesu ke fid da aljannu"
"Yesu ya kira mutanen wurinsa"
Yesu ya yi wannan tambaya don ya amsa maganar malaman attaura da cewa yana fid da aljan ta wurin ikon Ba'alzabul. AT: "Shaiɗan ba zai iya fid da kansa ba!" ko "Shaiɗan baya gãba da mugayen ruhohinsa!"
Kalman nan "mulkin" na nufin mutane da ke wannan mulkin. AT: "Idan mutanen da ke zama cikin mulki sun rabu suna gãba da juna"
Wannan na nufin cewa mutane ba za su haɗu kuma ba kuma za su faɗi. AT: "ba zai iya jimrewa ba" ko "zai faɗi"
Wannan na nufin mutane da ke zama a gidan. AT: "iyali"
Kalman nan "kansa" na nufin Shaiɗan, yana kuma nufin mugayen ruhohi. AT: "Idan Shaiɗan da mugayen ruhohinsa suna faɗa da juna." ko "Idan Shaiɗan da mugayen ruhohinsa na gãba da juna kuma sun rabu"
Wannan na nufin cewa zai fãɗi kuma ba zai jimre ba. AT: "ba zai haɗu ba" ko "ba zai jima ba kuma ta zo ga ƙarshe kenan" ko "zai fãɗi kuma ta zo ga ƙarshe kenan"
a sata kayan mutum da kuma mallaka
Wannan na nuna cewa maganar da za a iya mai muhimmanci ne kuma gaskiya ne.
"waɗanda mutum ne ya haifa." Wannan na nanata cewa 'yan adam ne. AT: "mutane"
magana
"mutane suna cewa"
Wannan karin magana da ke nufin aljan ya yi mulkin wani. AT: "na da baƙin aljani"
"Sai uwar Yesu da 'yan'uwansa suka zo"
"Sun aiki wani a ciki ya gaya masa da cewa suna a waje kuma suna so ya zo wurin su"
"na tambaya game da kai"
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya don ya koya wa mutanen. AT: "Zan gaya maki ko wanene uwata da 'yan'uwana"
"waɗanda ke aikata ... sune"
Wannan na nufin almajirans Yesu sune iyalinsa na ruhaniya. Wannan ya fi muhimmanci fiye da zama cikin iyalinsa na jiki. AT: "wannan mutum shi kamar ɗan'uwana, da 'yar'uwata, ko uwa a gare ni"
Suna duba Yesu su ga ko zai yi warkaswa a ranar asabar, saboda su yi masa zargi.
Yesu ya tambayi mutanen ko ya na kan doka a yi abu mai kyau ko lahani a ranar asabar?
Mutanen sun yi shuru.
Yesu ya yi fushi da su.
Farisiyawan sun fita su ƙulla mutuwar Yesu.
Taron mutane suka bi Yesu.
Aljanun sun yi kuka cewa Yesu shine Ɗan Allah.
Yesu ya naɗa almajirai guda goma sha biyu wadanda za su zama tare da shi, su yi wa'azi su kuma sami izni korin aljanu.
Almajirin da zai ci amanan Yesu shine Yahuza iskariyoti
Iyalin Yesu sun yi tunanin cewa ba ya cikin hankalin sa.
Malaman Attauran sun dora wa Yesu laifin koran aljanu ta wurin shugaban aljanu.
Yesu ya amsa ya ce babu wata masarauta da take a rabe tsakanin kanta da zata iya tsayawa.
Yesu ya ce zunubin sabon ruhu mai tsarki babu gafartawa.
Yesu ya ce uwarsa da yan'uwansa sune wadanda suke aikata nufin Allah.
1 Ya kuma fara koyarwa a bakin teku. Akwai babban taro kewaye da shi, sai ya shiga cikin jirgin ruwa a cikin tekun, ya kuwa zauna. Duk taron kuwa na kan tudu a bakin tekun. 2 Ya koya masu abubuwa da yawa da misalai, a cikin koyawarsa ya ce masu, 3 "ku saurara! wani mai shuka ya tafi shuka. 4 Yana cikin yafa iri, sai wadansu iri suka fadi a kan hanya, tsuntsaye kuma suka zo suka tsince su. 5 Wadansu kuma suka fadi a kan dutse inda ba kasa dayawa. Nan da nan kuwa suka tsiro saboda rashin zurfin kasa. 6 Da rana fa ta daga, sai suka yankwane da yake ba su da saiwa sosai, sai suka bushe. 7 Wadansu kuma suka fadi cikin kayayuwa su ka yi girma sai kayayuwan suka shake su, ba su yi tsaba ba. 8 Wadansu kuma suka fadi a kasa mai kyau, suka yi yabanya, suka yi tsaba, suka yi girma, wadansu ribi talattin wadansu sittin, wadansu kuma dari". 9 Sai ya ce, Duk mai kunnen ji, ya ji," 10 Sa'adda Yesu yake shi kadai, wadanda suke kusa dashi tare da sha biyun suka tambaye shi ma'anar misalan. 11 Sai ya ce masu, "ku an yardar maku, ku san asirin mulkin Allah, amma ga wadanda ba su cikinku, komai sai a cikin Misalai, 12 don gani da ido sun gani, amma ba su gane ba. ji kuma, sun ji, amma ba su fahimta ba, don kada su juyo a gafarta masu," 13 Ya ce masu, "Ashe, ba ku fahimci wannan misalin ba? yaushe za ku fahimci sauran? 14 Mai shukan nan fa maganar Allah yake shukawa. 15 Wadanda suka fadi a hanyar kuwa, su ne kwatancin wadanda. a aka shuka mganar a zuciyarsu, Da suka ji, nan da nan sai shaidan ya zo ya dauke Maganar da aka shuka a zuciyarsu. 16 Haka kuma wadanda aka shuka a wuri mai duwatsu, sune wadanda da zarar sun ji Maganar sai su karba da farin ciki. 17 Su kuwa basu da tushe, ba su da karfi, idan kunci ko tsanani ya zo saboda kalmar, nan da nan sai su yi tuntube. 18 Wadansu kuma su ne kwatacin wadanda suka fadi cikin kayayuwa, sune wadanda suka ji Maganar, 19 amma abubuwan duniya, da rudin dukiya da kuma kwadayin wadansu abubuwa, sukan shiga su shake Maganar, har ta zama marar amfani. 20 Wadanda aka shuka a kasa mai kyau kuwa, sune kwatancin wadanda suke jin Maganar, su karba, su kuma yin amfani da ita wadansu ribi talatin, wadansu sittin, wadansu dari." 21 ya ce masu, "Shin, ana kawo fitila a cikin gida don a rufe ta da kwando ko a ajiye ta a karkashin gado? ku kan kawo ta ne don ku dora ta a kan madorinta. 22 Ba abin da yake boye, da baza a sani ba ko kuma ba abinda ke asirce da bazaya bayyana a fili ba. 23 Bari mai kunnen ji, ya ji!" 24 Sai ya ce masu, ku mai da hankali a kan abin da kuka ji, Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a kara maka. 25 Domin mai abu akan karawa, marar abu kuma za a karba daga wurinsa a kuma karawa mai shi." 26 Sai ya ce, "Mulkin Allah kamar mutum yake mai yafa iri a kasa. 27 A kwana a tashi har irin ya tsiro, ya girma bai kuwa san ta yaya aka yi ba. 28 Kasa da kanta, takan ba da amfani, tsiro shine ne na farko, 29 Sai kai, sa'anan sai kwaya mai kwari. Sa, adda amfani ya nuna, sai ya sa lauje ya yanke nan da nan, wato kaka ta yi kenan." 30 Ya kuma ce, "Da me za mu kwatanta Mulki Allah? ko kuwa da wane misali za mu misalta shi? 31 Kamar kwayar zarra yake wadda, in an shuka ta, ko da yake ita ce mafi kankanta cikin kwayoyi a duniya. 32 Duk da haka in an shuka ta, sai ta yi girma fiye da duk sauran ita-tuwan da ke a jeji tayi manyan rassa, har tsuntsaye su iya yin sheka arassanta." 33 Da misalai da yawa, irin wadannan ya yi masu Magana, dadai gwargwadon ganewarsu, 34 ba ya fada masu kome sai da misali, amma a kebe, yakan bayyana wa almajiransa dukan abu. 35 A ranan nan da yama ta yi yace masu "Mu haye wancan ketaren." 36 Sai suka bar taron, suka tafi tare da shi acikin cikin jirgin. wadansu jirage kuma na tare da shi. 37 Sai babban hadari da iska mai karfi ya taso, rakuman ruwa kuma na ta girgizawa cikin jirgin, har jirgin ya cika. 38 Yesu kuwa na daga karshen bayan jirgin a kan kujera, yana barci, sai suka tashe shi, suka ce masa "Malam za mu hallaka ba ka kula ba?" 39 Sai ya farka, ya tsawata wa Iskar. Ya kuma ce wa ruwan tekun, "Ka natsu! ka yi shiru!" Sai Iskar ta kwanta, wurin duk ya yi shiru. 40 Ya ce masu, "Don me kuka firgita haka? Har yanzu baku da bangaskiya ne?" 41 Sai suka tsorata kwarai suka ce wa juna, "wanene wannan kuma, wanda har Iska da teku ma suke yi masa biyayya?"
A sa'ada Yesu ya koya masu daga cikin jirgin ruwa a bakin teku, ya basu misalin kasa.
Wannan Tekun Galili ne.
"Ku saurara! Wani manomi"
An yia maganar dukkan irin da manomin ya shuka kamar iri guda ɗaya ne. "irin ... waɗansu ... tsince su ... Wasu iri ... ba su sami ... suka tsiro ... ba su sami"
"A sa'ad da ya wasa iri a ƙasa." A al'adu daban-dabam mutane suna da hanyoyin shukin iri daban-dabam. A wannan misalin an shuka iri ta wurin wasa wa a ginar da aka shirya.
"irin da aka shuka a gonar da ke da duwasu sun fara girma da sauri"
Wannan na nufin datti da ke kasa wanda za a iya shuka iri.
Wannan na nufin shukin da basu kosa ba. AT: "ta yankwane shukin da basu kosa ba"
"domin shuki ba ta da saiwa sosai, sai suka bushe"
A nan an yi magana game da duk irin da manomin ya shuka kamar iri guda ɗaya ne. Dubi yadda ka juya wannan cikin [Markus 4:3]. "Wasu iri ... suka shake su ... ba su bada amfani ba"
Yawan tsaban da shukin ta bayar an kwatanta shi da iri guda da ya yi girma. AT: "Waɗansu shukin sun bada amfani fiye da irin da mutumin ya shuka sau talatin, waɗansu iiri sun bada tsaba sau sittin, waɗansu kuma sun bada amfanin tsaba sau dari"
"30 ... 60 ... 100." Za a iya rubuta waɗannan cikin adadi.
Wannan wata hanya ce da ake nufin duk wanda ke wurin wanda kuma na jin abin da Yesu yake faɗa. AT: "Kowa wanda zai iya ji na" ko "Duk wanda zai iya ji na"
A nan kalman nan "ji" na nufin saurara. AT: "yă saurara da kyau" ko "lalle ne ya suarari abin da ina faɗa da kyau"
Ba wai wannan na nufin cewa Yesu yana nan gabaɗaya shi kaɗai ba; maimakon haka, abin nufi shine, lokacin da taron sun tafi, Yesu kuma na tare da sha biyun da wasu masubinsa.
AT: "Allah ya ba ku" ko "Na ba ku"
"amma waɗanda ba sa cikin ku." Wannan na nufin dukkan mutanen da ba sa cikin sha-biyun ko sauran masubi Yesu na kusa.
Ana iya faɗin cewa Yesu ya ba wa mutanen misalai. AT: "Kowane abin da na faɗa, na yi shi cikin misali"
Ana ɗaukan cewa Yesu yana magana game da mutane suna ganin abubuwan da ya nuna masu suna kuma jin abin da ya gaya masu. AT: "sa'ad da suna ganin abin da nake yi ... sa'ad da suna jin abin da nake faɗa
Yesu yana magana game da fahimtar mutane ga abin da suka gani kamar a zahiri suna gani ne. AT: "sun gani ba su kuma gane ba"
"juyo wurin Allah." Anan "juyo" na nufin "tuba," AT: "za su tuba"
"Sai Yesu ya ce wa almajiransa"
Yesu ya yi amfani da waɗannan tambayoyi don ya nuna fushin sa cewa almajiransa ba su fahimci misalinsa ba. AT: "Idan ba ku iya fahimtar wannan misalin ba, yi tunani game da zai yi maku wahala ku fahimci sauran misalen."
"Manomi wanda ya shuka irinsa na wakilcin"
"maganar" na nufin saƙon Allah. Bada sakon na nufin koyar da ita. AT: "wanda yake koyawa mutane saƙon Allah"
"wasu mutane suna kamar iri da suka faɗi a gefen hanya" ko "wasu mutane suna kamar hanyan da wasu iri suka faɗi"
"tafarki"
A nan "ta" na nufin "maganan" ko "saƙon Allah"
"wasu kuma suna kamar irin." Yesu ya fara bayana yadda wasu mutane suna kamar iri da ta faɗi a kan ƙasa ma duwatsu.
Wannan kwatanci ne da shuki da jijiyoyin sa ba su yi zurfi ba. Wannan na nufin cewa mutanen sun yi murna sa'ada suka karɓi magana, amma basu dukufa ga maganar ba. AT: "suna kuma kamar shuki da ba shi da jijiya"
Wannan na nanata rashin zurfin jijiyoyin.
A wannan misali, "jimre" na nufin "bada gaskiya." AT: "cigaba cikin bangaskiyarsu"
Zai zama da taimako in an bayana cewa kunci na zuwa domin mutane sun bada gaskiya ga saƙon Allah. AT: "kunci ko tsanani na zuwa domin sun bada gaskiya ga saƙon Allah"
A wannan misalin, "tuntuɓe" na nufin "sun daina bada gaskiya ba saƙon Allah"
Yesu ya fara bayana yadda wasu mutane suke kamar iri da ya faɗi cikin ƙaya. AT: "wasu mutane kuma suna kamar irin da aka shuka cikin ƙaya"
"damuwoyin wannan rayuwa" ko "damuwan rayuwan yanzu"
"sha'awace sha'awacen dukiya"
Sa'anda Yesu ya cigaba da magana game da mutane wanda suke kamar irin da ta fadi cikin ƙaya, ya bayana ainihin mecece sha'awace sha'awace da damuwo'in ke yi wa kalmar a rayuwansu. AT: "sun shiga sun shake saƙon Allah cikin rayuwar su kamar yadda ƙaya ke shake shuki"
"maganan ba ta bada amfani gona a cikinsu ba"
Yesu ya fara bayana cewa wasu mutanen suna kamar iri da aka shuka a ƙasa mai kyau. AT: "kamar iri da aka shuka a ƙasa mai kyau"
Wannan na nufin tsaba da aka shukin ta bada amfanin ta. AT: " wasu sun yi tsaba talatin, wasu tsaba sittin, wasu kuma tsaba ɗari" ko "wasu sun bada tsaba fiye da abinda aka shuka sau 30, wasu sun bada tsaba fiye da abin da aka shuka sau 60, wasu kuma sun bada tsaba fiye da abin da aka shuka sau 100"
"Yesu ya cewa taron"
A nan iya rubuta wannan tambaya kamar ba tambaya ba. AT: "Haƙika ba a kawo fitila cikin gida don a rufe ta da kwando, ko a ajiye ta a ƙarƙashin gado!"
AT: "Gama duka abin da yake a ɓoye za a bayyana shi, kuma kowane abin da ke a asirce za a bayyana a fili"
"babu wani abin da ke a ɓoye ... babu wani abin da ke a asirce" Maganganu biyun nan na nufin abu ɗaya. Yesu yana nanata cewa kowane abu da ke a asirce za ta zama sanannen.
Dubi yadda ka juya wannan cikin [Markus 4:9]
"Yesu ya ce wa taron"
Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) Yesu yana magana game auwu da kuma bayarwa a yalwace ga wasu ko 2) wannan na nufin Yesu yana magana game da "fahimta" sai ka ce "auwu."
AT: "Allah zai auna maka, zai kuma kara maka"
AT: "Allah zai kara masa ... Allah zai karɓe" ko "Allah zai kara masa ...Allah zai karɓe daga wurinsa"
Yesu ya kwatanta mulkin Allah da manomi wand aya shika irinsa. AT: "kamar manomin da ya shuka irinsa"
Wannan abu ne da mutumin ya saba yi. AT: "Yana barci kowane dare, yana kuma tashiwa kowane rana" ko "Yana barci kowane dare ya kuma tashi kashegari"
"ya tashi da rana" ko "ya fara aiki da rana"
"kodashike mutumin bai san ya aka yi irin ya toho ya kuma yi girma ba"
kara ko toho
kan kara ko bangare shuke da ke rike 'ya'yan
A nan "lauje" na nufin manomin ko mutanen da manomin ya aike su girbin hatsin. AT: "nan da nan ya tafi gonar da lauje do ya yi girbin hatsi" ko "nan da nan ya aiki mutane da lauje zuwa cikin gonar su yi girbin hatsin"
wani wuka da ke a lanƙwashe ko wani kugiya mai kaifi da ana amfani da ita a girbe hatsi
A nan maganan nan "ta yi" na nufin hatsin ta yi don girbi. AT: "domin hatsi ta yi domin girbi"
Yesu ya yi wannan tambaya domin masu karatun su yi tunani game macece mulkin Allah. AT: "Da wannan misalin zan iya kwatanta mulkin sama."
AT: "sa'ad da wani ya shuka ta"
An bayana bishiyan mustad kamar an sa rassan tayi manya. AT: "da manyan rassa"
"Magana" anan na nufin "saƙon Allah." Kalman nan "su" na nufin taron. AT: "ya koyawa masu sakon Allah"
"kuma ida sun iya fahimtar wasu, sai ya cigaba da gaya masu"
Wannan na nufin cewa ba ya tare da taron, amma almajiransa suna tare da shi.
A nan "kowane abu" daɗaɗawa ne. Ya bayana masu duk misalinsa. AT: "Ya bayana masu duk misalinsa"
"wancan ƙetaren Tekun Galili" ko "wancan ƙetaren takun"
A nan "taso" na nufin "fara." AT: "sai babban hadari mai iska ya fara"
Zai yi taimako in an bayana cewa jirgin yana cika da ruwa. AT: "jirgin na hatsarin cika da ruwa"
A nan "kansa" na nanata cewa Yesu shi kaɗai ya kasan jirgin. AT: "Yesu kansa na nan shi kaɗai"
Wannan ita ce bayan jirgin. "bayan jirgin"
Kalman nan "su" na nufin almajiransa. Kwatanta zance dake kusan ɗaya da wanda ke a aya 39, "Ya tashi." "Ya" na nufin Yesu.
Almajiran sun yi wannan tambaya don su nuna soron su. A nan iya rubuta wannan tambaya a matsayin magana. AT: "ya kamata ka jawo hankalin ka ga abin da yake faruwa; mun kusa mu mutu dukkan mu!"
Kalman nan "mu" na nufin almajiran da Yesu kansa.
Waɗannan maganganu biyun suna nan kusan iri ɗaya ne kuma suna nanata abin da Yesu ya son iska da tekun su yi.
"an sami matuƙar kwantawar iska a tekun"
Yesu ya yi waɗannan tambayoyi don ya jawo hankalin almajiransa su duba dalilin da ya sa suka firgita a sa'ad da yake tare da su. AT: "Bai kamata ku ji tsoro ba. kuna bukatan ku sami bangaskiya sosai."
Almajiran sun yi wannan tamaya cikin mamaki saboda abin da Yesu ya yi. AT: "Wannan mutum ba kamar sauran mutane bane; har iska da teku sun yi masa biyayya!"
Yesu ya shiga kwalekwale ya yi koyarwa domin akwai taron mutane kwarai da suka tattaru a kewayen shi.
Tsuntsaye suka zo sun cinye su.
Sun yankwane domin basu da tushe.
Ƙayayuwa sun shaƙe su.
kwayan hatsin sun haifi 'ya'yan hatsi, har sau talatin , sau sitin da kuma wasu har sau dari abin da dã aka shuka.
Yesu ya ce an bawa guda sha biyun nan asirin mulkin Allah , amma ba tare da wadanda suke a waje ba.
Kwayar hatsin nan itace maganar Allah.
Yana wakiltan wadanada suka ji maganar Allah , amma nan da nan shaidan ya dauke ta.
Yana wakiltan wadanda suka ji maganar da farin ciki, amma da tsanani ya zo sai suka yi tuntube.
Yana wakiltan wadanda suka ji maganar, amma sha'awar duniya ta shaƙe maganar.
Yana wakiltan wadanda suka ji maganar, suka karba suka kuma yi amfani da shi.
Yesu ya ce za a kawo haske duka abubuwan da suke a boye da kuma na asiri.
Mutumin yana hsuka kwayan hatsi, tana kuma girma, amma bai san ko ta yaya ba, sannan a lokacin girbi ya kan tara su.
Kwayan mustar takan fara kamar karamin kwaya a cikin kwayoyi, amma ta kan yi girma ta zama wata babban itace inda abubuwa da yawa sukan yi gida.
Wata babban hadari ta fara, ta na yin kurarin cika kwalekwalen da ruwa.
Almajiran sun tambayi Yesu ko ya kula wai sun yi kusan mutuwa.
Yesu ya na barci.
Yesu ya tsawata iskan ya kuma natsad da tekun.
Almajiran suka cika da tsoro sosai sun kuma yi mamakin wanene Yesu da iska da teku suna masa biyayya.
1 Da su ka zo daya ketaren tekun, wanda ya ke cikin yankin Garasinawa. 2 Sa'adda Yesu ya sauko daga cikin jirgin ruwan sai wani mutum mai aljanu ya fito daga cikin kaburbura ya tarbe shi. 3 Mutumin yana zama a cikin kaburbura. An daure shi da sarkoki da mari 4 An daure shi da sarkoki da mari sau da yawa, amma ya tsuntsunke sarkoki da marin. har ma ba wanda zai iya daure shi kuma. 5 Dare da rana a cikin kabarbarun da duwatsu mutumin ya na ihu ya na yaiyage jikinsa da duwatsu masu kaifi. 6 Sa'adda ya hango Yesu daga nesa, sai ya tarbi Yesu ya durkusa a gabansa. 7 Ya tada muryarsa da karfi ya ce, ina ruwa na da kai? Yesu Dan Allah Madaukaki Ina rokon ka da sunan Allah kada ka bani wahala, 8 Gama Yesu ya ce masa kai aljani ka fito daga cikinsa." 9 Ya tambaye shi, "Yaya sunanka? Ya ce suna na tari gama muna da yawa. 10 Ya yi ta rokonsa kada ya raba su da wannan yankin kasar. 11 Akwai babban garken aladu a wurin suna kiwo a gindin tsauni. 12 Sai suka roke shi ya bar su su shiga cikin wadannan aladun. 13 Shi kuma ya yardar masu. Aljanun suka fita suka shiga cikin aladun su kimanin dubu biyu. Aladun dubu biyu suka gangaro daga gindin tsaunin suka fada cikin ruwa. 14 Mutanen da ke kiwon aladun su ka shiga cikin gari da kewaye suka bada labarin abin da ya faru. Mutane da yawa suka je su ga abin da ya faru 15 Sai suka zo wurin Yesu suka ga mutumin mai aljanun a zaune, cikin hankalinsa, saye da tufafi, sai suka tsorata. 16 Wadanda suka zo su ka ga abin da ya faru da mutumin mai aljanun, suka je suka fada wa mutane abin da suka gani game da aladun. 17 Mutanen suka roke shi ya fita daga yankin kasarsu. 18 Shi mutumin da aljanu ke iko da shi, sa'adda ya ga Yesu zai shiga cikin jirgin ruwa ya tafi, ya roki Yesu da ya bi shi. 19 Amma Yesu bai yarda masa ba. Ya ce masa ka tafi gidanku, wurin mutanenka ka gaya ma su alherin da Ubangiji ya yi maka. 20 Mutumin ya shiga cikin Dikafolis yana shaidar babban abin da Yesu ya yi masa, dukansu suka cika da mamaki. 21 Sa'adda Yesu ya sake ketaren kogin zuwa daya gefen, acikin jirgin, sai taron jama'a suka keweye shi, a gefen tekun. 22 Sai wani daya daga cikin shugabannin Majami'a mai suna Yayirus, ya zo, wurinsa sa'adda ya ganshi ya durkusa a gabansa. 23 Ya yi ta rokonsa, yana cewa, "Diya ta ba ta da lafiya har ma ta kusa mutuwa. Ina rokonka mu je gida na ka dora ma ta hannu domin ta warke. ta rayu." 24 Sai ya tafi tare da shi, babban taro suka biyo shi har ma suna matse shi. 25 Akwai wata mace wadda ta ke zubar jini ta kai tsawon shekara goma sha biyu. 26 Ta sha wahala kwarai da gaske ta je wurin likitoci da yawa ta kashe kudi sosai, amma ba ta warke ba abin ma sai karuwa ya ke yi. 27 Ta ji labarin Yesu. Sai ta biyo bayansa yana tafiya cikin taro, ta taba habar rigarsa. 28 Domin ta ce "Idan dai na taba ko da habar rigarsa zan warke." 29 Da dai ta taba shi sai zubar jinin ta ta tsaya, ta ji a jikin ta ta warke, daga damuwarta. 30 Nan da nan, Yesu ya ji iko ya fita daga gare shi sai ya ce "wanene ya taba rigata?" 31 Almajiransa suka ce, "a cikin wannan taron mutane da yawa ka ce wanene ya taba ni?" 32 Amma Yesu ya waiga ya ga ko wanene ya taba shi. 33 Matar ta san abin da ya faru sai ta zo cikin tsoro da rawar jiki ta durkusa a gaban Yesu ta fada masa gaskiya. 34 Sai ya ce da ita, "Diya bangaskiyarki ta warkar da ke, ki tafi lafiya kin sami warkewa daga cutarki". 35 Sa'adda ya ke magana da ita sai ga mutane daga gidan shugaban majami'a suka ce "Diyarka ta mutu me ya sa za ka dami malam?" 36 Amma sa'adda Yesu ya ji abin da suka ce, sai ya ce da shugaban majami'ar, "kada ka ji tsoro ka ba da gaskiya kawai." 37 Bai bari kowa ya kasance tare da shi ba sai Bitrus da Yakubu da Yahaya dan'uwan Yakubu. 38 Suka zo gidan shugaban majami'ar ya ga mutane suna bakin ciki, suna kuka sosai. 39 Sa'adda ya shiga gidan ya ce da mutane "Me ya sa kuke damuwa da kuka?" Yarinyar ba ta mutu ba barci ta ke yi. 40 Sai su kayi masa dariya. Amma ya fitar da su waje su duka. Ya kira baban yarinyar da mamar ta da wadansu da ke tare da shi su ka shiga wurin da yarinyar ta ke. 41 Ya kama hannun yarinyar ya ce da ita "Tilatha koum" wato yarinya na ce ki tashi" 42 Nan da nan yarinyar ta tashi ta yi tafiya (gama shekarun ta sun kai goma sha biyu). Nan da nan mutanen suka yi mamaki kwarai da gaske. 43 Ya ummurce su da gaske kada kowa ya sani. Ya ce da su su ba ta abinci ta ci.
Bayan Yesu ya kwantar da iska, ya wakar da wani mutum da ke da aljannu, amma Garasinawan ba su yi murna domin ya yi warkarwa ba, saboda haka sun roƙe Yesu ya tafi.
Kalman nan "Su" na nufin Yesu da Almajiransa.
Wannan na nufin Tekun Galili.
Wannan suna na nufi mutanen da zama cikin Garasa.
Wannan karin magana ne da ke nufin cewa baƙin ajan na "mulki" ko "ya haukatar da shi". AT: "baƙin aljan na mulkinsa" ko "baƙin aljan ya haukatar da shi"
AT: "Mutane sun ɗaure shi da sarkoki sau da yawa"
AT: "ya tsintsinke sarkokinsa"
karafuna da mutan sukan kewa hannu da kafafun ɗan sarka su kuma haɗa shi da sarka da kuma wani abu da ba ya motsi don kada fursunan ya yi motsi
Mutumin na da ƙarfi har ma ba wanda zai iya ɗaure shi. AT: "Ya na da ƙarfi sosai har ma ba wanda ke da ƙarfin ɗaure shi"
"mulke shi"
Sa'ad da aljan ya mallake mutumin, so da dama aljan zai sa mutumin ya yi munanan abubuwa da zai hallakas da shi, wato abu kamar, yaiyanke kansa.
Da ganin Yesu, mai yiwuwa Yesu na koƙarin fitawa da jigin ruwa kenan.
Wannan na nufin cewa ya durkusa a gaban Yesu don ya girmama ya kuma daraja shi, ba ya na masa sujada ba.
Bayanin da ke waɗannan ayoyi biyun ana iya săke shirya shi don a iya ba da labarin daidai yadda ya faru, kamar yadda yake a UDB.
"Baƙin aljanin ya tada murya"
Baƙin aljanin ya yi wannan tambayar don ya ji tsoro ne. AT: "Rabu da ni, Yesu, Ɗan Allah Maɗaukaki! Babu wata dalili da zai sa ka sami sabani da ni."
Yesu na da ikon ba wa baƙin aljanin azăba.
Wannan lakani ne mai muhimmanci na Yesu.
A nan baƙin aljanin na ransuwa da Allah a sa'ada yana roƙo Yesu. Dubi yadda ake irin wannan roƙo a harshen ku. AT: "a gaban Allah ina roƙon ka" ko "na rantse da sunan Allah, ina roƙon ka"
"Sai Yesu ya tambaye baƙin ajan"
Ɗaya daga ciki aljanun na magana a maɗaɗɗin sauran. Ya yi magana game da su sai ka ce su rundunan, rundunar sojojin Romawa da ke kusan sojoji 6,000. AT: "Sai aljan ya ce masa, 'ka kira mu rundunan, domin dayawan mu muna cikin mutumin nan."
"bakin aljanun sun roke Yesu"
Zai iya zama da taimako in an bayana a fili abin da Yesu ya bar su su yi. AT: "Yesu ya bar baƙin aljanun su yi abin da suka roƙa"
"aladun suka ruga a guje"
Ka na iya raba wannan zuwa jimla daban dabam: "zuwa cikin teku. Aladun kusan dubu biyu ne, sun kuma hallaka a cikin tekun"
"aladu kusan 2,000"
Ana iya bayana a fili cewa mutanen sun ba da rohoto abin da ya faru ga mutanen da ke cikin gari da kewaye. AT: "ga mutanen cikin gari da kewaye"
Wannan sunan aljanun da dã suna cikin mutumin. Dubi yadda ka juya wannan cikin [Markus 5:9].
Wannan na nufin cewa yana tunani da kyau. AT: "hankalinsa daidai" ko "tunani da kyau"
Kalman nan "su" na nufin mutanen da suka je su ga abin da ya faru.
"Mutanen da sun ga abin da ya faru"
Kodashike a yanzu mutumin ba shi da aljan, akan bayana shi a haka. AT: "mutumin da dã ke da aljan"
Ana iya bayana a fili abin da Yesu bai ba shi daman yi ba. AT: "Amma bai bar mutumin ya bi su ba"
Wannan suna wani yanki ne da ke nufin Birane Goma. Ya na a kudu-gabacin Tekun Galili.
Zai zama da taimakon in an bayana dalilin da ya sa mutanen suka yi mamaki. AT: "dukkan mutanen da suka ji abin da mutumin ya faɗa sun yi mamaki"
Zai zama da amfani in an kara bayani a wannan magana. AT: "ɗayan bangaren teku"
"a bakin tekun" ko "gaɓar teku"
Wannan sunan mutum.
"sai Yesu ya tafi tare da Yayirus." Almajiran Yesu ma sun tafi tare da shi. AT: "Sai Yesu da Almajiran sun tafi tare da Yayirus"
"Sa hannu" na nufin annabi ko malami ya sa hannunsa a kan wani, yana kuma warkar da shi ko sa masa albarka. A wannan al'amari, Yayiru yana tambayar Yesu ya warkar da 'yarsa.
AT: "ya kuma warkar da ita da sa ta ta rayu"
Wannan na nufin sun taru kewaye da Yesu sun matse kansu don su yi kusa da Yesu.
"yanzu" na bada alaman cewa an gabatar da wannan macen a labarin. Dubi yadda kuna gabatar da abon mutum cikin labarin a harshen ku.
Macen ba ta da wani ciwon da ke a buɗe; maimakon haka, hailar ta bai tsaya ba. Mai yiwuwa harshen ku na da wata hanya mai da'a da ana iya faɗin wannan yanayi.
"tsawon shekara 12"
"rashin lafiyar sai karuwa ya ke yi" ko "zub da jinin sai karuwa ya ke yi"
Ta ji labari game da Yesu yadda ya warkar da mutane. AT: "cewa Yesu ya warkar da mutane"
rigar da ake sa a waje ko kwat
AT: "zai warkar da ni" ko "ikonsa za ta warkar da ni"
AT: "cutar ya bar ta" ko "ta sami lafiya"
Sa'ad da macen ta taɓa Yesu, Yesu ya ji ikon warkar da ita.Yesu kansa bai rasa ikonsa na warkar da mutane ba sa'ad da ya warkar da ita. AT: "cewa ikonsa na warkarwa ya warkar da macen"
Wannan na nufin sun taru kewa da Yesu, sun matse junansu don su yi kusa da Yesu. Dubi yadda ka juya wannan cikin [Markus 5: 24]
"durkusa a gabansa." Ta durkusa a gaban Yesu a matsayin girmamawa da mika kai.
Maganan nan "gaskiyar gabakiɗaya" na nufin yadda ta taɓa shi har ta warke. AT: "faɗa masa gaskiyar gabakiɗaya game da yadda ta taɓa shi"
Yesu ya yi amfani da wannan kalma don yana duban macen a matsayin maibi.
"bangaskiyar ki a ciki na"
"Sa'ad da Yesu ke magana"
Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) waɗannan mutane sun zo daga gidan Yayirus ko 2) Yayiru ya riga ya umurce waɗannan mutane su zo su ga Yesu ko 3) mutumin da ke shugaban majami'a a sa'ad da Yayiru ba ya nan, shine ya turo waɗannan mutane.
"shugaban majamia" shine Yayirus.
"majami'a, cewa wa Yayirus"
AT: "Ba shi da amfani a dame malamin kuma." ko "Ba ku bukata ku dame malamin kuma."
Wannan na nufin Yesu.
In lallei ne, to ana iya faɗin abin da Yesu yake umurtan Jarus ga bada gaskiya ga shi. AT: "Ka dai gaskanta cewa zan ta da 'yar ka"
Cikin waɗannan ayoyi kalman nan "Ya" na nufin Yesu.
"ya bi shi ba." Zai zama da taimakon in an faɗa wurin da za suna koƙarin zuwa. AT: "ya bi shi zuwa gida Shugaban majami'a"
"Yesu ya cewa mutenen da suke kuka"
Yesu ya yi wannan tambaya don ya taimake su su ga reashin bangaskiyarsu. AT: "Wannan ba lokacin damuwa da kuka ba ne."
Yesu ya yi amfani da kalman da an saba amfani da ita na barci, haka kuma sai a yi amfani da shi a juyin. Ya kamata masu karatun su fahimta cewa mutanen da ke sauraron Yesu sun yi masa dariya domin ba su san bambanci tsakanin mutumin da ya mutu da wanda ya ke barci ba, suna kuma tunanin cewa shi bai sani ba.
"ya fitar da sauran mutanen da ke cikin gidan zuwa waje"
Wannan na nufin Bitrus, Yakub da Yahaya.
Zai zama da taimakon in an bayana inda yarinyar take. AT: "shiga cikin ɗakin da yarinyar take kwanciye"
Wannan jimlar da harshe Yahudanci ne, wanda Yesu ya yi magana da karamar yarinyar cikin harshen ta. Ku rubuta waɗannan kalmomin kamar yadda yake da haruffan ku.
"shakarun ta 12 ne"
AT: "Ya umurce su da gaske, 'kada kowa ya san game da wannan!' Sa'annan" ko "Ya umurce da gaske, 'Kada ku gaya wa kowa game da abin da na yi!' Sa'annan"
"Ya ba su umurni da gaske"
AT: "Sai ya ce masu, 'Bata abinci ta ci"
Wani mutum mai aljanu ya sadu da Yesu.
A lokacin da mutane sun yi kokari su tsare wannnan mutum da tsarkoki, ya ɓarke su sarkokin.
Aljanun suka kira Yesu Ɗan Allah mafi Girma.
Yesu ya cewa mutumin '''fito daga cikin mutumin nan, kai aljani''.
Sunan aljanin nan ita ce runduna, domin suna da yawa.
Aljanun nan suka fita sun shiga garken aladu, wadanda suka gangara tsauni sun nutsa cikin tafki.
Mutumin yana zaune da Yesu, da tufafi a jikin sa a kuma cikin hankalinsa.
Mutanen nan sun cewa Yesu ya tafi da ga yankin su.
Yesu ya gaya wa mutumin ya gaya wa mutanensa abun da Ubangiji ya yi masa.
Yayirus ya roka Yesu ya ta fi tare da shi ya sa hannun sa a kan diyar sa wanda take kusan mutuwa.
Matan ta na wahala da cutar fid da jini na tsawon shekaru goma sha biyu.
Matan ta yi tunani idan ta taba mayafin Yesu za ta samu warkarwa.
Yesu ya san cewa iko ya fita daga cikinsa ya kuma duba kewaye ya ga wanene ya taba shi.
Yesu ya gaya mata bangaskiyar ta ya warkar da ita, ta kuma tafi a cikin salama.
Diyar Yayirus ta mutu.
Yesu ya gaya wa Yayirus kada ya ji tsoro, amma ya ba da gaskiya.
Biturs, Yakubu da Yahaya suka tafi da Yesu cikin dakin.
Mutanen sun yi wa Yesu dariya da ya ce diyar Yayirus barci kawai take yi.
An shawo kan mutanen sosai suka kuma yi mamaki.
1 Ya bar su ya zo garinsu, almajiransa su ka biyo shi. 2 Sa'adda ranar Asabar tazo ya shiga cikin masujada ya yi koyarwa. Mutane da yawa da su ka ji koyarwarsa su ka yi mamaki, suka ce daga ina ya sami irin wannan koyarwar? Wacce irin hikima ce Allah ya ba shi haka? Wadanne irin ayyukan al'ajibi ya ke yi da hannuwansa? 3 Wannan ba kafintan nan ba ne dan Maryamu, dan'uwan Yakubu da Yosi da Yahuza da Saminu? Ba ga 'yan'uwan sa 'yan mata mu na tare da su ba? Ba su ji dadi ba a ransu saboda Yesu. 4 Yesu ya ce, "Annabi ba ya rasa daraja sai a gidansa da garinsa da cikin danginsa." 5 Bai iya yin wani aikin al'ajibi a wurin ba sai dai mutane kadan marasa lafiya ya dorawa hannu ya warkar da su. 6 Rashin bangaskiyarsu ya ba shi mamaki. Sai ya tafi cikin kauyuka na kewaye da su ya yi ta koyarwa. 7 Ya kira almajiransa su goma sha biyu, ya aike su biyu-biyu, ya ba su iko a kan aljanu, 8 ya dokace su kada su dauki komai tare da su domin wannan tafiya, sai dai sanda kadai. Kada su dauki abinci ko jaka ko kudi a cikin aljihunsu, 9 sai dai su sa takalmi kadai, kada su sa taguwa biyu a jikinsu. 10 Ya ce da su, idan ku ka shiga wani gida sai ku zauna a gidan har lokacin da za ku tashi. 11 Idan ku ka je wani gari aka ki karbar ku, ku karkabe kurar da ke kafufunku ta zama shaida kan mutanen garin. 12 Sai suka tafi suka yi ta shela ga mutane cewa su tuba daga zunubansu. 13 Sun fitar da aljanu da yawa, suka shafawa mutane da yawa mai suka warkar da su. 14 Sarki Hirudus ya ji wannan, gama sunan Yesu ya zama sananne a wurin kowa da kowa. Wadansu suna cewa Yahaya mai yin baftisma ne ya tashi daga matattu shi ya sa ake yin wadannan ayyukan al'ajibi ta wurinsa. 15 Wadansu kuma suna cewa, "Iliya," Har yanzu wadansu suna cewa daya "daga cikin annabawa ne na da can." 16 Sa'adda Hirudus ya ji wannan sai ya ce, "Yahaya wanda na fillewa kai shine ya tashi." 17 Saboda Hirudus ne ya sa aka kama Yahaya aka kulle shi a kurkuku saboda Hirodiya( matar Filibus dan'uwansa), domin ya aure ta. 18 Saboda Yahaya ya gaya wa Hirudus cewa bai halarta ya auri matar dan'uwansa ba. 19 Sai ita Hirodiya ta yi kudurin ta kashe Yahaya amma bai yiwu ba. 20 Domin Hirudus yana jin tsoron Yahaya, domin ya sani shi mai adalci ce, mai tsarki kuma. Domin haka Hirudus bai so wani abu ya faru da Yahaya ba, amma ya kan fusata idan ya ji wa'azin yahaya. Duk da haka da fari ciki yakan saurare shi. 21 Amma sai dama ta samu inda Hirodiya za ta iya yin abin da ta ke so ta yi. A lokacin kewayowar ranar haihuwar sa, sai Hirudus ya shirya liyafa domin manyan da ke aiki tare da shi a cikin gwamnatin sa, da shugabannin da ke cikin Galili. 22 Diyar Hirodiya ta zo ta yi masu rawa, rawarta kuwa tagamshi Hirudus da bakinsa. Sarki ya ce da yarinyar, "ki tambayi duk abin da ki ke so ni kuwa zan ba ki shi". 23 Ya rantse mata da cewa"Ko menene ki ka ce ki na so, ko da rabin mulkina ne" 24 Sai ta fita ta je ta tambayi mamarta, "me zan ce ya bani?" Sai ta ce kan Yahaya Mai Yin Baftisma. 25 Sai ta dawo da sauri cikin dakin taro wurin sarki ta ce da shi, "Ina so ka ba ni kan Yahaya Mai Yin Baftisma a cikin tire." 26 Sarki ya damu kwarai, amma saboda ya yi alkawari ga kuma ofisoshinsa, ba dama ya ce a'a. 27 Sai sarki ya aiki wani soja ya ba shi ummurni ya je ya kawo kan Yahaya. Sojan ya je ya fillo kan sa daga cikin kurkuku. 28 Ya kawo kan a cikin tire ya ba yarinyar, yarinyar kuma ta kai wa mamarta. 29 Da almajiran su ka ji labari, suka zo suka dauki gawarsa suka rufe a cikin kabari. 30 Almajiran suka zo wurin Yesu, suka fada masa dukkan abin da suka yi da abin da suka koyar. 31 Sai ya ce da su "ku je cikin kebabben wuri domin ku huta kadan," domin mutane suna ta kaiwa da komowa, ba su sami damar hutawa ba balle su ci abinci 32 Sai suka tafi kebabben wuri a cikin jirgin ruwa su kadai. 33 Amma mutane da yawa sun gansu suna tafiya sun kuma gane su, sai suka fito daga cikin dukan garuruwa da gudu har su ka kai wurin kafin su zo. 34 Sa'adda suka zo bakin gaba Yesu ya ga taron mutane da yawa sai ya ji tausayinsu domin sun yi kamar tumakin da ba da mai kiwo. Sai ya cigaba da koya masu abubuwa da yawa. 35 Sa'adda yamma ta yi, almajiran sa suka zo suka ce da shi, "wurinnan kebabben wuri ne kuma ga lokaci ya tafi. 36 Ka sallami mutanen nan domin su shiga cikin garuruwa da kauyuka da ke kusa domin su sayi abin da zasu ci. 37 Amma sai ya ba su amsa ya ce,"Ku ku basu abinci su ci mana". Sai suka ce da shi, "ma iya zuwa mu sawo gurasa ta sule dari biyu mu basu su ci?" 38 Sai ya ce dasu, "Dunkulen gurasa guda nawa kuke dasu? Kuje ku gani." Dasuka gano sai suka ce da shi, dunkule biyar ne da kifi guda biyu." 39 Sai ya ba da umarni mutanen su dukka su zauna a kan danyar ciyawa. 40 Suka zauna kungiya kungiya wadansu su dari wadansu hamsin. 41 Sai ya dauki dunkulen gurasa guda biyar da kifi guda biyu, ya ta da kansa sama, yasa albarka, ya kakkarya dunkulen gurasan, ya ba almajiran domin su rabawa taron jama'a duka. 42 Dukansu suka ci suka koshi. 43 Suka tattara gutsattsarin gurasar suka cika kwanduna guda goma sha biyu da gutsattsarin da kuma gutsattsarin kifin. 44 Mutanen da suka ci gurasar sun kai mutum dubu biyar. 45 Nan da nan ya ce almajiran sa su hau jirgin ruwa su yi gaba kafin ya zo, su je Baitsaida. Shi kuma ya tsaya domin ya sallami taron mutanen. 46 Bayan da suka tafi shi kuma ya hau kan dutse domin ya yi addu'a. 47 Har yamma ta yi jirgin ruwan ya na tsakiyar rafi shi kuma yana kan tudu shi kadai. 48 Ya gansu suna wahala gama iska ta hana su tafiya. Wajan karfe hudu na asuba sai ya tawo wurin su yana tafiya a kan ruwa, yana so ya wuce gaban su. 49 Sa'adda suka gan shi ya na tafiya a kan ruwa suka yi tsammani fatalwa ce, suka yi ihu, 50 gama su duka sun gan shi, tsoro ya kama su. Sai nan da nan ya yi magana dasu ya ce, "Ku karfafa ni ne! kada ku ji tsoro!" 51 Ya shiga cikin jirgin ruwan tare dasu, sai iska ta dena bugawa. Sai suka yi mamaki kwarai. 52 Gama basu gane batun dunkulen ba. Maimakon haka, sai zukatansu suka taurare. 53 Sa'adda suka haye su zo kasar Janisarita suka sa wa jirgin sarka. 54 Su na fitowa daga cikin jirgin kenan, mutane suka gane cewa Yesu ne. 55 Mutane suka ruga cikin yankin su, suka kawo marasa lafiya a bisa shinfidun su zuwa wurinsa, dukan inda suka ji yana zuwa. 56 Ko ina ya shiga birni da kauye, ko a cikin kasar sukan kawo marasa lafiya a kasuwanni suna rokonsa su taba ko da habar rigarsa, dukan wadanda suka taba kuwa suka warke.
Yesu ya komo garinsa, inda ba a karɓarsa.
Wannan na nufin garin Nazarat, inda Yesu ya yi girma da inda iyalinsa suke zama. Wannan ba ya nufin cewa yana da nasa fili a wurin.
AT: "Macece wannan hikima da ya samu?"
Wannan magana na nanata cewa Yesu kansa yana yin abin al'ajibin. AT: "wanda shi kansa ya yi"
Waɗannan tambayoyin ana iya rubuta su cikin jimlar da ba tambaya ba. AT: "Wannan kafinta ne kawai! Mun san shi da iyalinsa. Mun san uwa tasa Maryamu. Mun san 'yan'uwansa Yakubu, Yosi, Yahuza da kuma Saminu. 'yan'uwansa mata kuma suna tare da mu."
"wa taron"
AT: "Ana daraja Annabi a koyaushe, sai" ko "Wurin da ba a daraja annabi shine"
Annabi da malami na iya sa hannu a kan mutane don ya warkar da su ko albarkace su. Wannan yanayi, Yesu yana warkar da mutane ne.
Umurnin Yesu a aya 8 da 9, ana iya sake kasafa shi ta wurin raba abin da ya gaya wa almajiransa su yi daga abin da ya ce masu kada su yi, kamar yadda yake a UDB.
A nan kalman nan "kira" na nufin cewa ya urmuce sha biyun su zo wurinsa.
"2 da 2" ko "cikin biyu"
A nan "gurasa" na nufin abinci. AT: "ba abinci"
A wancan al'ada, mazaje na ɗauka kuɗi su ajiye a cikin damararsu. AT: "ba kuɗi a cikin jakunan kuɗinsu" ko "ba kuɗi"
"Yesu ya cewa sha biyun"
A nan "zauna" na nufin komowa zuwa gidan ko wani ranar don su ci su kuma yi barci a wurin. AT: "ku ci, ku kuma kwanta a wannan gida har sai lokacin da za ku bar wannan wuri"
"ta zama shaidan a kansu." Zai zama da taimako a bayana yadda wannan ya zama shaida a gare su. "ta zama shaida a gare su. Tawurin yin haka, za ku shaidi cewa ba su marabce ku ba"
Kalman nan "su" na nufin sha biyun, ban da Yesu. Zai zama da taimako kuma a bayana cewa sun tafi garuruwa daban dabam. AT: "Sun shiga garuruwa daban dabam"
A nan "juyo daga" na nufin a daina yi wani abu. AT: "bar yin zunubi" ko "tuba daga zunubansu"
Zai iya zama da taimako a faɗa cewa sun fitar da aljanu daga cikin mutane. AT: "Sun fid da aljanu da yawa daga cikin mutane"
Kalman nan "wannan" na nufin dukkan abin da Yesi da almajiransa sun yi ta yi a garuruwa daban dabam, duk da fid da aljannu da kuma warkar da mutane.
Wasu suna cewa Yesu, shine Yahaya Mai Baftisma. Wannan ana iya bayana shi a fili. AT: "Waɗansu suna cewa, "Shine Yahaya Mai Baftisma ne wanda aka"
"Tashi daga mattattu" anan wata karin magana ne na "sa mutum ya rayu kuma." AT: "Ana tashe Yahaya Mai Baftisma kuma" ko "Allah ya sa Yahaya Mai Baftisma ya rayu kuma"
Zai zama da taimakon in an bayana cewa wasu mutane suna tunanin cewa shine Iliya. AT: "Waɗansu sun ce, 'Iliya ne wanda Allah ya yi alkawari zai aika kuma.'"
A nan Hirudus ya yi amfani da kalman nan "na" don yana nufin kansa ne. Kalman nan "na" na nufin sojijin Hirudus. AT: "wanda na umurci sojoji na su fille kansa"
AT: "yana raye kuma"
AT: "Hirudus ya aiki sojojinsa su kama Yahaya su kulle shi a kurkuku"
"umurta a"
"ta dalili Hirodiya"
"matar ɗan'uwansa Filibus." Filibus ɗan'uwan Hirudus ba ɗaya ne da Filibus wanda an ambata cikin littafin Ayukan Manzani ko Filibus ɗaya daga cikin almajiran sha biyu na Yesu.
"domin Hirudus ya aure ta"
Hirodiya shine kan maganan wannan magana "ta" na nufin cewa ta na so wani ya kashe Yahaya. AT: "ta na so wani ya kashe shi amma ba ta iya kashe shi ba"
Waɗannan magana biyu ana iya haɗa don ya nuna a fili dalilin da ya sa Hirudus yana jin tsoron Yahaya. AT: "domin Hirudus yana jin tsoron Yahaya domin ya sani"
"Hirudus ya sani cewa Yahaya mutum ne mai adalci"
yakan saurare Yahaya"
A nan kalman nan "ya" na nufin Hirudus, yana kuma na nufin bawansa wanda ya bada umurni a shirya liyafa. AT: "ya shirya liyafa domin manyan ma'aikatansa ... Galili" ko "ya gayaci manyan ma'aikatansa ... Galili ci su kuma yi murna tare da shi"
wata abinci ta musamman ko liyafa
Kalman nan "kanta" an yi amfani da ita don nanata cewa yana da muhimmanci cewa 'yar Hirudiya ne wanda ta yi rawa a lokacin liyafa.
"shigo cikin dakin"
"zan ba ki har rabin abin da nake da shi da mulkina, in kin roƙa"
"fita daga dakin"
"kan katako" ko "a kan babban kwano da aka yi da itace"
Ana iya bayana abin da ke cikin alkawarin, da kuma dangantaka tsakanin alkawarin da bakin da sun zo liyafa, a fili. AT: "domin baƙin sun ji ya yi alkawarin cewa zai ba ta kowane abin da ta roƙa"
"a kan tire"
"Sa'ad da almajiran Yahaya"
wurin da ba kowa
Wannan na nufin cewa mutane suna zuwa wurin manzanin su kuma koma.
Kalman nan "su" na nufin manzanen.
A nan kalman nan "su" na nufin manzanen da Yesu.
"mutanen sun ga Yesu da manzanen suna tafiya"
Mutanen suna tafiya a kafa, wannan kuwa ya zama da bambanci da tafiyar almajiran a kwalekwale.
"Yesu ya ga gaggaruman taro"
Yesu ya kwatanta mutane da tumakin da sun rikice a sa'ad da ba su da makiyayi da ke shugabantansu.
Wannan na nufin can da yamma. AT: "Sa'adda yamma ya fara yi" ko "Can da rana"
"Amma Yesu ya amsa ya cewa almajiransa"
Almajiran sun yi wannan tambaya don su bayana cewa babu wata hanya da za su iya sayan abinci da zai ishe taron. AT: "Ba za mu iya sayan gurasa wanda zai isa ciyad da wannan taron ba, ko muna da denari ɗari biyu!"
"denari 200." Mufuradin wannan kalman "denari" shine "denarus." Denarus guda kuɗi ne na azurfa wanda Romawa ke amfani da shi a wancan lokaci don biyan hakin ma'aikata a rana ɗaya.
dunƙulallen gurasa da aka yi.
Ku bayana ciyawan da kalman kalan da ake amfani da shi a harshen ku na ciyawa mai kyau, wanda maiyiwuwa ba kore ba.
Wannan na nufin mutane da ke kowane kungiya. AT: "mutane kunsan hamsin a wasu kungiya, wasu kuma mutane kusan ɗari wa wasu kungiyan"
Wannan na nufin cewa ya daga kansa ya dubi cikin sama, wanda ake kamata shi da inda Allah yake.
"ya albarkaci" ko "ya mika godiya"
"ya raba kifi biyun don kowa ya samu"
Ma'ana ma yiwuwa na kamar haka 1) "Almajiran sun tattara" ko 2) "Mutanen sun tattara."
"gursarin gurasar sun cika kwanduna goma sha biyu"
"kwanduna 12"
"maza 5,000"
Ba a lisafta yawan mata da 'ya'ya ba. Idan ba za a iya fahimtar cewa ba a ambata yawan mata da 'ya'ya ba, to za a oya bayana a fili. AT: "mutum dubu biyar sun ci gurasan. Ba ma kirga mata da yara ba"
Wannan na nufin Tekun Galili. Anan iya bayana wanna a fili. AT: "zuwa wata bangaren Teku Galili" (Dubi: gs_ellipsis)
Wannan gari ne a arewacin Tekun Galili.
"Sa'ad da mutanen sun tafi"
Wannan lokaci ne tsakanin 3 a.m.
ruhu matatcen mutum ko kuwa wasu irin ruhu
Waɗannan jimla biyun suna da ma'ana kusan iri ɗaya, suna kuma nanata cewa almajiran ba sa bukatan su ji tsoroI. In ta zama wajibi, ana iya haɗa su su zama ɗaya. AT: "Kada ku ji tsoro!"
In kuna bukatan ku bayana a fili abin da ya sa su mamaki za ku iya yi. AT: "Sun yi mamakin abin da ya yi"
A nan maganan nan "gurasan" na nufin sa'ad da Yesu ya ninka dunƙunlen gurasa. AT: "abin da ake nufi da cewa Yesu ya ninka gurasan" ko "abin da ake nufin sa'ada Yesu ya sa dunkulen gurasa ta karu ta yi yawa"
Taurin zuciya na nufin kin ji don a fahimta. AT: "sun taurare zuciyar har sun kãsa fahimta"
Wannan sunan yankin arewa maso yammacin Tekun Galili.
Zai zama da taimako in an bayana dalili da ya sa sun ruga zuwa cikin yankin. AT: "sun ruga zuwa cikin yankin don ya gayawa sauran mutane cewa Yesu yana wurin"
Kalman nan "su" na nufin mutane sun gane Yesu, ba almajiran ba.
Wannan magana na nufin mutane. AT: "mutane marasa lafiya"
"Duk inda Yesu ya shiga"
A nan "su" na nufin mutanen. Ba ya nufin almajiran Yesu.
Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) "Marasa lafiyan sun roƙe shi" ko 2) Mutanen sun roƙe shi."
Kalman nan "su" na nufin marasa lafiyan.
"bakin tufafinsa" ko "gefen rigarsa"
"dukkan waɗanda"
Mutanen ba su san daga ina ne ya samu nasa koyarwa, da basira, da kuma ayukan al'ajabin sa ba.
Yesu ya ce annabi ba shi da daraja a garinsa, a tsakanin danginsa, da kuma gidansa.
Yesus ya yi mamakin rashin ĩmanĩn mutanen garinsa.
Yesu ya ba wa goma sha biyun izini bisan aljanu.
Goma sha biyun sun dauki sandunansu, da takalma, da kuma taguwa daya.
Yesu ya gaya masu su kaɗa kuran da ke karkashin kafafuwansu ya zama shaida a kansu.
Mutanen sun yi tsammani cewa Yesu shine Yahaya mai baftisma, ko kuwa Iliya, ko kuwa wani annabi.
yahaya ya gaya wa Hiridus ba akan doka ba ne Hiridus ya auri matan dan uwan sa.
Hiridus yayi fushi da ya ji yahaya yana wa'azi,amma yana murnan sauraron shi.
Hiridus ya rantse za ta samu duk abin da ta tambaya daga wurin shi,kusan rabin mulkin shi
Hirudiya ta bukaci kan Yahaya mai baptisma akan akushi.
Hiridus ya yi bakin ciki sosai,amma bai ki biyan bukatan ta ba domin rantsuwan da ya yi a gaban bakin sa.
Mutane da yawa sun gane su suka yi gudu su kai can kafin Yesu da almajiransa.
Yesu ya ji tausayinsu domin suna nan kaman tumaki marasa makiyayi.
Almajiran sun yi tunanin za su je su sayi gurasa na dinari dari biyu.
Daman Almajiran suna da gurasa guda biyar da kifi biyu tare da su.
Da ya karbi gurasa da kifin, Yesu ya dubi sama, ya sa wa gurasan albarka ya raba, sai ya kuma bawa Almajiransa.
Kwanduna goma sha biyu na gurasa da gudan kifi ya rage bayan kowa ya ci.
Mutane dubu biya aka ciyar.
Yesu ya zo wurin almajiransa ya na tafiya a bisan tafkin.
Yesu ya gaya wa almajiran su yi gabagadi kada su ji tsoro,
Almajiran ba su gane al'ajibin gurasan ba domin hankalinsu ba tayi saurin ganewa ba.
Mutanen sun kawo marasa lafiya a kan gadaje zuwa wurin Yesu a duk inda da su ka ji wai yana zuwa.
Wadanda suka taba bakin tufafin Yesu kawai sun sami warkarwa.
1 Farisawa suka taru wurin Yesu tare da wadansu marubuta wadda suka zo daga Urushalima. 2 Sun ga cewa wasu daga cikin almajiransa sun ci gurasa da hannuwa marasa tsabta, wato, basu wanke hannu ba, 3 (Domin Farisawa da dukan Yahudawa ba su cin abinci sai dole sun wanke hannu da kyau domin suna kiyaye al'adun dattawa. 4 Idan Farisawa suka dawo daga kasuwa, wajibi ne su yi wanka kamin su ci abinci. Akwai sauran al'adun da suke kiyayewa, kamar wanke moda, tukwane, da wasu santula na dalma, har da dakin cin abinci.) 5 Farisawa da Marubuta suka tambaye Yesu, "Don me almajiran ka basu kiyaye al'adun dattawa, domin suna cin abinci ba tare da sun wanke hannu ba?" 6 Amma ya amsa masu cewa, "Ishaya ya yi anabci akan ku masu bautan ganin ido, da ya rubuta cewa 'wadanan mutane suna girmama ni a baka amma zuciyar su tana nesa da ni. 7 Sujadar wofi suke mani suna koyar da ka'idodi na mutane a matsayin rukunansu'". 8 Kun watsar da dokar Allah sai kuka rungumi al'adun mutane. 9 Sai yace masu, kun yi nasara wurin kau da dokokin Allah domin ku kiyaye al'adun ku na mutane. 10 Koda shike Musa ya rubuta cewa, "ka girmama Ubanka da Uwarka", kuma, "duk wanda ya zagi Ubansa ko Uwatasa, ya cancanci mutuwa nan take". 11 Amma kun ce, 'idan mutum ya ce wa iyayensa, "duk taimakon da ya cacanci ku samu daga guna ya zama kebabbe (wato, 'na mika wa Allah)"'. 12 Sabo da haka, kun ba shi izini kada ya yi wa Ubansa ko Uwatasa wani abu. 13 Kuna mayar da dokan Allah abin banza, sabili da al'adun ku da kuka mika masu. Wannan, da wasu abubuwa kamar haka kuke yi." 14 Ya kara kiran taron jama'ar yace masu, "ku kasa kunne gareni, kuma ku gane. 15 Babu wani abu daga wajen mutum da zai iya gurbatar da shi har idan ya shiga cikinsa. Amma, abinda ya fita daga cikinsa shike gurbatar da shi" 16 Bari mai kunnen ji, ya ji. 17 Da Yesu ya bar taron jama'ar, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma'anar wannan misali. 18 Sai Yesu yace, 'ashe baku da ganewa? ko baku sani cewa abin da ya shiga cikin mutum daga waje ba zai iya gurbatar da shi ba, 19 domin ba zai iya kai wa cikin zuciyarsa ba, sai dai ya shiga cikin sa ya kuma fita a matsayin bayan gari a salga". Da wannan magana, Yesu ya mayar da dukan abinci ya zama da tsabta. 20 Ya ce, abinda ke cikin mutum shike gurbatar da shi 21 Domin daga cikin mutum, kuma daga cikin zuciyarsa ne, mugun tunani, lalata, sata, kisa, 22 zina, kwadayi, mugunta, hai'inci, mugun guri, kishi, zargi, girmankai, wawanci. 23 Duk wadannan miyagun abubuwa suna fitowa ne daga cikin mutum, kuma suke gurbatar da shi." 24 Ya tashi daga nan ya tafi shiyyar Sur da Sida. Ya shiga wani gida don baya son wani ya sani cewa yana nan, amma bai iya boyuwa ba. 25 Amma nan da nan wata mace, wadda diyarta ke da mugun ruhu-wannan mace kuwa ta ji game da Yesu sai ta zo ta durkusa a gabansa. 26 Matar yar kasar Girka ce, kuma asalinta daga Fonishiya take. Ta roke shi da ya fitar da mugun ruhun nan daga diyarta. 27 Sai ya ce mata, "Bari a ciyar da 'ya'ya tukuna. Domin bai kamata a dauki abincin yaya a ba karnuka ba". 28 Sai ta amsa masa cewa, "I, Ubangiji, Karnukan ma sukan ci abincin da ke fadowa daga teburin 'ya'yan." 29 Ya ce mata, "domin kin fadi haka, kina iya ki tafi domin aljani ya fita daga diyarki." 30 Ta koma gida sai ta iske diyarta na kwance akan gado, aljanin ya fice daga jikinta. 31 Ya sake fita daga shiyar Sur, ya biyo ta Sidon, har zuwa tekun Galili a shiyar Dikafolis. 32 Sun kawo masa wani kurma, kuma bebe ne shi, suna rokansa ya dora hanuwansa a bisansa. 33 Sai ya jawo shi daga taron jama'ar, zuwa gefe, sai ya sa hanunsa a kunuwan beben bayan ya tufa yawunsa, sannan ya taba harshensa. 34 Ya dubi sama, ya ja numfashi ya ce masa, "Ifatha", wato, "bude!" 35 Nan da nan ya mayar masa da jinsa. abinda ya daure harshensa ya sake shi, sai ya fara magana da kyau. 36 Ya umarce su da kada su gaya wa wani. Amma duk da umarnin da yake basu, suna ta shaida shi ko'ina. 37 kuma suna ta mamaki cewa, "Yayi kowanne abu da kyau, har ya sa kurame suna jin magana, da kuma bebaye na magana."
Yesu ya kwaɓe Farisiyawa da kuma mallaman attaura.
"taru a wurin Yesu"
A aya ta 3 da 4, marubucin ya ba da shahararen bayani game da al'adu na wankin Farisawan domin ya nuna dalilin da ya sa Farisawan suka damu da cewa almajaren Yesu basu wanke hannayen su kafin su fara cin abinci ba. Za a iya kara juya wannan bayanin domin a samu ganewa me kyau, kamar yadda take a UDB.
"Farisawan da mallamen attauran suka gani"
Kalman nan "basu wanke hannu ba" ya yi bayanin dalilin rashin tsabtan hannayen almajaren. AT: "cewa, da hannayen da basu wanke ba" ko "cewa, basu wanke hannayen su ba"
Dattawan Yahudawan shugabane ne a wurin su, kuma su Mahukunta ne ga mutanen.
"butan dalma" ko "tukunyan karfe"
"benci" ko "gado." A wancan lokacin, Yahudawan zasu jingina a kai iɗan suna cin abinci.
"kiyaye" kalma ce na yin "biyayya." Farisawan da mallaman attaturan sun yi tambayan nan domin su tsokane ikon Yesu. AT: "Almajaren ka sun rashin biyayya ga ala'dun dattawan mu! Su wanke hannayen su ta wurin anfani da hanyan al'adun mu."
Wannan kalma ce da take nufin abinci gabadaya. AT: "abinci"
A nan "baki" kalma ce na magana. AT: "ta wurin abin da suka ce"
A nan "zuciya" ya nufin shauƙi ko tunanin mutum. Wannan hanya ce da take cewa mutane basu ba da lokacin su da gaske ga Allah ba. "amma ba su ƙaunace ni da gaske ba"
"Sujadar wofi suke mani" ko "A banza suka bauta mani"
ki yin biyayya
"rike da ƙarfi" ko "kadai kuka ajiye"
Yesu ya yi anfani da kalman nan domin ya kwaɓe masu jin sa domin sun rabu da Umurnin Allah. AT: "Ku na tunanin kun yi adalci ta wurin kau da dokokin Allah domin ku iya kiyaye al'adun ku, ko kadan, abun da kuka yi ba shi da kyau"
"Kamar yadda kuka yi fasaha ta wurin kin"
"duk wanda ya zagi"
"lalle a kashe shi"
" AT: "Lallei ne hukuma ta zartadda kisa ga wanda ya zagi ubansa ko uwarsa"
Al'adan mallaman attaura sun zartadda da cewa da zaran an yi kautan kuɗi ko wani abu wa haikali, ba za a yi anfani da su wa waɗansu abubuwa ba.
"keɓaɓɓe" kalmar Yahudawa ne da yake nufin abubuwan da mutane suka yi alkawali cewa zasu mika wa Allah. AT: "kauta ce ga Allah" ko "na Allah ne"
Kalman nan ya ba da ma'anan kalman Yahudawan nan "keɓaɓɓe." AT: "Na rigaya na mika wa Allah"
Ta wurin yin haka, Farisawan suna hana mutane tanaɗa wa iyaye, iɗan suka mika wa Allah abun da suka yarda zasu mika masa.
abin da aka share ko aka manta da shi
"wasu abubuwan da kuke yi suna nan ƙamar haka ne"
"Yesu ya kira"
Kalman nan "Kasa kunne" da kuma "gane" suna kama. Yesu yayi anfani da su domin ya nanata wa masu jin sa cewa su kassa kunne ga abin da yake faɗi.
Zai zama da taimako a faɗa masu abin da Yesu yake so su gane. AT: "ku gane abin da nake so kokarin in gaya maku"
Yesu yana magana akan abin da mutum yake ci ne. Wannan ya bambanta da "abin da yake fita daga mutum." "babu wanu abu daga wajen mutu da zai iya ci"
Wannan na nufin abin da mutum yake yi ne ko kuma yana faɗa. Wannan ya bambanta da "abin da yake wajen mutum da yake kai ciki." AT: "abin da yake fitowa da cikin mutum ne yake faɗa ko ya aikata"
Ana anfani da wannan kalman anan domin a nuna alamar dakatawa a cikin ainihin labarin. Yanzu Yesu ya yi nesa da jama'a, a wani gida tare da almajarensa.
Yesu yayi anfani da tambayan nan domin ya nuna rashin jin daɗin sa cewa basu gane ba. AT: "Bayan abubuwan da na fada, na kuma aikata, ina gani kaman kun gane."
A nan "zuciya" kalma ce da take nuna cikin mutum ko zukatar sa. Anan Yesu na nufin cewa abinci bashi da anfani ga hallin mutum. AT: " ba zai taba shiga cikin zukatar s ba"
Yesu yayi anfani da tambayan nan domin ya koya wa almajaren sa abin da yakamata da daɗewa su sani. AT: "abin da ya shisga ... salga."
A nan "shi" na nufin abin da yake shigo cikin mutum; abin da mutum yake ci kenan.
Zai iya zama da taimako a bayyana ma'anan kalman nan a fili. AT: "duƙan abinci ya zama da tsabta, na ma'anan cewa mutum zai iya cin kowane abinci ba tare da Allah ya sabtace mai ci din ba"
"Yesu ya ce"
"abinda ke gubatar da mutum, shi ke a cikin sa"
rashin ƙame kai ga sha'awa
A nan kalman "cikin" na bayyana zuciyar mutum. AT: "na fitowa daga cikin zuciyar mutum" ko "na fitowa daga cikin tunanin mutum"
A nan "zuciya" kalma ce da yake nuna cikin zukatar mutum. AT: "daga cikin mutum ne, mugun tunani ke fitowa" ko "daga zukata ne, mugun tunani ke ftiowa"
Wannan ƙarin magana ne wande yake nufin ta kamu da mugun ruhu. AT: "kamu da mugun ruhu"
"durkusa." Wannan ayukan ba da girma ne da kuma mika kai.
Kalman nan "Yanzu" na nuna alamar dakatawa a cikin ainihin labarin, wannan maganan kuma na bamu shahararen bayani game da matan.
Wannan suna ne na inda matar ta fito. An haife ta ne a Phoenician yankin Syria.
A nan Yesu yana magana akan Yahudawa kaman su 'ya'ya ne, Al'ummai kuma kaman ƙarnuka ne. AT: "Bari a fara ciyar da 'ya'yan Isra'ila tukuna. Domin ba daidai bane a dauki gurasar 'ya'ya a ba wa Al'ummai, wanda suke kaman karnuka"
AT: "Lalle ne mu fara ciyes da 'ya'ya Isra'ila tukuna"
Wannan na nufin kananan karnuka wanda ake ajiyewa a matsayin abin wasa.
Yesu na nufin cewa ba dalilin ta saya ta tambaye shi cewa ya taimaki 'yar ta. Zai yi mata. AT: "za ki iya tafiya yanzu" ko "za ki iya tafiya gida da salama"
Yesu ya saka mugun ruhun ya ar jikin diyar matar. AT: "Na saka mugun ruhun ya bar jikin 'yar ki"
"bar jihar Sur"
AT:1) "a jihar" Da Yesu yake tekun a jihar Dikafolis ko 2) "ta jihar" da Yesu ya bi ta jihar Dikafolis domin ya iso tekun.
Wannan sunan wata jiha ce da take ma'anar Gariruwa Goma. Ana samun ta ne a ..................Galili
"Sai mutane suka kawo"
"wanda ba ya ji"
Annabai da mallamai suna saka hannuwan su akan mutane domin su wanrkas da su ko kuma su saka masu albarka. A wannan hali, mutane na roƙon Yesu ya warkas da wani mutum. AT: "sun roƙe Yesu ya saka hannun sa akan mutumin domin ya warkas da shi"
"Yesu ya dauki mutumin"
Yesu yana saka yatsosinsa a kunnen mutumin.
Yesu ya tofa wa mutumin yau, ya kuma taba harshen sa.
Zai iya zama da taimako a fadi cewa Yesu ya tofa yau a yatsosin sa ne. AT: "bayan da ya tofad da yau a yatsosin sa"
Wannan yana nufin cewa ya daga idanunsa zuwa sama, wanda ake zatto inda Allah yake.
A nan marubucin na nufin kalman da kalmar Aramaic. rubuta wannan kalma da sifar rubutu na ƙabilar ka. .........
Wannan na nufin cewa yayi nishi ko ya ja dogon numfashi da za a iya ji. Mai yiwuwa yana nuna tausayi d Yesu yake nuna wa mutum.
"faɗa wa mtumin"
Wannan na nufin cewa ya fara ji. AT: "kunnuwansa sun buɗu sai ya fara ji" ko "ya fara ji"
AT: "Yesu ya dauke abin da yake tsare harshen sa daga magana" ko "Yesu ya kwance harshen sa"
Wannan na nufin shi yake ba su umurni kada su fada wa kowa game da abin da yayi. AT: "duk da umarnin da yake basu kada su fada wa kowa"
"suna ta shaida shi ko'ina" ko "a yalwace"
"suka yi mamaki sosai" ko "suka yi mamaki kwarai" ko "suka yi mamaki gaba da kima"
Wannan na nufin mutane ne. AT: "kurmaye ... bebbe mutane" ko "mutanen da baswa iya ji ... mutanen da baswa iya magana"
Wasu almajiran suna cin abinci basu wanke hannunsu ba.
Yesu ya ce farisiyawa da malaman attaura suna koyarda da dokokin mutum amma suna watsi da dokokin Allah.
Sun yi watsi da dokan Allah ta wurin ga ya wa mutane su basu su korban kudin da ya kamata ya taimaki uba da uwarsu.
Yesu ya ce babu wata abu daga waje da idan ta shiga cikin mutum tana iya kazantar da shi.
Yesu ya ce abun da ke fita da ga cikin mutum take kazantar da shi.
Yesu ya ce babu wata abu da ga waje da idan ta shiga cikin mutum tana iya kazantar da shi.
Yesu ya bayyana kowace abinci ma tsabta.
Yesu ya ce abin da ke fita daga mutum ta ke kazantar da shi.
Yesu ya ce tunanin mugunta, lalata, sata, kisan kai, zina, kwace, mugunta, yaudara, sha'awan jiki, hassada, batanci, girman kai, da kuma wauta na iya fita da ga mutum ya kazantar da shi.
Matan da diyar ta tana da aljanu ya girka ce.
Matan ta amsa ta ce ko karnukan da suke karkashin tebur suna cin burbudin yaran.
Yesu ya fitar da aljanun da suke cikin diyar matan.
Yesu ya sa yatsan shi a cikin kunuwan mutumin, ya tufa miyawu ya kuma taba harshen sa, sai ya dubi sama ya ce '''bude!''
Da Yesu ya yawaita basu doka su yi shuru, su ku ma suka yawaita gaya wa mutane.
1 A kwanakin nan, akwai wani gagaruman taron mutane, kuma basu da abincin ci. Yesu ya kirawo almajiransa yace masu, 2 "Ina tausayin taron mutanen nan domin kwana uku kenan suna nan tare da ni babu abinci. 3 Idan na salame su su koma gidajensu ba tare da sun ci abinci ba, za su galabaita a hanya domin gidajensu na da nisa." 4 Almajiransa suka amsa masa cewa, "A ina za mu iya samu gurasa a wannan jeji da zai ishi wadannan mutane haka?" 5 Ya tambaye su, "gurasa nawa kuke da su?" Sai suka ce, "Bakwai." 6 Ya umarci mutanen da su zauna. Ya dauki gurasar bakwai, bayan da ya yi godiya, ya kakarya gurasar, sa'annan ya umarci almajiransa da su raba wa mutanen. Su kuwa suka raba masu. 7 Suna kuma da kananan kifaye kadan. Bayan da ya yi godiya akan su, ya umurci almajiran su rabawa mutanen. 8 Sun ci sun koshi. Suka tattara ragowar, har sun cika kwanduna bakwai. 9 Akwai maza kimanin dubu hudu a wurin. Yesu ya sallame su. 10 Nan take, ya shiga jirgin ruwa da almajiransa zuwa shiyyar Dalmanuta. 11 Sai Farisawa suka zo suka fara gardama da shi. Suna nema ya nuna masu alama daga sama, domin su gwada shi. 12 Ya ja numfashi a ruhunsa yana cewa, "Don me wannan tsarar tana neman alama. Hakika ina gaya maku, babu wata alama da za a ba wannan tsarar." 13 Sai ya bar su ya sake shiga jirgin zuwa hayin tafkin. 14 A lokacin nan, almajiransa sun manta su dauki gurasa. Domin gurasa daya ce tak a garesu cikin jirgin ruwan. 15 Ya gargade su, "ku yi hattara da yisti na Farisawa da Yisti na Hirudus." 16 Almajiran suka fara tattaunawa a tsakaninsu, "Saboda ba mu da gurasa ne." 17 Yesu yana sane da wannan, sa'annan ya ce masu, "Don me kuke tattaunawa akan rashin gurasa? Har yanzu baku gane ba? Har yanzu ba ku da sane? Ko zuciyar ku ta duhunta ne?" 18 Kuna da idanu, ba ku gani? Kuna da kunnuwa, ba ku ji? Ba ku tuna ba? 19 Da na kakkarya gurasar a cikin mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka samu ragowa? Suka ce masa, "Goma sha biyu." 20 Kuma da na kakarya gurasa bakwai a cikin mutane dubu hudu, kwanduna nawa kuka dauka cike da ragowar? Suka ce masa, "bakwai." 21 Ya ce masu, "har yanzu baku gane ba?" 22 Sun zo Baitsaida. Mutanen wurin suka kawo masa wani makaho, sai suka roke shi ya taba shi. 23 Yesu ya rike hanun makahon, ya jagorance shi zuwa bayan kauyen. Da ya tofa yawunsa a idon mutumin, kuma ya dora hanunsa akan mutumin, sai ya tambaye shi "kana ganin wani abu kuwa?" 24 Ya daga ido sai ya ce, "ina ganin mutane na tafiya kamar itatuwa." 25 Ya sake dora masa hannu a idanuwansa, mutumin ya bude idanuwansa, sai ya fara ganin gari da kyau. 26 Yesu ya sallame shi zuwa gidansa nan take, ya ce masa, "kada ka shiga cikin garin" 27 Yesu da almajiransa sun shiga kauyukan kaisariya ta Filibi. Da suke kan hanya, sai ya tambaye su, "Shin wanene mutane ke ce da ni?" 28 Suka amsa masa suka ce, Yahaya mai Baftisma. Wasu suka ce, "Iliya". wadansu kuma, 'Daya daga cikin anabawa". 29 Ya tambaye su, "Amma me ku ke ce da ni?" Bitrus ya ce, "Kai ne Almasihu." 30 Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa game da shi. 31 Sai ya fara koya masu cewa, dole ne Dan Mutum ya sha wahala, dattawa da marubuta da manyan Firistoci zasu ki shi, a kuma kashe shi. Bayan kwana uku, zai tashi daga matattu. 32 Ya fadi wannan afili. Sai Birus ya ja shi gefe ya fara tsauta masa. 33 Amma Yesu ya juya ya dubi almajiransa sa'annan ya tsautawa Bitrus yana cewa, "Ka koma bayana Shaidan, domin kana kula da abubuwan mutane ne kawai, ba na Allah ba." 34 Sai ya kira taron jama'ar da almajiransa a wuri daya, ya ce masu, "Duk wanda yake so ya bini, dole ne ya musunci kansa, ya dauki giciyensa ya biyo ni. 35 Domin duk wanda yake so ya ceci ransa zai rasa shi, amma duk wadda ya rasa ransa domina da kuma bishara zai cece shi. 36 Me zai amfani mutum idan ya sami dukan duniya sannan ya rasa ransa. 37 Me mutum zai bayar amaimakon ransa? 38 Duk wanda ke jin kunyata ko maganata a wannan mazinaciyar tsara mai zunubi, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa a lokacin da ya dawo cikin daukakar Ubansa da Malaiku masu tsarki."
Babban taron jama'an mutane da suke tare da Yesu suna jin yunwa. Yesu ya ciyes da su da gurasa biyer da kiman kifaye kafin shi da almajarensa suka shiga jirgi domin su je wani guri.
Ana anfani da wannan kalman domin a gabatar da sabon abu a cikin labarin.
"kwana uku kenan mutanen nan suna tare da ni, amma basu samu komai sun ci ba"
AT: 1) zahiri, " za su iya rasa hankulan su nan da nan" ko 2) misalin mangana "za su iya rasa ƙarfin su."
Almajaren suna mamaki cewa Yesu yana tsamanin cewa zasu sami ishashen abinci. AT: "Wannan wurin yayi shuru harma babu wurin da zamu samu ishashen gurasa da zai kosher da mutane!"
Gurasa dunkulen kunle ce da aka shirya ta a wata sifa sai a gasa shi.
"Yesu ta ya tambaye almajarensa"
Za a iya rubuta wannan kai saye a nassin. "Yesu ya umurci jama'an, 'Zauna a kasa'"
Yi anfani da kalmar kabilar ku domin nuna yadda mutane gargajiya suke cin abinci idan babu tabur, ko ta zama ko kwanciya.
Kalman nan "su" ana nufin Yesu da almajaren sa ne.
"Yesu ya yi godiya akan ƙifin"
"Mutanen suka ci"
"Almajaren suka tara"
Wannan na nufin raguwar ƙifi da gurasar bayan da mutane suka ci. AT: "raguwar gurasa da kuma ƙifin, wanda suka cika kwanduna baƙwai"
Zai zama da taimako a bayyana lokacin da ya sallame su. AT: " Bayan da suka ci, Yesu ya sallame su"
Zai zama da taimako a bayyana yadda suka kai Dalmanuta. AT: "suka yi ta yawo a tekun Galili a yankin Dalmanuta"
Wannan sunan wuri ne a kusa da arewa - kuɗu na tekun Galili.
"Suka tambaye shi akan"
Suna neman alama da zai tabbatar masu cewa iko Yesu daga Allah ne. 1) Kalman nan "sama" kalma ce da ke nufin Allah. AT: "alama daga Allah" ko 2) kalman nan "sama" na nufin sarari. AT: "alama daga sarari"
Farisiyawan sun yi kokari su gwada Yesu domin ya nuna masu ko shi daga Allah ne. AT: "ya tabbatar masu cewa Allah ne ya turo shi"
Wannan na nufin ya yi gardama ko ya ja numfashi da zurfi da mutane zasu iya ji. Mai yiwuwa ya nuna bacin ransa kwarai da Farisiyawan domin sunki su yarda da shi AT: [7:4]
"cikin sa"
Yesu yana masu faɗa. AT: "Kada wannan zamanin su nema alama"
A lokacin da Yesu yayi magana game da "wannan zamani," ya nufin mutane da suke rayuwa a lokacin ne. A wurin Farisiyawan ma an haɗa da su. AT: "ku da mutanen zamanin nan"
AT: "ba zan nuna alama ba"
Almajaren Yesu sun tafi tare da shi. Za a iya bayyana wasu bayanin a fili. AT: "ya bar su, ya shiga jirgin tare da almajaren sa"
Wannan ya yi bayanin tekun Galilin, wanda za a iya bayyana a fili. AT: a ɗayan gefe na tekun"
Ana amfani da wannan kalma domin a nuna alamar dakatawa a cikin ainhin labarin. Anan marubucin na ba da shahararen bayani game mantuwar da almajaren su ka yi su kawo gurasar.
Kalma mara amfanin nan "kar ya fi" ana anfani da shi a nuna kalilar yawan gurasar da suke da shi. AT: "gurasa ɗaya kawai"
Waɗanan kala
A nan Yesu yana magana da almajarensa a hanyan da zasu gane ne. Yesu yana kwatanta koyaswan Farisawa da kuma Hiridus game da yistin.
Za'a iya bayanin yanayin nan a fili. AT: "Idan sararin ta yi ja da asuba" ko "Idan sarari ta yi ja alokacin da rana tana tashiwa"
"Kun san yadda ake kallon sarari kun kuma gane wace irin yanayi ce za ku samu"
"Yesu yana magana game dazamanin sa ne. AT: "Ku muguye zamani maciya amana ne, wanda kuke neman alamu daga ni ... da za a baku" [12:39]
"saidai wancan alamar da aka ba wa annabi Yunusa."
A nan "yisti" magana ce da take nufin mugun shawara da kuma koyeswar ƙarya. Za a yi bayanin maganar nan gaba [16:12].
A nan "idanu" na nufin iko. AT: "inda dattawa, manyan firistoci da malaman attaura zasu ba shi wahala"
Wannan ƙarin magana ne da ke nufin "kada wannan ya faru." AT: "A' a" ko "Allah ya kiyaye wannan"
"sai ya guje wa sha'awan jikinsa" ko "sai ya bar sha'awar jikinsa"
Wannan na nufin mutane 4,000 da suka Yesu ya ciyes. AT: "mutane 4,000"
"Ina gaya maku gaskiya." Wannan kalmomin ƙari ce ga abin da Yesu ya fada a gaba.
Dukkan maganganun nan na nufin mala'ikun ne.
Wata gari ce wanda take kusa da Galili. [6:45]
Idan ya zama dole, za'a iya faɗin wannan maganan a wani juyi. AT: "Domin Yahaya ya faɗa wa Hiridus cewa bai kama Hiridus ya ɗauki Hirudiya a matsayin matar sa ba."
AT: "Bayan da mahaifuwarta ta umurce ta"
"Mutumin ya kalle sama"
A nan marubucin ya fara faɗa yadda Hiridus ya kashe Yahaya mai Baftisma. Waɗannan abubuwan sun faru a wasu lokatai kafin abun da ya faru a ayoyin da suka wuce.
"Sai Yesu ya kuma"
Idon akwai bukata, za ka iya mika yadda abubuwan suka faru a 14:3-4, yadda take a UDB
"Suka amsa shi, suna cewa"
Almajarensa suka amsa shi suka ce ga abin da mutane na cewa game da kai. AT: "Wasu sun ce kai Yahaya mai Baftisma ne"
Suka ce kai ne Yahaya mai Baftisma.
Yesu ya umarce su kada su gaya wa kowa cewa shi Almasihu ne. AT: Yesu ya umurce su, kada ku gaya wa kowa cewa ni Almasihu ne'"
Wannan lakani ne mai muhinminci na Yesu.
Wannan na faɗi cewa Hiridus yayi haka ne, domin ya umurce wasu ne suyi mashi. AT: "Hiridus ya umurce sojojin sa su kamo Yahaya mai Baftisma, su ɗaure shi, su kuma jefa shi a kurkuku"
Filibus dan'uwan Hiridus ne. Hiridus ya ɗauki matar Filibus ta zama matar sa.
AT: "a tsakanin baƙi da suka je bukin aihuwar"
AT: "Bayan da mahaifuwarta ta umurce ta"
"Ka yi nesa da ni"
Bin Yesu a nan na nufin zama ɗaya daga ciikin almajeren sa, AT: "zama almajerina " zama ɗaya daga ciikin almajerina"
AT: " Rokon da tayi ya saka Sarki bakin ciki sosai"
AT: "ya umurce mutanen sa su yi abin da ta faɗa"
"Ga duk wanda yake so"
Wannan na nnufin rayuwa ta jiki da na ruhaniya.
"domina da kuma bishara." Yesu yana magana game da mutanen da suka rasa ransu domin sun bi shi da kuma bisharar sa. AT: "domin ya bi ni ya kuma yi wa waɗansu bishara"
AT: "Idan ma mutum ya samu dukan duniya, ba riɓa bane idan ya rasa ransa."
AT: "idan ya samu dukkan duniya ya kuma rasa ransa"
Kalman nan "dikkan duniya" wannan magana ne da yake nuna arziki. AT: ya samu dukkan abin da yake bukata"
A rasa abu ko a bar wani ya kwashe ta.
AT: "Babu wani abu da mutum zai iya bayar a maimakon rayuwar sa" ko "Ba wanda zai bayar da komai a maimakon rayuwar sa."
A kabilar ka "bayarwa" na bukatar wani ya karbi abin da aka ba shi "Me mutum zai ba wa Allah"
"kunya ta da sako ta"
Yesu yayi magana game da wannan zamanin kamar "mazinaci ne," na nufin cewa ba suwa yin gaskiya cikin dagartakar su da Allah. AT: "a wannan zamanin mutane da suka yi zina suna kuma yin zunubi wa Allah" ko "a wannan zamani da mutane ba su da gaskiya suna kuma yin zunubi ga Allah"
"a lokacin da ya dawo"
Idon Yesu ya dawo, zai samu ɗaukaka daya da Ubansa.
"tare da mala'iku masu tsarki"
Yesu ya bayyana cewa yana damuwa da taron mutane mai girma da basu da abinci.
Almajiran suna da gurasa guda bakwai.
Yesu ya bada godiya, ya raba gurasan sai ya bawa almajiran su raba.
Kwandunan abinci bakwai suka rage bayan kowa ya ci.
Mutane kusan dubu hudu ne sun ci sun koshi.
Farisiyawan sun so Yesu ya basu wata alama daga sama.
Yesu ya yi wa almajiransa gargadi su yi tsaro a kan yisti na farisiyawa.
Almajiran sun yi tunani Yesu ya na magana game da batun cewa sun manta su kawo gurasa.
Yesu ya yi masu tuni cewa lokacin da ya raba gurasa biyar , mutane dubu biyar sun ci kuma kwanduna goma sha biyu ya rage.
Yesu ya tufa miyawu a idanunsa ya kuma sa hanu a kan sa.
Yesu ya sa hannun sa a kan idanunsa.
Mutanen suna cewa Yesu ne Yahaya mai baftisma, ko kuwa daya da ga cikin annabawa.
Bulus ya ce Yesu ne Almasihu.
Yesu ya koya wa almajiransa ce wa Ɗan mutum zai sha wahala, za a ki shi, za a kashe shi, sanan kuma zai tashi bayan kwana uku.
Yesu ya ce wa Bitrus, ''Koma baya na shaidan! ba ka kula da abubuwan Allah, amma sai dai abubuwa na mutane.
Yesu ya ce ya zama tilas ma duk wanda ya na son bin sa ya yi musun kansa sanan kuma ya dauki giciye.
Yesu ya ce, ''menene riban mutum idan ya samu duniya, sanan kuma ya rasa ran sa.
Yesu ya ce a lokacin zuwansa shi ma zai ji kunyar wadanda suka ji kunyar sa da kalmominsa.
1 Sai ya ce masu, "Hakika, ina gaya maku, akwai wasun ku anan da ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko." 2 Bayan kwana shida Yesu ya dauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kadai. Sai kamaninsa ya sake a gabansu. 3 Sai tufafinsa ya zama fari fat, yadda ba mai rinin da zai iya rininsa haka a duniya. 4 Sai Iliya da Musa suka bayyana gare su, suna magana da Yesu. 5 Sai Bitrus ya amsa ya ce, malam, bari mu da muke anan mu kafa bukka uku, daya ta ka, daya ta Musa, da ta Iliya, 6 Ya rasa abin da zai fada ne, don sun tsorota kwarai.) 7 Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga gajimaren, "ta ce Wannan shine kaunataccen Dana, Ku saurare shi. 8 Nan take da suka duba, ba su ga kowa ba, sai Yesu shi kadai. 9 Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai ya kwabe su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan da Dan Mutum ya tashi daga mattatu. 10 Sai suka bar zancen a tsakaninsu, amma suka tamabayi junansu "mene ne tashin matattu" ke nufi. 11 Suka tambaye shi yaya malaman attaura suka ce Iliya zai fara zuwa?" 12 Ya ce masu, laile ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwan. Don me a ka rubuta cewa Dan Mutum, zai sha wuya iri iri a kuma ki shi? 13 Amma ina gaya muku Iliya ya riga, ya zo, amma sun yi masa abin da suke so su yi kamar yadda littatafai suka yi magana a kansa." 14 Sa'adda suka dawo wurin sauran almajiran, suka ga taron jama'a masu yawa suna ta muhawara tare da manyan malaman attaura. 15 Da ganin sa, sai dukan taron yayi mamaki kwarai da gaske, suka dungumo wurinsa a guje, suna gaishe shi. 16 Ya tambayi almajiransa, "Wacce muhawara ce kuke yi da su?" 17 Daya daga cikin taron ya amsa masa"malam, ga shi na kawo maka dana don yana da beben aljani. 18 Duk lokacin da ya tasar masa yakan buga shi har kasa, na kuma yi wa almajiranka magana su fitar sun kasa. 19 Ya amsa masu ya ce ya ku mutanen zamaninnan marasa bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku ina jimrewa? ku dai kawo mini shi. 20 Sai suka kawo masa yaron. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan ya buge yaron jikinsa na rawa. Sai yaron ya fadi yana ta birgima, bakinsa yana kumfa. 21 Yesu ya tambayi mahaifin yaron, Tun yaushe wannan abu ya same shi? Mahaifin yaron ya ce tun yana karami. 22 Ya kuwa sha jefa shi a ruwa da wuta, don ya halakar da shi. Idan zaka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimakemu. 23 Yesu ya ce masa, "In zan iya? Ai dukan abu mai yiwuwa ne, ga duk wanda ya gaskata. 24 Nan da nan mahaifin yaron ya daga murya ya ce, Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata. 25 Da Yesu ya ga taron na dungumowa a guje, sai ya tsawata wa bakin aljanin ya ce masa, "kai, beben aljani na umarce ka, ka fita daga wannan yaron kar ka sake shigar sa. 26 Sai wannan aljanin ya daga murya ya fita ya rabu da wannan yaron. Sai yaro ya zama kamar mattacce, sai sauran mutanen suka ce, "Ai, yaron ya mutu. 27 Yesu ya kama hannunsa, ya daga shi, sai yaron ya mike tsaye. 28 Da Yesu ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi a kadaice, me ya sa muka kasa fitar da shi?" 29 Ya ce masu, "Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a." 30 Sai suka ratsa cikin Galili, amma ba ya son kowa ya san inda suke. 31 Da yake koyar da almajiransa, ya ce masu lokaci na zuwa da za'a ba da Dan mutum a hannun mutane, za su kuwa kashe shi, sa'adda aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi. 32 Amma fa ba su fahimci maganar ba, suna kuma jin tsoron tambayarsa. 33 Sai suka zo kafarnahum. A lokacin da ya ke cikin gida, ya tambayi Al'majiransa, Menene ku ke magana a kansa a hanya? 34 Amma suka yi shiru. don suna gardama da junansu akan hanya, a kan wane ne mafi girma. 35 Sai ya zauna, ya kira al'majiransa goma sha biyu, yace masu duk wanda ya ke so ya zama na fari, dole ya kankantar da kansa, sa'annan ya bautawa sauran duka. 36 Sai ya dauko karamin yaro a hannunsa ya sa shi a tsakiyarsu. Ya rumgome shi a kafadarsa ya ce masu. 37 Dukan wanda ya karbi dan karamin yaron nan a cikin sunana ni ya karba, kuma dukan wanda ya karbi wani, ni ya karba, bai kuma karbeni ni kadai ba, duk da wanda ya aiko ni." 38 Sai Yahaya ya ce masa, Malam mun ga wani yana fitar da aljanu da sunanka mun yi kokari mu hana shi domin ba ya tare da mu. 39 Sai Yesu ya ce masu ku kyale shi domin babu wanda zai yi irin wannan babban aikin, sa'annan ya fadi wasu maganganu mara sa kyau a kanmu. 40 Duk wanda ba ya gaba da mu, na mu ne. 41 Duk wanda ya ba ku ruwa ku sha domin kuna na Almasihu, gaskiya nake fada maku ba za ya rasa ladansa ba. 42 Amma duk wanda ya sa kananan nan tuntube, ya fi kyau a rataya masa dutsen nika a jefa shi a cikin teku. 43 Idan har hannun ka zai sa ka yi tuntube, zai fi kyau ka yanke shi. Domin zai fi kyau ka shiga aljanna da hannu daya da ka shiga jahannama da hannu biyu. 44 (Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa). 45 Idan kafarka za ta sa ka yi tuntube, ka yanke ta ka yar. Zai fi kyau ka shiga aljanna da kafa daya da ka shiga jahannama da kafa biyu. 46 (Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa). 47 Idan idonka zai sa ka yi tuntube, ka kwakule shi ka yar, domin gwamma ka shiga mulkin Allah da ido daya, da a jefa ka cikin wuta da idanu biyu. 48 Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa. 49 Domin da wuta za a tsarkake kowa. 50 Gishiri yana da kyau, amma idan ya rasa zakinsa, ta ya ya za ka sa shi yayi zaki kuma? Ku kasance da zaki, kuma ku yi zaman lafiya da kowa.
Yesu yana magana da mutane kuma almajaren sa suna ta kokarin bin sa. Bayan kwana ta shida, Yesu ya tafi tudu tare da almajarensa guda uku, inda watarana kamanin sa zai canza ba da daɗewa ba zuwa yanda zai zama a mulkin Allah.
"Yesu ya ce wa almajarensa"
Mulkin Allah da ke zuwa na nuna Allah da kansa a matsayin sarki. AT: "Yesu ya bayyana kansa a matsayin sarki da matukar iko"
Marubucin ya yi amfani da kalmar aiki ne anan "da kansu" domin ya nanata cewa da Yesu, da Bitrus, daYakubu, da Yahaya da kansu ne suka hau tudun.
Da suka kalle shi, kamanin sa ya canza dabam kamar yadda yake da farko.
AT: "Kamanin sa ya canza" ko "kamanin sa ya zama dabam"
"a gaban su" ko "domin su gan shi a fili"
"da haske." Tufafin Yesu yayi haske sosai har yana fitar da haske.
sosai ko fiye da take
AT: "yadda ba mai rinin da zai iya rininsa haka a duniya"
Za iya zama da taimako a fadi ko wanene mutanen nan suke. AT: "annabi guda biyu da suka yi rayuwa a tun zamanin da suka wuce, Iliya da Musa suka bayyana"
"Bitru ya ce wa Yesu." Kalman nan "amsa" an yi amfani da shi domin a gabatar da Bitrus cikin labarin. Bitrus bai amsa tambaya ba.
Kalman nan "mu" ba tabatar ba ko yana nufin Bitrus, ko Yakubu, da Yahaya ba ne, ko yana nufin duk wanda suke wurin wanda ya shafi Yesu, Iliya da Musa...
dan bukka da aka gyara domin a zauna ko a yi barci
Maganan nan ya ba da shahararen bayani game da Bitrus, Yakubu da kuma Yahaya.
"sun tsorata kwarai" ko "sun ji tsoro sosai"
"ya bayana ya rufe"
A nan "murya ta fito daga" kalma ce da take nuna wani na magana. Za a iya kuma bayana a filli wa ya yi maganan. AT: "Sai wani ya yi magana daga gajimaren" ko "Sai Allah ya yi magana daga gajimaren"
Allah Uba y nuna kaunar sa wa "kaunataccen Ɗan sa" Ɗan Allah.
Wannan lakaɓi ce mai muhinminci na Yesu. Ɗan Allah.
A nan "suka" na nufin Bitrus, Yakubu da kuma Yahaya ne.
Wannan na nufin cewa ya na basu izini su faɗa wa mutane abin da suka gani bayan da ya tashi daga mattatu.
"tashi daga cikin mattatu ... a tashi daga cikin mattatu." Wannan na magana game da zama rayayye kuma. Maganan nan "mattatu" na nufin "mattatun mutane" kuma magana ce na mutuwa. AT: "tashi daga mattatu ... tashiwa daga mattartu"
A nan "suka bar zancen a tsakaninsu" karin magana ne da yake nufin basu faɗa wa kowa ba abin da suka gani. AT: "Sai basu faɗa wa kowa ba abin da suka gani"
"Kalman nan "su" na nufin Bitrus, Yakubu da kuma Yahaha.
Anabci ya faɗi cewa Iliya zai sake zuwa daga sama. Sai Mai ceto, wanda shine Ɗan Mutum, zai zo domin yayi mulki. Almajaren suka rikice cewa ta yaya Ɗan Mutum zai mutu ya kuma tashi. AT: "don me malaman attaura suka ce Iliya zai fara zuwa kafin Mai ceton ya zo? "Dubi:
Bayan da faɗa haka, Yesu ya tabbatar da cewa Iliya zai fara zuwa.
Yesu yayi amfani da tambayan nan domin ya tunashe almajarensa cewa littafin ya koyas da cewa Ɗan Mutum zai sha wahala kafin a kashe shi. AT: "amma ina son ku duba abin da aka rubuta game da Ɗan Mutum.mlittafin ya faɗa cewa zai sha wahala sosai a kuma ki shi."
AT: "mutane zasu ki shi"
Zai zama da taimako a faɗi abiin da mutane suka yi wa Iliya. AT "dattawan mu sun yi mashi mugunta, kamar yadda suke so su yi"
Yesu, Bitrus, Yakubu da Yahaya sun dawo wurin sauran almajaren wanda basu tafi tare da su zuwa tuɗun ba.
"Yesu da almajaren nan guda uku sun ga babban taro kewaye da sauran almajaren"
Mallaman attaura suna musu da sauran almajaren da basu tafi tare da Yesu ba.
Zai zama da amfani a faɗi dalilin da suka yi mamaki. AT: "suka yi mamaki cewa Yesu ya zo"
Wannan na nufin aljani ya shige yaron. "Yana da aljani" ko "aljani ya shige shi"
ɗaukar ruwa daga baki, ko figar ruwa yan kan iya saka damuwa wa mutum ta wurin numfashi ko haɗiye abu. Wannan na saka farin kumfa ya fita daga baki. Idan harshen ka tana da wata hanyar bayyana wannan, ka yi amfani da ita. "kunfa ya fito daga bakin sa"
"ya kan zama da ƙauri" ko "jikin sa ya zama da ƙauri"
Wannan na nufin almajaren basu iya fitad aljanin daga yaron ba. AT: "basu iya fitad da shi daga jikin sa ba"
Kodashike, uban yaron ne ya tambaye Yesu, Yesu ya amsa wa dukkan jama'an"
" ku zamaninnan marasa bangaskiya." Yesu ya kira taron haka, da ya fara amsa masu.
Yesu yayi amfani da tambayoyin nan domin ya nuna damuwar sa. Tambayoyin nan suna da amsa iri daya. AT: "Na zama da damuwa kwarai domin rashin bangaskiyar ka!" ko "Rashin bangaskiyar ku ya ishe ni! Na rasa har yaushe ne zan hakkura da ku."
"jimre da ku" ko "hakkuri da ku"
"Kawo mani yaron"
Wannan na nufin aljani AT: [Markus 9:17]
Wannan yanayi ne da yake saka mutum ya rasa iko ga jikin sa, kuma jikin sa na kaɗewa da ƙarfi.
"Tun yana karamin yaro." AT: "Haka yake tun yana karamin yaro"
"ji tausayi"
Yesu ya sake maimaita abin da mutumin ya faɗa masa. AT: "Ka ce mani "Idan zan iya'?" ko "Don me ka ce 'Idan zan iya'?"
"Allah kan iya yin komai ga duk mutumin da ya ba da gaskiya gare shi"
"ga mutumin" ko "ma kowa"
Wannan na nufi ba da gaskiya ga Allah. AT: "ba da gaskiya ga Allah"
Mutumin na rokon Yesu ya taiake shi ƙoran rashi bangaskiyar shi ya kuma inganta bangaskiyar sa. AT: "Ka taimake ni idan ban gaskanta ba" ko "Ka taimake ni in samu bangaskiya"
Wannan na nufin mutanen suna zuwa inda Yesu yake a guje kuma taron na karuwa sosai.
Kalman nan "bebbe" da kuma "kurma" za a iya bayyana ta. AT: "Kai aljani, kai da kake hana yaron yin magana da kuma ji"
"aljanin ya daga murya"
"ya girgiza yaron da ƙarfi"
Wannan na nufin cewa aljani ya fita daga yaron. AT: "fita daga yaron"
An kwatanta fuskar yaron da mattatcen mutum. AT: "Yaron ya yi kaman ya mutu" ko "Yaron ya yi kama da mattacen mutum"
AT: [9:26]
Wannan na nufin Yesu ya kama hannun yaron da hannuwansa. AT: "ya kama yaron a hannu"
"ya taimake shi ya mike sama"
Wannan na nufin su kadai ne.
"fitar da aljanin." Wannan na nufin fitar da aljanin daga jikin yaron. AT: "fitar da aljanin daga jikin yaron"
Kalman nan "ba ya" da kuma "sai da" kalmomi mara amfani ne. zai fi kyau ayi amfani da kalmomi masu amfani a wasu harshen. AT: "sai ta wurin addu'a ne kawai za a iya fitad da su"
Wannan ya fasara aljanin. AT: "Irin wannan aljanin"
"Yesu da almajaren sa sun bar wancan yankin"
"suka bi ta" ko "suka wuce ta"
Yesu yana koyar da almajarensa a asirce, a nesa da jama'a. AT: "da yake koyar da almajaren sa a asirce"
AT: "Wani zai ba da Ɗan Mutum"
A nan Yesu yana kansa ne a matsayin Ɗan Mutum. Wannan laƙani ne mai muhinminci na Yesu. "Ni. Ɗan Mutum,"
A nan "hannu" kalma ce na iko na mutane. AT: "zuwa ga ikon mutane" ko "saboda mutane su iya samun iko a akan sa"
AT: "Bayan da aka kashe shi, kwana ta uku kuma ta wuce, ya"
Suna jin tsoro su tambaye Yesu mai nufin Maganar sa. AT: "suna jin tsoro sun tambaye shi mai yake nufi"
"suka iso." Kalman nan "su" na nufin Yesu da almajaren sa ne.
"kuna magana da junan ku ne"
Sun yi shiru domin suna kunyan faɗa wa Yesu abin da suke magana akai. AT: "sun yi shiru domin sun ji kunya"
A nan "mafi girma" na nufin "mai girma" a sakanin almajaren ne. AT: "wanene mafi girma a sakanin su"
A nan, kalmomin nan "farko" do "karshe" ƙishiyar junan su ne. Yesu yayi magana game da zama "mafi girman" kaman na "farkon ne" sai kuma "mara muhinminci" kaman na "karshen ne." AT: " idan akwai wanda yake son Allah ya duba shi a matsayin babba a sakanin su, sai ya mayar da kansa mara muhinminci a duka"
"a dukka mutane ... a dukkan mutane"
" a cikin su." Kalman nan "su" na nufin jama'a ne.
Wannan na nufin ya ɗauko yaron ya kuma ajiye shi a cinyar sa.
"irin yaron nan"
Wannan na nufin a yi abu domin kaunar Yesu. AT: "domin yana ƙauna ta" ko "domina"
Wannan nufin Allah ne, wanda ya turo shi zuwa duniya. AT: "Allah, da ya turo ni"
"Yahaya ya ce wa Yesu"
"korar aljani." Wannan na nufin cire aljani daga jikin mutane. AT: "fitar da aljani daga jikin mutane"
A nan "suna" ya shafe ikon Yesu da karfin sa. AT: "tawurin ikon sunan ka" ko "tawurin karfin sunan ka"
Wannan na nufin ba ya tare da almajaren. AT: "ba ya cikin mu" ko "ba ya tafiya tare da mu"
"ba ya gaba da mu"
AT: "yana kokarin yin nasara da mu ke"
Yesu yana magana akan ba wa wani ruwa, misali ne da yadda mutum ɗaya zai taimaki ɗan'uwan sa. Wannan magana ne na taimakon juna ta kowace hanya.
A wasu harshe, zai zama da tamako a yi amfani da kalmomi masu amfani. AT: "hakika, zai ƙarbi"
babbar, mulmulin dutse da ake yin amfani a niƙa kwayar hatsi zuwa gari
A nan "hannu"magana ne da yake nuna yin sha'awa ne da zai saka ka yin zunubi da hannun ka" AT: "Idan kana son ka yi zunubi da wani hannun ka"
"ka zama dungu sai ka shiga rai" ko "ka zama dungu kafin ka shiga rai"
A nan magana game da mutuwa sa'annan a fara rayuwan har'abada kammar shigar rai ne. AT: "ka shiga rai na har'abada" ko "ka mutu sa'annan ka fara rayuwa na har'anada"
Rasa wani gaba na jiki domin an cire ta ko ta wurin jin ciwo. Anan na nufin rasa hannu ne. AT: "ba hannu" ko "hannun da babu"
"inda ba za a iya kashe wutan ba"
A nan kalman nan "kafa" magana ne da yake nuna yin sha'awa ne da zai saka ka yin zunubi da ƙafafun ka, kamar inda bai kamata ka je ba. AT: "Idan kana son ka yi zunubi da wani ƙafafun ka"
"ka zama gurgu sa'a nan ka shiga rayuwa" ko "ka zama gurgu kafin ka shiga rai"
"rashin iya tafiya da kyau." A nan na nufin rashin iya tafiya domin babu wani ƙafa. AT: "babu ƙafa" ko "babu wani ƙafa"
AT: "da Allah ya wurga ka cikin wuta"
A nan kalmar "ido" 1) kalma ce da yake saka mutum sha'awar zunubi na kallo. AT: "Idan kana so ka yi wani abun zunubi ta wurin kallo, ka ƙwaƙule idanun ka" ko 2) sha'awar yin zunubi domin abin da ka kalla. AT" Idan kana so ka yi zunubi domin abin da ka kalla, ka ƙwaƙule idanun ka"
Wannan na nufin kamanin jikin mutum idan ya mutu. Mutum ba ya ɗaukan jikin sa tare da shi zuwa aljanna. AT: "ka shiga zuwa mulkin Allah bayan da ka yi rayuwa a duniya da ido ɗaya da ka yi rayuwa a duniya da idanu biyu"
AT: "da Allah ya wurga ka cikin wuta"
AT: "inda tsutsotsi masu cin mutane basu mutuwa"
AT: "Allah zai tsarkake kowa da wuta" ko "Kamar yadda wuta na tsarkake haɗaya, Allah zai tarkake kowa tawurin barin su su sha wuya"
A nan "wuta" magana ce na shan wuya, kuma saka wa mutane gishiri kalma ce na tsarkakewa. Hakannan "za a tsarkake su da wuta" magana ce na tsarkakewa ta wurin shan wuya. AT: "za a mayad da shi da tsabta cikin wutar mai wahala" ko "za a sha wuya domin a tsarkake a matsayin hadaya shine tsarkakewa da gishiri"
"zakinsa"
AT: "ba za ka iya samu ɗanɗanon ta kuma ba"
"ɗanɗanon kuma ba"
Yesu yana magana akan yi wa juna abubuwa masu kyau kamar abubuwa masu kyau gishiri ne da mutane ke gada. AT: Ku yi wa kowa kirki, kamar gishiri da yake kara ɗanɗano wa abinci"
Yesu ya ce wasu da suke ke tsaye da shi a wurin ba za su mutu ba kafin su ga mulkin Allah ya na zuwa da iko.
Yesu ya săke kuma tufafinsa suka haskaka.
Iliya da Musa suke magana da Yesu.
Muryar ta ce, ''wannan Ɗa na ne. Saurare shi''.
Yesu ya umarce su kada su ga ya wa kowa abun da suka gani, sai Ɗan mutum ya tashi da ga matattu.
Yesu ya ce Iliya ya zo na farko domin ya sabunta dukkan abubuwa, da kuma Iliya ya rigaya ya zo.
Almajiran ba su iya koran aljanun da ga ɗan Uban ba.
Aljanun sun jefar da yaron cikin wuta ko kuwa cikin ruwa don su na kokarin halakar da shi.
Uban ya amsa ya ce, ''na yi ĩmanĩ! taimaki rashin ĩmanĩ na!''
Almajiran sun kasa fitar da wannan ruhu domin ba za ta iya fita ba sai da addu'a.
Yesu ya gaya ma su za a kashe shi, sa'n nan bayan kwana uku zai tashi kuma.
Almajiran suna musun wanene a cikin su babba.
Yesu ya ce wanda ya ke bawan duka shine farko
a lokacin da wani ya karbi ƙaramin yaro a cikin sunan Yesu yana kuma karban Yesu ne da kuma wanda ya aiki Yesu.
Zai fi alheri ma mutumin nan idan an daure dutse a wuyan sa a kuma jefa shi cikin teku.
Yesu ya ce ka cire idon idan zata ta saka tuntuɓe
Yesu ya ce a wuta tsutsotsin basu mutuwa, kuma ba a kashe wutan.
1 Yesu ya bar wannan wurin, ya tafi yankin Yahudiya, wajen hayin kogin Urdun. Sai jama'a suka je wurinsa. Ya ci gaba da koya masu, kamar yadda ya zama al'adarsa. 2 Sai Farisawa su ka zo wurinsa, su ka ce, "dai dai ne mutum ya saki matarsa?" Wannan tambaya sun yi ta ne domin su gwada shi. 3 Ya amsa ya ce, menene Musa ya umarce ku? 4 Suka ce, "Musa ya yarda mutum ya rubuta takardar saki ga matarsa, ya sallameta ta fita." 5 "Domin taurin zuciyarku ne ya rubuta maku wannan dokar," Yesu ya ce masu. 6 Amman tun daga farkon halitta, 'Allah ya halicci namiji da ta mata.' 7 Domin wannan dalilin ne mutum zai rabu mahaifinsa da mahaifiyarsa ya mannewa matarsa. 8 Su biyu kuwa sun zama jiki daya, ba biyu ba, 9 Saboda haka abinda Allah ya hada kada mutum ya raba." 10 Lokacin da suke cikin gida, sai almajiransa suka sake tambayarsa akan wannan magana. 11 Ya ce da su. Dukan wanda ya saki matarsa ya kuma auro wata matar yayi zina da ita kenan. 12 Haka nan duk matar da ta saki mijinta ta auri wani ta yi zina da shi kenan." 13 Mutane suka kawo masa 'ya'yansu kanana don ya taba su, sai almajiransa suka kwabe su. 14 Da Yesu ya gani, ya ji haushi, ya ce masu. Ku bar yara kanana su zo wurina, kada ku hana su domin mulkin Allah na irinsu ne. 15 Gaskiya na ke fada maku duk mutumin da bai karbi mulkin Allah kamar karamin yaro ba, babu shakka ba zai shiga mulkin Allah ba. 16 Sai ya rungume su ya sa masu albarka. 17 Lokacin da ya fara tafiya, sai wani mutum ya rugo wurinsa, ya durkusa a gabansa. Ya tambaye shi, yace ya "Malam managarci, me zan yi domin in sami rai na har abada?" 18 Amma Yesu ya ce masa. Don me ka ke kira na managarci? Babu wani managarci sai dai Allah kadai. 19 Kasan dokokin. Kada ka yi kisan kai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar zur, kada ka yi zamba, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka." 20 Sai mutumin ya ce masa Malam ai na kiyayye duk wadannan abubuwa tun ina yaro. 21 Yesu ya dube shi duban kauna ya ce masa. Abu daya ka rasa. Shi ne ka je ka sayar da duk mallakarka ka ba mabukata, za ka sami wadata a sama. Sa'annan ka zo ka bi ni. 22 Da ya ji haka sai ransa ya baci, ya tafi yana bakin ciki, don shi mai arziki ne kwarai. 23 Yesu ya dubi almajiransa ya ce. "Yana da wuya masu arziki su shiga mulkin Allah!" 24 Almajiransa suka yi mamakin maganarsa. Sai Yesu ce masu, ya ku ya'ya'na yana da wuya kamar me a shiga mulkin Allah. 25 Zai zama da sauki ga rakumi yabi ta kafar allura da mai arziki ya shiga mulkin Allah. 26 Sai suka cika da mamaki sosai, su kace wa juna, "to idan haka ne wanene zai iya tsira kenan?" 27 Yesu ya dube su ya ce masu. Ga mutane a bu ne mai wuyar gaske, amma a wurin Allah komai yiwuwa ne. 28 Bitrus ya ce masa, "to gashi mu mun bar kome, mun bika". 29 Yesu ya ce. Gaskiya na ke fada maku, babu wanda zai bar gidansa, da yan'uwansa maza da mata, da mahaifiya ko mahaifi, ko 'ya'ya ko gona, saboda da ni da kuma bishara, 30 sa'annan ya rasa samun nikinsu dari a zamanin yanzu, na gidaje, da yan'uwa mata da maza' da iyaye mata da 'ya'ya da gonaki, game da tsanani, a duniya mai zuw kuma ya sami rai madawwami. 31 Da yawa wadanda suke na farko za su koma na karshe, na karshe kuma za su zama na farko. 32 Suna tafiya Urushalima, Yesu kuwa na gabansu. Almajiransa sun yi mamaki, mutane da ke biye da su kuwa sun tsorata. Yesu kuwa ya sake kebe sha biyun nan, ya fara fada masu abin da zai same shi. 33 "Kun ga, za mu Urushalima za a bada Dan mutum ga manyan Firistoci da malan Attaura, za su kuma yi masa hukuncin kisa su kuma bada shi ga al'ummai. 34 Za su yi masa ba a, su tofa masa yau, su yi masa bulala, su kashe shi, bayan kwana uku kuwa zai tashi." 35 Yakubu da Yahaya, 'ya'yan Zabadi, suka zo wurin sa, suka ce, "Malam muna so kayi mana duk abin da mu ka roke ka" 36 Ya ce masu. "Me ku ke so in yi maku?" 37 Suka ce, "ka yardar mana, a ranar daukakarka, mu zauna daya a damanka, daya kuma a hagunka." 38 Yesu ya ce masu. "Ba ku san abinda ku ke roka ba. Kwa iya sha daga kokon da zan sha? Ko kuma za a yi maku baftismar da za a yi mani?" 39 Suka fada masa, "Zamu iya." Yesu ya ce masu, "kokon da zan sha, da shi zaku sha, baftismar da za ayi mani kuma da ita za a yi maku." 40 Amma zama a damata, ko a haguna, ba na wa ba ne da zan bayar, ai na wadanda a ka shiryawa ne." 41 Da sauran almajiran nan goma suka ji, suka fara jin haushin Yakubu da Yahaya. 42 Yesu kuma ya kira su wurinsa ya ce masu, "kun sani wadanda aka san su da mulkin al'ummai sukan nuna masu iko, hakimansu kuma sukan gasa masu iko. 43 Amma ba haka zai kasance a tsakaninku ba. Duk wanda ya ke son zama babba a cikinku, lalle ne ya zama baranku. 44 Duk wanda ya ke so ya shugabance ku lalle ne ya zama bawan kowa. 45 Saboda haka ne Dan mutum ya zo ba domin a bauta masa ba, sai dai domin shi yayi bautar, ya kuma ba da ransa fansa saboda da mutane da yawa." 46 Sa'adda suka iso Yariko, yana fita daga Yariko kenan, shi da almajiransa, da wani babban taro, sai ga wani makaho mai bara, mai suna Bartimawas dan Timawas yana zaune a gefen hanya. 47 Da ya ji Yesu Banazare ne, ya fara daga murya yana cewa, "Ya Yesu, Dan Dauda, kaji tausayina" 48 Mutane da yawa suka kwabe shi, cewa yayi shiru. Sai ya kara daga murya kwarai da gaske, yana cewa, Ya Dan Dauda ka yi mani jinkai, ka ji tausayina!" 49 Yesu ya tsaya ya ce, ku kirawo shi. Su kuwa suka kirawo makahon suka ce masa. "Albishrinka, ta so! Yana kiranka." 50 Makahon ya yar da mayafinsa, ya zaburo wurin Yesu. 51 Yesu ya tambaye shi, ya ce, "me ka ke so in yi maka?" Makahon ya ce, "Malam in sami gani." 52 Yesu ya ce masa. "Yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai." Nan take idanunsa suka bude, ya bi Yesu, suka tafi tare.
Bayan da Yesu da almajiransa sunka bar Kafarnahum, Yesu ya tunashe Farisiyawan da kuma almajiransa, abin da Allah ke bukata a cikin aire da kuma kashe aure.
Almajiran Yesu suna cikin tafi tare da shi. Suna koƙarin barin Kafarnahum. AT: "Yesu da almajiransa sun bar Kafarnahum"
"zuwa kasar da ke wajen hayin Kogin Urdun" ko "zuwa gabacin Kogin Urdun"
Kalman nan "su" na nufin taron.
"zama al'adarsa" ko "ya saba yi"
Musa ya ba wa kakaninsu doka wanda yakamata su bi. AT: "Me Musa ya umuce kakaninku game da wannan"
Wannan wata takardar da ta bayana cewa macen ba matan shi bane kuma.
A wasu harsuna, mai magana ba ya katse maganar da aka ruwaito don a faɗa ko wa yake magana. Maimakon haka su kan faɗi wanda ke magana da farko ko a karshe maganar da aka ruwaita. AT: "Yesu ya ce masu, 'domin ... wannan dokar. Amma"
Tun da, Musa ya rubuta wannan dokar ga Yahudawa da zuriyarsu saboda sun taurare zukatansu. Yahudawan a lokacin Yesu su ma sun taurare zukatansu, saboda haka Yesu haɗa da su ta wurin yin amfani da kalman"ku." AT: "domin kakaninku da ku duk kuna da taurin zuciya shi ya sa ya rubuta wannan dokar"
A nan "zukatan" na nufin cikin mutum ko runaninsa. Maganan nan "taurare zukatan" na nufin "taurin kai." AT: "taurin kanku"
Yesu ya ruwaito wannan daga abin da Allah ya faɗa cikin littafin Farawa.
"Allah ya halicci mutane"
Yesu ya cigaba da ruwaito da abin da Allah ya faɗa a cikin littafin Farawa.
"Saboda haka" ko "saboda wannan"
"haɗuwa da mata tasa"
Wannan na misalta ɗayantakan su a matsayin miji da mata. AT: "mutane biyun suna kamar mutum ɗaya" ko "yanzu kam su ba biyu bane amma tare sun zama jiki ɗaya"
Maganan nan "abin da Allah ya haɗa" na nufin masu aure. AT: "Saboda haka, dashike Allah ya haɗa miji da mace, to, kada wani ya raba"
"Sa'adda Yesu da almajiransa suke"
Almajiran Yesu suna magana da shi a ɓoye. AT: "suke su kaɗai a cikin gidan"
Kalman nan "wannan" na nufin magnan da Yesu ya yi da Farisiyawan game da kashe aure.
"kowa"
A nan "ita" na nufin macen da ya aure ta da farko.
A wannan yanayi ta yi zina ga mijinta na dă. AT: "ta yi zina ga shi" ko "ta yi zina ga mutum na farkon"
"Mutane suna kawo." Wannan abin da ya faru nan gaba a labarin ne.
Wannan na nufin cewa Yesu zai taɓa su da hannunsa ya sa masu albarka. AT: "don ya taɓa su da hannunsa ya kuma sa masu albarka. ko "ya sa hannunsa a kansu ya albarkace su"
"sauta wa mutane"
Kalman nan "su" na nufin almajiran suna kwaɓen mutane wanda suke kawo 'ya'yan wurin Yesu.
"ya yi fushi"
Waɗannan maganganu biyu suna da ma'ana kusan iri ɗaya, an maimaita ta don nanaci. A wasu harsuna ba abune mai yiwuwa ba a nanata wannan a wanta hanya. AT: "Ku tabbata kun bar 'ya'ya kanana su zo wurina"
A wasu harsuna ba abune mai yiwuwa ba a yi amfani da magana da ke bada tabbaci. AT: "bar"
Mulkin ba mutane ne, na nufin mulkin har da su ma. AT: "mulkin Allah na haɗe da mutane kamar su" ko "domin mutane kamarsu sune kaɗai ke na mulkin Allah"
"duk wanda bai karɓi ... yaro, babu shakka ba zai shiga ba
Yesu ya kwatanta yadda ta zama tilas mutane su karɓi mulkin Allah da yadda kananan yara sun karɓi ta. AT: "daidai kamar yadda yaro zai yi"
"ba zai yi na'am da Allah a matsayin sarki ba"
Kalman nan "ta" na nufin mulkin Allah.
"ya rungume yara"
A nan mutumin ya yi maganar "karɓi" sai kace "gădo." Wannan na nanata muhimmancin karɓar. Haka kuma, "găji" anan ba ta nufin cewa dole wani ya mutu tukuna. AT: "karɓi rai madawwami"
Yesu ya yi wannan tambayar don ya tunashe mutumin cewa ba wani mutum da ke nagari kamar yadda Allah yake. AT: "Ba ka fahimci abin da kake faɗi ba a sa'adda ka kirani managarci."
"managarci. Allah kaɗai shine managarci"
"kada ka yi wa wani shaidar zur" ko "kada ka yi ƙarya game da wani a kotu"
"Akwai abu ɗaya da ka rasa." A nan "rasa" na nufin bukatan yin wani abu. AT: "Abu ɗaya kana bukata ka yi" ko "Akwai abu ɗaya da ba ka yi ba"
A nan kalman nan "ita" na nufin abubuwan da ya sayar. Wannan na nufin kuɗin da ya karɓa a sa'ad da ya sayar da su. AT: "ba da kuɗin ga matalauta"
Wannan na nufn mutane matalauta. AT: "mutane matalauta"
arziki, abubuwa masu daraja
"na da abubuwa masu yawa"
"Yana da matuƙar wahala"
"Yesu ya ce wa almajiransa kuma"
"'ya'yana, yana da." Yesu yana koya masu daidai kamar yadda uba zai koyawa 'ya'yansa. AT: "Abokaina, yana da"
"yana da matuƙar wuya"
Yesu ya yi amfani da wannan don ya nanata yadda yake da matuƙar wahala mutane masu arziki su shiga mulkin Allah.
Wannan na maganar yanayi da ba zai taba yiwuwa ba. In ba za ku iya bayana wanna a harshenku ba, to, to ana iya rubuta shi a matsayin misali. AT: "zai zama da sauki rãƙumi"
"ramin allura." wannan na nufin wata karamar rami a ƙarshen alluran dinki wanda zare ka wuce ta ciki.
"Almajiran sun yi"
AT: "In haka ne, to ba wanda zai tsira!"
Ana iya bayana abin da aka fahimta. AT: "Ba shi yiwuwa mutane su cece kansu, amma Allah zai iya ceton su"
A nan kalman nan "duba" an yi amfani da ita don a jawo hankali ga kalmomin da ke zuwa nan gaba. Abu makamancin haka ana iya bayana shi a wata hanya. AT: "Mun bar kowane abu, mun bi ka"
bar kowane abu a baya"
AT: "duk wanda ya bar ... zai sami"
"ko fili" ko "ko gonar da ke nasa"
"sabili da ni" ko "don ni"
"don shelar bishara"
"wannan rayuwa" ko "wannan zamani"
Daidai kamar jeri abubuwan da ke cikin aya 29, wannan na bayana iyali gabakiɗaya. Kalman nan "uba" ba a ambata shi a aya 30 ba , amma wannan bai canza ma'anar ba.
Ana iya sake rubuta wannan domin zance da ke wannan suna "tsanani" a bayana shi cikin aikatau "tsanantawa." Saboda jimlar ta yi tsayi kuma da wuyar fahimta, maganan nan"zai sami" ana iya maimaita shi. AT: "kuma ko mutane sun tsananta masu, a duniyan nan mai zuwa, za su sami rai madawwami"
"a duniyan da ke nan gaba" ko "a nan gaba"
A nan kalmomin nan "farko" da "ƙarshe" sun sha bam-bam da juna. Yesu yana magana game da zama "muhimmanci" a matsayin "farko" da kuma zama "marasa muhimmanci" a matsayin "ƙarshe." AT: "da ke da muhimmanci za su zama marasa muhimmanci, waɗanda basu da muhimmanci za su zama masu muhimmanci"
Maganan nan "na ƙarshe" na nufin mutanen da ke na "ƙarshe." Kuma, ana iya sa kalman aikatau da an fahimce ta a wannan magana. AT: "waɗanda ke ƙarshe za su zama farko"
"Yesu da almajiransa suna tafiya kan yanyan ... Yesu kuma na can gaban almajiransa"
"waɗanda ke biye da su." Wasu mutane suna tafiya biye da Yesu da almajiransa.
"Duba" ko "kassa kunne" ko "sa hankalin ku ga abin da zan gaya maku"
Yesu na magana game da kansa. Ana iya bayana wannan a fili. AT: "Ni, Ɗan Mutum, za a"
AT: "wani zai bashe Ɗan Mutum ga" ko "za su mika Ɗan Mutum ga"
kalman nan "su" na nufin firistoci da malaman attaura.
"sa shi karƙashin mulkin Al'ummai"
"Mutane za su yi masa ba'a"
"kashe shi"
Wannan na nufin tashiwa daga mattattu. AT: "zai tashi daga mattattu"
Waɗannan kalmomi na nufin Yakub da Yahaya ne kawai.
"sa'adda an ɗaukaka ka." Maganan nan "cikin ɗaukakarka" na nufin sa'adda an ɗaukaka Yesu a kuma yi mulki bisa mulkinsa. AT: "sa'adda kana mulki a bisa mulkin ka"
"Ba ku fahimci"
A nan "koko" na nufin wahalar da Yesu za sha. An yi maganar shan wahala sau da dama kamar sha daga ƙoƙo. AT: "sha ƙoƙon wahala da zan sha" ko "sha daga cikin ƙoƙon wahala da zan sha daga ciki"
A nan "baftisma" da kuma yin baftisma na wakilcin wahala. Kamar yadda ruwa ke rufe mutum a lokacin baftisma, wahala za ta shafe Yesu. AT: "jimre baftismar wahalar da zan sha"
Amsawarsu ta wannan hanya na nufin cewa sun za su iya sha da cikin ƙoƙon ɗaya su kuma jimre baftisma ɗayan.
"ku ma za ku sha"
"Amma ba ni bane zan bar mutane su zauna a hannu dama na ko kuwa hagu na"
"Amma waɗannan wurare ga waɗanda aka shirya wa ne." Kalman nan "ta" na nufin wurare a hannun damansa da hagunsa.
AT: "Allah ya shiya ta" ko "Allah ya shirya su"
Kalman nan "wannan" na nufin Yakub da Yahaya suna roƙo su zaun a hannun dama da hagun Yesu.
"Yesu ya kira almajiransa"
Ma'ana mai yiwuwa na kamar haka 1) mutane a takaice na duban waɗanda mutane a matsayin masu mulkin al'ummai. AT: "waɗanda mutane ke duba a matsayin masu mulkin Al'ummai" ko 2) Al'ummai na duban waɗannan mutane a matsayin masu mulkinsu. AT: "waɗanda Al'ummai na tunanin cewa sune masu mulkinsu"
mulki ko iko bisa
"nuna masu iko." Wannan na nufin cewa suna nuna ko amfani da ikonsu a yadda bai kamata ba.
Wannan na kai ga aya da ke a baya game da masu mulkin Al'ummai. Anan iya bayana wannan a fili. AT: "Amma kada ku zama kamar su"
"a girmama shi"
Wannan na nufin zama mafi muhimmanci. AT: "zama mafi muhimmanci"
AT: "Gama Ɗan Mutum bai zo don ya sa mutane su bauta masa ba"
"mutane su bauta masa ba, amma ya bauta wa mutane"
"gama mutane dayawa"
"makaho mai bara mai suna Bartimawas ɗan Timawas." Bartimawas shien sunan mutumin. Timawas kuma sunan mahaifinsa ne.
Bartimawas ya ji mutane suna cewa Yesu ne. AT: "Sa'adda ya ji mutane suna cewa ai Yesu ne"
An kira Yesu Ɗan Dauda saboda shi daga zuriyar Sarki Dauda ne. AT: "Kai da kake Mai Ceto daga zuriyar Sarki Dauda"
"Mutane da ya sun sauta"
"sosai"
AT: "umurci sauran su kira shi" ko "umurce su, 'ku kira shi ya zo nan.'"
Kalman nan "su" na nufin taron.
"Ka karfafa" ko "Kada ka firgita"
"Yesu yana kiranka"
"ya zabura"
"makahon ya amsa"
"in iya gani"
An rubuta wannan magana haka don a nanata bangaskiyar mutumin. Yesu ya warkar da mutumin don ya gaskanta cewa Yesu zai iya warkar da shi. Anan iya bayana wannan a fili. AT: "Ina warkar da kai don ka bada gaskiya a gare ni"
"ya bi Yesu"
Farisiyawan sun tambayi Yesu idan a kan doka ne miji ya kashe auren sa da matan sa.
Musa ya yarda wa na miji ya bawa matan wasikar kashe aure ya kuma kore ta.
Musa ya bada wannan umarni zuwa ga Yahudawa domin zuciyarsu ta taurara.
yesu ya yi misalin halittan miji da kuma mace a farkon lokacin da ya yi magana dame da shirin Allah a kan aure tun daga fari.
Yesu ya ce mutanen nan biyu su na zama jiki daya.
Yesu ya ce duk abin da Allah ya haɗa tare, kada wani mutum ya raba.
Yesu ya yi fushi da almajiransa ya kuma ga ya masu su bar yaran su zo wurinsa.
Yesu ya ce ya zama tilas a karbi mulkin sama kaman yaro ƙarami kafin a sami shiga.
Yesu ya gaya wa mutumin Kada ka yi kisan kai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar zur, kada ka yi zamba, tilas kuma ya girmama mahaifinsa da mahaifiyarsa."
Sa'an nan Yesu ya umarce mutumin ya sayar da dukka abubuwan da yake da shi ya bi shi.
Mutumin ya yi bakin ciki ya yi tafiyarsa, domin ya na da dukiya da yawa.
Yesu ya ce yana da wahala mai kudi ya shiga mulkin sama.
Yesu ya ce ga mutane ba ya yiwuwa, amma da Allah dukka abubuwa mai yiwuwa ne.
Yesu ya ce za su sami nikinsu dari a wannan duniya, da tsanani, da kuma rai na har abada a duniya mai zuwa
Yesu da almajiransa suna tafiya a hanya da ya tafi sama zuwa Urshalima.
Yesu ya gaya wa almajiransa za a kashe shi, sa'an nan bayan kwana uku zai tashi.
Yakubu da Yahaya sun roka su zauna a hannun dama da kuma hannun hagun Yesu a daukakansa.
Yesu ya ce Yakubu da Yahaya za su jimre kofin da zai sha, da kuma baftisman da za a yi wa Yesu.
A'a, Yesu ya ce kujeran hannun dama da hannun hagun sa ba na sa bane ya ba da.
Yesu ya ce shugabannin al'ummai suna rinjayan ma su yi masu aiki.
Yesu ya ce ya zama tilas ma wandanda suna so su fi girma a cikin almajiran su zama masu bautan dukan mutane.
Bartimawas ya cigaba da kuka ya na cewa, ''Ɗan Dauda, ka yi mani rahama!''
Yesu ya ce bangaskiyar Bartimawas ya warkar da shi.
1 Da suka kusa Urushalima, kusa da Betafaji, da Betanya, wajen dutsen zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu 2 ya ce masu, "ku shiga kauyen can kusa da mu. Da zarar kun shiga za ku ga aholaki a daure, wanda ba a taba hawa ba. Ku kwance shi, ku kawo mani. 3 In wani ya ce maku, "Don me kuke haka? ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsa, zai kuma komo da shi nan da nan."' 4 Sai suka tafi, suka tadda aholakin a daure a kofar gida a bakin hanya, suka kwance shi. 5 sai wadanda suke tsaye a gun suka ce masu, "Don me kuke kwance aholakin nan? 6 Suka fada masu abinda Yesu yace, sai suka kyale su suka tafi. 7 Almajiran nan biyu suka kawo wa Yesu aholakin, suka shimfida mayafansu a kai, sai ya hau. 8 Sai mutane da yawa suka shimfida mayafansu a hanya, wadansu kuma suka baza ganyen da suka yanko daga filayen. 9 Wadanda suke gaba da shi da wadanda ke bin bayansa suka yi sowa suna cewa, "Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa cikin sunan Ubangiji. 10 Albarka ta tabbata ga mulkin nan mai zuwa na Ubanmu Dawuda! Dukaka a cikin sama!" 11 San nan Yesu ya shiga Urushalima, ya shiga Haikalin. Sai ya dudduba komai, da magariba ta yi, ya fita ya tafi Betanya tare da goma sha biyu nan. 12 Kashe gari, suka tashi daga Betanya, sai ya ji yunwa. 13 Da ya hango itacen baure mai ganye daga nesa sai ya je ya ga ko za sami 'ya'ya. Da ya iso wurinsa bai ga komai ba sai ganye, don ba lokacin 'ya'yan baure ba ne. 14 Sai ya ce wa bauren, "Kada kowa ya kara cin "ya'yanka har abada!" Almajiransa kuwa sun ji maganar. 15 Suka iso Urushalima, da shigar su, ya kori masu saye da sayarwa, ya watsar da taburan 'yan canjin kudi, da kujerun masu sayar da tantabaru. 16 Ya hana kowa ya dauki wani abu da za a i ya sayarwa a cikin haikalin. 17 Sai ya koyar da su cewa, "Ashe ba rubuce yake ba, "Za a kira gidana gidan addu'a na dukan al'ummai? Amma ku kun mayar da shi kogon yan fashi". 18 Da mayan Faristoci da marubutan attaura suka ji maganar da ya yi, sai suka nami hanyar da za su kashe shi. Amma suka ji tsoronsa domin dukkan taron na mamakin koyarwarsa. 19 Kowace yamma kuma, sukan fita gari. 20 Da safe suna wucewa, sai suka ga bauren nan ya bushe. 21 Bitrus kuwa ya tuna ya ce "Malam, dubi! Baurenan da ka la'anta ya bushe." 22 Yesu ya amsa masu ya ce, "ku gaskata da Allah." 23 Hakika, ina gaya maku, duk wanda ya ce wa dutsen nan tashi ka fada cikin tekun', bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata haka kuwa zai faru, haka kuwa Allah zai yi. 24 Saboda haka ina dai gaya maku, komai kuka yi addu'a kuka roka, ku gaskata cewa samamme ne, zai kuma zama naku. 25 Duk sa'add da kuke addu'a ku gafarta wa wadanda suka yi maku laifi, domin Ubanku shima zai gafarta maku naku laifi." 26 (Amma in baku gafartawa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma da ke sama ba zai gafarta maku ba.) 27 Da suka sake dawowa Urushalima. Yasu na tafiya cikin haikali, sai manyan firistoci, da marubuta, da dattawa suka zo wurinsa, 28 suka ce masa, "Da wanne iko kake yin wadanan abubuwa? Ko kuwa wa ya ba ka ikon yinsu?" 29 Sai Yesu ya ce masu, "Zan yi maku wata tambaya. ku ba ni amsa, ni kuwa zan gaya maku ko da wanne iko ne nake yin wadannan abubuwan. 30 Baftismar da Yahaya yayi, daga sama take ko kuwa daga mutum take? ku bani amsa". 31 Sai suka yi mahuwara da juna, suka ce, "in kuwa muka ce, 'daga sama take,' za ya ce, "To, don me ba ku gaskata shi ba? 32 In kuwa muka ce, "amma in muka ce ta mutum ce zasu jejjefemu domi suna jin tsoron jama'a, don duk kowa ya tabbata, cewa Yahaya annabi ne. 33 Sai suka amsa wa Yesu suka ce, "Ba mu sani ba" Yesu ya ce masu, "Haka ni kuma ba zan fada muku ko da wanne iko nake yin abubuwan nan ba."
"Sa'ad da Yesu da almajiransa sun yi kusa da Urushalima, sun shiga Betafaji da Betanya kusa da Dutsen Zaitun" Sun zo Betafaji da Betanya cikin yankin Urushalima.
Wannan sunan kauye ne.
"gaba da mu"
Wannan na nufin karamin jaki da zai iya ɗaukan mutum.
AT: "wanda ba wanda ya taba hawa"
Za a iya rubuta abin da kalman nan "wannan" ke nufin. AT: "Me ya sa kuke kunce, da kuma tafiya da aholakin"
"bukatar ta"
Yesu zai mayar da ita bayan ya gama amfani da ita. AT: "zai mayar da ita da wuri a lokacin da baya bukatan shi"
"Almajiran biyun sun tafi"
Wannan na nufin karamin jaki da zai iya ɗaukan mutum. Dubi yadda ka juya wannan cikin [Mark 11:2].
"Sun amsa"
"kamar yadda Yesu ya ce masu su amsa." Wannan na nufin yadda Yesu ya gaya masu amsa tambayar mutanen game da ɗaukan aholakin.
Wannan na nufin cewa sun bar su su cigaba da yin abin da suke yi. AT: "bar su su tafi da jakin"
"shimfiɗa mayafinsu a bayan ta don Yesu ya iya hawa." Ya fi sauki a tuka aholaki ko doki a sa'ad da akwai bargo ko wani abu makamancinsa a bayan. A wannan yanayi, almajiran sun shimfiɗa mayafinsu a kan ta.
"riga" ko "tufafi"
Al'ada ce a shimfiɗa mayafi a kan hanya daidai gaban mutane masu muhimmanci don a daraja su. Za a iya bayana wannan a fili. AT: "Mutane da yawa sun shimfiɗa mayafinsu
Al'ada ce a shimfiɗa ganyayen dabino a hanya gaban mutane masu muhimmancin don a martaba su. AT: "wasu suka baza ganyayen a da suka yanka daga fili, a kan hanya, don su martaba su"
"wanda suka bi bayansa"
Wannan kalma na nufin "Ka cece mu," amma mutane sun yi iihun kira da farinci a sa'adda suke so su yi wa Allah yabo. Za ku iya juya ta bisa ga yadda aka yi amfani da kalman, ko kuwa ku rubuta "Hosanna" ta wurin yin amfani da harshen ku bayana kalma. AT: "Yabi Allah"
Wannan na nufin Yesu. Ana iya bayana wannan a fili. AT: "Albarka ta tabbata a gare ka, kai wanda"
Wannan na nufin ikon Ubangiji. AT: "ikon Ubangiji"
"Albarka ta tabbata ga mulkin ubanmu Dauda." Wannan na nufin zuwan Yesu ya yi mulkin a matsayin sarki. AT: "Albarka ta tabbata ga zuwan mulkin ka" ko "Bari Allah ya albarkace ka a sa'adda kake mulkin ka mai zuwa"
"Allah ya albarkace"
A nan ana duban zuriyan Dauda da za su yi mulki kamar Dauda ne da kansa. AT: "na mafi girma cikin zuriyar ubanmu Dauda" ko "wanda mafi girma cikin zuriyar Dauda zai yi mulki"
Ma'ana mai yiwuwa 1) "Yabo ga Allah na sama" ko 2) "Bari wanda suke cikin sama su yi sowa su ce 'Hosanna'."
AT: "sama" ko "sama"
"saboda can da rana"
"shi da almajiransa goma sha biyun sun bar Urushalima sun tafi Betanya"
"sa'adda suke komowa zuwa Urushalima daga Betanya"
Wannan ya faru ne a sa'adda Yesu da almajiransa suna tafiya zuwa Urushalima.
"ko akwai wani 'ya'ya a"
Wannan na nufin cewa bai sami wani ɓaure. AT: "ya sami ganyaye ne kawai babu ɓaure a itacen"
"lokaci na shekara"
Yesu yana magana da itacen ɓaure ya kuma la'anta ta. Ya yi magana da itacen don almajiransa su ji shi.
"Ya yi magana da itacen"
Kalman nan "ta" na nufin cewa Yesu yana magana da itacen ɓauren.
"Yesu da almajiransa sun zo"
Yesu yana korin waɗannan mutane daga cikin haikali. Ana iya rubuta wannan a fili. AT: "ya fara fid da masu sayarwa da saya daga haikalin"
"mutanen da ke siya da sayarwa"
Allah ya faɗa a cikin maganarsa tawurin annabi Ishaya, cewa, haikalinsa zai zama gidan addu'a ga dukkan alummai.
Yesu ya sautawa shugabannen Yahudawan don sun yi amfani da haikalin ta hanyar da bai dace ba. AT: "An rubuta cikin nassosin cewa Allah ya ce, 'Ina so a kira gida na gidan da al'umma dukka za su yi addu'a."
Yesu ya kwatanta mutanen da 'yan fashi, haikali kuma da kogon 'yan fashi. AT: "Amma ku kamar 'yan fashi ne wanda suka maishe gida kogon 'yan fashi"
"kogon da 'yan fashi ke ɓoyewa"
"suna neman hanyar"
"da yammaci"
"Yesu da almajiransa sun bar birnin"
"suna tafiya a kan hanya"
Ka juya wannan magana yadda zai bayana da cewa itacen ya mutu. AT: "itacen ɓauren ya yi yaushi har zuwa jijiyoyin sa sai ya mutu"
"bushe"
Zai zama da taimako a bayana abin da Bitrus ya tuna. AT: "Bitrus ya tuna abin da Yesu ya faɗa wa itacen ɓauren"
"Yesu ya amsa wa almajiransa"
"Ina gaya maku gaskiya." Wannan magana na nanata abin da Yesu ya faɗa nan gaba.
"in wani ya ce"
A nan "zuciya" na nufin tunanin mutumin da kuma rayuwarsa na ciki. AT: "hakika in ya bada gaskiya a zuciyarsa" ko "in bai yi shakka ba amma ya bada gaskiya"
"Allah zai sa abin ya faru"
"Don haka ina gaya maku"
An fahimta cewa wannan zai faru saboda Allah zai tanada abin da kuka roƙa. Ana iya bayana wannan a fili. AT: "Allah zai ba ku"
Al'ada ce a yahudanci a tsaya a tsaye sa'adda ana addu'a ga Allah. AT: "Sa'adda kuke addu'a"
"kowane ƙiyayya da kuke da shi game da wani." Anan kalman nan "kowane" na nufin kowane ƙiyayya da kuke da shi game da wani do ya yi maku laifi ko wani fushi da kuke da shi game da wani.
"Yesu da almajiransa sun zo"
Wannan na nufin cewa Yesu yana tafiya a cikin haikalin; ba wai yana koƙarin shiga haikalin ba.
Kalman nan "su" na nufin firistocin, malaman attaura da kuma shugabanin jama'a.
Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) Duk waɗannan tambayoyin suna da ma'ana iri ɗaya, an kuma yi su don a yi tambaya mai karfi game da ikon Yesu, saboda haka za a iya haɗa su. AT: "Wa ya ba ka ikon aikata waɗannan abubuwa?" 2) Tambayoyi biyu ne daban dabam, na farko na tambaya game da yanayin ikon, na biyun kuma na game da wanda ya ba shi ikon.
Kalmomin nan "waɗannan abubuwa" na nufin kife tabur na masu sayarwa da cikin haikali da Yesu ya yi, da kuma maganarsa da ke gãba da abinda firistocin da malaman attaura suke tunani. AT: "abubuwa kamar waɗanda ka yi anan jiya"
"ku ba ni amsa"
"baftismar da Yahaya ke yi"
"an ba shi ikon daga sama ne ko daga wurin mutane"
A nan "sama" na nufin Allah. AT: "daga Allah"
"daga mutane"
Wannan na nufin inda baftisman Yahaya ya fito.
Kalman nan "shi" na nufin Yahaya mai baftisma.
Wannan na nufin inda baftismar Yahaya ya fito.
Shugabannin addinin suna nufin cewa za su sha wahala daga wurin mutane in sun bada wannan amsar. AT: "Amma in mun ce 'daga mutum,' wannan ba zai zama da kyau ba." ko "Amma ba ma so mu ce, daga mutum ne."
Marubucin, Markus, ya bayana dalilin da ya sa shigabannin addinin ba sa son su ce cewa baftismar Yahaya daga mutum ne. Anan iya bayana wannan a fili. "Suka ce wa junansu don suna tsoron mutanen" ko "Ba sa so su ce cewa Baftismar Yahaya daga mutum ne domin suna tsoron mutane"
Wannan na nufin baftismar Yahaya. Abin da aka fahimta anan ana iya bayana shi. AT: "Ba mu san inda baftismar Yahaya ya fito ba"
Yesu ya aika su su kawo masa dakushi wanda ba a taɓa hawa ba.
Wasu mutane suka tambayi almajiran menene suke yi, sannan suka yi magana da mutanen kamar yadda Yesu ya gaya masu, sai mutanen suka bar su sun yi hanyar su.
Mutane sun shimfida tufafinsu, da kuma rashen da suka sare a gonaki.
Mutanen sun yi ihu cewa mulkin Ubansu Dauda yana zuwa.
Yesu ya dubi kewaye da shi ya kuma fita zuwa ga Betanya.
Yesu ya gaya wa itacen ɓauren, ''babu wanda zai sake cin 'ya'yan ki''.
Yesu ya kora masu siya da siyarwa, ya kuma hana kowa shigan haikalin da kayan ciniki.
Yesu ya ce ya kamata haikali ya zama wurin addu'a ne ma dukkan al'ummai.
Yesu ya ce sun mayar da haikalin kogon barayi.
Shugabannin firistoci da malaman attauran sun yi kokari su kashe Yesu.
Itacen ɓauren da Yesu ya yi wa magana ta bushe har tushen ta.
Yesu ya ce dukka abubuwan da muka tambaya a addu'a, mu yarda cewa mun karba, za ta kuma zama namu.
Yesu ya ce mu gafarta duk abubuwan da aka yi mana, saboda mu ma mu sami gafartawa daga Uban mu.
Sun so su san da wane izini ne ya na yin abubuwan da ya ke yi.
Yesu ya tambaye su ko Baftisman Yahaya daga sama ne ko kuwa mutane.
Basu so su bada amsa ba domin Yesu zai tambaye su me ya sa basu yarda da Yahaya ba.
Basu so su bada wannan amsan ba domin suna tsoron mutanen, wadanda suka yarda cewa Yahaya annabi ne.
1 Sai Yesu ya fara koyar da su da misalai. "Wani mutum ne ya yi gonar inabi ya shingen ta, ya haka ramin matse inabin, ya kuwa gina hasumayar tsaro. Ya ba wandansu manoma jinginar gonar, sa'an nan ya tafi wata kasa mai nisa. 2 Da lokaci ya yi, sai ya aika masu wani bawansa domin ya karbi wadansu daga cikin amfanin gonar. 3 Amma manoman suka kama shi, suka yin masa duka, suka kore shi hannu banza. 4 Ya sake aikar wani bawan. Shi kuma suka raunata shi aka, suka wulakanta shi. 5 Ya sake aiken wani. Shi kam, suka kashe shi. Haka fa aka yi ta yi da wadansu da yawa, sun dodoki wadansu, suka kuma kashe wadansu. 6 Yanzu dai yana da sauran daya tak, shine kaunatacen dansa. Daga karshe ya aike shi wurinsu, yana cewa, ai za su bashi girma. 7 Amma manoman nan suka ce wa juna, "ai, wannan shine magajinsa, 'ku zo mu kashe shi, gadon ya zama namu." 8 Sai suka kamo shi, suka kashe shi, suka jefar da shi bayan shinge. 9 To, me mai gonar inabin zai yi? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba wadansu gonar. 10 Ashe, ba ku karanta wannan nassi ba? cewa, ' Dutsen da magina suka ki, shi ne ya zama mafi mahmimanci. 11 Wannan daga Ubangiji ne, kuma ya yi dai dai a idanunmu."' 12 Sai suka nemi su kama shi, don sun lura a kansu ne ya yi masalin, amma suka ji tsoron jama'a. Don haka suka kyele shi, suka tafi. 13 Suka aika masa da wadansu farisiyawa da Heridiyawa, don su sa masa tarko da kalamai cikin maganarsa. 14 Da suka zo, suka ce masa, "Malam, gaskiya kana koyar da maganar Allah sosai, ba ka nuna bambanci tsakani mutane, sai koyar da tafarkin Allah kake yi sosai. "Shin, mu biya haraji ga Kaisar, ko a a?" 15 AmmaYesu ya gane munafuncinsu, ya ce masu, "Don me kuke gwada ni? ku kawo mani dinarin in gani." 16 Suka kawowa Yesu daya. Ya ce masu, "Kamar waye da kuma rubutun wanene? suka ce masa, "Na Kaisar ne." 17 Yesu ya ce, "to, ku ba Kaisar abinda yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah. Sai suka yi mamakinsa kwarai. 18 Sai Sadukiyawa suka zo wurinsa, su dake cewa babu tashin matattu. Suka tambaya shi suka ce, 19 "Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan dan'uwan mutum ya mutu, ya bar matarsa ba da, lallai ne dan'uwan mutumin ya auri matar, ya haifa wa dan'uwansa 'ya'ya.' 20 To an yi wadansu 'yan'uwa maza guda bakwai, na farko ya yi aure, ya mutu bai bar 'ya'ya ba. 21 Na biyu kuma ya aure ta, shi ma ya mutu, ba 'ya'ya. Na ukun ma haka. 22 Haka dai duk bakwai din, ba wanda ya bar 'ya'ya. A karshe kuma ita matar ta mutu. 23 To, a tashin matattu, matar wa za ta zama a cikinsu? Don duk bakwai din nan sun aure ta". 24 Sai Yesu ya ce, "Ba saboda wannan dalili ne kuka yi kuskure ba, wato don ba ku san littafin ba, kuma ba ku san ikon Allah ba? 25 Domin in an tashin daga matattu, ba a aure, ba a auraswa, amma sun zama kamar malaiku a sama. 26 Amma game da mattattun da suka tashi, ashe, ba ku taba karantawa a littafin Musa ba, yadda Allah ya ce masa? "Ni ne Allah na Ibrahim, da Ishaku, da kuma Yakubu'? 27 Ai, shi ba Allahn mattatu bane, amma na rayyayu ne. Hakika kun yi kuskure ". 28 Sai wani malamin attuara ya zo ya ji suna muhawara da juna. Da dai ya ga Yesu yana ba su kyakkyawar amsa, sai ya tambaye shi, "Wanne Umarni ne mafi girma dukka?" 29 Yesu ya amsa yace, "mafi girma shine, 'ku saurara ya Isra'ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji daya ne. 30 Sai ka kaunaci Ubangiji Allah da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka da dukkan tunaninka, da dukkan karfinka. 31 ta biyu itace, 'ka kaunaci makwabcinka kamar kanka, Ba wata doka da ta fi wadannan." 32 Sai malamin attaura ya ce masa, "Hakika gaskiyarka malam, Allah daya ne, ba kuma wani sai shi. 33 A kaunace shi kuma da dukkan zuciya, da dukkan hankali, da dukkan karfi, a kuma kaunaci makwabci kamar kanka, ai ya fi dukkan hadayu na konawa." 34 Da Yesu ya ga ya yi masa magana da hikima, sai ya ce masa, "Ba ka nesa da mulkin Allah." Bayan wannan kuma ba wanda ya sake tambayarsa wani abu. 35 Yesu ya amsa a lokacin da yake koyarwa a Haikali, ya ce "Yaya malaman attaura suke ce wa Kristi dan Dauda ne? 36 Domin Dauda kansa, ta ikon Ruhu Mai Tsarki ya ce, "Ubangiji ya ce wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na kaskantar da makiyanka'. 37 Dauda da kansa ya kira shi 'Ubangiji; To, ta yaya ya Almasihu zai zama Dan Dauda?" Babban taron jama'ar suka saurare shi da murna. 38 A koyarwa sa Yasu ya ce, "ku yi hankali da malaman attaura, masu son yawo da manyan riguna, suna so a gaishesu a kasuwa, 39 da kuma son wuraren zama masu daraja a haikali, da wurin bukukuwa. 40 Sun kuma kwace gidajen gwauraye, da yin doguwar addu'a, don mutane su gani. Wadanan mutanen zasu sami hukunci mai tsanani." 41 Sai ya zauna a gaban akwatin baiko a Haikalin, yana duban yadda jama'a suke zuba kudi a ciki. 42 Wadansu masu arziki da yawa suna zuba kudi masu tsoka. Sai gwauruwa mara abin hanu ta saka anini biyu a ciki akwatin baikon. 43 Ya kira almajiransa, ya ce masu, "Hakika, ina gaya maku, abinda gwauruwa nan ta saka a akwatin baikon nan ya fi na sauran dukka. 44 Su duk sun bayar daga yalwa tasu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta bada duk abinda take da shi."
Yesu ya yi wannan misalin saboda firistoci da malaman attaura da kuma shugabannin jama'a.
Kalman "su" a nan na nufin firistoci da malaman attaura da kuma shugabannin jama'a wanda Yesu ke magana da su a sura da ke a baya.
Ya sa abin toshe hanya kewaye da ita. zai iya zama kananan itatuwa da aka jera, shinge ko kuwa shingen da aka yi da duwatsu.
Wannan na nufin cewa ya sassaka rami a kan dutse wanda zai zama kasan wurin matse inabin wand da za a yi amfani da shi don tare ruwan 'ya'yan itacen inabin da aka matse. AT: "ramin da aka sassaka a dutse don matse inabi. ko "ya yi wata rami don tara ruwan inabi daga wurin matse inabi"
Har yanzu gonar na mai shi ne, amma ya ba bar manoman su lura da ita. A sa'anda inabin ya nuna, suna bukatan su ba wa mai gonar wasu sai su ajiya sauran.
Wanna na nufin lokacin girbi. Anan iya bayana wannan a fili. AT: "Sa'anda lokaci ya yi na girbin inabin"
"Amma manoman sun kama bawan"
Wannan na nufin cewa ba su ba shi wani 'ya'yan itacen ba. AT: "babu wani inabi"
"mai gonar ya aika wa manoman"
Ana iya rubuta wannan a fili. AT: "sun yi masa duka a kai, sun ji masa ciwo kwarai da gaske"
Waɗannan maganganu na nufin sauran barorin. AT: "aikan wani bawan ... waɗansu barorin"
Wannan na nufin barorin da mai gonar ya aika. Maganan nan "haka suka yi" na nufin cewa an wulakanta. Ana iya rubuta wannan a fili. AT: "Sun kuma wulakanta waɗansu barori wanda ya aika"
Na nufin cewa wannan ɗan mai gonar ne. AT: "ƙaunataccen ɗansa"
Wannan na nufin magaji mai gonar, wato wanda zai gaji gonar bayan mutuwar mahaifinsa. AT: "magajin mai gonar"
'Yan hayan na duban gonar a matsayin "gãdon." AT: "wannan gonar"
"Manoman suka kamo ɗan"
Yesu ya yi tambaya sai kuma ya bada amsan don ya koya wa mutanen. Ana iya rubuta tambayan ba a matsayin tambaya ba. AT: "Saboda haka ina gaya maku abin da mai gonar zai yi."
Yesu ya gama bada misalin, yanzu kuwa yana tambayan mutanen abin da suke tunani zai faru nan gaba.
kashe
Kalman nan "waɗansu" na nufin waɗansu manoma wanda za su lura da gonar. AT: "zai bada gonar ga manoma don su lura da ita"
Ana rubuta wannan nassi tun dã a cikin maganar Allah.
Yesu ya tunashe mutanen game da wata nassi cikin Littafi Mai Tsarki. Ya yi amfani da tambaya don ya sauta masu. AT: "Hakiƙa ba ku karanta wannan Nassi ba." ko "Ya kamata ku tuna da wannan Nassi."
AT: "Ubangiji ya maishe shi mafificin dutsen gini"
"Ubangiji ne ya yi wannan"
A nan "a idanunmu" na maɗaɗɗin gani, wanda ke nufin ra'ayin mutane. AT: "mun gani, mu kuma yi tunanin cewa ta yi daidai" ko "muna tunanin cewa abun ban mamaki ne"
"Su" na nufin firisitocin da malaman attaura da shugabannin jama'a. Waɗannan kungiya za a iya dubansu a matsayin "shugabannen Yahudawa."
"so"
Sun ji tsoron abin taron za su yi masu in sun kama Yesu. Ana iya bayana wannan a fili. AT: "amma sun ji tsoron abin da taron za su yi masu in sun kama shi:
"zarge su"
"Sai shugabannen Yahudawan suka aiki"
Wannan suna ce na jami'yan siyasa da ta yi goyon bayan Hiridus Antibas.
A nan marubucin ya bayana zambar da ake yi wa Yesu a matsayin "sa masa tarko." AT: "zambace shi"
A nan "su" na nufin waɗanda aka aika daga cikin Farisiyawan da mutanen Hiridus.
Wannan na nufin cewa Yesu ba damu ba. AT: "Ba ka damu da ra'ayin mutane ba" ko "ba ka damu da samun tagomashi a wurin mutane ba"
Riya suke yi. Anan iya bayana wannan a fili. AT: "Yesu ya san cewa ba so suke su san abin da Allah yana so su yi ba"
Yesu ya sautawa shugabannen Yahudawan don zambarsa suke koƙarin yi. AT: "Na san da cewa kuna so ku sa ni in faɗi wani abu da ba daidai ba don ku zarge ni."
Wannan kuɖin ya kai hakin ma'akaci na rana ɗaya.
Farisiyawan da Hiridiyawan sun kawo dinari ɗaya"
"hoto da suna"
A nan "Kaisar" na nufin kamaninsa da rubutunsa. AT: "Suka ce, 'Kamanin Kaisar da rubutunsa'"
Yesu yana koyar da cewa mutanensa su girmama gwamnati ta wurin biyan haraji. Anan iya bayana wannan a fili ta wurin canza sunan Kaisar zuwa gwamnatin Roma. AT: "Ba wa gwamnatin Roma abubuwan da ke na gwamnatin Roma"
Ana iya sa aikatau da aka fahimta . AT: "kuma ba wa Allah"
Sun yi mamakin abin da Yesu ya faɗa. Ana iya bayana wannan a fili. AT: "Sun yi mamakinsa da kuma abin da ya faɗa"
Wannan maganan ya bayana ko su wanene Sadukiyawa. Anan iya rubuta wannan a fili. AT: "wanda sun ce babu tashiwa daga cikin matattu"
Sadukiyawan suna ruwaita abin da Musa ya rubuta a attauran. Ana iya rubuta abin da musa ya rubuta kamar haka. AT: "Musa ya rubuta mana cewa ida ɗan'uwan mutum ya mutu"
"rubuto wa Yahudawa." Sadukiyawa wata kungiya ne na Yahudawa. Anan sun yi amfani da kalman nan "mu" don suna nufin kansu ne da kuma sauran Yahudawa.
"mutumin ya auri matar ɗan'uwansa"
"haifa wa ɗan'uwansa ɗa." Za a dubi ɗan farin mutumin a matsayin ɗan ɗan'uwan da ya mutu, zuriyar ɗan kuma za a dube su a matsayin zuriyar ɗan'uwan da ya mutu. Ana iya bayana wannan a fili. AT: "haifi ɗa wanda za a dube shi a matsayin ɗan ɗan'uwan da ya mutu"
Sadukiyawan sun yi magana game da yanayin da bai faru ba domin suna son Yesu ya faɗa masu abin da yake tunani daidai ne ko ba daidai ba. AT: "A misali akwai 'yan'uwa maza bakwai"
Waɗannan lambobin na nufin kowane ɗan'uwan kuma ana iya bayana shi a hakan. AT: "ɗan'uwan na farko ... ɗan'uwan na biyu ... ɗan'uwa na biyu"
Wannan na nufin dukka 'yan'uwan. AT: "'yan'uwa bakwain"
"na farkon ya aure matan ... na biyun ya aure ta." An yi maganar auren mace kamar an "ɗauke" ta.
Zai zama da taimako a bayana abin nufin da "haka kuma". AT: "ɗan'uwa na ukun ya aure ta kamar yadda ɗan'uwansa ya yi, sai shi ma ya mutu bai bar 'ya'ya ba"
Kowane daga cikin 'yan'uwan ya aure matan sai ya mutu kafin ya sami 'ya'ya da ita. Anan iya bayana wannan a fili. AT: "A ƙarshe dukka 'yan'uwa bakwai din sun aure wannan macen ɗaya bayan ɗaya, amma ba wanda ya sami 'ya'ya da ita, kuma ɗaya bayan ɗaya suka mutu"
Sadukiyawan suna gwada Yesu tawurin yin masa wannan tambayan. Idan masu karatunka za fahimci wannan a matsayin roƙo domin bayani, to ana iya rubuta wannan a matsayin magana. AT: "To, gaya mana ko matar wa za ta zama a ranar tashin matattu, a sa'adda sun tashi kuma."
Yesu ya sauta wa Sadukiyawan domin sun yi kuskure game da shari'ar Allah. Anan iya bayana wannan cikin magana. AT: "Kun yi kuskure domin ... ikon Allah."
Wannan na nufin cewa ba su fahimci abin da aka rubuta a cikin Nassosin Tsohon Alkawari ba.
"yadda Allah ke da iko"
A nan kalman nan "su" na nufin 'yan'uwan da macen da cikin misalin.
Tashiwa daga barci wata karin magana ne da ke nufin sake rayuwa kuma bayana an mutu.
Daga cikin duk waɗanda suka mutu. Wannan na bayana dukkan mutane da suka mutu a ƙarkashin ƙasa. Tashi daga cikin su na nufin sake rayuwa kuma.
"ba sa aure, kuma ba sa auraswa"
AT: "kuma ba wanda auras da su"
Wannan na nufin inda Allah ya ke.
AT: "wanda sun tashi" ko "wanda sun tashi don su rayu kuma"
"littafin da Musa ya rubuta"
Wannan na nufin bangaren Littafin Musa da ta yi bayani game da sa'adda Allah ya yi magana da Musa daga cikin jeji dake konewa amma bata kone ba. AT: "nassin game da jeji me konewa" ko "kalmomi game da jeji mai konewa"
Wannan na nufin kananan itace, wanda bai kai bishiya ba.
"game da sa'adda Allah ya yi wa Musa magana"
Wannan na nufin cewa Ibrahim da Ishaku da kuma Yakubu sun yi wa Allah sujada. Waɗannan mutane sun mutu, amma a ruhuniya suna a raye kuma suna yi wa Allah sujada.
A nan "mattattu" na nufin mutanen da suka mutu, "rayayyu" kuma na nufin mutanen da ke raye. Haka kuma, kalman nan "Allahn" ana iya bayana shi a fili cikin magana na biyu. AT: "ba Allah mattattun mutane ba, amma Allahn rayayyun mutane"
Wannan mutane ne wanda ke raye cikin jiki da kuma ruhaniya a haɗe.
Zai zama da taimakon a bayana abin da sun yin kuskure game da shi. AT: "In kun ce cewa mattattu ba za su rayu kuma ba, hakika kun yi kuskire"
"matuƙar kuskure" ko "ba daidai ba kwarai"
"Malamin attauran ya tambaye Yesu"
"Mafi muhimmanci" na nufin umurni mafi muhimmanci. AT: "umurni mafi muhimmanci dukka ... umurni mafi muhimmanci ta ce"
"Kassa kunne ya Isra'ila! Ubangiji Allahmu, Ubangiji ɗaya ne"
A nan "zuciya" da "rai" na nufin cikin mutum. Waɗannan maganganu huɗun na nufin "gabakiɗaya" ko "da naciya."
Yesu ya yi amfani da wannan don ya kwatantan yadda ya kyautu mutane su ƙaunaci juna da ƙuana iri ɗaya kamar yadda suke ƙaunar kansu. AT: "ƙaunaci makwabcinka kamar yadda kake ƙaunar kanka"
A nan kalman nan "waɗannan" na nufin dokoki biyun da Yesu ya gayawa mutanen.
"Amsa mai kyau, Malam" ko "Magana mai kyau, Malam"
Wannan na nufin cewa akwai Allah ɗaya ne kawai. AT: "Allah ɗaya ne kawai"
Kalman nan "Allah" an fahimce shi daga magana da ke a baya. AT: "babu wani Allah"
A nan "ziciya na nufin tunanin, ji ko kuwa cikin mutumin. Waɗanna maganganu uku an yi amfani da su tare ne kuma suna nufin "gabakiɗaya" ko "da naciya."
Wannan na kwatantan yadda ya kamata mutane su ƙaunaci juna da irin ƙaunar sa suke yi wa kansu. AT: "a ƙaunaci makwabci kamar yadda kake ƙaunar kanka"
Wannan na nufin cewa wani abu ya fi wani muhimmanci. A wannan yanayi, waɗannan dokoki biyun sun fi faranta wa Allah rai fiye da haɗayu. Anan iya bayana wannan a fili. AT: "ya fi muhimmanci fiye da" ko "ya fi faranta wan Allah rai fiye da"
A nan Yesu ya yi magana game da mutumin da ya shirya ya mika kansa ga Allah a matsayin sarki kamar yin kusa da mulkin Allah, sai ka ce wani wuri ne da ana gani. AT: "Kun yi kusa ku mika kanku ga Allah a matsayin sarki"
AT: "duk sun ji tsoro"
Bayan dan lokacin kaɗan, Yesu ya shi haikali. Wannan ba ya cikin hiran da ke a baya. AT: "Bayan haka, sa'anda Yesu yana koyaswa a cikin haikali, ya ce wa mutanen"
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya don ya sa mutanen su yi zurfin tunani game da Zaburan da zai ruwaita. AT: "Dubi dalilin da ya sa malaman attaura sun ce Almasihu shi Ɗan Dauda ne."
"zuriyan Dauda"
Kalman nan "kansa" na nufin Dauda, an yi amfani da
Wannan na nufin cewa Ruhu Mai Tsarki ya iza shi. Wato, Ruhu Mai Tsarki ya shugabance Dauda cikin abin da ya făɗa. AT: "Ruhu Mai Tsarki ya iza shi"
A nan Dauda ya kira Allah "Ubangiji", ya kira Almasihu kuma "Ubangijina." Anan iya bayana wannan a fili. AT: "faɗa game da Almasihun, 'Ubangiji Allah ya ce wa Ubangijina"
Yesu ya ruwaita daga ckin Zabura. Anan Allah na magana da Almasihu ne. Zama a "hannun daman Allah" alama ce na samun martaba da iko daga Allah. AT: "zauna a wuri mai daraja tare da ni"
A wannan da aka ambata, Allah ya yi magana game da cin nasara ga abokn găba kamar ɗora ka a kansu. AT: " har sai na yi nasara da makiyin ka gabakiɗaya"
A nan kalman nan "shi" na nufin Almasihu.
AT: "to dubi yadda Almasihu zai iya zama daga zuriyar Dauda"
Sunan nan "gaisuwa" za a bayana shi da aikatau nan "gaishe." Waɗannan gaisuwar na nufin cewa mutanen sun martaba malaman attaura. AT: "a gaishe su da martaba a cikin kasuwa" ko "mutane su gaishe su da martaba a cikin kasuwa"
A nan Yesu ya bayana magudi da malaman attaura ke yi wa gwamraye da sata gidajen su a matsayin "kwace" gidajensu. AT: "sun kuma yi wa gwamraye magudi don su sata gidajensu"
Kalman nan "gwamraye" da "gidaje" na nufin mutanen da ba su samu mai taimakon ba, da kuma mallakar masu muhimmanci na mutumin. AT: "kowane abu daga wurin mutanen da basu da mai taimako"
AT: "Hakiƙa Allah za hukunta su da hukunci mai tsanani" ko "Hakiƙa Allah zai yi masu hukunci mai tsanani"
Kalman nan "tsanani" na nufin kwatanci. Anan kwatanci an yi shi ne da sauran mutane wanda aka hunkunta. AT: "za a yi masu hukunci fiye da sauran mutane"
Wannan akwatin da kowa zai iya amfani da shi akan sa baikon haikali a ciki.
"kananan tsabar kuɗi biyu." Waɗannan sune tsabar kuɗi masu daraja da akwai.
"farashin ta kaɗan ne." Farashin dinari kaɗan ne. A juya "dinari" da sunan kuɗi mai karami farashin a harshenku in kuna da wanda farashin ta kaɗan.
"Yesu ya kira"
Wannan na nuna cewa maganar da ya bi baya gaskiya ne kuma na da muhimmanci. Dubi yadda ka juya wannan cikin [Markus 3: 28]
"na dukka sauran mutanen da suka sa kuɗi a ciki"
yawan dukiya, yawan abubuwa masu daraja
"rashin" ko "kaɗan da take da shi"
"rayu da shi"
Bayan ya gina gonar innabin ya kuma bada hayarta, mai gonan ya yi tafiya.
Masu noman innabin sun duke wasu, sun kashe wasu daga cikin bayin.
Mai gonan ya tura ɗan sa kaunatacce a karshe.
Masu noman innabin sun kama shi, sun kashe shi sun kuma fitar da shi da ga cikin gonan innabin.
Mai gonan innabin zai zo ya halakar da masu noman innabin ya kuma ba da gonar innabin ga wasu.
Dutsen da maginan suka ki ya zama ginshikin.
Sun tambaye shi ko a kan doka ne a biya haraji zuwa ga Kaisar.
Yesu ya ce su ba wa Kaisar abubuwan da ke na Kaisar, kuma zuwa ga Allah, abubuwan da ke na Allah.
Sadukiyawan ba su yarda da tashi daga matattu ba.
Matan tana da mazaje bakwai.
Sun tambaye shi wani mijin ne a cikin su zai zama maigidan matan a lokacin tashin matattu.
Yesu ya ce sadukiyawan ba su san littafi mai tsarki ba da kuma ikon Allah.
Yesu ya ce a lokacin tashin matattu, maza da mata ba za su yi aure ba, amma za su zama kama mala'iku.
Yesu ya mai da su littafin Musa, inda Allah ya ce shine Allah na Ibrahim, Ishaku, da kuma na Yakubu - dukka wadanda tilas ne a lokacin suna a raye.
Yesu ya ce ka kaunace Ubangiji Allahnka da dukka zuciyarka, da rai, da hankali, da kuma karfi itace umarni ma fi imuhimmanci.
Yesu ya ce ka kaunace makwabcin ka kamar kan ka itace umarni na biyu.
Yesu ya ce ta yaya David zai iya kiran Almasihu Ubangiji bayan Almasihun ɗan Dauda ne.
Yesu ya ce mallaman attauran suna marmarin girmamawa na mutum, amma suna shigan gidajen gwamraye, da kuma yin addu'oi masu tsawo domin mutane su gani.
Yesu ya ce ta sa fiye da domin ta bada a cikin rashin ta bayan saura sun bayar a cikin yawaita.
1 da Yesu ke fita daga Haikalin, sai daya daga cikin almajirnsa ya ce masa "malam, dubi kyawawan duwatsunnan da kyawawan gine-ginnenan!" 2 Ya ce masa, ka ga wadannan kyawawan gine- ginen? babu wani dutsen da za a bar shi akan dan'uwansa, da ba za a rushe shi ba." 3 Yana zaune a kan dutsen zaitun wanda yake kusa da Haikali, sai Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, da Andarawus suka tambaye shi a asirce, suka ce. 4 Gaya mana yaushe za a yi wadannan abubuwa? mecece zata zama alamar faruwar wadanna abubuwa da zasu faru?" 5 Yesu ya ce masu, "ku kula, kada kowa ya rudeku. 6 Da yawa za su zo da sunana, suna cewa nine shi, har su bad da mutane da yawa. 7 In kuka ji labarin yake- yake, da jita-jitarsu kada ku damu, wannan zai faru, amma karshen duniya bai gabato ba. 8 Al'umma za ta tasarwa al'umma, mulki ya tasarwa mulki. Za a yi girgizar kasa awurare dabam-dabam, da kuma yunwa, amma fa dukkan wadanna abubuwan mafarin azaba ne. 9 Amma, ku zauna a fadake. Don za su kai ku gaban majalisa. za a yi maku duka a cikin majami'u. Su kuma kai ku gaban masu mulki da sarakuna, saboda sunana, domin ku ba da shaida a gare su. 10 Amma lallai sai an fara yi wa dukkan al, ummai bishara. 11 Sa'ad da suka kai ku gaban shari'a suka mika ku, kada ku damu a wannan lokacin, za a baku abin da zaku fada, Amma duk abin da aka yi muku a wannn lokacin, shi za ku fada, domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhu mai tsarki ne. 12 Dan'uwa zai bada dan'uwarsa akashe shi, uba kuwa dansa. Yara kuma zasu tayar wa iyayensu har su sa akashe su. 13 Za a ki ku saboda sunana, amma duk wanda ya jumre har karshe zai cetu. 14 Sa'adda kuka ga an kafa mummunan aikin sabo mai ban kyama a wurin da bai kamata ba (bari mai karatu ya fahimta), to, bari wadanda suke kasar Yahudiya, su gudu zuwa dutse. 15 Wanda yake tudu kuma kada ya sauko ya shiga gida garin daukar wani abu. 16 Wanda yake gona kuma kada ya koma garin daukar mayafinsa. 17 Amma, kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokacin. 18 Ku yi addu, a kada abin ya faru da damina. 19 A lokacin za ayi wata matsanaciyar wahala, wadda bata taba faruwa ba, tun farkon halittar da Allah ya yi har zuwa yau, ba kuwa za a taba yi ba har abada. 20 In da ba ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba Dan adam din zai tsira. Amma saboda zabbabunan da ya zaba, ya rage kwanakin. 21 To, in wani ya ce maku, kun ga Almasihu nan!' ko, 'kun gan shi can, kada ku gaskata. 22 Gama almasihan karya, da annabawan karya zasu bayyana kuma, zasu yi abubuwan al'ajibai masu ban mamaki. 23 Amma ku zauna a fadake, Na dai fada maku wadannan abubuwan kafin lokacin. 24 Amma, bayan matsanaciyar wahalannan, rana zata duhunta, wata kuma ba zai bada haske ba. 25 Taurari za su fado daga sararin sama, za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama. 26 Sa' annan zasu ga Dan mutum na zuwa a cikin gajimare, da iko mai girma da daukaka. 27 Zai aiko da mala'ikunsa su tattaro zabbabunsa daga kusuwoyi hudu na duniya(watau Gabas da Yamma, kudu da Arewa) har zuwa karshen sama. 28 "Ku yi koyi da itacen baure. Da zarar rassansa sun fara taushi yana kuma fitar da toho, kun san damina ta yi kusa ke nan. 29 Sa'adda kuka ga wadannan abubuwa suna faruwa, ku dai sani ya kusato, a bakin kofa ma ya ke. 30 Hakika ina gaya maku, zamanin nan ba zai shude ba sai dukan abubuwan nan sun faru. 31 Sararin sama da kasa za su shude, amma maganata ba za ta shude ba. 32 Amma wannan rana ko sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun sama, ko Dan, sai dai Uban kadai. 33 Ku kula, ku zauna a fadake, kuna addu'a don baku san ranar da lokacin zai yi ba. 34 Kamar yadda mutum mai tafiya, in ya bar gida ya wakilta bayinsa kan gidansa, kowanne da aikinsa, ya kuma umarci mai gadi ya zauna a fadake. 35 To, ku zauna a fadake don ba ku san lokacin da maigidan zai zo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko da carar zakara ne, ko da safe ne. 36 Kada ya zo ba zato, ya samu kuna barci. 37 Abinda na gaya maku, ina gaya wa kowa, shine ku zauna a fadake!"
Sa'adda sun bar haikalin, Yesu ya gaya wa almajiransa game da abin da zai faru da kyawawan haikalin da Hiridus ya gina a nan gaba.
Su "duwatsun" na nufin duwatsun da an yi su gine-ginnen da su. AT: "kyawawan gine-ginnen da kyawawan duwatsun da an yi da"
An yi amfani da wannan tambaya domin a jawo hankali ga gine- ginen. AT: "Dubi wannan gine- ginen! Babu wani ɗutsen" ko "Kun gan waɗannan gine- ginen masu girma yanzu, Amma babu wani dutsen"
Ana nufin cewa makiyan sojoji za su rushe duwatsun. AT: "babu wani dutsen da zai kasance a kan ɗan'uwansa, don makiyan sojoji za su zo su rushe waɗannan gine- ginen"
Yesu ya gaya masu abin da zai faru nan gaba, a cikin amsan tambayoyin almajran game da rushewan haikalin da abin da zai faru.
Ana iya bayyana cewa Yesu da almajiransa sun yi tafiya zuwa Dutsen Zaitun. AT: "Bayan da sun isa Dutsen Zaitun, da yake akasi da haikalin, Yesu ya zauna. Sai Bitrus"
lokacin da suke su kadai
Wannan na nufin abin da Yesu ya ce zai faru da dutsunan haikalin. AT: "waddannan abubuwan sun faru da gine- ginen haikalin ... ya yi kusan faruwa da gine- ginen haikalin"
"da dukka wadannan abubuwa"
"wa almajiransa"
A nan "ruɗu misaline na canza wa wani ra'ayi ya yarda da abin da ba gaskiya bane. AT: "ruɗe ka ... za su ruɗe mutane dayawa" (Dubi: [[rc://*/ta//man/translate/figs-metaphor]])
AT: 1)" riya iko na" ko 2) "cewa Allah ya aiko su."
"Ni ne Almasihun"
"ji game da yake-yake da labarin yake-yake." AT: 1) "ji karan yake-yake a krukusa da labarin yake-yake da nisa" ko 2) "ji game da yake-yaken da sun fara kai ruhotu game da yake-yake da sun yi kusan faruwa"
"amma ba karshen ba ne" ko "amma karshen ba za ta faru ba sai anjuma" ko "amma karshen zai zama anjuma"
Mai yiwuwa wannan na nufin karshen duniya.
Wannan ƙarin magana na nufin yin faɗa da juna. AT: "za ta yi faɗa da juna"
An fahimci kalmomin "za ta tasarwa" daga jumla da ta wuce. AT: "mulki za ta tasarwa mulk" ko "mutanen wani mulki za su yi faɗa da mutanen wani mulki"
Yesu ya yi maganar waɗannan abubuwa kamar farkon azabar haifuwa domin mafi matsanancin abubuwa za su faru bayan su. AT: "Waɗannan abubuwa zasu zama kamar azaba na farko da mace take sha a loƙacin da ta yi kusan haifuwa"
"Ku shirya da abin da mutane za su
"ɗauke ku a sa ku cikin mulkin majalisa"
AT: "mutane za su yi maku duka"
Wannan na nufin hukunta ku. AT: "Za a sharanta ku a gaban" ko Za a sharanta a kuma hukunta ku ta wurin"
"saboda ni" ko "bisa labari na"
Wannan na nufin za su shaida game da Yesu. AT: "ku kuma shaida masu game da ni" ko "za ku kuma gaya masu game da ni"
Yesu ya na magana game da abubuwan da ɗole za su faru kafin karshen ya zo. AT: "Amma ɗole sai an fara yi wa dukkan al'ummai bishara kafin karshen ya zo"
Wannan anan na nufin sa mutane a ikon hukuma. AT: "kai ku gaban hukuma"
An fahimci kalmomin "zai yi magana" a jumla da ta wuce. AT: "amma Ruhu mai Tsarki zai yi magana ta wurinku"
"Wani ɗan'uwa zai sa wani ɗan'uwa cikin ikon mutanen da za su kashe shi" ko "Yan'uwane za su sa yan'uwanensu cikin ikon mutanen da za su kashe su." Wannan zai faru da sosai wa mutane dayawa. Yesu ba ya maganan mutum ɗaya da ɗan'uwansa.
Wannan na nufin 'yan'uwa mata da maza. AT: "Mutane ... yan'uwani"
An fahimci kalmomin "zai mika wa mutuwa" daga jumla da ta wuce. Wannan na nufin cewa waɗansu ubanne za su bashe yaransu, kuma wannan bashewan zai sa a kashe yaransun. AT: "ubanne za su ba da yaransu ga mutuwa" ko "ubanne za su bashe yaransu, mika su don a kashea su"
Wannan na nufin cewa yara za su yi hamayya da iyayensu su kuma bashe su. AT: "Yara za su yi hamayya da iyayensu"
Wannan na nufin cewa hukuma za su hukunta iyayen ga mutuwa. AT: "sa hukuma su hukunta iyayen ga mutuwa" ko "hukuman za su kashe iyayen"
AT: "Kowa zai ki ku"
Yesu ya yi amfani da "sunana" don ya na nufin kansa. AT: "saboda ni" ko "saboda kun gaskanta da ni"
AT: "duk wanda ya jumre har karshe, Allah zai ceci wannan mutum" ko "Allah zai ceci duk wanda ya jumre har karshe"
A nan "jumre" na wakilcin cingaba da aminci da Allah ko a wahala. AT: "duk wanda ya sha wahala ya kuma saya har karshe da aminci ga Allah"
AT: 1) "har ga karshen rayuwarsa" ko 2) har ga karshen loƙacin wahala"
Wannan jumla na daga littafin Daniel. Ya kamata masu saurarans
Masu sauraron Yesu na iya gani cewa wannan na nufin haikali ne. AT: "na tsaye a cikin haikalin, inda bai kamata ya tsaya ba"
Wannan ba Yesu ba ne ke magana. Matiyu ya kara wannan domin ya sami hankalin masu karatun, domin su ji wannan gargadi. AT: "bari duk wanda ya na karanta wannan ya kasa kunne ga wannan gargadin"
Kan tudu da Yesu ya yi zama na nan shimfiɗaɗɗe, kuma mutane na iya sayawa akansu.
Wannan na nufin koma zuwa gidansa. AT: "kada ya koma gidansa"
"ɗaukar mayafinsa"
Wannan wata hanya ne na ce wani na da juna biyu. AT: "na da ciki"
"Ku yi addu'a wannan kwanakin" ko "Ku yi addu'a waɗannan abubuwa"
"loƙacin sanyi" ko "sanyi, loƙacin damin." Wannan na nufin loƙacin da ke da sanyi kuma babu dadi da kuma wuyan tafiya.
"ba za a sake samin mafi yawa kuma ba." Wannan ya nuna irin muni da wuya da azaban zai zama. Ba a taba yin irin azaba mai muni kamar irin wannan ba.
"ba za a sake samin mafi yawa kuma ba" ko "kuma bayan azaban, ba za a sake wani azaba kamar haka ba"
"ya rage loƙacin." Zai yi kyau a takaita wane "kwanakin" ne ana nufi. AT: "ya rage kwanakin wahala" ko "ya rage loƙacin wahala"
Kalmar "Ɗan Adam" na nufin mutane, kuma "tsira" na nufin ceton jiki. AT: "babu wanda zai tsira" ko "kowa zai mutu"
"don a taimake zabbabun"
Jumlar "waɗanda ya zaba" na nufin abu ɗaya da "zabbabun." An nanata cewa Allah ya zabi waɗannan mutanen.
"mutanen da suke ce su Almasihu ne"
"begen a ruɗe" ko "niyar ruɗe"
Jumlar "har zabbabun" na nufin cewa Almasihan karya da annabawan karya za su so su ruɗe mutane, amma ba za su san ko za su iya rudin zabbabun ba. AT: "don a ruɗe mutane, a kuma rude zabbabun, in ya yiwu"
"mutanen da Allah ya zaba"
"ku zauna da shiri"
Yesu ya gaya masu waɗannan abubuwa domin ya ƙwabe su. AT: "Na dai faɗa maku waɗannan abubuwa kafin loƙaci don in ƙwabe ku"
AT: "rana zata zama da duhu"
An yi maganar wata anan kamar na da rai kuma na iya ba wa wani abu. AT: "watan ba za ta haskaka ba" ko "watan za ta yi duhu"
Wannan ba ya nufin cewa za su fado kasa ba amma za su faɗi daga inda suke. AT: "tauraron za su fadi daga inda suke a sararin sama"
AT: "za a kuma girgiza ikon da suke a sararin sama" ko "Allah zai girgiza ikon da suke a sararin sama"
"abubuwa masu iko a cikin sammai." AT: 1) "wannan na nufin rana, wata, da tauraro ko 2) wannan na nufin ruhuhi masu iko.
"sararin sama"
"Sai mutane za su gan"
"da iko da ɗaukaka"
Kalmar "zai" na nufin Allah kuma ƙarin magana ne wa mala'ikunsa, don su ne waɗanda za su tara zabbabun. AT: "za su tara" ko "mala'ikunsa za su tara"
An yi maganar dukka duniya kamar "kusuwoyi hudu," wanda na nufin jihohi: Gabas, Yamma, kudu da Arewa" ko "dukka yankin duniya"
An ba da waɗannan matsananci biyun don a nanata cewa za a tara zabbabun daga dukka duniya. AT: "daga kowane wuri a duniya"
Jumlar "reshe" na nufin reshen itacen bauren. AT: "reshensa sun fara taushi su na kuma fitar da ganyensu"
"kore da laushi"
An yi maganar itacen baure anan kamar ya na da rai kuma na iya sa ganyensa su yi girma. AT: "ganyensa sun fara tohowa"
sashin shekara mai dumi ko loƙacin shuki
Wannan na nufin loƙacin azaba. AT: "waɗannan abubuwa da na ƙwatanta"
"Ɗan Mutumin ya yi kusa"
Wannan ƙarin magana na nufin cewa ya yi kusa kuma yi kusan zuwa, na nufin mai tafiya ya yi kusan isan kofan garin. AT: "kuma ya yi kusa"
Wannan ya nuna cewa magana da ke biye na da muhimminci. Dubi yanda kun juya wanna a cikin 3:28.
Wannan hanya ne mai kyau na magana game da mutum da ke mutuwa. AT: "ba zan mutu ba" ko "ba zai kare ba"
Jumlar "waɗannan abubuwan" na nufin lokacin azaba.
An ba da matsananci biyu domin a bayyana dukka sarari, tare da rana,wata, tauraro, da tauraro masu kewayan rana da dukkan kasan. AT: "Sararin, da kasan, da komai a cikinsu"
"daina kasance." Wannan jumla anan na nufin karshen duniya.
Yesu ya yi maganar rasa ikon magana kamar abu ne da ba zai taba mutuwa ba. AT: "maganata ba za su taba rasa ikonsa ba"
Wannan na nufin loƙacin da Ɗan Mutum zai dawo. AT: "wannan rana ko sa'a da Ɗan Mutum zai dawo" ko "ranar ko sa'a da zan dawo"
Waɗannan kalmomin sun nuna waɗansun da ba su san loƙacin da Ɗan Mutum zai dawo ba, dabam ne daga Uban, wanda ya sani. AT: "ba wanda ya san-ko mala'ikun a sama ko Ɗan-amma Uban" ko "ko mala'ikun a sama ko Ɗan sun sani; ba wanda ya sani sadai Uban"
A nan "sama" na nufin wurin da Allah yake zama.
Zai yi kyau ku fasara "Uba" da irin kalma da harshenku na amfani a kirin uba na mutuntaka. Wannan kuma ƙarin magana ne da na bayyana cewa Uban ya san loƙacin da Dan zai dawo. AT: "amma Uban ne kadai ya sani"
Za a iya bayyana da kyau abin da "loƙacin" na nufi anan. AT: "loƙacin da dukka abubuwan nan zasu faru"
"gaya wa kowanne aikin da zai yi"
"zai iya dawo da yamma"
Zakaran tsuntsu ne da na "cara" da sammako ta wurin kira mai karfi.
A nan Yesu ya yi maganar rashin zama da shiri kamar "barci." AT: "same ku da rashin shirin dawowarsa"
Yesu ya ce babu wata dutse da za ta rage a kan wata da ba za a rushe ta ba.
Almajiran sun tambayi Yesu wani lokaci wadanan abubuwa za su faru kuma menene alaman.
Yesu ya ce tilas ne almajiran su yi hankali kada kowa ya ɓace su.
Yesu ya ce farkon zafin haifuwa zai zama yake - yake, jita-jita, girgizar kasa, da kuma yunwa.
Yesu ya ce za a kai su gaban majalisa, a yi maku duka a majami'u, za ku kuma tsaya a gaban masu mulki da sarakuna saboda sunana.
Yesu ya ce tilas ne sai anyi wa mutane duka wa'azi tukuna.
Yesu ya ce dan gida daya zai nema ya kashe ɗan'uwansa.
Yesu ya ce duk wanda ya jimre har karshe zai sami ceto.
Yesu ya ce wadanda suke Yahudiya su gudu zuwa kan duwatsu a lokacin da sun ga kazantar halaka
Yesu ya ce zai rage kwanakin tsanani saboda zababbun.
Yesu ya ce Almasihu na karya da annabawan karya za su tashi su ruɗa mutane.
Rana da wata za su yi duhu, tauraro za su faɗo da ga sama, kuma ikokin sama zasu girgiza.
Za su gan Ɗan mutum yana zuwa a cikin majimaren tare da iko mai girma da daukaka.
Ɗan mutum zai tattara zababbun sa Daga karshen duniya da sama.
Yesu ya ce wannan tsara ba za ta wuce ba sai dukka wadannan abubuwa sun auku.
Yesu ya ce kalmominsa ba za su taba wucewa ba.
Yesu ya ce babu wanda ya san rana ko sa'a, sai dai Uban.
Yesu ya gaya wa almajiransa su yi tsaro da kuma addu'a.
Yesu ya gayawa almajiransa su yi tsaro da lura.
1 Idin Ketarewa da bukin gurasa mara yisti sauran kwana biyu kenan, sai shugabanin firistoci da malaman attaura suka nemi yadda zasu kama Yesu a asirce domin su kashe shi. 2 Suna cewa amma "Ba a lokacin idin ba, domin kada su haddasa hargitsi a tsakanin mutane". 3 Yesu yana Betanya a gidan Saminu kuturu, yana shirin liyafa kenan sai ga wata mace dauke da kwalbar turare mai tamanin kwarai, ta shafa masa a kansa. 4 wasu dake tare da Yesu suka husata, suna kwalbarta da cewa 5 "Ai wannan turare ne mai tsada, ina laifin a sayar a raba wa talakawa kudin? ina dalilin wannan almubazaranci? 6 Sai Yesu yace masu "Ku kyaleta, don me kuke tsauta mata, 7 ai Idan kuna da niyyar taimakon talakawa ko matalauta, suna nan tare da ku ko a yaushe amma ni bazan kasance da ku kullum ba. 8 Macen nan tayi aiki nagari domin shirya jikina ga jana'iza. 9 hakika, Ina gaya maku, duk inda za'a yi bishara a duniya baza a mance da matan nan da hidimar da ta tayi mini ba." 10 Da jin haka sai Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin manzannin ya ruga zuwa wurin baban firist domin ya bashe shi a garesu, 11 Da mayan firistoci suka ji haka suka yi murna matuka tare da alkawarin kudi ga Yahuza, shi kuwa sai ya fara neman zarafin da zai mika Yesu a gare su. 12 A ranar farko ta bukin gurasa marar yisti da kuma hadayar ragon Idin ketarewa, almajiransa suka ce masa "Ina zamu shirya liyafar domin idin ketarewa? 13 Ya aiki biyu daga cikin almajiransa da cewa "Ku shiga cikin birnin, zaku tarar da wani mutum dauke da tullun ruwa. 14 Duk gidan da ya shiga ku bishi, sai ku cewa mai gidan, malam yace "ina bukatar masauki domin hidimar idin ketarewa tare da almajiraina?"' 15 Zai kuwa nuna maku babban bene gyararre. Sai ku yi mana shiri a can." 16 Da shigar almajiran cikin birnin, sai kome ya kasance yadda ya fada, su kuwa suka yi shirye shiryen idin ketarewar. 17 Da maraice ta yi, sai ya tare da sha biyun. 18 Yayin da suke zazzaune a teburin suna cin abincin, sai Yesu ya ce "Hakika ina gaya maku wani da ke ci tare da ni a nan zai bashe ni". 19 Sai suka damu suka tambaye shi daya bayan daya suna cewa "Hakika bani bane ko?" 20 Yesu ya amsa masu da cewa "Daya daga cikin sha biyu ne, wanda ke sa hannu tare da ni yanzu cikin tasar". 21 Dan Mutum zai tafi ne yadda nassi ya umarta game da shi amma kaiton wanda zai bashe shi! "zai, fiye masa, dama ba a haife shi ba". 22 Lokacin da suke cin abincin, Yesu ya dauki gurasa ya sa albarka, ya gutsuttsura ta, sai ya basu yana cewa "Wannan jikinana ne". 23 Ya kuma dauki koko, yayi godiya, ya basu, su kuwa suka sha daga kokon. 24 Ya ce "Wannan jinina ne na alkawari da an zubar ga yawancin mutane". 25 Hakika, bazan kara sha daga wannan ruwan inabi ba sai a ranar da zan sha sabo cikin mulkin Allah." 26 Bayan sun raira wakar yabo ga Allah, sai suka tafi wurin dutsen zaitun. 27 Yesu ya ce masu dukkan ku zaku yi tuntube harma ku fadi saboda ni gama rubuce take cewa "Zan buge makiyayin, tumakin kuwa za su watse; 28 Amma bayan tashina, zai yi gaba in riga ku zuwa Galili. 29 Bitrus ya ce masa "ko dukkansu sun fadi, faufau banda ni". 30 Yesu yace masa "Hakika ina gaya maka, cikin wannan dare kafin carar zakara ta biyu zaka yi musun sani na sau uku". 31 Amma Bitrus ya sake cewa "Koda za'a kasheni tare da kai ba zan yi musun sanin ka ba". Dukkan su kuwa suka yi wannan Alkawari. 32 Suka isa wani wuri da ake kira Getsamani, sai Yesu ya ce wa almajiransa "Ku dakata anan domin zan je inyi addu'a". 33 Sai ya dauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya. Ya fara jin wahala mutuka tare da damuwa kwarai. 34 Sai ya ce masu "Raina na shan wahala harma kamar in mutu. Ku dakata a nan, ku zauna a fadake". 35 Da Yesu yayi gaba kadan, sai ya fadi kasa yayi addu'a yana cewa idan mai yiwuwa ne "A dauke masa wannan sa'a daga gare shi. 36 Ya ce "Ya Abba Uba, kome mai yuwane gare ka, ka dauke mini kokon wahalan nan, duk da haka ba nufina ba sai dai naka". 37 Da komowarsa ya same su suna barci, sai ya ce wa Bitrus, Siman barci kake? Ashe, ba za ka iya zama a fadake ko da sa'a daya ba? 38 Ku zauna a fadake, kuyi addu'a kada ku fada cikin jaraba. Lalle ruhu na da niyya amma jiki raunana ne. 39 Sai ya sake komawa, yayi addu'a, yana maimaita kalmominsa na farko. 40 Har wa yau kuma ya sake dawowa, ya same su suna barci don barci ya cika masu idanu kwarai, sun kuwa kasa ce masa kome. 41 Ya sake komowa karo na uku yace masu "har yanzu barci kuke yi kuna hutawa? Ya isa haka! Lokaci yayi, an bada Dan Mutum ga masu zunubi". 42 Ku tashi mutafi kun ga, ga mai bashe ni nan ya kusato." 43 Nan da nan, kafin ya rufe baki sai ga Yahuza, daya daga cikin sha biyun da taron jama'a rike da takkuba da kulake. Manyan firistoci da malaman attaura da shugabanni suka turo su. 44 Mai bashe shi din nan ya riga ya kulla da su cewa "Wanda zan yi wa sumba shine mutumin, ku kama shi ku tafi da shi a tsare. 45 Da isowarsa kuwa, sai ya zo wurin Yesu ya ce "Ya malam!". Sai ya sumbace shi. 46 Su kuwa suka kama shi, suka tafi da shi. 47 Amma daya daga cikin na tsaye ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya yanke masa kunne. 48 Sai Yesu ya ce "kun fito kamar masu kama yan fashi da takkuba da kulake, domin ku kama ni? 49 Lokacin da nake koyarwa a Haikali, kowace rana da ku, baku kama ni ba. Amma anyi haka ne domin a cika abinda Nassi ya fada." 50 Daga nan duk wadanda suke tare da Yesu suka yashe shi, suka tsere. 51 Wani saurayi, daga shi sai mayafi ya bi shi, suka kai masa cafka. 52 Shi kuwa ya bar masu mayafin ya gudu tsirara. 53 Daga nan suka tafi da Yesu wurin babban firist. a can suka tara dattawa duk da manyan firistoci da shugabanni da marubuta, suka taru a wurinsa. 54 Bitrus kuwa ya bi shi daga nesa har cikin gidan babban firist. Ya zauna tare da dogaran Haikalin, yana jin dumin wuta. 55 Sai, manyan firistoci da duk 'yan majalisa Yahudawa suka nemi shaidar da za a tabbatar a kan Yesu, don su samu su kashe shi. Amma basu samu ba. 56 Da yawa kuma suka yi masa shaidar Zur (Karya), amma bakin su bai zama daya ba. 57 Sai wadansu kuma suka taso suka yi masa shaidar zur (karya) suka ce. 58 "Mun ji ya ce, wai zai rushe haikalin nan da mutane suka gina, ya sake gina wani cikin kwana uku, ba kuwa ginin mutum ba". 59 Duk da haka, sai shaidar tasu bata zo daya ba. 60 Sai babban firist ya mike a tsakanin su, ya tambayi Yesu yace "Ba ka da wata amsa game da shaidar da mutanen nan suke yi a kanka? 61 Amma yayi shiru abinsa, bai ce kome ba. Sai babban firist din ya sake tambayarsa "To, ashe kai ne Allmasihu Dan Madaukaki? 62 Yesu ya ce "Nine. Za ku kuwa ga Dan Mutum zaune dama ga mai iko, yana kuma zuwa cikin gajimare". 63 Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa yace "Wacce shaida kuma zamu nema? 64 Kun dai ji sabon da yayi! Me kuka gani? Duk suka yanke masa hukunci akan ya cancanci kisa. 65 Wadansu ma suka fara tottofa masa yau, suka daure masa idanu, suka bubbuge shi suna cewa "Yi annabci" Dogaran kuma suka yi ta marinsa. 66 Bitrus kuwa na kasa a filin gida, sai wata baranyar babban firist ta zo. 67 Da ta ga Bitrus na jin dumi, ta yi masa kallon gaske ta ce "Kaima ai tare kake da banazaren nan Yesu". 68 Amma ya musa ya ce "Ni ban ma san abinda kike fada ba balle in fahimta". Sai ya fito zaure. Sai zakara yayi cara. 69 Sai baranyar ta ganshi, ta sake ce wa wadanda ke tsaitsaye a wurin, "Wannan ma daya daga cikinsu ne". 70 Amma ya sake musawa, jim kadan sai na tsaitsayen suka ce wa Bitrus "Lalle kai ma dayansu ne don ba Galile ne kai". 71 Sai ya fara la'anta kansa yana ta rantsuwa yana ce wa "Ban ma san mutumin nan da kuke fada ba". 72 Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu, Bitrus kuwa ya tuna da maganar Yesu a gare shi cewa "Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sani na sau uku". Da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.
Kwana biyu kafin idin ketarewa, shugabanin firistoci da malaman attaura suna yin shiri a boye don su kashe Yesu.
ba tare da mutuane su gane ba
Kalmar "su" na nufin shugabanin firistoci da malaman attaura.
Wannan na nufin ba su kama Yesu a loƙacin idin ba. AT: "Kada mu yi a loƙacin idin"
Dama wannan mutumin na da kuturta amma yanzu babu. Wannan mutum dabam ne da Saminu Bitrus da kuma Saminu Zilot.
A al'adan Yesu, loƙacin da mutane sun taru don cin abinci, su na kwanciye da gefensu, jinginar da kansu akan pillo a gefen tuburin.
Wannan ƙwalba ne da an yi shi daga alabaster. Alabaster wata kore-farin dutse mai sada. AT: "kyaukyauwar farin ƙwalba"
"da ya ƙunsa turare mai tsada da ake kira nard." Nard na da tsada, kuma mai ne da kamshi da ana amfani don yin turare.
"a kan Yesu"
Sun yi wannan tambaya domin su nuna cewa sun ki yadda matan ta na zuba turaren akan Yesu. AT: "Abin tsoro ne cewa ta na batar da turaren!"
Markus na so ya nuna wa masu karatunsa cewa waɗanda suke a loƙacin sun damu da ƙudi. AT: "Da mun sayad da wannan turaren" ko "Da ta sayad da wannan turaren"
"dinari ɗari uku." Dinari sulen azurfa ne na Roma.
Jumlar "talakawa"na nufin mutane masu talauci. Wannan na nufin ba da ƙudin wa talakawa daga sayad da turare. AT: "a ba wa talakawa ƙudin"
Yesu ya tsauta wa mutanen don maganganu akan abin da matannan ta yi. AT: "Kar ku dame ta!"
Wannan na nufin mutane masu talauci. AT: "talakawa"
Wannan na nuna cewa magana da na biye gaskiya ne kuma ya na da muhimminci. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 3:28.
AT: " duk inda masubi na sun yi bishara"
"za a kuma yi shilar hidimar da matan nan ta tayi"
Yahuza bai rigaya bashe Yesu ba, ya je ya yi shiri da su. AT: "don ya shirya da su cewa zai ba su Yesu"
"kowa masu Yesu don su iya kama shi"
Zai yi kyau ku bayyana abin da mayan firistoci sun ji. AT: "Da mayan firistoci suka ji abin da ya ke da niyar yin masu"
A ranar farko ta bukin gurasa marar yisti, al'ada ne a yi hadayar rago. AT: "da loƙacin da al'adan su ya kai na yin hadayar ragon idin ketarewa"
"ɗauke da babban tullu cike da ruwa"
AT: "Malamman mu su na so su san inda masuakin yake, inda zai iya cin abincin idin ketarewa tare da almajiransa."
dakin baki
A nan "ketarewa" na nufin abincin idin ketarewa. AT: "ci abincin idin ketarewa"
Za su shirya abinci wa Yesu da almajiransa don su ci. AT: "Shirya mana abincin a can"
"Almajirai biyun suka tafi"
"kamar yadda Yesu ya faɗa"
Zai yi kyau ku faɗa inda sun zo. AT: "ya zo gidan da sha biyun"
A al'adan Yesu, loƙacin da mutane sun taru don cin abinci, su na kwanciye da gefensu, su kuma jinginar da kansu akan pillo a gefen tuburin.
Wannan na nufin cewa almajiran sun tambaye juna "ɗaya bayan ɗaya."
AT: 1) wannan tambaya ne da almajiran sun zata amsan ya zama babu ko 2) wannan tambaya ne da bai bukaci amsa ba. AT: "Hakika ba ni ne zan bashe ka ba!"
"Shi ne ɗaya daga cikin sha biyun, wanda yanzu"
A al'adan Yesu, mutane na yawan cin gurasa, tsomawa a cikin tasar miya ko mai da an hada da ganyen itace.
A nan Yesu ya na nufin annabcin nassi game da mutuwarsa. Idan ku na da wata hanya mai kyau na magana akan mutuwa a harshenku, ku yi amfani da shi. AT: "Gama Ɗan Mutum zai mutu kamar yadda nassi ya ce"
AT: "wanda ya bashe da Ɗan Mutum"
Wannan shimfiɗaɗɗer gurasa marar yisti. wanda an ci a abincin ketarewa.
Wannan na nufin cewa ya gutsuttsura gurasa wa mutanen su ci. AT: "ya gutsuttsura ta"
"Karba wannan gurasa. Jikina ne." Ko da shike yawanci sun fahimci wannan da cewa gurasa alama ne na jikin Yesu kuma ba ainahin jiki ba ne, zai yi kyau a fasara wannan magana a zahiri.
A nan "koko" ƙarin magana ne na ruwan inabi. AT: "Ya ɗauki kokon ruwan inabi"
Alkawarin na gafarta zunubai ne. Ana iya sa wannan a bayyane. AT: "Wannan jinina ne da ya tabbatar da alkawarin, jinin da an zub da domin yawancin su iya samin gafarar zunubai"
"Wannan ruwan inabin jinina ne." Ko da shike yawanci sun fahimci wannan da cewa ruwan inabin alama ne na jinin Yesu kuma ba ainahin jini ba ne, zai yi kyau a fasara wannan magana a zahiri.
"ruwan inabi." Wannan kwatanci ne na ce ruwan inabi.
AT: ) "kuma" ko 2) "a wata sabuwar hanya"
Wakar yabo wata irin waka ce. Al'ada ne masu su yi wakar zabura ta Tsohon Alkawari.
"Yesu ya ce wa almajiransa"
Wannan ƙarin magana ne da na nufin bari. AT: "bar ni"
"Ƙashe." "Zan" na nufin Allah.
AT: "Zan watsar da tumakin"
Wannan ƙarin magana na nufin cewa Allah zai sa Yesu ya tashi kuma bayan ya mutu. AT: "Allah ya ta da ni daga mattatu" ko "Allah ya sa ni rayuwa kuma"
"Zan tafi kafinku"
Ana iya bayyana "Ba zan" kamar "Ba zan faɗi ba." Jumlar "zai faɗi ba"na ɗauke da ma'ana mai yaƙini. AT: "ko da dukkansu sun bar ku, Zan zauna da ku"
Zakara tsutsu ne da na kirari
sau biyu
"za ka ce ba ka san ni ba"
"ko da ɗole ne in mutu"
Wannan na nufin cewa dukka almajiran su faɗa abin da Bitrus ya ce.
Kalmar "sun" na nufin Yesu da almajiransa.
cike da baƙin ciki
Kalmar "kwarai" na nufin Yesu ya damu sosai a rainsa. AT: "damuwa mai tsanani"
Yesu ya yi maganar kansa kamar "rain sa." AT: "Zan"
Yesu ya na zuguiguitawa domin ya na jin wuya da baƙin ciki har ya na ji kamar zai mutu, ko da shike ya san cewa ba zai mutu ba sai rana ya tashi.
Almajiran za su zauna a fadake sa'adda Yesu na addu'a. Wannan ba ya nufin cewa yakamata su kali Yesu sa'adda ya na addu'a.
Wannan na nufin cewa idan Allah zai bari ya faru. AT: "Idan Allah zai bari"
A nan "sa'an" na nufin loƙacin wahalar Yesu, yanzu da anjuma a lambun. AT: "ba sai ya yi wannan wahala ba"
kalma ne da 'ya'yan Yahudawa ke amfani da shi a yin magana da ubansu. Tun da ya na biye da "Uba," zai yi kyau a fasara wannan kalma.
Wannan muhimmin laƙabi ne wa Allah.
Yesu ya yi maganar wahala da zai sha kamar koko ne.
Yesu ya na rokon Allah ya yi abin da ya ke so a yi ba kuma abin da Yesu ya na so ba. AT: "Amma kada ka yi abin da nake so, yi abin da kake so"
Kalmar "su" na nufin Bitrus, Yakub da Yahaya.
Yesu ya ƙwabe Siman Bitrus domin barci. AT: "Siman, Kana barci bayan na gaya maka ka zauna a fadake. Ba ka iya zama a fadake ko na dan sa'a ɗaya ba."
Yesu ya yi maganar faɗi cikin jaraba kamar shigan cikin bayyananniyar wuri. AT: "kada a jarabta ku"
Yesu ya ƙwabe Siman Bitrus da cewa ba shi da ƙarfin yin abin da yake so ya yi a ƙarfinsa. AT: "Ka na da niyya a ruhunka, amma ka na raunana sosai a yin abin da ka ke so ka yi" ko "Ka na so ka yi abin da na ce, amma ka raunana"
Wannan na nufin kamani biyu na Bitrus. "Ruhun" shi ne bege na ciki. "Jikin" shi ne iyawa da ƙarfi na mutuntaka.
"maimaita addu'an da ya yi"
A nan marubucin ya yi maganar wuya da mutum mai jin barci ya ke ji a barin idannunsa a buɗe kamar "idannu masu nauyi." AT: "don sun ji barci sosai sun kasa barin idannunsu a buɗe"
Yesu ya je ya yi addu'a kuma. Sai ya kuma sau uku. AT: "Sai ya je ya yi addu'a kuma. Ya komo karo na uku"
Yesu ya ƙwabe almajiransa don rashin zama da fadake da kuma yin addu'a. AT: "Ku na nan ku na barci da hutawa!"
Loƙacin wahala da bada Yesu ya yi kusan faruwa.
"saurara!"
Yesu ya ƙwabe almajiransa cewa mai bashe shi ya yi kusa da su. AT: "Ni, Ɗan Mutum, an bashe ni"
Aya arba'in da hudu ya ba da tushen bayani game da yadda Yahuza ya shirya da shugabanin Yahudawa don ya bashe Yesu.
Wannan na nufin Yahuza.
A nan "ne" na nufin mutumin da Yahuza zai nuna. AT: "shi ne wanda ku ke so"
"Yahuza ya sumbace shi"
Waɗannan jumloli biyun na da ma'ana iri ɗaya don nanata cewa sun kama Yesu. AT: "rarume da kuma kama Yesu" ko "kama shi"
"wanda na tsaye a kusa"
Yesu ya na tsauta wa taron. AT: "abin ba'a ne cewa kun zo nan don ku kama ni da takkuba da kulake kamar na zama mai fashi!"
"Amma wannan ya faru domin"
Wannan ya na nufin almajiran.
kayan da an yi daga abin da ake tufkewa.
AT: "da ya yafa akansa"
"Da mutanen suka kama wannan mutumin"
Sa'adda mutumin ya na kokarin guduwa, sauran na iya kama kayansa, da kokarin hana shi.
Ana iya sakewa domin fahimta. "Dukka manyan firistoci, dattawa, da kuma marubuta sun taru a can"
An yi amfani da wannan kalma anan domin a sa alama a labarin sa'adda marubucin ya fara gaya mana game da Bitrus.
Sa'adda Bitrus ya bi Yesu, ya tsaya a fadar babban firist. AT: "kuma ya tafi da nisa har fadar babban firist"
Bitrus ya zauna tare da dogaran da suke aiki a fadan. AT: "ya zauna a cikin fadan tare da dogaran"
Basu ba ne za su kashe Yesu; maimakon haka, za su sa wani ya aikata. AT: "za su iya sa a kashe Yesu" ko "za su iya sa wani ya kashe Yesu"
Basu sami wani shaida akan Yesu da za su iya hukunta shi su kuma kashe shi ba. AT: "Amma basu samu wani shaida wanda za su iya hukunta shi ba"
A nan an kwatanta yin shaidar zur kamar abu ne da ana iya gani da wani na iya ɗauke. AT: "sun zarge shi ta wurin yin masa shaidar zur"
AT: "amma shaidarsu ya bambanta da juna"
"Mun ji Yesu ya ce." Kalmar "mun" na nufin mutanen da suna kawo shaidar zur akan Yesu, bai hada da mutanen da suke magana ba.
A nan "hannaye" na nufin mutane. AT: "da mutane sun yi ... ba tare da taimakon mutum ba" ko "da mutane sun gina ... ba tare da taimakon mutum ba"
"a cikin kwana uku." Wannan na nufin cewa za a gina haikalin a cikin kwana uku.
An fahimci kalmar "haikali" a jumla da ta wuce. AT: " zai gina wani haikali"
"bambanta da juna."
Yesu ya tashi a tsakiyar jama'a masu fushi don ya yi masu magana. Fasara wannan don ya nuna wanda ya na nan a loƙacin da Yesu ya tashi yin magana. AT: "mike a tsakanin manyan firistoci, marubuta, da dattawa"
Babban firist din bai tambayi Yesu akan bayanin game da abin da shaidun suka ce ba. Ya na tambayan Yesu don ya nuna cewa abin da shaidun sun ce ba daidai ba ne. AT: "Ba za ka amsa ba? Menene ka ce a amsa game da shaidan da waɗannan mutanen ke fada akan ka?"
A nan an kira Allah "Madaukaki." Zai fi kyau a fasara "Ɗan" da irin kalma da harshenku za su yi amfani a kiran "ɗan" uban mutum. AT: "Ɗan Maɗaukaki" ko "Ɗan Allah"
AT: 1) don amsa tambayar babban firist da kuma 2) don ya kira kansa "Nine," wanda shi ne yake abin da Allah ya kira kansa a cikin Tsohon Alkawari.
A nan "iko" ƙarin magana ne da na wakilcin Allah. Zama a "hannun damar Allah" alama ne na karban babban ɗaukaka da iko daga Allah. AT: "ya na zaune a wurin girma a gefen Allah mai iko dukka"
An ƙwatanta gajimaren a nan kamar su na rakiyar Yesu a dawowarsa. AT: "Indan ya soko a gajimaren a sararin sama"
Babban firist din ya kyakketa tufafinsa don ya nuna fushinsa da ƙyamarsa a abin da Yesu ya ce. AT: " kyakketa tufafinsa a cikin fushi"
AT: "Ba lallai ne muna son mutane kuma wanda za su shaida akan wannan mutum ba!"
Wannan na nufin abin da Yesu ya ce, wanda babban firist ya kira sabo. AT: "Kun dai ji sabon da ya ce"
Waɗannan jumlolin na nufin mutanen cikin taron.
Sun rufe masa idanunsa da ƙyalle ko abin ɗaure ido, don kada ya iya gani. AT: "don a rufe masa idanunsa da abin ɗaure ido"
Sun yi mashi ba'a, da ce masa ya yi annabcin wanda yake buga shi. AT: "Yi annabcin wanda ya buga ka"
mazajen da suke tsaron gidan gumna
"a waje a filin gida"
Baranyar yanmatan su na aiki wa babban firist. AT: "wata baranyar wanda su na yi wa babban firist aiki"
Wannan na nufin amince cewa wani abu ba gaskiya ba ne. Wannan lamarin, Bitrus na faɗa cewa abin da baranyar ta faɗa game da shi ba gaskiya ba ne"
Dukka "sani" da "gane" na da ma'ana iri ɗaya anan. An nanata ma'anar domin a nuna abin da Bitrus na ce. AT: "Ban gane abin da kike magana akai ba"
Wannan ne baranyar da ta nuna Bitrus a farko.
Mutanen suna nuna cewa Bitrus ɗaya ne daga cikin almajiran Yesu. AT: "ɗaya daga cikin almajiran Yesu" ko "ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da wannan mutumin da an kama"
Idan ɗole ne ya kamata ku ba da sunan mutumin da ya la'anta wani a harshenku, ku ce Allah. AT: "ce don Allah ya la'anta shi"
Zakara tsuntsu ne da ke kira da samako. Karar da yake yi ne "cara."
"Biyu" lamba ne.
Wannan ƙarin magana na nufin cewa ya cika da damuwa ya kuma rasa ikon shaukinsa. AT: "ya cika da bakin ciki" ko "ya rasa ikon shaukinsa"
Sun nema yadda za su kama Yesu shuru su kuma kashe shi.
Sun yi damuwa hargitsi yana iya tashi a tsakanin mutanen.
Wata mace ta zuba turare mai tsada a kan Yesu.
Wasu sun tsauta wa matan domin bata sayar da turaren ta ba da kudin ma tallakawa ba.
Yesu ya ce matan nan ta shafe jikin sa don biso.
Yesu ya ce duk inda aka yi wa'azi a duniya, za a yi maganar abin da matan nan ta yi don tuni da ita.
Yahuza Iskariyoti ya tafi wurin shugabanin firistoci saboda in ya yiwu ya isar da Yesu zuwa ga su.
Yesu ya gaya ma su su tafi gari su kuma bi wani mutum da ke dauke da tulun ruwa, su kuma tambaye shi ina ne dakin bakin ya ke da za su yi amfani da ita don cin abincin idin ƙetarewa.
Yesu ya ce daya da ga cikin almajiran da ya ke cin abinci da shi zai ci amanan shi.
Yesu ya ce almajirin da ya ke tsoma gurasansa tare da shi a kwano daya zai ci amanan shi.
Yesu ya ce ya fi da ba haife shi ba.
Yesu ya ce, ''gashi wannan. Jikina ne''.
Yesu ya ce, '''Wannan itace jinina na alkawari, jinin da ake zuba wa mutane dayawa''.
Yesu ya ce zai sake sha daga wannan 'ya'ya na innabi a ranar nan da ya sha ta sabuwa a cikin mulkin Allah.
Yesu ya faɗi cewa dukka almajiransa za su yi tuntube domin sa.
Yesu ya gaya wa Bitrus cewa kafin carar zakara ta biyu, Bitrus zai yi musun Yesu sau uku".
Yesu ya gaya masu su yi zama da lura.
Yesu yayi addu'a yana cewa idan mai yiwuwa ne a dauke masa wannan sa'a daga gare shi
Yesu ya na shirye ya yarda da duka abinda Uban ya so ma sa.
Yesu ya sami almajiran nan uku suna barci.
Yesu ya sami almajiran nan uku suna barci.
Yahuza ya yi wa Yesu sumba domin ya nuna wani mutum ne Yesu.
Yesu ya ce cikan ayan littafi mai tsarki ne domin sun zo su kama shi kamar ɗan fashi, da takobi da kulki.
Wadanda suke tare da Yesu duk suka rabu da shi suka gudu.
Saurayin nan ya bar tufafinsa a wurin ya gudu a tsirara.
Bitrus yana tare da masu tsaro, kusa da wuta suna jin dumi.
Shaidar karya aka yi wa yesu kuma bata sami yarda ba.
Babban firist ya yi wa Yesu tambaya ko shine Almasihu, Ɗan mai albarka.
Yesu ya amsa cewa shine Almasihu, Ɗan mai albarka.
Babban firistin ya ce wai Yesu ya yi laifin sabo.
sun tufa masa yawu, sun buga shi su ka kuma duke shi.
Bitrus ya amsa cewa bai sani ko kuwa gane abin da yarinyan ta ke fadi ba.
Bitrus ya rantse ya kuwa la'anta kansa cewa bai san Yesu ba.
Bayan da ya ji zakaran, Bitrus ya fadi yayi kuka.
Bayan da Bitrus ya amsa na uku, zakaran ya yi cara na biyu.
1 Da sassafe, sai manyan firistoci suka hadu da dattawa da manyan malamai, da majalisa suka daure Yesu, suka sa shi gaba suka mika shi ga Bilatus. 2 Bilatus ya tambaye shi, kaine sarkin Yahudawa? ya amsa ya ce "haka ka ce" 3 Sai manyan firistochi suka kawo zargi iri iri a kan Yesu. 4 Bilatus ya sake tambayarsa, ba ka da abin cewa? ka lura da yawan zargi da ake yi maka. 5 Amma Yesu baya sake yi masa magana ba. wannan ya ba shi mamaki. 6 A lokacin idi, Bilatus ya kan sakar masu da dan bursuna wanda jama'a suka bukaci a saka, 7 A cikin gidan yari, in da aka tsare wadansu yan tawaye, da masu kisan kai, akwai wani mai kisan kai, ana ce da shi Barrabbas. 8 Sai Jama'a suka zo wurin Bilatus ya yi masu kamar yadda ya saba yi. 9 Bilatus ya amsa masu ya ce, kuna so in sakar maku sarkin Yahudawa? 10 Yayi wannan domin ya sani cewa Firistoci sun bada shi ne domin suna kishin sa, 11 Sai Firistochi suka zuga jama'a, sai suka yi kuwwa suna cewa, a sakar masu Barrabbas amaimakon Yesu. 12 Bilatus ya sake yi masu tambaya "Yaya zan yi da Sarkin Yahudawa?" 13 sai suka amsa da kuwwa" a "giciye shi!" 14 Bilatus ya ce masu menene laifinsa sai suka kara ihu, "a giciye shi." 15 Bilatus don yana son ya farantawa jama'a zuciya sai ya sakar masu da Barrabbas sai ya yi wa Yesu bulala, sannan ya mika shi a giciye shi. 16 Sojoji suka kai shi cikin kagara, suka tara rundunan soja, 17 Suka sa masa tufafin shulaiya suka nada masa rawanin kaya, 18 Suna masa kirari na ba'a suna cewa, "A gaida sarkin Yahudawa!" 19 Sai suka buge shi a kai da kulki suka kuma tofa masa yau a fuska, suka kuma durkusa suna yi masa sujadar ba'a. 20 Bayan sun gama yi masa ba'a sai suka cire masa tufafin shunnaiya, sai suka maida masa tasa tufafinsa, sai suka fitar dashi don su giciye shi. 21 Suna cikin tafiya sai suka hadu da wani, mai suna Saminu Bakairawani (wato uban Alizanda da Rufus); suka tillasta shi ya dauki gijiyen Yesu. 22 Sojojin suka kawo Yesu wurin da ake kira Golgota (wato kokon kai) 23 Suka bashi ruwan inabi hade da mur, amma ya ki ya sha. 24 Sai suka giciye shi, suka kuma raba tufafinsa suka kuma jefa kuri'a domin kowanne soja ya sami rabonsa. 25 A sa'a ta uku aka giciye shi. 26 Sai aka rubuta alamar zargi da take cewa "Ga Sarkin Yahudawa" 27 Suka kuma giciye shi tare da wadansu yan fashi guda biyu. 28 Daya a hannun damansa daya a hannun hagunsa. Domin a cika abinda nassi ya fada. 29 suke wucewa suna zaginsa suna kada kai suna cewa, "Aha! kai da zaka rushe haikali ka kuma gina shi cikin kwana uku, 30 ka ceci kanka mana, ka sauka daga giciye!" 31 Haka ma manyan firistoci da malamai, suka yi masa ba'a suna cewa "Ya ceci wadansu amma bai iya ceci kansa ba" 32 Bari Almasihu Sarkin Yahudawa ya sauka daga giciye. Domin mu gaskata shi, sai wadanda aka giciye shi tare dasu, suma suka yi masa ba'a. 33 sa'a ta shida zuwa sa'a ta tara, duhu ya rufe ko'ina, 34 A sa'a ta tara, Yesu ya tada murya da karfi ya ce Eloi, Eloi lamathsabathani?" Ma'ana Ya Allahna Ya Allahna, me ya sa ka yashe ni?" 35 Wasu daga cikin na tsaye, da suka ji shi, sai suka ce, "Duba, yana kiran Iliya." 36 Sai wani ya hanzarta, ya dauki soso ya tsoma a ruwan inabi mai tsami, ya soka agora ya mika masa don yasha. Mutumin yace bari mu gani ko Iliya zai zo ya saukar da shi. 37 Sai Yesu yayi kuka da babban murya da karfi sannan ya rasu. 38 Sai labulen haikalin ya rabu kashi biyu daga sama har kasa. 39 Sa'adda da jarumin sojan da ke tsaye yana fuskantar Yesu ya ga yadda ya mutum, Sai ya ce "hakika, wannan mutum Dan Allah ne." 40 Akwai kuma mata wadanda ke dubawa daga nesa. Daga cikinsu akwai Maryamu Magadala, da Maryamu( Uwar Yakubu da Yusufu) da Salome. 41 Wadannan matan sune suka bishi sa'adda da yake Galilee suna yi masa hidima. Da wadansu mata da yawa suka zo Urushalima tare da shi. 42 Da maraice an shiga shirye shirye domin kashe gari asabbaci ce. 43 Sai Yusufu daga garin Arimatiya ya zo, mutumin kirki, mai girma kuma dan majalisar dattawa, mai sauraron mulkin Allah, da gaba gadi ya tafi wurin Bilatus ya bukaci a bashi jikin Yesu. 44 Bilatus ya yi mamakin mutuwar Yesu cikin lokaci kadan, sai ya kira jarumin ya tabbattar koYesu ya mutu. 45 Bayan ya tabbattar daga wurin jarumin soja cewa Yesu ya mutu, sai ya bada jikin ga Yusufu. 46 Yusufu ya sayo likafani. ya saukar da shi daga giciye, ya kawo likafanin nan ya lulube jikin Yesu dashi. Ya kai shi kabarin da aka sassaka da dutse, wadda ya shirya shi domin kansa. Ya kawo dutse ya rufe bakin kabarin da shi. 47 Maryamu Magadaliya da Maryamu Uwar Yusufu sun ga wurin da aka yi jana'izar Yesu.
Da manyan firistoci, da shugabanni, da malaman Attaura, da dukkan 'yan majalisa suka Yesu wurin Bilatus, sai suka zarge shi da aikata munanan abubuwa. Da Bilatus ya tambaya ko karan da suka kawo gaskiya ne, Yesu bai amsa shi ba.
Sun umurta a ɗaure yesu, amma yana iya zama cewa masu tsaro ne suka ɗaure shi suka sa shi gaba. AT: "suka umarta a ɗaure Yesu, sa'annan aka yi gaba da shi" ko kuma "suka umarce masu tsaron su ɗaura Yesu, sa'annan suke sa shi gaba"
Suka sa aka kai Yesu ga Bilatus, sa'annan suka bar shi yă bi da Yesu.
Wannan na iya nufin 1) ta wurin faɗin haka, Yesu yana cewa Bilatus ne ke ce da shi Sarkin Yahudawa ba Yesu ba. AT: "Ai kai da kanka ne ke ce haka" ko kuma 2) ta wurin faɗin haka, Yesu na nufin cewa shi ne Sarkin Yahudawa. AT: "I, yadda ka faɗa, Ni ne" ko kuma "I, haka ne yadda ka faɗa"
"suna zargen Yesu da laifuffuka iri iri" ko kuma "suna cewa Yesu ya aikata munanan abubuwa masu yawa"
"Bilatus ya sake tambayar Yesu kuma"
AT: "Kana da abin faɗi"
"Duba" ko kuma "ka Saurara" ko kuma "Ka mai da hankali ga abinda za faɗa maka"
Bilatus ya yi mamaki cewa Yesu bai tanka shi ko ma ya kare kansa ba.
A nan amfani ne da wannan kalmar don a nuna kaucewa daga ainihin labarin yayin da marubucin yana ba da tarihin al'adan Bilatus na saka wani ɗan kurkuku a bukukkuwa da kuma game da Barrabas.
"A wancan lokacin akwai wani mutum mai suna Barrabbas, yana kurkuku tare da wasu mutane. Sun yi kisankai yayin da suka yi tawaye da gwamnatin Roma"
Wato sakie ɗan kukuku a bukukkuwa. AT: "ya sake masu wani ɗan kurkuku kamar yadda ya saba yi"
Wannan na ba da tarihin dalilin da yasa aka ɗanka Yesu wa Bilatus.
Suna kishin Yesu, mai yiwuwa domin da yawa a cikinsu suna binsa suna kuma zama almajiransa. AT: "manyan firistocin suna kishin Yesu. Shi yasa suna" ko kuma "manyan firistocin suna kishin farin jini da Yesu ke da shi ne a cikin mutane. Shi ya sa suna"
AT: "ta da hankulan jama'a" ko kuma "suka rinjaye jama'a"
Sun roƙa a sake masu barrabbas a maimakon Yesu. AT: "a sakar a maimakon Yesu"
Bilatus yana tambayan abinda zai yi idan ya sake masu Barrabbas. Ana iya kara haske a wannan, AT: "Idan na sake maku Barrabbas, me zan yi da Sarkin Yahudawa"
"Bilatus ya ce wa taron"
"ya sa taron su jo daɗi ta wurin yin abinda shi yake son su yi"
Sojojin Bilatus ne sun bulale Yesu, ba Bilatus dai da kansa ba.
"duka." A "bulale" mutum na nufin a yi wa mutum duka mai za i da sumagiya.
Bilatus ya umarci sojoji su tafi da Yesu don su giciye shi. AT: "ya ce wa sojojin su tafi da Yesu su giciye shi"
A nan ne sojojin Roma da ke Urushalima su ke zama, kuma gwamna ma yakan zama anan ne idan yana Urushalima. AT: "fadar rundunan sojoji da ke bariki" ko kuma "kagarar gidan gwamna"
"iyakar sojojin da ke wurin gabaɗaya"
shulaiya kala ce da 'yan sarauta ke sakawa. Sojojin ba su yarda cewa Yesu sarki ba ne. Sun saka masa waɗannan tufafun ne domin su yi masa ba'a domin akwai masu cewa shi ne sarkin Yahudawa.
"rawani da aka yi da rasan ƙaya"
Akan yin irin wannan gaisuwar da hannu a sama ne musamman domin a kaishe Sarkin Roma. Sojojin basu gaskata cewa Yesu sarkin Yahudawa bane. A maimakon haka, suna faɗin haka ne domin su yi masa ba'a'.
"sanda" ko kuma "itace"
Mutumin da ya durkusa ya lankwasa guiwar sa, ana iya cewa duk wanda ya durkusa ya lankwasa guiwarsa kenan." AT: "durkusawa" ko " durkusa"
Dokan Roma ya ba wa sojoin Roma izini su tilasta duk mutumin da suka samu a hanya ya ɗauki masu kaya. A wannan hali, sun tilasta Saminu yă ɗauki giciyen Yesu.
"daga bayan garin"
Wannan na ba da tarihin mutumin da sojojin sun tilasta shi ya ɗauki giciyen
Waɗannan sunayen mutane ne maza.
Wannan sunan wani wuri ne.
"wurin koƙon kai" ko kuma "wurin koƙon." Wannan shi ne sunan wurin. Ba wai yana nufin cewa akwai su koƙon kai da yawa a wurin ba.
koƙon kai shi ne ƙwaƙwalwan kai, ko kuma kan da babu soka ko nama a jikinta.
Zai zama da taimako idan an yi bayani cewa mur wata mai ce mai rage zafi. AT: "ruwa inabi a haɗe za wata magani mai suna mur" ko kuma "ruwan inabi a haɗe da magani mai rage zafi da ake kira mur"
"uku" anan yana daidai jerin kirge. Wannan na nufin ƙarfe tara na safe. AT: "a ƙarfe tara na safe"
Sojojin sun manna wata alama a jikin jiciyen a bisa Yesu. AT: "Sun manna a giciyen a sama da kan Yesu wata alama da ke"
"laifin da suke zargin sa"
Ana iya kara haske a wannan. AT: "ɗaya a bisa giciye a hannun damansa sannan ɗaya kuma a bisa giciye a hannun hagu"
Wannan alama ce da ke nuna cewa mutane ke yi don su nuna cewa basu amice da Yesu ba.
Wannan alama ce na ba'a. Ku yi amfani da daidai yadda ake yin ba'a a harshen ku.
Mutanen suna tunashe Yesu da abinda ya anabta zai yi ne dama. AT: "kai da ka ce za ka rushe haikali ka ka sake gina shi a kwana uku"
Wato yadda mutanen da ke tare da Yesu ma suna masa ba'a.
"suna faɗin maganganun ba'a a kan Yesu a junansu"
Shugabannin basu gaskata cewa Yesu shi ne Almasihu, Sarkin Isra'ila. AT: "Yana ce da kansa Almasihu da kuma Sarkin Isra'ila. To ya sauka" ko kuma "Idan shi ne Almasihu na gaskiya da Sarkin Isra'ila kuma, sai yă sauka"
Wato a gaskata da Yesu. AT: "gaskata shi"
suka zazzage shi.
Wato tsakar rana kenan ko kuma 12 p.m.
A nan Marubucin yana bayanin yadda wuri yake yin duhu ne kamar wani kaɗi ne da ke masowa a bisa ƙasar. AT: "ƙasar gabaɗaya ya zama baki"
Wato ƙarfe uku na rana kenan. AT: "A ƙarfe uku na rana kenan. ko kuma "a sakar yini kenan"
Waɗannan kalamun Yahudnci ne da ake iya ɗauko so zuwa harshenke yadda muryar su suka fito anan.
"ma'ana"
Ana iya fada a fili cewa basu fahimci abinda Yesu ke cewa ba. AT: "Wasu da ke tsaye a wurin sun ji kalamunsa, amma basu fahimci abinda yake cewa ba"
"ruwan inabi mai tsami da gaske"
"sanda."
"ya ba wa Yesu." Mutumin nan ya daga sandar sama ne domin Yesu ya samu yă iya shan ruwan inabin daga soson. AT: "ya riƙe shi sama wa Yesu"
Markus yana nuna cewa Allah ne da kansa ya raɓa labulen haikalin. AT: "Allah ya raɓa labulen haikalin kashi biyu"
Wannan shi ne jarumin da ya kula da sojojin da suka giciye Yesu.
Anan "fuskanta" wata karin magana ne da ke nufin a kalli mutum. AT: "ya tsaya a gaban Yesu"
"yadda Yesu ya mutu"
Wannan wata lakaɓi ne mai muhimmanci na Yesu.
"suna kallo daga nesa"
A nan iya rubuta wannan a baka ba.
kanin Yakubu Ana ce da wannan "kani" mai yiwuwa domin a banbanta shi da wani mutum mai kuma mai suna Yakubu ne.
Wannan Yosis ba shi ne kanin Yesu ba. Duba yadda kun juya wannan a [Markus 6:3]
Salome sunan mace ce.
" Waɗannna matan sun bi Yesu, sa'ad da Yesu yake galili ... da shi zuwa Urushalima." Wannan shi ne ɗan tarihi game da matan da suke kallon yadda a ka giciye shi daga nesa.
Urushalima na sama da kowani gari a Isra'ila, shi yasa mutane sun saba cewa suna haurowa zuwa Urushalima da kuma saukowa.
A nan ana maganar yamma kama wani abu ne da ke iya sa wa a wani wuri. AT: "yamma ya yi" ko kuma "yamma ne ko"
Jimlar nan "ya zo" na nufin Zuwan Yusufu zuw wurin Bilatus, wadda aka yi bayaninsa bayan tarihin da aka bayar, amma ana maganar zuwansa ne domin a nanata, ya kuma taimaka a gabatar da labarin. Ana iya samun wata hanya daban na yin haka a harshenku. AT: "Yusugu ɗan garin Arimatiya, mutum ne mai girma"
Yusufu shi ne sunan mutumin, Arimatiya shi ne sunan inda ya fito.
Wannan shi ne tarihin Ysusfu.
"ya tafi inda Bilatus yake"
Kuna iya karin bayani cewa yana bukatan jikin Yesu ne domin ya bizne shi. AT: "ya bukaci izinin ɗaukan jikin Yesu ne domin ya bizne shi"
Bilatus ya ji mutane suna cewa Yesu ya mutu. Wannan ya ba shi mamaki, don haka, ya tambayi jarumin ko hakan gaskiya ne. AT: "Bilatu ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu, don haka, ya kira jarumin"
"sai ya ba wa Yusufu Izini ya tafi da jikin Yesu.
likafini wani yadi ne da aka yi shi daga zaren wani itace. Duba yaka kuka juya wannan a [Markus 14:51]
Kuna iya bayani cewa Yesufu ya nema wasu mutane su taya shi daukan jikin Yesu da ya saukar da shi daga giciye, ya shirya shi domin ya sa shi a kabari, ya kuma rufe kabarin. AT: "Sai shi da wasu mutane sun saukar da shi ... Sun kawo dutsen sun rufe"
AT: "kabarin da wani ya sassaka da sutse
"babban dutse da aka fafe aka sa a gaban"
AT: "inda Yusufu da sauran suka binne jikin Yesu"
Da safe, sun daure Yesu suka kuma mika shi ga Bilatus.
Bilatus ya yi mamaki cewa Yesu ya bar bashi amsa.
Bilatus ya kan yantad da wani fursuna wanda mutanen suka roka a lokacin bikin idin.
Bilatus ya san cewa shugabanin firistocin suna kishi ne shi yasa suka kawo masa Yesu.
Taron mutanen sun yi kuka a yantad da Barabbas.
Taron mutane sun ce a gicciye Sarkin Yahudawa.
Sojojin sun sa masa alkyabba mai ruwa jar a Yesu kuma sun sa a kan sa kambi wanda aka murda mai kaya.
Mai wucewa, Saminu Bakurane, an tilasta masa ya dauki gicciyen Yesu
Sunan wurin Golgota, wanda na nufin Wurin Kokon Kai.
Sojojin sun yi kuri'a ma tufafin Yesu.
Sojojin sun rubuta "Sarkin Yahudawa" a kan alaman.
Wadanda sun wuce sun kalubance Yesu ya cece kansa ya kuma sauka kasa daga gicciyen.
Shugabannin faristoci sun ce ya kammata Yesu ya sauka kasa daga gicciye domin su yi imani.
Shugabannin firistocin sun kira Yesu Almasihu da kuma sarkin Isra'ila.
A sa'a na shida, duhu ya zo kan dukka kasar.
Yesu ya yi kuka yana cewa, ''Ya Allah na, Ya Allah na, me ya sa ka yashe ni?''
Yesu ya yi kuka da murya mai karfi kafin ya mutu.
Labulen haikalin ya yage ciki biyu da ga sama zuwa kasa a lokacin da Yesu ya mutu.
Jarumin nan ya shaida cewa gaskiya wannan mutumin Ɗan Allah ne.
Yesu ya mutu a rana da ke zuwa kafin ranar Asabar.
Yusuf na garin Arimatiya ya saukar da Yesu daga giciye, ya kawo likafanin nan ya lulube jikin Yesu dashi. Ya kai shi kabarin da aka sassaka da dutse ya kawo dutse ya rufe bakin kabarin da shi.
1 Bayan ranar assabaci, Maryamu Magadaliya da Maryamu uwar Yakubu da Salomi, suka sayo man shafawa mai kamshi domin shafe jikin Yesu saboda jana'iza. 2 Da safiyar ranar farko ta mako sai suka tafi kabarin a dai dai fitowar rana. 3 Suna magana a tsakaninsu suna cewa, wanene zai gangarar da dutsen da aka rufe bakin kabarin da shi?" 4 Da suka daga ido, sai suka ga an riga an gangarar da dutsen, domin yana da girma. 5 Da suka shiga cikin kabarin sai ga wani saurayi saye da farar tufa, yana zaune a hannun dama, suna mamaki. 6 Sai ya ce masu, "Kada ku ji tsoro. Kuna neman Yesu banazare, wanda aka giciye. Ya tashi! Baya nan. Ku duba wurin da aka kwantar dashi. 7 Sai ku je, ku gaya wa almajiransa da Bitrus cewa ya rigaya ya yi gabanku zuwa Galili. A can zaku ganshi, kamar yadda ya fada maku." 8 Suka fita daga cikin kabarin da gudu suna rawar jiki da mamaki, ba su cewa kowa komai ba domin suna jin tsoro. 9 Da safiyar ranar farko ta mako ya fara bayyana kansa ga Maryamu Magadaliya wadda ya kori aljannu guda bakwai daga cikinta. 10 Sai ta tafi ta shaida wadanda suke tare da shi suke makoki da kuka. 11 Sai suka ji cewa ya tashi kuma ta ganshi, amma basu gaskata ba. 12 Bayan wadannan al'amura ya bayana kansa ta wata siffa ga mutum biyu sa'ilin da suke tafiya akan hanya. 13 Sai suka tafi suka gaya wa sauran almajiransa, duk da haka basu gaskata ba. 14 Bayan wani lokaci, Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa su goma sha daya, ya tsauta masu saboda rashin gaskatawa da taurin zuciya, bayansun ji daga wadanda suka ganshi bayan ya tashi daga matattu. 15 Sai ya umarcesu cewa "Ku tafi cikin duniya ku yi bishara ga dukan halitta. 16 Wanda ya ba da gaskiya aka kuma yi masa baftisma, zaya sami ceto, wanda baya bada gaskiya ba za ya hallaka. 17 Wadannan alamu za su kasance da wadanda suka gaskata; a cikin sunana, za su fidda aljannu, za su yi magana da sabbin harsuna. 18 Za su dauki macizai da hannayesu, idan sun sha guba ba ta cutar dasu ba, za su dibiya hannayensu ga marasa lafiya, za su sami warkaswa." 19 Bayan Ubangiji ya gama magana da su, sai aka dauke shi zuwa sama in da zai zauna a hannun dama na Allah. 20 Almajiransa kuma suka tafi ko'ina suna sheilar bishara. Ubangiji kuma yayi aiki tare da su, yana tabbatar da kalma ta wurin ayukan al'ajiba tare da su.
A rana ta farko na mako, sa matan suka yi sammako domin su shafe jikin Yesu da man kamshi. Sun yi mamaki ƙwarai da sukn ga wani saurayi yana faɗi masu cewa Yesu yana da rai, amma sun ji tsoro kuma basu gaya wa kowa hakan ba.
Wato, bayan Asabar, rana ta bakwai na mako, ta kare sa'annan rana ta farko ta fara.
AT: "wani ya riga ya gangarar da dutsen"
Mala'ikan yana magana ne da tabbaci cewa yesu ya tashi daga matattu. AT: "Allah ya ta da shi daga matattu!" ko kuma "Ya ta da kansa daga matattu!"
"ranar Lahadi"
"Sai suka ji Maryamu Magadaliya tana cewa"
"su biyun" sun gan Yesu, amma ya yi daban da yadda yake dama.
mutum biyu "waɗanda ke tare da shi" ([Markus 16:10])
Sauran almajiran basu gaskata da abinda mutum biyun da ke ke tafiya cikin ƙasar ke cewa ba.
Waɗannan su ne manzanni goma sha ɗaya da suka rage bayan da Yahuza ya bar su.
Wannan misali ne na cin abinci, wanna haye ne na kullum wanɗa mutane suke cin abinci. AT: "suna cin abinci"
A al'adan Yesu, mutane suka taru ne a waje ɗaya lokacin cin abinci.
Yesu yana sauta wa almajiransa ne domin basu gaskanta da shi ba. A juya wannan karin maganar yadda za a fahimci cewa almajiran basu gaskata da Yesu ba ne. AT: "ƙi gaskatawa"
A nan "duniya" karin magana ne da ke nufin mutanen da ke cikin duniya. AT: "Ku je duk wurin da akwai mutane"
Wannan ƙari ne a maganar kuma ya na nufin mutane a ko'ina. AT: "kowa da kowa gabakiɗaya"
Kalmar nan "wanda" na nufin ko ma wa. AT: "Allah za cece dukkan mutanen da sun ba da gaskiya sun kuma yarda a ku yi masu baftisma"
Kalmar nan "wanda" na nufin ko ma wa. AT: "Allah zai hallaka dukkan mutanen da basu ba da gaskiya ba"
Markus yana maganar mu'ajizai kamar su mutane ne da ke tafiya tare da masubi. AT: "Mutanen da ke kallon waɗannan sun gaskata za su ga waɗannan abubuwan suna faruwa, za su kuma sani cewa Ina tare da masubi"
Wannan na iya nufi 1) Yesu yana ba da jerin abubuwa: "A cikin suna na za su yi abubuwa kamar haka: Za su" 2) Yesu yana ba da daidai jerin abubuwa: "Ga abubuwan da za su yi a cikin sunana: Za su."
A nan "suna" yana haɗe ne da Iko ko kuma karfin ikon Yesu. Duba yadda kuka juya "a cikin sunar ka" a [Markus 9:38]. AT: "Ta wurin ikon sunana" ko kuma "Ta wurin karfin ikon sunana"
AT: "Allah ya ɗauke shi zuwa sama, ya kuma zaunar da shi"
A zauna a "hannun dama na Allah" alama ce na samun wata babban girma da iƙo daga gun Allah. AT: "zaune a wuri mai girma a gefen Allah"
Wanna karin magana na nufin yana nuna cewa jawabin su gaskiya. AT: "yaya nuna cewa jawabin nan da suke yi gaskiya"
Matan sun tafi kabarin a ranar farko ta mako a dai dai fitowar rana.
Wani ya rigaya ya naɗa babban dutsen daga kofar shigan.
Matan sun gan wani saurayi a cikin farin kaya yana zaune a hannun dama.
Saurayin ya ce Yesu ya tashi kuma baya nan a wurin.
Saurayin ya ce almajiran za su sadu da Yesu a kasan Galili
Yesu ya fara bayyana kansa ga Maryamu Magdaliya
Almajiran ba su yarda ba.
Almajiran basu yarda ba.
Yesu ya tsauta masu domin rashin yardan da suka yi.
Yesu ya umarci almajiransa su shiga duniya su kuma yi wa'azin bishara.
Yesu ya ce wadanda basu yi imani ba za a hukunta su.
Yesu ya ce wadanda sun yi imani an kuma yi masu baftisma za su sami ceto.
Yesu ya ce wadanda suka yi ĩmanĩ za su kora aljanu, za su yi magana a yare dabam dabam, babu abinda zai cutar da su, kuma zasu warkas da wasu.
Bayan da yayi magana da almajiransa, an dauki Yesu sama ya kuma zauna a hannun daman Allah.
Sai almajiran suka tafi suna wa'azi a ko ina.
Sai Ubangiji ya yi aiki da almajiransa ya kuma tabbatar da kalman da alamun al'ajibi
1 Mutane da dayawa sun yi kokarin rubutu akan abubuwan da suka cika a tsakaninmu, 2 kamar yanda suka danka mana su, wadanda tun daga farko suka zama shaidu da idanunsu kuma manzanni ne na sakon. 3 Sabili da haka, ni ma, bayan da na yi bincike da kyau akan yanayin wadannan abubuwa tun da farko na ga ya yi kyau in rubuta wadannan abubuwa bi da bi ya mafi girmaTiyofilas. 4 Ya zama haka domin ka san gaskiyar abin da aka koya maka ne. 5 A cikin zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, akwai wani firist mai suna Zakariya, daga yankin Abija. Matarsa daga cikin yaya mata na zuriyar Haruna ce, kuma sunan ta Alisabatu ne. 6 Dukan su biyu masu adalci ne a gaban Allah; marasa zargi a tafiyarsu cikin dukan dokoki da farilan Ubangiji. 7 Amma ba su da da, domin Alisabatu ba ta haihuwa, kuma a wannan lokacin dukansu sun tsufa kwarai. 8 Ya zama kuma a lokacin da Zakariya yana gaban Allah, yana yin hidimar sa ta firist bisa ga tsari da ka'idar aikinsa. 9 Bisa ga al'adar zaben firist da zai yi hidima, an zabe shi ta wurin kuri'a ya shiga cikin haikalin Ubangiji domin ya kona turare. 10 Dukan taron Jama'a suna addu'a a waje a sa'adda ake kona turaren. 11 A lokacin, mala'ikan Ubangiji ya bayana a gare shi yana tsaye a gefen daman bagadi na turaren. 12 Zakariya ya firgita sa'adda ya gan shi; tsoro ya kama shi. 13 Amma mala'ikan ya ce masa, "Kada ka ji tsoro, Zakariya, domin an ji addu'ar ka. Matar ka Alisabatu za ta haifa maka da. Za ka kira sunansa Yahaya. 14 Za ka yi murna da farin ciki, kuma da yawa za su yi murna da haifuwarsa. 15 Domin zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba zai sha ruwan inabi ba ko wani abu mai sa maye, kuma zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun daga cikin cikin mahaifiyarsa. 16 Kuma mutanen Isra'ila da yawa za su juya zuwa ga Ubangiji Allahnsu. 17 Zai yi tafiya a gaban Unbangiji a cikin ruhu da ikon Iliya. Zai yi haka domin ya juya zuciyar Ubanni zuwa ga 'ya'yansu, domin marasa biyayya su yi tafiya a cikin tafarkin adalai. Don ya shirya wa Ubangiji mutanen da aka shirya dominsa." 18 Zakariya ya ce wa mala'ikan, "Ta yaya zan san wannan? Ga shi na tsufa kuma matata tana da shekaru da yawa." 19 Mala'ikan ya amsa ya ce masa, "Nine Jibra'ilu, wanda ke tsaye a gaban Allah. An aiko ni in gaya maka wannan labari mai dadi. 20 Kuma duba, za ka zama bebe, ba za ka iya magana ba, sai ran da wadannan abubuwa suka cika. Ya zama haka domin ba ka gaskanta da kalmomina ba, wadanda za su cika a daidai lokacin." 21 Sa'adda mutane suke jiran Zakariya. Sun yi mamaki yadda ya dauki lokaci sosai a cikin haikali. 22 Amma da ya fita, bai iya yin magana da su ba. Sun gane da cewa ya ga wahayi lokacin da yake cikin haikali. Ya ci gaba da yi masu alamu, ba ya magana. 23 Ya zama bayan da kwanakin hidimarsa suka kare, ya tafi gidansa. 24 Bayan kwanakin nan, matarsa Alisabatu ta samu juna biyu. Ta boye kanta har na watani biyar. Ta ce, 25 "Wannan shi ne abin da Allah ya yi mani da ya dube ni domin ya dauke kunyata a gaban jama'a." 26 A cikin watan ta na shidda, an aiki Mala'ika Jibra'ilu daga wurin Allah zuwa wani birni a Galili mai suna Nazarat, 27 zuwa ga wata budurwa wanda aka ba da ita ga wani mutum mai suna Yusufu. Shi dan zuriyar Dauda ne, kuma ana kiran budurwar Maryamu. 28 Ya zo wurin ta ya ce, "A gaishe ki, ke da ki ke da tagomashi sosai! Ubangiji yana tare da ke. 29 Amma ta damu kwarai da wadannan kalmomi sai ta yi tunani ko wacce irin gaisuwa ce wannan. 30 Mala'ikan ya ce mata, "Kada ki ji tsoro, Maryamu, domin kin samu tagomashi a wurin Allah. 31 Duba, za ki sami juna biyu, za ki haifi da. Za ki kira sunansa 'Yesu'. 32 Zai zama mai girma, kuma za a ce da shi Dan Allah Madaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dauda. 33 Zai yi mulkin dukkan gidan Yakubu har abada, kuma mulkinsa ba shi da iyaka." 34 Maryamu ta ce wa mala'ikan, "Yaya wannan zai faru, tun da shike ni ban san namiji ba?" 35 Mala'ikan ya amsa ya ce mata, "Ruhu Mai-tsarki zai sauko a kan ki, kuma ikon Madaukaki zai lullube ki. Sabili da haka, za a kira mai tsarkin da za ki haifa Dan Allah. 36 Ki kuma duba, ga 'yar'uwarki Alisabatu ta samu juna biyu a tsufanta. Watannin ta shida kenan, ita wadda aka kira ta bakarariya. 37 Gama babu abin da ba shi yiwuwa a wurin Allah." 38 Maryamu ta ce, "To, ni baiwar Ubangiji ce. Bari ya faru da ni bisa ga sakonka." Sai mala'ikan ya bar ta. 39 Sai Maryamu ta tashi da sauri a cikin kwanakin nan, zuwa kasa mai duwatsu, zuwa wani birni a Yahudiya. 40 Ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Alisabatu. 41 Ya zama sa'adda Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, sai dan da ke cikinta ya yi tsalle, an cika Alisabatu kuma da Ruhu Mai Tsarki. 42 Ta daga murya, ta ce, "Mai albarka kike a cikin mata, kuma mai albarka ne dan cikinki. 43 Kuma don me ya faru da ni da uwar Ubangijina ta ziyarce ni? 44 Kuma duba, da na ji karar gaisuwan ki sai dan ciki na ya yi tsalle domin murna. 45 Kuma mai albarka ce wadda ta gaskanta cewa abubuwan da aka alkawarta mata daga wurin Ubangiji za su cika. 46 Maryamu ta ce, "Zuciyata ta yabi Ubangiji, 47 kuma ruhu na ya yi murna da Allah mai ceto na." 48 Domin ya dubi kaskancin baiwarsa. Duba, daga yanzu, dukkan tsararraki za su ce da ni mai albarka. 49 Domin shi madaukaki ya yi mani manyan abubuwa, kuma sunansa Mai Tsarki ne. 50 Jinkansa ya tabbata daga tsara zuwa tsara wadanda suke girmama shi. 51 Ya nuna karfinsa da hannuwansa; ya warwatsa ma su girman kai game da tunanin zuciyarsu. 52 Ya nakasar da magada daga kursiyoyinsu, ya kuma fifita nakasassu. 53 Ya ciyar da mayunwata da abubuwa masu kyau, amma ya aiki attajirai wofi. 54 Ya ba da taimako ga bawan sa Isra'ila, domin ya tuna ya kuma nuna jinkai 55 (kamar yanda ya fada wa ubaninmu) ga Ibrahim da zuriyarsa har abada." 56 Maryamu ta zauna da Alisabatu tsawon watanni uku sai ta koma gidanta. 57 Da lokaci yayi da Alisabatu za ta haifi danta, ta kuma haifi da namiji. 58 Makwabtanta da 'yan'uwanta sun ji cewa Ubangiji ya ribanbanya jinkansa akanta, sai suka yi murna tare da ita 59 Ya zama akan rana ta takwas, sun zo domin a yi wa yaron kaciya. Da sun kira sunansa "Zakariya" kamar sunan ubansa, 60 amma mahaifiyarsa ta amsa ta ce, "A'a, za a kira shi Yahaya." 61 Suka ce mata, "Babu wani a cikin danginku wanda ake kira da wannan suna." 62 Sun nuna alama ga ubansa bisa ga yanda ya ke so a rada masa suna. 63 Ubansa ya nemi a ba shi allon rubutu, sai ya rubuta, "Sunansa Yahaya." Dukan su suka yi mamaki kwarai da wannan. 64 Nan take, sai bakinsa ya bude kuma harshensa ya saki. Ya yi magana ya kuma yabi Allah. 65 Tsoro ya kama dukan wadanda suke zama kewaye da su. Sai labarin ya bazu cikin dukan kasar duwatsu ta Yahudiya. 66 Kuma dukan wadanda suka ji su, sun ajiye su a cikin zuciyarsu, suna cewa, "To me wannan yaro zai zama ne?" Domin hannun Ubangiji yana nan tare da shi. 67 Ruhu Mai-tsarki ya cika mahaifinsa Zakariya sai ya yi anabci cewa, 68 "Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra'ila domin ya zo ya taimaki mutanen sa kuma ya yi aikin ceto domin su." 69 Ya ta da kahon ceto dominmu daga gidan bawansa Dauda, daga zuriyar Dauda bawansa, 70 kamar yadda ya fada ta bakin annabawansa tsarkaka tun zamanin zamanai. 71 Zai kawo mana ceto daga magabtan mu da kuma daga hannun makiyanmu. 72 Zai yi haka domin ya nuna jinkai ga ubaninmu ya kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki, 73 rantsuwar da ya fada wa ubanmu Ibrahim. 74 Ya rantse zai yardar mana, bayan da an kubutar da mu daga hannun makiyanmu, mu bauta masa ba tare da tsoro ba, 75 a cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakin ranmu. 76 I, kai kuma, yaro, za a kira ka annabi na Madaukaki, domin za ka tafi gaban fuskar Ubangiji ka shirya hanyoyinsa, ka shirya mutane domin zuwansa, 77 domin ba mutanensa ilimin ceto ta wurin gafarar zunubansu. 78 Wannan zai faru ne domin girman jinkan Allahnmu, sabili da hasken rana daga bisa za ya zo wurinmu, 79 domin haskakawa akan wadanda ke zaune a cikin duhu da kuma cikin inuwar mutuwa. Zai yi hakan nan domin ya kiyaye kafafunmu zuwa hanyar salama. 80 Yaron ya yi girma ya kuma zama kakkarfa a cikin ruhu, yana kuma cikin jeji sai ranar bayyanuwarsa ga Isra'ila.
Luka ya bayyana dalilin rubutunsa zuwa ga Tiyofilas
"game da abubuwan da suka faru a tsakaninmu" ko "game da taronne da suka faru a tsakaninmu"
Ba wanda yake da tabbataciyar sani game da wayeTiyafilas. Idan shi maibine, kalman nan "mu" a a nan ya hada da shi kenan, amma idan shi ba maibi bane to kalman "mu" baya shafe shi ba.
"mashaidi" mutun ne wanda ya ga faruwan wani abu, bawan kalmar mutun ne da ke bautar Allah ta wurin gaya wa mutane sakon Allah. Za ka iya sa shi a bayyane yanda suka zama bayi na kalmar. AT: "ganin abin da ya faru da kuma bautawa Allah ta wurin shela wa mutane sakon sa"
Kalmar nan "kalma" na nufin hadden sako da ya kunshi kalmomi da yawa. AT: "bayin sako" ko "bayin sakon Allah"
"bincike da kula." Luka yayi binciken ainihin abin da ya faru cikin kula. Mai yiwuwa ya yi magana da mutane dabam-dabam wadanda sun ga abin da ya faru domin ya tabbatar cewa abin da ya rubuta game da al'amarin daidai ne.
Luka ya fadi haka domin ya ba Tiyofilas girma da martaba. Wannan na iya nufin cewa Tiyofilas muhimmin mutum ne a gwamnati. A wannan sashi, ku yi amfani da yadda ana martaba mutane dake da baban matsayi a al'adarku. Wasu mutane sun fi' son su sa gaisuwan da farko su ce, "Zuwa ga...Tiyofilas."
"mai daraja" ko "mai girma"
Ma'anar wannan suna shine "abokin Allah." Yana iya zama kwatancin halin wannan mutumin ne, ko kuwa sunan sa ne na ainihi. Yawancin fasara na anfani da shi a matsayin suna ne.
Mala'ikar yayi anabcin game da aihuwar Yohanna.
Wannan jimla "A lokacin da" ana mora don nuna sabon abu da ya faru. AT: A lokacin da Sarki Hirudus ke mulki akan Yahudiya"
"akwai wani musamman" ko "akwai wani." Wannan hanya ce da ake gabatar da sabon abu a cikin labari. Dubi yadda ana bayyana shi a harshen ka .
A nan an gane da cewa wannan na nufin firistoci ne. AT: "yankin fristocin" ko " kungiyar fristocin"
"wanda suka zo daga zuriyar Abaija." Abaija daga kaƙanin wadannan kungiyan fristocin ne, sa'anan dukkan su daga zuriyar Haruna ne, wanda shine fristi na farko daga Isra'ila.
"Matarsa daga zuriyar Haruna ne." Wannan ya nuna ita da Zakariya daga jerin zuriyar fristoci ne. AT: "Matarsa ma daga zuriyar Haruna ne" ko "Zakariya da Alisabatu matarsa duk daga zuriyar Haruna ne"
"daga zuriyar Haruna"
"a gaban Allah" ko "a ra'ayin Allah"
"dukkan ummurnai da Ubangiji ya bukata"
Wannan kalma ya nuna cewa abin da ke biye anan ya sha bam-bam da abin da ake tsamani. Mutane sunyi tsamani cewa idan sun yi abin da ke daidai, Allah zai barsu su sami 'ya'ya. Ko da shike wadannan ma'aurata sun yi abin da ke daidai, amma basu samu ya'ya ba.
Wanan jimla an mora a masayin alamar canji a labarin daga baya bayanai zuwa ga yan takara.
Ya nuni da cewa Zakariya dă yana haikalin Allah kuma yana nuna cewa wadannan hidimar firist yana bangarin sujada ga Allah.
"da ya kai ga lokacin kungiyarsu" ko "da lokacin kungiyarsu ya kai suyi bauta"
Wannan jumla ta bamu bayanai akan aikin firist.
" hanyar al'ada" ko " hanyar su ta kullum"
Kuri,a anan na nuna alaman dutse da aka wurgo, ko da aka mirgino zuwa kasa domin ya taimake su daidaitawa akan abu. Firistocin sun yaɗɗa da cewa Allah ya jagorance dayawa domin ya nuna masu wane firist ne yake so su zaba.
yakamata firistocin su kona turare karbbaɓe masu kamshi ga Allah kowace assuba da yammanci a bagadi na musamman a cikin haikali.
"Lambar mutane dayawa" ko "Mutane da yawa"
A nan ana nufi filin na kewaye da haikalin. AT: "wajen ginin haikalin" ko " wajen filin haikalin"
"a lokacin da aka shirya." Ba tabbaci cewa wannan safiya ce ko yammaci lokaci domin bayaswa na tiraren wuta.
Wannan kalma tana nuna alamar farkon labarin.
"sa'an nan ya zo mashi" ko " yana tare da Zakariya." A nan ana faɗi cewa mala'ikan na tare da Zakariya, ba wahayi bane kawai.
Wa'inan jimloli biyu na nufin abu daya ne, yana nanata yadda tsoro ya shiga Zakariya.
"sa'adda Zakariya ya gan mala'ikan." Zakariya ya tsorota domin bayannuwar mala'ikan akwai bansoro. Bai aikata laifin komai ba, sa bo da haka bai ji tsoron mala'ikar da kuma hukunci da zai yi masa ba.
An bayyana tsoro anan kaman abin da ya faɗawa ko ya fi-karfin Zakariya.
"Daina gin tsoro na" ko " bai kamata kaji tsoro na ba"
wannan ya nuna cewa Allah zai ba wa Zakariya abin da ya roka. AT: "Allah ya amsa adu'ar ka, kuma zai baka abin da ka roka"
"haifa da maka" ko "haifa maka da"
"Wannan saboda. zai zama mai girma" Zakariya da kuma "sauran" ma'anar su daya ne kuma ana za su yi farin ciki domin Yohanna zai zama "mai girma a gaban Ubangiji." Karshen aya 15 ya gaya yanda Allah ya na so Yohanna ya rayu.
Waddannan kalamai "murna" da kuma "farin ciki" biyun suna ma'anan abu daya kuma ana anfani da shi domin jaddada yanda girmam murnan zai zama. AT: "za ka sami farin ciki sosai" ko "zaka sami farin ciki"
"domin haifuwarsa"
"zai zama mutumin kirki ga Ubangiji" ko "Allah zai maishe shi mutumin kirki"
Za'a iya fadi wannan a kuzarin yanayi. AT: "Ruhu Mai Tsarki zai iza shi" ko " Ruhu Mai Tsarki zai jagorance shi" Ka tabbata bai yi kama da abin da mugun ruhu zai iya yiwa mutum ba.
"tun da yake cikin cikin uwata sa" ko "tun kafin a haife sa"
Idan ya yi kaman ba lisaffa Zakariya a cikin bayanin ba, ana iya fasarar wannan kalman kaman " dayawa cikin ku zuriyar Isra'ila ne" ko " dayawa cikin ku mutanen Allah, na Isra'ila ne." Idan an yi wannan canji, tabatar cewa "Allah su" za a canja ta zuwa " naku (jam'i) Allah."
"su juya" ko "juyo"
Zai yi gaba ya sanar wa mutane cewa Ubangiji zai bayyana a'garesu.
A nan "Fuskar" kalma ce da take nuna hallarar Ubangiji. Wasu lokatai ba a gaya wannan fasarar. AT: "a gaban."
"da ruhu daya da iko da Iliya yake da shi." Kalmar nan "ruhu" wanan ya shafi ko Ruhu Mai Tsarki na Allah ko halayen Iliya kokwa hanyar tunanin sa. Tabatar da cewa kalmar "ruhu" bai ya nufin fatalwa ko mugun ruhu.
"a lallashe ubanni su kuma damu da ya'yansu" ko "'hanyar mayar da dangantakar ubanni da ya'yansu".
Ana magana akan Zuciyan kaman abu ne da za a iya juya shi a wani hanya daban. Wanan na nufin canjin halayen wani zuwa ga abu.
"'tafiya" na nuna hanyar da mutun zai aikata a zaman rayuwarsa. AT: " marasa biyayya zai aikata" ko "marasa biyayya zai zama"
" mutane da basu biyayya"
Ba ambata yadda zasu yi shirin ba. Ana iya karin wannan tabbataccen bayanen. AT: " yin shirin aminche da sakon Ubangiji" ko "yin shirin biyayya na Ubangiji"
"Ta yaya zan san tabbaci da cewa abin da ka fadi zai faru? "A nan,"sani" na ma'anan; kayi koyi da kwarewa, ana shawara ko Zakariya na tambaya na alamar shaida. AT: Abinda za ka iya yi don tabatar mani da cewa wannan zai faru.
An fadi wannan tsaustauci zuwa ga Zakariya. A gaban Jibra'ilu, zuwa kai tsaye daga Allah, ya zama ishashen shaida donmin Zakariya.
"wanda ke bautawa"
Za iya kokarin fadi wannan kamar haka. AT: "Allah ya aiko ni in gaya maka labari"
Kalmar nan "gashi" yana son mu kula da bayanai masu ban-mamaki da ke biye.
Wadannan abu biyu din na ma'anan abi daya ne, ana kuma maimaitasu domin a nanata cikawan zama beben sa. AT: "cikaken ba za ka iya magana ba" ko " ba za ka iya magana ba ko kadan"
"baka gaskanta da abin da na ce ba"
"a lokcin da aka shirya"
Wannan ya nuna alamar canji a labarin, daga abun da ya faru a ciki zuwa wajen haikalin. AT: "cikin lolacin" ko " a lokacin da mala'ikan da Zakariya suna magana".
Watakila wadannan ababai sun faru a lokaci daya ne, kuma alamun Zakariya sun taimake mutane su gane cewa, ya ga wahayi. Zai iya zama abin taimako ga jama'ar ka, domin canjin yaɗɗa za a nuna, AT: "Ya cigaba da yi masu alamu, baya magana. Sun kuwa gane da cewa ya ga wahayi yayen da yake cikin haikali"
A kwatance na farko ya nuna cewa Jibri'lu ya zo gun Zakariya cikin haikali.
Wnnan kalman ya kai labarin zuwa ga lokacin da Zakariya, ya gama bauta.
Zakariya bai zamna a Urshalima ba, inda haikalin yake. Ya komo garinsa.
Wannan kalman "kwanakin nan" ya komar da mu zuwa lokacin da Zakariya na bauta a haikali. Yana yuwa a baiyana wannan kalman a fili. AT: "Bayan da Zakariya ya komo gida daga haikalin da yake bauta"
"matar Zakariya"
"bata bar gidan ta ba" ko " ta zamna ita kadai, a ciki"
Wannan kalman, ya komo damu zuwa asalin labarin da Allah ya bar ta tayi ciki
Wannan bayyani mai kyau ne. Ta yi murna sosai da abin da Ubangiji yayi mata.
"dube ni" kalma ne da yake ma'anan "a bi da" ko "a magance." AT " "ya ɗauke ni mai kirki" ko " ya ji tausayi na"
Wannan ya nuna kunya da ta ji domin bata iya ta samu ya'ya ba.
Mala'ika Jibrilu ya sanar wa Maryamu da cewa za ta zama Uwar wanda shi ne Ɗan Allah.
"a cikin wata na shidda da juna biyu na Alisabbatu." Yana yuwa wajibi ne a fadi wannan a fili idon zai zama rude ga wata ta shidda na shekarar.
Anna iya bayyana wannan cikin aiki. AT: "Allah ya gaya wa mala'ika Jibrilu ya je"
"Shi yare daya ne da Dauda" ko "Shi daga zuriyar Sarki Dauda ne" (UDB)
"rantsuwa" ko "alkawarin yin aure." Iyayen Maryamu sun mika kai domin ta aure Yusufu.
Wannan ya gabatar da Maryamu kaman sabuwar hali ce a labarin.
"Mala'ikan ya zo wa Maryamu"
Wannan yaɗɗa aka saba gaisuwar ne. Yana Ma'anan "Farin ciki" ko "Yi murna."
"ke da kin samu alheri mai yawa!" ko "ke da kin samu kirki na musamman!"
"da ke" kalma ne da yake nuna goyon baya da karbuwa. AT: " Ubangiji yana farin ciki da ke"
Maryamu ta gano wadannan kalamai dabam dabam, amma bata gane dalilin da mala'ikan ya mata wannan gaisuwa na ban mammaki ba.
Mala'ikan ba ya son Maryamu ta ji tsoron bayyanuwar sa, domin Allah ya aiko shi da sako mai kyau.
Kalman "a sami tagomashi" na ma'anan ka zama karbaɓɓe ta wurin wani. Ana iya canza wannan magana domin a nuna Allah kamar mai aikin. AT: "'Allah ya yanke shawarar baki alherin sa" ko "Allah na nuna maki kirkin sa."
Maryamu ta haifi "Ɗa" wanda za a kira shi" Ɗan Allah Madaukaki" (UDB). Yesu mutum ne ɗa haifaffe ta wurim macen mutum, shi kuma Ɗan Allah ne. Waddanan ambataccen labari na niman fasara da hankali sosai.
Ma'anna mai yiyuwa sune 1) " mutane, zasu ce da shi" or 2) "Allah zai ce da shi"
Wannan lakabi mai muhimminci ne na Allah, Ɗa na Allah.
Kursiyin na wakiltan izini sarkin ga mulkin. AT: "ba shi izinin ya yi mulki kamar sarki, kamar yadda kakkanen shi Dauda ya yi"
Mumunar kalman nan "mara iyaka" na nanata cigabawar sa na har'abada. Za a iya faɗe ta da kalma mai kyau. AT: "mulkinsa bashi da iyaka"
Maryamu bata gane yaɗɗa zai iya faruwa ba, bata kuwa yi shakkan zai iya faruwa ba. AT: "Ta yaya haka zai yiwu?"
Maryamu ta yi amfani da kalma mai ladabi, ta nuna bata sami kanta a ayukan jama'i ba. AT: "Ni budurwa ce."
Wannan hanyoyi da Maryamu ta ɗauka, zai fara da zuwan Ruhu Mai-tsarki gare ta.
"zai wuce" ko "zai faru da"
Allah ne "iko" Maryamu ta yi juna biyu da hanyar allahntakan sa duk da cewa i'ta budurwa ce. tabbatar wannan baya nufin saduwar jiki ko juma'i-wannan, abin al'ajibi ne.
"zai rufe ki kamar inuwa"
"Ɗa mai tsarki" ko "jariri mai tsarki"
Ma'anna mai yiwuwa sune 1) "jama'a zasu ce da shi" ko 2) "Allah zai ce da shi"
Duk da cewa Maryamu uwar Yesu mutumce, Allah ya
Wannan lakabi mai muhimminci ne ga Yesu.
Wannan magana na nanata bayanai masu muhimminci akan Alisabatu.
Idan ka na bukatar bayyana dangataka na musamman, mai yiwuwa Alisabatu innan Maryamu ce ko babban inna ta ce.
"ta samu juna biyu da ɗa, duk da cewa ta rigiya ta tsufa sosai" ko "duk da cewa ta tsufa, ta samu juna biyu kuma ta haifi ɗa."tabbar cewa ba a sa Maryamu da Alisabatu sun samu juna biyu a tsufan su ba.
"a watta na shida da juna biyun ta"
"Domin" ko "Wannan na nuna"
Wannan musu mai baki biyu, za a iya bayyana shi a sifar tabbaci. AT: "Wannan na nuna cewa Allah na iya yin kowace abu." Juna biyu na Alisabatu' tabbaci ne da cewa Allah ya iya yin kowace abu-da kuma ba wa Maryamu damar yin juna biyu ba tare da saduwa da mutum ba.
Maryamu ta yi amfani da kalma daya da Mala'ikan don ta nanata muhimmincin abin da ta yi ta wurin yanke shawar mika kai ga Ubangiji.
Zabi kalmar da ya nuna tayi kaskanci da biyyaya ga Ubangiji. Bata yi fahariyar zama bawar Ubangiji ba.
"Bari ya faru da ni" Maryamu na maganar yardawar ta akan abubuwan da zasu faru, da cewa abubuwan da mala'ikan ya gaya mata na hanyar faruwa.
Maryamu ta ziyarce yar'uwar ta Alisabatu wannda zata haifi Yohanna.
Wannan kalman na ma'anan bata tashi kadai ba, amma "tayi shiri." AT: "ta fara" ko "ta yi shiri"
"yanki mai duwastu" ko "yankin duwatsu na Isra'ila"
Ana nufin cewa Maryamu ta gama tafiyar ta kamin ta shigo gidan Zakariya. Za a iya fadi wannan a tsarari. AT "sa'adda ta iso, ta shigo"
Ana amfani da wannan kalma, a nuna sabuwar abin da ta faru a wannan sashi na labarin.
"a cikin Alisabatu"
"motsa a farat ɗaya"
Wadannan kalmomi biyu na ma'anan abu daya ne, kuma za'a iya amfani da ita a nanata farin cikin Alisabatu. Za iya hadda wadannan abu biyun zuwa kalma daya. AT: "faɗa da ƙarfi."
Wannan kalman na ma'anan"ta kara daga muryan ta"
Kalman "cikin mata" na ma'annan "fiye da kowace mace"
An yi magana akan ɗan Maryamu kamar itacen da ke haifa ya'ya. AT: "jaririn cikin ki" ko "jaririn da zaki haifa."
Alisabatu bata nima bayani ba. Tana nuna mamaki da murna da tayi sa'adda uwar Ubangiji ta zo wurin ta. "Abin banmamaki ne uwar Ubangiji ta ziyarce ni!"
Ana nufi Maryamu. "ke, uwar Ubangijina." (UDB)
Wannan kalma na jawo hankalin mu zuwa ga magana na ban-mamaki da Alisabatu ta yi.
"motsa farat daya da farin ciki" ko "juya da karfi domin yana murna sosai"
"mai albarkace ke da kika gaskanta" ko "domin kin gaskanta, za kiyi farin ciki"
"wadannan ababain zasu faru" ko "wadannan ababain zasu cika"
Za a iya bayyana wannan a wani yanayi. AT: "sakon da Ubangiji ya bata" ko "abubuwan da Ubangiji ya gaya mata"
Maryamu ta fara wakar yabo ga Ubangiji maiceton ta.
Maryamu ta yi amfani da kalman a wani yanayi da ta fadi abu daya zuwa kashi biyu kuma a hanyoyi dabam dabam. A fasara wadannan kalma ko kalmomi da su na da ma'anna iri daya zuwa hanyonyi dabam dabam.
Da "zuciya" da kuma "ruhu" yana nufin ruhaniyan mutum. Maryamu tana fadi cewa sujadarta na zuwa daga ciki cikin zuciyar ta ne.
"ta yi farin ciki sosai akan" ko "tayi murna sosai akan"
"Allah, wanda ya cece ni" ko "Allahn da ya cece ni"
"Domin ya"
"Dubi da idon tausayi" ko "kula da"
"talauci." iyalin Maryamu basu da arziki.
Wannan kalman na jawo hankalin mu zuwa ga bayyanainda ke biye.
"yanzu da kuma nan gaba"
"mutanen dukkan zamani"
"Allah, mai iko" (UDB)
A nan "sunan"na nufin dukkan tsifar Allah. AT: "shi"
"Jinkan Allah"
"daga tsara zuwa tsara mai zuwa" ko "cikin dukkan zamani" ko "ga mutannen kowace locaki"
A nan "hannuwansa" kalma ne da yake nuna ikon Allah. AT: "na nuna cewa yana da iko sosai"
"an kore su zuwa hanyoyi dabam dabam"
Wannan kalman na nufin zurfin tunanin su. AT: "tunani a cikin rayuwarsu"
Kursiyi kujera ce da mai mulki na zama, kuma alama ne na ikon sa. Idon an saukar da magada daga kujerar sa, ya nuna bashi da iko yayi sarauta. AT: "Ya dauke iko daga hannun magada" ko "Ya mier da mai mulki ya daina mulki"
Bambanci sakanin wadannan abubuwa dabam dabam din a bayyana shi a fili a cikin fasarar idon zai yiwu.
"'talauci." Iyalin Maryamu basu da arziki.
A hoton kalman nan, muhimman mutane suna gaban da kalilan muhimmanci. AT: "muhimman mutane ya mayad da su kaskantatun mutane" ko "ya bayar da martaba wa mutane da wadansu basu martaba ba"
Bambanci sakanin ayuka dabam dabam dinnan na niman bayyani cikin fili idon zai yiwu.
Ma'anna mai yiwuwa 1) " a ba wa mayuwanta abubuwa masu kyau su ci" ko 2) "ba wa mai nema abubuwa masu kyau."
"Ubangiji ya yi taimako"
Idon mai karatu ya rikice da mutum mai suna Isra'ila, za a iya fasarar shi kamar "bawar sa, jiha na Isra'ila" ko "Isra'ila, bawar sa."
"domin a"
Allah baya mantuwa. Lokacin da Allah "ya tuna," kalma ne da yake ma'annan Allah ya aikata alkawalin sa na farko.
"kamar yadda yayi wa kakkanen mu alkawali zai cika." Wannan kalma ya ba da shahareren bayani akan alkawalin Allah zuwa Ibrahim. AT: "domin yayi alkawalin jinkai wa kakkanenmu" (Dubi:
"Zuriyar Ibrahim"
"Maryamu ta koma gidanta(Maryamu)" ko "Maryamu ta koma gidanta na ainihi"
"haifi jaririn ta"
"Makwabta da 'yan'uwan Alisabatu"
"yana yi mata kirki"
"Alokacin da jaririn na kwana ta takwas" ko "A rana ta takwas bayan haifuwar jaririn"
Wannan biki ne da ake yi kullum, in da mutum daya ke yiwa jariri kaciya da kuma aboƙansa su kan yi murna tare da iyalin. AT: "domin bikin kaciyar jaririn"
"Da zasu ba shi suna" ko "Sun so su ba shi sunar." Wannan ainahin al'adar su ne.
"sunan ubansa"
"da wancan suna" ko "da irin sunan"
Wannan na nufin mutane wadanda su na nan a buki na kaciyan.
"motsi." Kokwa Zakariya bai iya ji ba da kuma yin magana, kokwa mutanen suna zaton cewa shi kurma ne.
"ga uban jaririn"
"wane suna ne Zakariya ya so a ba wa jaririn"
"Mai yiwuwa zai zama da taimako a fadi yadda Zakariya " yi tambaya,"da yake bai iya magana ba. AT: "Ubansa ya yi amfani da hanuwarsa ya nuna wa mutane ya son su ba shi allon rubutu"
"abin rubutu"
"mamaki sosai" ko "ji mamaki"
Hotunan kalamai biyun nan ya nanata tare yadda Zakariya ya yi magana nan da nan.
Ana iya bayyana wannan kalman cikin sifar aiki. AT: "Allah ya bude bakinsa da kuma sake harshensa"
Dukan wadanda suke zama kewaye da Zakariya da Alisabatu sun ji tsoro." Zai iya zama da taimako a bayyana a filli dalilin firgitar su. AT: "Dukan wadanda suke zama kewaye da su suna tsoron Allah wanda ya yi wa Zakariya wannan"
Wannan baya nufin makwaptan su na kusa kawai ba amma zuwa ga dukan wadanda suke zama a yankin.
Kalman "su" a nan na nufin ababai da suka faru.
Sashen nan "wanna labarin ya bazu" misali mutane ne da ke magana game da su. AT: "Dukan wanna zancen mutane ne suka yi maganarsu a cikin dukan dukan kasar duwtsun Yahudiya" ko "Mutanea dukan kasar duwatsun Yahudiya sun yi maga a kan wanna zancen"
"Dukan waɗanda su ji wanna zancen"
Ana maganar tunani a kai a kai a kan abubuwa sa suka rigaya su ka faru kamar sa waɗanna abuwa ne da sauki a zuciyarsu. AT: "tunani a hankali game da wanna zancen" ko "tunani da yawa game da abubuwan da suka faru"
"zuciya. su ka tambaya"
"Wane irin mutum mai girma ne wannan jaririn zai zama?" Yana kuma yiwuwa wannan tambayan yakamata ya zama bayani na mamakin su akan abin da suka ji game da jaririn. AT: "Wane mutum mai girma ne wannan yaro zai zama!"
Kalman "hannun Ubangiji" yana nufin ikon Ubangiji. "Ikon Ubangiji na tare da shi" ko "Ubangiji yayi aiki cikinsa da iko"
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "Ruhu Mai-tsarki ya cika mahaifinsa Zakariya"
Mahaifin Yohana
Dubi yadda aka saba gabatar da hanyoyi dake kai tsaye a kabilar ku. AT: "anabci, ya ce" ko "anabci, kuma ga abin da ya fadi"
"Isra'ila" anan na nufin jihar Isra'ila. Dagantaka tsakanin Allah da Irsra'ila ana iya bayyana shi akan hannya. AT "Allahn da yayi mulkin Isra'ila" ko "Allahn da Isra'ila suke masa sujada"
"Mutanen Allah"
kahon dabba alamar ikon sa ne ya tsare kansa. An yi magana akan Maiceto anan kaman shi ne kaho da yake da iko ya cece Isra'ila. AT: "Wanda yana da iko ya cece mu"
"gidan" Dauda anan na wakilin iyalinsa, takamaimain zuriyar sa. AT: "cikin iyalin bawansa Dauda" ko "wanda shi daga zuriyan bawansa Dauda"
"kamar yadda Allah ya fada"
Maganar Allah ta wurin annabawansa na kwatanta cewa Allah na sa annabawan su faɗi abin da yake so su fada. Za'a iya bayyana ikon Allah. "ya sa annabawan sa tsarkaka su ce"
Za a iya bayyana "cece" da "ceto" ko "ceta." AT: "da daɗewa). Za ya cece mu daga magabtan mu"
Wadannan kalamu biyu na nufin abu ɗaya da aka sake nanata wa don nuna yadda magabtan su suna gaba dasu sosai.
Kalman "hannu" na nuna ikon da miagun mutane ke amfani akan mutanen Allah. "iko" ko "iko."
"a nuna jinkai zuwa ga" ko "su yi ayuka bisa ga jinkansa zuwa ga"
A nan kalman nan "tuna" na nufin a miƙa kai ko cika wani abu.
Wadannan kalamai biyu suna nufin abu daya ne. Su na sake bayyana muhimmancin alkawalin Allah wa Ibrahim.
"ya zama mai yiwuwa garemu"
zai iya zama da taimako a canja yanayin wadannan kalaman. AT: "cewa zamu bauta masa ba tare da tsoro ba bayan ya cece mu daga ikon miyagu."
a nan "hannu" na nufin ikon mutum. Za 'a iya fadin wannan a fili. AT: "daga ikon miƙiyan mu"
Wannan na nufin tsoron maƙiyan su. AT: "ba tare da jin tsoron maƙiyan mu ba"
Za a iya ƙara fadin wannan. Ma'ana mai yuwuwa sune 1) za mu mu bauta wa Alla a tsarkar da adallun hanyoyi. AT: "yin abuwan tarki da adalci" ko 2) za mu zama masu tsarki da adalci. AT: "zama da tsarki da adalci"
Wannan kalma ne da ke nufin "a halararsa"
Zakariya ya yi amfani da wannan kalma domin ya soma wa yaronsa magana. Kana iya samun hanya mai kama da wannan magana 'a kabilar ka.
Mutane zasu gane cewa shi annabi ne. Ana iya fadi wannan cikin sifar aiki. AT: "mutane zasu sani cewa kai annabi ne"
"wanda ke bauta wa Madaukaki." Wannan na nufin Allah: "wanda ke wa Allah Madaukaki Magana."
Wannan na nufin cewa yahayya zai shirya mutane su ji, su kuma gaskanta saƙon Ubangiji.
"bada ilimi" na nufin koyarwa. za a iya yin bayanin "ceto" da "gafartawa" kamar "ceta" da "gafara." AT: "ya koya wa mutanen sa ceto ta wurin gafaran zunubansu" ko "ya koya wa mutanen sa yadda Allah yake ceton mutanen sa ta wurin gafaran zunubansu" (Dubi:
Zai zama da taimako a fadi cewa jinkan Allah na taimakon mutane. AT: "domin Allah mai tausayi da jinkai ga mu"
Haske a nan kalma ce da ake amfani da ita akai akai a yi magana akan abi daya kaman abu dabam dabam ne wa gaskiya. A nan, ruhaniya na gaskiya Mai-ceto zai tanada an yi magana akai kaman hasken rana dake haskaka duniya ne.
"ba da ilimi ga" ko "ba da haske ta ruhaniya ga"
Duhu anan kalma ce da ake amfani da ita a yi magana akan abi daya kaman abu dabam dabam ne na rashin ruhaniya na gaske. Anan, mutane da basu da ruhaniya na gaskiya ana magana akan su kaman suna zama cikin duhu ne. AT: "mutanen da basu san gaskiya ba"
Wadannan kalamai biyu suna aiki tare domin su nanata zurfin ayuka na duhun mutane kafin Allah ya nuna masu jinkai.
Inuwan na wakilcin abin da na hanyar faruwa akai akai. A nan, na nufin kusance mutuwa. AT: " waddanda suna hanyar mutuwa"
A nan "kiyayewa" na nufin loyarwa, da "hanyar salama" ya ɗauki matsayin dukan cikin mutum. AT: "koya mana yadda za mu yi zama tare da Allah"
"zama ƙosasshe cikin ruhaniya" ko "karfafa a zumuntarsa da Allah"
"zauna wa cikin jeji." Luka bai fadi ko a shekara nawa Yohana ya fara zama cikin jeji ba.
Wannan bai nuna alamar wurin tsayawa ba. Yohana ya chigaba yin rayuwa cikin jeji har bayan da ya fara wa'azi wa jama'a a fili.
"da ya fara wa'azi cikin jama'a a fili"
Anyi amfani da wannan anan a matsayin "lokaci" ko "lokaci da abu ya faru."
"Mashaidan" sune waɗanda suke tare da Yesu daga farkon al'amarin sa.
Sun rubuta bi da bi ko labarin abin da Yesu ya yi.
Ya so Tiyofalas ya san gaskiya akan abubuwa da ya koyar.
Allah ya duba su kamar masu adalci domin sun yi biyayyan dokokinsa.
Basu same yara ba domin Alisabatu ta kasa haifa yaro. Yanzu ita da Zakariya sun tsufa sosai.
Zakariya na hidiman firist.
Ya kone turare
Mutanen suna tsaya a waje a cikin tsakar gida su yi adu'a.
Mala'ikan Ubangiji ya bayyana ma Zakariya a cikin haikali.
A lokacin da Zakariya ya gan malai'kan, ya zama da tsoro sosai.
Malai'kan ya gaya ma Zakariya kada ya ji tsoro kuma wei matan sa Alisabatu ta same da. Sunan dan zai zama Yahaya.
Malai'kan ya ce Yahaya zai juyo 'ya'yan Isra'ilawa dayawa ga Ubangiji Allahnsu
Mutane da an shirya ma Ubangiji za su zama a shiryeyu.
Sunan Malai'kan Jibra'ilu kuma ya saba tsaya a kasancewar Allah.
Zakariya ba zai iya magana ba sai an haifi yaron.
Budurwa da suna Maryamu, wanda aka ba da ita ga Yusufu, na zuriyar Dauda.
Malia'kan ya ce wai Maryamu zata yi ciki.
Za ba ma yaron suna Yesu kuma zai yi mulki bisa zuriyar Yakubu har abada, mulkinsa ba karshe.
Malai'kan ya ce Ruhu Mai Tsarki zai sauko akan Maryamu kuma ikon Madaukaki zai lullube ta.
Malai'kan ya ce za'a kira yaron Dan Allah.
Ba kome.
Jinjirin ya yi tsalle da murna a mahaifa.
Alisabatu ta ce Maryamu da jinjirin ta na da albarka.
Zazu cika alkawarin da Allah ya yi da Ibrahim da kuma zuriyar sa wanda zai yi masu jin kai da kuma taimake su.
Zakariya.
Zakariya ya rubuta "Sunan shi Yahaya"
Nan da na bayan ya rubuta sunan yaron, Zakariya ya yi magana da kuma yabon Allah.
Sun gane cewa hanun Ubangiji na kan sa.
Allah yanzu ya yi hanya don ya yantacce da mutanen sa.
Yahaya zai taimake mutane sun yanda zasu same ceto ta gafarar zunubansu.
Yahaya ya yi girma a da kuma zauna a jeji.
1 Ananan cikin kwanakin, sai Kaisar Augustas ya yi shela ya umarta a kidaya dukan mutane da ke zaune a cikin duniya. 2 Wannan itace kidaya ta farko da aka yi lokacin da Kiriniyus yake mulkin Suriya. 3 Sabili da haka, kowa ya koma garinsa domin a yi masa rijista domin kidayan. 4 Yusufu kuma ya tashi ya bar birnin Nazarat zuwa garin Baitalami da ke Yahudiya, wanda ake kuma kira birnin Dauda, domin shi daga zuriyar iyalin Dauda ne. 5 Ya je can ya yi rijista tare da Maryamu, wadda yake tashi tana kuma da juna biyu. 6 Ya zama sa'adda suke can, lokaci ya yi da za ta haifi danta. 7 Ta haifi da, dan farinta kuwa, ta nade shi da kyau da 'yan tsummoki. Ta sa shi cikin wani kwami na dabbobi, gama babu daki dominsu a masaukin. 8 A cikin wannan yankin, akwai makiyaya wadanda suke zama a sarari suna tsaron garken tumakinsu da dare. 9 Nan da nan, sai mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare su, daukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, sai suka figita kwarai. 10 Sai mala'ikan ya ce masu, "Kada ku ji tsoro, domin na kawo maku labari mai dadi da zai kawo murna da yawa ga dukan mutane. 11 Yau an haifi maku mai ceto a cikin birnin Dauda! Shine Almasihu Ubangiji! 12 Wannan itace alama da za a ba ku. Za ku ga dan jariri nade cikin 'yan tsummoki kwance cikin kwamin dabbobi." 13 Nan take, sai ga babban taro daga sama tare da mala'ikan suna yabon Allah, suna cewa, 14 "Daukaka ga Allah daga bisa, bari salama ta kasance a duniya tsakanin mutanen da ya ke jin dadinsu." 15 Ya zama sa'adda mala'iku suka bar su zuwa cikin sama, sai makiyayan su ka ce wa junansu, "Bari mu je Baitalami mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya nuna mana." 16 Su ka yi hamzari suka tafi can sun iske Maryamu da Yusufu, suka ga jaririn kuwa kwance a cikin kwamin dabbobin. 17 Bayan da sun ga wannan, suka gaya wa mutane abinda aka gaya masu game da wannan yaro. 18 Dukan wadanda su ka ji, su ka yi mamaki kwarai game da abin da makiyayan su ka gaya masu. 19 Amma ita Maryamu ta ci gaba da tunani akan wadanan abubuwa da ta ji, tana tunani mai zurfi a cikin zuciyarta. 20 Makiyayan suka koma suna ta daukaka da yabon Allah domin dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, dadai da yadda aka gaya masu. 21 Da ya kai kwana takwas, lokacin da za a yi wa jaririn kaciya, sai aka rada masa suna Yesu, sunan da mala'ikan ya bashi kamin a yi cikinsa. 22 Da kwanakin tsarkakewar su ya wuce bisa ga shari'ar Musa, Yusufu da Maryamu suka kawo shi cikin haikali a Urushalima dominsu mika shi ga Ubangiji. 23 Kamar yadda aka rubuta a dokokin Ubangiji, "Za a kira duk da na fari kebabbe ga Ubangiji." 24 Suka kuma zo su mika hadaya bisa ga yadda aka fada a shari'ar Ubangiji, "Kurciyoyi biyu ko 'yan tantabaru biyu." 25 Ga shi akwai wani mutum a Ushalima mai suna Siman. Wannan mutum adali ne kuma mai ibada. Yana jiran mai ta'aziyar Isra'ila, kuma Ruhu Mai-sarki na bisansa. 26 An kuma bayyana masa ta wurin Ruhu Mai-tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kristi na Ubangiji. 27 Wata rana Siman ya zo cikin haikali ta wurin jagorar Ruhu Mai-tsarki. Da iyayen suka kawo yaron ciki, wato Yesu, domin su cika sharudan da shari'ar ke bukata, 28 sai Siman ya karbe shi cikin hanuwansa, ya yabi Allah ya ce, 29 "Yanzu bari bawanka ya tafi da salama, Ubangiji, bisa ga kalmarka. 30 Domin idanuna sun ga cetonka, 31 wanda ka shirya a gaban dukan mutane: 32 Haske ne na wahayi ga al'ummai, kuma daukakar mutanenka Isra'ila." 33 Mahaifin yaron da Mahaifiyarsa, sun yi mamaki kwarai domin abubuwan da aka fada akansa. 34 Sai Siman ya albarkace su ya ce wa uwatasa Maryamu, "Ki ji da kyau, wannan yaro zai zama sanadiyar faduwa da tashin mutane dayawa a Isra'ila, kuma alama wadda ake kushen ta. 35 Kuma takobi zai tsaga zuciyar ki yadda tunanin mutane za ya bayyana." 36 Wata annabiya mai suna Annatu ta na nan wurin. Ita diyar Fanuyila ce daga kabilar Ashiru. Ta riga ta manyanta a shekaru sosai. Ta kasance da maigidanta shekaru bakwai bayan auren ta, 37 sannan ta yi zama gwambranci na shekaru tamanin da hudu. Ba ta taba barin haikali ba, tana ci gaba da yi wa Ubangiji sujada, dare da rana. 38 A dadai lokacin nan, ta hau zuwa wurinsu ta fara yi wa Allah godiya. Ta gaya wa dukan wadanda ke jiran fansar Urushalima. 39 Da su ka gama komai da aka bukace su suyi bisa ga tafarkin shari'ar Ubangiji, sai suka koma Galili, zuwa birninsu, Nazarat. 40 Yaron kuma ya yi girma ya zama da karfi, yana karuwa da hikima, alherin Ubangiji kuma yana kansa. 41 Iyayensa sukan tafi Urushalima kowacce shekara domin idin ketarewa. 42 Da yana shekara goma sha biyu, suka sake haurawa daidai lokacin idin a al'adance. 43 Bayan da sun cika dukan kwanakin idin, sun fara dawowa gida. Amma dan yaron Yesu ya jinkirta ya zauna a Urushalima, kuma iyayensa basu sani ba. 44 Suna tsammani yana tare da sauran mutane da suke tafiya tare, sai suka yi tafiya na kwana daya. Suka fara neman sa a cikin danginsu da abokansu. 45 Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima suna cigiyar sa a can. 46 Ya zama bayan kwanaki uku, su ka same shi a cikin haikali, yana zama a tsakiyar malamai, yana sauraron su yana kuma yi masu tambayoyi. 47 Dukan wadanda suka ji shi suna ta mamakin fahimtar sa da amsoshin sa. 48 Da suka gan shi, suka yi mamaki kwarai. Mahaifiyarsa ta ce masa, "Da na, don me ka yi mana haka? Ka ji, mahaifinka da ni muna ta neman ka rai a bace." 49 Ya ce masu, "Don me kuke nema na? Ba ku sani cewa dole in kasance a gidan Ubana ba?" 50 Amma ba su gane abin da yake nufi da kalmomin nan ba. 51 Sa'annan ya koma gida tare da su zuwa Nazarat yana kuma masu biyayya. Mahaifiayarsa kuma ta ajiye dukan wadannan abubuwa a zuciyarta tana yin tunani akansu. 52 Amma Yesu ya ci gaba da hikima da girma, ya kuma karu da tagomashi wurin Allah da mutane.
Wannan ya ba da shaharenren labari domin nuna dalilin da ya sa Maryamu da Yusufu su ka tafi lokacin a haifuar Yesu.
Wannan kalma na nuna alamar sabuwar sashin labarin.
Ana amfani da wannan kalma domin nuna cewa wannan ne labari na farko. Idan kabilar ka tana da hanyar fara labari, kana iya amfani da wannan. Wasu suran basu haɗ da kalman nan ba.
"Sarki Augustas" ko "Daula Augustas." Augustas shine daula na farko a kasan Romawa.
Mai yiwuwa mesinjojin ne suka dauka wannan umurni a ƙasan gabadaya. AT: "umurce masinjojin da shela"
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "cewa su rubuta sunayen dukan mutane dake duniya" ko "su ƙirga dukan mutane da ke duniya, sukuma rubuta sunayen su"
"a sashin duniya da gwamnatin Romawa ne ke mulki" ko "a kasan da daulan Roma ne ke mulki"
An zabi Kiriniyus ne ya zama gwamnan Syria.
"kowa da kowa suka soma tafiya" ko "kowa na tafiya"
Wannan na nufin garin da kaƙƙanen mutane suka yi rayuwa. Mai yiwuwa mutane sunyi rayuwa a gari dabam dabam. AT: "garin da kaƙƙanen mu sunyi rayuwa"
"a samu sunayensu a rubuce cikin rijistan" ko "domin a saka su cikin ainihin kirgen.
A nan ana gabatar da Yusufu kaman sabon mutum ne a labarin.
Wannan shahareren bayani ne akan muhinmincin Baitalami. Ko da yake karamar gari ce, a năn aka haifi Sarki Dauda, kuma anyi anabci cewa a năn za'a haifi Mai Ceto. AT: "wanda ake kira birnin Sarki Dauda"
"domin Yusufu ɗan zuriyar Dauda ne"
Wannan na nufin ya je gaban hukumomin su domin su iya hada kirgen da shi. Nemi kalman da gwamnatin suna amfani da shi domin kirgen.
Maryamu tayi tafiyan da Yusufu daga Nazarat. Mai yiwuwa mataye ma na biyan harajin. Haka kuma Maryamu na bukacin tafiya domin ayi mata rijista.
"budurwarsa" or "wanda aka masa alkawalin ta." Bisa ga dokan su ana ganin budurrwa da saurayi da sukayi alkawali ma'aurata ne. Amma da babu saduwa ta jiki a saƙaninsu.
Wannan yayi magana akan haifuwar Yesu da kuma sanarwa daga mala'iku zuwa ga makiyayin tumakin.
Wannan kalma na nuna alamar abin da zai faru năn gaba cikin labari.
"sa'adda Maryamu da Yusufu suna Baitalami"
"lokaci ya yi da zata haifi danta"
Wannan hanya na kulum ne daa uwa tana kare dakuma kula da jinjirin ta a wancan al'ada. AT: "nade bargo mai kauri kewaye da shi" ko "nade shi cikin bargo mai dadi"
Wannan wani irin kwali ne kokwa tsaiko da mutane ke saka hatara kokwa abinci dabam dabam wa dabbobi suci. Mai yiwuwa ya kan zama da tsabta da kuma kila ya samu abu mai laushi da kuma busheshe kamar hatara a ciki da ke kama da matashin fata domin jinjirin. Sau da yawa akan ajiye dabbobi kusa da gidaje domin kiyayewa da kuma ciyad da su da sauki. Maryamu da Yusufu sun zamna cikin daki da ake amfani wa dabbobi.
"babu wuri zama dominsu a cikin dakin baki." Wannan zai iya yiwuwa domin mutane dayawa sun je Maitalami domin rijista. Luka ya kara wannan kaman shahareren bayani ne.
"Sai mala'ika daga Ubangiji" ko "Sain mala'ika wanda yama Ubangiji bauta"
"bayyana wa makiyayin tumakai"
Tushin haske mai walkiya daukakar Ubangiji ne, wanda ya bayyana a lokaci daya da mala'ikan.
"daina jin tsoro"
"da zai saka dukan mutane murna sosai"
Wasu sun gane wannan a nufin ga mutanen Yahudawa ne. Wasu kuma sun gane ta a masayin dukan mutane ne.
Wannan na nufin Baitalami ne.
Akan iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "Allah zai baku wannan alama" ko "za ku gan wannan alama daga Allah"
"tabbaci." Kokwa wannan zai iya zama alama domin a tabbatar da cewa abin da mala'ikan ke fadi gaskiya ne, ko zai iya zama alaman da zai taimake makiyayin tumakin su gane da jinjirin.
Wannan hanya na kulum ne daa uwa tana kare dakuma kula da jinjirin ta a wancan al'ada. AT: "nade bargo mai kauri kewaye da shi" ko "nade shi cikin bargo mai dadi"
Wannan wani irin kwali ne kokwa tsaiko da mutane ke saka hatara kokwa abinci dabam dabam wa dabbobi suci.
Kalman nan "runduna sama" zai iya nuna cewa zahiri wannan runduna mala'iku ne, ko zai iya zama karin magana a kan shiryayyen kungiyar mala'iku. AT: "babban Kungiyar mala'iku daga sama"
"suna yabon Allah"
Ma'ana mai yiwuwa sune 1) "Ba da girma ga Allah mafi ɗaukaka" ko 2) "Ba da girma mafi ɗaukaka ga Allah."
"bari mutane dake duniya wadanda Allah ke jin dadinsu su sami salama"
Ana amfani da wannan kalma domin nuna sabon abin da zai faru cikin labarin akan abin da makiyayan sunyi bayan tafiyan mala'ikun.
"daga makiyayan"
"wa junansu"
Tun da makiyayin yayi maganan akan kowani dayan, harsunan/yaranruka da suna da shi a wannan fanni sai suyi anfani da shi anan.
"Bari mu" (UDB)
Wannan nufin zuwa ga haifuwar jinjirin ne, amma ba bayyanuwar mala'ikun ba.
Wannan wani irin kwali ne kokwa tsaiko da mutane ke saka hatara kokwa abinci dabam dabam wa dabbobi suci.
Akan iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "abin da mala'iku suka gaya wa makiyayan"
"jinjirin"
Akan iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "abin da makiyayan suka gaya masu"
Ajiya wani abu ne mafi anfani ko ɗaraja. Maryamu ta gane abin da aka sanar da ita game da ɗanta yana da ɗaraja kwarai. AT: "tunawa da su a hankali" ko "tunawa da su a farinciki"
"makiyayam sun coma wurin tumakinsu"
Wadannan suna da kamani sosai da kuma nanata yadda suka yi murna aka abin da Allah yayi. AT: "magana akai dakuma yabon girman Allah"
Wannan kalma na nuna wucewar lokaci kafin wannan sobuwar abin.
"a kwana ta takwas bayan haifuwarsa" ko "yana kwana ta takwas"
Yusufu da Maryamu sun rada masa sunarsa.
Akan iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "sunan da mala'ikan ya kira shi"
wannan yana nuna wucewar lokaci kafin sabon taron
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "lambar kwanaki da Allah ke bukata"
"domin su zama da tsabta." Zaku iya bayyana aikin Allah. AT: "domin Allah ya sake yadda su zama masu sabta'
"A mika shi wurin Ubangiji" ko "su mika shi gaban Ubangiji." wannan wani biki ne don tabbatar da da'awar Allah game da ɗan fari a 'ya'ya maza.
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "Kamar yadda Musa ya rubuta" ko "Sunyi haka domin musa ya rubuta"
"bude mahaifa" kalmar alama ce da yake nufin ga jinjiri na fari da ya fito daga cikin ciki. Wannan nufin duk da dabbobi da kuma mutane ne. AT: "Dukan 'ya'ya na fari wanda na maza ne" ko "Dukan ɗa na fari"
"abin da dokar Ubangiji ya kuma ce." Wannan wani guri dabam ne cikin dokan. Na nufin dukan ɗa na fari, ko ɗa na fari ko ba ɗa na fari ba.
Kalman nan "ga ma" na faɗakar da mu zuwa wani sabon mutum a cikin labarin. Mai yiwuwa kabilar ka na da hanyar yin wannan.
Ana iya bayyana waɗanan kalmomi karmar aiki. AT: "ya aikata abin da yake faranta wa Allah rai, ya kuma yi biyyaya ga dokokinsa"
Wannan na nuna ta'aziyar Isra'ila sa'adda Mai ceto ya bayyana. AT: wanda zai ta'azantar da Isra'ila"
"Ruhu Mai Tsarki na tare da shi." Allah na tare da shi a hanya ta musamman, ya nuna mashi hanya, ya kuma bashi hikima dakuma cikin rayuwarsa.
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "Ruhu Mai Tsarki ya riga ya nuna masa" ko "Ruhu Mai Tsarki ya riga ya fadi masa"
"sai ya ga Ubangiji Mai ceto kafin ya mutu"
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki: "Kamar yadda Ruhu Mai Tsarki ya bi da"
Wasu kabilu zasu iya ce "ya je"
"cikin ginin haikalin." Firistoci ne kawai suna iya shigan ginin haikalin.
"Iyayen Yesu"
"ka'idar shari'ar Allah"
"Ni bawanka ne, bari in tafi da salama." Saminu yana nufin kansane.
Kalma ce da ake amfani da ita a ma'anan "mutuwa"
"kamar yadda ka ce" ko "domin ka fada, zan kuma yi"
Kalmomin nan na nufin, " na gani da kaina" ko "ni, da kaina, na gani"
Wannan kalman na nufin mutumin da zai kawo ceto - Yesu da yake jinjiri - wanda Saminu ke rike da shi. AT: "Mai ceto wanda ka turo" ko " wanda ka tura ya yi ceto"
Ya dangantaka ga yanda ka yi fasarar kalman da ya wuce, za'a iya canja wannan zuwa "wanda ka."
"wanda ka shirya" ko " ka sa ya faru"
Wannan na nufin cewa yaron zai taimake mutane su fahimci nufin Allah.
zai iya zama wajibi ne a faɗi abin da za'a bayyana. AT: "da zai bayyana gaskiyar Allah"
"zai zama dalilin da daukakar mutanen ka na Isra'ila zai zo"
Ana iya bayyana wannan cikin siffar aiki. AT: "abubuwan da Saminu ya fadi game da shi"
"ya fadi waMaryamu, Uwar jaririn ." Tabbatar da cewa bai yi kamman Maryamune Uwar Saminu ba.
Kalmomin nan "fadiwa" da kuma "tashiwa" ya bayyana juyewa daga hanyar Allah dakuma zuwa kusa da Allah. AT: "wannan jariri zai saka mutane dayawa a Isra'ila su fadi daga hanyar Allah ko su zo kusa da Allah"
"zai kuma zama sako daga Allah wanda mutane dayawa zasu ki"
Wannan karin maga ya bayyana surfin bakin cikin da Maryamu zata ji. AT: "Bakin cikin ki zai iya zama kaman takobin da ya tsaga ziciyar ki"
"zukata" na nufin zuwa ga mutane ne. AT: "tunannin zukata dayawa zasu bayyana"
Wannan na gabatar da sabon mutum cikin labarin.
"Fanuyila" sunan mutum na miji ne.
"shekaru 7
"bayan da ta aure shi"
Ma'ana mai yiwuwa sune 1) Ta yi zaman gwamranci na shekaru tamanin da hudu ko 2) ita gwamrurace harna shekaru tamanin da hudu.
zai iya yuwa karin bayyani ne kame da yawan lokaci da ta shafe a haikali ya iya nuna bata bari ba. AT: "ko da yaushe a haikali" ko "sau da yawa a haikali"
"ta wurin kin abinci na lokatai dayawa da kuma ta wurin adu'oi sosai"
"kusance su" ko "je wurin Yusufu da Maryamu"
A nan, anyi anfani da kalman nan "fansa" don a nufi mutumim da zai yi shi. AT: "wanda zai fanshe Urushalima" ko "mutumin da zai kawo albarkun Allah da kuma tagomashi zuwa ga Urushalima"
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "da sheri'ar Ubangiji ke bukata suyi"
Wannan kalma na nufin sunyi rayuwa cikin Nazarat. Yi tabbacin cewa bai yi kaman sune da birnin ba.
"karuwa da hikima sosai" ko "koyon abin da ke hikima"
"Allah ya albarkace shi" ko "Allah na tare da shi a hanya ta musamman"
Wannan shahareren bayyani ne.
"iyayen Yesu"
Urushalima na fiye da kusan kowane wuri a Isra'ila, haka kuma ba wani abu bane Isra'ilawa suyi maganan zuwa Urushalima.
"a daidai lokacin" ko "yadda suke yi a kowace shekara"
"Lokacin da murnan bikin idin ya wuce gabadaya" ko "Bayan murnan bikin idin na dukan kwanakin"
Wannan wani suna ne kuma domin idin ketarewa, da shike bai haɗa da cin abincin biki ba.
"Suna tunanin"
"suka yi tafiyan kwana daya" ko "suka kuma yi yadda mutane ke tafiya a kwana daya"
Wannan na nufin a filin kewaye da haikalin. Firistocin ne kawai ake bari acikin haikalin. AT: "a kewayen haikalin" ko "a haikalin"
Wannan baya nufin daidai tsakiyar ba ne. ya na nufin "tsakanin" ko "tare da" ko "kewaye da."
"malamen addini" ko "wanda suke koyas wa mutane game Allah"
Basu iya gane yadda yaron shekara goma shabiyu wanda bashi da illimi na addini zai iya bada amsa sosai haka ba.
"yawan ganewarsa" ko "cewa yana da ganewa sosai game da Allah"
"yawan amsoshi masu kyau da ya basu" ko "cewa ya amsa tambayoyin su da kyau"
"Lokacin da Maryamu da Yusufu suka same Yesu"
Wanan ba kaikaitacce tsautawa bane domin bai tafi tare da su ba garin comowa gida. AT: "bai kamata da ka yi wannan ba!"
Sau dayawa, akan yi amfani da wannan kalma domin nuna farkon sabuwar abu ko abu mai muhinminci. Ana iya amfani da shi domin nuna inda aikin ƙan fara. Idan kabilar ka tana da kalman da ake amfani da ita ta wannan hanya, yi tunanin ko alhali, za iya amfani da ita anan.
Yesu yayi amfani da tambayoyi guda biyu don ya tsauta wa iyayensa da lafazi mai taushi, ya kuma faɗa masu da cewa manufar zuwarsa a duhunce yake garesu. AT: "Bai kamata ku damu da ni ba."
Yesu yayi amfani da wannan tambaya na biyu domin yayi kokarin faɗa masu cewa yakamata iyayensa su sani game da nufin, wanda Ubansa ya turo shi.
A shekara ta 12, Yesu, Ɗan Allah, ya gane cewa Allah ne Assalin Ubansa
Ma'ana mai yiwuwa sune 1) "a gidan Ubana" ko 2) "game da aikin Ubana." ko dai, lokacin da Yesu yace "Ubana" yana nufin Allah ne. Idan yana nufin "gida ne," wato yana nufin haikalin ne. Idan yana nufin "aiki ne," yana nufin aikin da Ubangiji ya bashi ya yi. Amma, da yake aya na gaban ya fada cewa iyayensa basu gane abinda yake gaya masu ba, zai zama da kyau in ba yi bayyanin sa sosai ba.
"Yesu ya koma gida tare da Maryamu da Yususfu"
"masu biyayya" ko "yana masu biyayya kullum"
A nan "zuciya" na nufin "zuciyar mutum" ko tunanin mutum. AT: "tayi tunani cikin natsuwa game da dukan waddanan ababubuwa.
"ya zama da karfi da kuma hikima." Waddanan na nufin girma cikin hankali da kuma jiki.
Wannan na nufin girma ta jiki a kuma ruhaniya. Ana iya bayyana wannan dabam-dabam. AT: Ubaniji ya albarkace shi sosai, kuma mutane sun so shi sosai."
Mutanen sun je garinsu su yi regista.
Yusufu da Maryamu sun je Baitalami domin Yusufu daga zuriyar Dauda
A lokacin da an haifa yaron, Maryamu ta ajiye shi a wurin da dabbobi suna ciyar.
Malai'kan ya bayyana ma makiyayen wanda suna kula da dabbobin su.
Makiyayen sun ji tsoro.
Malai'kan ya gaya ma makiyayen wai an haifa mai Ceto, wanda shi ne Yesu Ubangiji.
Makiyayen sun je Baitalami su gan yaron da an haifa.
An yi wa Yesu kaciya a kwana na takwas bayan haihuwan sa.
Sun kawo shi haikali su mika shi ga Ubangiji su kuma yi hadaya bisa ga abin da aka fada a dokokin Musa.
Ruhu Mai Tsarki ya bayyana ma Saminu cewa ba zai mutu ba sai ya ganAlmasihun Ubangiji
Saminu ya ce wai Yesu zai zama haske mai bayyana gaskiya wa alummai da kuma daukakar jama'ar Allahn Isra'ila.
Saminu ya ce takobi zai huda zuciyar ta
Hannatu ta dara gode wa Allah da kuma ta gaya ma kowa akan yaron.
Yesu ya yi girma ya kuma zama da karfi, yana mai mutukar hikima, da kuma alherin Allah yana tare da shi.
Basu sani ba domin suna zaton yana a rukuni da na tafiya da su.
Iyayen Yesu sun same shi yana zama a haikali a tsakiyan malamai, yana sauraron su da kuma yi masu tambayoyi.
"Ba ku sani tilas ne in tsaya a gidan Ubana?"
Ya yi masu biyayya.
Yayi karuwa a hikima da girma, da kuma tagomashi wurin Allah da mutane.
1 A cikin shekara ta goma sha biyar da Tibariyus Kaisar ke mulki, Bilatus Babunti kuma ke jagorar Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, dan'uwansa Filibus yana sarautar yankin Ituriya da Tirakonitis, Lisaniyas kuma na sarautar yankin Abiliya, 2 kuma zamanin da Hanana da Kayafa suke manyan firistoci, maganar Allah ta zo wurin Yahaya dan Zakariya, a cikin jeji. 3 Ya yi tafiya cikin dukan yankuna da ke kewaye da Kogin Urdun, yana wa'azin baftismar tuba domin gafarar zunubai. 4 Kamar yadda aka rubuta a cikin littafin annabi Ishaya, "Ga muryan wani yana kira a cikin jeji, 'Shirya hanyar Ubangiji, ka daidaita tafarkunsa! 5 Za a cika kowani kwari, za a fasa kowani dutse a kuma baje kowani tudu, za a mike karkatattun hanyoyi, za a cike hanyoyi masu gargada, 6 kuma dukan mutane za su ga ceton Allah." 7 Sai Yahaya ya kara fada wa taron jama'ar da ke zuwa domin ya yi masu baftisma, "Ku 'ya'yan macizai masu dafi, wa ya gargadeku ku guje wa fushin nan mai zuwa? 8 Ku ba da 'ya'ya da sun cancanci tuba, kada ku kuma fara cewa a cikinku, 'Muna da Ibrahim a matsayin Ubanmu', domin ina gaya maku, Allah yana iya ta da wa Ibrahim 'ya'ya daga cikin wadannan duwatsu. 9 Yanzu kuwa, an rigaya an sa gatari a gindin itatuwa. Sabili da haka, duk itacen da bai ba da 'ya'ya masu kyau ba za a sare shi kasa a kuma jefa shi cikin wuta." 10 Sai mutanen da ke cikin taron jama'ar suka tambaye shi cewa, "To me za mu yi?" 11 Ya amsa ya ce masu, "Idan wani yana da taguwa biyu, sai ya ba wanda bashi da ita daya, kuma wanda yake da abinci ya yi haka nan." 12 Masu karban haraji ma suka zo domin a yi masu baftisma, suka ce masa, "Malam, me za mu yi?" 13 Ya ce masu, "Kada ku karba kudi fiye da yadda aka umarce ku." 14 Wasu sojoji ma suka tambaye shi cewa, "To, mu fa? Yaya za mu yi?" Ya ce masu, "Kada ku kwace wa wani kudi, kada ku kuma yi wa wani zargin karya. Ku dogara ga albashinku." 15 Ana nan da mutane ke sauraron zuwan Almasihu, kowa yana ta tunani a zuciyar sa game da Yahaya, ko shi ne Almasihu. 16 Yahaya ya amsa ya ce masu duka, "Game da ni dai, na yi maku baftisma da ruwa, amma akwai wani tafiye wanda ya fi ni iko, ban ma isa in kwance maballin takalmansa ba. Shi zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta. 17 Kwaryar shikarsa na hanun sa domin ya share masussukarsa da kyau ya kuma tara alkama a cikin rumbunsa. Amma zai kona buntun da wuta marar mutuwa. 18 Da gargadi masu yawa ya yi wa mutanen wa'azin bishara. 19 Yahaya kuma ya tsauta wa sarki Hirudus domin ya auri matar dan'uwansa, Hiruduya, da kuma sauran abubuwan da Hirudus ya yi. 20 Amma Hirudus ya kara yin wani mugun abu. Ya sa an kulle Yahaya a cikin kurkuku. 21 Ana nan, lokacin da ake yiwa dukan mutane baftisma, aka yiwa Yesu mai baftisma. Lokacin da yake yin addu'a, sai sama ta bude, 22 kuma Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa a kamanin kurciya, sai wata murya ta fito daga sama, "Kai ne kaunataccen Da na. Ina jin dadin ka." 23 Ana nan Yesu da kansa, da ya fara, yana kimanin shekara talatin. Shi dan (kamar yadda ake tsammani) Yusufu ne, dan Heli, 24 dan Matat, dan Lawi, dan Malki, dan Yanna, dan Yusufu, 25 dan Matatiya, dan Amos, dan Nahum, dan Hasli, dan Najjaya, 26 dan Ma'ata, dan Matatiya, dan Shimeya, dan Yuseka, dan Yoda, 27 dan Yowana, dan Resa, dan Zarubabila, dan Shiyaltiyel, dan Niri, 28 dan Malki, dan Addi, dan Kosama, dan Almadama, dan Er, 29 dan Yosi, dan Aliyeza, dan Yorima, dan Matat, dan Lawi, 30 dan Saminu, dan Yahuda, dan Yusufu, dan Yonana, dan Aliyakima, 31 dan Malaya, dan Mainana, dan Matata, dan Natan, dan Dauda, 32 dan Yesse, dan Obida, dan Bu'aza, dan Salmon, dan Nashon, 33 dan Amminadab, dan Adimi, dan Arama, dan Hezruna, dan Feresa, dan Yahuda, 34 dan Yakubu, dan Ishaku, dan Ibrahim, dan Tera, dan Nahor, 35 dan Serug, dan Reyu, dan Feleg, dan Abiru, dan Shela, 36 dan Kainana, dan Arfakshada, dan Shem, dan Nuhu, dan Lamek, 37 dan Metusela, dan Anuhu, dan Yaret, dan Mahalel, dan Kainana, 38 dan Enosh, dan Shitu, dan Adamu, dan Allah.
Kamar yadda annabi Ishaya ya fadi, Yohana ya fara shelar bisharar salama ga mutane.
Wadannan ayoyi suna bada shahareren bayyani don fadin abin da ke faruwa alokacin da dan'uwan Yesu ya fara bishararsa.
"Lokacin da Tibarius Kaisar yayi mulki har na tsawon shekaru goma sha biyar"
Wadannan sunayen maza ne.
Wadannan sunayen yankin kasashe ne.
"A lokacin da Hanana da Kayafa suke bauta tare a matsayin manyan firistoci." Hananiya ne babban firistin a lokacin, kuma Yahudawa suka chigaba da yarda (shaida) da shi a matsayinsa har bayan da Romawa suka naɗa sirikin sa, Kayafa, ya gaje shi a matsayin babban firistin.
"Allah ya fadi kalmar sa"
Kalmomin nan "baftisma" da kuma "tuba" ana iya fade su kamar aiki. AT: "sai kuma yayi wa'azi cewa ayi wa mutanen baftisma domin nuna cewa suna tuba"
Kalman nan "gafara" ana iya bayyana shi kaman aiki. AT: "domin a yafe masu zunubensu" ko "domin Allah ya yafe zunubensu." Zasu tuba domin Allah ya yafe zunubensu.
waddannan kalmonin na bayyana kalmomi daga annabi Ishaya. AT: "haka ya faru kaman yadda annabi Ishaya ya rubuta cikin littafinsa da ke dauke da kalmonin sa" ko "Yohana ya cika saƙon da annabi Ishaya ya rubuta cikin littafin sa"
Ana iya fadin wannan a matsayin magana. AT: "An ji muryar wanda ke kira daga cikin jeji" ko "Sun ji karar muryar wani da ke kira cikin jeji"
umurnin farko na bayani ko na ƙara bayani ga na farkon ne.
"Shirya hanya domin Ubangiji." Yin haka na wakiltcin yin shiri domin jin sakon Ubangiji alokacin da zai zo. Mutane na yin haka ta wurin tuba daga zunuben su. AT: "Yi shirin jin sakon Ubangiji alokacin da zai zo" ko "Ku tuba ku kuma yi shiri domin Ubangiji ya zo"
"hanyar" ko "hanyar
Idan mutane na shirya hanya domin zuwan mutum mai muhinmminci, suna yanke inda yayi tudu su kuma cika inda yayi kasa domin hanyar ya zama da lebur. Wannan sashin magana ya fara a ayan da wuce.
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "Zasu cika duk inda yayi kasa a hanyar"
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "zasu yi lebur na kowanne dutse" da "kuma kwanne tudu" ko " zasu cire kowanne wuri da ke da tudu a hanyar"
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "koyi yadda Allah ke ceton mutane daga zunubi"
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "domin Yohana ya masu baftisma"
A nan "yaya" na nufin zama da kwatancin. " AT: "Mugayen macizai na da dafi da hatsari sosai kuma ana kwatanta su da mugunta. AT: ku macizai masu dafi" ko "Kuna da mugunta, kamar macizai masu dafi
Bai yi zato za su bashi amsa ba. Yohana ya gargade jama'an domin suna so ya masu baftisma don kada Allah ya hukuntasu, amma, ba suwa son su daina yin zunubi. AT: "Ba zaku iya guje wa fushin Allah ta haka ba" ko "Ba zaku iya tsira daga fushin Allah ta wurin don yin baftisma ba kawai"
Kalman "fushi" ana amfani da shi domin nufin hukuncin Allah domin fushinsa ya riga shi. AT: "daga hukuncin da Allah zai aiko" ko "daga fushin Allah wanda yake shirin aikatawa"
A wannan kalman, ana kwatanta halayen mutane da 'ya'yan itace. Kamar yadda ake zacin itace ya ba da 'ya'ya wanda zai dace da ita, wanda yace ya tuba, ana zacin yayi rayuwan adalci. AT: "ba da irin 'ya'ya da zai nuna kun tuba" ko "yi abubuwa masu kyau da zai nuna kun juyo daga zunuben ku"
"cewa a tsakaninku" ko "tunani"
"Ibrahim kaƙan mu ne" ko "Mu zuriyar Ibrahim ne." Idan ba samu haske a dalilin da suka ce haka ba, zaku kuma iya karin asalin nufin bayyanin: "domin kada Allah ya hukunta mu"
Wannan kalma na ma'anan "hallita wa Ibrahim 'ya'ya" ko "sa mutane su zama zuriyar Ibrahim"
Watakila, Yohana na nufin ainihin duwatsu da suke hanyar Kogin Urdun
Gatari da yake a wurin domin yanke gindin itatuwa kalma ce da ake amfani domin hukunci da yake shirin farawa. Ana iya bayyana shi cikin sifar aiki. AT: "Allah kaman mutum ne da ya rigaya ya saka gatari a gindin itatuwan"
"wuta" Kalma ce da ake amfani domin hukunci. AT: "ya sare duk itacen da ba ta ba da 'ya'ya masu kyau zuwa kasa"
"tambaye shi, da cewa" ko "tambayan Yohana"
"amsa masu, yana cewa" ko "amsa masu" ko "ya ce"
"raba raguwar abinci kamar yadda kuka raba raguwar abin shan." Wannan na nufin koma wa bada abinci wa mabuƙata. AT: "ba da abinci wa wanda ba shi da komai"
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "domin Yohana ya yi masu baftisma"
"Kada ku tambayi kuɗi kuma" ko "kada ku yi neman ̀kuma." Masu karban haraji suna karban ƙudi fiye da yadda ya kamata. Su daina yin haka.
Wannan zancen na nufin masu karɓar haraji sukan karɓi ikonsu daga Roma ne. AT: "Fiye da abinda Romawa suka umurcesu su karɓa."
"Mu kuma fa sojoji, me za mu yi?" Kalman bai shafe Yohana ba" "da mu" da kuma "mu." Sojojin sun yi zaton cewa Yohana ya rigaya ya faɗa wa jama'a da kuma masu karɓan haraji abin da yakamata su yi ba da son me a matsayin sojoji za su yi ba.
kamar sojojin su na zargin karya game da mutane domin su samu kuɗi. Ana iya bayyana wannan da ƙarara. AT: "don haka kuma, kada ku wa wani zargin ƙarya domin ku samu ƙudi a wurin su" ko "kada ku ce mutum mara laifi ya ƙetare doka"
"Ku dogara ga albashinku"
"domin mutanen." Wannan na nufin mutanen ne suka zo gurin John.
kowa bai tabbata me zai yi tunani game da Yohana ba; sun tambayi kan su 'Ko shi ne Christi?' ko "ba wande ya tabbata abinda za yi tunani game da Yohana domin su na tunani ko ko zai iya zama shi ne Christi."
Amsar Yohana game da zuwan mutum mai muhinmincin na nufi cewa ba Yohana bane Christi. Zai iya zama da mahimmanci ka faɗa wa masu sauraronka. AT: "Yohana ya bayyana masu cewa ba shi bane ba Chiristi"
"Ina yin baftisma da ruwa" ko "Ina yin baftisma ta wurin amfani da ruwa"
"ban isa ba harma na kwance maballin takalmansa." Kwance maballin takalman aiki ne na bawa. Yohana yana faɗa cewa shi wanda ke zuwa mai muhinmici ne sosai, harma ni, Yohana, ban isa in zama bawansa ba.
Wannan kalma na zahirin kwatanta baftisma da ake yi da ruwa da baftisma na Ruhu da ke kawo su kusa da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta.
A nan, kalman nan "wuta" na iya nufin 1) hukunci ko 2) tsarki. Ya fi a bar shi a matsayin "wuta"
ya riƙe da ƙwaryar shiƙa domin yana shirye." Yohana na magana a kan zuwan Kristi domin sheri'a kaman shi manomi ne wanda yana shirye ya raba kwayan alkama daga dusan. AT: "Yana rike da kwayar shikar domin yana shirye" ko "Yana shirye ya yi hukunci kamar manomi wanda yana shirye"
Wannan kayan aiki ne da ake amfani domin busa alkama a iska, domin a raba kwayan alkaman da dusan. Ainihin kwayar na fadiwa zuwa ƙasa, sai kuma isca na hura dusa mara amfani. Yana nan kusa iri daya da abin shiƙa
Masussuƙan wuri ne da ake tara alkama domin shirin sussuƙa. A "share" ƙasan na nufin a gama tara kwayar. AT: "a gama tare kwayar"
Alkaman ne ya dace a ajiye a dakin ajiya bayan girbi.
ƙaiƙayin bashi da amfani 'a komai, sai, mutane na kona shi.
"Da gargadi masu karfi"
Hiridus, Mugu ne, amma ba sarki bane. Yana da ƙarancin ikon yin mulki a yankin ƙasar Galili.
"domin Hiridus ya auri matar dan'uwansa Hiruduya." Wannan mumunan abi ne domin dan'uwan Hiridus na nan da rai. Ana iya bayyana wannan a haske. AT: "domin ya auri matar dan'uwansa, Hiruduya, tun lokacin da dan'uansa yana da rai"
"ya gaya wa sojojinsa su saka Yohana a kurkuku"
Wannan kalman na alamar sonbon abin da zai faru na farko a cikin labarin. Idan kabilar ka tana da hanyar yin haka, za ka iya amfani da shi a nan.
"da Yohana ya yiwa dukan mutane baftisma." Kalman "dukan mutane" na nufin mutane da suna nan tare da Yohana.
Ana iya bayyana wannan cikin siffar aiki. AT: "Yohana ya yiwa Yesu ma baftisma"
"sararin sama ya bude" ko "sararin sama ya zama a bude." wannan na nufin yadda sararin sama ta yi haske, ko da shike ba a gane haskenta ba. wataƙila ya na nufin wani rami ya buɗe a sararin sama.
"a siffa ta jiki Ruhu Mai Tsarki ya sauko kamar kurciya a kan Yesu"
A nan "murya ta fito daga sama" wakiltar mutanen duniya masu jin Allah a sama yan magana. za a iya cewa Allah yayi magana da Yesus. AT: "murya daga sama ta ce" ko "Alla yati magana da Yesus daga sama, cewa"
Wannan baban sunane wa Yesu, ɗan Allah.
Ana amfani da wannan kalma don nuna alamar canji daga labarin zuwa shahareren bayyanen game da shekarun Yesu da ƙaƙanensa.
"Shekara 30"
"an yi tunanin cewa shi ɗan Yusufu ne" ko "mutane su yi tsammanin cewa shi ɗan Yusufu ne"
Ka lura da yadda mutane kan lisafta kakaninsu a yareka. Sai kayi amfani da yadda aka saɓa.
Wannan ne cigabawan sunaye na ƙakanen Yesu. Yi amfani da siffa iri daya da ka yi amfani da shi a ayoyin da suka wuce.
Wannan ne cigabawan sunaye na ƙakanen Yesu. Yi amfani da siffa iri daya da ka yi amfani da shi a ayoyin da suka wuce.
Wannan ne cigabawan sunaye na ƙakanen Yesu. Yi amfani da siffa iri daya da ka yi amfani da shi a ayoyin da suka wuce.
Wannan ne cigabawan sunaye na ƙakanen Yesu. Yi amfani da siffa iri daya da ka yi amfani da shi a ayoyin da suka wuce.
Wannan cigaba ne na lisafin kakanen Yesu. Yi amfani da irin sifan da aka yi aiki da shi a ayoyin da suka wuce.
"Adamu, hallitar Allah" ko "Adamu, wanda ya zo daga Allah" ko "Adamu, ɗan Allah, zamu iya ce, na Allah"
Yahaya ya yi a baftisma na tuba domin a gafarta musu zunubia.
Yahaya ya ce yana shirya hanya ma Almasihu.
Yahaya ya gaya musu su kera 'ya'yan itatuwa da na zuwa daga tuba
Yahaya ya ce za'a yanke shi ƙasa kuma a jefa a cikin wuta.
Yahaya ya ce wai tilas kada su karba kudin da ya fi abin da ya kamata.
Yahaya ya ce wani na zuwa wanda zai yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta.
Yahaya ya tsauta wa Hiradus domin Hiridus ya aura matan danwan shi, kuma ya yi ayukan mugunta dayawa.
Hiradus ne ya sa Yahaya a kurkuku.
Bayan Yahaya yayi ma Yesu baftisma, sama ya bude kuma Ruhu Mai Tsarki ya sauka akan shi kamar kurciya.
Muryar daga sama ta ce, "Kai ne dana kaunatacce, inna farin ciki da kai kwarai".
Yesu na nan wajen shekaru talatin a lokacin da ya fara koyarwa.
1 Sai Yesu, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga kogin Urdun, sai Ruhu Mai Tsarki ya bishe shi zuwa cikin jeji 2 kwana arba'in, shaidan kuma ya jarabce shi. A kwanakin nan, bai ci abinci ba, kuma yunwa ta kama shi bayan karshen lokacin. 3 Shaidan ya ce masa, "Idan kai Dan Allah ne, ka umarci wannan dutse ya zama gurasa." 4 Yesu ya amsa masa, "A rubuce yake, 'Ba da gurasa kadai Mutum zai rayu ba.'" 5 Sai shaidan ya kai shi zuwa wani tudu mai tsawo, ya kuma nuna masa dukan mulkokin duniyan nan a dan lokaci. 6 Shaidan ya ce masa, "Zan ba ka iko ka yi mulkin dukan wadannan, da dukan daukakarsu. Zan yi haka domin an ba ni su duka in yi mulkinsu, kuma ina da yanci in ba dukan wanda na ga dama. 7 Saboda da haka, idan ka rusuna ka yi mani sujada, dukansu za su zama naka." 8 Amma Yesu ya amsa ya ce masa, "A rubuce yake, 'Dole ne Ubangiji Allahnka za ka yi wa sujada, shi kadai kuma za ka bauta wa." 9 Sai shaidan ya kai Yesu Urushalima, ya tsayadda shi a bisan kololuwar haikali, kuma ya ce masa, "Idan kai Dan Allah ne, ka jefas da kanka kasa daga nan. 10 Domin a rubuce yake, 'Zai ba mala'ikunsa umarni su kiyaye ka, su kuma tsare ka,' 11 kuma, 'Za su daga ka sama a hannunsu, don kada ka yi tuntube a kan dutse." 12 Yesu ya amsa masa cewa, "An fadi, 'Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.'" 13 Da shaidan ya gama yi wa Yesu gwaji, sai ya kyale shi sai wani lokaci. 14 Sai Yesu ya koma Galili cike da ikon Ruhu, kuma labarinsa ya bazu cikin dukan wuraren dake wannan yankin. 15 Ya yi ta koyarwa a cikin majami'unsu, sai kowa na ta yabon sa. 16 Wata rana ya zo Nazarat, birnin da aka rene shi. Kamar yadda ya saba yi, ya shiga cikin majami'a a nan ranar Asabaci, ya kuma tashi tsaye domin ya karanta Nassi. 17 An mika masa littafin anabi Ishaya, ya bude littafin ya kuma ga inda an rubuta, 18 "Ruhun Ubangiji yana kai na, domin ya shafe ni in yi wa'azin Bishara ga matalauta. Ya aike ni in yi shelar yanci ga daurarru, da kuma budewar idanu ga makafi, in 'yantar da wadanda su ke cikin kunci, 19 in kuma yi shelar shekarar tagomashi na Ubangiji." 20 Sai ya rufe littafin, ya mai da shi ga ma'aikacin majami'ar, sai ya zauna. Dukan wadanda suke cikin majami'ar suka zura Idanuwansu a kansa. 21 Sai ya fara masu magana, "Yau wannan Nassi ya cika a kunuwanku." 22 Dukan wadanda ke wurin sun shaida abin da ya fadi kuma dukansu sun yi ta mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suna cewa, "Wannan ai dan Yusufu ne kawai, ko ba haka ba?" 23 Yesu ya ce masu, "Lallai za ku fada mani wannan karin magana, 'Likita, ka warkar da kanka. Duk abin da mun ji wai ka yi a Kafarnahum, ka yi shi a nan garinka ma.'" 24 Ya sake cewa, "Hakika na fada maku, annabi baya samun karbuwa a garinsa. 25 Amma na gaya maku gaskiya akwai gwauraye da yawa cikin Isra'ila a zamanin Iliya, lokacin da an rufe sammai shekaru uku da rabi babu ruwa, lokacin da anyi gagarumar yunwa a duk fadin kasar. 26 Amma ba a aiki Iliya zuwa wurin waninsu ba, sai wurin gwauruwa da ke a Zarifat can kusa da Sidon. 27 Akwai kutare da yawa kuma a Isa'ila a zamanin anabi Elisha, amma babu wanda aka warkar sai dai Na'aman mutumin Suriya kadai. 28 Dukan mutanen da ke cikin majami'a suka fusata kwarai sa'adda suka ji wadannan zantattuka. 29 Suka tashi suka tura shi zuwa wajen birnin, suka kai shi bakin dutsen da aka gina garinsu a kai dominsu jefar da shi kasa. 30 Amma ya ratsa tsakaninsu ya yi gabansa. 31 Sannan ya gangara zuwa Kafarnahum, wani birni a Galili. Wata Asabaci yana koya wa mutane a cikin majami'a. 32 Sun yi mamaki kwarai da koyarwan sa, domin maganarsa na da iko. 33 A wannan lokacin akwai wani mutum a cikin majami'a mai kazamin ruhu, sai ya yi kara da babbar murya, 34 "Ina ruwan mu da kai, Yesu Banazarat? Ka zo domin ka hallaka mu ne? Na san ko kai wanene! Kai ne Mai Tsarki na Allah!" 35 Yesu ya tsauta wa aljanin yana cewa, "Yi shiru ka fita daga cikinsa!" Da aljanin ya jefar da mutumin kasa a tsakiyarsu, ya fita daga cikinsa ba tare da yi masa rauni ba. 36 Dukan mutanen suka yi mamaki, kuma suna ta zancen wannan abu a tsakaninsu. Sun ce, "Wanda irin maganganu kenan? Ya umarce kazaman ruhohin da karfi da iko kuma sun fita." 37 Saboda da haka, an fara yada labarinsa zuwa dukan kewayen yankin. 38 Sai Yesu ya bar majami'ar ya shiga gidan Siman. A wannan lokacin, surukar Siman tana fama da zazzabi mai zafi, sai suka roke shi dominta. 39 Sai ya tsaya a kanta, ya tsautawa zazzabin, kuma ya rabu da ita. Nan take, ta tashi ta fara yi masu hidima. 40 Da faduwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan wadanda suke ciwo da cuttuttuka dabam dabam. Ya dora masu hannuwansa ya warkar da su. 41 Aljanu kuma sun fita daga wadasunsu da dama, suna kuka cewa, "Kai ne Dan Allah!" Yesu ya tsauta wa aljannun ya kuma hana su magana, domin sun sani cewa shine Almasihu. 42 Da safiya ta yi, ya kebe kansa zuwa wani wurin da babu kowa. Jama'a da dama suna neman sa suka zo inda yake. Sun yi kokari su hana shi barin su. 43 Amma ya ce masu, "Dole in yi bisharar Allah a wasu birane da dama, domin dalilin da aka aiko ni nan kenan." 44 Sai ya ci gaba da wa'azi cikin majami'u dukan fadin Yahudiya.
Yesu ys yi azumi na kwana arba'in, sai sheɗan ya hadu da shi ya su ya ringaye ya y zunubi.
Bayan da Yahaya ya yi wa Yesu baftisma.
AT: "ruhu ya bishe shi"
juye mafi yawa sun ce gwajin gaba ɗaya na kwanaki arba'in ne. UDB ya fada, "da ya ke agun, shaiɗan ya cegaba da gwada shi" don a bayya na shi.
"kwanaki 40"
AT: "kuma zaka iya bayyana shi shaiɗan ya gwada shi ya yi. ATL "shaiɗan ya yi ya rinjaye shi domin kada ya yi wa Allah biyyaya"
Wannan kalmar "ya" na nufin Yesu.
Shaidan ya tsokani Yesu ya yi wannan aikin al'ajibin domin ya tabbatas da cewa shi ɗan Allah ne "ɗan Allah"
shaidan ko ya reke dutse a hannun sa ko kuwa ya na nuna wata dutse kusa.
Yesu ya ki tsokanan shaidan ya nuna ba shakka a amsar sa.zai zama da taimako ka faɗi wannan ba shakka ga masu sauraro, kamar yadda UDB ya yi. AT: "Yesu ya amsa, 'A'a, ba zan yi haka ba domin a rubuce yake ... kadai."
Wannan maganar daga rubutun Musa ne a tsohowar alkawari. AT: "Musa ya rubuta a cikin littafi"
Wannan kalmar "gurasa" na nufin aabinci gaki ɗaya. abinci kamar yadda Allah ya hada, da kanta, bai isa ya ceci mutum ba. Yesu ya faɗi littafi ya ce abin da ya sa ba zai juya dutsen ya zama gurasa ba. AT: "Mutane ba za su rayu da gurasa kadai ba" ko "ba abinci ne kadai yake sa mutum ya rayu ba" ko "Allah ya ce akwai abubuwa mafi muhimmanci fiye da abinci"
ya kai Yesu wani tudu.
"cikin ƙaramin" ko "nan da nan"
Ma'ana mai yuwa da suke "su" na nufin 1) iko da mai girma na mulkin ko 2) mulkin. AT: "Allah ya bani su"
Wannan sashin biyun sun yi kusa. Za'a iya hada su. AT: "idan ka rusuna ka yi mani sujada
"Zan baka dukkan wannan mulkin, da girmam su"
"ya amsa masa" ko "amsa masa"
Yesu ya na faɗan umurni daga littafi ya faɗa abin da ya sa ba zai bauta wa shadan ba.
Wannan na nufin mutanen da suke tsohowa alkawari wanda suka karbi dokar allah. za ka iya amfani da siffar mafuradi na 'ku' domin kowanne mutum ya yi biyayya da shi, ko ka yi amfani da siffar jam'i na 'ku' domin dukkan mutanen su yi biyayya da shi. (Dubi:
Wannan kalmar "shi" na nufin Ubangiji Allah.
Wannan lungu ne na jinkan haikalin. Idan wani ya faɗi daga wurin, za su ji ciwo sosai ko su mutu.
Wannan masayi ne mafi muhimmanci wa Allah.
"yi tsalle zuwa ƙasa"
Shaidan ya nuna da cewa faɗin sa daga zabura na nufin Yesu ba zai ji ciwo ba idan shi aɗn Allah ne. Wannan za'a iya faɗan ta ba shakka, kamar yadda UDB ya yi. AT: "Ba za ka j ciwo ba, domin a rubuce yake"
"Shi" na nufin Allah. shaidan ya faɗa daga zabura domin ya rinjayi Yesu ya yi tsalle daga ginin.
Yesu ya faɗa wa shaidan abin da ya zai yi abin da ya ce ya yi ba. ƙin yin bun na a bayyane. AT: "A'a, ba zan yi hakan ba, domin an faɗa"
Ma'ana mai yuwa 1) Kada Yesu ya gwada Allah da yin tsalle daga saman haikalin, ko 2) kada shaidan ya gwada Yesu cewa shi ɗan Allah ne. yana da kyau a juya ayan yadda aka faɗe ta da ka so ka bayana ma'anar sa.
"sai ranar aukowar babban abu"
Wannan arin bai nuna da cewa shaidan ya ci nasara a gwajin da ya yi wa Yesu ba - Yesu ya ƙi yarda da kowanne ƙoƙari. AT: "Ya gama gwadawa ya ringayi Yesu ya yi zunubi"
Wannan ya fara sabuwar abu a labarin.
"sai ruhun yana ba shi iko." Allah ya na tare da Yesu a wata hanya na musamman, sa shi ya yi abubuwa da mutane ba za su iya yi kullum ba.
"Mutane sun baza labari akak Yesu" ko "mutanesun gaya wa wasu game dea Yesu" ko "ilmi akan sa aka faɗa daga mutum zuwa wani mutum." Wadanda suka ji Yesu sun gay wa wasu mutane game da shi, sai kuma wadannan mutane suka gaya wa wasu mutane game da shi sosai.
Wannan na nufin filaye ko wurare kewaye da Galili.
"kowa ya faɗa manyan abubuwa game da shi" ko "dukkan mutanen su yi magana akan sa a hanya mai kyau"
"Wurin da iyayan sa suka rene shi" ko "in da ya zauna lokacin da yake yaro" ko "in da ya yi girma"
"kamar yadda yake yi kowanne Asabaci. "al'adar yi ne na kullayomi ya je majami'a a ranar Asabar.
AT: "Wani ya ba shi littafin annabi Ishaya"
Wannan na nufintakar dan Ishaya wanda aka rubuta a littafi. Ishaya ya rubuta kalmomin tun da daɗewa, sai wani dabam ya kofa a littafi.
"wuri a littafin da wadannan kalmamomin." Wannan bayanin ya cigaba har zuwa aya ba biye.
"Ruhu mai tsaki yana tare da ni a hanya na musamman." sa'anda wani ya faɗi haka, yana yin riya cewa yana maganar kalmomin Allah.
A tsohowar alkawari, main bikin al'ada aka zuba a kan mutum sa'anda aka ba su ƙarfi ko iko su yi wani aiki na musamman. Yesu ya yi amfani da wannan misalin ya yi nufin ruhu mai tsarki fara akan shi ya shirya shi domn aikin sa. AT: "ruhu mai tsarki yana kai na ya
"matalautan mutane"
"gaya wa mutane wadanda suke ɗaurarru da cewa za su iya tafiya" ko "a sake ɗaurarrun yaki"
"ba wa makafai idanu" ko "sa makafai iya gani kuma"
"a sake wadanda aka wulakantasu"
"gaya wa kowa da cewa Allah ya shirya ya yi wamutanen sa albarka" ko "ayi shaila cewa wannan shekaran ne Allah zai nuna wa alheri"
A na kulle littafi ta wurin naɗewa kamar bututu domin ya tsare rubutun ciki ta.
Wannan na nufin masu aiki a cikin haikalin wanda suke kawo su kuma aijiye da hankali da grimama littafin dauke da littafin kirista
Wannan ƙarin na nufin "juya ɗon mudube shi" ko "muna kallonsa da gangan"
Yesu ya na cewa shi yana cika wannan anabcin da aikin sa da maganar sa a waccan lokaci. AT: "I na cika abinda aya ta faɗa yanzu da kuke jina"
Wannan karin na nufin "sa'anda kuke jina"
"mamaki game da abubuwan alheri da yake faɗawa." A nan "alheri" mai yuwa na nufin 1) yadda yake da kyau ko yadda maganar Yesu ke rinjayer, ko 2) Yesu ya yi magana akan alherin Allah.
Mutane suna tunanin cewa Yusufu na uban Yesu. Yusufu ba shugaban addini bane, suna mamakin yadda yaron sa ya yi wa'azi yadda ya yi. AT: "Wannan ɗan Yusufu ne kawai!" ko "uban sa Yusufu ne kawai!"
Nazarat gari ne inda Yesu ya yi girma.
"ba shakka" ko "babu shakka da cewa"
Idan wani ya ce yana warkar da cutan da shi da kansa yakeda shi, ba dalili sai dai a yarda da cewa lallai shi likitane. Mutane zasu yi wa Yesu wannan ƙarin magana su ce za su yarda shi annabi ne idan ya yi abin da suke ji ya yi a wasu wurare.
Mutanen Nazarat ba su yarda ba. Yesu annabi bane domin ƙaramin masayin sa ɗan Yusufu. baza su yarda ba sai sun gan shi ya na yin ayukan al'ajibi.
"ba shakka da gaskiye ne."Wannan bayani ne mai ƙarfi game da abin da ya biyu baya.
Yesu ya yi magana na baki ɗaya damin ya kwaɓi mutanen. ya na nufin cewa sun ki su yarda da shalar ayukan al'ajibin sa a Kafarnahum. suna tunanin cewa su riga su san komai game da shi.
"garin sa" ko "ɗan ƙasar" ko "garin da ya yi girma"
"Na gay amaku gaskiyan." Yesu ya yi amfani da wannan sasjin domin ya yi nauyin muhimmanci, gaskiya, da daidai bayanin da ya biyu baya.
Gwamraye mataye ne wanda mazajen su sun mutu.
Mutanen da Yesu yake yi masu magana sun sani da cewa Iliya ɗaya daga cikin annabawan Allah ne. Idan mai ƙaratun ka bai san wannan ba, zaka iya bayana wannan kamar yadda yake a UDB. AT: "sa'anda Iliya yake yin ananbaci a Isar'ila"
Wannan misali ne. an ga hoton sama kamar rufin ɗaki wanda ya kullu, sabo da haka ba ruwa da zai faɗi daga ita. AT: "sa'anda babu ruwan da ya faɗɩ daga sama" ko "sa'an da babu ruwa gaba ɗaya"
an yi rashin abinci mai nauyi." yunwa doguwar lokaci ne sa'anda baroro bata haifu abinci sosai wa mutane ba.
Mutanen dake zama a Zarifat al'umai ne, ba Yahudawa ba. Wadannan mutanen da suke sauraran Yesu sun gane da cewa mutanen Zarifat ba Yahudawa bane. AT: "zuwa ga ba al'umar gwamruwa da take zama a Zarifat"
Mutumin Suriya mutum ne daga Suriya. Mutanen Suriya al'umai ne, ba Yahudawa ba. AT: "Na'aman ba al'ume daga Suriya"
Mutanen Nazarat suka ji haushi sosai cewa Yesu ya fsɗi littafi inda Yesu ya taimaki al'umai a maimakon Yahudawa.
"suka sa shi da arfi ya bar garin" ko "bangaje shi zuwa wajen garin"
"baki bakin"
"ta tsakanin taron" ko "tsakanin mutanen da suke so su kashi shi."
"ya tafi abunsa" ko "ya tafi a hanyar sa" Yesu ya tafi anda ya yi shiri ya je a maimakon inda mutanen su ke sa shi dole ya ji.
Sa'anan Yesu." Wannan ya nuna sabuwar abu.
Wannan sashin "gangara" an yi amfani da shi a nan domin Kafarnahum ya yi ƙasa da Nazarat.
"Kafarnahum, wani birni ne a Galili"
babban mamaki, ya ji babban mamaki
"ya yi magana kamar wanda yake da iko" ko "kalmomin sa yana da babban ƙarfi"
Wannan sashin an yi amfani da shi anan domin a s alamar gabatar da wani sabuwar hali a labarin; a wannan yanayi, mutum mai aljanu.
"wanda yake da kazamin ruhu" ko "wanda mugayen ruhohi suke aiki da shi"
"ya yi ihu da arfi"
Wannan amsa mai ƙari ne wanda ke nufin: "mai muke da shi iri ɗaya?" ko "Wanne dama kake da shi na damun mu?"
Wannan tambayn za'a iya rubutashi kamar bayani. AT: "Me kai, Yesu Banazarat, za ka yi da mu!" ko "baka da dama na damun mu, Yesu Banazarat!"
"Yesu ya yiwa aljanun tsawa. yana cewa" ko "Yesu ya ce wa al'janun da tsanani"
Ya umurci al'janun su daina iko da mutumin. AT: "ku bar shi" ko kada ku zauna a ciki mutumin kuma"
Mutanen suna furta yadda suke da mamaki da cewa Yesu ya na da iko ya umurci aljanu su bar mutum. Wannan za'a iya rubuta shi kamar bayani. AT: "Wannan kalmomin ban mamaki ne!" ko "Kalmomin sa abin mamaki ne!"
"Ya na da iko da ƙarfi ya umarce ƙazamen ruhohin"
Wannan magana ne akan abin da ya faru bayan labari da ya sa da abin da ya auko da cikin labarin da kanta.
"rihoton Yesu ya yaduwa" ko "mutane sun fara yada labari game da Yesu"
Wannan ya gabatar da sabuwar abu.
"Maman matar Siman"
Wanna ƙari ne da yake nufin " tana fama da"
"fata mai zafi ... zafi" ko "fata mai zafi ... ya tsautawa zazzabin"
Wannan na nufin sun tambaye Yesu ya warkar da ita daga zazzabin. AT: " tambaye Yesu ya warkar da ita daga zazzabin" ko "tambaye Yesu ya warkar da zazzabin ta"
Wannan kalmar "sai" ya nuna da cewa ya yi wannan sabo da mutanen sun roke shi a madadin surkuwan Siman.
"je gunta ya jingina da ita"
"ya yi wa zazabin magana mai tsanani, kuma ya rabu da ita" ko "ya umurce zazabin kuma ya bar ta, kuma ya yi." Zai zama da taimako ka faɖa abin da ya gaya wa zazabin ya yi. AT: "ya umurce fatan ta ya zama da sanyi, kuma ya yi" ko "ya umurce ciwon ta ya bar ta, kuma ya yi"
A nan wannan na nufin ta fara yin abinci wa Yesu da sauran mutanen dake gidan.
"ya sa hanunsa akan" ko "taba"
Ya nuna da cewa Yesu ya aljanu su bar mutanen dake da aljanu AT: "Yesu ya kuma sa aljanu su fito da ƙarfi"
Wannan na nufin abu ɗaya, kuma mai yuwa ya na nufin tsoro ko kuka ko hayshi. wasu masu juyin sun yi amfani da ajili ɗaya. AT: "iho" ko " ko kururuwa"
"ya yi magana mai ƙarfi wa aljanun"
"bai bar su ba"
"Da rana ya tashi" ko "Da ya faɗi"
"wurin hadama" ko "wurin da ba mutane"
"zuwa ga mutane da dama a wasu birane"
AT: "Wannan shine dalilin da Allah ya aiko ni"
Tunda Yesu ya na Galili, kalmar nan "Yahudiya" na nufin yankin da Yahudawa suke zaune a waccan lokacin gabaɗaya. AT: "inda aYahudawa suke zaune"
Ruhu Mai Tsarki ya jagorance Yesu zuwa cikin jeji.
Iblis ya gwada Yesu a cikin jeji ma kwana arba'in.
Iblis ya gaya ma Yesu ya juye duwatsun zuwa gurasa.
Ba da gurasakadai mutum zai rayu ba.
Iblis ya nuna ma Yesu duka mulkokin duniya.
Iblis ya soYesu ya durkusa da yi mashi sujada.
Ka yi sujada wa Ubangiji Allahn ka, kuma dole shi kadai za ka bauta wa.
Ya gaya ma Yesu ya yi tsale zuwa kasa
Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.
Iblis ya rabu da Yesu dan lokaci tukuna.
Yesu ya karanta daga littafin Annabi Ishaya
Yesu ya ce littafin da ya karanta daga Ishaya yana cika a ranan.
Yesu ya ce ba annabi wanda anna karbi a kasan shi?
Allah ya aika Iliya zuwa Zarifat, kusa da kasar Sidon.
Allah ya sa Elisha ya taimake Na'aman, mutumin Suriya.
Sun cika da fushi kuma sun so so jefa shi a kan dutse.
Yesu ya yi tafiyarsa a tsakiyarsu.
Aljan ya ce ya san Yesu ne Mai Tsarki na Allah.
Mutanen sun yi mamaki kuma sun cigaba da magana akan shi da juna
Yesu ya daddora wa kowannensu hannu, ya warkar da su.
Aljanu sun ce Yesu Dan Allah ne, kuma Yesu bai yadda sun yi magana ba domin sun sani shi ne Almasihu.
Yesu ya ce an aike shi ya yi wa'azin bisharan mulkin Allah wa sauran garuruwa.
1 Ya zama sa'adda mutane sun taru a wurin Yesu suna sauraron maganar Allah, yana kuma yana tsaye a bakin tabkin Janisarata. 2 Ya ga jiragen ruwa biyu tsaye a bakin tabkin. Masu kamun kifin kuwa sun fita daga cikin jiragen suna wanke tarunsu. 3 Yesu ya shiga daya daga cikn jiragen wanda shike na Bitrus ne, sai ya umarce shi ya dan zakuda da jirgin daga bakin tabkin kadan zuwa cikin ruwa. Sai ya zauna ya kuma koya wa mutane daga cikin jirgin. 4 Da ya gama magana, ya ce wa Siman, "Zakuda jirgin zuwa wuri mai zurfi sa'annan ka zuba tarunka domin kamu." 5 Siman ya amsa ya ce, "Ubangiji, mun yi aiki dukan dare bamu kama komai ba, amma bisa ga maganarka, zan jefa tarun." 6 Da sun yi haka, suka kama kifaye da yawan gaske, har tarunsu suna yagewa. 7 Sai suka roki abokan aikinsu da ke a dayan jirgin su zo su taimake su. Suka zo sun cika jiragen biyu da kifaye, har suka fara nutsewa. 8 Amma Siman Bitrus, da ya ga haka, ya russuna a gaban Yesu, yana cewa, "Ka rabu da ni Ubangiji, gama ni mai zunubi ne." 9 Domin ya yi mamaki, da dukan wadanda suke tare da shi, sabili da yawan kifaye da suka kama. 10 Wannan ya hada da Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi abokan aikin Siman. Sai Yesu ya ce wa Siman, "Kada ka ji tsoro, domin daga yanzu, za ka kama mutane." 11 Da sun kawo jiragensu waje kan kasa, suka bar komai suka kuma bi shi. 12 Sa'adda yana daya daga cikin biranen, wani mutum dauke da kuturta yana nan wurin. Da ya ga Yesu, ya fadi bisa fuskarsa kasa yana rokansa, yana cewa, "Ubangji, idan ka yarda, za ka iya tsarkake ni." 13 Yesu ya mika hanunsa ya taba shi, yana cewa, "Na yarda. Ka tsarkaka." Sai nan da nan, kuturtar ta rabu da shi. 14 Ya umarce shi kada ya gaya wa kowa, amma ya ce ma sa, "Tafi ka nuna kanka ga firist sa'annan ka mika hadaya domin tsarkakewarka, kamar yadda Musa ya umarta, a matsayin shaida a garesu." 15 Amma labarinsa ya bazu nesa, taron mutane da yawa kuma suka zo wurinsa domin su ji shi, su kuma samu warkarwa daga cututtukansu. 16 Amma ya kan janye zuwa wuraren da babu kowa ya yi addu'a. 17 Ya zama daya a cikin kwanakin da yake koyarwa, akwai Farisawa da malaman attaura da ke zaune a wurin wandanda suka zo daga kauyukan da suke kewaye da Galili da Yahudiya da kuma birnin Urushalima. Ikon Ubangiji yana tare da shi domin warkarwa. 18 A lokacin nan, wasu mutane suka zo dauke da wani mutum shanyayye a kan tabarma, suka kuma nemi yadda za su shigar da shi ciki, su kwantar da shi a gaban Yesu. 19 Ba su iya samun hanyar da za su shigar da shi ba saboda taron, sai suka hau saman gidan, suka saukar da shi daga rufin, a kan tabarman sa, zuwa tsakiyar mutanen, dai dai a gaban Yesu. 20 Da ya ga bangaskiyarsu, Yesu ya ce, "Maigida, an gafarta zunubanka." 21 Marubuta da Farisawa suka fara sukar wannan, suna cewa, "Wanene wannan da ke sabo? Wa zai iya gafarta zunubi, idan ba Allah kadai ba?" 22 Amma da Yesu ya fahimci abin da suke tunani, sai ya amsa ya ce masu, "Don me kuke sukar wannan a zuciyarku? 23 Wanne ne ya fi sauki a ce, 'An yafe zunubanka' ko kuwa a ce, 'Tashi ka yi tafiya?" 24 Amma domin ku sani cewa Dan Mutum yana da yancin gafarta zunubai a duniya, na ce maka, 'Tashi, dauki tabarmanka, ka tafi gidanka.'" 25 Nan take, ya tashi a gabansu ya dauki tabarma da yake kwance; sai ya koma gidansa, yana daukaka Allah. 26 Kowa yana ta mamaki kuma suka daukaka Allah. Suna cike da tsoro, suna cewa, "Yau mun ga abubuwan al'ajibi." 27 Bayan wadannan abubuwa sun faru, Yesu ya fito daga can sai ya ga wani mai karban haraji mai suna Lawi yana zama a wurin karban haraji. Ya ce masa, "Ka biyo ni." 28 Sai Lawi ya bar komai, ya tashi, ya bi shi. 29 Lawi kuma ya shirya gagarumar liyafa a gidansa, kuma akwai masu karban haraji da yawa a nan, da wasu mutane da ke zama a gaban teburin liyafar suna cin abinci tare da su. 30 Amma Farisawa da Marubuta suka fara korafi ga almajiransa, suna cewa, "Don menene kuna ci da sha tare da masu karban haraji da mutane masu zunubi?" 31 Yesu ya amsa masu, "Masu lafiya basu bukatar likita, wadanda ke marasa lafiya kadai ke bukatar likita. 32 Ban zo domin kiran masu adalci ba, amma na zo ne domin kiran masu zunubi zuwa ga tuba." 33 Sun ce masa, "Almajiran Yahaya sukan yi azumi da addu'a, kuma almajiran Farisawa ma sukan yi haka. Amma almajiranka suna ci suna sha?" 34 Yesu ya ce masu, "Akwai wanda zai sa abokan ango su yi azumi, a lokacin da shi ango yana tare da su? 35 Amma kwanaki na zuwa wadanda za a dauke ango daga wurinsu, a kwanakin za su yi azumi." 36 Sai Yesu ya sake fada masu wani misali. "Babu wanda zai yage kyalle daga sabuwar tufa, ya kuma yi amfani da ita ya dinka tsohuwar tufa. Idan ya yi hakannan, zai yage sabuwar tufar, kuma kyallen daga sabuwar tufar ba zai dace da kyallen tsohuwar tufar ba. 37 Kuma, babu mutum da zai sa sabon ruwan inabi a cikin tsofafin salkuna. Idan ya yi haka, sabon ruwan inabin zai fasa salkunan, kuma ruwan inabin din zai zube, salkunan kuma za su lallace. 38 Amma dole ne a sa sabon ruwan inabi a sabobin salkuna. 39 Babu wanda zai yi marmarin sabon ruwan inabi bayan da ya sha tsohon, gama zai ce, "Tsohon ya fi sabon."
Yesu ya yi wa'azi daga daga cikin jirgin ruwan Siman da ake kira Bitrus a bakin tabkin Janisarata.
Wannan sashin an yi amfani da shi a nan domin a sa alama a sabuwar abin da ya auko a labarin. Idan yaren tana da wata hanyar yin haka, zai ku yi amfani da shi a nan.
Ma'ana mai yuwa 1) "sauraron maganar da Allah yake so su ji" 2) "sauraron sakon Yesu game da Allah"
Wannan kalmar ya na nufin tabkin Galili. Galili ya na yanman cin tebkin, ƙasa Janisarata yana gefen gabas, sabo da haka ana kira da dukkan sunan. Wasu juyin turanci suna ne daidai na jikin ruwa, tabkin Janisarata."
Suna wanke tarusu fifayen su domin su yi amfani da su su kama kifi.
"jirgin ruwan Bitrus"
"ya ce ma Siman ya matsar da jirgin ruwan nesa da ɠaban tekun"
Zama, zama matsayi na al'ada ga malami.
"ya koya wa mutane sa'anda ya zauna a jirgin ruwa." Yesu ya na jirgin ruwa nisa kaɗan daga tukun kuma yana magana da mutanen wanda suke a ɠaban tekun.
"da Yesu ya gama koya wa mutanen"
"domin ka gaya mini in yi haka"
Suna nesa da tekun su yi kira, sai suka yi motsi jiki mai nuna abin da yake zuciya, mai yuwa t awurin ƙamumin ruwa da hannayen su.
"kwalekwalen ya fara nutsewa." dalilin za'a iya faɗa ba shakka. AT: "kwalekwalen ya fara nutsewa domin domin kifin ya yi nauyi"
Ma'ana mai yuwa 1) "ya russuna a gaban Yesu" ko 2)durkusa a tafin Yesu" 3) bai faɗi ba da gangan ba . ya yi haka kamar alaman tawali'u da ban girma wa Yesu.
Wannan kalmar a nan "mutum" na nufin "gimshiƙeƙƙen namiji" ba kuma gada ɗaya "mutanen."
"kifaye masu yawa"
"abokin hurɗar Siman a kasuwancin kifi"
an yi aiki da hoton kama kifi a nan kamar misali na tara mutane su bi Almasihu. AT: "zaku kama mutane" ko "zaku tara mini mutane" ko "zaku kawu mini mutane su zama al'majerai na"
Wannan sashin ya sa alaman sabuwar abu a labarin.
"mutum da kuturta ya rufe shi." Wannan ya gabatar da sabuwar hali a labarin.
A nan "fadi bisa fuskarsa" ƙari ne da yake nufin ya durkusa ƙasa. AT: " ya daukusa ya taba ƙasa da fuskar sa" ko "ya durkusa a ƙasa"
"idan ka na so"
An gane da cewa ya na so Yesu ya warkar da shi. AT: "Dan Allah ka tsarkakeni, domin zaka iya"
Wannan na nufin tsarkake nz al'ada, amma an gane bai da tsarkake domin kuturta tan sa. AT: "warkar da ni daga kuturta na domin in zama da tsarki ... in warke"
"ba shi da kuturka kuma"
Wannan za'a iya juya shi kamar magana na kai tsaye: kada ka gaya wa kowa" Wannan tambayan na nuna cewa za'a iya baiyana shi
Dokan ya buƙatar mutum ya yi hadaya na musamman bayan da ya warke. wannan ya bar mutumin ya zama tsarkakke, kuma ya sami damar sake sa kai ga harkokin addini na al'ada.
"kamar hujja na warkas su warka"
Ma'ana mai yuwa 1) "zuwa ga firist" ko 2) "zuwa ga mutane."
"labari game da Yesu." Wannan zai iya zama ko "rehoto game da Yesu ya warkar da mutumin daga kuturka" ko "rehoto Yesu ya warkar da mutane."
" labarinsa ya bazu nesa zuwa gaba." AT: "mutane sun cigaba da bada labarin shi a wasu wurare"
"wuraren da ba kowa" ko "wuraren da ba wasu mutane"
Wadannan ne mutanen da suke labarin. mai yuwa yaren ku suna da hanyar nuna cewa wadannan sabobin mutane ne.
gammon barci ko gado ko gadon daukar mara lafiya
"ba zai iya masar da kansa ba"
A wasu yaren mai yuwa zai zama na halita aa sake wannan umurnin. AT: "Amma domin taron mutanen, ba za su iya samun hanyar da za su iya shigar da shi ciki ba. Sai"
Yana da sauƙin ganewa da cewa dalilin da ya sa basu iya shiga ba shi ne taron ya yi babba har babu ɗaki domin su.
Gidaje yana da kitan jinka, kuma wasu gidajen suna da matakala ko mataki a waje domin ya zama masu d asauki su hau sama. AT: "sun hau saman kitan jinkan gidan"
"daidai a gaban Yesu" ko "nan da nan a gaban Yesu"
An gane da cewa sun bada gaskiya Yesu zai warkar da shanyyayen mutumin. AT: "Da Yesu ya gane cewa sun ba da gaskiya cewa zai warkar da mutumin, ya ce masu"
Wannan kalma ne nagaba ɗaya da mutane suke amfani da shi sa'anda suke magana da mutum wanda basu san sunar sa ba. ba rashin ladabi bane, kuma bai nuna wani ba da girma na musamman ba.wasu yaren mai yuwa za su iya aiki da kalma kaman "aboki" ko "laƙabin girma."
AT: "an yafe maka" ko "Na yafe maka zunubinka"
"tattauna wannan" ko "yi tunani akak wannan." Abin da suka yi tambayan za'a iya faɗa. AT: "sun yi magana akan ko Yesu yana da iko ya yafe zunubai"
Wannan tambayan ya nuna yadda suka yi mamaki da haushi game da abin da Yesu ya faɗa. Wannan za'a iya rubuta shi kamar bayani. AT: "Wannan mutumin yana sabo ga Allah!" ko "Yana sabo ga Allah da faɗan haka!"
Wannan ya nuna da cewa idan mutum ya ce yana gafarta zunubi yana cewa shi Allah ne. Wannan za'a iya rubuta kamar bayani mai sauƙin ganewa. AT: "zai iya gafarta zunubi, idan ba Allah kadai !" ko "Allah ne kadai wanda zai iya yafe zunubi!"
Wannan sashin ya nuna da cewa suna tunani mai shuru, sai Yesu ya gana maimakon ya ji abin da suke tunani.
Wannan za'a iya rubuta shi kamar bayani. AT: "Kada ku yi gardama da wannna a zuciyar ku." ko "Kada ku yi shakka da cewa ina da iko in gafarta zunubi."
A nan "zuciya" misali ne na hankalin mutane ko cikin mutum.
Yesu ya yi amfani da tambaya ya sa marubutan su yi tunani akan abin da zai hakikanta ko zai iya ko ba zai iya yafe zunubia ba. AT: "Na faɗa ne kawai 'An yafe maka zunuban ka.' Zaku yi tunani da cewa yana da wuya a faɗa 'Ta shi ka yi tafiya,' domin hakikantan cewa zan warkar da mutumin zai nuna idan ya tashi ya yi tafiya ko in bai tashi ba." ko "Zaku yi tunani da cewa ya na da sauƙi a ce 'An yafe maka zunuban ka' da a ce Tashi ka yi tafiya."
Ilan maganar da ba 'a yi ba shi na abu ɗaya "ya na da saui a ce domin ba wanda ya san abin da ya faru," amma ɗayan aun shi ne "da wuya a faɗa domin kowa zai san abin da ya faru." mutane ba za su san in a yafe wa mutum zunubia ba, amma duk za su sani idan an warkar da shi ya tashi ya yi tafiya.
Yesu ya na magana da Farisawa da marubutan. Wannan kalmar "kai" jam'i ne.
Yesu yana nufin kansa.
Yesu ya na faɗan wannan wa shanyyeyen mutumin. Wannan kalmae "kai" mafuradi ne.
"a take ya tashi" ko "nan da nan ya tashi"
Zai zama da taimako ka faɗa ba shakka da cewa ya warke. AT: "mutumin ya warke!ya tashi"
"tsoro sosai" ko cike da fargaba"
"abubuwan ban mamaki" ko "sabobin abubuwa"
sashin "wadannan abubuwa" na nufin abin da ya faru a ayoyin ɗaya wuce. Wannan ya nu na sabuwar abu.
"dubi mai karban haraji da kulawa" ko dubi mai karban haraji a hankali"
ka "bini" wani ya zama al'majerin mutumin. AT: "ka zama al'majeri na" ko "zo, ka bini a masayin malamin ka"
"ya bar aikin sa a masayin mai karban haraji"
"a gidan Lawi"
Hanyar cin abincin Gareka a biki shi ne a kwanta a gado a madogari kanka sama da hanun hagu akan wasu filo. AT: "cin abinc tare" ko "cin abinci akan taburin"
"wa al'majeren Yesu"
Farisawa da marubutan suka yi wannan tambayan su nuna rashin yardan su da almajeren Yesu da cewa suna cin abinci da masu zunubi. AT: "Kada ku ci abinci da masu zunubi!"
Farisawa da marubutan sun yarda da cewa mutanen addini su raba kansu da masu zunubi. Wannan kalmar "ku" jam'i ne.
Yesu ya yi amfani da ƙarin magana ya fara gaya masu ya kira masu zunubi su tuba kamar yadda likita suke kiran marasa lafiya su warke.
likita
za ka iya kara abin da aka cire. AT: "marasa lafiya kadai suke nemam likita"
Wasu mutane suna tunanin cewa suna da adalci. Yesu ya yi nufin su kamar yadda suke tunani ko da shike ya sani cewa ba su da adalci. AT: "mutanen da suke tunanin cewa suna da adalci"
"Shugabanen adinin sun cewa Yesu"
Yesu ya yi amfani da wannan tambayan domin ya sa su su yi tunani game da yanayin da sun sani. Wannan za'a iya rubuta shi kamar bayani. AT: "Akwai wanda zai sa abokan ango su yi azumi, a lokacin da shi ango yana tare da su"
"baki" ko "abokai" Wannan abokai ne wadanda suke yi murna da wanda yake yin aure.
Azumi alamar bakin ciki ne. shugabanen adini sun gane da cewa abakan ango ba za su yi azumi ba sa'anda angon yana tare da su.
"kusa" ko "wata rana"
Yesy ya na kwatanta kan sa da angon, al'majeren kuma abokan angon. juyawa ya bayana shi idan ya zama dole.
Yesu ya gaya wa Farisawa da marubutan labari wadanda suke gidan lawi.
babu wanda zai girbe ... yi amfani ... shi ... shi" ko "mutane kada su yage ... yi amfani ... su... su"
gyara
Wannan bayanin yana yin da ba'a gani ba ya rega ya bayana dalilin da mutum ba zai gyara rega a waccan hamyar ba.
"ba zai hadu ba" ko "ba zai zam daidai ba kamar"
"ruwan inabi." Wannan ya na nufin ruwan inabi da bai tashi.
Wadannan jaka ne da aka yi da fatar dabba. Za'a iya kiran su "jakar ruwar inabi" ko "jakar da aka yi da fata."
sa'anda sabuwar ruwan inabin ya tashi kuma ya karu. zai fashe tsohowar fatar domin ba za su iya mikewa kuma ba. ma su sauraron Yesu sun gane bayanin game da ruwan inabi da ya tashi kuma ya karu.
AT: "ruwan inabin zai zuba daga cikin jakan"
"sabon fatar ruwan inabin" ko sabuwar jakan ruwan inabin." Wannan na nufin sabon fatar ruwan inabin, da ba'a yi aiki da shi ba.
Wannan misalin ya haɗa tsohowar koyas su wan shugabanen addinin akan sabuwar koyasuwan Yesu. maganar shi ne mutanen da suka saba da tsohowar kayasuwan ba su yarda su ji sabuwar kayasuwan da Yesu ya na koyarwa.
"ruwan inabi da ya tashi"
Zai zama da taimako ka kara: kuma baya so ya gwada sabuwar ruwan inabi"
Dauka kwalekwalen zuwa wuri mai zurfi a ruwan ka sa ragan ka a cikin ruwan don ka kama kifi.
Ya yi biyayya ya kuma sake da ragan.
Su kama kifi dayawa sosai har ragan su yana yagawa.
Saminu ya so Yesu ya tafi daga wurin shi domin Saminu ya sani wai (Saminu) mai zunubi ne.
Yesu ya ce nan gaba mutane zai rika kamowa.
Taron mutane dayawa suna zuwa wurin Yesu.
Malam an gafarta maka zunubanka.
Domin Allah kadai na gafarta zunubai.
Yesu ya warkar da mutumin ya nuna yana da izni a duniya ya gafarta zunubai.
Ya zo ya kira masuzunubi su tuba.
Almajiran sa za su yi azumi bayan an dauki Yesu daga su
Sabon rigan zai yage, kuma ba zai dace da tsohuwar tufar ba.
Tsofaffin salkuna zai fasa kuma sabon ruwan inabi zai zube.
Dole a sa sabon ruwan inabi a cikin sabobin salkuna.
1 Ana nan wata Asabaci Yesu yana ratsawa cikin gonar hatsi, almajiransa kuma na karyar zangarkun hatsin, suna murtsukawa a hanayensu suna ci. 2 Amma wasu daga cikin Farisawa suka ce, "Saboda me kuke yin abin da bai halatta a yi a ranar Asabaci ba?" 3 Yesu ya amsa masu, ya ce, "Ba ku karanta abin da Dauda ya yi a lokacin da yake jin yunwa ba, shi da mutanen da ke tare da shi? 4 Ya je cikin gidan Allah, ya dauki gurasar alfarwa ya kuma ci daga ciki, ya kuma ba mazajen da ke tare da shi su ci, ko da shike ya halarta ga Firistoci ne kadai su ci." 5 Sai ya ce masu, "Dan Mutum shi ne Ubangijin asabaci." 6 Ya kasance a wata ranar Asabaci ya shiga cikin majami'a ya kuma koya wa mutane a can. Wani mutum na can wurin wanda hannun damansa ya shanye. 7 Marubuta da Farisawa na kallonsa su ga ko zai warkar da wani a ranar Asabaci, domin su samu dalilin zarginsa da yin abin da bai cancanta ba. 8 Amma ya san abin da suke tunani, sai ya ce wa mai shanyeyen hannun, "Tashi, ka tsaya a nan tsakiyar jama'a." Sai mutumin ya tashi ya tsaya a nan. 9 Yesu ya ce masu, "Ina tambayar ku, ya halatta a ranar Asabaci a yi nagarta ko mugunta, a ceci rai ko a hallaka shi? 10 Sai ya dube su duka, ya kuma ce wa mutumin, "Mika hannunka." Ya yi haka, sai hannunsa ya koma lafiyayye. 11 Amma suka fusata kwarai, suka yi shawara da junansu game da abin da za su yi da Yesu. 12 Ya zama a kwanakin nan, ya hawo bisan dutse domin ya yi addu'a. Ya ci gaba dukan dare yana addua'a ga Allah. 13 Da safiya ta yi, ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya kuma zabi goma sha biyu daga cikinsu, wadanda ya kira su "Manzanni." 14 Sunayen Manzannin sune Siman (wanda ya kuma kira Bitrus) da dan'uwansa, Andrawus, Yakubu, Yahaya, Filibus, Bartalamawus, 15 Matta, Toma, Yakubu dan Halfa, Siman, wanda ake kira Zaloti, Yahuda dan Yakubu, 16 da Yahuda dan Iskariyoti, wanda ya zama maci amana. 17 Sai Yesu ya gangaro daga dutsen tare da su, suka kuma tsaya a sarari. Almajiransa da yawa na nan a wurin, tare da mutane da yawa daga Yahudiya da Urushalima, da kuma bakin tekun Taya da Sidon. 18 Sun zo domin su ji shi, da kuma su sami warkarwa daga dukan cututukansu. Mutane waddan da ke fama da kazaman ruhohi ma sun sami warkarwa. 19 Dukan taron jama'ar suna kokarin su taba shi domin ikon warkarwa yana fitowa daga wurinsa, ya kuma warkar da su duka. 20 Sai ya dubi almajiransa ya ce, "Masu albarka ne ku matalauta, gama Mulkin Allah naku ne. 21 Masu albarka ne ku masu yunwa yanzu, domin za a kosar da ku. Masu albarka ne ku masu kuka a yanzu, domin za ku yi dariya. 22 Masu albarka ne ku idan mutane sun ki ku, suka nuna maku wariya suna mai da sunayen ku na mugunta, domin Dan Mutum. 23 Za ku yi farin ciki a ranan nan kuna tsalle domin murna, domin hakika za ku samu lada mai girma a sama, domin haka kakannin-kakannin su suka yi wa annabawa. 24 Amma kaitonku mawadata! Domin kun rigaya kun samu ta'aziyar ku. 25 Kaitonku kosassu a yanzu! Domin za ku ji yunwa nan gaba. Kaitonku masu dariya yanzu! Domin za ku yi makoki kuna kuka nan gaba. 26 Kaiton ku idan kowadanne mutane suna yabon ku! Domin haka kakannin-kakanninsu suka yi wa annabawan karya. 27 Amma ina ce maku ku masu saurare na, ku kaunaci magabtanku, ku kuma aikata nagarta ga wadanda suke kinku. 28 Ku albarkaci masu zaginku, ku kuma yi addu'a ga wadanda suke wulakanta ku. 29 Wanda ya mare ku a wannan kunci, ku juya masa dayan. Idan wani ya dauki mayafinka, kada ka hana masa taguwarka. 30 Ku bayar ga duk wanda ya roke ku. Idan wani ya dauki wani abu da ke naku, kada ku bidi ya mayar da shi. 31 Duk abin da kake so mutane su yi maka, ka yi masu hakan nan. 32 Idan ka kaunaci masoyan ka ne kadai, me wannan zai amfane ka? Ko masu zunubi ma na kaunar masoyan su. 33 Idan kuna nuna alheri ga wadan da ke maku alheri kadai, menene ladan ku a nan? Ko masu zunubi ma na yin hakan nan. 34 Idan kun ba da rancen abubuwa ga mutanen da kuna sa zuciya zasu mayar maku ne kadai, menene ribar ku a nan? Ko masu zunubi suna ba masu zunubi rance, suna kuma sa zuciya a mayar masu dadai gwargwado. 35 Amma ku kaunaci magabtan ku, ku kuma nuna masu alheri. Ku basu rance, kada ku sa zuciya a maido maku, kuma sakamakon ku zai zama da girma. Za ku zama yayan Mafifici, domin shi da kansa yana nuna jinkai ga marasa godiya da miyagun mutane. 36 Ku zama masu jinkai, domin Ubanku mai jinkai ne. 37 Kada ku shari'anta, kuma ba za a shari'anta ku ba. Kada ku kayar, ku ma ba za a kashe ku ba. Ku yafe wa wasu, kuma za a yafe maku. 38 Ku bayar ga wasu, ku ma za a ba ku da yawa. Magwaji dankararre, girgizajje har ya cika yana zuba, za su zuba har cinyarku. Domin duk ma'aunin da ku ka yi amfani da shi, da shi za a auna maku. 39 Sai ya sake basu wani misali, "Makaho yana iya yi wa makaho jagora? Idan ya yi haka, dukansu biyu za su fada cikin rami, ko ba haka ba? 40 Almajiri baya fin Malaminsa, amma duk wanda ya samu horo sosai zai zama kamar malaminsa. 41 Don me kake duba dan hakin da ke a idon dan'uwanka, amma ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba? 42 Don me za ka ce wa dan'uwanka, 'Dan'uwa, bari in cire dan hakin da ke a idonka', bayan kai da kanka ba ka iya ganin gungumen da ke a idonka ba? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen da ke a idonka, sa'annan za ka gani da kyau yadda zaka cire hakin da ke a idon dan'uwanka. 43 Domin babu itace mai kyau da ke haifar rubabbun 'ya'ya, ko rubabben itace da zai haifi kyawawan 'ya'ya. 44 Domin ana iya sanin ko wani itace ta wurin 'ya'yan da yake bayarwa. Domin mutane basu kan tsinki 'ya'yan baure a jikin kaya, ko kuwa su dibi inabi daga jikin sarkakkiya. 45 Mutumin kirki, daga wadatar zuciyarsa ya kan ba da yaya masu kyau, kuma mugu daga cikin muguwar ajiyar zuciyarsa yake aikata mugunta. Domin daga cikar zuciyarsa ne bakinsa yakan yi magana. 46 Don me kuke ce da ni, 'Ubangiji, Ubangiji', amma ba ku yin biyayya da magana ta? 47 Duk wanda ya zo wurina ya ji kalmomina ya kuma yi biyayya da su, zan gaya maku yadda yake. 48 Yana kama da mutum da ke gina gida, wanda ya haka da zurfi zuwa cikin kasa ya kuma gina harshashin gidan sa a kan dutse. Da rigyawa ta zo, sai ruwa ya buga gidan, amma bai iya girgiza shi ba, domin an gina shi da kyau. 49 Amma duk mutumin da ya ji kalmomina ya kuma ki biyayya da su, yana kamar mutum wanda ya gina gidansa a kan kasa, babu harshashi. Amma da ambaliyan ruwa ta buga gidan, nan take ya rushe, ragargajewar gidan kuma da girma take.
sa'anda Yesu da al'majeren sa suke tafiya a gonar hatse, wasu Farisawa sun fara tambayan al'majeren game da abin da suke yi a ranar Asabaci, Wamda a dakar Allah an keɓe shi wa Allah.
Wannan kalmar "kai" anan jam;i ne, kuma ya na nufin al'majerensa.
Wannan sashin an yi amfani da shi anan domin a sa alama a sabuwar abin da ya auko a labarin. Idan yaren ku na da wata hanya na yin haka za ku iya amfani da shi anan.
a A wannan yana yi, akwai babbar gona wanda mutane suka wasa irin alkama domin ya yi girma.
Wannan shi ne sashi mafi sama na shukar hatsi, wanda shi ne irin babbar ciyawan. Ya rike nunannen, irin shukar mai ciyuwa.
Suna yin haka domin su raba irin hatsin. Wannan za'a iya bayyana shi ba shakka. AT: "Suna murtsukawa a hanayensu domin su raba hatsin daga ƙaiƙayin"
Sun yi wannan tambayan domin su zaigi al'majeren cewa suna ƙarya doka. za'a iya rubuta shi kamar bayyani. AT: "tsinan hatsi ranar Asabaci gana gaba da dokar Allah!"
Farisawan dubi karamin aikin murtsukawa a hanu ciki da hatsi aikin da ba na doka ba. Wannan za'a iya bayyana shi ba shakka. AT: "yin aiki"
Yesu ya kwaɓe Farisawan domin sun ki su koya daga lattafi. Wannan za' iya rubuta kamar bayyani. AT: "ku koya da ga abin da kuka karanta ... shi!" ko "ba shakka kun karanta ... shi!"
"gurasa mai tsarki" ko "gurasan da aka mika wa Allah"
Yesu ya na nufin kansa. Wannan za'a iya bayyana: AT: "Ni, Dan Mutum"
sunar "Ubangiji" anan ya yi nauyin bisa Asabaci. AT: "yana da iko ya yarda wa mutane abi da za su yi a ranar Asabaci!"
Wannan sashin an yi amfai da shi anan domin a sa alama akan sabuwar abin da ya aukoa labarin.
Wanna ya gabatar da sabuwar hali a labarin.
hanun mutumin ya bace a wata hanya da ba zai iya mikar da shi ba. mai yuwa ya lankwashekusan dunkulallen, ya zama karami da tamoji.
"suna kallon Yesu a hankali"
"domin suna so su samu"
"a gaban jama'a." Yesu yana so mutumin ta tsaya a wurin da jama'ar zasu gan shi.
"ma Farisawan"
Yesu ya yi tambaya domin ya sa farisawan su yarda da cewa ya yi daidai ya warkar a ranar Asabaci.niyar tambaya ba domin a ba shi amsa bane: ya sasu su yarda ne cewa duk sun sani gaskiya ne a maimakon ya sami bayyani. ko da shike Yesu ya ce, Na tambaye ku," saboda haka wannan tambayan ba kamar sauran tambayan da ba su bukatar amsa bane wanda suna so a juya su kamar bayyani. a juya su kamar tambaya. :
"ka taimaki wani ko ka hallakar da wani"
"rike hannun ka waje" ko "Mika hannun ka"
warke
Wannan sashin an yi amfani da shi anan domin a sa alama a sabuwar abin da ya auko a labarin.
"a kusa da lokacin" ko "bada daɗewa ba bayan" ko wata rana kusa da"
"Yesu ya je waje"
da safiya ta yi" ko "rana ta gaba"
"ya zabi al'majerensa goma sha biyu"
"wanda ya zamar da su manzanni" ko ka kuma sai ya zaɓe su su zama manzanni"
Luka ya rubuta tsarin sunayen manzannin. UDb ya yi amfani da wannan kalmar ya gabatar da tsarin.
"dan'uwan, Siman"
Ma'ana mai yuwa 1) "Zaloti suna ne wanda ya nuna da cewa ya na cikin sashin kungiyan da suka so su saki mutanen Yahudawa daga mulkin Romawa. AT: "yan kishin ƙasa" ko "yan ƙasar" ko 2) "Zaloti kwatancen da ya nuna cewa ya na da himma wa Allah ya sami daraja. AT: "mai so na kwaria"
Zai zama dole ka bayyana me "cin amana" yake nufi a wannan mahallin. AT: "ba she abokin sa" ko "ba da abokin sa ga makiyan sa" (yawanci a maimakon kuɗi a biya) ko "bijirar abokin sa ga hadari game da gaya wa makiyan game da shia"
"da sha biyun da ya zaba" ko "da al'majeren sa gama sha biyu"
AT: "Yesu ya warkar da su"
AT: "Yesu ya kuma warkar da mutane wanda suke fama da kazaman huhohi"
"mugun ruhohi ke damum su" ko "sarrafa da mugayen ruhohi"
"ya na da iko ya warkar da mutane" ko "yana amfani da ikon sa ya warkar da mutane"
Wannan sashin an maimaita shi sau uku. kowanni lokaci,ya nuna da cewa Allah ya bawa yarda ga wasu mutane ko yana yin su na da kyau ko mai yaƙani.
"Kumatalauta ku karɓe yardar Allah2 ko "Ku d akuke matalauta amfane"
Yaren da basu da kalma na mulkin za su iya cewa, "Allah ne mulkin ka" ko "domin Allah ne mai mulkin ka."
"mulkin Allah naku ne." Wannan zai iya zama 1) "ku na mulkin Allag ne2 ko 2) "za ku sami iko a mulkin Allah."
"za ku yi dariya da farinciki" ko "za ku zama masu murna"
"ki ku"
"domin kun hada kai da Dan Mutum" ko "domin su ki Dan Mutum"
"sa'anda suka yi wadannan abubuwan" ko "sa'anda ya faru"
Wannan ƙarin na nufin "yi marna sosai"
"babban biya" ko "kyautuna masu kyau"
"yada zai zama maku" Wannan sashin ya sake maimaitawa sau uku. kashiyar Allah ya sa maku albarka ne." kowanne lokaci, ya nuna da cewa hushin Allah ya na kanku daidai, ko da cewa wani abu mai kyau ko mumuna na jeran ku.
"yadda zai zama maku ku masu kuɗi" ko "damuwa zai zu maku ku masu kuɗi"
"abin da zai yi na ku ta'aziyar" ko "abin da zai biya maku bukata" ko abin da zai saku murna"
wanda cikin su ya cika yanzu" ko " wanda sun ci sosai"
"Wanda suke murna yanzu"
Anan "mutane" an yi amfani da su ma'ana danginsu hada da dukkan mutane. AT: "sa'anda kowanne mutum ya yi magana" ko "sa'anda kowa ya yi magana"
"kakannin-kakanninsu sun yi magana da kyau game da annabawan karya"
Yesu yanzu ya fara yi wa dukkan taron magana,a maimakon al'majerensa kadai.
kowanne umurnin ya ka mata acigsbs da bi,bana lokaci daya ba.
Wannan bai yi nu fin cewa su kaunaci magabtan su kadai ba ba abokan su ba. Wannan za'a iya bayyana. AT: kaunaci magabtan ku, ba abokan ku kwai ba"
Wannan sashi biyun na nufin abu ɗaya, kuma tare yake yin nauyin aya.
Allah ne wanda zai yi albarku. Wannan za'a iya bayyana. AT: "tambayi Allal ya albarkaci wadanda"
"wadanda suka zage ku akidar"
"wadanda suka wulakanta ku akidar"
"Idan wani ya buga ku"
"a gefen fuskan ku"
Zai zama da taimakoa ce ma harin zai yi wamutumin. AT: "juya fuskar ka saboda yamare ka a ɗayangefen kuncinkuma"
"kada ka hana shi daga dauka"
Idan kowa ya tambaye ka abun, ka ba shi"
"kadaku nemi ya bayar" ko "kada ku bukata ya bayar"
A wasu yareuka zai iya zama na halita a juya wannan umurnin. AT: "Duk abin da kake so mutane su yi maka, ka yi masu hakan nan" ko "yi wa mutane yadda ka ke so a yi maka"
"wani lada za ka karba?" ko "wani yaba za ka masu don yin haka?" baza ka barbi wani lada don yin haka ba." ko "Allah ba zai baka lada don yin haka ba."
Dokan Musa ya umurci Yahudawa kada su karbi riba akan kuɗin rancen da kuka ba wa juna.
kada ku sa zuciya a maido maku
"kada ku sa zuciya mutumin ya maido maku abin da kuka ba shi" ko "kada ku sa zuciya mutumin ya baku komai"
" za ku karbe babban sakamako" ko "zaku karbe biya mai kyau" ko "zaku sami kyau ta masu kyau sabo da shi"
Zai fi kyau ka juya" 'ya'yan" da kalma iri ɗaya yarenku zasu iya nufin cewa yaron mutum ne ko ɗa.
ya zama na cewa kalmar nan "ya'ya" jam'i ne domin kada a rikice da sunar Yesu "Dan Mafifici."
"mutanen da ba su yi masa godiya ba kuma mugaye ne"
Wannnan na nufin Allah. zai fi kyau a juya "Uba" da kalaman da yaren ku suke anfani da shi ga uban mutum.
"Kada ku shari'anta mutane" ko "kada ku zargi mutane mummunan"
"domin sakama kon ku"
Yesu bai fada wanda ba za'a shari'anta ba. Ma'ana mai yuwa 1) "Allah ba zai shari'anta ka ba" ko 2) "ba wanda zai shari'anta ka"
"Kada ku hukunta mutane"
Yesu bai fada wanda ba za'a hukunta ba. Ma'ana mai yuwa 1) "Allah ba zai hukunta ka ba" ko 2) "ba wanda zai hukunta ka"
Yesu bai fada wanda zai yafe ba. Ma'ana mai yuwa 1) "Allah zai yafe ku" ko 2) "mutane za su yafe maku"
Yesu bai fada asalin wanda zai bayar ba. Ma'ana mai yuwa 1) "wani zai baka" ko 2) "Allah zai baka"
Yesu ya yi magana ko a kak Allah ko mutane suna bayar karaminci kamar yana magana akan mai say da sayar da karimi hatsi. AT: "Allah zai zuba maku a cinyar ku karimi iya yawan kuɗi- dankararre girgizajje har ya cika yana zuba" ko "Kamar mai say da sayar da karimi hatsi wanda ya dankare hatsin ya girgizajje su tare kuma ya hatsi sosai hay rana zuba, za'a baku karaminci"
"babban kuɗi"
Yesu bai fada asalin wanda zai auna maka ba. Ma'ana mai yuwa 1 ) "za'a auna maku" ko "Allah zai auna maku"
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya sa mutanen su yi tunani wani abun da sun riga sun sani. Wannan za'a iya rubu ta kamar bayyani. AT: "dukka mun sani da cewa makaho ba zai iya yi wa makaho jagora ba."
Mutum wanda baya gani "makaho" misali ne na mutum wanda ba'a taba koya masa ba kamar al'majeri.
wasu yaren za su so, "Idan wani ya yi."wanna abu mara ma'ana ne wanda zai ba mutum dariya yana yin da ba zai iya faru ba.
Wannan za'a iya rubuta shi kamar bayyana. AT: "dukkan su zasu fadi a rami"
"Almajiri baya fin Malaminsa." Ma'ana mai yuwa 1) " Al'majeri ba ya yin ilimi fiya ea malaminsa" ko 2) "Al'majeri ba shi da iko mafi yawa fiye da malaminsa."
"kowani al'majeri wanda aka horas da shi da kyau" ko "kowani al'majeri wanda malaminsa ya koya masa"
Yesu ya yi amfani da tanbaya domin ya tsokane mutanen su kasa kunne ga zunuban su kamin su kasa kunne ga ga zunuban wasu. AT: "gungume da ke idanun ku."
Wannan misali na nufin mutane laifi mara muhimmanci na yan'uwa masubi.
"ɗigo" ko "tsage" ko "kura da ƙadan." yi amfani da ƙaramin abu da yawanci ya ke faɗiwa a idanuwan mutane.
Anan "dan'uwa" na nufin yan'uwa masubi Yahudawa ko yan'uwa masubi a cikin Yesu.
Wannan masalin ne na laifin mutum mafi muhimmanci. gungume ba na zahiri ba ne ya shiga idon mutum. Yesu ya yi furci domin ya yi nauyin mutum ya kasa kunne ga laifin sa mai muhimmanci kamin jiwa laifin wasu mutane mara muhimmanci.
"azara" ko "katako"
Yesu ya yi amfani da ya yi amfani da tambaya domin ya tsokane mutane su kasa kunne ga zunuban su kamin su kasa kunne ga zunubin wasu. AT: "Kada ka ce ... ido."?
Wannan domin babu." Wannan ya nuna da cewa abin da ya biyo baya dalili ne domi kada mu sharanta dan 'uwar mu.
"lafiyayen itace"
'ya'yan da suka bace ko mara kyau ko mara amfani
Mutane suna gane irin itace da 'ya'yan da take haifa. AT: "mutane suna gane irin itacen" ko "mutane suna gane itacen"
shuke ko ƙaramin itace mai ƙaya
inabi ko ƙaramin itace da yake da ƙayoyi
Wannan kalmar "kirki" anan na nufin adalci ko na halin kirki.
Kalmar nan "mutum" anan na nufin mutum, ma miji ko ta mace. AT: "mutumin kirki"
A nan tunanin mutum na kirki ana maganar sa kamar wadatar da aka yi ajiyar ta a zuciyar mutum, da "zuciya" misali ne na cikin ran mutum. AT: "abubuwa masu kyau da ya ajeye a cikinsa" ko "abubuwan da ya daraja mai yawa"
Haifar abin da ke da kyau misali ne na yin abin da ke da kyau. AT: "yi abin da ke da kyau"
A nan tunanin muguntar mutum an yi maganar sa kamar abubuwar mugunta ne aka ajiye a zucuyar mutum , kuma "zuciyarsa" misali ne na cikin ran mutum. AT: "abubuwar mugun ta da ya ajiye a cikin sa" ko "abubuwar mugun ta da ya daraja sosa"
A nan "zuciyz" misali ne na ran mutum ko cikin rai. sashin nan "bakinsa" misali ne na mutum gaba ɗaya. AT: "abin da yake tunani a zuciyar sa yana safar abin da bakin sa ya ke faɗa" ko "mutum zai yi magana da ƙarfi abin da ya daraja a cikin sa"
Maimaitawan wannan kalmar ya nuna da cewa yawanci suna kiran Yesu "Ubangiji."
Mai yuwa zai zama da kyau ba shakka a sake umurnin wannan bayanin. AT: "zan gaya maku yadda yake wanda ya ji magana na ya yi umurni da su"
tona tushin gidan sa da nisa sosai ya kai tushin a kan dutse." wasu al'adun ba su gane yin gini akan gadon dutse, kuma za su so su yi amfani da wata hoto domin wata tushi mai daɗi.
sashin gida da ya hada shi da ƙasa. Mutane a lokacin Yesu su na tuna zuwa cikin ƙasa zuwa kan dutse mai ƙaure sia su fara gini a kak dutse mai ƙaure. dutsen shi nn tushin.
gadom dutse." Wannan babab, dutse mai ƙarfi wanda yana ƙarƙashin ƙasa.
"ruwa mai gudu" ko "rafi"
"rushe akan"
Ma'ana mai yuwa 1) "ya sa shi girgiza" ko "rushe shi."
AT: "domin mutumin ya gina shi da kyau"
"Amma" nuna bambanci mai ƙarfi zuwa ga mutumin da aka yi maganar sa a baya wanda ya gina gidan da tushi.
Wa su al'adun ba su sani da cewa gida mai tushi ya fi ƙarfi. ƙarin bayani zai zama da taimako. aT: "amma bai tuna ƙasa da farko ya gina tushin"
faɗi ƙasa ko zo rabe
"waccan gidan ya rushe gaba ɗaya"
Suna zagi alkamar, suna murtsukewa a tsakanin hanayen su, kuma suna cin hatsi.
Yesu ya da'awa sunan, Ubangijin Ashabar.
Sun husata kwarai, suka yi shawarar abin da za su yi wa Yesu.
Yesu ya kira su "manzanni".
Wadanda su matalauta, fama da yunwa, kuma wanda a ki su saboda Dan Mutum suna da albarka.
Domin za su same lada mai yawa a sama.
Su kaunaci magabranku su kuna su yi alheri ma makiyansu.
Yana masu alheri kuma yana musu rahama.
Farko, dole mu cire gungume daga idanun mu, don kada mu zama munafukai.
Abin da na fito daga zuciyar mutum mai kirki na da kyau.
Abin da na fito daga zuciyar mutum mai muguta shi ne mugu.
Ya ji maganan Yesu, ya kuma aikata su.
Ya ji kalmomin Yesu kuma bai aikata su ba.
1 Bayan da Yesu ya gama fadar dukan abubuwan da zai fadi a jin kunnen dukan mutanen, sai ya shiga Kafarnahum. 2 Bawan wani jarumi, wanda yake kauna, ba shi da lafiya har ma ya kusa mutuwa. 3 Amma da ya ji labarin Yesu, jarumin ya aiki wadansu dattawan Yahudawa, ya ce a roki Yesu ya zo ya ceci bawansa daga mutuwa. 4 Sa'adda su ka zo kusa da Yesu, su ka roke shi da gaske, cewa, "Wannan ya isa ka yi masa haka, 5 saboda shi mai kaunar kasar mu ne, kuma shi ne ya gina mana majami'a. 6 Sai Yesu ya tafi tare da su. Amma sa'adda ya zo kusa da gidan mutumin, jarumin ya aiki abokansa su ka ce da shi, "Ubangiji kada ka damu domin ni ban isa ka zo gida na ba. 7 Shi ya sa na ga ban isa in zo wurinka ba, ka yi magana kadai bawa na kuwa zai warke. 8 Gama ni ma mutum ne mai iko, ina da sojoji karkashina. Ina iya cewa da wannan, 'Ka je' sai ya tafi, in kuma ce da wani 'ka zo' sai ya zo, in kuma ce da bawa na, 'Yi kaza,' sai ya yi." 9 Sa'adda Yesu ya ji haka, ya yi mamakin mutumin, ya juya wajen taron da su ke biye da shi, ya ce, "Na gaya maku, ko a cikin Isra'ila ban sami wani mai bangaskiya irin wannan ba" 10 Daga nan wadanda a ka aika, suka dawo gida suka tarar da bawan cikin koshin lafiya. 11 Wani lokaci bayan wannan, ya zama Yesu yana tafiya wani gari da ake kira Na'im. Almajiransa su na tare da shi, da kuma taron mutane masu yawa. 12 Sa'adda ya kusa da kofar garin, sai ga wani matacce ana dauke da shi. Kuma shi kadai ne da a wurin mahaifiyarsa. Ita kuwa gwauruwa ce, mutane da dama daga cikin gari suna tare da ita. 13 Da ganin ta, sai Ubangiji ya cika da tausayi a game da ita ya ce da ita, "Kada ki yi kuka." 14 Sai ya zo ya taba makarar, sai masu dauke da shi su ka tsaya. Ya ce 'Saurayi na ce ma ka ka tashi." 15 Sai mataccen ya tashi ya fara yin magana. Sai Yesu ya ba mahaifiyar danta. 16 Sai tsoro ya kama su duka. Su ka kama yabon Allah, su na cewa, "An ta da wani annabi mai girma a cikinmu" kuma "Allah ya dubi mutanensa." 17 Wannan labari na Yesu, ya ba zu a cikin dukan Yahudiya da yankuna da su ke kewaye. 18 Almajiran Yahaya suka gaya masa dukan wadannan abubuwa. 19 Sai Yahaya ya kira biyu daga cikin almajiransa, ya aike su wurin Ubangiji, suka ce da shi, "Kai ne mai zuwan nan, ko akwai wani wanda za mu saurari zuwansa?" 20 Sa'adda suka zo kusa da Yesu, sai mutanen suka ce, "Yahaya Mai Baftisma, ya aiko mu, mu tambaya, "Kai ne mai zuwan nan, ko akwai wani wanda za mu saurari zuwansa?" 21 A cikin wannan lokaci, ya warkar da mutane da yawa daga cututtuka da matsaloli da miyagun ruhohi. Makafi da yawa sun sami ganin gari. 22 Yesu, ya amsa ya ce masu, "Bayan kun tafi, ku ba Yohanna rahoton abin da ku ka ji da abin da ku ka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana kuma tsarkake kutare. Kurame suna ji, ana tayar da matattu, ana gaya wa matalauta labari mai dadi. 23 Mai albarka ne mutumin da ya tsaya a kan ba da gaskiya gare ni saboda ayukan da na ke yi." 24 Bayan da mutanen da Yahaya ya aiko suka tafi, Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yahaya. "Me ku ka tafi ku gani a cikin hamada, ciyawa wadda iska ta ke girgizawa? 25 Amma me ku ka tafi domin ku gani, mutum mai saye da tufafi masu taushi? Duba mutanen da su ke saye da tufafi masu daraja, kuma suna rayuwa cikin jin dadi suna fadar sarakuna. 26 Amma me ku ka tafi domin ku gani, annabi ne? I, ina gaya ma ku, ya ma fi annabi. 27 Wannan shine wanda aka rubuta a kansa, "Duba, ina aika manzo na a gabanka, wanda za ya shirya maka hanya a gabanka. 28 Ina gaya maku, a cikin wadanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka, wanda ya fi kankanta a mulkin Allah, ya fi shi girma. 29 Sa'anda dukan mutane suka ji haka, har da ma su karbar haraji, suka shaida Allah mai adalci ne. Su na cikin wadanda Yahaya ya yi wa baftisma. 30 Amma Farisawa da wadanda su ke kwararru a cikin shari'ar Yahudawa, wadanda ba shi ne ya yi masu baftisma ba, suka yi watsi da hikimar Allah don kansu. 31 Sa'annan Yesu ya ce, "Da me zan kamanta mutanen wannan zamani? Da me suka yi kama? 32 Suna kama da yaran da suke wasa a kasuwa, wadanda suke magana da junansu suna cewa, "Mun yi maku busa, ba ku yi rawa ba. Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba." 33 Haka, Yahaya ya zo, bai ci gurasa ba, bai sha ruwan inabi ba, amma ku ka ce, 'Aljani ne yake mulkinsa. 34 Dan Mutum, ya zo, yana ci, yana sha, amma, kuka ki shi, kuna cewa dubi mutum mai hadama, mai shan ruwan inabi da yawa, abokin masu karbar haraji da masu zunubi! 35 Amma hikimar Allah tana shaidar dukan 'yayanta." 36 Wata rana wani Bafarise, ya roki Yesu ya je ya ci abinci tare da shi. Bayan da Yesu ya shiga gidan Bafarisen, ya zauna a teburi domin ya ci abinci. 37 Sai ga wata mace mai zunubi, ta fito daga cikin birni. Sa'anda ta ji labari Yesu yana gidan Bafarisen, domin ya ci abinci. Ta dauki tandun mai na alabastar mai kamshi. 38 Ta tsaya kusa da Yesu tana kuka. Ta fara jika kafafunsa da hawayenta, tana shafe kafafunsa da gashin kanta. Tana yi wa kafafunsa sumba, tana shafe su da turare. 39 Sa'anda Bafarisen da ya gaiyaci Yesu, ya ga haka, sai ya yi tunani a cikin ransa, da cewa, "In da wannan mutum annabi ne, da ya gane ko wacce irin mace ce, wannan da take taba shi, ita mai zunubi ce." 40 Yesu ya amsa ya ce masa, "Siman, ina so in gaya maka wani abu." Ya ce, "malam sai ka fadi!" 41 Yesu ya ce, "wani mutum mai ba da bashi yana bin wadansu mutane su biyu kudi, yana bin dayan sule dari, dayan kuma yana bin sa sule hamsin. 42 Da yake ba su da kudin da za su iya biyan sa, sai ya yafe masu, su duka biyu. A cikin su biyu, wanne ne zai fi nuna kauna ga wannan mutum?" 43 Siman ya amsa ya ce, "Ina tsammani wanda ya yafe wa kudi da yawa." Yesu ya amsa ya ce masa, "Ka shari'anta dai dai." 44 Yesu ya juya wajen matar, ya ce da Siman, "Ka ga matan nan. Na shiga gidanka. Ba ka ba ni ruwa domin kafafuna ba, amma ita ta ba ni, da hawayenta ta wanke kafafuna, ta kuma shafe su da gashin kanta. 45 Kai ba ka yi ma ni sumba ba, amma ita ta yi, tun sa'adda na shigo nan ba ta dena sumbatar kafafuna ba. 46 Kai ba ka shafe kai na da mai ba, amma ita ta shafe kafafuna da turare. 47 Saboda haka, ita wadda ta ke da zunubi da yawa ta bayar da mai yawa, ta kuma nuna kauna mai yawa. Amma shi wanda aka gafarta wa kadan, ya kuma nuna kauna kadan." 48 Daga nan sai ya ce mata, "An gafarta zunubanki." 49 Wadanda su ke a nan zaune tare da shi suka fara magana da junansu, "Wanene wannan wanda har yake gafarta zunubai? 50 Sai Yesu ya ce da matar, "Bangaskiyarki ta cece ki. Ki tafi da salama."
Yesu ta shiga Kafarnahum inda ya warkar da bawa na shakaru dari.
ƙarin "a jin" ya yi nauyin da cewa ya na son su su ji abin da zai faɗa. AT: "ga mutanen da suki jin sa" ko "ga mutanen da su ke gun" ko ga mutanen su ji"
Wannan ya fara sabuwar abnu a labarin
"wanda jarumin yake daraja" ko "wanda yake grimamawa"
"ya yi masa rok" ko "roke shi"
"jarimin ya isa"
"mutanen mu." Wanna na nufin mutanen Yahudawa.
"tafi tare"
Yare na ƙasa za ' iya mai da. AT: "kusa da gidan"
Jarumin ya mai da ladabi yana magana da Yesu. AT: "kada ka dami kanka da zuwa gida na" ko "Ba na so in dameka"
Wannan sashin ƙari ne da yake nufin "shigo gida na." Idan yaren ku na da ƙari da yake nufin "shigo gida na," ti tunani ko yana da kyau a yi amfani da shi anan. ̇
Bawan ya gane da cewa Yesu zai iya warkar da bawan da magana kawai. Anan "kalma" na nufin umurni. AT: "ka bada umurni kawai"
Kalmar da aka juya anankamar "bawa"an saba juya ta kamar "yaro." zai nuna da cewa bawan karamin yaro ne ko nuna ƙaunar jarumin mi shi.
"I na da wani fiye da ni wanda dole in yi biyayya dashi"
"a karka shin iko na"
Kalmar da aka juya anan kamar "bawa" na hali kalma ne na bawa.
"ya yi mamakin jarumin"
Yesu ya faɗi wannanya yi nauyin abin mamakin da yake so ya faɗa musu.
Ma'ana shi ne Yesu yana tsammani mutanen Yahudawa su samu irin wannan bangaskiya, amma basu da shi. Ba ya tsammanin al'umai su samu irin wannan bangaskiya. duk da haka wannan mutum ya na da shi. mai yuwa za ka iya kara irin wannan labarin. AT: "Ban sami wani dan Isa'ilawa wanda ya gaskanta da ni kamar yadda wannan ba al'ume ya yi!"
An gane da cewa wadannan sune mutanen da jarumin ya yi aika. AT: "mutanen da hafsa Roma ya aika wa Yesu"
Yesu ya ji ƙasar Na'im, Inda ya warkar da wani mutum da ya mutu.
sunsr birnin
Wannan kalmar "gama" ya fahimtar da mu da mu da gabatar da mu ga wani mattacan mutum a labari. Mai yuwa Yaren ku suna da wani iri hanyan yin haka. AT: "akwai wani mutum wanda"
AT: "mutanen su na daukan mutanen da suka mutu zuwa wajen garin"
"dauka waje. shi ne ɗa a wurin mahaifiyarsa, kuwa ita gwauruwa ce. kokuwa taro dayawa." wannan bayani ne na ƙasa game da mutun wanda ya mutu da mahaifiyarsa.
matan da maigidan ta ya mutu kuma ba ta yi aure ba
"ya ji tausa yin ta"
"ya tafi gaba" ko "ya kusata da mutumin da ya mutu"
Wannan gadon daukan mara lafiya ko gado da ake amfani da shi a dauke jiki zuwa wurin biso. Bai zama wani abun da aka binne jikin ba. wasu masu juyan mai yuwa suna da kadan na kullum "anna'ashi" ko "gadon jana'izan."
Yesu ya faɗa wannan domin ya yi nauyin da cewa ya kamata wannan mutum ya yi umurni da shi. saurare ni! tashi"
mutumin har yanzu a mace yake; yanzu ya na da rai. zai zama da kyau ka bayana wannan. AT: "mutumin da ya mutu"
"dukak su sun ciki da tsoro." AT: "sun cika da tsoro sosai"
Suna nufin Yesu ba wa wani annabin da ba 'a gane shi ba." anan ƙari ne "na saka zama." AT: "Allah ya sa wani a cikin mu ya zama annabi" da
Wannan ƙarin na nufin "kula ga"
"Wannan labarin" na nufin abun da mutane suke faɗa a aya 16. AT: "Mutanen sun baza rehoton game da Yesu" ko "Mutane sun gaya wannan rehoton game da Yesu"
"Wannan rehoton" ko "Wannan labarin"
Wannan ya gabatar da sabuwar abu a labarin.
"gaya wa Yahaya"
"dukkan wadannan abubuwan da Yesu yake yi"
Wannan bayanin za'a iya rubuta domin a sa ya zama fɗi daidai guda ɗaya. AT: "mutanen sun ce Yahaya mai baftisma ya aike su gun sa su yi tambaya, 'Kai ne wanda kake zuwa, ko mu sa ido ga wani?"' ko "mutaanen sun ce, 'Yahaya mai baftis ma ya aike mu gun ka mu yi tambaya cewa kai ne kake zuwa ko mu sa ido ga wani'"
"ko mujire wani" ko "ko mu tsammaci wani dabam"
"A waccan lokacin"
Zai zama da taimako to a sake faɗan warkasuwan. AT: "ya warkar da su daga miyagun ruhohi" ko "sabo da haka ya warkar da mutane daga miyagun ruhohi"
"ya gaya wa dan aikan Yahaya" ko "ya gaya wa mai aikan Yahaya"
"gaya wa Yahaya"
"mutanen da suka mutu suna raye kuma"
"matalauta mutane"
AT: "Allah zai albarkace mutumin da ya daina bada gaskiya da ni saboda ayukana"
"Mutanen da basu yarda ... masu albarkane" ko "Duk wanda bai ... mai albarkane" ko "Duk wadda bai yarda ba ...mai albarkane." Wannan ba tabbatatcen mutum bane.
Wannan mara yaƙani yana nufin "cigaba da yarda da ni koda"
"bada gaskiya gaba ɗaya"
Wannan ana sammanin amsa mara yaƙani. ka je waje ka gan ciyawa wadda iska ta ke girgizawa? A'a!" za'a iya rubuta shi kamar bayani/ AT: "ba shakka ba ka je waje ka gan ciyawa wadda iska ta ke girgizawa!"
Ma'ana mai yuwa 1) mutumin da yana iya sake hankalin sa, ko 2) mutumin da yana magana dayawa amma baya faɗan abin mai muhimmanci, kamar yadda ciyawa yana cikasaura da makamancinsa da amon motsinsu idan iska ya hura su.
Wannan ma yana sammanin amsa mara yaƙani, tunda Yahaya ya sa tufafi mara kyau. "ka je waje ka ga mutumin da ya sa tufafi masu taushi? A'a!" Wannan za'a iya rubuta shi kamar bayani. AT: "kai ba shakka baka je waje ka ga mutumin da ya sa tufafi masu taushi!"
Wannan na nufin tufafi masu tsada. tufafi na kullum ba su da kyau. AT: "sa tufafi masu tsada"
fada na da babbane, gida mai tsada da sarki yake zama a ciki.
Wannan ya kai ga amsa mai yaƙani. ka je waje ka gan annabi? a ai ka yi!" Wannan za'a iya rubuta shi kamar bayani. AT: "Amma ainihi ka je waje ka ga annabi!"
Yesu ya faɗa haka domin ya yi nauyin muhimmancin abin da zai faɗa na biye.
Wannan sashin ya nuna da cewa gaskiya Yahaya annabi ne, amma ya ma fi annabi. AT: "ba annabi kawai ba" ko "ya ma fi muhimmanci da annabin kullum"
"Da cewa annabi shi ne wanda annabi suka rubuta a kan sa" ko "Yahaya shi ne wanda annabawa suka rubu ta akan sa tun da daɗewa"
A wannan ayan, Yesu yana faɗin annabi Malachi kuma yana cewa Yahaya shi ne dan aika wanda annbi Malachi ya yi magana.
Wannan ƙarin ya na nufin "a gabanka" ko "yav tafi a gabanka"
Wannan kalmar "naka" mafuradi ne domin Allah yana magana akan Mai ceto a faɗin.
"a cikin wadanda mata suka haifa." Wannanmisali ne da ya ke nufin dukkan mutane. AT: "a dukkan mutanen da suka taba rayuwa"
"Yahaya ya fi girma"
Wannan yana nufin duk wanda ya sashin mulkin da Allah zai kafa.
Wannan ruhaniyan mutane a mulkin Allah zai fi na mutane kamin a kafa mulkin. AT: "yana da ruhaniya sosai fiye da Yahaya"
Wannan ayan za'a iya rubuta domin ya zama mai sauki. AT: "Sa'anda dukkan mutanen da Yahaya ya yi masu baftisma, har da masu karban haraje , sun je haka, sun shaida da cewa Allah mai adalcine"
"sun ce da cewa Allah ya nuna kansa mai adalci" ko "sun shaida da cewa Allah ya yi aikin Adalci"
AT: "domin sun bar Yahaya ya yi masu baftisma" KO "domin Yahaya ya yi masu baftisma"
"suka ƙi abin da Yesu yana so su yi" ko "suka so su yi rashin biyyaya da abin da Allah ya gaya masu su yi"
AT: "ba su bar Yahaya yayi masu baftisma ba" ko "sun ƙi baftismam Yahaya"
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya gabatar da kwatantawa. za'a iya rubuta su kamar bayani. AT: "Wannan shi ne abin da na kwatanta wannan zamanin da shi, kuma suna kamar me."
Wannan hanya biyu ne na faɗan cewa wannan kwatanci ne.
mutanen da suke zama sa'anda Yesu yana magana.
Wadannan kalmomin sune farkon kwatancin Yesu. ya cewa mutanen suna kamar yara wanda basu gamsuwa da yadda wasu yara suke aikatawa".
babban budaɗen fili da mutane suke zuwa su sayar da kaya
"amma ba ku yi rawa wakar ba"
"amma ba ku yi kuka da mu ba"
Ma'an mai yuwa 1) "azumi koyaushe" ko 2) "ba su cin abin ci kullum."
Yesu ya na faɗan abin da mutane suka ce game da Yahaya. wannan za'a iya faaɗ ba da faɗi daidai ba. AT: "kun ce yana da aljanu." ko "kun yi masa shari cewa ya na da aljanu."
Yesu yana sammanin mutanen su gane da cewa yana nufin kansa, AT: "Ni, Ɗan Mutum"
Wannan za'a iya juya kamar daidai faɗi. AT: "kuncu shi mutum mai handama ne da kuma ma shayi ... zunubi." ko "kun yi masa shere da cewa yana ci yana sha da yawa kuma ya na zama ... zunubi."
"shi mai cin zari ne" ko "ya cigaba da cin abin ci"
"mai sha" ko "ya cigaba da shan barasa"
Wannan ƙarin magana ne da Yesu ya yi a yanayin, mai yuwa ya koya wa masu hikima da cewa da ba su ƙi su aƙrbi Yesu da Yahaya.
Alamar farawa a sabuwar sashin labarin kuma ya gabatar da Bafarise a cikin labarin.
"ya zauna a tebur don abinci." aladane hutun cin abincin dare kamar haka wa mutane su ci suna kwance da daɗi kewaye da tebur.
Kalmar "gama" ya ba mu saurin fahimtan wani sabon mutum a labarin. mai yuwa yaren ku na da wata hanyar yin haka.
"wa yake zaman zunubi" ko "wa yake da sunan zaman rayuwan zunubi." mai yuwa karuwa ce.
"tulun da aka yi da duwatsu mai taushi." alabastar farin dutse ne mai taushi. mutane su na ajiya abubuwa masu kyau a tulun alabastar.
"da mai mai kamshi a cikin." mai din yana da wata abu abu a cikin ta daya ke sa ta yi kamshi mai kyau. mutane suna sha fa akan su ko su yayafa a tufafin su domin su yi kamshi mai kyau.
"da gashin ta"
"wasa turarea kan su"
"ya cewa kansa"
Bafarise ya yi tunani da cewa Yesu ba annabi bana domin yana barin masu zunubi su taba shi. AT: "A bayyane Yesu ba annabi bana, domin annabi zai sani wannan matan da take taba shi mai zunubi ce"
Siman ya yi tunani da cewa annabi ba zai taba barin mai zunubi ya taba shi ba. Wannan sashin tunanin sa za'a iya bayana shi ba shakka. AT: "da cewa ita mai zunubi ne, kuma ba zai barta ta ba shi ba"
Wannan sunan Bafarisen ne wanda ya gayaci Yesu zuwa gidan sa. Wannan ba Siman Bitrus bane.
"mutane biyu sun karba bashin kuɗi a wurin wani mai bada bashin"
"kwana 500' hakin." "dinari jam'i dinari ne." dinari ƙarreran kuɗin azurfa ne.
"dayan mai bashin ya reke masa dinari hamsin" ko "hakin kwana 50"
"ya yafe masu bashin su" ko "ya share masu bashin"
Siman yana hankali game da amsan sa. AT: "mai yuwa"
"ka yi daidai"
Yesu ya sa hankalin Siman ya koma gun matar ta juyawa wajen ta.
hakin mai gida ne ya bawa baƙi ruwa da tawul domin su wanke ƙafafun su sai su dushar bayan da su yi tafiya a hanya mai kura.
Yesu ya yi amfani da sashin sau biyu domin ya hada rashin ladabin Siman da masanancin aikin godiyar zuciya.
Matan ta yi amfani da hawayenta a maimakon ruwa.
Matn ta yi amfani da gashin kanta a masayin tawul.
Mai gida mai kyau a aladar zai gaishe baƙi da sumba a ƙunci ba. Siman bai yi haka ba.
"ta cigaba da yin sumbantar ƙafafuwana"
Matar ya yi sumbatar ƙafan Yesu a maimakon ƙuncin sa a masayin masanancin nuna tawali'u.
Yesu ya cigaba da hada rashin kyaun liyafar Siman da aikin matar.
"sa mai a kai na." Wannan aladane na marabtan bako mai daraja. AT: "marabtana da shafa mini mai a kai na"
Matar ta daraja Yesu sosai da yin haka. ta kwatanta tawali'u da shafe ƙafafun sa a maimakon kansa.
AT: "Allah ya yafe zunuban ta masu yawa"
ƙuanar ta shaida ce da cewa an yafe zunuban ta. Wasu yaren suna neman abu na " ƙauna" a faɗa. AT: "gama tana ƙaunar wanda ya yafe mata zunuban ta sosai" ko "gana tana son Allah sosai"
"duk wanda aka yafe masa abubuwa kadan." A wannan jumlan Yesu ya faɗa ƙa'da na gaba ɗaya. yadda da ya na sammanin Siman ya gane da cewa ya nuna wa Yesu ƙauna kadan.
"Sai ya ce wa matar"
"An yafe miki." AT: "Na yafe zunubanki"
"zaune tare kewaye da tebur" ko "cin abinci tare"
Shugabanen adini sun sani da cewa Allah ne kadai yake gafrta zunubi kuma basu yarda da cewa Yesu Allah ne ba. Wannan tambayan mai yuwa domin a yi zargi ne. AT: "Wannan mutumi ya na tunanin shi wanene? Allah ne kadai yake gafrta zunubi!" ko Me ya sa wannan mutumin ya na yi kamar shi Allah ne, wanda shi kadai ne yake gafarta zunubi?"
"Domin bangaskiyarki, kin sami ceto." tsamo isimi "bangaskiya" za'a iya faɗan ta kamar aiki. AT: "Domin kin bangaskiya, kin sami ceto"
Wannan hanya ce na ce sai anjema da bayar da albarka a lokaci ɗaya. AT: "sa'anda kin tafi, kada ki damu kuma" ko "bari Allah ya baki salama sa'anda kin tafi"
Ya tambai Yesu ya zo gidan shi kuma ya warkar da bawan sa.
Jarumin ya ce bai isa har Yesu ya zo gidan sa ba.
Jarumin ya so Yesu ya warkar da bawan sa ta wurin fadi kalma.
Yesu ya ce ko a cikin Isra'ila bai taba samun bangaskiya mai karfi irin wannan ba.
Ya yi motsi warai da tausayinta.
Sun ce wai annabi mai girma ya bayyana a cikin su, kuma Allah ya kula da mutanen shi.
Yesu ya warkar da makafi, guragu, kutare, da kurame, da kuma tayar da matattu.
Yesu ya ce Yahaya ne ya fi kowannne annabi.
Sun shure abin da Allah yakw nufinsu da shi.
Sun ce, "Yana da iska".
Sun ce, "Shi mutum mai hadama da mashayi".
Ta jika kafafunsa da hawayen ta, ta share da tsuman ta, ta yi sumba da su, da kuma ta shafa kafafunsa da man kanshi.
Zata yi kauna mai yawa.
Sun tanbaya, "Wannan kuwa wane ne wanda har gafarta zunubai?".
1 Bayan haka, Yesu da almajiransa goma sha biyu, su ka zagaya cikin birane da kauyuka dabam dabam, suna wa'azi da shelar labari mai dadi game da mulkin Allah, 2 mata da yawa wadanda Yesu ya warkar daga aljanu da cututtuka iri iri suna tafiya tare da su. A cikinsu akwai Maryamu wadda a ke ce da ita Magadaliya, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta, 3 da Yuwana matar Kuza wakilin Hirudus, da Suzanatu da kuma wasu mata da yawa. Daga abin hannunsu suka tanada masu. 4 Wata rana aka tara taron mutane da yawa, saboda mutane su na zuwa daga birane da yawa domin su ga Yesu. Ya yi magana dasu cikin misali. 5 "Wani mai shuka ya tafi domin ya shuka iri. Sa'adda ya ke yafa iri, wadansu iri suka fada a kan hanya. Sai mutane suka tattake su, tsuntsaye kuma suka tsince wadansu suka cinye. 6 Wadansu kuma suka fada a kan duwatsu inda babu kasa da yawa. Da suka tsaro suka fara girma, sai nan da nan suka bushe saboda babu laima a wurin. 7 Wadansu irin kuma suka fada inda yake da kayayuwa. Tsiretsiren kayayuwan suka fito tare da irin da aka shuka, suka shake su yadda basu iya yin girma ba. 8 Amma wadansu irin suka fada a kan kasa mai kyau, suka yi girma sosai suka ba da anfani da yawa, har rubi dari." Bayan da Yesu ya fadi wadannan abubuwan, sai ya yi kira gare su, "Duk mai kunnen ji, bari ya ji." 9 Sai almajiran Yesu suka tambaye shi ya gaya ma su ma'anar labarin. 10 ya ce da su, "Ku aka ba dama ku gane boyayyun abubuwa, na mulkin Allah. Amma ga sauran mutane ina yi masu magana cikin misalai, 'Domin ko da sun gani ba za su gane ba, kuma ko da sun ji ba za su fahimta ba." 11 To ga ma'anar misalin. Irin shi ne maganar Allah. 12 Irin da ya fada a kan hanya sune mutanen da suka ji maganar Allah amma daga baya sai shedan ya zo ya dauke maganar daga cikin hankulansu, domin kada su bada gaskiya su tsira. 13 Sa'annan, wadanda suka fada kan duwatsu sune mutanen da, da zarar sun ji maganar, sukan karbe ta da murna, amma ba su da sauyu; su kan bada gaskiya na dan lokaci kadan kawai, da zaran gwaji ya same su sai su ridda. 14 Irin da suka fada cikin kayayuwa, sune mutanen da suka ji maganar, amma da suka ci gaba da rayuwa, sai suka bari matsalolin rayuwa kamar dukiya da jin dadin rayuwa suka fi karfinsu, sai ya zama ba su iya bada 'ya'yan da suka yi girma ba. 15 Amma irin da suka fada a kan kasa mai kyau, wadannan sune mutanen da suka ji maganar, suka karbe ta da gaskiya da zuciya daya, sun rike ta kam-kam, suna jimrewa wurin ba da 'ya'ya. 16 Ba mai kunna fitila, ya rufe ta da kasko, ko su sa ta a karkashin gado. Amma sai a sa ta a wurin zaman ta domin duk wanda ya shigo ya iya ganin hasken ta. 17 Babu abin da yake a boye wanda ba za a tone shi ba, ko wani asiri da ba za ya fito fili a san shi ba. 18 Ku yi hankali da yadda kuke ji, domin duk mai abu, shi za a kara wa, kuma duk mara abu, dan kadan da yake tunani yana da shi ma, za a dauke." 19 Sai mahafiyar Yesu da 'yan'uwansa, su ka zo wurinsa, amma ba su iya zuwa ko kusa da shi ba saboda taron jama'a. 20 Sai wani ya gaya masa, "Ga mahaifiyarka da 'yan'uwanka, su na tsayuwa a waje, su na son ganin ka." 21 Amma Yesu ya amsa ya ce ma su, "Mahaifiyata da 'yan'uwana sune wadanda suke jin maganar Allah, suke yin biyayya da ita." 22 Wata rana kuma Yesu ya shiga cikin jirgin ruwa, shi da almajiransa. Ya ce masu, "Ina so mu je dayan ketaren tafkin." Sai su ka fara tafiya domin su ketare tafkin. 23 Amma sa'adda su ke tafiya sai Yesu ya yi barci, sai wata iska mai karfi ta taso cikin tafkin, nan da nan sai jirgin ya fara cika da ruwa, kuma su na cikin hatsari. 24 Sai almajiran Yesu su ka zo su ka tashe shi daga barci. Suka ce da shi, "Ya Shugaba! Ya Shugaba! Za mu mutu!" Sai ya tashi ya umarci iskar, sai iskar mai hauka da tumbatsar ruwan sun tsaya tsit. 25 Daga nan sai ya ce da su, "Ina bangaskiyar ku?" Almajiran suka tsorata suka yi mamakin abin da ya faru nan take. Suka ce wa junansu, "Wanene wannan wanda har zai ba iska da ruwa umarni kuma su yi masa biyayya?" 26 Suka zo yankin Garasinawa, wanda ke kusa da Gallili. 27 Sa'adda Yesu ya sauka kasa, sai wani mutum daga wannan yankin ya tarbe shi. Wannan mutum kuwa yana da aljanu. Mutumin ya dade ba ya sa tufafi, kuma ba ya zama a gida. Maimakon haka, sai a cikin kabarbura ya ke zama. 28 Sa'adda ya ga Yesu, mutumin ya yi ihu da karfi, ya rusuna a gabansa da babban murya ya ce, "Me zan yi da kai, Yesu, Dan Allah Madaukaki? Ina rokonka, kada ka ba ni azaba!" 29 Domin Yesu ya umarci aljanun su fita daga cikinsa, domin sau da dama aljanun sukan kama shi. Ko an daure mutumin da sarkoki an kuma tsare shi, yakan tsuttsunke su, kazaman ruhohin sukan kora shi cikin jeji. 30 Sa'annan Yesu ya tambaye shi, "Yaya sunanka?" Sai ya ba da amsa, "Suna na dubbai." Ya ce haka ne domin aljanu da yawa sun shiga wannan mutum. 31 Aljanun suka yi ta rokon Yesu kada ya ummarce su su shiga cikin rami mai zurfi. 32 Akwai babban garken aladu su na kiwo a kan tsauni kusa da wurin. Aljanun suka roki Yesu da ya barsu su shiga cikin aladun, shi kuwa ya yarda masu. 33 Aljanun suka bar mutumin suka shiga cikin aladun, sai garken aladun suka gangara kwari suka fada cikin tafkin, suka nutse. 34 Lokacin da mutanen da su ke kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka gudu! Suka ba da rahoton abin da ya faru ga mutanen cikin gari da na wannan kewayen. 35 Don haka, mutanen da suka ji haka suka tafi domin su ga abin da ya faru, suka zo wurin da Yesu yake, suka ga mutumin wanda aljanu suka fita daga cikinsa. Suka ga ya na sanye da tufafi, kuma ya na cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su. 36 Mutanen da suka ga abin da ya faru, suka gaya wa wadansu yadda aka warkar da mutumin da aljanu suke iko da shi. 37 Sai dukan mutane wadanda suke cikin yankin Garasinawa da wadanda suke kewaye, suka roki Yesu da ya fita daga cikin yankin kasarsu domin sun ji tsoro kwarai da gaske. Daga nan Yesu da almajiransa suka shiga cikin jirgin ruwa suka koma. 38 Mutumin wanda aljanu suka fita daga cikinsa, ya roki Yesu cewa, "Ka barni in tafi tare da kai!" Amma Yesu ya sallame shi cewa, 39 "Ka koma gida ka gaya wa mutanen ka abubuwa masu girma wadanda Allah ya yi maka." Daga nan sai mutumin ya tafi yana ta gayawa dukan mutanen birnin game da abubuwan da Yesu ya yi masa. 40 Sa'adda Yesu ya dawo, mutanen suka marabce shi, gama, dukansu suna jiransa. 41 Sai ga wani mutum mai suna Yayirus, daya daga cikin shugabannin majami'a, ya zo kusa da Yesu ya rusuna da kansa a kasa. Ya roke shi domin ya zo gidansa, 42 saboda diyarsa mai kimanin shekara goma sha biyu ta na bakin mutuwa, kuma ita kadai ce diya a gare shi. Amma sa'adda yake tafiya, taron mutane da yawa suna matsa shi. 43 Akwai wata mace a nan wadda take zubar jini har shekara goma sha biyu. Ta kashe kudinta duka a wurin likitoci, domin su warkar da ita amma ba wanda ya iya warkar da ita. 44 Sai ta biyo ta bayan Yesu ta taba habar rigarsa. Nan take sai zubar jinin ya tsaya. 45 Yesu ya ce, "Wanene ya taba ni?" Wadanda suke kewaye da shi, kowa ya ce bai taba shi ba, Bitrus ya ce, "Shugaba, mutane da yawa suna ta taruwa kewaye da kai suna ta matsowa kusa da kai." 46 Amma Yesu ya ce, "Na sani, wani ya taba ni, domin iko ya fita daga wurina." 47 Sa'adda matar ta gane cewa ba za ta iya boyewa ba, sai ta zo wurinsa cikin tsoro. Ta durkusa a gaban Yesu, ta fada a gaban dukan jama'a dalilin da ya sa ta taba shi kuma nan da nan ta warke. 48 Sai ya ce da ita, "Diya, bangaskiyarki ta warkar da ke. Tafi cikin salama." 49 Yana cikin yin magana, wani daga cikin gidan shugaban majami'ar ya zo, ya ce, "Diyarka ta riga ta mutu, kada ka dami malam." 50 Amma sa'adda Yesu ya ji haka, sai ya ce da shi, "Kada ka ji tsoro. Ka bada gaskiya za ta rayu." 51 Sa'adda ya zo gidan, bai bar kowa ya shiga gidan tare da shi ba sai Bitrus da Yahaya da Yakubu, da mahaifiyar yarinyar da babanta. 52 Dukan mutane a wurin, suna ta kuka da karfi saboda sun damu da yarinyar ta mutu. Amma Yesu ya ce da su, "Ku dena kuka! Ba mutuwa ta yi ba! Barci ta ke yi kawai!" 53 Mutanen suka yi ma sa dariyan reni, saboda sun sani yarinyar ta mutu. 54 Amma ya kama hannun ta yayi kira cewa, "Yarinya, na ce ki tashi!" 55 Nan da nan ruhun ta ya dawo jikin ta sai ta tashi. Ya ce masu su ba ta wani abu ta ci. 56 Iyayenta suka yi mamaki, amma Yesu ya ce da iyayen kada su gaya wa kowa abin da ya faru.
Wannan ayan ya ba da labari na ƙasa game da Yesu yana koyasuwa sa'anda yake tafiya.
Wannan sashin an yi amfani da shi a nan domin a sa alama a sabuwar sashin labarin.
AT: "wadanda Yesu ya warkar da su daga aljanu da cututtuka iri iri"
Uku da ga cikin maatan aka lissafa: Maryamu, Yuwana, da Suzanatu.
AT: "Maryamu wanda mutane suke kira Magadaliya ... wanda Yesu ya cire aljanu bakwai daga cikin"
Yuwana, matar Kuza kuma kuza wakilin Hirudus, "Yuwana, matar wakilin Hirudus, kuza"
"sun taimaki Yesu da almajerensa da kuɗi"
"zuwa gun Yesu"
"Wani mai shuki ya fita ya wasa iri a gona" ko "Wani manomi ya je gona ya warwasa iri a gona"
"wasu irin sun faɗi" ko "wasu irin ya faɗi"
AT: "mutane suka yi tafiya a kan shi" ko "mutane suka yi tafiya akai"
Wannan ƙarin za'a iya juya shi da sauki kamar "tsuntsaye" ko "tsuntsaye suka faɗi ƙasa kuma" a ajiye hankalin "sararin sama."
"ya bushi sosai" ko "suka bushi sosai." Abin da ya saza'a iya faɗan ta. AT: "ƙasan ya bushi sosai"
Yesu ya gama gaya wa taron misali.
ƙayan shukin ya dauki dukkan abin da zai sa shi girma, ruwa, hasken rana,sabo da haka shukin manomin ba zai yi girma da kyau ba.
"girmar da girbi" ko "girmar da iri iri sosai"
Wannan na nufin sau dari fiye da abin da aka shuka.
Zai iya zama na halita ga wasu yaren su yiamfani da mutum na biyu: "kai da kake da kunnene ji, ka ji"
Ma'ana mai yuwa 1) "kowani ɗaya" tun da kowa yana da kunne ko 2) "duk wanda zai iya ganewa" wanda yake nufin wanda yana so ya saurari Allah.
"sai ya ji da kyau" ko "ya nasu ya ji abin da na faɗa"
AT: "Allah ya ba ku damar gane ... Allah" ko " Allah ya sa ku ku gane ... Allah"
Wannan gaskiya na da aka boye, Amma yanzu Yesu yana bayana masu.
"wa wasu mutane." Wannan na nufin mutanene da suka ki koyasuwan Yesu kuma sun ki su bishi.
"ko da sun gani, ba za su gane ba." Wannan faɗi ne daga annabi Ishaya. Wasu yaren za su so su faɗa manufan wannan fi'ilin. AT: "koda shike suna ganin aabubuwa,ba za su gane su ba" ko "ko da sun gan abu na faruwa, ba za su gane abin da suke nufi ba"
"ko da sun ii, ba za su gane ba." Wannan faɗi ne daga annabi Ishaya. Wasu yaren za su so su faɗa manufan wannan fi'ilin. AT: "koda sun ji umurni, ba za su gane gaskiyan ba"
"Irin saƙone da Allah"
Wannan irin da suka faɗi tare a kan hanya sune wadanda." Yesu ya faɗa abin da ya faru da irin kamar ya ruwaita da mutane. AT: "Irin da suka faɗi akan hanya na nufin mutane" ko "a misalin iri da suka faɗi akan hanya sune mutane"
Yesu ya yi magana akan irin ya na nuna wani abu game da mutane kamar irin mutane ne AT: "nuna abin da ya faru da mutane"
A nan "zuciya" misali ne na hankalin mutane ko na ciki mutum. AT: "shedan ya zo ya dauke magana Allah daga cikin zuciyanansu"
A wannan misalin ne wannan tsuntsun ne ya ƙwace irin. yi ƙoƙi ka yi amfani da kalma a yaren ku da zai ajiye hotan wannan.
tunda wannan manufan shaidan, za'a iya juya shi kamar: AT: "domin shiadan ya yi tunani, domin kada su bada gaskiya su tsira,' ko" kada ya zama sun yarda da Allah sun tsira."
"Irin da suka faɗia kan duwatsu sune wadanda."Yesu ya faɗa abin da ya faru da irin kamar ya ruwaita da mutane. AT: "Wannan irin da suka faɗi akan duwatsu na nufin mutane" ko "A misalin irin da suka faɗi akan duwatsu na nufin mutane"
"dueasun ƙasa"
"sa'anda suka ji wahala"
Wannan ƙarin na nufin "sun daina bada gaskiya" ko "sun daina bin Yesu"
"Irin da suka fada cikin kayayuwa, na nufin mutanen" ko " A misalin irin da suka faɗi a kayayuwa na nufin"
AT: "kula, da arziki dajin dadin wannan rayuwa ya ware su"
abubuwan da mutane suka damu a kai
"abubuwan wannan rayuwa da mutane suke jindadin"
Wannan misalin na nufin yadda iri ya ke yanka wuta da abin da ya ke sa su girma daga shukin kuma ya hana su girma. AT: "kamar yadda ciyawa yake hana shuki girma, da kila da arziki da jin dadin wannan rayuwa ya na hana wadannan mutane daga girma"
"ba su haifan 'ya'yan da suka nuna." nunannae 'ya'ya misali ne na kyawawan ayuka. AT: "sabo da haka kamar yadda shuki ba ta haifan nunannen 'ya'ya,ba su yin kuawawan ayuka"
"irin da suka fada a kan ƙasa mai kyau na nudin mutane" ko "A misalin irin da suka fada a kan ƙasa mai kyau na nudin mutane"
"jin wannan saƙon"
A nan "zuciyz" misali ne na tunanin mutum ko niyya. AT: "da gaskiye da bege mai kyau"
"haifan 'ya'ya da hakurin jimrewa" ko "haifan 'ya'ya da ƙokrin cingaba." 'ya'ya misali ne na ayuka masu kyau. AT: "kamar yadda shuki masu kyau suke haifan 'ya'ya masu kyau,suna haifan ayuka masu da jumriya"
Wannan ya sa alaman farawa na wata misali
AT: " duk abin da ya ke rufe za a bayyana ta"
Wannan abin da ba mai yaƙani ba za'a iya rubu ta shi kamar bayani mai yaƙani. AT: " duk wani abu da ya ke asirance za'a san shi kuma zai bayyana a hhaske"
Mai saukin gana wa ne a mahallin da Yesu yana magana game da ganewa da bada gaskiya. Wannan za'a iya faɗa ba shakka domin a sake siffa mai ƙoƙari. AT: "duk wanda ya gane za'a sake ganer da shi" ko "Allah zai sa wanda suka yarda da gaskiya su sake yarda soasi"
Mai saukin gana wa ne a mahallin da Yesu yana magana game da ganewa da bada gaskiya. Wannan za'a iya faɗa ba shakka domin a sake siffa mai ƙoƙari. AT: "Amma duk wanda ba shi da ganewa zai rasa ganewa da yake tunani yana da shi" ko Allah zai sa duk wanda ba su yarda da gaskiya ba kada su gane ko kaɗan da suke tunani sun gane"
Wadannana ƙannen Yesu ne- sauran yaran Maryamu da Yusufu wanda aka haife su bayab Yesu. Tunda Uban Yesu Allah ne, sanannun rabin yan'uwansa ne. Wannan bayyani ba a juya shi kullum.
AT: "mutane suka gaya masa" ko "wani ya gaya masa"
"kuma suna so su ganka"
Wannan misalin ya kwatanta da cewa mutanen da suke zuwa gun Yesu suna da muhimmaci masa feye da iyalin sa. AT: "Wadanda suke jin maganar Allah, suke yin biyayya da ita sune kamar mahaifiyata da 'yan'uwana ne"
"maganar da Allah ya faɗa"
Wannan tafkin janisarata ce wanda ake kira tekun Galili.
Wannan kwatancin ya na nufin cewa sun fara tafiya a ketaren tafkin ƙyallen kwalekwale.
"sa'anda suke tafiya"
"fara barci"
"iska mai ƙarfi ya fara" ko "iska mai ƙarfi nan da nan ya fara busawa"
Iska mai ƙarfin ya sa raƙumin ruwa ya yi yawa har ya tira ruwa a gefen jirgin. AT: "iskan ya sa raƙumin ruwa mai ƙarfi da ya fara ya cika jirgin su da ruwa"
magana nan da nan wa
"raƙumin ruwa mai ƙarfi"
"iskan da raƙumin ruwan su tsaya" ko "sun tsaya tsit"
Yesu ya kwaɓi su mara tsanani domin ba su gaskak ta da shi ya kula da su ba. Wannan za'a iya rubu ta shi kamar jumla. AT: "ku sami bangaskiya" ko "ku yarda da ni!"
"Wani irin mutum ne wannan ... yi biyayya da shi?" Wannan tambayan ya furcin ya nuna motse mai tsanani da rikicewa bisa yadda Yesu ya yi mulki da iskan.
Wannan za'a iya juya shi kamar jumla: "Toh wanene wannan mutuimn? ya umurta ... yi biyayya da shi!"
Garasinawa inda mutane birnin suke kira jarasa.
"a ɗayan gefen tafkin Galili"
"wani mutum daga birnin jarasa"
mutumin yana da aljanu; ba birnin bane yake da aljanu. AT: "wani mutum daga birnin, kuma wannan mutumin yana da aljanu"
"wanda aljanu suke mulki da shi" ko "wanda aljanu na mulki da shi"
Wannan labari ne na ƙasa game da muyumin.
"bai sa tufafi ba"
Wannan wurare ne inda mutane suke sa mattatu, mai yuwa kogon dutse ko karamin gini da mutane za su iya amfani da shi kamar tsari.
"Sa'anda mutumin da yake da aljanu ya ga Yesu"
"yi ihu" ko "ya yi kururuwa"
ya kwanta a ƙasa a gaban Yesu." bai faɗi da hadari ba.
"ya ce da ƙarfi" ko "ya yi ihu"
Wannan ƙarin yana nufin "don me kake damuna?"
Wannan suna mai muhimmanci ne ga Allah.
"sau da dama ya yi mulkin mutumin" ko "sau da dama ya shige shi." Wannan ya faɗa abin da aljanun ya yi wa muyumin kamai Yesu ya hadu da shi.
AT: "ko da shike mutanen sun daura shi da sarka da mari kuma sun tsare shi"
AT: "aljanun za su sa shi ya tafi"
Juya wannan kalmar da ya ke nufin lambar sojoji dayawako mutane. wasu masu juyin suka ce "runudnar yaƙi." AT: "bataliya" ko "sashin rundunar sojoji"
"suka yi ta rokon Yesu"
Wannan ya bada labari na ƙasa ya gabatara da aladu.
"suna kusa suna ci ciyawa a kak tsauni"
Kalmar " sai" an yi amfani da shi anan domin a bayyana dalilin da aljanun su ka fito waje daga cikin mutumin domin Yesu ya ce masu su je cikin aladu.
gudu da sauri
"garkin ... suka nutse." ba wanda ya sa aladun su nutse tunda su ke cikin ruwa.
"sun gan mutumin wanda aljanu suka bar shi"
"mai hankali" ko "yana yin hali na kullum"
"zaune a ƙafafu" a nan ƙari ne da yake nufin "zaune da tawali'u kusa" ko "zaune a gaba AT: "zaune a gaban Yesu"
Zai zama da taimako ka bayyana da cewa sun jin tsoron Yesu. AT: "suna jin tsoron Yesu"
"wandanda suka gan abin da ya faru"
AT: "Yesu ya warka da mutumin da aljanu suka yi iko da shi" ko "Yesu ya warkar da mutumin wanda aljanu sun yi mulki da shi"
"waccan filin Garasinawa" ko "filin da inda mutanen Garasinawa suke zama"
AT: "sun fara ji tsoro sosai"
wurin zaman za'a iya faɗa. AT: "suka koma ketaren tafkin"
Abin da ya auko a wannan ayan ya faru kamin Yesu ya bar jirgin. zai zama da taimako ka faɗe shi ba shakka daga farko. AT: "Kamin Yesu da almajeren sa su bar mutumin" ko "Kamin Yesu da almajeren sa su shirya ƙyallen da aka rataya a kwalekwalen, mutumin"
"gidanka" ko "iyalin ka"
"gaya masu komai game da abin da Allah ya yi maka"
"taron suka gaishe shi da murna"
"ɗaya daga cikin shugabannin majami'a na wuri ɗaya" ko "shugaban mutanen wanda sun hadu a cikin majami'a"
Ma'ana mai yuwa 1)"ya runsuna a ƙafafun Yesu" 2)"ya kwanta a ƙasa aƙafafun Yesu."Yayirus ya rusuna da kansa a ƙasa bai faɗi da hadari ba. ya yi haka a alamar tawali'u da bada girma wa Yesu.
"ta kusa mutuwa"
Wasu masu juyin za su ce Yesu ya yarda da farko ya tafi da Yayirus. AT: "sai Yesu ya yarda ya je da shi. da yana kan hanya"
"tarom sun matsu kewaye da Yesu"
Wannan ya gabatar da sabuwar hali a labarin.
"tana da zuban jini." mai yuwa tana zubar da jini daga mahiafa ko da ba lokacin haka ba. wasu aladun suna da wata hanya mai sauki na nufin wannan yana yin.
AT: "amma ba wanda zai warkar da ita"
"ta taba geza rigansa." Mutanen YahudawaMai yuwa wannan shi ne abin da ta tabba. suna sa tunku a habar rigunar su kamar kayan biki kamar yadda aka umurta a dokan Allah. Mai yuwa wannan shi ne abin da ta tabba.
ba faɗan haka, Biturus ya na nuna da cewa kowa zai iya taba Yesu. Wannan bayanin za ka iya bayyana shi in ya zama dole. AT: "akwai taron mutane dayawa kewaye da kai da suna ta taruwa kewaye da kai kowa a cikin su zai iya tabaka"
Zai zama da taimako ka bambanta wannan da sanin ta "tabawa" daga tabawa hadari daga taron. AT: "Wani ya tabani da sanin sa"
Yesu bai rasa ƙarfi ba ko ya zama mara ƙarfi, amma ikon sa ya warkar da matan. AT: "Na sani da cewa ikon warkar wa ya fita daga jikina" ko " Na ji iko na ya warkar da ni"
"da cewa ba za ta iya boye asirin abin da ta yi ba." Zai zama da taimako a faɗa abin da ta yi. AT: "da cewa ba za ta iya baye asirin abin da ta yi ba da cewa ita ne ta taba Yesu"
"ta zo wurin sa ciki da tsoro
"dukkan mutanen na gani"
"Wannan hanya ne mai na kirki na magana da mata. mai yuwa yaren ku na da wata hanya na faɗan wannan kirkin.
"domin bangaskiyar ki, kin warke." tsamo isimi "bangaskiya" za'a iya faɗan ta kamar aiki . AT: "domin kin yarda, kin warke"
Wannan ƙarin hanya ne na faɗan, "sai anjima" da kuma bada albar ka a lokaci ɗaya. AT: " sa'an da ka tafi , kada ka damu kuma " ko "bari Allah ya baka salama sa;anda ka tafi"
"Yana cikin magana da wata mata"
Wannan na nufin yayirus. (Dubi: Luka 8:41)
Wannan bayanin ya nuna da cewa Yesu ba zai iya yin komai yanzu ya ceci yarin yan yanzu da ta mutu.
Wannan na nufin Yesu.
"zata sami lafiya" ko "za ta rayu kuma"
"Sa'anda suka zo gidan." Yesu ya tafi da Yayirus. wasu almajeren Yesu suma sun tafi.
Wannan za'a iya faɗa da yaƙani. AT: "Yesu ya bar Bitrus da Yahaya da Yakubu, da mahaifiyar yarinyar da babanta su shi ga gidan da shi"
Wannan na nufin Yyirus.
Wannan hanya ce na nuna bakin ciki a waccan aladan. AT: "dukka mutanen da suke wurin suna nuna bakin cikisu su na kuka da ƙarfi yarin yarta mutu"
"suka yi ma sa dariyan reni, saboda sun sani yarinyar"
"Yesu ya kama hanun yarinyar"
"ruhun ta ya dawo jikin ta ." Yhudawa sun gane da cewa rai sakamakon ruhu ne ya dawo cikin mutum. AT: "Ta fara nunfashi kuma" ko Ta dawo da rai kuma" ko "Tana raye kuma"
Wannan za'a iya faɗa dabam da ban. AT: "kada sun gaya wa kowa"
Matan sun tanada musu daga kayan su.
Irin shine maganar Allah.
Sune mutanen da suka ji maganar, sa'an nan iblis ya zo ya dauke maganar shi, don kada su ba da gaskiya su sami ceto.
Sune mutanen da suka karbi maganar da farin ciki, amma a lokacin gwaji, sai su baude.
Sune mutanene da sun ji maganar, amma sai yawan taraddadin duniya, da dukiya, da shagalin duniya su sarke su, har sun kasa yin amfani.
Sune mutanen da sun ji maganar, suka rike shi, kuma suka jure har suka yi amfani.
Sune mutanen da sun ji maganar Allah da kuma aikata shi.
Suka ce, " Wa ke nan kuma, har iska da ruwa ma yake yi wa umarni, suna kuwa yi masa biyayya?".
Sun sa shi ya yi zama ba tufa ba a makabarta, sun sa shi ya karya sarkoki da kugiya, sun kuma dinga kore shi zuwa jeji.
Aljanu sun shiga cikin garkin alade, suka rungungunta ta gangaren taku, sun kuma halaka.
Yesu ya gaya masa ya je gidan sa ya fadi irin manyan abubuwan da Allah ya yi masa.
Ta same warkarsuwa domin bangaskiyan ta a Yesu.
Yesu ya tashir da yarinyan Jairus daga matattu.
1 Ya kira almajiransa goma sha biyu, ya ba su iko su fitar da kowanne irin aljani, su kuma warkar da cututtuka daga mutane. 2 Ya aike su, su yi wa'azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya. 3 Ya ce masu, "Kada ku dauki komi tare da ku domin wannan tafiya. Kada ku dauki sanda, ko jakar matafiyi, ko gurasa, ko kudi - Kada ma ku dauki taguwa biyu. 4 Dukan gidan da ku ka shiga, ku zauna a gidan har zuwa lokacin da za ku tafi daga wannan yankin. 5 Dukan wadanda ba su marabce ku ba, sa'adda ku ke barin wannan gari, ku karkabe kurar kafufunku a matsayin shaida a kansu." 6 Daga nan sai almajiran suka tafi zuwa cikin kauyuka, suka yi ta shelar bishara, su na warkar da mutane a ko'ina. 7 Ana nan Hirudus, mai mulki, ya ji labarin dukan abubuwan da su ke faruwa. Ya yi mamaki saboda wadansu mutane suna cewa Yahaya mai yin Baftisma ne ya sake dawowa da ransa. 8 Wadansu kuma suna cewa, annabi Iliya ne ya sake bayyana, wadansu kuma suna cewa daya daga cikin annabawa na da can ne ya sake bayyana da rai. 9 Hirudus ya ce, "Ba zai yiwu Yahaya ne ba, domin na datse masa kai. To, wanene wannan da ni ke jin wadannan abubuwa a kansa?" Daga nan sai ya cigaba da neman hanyar da zai ga Yesu. 10 Sa'adda manzannin suka dawo daga tafiyarsu, suka gaya wa Yesu dukan abubuwan da suka yi. Daga nan sai ya dauke su domin su tafi tare da shi zuwa garin Baitsaida. 11 Amma sa'adda taron suka ji inda Yesu ya tafi, sai suka bi shi can. Ya marabce su ya yi masu jawabi a kan mulkin Allah, kuma ya warkar da wadanda su ke bukatar warkarwa. 12 Da yake yamma ta fara yi, sai almajiransa goma sha biyu suka zo suka ce da shi, "Idan ka yarda ka sallami wannan babban taron mutane dominsu shiga cikin kauyuka, da ke kewaye da gonaki, dominsu sami abinci da wuraren da za su kwana, da yake mu na nan a wurin da ba kowa." 13 Amma sai ya ce da su, "Ku ba su abin da za su ci." Suka amsa masa, "Dukan abin da muke da shi shine, 'Yan dunkulen gurasa biyar da 'yan kifaye guda biyu, ba za mu iya zuwa mu sawo abincin da zai ishi mutanen nan su duka ba." 14 Mutanen da suke wurin sun kai kimanin mazaje dubu biyar. Sai Yesu ya ce da almajiran, "Ku ce da mutanen su zauna kungiya-kungiya, mutane hamsin a kowacce kungiya." 15 Sai almajiran suka yi haka, dukan mutanen suka zauna. 16 Ya dauki dunkulen gurasan guda biyar, da kifin guda biyu, yana dubawa zuwa sama ya albakarce su, sa'annan ya gutsuttsura, ya ba almajiran domin su rarraba wa mutane. 17 Dukansu suka ci kowa ya koshi. Daga nan almajiran suka tattara sauran abin da ya rage, har kwanduna goma sha biyu suka cika! 18 Wata rana Yesu yana yin addu'a shi kadai, sai almajiransa suka zo sai ya tambaye su, "Wa mutane suke cewa da ni?" 19 Suka amsa, "Wadansu suna cewa, Yahaya mai yin Baftisma, wadansu suna cewa kai annabi Iliya ne, har yanzu wadansu suna cewa kai wani cikin annabawa na da can ne ya dawo da rai." 20 Ya tambaye su, "Ku fa? Wa kuke cewa da ni?" Bitrus ya amsa, "Kai Almasihu ne wanda ya zo daga wurin Allah." 21 Sai Yesu ya gargade su da karfi, kada su gayawa kowa haka tukuna. 22 Sa'annan ya ce, "Dan Mutum dole ya sha wahalar abubuwa da yawa; dattawa za su ki shi da manyan fristoci da marubuta, sa'annan za a kashe shi. Bayan kwana uku, za a tashe shi da rai." 23 Sai ya ce da su duka, "Dukan wanda ya ke so ya biyo ni, dole ne ya yi musun kansa, ya dauki gicciyen sa kulluyomin, ya biyo ni. 24 Dukan wanda yake so ya ceci ransa, za ya rasa shi, amma dukan wanda ya ba da ransa domina, za ya cece shi. 25 Wacce riba mutum zai samu idan ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? 26 Dukan wanda yake jin kunya ta da magana ta, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa, sa'adda ya dawo cikin darajarsa da darajar Uba da ta mala'iku masu tsarki. 27 Amma ina gaya maku wannan tabbas, wadansu cikinku da ke nan tsaye, ba za su mutu ba sai sun ga mulkin Allah." 28 Kwana takwas bayan Yesu ya fadi wadannan kalmomi, sai ya dauki Bitrus da Yahaya da Yakubu, ya hau kan dutse domin ya yi addu'a a can. 29 Sa'anda ya ke yin addu'a sai yanayin fuskar sa ya canza sosai, tufafinsa kuma suka yi sheki da haske kamar walkiya. 30 Nan da nan sai ga mutane biyu suna magana da shi, wato Musa da Iliya. 31 Suka bayyana da daraja kewaye da su, suka yi magana da Yesu a kan tafiyarsa wadda za ta zo ba da dadewa ba a cikin Urushalima. 32 Bitrus da almajiran da suke tare da shi barci mai nauyi ya dauke su. Sa'adda suka farka sai su suka ga daukakar Yesu; kuma suka ga mutanen su biyu da ke tsaye tare da shi. 33 Sa'adda Musa da Iliya suke shirin su bar wurin Yesu, sai Bitrus ya ce, "Ya shugaba, ya yi kyau da muke a nan. Zai yi kyau mu yi runfuna uku, daya dominka, daya domin Musa, daya kuma domin Iliya." Amma hakika bai san abin da ya ke fadi ba. 34 Sa'adda yake fadin haka sai wani girgije ya zo ya rufe su. Sai suka ji tsoro sa'adda girgijen ya kewaye su. 35 Sai ga wata murya daga cikin girgijen tana cewa, "Wannan Dana ne wanda na zaba, ku ji shi." 36 Sa'adda muryar ta gama magana, Yesu yana nan shi kadai. Suka yi shiru ba su iya cewa kome ba a kan abin da suka gani a kwanakin nan. 37 Washe gari, da suka sauko daga kan dutsen, sai taron mutane da yawa suka zo wurinsa. 38 Nan da nan, wani mutum daga cikin taron mutanen ya yi magana da karfi, "Mallam, kayi wani abu dominka taimaki da na, shi kadai ne gare ni. 39 Mugun ruhu ya kan hau kansa, ya sa shi ya yi ta magowa. Ya kan girjiza shi da karfi ya sa bakinsa ya yi ta kumfa. Da kyar ya ke rabuwa da shi, kuma ya kan ji masa ciwo ba kadan ba bayan da ya bar shi. 40 Na roki almajiran ka su umurci mugun ruhun ya fita daga cikinsa, amma ba su iya ba!" 41 Yesu, ya amsa, ya ce, "Ku karkatattun tsara marasa bangaskiya, har yaushe zan zauna da ku ina jimrewa da ku? "Kawo yaronka anan." 42 Sa'adda yaron yake zuwa, sai mugun ruhun ya fyada yaron a kasa, ya jijjiga shi sosai. Amma Yesu ya tsauta wa mugun ruhun, ya warkar da yaron. Sa'annan ya mika yaron wurin mahaifinsa. 43 Dukansu suka yi mamaki da girman ikon Allah. Amma sa'anda suke ta yin mamaki a kan dukan al'ajiban da ya yi, ya ce da almajiransa, 44 "Ku saurara da kyau a kan abin da zan gaya maku, ba da dadewa ba za a bada Dan Mutum ga mutane." 45 Amma almajiran ba su gane abin da yake nufi da haka ba, an hana su fahimta, domin kada su gane abin da ya ke nufi tukuna, kuma suna jin tsoron su tambaye shi. 46 Wani lokaci, almajiran suka fara gardama a tsakaninsu game da wanene za ya zama mafi girma a cikinsu. 47 Amma Yesu ya san abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya kawo dan karamin yaro ya tsaya a kusa da shi, 48 sai ya ce da su, "Idan wani ya karbi dan karamin yaro kamar wannan saboda ni, dai dai yake da ya karbe ni. Idan kuma wani ya karbe ni, ya karbi wanda ya aiko ni kenan. Wanda yake mafi kankanta a cikinku, shi ne mafi mahimmanci." 49 Yahaya ya amsa yace, "Ya shugaba, mun ga wani mutum yana ba miyagun ruhohi umarni su fita daga cikin mutane da sunanka. Sai muka ce da shi ya dena yin haka saboda baya tare da mu." 50 Amma Yesu ya ce, "Kada ku hana shi yin haka, domin dukan wanda ba ya gaba da ku, yana tare da ku." 51 Sa'adda rana ta kusato da zai hawo zuwa sama, ya kudurta sosai zai tafi Urushalima. 52 Ya aiki wadansu manzanni su shirya wuri dominsa kafin ya zo. Suka shiga wani kauye a cikin kauyen Samariya domin su shirya masa wuri a can. 53 Amma mutanen can ba su karbe shi ba tun da ya ke Urushalima zai tafi. 54 Sa'adda biyu daga cikin almajiransa, wato Yakubu da Yahaya suka ga haka, suka ce, "Ubangiji, kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama, ta hallaka su?" 55 Amma, ya juya ya tsauta masu. 56 Sai suka tafi wani kauye dabam. 57 Da suna cikin tafiya a kan hanya, sai wani mutum ya ce da shi, "Zan bi ka dukan inda za ka tafi." 58 Yesu ya amsa masa, "Dila suna da ramuka a kasa inda za su shiga, tsuntsaye kuma suna da sheka, amma Dan Mutum ba shi da inda zai kwanta." 59 Yesu, ya ce da wani mutumin kuma, "Ka biyo ni." Amma mutumin ya ce, "Ubangiji, ka bari in koma gida in bizine mahaifina tukuna." 60 Amma Yesu ya ce masa, "Ka bar matattu su bizine matattunsu; amma kai ka tafi ka yi wa mutane shelar mulkin Allah a ko'ina." 61 Wani kuma ya ce, "Ubangiji zan tafi tare da kai, amma bari in je gida inyi ban kwana da mutanena tukuna." 62 Yesu ya ce da shi, "Dukan wanda ya fara huda a gonarsa idan ya dubi baya, bai isa ya shiga mulkin Allah ba."
Yesu ya tunashe al'majerensa kada su dogara akan kuɗi da abubuwan su, ku basu ƙarfi, ku kuma aike su zuwa wurare dabam daban.
Wannan ajilin guda biyuan yi amfani da su tare domin a nuna da cewa dukkan goma sha biyun suna da dama da kuma za su yia warkar da mutane. juya wannan sashin da haɗin kalmar da ya hada dukkan ra'ayin.
Ma'ana mai yuwa1) "kowanne aljani" ko 2) "kowanne irin aljani."
rashin lafiya
"ya aiki su wurare dayawa" ko "gaya masu su je"
"Yesu ya gaya wa goma sha biyun." Zai zama da taimako ka tada cewa ya faru kamim ya aiki su . AT: "Kamim su tafi, Yesu ya ce masu"
"Kada ku dauki komi tare da ku" ko "Kada ku kawo komai tare da ku"
"domin yar tafiyan ku" ko "sa'anda ku ka yi tafiya." Kada su dauki komai a duk tafiyan su, da suke tafiya daga kauye zuwa kauye, har sai sun zo gun Yesu.
babbar sandada mutane suke amfani da shi domin su daidaita saanda suke hauwa ko tafiya akan ƙasa wanda ba bai ɗaya bane,da kuma tsaro ga masu faaɗwa
jakar tafiya da ake daukan abin da ake so don tafiya
An yi amfani da wannan a nan domin shaida na "abinci." gaba ɗaya
"Dukan gidan da kuka shiga"
"tsaya a wurin" ko "ku zauna a gidan na dan lokaci kamar baki"
"zuwa lokacin da za ku bar garin" ko "zuwa ran da zaku bar wurin"
"A nan ga abin da za ku yi a garin in da mutane basu karbe kuba: sa'anda za ku tafi"
ku "karkabe kurar kafufunku" kwatanci ne na ƙi mai ƙarfi a waccan al'adar. Ya nuna da cewa basu son ku kurar garin nan ya ragu a sun su.
"sum bar wurin da Yesu yake"
"warkar a ko'ina da suka je"
Wannan ayan ya tura bayani ciki game da Hirudus.
Wannan sashin ya sa fashi a labarin. A nan Luka ya bada bayani na ƙasa game da Hirudus.
Wannan na nufin Hirudus Antifas, wanda ya ke mulkin ɗaya bisa hudu na Isra'ila.
ba'a iya ganewa ba, rekice
AT: "wadansu mutane suna cewa"
Wannan kalmar "ce" an gane shi a sashin da ya wuce. AT: "kuma suna cewa daya daga cikin annabawa na da can ne ya sake bayyana da rai"
Hirudus yana tsammanin cewa ba zai yu Yahaya ya tashi daga mattatu ba. Wannan za'a iya bayana ba shakka. AT: "Ba zai zama Yahaya ba domin Na datse masa kai. sabo da haka wanene wannan mutum"
Sojojin Hirudus su suka yanke hukuncin kisan. AT: "Na umurci sojoji na su datse kan Yahaya"
"manzannin sun dawo inda Yesu yake"
Wannan uana nufin warka suwa da koyarwa da suka yi sa'anda suka tafi biranen.
Wannan sunar birni ne.
"ranar ya kusan karewa" ko kusan karewan ranar"
dunƙulen gurasa dunƙulen ƙullun gurasa ne da aka siffa kuma an gasa.
Idan "sai dai" yana da wuya a gane a yeren ku, zaka iya yin sabuwar jumla. "kifaye guda biyu. domin a ciyar da wannan mutanen, sai dai mum je mu siya abinci"
"kimanin mazaje 5,000." Wannan lambar bai hada da yara da mataye ba wadanda mai yuwa suna nan.
"ku gaya masu su zauna"
"50 kowacce"
"Wannan" na nufin abin da Yesu ya ce su yi Luka 9:14. sun gaya wa mutanen su zauna akungiya kimanin mutane hamsin.
"Yesu ya dauki dunƙulen gurasan guda biyar"
Wannan na nufin kallon sama, zuwa sararin sama. Yahudawa sun yarda da cewa ana samun sama a sararin sa.
Wannan na nufin dunƙulen gurasan guda biyar da kifi guda biyu.
"ya raba wa" ko "ya băwa"
Wannan ƙarin ya na nufin sun ci abinci sosai har ba su jin yunwa. AT: "sun samu sosai kamar yadda suke bukata su ci"
AT: "al'majeren suka tara abin da ya rage" ko "al'majeren suka kwashe sauran abin da ya rage"
Wannan sashin an yi amfani da shi a nan domin a sa alama akan sabuwar abi da ya auko.
"yana yin addu'a shi kadai." al'majeren suna tare da Yesu, amma yana addu'a shikadai asirace da kansa.
Zai zama da taimako ka sakr faɗan sashin wannan tambayan a nan. AT: "Wasu sun ce kai ne Yahaya mai yin Baftisma"
Zai zama da taimako ka ganar da yadda wannan tambayan yadda ya hadu da tambayar Yesu. AT: "da cewa kai ɗaya daga cikin annabawa na da can ne ya dawo da rai"
"ya dawo da rai"
"Yesu ya ce wa al'majeran sa"
"kada su gayawa kowa" ko "da cewa kada su gaya wa kowa." Wannan za'a iya faaɗ kamar daidai faɗi. AT: "Kada ku gaya wa kowa."
"Mutaneza su sa Ɗan Mutum ya sha babar wahala"
Yesu yana nufin kansa. AT: "Ni, Ɗan Mutum ... kuma zan"
AT: "dattawa za su ki shi da manyan fristoci da marubuta"
AT: "za su kashe shi"
"kwana uku bayan da ya mutu" ko "a rana ta uku bayan mutuwarsa"
"zai tashi da rai kuma." AT: "Allag zai ... sa shi ya zama da rai kuma" ko "zai rayu kuma"
"Yesu ya ce "
Wannan na nufin al'majeren da suke tare sa Yesu.
"biyo ni" biyo Yesu ya na nufin zama ɗaya daga cikin al'majeren sa. AT: "zama al'majeri na" ko "zama ɗaya daga cikin al'majeria na"
"dole ba zai băwa sa'awar sa ba" ko "dole ya ki sa'awar sa"
"dauki gicciyen sa kulluyomin, ya biyo ni." giciyen na nufin wahala da mutuwa. dakar giciyen na nufin ya yarda zai sha wahala kuma ya mutu. AT: "zai yi biyayya dani kowace rana ko a ajilin wahala da mutuwa"
Bin Yesu a nan ya na nufin yin biyayya da shi. AT: "biyyaya da ni"
Amsar wannan tambayan shi ne bai da kyau. AT: "ba zai amfane wani ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa."
"ya sami komai a duniya"
"rasa kansa ko bada ransa"
"abin da na ce" ko "abin da na koyad"
AT: "Dan Mutum ma zai ji kunyarsa"
Yesu yana magana game da kansa. AT: "Ni, Dan Mutum ... sa'adda Na dawo"
Wannan suna ne mai muhimman ci wa Allah.
Yesu ya yi amfani da wannan sashin ya yi nauyin mumanci abin da ya ke so ya faɗana biye.
"wadansun ku dake tsaye a nan ba za su ɗanɗana mutuwa ba"
Yesu yana magana game da mutanen da yake magana akai. AT: "kamin ku gani"
Wannan ra'ayin " ba ... har sai" za'a iya furta da mai yaƙani da "kamim." AT: "za su ga mulkin Allah kamin su mutu" ko "za ka gan mulkin Allah kamin ka mutu"
Wannan ƙarin na nufin "mutuwa"
Wannan na nufin abin da Yesu ya gaya wa al'majeren a ayoyin da ya wuce.
Wannan kalmar "dubi" a nan ya samu saurin fahimta mu kula da bayanin ban mamakin da ya biyo baya. AT: "ba zato"
Wannan sashin ya ba da bayani game da yadda Musa da Iliya suke. Wasu yaren za su juya shi kamar sharaɗi dabam daban. AT: "kuma sun bayyana cikin daraj" ko "suna walkiya da haske"
"tafiyarsa" ko Yadda Yesu zai bar wannan duniyan nan." Wannan hanya ce mai ladabi na magana game da mutuwar sa. AT: "mutuwar sa"
Wannan kalmar an yi amfani da shi a nan domin a sa alaman fashi a asalin labarin. A nan Luka ya ba da labari akan Bitrus, Yakubu da Yahaya.
Wannan ƙarin na nufin "barci sosai"
Wannan na nufin hasky mai walƙiya ya ƙewaye su. AT: "sun ga haske mai walƙiya yana zuwa daga gun Yesu" ko "sun ga wuta mai haske ya fitowa daga gun Yesu"
Wannan yana nufin Musa da Iliya.
"Da Musa da Iliya suke barin wurin"
mai sauƙi, maficin wuri wanda za'a iya zama ko barci
"Wa'anda Bitrus yana faɗan wannan abubuwan"
cikakku al'majeren ba su ji tsoron gajimarai. Wannansashin ya nuna da cewa wani iri tsoro da ba na kullum ba ya ƙama su da gajimarin. AT: "suka ji tsoro"
Wannan za'a bayana a ajili da gakimarai ya yi. AT: "gajimaran ya zagaya su"
An gane da cewa muryan zai zama na Allah ne kawai. AT: "Allah ya yi magana da su a gajimaran"
Wannan suna ne mai muhimmanci wa Yesu, Ɗan Allah.
AT: "wanda Ni na zaba" ko "Na zabe shi"
Wannan bayanin ya faɗi abin da ya faru bayan labarin a sakamakon abin da ya auko a labarin da kanta.
Sashi na farko ya na nufin amsawar su nan da nan, na biyu kuma ya na nufin abin da suka yi a kwanakin da ya biyu.
Kalmar nan "gama" ya samu fahimtar sabuwar mutum a labarin. mai yuwa yaren ku na da wata hanyar yin haka Turaci sun yi amfani da "Akwai wani mutum a cikin taron wanda"
Saahin nan "kun ga" ya gabatar mana da mugun ruhu a labarin mutumin. mai yuwa yaren ku na da wata hanyar yin haka. AT: "Wannan mugun ruhu na da ya"
"kumfa ya fito daga bakinsa." Sa'anda mutum yana da waso, za su samu munfashi biyu ko haɗeyewa. Wannan ya na sa farin kumfa ya taru a bakin sa.
"Yesu ya amsa da cewa"
Yesu ya cewa taron da suka taru, ba wa al'majeren sa ba.
"tsara marasa kirki"
A nan "ku" jam'i ne. Yesu ya yi amfani da wannan tambayan ya bayyana bakin cikin sa da cewa mutanen ba shu gaskanta ba. Za'aiya rubuta su kamar bayani. AT: "na daɗe da ku, amma ba ku gaskanta ba. ina mamaki har yaushe zan zauna da ku ina jimrewa da ku."
A nan "na ka" mafuraɗi ne. Yesu ya na magana ne da uban wanda ya yi masa magana.
Yesu ya yi aiki al'ajibi, amma taron sun gane da cewa Allah mai iko wannan warkasuwa.
"komai da Yesu yake yi"
Wannan ƙari ne da yake nufin su kasa kunne. AT: "ku saurara ku tuna" ko "Kada ku manta da wannan"
Wannan za'a iya faɗan ta da shiraɗ mai yaƙani. A nan "hannaye" na nufin ƙarfin yin mulki. AT: "za a bada Ɗan Mutum a sa shi a iko mutane"
AT: "Allah ya boye masu ma'anar"
"tsakaninsu al'majeren"
A nan "zuciyz" misali ne na hankalin. AT: "sani dalilin a zuciyarsu" ko "sani abin da suke tunani"
Wannan na nufin mutum da ya yin abu kamar wakilin Yesu. AT: "domi na"
"Allah, wanda ya aike ni"
"wadanda Allah ya dauke su mafi mahimmanci"
"A amsawa Yahaya ya ce" ko "Yahaya ya amsa wa Yesu." Yahaya yana amsawa ga abin da Yesu ya ce akan zama mafi girma. bawai yana amsa tambayan bane.
Yahaya ya yi maganar kansa amma ba Yesu ba, sabo da haka "mu" a nan banda shi
Wannan na nufin mutum yana magana da iko da ƙarfi Yesu.
AT: " kubar shi ya cigaba"
Wasu yare na zamanin yanzu faɗi da yake nufin abu ɗaya. AT: "idan mutum bai hana ka aiki ba, kamar yana taya kane" ko "idan wani baya aikin gaba da kai, yana aiki tare da kai"
"Sa'adda rana ta kusato da zai hawo zuwa sama" ko "Sa'anda lokaci ya yi kusa da zai tafi sama"
Wannan ƙrin na nufin ya "ya kudurta sosai." AT: "ya shiya hankalin sa" ko "ya kudurta"
Wannan na nufin su shirya domin zuwansa gun, mai yuwa wurin magana, wurin zama, da abinci.
"ba su so ya zauna"
Samariyawa da Yahudawa su ƙi juna sosai. sabo da haka Samariyawa ba za su taimaki Yesu ba a tafiyar sa zuwa Urushalima, hed-kwatan Yahudawa.
"gani da cewa Samariyawan ba su ƙarbi Yesu ba"
Yakubu da Yahaya suka bada shawara a wannan hanyar shariyar domisun sani haka ne annabi Iliyay asharanta mutanen da suka ƙi Allah.
"Yesu ya juya ya tsauta wa Yakubu da Yahaya." Yesu bai huƙunta Samariyawan kamar yadda almajeren sa suke sammani ba.
Wannan ba ɗaya daga cikin almajeren ba.
Yesu ya amsa ƙairn maganar domin ya koya wa mutumin zama almajerin Yesu. Yesu ya nuna da cewa idan mutum ya bi shi, mutumin shi ma ba zai sami gida ba. AT: "Dila suna da ramuka ... ba shi da inda zai kwanta. sabo da haka kada ka yi sammani cewa za ka sami gida"
Wannan babbobin ƙasa ne kama da ƙararnuka. suna kwana a kogon ko a ramia ƙasa.
"tsuntsaye da suke firiya a iska"
Yesu yana magana a kansa a mutum na uku. AT: "Ni, Dan Mutum, yana ... inda zai kwana"
"ba inda zai huta da kansa " ko "ba inda zai yi barci." Yesu ya kwatanta ya yi nauyin cewa bai da asalil gida kuma mutane basu gayatan sa kullum ya zauna da su.
Ba'a gane ba ko mahaifin mutumin ya mutu kuma zai bizine shi nan da nan, ko mutumin zai daɗe na dan lokaci har sia uban sa ya mutu sai ya bizine shi asalin ajilin shi ne mutumin ya na so ya yi wani abu ne kamin ya bi aYesu.
"kamin in yi haka, bari in koma"
Asalin nufin Yesu bawai mattatu mutane su bizine mattatu mutane bane. Ma'ana mai yuwa na mattatu shi ne 1)misali ne na wadanda su kusa su mutu, ko 2)misali ne na wadan da sunki su bi Yesu kuma sun mutu a ruhaniyance. asalin maganar shi ne kada al'majeri ya bar wani abu ya hana shi bin Yesu.
Wannan na nufin wanda suka mutu gaba ɗaya. AT: "matattun mutane"
"Zan haɗu da ku a masayin almajeri" ko "Ina shiye in bika"
kamin in yi haka, bari in yi ban kwana da mutanena gida na tukuna"
Yesu ya amsa masu da ƙarin magana ya koya wa mutuminda yana so ya zama al'majerin sa. Yesu ya na nufin cewa mutum bai isa ya shi ga mulkin Allah ba idan ya damu da mutane dake a baya a maimakon bin Yesu.
A nan "ya sa hannun sa akan" wani abu ƙari ne na da yake nufin mutum ya fara yin wani abu. AT: "Ba wanda ya fara ɦuda a gonarsa"
Duk wanda ya juya baya sa'anda ya ke ɦudaba zai iya jagoran hudan in da ya ke so ya je ba. waccan mutumin dole ya nasu ya na kallon gabadomin ya yi huɗa da kyau.
"amfani ga mulkin Allah" ko "da cewa da mulkin Allah"
Yesu ya aike su su fita su wa'azin mulkin Allah su kuma warkar da marasa lafiya.
Wadansu su ce Yesu ne Yahaya mai Baftisma aka tashe shi daga matattu, wadansu suka ce Iliya ne ya bayyana, wadansu kuma suka ce annabawa daa ne ya tashi.
Sun same gurasa biyar da kifi biyu.
Maza sun yi wajen dubu biyar da suna wurin.
Ya daga kai sama, ya albarkace su, ya gutsuttura su ya kuma ba wa almajiran sa su ba wa jama'an.
Akwai kwando goma sha biyu na ragowar abincin.
Ya ce, "Almashihu daga Allah."
Sai ya ki kansa, ya dauki gicciyensa kowace rana, ya bi Yesu.
Bayyanawan fuskar sa ya canza kuma tufafin sa sun zama fari fat da kuma kyalli.
Musa da Iliya suka bayyana da Yesu.
Muryar ta ce, "Wnnan shi ne Dana zabanbbena; ku saurare shi."
Aljan ya sa shi ya yi ihu kuma jinkin sa ya yi ta rawa da kumfa a bakin sa
Ya ce, "Za a ba da Dan Mutum ga hannayen mutane."
Wanda yake karami a sakanin su shi ne babba.
ya himmantu sosai ga zuwa Urushalima.
Dole mutumin ba zai duba baya ba.
1 Bayan wadannan abubuwa, Ubangiji ya sake nada wadansu saba'in ya aike su biyu biyu, domin su tafi kowanne birni da wurin da yake niyyan zuwa. 2 Ya ce da su, "Girbin yana da yawa, amma ma'aikatan sun yi kadan. Saboda haka kuyi addu'a sosai ga Ubangijin girbin, domin ya aiko da ma'aikata cikin gonarsa. 3 Ku tafi, duba na aike ku kamar 'yan raguna cikin kyarkyetai. 4 Kada ku dauki jakan kudi, ko jakar matafiyi, ko takalma, kada ku gai da kowa a kan hanya. 5 Dukan gidan da ku ka shiga, ku fara cewa, 'Bari salama ta kasance a wannan gida.' 6 Idan akwai mutum mai salama a gidan, salamar ku za ta kasance a kansa, amma idan babu, salamar ku za ta dawo wurinku. 7 Ku zauna a wannan gidan, ku ci ku sha abin da suka tanada maku. Gama ma'aikaci ya wajibci ladansa. Kada ku bi gida gida. 8 Dukan birnin da ku ka shiga kuma sun karbe ku, ku ci abin da suka sa a gabanku. 9 Ku warkar da marasa lafiyar da ke wurin. Ku ce da su, 'Mulkin Allah ya zo kusa da ku.' 10 Amma dukan birnin da ku ka shiga, idan ba su karbe ku ba, ku tafi cikin titunansu, ku ce, 11 'Ko kurar birninku da ta like a kafafunmu, mun karkabe maku ita a matsayin shaida a kanku! Amma ku sani mulkin Allah ya zo kusa da ku.' 12 Na gaya maku, a ranar shari'a Saduma za ta fi wannan birni samun sauki. 13 Kaiton ki, Korasinu! Kaiton ki, Baitsaida! Ayyuka masu girma da aka yi a cikinku, da an yi su a cikin Taya da Sidon, da sun tuba tuntuni a zaune cikin toka da tufafin makoki. 14 Amma a ranar shari'a Taya da Sidon za su fi ku samun sauki. 15 Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani har zuwa sama za a daukaka ki? Babu, za a gangarar dake har zuwa hadas. 16 Wanda ya saurare ku ya saurare ni, wanda ya ki ku, ya ki ni, kuma wanda ya ki ni, ya ki wanda ya aiko ni." 17 Su saba'in din suka dawo da murna, suna cewa, "Ubangiji, har ma aljanu suna yi mana biyayya, a cikin sunanka." 18 Sai Yesu ya ce masu, "Na ga Shaidan yana fadowa daga sama kamar walkiya. 19 Duba, na ba ku iko ku taka macizai da kunamai, da kuma kan dukan ikon magabci, kuma ba zai iya yin illa a gareku ba ko kadan. 20 Amma duk da haka kada ku yi murna a kan wannan kadai cewa ruhohi suna yi maku biyayya, amma ku yi murna domin an rubuta sunayenku a cikin sama." 21 Cikin wannan lokacin, ya yi farin ciki kwarai cikin Ruhu Mai Tsarki, ya ce, "Na ba ka girma, ya Uba, Ubangijin sama da kasa. Domin ka rufe wadannan abubuwa daga masu hikima da ganewa, ka bayyana su ga wadanda ba koyayyu ba ne, kamar kananan yara. I, Uba gama haka ne ya gamshe ka." 22 Dukan abu, Ubana ya damka su gare ni, kuma babu wanda ya san Dan, sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Dan. Sai kuma wanda Dan ya yi niyyar ya bayyana Uban a gareshi." 23 Ya juya wajen almajiran, ya ce da su a kadaice, "Masu albarka ne su wadanda suka ga abin da kuke gani. 24 Na fada maku, annabawa da yawa, da sarakuna da yawa sun so da sun ga abubuwan da kuke gani, amma ba su gani ba. Kuma sun so da sun ji abubuwan da kuke ji, amma ba su ji su ba." 25 Sai ga wani malamin shari'ar Yahudawa, ya zo ya gwada shi da cewa, "Malam, me zan yi domin in gaji rai na har abada?" 26 Sai Yesu ya ce masa, "Yaya kake karanta abin da aka rubuta cikin shari'a?" 27 Ya amsa ya ce,"Dole ne ka kaunaci Ubangiji Allah da dukan zuciyarka, da dukan ranka da dukan karfinka, da dukan lamirinka. Ka kuma kaunaci makwabcinka kamar kanka." 28 Yesu ya ce ma sa, "Ka amsa daidai, idan ka yi haka za ka rayu." 29 Amma, malamin ya na so ya 'yantar da kansa, sai ya ce da Yesu, "To, wanene makwabcina?" 30 Ya amsa ya ce, "Wani mutum yana tafiya daga Urushalima za shi Yariko. Sai ya fada hannun mafasa, suka tube shi, suka kwace dukan abin da ya ke da shi, suka yi masa duka, suka bar shi kamar matacce. 31 Ya zama sai ga wani firist ya na bin wannan hanya, da ya gan shi sai ya bi ta gefe daya ya wuce. 32 Haka kuma sai ga wani Balawi, sa'adda ya zo wurin, ya gan shi sai ya bi ta wani gefe ya wuce shi. 33 Amma wani Basamariye, ya na tafiya sa'adda ya zo wurin da mutumin yake, sa'adda ya ga mutumin sai tausayi ya kama shi. 34 Ya zo inda mutumin yake, ya daure masa raunukan da aka ji masa, yana shafa masu mai da ruwan inabi. Ya dora shi a kan dabbarsa ya kawo shi wurin kwana, ya kula da shi 35 Washegari ya kawo dinari biyu, ya ba mai wurin kwanan ya ce 'Ka kula da shi, idan ma ka kashe fiye da haka, idan na dawo zan biya ka.' 36 A cikinsu ukun nan, wanene kake tsammani makwabcin wannan mutum da ya fada hannun 'yan fashi?" 37 Sai malamin ya ce, "Wannan da ya nuna masa jinkai" Sai Yesu yace masa, "Ka je kai ma ka yi haka." 38 Sa'adda suke tafiya, sai ya shiga cikin wani kauye, sai wata mata mai suna Marta ta marabce shi a gidanta. 39 Tana da 'yar'uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a kafafun Ubangiji tana jin abin da yake fadi. 40 Amma ita Marta ta na ta kokari ta shirya abinci. Sai ta zo wurin Yesu ta ce, "Ubangiji, ba ka damu ba 'yar'uwata ta bar ni ina ta yin aiki ni kadai? Ka ce da ita ta taya ni." 41 Amma Ubangiji ya amsa ya ce da ita, "Marta, Marta, kin damu a kan abubuwa da yawa, 42 amma abu daya ne ya zama dole. Maryamu ta zabi abu mafi kyau, wanda ba za a iya kwace mata ba."
Yesu ya aiki feye da saba'in agaba da shi. mutane saba'in dinnan sun dawo da murna, sai Yesu ya amsa da yabo ga ubansa na sama.
wannan kalman anyi amfani da ita anan domin ya nuna alamar sabon labarin da ya auko.
" saba'in"wasu juyin sun ce "saba'in da- biyu" ko "72." za ku iya kara bayanin da ya fada haka.
"ya iaki su a kungiya biyu" ko "ya aiki su da mutane biyu a kowace kungiya"
Ya fada abin yadda yake kafin mutumin ya fita waje. AT: "ya fada masu" ko "kamin su fitawaje ya fada ma su"
akwai babban baroro, amma ma'aikatan kadan nae sukawa shi ciki." Yesu na nufin akwai mutane daya wa da suke so su shiga mulkin sama, amma babu a'lmagiren da zasu taimake mutanen.
"ku tafi biranan" ko "ku tafi gun mutanen"
kyarkyetai suna harin tumakin domin su kashe su. wannan na misalin cewa akwai wadan su mutane wadda suki kokara su kashe a'lmajiran wadda Allah zai aike su. za'a iya chire sunayen wasu dabbobi. AT: "idan na aike ku,mutane zasuso su lahane ku, kamar yadda kyarkyetai suke harin tumaki"
"Kada ku dauki jaka jakan tafiya ko takalma"
"kada ku gaida kowa akan hanya. " Allah yana nauyin dacewa su tafi da sauri zuwa biarnan suyi aikin sa.bawai su zama marasa ladabi ba.
wannan duka biyu gaisuwa ne da salama. Anan "gida" na nufin wadda suke zama a gida. AT: bari mutanen da suke wannan gida su sami salama"
"mutumin salama." wannan shi ne mutum mai son salama da Allah da kuma mutane.
Anan "salama" ana kwatanta salama kamar abu mai rai wadda zai iya zaba inda zaya zauna. AT: "zai sami salaman da ka albarka ce shi dashi"
Zai iya sake dukan kalman mai fatan alhari. AT: idan babu mutun mai salama" ko idan mai gidan ba mai son salama bane"
Anan "salama" ana kwatanta tane kamar abu mai rai wadda zaya iya za ban wurin da zai zauna. AT: "zaku sami wancen salamar" ko "ba zai sami salama can da ka a'lbarkace shi da shi ba "
Bawai Yesu yana nufin su zauna a wancan gidan dukan rana ba,amma suyi barci a gida daya wadda suke. AT: "cigaba da yin barci a wannan gida"
wannan shine babban wata muhimmin da Yesu yayi amfani da shi wa mutanen da ya aika. tun da zasu koyar su kuma warkar da mutane, mutanen kuwa zasu basu abinci da wurin kwaciya.
tafiya daga gida zuwa guda na nufin zuwa gidaje daban daban. zai iya za ma da ciwa yana tafiya yayi dare a gidaje daban daban. "kada ka je kayi barci kowace dare a gidaje daban daban"
" idan sun karbe ku"
za'a iya bayyana shi wa wata sifa. AT: "ci kowace irin abincin da suka baku"
wannan na nufin mutane marasa lafiya gabaki daya. AT: "mutane marasa lafiya"
wannan kalman "mulkin" za'a iya bayyana ta kamar fi'ili "shekarun sarauta" ko "mulki" ma'ana mai yuwa 1) mulkin Allah ya kusan farawa. AT: "Allah ya kusa ya fara mulki kamar sarki" ko 2) ayukan mulkin Allah suna faruwa kewaye daku. AT: "Abin shaida cewa Allah yana mulki na kewaye daku"
"idan mutanen garin sun ki ku"
wannan alamar aikatawa cewa sun ki karban mutanen garin. AT: "kamar yadda kuka ki mu, muma mun kiku sosai. muma mun ki kurar birninku da ta like a kafafunmu
tunda yesu yana aikan mutanen a kungiya biyu, zai zama mutane biyu ne na fadin wannan. yare dayake da sifa biyu "mu" zasu yi afani da ita.
wannan kalman "Amma kusan wannan" yana gabatar da gargadi. yana nufin "koda shike kun ki mu, bai canja damar cewa mulkin Allah ya kusan zuwaba!"
wannan kalman "mulkin" fadan ta da fi'ili "shekarun mulki" ko "mulkin" dubi yadda aka juya magana irinta acikin [luka 10:8]
Yakubu ya na fadin wannan wa mutane 70 da zai aiki su. Ya fada hakana domin ya nuna cewa ya na so ya fada wata abu mai muhimin amfani
wannan a'lamjiren yaka mata su ga na cewa wannan ya nufin ranan shari'a na karshe ga masu zunubi.
"Allah ba zai yiwa saduma shari'a mai tsanani feye da wannan brinin." AT: Allah zai yiwa mutanin brinin shari'a mai tsanani feye da mutanen saduma"
Yakubu yayi magana akan mutanen biranen Kaiton da Baisaida kamar suna jins, amma basu ji.
Yakubu yana bayyana yanayin da ya kama ta ya faru a baya amma bai faru ba. AT: "Idan wani ya yi aikin alajibi wa mutanen Taya da Sidon da na yi maku"
"mugayen mutanen da suka zauna awurin da sun nuna cewa sun tuba da kuskuren zunuban su a zaune"
"sa tufafin makoki da zama cikin toka"
Zai zama da fatan alheri a fade she ba shaka dalilin shari'an su. AT: "amma baku tuba ku yarda da ni ba koda sheke kunga aikin al'ajibin da na yi, allah zai yi maku shari'a mafi tsanani fiye da mutanen Taya Sidon"
"a ranan karshe ran da Allah zai sharanta kowa"
Yesu yayi magana yanzu da mutanen brinin Kafarnahum kamar suna jinsa, amma basu ji.
Yesu yayi amfani da tambaya domin ya kwabe mutanen Kafarnahum game da griman kansu. AT: "ba shaka baza ku ji sama ba" ko "Alllah bazai daukaka kuba!"
wannan furcin na nufin "daukaka mai grima"
Za'a iya bayyana ta a wata sifa. AT: za ku gangara kasan hadas"
wannan kwatanci za'a iya fadin ta ba shaka kamar tamka. AT: "Idan wani ya ji ku, kamar suna ji na ne"
wannan kwatanci za'a iya fadin ta ba shaka kamar tamka. AT: "Idan wani ya kiku, kamar ya kina ne"
wannan kwatanci za'a iya fadin ta ba shaka kamar tamka. AT: "Idan wani ya kini, kamar yana kin wadda ya aiko ni ne"
wannan na nufin Allah Uban, wanda Yesu ya aza domin aikinan na susamman "Allah wanda ya aikoni"
wasu yarurukan zasu iya fa da cewa saba'in daidai ne sun fita da farko kamar yadda UDB yayi. wannan sanarwan ba'a bayyane yake ba amma za'a iya bayyana shi.
Anan "suna" na nufin karfi da ikon Yesu.
Yesu yayi amfani da tamka ya kwatanta yadda Allah yana yin nasara da shaitan yadda walkiya yana bugawa idan almajiren sana yin wa'azi a garuruwa.
"Na baku iko ku rugurguje karfin magabci" ko "Na baku iko ku ci nasara akan magabci." magabcin she ne shaitan.
"kada kuyi murna kawai domin ruhun yayi biyayya maku" za'a iya fadanta a wata sifa mai yaƙani. AT: " yi murna domin sunan ku na rubuce a sama ko da sheke kuyi murna domin ruhun yana biyayya daku"
wannan za'a iya bayana ta a wata sifa. AT: "Allah ya rubuta sunayen ku a cikin sama" ko "sunayen ku na cikin mutanen magadan mulkin sama"
wannan muhinmin shaida nena Allah.
"sama" da "kasa" na nufin ka mai da yake kasan ce AT: "Maigidan kowa da komai a sama da kasa"
wannan na nufin koyasuwan Yesu wadda suka wuce akan ikon almajirai.zai fi kyau a ce "wadannan abubuwa" da mai karatu ya gane ma'anar.
wannan kalman "hikima" da "fahimta" siffs ce ta wajen sunaye da ake nufin mutane da suke da nau'i. domin Allah ya boye masu gaskiya wadan nan mutane kuwa basu da hikima da fahimta,koda sheke suna tunanin cewa sunada shi. AT: daga mutanen da suke tunani cewa suna da hikima da fahimta "
wannan na nufin waddan da basu da ilmi sosai amma suna so su karbi koyasuwan Yesu haka kuma kananan yara suna so suji wadda da suka yarda da su. AT: "mutanen da suki da ilmi kadan, amma wanda yaji Allah kamar yadda yara suke yi"
"gama ya gamshe ku kuyi wannan"
wannan za'a iya bayayyana shsi a wata siffa. AT: "Ubana ya mika mini komai a hanuna"
Wannan shaida ne wanda ya kwatanta dagantaka Allah da Yesu.
wannan kalmar da aka juya ta kamar "sani" sabawa da mutun da kansa. Allah Uban yasan Yesu a wannan hanyan.
Yesu na nufin kansa a masayin mutum na uku.
wannan na nufin cewa Uban ne kawai ya san ɗan.
wannan kalman an juya ta kamar "sani" sabawa da mutumda kansa. Yesu yasan Allah Ubansa a wannan hanya.
wannan na nufin cewa ɗan ne kawai ya san wanene Uban.
"duk wanda ɗan ya so yanuna mishi Uban"
wannan kalman "asirance" ya nuna da cewa she kadai ne da almajiren sa. AT: anjima da ya gan shi da almajiren sa ne kawai, ya juya gunsu ya ce"
wannan mai yuwa ya na nufin ayuka masu kyau da aikin al'ajibi da Yesu ya ke yi. AT: "yadda yake da kyau ga wadanda suke ganin abubuwan da nake yi"
wannan nufin cewa Yesu baya yin wadan nan abubuwa tukunna. AT: " amma domin ba na yin su tukunna"
wannan mai yuwa na nufin koyassuwan Yesu. AT: "wadan nan abubuwa da kuke ji ina faɗa"
wannan na nufin cewa Yesu ba ya yin koyassuwa. AT: "amma baku jin su domin ban farayin koyassuwa ba tukunna"
Yesu ya amsa da labari wa malamin yahudawan wanda yake so ya gwada Yesu.
wannan ya sa mu saurin fahintan wata sabuwar abu da sabuwar mutum a cikin labarin.
"tsokana Yesu"
yesu baya neman labari.yayi amfani da tambayan domin ya koya wa malamin yahudawan. AT: "gaya mini abin da Musa ya rubuta acikin shari'a kuma mene ne ma;anarsa a tunanin ka."
wannan za'a iya tambaya a wata siffa. AT: " Me Musa ya rubuta a cikin shar'a?"
"Me kuka karata a ciki?" ko "Me ka fahinta kace?"
wannan mutum yana faɗin abin da Musa ya rubuta a shari'a.
Anan "zuciya" da "ranka" na nufin cikin ran mutum. wannan sashe guda hudun ana aiki da su ma'ana "gabaɗaya" ko "mai himmanci"
wannan tamka za'a iya faɗan ta ba shaka. AT: "kaunaci makwabcin ka sosai kamar kanka"
Amma malamin yana so ya yantar da kansa, sai ya ce" ko "Amma yana so ya bayyna kamar a'dali malamin ya ce"
Yesu ya amsa wa mutumin da wata misali. AT: "A amshe, Yesu ya bashe labarin"
Mutumin ya na so ya sani wadda ake so ya kaunaci. AT: "Wazan duba ya zama makwobci na in kuma soshe kamar kaina?" ko "wani mutane ne makwobci ci na da zan so su?"
wannan ya kawo sabuwar hali a cikin misalin.
"Mafasa suka zagayashe, wa" ko "wasu mafasa suka hareshe. su"
"karɓi dukan abin da ya ke dashi" ko "sata duk abubuwa shi"
wannan na nufin "kusan mutuwa"
wannan ba abun da mutum ya shriya bana.
wannan nannaga yana gabatar da sabuwar mutum a labarin, amma bai ambatasi da sunaba.
"da firist ya gan mutumin da ya jiciwo." Firist mutumin adini ne sosai, masu sauraron suna samanin cewa zai taimaki wanda ya ji ciwo. amma da bai yi ba, wannan magana za'a iya fadan ta kamar "amma da ya gan shi" a kira karsashi akan abin da ba a sammani.
ya nuna da cewa bai taimaki mutumin ba. AT: "bai taimaki mutumin da ya ji ciwo ba amma ya bi ta gefen hanya ya wuce" Dubi:
Balawin ya yi aiki a haikali. yaka mata ya taimaki ɗan'uwansa mutumin bayahude. tunda bai yi ba,zai iya zama da taimako a cewai. AT: Balawi ...ta wani gefe amma bai tai makeshi ba"
wannan ya gabatar da sabuwar mutum a labarin amma bai ambaci sunan saba. mum sani da cewa shi daga samariya ne.
Yahudawa suka raina Basamariye kuma suna tunanin cewa ba zai taimaki mutumni Yahudawan da ya ji ciwo ba.
"ya tausayamasa"
ya ka mata ya zuba masa mai da ruwan inabin da farko. "AT: ya sa masa mai da ruwan inabin akan ciwon sai ya ƙunsa masa da riga"
ya yi amfani da ruwan inabin ya share masa ciwon, mai kuma domin ya hana wata harbi. wannan za' iya fadan ta kamar. AT: zuba mai da ruwan inabi domin ya taimaka su warke"
"akan dabarsa ya kintsa." wannan dabane wadda ya ke amfani ya dauki kaya mai nauyi. maiyuwa jakine.
ladan aiki na kwana biyu." "dinari jam'i nw na dinariya."
mai ajiyan ƙaramar ɗaki" ko " mutumni mai lura da ƙaramai ɗakin"
wannan za; iya rubuta shi kamar tambayoyi guda biyu. AT: "meka ke tunani? wa kake sammani acikin ukun nan makwabci... 'yanfashi?"
"nuna kansa ya zama shi ne makwabci na gaskiye"
"ga mutumin wadda 'yanfashi suka hara"
zai iya zama da taimako ka bada labari da ya wa. AT: "a hanya daya,kaje ka taimaki duk wanda za ka iya"
"sa'adda Yesu da almajiren sa suke tafiya"
wannan ya gabatar da wata kauye a wata sabuwar wuri amma bai ambace sunan ta ba.
wannan ya gabatar da marta a masayin sabuwar hali, yaren ku zai iya samun wata hanya na gabatar da sabobin mutane.
wannan wurin zamane na ba da grima kullum ga mutanen da suke da ilmi a wancen zamani. AT: " zauna a kasa kusa da Yesu"
wannan na nufin komai da Yesu ya faɗ da yake gidansu Marta. AT: ji koyasu wan Yesu"
"hidimomi sosai" ko "hidima kuma"
Marta ta yi ƙara da cewa Uangiji ya bar Maryamu ta zauna tana sauraron sa kuma ga aiki sosai da zata yi. ta ba wa Ubangiji grima sosai sai ta yi amfani da bai damu da amsa ba domin ta zamar da ƙaran sa mai ladabi. AT: "kamar ba ka damu ba ... ni kadai."
Yesu ya nanata sunan Marta domin nauyi AT: "Masoyiya Marta" ko "Ke Marta"
Yesu ya nuna banbancin abun da Maryamu tana yi da kuma wanda Marta tana yi.zai za ma da taimako a mayar da shi a bun da ba sai an bayana ba. AT: "abun da ya za ma dale shine a saurari koyasuwa na" ko "Sauraron koyasuwana yafi shirya abinci"
Ma'ana mai yuwa 1) "Bazan kwace wannan daman daga wurin ta ba" ko 2) baza ta rasa abin da ta samu daga saurarona ba"
Kada su dauki jakar kudi, ko burgami, ko takalma.
Ya gaya musu su warkar da marasa lafiya kuma su ce wa mutanen, "Mulkin Allah ya zo kusa da ku."
Zai fi muni fiye da hukurcin Saduma.
Ya ce, "Ku fi yin farin ciki wai an rubuta sunayen ku a sama."
Ya yi farin ciki matuka zuwa ga Uba da ya nuna mulkin Allah ma wadanda jalilai, kamar kananan yara.
Dole ka kaunaci Ubangiji Allahn ka da dukkan zuciyar ka, da dukkan ran ka, da dukkan karfin ka, da dukkan hankalin ka, ka kuma kaunaci da'uwan ka kamar kanka.
Ya wuce ta dayan gefen.
Ya wuce ta dayan gefen.
Ya daddaura masa raunukansa, ya dora shi a kan dabbar sa, ya kai shi masauki, ya kuma yi masa jinyya.
Je ka nuna rahama kamar Basamariya a misalin.
Ta zauna a kafar Yesu ta kuma saurare shi.
Yawan hidimomi na shirin abinci ya dauke mata hankali.
1 Wani lokaci, Yesu yana yin addu'a a wani wuri, sai daya daga cikin almajiransa yace da shi, "Ubangiji, ka koya mana yin addu'a kamar yadda Yahaya ya koya wa almajiransa." 2 Yesu ya ce ma su, "Sa'anda ku ke yin addu'a ku ce, 'Uba a tsarkake sunanka. Mulkin ka ya zo. 3 Ka ba mu abin da za mu ci a kowacce rana. 4 Gafarta mana zunubanmu, kamar yadda muke gafarta ma wadanda suke mana laifi. Kada ka kai mu cikin jaraba.'" 5 Yesu ya ce masu, "Wanene a cikinku idan yana da aboki, za ya je wurinsa da tsakar dare ya ce masa, "Aboki, ka ba ni rancen dunkulen gurasa guda uku, 6 da ya ke wani abokina ya iso yanzu daga tafiya, kuma ba ni da abin da zan ba shi ya ci,' 7 Sai wanda yake ciki, ya amsa, ya ce, 'Kada ka dame ni. Na riga na rufe kofa ta, kuma ni da yarana mun riga mun kwanta. Ba zan iya tashi in ba ka gurasa ba.' 8 Na fada maku, ko da bai tashi ya ba ka gurasar ba, a matsayin abokinsa, ba ka ji kunya ba, ka nace da rokonsa, za ya tashi ya ba ka dukan yawan gurasar da kake bukata. 9 Ni kuma ina ce maku, ku roka za a ba ku; ku nema za ku samu; ku kwankwasa za a bude maku. 10 Domin dukan wanda yake roko ya na karba; dukan wanda ya ke nema kuma yana samu; kuma wanda yake kwankwasawa, za a bude masa. 11 Wanne uba ne a cikinku, idan dansa ya tambaye shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon kifi? 12 Ko kuwa idan ya tambaye shi kwai, za ya ba shi kunama? 13 To, da yake ku da kuke masu mugunta kun san ku ba 'yanyan ku abu mai kyau. Yaya fa ga Ubanku wanda yake cikin sama, za ya ba da Ruhu Mai Tsarki ga wadanda suka roke shi?" 14 Wani lokaci, Yesu yana fitar da wani beben aljani. Sa'adda aljanin ya fita, sai mutumin da yake bebe ya yi magana. Sai taron mutanen suka yi mamaki! 15 Amma, wadansu daga cikin mutanen suka ce, "Da ikon Ba'alzabuba sarkin aljanu ne yake fitar da aljanu." 16 Wadansu suka gwada shi, suka nemi ya nuna masu wata alama daga sama. 17 Amma Yesu da yake ya san tunaninsu, ya ce da su, "Dukan mulkin da ya rabu biyu, gaba da kansa, ya rushe kenan, kuma idan gida ya rabu biyu, gaba da kansa za ya fadi. 18 Idan Shaidan ya rabu biyu gaba da kansa, ta yaya mulkinsa zai iya tsayawa? Gama kun ce ina fitar da aljanu ta wurin Ba'alzabuba. 19 Idan ni na fitar da aljanu ta wurin Ba'alzabuba, ta wurin wa wadanda suke bin ku suke fitar da aljanu? Saboda haka, su ne zasu zama masu yi maku shari'a. 20 Amma idan daga wurin Allah na ke fitar da aljanu, to, ya zama ke nan mulkin Allah ya zo wurinku. 21 Idan mutum mai karfi, mai kayan fada ya tsare gidansa, kayansa za su tsira. 22 Amma idan wani mutum wanda ya fi shi karfi ya zo ya ci nasara a kansa, zai dauke kayan fadan daga wurin mutumin, kuma ya kwashe kayansa. 23 Wanda ba ya tare da ni, gaba da ni ya ke yi, kuma wanda ba ya tattarawa tare da ni, watsarwa yake yi. 24 Idan kazamin ruhu ya fita daga cikin mutum, ya kan bi ta wurin busassun wurare yana neman wurin da zai huta. Idan bai samu ba sai ya ce, 'Bari in koma gidana inda na baro. 25 Sa'adda ya dawo, ya tarar an share gidan, an kuma gyara shi tsaf. 26 Sai ya je ya dauko wadansu aljanu guda bakwai wadanda su ka fi shi mugunta, su zo su zauna a wurin. Sai karshen mutumin nan ya fi farkonsa muni." 27 Ya zama, lokacin da ya ke fadin wadannan abubuwa, wata mace ta tada muryarta a cikin taron mutanen ta ce da shi, "Mai albarka ne cikin da ya haife ka, da maman da ka sha." 28 Sai shi kuma ya ce, "Masu albarka ne wadanda suke jin maganar Allah suke yin biyayya da ita." 29 Lokacin da mutane suke kara taruwa, sai ya fara cewa, "Wannan tsara, muguwar tsara ce. Ta na neman alama, Ko da yake ba wata alamar da za a bata sai irin ta Yunusa. 30 Domin kamar yadda Yunusa ya zama alama ga mutanen Neneba, haka kuma Dan Mutum za ya zama alama ga wannan tsara. 31 Sarauniyar Kudu, za ta tsaya ta yi shari'a da mutanen wannan tsara, kuma za ta kashe su, gama ta zo daga wuri mai nisa domin ta saurari hikimar Sulaimanu. Kuma ga wani wanda ya fi Sulaimanu a nan. 32 Mutanen Neneba, za su tsaya shari'a da matanen wannan tsara, kuma za su kashe su. Gama sun ji wa'azin Yunusa sun tuba. Kuma ga wani wanda ya fi Yunusa a nan. 33 Ba wanda zai kunna fitila ya boye ta, ko kuwa ya sa ta a karkashin kasko, amma zai sa ta a mazaunin ta domin dukan wanda ya shiga dakin ya ga haske. 34 Idon ku shine fitilar jikinku. Idan idonku yana gani sosai, jikinku zai cika da haske. Amma idan idonku ba ya gani sosai, jikinku zai cika da duhu. 35 Ku yi hankali fa, domin kada hasken da ya ke wurinku ya zama duhu. 36 Idan dukan jikinku yana cike da haske, babu duhu ko kadan, to sai dukan jikinku ya zama kamar fitilar da take bada haskenta a bisanku." 37 Sa'adda ya gama jawabi, sai wani Bafarise ya ce da shi ya zo gidansa ya ci abinci, sai Yesu ya shiga ya zauna. 38 Sai Bafarisen ya yi mamaki da ganin bai wanke hannu kafin ya ci abinci ba. 39 Amma sai Ubangiji ya ce da shi, "Ku Farisawa kuna tsabtace bayan kofi da bangaji, amma cikin yana cike da kazamta da mugunta. 40 Ku mutane marasa tunani, wanda ya yi wajen, ba shine ya yi cikin ba? 41 Ku bayar da abin da ke ciki ga matalauta, kuma dukan abu zai zamar maku da tsafta. 42 Amma kaitonku Farisawa, gama kuna karbar zakka da daddoya da karkashi da kowanne irin ganye na lambu, amma kun watsar da adalci da kaunar Allah. Dole ne a yi adalci, a kaunaci Allah, a yi sauran abubuwan kuma. 43 Kaitonku Farisawa, domin kuna so a ba ku wuraren zama masu kyau a cikin masujadai, a kuma yi maku gaisuwar bangirma a cikin kasuwanni. 44 Kaiton ku, gama kuna kama da kabarbarun da ba yi masu shaida ba, mutane kuwa suna tafiya akansu ba tare da saninsu ba." 45 Wani malami a cikin shari'ar Yahudawa ya amsa masa ya ce, "Malam, abin da ka ce ya bata mana rai mu ma." 46 Sai Yesu ya ce, "Kaitonku malaman shari'a! Gama kun dora wa mutane kaya mai nauyi wanda ya fi karfinsu dauka. Amma ku, ko da dan yatsa ba ku taba kayan ba. 47 Kaiton ku, gama kuna gina abubuwan tunawa a kabuburan annabawa, alhali kuwa kakanni-kakanninku ne suka kashe su. 48 Ya zama kenan kuna sane da ayyukan kakanni-kakanninku, domin sune suka kashe annabawan da kuke tunawa da su. 49 Saboda wannan daliline hikimar Allah ta ce, "Zan aika manzanni da annabawa a wurinsu, kuma za su tsananta masu har ma za su kashe wadansu daga cikinsu.' 50 Wannan tsarar, za ta dauki alhakin jinin dukan annabawan da aka kashe tun kafuwar duniya. 51 Tun daga jinin Habila, har zuwa jinin Zakariya wanda aka kashe tsakanin bagadi da wuri mai tsarki. I, na gaya ma ku za a nemi hakin su a wurin wannan tsarar 52 Kaitonku malaman shari'a na Yahudawa, domin kun dauke mabudin sani, ku da kanku ba ku shiga ba, kuma kun hana masu shiga su shiga." 53 Bayan da Yesu ya bar nan wurin, Marubuta da Farisawa suka yi gaba da shi, suka yi jayayya da shi a kan abubuwa da yawa, 54 suna kokari su kafa masa tarko domin su kama shi a cikin kalmomin da yake fadi.
wannan wata farkon sashi na a labarin. Yesu ya koya wa almajiren sa yadda za su yi addu'a.
wannan sashen maganan anyi amfani da ita anan domin a nuna wata sabuwar sashi na labarin. idan yaren ku tana da wata hanyan yi haka, za'a iya amfani da ita anan.
zai yiya zama kace Yesu ya gama addu;a kamin almajiren sa suka yi tambaya. AT: "da cewa Yesu yana addu'a a wani wuri. sa'an da ya gama addu'a daya daga "
"Yesu ya cewa almajiren sa"
Yesu yana umurtan almajiren sa su ɗaukaka sunan Allah Uba da kiran sa kamar "Uba" sa'an da suke addu'a. wannan masayine mai muhimmaci wa Allah.
" ka sa kowa ya ɗaukaka sunan ka." "Suna ya na nufin dukan mutum. AT: bari dukan jama'a su ɗaukaka ka"
Aikin Allah yayi mulki akan kowa anyi magana kamar Allah da kansa. AT: "bari ka zo kayi mulki a kan kowa"
Yesu ya cigaba da koya wa almajirensa yadda za su yi addu'a.
wannan wajibi na, amma za'a iya juya shi kamar roko, ba kamar dokoki ba. zai iya da amfani a kara wani bau kamar "in ka yarda" domin kusa a gane. AT: "in ka yarda ka bamu ... inka yar da ka yafe mana ...in ka yarda kada ka kaimu"
gurasa abinci ne mara sada wadda mutane suke ci kullum.anyi amfani da ita anan a masayin abinci na gaba daya. AT: "abincin da muke bukata kowane rana"
"Kayafe mana zunuban da muke yi maka" ko "kayafe mana zunuban mu"
"tunda muma muna yafewa"
"wanda ya yi mana zunubi" ko "wanda yayi mana abin da ba kyau"
wannan za;a iya faɗan ta a siffa mai yaƙani. AT: "kadau ke mu daga wurin jaraba"
Yesu yayi amfani da tambaya domin ya koya wa almajiren sa. AT: "Misali wdaya a cikin ku yana da ...ya sa a gaban shi.' " ko "Misali kana da ... Bin da za ka sa a gaban shi.' "
"bari in ranci gurasa uku" ko "kaba ni garasa uku zan biya anjima" Mai gidan bashi da wani abincin da zai ba wa bakon.
Ana amfani da gurasa amasayin abinci na gaba ɗaya. AT: dayawa suna ɗafa abinci domin a ci" ko "ɗayawa suna ɗafa abinci domin mutum ya ci"
wannan na nufin bakon ya zo da gidan sa can da nisa. AT: "yana tafiya sai ya shiga gida na"
"akwai abincin da ya yi a ba shi"
"Ba ji dadin tashiwa ba "
Yesu ya wa almajiren sa magana. wannan kalma "kai" jam'i ne.
Yesu yana magana da almajiren sa kamar su ne suke tambayan gurasan. AT: " ka bashi gurasan ka domin shi ne ... nasa... shi shi ke bukata"
wannan sashin za'a iya ba da lada a fid da isimi "nacewa." AT: " domin ka nace da rashin kunya" ko "domin cigaba da tambaya shi"
Yesu ya ba da wannan umurnin domin ya karkafa almajiren sa su cigaba da addu'a. wasu yaren za su nemi wasu labarai da wannan fi'ili. ku yi amfani da siffa "ku" da ya dace da wannan mahilli. AT: ci gaba da tambayan abin da kake so ... ci gaba da neman abin da kake sa daga Allah ...neme shi ... ci gaba da kwankwasa kofan"
wannan za'a iya fadan ta a wata siffa. AT: "Allah zai ba ka shi" ko "za ka same shi"
Kwankwasa kofa shi ne ka buga na ɗanlokaci domin mutumin da ya ke ciki ya sani cewa ka na tsaye a bakin kofar. za'a iya juya ta kamar yadda mutani al'adun ku suke nuna cewa sun iso, kamar "fito waj" ko "tari" ko "tafi" anan an nufin cewa mutum ya ci gaba da addu'a sai Allah ya amsa.
wannan za'a iya fadan ta a wata siffa. AT: Allah za ya buɗe maka kofar" ko "Allah za ya karɓe ka ciki"
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya koyar da almajiren sa. za'a iya rubu ta shi kamar bayani. AT: "Ba wani uba ... kifi"
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya koyar da almajiren sa. za'a iya rubu ta shi kamar bayani. AT: "Kuma baza ka iya ba shi kunama ba idan ya tambayi kwai"
Kunama yana kama da gizogizo, amma ya na da wutsiya da ƙari mia dafi. idan ba a san kunama ba a inda kake, za ka iya juya shi kamar "gizogizo mai dafi" ko "gizogizo mai ƙari"
"tunda ku mugaye kun sani" ko ko dashi ke kuna da zunubi, kun sani"
"yaya tabbacin ka ceaw Uban ka da ke cikin sama zai ba ka Ruhu mai Tsarki ... shi? Yesu kuma ya yi amfani da tambaya domin ya koyar da almajiren sa. za'a iya rubu ta shi kamar bayani. AT: "kana da tabbacin cewa Uban ka da ke sama zai baka Ruhu mai Tsarki ... shi."
Mai wallafa ya yi amfani da wannan kalman domin ya sa lamba a farkon sabuwa abin da ya auko.
zai za da amfani a kara wa ta bayani. AT: "Yesu yana fitar da aljini a cikin wani mutum" ko "Yesu yana sa aljani ya bar mutum"
Aljani ya na da karfi ya hana mutane magana. AT: " aljani ya sa mutumin kar ya yi magana"
zai za da taimako a kara wata labari fiye da kima. AT: " Da aljani ya fita daga cikin mutumin" ko "da aljani ya bar mutumin"
"mutumin da bai iya yin magana ba yayi magana"
"Ya na fitar da aljani da ikon Ba'alzabuba, sarkin aljanu"
"Wasu mutane sun gwada Yesu," Suna so ya hakikanta cewa ikon sa daga Allah ne.
suka tambaya shi ya bada wata alama daga sama" ko "suna neman ya ba su wata alama daga sama." Hakan ne suke so ya hakekance da cewa ikon sa daga Allah ne.
"mulkin" a nan an nufin mutane a ciki. wannan za'a fadan ta a wata siffa. AT: "idan mutanen mulki sun yi fada a tsakaninsu, za su hallakar da mulkin"
A nan "gida" na nufin iyali. AT: idan mutanen iyali suna faɗa da juna, zasu rusa iyalin su"
"faɗuwa kasa da rushewa."wannan sifar gidan rushe wa na nufin hallakan iyalin idan su na faɗa da juna.
"sheɗan" a nan na nufin aljanu wanda suke bin sheɗan da sheɗan da kansa. AT: "Idan sheɗan da membobin sa suna faɗa da junan su"
Yesu yayi amfani da tambayan domin ya koya wa mutane. wannan za'a iya juya ta kamar bayani. AT: Idan shaiɗan ... da mulkin sa ba za su dawama ba." ko "Idan sheɗan ... da mulkin sa zai rabu."
Domin kun ce da karfin Ba'alzabuba nake sa aljanu su bar mutane." Mahawaran sa mai zuwa za'a iya faɗan ta kamar baro-baro: AT: "Domin kun ce da karfin Ba'alzabuba nake sa aljanu su bar mutane. wannan na nufin cewa sheɗan ya rabu gaba da kan sa"
Idan ni ... da ikon wa masubin ka suke sa aljanu sa fita da karfi su bar mutane?" Yesu yayi amfani da tambaya domin ya koya wa mutane. ma'anar tambayan Yesu za'a iya bayyana. AT: "Idan ni ... toh za mu iya yarda da cawa masubin ka suma suna fitar da aljanu da ikon Ba'alzabuba. amma baku yarda da cewa gaskiya ne."
"masubin ka wadda suke fitar da aljanu da ikon Allah zasu sharanta ku domin kun ce ina fitar da aljanu da ikon Ba'alzabuba"
"Yatsa Allah" na nufin ikon Allah.
"wannan ya nuna cewa mulkin Allah ya zo gun ku"
wannan na magana akan Yesu yadda ya yaki sheɗan da dukkan aljanu sa kamar Yesu mutum mai karfi ne wanda ya kwashe abin mutum mai karfi.
"cire kayan faɗan mutumin da kariyansa"
"ba wanda zai sata abun"
"saci kayan sa" ko dauki ko mai da yake so"
wannan na nufin kowane mutum ko kugiyan mutane. "Wanda ba nawa bane gaba yake dani, wanda kuma baya taya ni tarawa watsarwa yake yi" ko "wandanda basu tare dani gaba suke dani wadan da kuwa basu taya ni tarawa watsarwa suke yi"
"wanda baya tallaba mini" ko "wanda ba ya aiki da ni"
"aikin gaba dani"
Yesu na nufin tara almajiren da suke bin sa. Wannan za'a iya fadin ta baro baro. AT: "duk wanda ba ya sa mutanesu guna ya na sa mutane su guje ni"
Wannan na nufin "wurin da ba'a feya zuwa" wurin da ruhun mugaye ke yawo.
"Idan ruhun bai sami hutawa a wurin ba"
wannan na nufin mutum wanda da yake raye. AT: "mutum wanda ni na ke a raye"
Wannan misalin ya yi magana akan mutum kamar shi gida ne wanda aka share tsaf an kuma sa komai a inda ya kamata. na nufin cewa gidan ba komai. wannan za'a iya bayana ta a wata siffa da labarin a bayyane. AT: "neman mutum kamar gidan da wanda mutum ya share ya kuma shriya ya sa komai a ida ya kamata, amma ya bari ba komai" ko "neman mutumin kamar gidan da aka share an gyara amma ba komai"
Wannan kalman" farko" na nufin yanayi mutum lokacin da ya na da ruhu mara kyau kamin ya barshi. AT: "muni fiye da yanayin ɗanekamin ruhun ya barshi"
Wannan sashin maganar anyi amfani da ita a nan damin a nuna abu mai muhimmanci a labarin da ya auko. idan yarenku suna da wata hanyan yin haka,zaku iya amfani da shi anan.
Wannan karin maganar na nufin " yi magana da karfi feye da amon taron"
Wannan sashin jikin matan an nufim mace gaba daya. AT: "Yana da kyau ga macen da ta haife ka ta kuma shayar da kai a maman ta" ko "Yaya murnan macen da ta haife ka ta kuma shayar da kai a mamanta zai zama"
"Zai iya zama mafe kyau ga wadansu"
"ji sakon da Allah ya fada"
"Da mutane suna karuwa a taron" ko "Da taron suna kara grima"
A nan "zamani" ana nufin mutanen da ke cikin ta. AT: "Mutanen dake zama a wancen lokacin mugayen mutane ne. suna nema... ma su" ko Mutanen da ke zama a wannan lokacin mugayen mutane ne. kuna nema... ma ku"
Wannan labarin akan wace irin alama take nema za'a iya bayyana ta. AT: "suna so in yi wata aikin al'ajibi da zai zama shaida cewa na zo daga Allah"
Wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: " Allah ba zai ba ta wa alama ba"
"meya faru da Yunana" ko "aikin al'ajibin da Allah ya yi wa Yunana"
wannan na nufin cewa Yesu zai zama alaman daga Allah wa Yahudawan wancan ranan daidai yadda Yunana ya zama alama daga Allah wa mutanen Nineba
Yesu yana magana akan sa.
"wannan mutanen da suke zama ayau"
wannan na nufin Sarauniyar Sheba. Sheba wata mulki na kudun cin israi'la.
"zai tashi tsaye ta yi shari'a wa mutanen wannan zamani"
Wannan karin magana na nufin cewa ta zo daga wuri mai nisa. AT: ta zo da wuri mai nisa sosai" ko "ta zo daga wuri mai nisa"
Yesu yana magana akak sa. AT: Ni, wanda na fi Sulemanu, ina nan"
Yesu yana magana akak sa. AT: Ni, na fi Sulemanu"
zai zama da taimako ka bayyana cewa wannan na nufin tsohon brinin Neniba. AT: "mutanen da ssuka zauna a tsohon brinin"
wannan ya kumshe maza da mata. AT: " mutanen"
"mutanen wannan zamani"
"domin mutanen Nineba sun tuba"
Yesu ya na magana akak sa. zai zama da taimako a bayyana cewa ba su saurare shi ba. AT: "ko da shike na fi Yunana, amma baku tuba ba"
"boye shi ko ya sa ta a karkashin kwando"
Fahimtatciyar batun da fi'ili a cikin kashi za iya samarma. AT: amma mutum ya sa shi a mazaunin ta" ko " mutumin ya sa shi a kan tebur"
a sashin wannan misalin, abin da suka gan yesu ke yi ya ba su ganewa kamar yadda ido ke bada gani wa jiki. AT: "idon ka kamar fitilar jikine"
Ido misali ne na gani.
jiki shine dukan rayuwan mutum.
A nan "ido" na misalin gani. AT: "Idan gani ka na da kyau" ko "idan kana gani da kyau"
Wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: "haske zai cika dukan jikin ku" ko "za ka iya gann kowace irin abu da kyau"
A nan "ido" na misalin gani. AT: " Idan ba ka gani da kyau" ko " kana talauci a gani"
"ba za ka iya gani ba"
"ka tabbata cewa abin da kake tunani haske ne ba duhu ba" ko "ka tabbata cewa ka san abin ka haske ka kuma tabbata cewa ka san abin dake duhu"
Yesu ya faɗi gaskiyar kuma kamar tamka. yayi maganar mutane da suki ciki da gaskiya kamar fitilar da hasken sa ya haskaka.
Marubucin yayi amfani da wannan kalman domin ya sa alama a sabuwar abin da ya auko.
wannan na nufin gidan Farisawa.
Wannan al'adane na cin abincin shakatawa kamar dina wa mutane su ci suna kwance da daɗi kewaye da tebur. za ka iya juya shi da kalma da yaren ka suke amfani da shi yadda mutane ke yi idan suna cin abin ci. AT: "zauna a tebur"
Farisawan suna da doka wanda sai mutane sun wanke hannayen su kamin su zama da tsabta kamar masu biki a ga ban Allah.AT: "wanke hannayen ka" ko "wanke hannayen ka kamin ka za ma sa tsabta"
wankin bayan ganga sashi ne na al'adun al'adar yin Farisawa ne
wannan sashin misali ne bambanci ne na dubawa a hankali yadda suke wanke bayan kwanuka da yarda suke watsar da yanayin su na ciki.
wannan furcin zai iya zama maza ko mata, ko da shike Farisawa da Yesu yake magana da su maza ne.
Yesu ya yi amfani da tambayan domin ya kwaɓi Farisawan da rashin ganawar su cewa abin da ke zuciyar su al'amrin Allah. wannan za'a iya juya shi kamar bayyani. AT: "wanda yayi cikin shine ya yi wajen"
wannan na nufin abin da za su dinga yi da kwapina su da tasaar su. AT: "Ku ba wa talakoki abin da ke ciki" ko "ko zama masu bayarwa"
"za ku zama da tsabta gaba daya" ko "za ku zama da tsabta ciki da waje"
"kuna bawa Allah daya daga cikin goma na'ana'a da yin nadama da wasu ganye daga cikin lambun ku. "Yesu ya na bada misali ya da Farisawan suke ba da zakkan abin da suka samu.
wannan ganyayene. mutane suna saganyayen kadan ne a cikin abincin su domin ya ba shi dandano. idan mutanen basu san na;ana'a da yin nadama ba,sai ku yi amfani da sunan ganye da suka sani ko gabadayan furci kamar "ganye"
ma'ana mai yuwa 1) " kowace irin kayan lambu" 2) " kowace irin ganyen lambu" ko 3) "kowace irin shukin lambu."
"son Allah" ko "kauna ga Allah." Allah shine kauna.
"babu kasawa" yi nauyin da cewa wannan yaka mata a dinga yi.wannan za'a iya bayanata kamar mai yaƙani. AT: "ka kuma yi duk sauran abubuwa masu kyau"
" kujera mafi kyau"
"kuna so mutane su gaishe ku da daraja"
Farisawan suna kama da kabarbarun da ba alama domin kuna da kyau kamar masu biki, amma kuna sa mutane kewaye da ku su zama mara tsabta.
Wannan kabarbarun ramuka ne a ƙasa ida ake binne mattce. ba su da farin dutsen da mutane suki sawa akan kabarbarun domin souran su gan su.
Idan yahudawan suna tafi ya akan kabarin, za su zama marasa tsabta. wannan kabarbarun marasa alama neke sasu su yi haka.wannan za'a iya fadan ta da kyau. AT: "da rashin sani kuma yana sasu su zama marasa tsabta"
Wannan ya gabatar dawani sabuwar hali a labarin.
maganar Yesu game da Farisawa mai yuwa ta shafe malaman ataura ta Yahudawa.
Yesu ya bayyana cewa yayi niya ya hukunta aikin malaman ataura da Farisawa.
"kun sa wa mutane damuwa mai nauyi wanda baza su iya daukawa ba." Yesu ya yi magana akan wani game da sa wa mutane doka kamar ya basu kaya ne mai nauyi su dauka. AT: "kun dame mutane da ba su dokoki daya wa su bi"
Ma'ana masu yuwa 1) " ku yi komai duka ku taimaki mutanen daukan kayan" 2) "yi dukan kokari ku dauki kayan da kan ku."
Yesu ya kwaɓi Farisawan da malaman shari'an. sun sani game da kisan annabawan, amma basu hukunta su kakan kakanninsu domin kashe su. AT: "Toh amma sun yi ƙarar su, kun tabbata ku kuma yarda"
wannan yana nufin maganar da aka yi a baya da cewa malamin atauran suna damin mutane da dokoki.
"hikima" an yiwa kamar zai iya yi wa Allah magana. AT: "Allah cikin hikimar sa ya ce" ko " Allah cikin hikima yace"
"Zan aika annabawa da manzannai wa mutane na. "Allah ya bayyana kafin da cewa zai aika annabawa da manzanai wa kakan kakar Yahudawa maso sauraron wanda Yesu yake yi masu magana.
"mutane na za su tsananta su kuma kashe wasu annabawa da manzanai."Allah ya bayyana kafin da cewa kakan kakar Yahudawa maso sauraron wanda Yesu yake yi masu magana za su tsananta su kuma kashe wasu annabawa da manzanai.
Mutanen da Yesu yake yi masu magana za'a rike su alhakin ƙashe annabawan da suka yi da kakan kakanin nasu. AT: "saba da haka Allah zai rike tsaran alhakin dukan mutuwar annabawab da mutane suka ƙashe"
"jinin" ... zubar" na nufin jinin da ya zuba da aka ƙashe su. AT: "kisan kai da aka yi wa annabawa"
Wannan yana yuwa fada na a tsohon alkawari wada ya kwaɓi mutanen isra'ilawa akan bautar gumaka. wannan ba uban yahaya mai baftisma bane
Wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: "wanda mutane suka kashe"
Yesu ya yi maganan gaskiyar Allah kamar gida ne wanda malaman sunki su shiga sun kuma ha wasu samun makullin su shiga suma. Allah, sun kuma hana wasu sani shi kuma.
Wannan misalin na nufin samun hanya na shigan gida ko dakin ajiya
"kai da kanka ba ka shiga ka sami sani ba"
"Sa'an da Yesu ya bar gidan Farisawa"
marubata da Farisawa basu yi jayayya doimn su kare ra'ayinsu ba, amma domin su yiwa Yesu tarko cewa ya karya dokan Allah.
wannan na nufin suna so su fadi wani abu wanda ba daidai ba su yi masa shari.
Ya yi adu'a, "Uba, a tsarkake sunan ka. mulkin ka ya zo. Ka ba mu abincin yau da kullum kuma ka gafarta mana zunuban mu, gama mu ma muna gafarta wa duk wanda yake mana laifi. Kuma kada ka kai mu wurin jaraba."
Soboda rashin kunyan nacewan abokin
Zai ba su Ruhu Mai Tsarki.
Sun la'anta shi wai yana fitar da aljannu da ikon Ba'alzabul, sarkin aljannu.
Ya fitar aljannun ta yatsan Allah
Karshen yanayin mutumin zai fi muni da yanayin farko.
Wanda sun ji maganar Allah suka kuma kiyaye ta.
Sulemanu da Yunusa.
Ya ce sun cike da zalunci da mugunta.
Sun watsar da aikata gaskiya da kaunar Allah.
Suna jibga ma mutane kaya masu yawar dauka, amma su da kansu ba swa taba wadanan kaya.
Alhakin jinin dukan annabawa da aka zubar tun daga farkon duniya, a bi shi a kan mutanen wannan zamani.
Sun yi tsayayya da kuma gardama da shi, suna hakwansa su burma shi a cikin maganar sa.
1 Da jimawa kadan, bayan da mutane da yawa suka taru kwarai har suna tattaka junansu. Sai ya fara yin magana da almajiransa. "Ku yi lura da yisti na Farisawa, wanda shine manufunci. 2 Amma ba abin da ke rufe wanda ba za a tone ba, ba kuma abin da ke boye wanda ba za a sani ba. 3 Saboda haka ba abin da za ku fadi a asirce wanda ba za a ji shi a cikin sarari ba. Abin da ku ka fadi da rada cikin lungu, za a yi shelarsa a ko'ina. 4 Ina gaya maku abokaina, kada ku ji tsoron wanda da za su kashe jiki. Bayan haka kuma ba abin da za su iya yi. 5 Bari in gargade ku a kan wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron shi wanda bayan ya kashe zai iya jefa ku cikin jahannama. I, ina ce maku ku ji tsoronsa. 6 Ba a kan sayar da 'yan tsuntsaye biyar a kan anini biyu ba? Duk da haka, Allah ba zai manta da ko daya daga cikinsu ba. 7 Har ma gashin da ke kan ku ya san yawan su. Kada ku ji tsoro, ku kun fi tsuntsaye daraja a wurinsa. 8 Ina gaya maku, dukan wanda za ya shaida ni a gaban mutane, Dan Mutum kuma za ya shaida shi a gaban mala'kun Allah. 9 Kuma dukan wanda ya ki ni a gaban mutane, za a ki shi a gaban mala'ikun Allah. 10 Dukan wanda ya yi magana gaba da Dan Mutum, za a gafarta masa. Amma shi wanda ya yi sabon Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba. 11 Idan suka kawo ku gaban majami'a, ko gaban masu shari'a, ko gaban masu iko, kada ku damu da abin da za ku fada domin ku kare kanku. Ko kuwa abin da za ku ce. 12 Gama Ruhu Mai Tsarki zai koya maku abin da za ku fadi a wannan lokaci." 13 Sai wani a cikin taron ya ce masa, "Malam, ka yi wa dan'uwana magana ya raba gado da ni 14 Yesu ya ce masa, "Kai, wanene ya sa ni in zama alkali, ko matsakanci a kanku?" 15 Sai kuma ya ce masu, "Ku yi lura kada ku zama masu hadama, gama ba abin da mutum ya mallaka ne ya fi mahimmanci a cikin rayuwar sa ba." 16 Sa'annan Yesu ya fada masu wani misali, ya ce, "Gonar wani mutum ta bada amfani sosai, 17 ya yi tunani, ya ce, 'Me zan yi, domin ba ni da wurin da zan iya ajjiye amfanin gonata?' 18 Sai ya ce, na san abin da zan yi. Zan rushe rumbuna na in gina wadansu manya-manya, a nan zan ajjiye hatsi na da dukan abubuwa. 19 Sai in ce da raina, "Ya raina, kana da abu da yawa da aka ajjiye dominka, sai ka huta, ka ci, ka sha, ka yi murna." 20 Amma sai Allah ya ce da shi, 'Wawan mutum, a cikin daren nan ana son ranka daga wurinka. Kayan da ka tara ka shirya wa kanka, na wa za su zama?' 21 Haka wanda ya tara wa kansa dukiya yake, idan ba shi da dukiya a wurin Allah." 22 Yesu, ya ce da almajiransa, "Saboda haka ina cewa da ku, kada ku damu da rayuwarku, wato, abin da za ku ci, ko abin da za ku sa a jikinku. 23 Gama rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi. 24 Ku dubi hankaki wadanda ba sa yin shuka, ba sa yin girbi. Ba su da rumbuna ko dakunan ajjiya, amma Allah ya na ciyar da su. Ku fa kun fi tsuntsaye daraja! 25 Wanene a cikinku ta wurin sha'awarsa za ya iya karawa kansa kwanaki? 26 Idan ba ku iya yi wa kanku dan karamin abu ba, me ya sa za ku damu da sauran abubuwa? 27 Ku dubi furanni a daji - yadda suke yin girma. Ba su kan yi aiki ba, ba su kan yi kadi ba. Ina gaya maku, ko Sulaimanu, a cikin darajarsa, bai sa tufafin da suka fi nasu kyau ba. 28 Idan Allah ya sa wa ciyawa tufafi masu kyau haka, wadda yau tana nan, gobe kuma a sa ta a wuta, ta yaya zai kasa sa maku tufafi, ku masu kankantar bangaskiya! 29 Kada ku damu da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kuma kada ku yi alhini. 30 Gama dukan al'umman duniya suna neman wadannan abubuwa, kuma Ubanku ya san kuna bukatar wada nan abubuwan. 31 Amma ku bidi mulkinsa, wadannan abubuwa kuma za a kara maku su. 32 Kada ku ji tsoro, ku 'yan kanana, domin da murna Ubanku zai ba ku mulkin. 33 Ku sayar da abin da ku ke da shi ku ba matalauta. Kuyi wa kanku jakukkuna wadanda ba za su lalace ba, ku yi ajjiya cikin sama inda abin ba ya karewa, inda barayi ba za su iya zuwa ba, kwari kuma ba za su iya lalatawa ba. 34 Domin inda dukiyarka take, can zuciyarka za ta kasance kuma. 35 Ku rage tsawon tufafinku, ku yi dammara, ya zama fitilarku tana ci koyaushe, 36 ku kuma zama kamar wadanda suke jiran mai gidansu ya dawo daga gidan buki, domin duk sa'adda ya zo ya kwankwasa kofa, nan da nan za su bude masa. 37 Masu albarka ne wadannan bayi, wadanda ubangijinsu za ya tarar suna jiran dawowar sa. Gaskiya ni ke gaya ma ku, zai yi dammara yasa su zazzauna ya ba su abinci shi da kansa. 38 Ko da ubangijinsu ya zo da dare, ko da tsakar dare, ya tarar da su a shirye suna jiransa. Masu albarka ne wadannan bayi. 39 Kuma ku san wannan, da mai gida ya san lokacin da barawo zai zo, ba zai bari a fasa masa gida a shiga ba. 40 Sai ku zauna da shiri fa domin ba ku san lokacin da Dan Mutum zai dawo ba." 41 Sai Bitrus ya ce masa, "Ubangiji, mu ka ke fadawa wannan misali, ko ga kowa da kowa ne?" 42 Sai Ubangiji ya ce, "Wanne shugaba ne, mai aminci, mai hikima kuma wanda ubangijinsa za ya damka bayinsa a hannunsa, domin ya kula da su, ya ba su abincinsu a kan lokaci? 43 Mai albarka ne wannan bawa, wanda ubangijinsa za ya tarar da shi yana yin abin da aka sa shi ya yi. 44 Hakika, ina gaya maku, zai danka dukan malakarsa a gareshi. 45 Amma idan wannan bawa, ya ce a cikin zuciyarsa, 'Ubangiji na yayi jinkirin dawowa,' sai ya fara dukan bayin, maza da mata abokan bautarsa, ya ci ya sha, ya bugu, 46 ubangijin bawan nan zai dawo a lokacin da bawan bai sa tsammani ba, kuma a cikin lokacin da bai sani ba, ya daddatsa shi gunduwa-gunduwa, ya kuma hada shi da marasa aminci. 47 Bawan nan, ya san halin ubagijinsa, amma bai shirya yayi abin da ubangijinsa yake so ba. Zai sha duka da bulala da yawa. 48 Amma shi wanda bai sani ba, kuma yayi abin da ba daidai ba, ba zai sha duka da bulala da yawa ba. Dukan wanda aka ba abu da yawa, za a kuma nemi abu da yawa daga wurinsa. Kuma ga wanda aka ba abu da yawa amana, za a nemi abu mafi yawa daga gareshi. 49 Na zo domin in sa wuta a duniya, na so da ta riga ta kama. 50 Amma ni, ina da baftisma wadda za a yi mani baftisma da ita, kuma na kagara, da an riga an yi ta! 51 Kuna zaton na zo duniya domin in kawo salama? Na ce maku a'a, amma tsattsaguwa. 52 Daga yanzu za a sami mutane biyar a cikin gida daya, kuma za su rarrabu, mutane uku suna gaba da biyu, biyun kuma suna gaba da ukun. 53 Da da mahaifi za su yi gaba da juna, dan zai yi gaba da mahaifinsa. Mahaifiya za ta yi gaba da diyarta, diya kuma gaba da mahafiyarta; uwar miji za ta yi gaba da matar danta, matar da kuma gaba da uwar mijinta." 54 Yesu, ya kuma gaya wa taron, "Da kun ga hadari ya taso daga yamma, nan da nan sai ku ce za a yi ruwa, haka kuwa ya kan zama. 55 Idan iska tana busowa daga kudu sai ku ce za a yi zafi mai tsanani, haka kuwa ya kan faru. 56 Munafukai, kun iya fasarta yanayin kasa da sama, amma baku iya fasarta abin da yake faruwa yanzu ba? 57 Me ya sa ba ku iya gane abin da zai tamake ku? 58 Idan kuna tafiya wurin shari'a da abokin husumarka, ka yi kokari ku daidaita tun a kan hanya domin kada ya kai ka wurin mai shari'a. Domin kada mai shari'a ya mika ka ga mai tsaron kurkuku, shi kuwa mai tsaron kurkuku ba zai nuna maka sani a cikin kurkuku ba. 59 Na gaya maka, ba za ka iya fitowa ba sai ka biya dukan kudin da a ke binka?
Yesu ya fara koya wa almajiren sa a gaban mutane dubu.
Wannan yana yuwa alokacin da marubucin da farisawan suke neman hanya su yiwa Yesu tarko.marubucin ya yi amfani da wannan domin ya sa alama a sabuwar abin da ta auko.
Wannan labarin baya ne awnda yake fadan saitin labarin.
"taro mai yawa sosai"
Wannan yana yuwa an ari ayi nauyi saboda mutane suna ma'il kusa da juna kuma zasu iya taka juna" ko "suna taka junan su a kafa"
"Yesu ya fara magana wa almajiren sai ya ce masu"
Kamar yadda yisti yake bazuwa a dukan kullun dun kulen burodi, nasu munafurcin ya na bazuwa a cikin al;umma. AT: " Ka tsare kan ka game da munafurcin Farisawan, wanda ke kama da yisti" ko "Kayi hankali kada ka zama kamar munafurcin Farisawan. halin muguntar su ya na shafan kowa kamar yanda yisti ya shafan kullun dun ulen burodi"
Wannan kalman "Amma" ya hada aya da ayan da ya wuce a baya akan munafurcin Farisawan.
"komai da yake a ɓoye zai bayyanu, "Wannan za'a iya bayyana shi a wata siffa. AT: "mutane za su san abin da mutani suka yi a boye"
Wannan na nufin abu daya ne yadda ya ke a farkon sashin bayanin domin a yi nauya gaskiyan ta. za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: mutane zasu san kowanni abu da wasu suka boye"
A nan "duhu" misali ne na "dare" wanda yana misalin "asirce . da "haske" wato misalin "rana" wanda shi ne misalin "abayyane. wannan saahin "za'a ji" za'a iya bayyana a wata siffa . AT: duk abin da ka fada asirce da dare, mutane za zasu ji ta da hasken rana"
wanna za'a iyabayyana ta a wata siffa. AT: "raɗa wa wani mutun"
"a dakin kulle" wannan na nufin magana asirce. " "asirce" ko "ɓoye"
"za'a yi iho da karfe" wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: " mutane za su yi shelar"
gidaje a Isra'ilasuna da kitan jinka, mutane sukan je su tsaya a sama su. idan zai janye hakalin mai karatu yayi tunanin yadda mutum zai je ya hau saman gida, toh sai a juya she da furcin gaba daya kamar "a wuri mafi tsaho domin kowa ya ji"
Yesu ya yi magana da al'majeren sa su daina wannan maganar su koma wata sabuwa, a wannan magana sai su yi magana akan rashin jin tsoro.
"baza su iya yin wata lahani ba"
wannan shashin "wanda" na nufin Allah. wannan za'a iya bada lada. AT: "ji tsoron Allah wanda, bayan ...yana da iko" ko "ji tsoron Allah, domin bayan ... yana da iko"
"bayan da ya kashe ka"
wannan bayani ce gaba daya akan ikon Allah ya sharanta mutane. baya nufin cewa wannan zai faru ne da al'majiren sa. AT: "yana da iko ya jefa mutane a cikin gidan wuta "
Yesu ya yi amfani da tambaya ya koya wa al'majiren sa. AT: "kun sani da cewa yan tsunsaye biyar akan sayar anini biyu."
kankananan tsuntsaye masu cin iri
wannan za'a iya bayaana ta a wata siffa da siffa mai yaƙini. AT: "Allah ba ya manta da ko dayan su" ko "Allah yana sane da kowa ce tsuntsaye"
wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: " Allah ya sani gashi nawa ne akan ka"
dalilin tsoron ba a fada ba. ma'ana mai yuwa 1) "Kada ka ji tsoron abin da zai faru da kai" ko 2) "sabada haka kada ka ji tsoron mutane cewa za su ji maka ciwo."
"Kuna da daraja sosai a gun Allah feye da tsuntsaye"
Yesu yayi magana da masu sauraron sa cewa suko ma wata magana su yi magana akan shaidawa.
menene shaidawaza'a iya faɗan ta ba shakka. AT: "duk wanda ya gaya wa wani cewa shi al'majiri na ne" ko "duk wanda ya yarda agaban mutane cewa yana biyayya da ni"
Yesu yana mai da kansa. AT: "Ni ɗan mutum"
"wanda ya musan ce ni a gaban mutane. "menene musu za'a iya fadan ta ba shakka. AT: duk wanda ya ki ya yarda da cewa shi al'majiri na ne" ko "ko ya ki ya cewa ya na beyayya da ni, shi"
"za'a ki shi." wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: "ɗan mutum zai yi musun sa" ko " Ni zanyi musu cewa shi ba al'majiri na bane"
"Duk wanda yayi maganan da babu kyau akan ɗan mutum"
"za'a yafe masa."wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: "Allah zai yafe masa wancan"
"maganar mugunta akan Ruhu Mai Tsarki"
wannan za' a iya furta da siffan fi'ili. AT: "amma shi...Allah ba zai yafe masa ba" ko "amma shi Allah zai dube shi da laifi harabada"
Ba'a fada wa ya kawo su ga shari'a ba.
"a cikin majami'a a yi maku tambayoyi a gaban shugabanan adini"
zai iya zama na tilas ka hada wanan ya za ma bayani. AT: "wasu mutane wanda suke da karfi a cikin ƙasa"
"a wan can lokaci" ko sa'a nan"
A wata al'ada, gado yana zuwa daga uba musamman in ya mutu. zaka iya ka bayyana cewa uban mai maganar ya mutu. AT: karaba gadon da ni tun da ubana ya mutu"
ma'ana mai yuwa 1)wannan wata hanya ce mai sauki na magana da bako ko 2)Yesu ya kwaɓe mutumin. yaren ku kila tana da wata hanya da suki magana da mutane kamar haka. wasu mutane basu juya wannan gaba daya.
Yesu yayi amfani da tambayan domin ya kwaɓe mutumin. wasu yaren zasu yi amfani da siffar jam'i "ku" ko "kai." AT: Ni ba alkali ko komatsakacin ku bane."
Wannan kalman "su" anan mai yuwa tana nufin dukan taron jama'a ne. AT: " sai Yesu ya cewa taron"
"ku kare kanku daga kowace irin handama." AT: "kada ku bar kanku ku so kawace irin abu" ko "kada ku bar sha'awancen kuna samun abubuwa ya yi mulki akan ku"
wannan tabbataccen labari ne na kowa. baya nufin takamaiman mutum. wasu yaren suna da hanyan furta wannan .
"abu nawane yake da su" ko "arziki nawa ne ya ke da su"
Yesu ya cigaba da koyasuwan sa da ba da almara.
Mai yuwa Yesu yana magana da dukan taron jama'a ne
"girman da gribi mai kyau"
wannan tambayan ya nuna yadda mutum yake tunani wa kansa.AT: "ban san abin da zanyi ba, domin bani da wani wuri babba da zan iya ajiye amfanin gonata!"
gini wanda manomi suke ajiya amfanin gana idan suka gribe
mallaka
zan ce wa kaina ,inada shi ... shekaru. huta... murna." ko "zan gaya wa kai na inada shi ... shekaru, domin in huta ... murna."
"Rai" yana nufi rayuwan mutum. AT: "za ka muyu yau da dare" ko "za dauki ran ka daga wurin ka yau da dare"
wa zai reki abin da ka tara?" ko "wa zai samu abin da ka shirya?" Allah ya yi amfani da tambaya domin ya sa mutum ya sani cewa ba zai reke wadannan abubuwan kuma ba. AT: "abubuwan da ka shirya zai zama na wani"
"tara abubuwa masu daraja a sama"
bai yi amfani da lokacin ko da dukiyan sa akan abubuwa masu amfani a wurin Allah ba
"domin wanan dalilin" ko "domin abin da wannan labarin ya koyas"
"sabo da rayuwan ka da abin da zaka ci" ko "sabo da samin abincisosai domin ka rayu"
"sabo da jikin ka, abin da za ka sa" ko "sabo da samun kaya da za ka sa a jikin ka"
wannan labari ne na daraja ga kowa. AT: "rayuwa yana da amfani sosai fiye da abincin da muke ci"
"jikin ka ya na da amfani sosai fiye da kayan da kake sawa"
Wannan na nufin kowanne1) hankaka, irin tsuntsu wanda take cin musamman hatsi, ko 2) hankaki, wata irin tsuntsu wanda take cin naman mataccen dabbobi. Masu sauraron Yesu suna daukan hankaki marasa amfani domin Yahudawa basu cin irin wannan tsuntsayen.
wannan warare ne wanda ake ajiye abinci.
Wannan maganar motsin rai ne, ba tambaya ba ne. Yesu yanuna nauyi akan yadda mutane su ke da daraja ga Allah fiye da tsuntsaye.
Yesu yayi amfani da tambaya domin ya koya wa al'majiren sa . AT: bawa ni a cikin ku da zai iya karawa kansa kwanaki da zama mai radɗaɗi!"
Yesu yayi amfani da tambaya domin ya koya wa al'majiren sa. AT: "Tunda baza ku iya yi wa kanku karamin abu ba, kada kudamu da sauran abubuwan."
"Yi tuntni yadda furanni suke grima"
furanni fure ne kyau da suke grima a daji.idan yarenku ba su da kalma wa lily.za ka iya yin iaki da wata fure mai kamar ta ko ka juya ta kamar "furanni"
tsarin da ake yin zare ko yadi na riga ana kiran ta "kadi."zai zama da taimako ka bayyana. AT: ba su yun zare domin su yi riga" ko "kuma ba su yin zare"
"sulemanu, wanda ya ke da dukiya mai grima" ko "sulemanu, wanda ya ke sa kaya masu kyau"
"Idan Allah ya sawa ciyayin gona reguna kamar haka, kuma shi" ko "Idan Allah ya ba wa ciyayin gana reguna mau kyaukamar haka, kuma shi." ana maganar Allah ya sa ciyayin sunyi kyau kamar Allah ya sa masu reguna ne masu kyau. AT: "Aian Allah ya sa ciyayin gonar sunyi kyau kamar haka, kuma shi"
Wannan za'a iya bayyana ta a watasiffa. AT: "wani yajefa shi cikin wuta"
wannan magana ce ba tambaya ba ne. Yesu yayi nauyi cewa zai hakika zai lura da mutane feye da yadda ya ke yi wa ciyawa. wannan za'a iya bayyana ssshi ba shakka. AT: "hakika zai sa mana kaya mafi kyau"
"kada ku damu akan abin da za ku ci ko za ku sha" ko "kada ku damu sosai da abun da za ku ci ko sha"
A nan "kashashen"tana nufin "marasa bangaskiya." AT: "dukka mutanen wasu kashassshe" ko " dukka marasabi na duniya"
wannan suna ci mai muhimmanci ga Allah.
"sa zuciya ga mulkin Allah" ko " sa bege ga mulkin Allah"
"wadannan abubuwa kuma za'a kara maka" "wadannan abubuwa" na nufin abinci riguna. wannan za'a iya bayyana shi a wata siffa. AT: "Allah kuwa zai ba ka wadan nan abubuwa"
Yesu yana kiran al'majiren sa garki. graki tarone na raguna ko akuyoyi wanda makiyayi yake lura da su kamar yadda makeyayi ya ke lura da tumakin sa, haka ne Allah ya ke lura da al'majiren sa. AT: "karamin kungiya" ko "tsada kungiya"
zai zama da taimako a fada abin da suka karba. AT: "ku bawa talakokin mutane kudin da kuka karba daga sayarwa"
Jakukkuna da ajiya a sama abu daya ne. duk suna nufin albarkan Allah a sama.
wannan shi ne albarkan ba wa ta;akoki. AT: "ta haka zaka yi wa kanka"
"jakan kuɗi wanda ba za a sami rami a kai ba"
"wanda ba zai kare ba " ko "mara ƙanƙnata"
"barayi ba za su zo kusa ba"
"asu ba su batarwa"
asu karamin ƙwaro ne wanda yake cin rami a kaya. za ka iya amfani da wata ƙwaro kamar tururuwa ko gara.
"zuciyar ka yana gun da ka ajiye arzikin ka"
A nan "zuciya" na nufin tunanin mutum.
Mutane suna sa rigunar tsarauta mai filawa. su na yin dama ra da shi domin su ɗage sa'anda su ke tafiya. AT: "Yi damara da regunar ku domin ku yi shirin bauta" ko "ka shirya domin bauta"
Wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: "ya zama fitilarku tana ci"
yesu ya umurce al'majiren sa su shirya domin sa haka kuma su zama kamar yaron gida wanda yake a shirye domin zuwan maigidan sa.
"dawo gida daga bukin aure"
Wannan na nufin kofan maigidan aikin yaron gidan ne ya buɗe masa kofa.
"yadda ya ke da kyau wa"
"wadan da maigidan ya same su a shirye su na giran dawa wan sa" ko "wanda suke a shirye lokacin da ya zo"
domin yaron gidan amintacce ne kuma yana a shirye ya bauta wa maigidan sa, mai gidan kuma zai basu lada ta wurin yi masu bauta.
tsakar dare wato daga karfe 9:00 pm da tsakar dare. AT: "tsakar dare" ko "kafin tsakar dare"
agogo na uku wato daga karfe 3:00am. AT: "ko idan ya zo da lati a cikin dare"
"san yaushe"
Wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: "da bai bar barawo ya fasa ma sa gidan sa ba"
Abin da ke kama kaɗai da barawo da kuma ɗan mutum shine mutane basu san lokacin da ko dayan su zai zo ba, ya ka mata su zauna a shiri.
"ba su san a wani lokaci ba ne"
Yesu yan amagana a kan sane. AT: Ni ɗan mutum zan zo"
Yesu yayi amfani da tambaya domin ya amsa wa Bitrusba ta hanya kusakusa ba. ya sammanin wadanda su na so su za amintaccen manaja su gane da cewa wanan misalin akan su ne. AT: "Na fada na kowa ne wandanda ... daidai lokaci"
Yesu ya ba da wani misali yadda yaron gida zai zama da aminci sa'anda ya na jeran maigida.
"wanda ubangiji sa zai damka masa sauan yaran gidan a hanunsa"
"Yadda yake da kyau ga yaron gidan"
"idan ubangijin sa ya same shi ya na yin wancan aikin idan ya dawo"
Wannan furcin yana mufin ku lura kuna kulawa ma musamman da abin da zan fada.
"zai sa shi bisa udkan malakarsa"
Wannan nanufin yarao gidan wanda ubangijin sa ya damka masa sauran yaran gidan.
Anan " zuciya" misali hankali ne na mutum ko cikin zucicyar mutum. AT: " yi tunani wa kansa"
"maigida na ba zai dawo yan zu ba"
Kalman nan da aka juya anan "yaran gida namiji da namace" akan juyan su kamar "maza" da "mata" ya nuna da cewa yaran gidan kananane ko suna kaunar maigidan su.
Wannan kalman "rana" da "lokaci"
Ma'ana mai yuwa 1) wannan zuguiguita ne wa maigidan ya yi ma'amala da matsanancin horon yaron gidan, ko 2) wannan ya kwatanta yanayin da yaron gidan zaifalle kan a kuma binne shi kamar horo.
Wannan za'a iya juya ta a wata isffa mai yakani. AT: "Amma ga yaron gidan da ya san ra'ayin ubanjigin sa kuma bai shirya ya yi yadda ya kamata, maigidan zai yi masa bulala da yawa"
"abin da maigidan sa yake so ya yi ...shi"
dukkan yaren gidan an yi masu horo, amma wanan sashin ya nuna dukyaron gidan da ya ki ya yi beyyaya da maigidan sa za'a yi ma sa horo sosai fiye da tsoran yaran gidan.
Wanan za'a iya bayana ta a wata siffa. AT: "za'a nemi sosai ga duk wannan da ya karba sosai" ko "maigidan zai nemi sosai ga duk wanna da aka bashi dayawa"
Wanan za'a iya bayana ta a wata siffa. AT: "mai gidan zai tambaya fiye da dayen ... da yawa" ko "maigidan za' nemi fiye da dayan ... da yawa"
Wanan za'a iya bayana ta a wata siffa. AT: "duk wanda maigidan ya ba shi dukiya da yawa ya lura da su" ko "duk wanda maigidan ya ba shi abin da zai yi"
"Na zo in jefa wuta akan duniya" ko "Na zo in sa wa duniya wuta." Ma'ana mai yuwa1) Yesu ya zo domin ya sharan ta mutanen duniya ko 2) Yesu ya zo domin ya tsakake masubi ko 3) Yesu ya zo domin ya kawo rabuwa tsakanin mutane.
Wannan magana ya nuna nauyin yadda yake so ya faru.AT:"na so sosai da ya kama" ko "na so da ta riga ta kama"
Anan " baftisma" ya na nufin yadda Yesu zai sha wahala. kamar yadda ruwa ya ke rufemutum sa'anda ake yi ma sa batisma, tadda wahala za ta rufe Yesu. AT: "Dole na in sha wahala ta hanyan batisma mai ban tsoro" ko "Dole ne wahala ta rufe ni a masayin mutum yin batisma kuma ruwa ta rufe"
Kalman "amma" anyi aiki da shi ya nuna cewa a zai iya jefa wuta a duniya ba sai ba yan da ya ga ma batisman sa.
Wannan furcin nauyin yadda ya sha wahala. AT: " Na sha wahala mai ban tsoro kuma zai zama haka sai na gama wannan batisma na shan wahala"
Yesu ya yi tanbaya domin ya nuna masu cewa ya zo ya gyara abin da su ke yi da mara kyau. zaku iya kawo kalman "Na zo" da aka cire a bayani na biyu. AT: "Kuna sammanin na zo in ba da zaman lafiya ne a duniya, amma na gaya ma ku ban kawo ba. amma na zo in kawo rabuwa"
"abokan gaba" ko "saɓani"
Wannan misalin irin rabuwan da za'a samu ne a cikin iyali.
zai zama da taimako ka fada cewa wannan na nufin mutane. AT: "za'a sami mutane biyar a gida daya"
"yi wa hamayya ... yi wa hamayya ... yi wa hamayya ... yi wa hamayya ... yi wa hamayya ... yi wa hamayya ... yi wa hamayya ... yi wa hamayya ..."
Wannan yanayi na kullum ya nufin ruwa na zuwa a isra'ila.
"Ruwa na zuwa" ko "za'a yi ruwa"
Wannan yanayi na kullum ya na nufin cewa zafin yanayi na zuwa a isra'ila
"duniya da sararin sama"
Yesu ya yi amfani da tambaya ya ƙwabe taron. Yesu ya yi amfani da tanbayan domin ya fursuna su. za'a iya juya ta kamar bayani. AT: "ku san yadda za ku bayyana wannan lokacin
Yesu ya yi amfani da tanbaya domin ya ƙwabe taron. za'a iya juya ta kamar bayani. AT: "Ku dakan ku iya gane abin da ke mai kyau. "
"a na ku yin"
Yesu ya yi amfani da yanayin munafurci domin ya koyar da taron. tsini sa she ne su tsida shawara a abubuwan da za su iya tsi da shawara ba sai sun je kotu jama'a ba. Wannan za'a iya sake fadan ta domin ya zama mai sauƙin ganawa ba zai iya faruwa ba. AT: "Amma in za ku je ... kudi kaɗan"
tunanin Yesu ya na magana da taron, yanayin da ya ke bayana abu ne wanda mutum zai je ya yi tunani akai shi kadai. a wasu yaren kalmanan "ku" zai zama mafuradi.
"shriya sha'anin da abokin gaban ka"
Wannan na nufin majistare, amma ajilin anan ƙayyadadde ne da yi wa kurari.
"bai dauke ku ba"
"duka kudin da abokin gaban ka ke so"
Za'a ji a haske.
Ku ji tsoron wanda na da iko ya yar da ku a cikin wuta.
Yesu zai furta sunan mutumin a gaban malai'kun Allah.
Rayukar mu bai kunshi yawar dukiyar mu ba.
Zai rushe rumbunan sa, ya gina wadansu manya, in kuma huta, in ci, in sha, ina kuma shagali.
Ya ce masa, "kai marar azanci, a daren nan za'a karbi ran ka; kuma abubuwan da ka shirya, na wa za su zama?"
Mu kwallafa rai ga al'amuran mulkin Allah.
Mu yi ajiyar dukiyar mu a sama, domin a wurin ba barawo da zai gabato, ba kuma asun da zai bata.
Albarka ta tabbata ga bayin nan wadanda ubangijin su da zuwan sa zai same su a fadake.
A'a
Mai gidan zai farfasa masa jiki ya kuma ba shi robon sa tare da marasa rikon amana.
Ana bukata mai yawa daga su.
Akwai mutanw a gida daya wanda za su rabu da juna.
Mu yi kokari mu yi jiyayya da shi tun a hanya.
1 A lokacin, wadansu mutane suka gaya masa game da galilawa wadanda Bilatus ya gauraye jininsu da hadayunsu. 2 Sai Yesu ya amsa masu yace "Kuna tsammani wadannan Galilawa sun fi duk sauran Galilawan zunubi ne, da suka sha azaba haka? 3 A'a, ina gaya maku. In ba ku tuba ba, dukanku za ku halaka kamarsu. 4 Ko kuwa mutane goma sha takwas din nan da suna Siluwam wadanda hasumiya ta fado a kansu ta kashe su, kuna tsamani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne? 5 Ina gaya maku ba haka bane. Amma duk wanda ya ki tuba, dukanku za su hallaka" 6 Yesu ya fada wannan misali, "Wani mutum yana da baure wanda ya shuka a garkar inabinsa sai ya zo neman 'ya'yan itacen amma bai samu ba. 7 Sai mutumin ya ce wa mai kula da garkar, "ka ga, shekara uku kenan nake zuwa neman 'ya'yan wannan baure, amma ban samu ba. A sare shi. Yaya za a bar shi ya tsare wurin a banza? 8 Sai mai lura da garkar ya amsa yace, 'Ka dan ba shi lokaci kadan in yi masa kaftu in zuba masa taki. 9 In yayi 'ya'ya shekara mai zuwa to, amma in bai yi 'ya'ya ba sai a sare shi!"' 10 Wata rana Yesu yana koyarwa a wata majami' a ran Asabaci. 11 Sai, ga wata mace a wurin shekarunta goma sha takwas tana da mugun ruhu, duk ta tankware, ba ta iya mikewa. 12 Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, an warkar da ke daga wannan cuta." 13 Sai Yesu ya dora hannunsa a kanta, nan da nan sai ta mike a tsaye ta fara daukaka Allah. 14 Amma shugaban majami'a yayi fushi domin Yesu yayi warkarwa a ranar Asabaci. Sai shugaban ya amsa yace wa jama'a, "Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo domin a warkar da ku amma ba ranar Asabaci ba." 15 Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, "Munafukai! Ashe kowannenku ba ya kwance Jakinsa ko Sa daga turkensa ya kai shi banruwa ran Asabaci? 16 Ashe wannan 'yar gidan Ibrahim, wanda shaidan ya daure ta shekara goma sha takwas, wato ba za a iya kwance ta a ranar Asabaci kenan ba? 17 Da ya fada wadannan abubuwa, dukansu da suka yi adawa da shi suka kunyata, duk taron kuwa suka yi ta farin ciki da abubuwa masu daraja da yayi. 18 Sai Yesu ya ce, "Yaya za a misalta mulkin Allah, kuma da me zan kwatanta shi? 19 Yananan kamar kwayar mastad, wanda wani mutum ya dauka ya jefa ta a lambunsa, ta kuma yi girma ta zama gagarumin itace, har tsuntsaye suka yi shekarsu a rassanta." 20 Ya sake cewa, "Da me zan kwatanta mulkin Allah? 21 Yana kamar yisti wanda wata mace ta dauka ta cuda da mudu uku na garin alkama don ya kumburar da shi." 22 Yesu ya ziyarci kowanne birni da kauye, a hanyar sa ta zuwa Urushalima yana koyar da su. 23 Sai wani ya ce masa, "Ubangiji, wadanda za su sami ceto kadan ne?" Sai ya ce masu, 24 "Ku yi kokari ku shiga ta matsatsiyar kofa, domin na ce maku, mutane dayawa za su nemi shiga amma ba za su iya shiga ba. 25 In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe kofa, sannan za ku tsaya a waje kuna kwankwasa kofar kuna cewa, 'Ubangiji, Ubangiji, bari mu shiga ciki'. Sai ya amsa yace maku, 'Ni ban san ku ba ko daga ina ku ka fito.' 26 Sannan za ku ce, 'Mun ci mun sha a gabanka, ka kuma yi koyarwa a kan titunanmu.' 27 Amma zai amsa ya ce, "Ina gaya maku, ban san ko daga ina ku ka fito ba, ku tafi daga wurina, dukanku masu aikata mugunta!' 28 Za a yi kuka da cizon hakora a lokacin da kun ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu da dukan annabawa a mulkin Allah amma ku-za a jefar da ku waje. 29 Za su zo daga gabas, yamma, kudu, da arewa, za su ci a teburin abinci a mulkin Allah. 30 Ku san da wannan, na karshe za su zama na farko, na farko kuma za su zama na karshe." 31 Nan take, wadansu farisiyawa suka zo suka ce masa, "Ka tafi daga nan domin Hirudus yana so ya kashe ka." 32 Yesu ya ce, "Ku tafi ku gaya wa dilan nan cewa, 'Duba, na fitar da aljanu, ina warkarwa yau da gobe, kuma a rana ta uku kuwa zan gama aiki na.' 33 Ko da kaka, dole ne in ci gaba da tafiyata yau, da gobe, da kuma jibi, don bai dace a kashe annabi nesa da Urushalima ba. 34 Urushalima, Urushalima masu kisan annabawa, masu jifan wadanda aka aiko gare ku. Sau nawa ne ina so in tattara 'ya'yanki kamar yadda kaza take tattara 'ya'yanta a cikin fukafukanta, amma ba ki so wannan ba. 35 Duba, an yashe gidanki. Ina kwa gaya maku ba za ku kara ganina ba sai ran da kuka ce, 'Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.'"
Yesu ya cigaba da magana a gaban taron. wasu mutane a cikin taron sun yi masa tambaya sai ya fara amsa masu. wannan ya cigaba da labarin da yake luka 12: 1.
wannan shashin ya hada abin da ya auko zuwa ga karshen aya 12, da Yesu ya na kayar da taron jama'an.
a nan "jini" yana nufin mutuwan Galilawa. mai yuwa an kashe su ne sa'anda su ke hadayan su. wannan za'a iya bayyana kamar yadda ya ke a cikin UDB.
Galilawa sunfi yin zunubi ne ... hamya? A'a, na gaya maku." ko "wannan ya nuna maku cewa Galilawa sun fi yin zunubi ... hanya? A'a, na gaya maku."Yesu ya yi amfani da tambaya ingiza gane wa mutanen. AT: "ka na tunanin cewa wannan mutanen Galilawa sun fi yin zunubi ... hanya, amm basu yi" ko "kada ka yi tunanin cewa mutanen galilawa sun fi yin zunubi ... hanya"
Anan "NA gaya maku" nauyin." AT: ba shakka ba su yin zunubi" ko "ka yi kuskure ka yi tunani cewa wahalar su ne yake nina cewa sun fi yin zunubi"
"dukan ku kuma za ku mutu a wanna hanya" za su gan sakamakon sa, ba wai cewa za su mutu a irin wannan hali.
mutu
Koyasuwan Yesu na biyu akan mutane da suka sha wahala. AT: "koka duba waɗancan" ko "yi tunani akan waɗancan"
"mutane 18"
Wannan sunan wuri na a c.
"shin wannan ya hakikanta maku cewa su suka fi yin zunubi ... Urushalima? A'a, na ce." Yesu ya yi tambaya domin ya tsokani ganawan mutanen. AT: "kuna tunanin cewa sun fi yin zunubi ... Urushalima, amma na ce ba su bane" ko "Na ce kada kuyi tunanin cewa sufi yin zunubi ... Urushalima
Taron sun dauka ce wa sun mutu a cikin wannan yanayi mai ban tsoro domin ƙwarai sun fi yin zunubi. Wannan zai iya zama a bayane. AT: "sun mutu domin su suka fi yin zunubi mzfi muni"
"wasu mutane." Wannan kalman anan ajili ne na gaba daya na mutum.
A nan "Na ce a'a" nauyin "A'a." zai zama da taimako a fadi tsini Yesu ba shakka. AT: " Na tabbata cewa basu mutu ba domin su fi yin zunubi" ko "b daidai bane ka yi tunanin cewa wahalar su ya nuna su fi yin zunubi"
Yesu ya fara gaya wa taron misali domin ya bayyana maganar sa na karshe, " Amma in ba ku tuba ba, sukan ku za ku hallaka."
Mai garkar inabin yana da wani mutum wanda ya shuka bishiya a garkar inabin.
Mutumin ya amfani da tanbaya ya yi nauyin da cewa itacen banzane sai ya cewa gadina ya tsare shi. AT: "Kada ka bar shi ya ɓata ƙasa abanza."
"Kada ka yi komai wa itacen" ko " Kada ka tsare shi"
"sa masa taki a ƙasa." taki kashain babboni ne. mutane sukan sa shi a ƙasa domin ya sa ƙasa da itace su yi kyau don shuki. AT: " Sa ma sa taki"
zai za da taimako ka fada abin da zai faru. AT: "Idan ya na da 'ya'ya shakara mai zuw, sai mu bar shi ya cigaba da grima"
bawan yana ba da na shi shawaran; ba doka ya ke bayar wa ga mai sh ba. AT: "ka gaya mini in tsare shi" ko "Zan tsare shi"
mai wallafa ya yi amfani da wannan kalman domin ya nuna farkon abin da ya auko.
" a rana Asabaci" wasu yare za su ce " Asabaci" domin ba mu san wace rana ce Asabaci ba.
Wannan kalma "ga" anan ya nuna mana wani sabon mutu a labarin.
"shekara 18"
"mugun ruhu da ya sa ta mara ƙarfi"
"Mata, an warkar da ke daga cutan ki." Wannan za'a iya bayyana shi a siffar fi'ili: AT: "Mata, na warkar da ke daga rashin ƙarfi"
" Ya taɓa ta"
Wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: "sai ta mike"
"da haushi sosai"
"ce" ko amsa"
Wanna za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: "Bari wani ya warkar da ki cikin wannan kwanaki shida"
"a rana Asabaci." Wasu yaren za su ce "Asabaci" domin ba mu san wata rana ce Asabaci ba.
"Ubangiji ya amsa wa mahukuncin ikilisiyan"
Yesu ya yi magana nan da nan da mahukuncin ikilisiyar, amma ajm'i ya hada da sauran mahukuntan adini kuma, Wannan za'a iya bayyana. AT: "kai da sauran mahukuntan adinin manafukai ne"
Yesu ya yi amfani da tanbaya domin ya sa su su yi tunani akan abin da sun riga sun sani. AT: "kowannenku ba ya kwance Jakinsa ko Sa daga turkensa ya kai shi banruwa ran Asabaci."
Wadan nan dabbobi ne wanda mutane suke lura da su ta wurin basu ruwa.
" a rana Asabaci" wasu yare za su ce " Asabaci" domin ba mu san wace rana ce Asabaci ba.
Wannan kari ne wanda take nufin, "zuriyar Ibarhim"
Yesu ya kwatanta ya da mutane suke daura dabbobi da yadda shaiɗan ya ƙuntata matan da wannan cuta. AT: "wandab shaiɗan ya ajiye naƙasasshe da ciwon ta" ko "wanda shaiɗan ya daure da wannan cuta"
"dogon shekar. 18." Wannan kalmar "dogo" anan na nuna nauyin shekara goma sha takwas doguwan lokaci ne wa matan ta sha wahala. wasu yaren zasu iya samun yadda za su yi nauyin akan wannan.
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya gaya wa mahukuntan ikilisiya cewa basu yi daidai ba. Yesu ya yi magana akan cutan matan kamar igiya ne ya daure ta. Wanna za'a iya juya ta kamar bayani mai ƙoƙari. AT: "ya na da kyau a kunce ta daga wannan daurin ciwon ... rana."
"Da Yesu ya faɗa wadannan abubuwa"
"abin ban mamakin da Yesu yake yi"
Yesu ya yi amfani da tambaya biyu domin ya gabatar da abin da ya ke so ya koyar. AT: "Zan gaya maku yadda mulkin Allah yake ... da me zan kwatanta da shi."
Asalin wannan tambayan daya ne da wanda ya rigaya. wasu yaren zasu yi amfani da dukan tambayan biyu wasu kuma zasu yi da daya.
Yesu ya kwatanta mulkin kamar kwayar mastad. AT: "Mulkin Allah kamar kwayar mastad ce"
kwayar mastad karamin iri ne wanda yake grima ya zama babban tushi. Idan wannan irin ba'a santa ba, wannan shashin za'a iya juya ta da sunan wata iri mai kamar ta ko karamin iri."
"shuka ta cikin lambu."mutane suna shuka wata iri ta gun jefa su domin su warwasu a cikin lambun.
Wannan kalmar "babba" magana ne da ta nuna bambancin itacen da karamin iri. AT: "karamin babban itace"
"tsuntsayan sararin sama." AT: "tsuntsayen da suke tashi sama" ko " tsuntsayen"
Yesu yayi amfani da wata tambayan domin ya gabatar da abin da yake soya koyar. AT: "zan gaya maku wata abu wanda zan kwatanta da mulkin Allah."
Yesu ya kwatan ta mulkin sama kamar yisti data ke cikin kullun burodi. AT: "Mulikn Allah kamar yisti ne"
Karami yisti ne ake bukata ya ta da kullun . Wannan za'a iya fadan ta da saukin ganawa kamar tadda take a UDB.
Wannan garin na da yawa, tunda kowane mudu yana kamar lita 13.zaka iya amfani da ajilida al'adan ku suke amfani da ita su auna gari. AT: "wannan garin na da yawa"
Wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa Alla .AT: "Allah zai cece mutane kadan ne?
"Yi kokari domin ka shiga ta matsatsiyar kofa." Yesu yana maganar hanyan shiga mulkin Allah kamar karamin kafa ne a gidan.tumda Yesu ya na magana da kungiyan, "ku" a wannan umurni jam'i ne.
Da cewa tabbatacceyar kafan matsatsiya ce yana da wuya ka shiga ciki. juya shi a inda za ka ajiye ma'a nar tukuru.
ya nuna cewa ba za su iya shiga ba domin wahalar shigan. iya na gaba ya bayyana wahalar.
"bayan da mai shi"
Wannan na nufin mai gidan dake da matsatsiyar kofa a ayan wanda su regaya. wannan misali Allah ne a masayin mahukuncin mulkin.
Yesu ya yi wa taron magana. siffar "kai" jam'i ne. yana yi masu magana kamar baza su shiga mulkin ta matsatsiyar kofan ba.
"buga kofan." wannan ƙoƙene na samun hankalin mai shi.
"tafi daga wurina"
Wannan aikin yana sananniyar aikatawa, nuna babban ɓakin ciki da baƙin ciki. AT: "kuka da cizon hakora domin babban baƙin ciki"
Yesu ya cigaba da magana da taron kamar ba za su shiga mulkin sama ba.
"amma kai da kanka ka jefa waje." Wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: "amma Allah zai sa ka da karfi a waje"
Wannan na nufin "daga kowane wuri."
zai za na ko ina a yi magana akan murnan mulkin Allah kamar buki. AT: "zasu yi buki a mulkin Allah"
zama farko na nufin muhimmanci ko grimama. AT: "zama mai muhimmanci ... zama mai muhimmanci na karshe" ko "Allah zai grimama ... Allah zai kunyatar"
"anjima bayan Yesu ya gama magana"
juya wannan kamar gargaɗi ne wa Yesu. suna bashi shawara ya tafi wani waje ya zama mara haɗari.
Heridus zai sa mutane su kashe Yesu. AT: "Heridus zai aika mutanen sa su kashe ka"
Yesu yana kiran Heridus yanyawa. yanyawa wata karamin karan daji ne. Ma'ana mai yuwa 1) Heridus ba kurari bane gaba daya 2) Heridusmai sa ruɗewa ne.
"ba kome" ko "duk yadda" ko "duk abinda ya faru"
Shugaban Yahudawa ya nemiya bautawa Allah. amma duk da haka kakan kakanninsu sun kashe annabawan Allah da yawa a Urshelima, kuma Yesu ya san za'a kashe a wurin shima. AT: "
Yesu yayi magana kamar mutanen Urshelima suna jinsa. Yesu ya faɗa haka say biyu domin ya nuna masu yadda yake baƙin ciki da su.
Idan zai zama da mamaki ka yi magana da ƙasar, zaka iya faɗan she dasaukin ganewa cewa Yesu yana magana ne da mutanen ƙasar: "ku mutanen da kuka kashe annabawan kuma kun jefi wanda aka aika maku"
Wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: "wadanda Allah ya aika maku"
"Na so in." Wannan magana ne ba tanbaya bane.
anyi kwatancin mutane kamar 'ya'yan Urshelima." AT: "in tattara mutanen ki" ko "in tattara mutanen Urshelima"
Wannan ya nuna kwatanci yadda kaza ta ke tattara 'ya'yan ta daga lahani ta wurin rufe su da fukafukanta
Wannan annabine yake yin anbci akan wata abun da ya kusan faru. ya nuna cewa Allah ya daina lura da mutanen Urshelima, da haka miyagu zasu iya faɗawa su kore so. Ma'ana mai yuwa1) Allah zai yashe su. AT: "Allah zai yashe ka" ko 2) ƙasan su zai zama ba komai. AT: "za'a yashe gidan ku"
"baza ku gan ni ba sai lokacin yazo da za ku ce" ko "lokacin daza kugan ni za ku ce"
A nan "suna" yana nufin karfi da ikon Ubangiji.
A'a
An bashi taki kuma an kara mashi shekara daya ta yi 'ya'ya; idan ba ta yi ba, za'a sare shi kasa.
Ruhun mugunta rashin karfin daga shaidan ya daura ta.
Domin Yesu ya warkar da ita a ranar Asabar
Yesu ya tunashe shi wai zai kwance dabban shi a ran Asabar, amma yana jin fushi lokacin da Yesu ya sake matan a ran Asabar.
Domin yana fara kamar kwaya, amma zai girma zuwa baban abu da wurare dayawa na zaune.
Ya ce, "Ku yi famar shiga ta kunkuntar kofa, domin dayawa za su nema shiga amma ba za su iya ba.
Za su yi kuka da cizon hakoran su.
Ibrahim, Ishaku, Yakubu, da dukan annabawa, da dayawa dagagabas, yamma, arewa, da kudu
Dole a kashe shi a Urushalima.
Ya yi marmarin ya tattaro su kamar yadda kaza na take tattara 'yan tsakinta.
Sun ki.
Za'a yashe gidan su, kuma ba za su kara gan Yesu ba sai dai sun ce, "Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.
1 Wata ranar Asabaci, ya shiga gidan wani daya daga cikin shugabanin Farisawa domin cin abinci, mutane kuwa suna sa masa idanu. 2 Sai ga wani a gabansa mai ciwon fara. 3 Yesu ya tambaye masanan attaura da Farisawa, "Ya halata a wakar a ranan Asabaci, ko a'a?" 4 Amma suka yi shiru. Yesu kuwa ya kama shi, ya warkar da shi, ya kuma sallame shi. 5 Sai yace masu, "Wanene a cikinku in yana da jaki ko takarkari ya fadi a rijiya ran Asabaci, ba zai fitar da shi nan da nan ba?" 6 Sai suka kasa ba da amsar wadannan abubuwa. 7 Sa'adda Yesu ya lura da yadda wadanda aka gayyato sun zabi mazaunan alfarma, sai ya ba su misali yana ce masu, 8 "Sa'adda wani ya gayyace ka zuwa bikin aure, kada ka zauna a wuri mai daraja, domin yana yiwuwa an gayyaci wani wanda ya fi ka daraja. 9 Sa'adda wanda ya gayyace ku duka biyu ya zo, zai ce maka, 'Ka ba mutumin nan wurinka,' sa'annan a kunyace za ka koma mazauni mafi kaskanci. 10 Amma idan an gayyace ka biki, sai ka je ka zauna a wuri mafi kaskanci, domin idan wanda ya gayyace ka ya zo, yana iya ce maka, 'Aboki, hawo nan mana'. Sannan za ka sami girma kenan a gaban dukan wadanda kuke zaune tare a kan teburi. 11 Duk wanda ya daukaka kansa, za a kaskantar da shi, wanda ya kaskantar da kansa, kuma daukaka shi za a yi". 12 Yesu ya ce wa mutumin da ya gayyace shi, "Idan za ka gayyaci mutum cin abinci ko biki, kada ka gayyaci abokanka, ko 'yan'uwanka, ko danginka, ko makwabtanka masu arziki, kamar yadda suna iya gayyatar ka, sai ya zama an maida maka. 13 Amma idan za ka kira biki sai ka gayyace matalauta, da nakasassu, da guragu, da makafi, 14 za ka kuwa sami albarka da yake ba su da hanyar saka maka. Gama za a saka maka a ranar tashin masu adalci." 15 Da daya daga cikin wadanda ke zama akan teburi da Yesu ya ji wadannan abubuwa, sai ya ce masa, "Albarka ta tabbata ga wanda zai ci abinci a mulkin Allah!" 16 Amma Yesu ya ce masa, "Wani mutum ne ya shirya babban biki ya gayyaci mutane da yawa. 17 Da lokacin biki ya yi, sai ya aiki bawansa ya ce wa wadanda aka gayyata, "Ku zo, duk an shirya kome." 18 Sai dukansu, suka fara kawo dalilai. Na farko ya ce masa, 'Na sayi gona, lalle ne in je in gan ta. Ina rokonka ka dauke mani.' 19 Sai wani ya ce, 'Na sayi shanu garma biyar, ina so in gwada su. Ina ronkan ka, ka dauke mani.' 20 Wani mutum kuma ya ce, 'Na yi aure, don haka ba zan iya zuwa ba.' 21 Da bawan ya zo ya fadi wa maigidansa wadannan abubuwa, sai maigidan yayi fushi, ya ce wa bawansa, jeka da sauri ka bi cikin titunan birni da kwararo-kwararo, ka kawo gajiyayyu, da nakasassu, da makafi, da guragu.' 22 Sai bawan ya ce, 'Maigida, abin da ka umarta an gama, amma har yanzu da sauran wuri." 23 Sai maigidan ya ce wa bawan, 'Jeka, ka bi kwararo-kwararo da hanyoyin karkara, ka rinjayi mutane su shigo, don a cika gidana. 24 Gama ina gaya maku, babu ko daya daga cikin mutanen da na gayyata da farko da zai dandana bikina." 25 Ana nan, taron suna tafiya tare da shi, sai ya juya ya ce masu, 26 "Duk mai zuwa wurina amma bai ki mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa, da 'ya'yansa, da 'yan'uwansa maza da mata ba - I, har da ransa ma, ba zai iya zama almajirina ba. 27 Duk wanda bai dauki gijiyensa ya biyo ni ba, ba zai iya zama almajirina ba. 28 Wanene a cikinku wanda yake niyyar gina bene, da ba zai zauna ya yi lissafin abin da zai kashe ba tun da farko, ko yana da ishashen kudi da zai iya kare aikin? 29 Kada ya zama bayan da ya sa harsashin ginin, ya kasa gamawa, har duk wadanda suka gani su fara yi masa ba'a, 30 su rika cewa, ga mutumin nan ya fara gini amma ya kasa gamawa.' 31 Ko kuwa wanne sarki ne, in za shi je yaki da wani sarki, da ba zai zauna da farko ya yi shawara ya ga ko shi mai jarumawa dubu goma zai iya karawa da dayan sarkin mai jarumawa dubu ashirin ba? 32 In kuwa ba zai iya ba, to tun wancan yana nesa, sai ya aiki wakili ya kuma tambayo sharudan salama. 33 Haka ma, ba wani a cikinku wanda bai rabu da duk abin da ya mallaka ba, da zai iya zama almajirina." 34 "Gishiri abu ne mai kyau, amma idan gishiri ya sane, da me za a dadada shi? 35 Ba shi da wani anfani a kasa, ko ya zama taki. Sai dai a zubar kawai. Duk mai kunnen ji, ya ji."
Ranan Asabaci, Yesu yana gidan Farisawa. Aya 1 ya ba da labarin abin da ya auko.
Wannan ya nuna sabuwar abin da ya auko.
"ka ci" ko "Don cin abinci" burodi abu ne mai muhimmanci a sashin abinci kuma an yi amfani da shi alabarin a masayin abinci.
Suna so gan ko za su iya yima sa shari cewa ya yi waniabin da ba kyau.
Wannan kalmar "ga" yana nuna mana wani sabuwar mutum a labarin. yaren ko zasu iya samun wata hanya ta yin haka.Turanci sun yi amfani da "akwai wani mutum a gaban sa"
ciwon fara kuburin jiki ne wanda ruwa yake kawo wa daga wasu sashin a jiki. wasu yaren zasu samu suna wannan yana yi. AT: "yana shan wahala domin shashin jikin sa kubura da ruwa"
"shin dokan ya yarda mana mu yi warkasuwa a ranan Asabaci, ko ya hana"
Shugabanan ikkilsiyan sun ki su amsa tanbayan Yesu.
"Yuse ya kama shi mutumin wanda yake da ciwon fara"
Yesu ya yi amfani domin yana so su ga ne cewa za su taimake yaron su ko jikin su koda rana Asabaci ne. saboda haka yana da kyau ya warkar da mutane ko da ranan Asabaci ne. AT: "Idan wanin ku yana da yaro ko jaki ... za ku cire shi nan da nan."
sun sani da cewa abin da Yesu yake fadi daidai ne amma ba su so su yarda cewa ya fada daidai. AT: "Ba su da abin da zasu ce"
Yesu ya ci gaba da yiwa bakin magana a gidan farisawan wanda suka gayyace shi ya ci abin ci.
Zai za ma da taimako a gane wadannan mutane, kuma a bayyana wannan a wata siffa. AT: "wadan da shugabanan Farisawan suka gayata su ci abin ci"
"kujera na mutane masu daraja" ko "kujeran mutane masu muhimmanci"
Wannan za'a iya bayyana shi a wata siffa. AT: "Idan wani ya gayyace ka" *Dubi:
Wadannan aukuwa na "kai" mufuradi ne. Yesu yana magana da kungiyan kamar ya na magana da kowane dayan su.
Wannan za'a iya bayyana shi a wata siffa. AT: "domin mai bikin za gayaci wani wanda ya fika muhimmmanci"
Wannan aukuwa na "kai" yana nufin mutane biyu wanda suke son kujeran daraja.
"zaka je kunya da"
"wurn da bai da amfani sosai" ko "wurin mutane da ba su da muhimmanci"
Wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. " idan wani ya gayace ka"
"ka zauna a nan wurin mutane mafi muhimmanci"
Wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: sa'a nan wanda ya gayyaci zai daraja ka"
"wanda yake so ya sami muhimmanci" ko "wanda ya dauki mutum mai muhimmanci"
zai zama mara muhimmanci" ko "za'a bashi wurin mara muhimmanci." Wanna za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: "Allah zai za mar da shi mai kaskanci"
"wanda ya zaba ya zama mara muhimmanci" ko "wanda ya dauki wuri mara muhimmanci"
"zai zama mai muhimmanci" ko2 za'a bashi wuri mafi muhimmanci." Wanna za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: "Allah zai daukaka shi"
"Farisawan da ya gayyace shi zuwa cin abincin"
"kai" mafuradi ne domin Yesu yana magana kai tsaye da Farisi daya gayyace shi.
wannan mai yuwa ba ya nufin cewa kada su gayyaci wadan nan mutane. kamar su gayyaci wadan su ma. AT: "kada ku yi gayyata kawai" ko "kada ku yi gayyata ko da yaushe"
"domin zasu iya"
"gayyace ku bikin cin abincin dare"
Wanna za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: "a wannan hanya zasu biya kui"
zai zama da taimako a kara "har ila yau" tunda wannan bayyanin mai yuwa ba na kowa bane. AT:har ila yau gayyace talaka"
Wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT Alllah za yi maka albarka"
"baza su iya gayyatan ka zuwa biki ba"
Wannan na nufin shari'a na karshe. AT: "idan Allah ya dawo da masu adalci rayuwa"
wannan ya shigar da wani mutum.
Mutumin baya maganar wani takamaimain mutum. AT: "Albarka ya tabbata ga duk wanda" ko "yadda yake da kyau ga kowanne"
Wannan kalman " burodi" yana nufin dukan abinci. AT: "shi wanda zai ci abinci"
Yesu ya fara faɗan wani misali.
Mai karaun ya iya gane cewa mai yuwamutumni yana da yaron gida wanda ya shirya abincin ya kuma gayyaci bakin.
Wannan sashin hanya ne na maganan wani mutum wanda ba a bada yakamaiman abu a kan sa ba.
"gayyaci mutane da yawa" ko "gayyaci baki da yawa"
"A lokacin abincin daren" ko "Idan za'a fara cin abin cin daren"
"a ce may ya sa ba su zo cin abincin daren ba"
Mai karatu ya iya gane da cewa wadan nan mutane sun yi magana kai tsaye da yaron gidan wanda mai gidan ya aika
"don Allah ka ya fe ni" ko "don Allah karbi uzuri na"
an yi amfani da shanu biyar domin aja kayan aikin noma. AT: "shanu 10 suyi aiki a filin"
ka yi amfani da furci na halitta a yaren ku. wasu yaren zasu ce "yin aure" ko "taukan mata."
"yaji haushi da mutanen da ya gayyata"
"ku kawo su anan su ci abin cin dare"
Zai zama dole ka fada ba shakka ka bayyana cewa yaron gidan ya yi yadda maigidan ya fada mishi yayi. AT: "da yaron gidan ya je yayi abin da aka ce yayi, ya dawo ya ce"
Wannan za'a iya bayyana shi a wata siffa. AT: "Na yi abin da ka ce inyi"
Wannan ya na nufin hanyoyi da suke wajen gari. AT: "asalin hayoyi garin"
"bukace su su shigo"
Wannan kalman "su" na nufin kowane wanda yaro gidan ya samu. "rinjaye duk wanda ka samu"
saboda mutane su caka gida na"
Wannan kalman "kai" jam'i ne, saboda haka ba 'a sarari yake ba da wanda ake magana.
Wannan kalmar anan "mutane" na nufin na miji da ya baligi" ba mutane gaba daya ba.
Wannan za'a iya bayyana ta a wata siffa. AT: "wadan da na gaya ta"
"zasu ji dadain abincin da na shirya"
A nan "ki" wannan magana ne yadda mutane zasu ƙarancin son da mutane zasu nuna wa mutane wani daban ban da Yesu. AT: Idan wani ya zo wuri na kuma bai nuna mina kauar da fiye da wanda yake nuna wa uban sa ... bazai iya zama almajire na ba " ko "sai dai kawai mutum ya nuna mini kauna fiye da wanda ya ke dashi wa uban sa ... ba zai iya zama almajire na ba"
Wannan za'a iya fadan ta da fi'ili. AT: "Idan wani yana so ya zama almajiri na, sai ya dauki giciyen sa ya bini"
Yesu baya nufin cewa kowan ne kirsta za'a giciye shi. Romawa su kan sa mutane su dauki giciyan su kafi a giciye su kamar alaman cewa mutum ya mika wuya ga Roma. Wannan misalin ya nuna cewa sun mika wuya ga Allah kuma sun yarda su sha wahala a kowa ce hanya domin su zama almajiren Yesu.
Yesu yayi amfani da tambaya domin ya hakikanta wa mutane cewa su kirga farashin aiki kafin su fara shi. AT: "Idan mutum yana so ya gina hasumiya, ba shakka zai zauna ya ƙudura ko yana da kudin da zai kare aikin."
Wannan zai zama hasumiyan kallo. "dogon gini" ko "dogon dandamali na kallon waje"
Zai zama da amfani a kara bayayni. AT: "Idan bai kirga farashin ba"
"bayan da ya gina tushin" ko "bayan da ya gama wata sashin ginin"
An gani da cewa bai iya ya gama ba domin ba shi da isasshen kudi. Wannan za'a iya bayyana. AT: "ba shi da isasshen kudi da zai gama"
Yesu yayi amfani da wannan kalman domin ya gabatar da wani yana yi yadda mutane za su kirga farashi kamin su yanke shawara.
Yesu yayi amfani da wata tambaya domin ya koya wa taro akan yadda zasu kirga farashi. AT: "kun sani cewa sarki ... za zauna tukun na ya nemi shawara ... mutane."
Ma'a na mai yuwa 1) "yi tunani a hankali" ko 2)"ji shawara ma shawarcinka."
"10,000 ... 20,000"
zai zama da taimako ka kara bayyanai.AT: "Idan ya ga da cewa ba zai iya yaki dayan sarkin ba"
"kalmomin da za su tsayar da yakin" ko "abin da dayan sarkin yake so yayi domin a tsayar da yakin"
Wannan za'a iya fadan ta da fi'ili mai yakani. AT: "sai dai wadan sun ku zasu iya ba da abin da suke da shi za su iya zama almajirai na"
"bar dukan abin da yake da shi"
"gishiri yana da amfani." Yesu yana magana akan wadan da zasu zama almajiren sa.
Yesu yayi amfani da tanbaya domin ya koya wa taron. AT: "bazai zama mai gishiri kuma ba." ko "ba wanda zai sa ya zama mai gishiri kuma."
mutane suna amfani da taki wa lambu ko a fili. gishiri n da bashi da ɗanɗano banzane bai isa ma a hadashi da taki ba. AT: @takin da yake warwase" ko taki"
Wannan za'a iya bayyana shi a wata siffa. AT: "wani zaya wurga shi"
zai za na halitta ga wasu yaren su yi amfani da mutum na biyu "kai" wanda yake da kunne, yaji
Ma'ana mai yuwa1)"kowane" tun da mutane na daidai suna da kunne, ko 2)"duk wanda zai iya gane," wanda yake nufin wanda suke so su ji Allah
"ya ji da kyau" ko "ya kasa kunne da abin da Na fada"
Ya halatta a warkar ran Asabar, ko kuwa?
Sun yi shiru.
Yesu ya tunashe su wai su taimake dan su ko takarkari da ya fadi a rijiya a ran Asabar.
Za'a kaskantar da shi.
Za'a girmama shi.
Za'a saka masu ranar tashin masu adalci.
Sun fara kawo hanzari akan delili da baza su iya zo bikin ba.
Gajiyayyu, musakai, makafi, da guragu.
Dole mutumin ya yi lissafin abin da zai kashe.
Dole su ki iyalin su da rayuwan su, su dauke giciyen sa, ya bi shi, kuma ya bayar da duk abin da yake da shi.
Ana jefa daga nan.
1 To sai duk masu karbar haraji da masu zunubi suna ta zuwa wurin Yesu suna sauraronsa. 2 Dukan Farisawa da Marubuta suna ta gunaguni da junansu, cewa, "Wannan mutum yana karbar masu zunubi, har ma tare suke cin abinci." 3 Yesu ya fadi wannan misali, ya ce, 4 "Idan waninku yana da tumaki dari, sai dayarsu ta bace, wato ba zai bar tasa'in da taran nan a makiyaya, ya bi sawun wadda ta bata gudan nan har sai ya same shi ba? 5 Idan kuwa ya same ta, sai ya dauke ta a kafadarsa yana farin ciki. 6 In ya dawo gida, sai ya kira abokansa da makwabta, yace masu, 'Ku taya ni murna don na samo tunkiyata da ta bata.' 7 Ina gaya maku, haka kuma za a yi farin ciki a sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan masu adalci tassa'in da tara wadanda ba su bukatar tuba. 8 Ko kuwa wacce mace ce, in tana da kudi azurfa guda goma, in ta batar da daya, ba za ta kunna fitila ta share gidan, ta yi ta neman shi har sai ta same shi ba? 9 In kuwa ta same shi sai ta tara kawayenta da makwabtanta, ta ce, 'Ku taya ni farin ciki don na sami kudin nan nawa da ya bace.' 10 Haka nake gaya maku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah idan mai zunubi guda ya tuba." 11 Sai Yesu ya ce, "Akwai wani mutum mai 'ya'ya biyu maza, 12 sai karamin ya ce wa mahaifinsa, 'Baba, bani rabona daga cikin dukiyarka.' Sai mahaifinsa ya raba masu dukiyarsa tsakaninsu. 13 Bayan 'yan kwanaki kadan, sai karamin dan ya tattara duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa wata kasa mai nisa. A can ya batas da kudinsa, yana sayan abubuwan da ba ya bukata, ya kuma batas da kudinsa a wajen masha'a. 14 Bayan da ya batas da duk abin da ya ke da shi, sai aka yi babbar yunwa a kasar, sai ya shiga fatara. 15 Ya je ya mika kansa domin aiki ga wani dan kasar, sai ya aike shi cikin gonakinsa domin ya rika ba aladu abinci. 16 Har yayi marmarin ya ci daga cikin barbashin da aladu suke ci, domin babu wanda yake ba shi wani abu ya ci. 17 Amma da hankalinsa ya dawo, ya ce, 'Barorin mahaifina su nawa ne da suke da abinci isasshe, amma ina nan a nan, ina mutuwa sabili da yunwa! 18 Zan tashi, in tafi gun mahaifina, in ce masa, "Baba, na yi wa sama zunubi, na kuma saba maka. 19 Ban cancanci a kara kira na danka ba; ka mai da ni kamar daya daga cikin barorinka.'" 20 Sai ya tashi, ya taho wurin mahaifinsa. Amma tun yana daga nesa, sai mahaifinsa ya hango shi tausayi ya kama shi, ya ruga a guje, ya rungume shi, ya yi ta sumbatar sa. 21 Dan kuma ya ce masa, 'Baba, na yi wa sama zunubi, na kuma saba maka. Ban isa a kara kira na danka ba.' 22 Amma mahaifinsa ya ce wa bayinsa, 'Ku yi hamzari ku kawo riga mafi kyau, ku yafa masa. Ku sa masa zobe a hanunsa da takalma a kafafunsa. 23 Sa'annan a kawo kiwataccen marakin nan, a yanka. Mu yi buki! 24 Gama da na ya mutu a da, amma yanzu yana a raye. Ya bata a da, amma a yanzu an same shi.' Sai suka fara liyafa. 25 A wannan lokacin, babban dansa yana gona. Da ya kai kusa da gida, ya ji ana kade-kade da raye-raye. 26 Sai ya kira wani bawan gidan, ya tambayi manufar wadannan abubuwa. 27 Bawan ya ce masa, 'Dan'uwanka ne ya dawo gida, mahaifinka kuma ya yanka kiwataccen marakin nan, saboda ya dawo gida lafiya.' 28 Amma dan'uwan ya yi fushi, ya ki ya shiga ciki, mahaifinsa kuwa ya fito, ya roke shi. 29 Amma babban dan ya amsa wa ubansa ya ce, 'Duba, duk yawan shekarun nan da nake bauta maka, ban taba karya umarnin ka ba, duk da haka ba ka taba bani ko dan taure da zan yi shagali tare da abokaina ba, 30 amma da dan nan naka ya zo wanda ya fallasar da dukiyarka a kan karuwai, ka yanka masa kiwataccen marakin nan. 31 Sai mahaifin ya ce masa, 'Dana, ai kullum kana tare da ni, duk abin da yake nawa naka ne. 32 Amma, daidai ne a yi murna da farinciki, don dan'uwan nan naka da ya mutu, amma yanzu yana da rai, da ya bata, amma yanzu an same shi.'"
Bamu san a inda wannan ya faru ba; ya faru randa Yesu yana koyaswa.
Wannan ya ba da almar sabuwar abin da ya auko.
Wannan magana ne domin ya nuna cewa suna da yawa. AT: "masu karban haraji da yawa"
"Wannan mutumin ya bar masu zunubi a gaban sa" ko "Wannan mutumni ya na dangantaka da masu zanubi"
Suna magana akan Yesu.
Wannan kalman" harma" ya nuna cewa harma suna tunanin cewa bai da kyau Yesu ya bar masu zunubi su zo kusa da shi,amma ya fi muni ya ci abinci da su.
A nan "su" anna nufin shugabanen adinin.
Yesu yayi amfani da tabayan domin ya tuna she mutanen cewa idan wani a cikin su ya rasa tunkiya sa, ba shakka za su je su nume shi. AT: "kowane da yan ku ... ba shakka za ku tafi ... sai kun same shi"
tun da misalin ya fara da "waye a cikin ku," wasu yaren zasu fara misalin da mutum na biyu. "Waye a cikin ku, Idan yana da tunkiya dari
"100 ... 99"
Haka ne makiyayi yake daukan tumakin sa. Wannan za'a iya bayyana . AT: " dauke ta a kafadarsa ya kai su gida"
"Idan mai tumakin ya dawo gida" ko "Idan ka dawo gida." ana nufin mai tumakin kamar yadda da ka yi a ayan da ya wuce.
"a wannan hanya" ko "kamar yadda makiyayin da abokan sa da makwabcin sa zasu yi murna"
"kowan ne daya zai yi murna a sama "
Yesu ya yi amfani da gatse yace Farisawan sun yi kuskura su yi tunani cewa ba su bukatan tuba. yaren ka zasu iya samun wata hanya dabam wanda za su iya furta wannan ra'ayi. AT: "mutane tasa'in da tara kamar ka, wanda suke tunani cewa ba su bukatan tuba"
"99"
Yesu ya ci gaba da bada wani misali. akan wata mata mai azurfa 10.
Yesu yayi amfani da tanbaya domin ya tunshe mutanen cewa idan suka rasa kuɗin azurfa su ba shakka zasu neme shi da ƙwazo. AT: "ko wace mata...bashakka zata kunna fitila ... ta nema da ƙwazo sai ta sa me shi."
Wannan yana yin da ba'a gani bane da labari gaskiye akan matan bane. wasu yaren zasu iya samum yadda za su nuna wannan, (Dubi:
"Idan mai zunubi guda ya tuba"
Wannan ya gabatar da wani sabuwar hali a misalin. wasu yaren zasu ce "Akwai wani mutum wanda"
Yaron yana so uban sa ya bashi nan da nan. Yarurukan da suke da siffar ummurni kamar ina som sa nan da nan zasu iya amfani da siffar.
""sashin gadon wanda ka shirya mini in kaba idan ka mutu"
"sakanin yaran sa biyu"
"ya kwashe abubuwan sa" ko "ya sa abubuwan sa a jaka"
"zama baya tunanin abin da zai biyo baya a abin da ya yi" ko "zaman mai wuya"
"rashin ruwa ya fita a gun kuma dukkar ƙasar ba abinci"
"ka rasa abin da kake so" ko "ba sa muwa sosai"
Wannan kalman "shi" yana nufin karamin ɗan.
"karɓa aiki da" ko "ya fara aiki wa"
"mutumin wancan ƙasar"
"ya bawa aladun mutumin abinci"
"yaso so sai ma ya ci." mun gane sosai domin ya na jin yunwa. Wannan za'a iya bayana. AT: "yana jin yunwa sosai har yana murnan ci"
Wannan bawon wake wanda yake yin grima a bayan itacan. AT: " " ko" "
Wannan ƙari na nufin ya gane menene gaskiyan, cewa yayi babban kuskure. AT: "ba shakka ya gane yana yin sa"
Wannan sashin furcin, ba tanbaya bane. AT: "Dukkan barorin mahaifina su nawa ne da suke da abinci isasshe"
Wannan mai yuwa ba maganan ba ne. Wannan karamin ɗan mai yuwa ya na jie yunwa sosai.
Mutanen Yahudawa wani lokaci suna kin fadan wannan kalman " Allah" sai su yi amfani da Wannan kalman "sama" a maimako. AT: " Na yi zunubi ga Allah"
"Ban isa a ci dani ɗanka ba. "Wannan za'a iya bayana shi a wata siffa. AT: "Ban isa a ci dani ɗanka ba
kayi haya na kamar barorinka" ko "kayi haya na sai in zama kamar barorinka." Wannan roƙo na ba ummurni bane. zai iya zama da taimako ka kara don Allah kamar yadda UDB yayi.
sai ya bar ƙasar ya fara tahowa gun ubansa."Wannan kalman "sai" ya ba da alamar abin da ya auko sabo da abin ya faru da farko. aA wannan hali, karamin yaron ya cikin bukata sai ya shirya ya koma gida.
"Amma tun yana daga nesa daga gida" ko " Tun yana daga nesa daga gidan ubansa "
"ya ji tausayin sa" ko "ya so shi daga cikin zuciyar sa"
Wannan uban yayi haka domin ya nuna wa ɗansa cewa ya na kaunar sa kuma ya ji dadi yadda ɗan ya dawo gida. Idan mutane suna tunanin cewa sabo ne ko bai yi kyau wa uban ya rungume shi har ma yayi wa ɗansa sumba, zaka iya sa yadda mutane a yaren ku suke nuna kauna wa yaran su. AT: "ya karbe sa da kauna"
Mutanen Yahudawa wani lokaci suna kin fadan wannan kalman " Allah" sai su yi amfani da Wannan kalman "sama" a maimako. dubi yadda ka juya wanna a [Luka 15:18]
riga mafi kyau a gidan." AT: " ko "tufa mafi kyau"
zobe alama me na iko wanda mutane suke sa wa a hanunsa.
mutane masu kudi a wancan lokacin suna sa takalma. amma daidai na zamani yanzu shi ne "takalma"
marakin karamin saniya ne.mutane suna bawa marakin su abinci domin su yi grima da kyau, idan suna so suyi buki sai su ci marakin. AT: "maraki mafi kyau" ko "karamin dabban da muke ta sa shi yayi ƙiba"
ya bayana cewa suna so a dafa naman za'a iya bayyana. AT: "a yanka a dafa"
Wannan misalin yayi maganar yaron kamar ya mutu. AT: "kamar da na ya mutu a da, amma yanzu yana a raye" ko "na ji kamar da na ya mutu, amma yanzu yana a raye"
Wannan misalin yayi maganar dan yata fi kamar ya bata. AT: "kamar da na ya bata amma yanzu na same shi" ko "da na ya bata amma yanzu ya dawo gida"
ya nuna cewa ya na gona domin ya na aiki a gurin.
Wannan kalman da a ka juya anan kamar "yaron gida" kullum an juya ta kamar "yaro." yana nuna cewa yaron gidan karami ne.
"me yake faruwa"
marakin karamin saniya ne.mutane suna bawa marakin su abinci domin su yi grima da kyau, idan suna so suyi buki sai su ci marakin dubi yadda zaka juya wannan sashin a cikin Luka 15:23. AT: " marakin mafi kyau" ko "karamin dabban da muke ta sa shi yayi ƙiba"
" a yawan shekarun nan"
"Na yi maka matsananciyar aiki mai tauri" ko "Na yi maka aiki mai turi kamar yaron gidan ka"
ban taɓa yimaka rashin biyayya ba ko in karya ummurninka" ko " ko yaushe i na yin biyayya da abin da ka gaya mini in yi"
Karamin akuya kankani ne kuma bai da sada kamar kiwataccen marakin. AT: "koda karamin akuya ne"
"wancan ɗan ka." babban yaron yana nufin ɗan uwan sa domin ya nuna yadda ya ji haushi.
Abinci misali ne na kuɗi. Bayan da wani ya ci abin ci, abin cin kuma bayanan ya zama ba abin da za'a ci. kuɗin da ɗan'uwan sa ya karba babu shi kuma ya zama ba abin da zai kashe. AT: "batar da dukiyan ka" ko "jefar da duk dukiyan ka"
Ma;ana mai yuwa 1) ya yi tunanin cewa yadda ɗan'uwan ya batar da kuɗin sa kinan ko 2) ya yi maganan karuwai kamar sun zuguiguita zunubin ɗan'uwan sa ya aikata a wancan ƙasa mai nisa"
Wannan kalman "shi" na nufin babban ɗan.
Uban yana tunashe babban aɗn cewa wannan ɗan daya dawo ɗan'uwan ka ne
Wannan misalin yayi maganar ɗan'uwan kamar ya mutu. dubi yadda aka juya wannan a [Luka 15:24]
Wannan misali yayi maganar ɗan ya tafi kamar ya bata. dubi yadda za'a juya wannan sashin a [Luka 15:24]
Zai bar sauran casain da tara ya je ya nema tunkiya da ta bata, sai ya kawo, da farin ciki.
Ta yi nacin nemansa har ta same shi, sai ta yi farin ciki da kawayen ta da makwabta.
Akwai farin cikin a gaban mala'ikun Allah
Ba ni dukiya na yanzu wanda zan gada.
Ya batar da kudin da bazzarawa rayuwa.
Ya haya kansa ya ciyad da aladun wani mutum.
Ya hukunta zai je ya kuma furta zunubin sa ma uban, ya kuma tambaya a haya shi kamar daya bawan.
Ya gudu, ya rungume shi, ya kuma sumbatarsa.
Uban ya ba shi tufafi, zobe, da takalma, aka kuma shirya masa biki.
Ya yi fushi kuma ba zai je bikin ba.
Mazon dan ya yi gunaguni wai ya bi dokokin uban, amma ba taba ba shi akuya ya yi biki da abokanen sa ba.
Ya ce, " Da, kullum kana tare da ni, kuma duk abin da ke nawa naka ne."
Domin karamin dan ya bata da, amma yanzun an same shi.
1 Yesu ya kuma ce wa almajiransa, "Akwai wani mai arziki da yake da wakili, sai aka yi karan sa da cewa wannan wakili yana fallasar masa da dukiya. 2 Sai mai arziki ya kira shi ya ce masa, 'Labarin me nake ji game da kai? Kawo lissafin wakilcin ka, don ba za ka sake zama wakili na ba.' 3 Sai wakilin ya ce a ransa, 'Kaka zan yi, da yake maigida na zai karbe wakilci daga hannuna? Gashi, ba ni da karfin noma ina kuwa jin kunya in yi roko. 4 Na san abin da zan yi domin idan an fitar da ni daga wakilcin, mutane su karbe ni a gidajensu. 5 Sai wakilin ya kira kowanne daya da maigidansa ke bi bashi, yace wa na farkon, 'Nawa maigida na yake bin ka?' 6 Ya ce, 'Garwan mai dari.' Sai ya ce masa, 'Ga takardarka, maza ka zauna, ka rubuta hamsin.' 7 Ya kuma ce wa wani, 'Nawa ake binka?' Ya ce, 'Buhu dari na alkama.' Ya ce masa, 'Ga tarkardarka, ka rubuta tamanin.' 8 Sai maigida ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama 'ya'yan zamanin nan a ma'ammalar su da mutanen zamaninsu sun fi 'ya'yan haske wayo. 9 Ina gaya maku ku yi abuta ta dukiya ta rashin gaskiya, saboda idan ya kare, su karbe ku a gidaje masu dauwama. 10 Wanda yake da aminci a karamin abu, mai aminci ne a babban abu, wanda yake marar gaskiya a karamin abu, marar gaskiya ne a babban abu. 11 Idan fa ba ku yi aminci da dukiya mara adalci ba, wa zai amince maku da dukiya ta gaskiya? 12 Idan kuma ba ku yi aminci da kudin wani ba, wa zai ba ku kudin da ke naku? 13 Ba bawan da zai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ki daya, ya so daya ko kuwa ya amince wa dayan, ya raina dayan. Ba za ku iya bauta wa Allah ku kuma bauta wa dukiya ba." 14 Da Farisawa da ke da kaunar kudi suka ji dukan wadannan abubuwa, suka yi masa ba'a. 15 Sai ya ce masu, "Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane, amma Allah ya san zuciyarku. Abin da mutane suke girmamawa kwarai abin kyama ne a gun Allah. 16 Attaura da litattafan annabawa suna nan har zuwan Yahaya. Tun daga lokacin nan ake yin bisharar mulkin Allah, kowa kuma yana kokarin kutsawa zuwa cikinta. 17 Duk da haka, zai fi sauki sama da kasa su shude, da ko digo daya na attaura ya shude. 18 Duk wanda ya saki matansa ya auri wata ya aikata zina, kuma wanda ma ya auri sakakkiya ya aikata zina. 19 Akwai wani mai arziki, mai sa tufafi na alfarma masu tsada yana shagalin sa kowace rana. 20 Aka ajiye wani gajiyayye a kofarsa, mai suna liazaru wanda duk jikinsa miki ne, 21 Shi kuwa yana marmarin ya koshi da barbashin da ke fadowa daga teburin mai arzikin nan har ma karnuka sukan zo suna lasar mikinsa. 22 Ana nan sai gajiyayyen nan ya mutu, malaiku kuma suka dauke shi suka kai shi wurin Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi, 23 yana cikin hades yana shan azaba, sai ya daga kai ya hangi Ibrahim daga nesa, da Li'azaru a kirjinsa. 24 Sai ya yi kira ya ce, 'Baba Ibrahim, ka ji tausayi na, ka aiko Li'azaru ya tsoma dan yatsansa a ruwa ya sanyaya harshena, don azaba nake sha a cikin wannan wuta.' 25 Amma Ibrahim ya ce, 'Yaro, ka tuna fa a zamanka na duniya ka sha duniyarka, ka kuma karba abubuwa masu kyau, amma Li'azaru kuma sai wahala. Amma yanzu dadi ake bashi a nan, kai kuwa kana shan azaba. 26 Banda haka ma, akwai rami mai zurfi, domin wadanda suke son ketarewa zuwa wurinku kada su iya, kada kuma kowa ya ketaro zuwa wurinmu daga can.' 27 Sai mai arziki ya ce, 'To ina rokonka, Baba Ibrahim, ka aike shi zuwa gidan mahaifina - 28 domin ina da 'yan'uwa maza biyar, ya je ya yi masu gargadi kada su ma su zo wurin azaban nan.' 29 Amma Ibrahim ya ce, 'Suna da Musa da annabawa; bari su saurare su.' 30 Sai mai arziki ya amsa, 'A'a, Baba Ibrahim, idan wani daga cikin matattu ya je wurinsu, zasu tuba.' 31 Amma Ibrahim ya ce masa, 'In dai har basu saurari Musa da na annabawa ba, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su rinjayu ba.'"
Yesu ya fara gaya masu wani misali. akan maigida ne da manaja wanda ya ke bin sa kuɗi. wannan dukkan labari daya ne a rana daya kuma ya fara a [Luka 15:13]
Kashi na karshe kai tsaya akan Farisawa ne da marubucin, tagun almajiren Yesu mai yuwa suna cikin taron suna ji.
wannan ya gabatar da wani sabuwar hali a misalin.
Wannan za'a iya bayana a wata siffa. AT: "mutane sun shaida wa mutum mai kuɗin"
"shashancin sarafa arzikin mai kuɗin"
wannan mai kuɖɖin yayi amfani da tsawa wa manajan. AT: "na ji abn dakake yi"
"ka shirya rubutacceyan labari domin ka bawawani kuma" ko "ka shirya rubutaccen labari akan kuɗi na"
manaja yayi wannan tambayan wa kansa, kamar hanya ne na tunawa da abin da zai yi. AT: "ya kamata inyi tunanin abin da zan yi ... aiki"
Wannan na nufin mai kuɗi. manajan ba yaron gida ba ne. AT: "wanda ya bani aiki"
"Bani da karfi sosai da zan yi tonon ƙasa" ko Ba zan iya yin tono ba"
Wannan za'a iya bayana a wata siffa. AT: "idan na rasa aikin wakilci na" ko "idan mai gidana ya kabe aikin wakilci na"
Wannan ya nuna cewa mutane zasu bashi aiki, ko ko wasu abubuwan da zai nema don zama.
"mutane wanda suke da bassshin maigidan sa" ko "mutane wanda suke da abubuwan maigidan sa." a wannan labarin wanda yake bin su bashi sun rike masa mai zaitun da alkama.
"Wanda ake bin sa bashi ya ce ... manajan ya cewa wanda ake bin sa bashi"
wannan kiman 3,000 lita na mai zaitun.
"100 ... 50 ...80"
"Bill" karamin takarda ne wanda yake fadan nawa ake bin ka.
"manajan ya ce wa wani wanda ake bin sa ... wanda ake bin sa ta ce ...manajan ya gaya ma wani ya ce"
zaka iya juya wannan a mudun zamani. AT: "lita ashirin na alkama" ko kwando dubu na alkama"
"rubuta buhu takwas na alkama."zaka iya juya zuwa ga mudun zamani. AT: "rubuta lita dubu gama sha shida" ko "kwando dari takwas"
ayan bai gaya mana yadda maigidan ya koyi aikin manajan.
"yaba" ko "yi magana da kyau akan" ko " yarda da"
ya aikata wayo" ko "yayi abu mai hankali"
wannan ya na nufin manaja marasa aldalci wanda basu damu da Allah ba . AT: "mutanen wannan duniya" ko yan duniya"
A nan " haske" misali ne na abubuwan da ba na Allah ba ne. AT: "mutanen Allah" ko "mutanen allah"
"Ni" na nufin Yesu. Wannan sashin "Na gaya maku" ya nuna alaman labarin da yadda Yesu ya gaya wa mutanen suyi amfani da shi a rayuwan su.
Abin kula anan sine yin aiki da kuɗi domin taimaka wa mutane. AT: "yi abokantaka da mutane tawurin taimaka masu da arzikin duniya"
Ma'ana mai yuwa 1)yesu yayi amfani da da ya kira kuɗi "rashin gaskiya" domin bashe da amfani madawomi. AT: "da yin amfani da kuɗin duniya" ko "Yesu yayi amfani da misali da ya kira kuɗi rashin gaskiya domin mutane wani lokaci suna juya su yi amfani da shi ta hanyan rashin gaskiya. AT: "da yin aiki da kuɗin da ka samu a hanyan rashin gaskiya"
Wannan mai yuwa na nufin 1) Allah a sama,wanda yake jin dadi cewa kana aiki da kuɗi ka taimaki mutane, ko 2)abokan da ka taimaka wa da kuɗi.
Wannan na nufin sama, inda Allah yake zaune.
Mutanen da suke da aminci ...masu aminci ne kuma ...mutanen marar gaskiya marar gaskiya ne kuma." Wannan ya hada da mata.
"mai aminci ko a abubuwa kaɗan" ka tabbata cewa bai yi ka ba ka da aminci sosai ba.
" rashin gaskiya ko ma a abubuwa ɗan kaɗan. "ka tabbata cewa wannan bai yi kamar sau da yawa baka da gaskiya.
Dubi yadda zaka juya wannan a [Luka 16:09]
Yesu yayi amfani da tanbaya domin ya koya wa mutane. AT: "ba wanda zai yarda da kai da arzikin gaskiye." ko ba wanda zai baka arzikin gaskiye kayi wakilin ta."
Wannan yana nufin arzikin na gaskiye, ainihi kodadewa fite da kuɗi.
Yesu ysyi amfani da tanbaya domin ya koya wa mutane. AT: "ba wanda zai baka kuɗi domin kanka."
"yaron gida ba zai"
Ya nuna da cewa ba zai iya bauta wa mai gida dabam dabam a lokaci daya ba"
Wadannan sharaɗi biyu lallai iri daya ne. bambancin kawai shi ne na maigida farko an kishi a sharaɗi na farko, amma maigada na biyu a ki shi a sharaɗi na biyu.
"yaron gidan zai ki"
"ya so daya sosai"
"ko ya raina " ko "yaki dayan"
Wannan yana nufi kamar "ki" a sashin da ya wuce.
Yesu yana ma wasu kungiyan mutane magana, yaren da suke ka jam'i na "kai" zasu iya amfani da shi.
Wannan briki ne a koya suwan Yesu, kamar yadda aya 14 ya gaya mana labarin daga kasa yadda Farisawan suka yi wa yesu ba'a. aya 15,Yesu ya ciga ba da koyasuwa da amsa wa Farisawan.
Wannan kalman ya sa alama matsi a labarin daga kasa.
"wanda suke son samun kuɗi" ko "wanɗan da handaman kuɗi sosai"
"Farisawan sun yi wa Yesu ba'a"
"sai Yesu ya ce wa Farisawan"
"Kun ya kokari kuyi kyau a gaban mutanen"
A nan "zuciya" na nufin begen mutane. AT: Allah ya gane begen ka na gaskiye" ko "Allah ya san muradinka"
wannan za'a iya bayana a wata siffa. AT: "Abubuwan da mutane suke dauka cewa suna da amfani sosai Allah ya ki su"
Wanna yana nufin dukkan maganar Allah Wanda aka rubuta har zuwa wancan lokaci.
wannan yana nufin Yahaya mai baptisma. AT: "Yahaya mai baptisma ya zo"
Wannan za'a iya bayana a wata siffa. AT: "I na koya wa mutane bishara akan mulkin Allah
Wannan yana nufin mutane wadan da suke so so karbe koyasuwan Yesu. AT: Mutane da yawa suna yin duk abubuwan da zasu iya yi domin su shiga cikin ta"
Za'a iya fadan wannan bambancin a umurtan baya. AT: "ko kankanin digo daya na attaura zai dade sosai fiye da yadda sama da ƙasa zai bayana"
"digo" kankanin sashi ne na attaura.ya na nufin wani abune a attaura wanda kamar bashi da amfani, AT: "da ko kankanin bayanin attaura"
"bata2 ko dana bayanuwa"
"duk wanda ya saki matansa" ko "duk mutum da ya saki matansa"
"mai laifin zina ne"
"duk wani mutum da ya mata"
Wannan sashin ya gabatar da wani mutum a labarin Yesu. bai nuna da kyau ko mutum ne na gaskiye komutum ne kawai a labarin da Yesu yake fada domin ya umuta tsini.
"wanda ya sa tufafi mai kyau na lilin da rinan shunayya " ko "wanda ya sa tufafi mai tsada."ranin shunayya da tufafin lilin mai tsada sosai.
"yana jin dadin cin abinci mai tsada kowace rana" ko "yana kashe kuɗi da yawa ya tsaya abin da yake so"
Wannan za'a iya bayana a wata siffa. AT: "mutane sun ajiye wani mai roko mai suna liazaru a kofar sa"
Wannan sashin ya gabatar da wani mutum a labarin Yesu. bai nuna da kyau ko wannan mutum gaskiya ne ko mutum ne kawaia labarin da Yesu yake fada domin ya umurta tsini.
"a kofar gidan mai kuɗin" ko "a hanyan shiga gidan mai dukiyan"
"da miki a duk jikin sa"
"yana marmari da zai ci barbashi abin da ya fadi"
Wannan kalman "sumul" anan an nuna cewa abin da ya bi ya mafi muni fite da abin da aka rigaya an fada akan Liazaru. AT: "karin bayani akan wannan karnuka ma sun zo" ko "mafi muni, karnuka ma sun zo"
Yahudawa suna daukan karnuka kamar dabbobi ne mara tsarki. Liazaru yana ciwo sosai kuma mara ƙarfi ne ya hana karnuka lasan jikin ciwon sa
Wannna sashin anyi amfani da ita domin a sa alam a abin da ya auko a labarin. idan yaren ku suna da hanyan yin haka,zaku iya amfani da ita.
Wannan za'a iya bayana a wata siffa. AT: "malaiku kuma suka dauke shi daga nan"
Wannan ya nuna cewa Ibrahim da Liazaru suna zaune kusa da juna abikin Grika, a rubutun greek na biki. farincikin sama an bayana shi a litafi mai tsarki da ra'ayin biki.
Wannan za'a iya bayana a wata siffa. AT: mutane suka binne shi"
"ya tafi hades, inda yake shan wahala mai ban tsoro"
Wannan kari na nufin " ya kali sama"
"mai kuɗin ya yi kira ya ce" ko "ya yi iho wa Ibrahim"
Ibrahin kakan kakanin Yahudawane har da mai kuɗin.
dan Allah ka ji tausayi na" ko "dan Allah ka ji tausayi na"
"ka aiki liazaru" ko ka gaya wa Liazaru ya zo guna"
wannan don ya nuna kankani abin da ya ke roko. AT: "yana son dan yatsansa"
Ina wahala mai ban tsoro a cinkin wannan wuta" ko "ina shan wahala mai ban tsoro cikin wannan wuta"
mai arzikin daya daga cikin zuriyan Ibrahim ne.
"abubuwa masa kyau" ko "abubuwa masu dadi"
a wata irin hanya karban abubuwan mugunta" ko "a wata hanya karban abubuwan da suka sa shi shan wahala"
wannan ya ba da tabbacen cewa dukkan su sun karbe abu sa'an da suke masu rai a duniya. bawai an ce abin da suka karba daidai bane. AT:" sa'an da ya ke da rai ya karba"
"daidai yake anan" ko murna yake anan"
"wahala"
"kari akan wannan dalili"
Wannan za'a iya bayana a wata siffa. AT: "Allah ya sa katon kwazazzabo tsakanin mu da kai"
mai gangare da zurfi kwarai dakwari mai faɗi" ko "babbab rabuwa" ko " katon kwazazzabo"
"mutanen dasu ke so su ketare bayan kwazazzabo ... kada su iya" ko "idan wani yana so ya ketare ... kada ya iya"
"ka cewa Liazaru ya je gidan mahaifina" ko "don Allah ka aike shi gidan mahaifina"
Wannan na nufin mutanen gidan. AT: "iyali na"
"domin Liazaru ya yi masu gargadi"
"wannan wurin da muke shan azaba" ko "wannan wurin da make shan azaba mai ban tsoro"
Ya nuna cewa Ibrahim yaki ya aiki Liazaru zuwa ga yan'uwan mai kuɗin. Wanna za'a iya bayana . AT: "A'a bazan yi haka ba, domin yan'uwan ka suna da abin da Musa da annabawa suka rubuta da dadewa"
Wannan na nufin rubutun su. AT: "abin da Musa da annbawa suka rubuta"
"yan'uwam ka su saurara ga Musa da annabawa"
Wannan ya bayana yanayin da bai faru ba, amma mai kuɗin yana so ya faru. AT: "idan mutum da ya mutu ya ji wurin su" ko "idan wani wanda ya mutu ya ji ya gargaɗe su"
daga cikin duk wadan da su mutu. wannan furcin ya yi kwatancin duk wanda suka mutu cikin karkashin ƙasa.
A nan "Musa da annabawa" suna nufin abin da suka rubuta. AT: "Idan basu saurari abin da Musa da annabawa suka rubuta ba"
Ibrahim ya bayana abin da zai faru idan yana yin da ba 'a gani ba ya faru. za'a iya bayana a wata siffa. AT: "haka kuma ba wanda ya mutu da zai iya dawo ya basutabbaci" ko "ba za su yarda ba ko da matttace ya gaya masu"
Wannan kalman "daga matattu" yayi maganar duk wanda suka mutu daga karkashin ƙasa. su tashi daga cikin su wato su zama a raye kuma.
Ya ji wai wakilin na fallasarwa da dukiyan mai arzikin.
Ya kira ko wane mabartan mai arzikin ya kuma rage bashin su.
Ya yaba wakilin domin wayon sa.
Ya ce, "Yi abokai, ku da yake aba ce wadda take iya aikata, don sa'ad da ta kare su karbe ku a gidaje masu dawwama."
Mutumin zai yi aminci da dayawa.
Dole mu zabi tsakanin Allah ko arziki.
Akwai Doka anabawan.
Yanzu ana wa'azin bisharan mulkin Allah.
Mutum din mazinaci ne.
Malai'ku sun dauke Marokin Li'azaru zuwa gefen Ibrahim.
Ya sha azaba a cikin hades.
Ya ce, "Ka ji tausayi na ka aiko Li'azaru ya zo ya kawo mani ruwa kadan domin azaba nake sha a cikin wanan wuta"
Ya ce, "Akwai baban rami tsakanin mu, ba wanda zai iya tsaleke."
Ya ce, "Ina rokan ka ka aika Li'azaru zuwa 'yanwani na ya gargadi su akan wanan wuri."
Ya ce, "Suna da Musa da kuma anabawa; su saurare su."
Ba za su ji lallashi ba ko da wani ya tashi daga mattatu.
1 Sai Yesu ya ce wa almajiransa, 'Babu shakka akwai sanadodin tuntube da za su sa mu yin zunubi amma kaiton wanda shine sanadin su! 2 Zai gwammaci a rataya masa dutsen nika a wuyansa, a jefar da shi a cikin teku fiye da wanda zai zama sanadiyar tuntube ga wadannan kananan. 3 Ku kula da kanku. Idan dan'uwanka ya yi laifi, ka tsauta masa, in kuwa ya tuba ka yafe masa. 4 Idan ya yi maka laifi sau bakwai a rana daya sa'annan ya juyo wurinka sau bakwai ya ce, 'Na tuba,' ya wajabta ka yafe masa!" 5 Sai Manzannin suka ce wa Ubangiji, 'Ka kara mana bangaskiya.' 6 Ubangiji kuwa ya ce, "In kuna da bangaskiya kamar kwayar mastad, za ku ce wa wannan durumin, 'Ka tuge, ka kuma dasu a cikin teku,' zai yi biyayya da ku. 7 Amma wanene a cikinku, idan yana da bawa mai yin masa noma ko kiwon tumaki, da zarar ya dawo daga jeji, zai ce masa, 'Maza zo ka zauna ka ci abinci'? 8 Ba zai ce masa, 'Ka shirya mani wani abu domin in ci ka kuma yi damara, ka yi mini hidima har in gama ci da sha. Bayan haka sai ka ci ka sha'? 9 Ba zai yi wa bawan nan godiya ba domin ya yi biyayya da abubuwan da aka umarce shi ya yi, ko zai yi haka? 10 Haka kuma, idan kuka bi duk abin da aka umarce ku, sai ku ce, 'Mu bayi ne marasa amfani. Mun dai yi abin da yake wajibi ne kurum.'" 11 Wata rana yana tafiya zuwa Urushalima, sai ya bi iyakar kasar Samariya da Galili. 12 Yayin da yana shiga wani kauye kenan, sai wadansu kutare maza guda goma suka tarye shi suna tsaye daga nesa da shi 13 sai suka daga murya suka ce, "Yesu, Ubangiji, ka yi mana jinkai." 14 Da ya gan su, ya ce masu, "Ku je ku nuna kanku a wurin firistoci." Ya zama sa'adda suke tafiya, sai suka tsarkaka. 15 Daya daga cikinsu da ya ga an warkar da shi, ya koma, yana ta daukaka Allah da murya mai karfi. 16 Ya fadi a gaban Yesu, yana masa godiya. Shi kuwa Basamariye ne. 17 Yesu ya amsa ya ce, "Ba goma ne aka tsarkake ba? Ina sauran taran? 18 Babu wani da ya dawo ya girmama Allah sai wannan bakon kadai?" 19 Sai ya ce masa, "Tashi, kayi tafiyarka. Bangaskiyarka ta warkar da kai." 20 Da Farisawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai bayyana, Yesu ya amsa masu ya ce, "Mulkin Allah ba lura ake yi da shi ba. 21 Ba kuwa za a ce, 'Gashi nan!' Ko kuwa, 'Ga shi can ba!' domin mulkin Allah yana tsaknaninku." 22 Yesu ya ce wa almajiran, "Kwanaki na zuwa da za ku yi begen ganin rana daya cikin ranakun Dan Mutum, amma ba zaku gani ba. 23 Za su ce maku, 'Duba can! 'Duba nan!' Amma kada ku je kuna dubawa, ko kuwa ku bi su. 24 Kamar yadda walkiya take haskakawa daga wannan bangaren sararin sama zuwa wancan bangaren, haka ma dan mutum zai zama a ranar bayyanuwarsa. 25 Amma lalle sai ya sha wahaloli dabam dabam tukuna, mutanen zamanin nan kuma su ki shi. 26 Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka kuma zai faru a lokacin bayyanar Dan Mutum. 27 Ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har zuwa ga ranar da Nuhu ya shiga jirgi - ruwan tufana kuma ya zo, ya hallaka su duka. 28 Haka ma aka yi a zamanin Lutu, ana ci, ana sha, ana saye, ana sayarwa, ana shuke-shuke da gine-gine. 29 Amma a ranar da Lutu, ya fita daga Saduma, aka zubo wuta da kibiritu daga sama, aka hallaka su duka. 30 Haka kuma zai zama a ranar bayyanuwar Dan Mutum. 31 A ranar nan fa, wanda yake kan soro kada ya sauka domin daukan kayansa daga cikin gida. Haka kuma wanda yake gona kada ya dawo. 32 Ku tuna fa da matar Lutu. 33 Duk mai son ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai same shi. 34 Ina gaya maku, a wannan dare za a sami mutum biyu a gado daya. Za a dauka daya, a kuma bar dayan. 35 Za a sami mata biyu suna nika tare. Za a dauka daya a bar daya." 36[1]37 Sai suka tambaye shi, "Ina, Ubangiji?" Sai ya ce masu, "Duk in da gangar jiki yake, a nan ungulai sukan taru."
Yesu ya cigaba da koyasuwa, amma ya sa hankalin sa a kan almajiren sa. wannan labarin daya ne kuma ya fara rana daya a cikin Luka 15:3.
"Abubuwan dasu ke riya wa mutane suyi zunubi ba shakka ya na faruwa"
ga duk wanda zai sa gwaji ya zo" ko "ga duk mutumin da zai sa mutane cikin gwaji"
wannan ya gabatar da yana yin da ba'a gani ba. yana nufin cewa horon mutum da ya wasu tun tube zai zama da tsanani da su mutu a cikin teku.
Wannan za'a iya bayan aa wata siffa. AT: "gwammaci a rataya masa dutsen nika a wuyansa, a jefar da shi" ko "ko wani zai rataye masa dutse mai nauyi a wuyan sa a jefa shi"
Wannan ajili na nufin maza tare da mata.
Wannan babba ne sosai. dutsen madauwari mai nauyi wanda ake amfani dashi domin nikan alkama gairn zuwa garin alkama. AT: "dutse mai nauyi"
Wannan anan ana nfin mutune wanda bangaskiyan su har yanzu mara ƙarfi ne. AT: "wannan mutunen wanda bangaskiyan su kanana ne"
Wannan na nufin zunubin da ba na gangan ci ba ne. AT: "yi zunubi"
Wannan bayanin na da sharaɗi kuma na magana akan abin da mai yuwa zai iya faruwa a nan gaba.
"dan'uwa" anan an yi amfani da hankalin wani wanda ku ke da yarda da. AT: "maibi
"gaya masa sosai cewa abin da ya yi bai da kyau" ko "gyara shi"
Wannan yana yin da ba a gani ba ne. ba zai taba faru ba, amma ko da ya faru, Yesu ya gaya wa mutane su yafe.
Wannan lamba bakwai a litafi mai tsarki sananniyar alama ce na cikawa. AT: "sau dayawa a rana, da kowanne lokaci"
Wannan da gajeran fashi ne a koyasuwan Yesu sa'anda almajeran sa suke yi masa magana. sai Yesu ya cigaba da koyasuwa.
"Ɗan Allah kara ma bangaskiya" ko "Ɗan Allah kara mana bangaskiya akan bangaskiyan mu"
kwayar mastad dan kankanin iri ne. Yesu ya nuna cewa basu da ko ɗan bangaskiya. AT: "Idon kuna da bangaskiya ko da karami ne kamar kwayar mastad,, ku" ko "Bangaskiyar ku bai yi babba kamar kwayar mustad ba - amma aidan ku, ne
Idon ba' a gane irin wannan itacen ba, zai zama da taimako a fada wani iri dabam. AT: "itacen ɓaure" ko "itace"
AT: "ka tuge kanka ka kuma dasa kanka a cikin teku" ko "ka cire gigiyan ka a ƙasa ka sa shi a cikin babban teku"
"itacen zai yi maka biyayya." wannan sakamakon na da sharaɗi. zai iya faru idan su na da bangaskiya ne kawai.
Yesu ya tambaye almajeransa domin ya taimake su su yi tunani akan ayukan yaron gida. Wannan zai iya juyata kamar bayyani AT: "amma ba ko ɗaya a cikin ku ...barci zai ce ... zauna ka ci abinci"
"bawa mai yi maka noma a gona ko lura da tumakin ka"
Yesu ya yi amfani da tambaya na buyu domin ya bayana wa al'majeren sa yadda ya kama ta su yi wa bawa. AT: "ba shakka zai ce masa ... ce ka sha"
"yi damara, ka yi mini hidima" ko "ka yi shiri da kyau ka lura da ni." mutane suna yin damara da kyau domin idan suna yin aiki kada rigunar su ya hana su yin aiki.
"Bayan haka sai ka yi mini hidima"
Yesu ya yi amfani da tambayan domin ya nuna wa mutane yadda suke yi wa bayi. AT: "Ba zai yi wa bawan nan godiya ba ... umarce."
AT: "abubuwan da aka umarce shi ya yi"
"daidai" ko "wannan ba gaskiya bane?"
Yesu yana magana da al'majeren sa, yaren da suke da jam'i na "kai" su yi amfani da shi. i:
AT: "da cewa Allah ya umurce ka"
Wannan kwatance ne ya bayana da cewa basu yi abin kirki da za'a yabe su ba. AT: "Mu bayi ne na gama gari" ko Mu bayin ba mu cencenci yabon ka ba"
Wannan sashin an yi amfani da ita domin a sa alamar a sabuwar abin da ya auko. Idan yaren ku na da wata hanya na yin wannan, sai su yi amfani da ita anan.
"da Yesu da al'majeren sa su na tafiya zuwa Urushalima"
Wannan shashin ba'a gane ainihin kauye ba.
AT: "maza goma kutare sun hadu da shi" ko "maza goma wanda suke da kuturta sun hadu da shi"
Wannan motsin jiki da ke nuna abin da ke zuciya mai ladabi domin ba'a barin kutare su zo kusa da mutane.
Wannan kari "a tada murya wani" na nufin a yi magana da ƙarfi. AT: "sun yi kira da murya mai ƙarfi" ko "sun kira da ƙarfi"
Takamenmen tambayan su su warke ne. AT: "Dom Allah ka yi mana jinkai ka warkar da mu"
Kutare suna so su nuna wa firistoci cewa sun warke da ga ciwon kukurta. AT: "ku nuna kanku wa firistoci domin su gwada ku"
Idon mutane sun warke, ba su da tsabta kamar wadan da su ka je biki. Wannan za'a iya bayyana. AT: "sun warke da ga ciwon kuturtan su sai sun zama da tsabta" ko "an warkar da su ga da ciwon kuturta"
"ya gane da cewa ya warke" ko "ya gane cewa Yesu ya warkar da shi"
"ya koma gun Yesu"
"ya daukaka Allah da ƙarfi"
ya durkusa ya sa fuskar sa kusa da kafafun Yesu"ya yi haka domin ya ɗaukaka Yesu
Yesu ya amsa game da abin da mutumin ya yi, amma ya na magana da taron jama'a da suke gun sa. AT: "Yesu ya cewa taron"
Yesu ya amfani da tambayan da bai damu da amsa ba na farko cikin uku domin ya nuna wa mutanen da ke kewaye da shi yadda ya ji mamaki da abin sa cizon yatsa da cewa mutun ɗaya ne cikin goma ya dawo ya ɗaukaka Allah. AT: "maza goma aka warkar" ko "Allah ya warkar da maza goma."
"Mai ya sa sauran taran ba su dawo ba?" AT: "sauran taran ma ya kama ta su dawo, suma."
AT: "Babu wani amma wannan bakon ya dawo ya ɗaukaka Allah!" ko "Allah ya warkar da maza goma, amma wannan bakon ne kawai ya dawo ya ɗaukaka Allah!"
Basamariyan bai da- kakan Yahudawa kuma basu bautawa Allah kamar yadda Yahudawa ke yi.
"Domin bangaskiyarka ka warke." Wannan ra'ayi "bangaskiya" za'a iya furta ta da jam'i "yarda." AT: "Domin ka yarda, ka warke kuma"
Wannan farkon. sabuwar abin da ya auko ne wasu juyin sun fara ta da "Wata rana" ko "sau ɗaya" AT: "Wata rana Farisawa suka tambaye Yesu, "Wane lokaci ne mulkin Allah zai bayyana?"
Mutane na tunanin cewa za su iya ganin wata alama zuwan mulkin. ra'ayin alama za'a iya faɗan ta ba shakka. AT: "Mulkin Allah ba ya zuwa da alama da mutane za su lura da shi"
Ra'ayin isimi nan "masarauta" za'a iya furta da fi'ili " mulki." AT: "Allah ya yi mulki a tsakanin ku"
Ra'yin kwanaki kwanaki masu zuwa na nufin zama jim kaɗan. AT: "Lokaci na zuwa da za ku" ko "Jim ka ɗan"
"za ku so ku gani sosai" ko "za ku so ku ji"
Wannan na nfin mulkin Allah. AT: " ɗaya cikin ranakun da Dan Mutum zai yi malki kamar sarki"
Yesu ya na magana a kansa.
"ba za ka ji shi ba"
Wannan na nufin neman mai ceto. AT: "Dubi nan ga Mai ceton! Ga shi a nan!"
Dalilin zuwa waje za'a iya faɗan ta ba shakka. AT: "ka da ka bi su ka na dubawa"
Zuwan Dan Mutun zai zama mai saukin ganewa da ba zato, kamar yadda da walkiya take bayanuwa. AT: "kamar yadda kowa ya ke ganin walkiya idan ya bayana da" ko "kamar yadda walkiya take bayana ba zato"
Wanna na nufin malkin Allah na nan găba. AT: "zai zama kamar wancan ranar ran da Dan Mutum zai zo ya yi mulki"
"Amma da farko dole ne Dan Mutum ya sha wahala. "Yesu ya na magana a kan sa a masa yin mutum na uku.
AT: "dole mutanen zamanin nan kuma su ki shi"
"Kamar yadda mutane suke yin abubuwa ... haka kuma mutane za su cigaba da yin irin abubuwan"
"zamanin Nuhu" na nufin lokacin da Nuhu ya na a raye kamin Allah ya hukunta mutanen duniya. AT: "lokacin da Nuhu yake a raye"
"zamanin Dan Mutum" na nufin ƙayadadden lokacin kamin Dan Mutum ya zo. AT: "lokacin kamin Dan Mutum ya yi kusan zuwa"
Mutane su na yin abubuwa na gama gari. ba su sani ko su damu cewa Allah ya kusan sharanta su ba.
AT: "iyaye sun bar 'ya'yan su suna auren maza"
"jirgin ruwa" ko "babban kwalekwale"
Wannan kari bai hada da Nuhu da iyalin sa da suke cikin jirgin ba. AT: "hallakar da duka wadan da suke cikin kwalekwalen"
"a zamanin Lutu" na nufin lokaci kamin Allah ya hukun ta birnin sadoma da Gomora. AT: "wani misali shine kamar yadda ya faru a zamanin Lutu" ko "kamar yadda mutane suke yi bayan da Lutu ya mutu"
"mutanen sadoma suna ci suna sha"
"wuta da ƙonannen kibiritu ya na fadowa daga sama kamar ruwa"
"zai zama kamar haka. "AT: "A haka kuma mutane ba za su shirya ba"
AT: " idan Dan Mutum ya bayyana" ko "Idan Dan Mutum ya zo"
Yesu ya na magana a kan sa. AT: "Ni Dan Mutum, na bayyana"
"duk wanda ya ke saman gida kada ya sauko ƙasa" ko "Idan wani ya na saman gidan sa ka da ya sauko ƙasa"
saman gidajen su lebur ne kuma mutane za su iya tafiya ko su zauna akan su.
"dukiyar sa " ko " abubuwan sa"
Kada su dawo gida dauki wani abu. sai su guda da sauri.
"Ku tuna da abin da ya faru da matar Lutu" Wannan gargaɗine. ta dubi baya ta sadoma Allah ya hukunta ta ita kadai da mutanen sadoma. AT: " kada ku yi abin da matar Lutu ta yi"
"Mutanen da suke so su ceci rayuwar su za su rasa shi" ko "duk wanda ya yi kokari ya ceci sohuwar hanyar rayuwan sa zai rasa ransa"
duk"amma mutanen da su ka rasa ransu za su cece shi" ko wanda ya bar hanyar sohuwar rayuwar sa zai ceci ransa
kamar yadda Yesu ya cigaba da yi wa al'majeren sa magana, ya yi nauyi akan muhimmamcin abin da ya ke fada masu.
Wannan na nufin abin da zai faru idan, Dan Mutum ya zo da cikin lokacin dare.
nauyin ba akan mutanen nan biyu ba, amma akan tabbacin cewa za'a ɗauki wasu a bar wasu
"gado" ko "gadon jariri"
Za'a ɗauki mutum ɗaya a bar mutum ɗaya a baya. " Wannan za'a iya bayana ta a wata siffa. AT: "Allah zai aɗuki mutum ɗaya ya bar ɗaya" ko "Mala'iku za su ɗauki ɗaya su bar ɗayan a baya"
Wannan nauyin ba a kan mata biyun nan ba ko ayukan su, amma akan tabbacin cewa za'a ɗauki wasu mutane a bar wasu.
"nikan hatsi tare"
"Ubangiji, a ina wannan zai faru?"
Abayyane, wannan karin magana ne wanda ke nufin "zai zama a fili" ko "za ka sani idan ya faru. "AT: " Idan ungulai sukan taru ya nuna cewa akwai gangar jiki anan haka wadannan abubuwa ya nuna cewa dan Mutum ya na zuwa"
ungulai babban tsuntsaye ne wanda su ke tashi sama tare su kuma ci gagar jikin dabba da suka samu. zaka iya bayyana wannan dabbar kamar haka ko yi amfani da kalmar wata tsuntsu na al'adar wani wuri ka yi wannan.
Dole mu gafarce shi.
Ya kammata mu ce, "Mu bayi ne marasa cancanci; mu na yi abin da ya kamata mu yi kadai."
Ya hadu da kutare goma.
Ya gaya masu su je su nuna kansu a wurin firistoci.
Suka sami tsarkakewa.
Guda daya kawai ya dawo.
Shi daga Samariya.
Mulkin Allah na cikin ku.
Zai zama kamar yadda walkiya take wulgawa, daga wannan sashi sama zuwa wani.
Dole ya sha wahalan abubuwa dayawa a kuma wancan tsara su ki sa.
Dayawa za su ci, sha, yi aure, su siya, su sar, shuka, da kuma yi gini, ba su san wai ranar hallaka ya zo.
Dole kadda mu juye baya mu yi kokarin ajiye rayuwan mu a ranan.
Inda akwai jiki, akwai taruwan angulaye tare.
1 Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a kada kuma su karaya, 2 yace, "A wani gari an yi wani alkali mara tsoron Allah, kuma baya ganin darajan mutane. 3 Akwai wata mace gwauruwa a wannan garin, wadda ta rika zuwa wurinsa, tana ce masa, 'Ka taimake ni yanda zan sami adalci a kan abokin gaba na.' 4 An dade bai so ya taimaka mata, amma daga baya sai ya ce a ransa, 'ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma darajanta mutane, 5 duk da haka saboda gwauruwar nan ta dame ni, zan taimake ta domin ta sami adalci, yadda ba za ta gajiyar da ni da zuwanta wurina ba.'" 6 Sai Ubangiji ya ce, "Ku ji fa abin da alkalin nan marar gaskiya ya fada. 7 A yanzu Allah ba zai biya wa zababbunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne? 8 Ina gaya maku, zai biya masu hakkin su da wuri. Amma sa'adda Dan Mutum ya zo, zai tarar da bangaskiya a duniya?" 9 Ya sake ba da misalin nan ga wadansu masu amincewa da kansu, wai su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane, 10 "Wadansu mutane biyu suka shiga haikali domin yin addu'a - daya Bafarise, dayan kuma mai karbar haraji ne. 11 Sai Bafarisen ya mike, ya yi addu'a a kan wadannan abubuwa game da kansa, 'Allah, na gode maka, da cewa ni ba kamar sauran mutane dake mazambata ba, ko marasa adalci, ko mazinata, ko kamar wannan mai karbar harajin. 12 Duk mako ina azumi sau biyu. Nakan bayar da zakkar dukan abin da na samu.' 13 Amma mai karbar harajin kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya daga kai sama ba, sai dai yana bugun kirjin sa, yana cewa, 'Allah, ka yi mini jinkai, ni mai zunubi.' 14 Ina gaya maku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar dayan ba, domin dukan wanda ya daukaka kansa, za a kaskantar da shi, amma duk wanda kaskantar da kansa kuwa daukaka shi za a yi." 15 Sai mutanen suka kawo masa jariransu, domin ya taba su, da almajiransa suka ga haka, sai suka kwabe su. 16 Amma Yesu ya kira su wurinsa, ya ce, "Ku bar yara kanana su zo wurina, kada ku hana su. Ai mulkin Allah na irin su ne. 17 Gaskiya ina gaya maku, duk wanda bai karbi mulkin Allah kamar karamin yaro ba, lallai ba zai shige shi ba." 18 Wani shugaban jama'a ya tambaye shi ya ce "Malam managarci, me zan yi in gaji rai Madawwami?" 19 Yesu ya ce masa, "Don me ka kira ni managarci? Babu wani managarci sai Allah kadai. 20 Ka dai san dokokin - kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar karya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka." 21 Sai shugaban ya ce, "Dukan wadannan abubuwa na kiyaye su tun a kuruciya ta." 22 Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, "Abu daya ne kadai ya rage maka. Dole ne ka sayar da dukan mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka kuma sami wadata a sama - sa'annan ka zo ka biyoni." 23 Amma da mai arzikin ya ji wadannan abubuwa, sai yayi bakin ciki kwarai, don shi mai arziki ne sosai. 24 Yesu kuwa, da ya ga ransa ya baci, sai ya ce, "Yana da wuya masu dukiya su shiga mulkin Allah! 25 Zai zama da sauki rakumi ya shiga kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah." 26 Wadanda suka ji wannan magana suka ce, "Idan hakane wa zai sami ceto kenan?" 27 Yesu ya amsa, "Abin da ya fi karfin mutum, mai yiwuwa ne a gun Allah." 28 Sai Bitrus ya ce, "To, ga shi mun bar mallakarmu, mun bi ka." 29 Yesu ya ce masu, "Hakika, ina gaya maku, ba wanda zai bar gida, ko matarsa, ko 'yan'uwansa, ko iyayensa, ko kuma 'ya'yansa, saboda mulkin Allah, 30 sa'annan ya kasa samun ninkin ba ninkin a duniyan nan, da rai na har abada a duniya mai zuwa." 31 Bayan da ya tara su goma sha biyun nan, ya ce masu, "Ga shi, muna tafiya zuwa Urushalima, duk abubuwan da aka rubuta game da Dan Mutum ta hannun annabawa zasu tabbata. 32 Gama za a bashe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa miyau. 33 Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma zai tashi." 34 Amma ba su fahimci ko daya daga cikin wadannan abubuwa ba, domin zancen nan a boye yake daga garesu, ba su ma gane abin da aka fada ba. 35 Da ya kusato Yariko, ga wani makaho zaune a gefen hanya, yana bara, 36 da ya ji taro na wucewa, sai ya tambaya ko menene. 37 Suka ce masa Yesu Banazarat ne yake wucewa. 38 Sai makahon ya ta da murya mai karfi, ya ce, "Yesu, Dan Dauda, ka yi mani jinkai." 39 Sai wadanda suke gaba suka kwabe shi, suna gaya masa ya yi shiru. Amma ya kara daga murya kwarai da gaske, yana cewa, "Dan Dauda, ka yi mani jinkai." 40 Sai Yesu ya tsaya, ya umarta a kawo shi wurinsa. Da makahon ya zo kusa, sai Yesu ya tambaye shi, 41 "Me kake so in yi maka?" Ya ce, "Ubangiji, ina so in samu gani." 42 Yesu ya ce masa, "Karbi ganin gari, bangaskiyarka ta warkar da kai." 43 Nan take ya samu gani, ya bi Yesu, yana daukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama'a suka yabi Allah.
Yesuya fara ba da wani misali da ya cigaba da koya wa al'majeren sa. wannan labari ɗaya ne da ya fara a [Luka 17:20]
"Sai Yesu"
za'a fara sabuwar bayyani anan: "karaya. ya ce"
A nan "wani gari" wata hanya ne na gaya wa masu sauraro cewa labarin da ake bada ya faru a wani gari, amma sunar garin da kan ta bai da amfani.
"bai damu da wasu mutane ba"
Yesu ya yi amfani da wannan sashin ya gabatar da wani sabuwar hali a labarin.
gwauruwa mace na wanda maigidan ta ya mutu kuma ba ta sake yin wani aure ba. ma su sauraron Yesu za su iya yin tunani ta kamar wanda bai da wani da zai kula da ita daga wadan da suke so su ma ta illa.
Wannan kalmar "shi" na nufin mai shari'an.
"Kabani mulki mai gaskiya akan"
"abokin gaba na" ko "mutumin da ya ke so ya yi mini illa." Wannan abokan gaba ne a cotun shari'a. ba'a gani ba ko gwauruwa ne ta kai karar mutumin ko mutumin ne ya kai karar gwauruwa.
Wannananan na nufin "mutane" gaba ɗaya.
"addabe ni"
"gajiyar da ni"
"da zuwa guna kullum"
Yesu ya gama ba da misalin yanzu ya na magana akan al'majeren sa,
"yi tunani akan abin da mai shari'an mara gaskiya ya ce." juya wannan a hanyan da mutane za su iya gane cewa Yesu ya riga ya fada abin da mai shari'an ya ce.
Wannan kalmar ya nuna da cewa Yesu ya ga ba da misalin sai ya fara ba da ma'anar sa.
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya koya wa al'majeren sa. AT: "Ba shakka Allah zai kuma ... dare?"
"mutanen da ya zaba"
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya koya wa al'majeren sa. AT: Ba shakka ba zai yi jinkiri a wajen su!"
Yesu ya yi amfani da tambaya domin masu sauraron su dai na tunanin cewaAllah baya yin sauri amsa wa wadan da suka kira bisa sunan sa ga nemam adalci su gane cewa asalin damuwar she ne ba su da bangaskiya na gaskiye cikin Allah. AT: "idan Ɗan Mutun ya zo, ya ka mata ka tabbat cewa zai same ka da gaskiyar bagaskiya a cikin sa." ko "idan Ɗan Mutun ya zo, zai same kadan a duniya wanda sun ba da gaskiya."
Yesu ya na nufin kansa. AT: "Ni, Ɗan Mutum ya zo, zai same ka da gaskiye"
"ga wadansu mutane"
"wanda suka tabbata da kansu cewa su masu adalci ne" ko "wanda suke tunanin cewa su na da adalci"
ki sosai ko ki
"a cikin haikalin
Ma'a nar wanan matani a greka bai fita da saukain ganewa ba. Ma'ana mai yuwa 1) Bafarisen ya mike, ya yi addu'a a kan wadannan abubuwa game da kansa a wannan hanya" ko "Bafarisen ya mike da kansa ya yi addu'a."
ɓarayi mutane ne wanda suke yi wa wasu mutane sata su kwata abubuwan wasu mutane da karfi, ko ta wurin yi masu karari cewa zasu lahani idan sun ki su ba su abin da suka tambaya.
Farisawa sun yarda cewa ma su karban haraji su na da zunubi kamar barayi, mutane marasa adalci, da ma su zina. Wannan za ' iya bayyana. AT: "hakiki ba kamar wannan mai zunubi da karban haraji ba wanda suke cutan mutane"
" komai danake samu"
"tsaye nesa da Farisawan." Wannan alama ne na tawali'u. ko na kirki bai ji cewa ya na kusa da ba Farise ba.
ka " daga idanuwan ka" nanufin cewa ka dubi wana abu. AT: "dubi ta sama" ko "dubi sama"
Wannan furci ne na jiki da babban bakin ciki da nuna tuba da tawali'u. AT: "ya bugun kirjin sa ya nuna bakin ciki"
"Allah, Dao Allah ka yi mini jinkai.ni mai zunubi ne " ko "Allah, dan Allah ka yi mini jinkai ko da shike na yi zunubi da yawa"
Ya zama baratacce Allah ya yafe masa zunubin sa. AT: "Allah ya yafe wa mai karban harajin"
"ba kamar dayan mutumin ba" ko "ba dayan mutumin ba." AT: "ammam Allah bai yafe wa ba Farasen ba"
Da wannan sashin, Yesu ya matsa da ga labarin ya faɗa ƙa'ida da labarin ya ke kwantanta.
AT:"Allah zai kaskantar"
AT: "Allah zai daukaka sosai"
Wannan za'a iya bayyana kamar wata bayani dabam: "taɓa su, amma"
"al'majeran sa suka yi kokari su tsayar da iyayen daga kawo 'ya'ya su gun Yesu"
"Yesu ya gaya wa mutanen su kawo jariransu wurin sa"
Wadan nan bayani guda biyu yana da ma'ana kusan ɗaya an hada su domin a yi nauyi. wa su yaren sukan yi nauyin a hanyoyi dabam dabam. AT: "Hakika ku bar yara kanana su zo wurina"
AT:"na irin mutane ne wadan da suka zamar da kansu kamar yara kanana"
"lallai ina gaya maku." Yesu ys yi amfani da wannan furcin domin ya yi nauyi akan muhimmancin abin da yake so ya faɗa.
Allah ya bukaci mutane su karbi mulkin sa akan su da yarda datawali'u. AT: "Duk wanda ya na so ya shiga mulkin Allah dole ne ya karɓe shi da yarda da tawali'u kamar karamin yaro"
Wannan ya gabatar da wani sabuwar hali a labarin. ya gane shi da masayin sa.
"me ya kamata in yi" ko "me ake bukata a guna"
"karɓe rai da bata karawa." Wannan kalmar "gaji" kullum na nufin dukiya da mutum ya bar wa 'ya'yan sa bayan ya mutu.saboda haka wannan misalin zai iya zama ya gane kansaya zama ɗan Allah kuma yana sa bege ga Allah ya ba shi rai madawami.
Yesu ya yi tambaya domin ya sani cewa shugaban ba zai so amsan Yesu ga shugabanen ba tambaya na aya 18. Yesu bai yi tsammanin shugaban ya amsa tambayan Yesu ba. Yesu ya na so shugaban ya gane cewa amsan Yesu ga shugabanen tambayane daga Allah, waye kadai Allah,sai dai Allah kadai sabada haka ka kira ni managarci shi ne ka hada ni da Allah"
"kada ku yi kisan kai"
"duk wadan nan dokoki"
"Da Yesu ya ji cewa mutumin ya fadi haka"
"ya amsa masa"
"zaka sake yin abu ɗaya" ko "akwai abu ɗaya da har yanzu baka yi ba"
"sayar da duk dukiyan ka" ko "sayar da duk abin da kake da shi"
"ka bada kuɗin wa gajiyayyun mutane"
"wadata a sama" anan na nufin albarkan Allah. AT: "zaka sami albarkan Allah a sama"
"zo ka zama almajiri na"
Wannan maganar motsin rai ne ba tambaya bane. AT:"ya na da wuya sosai ... mulkin Allah.!"
ba zai yu wa rakumi ya shiga ta idon allura ba. mai yuwa Yesu ya yi amfani da alama da nufin cewa zai zama da wuya sosai wa mai kuɗi ya shiga mulkin Allah.
idon allura rami ne a allurar dinki ta inda zare ke wucewa.
"mutanen da su ka ji Yesu ya ce"
ya zamana mai yuwa suna nemam amsa. amma yaza ma kamar sun yi amfani da tanbayan su nuna mamakin su ga abin da Yesu ya ce. AT: "Idan hakane ba wanda zai sami ceto daga zunubi!" ko "wata siffa mai ƙoƙări: "Idan haka Allah ba zai ceci kowa ba!"
"mutane ba za su iya yi ba mai yuwa ne ga Allah ya yi" ko "mutane ba za su iya yi ba Allah zai iya yi"
Wannan sashin na nufin al'majeren ne kawai, kuma ya hada su da shugaba mai kuɗin.
"mun cire zato" ko "mun bari a baya"
duk arzikin mu" ko "duk dukiyan mu"
Yesu ya yi amfani fa furcin domin ya nu na muhimmincin abin da ya ke so ya fada.
Wannan furcin ya so ya hada ba al'majeren kawai ba, duk wani kuma wanda ya so ya yi irin hadayan.
AT: "duk wanda ya bari ... zai samu"
" rai madawami a duniyan mai zuwa"
Yesu ya dauki al'majeren nan goma sha biyu daga gun mutane inda za su zauna su kadai.
Wannan ya nuna sake mai ma'ana a aikin bisharan Yesu da ya tafi Urushalima na karshe.
AT: " da annabawa suka rubuta"
Wannan na nufin annabawa tsohon alkawari.
Yesy ya na magana akan sa kamar " Dan Mutum." AT: "ni Ɗan Mutum,... Ni ...ni ...ni ...Ni"
AT: "zai faru" ko "zai bayana"
AT: "Domin shugaban Yahudawan zai ba da shi ga al'ummai"
AT: "a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa miyau"
Wannan na nufin rana ta uku bayan ya mutu. duk da haka, al'majeren har yanzu ba su gane wannan ba, zai zama da kyau kada ka bayana wannan idan kana juyawannan aya.
"Ba su ko gane waɗannan abubuwan ba"
Wannan na nufin kwatancen Yesu yadda zai sha wahalaya kuma mutu a Urusalima, sa'anan kuma ya tashi da ga mattatu.
Wannan za'a iya bayyana shi a wata siffa amma ba a gane ba ko Allah ne ko kuma Yesu ne ya boye masu wannan kalman. AT: "Yesu ya boye masu wannan sakon" ko "Allah ya hana su gane abin da Yesu yake gaya ma su"
AT: "abubuwan da Yesu ya faɗa"
Wannan sashin an yi amfani da a nan domin a sa alama akan sabuwar sashin labarin.
"akwai wani makaho a zaune. "A nan" "wani" na nufin cewa mutumin na da amfani kuma sabon kasancewa ne a labarin amma Luka bai ambace sunan sa ba. sabon kasancewa ne a labarin.
zai za ma da taimako ka fadi sabuwar bayyani a nan. AT: "bara da ya ji"
"Mutane a cikin taron sun gaya wa makahon"
Yesu ya zo da ga wani gari a nazarat,wanda ake samu a galili
"yake wucewa ya wuce shi"
Wannan kalmar ya sa alama akan abin da ya faru domin wani abun da ya faru a farko.a wannan yana yi, taron sun gaya wa makahon cewa Yesu ya na kan tafiya.
"ya yi kira" ko "ihu"
Yesu daga zuriyan Dauda ne,sarkin Isra'ila mafi duka.
"ji tausayi na" ko "ka ji tausayi na"
"Mutanen da suke tafiya a gaban taron"
"ka yi shiru" ko "kada ka yi ihu"
Wannan zai iya nufin cewa mutumin ya kara daga murya sosai koya kara daga murya da nacewa.
AT: "mutanen su kawu makahon gun Yesu"
"ka iya gani"
Wannan umurni ne, amma Yesu bai umurci mutumin ya yi wani abu ba. Yesu yana warkar da mutumin da umurni. AT: "ba za ka sami ganin gari ba"
Wannan kalmar misali ne. Domin bangaskiyar mutumin ne Yesu ya warkar da shi. AT: "Na warkar da kai domin ka yarda da ni ne"
"ka yi wa Allah daukaka" ko "yabon Allah"
Ya so ya koya masu wai kullum su yi aduwa, kada kuma su karai
Ta tambaya ma adalci daga abokin gaban ta.
Ya ce, " Domin wacenan gwauruwan ta dame ni kuma tana zuwa kullum, zan taimake in ba ta hakin ta."
Ya so ya koya masu cewa Allah zai kawo adalci ma wadanda sun yi kuka masa.
Yana tsammani ya fi sauran mutane adalci.
Bafarisiye da mai karbar haraji sun ke cikin haikali su yi adu'a.
Ya yi adu'a, "Allah, ka ji tausayi na, mai zunubi."
Mai karbar haraji an wajaba a kansa gaban Allah.
Ya na tare da wadanda suna nan kamar yara.
Yesu ya tambaye shi ya sar da duka abin da yake da shi ya kuma rarraba ma matalauta.
Ya zama da bakin cikin musamman, domin shi mai arziki ne sosai.
Yesu ya yi masu alkawari abin da yafi yawa a duniyan nan, kuma rai madawwami a Lahira.
Wai za a bashe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, su bulale shi, a kuma kashe shi, amma a ranar na uku zai tashi kuma.
Ya ce, "Yesu, 'Dan Dauda, ka ji tausayi na."
Sun daukaka da kuma yabi Allah.
1 Yesu ya shiga Yariko ya na wucewa cikinta. 2 Sai ga wani mutum a wurin mai suna Zakka. Shugaba ne na masu karban haraji, kuma mai arziki ne. 3 Yana kokarin ya ga ko wanene Yesu, amma bai iya gani ba sabo da yawan jama'a, domin shi gajere ne. 4 Sai ya ruga gaba ya hau itacen baure domin ya gan shi, saboda Yesu zai wuce ta wannan hanya. 5 Sa'adda Yesu ya zo wurin, ya kalli sama sai ya ce masa, "Zakka, ka sauko da sauri, domin yau dole in sauka a gidanka." 6 Sai ya sauko da sauri, ya karbe shi da farin ciki. 7 Sa'adda dukansu suka ga wannan, sai suka yi gunaguni, cewa, "Ya ziyarci mutum mai zunubi." 8 Zakka ya tsaya ya ce wa Ubangiji, "Duba, Ubangiji, zan ba matalauta rabin arzikina, idan kuma na cuci wani a kome, zan mai da adadinsa sau hudu." 9 Yesu ya ce masa, "Yau ceto ya shigo wannan gida, domin shi ma dan Ibrahim ne. 10 Gama Dan Mutum ya zo ne domin ya nemi, ya kuma ceci batattun mutane." 11 Da suka ji wadannan abubuwan, ya cigaba da magana, sannan ya fada masu wani misali, domin yana kusa da Urushalima, sai suka yi tsamani mulkin Allah za ya bayyana nan da nan. 12 Sai ya ce, "Akwai wani mutum mai sarauta wanda ya tafi wata kasa mai nisa domin ya karba wa kansa mulki sa'annan ya dawo. 13 Sai ya kira bayinsa guda goma, ya ba su fam goma, sai ya ce masu, 'Ku yi kasuwanci da wannan har sai na dawo.' 14 Amma mutanensa suka ki shi sai suka aiki jakadu bayansa, cewa, 'Ba za mu yarda wannan mutum ya yi mulki a kanmu ba.' 15 Anan nan sa'adda ya koma kuma, bayan da ya sami mulkin, sai ya ba da umarni a kira masa bayin da ya basu kudi, domin ya san ribar da suka samu wajen kasuwancin da suka yi. 16 Na farkon ya zo wurinsa, cewa, 'Ubangiji, fam nan na ka ya yi riban fam goma.' 17 Masaraucin ya ce masa, 'Madalla, bawan kirki. Domin ka yi aminci a karamin abu, za a baka iko kan birane goma.' 18 Na biyun ya zo, yana cewa, 'Fam na ka, Ubangiji, ya yi ribar fam biyar.' 19 Sai masarauncin yace masa, 'Ka dauki mulkin birane biyar.' 20 Wani kuma ya zo, yana cewa, 'Ubangiji, ga fam naka da na ajjiye shi da kyau cikin kaya, 21 gama na ji tsoronka, domin kai mutum mai tsanani ne. Kana daukar abu da baka ajiye ba, kana kuma girbin abin da ba ka shuka ba.' 22 Masarauncin ya ce masa, 'Da kalmominka zan shari'antaka, kai mugun bawa. Ka sani cewa ni mutum mai tsanani ne, ina daukan abinda ban ajiye ba, ina kuma girbin abinda ban shuka ba. 23 To don me ba ka kai kudi na wurin masu banki ba, saboda bayan da na dawo zan karbe shi da riba?' 24 Masaraucin ya ce wa wadanda suke a tsaye a wurin, 'Ku karba fam da ke a wurinsa, ku ba mai fam goman nan.' 25 Suka ce masa, 'Ubangiji, yana da fam goma.' 26 'Ina ce maku, duk wanda yake da abu za a kara masa, amma wadda bai da shi, za a karba sauran da ke wurinsa. 27 Amma wadannan abokan gabana, wadanda ba sa so in yi mulki bisansu, a kawo su nan a kashe su a gaba na.' 28 Da ya fadi wadannan abubuwan, sai ya yi gaba, yana tafiya zuwa Urushalima. 29 Ananan sa'adda ya zo kusa da Baitfaji da Baitanya, a kan tudu da a ke kira Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu, cewa, 30 cewa, "Ku tafi cikin kauye da ke gabanku. Sa'adda ku ka shiga, za ku same dan aholaki da ba a taba hawansa ba. Ku kwance sai ku kawo mani shi. 31 Idan wani ya tambaye ku, 'Don me ku ke kwance shi?' Ku ce, 'Ubangiji ne ke bukatarsa." 32 Wadanda aka aike su suka je sun sami aholakin kamar yadda Yesu ya gaya masu. 33 Sa'adda suna kwance aholakin, sai masu shi suka ce masu, "Don me ku ke kwance aholakin?" 34 Suka ce, "Ubangiji yana bukatar sa." 35 Suka kawo wa Yesu, suka shimfida tufafinsu akan aholakin sai suka dora Yesu akansa. 36 Da yana cikin tafiya, suka shimfida tufafinsu akan hanya. 37 Da ya yi kusa da gangaren tudun Zaitun, sai dukan taron almajiransa suka fara yin murna suna kuma yabon Allah da murya mai karfi domin dukan ayukan al'ajibi da suka gani, 38 cewa, "Albarka ta tabbata ga sarki da ke zuwa cikin sunan Uba! Salama a sama da daraja mafi daukaka kuma!" 39 Wadansu Farisawa daga cikin taron jama'a suka ce masa, "Malam, ka tsauta wa almajiranka." 40 Yesu ya amsa ya ce, "Ina gaya maku gaskiya, in wadannan sun yi shiru, duwatsu za su yi shewa." 41 Sa'adda Yesu yana kusatowa, sai ya yi kuka akan birnin, 42 cewa, "Da kun san wannan rana, ko ku ma, abubuwan da ke kawo maku salama! Amma yanzu an boye su daga idanunku. 43 Gama rana zata ta zo a gareki, da makiyan ki zasu gina ganuwa a kewaye da ke, su kuma fada maki daga kowace gefe. 44 Za su sare ki kasa tare da 'ya'yanki. Ba za su bar wani dutse akan dan'uwansa ba, domin ba ki lura da lokacin da Allah ya na kokarin ceton ki ba." 45 Yesu ya shiga Haikalin sai ya fara korar masu sayarwa, 46 ya na ce masu, "A rubuce yake, 'Gida na zai zama wurin addu'a,' amma kun mayar da shi kogon mafasa." 47 Yesu yana nan yana koyarwa kowace rana a cikin haikali. Amma manyan firistoci da marubuta da shugabanin jama'a suna so su kashe shi, 48 amma ba su sami hanyar yin wannan ba, domin mutane suna sauraron sa sosai.
Aya 1-2 zai ba da labarin da ga kasa na abin da ya auko.
Wannan kalmar "duba" ya nuna mana wani sabuwar mutum a labarin. me yuwa yaren ku suna da wa ta hanya na yin haka. AT: "kwai wani mutum wanda ya"
Wannan labari ne da ga kasa akan Zakka.
"Zakka yana ƙoƙari"
"domin shi gajere ne"
Mai walafawar ya ga ma ba da labari daga kasa na abin da ya auko yanzu ya fara kwatanta abin da ya faru da kanta.
"itacen 'ya'yan baure." yana haifan kewayyayen ''ya'ya mai kimanin 2.5 santi mita. AT: " 'ya'yan baure" ko itace"
"itacen" ko "ida Zakka ya ke"
"Zakka ya yi sauri"
Yahudawan sun ki jinin mai karban harajin kuma su yi tunanin cewa kada wani mutum mai kyau ya yi haɗu da su.
"Yesu ya ji gidan mutum mai zunubi ya ziyarci shi"
"mai zunubi a fili" ko "mai zunubi da gaskiye"
Wannan na nufin Yesu.
" zan mai da adadinsa sau hudu fiye da yadda na karba a gun su"
An gane da cewa cat ya na zuwa ne da ga Allah. AT: "Allah ya ceci wannan iyali"
Wannan kalmar "gida" a nan na nufin muttanen da suke zama a wannan gida ka kuma iyali.
"wannan mutumin ma" ko "Zakka kuma"
Ma'ana masu yuwa 1) "zuriyar Ibrahim" 2) "mutum wanda ya na da bangaskiya kamar yadda Ibrshim ya yi."
Yesu ya na magana akan sa. AT: "Ni ne ɗan Mutum, zo"
" mutanen da suka yi gilo daga Allah" ko "wadan da suka yi gilo ta hanyar zunubi da ga Allah"
Yahudawa sun yarda da cewa Mai ceto zai kafa mulkin sa nan da nan idan ya zo Urusalima. AT: "da cewa nan da nan Yesu zai fara yin mulkin bisa mulkin Allah"
Wani mutum wanda shi daya ne da cikin kungiyan masu mulikn" ko "Wani mutum da ga iyali mai muhimmanci"
Wannan hoton karanin sarki ne zuwa ga babban sarki. babban sarkin zai bawa karamin sarkin dama da ika ya yi mulki bisa ga mutanen ƙasar sa.
Yesu ya cigaba da bada misalin ya fara a cikin Luka 19:11(./11.md).
"Mai sarautan ya yi kira." zai zama da amfani ka fada cewa mutumin ya yi kira kamin ya ji ya karɓe mulkin. AT: "kamin ya tafi, ya yi kira"
"bama kowa fam ɗaya"
fam kuwa 600 nauyin sa, mia yuwa na azurfa. kowane fam dai dai ne da kwana 100' hakin da za 'a biya mutane na kusan aikin watani hudu, fam goma zai zama na hakin shekara uku. AT: "ƙerarren kuɗi goma mai amfani" ko "kuɗi mai yawa"
"Yi kasuwanci da wannan kuɗi" ko "Yi amfani da wannan kuɗi domin ka sami wani"
"mutanen ƙasar sa"
"kungiyan mutane domin su ji a madadin su" ko "sakonni ɗaya wa"
Wannan sashin an yi amfani da ita anan domin a sa alama akan abu mai amfani da ya faru a labarin. Idan yaren uk na da wata hanyan in haka sai ku yi amfani da ita anan.
"bayan da ya zama sarki"
AT: "ya zo gun sa"
"kuɗi nawa suka samu"
"Bawa na farko"
"ya zo gaban mai sarautan"
Ya nuna da cewa bawan nan ne ya jawo riban. AT: "Na yi amfani da famna ka na yi riban fam goma kuma"
fam kuwa 600 nauyin sa, mia yuwa na azurfa. kowane fam dai dai ne da kwana 100' hakin da za 'a biya mutane na kusan aikin watani hudu. Dubi yadda zaka juya wannan a [Luka 19:13]
"Ka yi mai kyau. "mai yuwa yaren ku na da sashin da wanda ya ba wani aiki zai yi amfani da shi ya nuna ya karɓe shi, kamar "aiki mai kyau."
Wannan na nufin fam ɗaya wanda mai sarautan ya kalla kamar ba kuɗi mai yawa bane.
"Bawa na biyu"
Ya nuna da cewa bawan nan ne ya jawo riban. AT: "Ubangiji, Na yi amfani da famna ka na yi riban fam biyar kuma"
"Zaka sami iko bisa birane biyar
"wani bawan ya zo"
"ya naɗe a kaya sai ya boye"
"mutum mai sashin baya na jirki" ko "mutum wanda ya na tsammanin da yawa da ga gun bayin sa"
Wannan mai yuwa karin magana ne. mutumin da ya ke dauka wa da ga cikin abin da aka ajiye ko kuma da ga cikin abin da ba komai da bai sa a cikin misali ba ga wani ya ci riba da ga ikin wahala na wa su. AT: "Kana daukar abu da baka ajiye ba" ko "Kana kamar mutun wanda ya ke daukar abin da wa su mutane su ka ajiye"
Wannan mai yuwa karin magana ne. mutum da ya griɓe abincin da wani dabam ya shuka misal ne na wani wanda ya ke cin muriyan aikin wahala da wasu su ka yi. AT: "ka na kamar mutum wanda ya griɓe 'ya'yan itace da wa su mutane suka shuka"
"kalmominka" na nufin duk abin da ya faɗa. AT: "bisa ga abin da ka faɗa"
wannan mai sarautan ya na maimaita abin da bawan ya faɗa akan sa. bai faɗa cewa haka gaskiya bane. AT: "Kace cewa ni mutum ne mai neman hakki"
mai sarautn ya yi amfani da tambaya domin ya kwaɓe mugun bawan. AT: "da ka sa kuɗi na ... riba."
"ara wa banki kuɗi na." Al'adan da ba su da banki za su iya juya shi kamar wani ya karbi aron kuɗi na."
Banki kasuwanci ne da suke ajiye kuɗi da kyau wa mutane. banki sun ara kuɗi wa wasu domin riba. sabo da haka ya biya wata kuɗi, ko riba, wa wadan da suka ajiye kuɗin su a banki.
"da na karba kuɗin da riba" ko " da na sami riba akai"
riba kuɗi ne da banki su ke biyan mutane wanda suka ajiye kuɗin su a banki.
Mai sarautan ya zama sarki. Dubi yadda za ka juya wannan a Luka 19:12.
"mutanen da suka tsaya kusa da su"
"yana da fan goma dama!"
Wannan srakin ne yake magana. wasu masu juyawan za su so su fara da wannan ayan da "sai sarkin ya amsa, Na gaya maka " ko "amma sarkin ya ce Na gaya maka wannan"
Ya nuna cewa abin da ya ke da shi kuɗi ne da ya samu ta wurin amfani da fam na sa da aminci. AT: "duk wanda ya yi amfani da abin da aka ba sa da kyau, zan ba sa kuma" ko "ga duk wanda ya yi amfani da abin da na ba shi da kyau zan ba shi kuma"
Ya nuna da cewa mutumin bai da kuɗi domin bai ya amfani da fam nasa da aminci. AT: "daga mutumin da bai yi aiki da abin da na ba shi da kyau ba"
AT: "zan karba da ga gun sa"
tunda abokan gaba na ba su nan, wa su yaren za so ce "wadancan abokan gaba na."
"Da Yesu ya faɗi wadannan abubuwa"
Urushalima ya na sama da Yariko, daidai ne wa Isra'ilawa su yi maganr tafiya sama zu wa Urushalima
Wannan sashin an yi amfani da ita domin a sa alama akan sabuwar abin da ya auko. Idan yaren ku na da wata hanya na yin haka, za ku iya yin amfani da ita anan.
Wannan kalmar "shi" na nufin Yesu. al'majeren sa su na tafiya tare da shi.
Baitfaji gari ne ɗa
"tudun da ake kira hauwan Zaitun" ko "tudun ana kira dutsen itacen Zaitun"
"karamin jaki" ko "karamin dabban hauwa"
AT: "da ba wanda ya taba hauwansa"
Yesu ya gaya wa al'majeren sa yadda za su amsa tambayan da ba'a riga an tambaye su ba. koda shi ke mutanen da suke a kauyen su yi kusa su yi tambayan.
Faɗan na ciki za a iya juya ta kaman ba faɗan ba na hanya kusu-kusa ba. AT: "Idan wani ya tambaye ku, Don me ku ke kwance shi, Ku ce
AT: "Al'majerai biyu da Yesu ya aika"
"mai aholakin"
"sa rigan sarautan su akan dan aholakin."alkyabba rigunar sarauta ne na waje.
"taimaki Yesu ya hau kan aholakin"
"mutane suka shimfida tufafinsu." Wannan alama ne na ba wani daraja.
" da Yesu ya yi kusa." al'majeren sa su na tafi ya da shi.
" daga ida hanya ya ƙasa daga tudun Zaitun"
"mayan abubuwa da suka gan Yesu ya yi"
su na fadan wannan akan Yesu.
A nan "suna" na nufin iko da ƙarfi.kuma Uangiji na nufin Allah.
"bari a sami salama a sama" ko "Muna so mu gan salama a sama"
"Bari a sami daukaka a sama" ko Wmuna so mu ga daukaka a sama." Wannan kalmar "a sama" na nufin sama, wada shine misalin Allah, wanda yake zaune a sama. AT: "bari kowa ya ba wa Allah daukaka wanda ya ke saman sama"
"a cikin taro mai yawa"
"gaya wa al'majeren kasu daina yin wadannan abubuwan"
Yesu ya fada wannan domin ya yi nauyin akan abin da zai fada nan gaba.
Wannan yana yin da ba 'a gani bane.wasu masu juyawa za su so su bayyana abn da Yesu yake nufi daya ce: "a'a, ba zan kwaɓe su ba,idan wadannan mutane za su yi shiru ... za su yi ihu"
"duwasun za su kira yabo"
Wannan na nufin Urushalima.
Wannan kalmar "ita"na nufin brinin Urushalima, amma ya na wakilcen mutanen da ke zaune cikin brinin.
Yesu ya nuna bakin cikin sa da cewa mutanen Urushalima sun rasa daman zama na salama da Allah.
Wannan kalmar "kai" mafuradi ne domin Yesu ya na magana da brinin. Amma idan wannan zai zama mai saɓa wa dabi'a a yaren ku za ku iya amfani da jam'i na "kai" ku nufa ga mutanen brinin.
"idanuwan ka" na nufin gani. AT: "ba za ka iya ganin su ba"
Me ya biyo bakin cikin Yesu.
Wannan ya nuna da cewa za su faskan ce lokacin wahala. wasu yaren ba su yin maga na akan lokaci "zuwa." AT: "a nan gaba wadannan abubuwan za su faru da ku: abokan gaban ku" ko "ba da ji ma wa ba za ku faskanci lokacin damuwoyi. abokan gaban ku"
Wannan kalmar "ke" mafuradi ne domin Yesu yana magana da brinin kamar yadda zai yi da mace. Amma idan wannan zai saɓa wa dabi'a a yaren ku za ku iya amfani da jam'i na "ke" ku nufa ga mutanen brinin.
Wannan na nufin bamgo da zai tsare mutane daga fitan wajen brinin.
Yesu ya na magana da mutanen brinin kamar ya na magana da brinin da kanta kamar yadda yake magana da mace. ya yi maganar mutanen da suke zama a brinin kamar su matane yarane, haka yaran brinin. a sare brinin shi ne a rushe bangon ta da gigegigenta, a kuma sare 'ya'yan ta wato a kashe wanda suke zaune a cikin ta. AT: "za su rushe ki gaba ɗaya su kuma kashe dukkan wanda suke zaune a cikin ta" ko "za su rushe brinin ki gaba ɗaya su kuma kashe dukkan ku"
"ke ba ki yarda"
za ka iya bayyana cewa ya shiga Urushalima, ida haikalin yake. AT: "Yesu ya shiga Urishalima sai ya je cikin harabar haikalin"
Firistoci ne kawai ake bari su shiga cikin ginin haikalin. AT: "shiga cikin harabar haikalin
"wurga waje" ko "fitar waje da ƙarfi"
Wannan tambayane daga Ishaya. AT: "alittafin yace" ko "Annabi ya rubuta wadannan kalmomin a cikin littafin"
Wannan kalmar "-na" na nufin Allah "gida" kuma na nufin haikali.
"wurin da mutane suke yi mini addu'a"
Yesu ya na maganar haikali kamar wurin da barayi suke haduwa. AT: "wurin da barayi suke boyewa"
"a cikin harabar haikalin" ko "a haikalin"
"sun kasa kunne sosai ga abin da Yesu yake fadi"
Shine Zakka, mai arziki mai karbar haraji.
Sun ce, "Yesu ya je a ziyarce mutum wanda mai zunubi ne."
Ya ce, "Yau ceto ya sauka a gidan na."
Suna tsammani wai mulkin Allah zai bayyana nan da nan.
Zai je kasa mai nisa ya karbi mulki, kuma zai dawo.
Ya ba shi izni a kan birni goma.
Ya bashi izni a kan birni biyar.
Ya tsammani mutum mai daraja mutum mai tsanani ne.
Mutum mai daraja ya sa a kashe su a gaban sa.
Aholaki wanda ba tab hawa ba.
Sun ce, "Albarka ta tabbata ga Sarkin na mai zuwa da suna Ubangiji!"
Ya ce wai duwatsu za su yi kuka.
Ya yi kuma.
Ya ce wai za a tsattsare mutanen kuma ba dutse daya da za bari a kan dan'uwansa.
Manyan firisti da malaman Attaura da shugabannin jama'a suka nema su kashe Yesu.
Domin jama'a suna saurare shi da duk hankalin su.
1 Ana nan wata rana, Yesu yana kan koyarwa a haikali da wa'azin bishara, sai shugaban firistoci da marubuta suka zo wurinsa da dattawa. 2 Suka yi magana, su na ce masa, "Gaya mana da wanne iko ne ka ke yin wadannan abubuwan? Ko wanene ya baka wannan ikon?" 3 Ya amsa sai ya ce masu, "Ni ma zan yi maku tambaya. Gaya mani game 4 da baptisman Yahaya. Daga sama take ko kuwa daga mutane ne?" 5 Sai suka yi mahawara da junansu, suna cewa, "In mun ce, 'Daga sama,' zai ce, 'To don me ba ku ba da gaskiya gareshi ba?' 6 Amma in mun ce, 'Daga mutane ne,' dukan mutane za su jejjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata a ransu Yahaya annabi ne." 7 Sai suka amsa cewa ba su san ko daga ina ne take ba. 8 Yesu yace masu, "To haka ni ma ba zan gaya maku ko da wanne iko nake yin wadannan abubuwan ba." 9 Ya gaya wa mutane wannan misali, "Wani mutum ya dasa gonar inabi, ya ba wadansu manoma jinginarta, sai ya tafi wata kasa har ya dade. 10 Da lokacin girbi ya yi sai ya aiki wani bawansa zuwa wurin manoman, saboda su bashi daga cikin anfanin gonar. Amma manoman suka doke shi, sai suka kore shi hannu wofi. 11 Ya aike wani bawa kuma sai suka daddoke shi, suka kunyatar da shi, suka kore shi hannu wofi. 12 Ya kuma sake aike na uku suka yi masa rauni, suka jefar da shi a waje. 13 Sai mai gonar inabin ya ce, 'Me zan yi? Zan aiki kaunattacen dana. Watakila zasu ba shi daraja.' 14 Amma sa'adda manoman suka gan shi, suka yi shawara a tsakaninsu, cewa, 'Wannan ne magajin. Bari mu kashe shi, saboda gadon ya zama namu.' 15 Suka jefar da shi waje daga gonar, suka kashe shi. Menene ubangijin gonar inabin zai yi da su? 16 Zai zo ya halakar da wadannan manoma, sai ya ba wadansu gonar." Da suka ji wannan, suka ce, "Allah ya sawake!" 17 Amma Yesu ya kalle su, sai yace, "Menene ma'anar wannan nassi? 'Dutsen da magina suka ki, an mayar da shi kan kusurwa'? 18 Duk wanda ya fadi kan dutsen zai farfashe. Amma duk wanda dutsen ya fadi a kansa, zai rugurguza shi." 19 Sai marubutan da manyan firistocin suka so su kama shi a wannan sa'a, domin sun sani ya yi wannan misali a kansu ne. Amma sun ji tsoron mutane. 20 Suna fakonsa, suka aiki magewaya, wadanda suke kamar masu adalci, saboda su sami kuskure cikin maganarsa, don su mika shi ga hukumci da kuma ikon gwamna. 21 Suka tambaye shi, cewa, "Malam, mun sani da cewa kana fada da koyar da abin ke daidai, kuma ba wanda yake cusa maka ra'ayi, amma kana koyar da gaskiya game da hanyar Allah. 22 Wai shin doka ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?" 23 Amma Yesu ya gane makircinsu, sai ya ce masu, 24 "Nuna mani dinari. Sifar wanene da kuma rubutun wanene akan sa?" Suka ce, "Na Kaisar ne." 25 Sai ya ce masu, "To sai ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar, ku kuma ba Allah, abin da ke na Allah." 26 Marubutan da manyan firistocin ba su sami abin zargi cikin maganarsa, a gaban mutane ba. Suka yi mamakin amsar sa, ba su kuma ce komai ba. 27 Sa'adda wadansu Sadukiyawa suka zo wurinsa, wadan da suka ce babu tashin mattatu, 28 suka tambaye shi, cewa, "Malam, Musa ya rubuta mana cewa idan dan'uwan mutum ya mutu, mai mace kuma ba shi da yaro, sai dan'uwansa ya auri matar, ya samar wa dan'uwansa yaro. 29 Akwai 'yan'uwa guda bakwai kuma na farin ya yi aure, sai ya mutu babu da, 30 haka ma na biyun. 31 Na ukun ya aure ta, haka nan na bakwai ma bai bar yaya ba, har suka mutu. 32 Daga baya sai matar ma ta mutu. 33 To a ranar tashin mattatu, matar wa za ta zama? Domin duka bakwai din sun aure ta." 34 Yesu ya ce masu, "'Ya'yan duniyan nan suna aure, ana kuma ba da su ga aure. 35 Amma wadanda aka ga cancantarsu a waccan tsara, sun isa su sami tashin mattatu, ba za suyi aure ko a aurar da su ba. 36 Gama ba za su mutu kuma ba, domin suna daidai da mala'iku kuma su 'ya'yan Allah ne, da shike su 'ya'yan tashin matattu ne. 37 Amma batun tashi matattu, ko Musa ma ya nuna wannan, a cikin jeji, inda ya kira Ubangiji, Allah na Ibrahim da kuma Allah na Ishaku da Allah na Yakubu. 38 Yanzu shi ba Allahn matattu ba ne, amma na masu rai, saboda duka suna raye a wurinsa." 39 Wadansu marubuta suka amsa, "Malam, ka amsa da kyau." 40 Gama ba su sake yi masa wadansu tambayoyi ba. 41 Yesu ya ce masu, "Yaya suke cewa Almasihu dan Dauda ne? 42 Gama Dauda da kansa ya ce a cikin littafin Zabura, Ubangiji ya ce wa Ubangiji na, 'Zauna a hannun dama na, 43 sai na maida makiyanka a karkashin tafin sawunka.' 44 Dauda ya kira Kristi 'Ubangiji', to ta yaya ya zama dan Dauda?" 45 Dukan mutane suna ji ya ce wa almajiransa, 46 "Ku yi hankali da marubuta, wadanda suna son tafiya da manyan riguna, suna kuma son a gaishe su a cikin kasuwanni, da mayan wuraren zama a cikin majami'u, da kuma manyan wurare a wurin bukukkuwa. 47 Suna kuma kwace wa gwamraye gidaje, suna kuma badda kama ta wurin yin doguwar addu'a. Wadannan za su sha hukumci mai girma."
sai shugaban firistoci da marubuta da dattawa suka yiwa Yesu tambaya a haikali.
Wannan sashin an yi amfani da ita anan domin a sa alama a wata sabuwar sashin labarin.
"a cikin harabar haikalin" ko "a haikalin"
Yesu ya amsa wa shugaban firistoci, marubuta da dattawa.
"Yesu ya amsa"
Wannan kalmar "Ni ma ... zan yi maku tambaya" bayyani ne. Wannan kalmar "ku gaya mini" ummurni ne.
Yesu ya sani cewa iko yahaya ya zo daga sama ne, baya tambaya saboda bayayni. ya yi tambayan saboda shugabanen Yahudawa su gaya wa masu sauraron abin da suke tunani.wannan tambayan ba ya bukatan amnsa amma mai yuwa za ka iya juya shi kamar tambaya. AT: "ku na tunanin cewa ikon Yahaya ya yi wa mutane baftisma ya zo daga sama ne ko daga mutane" ko "Allah ne ya cewa Yahaya ya yi wa mutane baftisma, mutane ne suka ci masa ya yi"
"daga Allah." Mutanen Yahudawa ba su Allah da sunan sa " "kowa ne lokaci su na amfani da "sama" a mai mako shi.
" Sun yi batun" ko "Sun duba amsan su"
"asakanin su" ko "da kowanne ɗayan su"
Wa su yaren za su so su yi amfani da faɖi. AT: "Idan na ce ikon Yahaya daga sama ne, shi"
"Yesu zai ce"
Wa su yaren za su so su yi amfani da faɖi. AT: "Idan na ce ikon Yahaya daga mutane ne,"
"kashe mu da jefan mu da duwatsu." shari'an Allah ya yi umurtan cewa mutanen sa su na jefin wadan can mutanen sa wanda suke yi ma sa ba'a ko annabawan sa.
"sai shugaban firistoci, marubutan, da dattawan." Wannan kalmar "sai" ya sa alama akan wani abu da ya faru domin wani abun da ya faru da farko. a wannan hali, sun yi mahawara da kansu a cikin Luka 20:5-6, kuma ba su samu amsan da suke so su fada ba.
AT: "sun ce, ' ba mu san inda ya fito ba."'
"daga ina baftisman Yahaya ya fito." AT: "daga ina ikon Yahaya ya yi wa mutane baftisma ya fito" ko "wa ya bawa Yahaya iko ya yi wa mutane baftisma"
"Ni ma ba zan gaya maku ba." Yesu ya sani cewa ba su so su gaya masa amsan, sai ya amsa masu a irin yana yin, AT: "kamar yadda ba za ku gaya mini ba ni ma ba zan gaya maku ba"
"Ya bar wasu masu manoman itacen inabi su yi aiki da shi domin furfura da kuɗi" ko "Ya bar wasu masu manoman itacen inabi su yi aiki da shi su biya shi anjima." biyan zai zama ko da kuɗi ko kuma da amfanin gona.
Wadannnan mutane ne wadan da suke yin kiwon itacen inabi su grimar da inabin. AT: "manoman inabi"
"lokacin dasuka yarda zasu biya shi." Wannan zai zama lokacin gribi.
"waɗan su inabin" ko "waɗan su abin da suka haifar a gonar inabin." zai iya zama abin da suka samu daga inabin ko kuɗin da suka samu da suka siyar da inabin.
Hanun wofi misali ne na "ba komai." AT: "suka kore shi ba biyan shi" ko "suka kore shi ba inabin"
"daddoke wancan bawan "
"wulakanta shi"
"harma bawa na uku" ko "wanu bawa kuma." Wannan kalmar "tukunna" ya ɗan ambata wani tabbatcan abu da cewa mai gonar bai kamata ba ya aike bawa na biyu ba, amma ya je har ya aiki bawa na uku.
"jima wancan bawan ciwo"
" jefar da shi a wajen gonar inabin"
Wannan tambayan ya yi nauyin cewa mai gonar inabin ya yi tunani a hankali akan abin da zai yi. AT: "ga abin da zai yi:"
"sa'adda manoman suka ga ɗan shi"
Bawai suna tambayan izni bane.Sun fada haka domin su karfafa juna ne su kashi magajin.
"Manoman itacen inabin suka kori ɗan daga gonar"
Yesu ya amfani da tambaya ya sa ma su sauraron su kasa kunne ga abin da mai gonar inabin zai yi. AT: "To yanzu, ku saurari abin da ubangijin gonar inabin zai yi ma su."
"Allah ya sa kar ya faru"
"Amma Yesu ya duɓe su" ko "Amma Yesu ya kalle su." ya yi haka domin ya reke su su gane abin da ya ke fada.
Yesu ya yi amfani da tambay adimon ya koya wa taron. AT: "Ya kamata ku gane nassin: 'Dutsen ... kusurwa'"
"wannan littafin"
Wannan shi ne farko na misalai uku a cikin anabci daga littafin Zabura. Wannan na nufin Mai ceto kamar shi ne dutsen da magina suka zaba kar su yi aiki da shi, amma Allah ya mai da shi dutse ma fi amfani.
"Dutsen da magina suka ki cewa ba shi da kyau sosai domin aikin gini." a wancan kwanaki mutane su na amfani da duwatsu su gini bangon gidaje da wa su ganaginai.
Wannan na nufin shugabanen addini wadan da suka ki Yesu a masa yin Mai ceto.
"babban dutse na gini" ko "dutsen gini mafi amfani"
Wannan misalin na biyu ya yi maganar mutane wanda suka ki Mai ceto kamar sun faɗi akan dutse sun ji ciwo.
Wannan shi ne saka mokon fadowa akan dutsen. AT: "zai farfashe"
"Amma akan duk wanda dutsen ya faɗi." Wannan misali na uku na magana akan wanda suka ki shi kamar shi babban dutse ne wanda rugurguje su.
A wannan ayan, a "sa hanu akan shi" wani lokaci na nufin a kama shi mutumin. AT: "nemi hanya ku kama shi"
"nan da nan"
Wannan shi ne dalilin da ya sa ba su kama Yesu nan take ba. Mutanen sun ba wa Yesu grima, kuma shugabanen addinin suna tsoronabin da mutane za su yi idan sun kama shi. AT: "ba su kama shi ba domin su na tsoron mutanen"
"marubutan da shugaban firistoci suka aiki magewaya su duba Yesu"
"domin suns so su zaigi Yesu da cewa ya faɗa abin da ba kyau"
hukumci" da " ikon" hanya ne guda biyu wanda na cewa suna so gwamna ya yi wa Yesu shari'a. za'a iya bayya na shi da furci ɗaya ko biyu. AT: "domin gwamna ya hukunta Yesu"
"Magewayan suka tambaye Yesu"
Magewayan suna kokari su ruɗe Yesu. ba su yarda da wadannan abubuwa akan Yesu ba.
"mu" na nufin magawayan.
Ma'ana mai yuwa 1)"ka faɗi gaskiya koda mutane masu muhimmanci ba su son shi" ko 2) "kada ka so wani bisa ɗayan"
Wannan shi ne sashin da magawayan suke fada cewa sun san Yesu.
Su na sammanin Yesu ys ce "i" ko "a'a." Idan ya ce "i" mutanen Yahudawan zasu yi haushi da shi domin ya ce masu su biya harajin ga gomnatin wata ƙasa dabam. Idan ya ce "a'a," shugabanen addinin za su gaya wa Romawa cewa Yesu ya na koya wa mutane su karya dokan Romawa.
Suna tambayan dokan Allah, ba dokan Kaisar ba. AT: "ko dokan mu ya yarda mana"
Domin Kaisar shi ne yake mulkin gomnatin Romawa, za su iya nufin gomnatin Romawa da sunan Kaisar.
"A Yesu ya gane yadda uske da sha'ani mai wuyan gane wa" ko "Amma Yesu ya ga suna so su yi masa tarko." Wannan kalmar "nasu" nanufin magawayan.
Wannan ƙirarren kuɗin azurfa ne na Romawa wanda ya isa ladan aiki na rana ɗaya.
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya amsa wa wadan da suke so su yi masa wayo.
"hoto da suna"
" Sai Yesu ya ce masu"
Wannan kalmar "bayar" an gane a sashin da ya wuce. za'a iya maimaita ta anan. AT: " ku kuma ba Allah"
"Magewayan ba su iya samun abin da ba daidai ba, a abun da ya fada
"amma sun yi mamaki da amsar sa kuma ba su iya ce komai ba"
Wannan sashin ya nuna Sadukiyawa sun zama kungiyan Yahudawa da suka ce ba wanda zai tashi daga mattatu. bai nuna da cewa wasu Sadukiyawa sun yarda da cewa akwai tashin mattatu wa su kuma ba su yarda ba.
"idan dan'uwan mutum ya mutu sa'anda yake da mata amma ba shi da yara"
"mutumin ya aure matan dan'uwar sa gomruwa daya mutu"
Yahudawa sun duba yaro na farko da matan tahaifa wanda ta aure dan'uwan mijin ta da ya mutu kamar shi yaron mijin matan ne na farko. Wannan yaron zai gaji dukiyan jijin mahaifiyar sa na farko da sunar sa.
Wannan mai yuwa ya faru, amma mai yuwa labari ne sun yi su gwada Yesu.
"dan'uwa na ɗaya ... dan'uwa na biyu ... dan'uwa na uku"
"ya mutu ba shi da yara" ko "mutu, amma ba shi da yara"
ba su maimaita takaicecen abubuwa da yawa ba domin a bar labarin guntu. AT: "na biyun ya aure ta abu iri ɗaya kuma ya faru" ko "dan'uwan na biyu ya aure ta ya kuwa mutu ba shi da yara"
"Na ukun ya aure ta"
Ba su maimaita takaicecen abubuwa da yawa ba domin a bar labarin guntu. AT: "a hanya ɗaya sauran yan'uwa bakwai sun aure ta har sun mutu ba su da yara"
"dukka yan'uwa bakwain nan" ko "kowane yan'uwa bakwain"
"Sa'anda mutane suka tashi daga mattatu" ko "Sa'anda mutanen da suka mutu sun dawo a raye kuma." wa su yaren suna da hanyar nuna da cewa Sadukiyawan ba su yarda da cewa za su tashi da ga mattatu ba, kamar "A sammanin tashin mattatun" ko Sammanin mutanen da suka mutu sun tashi daga mattatu."
"Mutanen duniyan nan" ko "Mutanen wannan lokacin." Wannan na nuna bambanci da nutanen da suke sama ko mutanen da su ke raye bayan tashin mattatu.
A al'adu an yi maganar maza suna auren mata da mata kuma ana bada su a aure ga mazan su. AT: "yi aure"
AT: "mutanen waccan tsara da Allah ya duba suna da kirki"
"a tashi su daga mutuwa" ko "su tashi daga mutuwa"
Daga cikin duk wadanda su ka mutu. Wannan furcin ya kwatanta duk mattattun mutane tare a cikin ƙarƙashin ƙasa. su karba tashin mattatu a sakanin su yin maganar sake rayuwa kuma.
A al'adu can an yi maganar maza suna auren mata da mata kuma ana bada su a aure ga mazan su. AT: "ba za suyi aure ba" ko "ba za su sami aure ba." Wannan bayan tashin mattatu.
Wannan bayan tashin mattatu. AT: "Ba za su iya mutuwa kuma ba"
"su 'ya'yan Allah ne domin ya dwao da su daga mattatu"
Wannan kalmar " ko" ya na nan domin Sadukiyawan basu yi mamaki ba da litafin ya ce mattatu sun sahi, amma ba su yi sammanin Musa ya rubuta wani abu kamar haka ba. AT: "Amma ko Musa ya nuna cewa mattatun mutane sun tashi"
AT: "Allah aya sa mattatu sun tashi kuma"
"a wata sashin littafin ida ya rubuta game da konewar jeji" ko "a cikin littafin game da konewar jeji"
"inda Musa ya kira Ubangiji"
"Allah na Ibrahim, Ishaku da Yakubu." Duk suna bauta wa allah ɗaya.
Wannan kalmaran yi amfani d ita a nan domin a sa fashi a asalin koyasuwan. A nan Yesu ys bayyana yadda labarin ya hakikanta da cewa mutane sun tashi da mattatu.
Wadannan magnar tana da ma'ana iri ɗaya an fade ta sau biyu domin nauyi. wasu yaren suna da daban daban na yn nauyin. AT: "Ubangiji shi ne Allah mutanen da suke raye kawai"
"ammam allah mutane maus rai." tunda wadannan mutane sun mutu na fuska, za su zama a raye a ruhaniyance. AT: "amma Allah mutane da ruhun su ya na a raye, ko da shike jikin sy ya mutu"
"domin a gun Allah duk suna a raye" ko "domin ruhun su ya na zaune a gaban Allah"
"wadansu marubutan suka ci wa Yesu." akwai marubutan da suke nan sa'anda Sadukiyawan suke tambayan Yesu.
Ba'a bayyane yake ba ko wannan ya na nufin marubutan ko Sadukiyawan, ko dukan su. yana da kyau ka ajiye bayyanin na gaba ɗaya.
"suna jin tsoro su tambaye shi ... tambayoyi" ko "ba su yi kasadan tambayan ... tambayoyi ba." sun gane da cewa basu san dayawa kamar yadda Yesu ya sani ba, amma ba su so su faɗa haka.Wannan za'a iya bayyana shi. AT: "ba su sake yi masa wani tambaya da wayo ba domin sun ji tsoro kada amsan sa ai hikkma ya sa su su zama wawayi koma"
Donme suka ce ... ɗa?" Yesyu ya yi amfani da tambaya domin ya sa marubutan su yi tunani akan wanene Mai ceto. AT: "Mu yi tunani akan su cewa ... ɗa." ko "Ni zan yi magana akan su cewa ... ɗa"
Annabwa, shugabanen addini, da mutanen Yahudawa gaba ɗaya sun sani da cewa Mai ceto ɗan Dauda ne. AT: "kowanne ya ce" ko "mutane sun ce"
"Zuriyan sarki Dauda." Wannan kalmar "ɗa" an yi amfani da shi a nan doimn nufin zuriya. a wanan yanayi ya na nufin wanda zia yi sarauta bisa mulkin Allah.
Wannan tambaya ne daga littafin Zabura wanda ya ce "Yahweh ya cewa Ubangiji na." Amma Yahudawa sun daina cewa " Yahweh"sun cigaba da ce Ubangiji" amimakon. AT: "Ubangiji ya ce wa Ubangiji na" ko "Allah ya cewa Ubangiji na"
Dauda na kiran Almasihu "Ubangiji na"
Ka zauna a "hanun dama na Allah" sananniyar aiki ne na karban babban daraja da iko daga Allah. AT: "Zauna a wuri mai daraja a gefe na"
An yi maganar makiyin Mai ceto kamar wani kayan ɗaki wanda zai iya sa ƙafafun sa akai ya huta. Wannan hoton biyayya ne. AT: "sai na maida makiyanka kamar karkashin tafin sawunka" ko "sai na yi maka nasara akan makiyanka"
A al'adun waccan lokaci, an fi bawa baba daraja fiye da yaro. Dauda mu na sunar 'Ubangiji' domin Almasihu ya nuna ya fi Dauda grima.
"to ta yaya Almasihu ya za ma ɗan Dauda?" AT: "Wannan ya nuna da cewa Almasihu ba zuriya Dauda bane kawai"
"ku zama a fadake game da"
Mayan riguna zai nuna cewa suna da muhimmanci. AT: "wanda suke so suna tafiya suna sa riguna su masu muhimmanci"
"Suna kuma cin gudajen gwamraye. "An yi maganar marubutan kamar suna dabba ne masu jin yunwa wanda suka cinye gidajen gwamraye. Wannan kalmar "gidaje" kalmane na duk inda gwamruwa take zama kuma dukkan kayanta da tasa a gidanta. AT: "sun kuma dauka wa gwamruwan dukkan kayanta"
"suna yin bokon adalci su kuma yi doguwar addu'a" ko "suna yin doguwar addu'a saboda mutane su gan su"
"Za su karɓi shari'a mafi tsanani." AT: "Ba shakka Allah zai hukumta su da tsanani"
Ya tambaya, "Baftisma da Yahaya ya yi daga sama ne ko daga mutane?"
Shugabanni Yahudawa sun tsammani wai Yesu zai ce, "Sai don me baku yi imani da shi ba?"
Sun yi tsammani wai mutanen za su jefe su.
Sun yi bayin duka, suka wulakanta su, sun kuma komar da su hannu wofi.
Ya aika kaunatacen dan sa.
Suka jefa shi wajen gonar inabin sun kuma kashe shi.
Zai hallakar da manomin inabin ya kuma ba da gonar inabin ma wasu.
Ya gaya wanan misali don ya tsauta wa malamin Attaura da manyan firistoci.
Ya ce su ba wa Kaisar abubuwa da ke na Kaisar, kuma ma Allah abubuwa da ke na Allah.
Basu yi imani a tashin matattu ba.
A duniya akwai aure, amma babu aure a har abada.
Ya yi tunanin labarin Musa a jeji, wanda Musa ya kira Ubangiji Allahn Ibrahim da Allahn Ishaku da Allahn Yakubu.
Ya fasara, "Ubangiji ya ce wa Ubangiji na, zauna a dama na, sai na sa ka taka makiyanka."
Suna cin kayan matan da mazansu suka mutu, da kuma yin doguwar addu'a don bad da sawu.
Za a yi masu hukunci mafi tsanani.
1 Yesu ya tada ido sai ya ga mutane masu arziki wadanda suke saka baikonsu a cikin ma'aji. 2 Ya ga wata gwauruwa matalauciya tana saka anini biyu a ciki. 3 Sai ya ce, "Gaskiya ina gaya maku, wannan matalauciyar gwauruwa ta saka fiye da dukansu. 4 Duka wadannan sun bayar da baikonsu daga cikin yalwarsu. Amma wannan gwauruwan, daga cikin talaucin ta, ta saka dukan iyakar kudinta na zaman gari da take da shi." 5 Kamar yadda wadansu suke maganan haikali, yadda aka yi masa ado da duwatsu masu daraja da bayebaye, ya ce, 6 "Game da wadannan abubuwa da ku ke gani, rana tana zuwa da ba dutse ko daya da zai zauna kan dan'uwansa da ba za a rushe kasa ba." 7 Sai suka yi masa tambaya, cewa, "Malam, yaushe ne wadannan abubuwan zasu faru? Menene kuma zai zama alama sa'adda wadannan abubuwa suna shirin faruwa?" 8 Yesu ya amsa, "Ku yi hankali kada a rude ku. Gama dayawa zasu zo a cikin sunana, suna cewa, 'Ni ne shi,' kuma, 'Lokaci ya yi kusa.' Kada ku bi su. 9 Sa'adda ku ka ji game da yakoki da hargitsi, kada ku firgita, dole ne wadannan abubuwa su faru tukuna, amma karshe ba zai faru nan da nan ba." 10 Sa'annan ya ce masu, "Al'umma za ta tasar ma al'umma, mulki kuma za ya tasar wa mulki. 11 Za a yi babbar girgizan kasa, a wurare dabam dabam kuma za a yi yunwa da annoba. Za a yi al'amura masu ban tsoro da manyan alamu daga sama. 12 Amma kafin abubuwan nan duka, za su kama ku, su kuma tsananta maku, suna mika ku ga majami'u da kuma gidajen kurkuku, za su kawo ku gaban sarakuna da gwamnoni saboda sunana. 13 Zai zamar maku zarafin shaida. 14 Saboda haka ku kudurta a ranku kada ku shirya yadda za ku amsa, 15 gama ni zan ba ku kalmomi da hikima, wadda dukan makiyanku ba za su yi tsayayya ko su karyata ku ba. 16 Amma har da mahaifa da 'yan'uwa da dangi da abokai za su bashe ku, su kuma kashe wadansun ku. 17 Kowa zai ki ku saboda sunana. 18 Amma ba ko gashin kanku da zai hallaka. 19 A cikin hankurin ku za ku ribato rayukanku. 20 Sa'adda ku ka ga Urushalima tana kewaye da sojoji, sai ku sani da cewa faduwarta ta yi kusa. 21 Sai wadanda su ke Yahudiya su gudu zuwa kan tuddai, wadanda suke tsakiyar gari kuma su tafi, kada su bar wadanda suke kauyuka su shigo ciki. 22 Gama wadannan ranakun ramako ne, saboda duka abubuwan da aka rubuta su cika. 23 Kaiton wadanda suke da juna biyu da masu ba da mama a wannan kwanakin! Gama za a sha kunci mai girma a kasan, da fushi kuma zuwa ga mutanen nan. 24 Za su fadi ta kaifin takobi kuma za a kai su cikin bauta ga dukan kasashe, al'ummai za su tattake Urushalima, har ya zuwa lokacin al'ummai ya cika. 25 Za a ga alamomi cikin rana da wata da kuma taurari. A duniya kuma, al'ummai za su sha kunci, za su rude saboda rurin teku da rakuman ruwa. 26 Mutane za su suma da tsoro da kuma da tunanin abubuwa da za su abko wa duniya. Gama za a girgiza ikokin sammai. 27 Sa'annan za su ga Dan Mutum yana zuwa a cikin gajimarai da iko da daukaka mai girma. 28 Amma sa'adda wadannan abubuwa suka fara faruwa, tashi saye, sai ku daga kanku sama, saboda ceton ku ya kusato." 29 Yesu ya bada misali, "Duba itacen baure, da duka itatuwa. 30 Sa'adda su ke fitar da ganye, za ku gani da kanku cewa bazara ta yi kusa kuma. 31 Haka kuma, sa'adda ku ka ga wadannan abubuwa suna faruwa, ku sani cewa mulkin Allah ya yi kusa. 32 Gaskiya, na ke gaya maku, wannan zamani ba za ya shude ba, sai duka abubuwan nan sun faru. 33 Sama da kasa za su shude, amma maganata ba za ta shude ba. 34 Amma ku lura da kanku, domin kada ku nawaita zuciyarku da tararradin duniya da shayeshaye da damuwa ta rayuwa. Gama ranar za ta zo babu shiri 35 kamar tarko. Gama zai zo akan kowa da ke rayuwa a fuskar dukan duniya. 36 Amma ku zama a fadake kowanne lokaci, kuna addu'a domin ku iya samun karfin tserewa dukan wadannan abubuwa da za su faru, da kuma yadda za ku tsaya a gaban Dan Mutum." 37 Da rana yana koyarwa a cikin haikali, dukan dare kuma yakan tafi dutsen da a ke kira zaitun. 38 Dukan mutane suka rika zuwa wurinsa da sassafe domin su ji shi a haikali.
Wannan shi ne abin da ya auko mai zuwa a labarin. ko a rana ɗaya da sadukiyawa suka tambaye Yesu [Luka 20:27]
za ka iya bayyana menene kyautan. AT: " kyautan kuɗi"
wani akwati ne a cikin haikali wanda mutane suke sa kuɗin su domin yi wa Allah kyauta
Wannan wata hanya ne na gabatar da wani sabuwar hali a labarin.
"kananan ƙerarren kuɗi gu da biyu" ko "kankanana ƙerarrun kuiɗ na tagulla." Wadannan su ne kuɩ mafi ƙanƙanta mafi daraja da mutane suke amfani da su a wancan lokaci. AT: "kwobobi biyu" ko ƙananan kuɗi mai daraja kaɗan"
Wannan na nufin cewa abin da Yesu ya ke so ya faɗa na da amfani sosai.
Yesu ys na magana da al'majeren sa. wannan kalmar " kia" jam'i ne.
Allah ya duba kyautar ta,karamin kuɗi ne,mafi muhimmanci feye da babban kuɗin da mutanen suka bayar. AT: "kyautar gwauruwa ya fi daraja da fiye da babban kyautar da masu kuɗin suka bayar"
"su na da kuɗi dayawa amma sun bayar da karami daga cimim ta"
"wanda take da ƙaramin kuɗi sosai"
abubuwan da mutane suka bawa Allah
Wannan na nufin haikali mai kyau da adonta.
"lokaci na zuwa" ko "wata rana"
Za'a iya fada sabuwar bayyani anan. AT: "bari aka daya. za a rushe su a kasa" ko "bari akak dayan.abokan gaba zasu yaga kowane dutse a ƙasa"
AT: "kowanne dutse za'a cire daga wurin sa kuma za a rushe su ƙasa"
"al'majeren suka yi wa Yesu tambaya" ko al'majeren Yesu suka yi masa tambaya"
Wannan na nufin abin da Yesu ya gama fada game da abokan gaba zasu rushe haikali.
Yesu ya na magana wa almajeren sa. Wannan kalmar "kai" jam'i ne. AT: "kada ku yarda da ƙarya" ko "kada wani ya ruɗe ku"
Mutane na zuwa a cikin sunar sa cewa suna wakilcin sa. AT: "cewa sune ni" ko "naman su sami iko na"
" Ni ne Almasihu" ko "Ni ne Mai ceto"
"Kada ku yarda da su" ko "Kada ku zama al'majeren su"
A nan "yakoki" mai yuwa na nufin faɗa sakanin ƙasashe, "hargitsi" kuma na nufin mutane na faɗa da shugabanen su ko sakanin wasu a cikin ƙasan su. AT: "yakoki da tawaye" ko yakoki da kewayewa"
"kada ku bar wadan nan abubuwa su firgitar da ku" ko "kada ku ji tsoro"
Wannan na nufin shari'an karshe. AT: "karshen duniyan ba zai faru nan da nan ba bayan yakoki da hargitsi" ko "duniyan ba zai kare nan da nan ba bayan wadannan abubuwa sun faru"
"karshen komai" ko "karshenlokaci"
"Sa'annan Yesu ya cewaal'majeren sa." tunda wannan cigaba ne a maganar Yesu daga ayan da ya wuce, wasu yaren za su so su ce "Sa'annan Yesu ya ce ma su."
A nan "Al'umma" misali ne na mutane alumma, "tasar wa" kuma misali ne na hari. Wannan kalmar "alumma" na wakilcin alummai gaba ɗaya, ba wata alumma ɗaya ba. AT: "Mutanen alumma ɗaya za su faaɗ wa mutanen wata alummai" ko "mutanen wasu alummai za su faɗa wa mutanen wa su alummai"
Wannan na nufin kananar yaruruka na mutane dai da ƙasashe biyu.
Wannan kalmar "za ya tasar" an gane daga ayan da ta wuce kuma ta na nufin faɗa wa. AT: "mulki kuma za ya tasar wa mulki" ko "mutanen wata mulki za su tasar wa mutanen wa su mulki"
Wannan kalmar "za'a yi" an gane a sashin da ta wuce. AT: "za a yi yunwa da annoba a wurare dabam dabam" ko "za'a yi lokacin yunwa da cututtuka a wurare dabam dabam"
"al'amura da za su bawa mutane tsoro" ko "al'amura da za su mutane su ji tsoro"
"za su kama ku." Wannan furcin na nufin mutane za su nuna iko a kan al'majeren. AT: "za su kama ku"
mutane zasu" ko abokan gaba zasu"
Yesu yana yi wa al'majeren sa magana. Wannan kalmar " ku" jam'i ne.
"bada ku ga shugabanen majami'u"
"da ba da ku a cikin kurkuku" ko "sa ku a cikin kurkuku"
Wannan kalmar "suna" an yi amfani da shi anan amasa yin Yesu da kansa, AT: "domin na" KO "domin ku na bi na"
"domin ku yi shaida a kai na"
"Domin wannan," nufa ga komai Yesu ya ce, farawa a [Luka 21:10]
Anan "zukata" misali ne na hankalin mutane. AT: "ku kudura hankalin ka" ko "shirya da ƙarfi" :
"kada ki siffa akan lokaci abin da zaku fada ku ƙare kanku game da zargin"
"hikiman da ba wani makiyanku da za su yi tsayayya ko su karyata ku ba"
"Ni zan gaya maku abu mai hikima da za ku fada"
Wannan za'a iya hada su a sashi ɗaya. AT: "kalmomi da hikma" ko "kalma mai hikma"
AT: "har ma da iyaye, abokanaye, da dangi za su bada ku ga hukumomi"
"za su kashe wadan sun ku." Ma'a na mai yuwa 1) "hukumomin za su kashe wadan sun ku" ko 2)wadan da su ka ba da ku za su kashe wa sun ku." Ma'ana na farkon ya fi yuwa.
AT: "Wannan kalmar "kowa" na nuna nauyin yadda mutane da ya wa za su ki al'majeren, ko ta fadawa1) "zai za ma kamar kowa ya ki ka" ko "zai zama kamar kowa ya ki ku" ko 2) gaba ɗaya. AT: "mutane mafi duka za su ki ku" ko "Mutane dayawa za su ki ku"
Yesu ya yi magana akn karamin sashin mutum. ya na yin nauyin cewa mutumin gaba ɗaya ba zai hallaka ba. Yesu ya riga ya fada cewa wasun su za a kashe su, wasu sun gane wannan cewa ba za su ji illa ba a ruhaniyance. AT: "Amma wadannan abuuwa ba za su yi ma ku illa ba " ko "kowane gashi a kan ku zai mara haɗari"
"Da rekewa da ƙarfi." AT :" Idan baku bari ba"
"rai" an gane ya na nufin madowamiyar sashin mutum. AT: "za ku karbi rai" ko "za ku ceci kan ku"
AT: " sojoji sun kewaye Urushalima"
"da cewa ta kusan hallaka" ko "da cewa sun kusa su hallakar da ita"
guje wa haɗari
Wannan na nufin kauyen da ke wajen Urushalima, ba wa alumma ba . AT: "a wajen garin"
"shigo cikin Urushalima"
"wadannan ranakun harasuwa ne" ko "wannan zai zama lokacin da Allah zai haras da garin"
AT: "duk abuin da annabawa suka rubuta a cikin littafi tunda daɗewa"
AT: " zai faru"
"ga iyaye da suke ba wa 'ya'yan su mama"
Ma'ana mai yuwa1) mutanen ƙasar za su sha kunci ko 2) za'a fuskance masifa a ƙasar.
"za'a yi fushi ga mutanen nana wancan lokaci." Allah zai kawo wannan fushin. AT: "wadannan mutane za su ga fushin Allah" ko "Allah zai yi haushi sosai kuma zai hukunta wadanan mutane"
"za'a kashe su ta kaifin takobi." A nan "faɗi ta kaifin takobi" na nufin cewa abokan gaba soja za su kashe su. AT: "abokan gaba soja za su kashe su"
AT: "abokan gaba za su kama su su kai su wa su ƙasashe"
Wannan kalmar "dukka"furci ne a nuna nauyin cewa za'a kai su ƙassashe dayawa. AT: "zuwa wasu ƙasashe dayawa"
Ma'ana mai yuwa1) al'ummai za su ci nasara a Urushalima zauna a cikin ta ko 2) al'ummai za su hallakar da garin Urushalima ko 3) al'ummai za su hallakar da mutanen Urushalima.
Wannan misalin ya yi maganar Urushalima kamar mutanen wasu ƙasashe suna aiki akan ta su kuma rugurguju shida tafin su.
AT: "lokacin al'ummai ya zo ga karshe"
A nan " al'ummai" na nufin mutanen da ke cikin ta. AT: "mutanen al'ummai za su sha kunci"
"kunci saboda za su rude da rurin teku da rakuman ruwa" ko "kunci sabada karan surutun ruwan teku motsin ta mai kaushi zai sauratar da su." Wannan ya yi kamar babban haɗari da kunci da ba'a saba gane ba a saba gane ba a teku.
"abubuwan da za su faru a duniya" ko "abubuwan da za su faru wa duniya"
AT: Ma'ana mai yiwu1)Allag zai grigiza wata rana da tauraru domin kada su yi motsi yadda suka saba ko 2) Allah zai sokani ikokin ruhohi da ke a sama. na farkon aka yaba.
Yesu yana nufin kansa. AT: "ni,Dan Mutum, i na zuwa"
"zuwa ƙasa a cikin gajimarai"
A nan "ƙarfi" mai yuwa na nufin ikon sharanta duniya. Anan "daukaka"zai iya zama hasken wuta. Allahwani lokaci yana nuna daukakar sa da hasken wuta. AT: "ƙarfi sosai da daukaka mai girma" ko "zai zama mai ƙarfi da daukaka sosai"
wani lokaci idan mutane su na tsoro, su kan sunkuya ƙasa saboda kada aji musu ciwo. idan sun dain tsoro za su tashi tsaye. AT: "tashi tsaye da rashin tsoro"
daga kai misali ne na kallon sama. idan suka daga kansu sama,za su iya ganin mai ceton su yana zuwa gun su. AT: "kalli sama"
Allah wanda ya ceci an yi maganar sa kamar shi ceton ne ya s. Wannan kalmar "ceton" wannan tsamo aikatau ne wanda za' aiya juya ta kamar fi'ili. AT: "domin Allah ya kusa ya cece ka"
"Sa'adda sabuwar ganye ya fara girma"
"bazara ya yi kusa ya fara. "Bazara a Isra'ila tana bin inda itacen baure take fitowa kuma lokacin ne bauren take nuna. AT: "lokacin gribi yayi kusa a fara"
Alamar bayanuwa da Yesu ya kwatanta na mulkin Allah kamar almar bayanuwa na ganyen itacen baure ya ke nu na zuwan bazara.
"Allah ya yi kusa ya ƙafa mulkin sa." AT: "Allahya yi kusa ya yi mulki kamar sarki"
Ma'ana mai yiwa1) zamanin da za su gan alama na farko da Yesu ya yi maganar ta ko 2) zamanin da Yesu yake yi masu magana. na farkon ya fi yuwa.
AT: "zai zama da rai sa'anda"
"Sama da ƙasa za ta dena bayanuwa." Wannan kalmar "sama" anan na nufin sararin sama da dukan komai gaban shi.
"maganata ba za ta dena bayanuwa ba" ko "magana ta ba za ta fadi ba." Yesu ya yi amfani da "kalmomin" anan ya nufa duk abin da ya fada.
AT: "zai cigaba har abada"
"zuciya" a nan na nufin hankali da tunanin mutum. AT: "domin kada ku cika"
Yesu anan ya yi maganar zunubin da take biyowa kamar nawaya ne na fuskawadda mutum zai dauka.
"abin da shayeshaye sosai zai yi maka" ko "bugagge"
"damuwa sosai akan wannan rayuwa"
kamar yadda tarko take kulle dabba sa'anda dabban bata sammance ta ba. ranar zata faru sa'anda mutane basu sammance ta ba. AT: "wacan rana za ta faru sa'anda ba ku sammace ta ba, kamar tadda tarko kulle dabba ba zato"
zuwan wacan rana za ta za ma ba zato ba sammani ga wadan da ba su shriya su na kallon ta ba. AT: "rayuwa. gama idan ba ka yi hankali ba ,, wacan rana za ta kulle ka ba zato"
Wannan na nufin ranar da Mai ceto zai dawo. AT: "ranar da Ɗan Mutum zai dawo"
"zai shafi kowa" ko "abin da zai auko a wacan rana da ta shafi kowa"
an yi magaar faskar duniya kamar faskar mutum ne. wato sashin waje. AT: "a faskar dukkan duniya" ko "a dukan duniya"
"ku shriya ma zuwa na"
Ma'ana mai yuwa1) "ƙarfi sosai ku jumre wadannan abubuwa" ko 2) "ku iya guje ma wadannan abubuwa."
"wadannan abubuwan da zai faru." da Yesu ya gama gaya masu akan abbuwan ban tsoro da zai faru, kamar zalumci, yaki, da kamakamai.
"tsaya ba tsoro a gaban Ɗan Mutum." Wannan mai yuwa na nufin sa'anda Ɗan Mutum ya sharanta kowa. mutumin da bai shirya ba zai ji tsoron Ɗan Mutum kuma ba zai iya tsaya wa ba tsoro ba.
"da rana zai koyar" ko "zai koyar kowanne rana." aya na beye ya faɗa game da abubuwan da Yesu da mutane suke yi a kowanne mako kamin ya mutu.
fristoci ne kawai aka bari a cikin haikali" ko "acikin haraban haikalin"
"da dare ya kan je wajen brinin" ko "yana fita kowanna dare"
Wannan kalmar "dukka" mai yuwa an kwatanta domin a yi nauyin cewa taron na da yawa. AT: "mutane dayawa ne a garin" ko "kusan dukka kowa a garin"
"za su zo kowace rana da sassafe"
"su ji shi yana koyarwa"
Domin ta bayar daga cikin talaucin ta kuma sauran sun bayar daga yawan su.
Ya ce za rushe kuma ba dutse daya da za bari a kan dan'uwansa.
Sun tambaya, "A lokacin da abubuwan na sun faru, kuma wani alama ne zai nuna wai zai faru kenan?
Za su ce, "Ni ne shi," kuma "Lokacin ya yi kusa."
Za a yi yaki, girgizar kasa, yunwa, annoba, da kuma manyan alamu daga sama.
Zai kawo daman ma shaidar su.
Iyaye, 'yan'uwa, dangi, abokakane da "kowa" zai ki su.
A lokacin da an kewaye Urushalima da sojojin, hallakan sa ta yi kusa.
Ya gaya masu su gudu zuwa duwatsu, su bar birnin, kada kuma su shiga birnin.
Ya kira su ranakun ramoko, don a cika duk abin da ke rubuce.
Al'umai za su taka Urushalima har lokacin da Al'umai zai cika.
Ya ce za samu alamun da rana, wata, da tauraro, da kuma wuyan al'ummai a duniya.
Ya kira ma itacen dan baure - a lokacin da ya toho za su sani wai rani ya yi kusa.
Sama da kasa zai shude.
Ya gargadi su kadda su yarda zukatar su ya zama da nauyin zina, shaye-shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya.
Ya gargadi su zu zama da fadake da kuma addu'a
1 Anan nan idin gurasa mara yisti ya yi kusa, wanda a ke kira Idin ketarewa. 2 Manyan firistoci da marubuta suka yi shawara yadda za su kashe Yesu, gama suna jin tsoron mutane. 3 Shaidan ya shiga Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin goma sha biyun. 4 Yahuza ya je ya yi shawara da manyan firistoci da Jarumawa yadda zai ba da Yesu a garesu. 5 Suka yi farin ciki, suka yarda su ba shi kudi. 6 Sai ya yarda, sai ya nimi dama yadda zai ba da shi garesu a lokacin da babu taro. 7 Ranar idin gurasa mara yisti ya yi, da dole za a yi hadayan rago na Idin ketarewa. 8 Yesu ya aiki Bitrus da Yahaya, ya ce masu, "Ku je ku shirya mana abincin Idin ketarewa, domin mu ci." 9 Suka tambaye shi, "A ina ka ke so mu shirya?" 10 Ya amsa masu, "Ku ji, sa'adda ku ka shiga birnin, wani mutum mai dauke da tulun ruwa zai same ku. Ku bishi zuwa cikin gidan da za ya shiga. 11 Sai ku gaya wa mai gidan, 'Malam ya ce, "Ina dakin baki, inda zan ci abincin Idin ketarewa da almajirai na?'" 12 Zai nuna maku babban bene wanda yake a shirye. Ku shirya a can." 13 Sai suka tafi, suka sami komai kamar yadda ya gaya masu. Sai suka shirya abincin Idin ketarewan. 14 Sa'adda lokacin ya yi, ya zauna da almajiran. 15 Sai ya ce masu, "Ina da marmari matuka in ci wannan abincin Idin ketarewa da ku kamin in sha wahala. 16 Gama na ce maku, ba zan ci shi kuma ba, sai dai an cika shi a mulkin Allah." 17 Sai Yesu ya dauki koko, sa'adda ya yi godiya, sai yace, "Karba wannan, ku rarraba a tsakaninku. 18 Gama ina ce maku, ba zan sha wannan ruwan inabi kuma ba, sai dai mulkin Allah ya zo." 19 Sai ya dauki gurasa, sa'adda ya yi godiya, ya kakkarya shi, sai ya ba su, cewa, "Wannan jikina ne wanda aka bayar dominku. Ku yi wannan domin tunawa da ni." 20 Sai ya dauki kokon kuma bayan jibi, cewa, "Wannan koko sabon alkawari ne cikin jinina, wanda aka zubar dominku. 21 Amma ku yi lura. Wanda zai bashe ni yana tare da ni a teburi. 22 Gama Dan Mutum zai tafi lallai kamar yadda aka kaddara. Amma kaiton wannan mutum da shine za ya bashe shi!" 23 Sai suka fara tambaya a tsakaninsu, wanene a cikinmu da zai yi wannan abu. 24 Sai gardama ta tashi a tsakaninsu game da wanene mafi girma. 25 Ya ce masu, "Sarakunan al'ummai suna nuna iko akansu, kuma wadanda suke da iko a kansu ana ce da su masu mulki da daraja. 26 Amma kada ya zama haka da ku. A maimakon haka, bari wanda ya ke mafi girma a cikinku ya zama mafi kankanta. Bari wanda yafi muhimmanci kuma ya zama kamar mai hidima. 27 Gama wanene yafi girma, wanda ya zauna a teburi, ko kuwa wanda yake yin hidima? Ba wanda ya zauna a teburi ba? Duk da haka ina kamar mai hidima a tsakaninku. 28 Amma ku ne wadanda ku ke tare da ni a cikin jarabobina. 29 Na baku mulki, kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, 30 domin ku ci ku kuma sha a teburi na mulkina. Za ku zauna a kan kursiyai kuna shari'anta kabilun nan goma sha biyu na Israila. 31 Siman, Siman, ka yi hankali, shaidan ya nemi izini a bada kai domin ya tankade ka kamar alkama. 32 Amma na yi maka addu'a, saboda kada bangaskiyarka ta fadi. Bayan da ka juyo kuma, ka karfafa 'yan'uwanka." 33 Bitrus ya ce masa, "Ubangiji, ina shirye in tafi tare da kai zuwa cikin kurkuku da zuwa mutuwa." 34 Yesu ya amsa masa, "Ina gaya maka, Bitrus, kamin caran zakara a yau, za ka yi musu na sau uku cewa ba ka sanni ba." 35 Sa'annan Yesu ya ce masu, "Lokacin da na aike ku babu jaka, ko burgami ko takalma, ko kun rasa wani abu? Sai suka amsa, "Babu." 36 Ya kuma ce masu, "Amma yanzu, wanda ya ke da jaka, bari ya dauka, da kuma burgami. Wanda ba shi da takobi sai ya sayar da taguwarsa ya sayi guda. 37 Gama ina ce maku, abin da aka rubuta game da ni dole sai ya cika, 'An lisafta shi kamar daya daga cikin masu karya doka.' Gama abinda aka fada akaina ya cika." 38 Sai suka ce, "Ubangiji, duba! Ga takuba biyu." Sai ya ce masu, "Ya isa." 39 Bayan cin abincin yamma, Yesu ya tafi, kamar yadda ya saba yi, zuwa dutsen Zaitun, sai almajiran suka bi shi. 40 Sa'adda suka iso, ya ce masu, "Ku yi addu'a domin kada ku shiga cikin jaraba." 41 Ya rabu da su misalin nisan jifa, sai ya durkusa kasa ya yi addu'a, 42 yana cewa "Uba, in ka yarda, ka dauke wannan kokon daga gareni. Ko da yake ba nufina ba, amma bari naka nufin ya kasance." 43 Sai mala'ika daga sama ya bayyana a wurinsa, yana karfafa shi. 44 Yana cikin wahala sosai, sai ya dukufa cikin addu'a, har zufarsa kuma tana diga a kasa kamar gudajen jini. 45 Sa'adda ya tashi daga addu'arsa, sai ya zo wurin almajiran, ya same su suna barci domin bakin cikinsu, 46 sai ya tambaye su, "Don me kuke barci? Tashi ku yi addu'a, saboda kada ku shiga cikin jaraba." 47 Sa'adda yana cikin magana, sai, ga taron jama'a suka bayana, tare da Yahuza, daya daga cikin sha biyun, ya na jagabansu. Sai ya zo kusa da Yesu domin ya yi masa sumba, 48 amma Yesu ya ce masa, "Yahuza, za ka ba da Dan Mutum da sumba?" 49 Sa'adda wadanda suke kewaye da Yesu suka ga abin da yake faruwa, sai suka ce, "Ubangiji, mu yi sara da takobi ne?" 50 Sai daya daga cikinsu ya kai wa bawan babban firist sara a kunne, sai ya yanke masa kunnensa na dama. 51 Yesu ya ce, "Ya isa haka." Sai ya taba kunnensa, sai ya warkar da shi. 52 Yesu yace wa manyan firistoci, da masu tsaron haikali, da dattawa wadanda suke gaba da shi, "Kun fito kamar za ku kama dan fashi, da takuba da sanduna? 53 Sa'adda nake tare da ku kowace rana a haikali, ba ku kama ni ba. Amma wannan shine lokacinku, da kuma ikon duhu." 54 Suka kama shi, sai suka tafi da shi, suka kawo shi cikin gidan babban firist. Amma Bitrus yana binsa daga nesa. 55 Bayan da suka hura wuta a tsakiyar gidan da suka zazzauna tare, Bitrus ya zaune a tsakaninsu. 56 Sai wata baranya ta ganshi ya zauna a hasken wuta, sai ta zura masa ido ta ce, "Wannan mutum ma yana tare da shi." 57 Amma Bitrus ya yi musu, yana cewa, "Mace, ban san shi ba." 58 Bayan dan karamin lokaci sai wani mutum ya gan shi, sai ya ce, "Kaima kana daya daga cikinsu." Amma Bitrus ya ce, "Mutumin, ba ni ba ne." 59 Bayan sa'a daya sai wani mutum ya nace da cewa, "Gaskiya wannan mutum yana tare da shi, gama shi dan Galili ne." 60 Amma Bitrus ya ce, "Mutumin, ban san abin da kake fada ba." Sai nan da nan, da yana cikin magana, sai zakara ta yi cara. 61 Yana juyawa, sai Ubangiji ya dubi Bitrus. Sai Bitrus ya tuna kalmar Ubangiji, sa'adda ya ce masa, "Kafin zakara ya yi cara yau za ka musunce ni sau uku." 62 Da fitowarsa waje, Bitrus ya yi kuka mai zafi. 63 Sai mutanen da ke tsare da Yesu suka yi masa ba'a da bulala kuma. 64 Bayan da suka rufe masa idanu, suka tambaye shi, cewa, "Ka yi annabci! Wa ya buge ka?" 65 Suka yi wadansu miyagun maganganu na sabo game da Yesu. 66 Da gari ya waye, sai dattawa suka hadu tare, da manyan firistoci da marubuta. Sai suka kai shi cikin majalisa 67 suka ce, "Gaya mana, in kai ne Almasihu." Amma yace masu, "Idan na gaya maku, ba za ku gaskanta ba, 68 idan na yi maku tambaya, ba za ku amsa ba. 69 Amma nan gaba, Dan Mutum zai zauna a hannun dama na ikon Allah." 70 Suka ce masa, "Ashe kai Dan Allah ne?" Sai Yesu ya ce masu, "Haka kuka ce, nine." 71 Suka ce, "Don me muke neman shaida? Gama mu da kanmu munji daga bakinsa."
Yahuza ya yarda ya ba da Yesu.Wannan ayan ya bada labari na ƙasa akan abin da ya auko.
Wannan kalmar an yi amfani da ita anan domin a gabatar da sabuwar abin da ya auko.
Ana kiran ranar idin da wannan suna domin ranar idin , Yahudawa ba su cin gurasa da aka yi da yisti. AT: "rabar idin sa'anda su ke cin gurasa mara yisti"
"an yi kusa a fara"
Firistoci da marubutan ba su da iko su kashe Yesu da kansu, amma su na sa sammani cewa za su sami wasu su kashe shi. AT: "Yadda za su sa a kashe Yesu" ko "yadda za su sa wani ya kashe Yesu"
Ma'an mai yuwa 1) "suna jin tsoron abin da mutane za su yi" ko 2) "suns tsoro cewa mutane za su zama da Yesu sarki."
Wannan mai yuwa ya na kama da kayan iblis.
"shugaban firistoci"
hafsa na masu tsaron haikalin
"yadda zai taimakesu su kama Yesu"
"Manyan firistocin da kaftin su ka yi farin ciki"
"su bawa Yahuza kuɗi"
"Ya yarda"
Wannan aiki ne da ake kan yi da ya cigaba bayan da labarin ya kare.
"dauke shi"
"asirance" ko "lokacin da babu taron"
" rana ta gurasa mara yisti." Wannan rana ce wanda dukkan Yahudawa za su ci gurasan da aka yi yisti a gidajen su. sa'anna za su bayyana murna na idin gurasa mara yisti na kwanaki bakwai.
kowanna iyali ko kungiya za su kashi tunkiya su ci tare, ana kashi tunkiyoyi da yawa. AT: "dole mutane su kashi tunkiya domin abincin idin ketarewa"
Wannan kalman ne na gaba ɗaya "ku shirya." ba wai Yesu yana gaya wa Yahaya da Bitrus su yi dahuwan dukka ba.
Yesu ya hada da Bitrus da yahaya sa'anda ya ce "mu"Bitrus da yahaya su na cikin kungiyan al'majeren da za su ci abincin.
Wannan kalmar "mu" bai hada da Yesu ba. Yesu ba ya cikin kungiyan da za su shirya abincin.
"yi shirin domin abincin" ko "shirya abincin"
"Yesu ya amsa wa Bitrus da Yahaya"
Yesu ya yi amfani da wannan kalmar domin ya gaya masu kasa kunne su yi daidai abin da ya gaya masu.
"za ku gan mutum ya na dauke da tulun ruwa"
dauke da tuluda ruwa a cikinta." Mai yuwa zai dauka tulun a ƙafadar sa.
"Ku bishi, ku shiga cikin gidan"
Faɗin ya fara da "Ina dakin baki" faɗi na daidai na abin da Yesu ya faɗa, malamin ya na so ya cewa maigidan. zaka iya juya shi kamar faɗin abin da wani ya ce ba ta hanya kusa- kuas ba. AT: "Malamin mu ya tamabaya ina dakin baki wanda zai ci abinin idan ketarewa da al'majeren sa." ko "Malamin mu ya cw ku nuna mana da kin baki inda za mu ci abincin idin ketarewa da mu da sauran al'majeren."
Wannan na nufin Yesu.
"ci abincin idin ketarewa"
Yesu ya cigaba da bawa Bitrus da Yahaya ummurni.
"Maigidan zai nuna maku"
"daki na sama." Idan jama'an ku ba su da gidaje da yake da daki bisa wani dakuna, zaka su ka kwatanta yadda gidaje a birni suke.
"Sai Bitrus da Yahaya suka je"
"Sa'anda lokacin cin abincin ya yi"
"Yesu ya zauna"
"Ni ina so sosai"
Yesu ya na nufin mutuwar sa nan gaba. Wannan kalmar "wahala" anan ta na nufin ka shiga cikin wani yanayin mai wuya da ba ka saba ba ko ka ji zafi sosai.
Yesu ya yi amfani da wannan sashin domin ya yi nauyi akan abin da zai faɗa mai zuwa.
AT: "Ma'ana mai yuwa 1)sa dai dalilin idin ketarewa ya cika. AT: "sai Allah ya cika shi" ko "sai Allah ya cika dalilin idin ketarewan" ko 2) "sai mun bayyana murnan idin ketarewa na ƙarshe"
"ya dauki kokon ruwan inabi sama"
"sa'adda ya yi godiya ga Allah"
"ya cewa annabawan sa"
Su raba abin da ke cikin koko din, ba kuwa kokon da kantaba. AT: "ku raba ruwan inabin da ke cikin kokon a tsakaninku" ko "kowane ɗayan ku ya sha ruwan inabin daga cikin kokon"
Wannan na nufin ruwan da aka matse da ƙarfi daga inabin da ya yi grima a gonar inabin. aruwan inabi ana samun ta daga ruwan inabin da ya tashi.
"sai Allah ya ƙafa mulkin sa" ko "sai Allah ya yi mulki a mulkin sa"
Wannan gura san bai da yisti a ciki, saboda haka a kita take.
"ɓarka shi" ko "ya yaga shi." mai yuwa ya gutsutsura shi ko kuwa ya gutsura shi kashi biyu sai ya bawa annabawan su raba a tsakaninsu. Idan zai yu yi amfani fa da furci da za a iya sa ma kowanne yana yi.
Ma'ana mai yuwa 1) "Wannan gurasan jiki na ne" da 2) "Wannan gurasan na nufin jikina."
AT: "jikina ne wanda aka bayar dominku" ko "jikina ne wanda sadokad dominku"
"ci wannan gurasan"
"domin tunawa da ni"
Wannan kalmar "koko" yana nufin ruwan inabi da yake cikin kokon. AT: "ruwan inabi da yake cikin kokon" ko "Wannan kokon ruwan inabi"
Wannan alkawarin zai faru nan da nan bayan da jininsa ya zuba. AT: "sabuwar alkawarin da za'a yarda ta wurin jinina"
Yesu ya yi maganar mutuwar sa da nufin jininsa ya zubar waje. AT: "wanda aka zubar waje da mutuwa diminku" ko "wanda zai fito waje daga ciwo na dominku sa'anda na mutu"
"Wanda zai ba da ni"
"Gama, lallai, Dan Mutum zai tafi" ko "Gama Dan Mutum zai mutu"
Yesu ya na magana game da kansa a mutum na uku.AT: "Ni, Ɗan Mutum, lallai zan tafi"
AT: "kamar yadda allah ya kadara" ko "kamar yadda Allah ya shirya"
AT: "Amma kaiton wannan mutum wanda shi ne za ya bashe Dan Mutum" ko "Amma yadda zai zama mai ban tsoro ga wannan mutum wanda zai bashe Dan Mutum"
"Sai annabawan suka fara yin muhawara a tsakaninsu"
AT: "mafi muhimmanci" ko "mutanen su yi tunani shi ne mafi muhimminci"
Yesu ya ce ma annabawan"
"yi mulki da ƙarfi bisa Al'ummai"
Mutanen mai yuwa ba su yi tunani waccan mutane masu mulkin wadan suka yi wa mutanen su kirki. AT: "suna so a kira su" ko "suna kiran kansu"
"kada ka aikata haka"
Ana ba wa tsofafin mutane girma a waccan al'adan. shugabanen yawanci tsofofin mutane ne kuma an kiran su "dattibai." Mutum mafi kankanta zai zama mafi kankanta ya darma, da muhimmanci mafi kankantan. AT: "muhimmanci mafi ƙanƙantan"
"bawa"
Wannan ya hada umurnin Yesu a aya 26 da dukkan aya 27. yana nufin mutum mafi muhimmanci ya yi bauta domin Yesu bawa ne.
Gama wanene mafi muhimmanci ... hidima?" Yesu ya yi amfani da wannan tambayan domin ya bayyana wa manzanne wanene mafi girma da gaskiye. AT: "ina sonku ku yi tunani akan wanene mafi girma ... hidima."
"wanda yake cin abinci"
Yesu ya yi amfani da wani tambayan ya koya wa al'majeren sa. AT: "haka ne kam wanda ya zauna a teburi ya fi bawan muhimmanci!"
"Amma ina tare da ku in zama bawa" ko "Amma ina tare da ku in nuna maku yadda bawa ya ke aikatawa." Wannan kalmar "amma"yana nan domin akwai bambanci sakanin abin da mutane suke sammani Yesu ya zama kamar da abin da yake kamar.
"sun tsaya da ni a lokacin da nake fama"
Wasu yaren za su so su saka umarnin. AT: "Jamar yadda Ubana ya bani mulki, Na baku mulki"
Na mai da ku masu mulki a mulkin Allah" ko "Na baku iko ku yi mulki a mulkin" ko "Zan mai da ku sarki"
" kamar yadda Ubana ya bani iko in yi mulki kamar sarki a mulkin"
Sarakai suna zama a kursiyi. Zama a kursiyi sanenniyar alama ce na mulki. AT: "zaku yi aiki kamar sarkai" ko "zaku yi aikin sarakai"
Yesu ya faɗi sunar sa sau biyuya nuna da cewa abin da yake so ya faɗa masa yana da muhimmanci sosai.
Wannan kalmar "kai" na nufin dukakan annabawan.Yaren ku tana da siffofi daba dabam na "kai"ka yi aiki da jam'i.
Wannan na nufin shiaɗan yana so ya gwada al'majeren ya nemi wani abun da ba daidai ba. AT: "gwada ka kamar wani yana wucewa da hatsi ta rariya"
Wannan kalmar "kai" anan yana nufi takamaimai ga Siman. Yaren da ta ke da siffofi na kai dabam daban ta yi amfani da siffar mafuradi.
AT: "saboda ka cigaba da samun bangaskiya" ko "ka cigaba da yarda da ni"
A nan "juye baya kuma" misali ne na sake yarda dani kuma . AT: "Bayan da ka sake yarda da ni kuma" ko "Bayan da ka sake bauta mini"
"ka karfafa yan'uwan ka su sake yin karfi cikin bangaskiyar su" ko "taimake yau'uwanka su yarda da ni"
Wannan na nufin sauran al'majeren. AT: "masubi" ko "sauran al'majeren"
Umurnin wannan sashin ayan za'a iya juya ta. AT: "zaka yi musu sau uku cewa ka sanni kamn zakara tayi cara wannan rana"
AT: "zakara za ta yi cara wannan rana kawai bayan ka yi musu na" ko "kamin zakara ta yi cara wannan rana za ka yi musu"
A nan, caran zakaran ta na nufin wani lokaci ne a rana. zakara ta na cara ne kamin rana ta bayyana da safe.saboda haka, wannan na nufin asalatu.
tsuntsun da take kira da ƙarfi kusa da lokacin da rana ta fito
Ranar Yahudawa ta na farawa bayan da rana ta faɗi.Yesu ya na magana bayan da rana ta faɗi. zakara za ta yi cara kamin safe. safiyan sashi ne na "wannan rana." AT: "yau da dare" ko "da safe"
Yesu ya yi tambaya ya taimake annabawan tunawa yadda mutanen suka basusa;anda su ke tafiya. koda shike wanan tambayan ba ya bukatan amsaKuma Yesu baya bukatan bayyani,ka juya shi kamar tambaya sai dai idan bayyani ne kawai zai sa al'majeren su amsa da cewa sun rasa komai.
Yesu ya na magana da al'majeren sa. Yaren da ta ke da sifofin dabam daban na "kai" su yi amfani da siffar jam'i.
Alabe jaka ne na rike kuɗi. Anan ana amfani da ita a masa yin "kuɗi."
"jakan masu tafiya" ko "jakan abinci"
Zai zama da taimako ga masu sauraron a kara da yawa game da maganar. AT: "Ba mu rasa komai ba" ko "Muna da komai da muke bukata"
Yesu baya nufim takamaimain mutum wanda ba shi da takobi. AT: "Idan wani ba shi da takobi sai ya sayar da taguwarsa"
kwat" ko "tufa na waje"
AT: "abin da annabawa suka rubuta game da acikin littattafai"
Annbawan yaka mata su gane da cewa Allah zai sa komai da yake rubuce a littatafai zai faru. AT: "Allah zai cika" ko "Allah zai sa ya faru"
Anan Yesu yana faɗi littafi.AT: "Mutane sun kirga shi ɗaya daga cikin kungiyan mutane masu karya doka"
"wadanda suke karya doka" ko "mai lefi"
Ma'ana mai yuwa 1) "Gama abin da annabawa suka fada a kaina ya kusan faru" 2) "Gama rayuwana ya kusa ga karshe"
Wannan na nufin mai ƙanƙantaal'majeren Yesu biyu.
Ma'ana mai yuwa 1) suna da takobi isasshe. "yanzu muna da isasshe takobi." ko 2) Yesu ya so su daina magana game da samun takobi." yana gaya masu ne kawai game da hadarin da dukkansu za su fuskata. mai yuwa bawai yana so su siya takobi su yi fada ba.
"domin kada a gwada ku" ko "domin kada wani abu ya gwada ya saku zunubi"
"misalin nisar da wani zai iya jefa dutse." AT: "guntun nesa" ko kimantan gwadawa kamar "mita talatin"
Yesu zai dauki alhakin zunubin kowani mutum akan giciye. Ya yi addu'a ga Uban sa, tambaya ko akwai wanu hanya.
Wannan suna ne mai muhimmanci wa Aallah.
Yesu ya na nufin abin da zai ji kamar kwafin mai ɗaci ruwa ruwa da zai sha. AT: "kada ka bar ni in sha dga wannan kwafin" ko "kada ka bar ni in ji abin da ya yi kusan faru"
"Yesu ya bayyana"
"ya karfafa shi"
"yana shan babban wahala, sai ku,a ya yi addu'a"
"ya yi addu'a mai yawa da gaskiye"
"zufarsa tana diga a ƙasa kamar babban gudajen jini"
"Sa'anda Yesu ya ta shi daga addu'a, ya" ko "bayyaan addu'a,Yesy ya ta shi sai ya"
"ya gani da cewa su na barcidomin su gaji dadaga bakim cikinsu"
Ma'ana mai yuwa 1) "ina mamaki da cewa kuna barci yanzu" ko 2) " bai kama ta kuna barci yanzu ba!"
"domin kada a gwada ku" ko "domin kada wani abu ya gwada ku ya sa ku zunubi"
Wannan kalmae "duba" ya shiya mu ga sabuwar kungiya a labarin Yaren ku sana da hanyan yin haka. AT: "akwai taron da ta bayyana"
Yahuza ya na nuna wa mutanen inda Yesu ya ke.baya gaya wa taron abin da za su yi. AT: " jagaban su zuwa gun Yesu"
"ya gaisheshi da sumba" ko "ya gaishe shi ta wurin yi masa sumba." sa'anda maza su ka gaishe wasu mazan wanda suke iyali ko abokanai, za su yi masu sumba a ƙunci ɗaya ko ƙunci biyu. idan masu karatun ka za su ji kunya su ce na miji zai yi ma wani na miji sumba,sai ka juya shi mafi yawa a hanya na kowa: "ya yi masa gaisuwa na abokantaka."
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya kwaɓe Yahuza da ba da shi da sumba. akulayomi sumba alama ce na ƙauna. AT: "da sumba za ka ba da Ɗan Mutum!"
Yesu yana amfani ta wannan ajali ya yi nufin kansa. AT: "Ni Ɗan Mutum, da"
Wannan na nufin al'majeren Yesu.
Wannan na nufin firistoci da sojoji na zuwa su kama Yesu.
Tambayan game da wani irin fada za su yi
"ɗaya daga cikin al'majeren"
"ya kai wa bawan babban firist sara da takobin"
"Kada ku yi fiye da haka"
"ya taba bawan a inda aka yanka masa kunne"
"Kun fito takuba da sanduna domin kuna tunani cewa ni dan fashi ne?" Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya yi washugabanen Yahudawa. AT: "kunsa ni da cewa ni ba dan fashi bane, duk da haka kun zu wuri na da takuba da sanduna."
"i na tsakanin ku kowanni rana"
firistoci ne kawai suke shiga haikalin. AT: "a cikin haraban haikalin" ko a haikalin"
A wannan ayan, a sa hanu a kai wani na nufin a kama mutumin. AT: "kama ni"
"lokacin ka" ko "lokacin kane ka aikata"
Zai zama da taimako a sake shaidan lokaci. AT: "lokacin ikon duhu"
"tafi da Yesu daga lambun ida suka kama shi"
"cikin haraban gidan babban firist"
"wasu mutane suka yi wuta." wutan domin ya sa mutane suji dumi a lokacin sanyi da dare. AT: "wasu mutane sun kunna wuta domin su ji dumi"
Wannan haraban gidan firist ne. ya na da bango kiwaye da shi, amma babu jinka.
"tare da su"
Ya zauna kusa da wutan ga layin hasken a kak shi.
"sai ta zara wa Bitrus ido ta ce wa sauran mutanen a cikin haraban gidan"
Wannan matan tana gaya wa mutane game da Bitrus cewa ya na tare da Yesu. Mai yuwa ba ta san sunar Bitrus ba.
"Amma Bitrus ya ce ba gaskiya bane"
Bitrus bai san sunar matan ba. Ba zagin ta yake yi ba da ya ki ra ta "mace." Idan mutane za su yi tunanin cewa ya na zagin ta, sai ka yi aiki da hanya na karban mutum a al'adan yadda na miji zai kira matan da bai san sunar ta ba, ko ka bar kalmar.
"Kai ma kana ɗaya daga cikin wanda suna tare da Yseu"
Bitrus bai san sunar matumin ba. Ba zagin sayake yi ba da ya ki ra shi "mutumin." Idan mutane za su yi tunanin cewa ya na zagin shi, sai ka yi aiki da hanya na karban mutum a al'adan yadda na miji zai kira na miji da bai san sunar sa ba, ko ka bar kalmar.
"ya nace da cewa" ko "ya fada da ƙarfi"
Anan "wannan mutumin" na nufin Bitrus. mai maganar mai yuwa bai san sunar Bitrus ba.
Wannan mutumin mai yuwa ya fada cewa Bitrus daga Galili ne daga yadda yake magana.
Bitrus bai san sunar matumin ba. Ba zagin sayake yi ba da ya ki ra shi "mutumin." Idan mutane za su yi tunanin cewa ya na zagin shi, sai ka yi aiki da hanya na karban mutum a al'adan yadda na miji zai kira na miji da bai san sunar sa ba, ko ka bar kalmar. Dubi yadda zaka juya wannan a Luka 22:58,
"Ni ban san abin da kake magana akai ba." Wannan furcin yana nufin cewa Bitrus bai yarda gaba ɗaya da abin da wannan mutumin ya ke fada ba. AT: "abin da ka fada gaba ɗaya ba gaskiya bane" ko "abinda ka fada gaba ɗaya ƙaryane"
"da Bitrus yana cikin magana"
Zakara tana cara ne kamin rana ta fito da safe. Dubi yadda za ka juya sashin kusan ɗayaa Luka 22:34.
"Ubangiji ya juya ya dubi Bitrus"
"abin da Yesu ya fada" da Yesu ya fada cewa Bitrus zai bashe shi
Zakara tana cara ne kamin rana ta fito da safe. Dubi yadda za ka juya sashin kusan ɗayaa Luka 22:34.
Ranar Yahudawa ta na farawa bayan da rana ta faɗo sai ta cegaba zuwa yanma mai zuwa. Yesu ya yi maganar yanman da ta wuce game da abin da zai farukadan kamin asalatu ko da asalatu. AT: "yau da dare"
"musu sau uku cewa baka sanni ba"
"Bitrus ya tafi wajen gidan
"suka rufe masa idanu domin kada ya gani"
Ma su tsaron basu yarda cewa Yesu annabi bane. ko dai,sun yarda da cewa annabin gaskiya zai san wanda ya buga shi ka da idanun sa suna a rufe. Sun kira Yesu annabi,amma suna gwada shi suna nuna masa abin da ya sa ba su yi tunni cewa shi annabai bane. AT: "hakikanta cewa kai annabi ne. gaya ma na wa ya buge ka!" kai annabi wa ya buge ka"
"yi maganar kalma daga Alah!" Wannan bayyanin ya nuna cewa Allah ya kama ta ya nuna wa Yesu wanda ya buge shi tun da an kulle masa ido kuma baya gani.
"Da asalatu safe mai zuwa"
Ma;ana mai yuwa 1) "dattawan suka kai Yesu gun majalisa" 2) "masu tsaron suka kai Yesu gun majalisan dattawan." wasu yare za su ki fadan wanda ya kai shi da amfani da wakilin isimi "su" ko aiki da fi'ilin karban abin da mutane suka yi ba sakewa:" An kai Yesu gun majalisa"
Za'a iya fara sabuwar lbayyani anan. AT: "majalisan. dattawan sun ce wa Yesu"
"Gaya mana Idan kai Almasihu ne"
Yesu yana cewa aidan yayi magana ko ya ce su yi magana, ba za su amsa daidai ba, Wannan sashin tare ya nuna cewa Yesu bai yarada da cewa majalisan suna neman gaskiya ba.
Wannan shi ne farko na biyu bayyanin da Yesu ya yi na yana yin da ba'a gani ba. hanya ne wa Yesu ya amsa ba tare da ba su dalili su ce da cewa yana mai lefin maganar saɓo ne. Mai yuwa yaren ku suna da hanyan nuna cewa aikin nan bai faru ba.
Wannan shi ne bayyanin da Yesu ya yi na biyu na yana yin da ba'a gani ba. Hanya ne wa Yesy ya kwaɓe su ba tare da ba su dalili su fursuna shi ba. Mai yuwa yaren ku suna da hanyan nuna cewa aikin nan bai faru ba.
"daga wannan rana" ko "farawa daga yau"
Yesu ya yi amfani da wannan sashin ya yi nufin kansa. AT: "Ni, Ɗan Mutum zan"
"ka zauna a "hanun dana na Allah" sananniyar alama ce na aikin ƙarban babban daraja da iok daga Allah. AT: "zaune a wurin daraja kusa da ikon Allah"
"Allah mai dukakn ƙarfi." Anan "ƙarfi" na nufin maɗaukakin ikonsa.
Majalisan su yi wannan tambayan domin suna so Yesu ya bayyana masu ganewar suda cewa ya ce shi Ɗan Allah ne. AT: "Sa'anda ka fada haka, kana nufin kai Ɗan Allah ne?"
Wannan suna nu mai muhimmanci ga Yesu.
"I, kamar yadda ku ka fada"
Su yi amfani da tambaya domin nauyin. AT: "ba mu neman wani shaida!"
Wannan sashin "daga bakin sa" na nufin maganar sa. AT: "munji shi ya ce ya bada gaskiya cewa shi Dan Allah ne"
Bikin marar yisti, wanda ake kira Idin Ketarewa.
Yana neman zarafi a lokacin da Yesu na daga nan da taron mutane.
Sun ci sa a dakin bako a Urushalima.
Zai ci abincin Idin Ketarewa kuma a lokacin da ya cika a mulkin Allah.
Ya ce, "Wannan jikina ne da za a bayar domin ku. Ku din ga yin haka domin tunawa da ni."
Ya ce, "Kokon nan sabon alkawari ne a jini na, wanda an zubar don ku."
I.
A'a.
Babban shine wanda na hidima.
Ya yi zama kamar mai hidima.
Ya ce za su yi zama a kursiyai, suna hukunta kabilan goma sha biyu na Isra'ila.
Ya ce wai Bitrus zai yi musu wai ya san Yesu son uku kafin carar zakara.
Hasashen a nassosi da ya ce, "Kuma an lasafta shi kamar daya daga masu laifi."
Ya so su yi addu'a saboda kadar su shiga cikin jaraba
Ya yi addu'a, "Uba, in dia ka yarda, ka dauke mini kokon wahalan nan. Duk da haka dai, ba nufina ba, sai naka za a bi."
Suna barci.
Ya ci amanan Yesu da sumba.
Ya taba masa kunnen, ya kuma warkar da shi.
Yana cikin haikalin.
Sun kai shi gidan babban firist.
Ya ce, "Ke, ban ma san shi ba."
Zakara ya yi cara.
Ya fita waje kuma ya yi rusa kuka.
Sun yi masa ba'a, sun yi masa duka, sun kuma yi masa sabo.
Ba za su gaskata ba.
Domin sun ji daga bakin Yesu da kan sa.
1 Sai duk taron suka tashi, suka kawo Yesu gaban Bilatus. 2 Suka fara saransa, cewa "Mun same wannan mutum yana ruda kasarmu, ya haramta a ba Kaisar haraji, yana kuma cewa shi da kansa ne Almasihu, sarki." 3 Bilatus ya tambaye shi, cewa "Shin kaine Sarkin Yahudawa?" Sai Yesu ya amsa masa ya ce, "Haka ka ce." 4 Sai Bilatus ya ce wa manyan firistocin da taro mai yawa, "Ban samu ko laifi daya game da wannan mutumin ba." 5 Amma suka yi ta cewa, "Yana ta da hankalin mutane da koyarwa a dukan Yahudiya, ya fara daga Galili har zuwa ga wannan wuri." 6 Sa'adda Bilatus ya ji wannan, sai ya tambaya ko mutumin daga Galiline. 7 Sa'adda ya gane cewa yana karkashin mulkin Hirudus, sai ya tura Yesu wurin Hirudus, wanda shi da kansa yana Urushalima a wadannan kwanakin. 8 Sa'adda Hirudus ya ga Yesu, sai ya cika da farin ciki sosai, saboda ya so ganinsa tunda dadewa. Tun can ya ji game da shi sai ya yi begen ganin wadansu al'ajibai da zai yi. 9 Hirudus ya tambaye Yesu cikin kalmomi masu yawa, amma Yesu bai amsa masa da komai ba. 10 Sai manyan firistoci da marubuta suka tsaya, suna ta yi masa zargi mai zafi. 11 Hirudus da sojojinsa suka zarge shi, suka kuma yi masa ba'a, suka sa masa tufafi masu kyau, sa'annan ya sake aika Yesu zuwa wurin Bilatus. 12 Sai Hirudus da Bilatus suka zama abokai a wannan rana (da ma su abokai gaba ne). 13 Bilatus ya kira manyan firistoci tare da masu mulki da kuma taron jama'ar, 14 sai ya ce masu, "Kun kawo mani wannan mutum kamar wanda yake jagorar mutane ga munanan ayyuka, ku kuma gani, Ni, na tuhume shi a gabanku, ban sami ko kuskure daya daga mutumin nan game da abinda ku ke zarginsa da shi ba. 15 Babu, ko Hirudus ma, ya sake komar mana da shi, kun gani, babu wani abu wanda ya yi da ya cancanci mutuwa, 16 saboda haka zan yi masa horo sa'annan in sake shi." 17[1]18 Amma dukansu suka yi ihu tare, cewa, "A tafi da wannan mutumin, sai a sako mana Barabbas!" 19 Barabbas mutum ne wanda aka sa a cikin kurkuku saboda wani tada hankali a cikin birni da kuma kisankai. 20 Bilatus ya sake yi masu magana, yana so ya saki Yesu. 21 Amma suka yi ihu, cewa, "A giciye shi, a giciye shi." 22 Sai ya sake ce masu sau na uku, "Don me, wace magunta wannan mutum ya yi? Ban sami wani abu da ya isa sanadin mutuwa game da shi ba. Saboda haka bayan na hore shi, zan sake shi." 23 Amma suka nace da murya mai karfi, suna so a giciye shi, sai muryarsu ta rinjayi Bilatus. 24 Sai Bilatus ya yarda ya yi masu bisa ga abin da suke so. 25 Ya sako masu wanda suka tambaya ya ba su wanda aka sa a kurkuku domin tada hankali da kuma kisankai. Amma ya ba da Yesu bisa nufinsu. 26 Da suka tafi da shi, sai suka kama wani mai suna siman Bakurane, yana zuwa daga karkara, sai suka daura masa giciyen ya dauka, yana biye da Yesu. 27 Babban taron jama'a, da na mata da suke makoki da kuka dominsa, suna binsa. 28 Amma da ya juya wurinsu, Yesu yace, "Yan matan Urushalima, kada ku yi kuka domina, amma ku yi kuka domin kanku da 'ya'yanku. 29 Gama ku gani, kwanaki suna zuwa da za su ce, 'Albarka ta tabbata ga bakararru da wadanda basu taba haihuwa ba da kuma wadanda ba a taba shan mamansu ba.' 30 Sa'annan za su fara ce wa duwatsu, 'Ku fado bisanmu,' da tuddai ma, 'Ku rufe mu.' 31 Gama idan sun yi wadannan abubuwan lokacin da itace yana danye, me zai faru sa'adda ya bushe?" 32 Aka kai wadansu mutum biyu masu laifi, domin a kashe shi tare da su. 33 Sa'adda suka zo wurin da a ke kira kwalluwa, nan suka giciye shi da barayin, daya daga hannun damansa dayan kuma daga hannun hagu. 34 Yesu yace, "Uba, ka yafe masu, gama basu san abin da suke yi ba." Sai suka jefa kuri'a, suka rarraba tufafinsa. 35 Mutane sun tsaya suna kallo sa'annan masu mulki suna ta yin masa ba'a, cewa, "Ya ceci wadansu. Bari ya ceci kansa, idan shine Almasihu na Allah, zababben nan." 36 Sojojin ma suka yi masa dariya, suna zuwa wurinsa, suna mika masa ruwan tsami, 37 suna cewa, "Idan kai Sarkin Yahudawa ne, ceci kanka." 38 Akwai wata alama bisansa, "Wannan shine Sarkin Yahudawa." 39 Daya daga cikin barayi wanda aka giciye, ya zage shi, cewa, "Ba kai ne Almasihu ba? Ka ceci kanka da mu." 40 Amma dayan ya amsa, ya tsauta masa cewa, "Ba ka tsoron Allah, da yake shari'arka daya ne da nasa? 41 Mu kam an yi ma na daidai, gama mun samu bisa ga abin da muka yi. Amma wannan mutum bai yi wani abu mara kyau ba." 42 Sai ya kara, "Yesu, ka tuna da ni sa'adda ka shiga mulkinka." 43 Yesu ya ce masa, "Gaskiya ina ce maka, yau za ka kasance tare da ni a firdausi." 44 Anan nan a wajen sa'a na shida, sai duhu ya mamaye kasar duka har zuwa sa'a na tara 45 sa'adda rana ya fadi. Sai labulen haikalin ya rabu a tsakiya zuwa kasa. 46 Da kuka da murya mai karfi, Yesu yace, "Uba, na mika Ruhu na a hannunka." Bayan da ya fadi wannan, sai ya mutu. 47 Sa'adda jarumin ya ga abin da ya faru, ya daukaka Allah, cewa, "Lallai wannan mutumin mai adalci ne." 48 Sa'adda dukan taro mai yawa wadanda suka zo tare domin su shaida da idanunsu suka ga abubuwan da suka faru, suka koma suna bugan kirjinsu. 49 Amma duk idon sani, da kuma matan da suka bi shi tun daga Galili, suka tsaya daga nesa, suna duban wadannan abubuwa. 50 Ga shi kuwa, wani mutum mai suna Yusufu, shi dan majalisa ne, nagari ne kuma mutum mai adalci ne 51 (bai yarda da shawarar da kuma abin da suka aikata ba), daga Arimatiya a kasar Yahudiya, wanda yake jiran mulkin Allah. 52 Wannan mutum, ya sami Bilatus, ya tambaya a bashi jikin Yesu. 53 Ya saukar da shi kasa, sai ya nade shi cikin likafani na linin mai kyau, ya kwantar da shi cikin kabari da aka sassaka shi daga dutse, inda ba a taba binne wani ba. 54 Ranar kuwa, ranar shiri ce, Asabaci kuma ta kusato. 55 Matan da suka taho da shi tun daga Galili, suka biyo baya, su ga kabarin da inda aka ajiye shi. 56 Suka koma, sai suka shirya kayan kamshi da mai. Suka kuma huta a ranar Asabaci bisa ga doka.
An kawo Yesu gaban Bilatus.
"Dukkan shugabanen Yahudawan" ko " Dukkan kungiyan majalisan"
"sun mike" ko "sun mike a ƙfafun su"
ka bayyana a gabam wani na nufin ka shiga ikon sa. AT: "domin Bilatus ya yi ma sa shari'a"
"Mu" na nufin mutanen majalisan, ba wa Bilatus na wasu mutanen da su ke kusa ba.
"ya sa mutanen mu su yi abubuwan da ba daidai ba" ko "sa jaraba da gaya wa mutanen mu su yi ƙarya"
"ya gaya masu kada su biya haraji"
Kaisar na wakilin daula na Romawa. AT: "zuwa ga daula"
"Bilatus ya tambaye Yesu"
Ma'ana mai yuwa 1) da fadan wannan, Yesu ya nuna cewa shi sarkin Yahudawa ne. AT: "I, kamar yadda ka fada nine" ko "I, kamar yadda ka fada ne" ko 2) da fadan wannan, Yesu yana cewa Bilatus, ba Yesu ba, shi ne wanda yake kiran Yesu sarkin Yahudawa. AT: "Kai da kanka ka fada haka"
kungiyan mutane da yawa
"ban sa mi wannan mutumin da halakin komai ba"
"sa damuwa a sakani "
Wannan za'a iya juya ta kamar bayyani. AT: "dukan Yahudiya. yafara sa damuwa a galili yanzu kuma ya na sa damuwa a nan"
"ya ji cewa Yesu ya fara koyasuwa a Galili"
Bilatus yana so ya sani daga wani filiYesu ya zo domin yana so ya sami karaminmai'kacin hukumar gwamnati su yi wa Yesu shari'a. Idan Yesu dan Galili ne, Bilatus zai sa Hiridus ya yi wa Yesu shari'a domin Hiridus yana da iko a Galili.
Wannan na nufin Yesu.
"Bilatus ya gane"
Labarin bai nuna tabbatacciyan cewa Hiridus shi ne yake mulkin Galili. AT: "Yesu yana ƙarƙashin ikon Hiridus domin Hiridus shi ne yake mulkin bisa Galili"
"Bilatus ya aiki"
Wannan na nufin Hiridus.
"a waccan lokaci"
"Hiridus ya cika da farin ciki sosai"
"Hiridus ya so ganin Yesu"
"Hiridus ya ji game da Yesu"
"Hiridus yi begen"
AT: "ya gan shi ya na yin wasu irin al'ajibi"
"Hirudus ya tambaye Yesu da yawa"
"bai amsa ba" ko "bai ba wa Hiridus amsa ba"
"marubutan suna tsaye anan"
sau da yawa su ka zargi Yesu" ko "suka yi masa zargin kowane irin laiifufuka"
"Hirudus da sojojinsa"
"sa masa tufafi masu kyau." mai juyawan kada ya nuna cewa anyi wannan domin a daraja Yesu ko an damu da shi. Sun yi haka su ma Ysu ba'a su kuma yi wasa da shi.
Wannan labarin ya nuna da cewa sun zama abokai domin Hiridus ya ji daɗin Bilatus domin ya bar shi ya yi wa Yesy shari'a. AT: "Hirudus da Bilatus suka zama abokai a wannan rana domin Bilatus ya aiki Yesu zuwa Hiridus domin ya yi masa shari'a"
Wannan labarin dama a kulle yake an karane domin ya nuna cewa labarin ƙasa ne. ka yi aiki da wata irin shiri da masu sauraron ka za su gane.
"kira manyan firistoci tare da masu mulki da kuma taron jama'ar su hadu tare"
Bai zama mai yuwiwa da Bilatus ya cewa taron su zo. Mai yuwa taron har yanzu suna jera su gan abin da za'a yi wa Yesu. AT: "taron haryanzu suna nan"
Wannan na nufin Yesu.
"cewa shi"
"Na yi wa Yesu tambya a gaban ka, kuma." Ya nuna da cewa sun yi shaidanci gaban. AT: "Na yi wa Yesu tambya da ku a masa yin shaiduna, da"
"ban yi tunani cewa yana da laifi ba"
Bilatus ya cigaba da yin magana wa shugabanen Yahudawa da taron.
Zai zama da taimako ka ƙara labarin da ba'a ƙara ba a guntun bayyanin. AT: "ko Hiridus ma bai yi tunanin cewa shi mai liafi bane" ko Ko Hiridus Ya yi tunanin cewa shi mara laifi ne"
"haka ma Hiridus, domin" ko "haka ma Hiridus .Mu san wannan domin"
"Hiridus ya sake komar mana da Yesu," wannan kalmar "mu" yana nufin Bilatus da sojojinsa, da firistoci da marubutan, amma ba wadanda suke jin Bilatus ba.
AT: "bai yi wani abu wanda ya canceci mutuwa ba"
Domin Bilatus bai sami Yesu da wani laifi ba ya ka mata ya sake shi ba tare da horo ba. Ba dole bane ka sa wannan bayyanin ya shiga makama a juyin ba. Bilatus ya horas da Yesu wanda ya san cewa shi ba mai laifi bane, kawai domin ya na tsoron taron.
"Dukkan mutanen taron suka yi ihu"
"A tafi da wannan mutumin! sake." Suna tambayan sa cewa sojojin sa su kashe Yesu. AT: "tafi da wannan mutumin fille kan shi! sake"
"mu" yana nufin taron kawai, ba kuwa ga Bilatus da sojojinsa ba.
Wannan bayyani ne daga ƙasa wanda Luka ya bayar akan wanene Barabbas.
AT: "Wanda Romawa suka sa a cikin kurkuku"
"yana ƙoƙarin ya rinjaye mutanen birnin su yi tawaye wa gwomnatin Romawa"
"yi masu magana kuma" ko "yiwa mutanen magana kuma a cikin taron da ma su mulkin addini"
"domin ya na so ya saki Yesu"
"Bilatus ya ce wa tarom kuma , na uku"
Bilatus ya yi amfani da tambaya domin ya sa taron su gane da cewa Yesu bai yi laifin komai ba. AT: "wannan mutumin bai yi wani abun da ba daidai ba!"
"Bai yi wani abu da ya cancenci mutuwa ba"
Kamar a Luka 23:16, Bilatus ya ka ma ta ya saki Yesu ba tara da horas da shi ba. Duk da haka ya bd Yesu a yi masa horo saboda ya rarrashe taron.
"Ni zan sake shi ya tafi"
"taron suka nace"
"da ihu"
AT: "gama Bilatus ya sa sojojin sa su giciye Yesu"
"Taron suka cigaba da ihu har sai da suka rinjayi Bilatus"
"ya yi abin da taron suka tambaya"
Bilatus ya saki Barabbas daga kurkuku. AT: "Bilatus ka saki Barabbas, wanda taron suka tambaya a sake"
"Bilatus ya umurci sojojin su kawo Yesu ma taron su yi duk abin da suke so"
"Da sojojin suka tafi da Yesu da ga gun da Bilatus ya ke"
Sojojin Romawan su na da iko tilasta mutane su dauki kayan su. Kada ka juya wannan a hanyan da zai nina da cewa an kama siman ko ya yi wani abun da ba daidai ba.
" mutum mai suna siman Bakurane, daga birnin karkara"
"wanda yake zuwa cikin Urushalima daga gefen ƙasar"
"sa masa giciyen a kafadar sa"
"sai yana bi a bayan Yesu"
"Taro da yawa"
Matan suna cikin babban taron, ba'a ware su daban ba.
"suna makoki wa Yesu"
Wannan bai nuna da cewa su al'majeren Yesu bane. Saidai yana nuna cewa suna bin sa a baya ne.
Wannan ya nuna da cewa Yesu ya juya ya kalli matan sai ya yi masu magana kai tsaye.
"Yan matan" birnin na nufin matan birnin. Wannan ba mai ladabi bane. hanya ne daidai na nagama da kungiyan matan daga wuri ɗaya. AT: "Ku mata wanda kuke daga Urushalima"
Mutumin misali ne na abin da ya faru da mutum. AT: "kada ku yi kuka da abubuwan da basu da kyau da ya faru dani. amaimako, ku yi kuka domin abubuwa mafi muni da zai faru da ku da 'ya'yanku" ko " kuna kuka domin abubuwan da ba kyau suna faruwa dani, amma za ku yi kuka sosai sa'anda abubuwan mafi muni za su faru da ku da 'ya'yanku"
Wannan ya nuna dalilin da ya sa matan Urushalima za su yi kuka wa kansu.
"kwanaki suna zuwa"
"da mutane za su ce"
"matan da ba su taba haihu ba"
Wannan kashi an yi amfani da su domin a yi kwantanci sosai akan "bakararru." waccan matan da ba su haihu ba kuma ba su shayar da 'ya'ya ba. zai zama da taimako ka hada wannan da "bakararru." AT: "matan da ba su taba haifan yara ba ko ba su taba shayar da 'ya'ya ba
a waccan lokacin
anbar kalmomin domin a sa sashin ya yi guntu. AT: "za su cewa tudun"
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya sa taron su gane cewa mutane suna yin abubuwa da ba kyau yanzu a lokatai masu kyau, to ba shakka za su yi abubuwa mafi muni a lokacin da ba kyau nana gaba .AT: "akuna gane cewa suna yin wadannana abubuwan da ba kyau tun itacen ya na danye, sai ku tabbata cewa za su yi abubuwa mafi muni sa'anda itacen ya bushe."
Ɗanye itace misali ne na abubuwa masu kyau. Idan yaren ku na da misali kama da wannan za su iya amfani da shi a nan.
Itacen da ya bushe misali ne na abin da ke da amfani kawai a kona.
Wannan mai yuwa ya na nufin Romawa ko shugaba nen Yahudawa ko ba ko dayan su.
AT: "Sojojin suna tafiye da Yesu da masu laifi biyu wanda za a kashe su suma"
Mutane biyu masu laifi" ko "Masu laifi biyu." Luka ya kauce wa " sauran masu laifn domin Yesu bai da laifi, koda shike an yi masa kamar mai laifi. Luka ya kira suaran mutanene masu laifi, amma ba Yesu ba.
Wannan kalmar " su" na hade da sojojin, masu laifin da Yesu.
"sojojin Romawa suka giciye shi"
"sun giciye masu laifin a gefen hanun damar Yesu dayan kuma a gefen hanun damar Yesu"
Wannan kalmar "su" na nufin wadanda suke giciye Yesu. Yesu ya magana da Ubansa da tausayi game da mutanen da suke giciye shi.
Wannan babban suna ne wa allah.
"domin ba su gane abin da suke yi ba." Sojojin Romawa ba su gane cewa suna giciya Dan Allan bane. AT: "Idan ba su san asalin wanda suke giciye ba"
Sojojin suka halarci a wani irin cãca. AT: "su yi cãca"
"jefa sosai su yanke shawara wani soja ne a sakanin su zai tafi da gutsure tufafin Yesu"
"Mutanen suna tsaye agun"
Wannan na nufin Yesu.
Luka ya rikodin kalmomin habaici na shugabanen. Hanyan da kawai Yesu zai ceci wadansu shi ne ta mutuwa amaimakon ya cece kansa.
"Yesu zai iya ceci kansa." sun fadi haka domin su yi wa Yesu ba'a. ba su yarda cewa zai iya ceci kansa, AT: "za mu so mu ga shi ya tabbatar man wanene shi da cetan kansa daga giciye"
"wanda Allah ya zaba"
"zuwa gun Yesu"
"suna ba wa Yesu ruwan tsami ya sha" ruwan tsami abin sha ne mai arhr da mutane suke sha. Sojojin suna yi wa Yesu ba'a da ba shi abin shamai arha ya sha wani da ya ke cewa sshi sarki ne.
Sojojin suna yiwa Yesu ba'a. AT: "bamu yarda dacewa kai sarkin Yahudawa bane, amma idan kai sarki ne sai ka hakikanta mana da cecen kanka"
"takardar sanarwa wanda ake liƙaga allo a samam giciyen Yesu da yake cewa"
Mutanen da suka sa alamar a samam Yesy suna yi masa ba'a. ba su yi tunanin cewa asali she sarki bane.
"zage shi Yesu"
Mai laifin ya yi amfani da tambaya ya yi wa yesu ba'a, AT: "ka ce wai kai Almasihu ne. ceci kanka" ko "Idan asali kai Almasihu ne, zaka ceci kanka"
Mai laifin bai ti tunani da cewa Yesu zai cece su daga giciyen.
"dayan mai laifin ya tsauta masa"
Mai laifin ya yi amfani da tambaya ya yiwa dayan mai laifin tsawa. AT: "ka ji tsoron Allah, domin suna yi ma ka hukunci daidai da yadda suke yi masa" ko "baka da tsoron Allah, tunda ka na yi masa ba'a bayan an yataye ka kan giciye daidai da yadda aka yi masa"
Wannan nan amfani da " mu" na nufin ,asu laifin biyu, ba wa Yesu da sauran mutanen ba.
"Da gaskiye mun cancanci wannan hukunci"
"Mai laifin ya kuma ce"
"ka yi tunani na ka yi mini da kyau"
"shiga ciki" mulkin na nufin a fara mulki. AT: "fara mulki kamar sarki"
"Gaskiya" kara nauyin ga abin da Yesu yana faɗa. AT: "Ina so ka sani da cewa yau"
Wannan wuri ne da masu adalci suke zuwa sa'anda sun mutu. Yesu ya tabbatar da mutumin cewa zai zauna da Allah kuma Allah zai karbe shi. AT: "wurin da masu adalci suke zama" ko "wurin da mutane suke zama da kyau"
"wajen tsakar rana." Wannan ya nuna a'ladun a lokacin kirga sa'a farawa da safiya 6 a. m.
"duka ƙasar ya yi duhu"
"har zuwa 3 p. m." Wannan ya nuna a'ladun a lokacin kirga sa'a farawa da safiya 6 a. m.
Wannan ba ya nufin fadiwar rana. amma, hasken rana ta yi duhu a tsakiyar rana. yi amfani ta ajili ka kwatanta rana ya yi duhu amaimakon rana ta fadi.
"labulencikin haikalin." Wannan she ne labulen da ta raba wuri mafi tsarki da sauran wurin a cikin haikalin.
"labulen haikalin ya yage zuwa kashi biyu." AT: "Allah ya yaga labulen haikalin zuwa kashi biyu daga sama zuwa ƙasa"
"Ihu da ƙarfi." Zai zama da taimako ka nuna yadda wannan yana da dangantaka da abi da ya auko a ayoyin da ya wuce. AT: "Sa'anda waccan ya faru Yesu ya yi ahu da ƙarfi"
"Sahin" a hannunka" Nanu fin a kulan Allah. AT: "Na ba da ruhu ne ga kullan ka" ko "Na baka ruhu na, da sanin cewa zaka kula da shi"
"Bayan da Yesu ya fadi wannan"
"Yesu ya mutu"
Wannan suna ne wa hafsan Romawa wanda yake lura da sauran sojojin Romawa. yana duban gicciye.
AT: "duk abin da ya faru"
"wannan mutumin bai ye abin da ba daidai ba" ko "wannan mutum bai yi wani abun da ba daidai ba"
"wanda suka taru tare"
"gani wannan abin da ya auko" ko "dubi abin da ke faruwa"
AT: "abin da ya faru"
"suka koma gida suna bugan"
Wannan sananniyar shaida ne na nuna bakin ciki da nadama. AT: "buga karjinsu su nuna cewa su na da bakin ciki"
"yi tafiya da Yesu"
"daga nesa da Yesu"
"abin da ya faru"
Wannan kalmar "ga shi kuwa" yana gaya mana wani mutum a labarin. yarenku mai yuwa suna da hanyar yin haka. AT: "akwai wani mutum wanda"
"majalisan Yahudawan"
Menene shawaran za'a iya faɗa ba shakka. AT: "ko da shawaran majalisan a kashe Yesu ko da aikin su a kashe shi"
A nan "ƙasar Yahudiya" yana nufin cewa ana gano wurin a Yahudiya. AT: "garin da yake Arimatiya, wanda yake Yahudiya"
"Wannan mutumin ya je gun Bilatus ya neme jikin Yesu domin ya bizine shi."
"Yusufu ya dauki jikin Yesu akan giciye"
"ya nade jikin Yesu a likafani na linin." Wannan shi ne jana'iza na a'ladaun waccan lokacin.
AT: "wanda wasu suka sassaka a cikin dutse a bakin tuku mai gangare ƙwarai"
wannan za'a iya fadan ta a sabuwar bayyani. AT: "ba wanda ya taba sa jiki a wannan ƙabarin"
"ranar da mutane suke shiri domin hutun Yahudawa kira Asabaci"
Gama ga Yahudawan, ranar ta na fara wa ne bayan rana ta fadi. AT: "rana ta kusato ta fadi, farawan Asabacin"
"wanda suka yi tafiya da Yesu daga jihae Galili"
AT: "yi tafiya da Yusufu da mutanen da suke tare da shi; matan ta ga kabarin da inda a ka binne jikin Yesu a cikin kabarin"
"Matan ta ji gidajen da matan suke zama"
Domin ba su da lokaci da za su daraja Yesu da sa mishi kayan kamshi da mai a jikin saranar da ya mutu, suna so su yi shi da safe na farkon makon. AT: "suka shirya kayan kamshi da mai su sa a jikin Yesu"
"matan ba su yi aiki ba"
"bisa ga dokan Yahudawa" ko "yadda dokan Yahudawan ya bukata." ba'a barsu su shirya jikin ba a ranar Asabaci bisa ga dokan.
Sun ce wai Yesu yana bad da jama'armu, yana hana biyar Kaisar haraji, kuma yana cewa shine Almasihu, sarki.
Ya ce, " Ban sami wanan mutum da wani laifi ba."
Hirudus ya so ya gan Yesu ye yi mu'ujiza
Bai amsa shi komai ba.
Ya ce, "Ban sami wanan mutum da wani laifi ba."
Sun so Barabbas, dan tawaye.
Sun yi ihu, "Gicciye shi, gicciye shi."
Bilatus ya ce, "Ban sami delilin kisa a gare shi ba."
Domin sun nace da muryoyi da karfi.
Saminu na Bakurane ya dauka gicciyen Yesu.
Su yi kuka ma kansu da 'ya'yan su.
An gicciye Yesu da wadansu mutum biyu masu laifi.
Ya yi addu'a, "Uba, ka yi masu gafara, don ba su san abin da suke yi ba."
Sun yi masa ba'a ya ceci kansa.
Sun yi masa ba'a ya ceci kansa.
Ya ce, "WANNAN SHI NE SARKIN YAHUDAWA."
Sun yi masa ba'a ya ceci kansa.
Ya ce, "Ka tuna da ni sa'ad da ka shiga sarautar ka."
Ya ce, "Yau ka kasance tare da ni a firdausi."
Duhu ya rufe kasa duka kuma labulen da yeke cikin haikali ya tsage har kasa daga tsakiya.
Ya ce, "Hakika mutumin nan marar laifi ne."
Ya tambai Bilatus ma jikin ya kuma sa shi a kabari.
Ranar Asabar zai fara kenan
Sun huta, bisa ga umurnin Allah.
1 Da sassafe a ranar farko ta mako, suka zo kabarin, suka kawo kayan kamshi wadda suka shirya. 2 Sai suka samu dutsen a mirgine shi daga kabarin. 3 Suka shiga ciki, amma ba su sami jikin Ubangiji Yesu ba. 4 Ya faru kuwa, yayin da suke a rikice game da wannan, ba zato, mutane guda biyu suka tsaya a gabansu da tufafi masu walkiya. 5 Sa'adda matan suka sunkuyar da kansu kasa domin tsoro, suka ce wa matan, "Don me kuke neman mai rai ciki matattatu? 6 Baya nan, amma ya tashi! Ku tuna fa yadda ya yi maku magana tun sa'adda ya ke Galili, 7 cewa za a ba da Dan Mutum ga mutane masu zunubi su kuma giciye shi, a rana ta uku, zai tashi kuma" 8 Sai matan suka tuna da kalmominsa, 9 suka koma daga kabarin sai suka gaya wa sha dayan wadannan abubuwan da dukan sauran. 10 Su Maryamu Magadaliya, Yuwana, Maryamu uwar Yakubu, da sauran matan da ke tare da su suka ba manzanni rohoton wadannan abubuwan. 11 Amma manzannin suka dauki maganar kamar ba ta da amfani, kuma ba su bada gaskiya ga matan ba. 12 Duk da haka Bitrus ya tashi, sai ya gudu zuwa kabarin, ya sunkuya yana kallon ciki, sai ya gan likaftani linin kadai. Sa'annan Bitrus ya tafi gidansa, yana ta mamakin abinda ya faru. 13 A ranan nan, sai ga biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani kauye suna Imawus, wanda nisansa kimanin mil ne daga Urushalima. 14 Suna tattaunawa da junansu game da dukan abubuwan da suka faru. 15 Sai ya zama da cewa, sa'adda su ke tattaunawa tare da tambayoyi, sai Yesu da kansa ya matsa kusa yana tafiya tare da su. 16 Amma idanunsu basu iya ganewa da shi ba. 17 Yesu ya ce masu, "Menene ku ke magana akai sa'adda ku ke tafiya?" Suka tsaya a wurin suna bakin ciki. 18 Daya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa, "Kai ne kadai mutumin da ke Urushalima wanda bai san abubuwan da suka faru a can a wannan kwanakin ba?" 19 Yesu ya ce masu, "Wadanne abubuwa?" Suka amsa masa, "Abubuwa game da Yesu ba Nazarat, wanda ya ke annabi ne, mai manyan ayuka da kalmomi daga Allah da kuma mutane. 20 Da yadda manyan firistoci da masu mulkinmu suka bada shi domin a hukunta shi ga mutuwa a kuma giciye shi. 21 Amma mun yi begen cewa shine wanda za ya yantar da Isra'ila. I, bayan wannan kuma, yanzu kwana uku kenan tunda wadannan abubuwan suka faru. 22 Amma har'ila yau, wadansu mata da ke tare da mu sun yi mana abin al'ajabi, da suka kasance a kabarin tunda sassafe. 23 Sa'adda ba su sami jikinsa ba, suka zo, da cewa su ma sun ga wahayin mala'iku wadanda suka ce masu ya na da rai. 24 Wasu maza wadanda ke tare da mu suka tafi kabarin, suka tarar da shi kamar yadda matan suka fada. Amma ba su ganshi ba." 25 Yesu ya ce masu, "Ku mutane masu wauta da marasa ba da gaskiya ga abin da annabawa suka fada! 26 Bai zama dole ne Almasihu ya sha wahalan wadannan abubuwan ba, ya kuma shiga cikin daukakarsa?" 27 Sa'annan da farko daga Musa da har zuwa dukan annabawa, Yesu ya fasara masu duka abubuwa da ke game da kansa a dukan littattafai. 28 Da suka yi kusa da kauyen, inda suke tafiya, ko da yake Yesu ya yi kamar zai wuce su. 29 Amma suka tilasta shi, cewa, "Ka zauna da mu, gama yamma ta yi kusa rana kuma ta kusa karewa." Sai Yesu ya tafi ya zauna da su. 30 Ya faru cewa, sa'adda ya zauna tare da su domin ya ci abinci, sai ya dauki gurasan, ya albarkace shi, ya kakkarya, sai ya ba su. 31 Sa'annan idanunsu suka bude, da suka gane shi, sai ya bace daga garesu, 32 Suka ce wa junansu, ashe zuciyarmu ba ta yi kuna a cikinmu ba, sa'adda yake magana da mu a hanya, sa'adda ya bude mana littattafai?" 33 Suka tashi a wancan sa'a, sai suka koma Urushalima. Suka sami sha dayan nan tare, da wadanda suke tare da su, 34 cewa, "Lalle ne Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman." 35 Sai suka fadi abubuwan da suka faru a hanya, da yadda aka bayyana masu Yesu sa'adda ya kakkarya gurasa. 36 Sa'adda suke fadin wadannan abubuwan, sai Yesu ya tsaya a sakaninsu, sai ya ce masu, "Salama a gareku." 37 Amma suka firgita suna cike da tsoro, suna tsammani sun ga fatalwa. 38 Yesu ya ce masu, don me ku ke damuwa? Don me tambayoyi ke tasowa a zuciyarku? 39 Duba hannayena da kafafuna, cewa nine da kaina. Taba ni ku gani. Gama ruhu ba shi da jiki da kashi, kamar yadda ku ka ga nake da su." 40 Bayan da ya fadi wannan, sai ya nuna masu hannayensa da kafafunsa. 41 Sa'adda suke cike da farin ciki, da mamaki, Yesu ya ce masu, "Kuna da wani abinci?" 42 Sai suka bashi gasasshen kifi. 43 Yesu ya karba, ya ci a gabansu. 44 Sai ya ce masu, "Sa'adda nake tare da ku na gaya maku cewa duka abin da aka rubuta a cikin dokokin Musa da na annabawa da Zabura dole su cika." 45 Sai ya bude hankalinsu, saboda su gane littattafai. 46 Ya ce masu, "A rubuce yake, cewa Almasihu za ya sha wuya, zai tashi kuma daga matattu a rana ta uku. 47 Ku yi wa'azin tuba da gafarar zunubai a cikin sunansa ga dukan al'ummai, ku fara daga Urushalima. 48 Ku shaidu ne ga wadannan abubuwan. 49 Duba, ina aiko da alkawarin Ubana a kanku. Amma ku jira a birni, sai an suturta ku da iko daga sama." 50 Sa'annan Yesu ya tafi tare da su har sai da suka kai kusa da Betanya. Sai ya daga hannunsa ya albarkace su. 51 Ya zama sa'adda yake sa masu albarka, ya bar su sai aka dauke shi zuwa cikin sama. 52 Sai suka yi masa sujada, suka komo Urushalima da murna mai yawa. 53 Kullayaumin suna cikin haikali, suna albarkatar Allah.
Matan ta koma kabarin da yajt da makamancinsa ta sa a jikin Yesu.
"kamin asalatu ranar Lahadi"
"matayen suka iso kabarin"
Wannan kabarin an yanke daga duwatsu a bakin teku mai gangare kwarai.
Wannan kayan kamshi iri ɗaya ne da suka shirya a Luka23:56.
"Su ka gani cewa dutsen"
AT: "da cewa wani ya mirgine dutsen"
Wannan babban yanka kewayyaye babba ya isa ya yi tare ƙofar shiga kabarin.yana neman mutane dayawa su mirgine shi.
za ka iya bayyana da cewa ba su sami shi ba domin ba ya wurin. AT: " jikin Ubangiji Yesu ba ya wurin"
Wannan sashin an yi amfani da shi a nan domin a sa alama akan wani abu mai muhimmancida ya auko a labarin. Idan yaren ku na da wani hanya na yin haka za su iya amfani da ita anan.
"sun fara tsoro"
"sunkuyar zuwa ƙasa." Yin wannan ya nuna kaskancin su da biyyaya zu wa ga mutanen.
Wadannan mutanen sun yi amfani da tanbaya mara tsanani su soka matan domin neman rayayye mutum a kabari. AT: "kuke neman mai rai ciki matattatu!" ko "kada ku dinga nemen mutumin da yake da rai a wurin da ake binne matattatun mutane!"
A nan "kai" jam'i ne. ana nufin matan da su ka zo.
Mala'ikun sun gama magana da matan.
"amma ya za ma rayayye kuma." " tashi" anan kari nena "sa ya yi rayuwa kuma." AT: "domin Allah ya ta da shi kuma"
"ku tuna da abin"
Wannan kalmar "ku" jam'i ne. ya na nufin matan mai yuwa kuma da al'majeren.
Wannan shi ne farkon faɗi ba na kusa-kusa ba. za'a iya juya da faɗi na nuna kamar yadda yake a UDB.
Wannan sashin "za'a" na nufin cewa ba shakka wani abu zai faru domin Allah ya riga ya yanke cewa zai faru. AT: "ya zama dole cewa za a ba da Dan Mutum ga mutane masu zunubi wanda kuwa za su giciye shi"
A nan "hannaye" na nufin ƙarfi ko iko.
Yahudawa na kirga kowanne rabin rana kamar rana. saba da haka, ranan da Yesu ya tashi "rana ta uku" domin ya biyo ranar da aka bizine shi da rana ta Asabaci.
A nan "kalmar" na nufin bayaynin da Yesu ya yi. AT: "tuna da abin da Yesu ya fada"
"annabawan goma sha ɗayan da dukan sauran al'majeren da suke tare da su"
Wannan shi ne farkon shida zuwa ga goma sah ɗayan, domin Yahuda ya bar goma sah ɗayan ya ba she Yesu.
Wannan kalmar an yi amfani da shi anan a sa alaman fashe a aslin labarin. Anan Luka ya ba da sunayen wa su mata wanda suka zo daga kabarin san gaya wa annabawan abin da ya faru a gun
"Amma annabawan sun yi tananin cewa abin da matan suka gaya ma su maganar banza ne"
Wannan sashin ya hada Bitrus da sauran annabawan. bai tuɓe abin da matan suka fada ba, amma ya ruga a guje zu wa kabarin ya ga wa kansa.
Wannan kari na da ke nufin "ya fa ra aikatawa." ko da Bitrus yana tsaye ko ya na zaune da ya yanke shawara ya fara aikatawa bai da amfani. AT: "fara awaje"
Bitrus ya sunkuya domin ya ga cikin kabarin domin kabarin da aka yanka a cikin dutse gajere na. AT: "ya sunkuya zu wa gunɗuɗu"
"likaftani linin kadai." wannan na nufin kaya da aka ƙunshe kewaye a jikin Yesu da aka bine shi a ciki [Luka 23:53]
"ya tafi abin sa zu wa gida"
Mai wallafawan ya yi amfani da kalmar domin ya sa alama aka sabuwar abin da ya auko.
"al'majeren biyu"
"a rana ɗayn can." Wannan na nufin ranar da matan suka sami kabarin ba komai.
Wannan sunan gari ne.
"kilomita goma sha ɗaya." babban fili da aka keɓe don wasnni" mita 185 ne
Wannan sashin an yi amfani da shi anan a sa alama a inda aikin ya fara. Ya fara da Yesu ya na zu wa gun su. Idan yaren ku na da wata hanya na yin haka za su iya amfani da ita anan.
Wannan kalmar "da kanda" ya nuna nauyin cewa Yesun da suke magana akai ke nan ya bayayna ga su. tun da ma matan su gan mala'iku, amma ba wanda ya gan Yesu.
"an ajiye idanuwan su domin kada su gane Yesu."iyawar mutane su gane Yesu an yi magana kamar iyawan idanuwa su gane shi.AT: "zai iya zama da cewa Allah ne yahana su daga gane Yesu. AT: "wani abu ya faru da su domn ka da su gane shi" ko "Allah ya hana su da ga gane shi"
"Yesu ya cewa mutane biyun"
Wannan sunan mutum ne.
Kiliyobas ya yi amfani da tambaya ya nuna mamakin sa da cewa wannan mutumin nuna cewa bai san abubuwan da ya ke faruwa a Urushalima ba. AT: "Kai ne kadai mutumin ... kwanakin"
A nan "kai" mafuradi ne.
"Wadanne abubuwa suka faru?" ko "Wadanne abubuwa suka faru a nan wurin?"
Wannan na nufin cewa Allah ya sa Yesu ya zama mai ƙarfi da iko kuma mutane sun ga shi da ikon. AT: "annabi wanda Allah ya ba shi iko ya yi kuma ya koyar da mayan abubuwa da suke da ban mamaki ga mutane"
"ba da shi ga"
AT: "domin gomna ya kashe Yesu ta wurin giciye shi"
Romawa sun yi mulki akan Yahudawa. AT: "wa zai ceci Isra'ilawa da ga magabtan mu Romawa"
Wannan ya gabatar da wani dalili da sun yarda cewa Yesu ba zai ceci Isra'ila ba. AT: "Yanzun da ba zai yuba domin"
Yahudawa su na kirgan kowane rabin rana kamar rana. sabo da haka, ranar da Yesu ya tashi "rana ta uku" domin ya biyo ranar da aka bine shi da ranar Asabanci. Dubi yadda za ka juya Wannan a [Luka24:7]
"tunda ayuka da ya wa sun sa mutuwa Yesu ya bayayna"
Wannan ya gabatar da wani dalilin da ya sa mutanen ba su gane abin da ke faruwa game da Yesu.
"a cikin kugiyan mu"
Matayen su ne wadda suke a kabarin.
"mala'iku a wahayin"
"ba su gan Yesu ba"
A nan "zuciya" misali ne na hankalin mutum. AT: "hankali ku mara sauri ya ƙarba" ko "ku mara sa ƙarba da sauri"
Yesu ya yi amfani da tambaya ya tuna she al'majeran aka abin da annabi ya fada. AT: "Bai zama dole ... daukakarsa."
Wannan na nufin Yesu ya fara mulki ya karba daraja da daukaka.
Musa ya rubata kakarda na farko a litafi mai tsarki. AT: "farawa daga rubutun Musa"
"Yesu ya bayyana masu"
Mutanen biyu sun gane daga aikatawar sa cewa ya na tafiya zuwa ga ɗayan wurin ne. watakila ya cigaba da tafiya akan hanya da suka juye su shiga ƙofar garin.ba alama cewa Yesu ya ruɗe su da kalmomi.
za ka iya yin bayyani akan abin da ya sa suka tilasta ma sa ya yi. Mai yuwa wannan furcin ya nuna ya da suke so su yi magana da shi na dan lokaci kamin su canja hankalin sa. Wannan kalmar "tilas" na nufin a yi aiki da ƙarfi na jiki, amma ya yi kaman sun tabbatar shi da kalmomi. AT: "sun tabbatar da shi sun ce"
Ranan Yahudawa ta na karawa idan yana ta fadi.
"Yesu ya shi ga cikin gidan"
"zauna da al'majeren biyu"
Wannan na nufin gyrasa mara yisti. ba ya nufin abinci gaba ɗaya.
"ya yi godiya ga shi" ko "ya godewa Allah ga shi"
"idanuwan su" na nufin ganewar su. AT: "Sa'annan suka gane" ko "sa'anan sun ankara"
"sun gane shi." Wadannan al'majeran sun san shi kamin ya mutu.
Wannan na nufin atake baya nan a gun. bawai ya na nufin ba'a ganin shi ba.
Sun yi amfani da tanbaya su nuna nauyin su akan wannan haduwa da Yesu. ciwo mai zafin da suke ji da gaskiye sa'anda suke magana da Yesu an yi maganar sa kamar akwai wutan da ya ke konewa a cikin su. AT: "zuciyan mu yana konewa... littattafai."
Mutane biyun su na magana da kan su. Wannan kalmar "mu" shi ne na mutum biyu ga yaren da suka sa wannan bambanci.
Yesu bai buɗe litafi ba ko abin rubutu. "buɗe" na nufin ganewar su. AT: "sa'anda yake bayyana mana littattafai" ko "sa'anda ya samu gane littattafai"
"Su" na nufin mutane ne biyun.
"goma sha ɗayan ... a sauran da suke tare da su, da sauran da suka gaya wa mutane biyun"
"mutane biyun sun gaya ma su"
Wannan na nufin Yesu ya bayyana ma su sa'anda suke tafiya a hanya zuwa garin Imawus.
AT: "yadda suka gane Yesu"
"sa'anda Yesu ya karya gurasan" ko "sa'anda Yesu ya yage gurasan"
"a cikin su"
"Bari ku kasance da salama" ko "Allah ya ba ku salama!" Wannan kalmar "ku" jam'i ne.
"Amma" ya nuna bambanci mai ƙarfi. Yesu ya ga ya masu su zama da salama, amma sun ji tsoro amaimako.
"firgitad da tsoro." Wadannan saahi biyun na nufin abu ɗaya, kuma an yi amfani da su a yi nauyin akan tsoron su.
"tunanin cewa suna ganin irin fatalwa." Har yauzu ba su gane da gaskiye cewa Yesu ya na a raye.
A nan na nufin ruhun mutum da ya mutu.
Yesu yaa yi amfani da tambaya ya karfaf su. AT: "kada ku ji tsoro."
Yesu ya yi amfani da tambaya domin ya kwabe su mara tsanani. Yesu ya na gaya masu kada su yi shakka cewa yana a raye. kalmar "zuciya" misali ne na hankalin mutum. AT: "kada ku yi shakka a zuciyar ku!" ko "ku daina shakka!"
Yesu ya tambaye su su tabbata da taba shi da cewa shi ab fatalwa bane. zai zama da taimako rubuta ko ka hada wannan jumlan. AT: "Taba ni ku gani inada naman jiki da ƙashi da fatalwa bai da shi"
Wannan hanya ne na nufin jiki na fuska.
An gane da cewa hannayensa da ƙafafunsa suna da alamar ƙusa na giciyar sa da zai haƙikanta cewa lallai Yesu ne. Wannan za'a iya bayana shi. AT: "ciwon da yake hanunsa da ƙafarsa"
"Sun cika da murna sosai har ma ba su yarda cewa da gaskiye ne"
Yesu ya yi haka domin ya nuna ma su cewa yana da jiki na fuska. Ruhu ba za su iya cin abinci ba.
"a gabansu" ko "sa'anda suke kallo"
"Sa'adda nake tare da ku kamin"
AT: "Allah zaya cika duk abin da ke rubuce ... Zabura" ko "Allah zai sa duk abin da ke a rubuce ... Zabura ya faru"
Wannan kalmar "dokokin Musa," " annabawa," da " Zabura" sunaye ne daidai na saahin littafi mai tsrki na Ibraniyawa. AT: "duk abin da Musa ya rubuta a cikin dokoki, duk abin da annabawa suka rubuta, da duk abin da marubucin Zabura ya rubuta akai na"
A "buɗe zuciya" kari ne da yake nufin ka sa wani ya gane. AT: " sai ya sa su sun gane littattafai "
AT: "Wannan abin da ya faru ne da daɗewa rubuta"
A wannan aya, "a tashi" shine ka dawo rayuwa kuma. Wannan kalmar "daga mattatu" ya yi maganar duk mutanen da su ka mutu daga ƙarƙashin ƙasa.
AT: "mabiyan Almasihu su yi wa'azi ga mutanen dukan al'ummai da suke so su tuba kuma suna so Allah ya yafe masu zunubin su ta wurin Yesu"
"sunar " sa anan na nufin ikon sa. AT: "da ikon Almasihu"
"dukan kananaa garuruwa" ko dukan kungiyoyin mutane"
"farawa daga Urushalima"
"ku gaya wa wasu da cewa abin da kuka gani akain na gaskiyane." al'majeren sun dubi rayuwan Yesu, mutuwa da tash iwar,kuma za su iya kwatanta wamutane abin da ya yi.
"Zan ba ku abin da Ubana ya yi alkawari zai ba ku." Allah ya yi alkawari zai ba ku Ruhu mai Tsarki. UDB ya bayyana wannan.
Wannan suna ne mai muhimmanci ga Allah.
Ikon Allah zai rufe su a hanya ɗaya kamar yadda riga ya ke rufe mutum. AT: "za ku karbe iko"
"daga sama" ko daga Allah"
"Yesu ya tafi tare da al'majeren wajen garin"
Wannan aiki ne da firist su ke aikatawa idan suka sa wa mutane albarka.
"sa'anda Yesu ya ke tambayan Allah ya yi ma su abu mai kyau"
Tunda Luka bai faɗa wanda ya dauke Yesu sa ba,ba mu san ku Allah ne da kansa ko wani ko mala'iku. Idan yaren ku su na so su fada wanda ya dauke shi,zai zama da kyau su yi amfani da "tafi" a maimakon, kamar yadda UDB ya yi.
"al'majeren suka yi wa Yesu sujada"
"sai suka koma"
Wannan kwatanci ne ya furta cewa su na zuwa cikin haikali kowace rana.
firist ne kawai ake bari su shiga cikin ginin haikalin. AT: "a cikin haikalin"
"yabon Allah"
Sun zo da sasafe a rana na farko na mako.
Sun same wai an mirgin dutsen daga kabarin kuma wai jikin Yesu baya wurin.
Sun ce Yesu ya tashi.
Sun sallame rahoton kamar zance ne kawai.
Ya gan likkafanin linin su kadai.
An hana idanun su daga gane da shi.
Suna fatan wai zai fanshi Isra'ila daga abokan gaba.
Ya bayana mene nassosi sun ce game da shi.
Ya bace musu.
Sun gane shi a lokacin da ya albarkace gurasan, ya karya shi, ya kuma ba su
Ya ce, "Salama alaikun."
Ya gayaci almajirain sa su taba shi, kuma ya nuna musu hannaye da kafafun sa.
Yesu ya bude masu zukatan su don su iya gane.
A yi wa'azin tuba da gafarta da zunubia ma duka al'ummai
Ya gaya musu su dakata sai an yi musu baiwar iko daga sama.
An dauke sa zuwa sama.
Ko yaushe kume suna a haikali, suna yabon Allah.
1 A cikin farko akwai Kalma, Kalmar kuma tana tare da Allah, wannan Kalma kuwa Allah ne. 2 Shi kuwa tare da Allah yake tun farko. 3 Dukan abu ta wurinsa aka yi su, babu abin da aka halitta sai ta wurin sa. 4 A cikinsa rai ya ke, kuma wannan rai ya zama haske ga dukan mutane. 5 Hasken ya haskaka a cikin duhu, kuma duhun bai rinjaye shi ba. 6 Akwai wani mutum wanda Allah ya aiko, mai suna Yahaya. 7 Ya zo a matsayin mai ba da shaida game da hasken, domin kowa ya ba da gaskiya ta wurinsa. 8 Ba Yahaya ne hasken ba, amma ya zo ne domin ya shaida hasken. 9 Wannan shine haske na gaskiya mai ba da haske ga dukan mutane, da ke zuwa cikin duniya. 10 Yana cikin duniya, kuma an halicci duniya ta wurinsa, amma duniya bata san shi ba. 11 Ya zo wurin nasa, amma nasa basu karbe shi ba. 12 Amma duk iyakar wadanda suka karbe shi, suka kuma ba da gaskiya ga sunansa, ya ba su 'yanci su zama 'ya'yan Allah. 13 Wadanda aka haife su ba ta wurin jini ba, ko ta wurin nufin jiki, ko nufin mutum, amma ta wurin Allah. 14 Kalmar kuma ya zama jiki ya zauna cikin mu. Mun ga daukakarsa, daukaka irin ta makadaici shi kadai wanda ya zo daga Uban, cike da alheri da gaskiya. 15 Yahaya ya yi shaida akansa yana kira da karfi, cewa, "Wannan shine wanda na yi magana a kansa cewa, 'Shi wanda ke zuwa bayana, ya fi ni, domin ya kasance kafin ni.'" 16 Domin daga cikarsa ne muka karbi alheri akan alheri. 17 Gama shari'a ta zo daga wurin Musa. Alheri da gaskiya sun zo ta wurin Yesu Almasihu. 18 Babu lokacin da wani ya taba ganin Allah, shi wanda shi kadai ne Allah, wanda ke jingine da kirjin Uba, shi ya bayyana shi. 19 Wannan ita ce shaidar Yahaya sa'adda Yahudawa suka aika da Firistoci da Lawiyawa zuwa gareshi don su tambaye shi, "Wanene kai?" 20 Ya fada dalla dalla, kuma bai musunta ba, yana amsa masu cewa, "ba nine Almasihu ba." 21 Sai suka tambaye shi, "To kai wanene? Kai Iliya ne?" Yace, "Ba ni ba ne." Suka ce, "Kai ne anabin?" Ya amsa, "A'a". 22 Sai suka ce masa, "Kai wanene, domin mu bada amsa ga wadanda suka aiko mu? Me kake fadi game da kanka?" 23 Yace, "Ni murya ne, da ke kira cikin jeji, 'Ku daidaita hanyar Ubangiji,' kamar yadda annabi Ishaya ya fada." 24 Su wadanda aka aika daga wurin Farisawa suke. Sai suka tambaye shi cewa, 25 "To don me kake baftisma idan kai ba Almasihu bane, ko Iliya, ko annabin?". 26 Yahaya ya amsa masu, cewa, "Ina baftisma ne da ruwa. Amma a cikinku akwai wani tsaye wanda ba ku sani ba, 27 shi wanda ke zuwa bayana, wanda ko igiyar takalminsa ban isa in kwance ba." 28 Wadannan abubuwa sun faru ne a Baitanya, a dayan ketaren Urdun, a wurin da Yahaya ke Baftisma. 29 Washegari, Yahaya ya ga Yesu yana zuwa wurinsa ya ce, "Duba, ga Dan Ragon Allah wanda ke dauke zunubin duniya! 30 Wannan shine wanda na fada maku cewa, "Shi wanda ke zuwa bayana ya fi ni, domin ya kasance kafin ni.' 31 Ban san shi ba, amma saboda a bayyana shi ga Isra'ila ne nazo ina baftisma da ruwa." 32 Yahaya ya shaida, cewa, "Na ga Ruhu yana saukowa kamar kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa. 33 Ban gane shi ba, amma shi wanda ya aiko ni in yi baftisma cikin ruwa ya fada mani cewa, 'duk wanda ka ga Ruhun ya sauka kuma ya zauna a kansa, shine wanda ke yin baftisma cikin Ruhu mai tsarki.' 34 Na gani, na kuma shaida cewa wannan shine Dan Allah." 35 Kuma, washegari, da Yahaya na tsaye da biyu daga cikin almajiransa, 36 suka ga Yesu na wucewa, sai Yahaya ya ce, "Duba, ga Dan rago na Allah!" 37 Sai almajiransa biyu suka ji ya fadi haka, suka kuwa bi Yesu. 38 Da Yesu ya waiwaya ya gan su suna bin sa, sai ya ce masu, "Me kuke so?" Suka amsa, "Rabbi (wato 'Mallam'), ina kake da zama?" 39 Yace masu, "Zo ku gani." Sai suka zo suka ga inda yake zama; suka zauna da shi ranan nan, gama wajen sa'a ta goma ne. 40 Daya daga cikin wadanda suka ji maganar Yahaya suka kuma bi Yesu shine Andarawus, dan'uwan Siman Bitrus. 41 Ya fara neman dan'uwansa Siman yace masa, "Mun sami Almasihu" (wanda ake kira 'Kristi'). 42 Ya kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi yace, "Kai ne Siman dan Yahaya. Za a kira ka Kefas," (ma'ana, 'Bitrus'). 43 Washegari, da Yesu yana shirin tafiya zuwa Galili, sai ya sami Filibus, ya ce masa, "ka biyo ni." 44 Filibus dan asalin Baitsaida ne, garin Andarawus da Bitrus. 45 Filibus ya sami Natana'ilu yace masa, "Mun same shi, shi wanda Musa ya rubuta shi a cikin attaura, da annabawa: Yesu Dan Yusufu, Ba-Nazarat." 46 Natana'ilu ya ce masa, "za a iya samun wani abu nagari a Nazarat?" Filibus yace masa, "Zo ka gani." 47 Yesu ya ga Natana'ilu yana zuwa wurinsa sai yayi magana game da shi, "Duba, Ba-Isra'ile na hakika wanda babu yaudara a cikinsa." 48 Natana'ilu yace masa, "Ta yaya ka san ni?" Sai Yesu ya amsa masa yace, "Tun kafin Filibus ya kira ka, sa'adda kake a gindin baure, na gan ka." 49 Natana'ilu ya amsa, "Rabbi, Kai Dan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!" 50 Yesu ya amsa masa yace, "Don na ce maka, 'Na gan ka a gindin Baure', ka gaskanta? Za ka ga abubuwa da suka fi wannan girma." 51 Sai yace, 'Hakika, hakika ina gaya maka, zaka ga sammai a bude, mala'ikun Allah kuma suna hawa suna sauka akan Dan Mutum."
Wannan na nufin farkon farin loƙaci kamin Allah ya halicci samai da duniya.
Wannan na nufin Yesu.
"Allah ya halicci dukan komai ta wurin sa" (Dubi:|)
Idan harshen ku be yarda da kalmar da ba daidai ba yakamata wannan kalman ya bayyana shi da kyau a "An halicci dukkan komai ta wurin sa." AT: "Allah ya halicci komai tare da shi" ko kuma "tare da shi akowai komai da an halitta wadda an riga an halitta " Allah ya halicci tare da shi komai da ya halitta"
"A cikinsa rai ya ke" magana ne game da sa komai ya rayu. kuma, "haske" magana na game da "gaskiya." AT: "shi ne ya sa komai ya rayu. Kuma ya bayyana wa mutane game da gaskiya akan Allah"
A nan "sa" ya na nufin wadda ake kiransa kalma.
Ku yi amfani da kalma ta musamman na "Rai." Idan kuna son ku daidaita, ku fasara ta kamar "rai ta ruhaniya."
A nan "haske" magana ne game da abin da ke da gaskiya da kuma kyau. Anan "duhu" magana ne game da abin da ba daidai ba ko mugu.
A nan "haske" magana ne game da wahayin Allah a cikin Yesu. AT: "nuna yaɗa Yesu ya ke kamar hasken gaskiya na Allah"
A nan haske magana ne da ke wakilcin Yesu wadda ya bayyana gaskiyan game da Allah kuma shi ne wannan gaskiyan.
"ko da shike yana cikin wannan duniya, kuma Allah ya halicci komai ta wurinsa, mutane basu gane shi ba"
Kalmar "duniya" magana ne da ke kamar mutane da suka yi rayuwa a duniya. "Mutanen basu san ko shi waye ne ba"
"Ya zo wurin mutanen kasar sa, amma mutanen kasar sa basu karbe shi ba"
"karɓe shi." Karban wani ya na nufin marabshen sa da kuma martaba shi da daraja da begen gina mutunshi tare da shi.
Kalmar "suna" magana ne da ke kamar halin Yesu do komai game da shi. AT: "gaskanta da shi"
"ya basu yanchin" ko " ya sa komai yiwuwa masu"
Kalmar "'ya'ya" magana ne da ke nufin dangantakan mu da Allah, wadda yake kamar 'ya'ya da Uba.
A nan "jiki" na wakilcin "mutum." AT: "zama mutum"
Jumlan nan "makadaici" na nufin cewa shi dabam ne, babu wani kamarsa. Jumlan "wanda ya zo daga Uban" na nufin cewa shi ne ɗan Uba. AT: "ɗa na Uba wanda ya na nan dabam" ko kuma "Ɗa wanda shi ne kadai na Uba"
Wannan laƙani ne na mahimmi ga Allah
"cike da kyaukyawan aiyuka zuwa gare mu wadda bamu chanchanta ba"
Yohanna na magana game da Yesu. Jumlan "zuwa a bayana" na nufin cewa aikin Yohanna ya riga ya fara kuma aikin Yesu ze fara jim kadan.
"ya fi muhimmanci fiye da ni" ko kuma" ya na da ikon fiye da ni"
Ku yi hankali ka da ku fasara a hanyar da ze nuna cewa Yesu ya fi muhimmi domin ya girmi Yohanna bisa ga shekarun mutuntaka. Yesu ya fi Yahaya domin shi Ɗan Allah ne, wanda ya na da rai kullum.
Wannan kalma na nufin alherin Allah da babu iyaka.
"albarka akan albarka"
kalmar "Yahudawa" na nufin " shugabannin yahudawa". AT: "Shugabannin yahudawa suka aika... zuwa gareshi daga Urushalima"
Jumla na biyu ya bayyana abubuwan da jumla na farko ya bayyana a hanyar da ba daidai ba domin ya nanata cewa Yahaya yana faɗan gaskiya ne, yana kuma cewa ba shi ne Almasihu ba. Mai yiwuwa harshen ku ya na da hanya dabam na yin wannan.
"Me ne zancen, idan ba kai ne mai ceto ba?" ko kuma "Me ya ke faruwa?" ko kuma "Me ku ke yi?"
Yahaya ya shigaba da magana da fristoci da kuma levites.
"fristocin da levites sun ce wa Yahaya"
fristocin da levites, ba Yahaya ba
"Yahaya ya ce"
Yahaya ya na cewa anabcin Ishaya na game da shi. Kalmar "murya" a nan na nufin mutumin da ke kira a cikin jeji. AT: "ni ne ina kira a cikin jeji"
A nan an yi amfani da kalmar "hanya". AT: "shirya kanku wa zuwan Ubangiji kamar yadda mutane su ke shirya hanya wa mutum mai daraja"
Wannan bayanin labari ne game da mutane da sun tambaye Yahaya.
Aya 28 ya faɗa mana asalin bayani game da shirin labarin.
Ya kamata ku bayyana abin da zai yi idan ya zo. AT: "wanda zai yi maku wa'azi bayan na tafi"
Dama kwancen takalma aikin bawa ne.Wannan magana ne na aiki mara daɗi na bawa. AT: "ni, wanda ban cancanta in yi bauta a hanya da ba daɗi" ko "ni. ban cancanci in kwance igiyar takalminsa ba"
Wannan magana ne wadda yake wakilcin cikakken hadayan Allah. Ana kirin Yesu "Ragon Allah" domin an yi hadayarsa domin zunuban mutane.
Kalmar "duniya" magana ne wadda ya ke nufin dukkan mutane a cikin duniya.
Dubi yadda an fasara wannan a cikin 1:15.
saukowa daga sama
Wannan jumlan tamka ne. "Ruhun" ya sauka kamar yadda kurciya yake sauka a kan mutum.
Kalmar "sama" na nufin "sarari."
Wadansu matanin sun ce "Ɗan Allah"; wadansu kuma suka ce "zaɓi na Allah."
Wannan muhimmin laƙani ne wa Yesu, Ɗan Allah.
Wannan wata rana ne. Rana na biyu ne wadda Yahaya ya gan Yesu.
"sa'a ta goma." Wannan Jumlan ya na bayyana loƙacci da rana, kafin duhu, wadda ba za a iya yin tafiya zuwa wata gari ba, mai yiwuwa sa'a hudu na yamma.
Wannan ba Yahaya mai baftisma ba ne. "Yahaya" sanannen suna ne.
Wannan ne labari game da Filibus.
"Natana'ilu ya ce wa Filibus"
Wannan furucin ya bayyana kamar tambaya ne domin a kara nanaci. AT: "Ba bu abu mai kyau da zai fito daga Nazarat!"
AT: "cikakken mutumin gaskiya"
Wannan furucin ya bayyana kamar tambaya domin a ba da nanaci. AT: "ka gaskanta domin na ce, na gan ka a karkashin bishiyan baure'!
Ku fasara wannan a yadda harshen ku zai nanata cewa an fahinci muhimmin abin da ke da gaskiya.
Kalmar na tare da Allah.
Kalmar Allah ne.
A cikin farko akwai Kalma.
Dukan abu ta wurinsa aka yi su, babu abin da aka halitta ba tare da shi ba.
4A cikinsa akwai rai.
Sunarsa Yahaya.
Ya zo a matsayin mai ba da shaida game da hasken, domin kowa ya ba da gaskiya ta wurinsa.
10Yana cikin duniya, kuma an halicci duniya ta wurinsa, amma duniya bata san shi ba. 11Ya zo wurin nasa, amma nasa basu karbe shi ba. Duniyar ba ta san hasken da Yahaya ya zo ya shaida ba kuma mutanen wannan hasken basu karbe shi ba.
Ga waɗanda sun ba da gaskiya ga sunarsa, ya ba su 'yanci su zama 'ya'yan Allah.
Za su iya zama 'ya'yan Allah ta wurin haifuwar Allah.
A'a! Kalmar ne kadai mutumin da ya zo daga Uba.
Daga cikarsa ne muka karbi alheri akan alheri.
Alheri da gaskiya sun zo ta wurin Yesu Almasihu.
Babu mutumin da ya gan Allah a ko yaushe.
Shi wanda ke jingine da kirjin Uba, shi ya bayyana mana shi.
Yace, "Ni murya ne, da ke kira cikin jeji, 'Ku daidaita hanyar Ubangiji,' kamar yadda annabi Ishaya ya fada."
Ya ce, "Duba, ga Dan Ragon Allah wanda ke ɗauke zunubin duniya".
Ya zo ya na baftisma da ruwa domin a bayyana Yesu, Dan Ragon Allah wanda ke ɗauke zunubin duniya ga Isra'ila.
Alamar shi ne duk wanda Yahaya ya gan Ruhun ya sauka ya kuma zauna a kansa, shine wanda ke yin baftisma cikin Ruhu mai tsarki.
Sun bi Yesu.
Sunar ɗaya daga cikin biyun shi ne Andarawus
Andarawus ya ce wa Siman, "Mun sami Almasihu".
Yesu ya ce za a kira Siman "Kefas" (ma'ana, 'Bitrus').
Garin Andarawus da Bitrus Baitsaida ne.
Natana'ilu ya amsa, "Rabbi, Kai Dan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!"
Yesu ya faɗa wa Natana'ilu cewa zai gan sammai a buɗe, mala'ikun Allah kuma suna hawa suna sauka akan Dan Mutum."
1 Bayan kwana uku, akwai aure a Kana ta Galili, mahaifiyar Yesu kuma tana wurin. 2 An gayyaci Yesu da almajiransa zuwa auren. 3 Da ruwan inabin ya kare, maihafiyar Yasu tace masa, "basu da ruwan inabi." 4 Yesu yace mata, "Mace, me yasa kika zo wurina? Lokaci na bai yi ba tukuna". 5 Maihafiyarsa tace wa ma'aikatan, "Ku yi duk abin da yace maku." 6 To akwai randunan ruwa na dutse guda shidda a wurin wadanda Yahudawa ke amfani da su domin al'adansu na tsarkakewa, kowace zata iya daukar durom guda. 7 Yesu yace masu, "Cika randunan da ruwa". Sai suka cika randunan makil. 8 Sai yace wa ma'aikatan, "Ku diba daga ciki ku kai wa shugaban biki." Sai suka yi hakannan. 9 Shugaban bikin ya dandana ruwan da ya zama ruwan inabin, amma bai san inda ya fito ba (amma ma'aikatan wadanda suka jawo ruwan sun sani). Sai ya kira ango 10 yace masa, "Kowane mutum yakan raba ruwan inabi mai kyau da farko, kafin mai arhar bayan an shanye mai kyaun. Amma kai ka ajiye mai kyaun sai yanzu." 11 Wannan alama ta farko ce da Yesu yayi a Kana ta Galili, ya kuma bayyana daukakarsa, almajiransa kuma suka gaskata da shi. 12 Bayan wannan, Yesu, da mahaifiyarsa, da 'yan'uwansa da almajiransa suka tafi Kafarnahum, kuma suka zauna can wasu 'yan kwanaki. 13 To idin ketarewa na Yahudawa ya kusato, Yesu kuwa ya wuce zuwa Urushalima. 14 Ya iske wadanda suke sayar da shanu da tumaki da tantabaru, masu canjin kudi kuma na zaune a wurin. 15 Sai yayi tsumingiya da igiyoyi ya kore su duka daga cikin haikalin, duk da tumakin da shanun. Sai ya watsar da sulallan masu canjin kudin ya birkitar da teburansu. 16 Yace wa masu sayar da tantabaru, "Ku fitar da wadannan abubuwa daga nan. Ku daina maida gidan Ubana wurin kasuwanci." 17 Almajiransa suka tuna a rubuce yake, "Himma domin gidanka za ta cinye ni." 18 Sai shugabannin Yahudawa suka amsa suka ce masa, "Wace alama za ka nuna mana, da shike kana yin wadannan abubuwan?" 19 Yesu ya amsa, "Ku rushe wannan haikali, kuma a cikin kwana uku zan gina shi." 20 Sai shugabanin Yahudawa suka ce, "An dauki shekaru arba'in da shidda kamin a gama gina wannan haikalin, za ka dau kwanaki uku kadai wajen gina shi?" 21 Amma yana nufin haikali na jikinsa ne. 22 Bayan da aka tashe shi daga matattu, sai almajiransa suka tuna ya fadi haka, suka kuma ba da gaskiya ga nassi da wannan kalami da Yesu ya fada. 23 Kuma, da yana Urushalima a idin ketarewa, a lokacin idin, mutane da yawa suka gaskata ga sunansa, sa'adda suka ga alamun da ya yi. 24 Amma Yesu bai yadda da su ba domin ya san su duka, 25 saboda baya bukatar wani ya shaida masa game da mutum, domin ya san abinda ke cikin sa.
An gayyaci Yesu da almajiransa zuwa aure. Wannan ayan ya ba da asalin bayani game da shirin labarin.
Yawancin masu fasara su na karanta wannan da cewa bayan kwana na uku ne Yesu ya kira Filibus da Nataniel don su bi shi. Ranar farko ya faru a cikin 1:35 da kuma na biyun a cikin 1:43.
AT: "Wani ya gayyaci Yesu da almajiransa zuwa aure"
Wannan ya na nufin Maryamu. Idan ba shi da kyau ɗa ya kira Uwarsa "Mace" a harshenku, sai ku yi amfani da da wata kalma mai kyau ko kuma ku bari.
An yi wannan tambaya domin a ba da nanaci. AT: "wannan bai shafe ni ba." ko kuma "kadda ku faɗa mani abin da zan yi."
Kalmar "loƙaci" magana ne da ke wakilcin loƙacin da ya cancanta wa Yesu don ya nuna cewa shi ne mai ceto ta wurin aikin al'ajibi. AT: "Loƙacin bai kai ba da zan yi baban abu"
Za ku iya juya wannan zuwa awu na zamani. AT: "75 zuwa lita 115"
Wannan ya na nufin "zuwa sama" ko kuma "cikakke."
Wannan ya na nufin mutumin da ke dauki da shugabancin abinci da ruwan sha.
Wannan ita ce bayanin zancen.
rashin iya bambanta sakanin ruwa mai arha da ruwa mai tsada domin shan giya dayawa
Wannan ayan bata cikin asalin labarin, amma ta na ba da ra'ayi game da labarin.
Wannan sunan wuri ne.
A nan "daukakarsa" ya na nufin baban ikon Yesu. AT: "nuna ikonsa"
Wannan ya na nuna cewa sun wuce daga wuri mai sauki zuwa wuri mai tsawo. Kafarnahum ya na ta arewankudu na Kana da tsawo mai sauki.
Kalmar "'yan'uwansa" na a hade ne da 'yan'uwa da kuma 'yar'uwa. Yesu ya girme dukkan 'yan'uwaninsa.
Wannan ya na nuna cewa ya wuce daga wuri mai sauki zuwa wuri mai tsawo. An gina Urushalima a kan tudu.
Aya na biye ya nuna cewa wadannan mutanin na cikin fegan haikali. An yi wannan wurin domin sujada ne ba domin kasuwanci ba.
Mutane su na sayan dabbobi a cikin fegan haikali domin su yi hadaya wa Allah.
Hukumomin Yahudawa sun so mutanin da za su saya dabbobi don hadaya da cewa su canza kuɗin su zuwa ga wata kuɗi daga "masu canjin kuɗi."
Wannan kalmomin ya na da alamun abubuwan da ya faru domin wani abin da ya faru a farko. Don hakka, Yesu ya gan masu canza kuɗi a zaune a cikin haikali.
"Daina saya da sayad da abubuwa a cikin gidan Ubana"
Wannan jumla ne wadda Yesu ya yi amfani a matsayin haikali.
Wannan lakami ne ta muhimmi da Yesu ya yi amfani wa Allah.
AT: "wani ya rubuto"
Wannan ya na nufin haikali, gidan Allah.
Kalmar "cinye" ya na nuna maganar "wuta." Kaunar Yesu ga haikalin ya na nan ne kamar wuta da ke konewa a cikinsa.
Wannan ya na nufin abu ne wadda ya ke nuna cewa abin gaskiya ne.
Wannan ya na nufin yadda Yesu ya yi wa masu canza kuɗi a cikin haikali.
Yesu ya na bayyana yanayin abin da zai faru idan abin da ba gaskiya ba ne ya zama gaskiya. Don haka, zai gina haikalin idan hukumomin Yahudawa sun rushe ta. Ba wai yana yabon hukumomin Yahudawan don su rushe haikalin ba. Za ku iya fasara kalmomin "rushe" da kuma "gina" ta wurin amfani da kalmomin. AT: "Idan kun rushe wannan haikalin, Haƙiƙa zan gina shi" ko kuma " Za ku iya tabatar da cewa idan kun rushe wannan hakalin, Zan gina shi"
"sa shi ya tsaya"
shekaru arba'in da shidda ... kwanaki uku"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nuna cewa hukuman Yahudawa sun gane cewa Yesu ya na so ya rushe haikalin sai ya kuma gina ta a kwanaki uku. "gina" karin magana ne na "kafa." AT: "za ku kafa ta a kwanaki uku?" ko kuma "ba za ku iya gina ta a cikin kwanaki uku ba!"
A nan "gaskanta" ya na nufin amsa wani abu ko kuma yarda cewa gaskiya ne.
Wannan ya na nufin kalamin Yesu a cikin 2:19.
Kalmar "yanzu" yana gabatar da mu zuwa ga sabon abu a cikin labarin.
A nan "suna" magana ne da ke wakilcin Yesu. AT: "gaskanta da shi"
Ana iya kiran abin ban mamaki "alamu" domin an yin amfani da su don su nuna cewa Allah mai iko ne wadda yake da iko akan duniya.
A nan kalmar "mutum" ya na wakilcin mutane. AT: "game da mutane, domin ya san abin dake a cikin mutane"
Yesu, mahaifiyarsa, da kuma almajiransa suna wurin bukin aure a Kana na Galili.
Ta faɗa wa Yesu wannan domin ta zata za su yi wani abu game da halin da ake ciki.
Ya fara ce masu su cika randunan da ruwa. Sai yace wa ma'aikatan, su diba daga "ruwan" su kai wa shugaban biki.
Shugaban bikin yace, "Kowane mutum yakan raba ruwan inabi mai kyau da farko, kafin mai arhar bayan an shanye mai kyaun. Amma kai ka ajiye mai kyaun sai yanzu."
Almajiran Yesu sun gaskanta da shi.
Ya iske masu sayar da shanu da tumaki da tantabaru, da masu canjin kuɗi.
Yayi tsumingiya da igiyoyi ya kore su duka daga cikin haikalin, duk da tumakin da shanun. Ya kuma watsar da sulallan masu canjin kuɗin ya birkitar da teburansu.
Yace wa masu sayar da tantabaru, "Ku fitar da waɗannan abubuwa daga nan. Ku daina maida gidan Ubana wurin kasuwanci."
Sun amsa suka ce masa, "Wace alama za ka nuna mana, da shike kana yin wadannan abubuwan?"
Ya amsa su ta wurin faɗa cewa, "Ku rushe wannan haikali, kuma a cikin kwana uku zan gina shi."
Yesu yana maganar haikali na jikinsa.
Sun gaskata domin sun ga alamun da ya yi.
Bai yadda da su ba domin ya san su duka mutane, saboda baya bukatar wani ya shaida masa game da mutum, domin ya san abinda ke cikin sa.
1 akwai wani Bafarise da ake kira Nikodimu, shugaba a cikin Yahudawa. 2 Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dare ya ce masa, "Rabbi, mun sani cewa kai malami ne da kazo daga wurin Allah, gama ba wanda zai iya yin wadannan alamu da kake yi sai idan Allah na tare da shi." 3 Yesu ya amsa masa, "Hakika, hakika, idan ba a sake haifuwar mutum ba, ba zai iya ganin mulkin Allah ba." 4 Nikodimu ya ce masa, "Yaya za a sake haifuwar mutum bayan ya tsufa? Ba zai iya sake shiga cikin cikin uwarsa kuma a haife shi ba, zai iya?" 5 Yesu ya amsa, "Hakika, hakika, idan ba a haifi mutum da ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga cikin mulkin Allah ba. 6 Abin da aka haifa ta wurin jiki, jiki ne, kuma abin da aka haifa ta wurin Ruhu, Ruhu ne. 7 Kada ka yi mamaki don na ce maka, 'dole a maya haifuwar ka.' 8 Iska takan hura duk inda ta ga dama. Ka kan ji motsin ta, amma ba ka san inda ta fito ko inda za ta tafi ba. Haka duk wanda aka haifa daga Ruhu." 9 Nikodimu ya amsa yace masa, "Yaya wannan zai yiwu?" 10 Yesu ya amsa yace masa, "Kai malami ne a Israila amma ba ka san wadannan al'amura ba? 11 Hakika, hakika, ina gaya maka, muna fadin abubuwan da muka sani, kuma muna shaida abubuwan da muka gani. Duk da haka ba ku karbi shaidar mu ba. 12 Idan na gaya maka abubuwan da ke na duniya amma baka gaskata ba, to yaya zaka gaskata idan na gaya maka abubuwa na sama? 13 Babu wanda ya taba hawa zuwa sama sai dai shi wanda ya sauko daga sama: wato Dan Mutum. 14 Kamar yadda Musa ya ta da maciji a jeji, haka ma dole a ta da Dan Mutum 15 domin dukan wadanda suka bada gaskiya gareshi su sami rai na har abada. 16 Gama Allah ya kaunaci duniya sosai, har ya ba da makadaicin Dansa, domin duk wanda ya bada gaskiya gareshi, kada ya mutu, amma ya samu rai madawwami. 17 Gama Allah bai aiko da Dansa cikin duniya domin ya kayar da duniya ba, amma domin a ceci duniya ta wurin sa. 18 Duk wanda ya bada gaskiya gare shi ba a kayar da shi ba, amma duk wanda bai bada gaskiya gare shi ba an riga an kayar da shi, domin bai bada gaskiya ga sunan wannan da shi kadai ne Dan Allah ba. 19 Wannan shi ne dalilin shari'ar, domin haske ya zo duniya, amma mutane suka kaunaci duhu fiye da hasken, sabili da ayyukan su na mugunta ne. 20 Domin duk wanda ke mugayen ayyuka ya ki haske, kuma baya zuwa wurin hasken domin kada ayyukansa su bayyanu. 21 Sai dai duk wanda yake aikata gaskiya kan zo wurin hasken domin ayyukansa, da ake aiwatarwa ga Allah, su bayyanu. 22 Bayan wannan, Yesu da almajiransa suka tafi kasar Yahudiya. A can ya dan zauna tare da su ya kuma yi Baftisma. 23 Yahaya ma yana Baftisma a Ainon kusa da Salim domin akwai ruwa da yawa a can. Mutane na zuwa wurin sa yana masu Baftisma, 24 domin a lokacin ba a jefa Yahaya a kurkuku ba tukuna. 25 Sai gardama ta taso tsakanin almajiran Yahaya da wani Bayahude akan al'adun tsarkakewa. 26 Suka je wurin Yahaya suka ce, "Rabbi, wanda yake tare da kai a dayan ketaren kogin Urdun, kuma ka shaida shi, duba, yana baftisma, kuma mutane duka suna zuwa wurin sa." 27 Yahaya ya amsa, "Mutum ba zai iya samun wani abu ba sai an ba shi daga sama. 28 Ku da kanku zaku shaida na ce, 'Ba ni ne Almasihu ba' amma amaimakon haka, 'an aiko ni kafin shi.' 29 Amaryar ta angon ce. Yanzu abokin angon, wanda ke tsaye yana saurarensa, yana murna sosai saboda muryan angon. Murnata ta cika domin wannan. 30 Dole shi ya karu, ni kuma in ragu. 31 Shi wanda ya fito daga sama ya fi kowa. Shi Wanda ya zo daga duniya, na duniya ne, kuma game da duniya yake magana. Shi wanda ya fito daga sama yana saman kowa. 32 Ya shaida abubuwan da ya ji ya kuma gani, amma babu wanda ya karbi shaidarsa. 33 Duk wanda ya karbi shaidarsa ya tabbatar Allah gaskiya ne. 34 Domin duk wanda Allah ya aika kan yi magana da kalmomin Allah. Domin bai bada Ruhun da ma'auni ba. 35 Uban ya kaunaci Dan, ya kuma ba da dukan komai a hanunsa. 36 Shi wanda ya bada gaskiya ga Dan ya na da rai madawwami, amma wanda ya ki yiwa Dan biyayya ba zai ga rai ba, amma fushin Allah na kansa.
Nikodimu ya zo ya gan Yesu.
An yi amfani da wannan kalma a nan domin a nuna sabon sashin labarin da kuma gabatar da Nikodimu.
"A nan "ku" ya na nufin Nikodimu da kuma sauran mutanin majalisan Yahudawa.
Yesu da Nikodimu sun cigaba da magana.
Dubi yadda an fasara wannan a cikin 1:51.
"haifafe daga sama" ko kuma "haifafe na Allah"
Kalmar "mulki" magana ne game da shugabancin Allah. AT: "wurin da Allah yake shugabanci"
Nikodimus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya nanata cewa ba zai iya faruwa ba. AT: "hakika, ba za a iya haifan mutum kuma bayan ya tsufa ba!"
Nikodimus ya kuma yi amfani da wannan tambayan domin ya bayyana ra'ayin shi da cewa haifuwa na biyu ba shi yiwuwa. "hakika, ba zai iya shigan cikin cikin Uwarsa na biyu ba!
"kuma"
wata sashin jikin mace wadda yaro yake girma a ciki
AT: 1) "yi baftisma a cikin ruwa da kuma ruhu" ko kuma 2) "haifafe ta jiki da kuma ta ruhaniya"
Kalmar "mulki" magana ne game da shugabancin Allah a rayuwan mutum. AT: "ya ji shugabancin Allah a rayuwansa"
"Dole ne a haife ku daga sama"
A ainihin harshen, iska da Ruhu kalma daya ne. Mai magana a nan ya na maganan iska kamar mutum ne. AT: "Ruhu mai Tsarki ya na nan kamar iska wadda yake huruwa a duk inda yake so"
Wannan tambayan ya kara bayani ne a jumlan. AT: "Wannan ba ya yiwuwa!" ko kuma "Wannan ba zai iya faruwa ba!"
Wannan tambayan ya kara bayani ne a jumlan. AT: "Kai mallami ne na Israila, Ina mamaki cewa ba ka gane wadannan abubuwa ba!"
Yesu bai haɗa da Nikodimu ba a loƙacin da ya ce "mu". (Dubi:
Wannan tambaya ya nanata rashin gaskantawar Nikodimu. AT: "hakika, ba za ku gaskanta ba idan na gaya maku game da abubuwan sama!"
A dukkan wuraren "ka" ɗaya ne.
abubuwan ruhaniya
Wannan ya na nufin wurin da Allah yake.
Wannan karin magana ne. Wadansu mutane za su "ta da" Yesu kamar yadda Musa ya "ta da" macijin a cikin jeji.
Jejin ya bushe, tsararin wuri, amma a nan ya na nufin wurin da Musa da Isra'ilawa su ka yi tafiya na shekaru arba'in.
A nan "duniya" magana ne da ke nufin kowa a duniya.
Wannan ne irin kauna da ke zuwa daga Allah kuma ya na nan a kan wadansu, ko a loƙacin da bai ribanya ba. Allah da kansa ne kauna kuma shi ne hanyar kauna ta gaskiya.
An bayyana wadannan kalmomin da ke nufin abu ɗaya, na farko daidai sai kuma wadda ba daidai ba. Wadansu harshen su na iya nanata a hanya dabam. AT: "Ainahin dalilin da Allah ya aiko ɗansa a duniya shi ne domin ya cece ta"
"ya hukunta." "Hukunta" ya na nuna cewa Allah ya na karban mutum bayan an hukunta shi. A loƙacin da an kayar da mutum, ana hukunta shi kuma Allah ba ya karban shi.
Wannan muhimmin lakabi ne wa Yesu.
Kalmar "haske" magana ne game da gaskiyar Allah da ke a bayyane a cikin Yesu. Yesu ya yi magana game da kansa a cikin mutum na uku. Idan harshen ku ba ya yarda mutane su yi maganan kansu a cikin mutum na uku, za ku iya bayyana wadda ya kasance hasken. "Duniya" magana ne game da dukkan mutane da suke a cikin duniya. AT: "Wadda yake kamar haske ya bayyana gaskiyar Allah wa dukkan mutane" ko kuma "Ni, wadda nake kamar haske, na zo cikin duniyan"
A nan "duhu" magana ne game da mugu.
AT: "domin kadda hasken ya nuna abin da yake yi" ko kuma "domin kadda hasken ya bayyana ayukansa"
AT: "mutane za su iya ganin ayukansa da kyau" ko kuma "kowa zai iya ganin abubuwan da yake yi da kyau"
Wannan ya na nufin bayan Yesu ya yi magana da Nikodimu. Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 2:12.
Wannan kalmomin na nufin "rafi," kamar na ruwa.
wata kauye dake kusa da rafin Joda
"domin akwai rafi dayawa a wurin"
AT: "Yahaya ya na yi masu baftisma" ko kuma "ya na yi masu baftisma"
AT: "Sai almajiran Yahaya da wani Bayahude suka fara jayayya"
faɗa da amfani da kalmomi
A cikin wannan jumlan, "duba" umurni ne dake nufin "sa hankali!" AT: "ka shaida, 'duba! Ya na yin baftisma," ko kuma "ka shaida. ;dubi wancan! Ya na yin baftisma," (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)
"Ba bu wanda yake da iko saidai"
A nan maganan "sama" na nufin Allah. AT: "Allah ya ba shi shi"
Wannan "ku" ya na nufin dukkan mutane da Yahaya yake magana da su. AT: "Dukkan ku"
AT: "Allah ya aike ni don in isa kafin shi"
A nan "amarya" da "anga" karin magana ce. Yesu ya na nan kamar "angon" kuma Yahaya ya na nan kamar abokin "angon."
AT: "Don haka na yi farinciki sosai"
Kalmar "na" ya na nufin Yahaya mai baftisma, wadda yake magana.
"Shi" ya na nufin ango, Yesu, wanda zai cigaba da girma a cikin daraja.
"Shi wanda ya fito daga sama ya fi kowa muhimmi"
Yahaya ya na nufin cewa Yesu ya fi shi da shike Yesu ya na daga sama, kuma an haife Yahaya a duniya. AT: "shi wadda yake haifaffe a duniyan nan ya na nan kamar kowane mutum da yake rayuwa a duniya kuma yana magana game da abin da yake faruwa a cikin wannan duniya"
Wannan ya na nufin abu ɗaya ne a jumla na farko. Yahaya ya nanata wannan don bayani.
Yahaya ya na magana game da Yesu. AT: "wadda yake sama ya na magana game da abin da ya ji ya kuma gani a sama"
Yahaya ya nanata bayanin a nan cewa mutane kadan ne suka gaskanta da Yesu. AT: "mutane kadan ne sun gaskanta da shi"
"Duk wanda ya gaskanta da abin da Yesu ya ce"
"nuna" ko "yarda"
"Wannan Yesu, wadda Allah ya aike shi don ya zama wakilinsa"
"Domin shi ne wadda Allah ya ba da dukkan ikon Ruhunsa"
Wadannan muhimmin lakaɓi ne wadda suke kwatanta dangantaka sakanin Allah da Yesu.
Wannan ya na nufin sa a ikonsa.
"mutum da ya gaskanta"
Ana iya bayyana kalmar "fushi". AT: "Allah zai cigaba da hukunta shi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)
Nikodimu Bafarise ne, shugaba a cikin Yahudawa.
Nikodimu ya faɗa wa Yesu cewa, "Rabbi, mun sani cewa kai malami ne da kazo daga wurin Allah, gama ba wanda zai iya yin wadannan alamu da kake yi sai idan Allah na tare da shi."
Yesu ya faɗa wa Nikodimu cewa ɗole a sake haifuwar mutum kafin ya shaga mulkin Allah.
Nikodimu ya "Yaya za a sake haifuwar mutum bayan ya tsufa? Ba zai iya sake shiga cikin cikin uwarsa kuma a haife shi ba, zai iya?"
Ya tsauta wa Nikodimu da cewa, "Kai malami ne a Israila amma ba ka san waɗannan al'amura ba?"
Babu wanda ya taba hawa zuwa sama sai dai shi wanda ya sauko daga sama, wato Ɗan Mutum.
Ɗole a ta da Ɗan Mutum domin dukan waɗanda suka bada gaskiya gareshi su sami rai na har abada.
Ya nuna ƙaunarsa ta wurin ba da makadaicin Ɗansa, domin duk wanda ya bada gaskiya gareshi, kada ya mutu, amma ya samu rai madawwami.
A'a. Allah Y aiko da Ɗansa cikin duniya domin a ceci duniya ta wurin sa.
A na sharanta mutane domin haske ya zo duniya, amma mutane suka ƙaunaci duhu fiye da hasken, sabili da ayyukan su na mugunta ne.
Waɗanda suke mugayen ayyuka sun ƙi haske, kuma basu zuwa wurin hasken domin kada ayyukansu su bayyanu.
Suna zuwa ga haske domin a iya ganin ayyukansu da kyau, kuma ya zama sananne cewa ayyukansu da ake aiwatarwa ga Allah, su bayyanu.
Yahaya ya ce, "Ɗole shi ya karu, ni kuma in ragu".
Sun tabbatar cewa Allah gaskiya ne.
Ya ba da dukan komai a hanun Ɗan.
Ba za su ga rai ba, amma fushin Allah na kanss.
Su na da rai madawwami.
1 Da Yesu ya sani cewa Farisawa sun ji cewa yana samun almajirai yana kuma yi masu baftisma fiye da Yahaya 2 (ko da shike ba Yesu da kansa ke yin baftismar ba, amma almajiransa ne), 3 ya bar Yahudiya ya koma Galili. 4 Amma ya zamar masa dole ya ratsa ta Samariya. 5 Ya zo wani birnin Samariya, mai suna Sika, kusa da filin da Yakubu ya ba dansa Yusufu. 6 Rijiyar Yakubu na wurin. Da Yesu ya gaji da tafiyarsa sai ya zauna gefen rijiyar. Kusan karfe goma sha biyu na rana ne. 7 Wata mace, Ba-Samariya ta zo domin ta dibi ruwa, sai Yesu ya ce mata, "Ba ni ruwa in sha." 8 Gama almajiransa sun tafi cikin gari don sayen abinci. 9 Sai ba-Samariyar tace masa, "Yaya kai da kake Bayahude kake tambaya ta ruwan sha, ni da nike 'yar Samariya?" Domin Yahudawa ba su harka da Samariyawa. 10 Sai Yesu ya amsa yace mata, "In da kin san kyautar Allah, da shi wanda yake ce da ke, 'Ba ni ruwan sha,' da kin roke shi, sai kuma ya ba ki ruwan rai." 11 Matar tace masa, "Mallam, ga shi ba ka da guga, kuma rijiyar tana da zurfi. Ina za ka samu ruwan rai? 12 Ai ba ka fi Ubanmu Yakubu ba, ko ka fi shi, shi wanda ya ba mu rijiyar, shi kansa kuma ya sha daga cikin ta, haka kuma 'ya'yansa da shanunsa?" 13 Yesu ya amsa yace mata, "duk wanda ya sha daga wannan ruwan zai sake jin kishi, 14 amma duk wanda ya sha daga ruwa da zan ba shi ba zai sake jin kishi ba. Maimakon haka, ruwan da zan bashi zai zama mabulbular ruwa a cikinsa wanda ke bulbula zuwa rai madawwami." 15 Matar tace masa, "Mallam, ka ba ni wannan ruwa yadda ba zan kara jin kishi ba ba kuma sai na zo nan don in dibi ruwa ba." 16 Yesu ya ce mata, "Je, ki kira maigidanki ku zo nan tare." 17 Matar ta amsa tace masa, "Ba ni da miji." Yesu yace, "Kin fadi daidai da kika ce, 'ba ni da miji,' 18 domin kin auri mazaje har biyar, kuma wanda kike da shi yanzu ba mijin ki bane. Abinda kika fada gaskiya ne." 19 Matar tace masa, "Mallam, Na ga kai annabi ne. 20 Ubaninmu sun yi sujada a wannan dutse, amma kun ce Urushalima ce wurin da ya kamata mutane su yi sujada." 21 Yesu ya ce mata, "Mace, ki gaskata ni, cewa lokaci na zuwa wanda ba za ku yi wa Uban sujada ba ko akan wannan dutse ko a Urushalima. 22 Ku kuna bauta wa abinda ba ku sani ba. Mu muna bauta wa abinda muka sani, gama ceto daga Yahudawa yake. 23 Sai dai, sa'a tana zuwa, har ma ta yi, wadda masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a cikin ruhu da gaskiya, domin irin wadannan ne Uban ke nema su zama masu yi masa sujada. 24 Allah Ruhu ne, kuma mutanen da ke yi masa sujada, dole su yi sujada cikin ruhu da gaskiya." 25 Matar ta ce masa, "Na san Almasihu na zuwa (wanda ake kira Kristi). Sa'adda ya zo, zai bayyana mana kowane abu. 26 Yesu ya ce mata, "Ni ne shi, wanda ke yi maki magana." 27 A daidai wannan lokaci, almajiransa suka dawo. Suna ta mamakin dalilin da yasa yake magana da mace, amma babu wanda yace, "Me kake so?" Ko kuma, "Don me ka ke magana da ita?" 28 Sai matar ta bar tulunta, ta koma cikin gari, tace wa mutanen, 29 "Ku zo ku ga wani mutum wanda ya gaya mani duk wani abu da na taba yi. Wannan dai ba Almasihun bane, ko kuwa?" 30 Suka bar garin suka zo wurinsa. 31 A wannan lokacin, almajiransa suna rokansa, cewa, "Mallam, ka ci." 32 Amma ya ce masu, "ina da abinci da ba ku san komai akai ba." 33 Sai almajiran suka ce da junansu, "Babu wanda ya kawo masa wani abu ya ci, ko akwai ne?" 34 Yesu ya ce masu, "Abincina shine in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa. 35 Ba ku kan ce, 'akwai wata hudu tukuna kafin girbi ya zo ba?' Ina gaya maku, daga idanunku ku ga gonakin, sun rigaya sun isa girbi. 36 Shi wanda ke girbi yakan karbi sakamako ya kuma tattara amfanin gona zuwa rai na har abada, ta haka shi mai shuka da shi mai girbi za su yi farinciki tare. 37 Gama cikin wannan maganar take, 'Wani na shuka, wani kuma na girbi.' 38 Na aike ku ku yi girbin abinda ba ku yi aiki a kai ba. Wandansu sun yi aiki, ku kuma kun shiga cikin wahalarsu. 39 Yawancin Samariyawan da ke wannan birni suka gaskata da shi sabili da labarin matar data bada shaida, "Ya gaya mani duk abinda na taba yi." 40 To sa'adda Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roke shi ya zauna tare da su, ya kuwa zauna wurin kwana biyu. 41 Wasu da dama kuma suka gaskata domin maganarsa. 42 Suka cewa matar, "Mun bada gaskiya, ba saboda maganar ki kadai ba, amma mu kanmu munji, yanzu kuma mun sani cewa wannan lallai shine mai ceton duniya." 43 Bayan wadannan kwana biyu, ya bar wurin zuwa Galili. 44 Domin Yesu da kansa yace, ba a girmama annabi a kasarsa. 45 Da ya zo Galili, Galiliyawan suka marabce shi. Sun ga dukan abubuwan da ya yi a Urushalima wurin idin, domin su ma sun je idin. 46 Kuma ya koma Kana ta Galili inda ya mayar da ruwa zuwa ruwan inabi. Akwai wani ma'aikacin fada wanda dansa na rashin lafiya a Kafarnahum. 47 Da ya ji cewa Yesu ya bar Yahudiya ya koma Galili, sai ya tafi wurin Yesu ya roke shi ya sauko ya warka da dansa wanda ke bakin mutuwa. 48 Yesu yace masa, "Idan ba ku ga alamu da mu'ujizai ba, ba za ku gaskata ba." 49 Ma'aikacin ya ce masa, "Mallam, ka sauko kafin da na ya mutu." 50 Yesu yace masa, "Je ka. Dan ka ya rayu." Mutumin ya gaskata maganar da Yesu ya gaya masa, Sai yayi tafiyarsa. 51 Yayin da yake sauka kasa, bayinsa suka same shi, suna cewa, danka yana raye. 52 Sai ya tambaye su sa'ar da ya fara samun sauki. Suka amsa masa, "Jiya a sa'a ta bakwai zazabin ya bar shi." 53 Sai Uban ya gane cewa wannan sa'a ce Yesu ya ce masa, "Jeka, danka na raye." Sabili da haka, shi da dukan gidansa suka bada gaskiya. 54 Wannan ce alama ta biyu da Yesu ya yi bayan da ya bar Yahudiya zuwa Galili.
Yahaya 4:1-6 ya ba da bayanin abin da zai faru, maganan Yesu da ba-Samarya.
"Yanzu yesu ya na yin ... Yahaya (ko da shike ... ke), kuma Farisawa su ka ji game da ci gaban da yake yi. Ya sani cewa Farisawan sun ji, sai ya bar ... Galili"
An yi amfani da kalmar "yanzu" domin ya nuna ainahin abin da ze faru. A nan Yahaya ya fara faɗan sabon sashin bayyanin.
Maganar "kansa" ya kara bayyana cewa ba Yesu ne ya ke yin baftisma ba, amma almajiransa ne.
"Wannan ruko ne da ladabi, ba umurni ba.
Bai ce wa almajiransa su diba ma shi ruwa ba domin sun tafi.
Kalmar "masa" ya na nufin Yesu.
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya domin ya nuna mamakin ba-Samariya, cewa Yesu ya tambaye ta abin sha. AT: "Ban yarda cewa, yadda ke Bayahude, ka na tambayan abin sha ba!"
"ba ya tare da "
Yesu ya yi amfani da maganan "ruwan rai" don ya nuna Ruhu mai Tsarki wadda yake aiki a cikin mutum domin canza da kuma sabonta rayuwa.
Wannan maganan ya zo kamar tambaya domin karin bayani. AT: "Ba ku fi Uban mu Yakubu ba ... shanu!"
"kakaninmu Yakubu"
"sha ruwan da ya fito daga ita"
"ba zai sake shan ruwa kuma ba"
A nan kalmar "mabulbular" magana ne na rai da ke ba da ruwa. AT: "ruwan da zan ba shi zai zama kamar bulbular ruwa a cikinsa"
A nan "rai" ya na nufin "rai na ruhaniya" wadda Allah ne kadai zai iya ba da.
A cikin wannan lamarin, ba-Samariyar ta na kiran Yesu "Mallalm," wadda yake a matsayin biyayya ko ladabi.
"samu ruwa" ko kuma "ja ruwa daga rijiya" ta amfani da guga
Yesu ya sake nanata wannan jumala domin ya bayyana cewa ya san matan ta na faɗan gaskiya ne.
"Na iya gane cewa kai annabi ne"
"Ubaninmu" ko kuma "Kakaninmu"
gaskanta da mutum ya na nufin yarda da cewa abin da mutumin ya ce gaskiya.
Yesu ya na nufin cewa Allah ya bayyana kansa da dokokinsa wa mutanin Yahudawa, ba wa yan samariya ba. Ta wurin littafi ne mutanin Yahudawan sun san Allah da kyau fiye da yan Samariya.
Ceta na har abada daga zunubi ya na zuwa ne daga Allah Uba, wadda shi ne Yahwe, Allah Yahudawa.
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
Wannan ba ya nufin cewa mutanin Yahudawa ne za su cece sauran daga zunubinsu. Ya na nufin cewa Allah ya zabi Yahudawa a matsayin mutane wadda za su gaya wa mutane game da cetonsa. AT: "gama dukkan mutane za su san game da ceton Allah saboda Yahudawan"
Yesu ya ci gaba da magana da ba-Samariyar.
"Koda shike, yanzu ne loƙacin da ya kamata masu sujada na gaskiya su"
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
"yi masa sujada a hanya mai kyau"
Duk kalmomin nan suna nufin "sarkin da Allah ya alkawarta."
Kalmar "bayyana kowane abu" ya na nufin dukkan abin da yakamata mutane su sani. AT: "zai gaya mana kowane abu da ya kamata mu sani"
"Yayin da Yesu ya na faɗan wannan, almajiransa suka dawo daga gari"
Ba sananne abu ne ba-Yahude ya yi magana da mace da bai sani ba, har idan matan ba-Samariyar.
AT: 1) Almajiran suke yi wa Yesu tambayoyin ko kuma 2) "ba bu wadda ya tambayi matan, 'Me ... so?' ko kuma tabayi Yesu, 'Me ... ita?"
ba-Samariyar ta zuguiguita domin ta nu na cewa ta yi farinciki da yadda Yesu ya san komai game ta ita. AT: "Zo ku ga wani mutum wadda ya san ni sosai, koda shike ban san shi ba"
Matan ba ta tabatar cewa Yesu ne Almasihu, sai ta yi tambaya da ta ke tsammanin amsan "babu," amma ta sake yin tambaya a maimakon yin magana domin ta na son mutanin su zaba wa kansu.
"Loƙacin da matan ta na shigan cikin gari"
"almajiran su na gaya wa Yesu" ko kuma "almajiran su na karfafa Yesu"
A nan Yesu ba ya maganan asalin "abinci," amma ya na shirya almajiransa domin koyi ta ruhaniya a cikin 4:34.
Almajiran su na tunani ko ya na magana game da asalin abinci ne. Sun fara tambayan junansu wannan tambaya, su na sa rai da amsan "babu." AT: "hakika ba bu wadda ya kawo masa abinci a loƙacin da muke cikin gari!"
A nan "abinci" magana ce da ke wakilcin "yin biyayya da nufin Allah." AT: "Kamar yadda abinci ya ke kosad da mutum mai yunwa, biyayya da nufin Allah ne abin da ke ƙosad da ni"
"ba wannan ne wata sanannan magana ba"
Kalmomin "gonaki" da "isa girbi" zance ce. Gonakin na wakilcin mutane. Kalmar "isa girbi" ya na nufin cewa mutanin su na shirye domin su karba sakon Yesu, kamar gonaki da sun isa girbi. AT: "Dubi sama ku ga mutane! Su na a shirye don su gaskanta da sako na, kamar 'ya'ya a gonaki na da sun isa mutane su girba su"
A nan "amfanin gona zuwa rai na har abada" magana ce dake wakilcin mutane da sun gaskanta da sakon Almasihu sun kuma karbi rai na har abada. AT: "kuma mutanin da sun gaskanta da sakon sun kuma karbi rai na har abada su ne su na nan kamar amfanin gona da mai girbi yake tarawa"
Kalmomin "shuka" da kuma "girbi" zance ne. Wadda ya na "shuka" ne yake bayyana sakon Yesu. Wadda yake "girbi" ne yake taimake mutanin don su karɓi sakon Yesu. AT: "mutum ɗaya ya na shuka irin, sai kuma wani mutum yana girbe 'ya'yan"
"yanzu kana saduwa da aikinsu"
"gaskanta da" wani ya na nufin "yarda" da mutumin. A nan, wannan ya na kuma nufin gaskanta cewa shi ne Ɗan Allah.
Wannan zuguiguita ce. Matan ta ji daɗi da yadda yesu ya san game da ita. AT: "ya gaya mani abubuwa dayawa game da rayuwana"
A nan "kalma" magana ne da ke wakilcin sakon da Yesu ya faɗa. AT: "sakonsa"
"duniya" magana ne wa masubi a dukkan duniya. AT: "dukkan masubi a cikin duniya"
daga Juda
An kara kalmar "kansa" domin a bayyana cewa Yesu ya "ce" wannan ... Ku na iya fasara wannan a harshen ku a hanyar da zai bayyana wa mutum.
"mutane ba su nuna daraja ko girma wa annabin kasarsu" ko kuma "mutane ba su daraja annabi a garinsa"
A nan idin ita ce idin ketarewa.
An yi amfani da wannan kalma domin a sa alaman fashi a ainahin labarin, a kuma je wata sashin labarin. Idan ku na da wata hanyar yin wannan a harshen ku, za ku iya amfani da shi.
wanin da yake aiki wa sarki
"Sai dai ... ba za ku gaskanta ba." A wadansu harshuna, yana da kyau a fasara wannan jumla a hanya mai kyau. AT: "da ce kun ga abin al'ajibi ne da kun gaskanta"
A nan "kalma" magana ce dake nufin sakon da Yesu ya yi magana. AT: "gaskanta da sakon"
An yi amfani da wannan kalma a abubuwa biyu da ke faruwa a loƙaci ɗaya. Yayin da ma'aikacin ya na tafiya gida, bayinsa suna zuwan samin shi a hanya.
An yi amfani da kalmar "kansa" domin a bayyana kalmar "shi." Idan ku na da wata hanyar yin wannan a harshen ku, za ku iya amfani da shi.
Ana iya kiran abubuwan al'ajibi "alamu" domin su na nuna cewa Allah mai daraja ne wadda yake da cikakken iko a duniya.
Yesu ya bar Yahudiya ya koma Galili bayan ya san cewa Farisawa sun ji cewa yana samun almajirai yana kuma yi masu baftisma fiye da Yahaya.
6Rijiyar Yakubu na wurin. Da Yesu ya gaji da tafiyarsa sai ya zauna gefen rijiyar. Kusan karfe goma sha biyu na rana ne. 7Wata mace, Ba-Samariya ta zo domin ta dibi ruwa, sai Yesu ya ce mata, "Ba ni ruwa in sha." 8Gama almajiransa sun tafi cikin gari don sayen abinci.
Wata mace, Ba-Samariya ta zo domin ta dibi ruwa a wurin.
Sun tafi cikin gari don sayen abinci.
Ta yi mamaki saboda Yahudawa ba su harka da Samariyawa.
Yesu ya amsa yace mata In da ta san ƙyautar Allah, da shi wanda yake ce da ita, ba ni ruwan sha,' da kin roƙe shi, sai kuma ya ba ki ruwan rai.
Matar ta masa tace, "Mallam, ga shi ba ka da guga, kuma rijiyar tana da zurfi. Ina za ka samu ruwan rai?
Yesu ya faɗa wa matan cewa duk wanda ya sha daga wannan ruwan da zan ba shi ba zai sake jin kishi ba kuma ruwan da zan bashi zai zama mabulbular ruwa a cikinsa wanda ke bulbula zuwa rai madawwami.
Ta na son wannan ruwan don kar ta kara jin kishi kuma ba sai ta zo rijiya don diba ruwa ba.
Yesu ya ce mata, "Je, ki kira maigidanki ku zo nan tare."
Matar ta amsa tace masa, ba ta da miji
Ya ce mata ta na da mazaje har biyar, kuma wanda take da shi yanzu ba mijin ta bane.
Ta kawo garɗama game da inda ya kamata a yi sujada.
Yesu ya faɗa mata cewa Allah Ruhu ne, kuma mutanen da ke yi masa sujada, ɗole su yi sujada cikin ruhu da gaskiya.
Yesu ya faɗa mata cewa shi ne mai ceto (Almasihu).
Matar ta bar tulunta, ta koma cikin gari, tace wa mutanen, "Ku zo ku ga wani mutum wanda ya gaya mani duk wani abu da na taba yi. Wannan dai ba Almasihun bane, ko kuwa?"
Sun bar garin suka zo Yesu.
Yesu ya ce bincinsa shine ya yi nufin wanda ya aiko shi, ya kuma cika aikinsa.
Masu girbi sukan ƙarbi sakamako su kuma tattara amfanin gona zuwa rai na har abada, ta haka shi mai shuka da shi mai girbi za su yi farinciki tare.
Labarin matar da ta bada shaidar ne ta sa Yawancin Samariyawan da ke wannan birni suka gaskata da Yesu.
Sun faɗa cewa sun sani cewa Yesu lallai shine mai ceton duniya."
Sun marabce shi domin sun ga dukan abubuwan da ya yi a Urushalima wurin idin.
Akwai wani ma'aikacin da ɗansa na rashin lafiya sai ya zo wurin Yesu, ya roke shi ya sauko ya warka da ɗansa wanda ke bakin mutuwa.
Yesu ya faɗa masa cewa mutane ba za su gaskanta ba sai sun gan alamu da mu'ujizai
Mutumin ya gaskata maganar da Yesu ya gaya masa, Sai yayi tafiyarsa.
Sakamakon shi ne, babban shugaban da dukan gidansa suka bada gaskiya.
1 Bayan haka akwai idi na yahudawa, kuma Yesu ya tafi Urashalima. 2 To a cikin Urashilima kusa da kofar tumaki akwai tabki, wanda ake kira Baitasda da harshen Ibraniyanci, yana da shirayi biyar. 3 Taron mutane dayawa masu ciwo da, makafi da guragu da shanyayyu suna kwance a wurin. [1]4[2]5 Akwai wani mutum a bakin tabki yana kwance yana da rashin lafiya har shekara talatin da takwas. 6 Da Yesu ya gan shi yana kwance a wurin sai ya gane ya dade a wurin, sai ya ce masa, "Ko kana so ka warke?" 7 Sai mai rashin lafiyar ya amsa ya ce, "Malam, bani da kowa da zai sa ni a cikin tabkin idan ruwan ya motsa. Yayinda na ke kokari sai wani ya riga ni." 8 Yesu ya ce masa," Ka tashi ka dauki shimfidarka ka tafi." 9 Nan dan nan Mutumin ya warke, ya dauki shimfidarsa ya tafi. Ranar kuwa Asabar ce. 10 Sai Yahudawa suka ce da wanda aka warkar din, "Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka dauki shimfidarka ba." 11 Sai ya amsa ya ce, "Ai wanda ya warkar da ni, shine ya ce mani 'Dauki shimfidarka, ka tafi." 12 Suka tambaye shi, "wane mutum ne ya ce maka, 'Dauki shimfidar ka yi tafiya'?" 13 Sai dai, shi wanda aka warka din, ba san ko wanene ya warkar da shi ba, domin Yesu ya riga ya tafi aboye, saboda akwai taro a wurin. 14 Bayan haka, Yesu ya same shi a Haikalin, ya ce masa, "ka ga fa, ka warke. To, kada ka kara yin zunubi don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka." 15 Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahuduwa cewa Yesu ne ya warkar da shi. 16 To saboda haka Yahudawa suka fara tsanantawa Yesu, don ya yi wadannan abubuwa ran Asabar. 17 Yesu kuwa ya amsa masu ya ce, "Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki." 18 Saboda haka, Yahudawa suka kara nema su kashe shi ba don ya keta Asabar kadai ba, amma kuma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato yana maida kansa dai-dai da Allah. 19 Yesu ya amsa masu ya ce, hakika hakika, ina gaya maku, Dan ba ya yin kome shi kadai, sai abin da ya ga Uba yana yi. 20 Domin Uban na kaunar Dan, yana kuma nuna masa dukan abinda shi da kansa yake yi, kuma zai nuna masa abubuwan da suka fi wadannan, domin ku yi mamaki. 21 Gama kamar yadda Uba yakan tada matattu ya kuma basu rai, haka Dan ma yake bada rai ga duk wanda ya nufa. 22 Gama Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya damka dukan hukunci ga Dan, 23 domin kowa ya girmama Dan, kamar yadda suke girmama Uban. Shi wanda ba ya girmama Dan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi. 24 Hakika, hakika, duk mai jin Maganata, yana kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami ba kuma za a kashe shi ba, domin ya ratse daga mutuwa zuwa rai,. 25 Hakika hakika, ina gaya maku, lokaci na zuwa, har ma ya yi da matattatu za su ji muryar Dan Allah, wadanda suka ji kuwa za su rayu. 26 Kammar yada Uba ya ke da rai a cikinsa, haka ya ba Dan don ya zama da rai cikin kansa. 27 Uban ya kuma ba Dan ikon zartar da hukunci, saboda shi ne Dan Mutum. 28 Kada ku yi mamakin wannan, domin lokaci na zuwa da duk wadanda suke kaburbura za su ji muryarsa, 29 su kuma fito: wadanda suka aikata nagarta zawa tashi na rai, wadanda suka aikata mugunta kuwa zuwa tashi na hukunci. 30 Ba na iya yin kome ni da kai na. Yadda na ke ji, haka nake yin hukunci, Hukunci na kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni. 31 Idan zan yi shaida game da kaina, shaidata baza ta zama gaskiya ba. 32 Akwai wani wanda ya ke bada shaida game da ni, na kuwa sani shaidar da yake bayarwa game da ni gaskiya ce. 33 Kun aika zuwa wurin Yahaya, shi kuma ya yi shaidar gaskiya. 34 Duk da haka shaidar da na karba bata mutum bace. Na fadi wadanan abubuwa domin ku sami ceto. 35 Yahaya fitila ne mai ci, mai haske ne kuma, kun yarda ku yi farinciki da haskensa dan lokaci kadan. 36 Amma shaidar da ni ke da ita ta fi ta Yahaya karfi. Domin ayyukan da Uba ya bani ni in yi, wato ainihin ayyukan da nake yi, su ne suke shaida ta cewa, Uba ne ya aiko ni. 37 Uba wanda ya aiko ni, shi da kansa ya shaide ni. Ba ku taba jin muryar sa ba, ko ganin kamanninsa. 38 Maganarsa kuwa ba ta zaune a zuciyarku, domin baku gaskata da wanda ya aiko ni ba. 39 Kuna nazarin littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai Madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata. 40 kuma baku niyyar zuwa wurina domin ku sami rai. 41 Ba na karbar yabo daga wurin mutane, 42 amma na sani baku da kaunar Allah a zuciyarku. 43 Na zo a cikin sunan Ubana, amma ba ku karbe ni ba. Idan wani ya zo da sunan kansa, za ku karbe shi. 44 Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karban yabo daga junanku, amma ba ku neman yabon dake zuwa daga wurin Allah? 45 Kada ku yi tunani zan zarge ku a wurin Uba. Mai zargin ku shine Musa, wanda kuka sa begenku a cikin sa. 46 Inda kun gaskata Musa, da kun gaskata da ni domin ya yi rubutu game da ni. 47 Idan kuwa ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, ta yaya za ku gaskata maganata?"
Wannan ne abin da ya faru a labari na biye, wadda Yesu ya tafi Urushalima ya kuma warkad da mutum. Wadannan Ayoyin sun ba da ainahin bayani game da shirin labarin.
Wannan ya na nufin bayan Yesu ya warkad da ɗan ma'aikacin. Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 3:22
"Yahudawan su na bikin idi"
Urashalima ya na kan tudu. Hanyoyi zuwa Urashalima su na tafiya sama da kasan ƙanƙanin tudu. Idan harshen ku ta na da wata hanya dabam na tafiya a kan tudu fiye da na tafiya a kan hanya, za ku iya yin amfani da shi a nan.
Wannan rami ne wadda mutane su ke cika da ruwa. Wata loƙaci suna bin su tabkin da tiles ko da aikin duse.
sunan wuri
jinkan gini wadda bango daya ya bata kuma ya na haɗe da su gini
"mutane dayawa"
"ya na tabkin Baitasda" (John 5:1)
"shekaru talatin da takwas"
"ya fahinci"
"Yesu ya ce wa mutum da ya cakume"
A nan kalmar "Mallam" hanya ce na magana da ladabi.
AT: "loƙacin da mala'ika ya motsa ruwan"
Wannan rami ne a kasa wadda mutane su ke cika da ruwa. Wata loƙaci suna bin su tabkin da tiles ko da aikin duse. Dubi yadda kun fasara "tabkin" a cikin 5:2.
"kullum wani dabam ya na riga ni shigan cikin ruwan"
"tashi tsaye"
"ɗauki shimfidarkuanar ka, ka yi tafiya!"
"mutumin ya samu lafiya kuma"
Marubucin ya yi amfani da kalmar "yanzu" domin ya nuna cewa kalmomin na bayani ne wadda ke biye.
Yahudawa (musamman shugabanin Yahudawa) sun yi fushi a loƙacin da sun ga mutumin ya dauki shimfidarsa a ranar Asabar.
"Ranar hutun Allah ce"
"mutumin da ya sa ni lafiya"
"Shugabanin Yahudawa su ka tambaye mutumin da an warkar da shi"
"Yesu ya same mutumin da ya warkar"
An yi amfani da kalmar "Dubi" a nan domin a jawo hankali zuwa kalmomin da zai bi.
Marubucin ya yi amfani da kalmar "yanzu" don ya nuna cewa kalmomin da suke biye ne ainahin bayanin.
Wannan ya na nufin yin aiki, tare da ko wane abu da ake yi don a bauta wa mutane.
A nan "Yahudawa" magana ce da ke wakilcin "shugabanin Yahudawa." AT: "shugabanin Yahudawa"
"cewa shi kamar Allah ne" ko kuma "cewa ya na da yawan iko kamar Allah"
Wannan muhimmin lakaɓi ne wa Allah.
Yesu ya cigaba da magana da shugabanin Yahudwa.
Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 1:51
"za ku gigice"
Yesu, Ɗan Allah, ya bi shugabancin Ubansa a duniya, domin Yesu ya san cewa Uban ya na kaunarsa.
Wadannan muhimmin lakabi ne wadda ya ke kwatanta dangantaka sakanin Yesu da Allah.
Irin kauna da ya ke zuwa daga Allah ya na duba kirkin wadansu, ko a loƙacin da bai amfane ku ba. Allah da kansa kauna ne kuma shi ne tushen kauna.
Wadannan muhimmin lakaɓi ne wadda ya ke kwatanta dangantaka sakanin Yesu da Allah.
Wannan ya na nufin "rai na ruhaniya."
Kalmar "gama" ya na nuna kwatanci. Ɗan Allah ya na yin hukunci wa Allah Uba.
Dole a girmama a kuma yabe Allah Ɗa kamar Allah Uba. Idan mun kasa girmama Allah Ɗa, to mun kuma kasa girmama Allah Uba.
A nan "magana" zance ne da ke wakilcin sakon Yesu. AT: "duk wanda ya ji sako na"
AT: "za a sharanta shi ya zama da gaskiya"
Muryar Yesu, Ɗan Allah, zai ta da matattu daga kabari.
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
Kalmar "gama" ya na nuna kwatanci. Ɗan Allah ya na da ikon ba da rai, kamar yadda Uban yake.
Wadannan muhimmin lakaɓi ne wadda ya ke kwatanta dangantaka sakanin Yesu da Allah.
Ɗan Allah ya na da ikon Allah Uba don ya yi hukunci.
"Wannan" ya nufin cewa Yesu, Ɗan Mutum, ya na da ikon ba da rai na har abada da kuma yin hukunci.
"ji murya na"
Kalmar "shi" ya na nufin Allah Uba.
Akwai wani kuma wanda ya na gaya wa mutane game da ni"
Wannan ya na nufin Allah.
"abin da ya ke gaya wa mutane game da ni gaskiya ne"
"ba na son shaidar mutum"
AT: "don Allah ya cece ku"
A nan "fitila" da "haske" zance ne. Yahaya ya koya wa mutanin game da Allah kuma wannan ya na nan kamar fitilar da yake haskaka haskensa a cikin duhu. AT: "Yahaya ya koya maku game da Allah kuma wannan ya na nan kamar fitila da ya ke haskaka haskensa. Abin da Yahaya ya ce a dan loƙaci kadan ne ya sa ku murna"
Allah Uba ya aiko Allah Ɗan, Yesu, a duniya. Yesu ya cika abin da Uban ya ba shi ya yi.
Kalmar "kansa" ya na bayyana cewa Uban ne, ba wani ne da kankancin muhimmi ne wadda ya shaida ba.
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
" baku gaskanta da wanda ya aiko ni ba. Haka ne na san cewa ba ku da maganarsa a cikinku"
Yesu ya yi magana game da yadda mutane suke rayuwa bisa maganar Allah kamar gidaje da kuma maganar Allah kamar mutum da ya ke zama a cikin gidaje. AT: "Ba ku rayuwa bisa maganarsa" ko kuma "ba ku biyayya da maganarsa"
"sakon da ya gaya maku"
"za ku samu rai madawwami idan kun karantasu" ko kuma "littafi zai gaya ma ku yadda za ku samu rai madawwami"
"kun ki ku gaskanta da sako na"
amsa
AT: 1) "ba ku kaunar Allah" ko kuma 2) "ba ku karbi kaunar Allah ba."
A nan kalmar "suna" magana ne da ke nuna ikon Allah. AT: "Na zo da ikon Ubana"
Kalmar "suna" magana ne da ke wakilcin iko. AT: "idan wani ya zo a ikonsa"
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya domin karin nanaci. AT: "Ba yanda za ku gaskanta domin kun karbi yabo ... Allah!"
Wannan ya na nufin gaskanta da Yesu.
"Musa" a nan magana ne na doka da kansa. AT: "Musa ya yi zargin ku a cikin doka, doka da kun sa begenku"
"amincewar ku" ko kuma "gaskantawar ku"
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya domin karin nanata. AT: "ba ku gaskanta da rubutun shi ba, don haka ba za ku taba gaskanta da maganganuta ba!"
"abin da na faɗa"
Ana kira wannan tabkin Baitasda.
Taron mutane dayawa masu ciwo da, makafi da guragu da shanyayyu suna kwance a wurin.
Yesu ya tambaye wani mutum mai rashin lafiya har shekara talatin da takwas kuma ya daɗe yana kwance a wurin.
Mai rashin lafiyar ya amsa ya ce, "Malam, bani da kowa da zai sa ni a cikin tabkin idan ruwan ya motsa. Yayinda na ke kokari sai wani ya riga ni."
Nan dan nan Mutumin ya warke, ya ɗauki shimfidarsa ya yi tafiya.
10Sai Yahudawa suka ce da wanda aka warkar din, "Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka dauki shimfidarka ba." 11Sai ya amsa ya ce, "Ai wanda ya warkar da ni, shine ya ce mani 'Dauki shimfidarka, ka tafi." Ya dame su domin ranar Asabar ne kuma sun ce ba halatta ya ɗauki shimfidarsa a ranar Asabar ba.
Yesu ya ce masa, "ka ga fa, ka warke. To, kada ka kara yin zunubi don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka."
Mutumin ya tafi ya gaya wa Yahuduwa cewa Yesu ne ya warkar da shi.
Yesu ya ce masu, "Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki."
Wannan ya faru ne domin Yesu bai keta Asabar kadai (a zuciyarsu) ba amma ya ce Allah Ubansa ne, wato yana maida kansa dai-dai da Allah.
Ya yi abin da ya ga Uban na yi.
Uban zai nuna masa dukan abinda shi da kansa yake yi, kuma zai nuna masa abubuwan da suka fi waɗannan, domin Shugabanin Yahudawa su yi mamaki.
Uban ya ba da dukan hukunci wa Ɗan domin kowa ya girmama Ɗan, kamar yadda suke girmama Uban.
Idan ba ka ɗaukaka Ɗan ba, ba ka ɗaukaka Uban da ya aiko shi.
Idan haka ne, kana da rai madawwami ba kuma za a kashe ka ba, domin ya ratse daga mutuwa zuwa rai.
Uba ya ba Ɗan don ya zama da rai cikin kansa.
Za su fito. Waɗanda suka aikata nagarta zawa tashi na rai, waɗanda suka aikata mugunta kuwa zuwa tashi na hukunci.
Hukuncinsa adalci ne saboda ba nufin kainsa yake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko shii.
Ayukan da yesu ya yi ya shaida cewa an aiko shi daga Uban.
Shugabanin Yahudawa ba su taba jin muryarsa ko gan kamaninsa ba.
Nassin na shaida game da Yesu.
Sun yi nazarin domin suna tsammanin cewa a cikinsu za su sami rai Madawwami.
Ba su neman yaɓon dake zuwa daga wurin Allah.
Musa na zai yi zargin shugabanin Yahudawa a gaban Uban.
Yesu ya ce shugabanin Yahudawan za su gaskata da shi domin Musa ya yi rubutu game da shi ne.
1 Bayan waddannan abubuwa, Yesu ya ketare tekun Galili, wanda a ke kira tekun Tibariya. 2 Sai taro mai yawa suka bi shi domin suna ganin alamu da yake yi akan marasa lafiya. 3 Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa. 4 (Kuma da idin Ketarewa, wato idin Yahudawa, ya kusato.) 5 Da Yesu ya daga kai sai ya ga babban taro yana zuwa wurinsa, sai ya ce ma Filibus, "Ina za mu sayi gurasar da Mutanen nan za su ci?" 6 (Ya fadi haka ne domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi.) 7 Filibus ya amsa masa, "gurasar dinari biyu ma ba zata ishi kowannensu ya samu ko kadan ba." 8 Daya daga cikin almajiransa, wato Andarawus, dan'uwan Siman Bitrus, ya ce masa, 9 "Ga wani dan yaro nan da dunkule biyar na sha'ir, da kifi biyu. Amma menene wadannan za su yi wa mutane masu yawa?" 10 Yesu ya ce, "ku sa mutane su zauna."( wurin kuwa akwai ciyawa.) Sai mazajen suka zauna, sun kai wajen dubu biyar. 11 Sai Yesu ya dauki gurasar, bayan da ya yi godiya, sai ya rarraba wa wadanda suke zaune. Haka kuma ya rarraba kifin gwargwadon abin da zai ishe su. 12 Da Mutanen suka ci suka kuma koshi, sai ya ce wa almajiransa, ku tattara gutsattsarin da suka rage, kada ya zama asara." 13 Sai suka cika kwanduna goma sha biyu da gutsattsarin gurasar nan biyar da ya rage bayan da kowa ya ci. 14 Da jama'a suka ga alamar da ya yi, sai suka ce, "Hakika wannan shi ne annabin nan mai zuwa cikin duniya. 15 "Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su dauke shi da karfi da yaji su nada shi sarki, sai ya sake komawa kan dutsen da kansa. 16 Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara teku. 17 Suka shiga cikin jirgi, suka haye teku zuwa kafarnahum. (A lokacin duhu ya yi, Yesu kuwa bai riga ya iso wurinsu ba tukuna.) 18 Iska mai karfin gaske tana kadawa, kuma tekun yana hargowa. 19 Bayan da almajiran suka yi tuki na wajen kimanin mil ashirin da biyar ko talatin, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan teku ya kuma kusa da jirgin, sai suka firgita. 20 Amma ya ce masu, "Ni ne! kada ku firgita." 21 Sa'an nan suka yarda suka karbe shi a cikin jirgin, kuma nan da nan jirgin ya kai gacci. 22 Kashe gari, sauran taron da suke tsaye a dayan hayin tekun suka ga cewa babu wani jirgi a wajen sai dayan, Yesu kuma bai shiga ciki da almajiransa ba, amma almajiransa suka tafi su kadai. 23 Sai dai, akwai wadansu jirage da suka zo daga Tibariya kusa da wurin da taron suka ci gurasa bayan da Ubangiji ya yi godiya. 24 Sa'anda taron suka gane cewa Yesu da almajiransa ba su wurin, su da kansu su ka shiga cikin jiragen suka tafi Kafarnahum neman Yesu. 25 Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, "Mallam, yaushe ka zo nan?" 26 Yesu ya amsa masu, da cewa, "hakika, kuna nema na ne, ba don kun ga alamu ba, amma domin kun ci gurasar nan kun koshi. 27 Ku daina yin wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama wanda zai kaiku ga rai madawwami wanda Dan Mutum zai ba ku, domin Ubangiji Allah ya sa hatiminsa a kansa." 28 Sai suka ce Masa, "Me za mu yi, domin mu aikata ayyukan Allah? 29 Yesu ya amsa, "Wannan shi ne aikin Allah: wato ku gaskata da wanda ya aiko." 30 Sai suka ce masa, "To wace alama za ka yi, don mu gani mu gaskata ka? 31 Me za ka yi? Kakanninmu sun ci manna a jeji, kamar yadda aka rubuta, "Ya ba su gurasa daga sama su ci." 32 Sa'an nan Yesu ya ce masu, "hakika, hakika, ina gaya maku ba Musa ne ya ba ku gurasa nan daga sama ba, amma Ubana ne ya baku gurasa ta gaskiya daga sama. 33 Gurasar Allah itace mai saukowa daga sama mai kuma bada rai ga duniya," 34 Sai suka ce masa, "Mallam, ka rika ba mu irin wannan gurasa kodayaushe." 35 Yesu ya ce masu, "Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo wurina ba zai ji yunwa ba, wanda kuma ya gaskanta da ni ba zai kara jin kishi ba. 36 Amma na gaya maku cewa, hakika kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba. 37 Duk wanda Uba ya bani zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kadan. 38 Gama na sauko daga sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni. 39 Wannan shi ne nufin wanda ya aiko ni, kada in rasa ko daya daga cikin wadannan da ya bani, sai dai in tashe su a ranar karshe. 40 Gama wannan shi ne nufin Ubana, duk wanda yake ganin Dan ya kuma gaskata da shi zai sami rai madawwami, ni kuma zan tashe shi a ranar karshe. 41 Sai Yahudawa suka yi gunaguni akansa, domin ya ce, "Nine Gurasar da ta sauko daga sama." 42 Suka ce, "Ba wannan ne Yesu Dan Yusufu, wanda Ubansa da Uwarsa mun san su ba? Ta yaya yanzu zai ce, 'Na ya sauko daga sama'? 43 Yesu ya amsa, ya ce masu, "Kada ku yi gunaguni a junanku. 44 Ba mai iya zuwa wurina sai dai in Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta karshe. 45 A rubuce yake cikin litattafan anabawa cewa, 'Dukkansu Allah zai koya masu'. Duk wanda ya ji ya kuma koya daga wurin Uba, ya kan zo gare ni. 46 Ba cewa wani ya taba ganin Uban ba, sai shi wanda yake daga wurin Allah - shine ya ga Uban. 47 Hakika, hakika, wanda ya bada gaskiya, yana da rai Madawwami. 48 Ni ne Gurasa ta rai. 49 Ubanninku sun ci manna cikin jeji, suka kuma mutu. 50 Ga gurasa da ta sauko daga sama, domin mutum ya ci daga cikinta ba kuwa zai mutu ba. 51 Ni ne gurasa mai rai da ya sauko daga sama. Duk wanda ya ci daga gurasar, zai rayu har abada. Wannan gurasar da zan bayar jiki na ne don ceton duniya." 52 Sai Yahudawa suka fusata a tsakanin junansu suka kuma fara gardama, cewa, "Yaya mutumin nan zai iya bamu naman jikinsa mu ci? 53 Sai Yesu ya ce masu, "hakika, hakika, in ba ku ci naman jikin Dan mutum ba, ba ku kuma sha jininsa ba, ba za ku sami rai a cikin ku ba. 54 Dukan wanda ya ci nama na ya kuma sha jinina yana da rai Madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar karshe. 55 Domin namana abinci ne na gaske, jinina kuma abin sha ne na gaskiya. 56 Duk wanda ya ci namana, ya kuma sha jinina yana zamne a ciki na, ni kuma a cikinsa. 57 Kamar yadda rayayyen Uba ya aiko ni, nake kuma rayuwa saboda Uban, haka ma wanda ya ci namana, zai rayu sabo da ni. 58 Wannan itace gurasar da ta sauko daga sama, ba irin wadda Ubanninku suka ci suka mutu ba. Dukan wanda ya ci gurasar zai rayu har abada." 59 Yesu ya fadi wadan nan abubuwa a cikin majami'a sa'ad da yake koyarwa a Kafarnahum. 60 Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, "Wannan Magana yana da karfi, wa zai iya jinta?" 61 Yesu, kuwa da yake ya sani a ransa da cewa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce masu, "Wannan ya zamar maku laifi? 62 Yaya Ke nan in kun ga Dan Mutum yana hawa inda yake a da? 63 Ruhu shine mai bayar da rai; Jiki ba ya amfana komai. Kalmomin da na fada maku ruhu ne, da kuma rai. 64 Amma fa akwai wadansun ku da ba su ba da gaskiya ba. Domin tun farko Yesu ya san wadanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bashe shi. 65 Ya fada cewa, "shiyasa na gaya maku, ba mai iya zuwa wurina, sai ta wurin Uban." 66 Bayan haka, da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su kara tafiya tare da shi ba. 67 Sai Yesu ya ce wa goma sha biyun, "ku ba kwa so ku tafi, ko ba haka ba? 68 Bitrus ya amsa masa ya ce, "Ya Ubangiji, gun wa za mu je? kai kake da maganar rai madawwami. 69 Mu kwa mun gaskata mun kuma sani kai ne mai tsarkin nan na Allah." 70 Yesu ya ce masu, "Ba ni na zabe ku, goma sha biyu ba, amma dayanku Iblis ne?" 71 Wato yana magana akan Yahuda dan Siman Iskariyoti, shi kuwa daya daga cikin sha-biyun ne, wanda zai ba da Yesu.
Yesu ya yi tafiya daga Urushalima zuwa Galili. Taru suka bi shi zuwa saman dutse. Waɗɗannan Aya suna faɗan shirin wannan sashin labarin.
Jumlan "waɗɗannan abubuwa" ya na nufin abubuwan da ya faru a cikin 5:1-46 ya kuma gabatar da abin da zai faru a gaba.
Ya nuna a cikin littafin cewa Yesu ya yi tafiya a kwalekwale ya kuma dauki al'majiransa tare da shi. AT: "Yesu ya yi tafiya da al'majirinsa a kwalekwale"
"mutane da yawa"
Wannan ya na nufin abubuwan al'ajibi da an yi amfani a matsayin shaida cewa Allah ne mai iko wadda ya ke da cikakken iko a komai.
Yahaya ya daina faɗa wa mutane game da abin da zai faru a labarin domin ya ba da tushin bayani game da loƙacin da abin ya faru.
Yahaya ya daina faɗa wa mutane game da abin da zai faru a labarin domin ya bayyana dalilin da Yesu ya tambaye Filibus wurin da za a saya burodi.
Kalmar "kansa" ya bayyana cewa kalmar "shi" ya na nufin Yesu. Yesu ya san abin da zai yi.
Kalmar "dinari" da ya ne da "su dinari." AT: "kuɗin burodi da ya kai kuɗin aikin kuanaki dari"
"dunƙule biyar na sha'ir." Sha'ir sananne abinci ne.
Ana gasa dunƙulan burodi da ya na da siffa. Mai yiwuwa kananan mulmulallen dunƙule ne.
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nanata cewa ba su da abinci da za su ciyad da kowa. AT: "wadannan dunƙule da kifi ba za su isa a ciyad da mutane dayawa ba!"
"kwanta"
Yahaya ya daina faɗa wa mutane game da abin da zai faru a labarin domin ya ba da tushen bayani game da wurin da abin ya faru.
Bayan mai yiwuwa taron ta shafi mata da 'ya'ya 6:4-5, Yahaya ya na kirga mazaje na kadai anan.
Yesu ya yi addu'a wa Allah Uba, ya kuma gode masa da kifi da kuma su dunƙule.
a nan "ya" yana wakilcin "Yesu da al'majiransa." AT: "Yesu da al'majiransa su ka ba da shi"
"al'majiran sun tara"
abincin da ba wadda ya taba ci
Ciyad da mutane dubu biyar da dunƙule da kuma kifi biyu da Yesu ya yi
annabin na musamman da Musa ya ce zai zo cikin duniya.
Wannan ne abu na biye a cikin labarin. Al'majiran Yesu sun fita zuwa rafi a cikin kwalekwale.
Yi amfani da yadda harshenku ya na nuna cewa wannan ne tushen bayani.
Kwalekwale ya na yawan kasance da mutane biyu, hudu, ko shida da suke tuki da matuki a kowane gefe. Al'adunku na iya samu hanya dabam na sa kwalekwale ya haye ruwa.
"filin wasanni" na da tsawo 185. AT: "wajen mita biyar ko shida"
"daina jin tsoro!"
Wannan ya na nufin cewa Yesu ya shiga cikin kwalekwale. AT: "sun karbe shi zuwa cikin kwalekwale da farinciki"
"Tekun Galili"
Yi amfani da yadda harshen ku ya ke nuna cewa wannan ne tushen bayani.
A nan, Yahaya ya kara ba da tushen bayani. Washegari, bayan Yesu ya ciyad da mutane, wadansu jirage da mutane daga Tibariya sun zo su ga Yesu. Ko da shike, Yesu da al'majiransa sun tafi a cikin daren.
Dubi yadda an fasara wannan a cikin 1:51.
Allah Uba ya ba da izini wa Yesu, Ɗan Mutum, don ya ba da rai madawwami ga wanda sun gaskanta da shi.
Waddannan muhimmin laƙani ne da ya ke kwatanta dangantaka a sakanin Yesu da Allah.
"sa hatimi" a abu ya nufin saka alama don ya nuna mai shi. Wannan ya na nufin cewa Ɗan na Uban ne kuma Uban ya yarda da shi a komai.
"Kakanninmu"
Wannan ya na nufin wurin da Allah ya ke.
" gurasa ta gaskiya" magana ce game da Yesu. AT: "Uban ya na ba ku Ɗan a matsayin gurasa ta gaskiya daga sama"
Wannan muhimmin laƙani ne wa Allah.
"ba da rai na ruhaniya ga duniya"
A nan "duniya" magana ne na dukkan mutane da suke gaskanta da Yesu.
Yesu ya kwatanta kansa da gurasa ta wurin gurasan. Kamar yadda gurasa ya na da amfani a rayuwa, Yesu ya na da amfani don rai na ruhaniyar mu. AT: "Kamar yadda abinci yake sa ku rayu, Zan iya ba ku rai ta ruhaniya"
Wannan ya na nufin gaskanta cewa Yesu ne Ɗan Allah, yarda da cewa shi ne mai ceto, da kuma yi rayuwa a hanyar da zai girmama shi.
Allah Uba da kuma Allah Ɗa zai cece wadda sun gaskanta da shi har abada.
Wannan muhimmin laƙani ne wa Allah.
Wannan Jumla ya bayyana abin da ba shi ne yake nufi ba domin nanaci. AT: "Zan ajiye duk wanda ya zo wuri na"
"Uba na, wadda ya aiko ni"
An yi amfani da karin magana domin a bayyana cewa Yesu zai ajiye duk wadda Allah ya ba shi. AT: "In ajiye dukkansu"
A nan tashi karin magana ne na sa mutumin da ya mutu ya kuma rayu kuma. AT: "zan sa su su rayu kuma"
yi magana da rashin farinciki
Kamar yadda gurasa na da amfani a rain mu, haka ne Yesu ya na da amfanai a rai na ruhaniyarmu. Dubi yadda an fasara wannan a cikin 6:35. AT: "Ni ne wadda yake kamar gurasan gaskiya"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya bayana cewa shugabanin Yahudawa ba su yarda cewa Yesu dabam ba ne ba. AT: "Wannan Yesu ne, dan Yusuf, wadda Ubansa da Uwarsa mun sani!
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya bayana cewa shugabanin Yahudawa ba su yarda cewa Yesu ya zo daga sama ba. AT: "Ya na karya ne a lokacin da ya ce ya zo daga sama!"
Wannan karin magana ne. AT: "sa shi ya rayu kuma"
AT: 1) "ja 2) "jawo hankali."
AT: "annabawan sun rubuta"
Yahudawa su na zato cewa Yesu "ɗan Yusuf ne" (See: John 6:42, amma shi ne Ɗan Allah saboda Uban shi ne Allah, ba Yusuf ba. Waddanda sun koya daga Allah Uba sun gaskanta da Yesu, wadda shi ne Allah Ɗa.
Ko da shike ba bu mutum da ke raye a duniya da ya ga Allah Uba, Yesu, Ɗan Allah, ya gan Uban.
Allah ya na ba da "rai Madawwami" ga wadda sun gaskanta da Yesu, Ɗan Allah.
"Kakanninku"
Wannan ya na nufin asalin mutuwa.
A nan "gurasa" magana ne da ya ke nuna Yesu wadda shi ne mai ba da rai na ruhaniya kamar yadda gurasa ya na rike rai. AT: "Ina nan kamar gurasar gaskiya"
"rayu har abada." A nan kalmar "mutu"ya na nufin mutuwa ta ruhaniya.
Wannan ya na nufin "gurasa da ya ke sa mutane su rayu" (John 6:35).
A nan "duniya" magana ne da ke wakilcin rayuwar dukkan mutane a cikin duniya. AT: "cewa zai ba da rai ga dukkan mutane a cikin duniya"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya bayyana cewa shugabanin Yahudawa ba su yarda da abin da Yesu ya ce game da "namansa" ba. AT: "Ba bu yadda wannan mutum zai ba mu namansa mu ci!"
A nan su jumlolin "ci nama" da " sha jinina" karin magana ne da ya ke nuna yadda gaskanta da Yesu, Ɗan Mutum, yake kamar karban abinci da ruwa na ruhaniya. AT: "karɓa Ɗan Mutum kamar yadda ku na karɓan abinci da ruwa"
"ba za ku karɓi rai na har abada ba"
Su jumlan "ci nama" da " sha jinina" karin magana ne. Kamar yadda wani ya na son abinci da ruwa domin ya samu rai, waddanda sun gaskanta da Yesu za su samu rai na ruhaniya. AT: "Duk wanda ya gaskanta da ni don abincin ruhaniyarsu da kuma ruwa za su samu rai na har abada"
"a ranar da Allah zai hukunta kowa"
Kalmomin "abinci ne na gaske" da kuma "sha ne na gaskiya" maganganu ne da yake nufin cewa Yesu ya tanada abincin ruhaniya da ruwan sha wa waddanda sun gaskanta da shi. Karban Yesu a bangaskiya ya na tanada rai na har abada kamar yadda abinci da ruwan sha ya ke amfana jiki. AT: "Ni ce abincin ruhaniya ta gaskiya da kuma ruwan sha"
"na da dangantaka na kusa da ni"
"wadda ya gaskanta da ni"
AT: 1) "Uban da yake ba da rai" ko kuma 2) "Uban da yake rayayye."
"Gurasan" misali ne wa Yesu, wadda ya zo daga sama. AT: "Ina nan kamar gurasa da ya zo daga sama"
Wannan zance ce. Wadda sun yarda da Yesu domin rai na ruhaniyarsu suna nan kamar wadda suke dogara a kan gurasa ko abinci don rayuwarsu. AT: "Duk wadda ya yarda da ni"
"kakanin"
A nan Yahaya ya ba da tushen bayani game da loƙacin da abin ya faru.
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya domin ya bayana cewa al'majiran sun sha wuyan fahimtar abin da Yesu ya faɗa. AT: "ba bu wadda zai karbe shi!" ko kuma "ya na da wuyan ganewa!"
"Wannan ya ba ku mamaki?" ko kuma "Wannan ya dame ku?"
Yesu ya ba da wannan magana a matsayin tambaya domin ya bayyana cewa al'majiransa za su ga wadansu abubuwa da suke da wuyan fahimta. AT: "Sai ba za ku san abin da za ku yi tunani ba a loƙacin da kun gan ni, Ɗan Mutum, hawa cikin sama!"
Kalmar "amfana" ya na nufin sa abubuwa masu kyau su faru.
AT: 1)kalmomin Yesu a cikin 6:32-58 ko kuma 2) komai da Yesu ya koyar.
"Abin da na faɗa maku"
AT:1) "na game da Ruhu da kuma rai na har abada" ko kuma 2) "na daga Ruhu kuma su na ba da rai" ko kuma 3) "na game da abubuwan ruhaniya da rai."
A nan Yahaya ya ba da tushen bayani game da abin da Yesu ya san zai faru.
Dole ne duk wadda yake so ya gaskanta ya zo wurin Allah ta Ɗan. Allah Uba ne kadai ya na yarda mutane su zo wurin Yesu.
"bi ni ku kuma karbi rai na har abada"
Muhimmin Bayani:
Yesu ya tafi wurare da kafa, gaskiya ne cewa ba su yi tafiya a wurin da ya tafiya ba, amma mai sauraran ya gane cewa wannan magana ya na nuna cewa bai so a ji abin ya ke so ya faɗa ba.
Siman Bitrus ya ba da wannan magana a matsayin tambaya domin ya bayyana cewa ya na so ya bi Yesu kadai. AT: "Ubangiji, ba za mu iya bin wanna ba sai kai!"
A nan "al'majiransa" ya na nufin muhimmin kungiyar mutane da sun bi Yesu.
Wannan bayani ne na "al'majira sha biyun," takamaiman mutane sha biyu da sun bi Yesu don hidimarsa. "al'majira sha biyun"
Yesu ya ba da wannan magana a matsayin tambaya domin ya jawo hankali ga cewa ɗaya daga cikin al'majiransa zai bashe shi. AT: "Na zabe ku da kaina, da haka wani a cikinku bawan shaidan nen!"
Ana kiran Tekun Galili, Tekun Tibariya.
Suna bin shin domin suna ganin alamu da yake yi akan marasa lafiya.
Ya ga babban taro suna zuwa wurinsa.
Yesu ya faɗa wannan domin ya gwada Filibus ne.
Filibus ya amsa masa, "gurasar dinari biyu ma ba zata isa kowannensu har ya samu ko kadan ba."
Andarawus ya ce, "Ga wani ɗan yaro nan da dunkule biyar na sha'ir, da kifi biyu, mma menene waɗannan za su yi wa mutane masu yawa?"
A kwai mutane kusan dubu biyar a wurin.
1Sai Yesu ya ɗauki gurasar, bayan da ya yi godiya, sai ya rarraba wa waɗanda suke zaune. Haka kuma ya rarraba kifin.
Sun samu daidan yadda sun so su ci.
Almajiran suka cika kwanduna goma sha biyu da gutsattsarin gurasar nan biyar da ya rage bayan da kowa ya ci.
Yesu ya sake komawa kan dutsen da kansa domin ya gane cewa bayan mutanen sun gan abin al'ajibi da ya yi (ciyar da wajen dubu biyar) suna shirin zuwa su ɗauke shi da karfi da yaji su nada shi sarki.
Iska mai karfin gaske tana kadawa, kuma tekun ya fara hargowa.
Sun ji tsoro domin sun gan Yesu yana tafiya a kan teku ya na kuma zuwa kusa da jirgin.
Yesu ya ce masu, "Ni ne! kada ku ji tsoro."
26Yesu ya suna nema sa ne, ba don sun ga alamu ba, amma domin sun ci gurasar nan sun kuma koshi.
Yesu ya ce masu su daina yin wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama wanda zai kaiku ga rai madawwami.
Yesu ya ce ma taron, "Wannan shi ne aikin Allah: wato ku gaskata da wanda ya aiko."
Yesu ya ce shi ne gurasar rai.
Duk wanda Uba ya ba Yesu zai zo gare ni.
Nufin Uban shine kada Yesu ya rasa ko ɗaya daga cikin waɗannan da Uban ya bashi kuma duk wanda ya gan Dan ya kuma gaskata da shi zai sami rai madawwami, ni kuma zan tashe shi a ranar karshe.
Mutum zai iya zuwa wurin Yesu idan Uba wanda ya aiko shi ya jawo sh.
Wanda yake daga wurin Allah - shine ya ga Uban.
Gurasar da Yesu zai bayar jikinsa ne don ceton duniya.
Saboda mu sami rai a cikin mu, ɗole mu ci naman jikin Dan mutum, mu kuma sha jininsa.
Idan mun ci namasa, mun kuma sha jininsa, za mu zauna a cikinsa shi kuma a cikinmu.
Yesu ya na rayuwa saboda Uban.
Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, "Wannan Magana yana da karfi, wa zai iya jinta?" Bayan wannan, yawancin almajiran sun koma sun kuma daina yi masa aiki.
Tun farko Yesu ya san waɗanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bashe shi.
Siman Bitrus ya amsa masa ya ce, "Ya Ubangiji, gun wa za mu je? kai kake da maganar rai madawwami. kuma mun gaskata mun kuma sani kai ne mai tsarkin nan na Allah.
Yesu na maganar Yahuda ɗan Siman Iskariyoti, shi kuwa ɗaya daga cikin sha-biyun ne, wanda zai ba da Yesu.
1 Bayan wadannan abubuwa Yesu ya zagaya cikin Gallili, saboda baya so ya shiga cikin Yahudiya domin Yahudawa suna shirin su kashe shi. 2 To Idin Bukkoki na Yahudawa ya kusa. 3 Sai 'yan'uwansa suka ce da shi, "ka tashi ka tafi Yahudiya, domin almajiranka su ga ayyukan da kake yi su ma. 4 Ba wanda ya ke yin wani abu a boye idan dai yana so kowa da kowa ya san shi. Da yake ka na yin wadannan abubuwa sai ka nuna kan ka a fili ga duniya. 5 Domin ko 'yan'uwansa ma basu bada gaskiya gare shi ba. 6 Yesu ya ce dasu, "lokaci na bai yi ba tukuna, amma ku koyaushe lokacin ku ne. 7 Duniya baza ta iya kin ku ba, amma ta ki ni saboda ina fadin cewa ayyukanta ba su da kyau. 8 Ku ku je wurin idin, ni ba zan je wurin idin ba domin lokacina bai yi ba tukuna. 9 Bayan da ya gaya masu wadannan abubuwa, ya tsaya a cikin Gallili. 10 Amma bayan da 'yan'uwansa su ka tafi wurin idin shi ma ya tafi, amma a asirce ba a fili ba. 11 Saboda Yahudawa suna neman sa a wurin idin, su na cewa "Ina yake?" 12 Akwai maganganu dayawa a kansa cikin taron. Wadansu suna cewa, "shi mutumin kirki ne." Wadansu kuma suna cewa,"A'a yana karkatar da hankalin jama'a." 13 Amma duk da haka ba wanda ya yi magana a fili a kansa saboda suna jin tsoron Yahudawa. 14 Sa'anda aka kai rabin idin, sai Yesu ya shiga cikin haikali ya fara koyarwa. 15 Yahudawa suna mamaki suna cewa,"Yaya aka yi wannan mutum ya sami ilimi dayawa haka? Shi kuwa bai je makaranta ba." 16 Yesu ya ba su amsa ya ce,"Koyarwata ba tawa ba ce, amma ta wanda ya aiko ni ce." 17 Idan wani yana so ya yi nufinsa, za ya gane koyarwannan ko daga wurin Allah ta zo, ko ko tawa ce ta kaina. 18 Ko wanene yake maganar kansa, yana neman darajar kansa kenan, amma ko wanene ya nemi darajar wanda ya aiko ni, wannan mutum mai gaskiya ne, babu rashin adalci a cikin sa. 19 Ba Musa ya baku dokoki ba? Amma duk da haka ba mai aikata dokokin. Me yasa ku ke so ku kashe ni? 20 Taron suka ba shi amsa, "Ka na da aljani. Wanene yake so ya kashe ka?" 21 Yesu ya amsa ya ce masu, "Nayi aiki daya, dukan ku kuna mamaki da shi. 22 Musa ya baku kaciya, {ba kuwa daga Musa take ba, amma daga kakannin kakanni ta ke}, kuma a ranar Asabar kukan yi wa mutum kaciya. 23 Idan mutum ya karbi kaciya ranar Asabar, domin kada a karya dokar Musa, don me kuka ji haushi na saboda na mai da mutum lafiyayye sarai ranar Asabar? 24 Kada ku yi shari'a ta ganin ido, amma ku yi shari'a mai adalci." 25 Wadansun su daga Urushalima suka ce, "wannan ba shine wannan da suke nema su kashe ba?" 26 Kuma duba, yana magana a fili, sannan ba wanda ya ce da shi komai. Ba zai yiwu ba mahukunta su sani cewa wannan Kristi ne, ko ba haka ba? 27 da haka, mun san inda wannan mutum ya fito. Amma sa'anda Kristi za ya zo, ba wanda zai san inda ya fito." 28 Yesu yayi magana da karfi a haikali, yana koyarwa ya na cewa, "Kun san ni kuma kun san inda na fito. Ban zo domin kaina ba, amma wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, ku kuwa baku san shi ba. 29 Ni na san shi domin daga wurinsa na fito, kuma shine ya aiko ni." 30 Suna kokari su kama shi, amma ba wanda ya iya sa masa hannu domin sa'arsa ba ta yi ba tukuna. 31 Duk da haka wadansu dayawa a cikin taron suka bada gaskiya gare shi suka ce,"Sa'anda Kristi ya zo, zai yi alamu fiye da wadanda wannan mutum ya yi?" 32 Farisawa suka ji tattarmukan suna yin rada a kan wadannan abubuwa game da Yesu, Sai manyan malamai da Farisawa su ka aika jami'ai su kama shi. 33 Sa'annan Yesu yace ma su," jimawa kadan ina tare ku, sa'annan in tafi wurin wanda ya aiko ni. 34 Za ku neme ni ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba." 35 Yahudawa fa su ka cewa junan su, "Ina wannan mutum zai je inda ba za mu iya samun sa ba? Ko za ya tafi wurin Helinawa na warwatsuwa ya koyawa Helinawa? 36 Wace kalma ya ke fadi haka, 'za ku neme ni amma ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba'?" 37 To a rana ta karshe, babbar rana ta idin, Yesu ya mike ya yi magana da karfi cewa, "Idan kowa yana jin kishi, ya zo wuri na ya sha. 38 Shi wanda ya bada gaskiya gare ni kamar yadda nassi ya fadi, daga cikin sa rafukan ruwa na rai za su bulbulo." 39 Amma ya fadi haka a kan Ruhu, wanda wadanda suka bada gaskiya gare shi za su karba; ba a ba da Ruhun ba tukuna, saboda ba a rigaya an daukaka Yesu ba. 40 Wadansu a cikin taron, sa'anda suka ji wadannan kalmomi, suka ce, "Wannan lallai annabi ne." 41 Wadansu suka ce, "Wannan Almasihu ne." Amma wadansu suka ce, "Almasihu zai fito daga Gallili ne? 42 Ba nassi ya ce Almasihu zai fito daga cikin dangin Dauda daga Baitalami ba, daga kauyen da Dauda ya fito? 43 Sai aka sami rabuwa a cikin taron saboda shi. 44 Da wadansun su sun kama shi, amma ba wanda ya sa masa hannu. 45 Sa'annan jami'an suka dawo wurin manyan Fristoci da Farisawa, wadanda suka ce," me yasa ba ku kawo shi ba?" 46 Jami'an su ka amsa, "Ba mutumin da ya taba yin magana kamar haka." 47 Farisawa suka amsa masu, "kuma an karkatar da ku? 48 Ko wani daga cikin mahukunta ya bada gaskiya gare shi, ko kuwa daga cikin Farisawa? 49 Amma wannan taro da basu san shari'a ba, la'anannu ne." 50 Nikodimus ya ce masu, (shi wanda ya zo wurin Yesu da, daya daga cikin Farisawa), 51 " Ko shari'armu bata hana hukunta mutum ba, sai ta ji daga gare shi ta kuma san abin da ya aikata ba?" 52 Suka amsa masa suka ce,"kai ma daga Galili ka fito? Ka yi bincike ka gani ba annanbin da zai fito daga Galili." 53 Daga nan sai kowa ya tafi gidansa.
Yesu ya na magana wa 'yan'uwansa a cikin Galili. Waddannan sura su na magana game da loƙacin da abin ya faru.
Waɗɗannan kalmomin ya gaya wa mai sauraran cewa marubucin zai fara magana game da sabon abu. "Bayan ya gama magana da al'majiransa" (See: John 6:66-71) ko kuma "da saran loƙaci"
Ya kamata mai saurara ya gane cewa mai yiwuwa Yesu ya yi tafiya ne ba kuwa ya hawo mota ko dabba ba.
A nan "Yahudawa" magana ne na "shugabanin Yahudawa." AT: "shugabanin Yahudawa su na shirin su kashe shi"
"Yanzu loƙacin idin Yahudawa ya yi kusa"
Wannan ya na nufin ainahin kananan 'yan'uwanin Yesu, 'ya'yan Maryamu da Yusuf.
Kalmar "ayyuka" ya na nufin abin mamaki da Yesu ya yi.
Kalmar " kansa" magana ne da ke bayyana kalmar "shi."
A nan "duniya" magana ne game da dukkan mutane a cikin duniya. AT: "dukkan mutane" ko "kowane mutum"
Wannan maganan fashi ne daga ainahin labarin kamar yadda Yahaya ya gaya mana tushen bayanin game da 'yan'uwan Yesu.
"kananun 'yan'uwansa"
Kalmar "loƙaci" karin magana ne. Yesu ya na nufin cewa loƙaci bai kai da zai gama hidimarsa ba. AT: " loƙaci bai kai da zan daina aiki na ba"
"kowane loƙaci ya na da kyau maku"
A nan "duniya" magana ne game da mutane da suke cikin duniya. AT: "Dukka mutane a duniya ba za su iya ki ka ba"
"ina faɗa masu cewa abin da suke yi ba bu kyau"
Yesu ya cigaba da magana da 'yan'uwansa.
A nan Yesu ya na nufin cewa idan ya tafi Urushalima, zai kawo aikinsa ga karshe. AT: "loƙaci na bai kai tukuna da zan tafi Urushalima ba"
'Yan'uwannan ne kannen Yesu.
Urushalima ya na tudu fiye da Galili, wurin da Yesu da 'yan'uwansa suke adda.
Waɗɗannan jumla su na nufin abu ɗaya. Ana sake nanata maganan domin bayani. AT: "ɓoyeyye sosai"
A nan kalmar "Yahudawa" karin magana ne na "shugabanin Yahudawa." kalmar "sa" ya na nufin Yesu. AT: "Shugabanin Yahudawa suna neman Yesu"
Wannan ya na nufin rashin daɗi da mutum ya ke da shi a loƙacin da akwai kurarin lahani a kansa ko kuma wasu.
Kalmar "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa da suke hamayya da Yesu. AT: "shugabanin Yahudawa"
A nan "karkatar" na nufin a rinjaye mutum ya gaskata da abinda ba gaskiya bane. AT: "ya rinjaye mutanin"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya bayana mamakin da shugabanin Yahudawa sun yi akan cewa Yesu ya na da sani sosai .
"amma ya na zuwa daga Allah, wanda ya aiko ni"
"loƙacin da mutum ya na so ya girmama wadda ya aiko shi kadai, mutumin ya na faɗan gaskiya ne. Ba ya karya"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya kara bayani. AT: "Musa ne ya ba ku dokan"
"bi doka"
Yesu ya daidaita muradin shugabanin Yahudawa da suke so su kashe shi domin ya karye dokan Musa. Ya na nufin cewa shugabanin da kansu ba su bin dokan. AT: "Ku na karye dokan da kanku kuma ku na so ku kashe ni!"
"Wannan ya nuna cewa kai mahaukaci ne, ko kuma aljani ya na mulki da kai!"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya kara bayani. AT: "ba bu wadda ya ke so ya kashe ka!"
"abin al'ajibi daya" ko "alama ɗaya"
"dukkanku kun gigice"
Yahaya ya kara tanada karin bayani anan game da kaciya.
Yesu ya na nufin cewa yin kaciya ya na tare da aiki. AT: "kun yi wa ɗa na miji kaciya a ranar Asabar. Wannan ma aiki ce"
"a ranar hutun Yahudawa"
"Idan kun yi wa ɗa na miji kaciya a ranar Asabar domin kada ku karye dokar Musa"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya kara bayani. AT: "kadda ku yi fushi da ni domin na sa mutum lafiya a ranar Asabar!"
Yesu ya na nufin cewa kada mutane su zaba abin da ba daidai ba, amma su tsaya akan abin da su na iya gani. A kowane ayuka akwai wani muradi da ba a iya gani. AT: "Daina hukunta mutane bisa abin da ku na iya gani! Ku fi hankali da abin da ke daidai bisa ga Allah"
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya ne domin karin bayani. AT: "Wannan Yesu ne wadda suke nema su kashe shi!"
Wannan yana nufin cewa shugabanin Yahudawa basu yin hamaiya da Yesu. AT: "ba su faɗa komai na hamayya da shi ba"
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya ne domin karin bayani. AT: "Watakila sun yarda da gaskiye cewa shi ne Mai ceto!"
"yi magana da murya mai karfi"
Yesu da mutanin su na cikin faɗan haikali. AT: "a cikin fadan haikali"
Yahaya ya yi amfani da karin magana a cikin wannan jumla. Mutanin sun gaskanta cewa Yesu daga Nazarat ne. Ba su san cewa Allah ne ya aike shi daga sama ba kuma an haife shi a cikin Baitalami. AT: "Dukkan ku kun san ni kuma ku na tunani cewa kun san wurin da na fito"
"akan iko na." Dubi yadda kun fasara "na kansa" a cikin 5:19.
"Allah ne wadda ya aiko ni kuma shi gaskiya ne"
Kalmar "sa'ar" magana ne da ya ke wakilcin loƙacin da ya kamata a kama Yesu, bisa shirin Allah. AT: "ba loƙacin da ya kamata su kama shi ba ne"
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya ne domin karin bayani. AT: "A loƙacin da Almasihu zai zo, hakika ba zai iya yin alamu fiye da wadda wannan mutumin ya yi ba!"
Wannan ya na nufin abin al'ajibi da ya nuna cewa Yesu ne Almasihu.
"Zan kasance tare da ku na da dan loƙaci kadan"
A nan Yesu ya na nufin Allah Uba, wadda ya aike shi.
"ba za ku iya zuwa wurin da na ke ba"
"Yahudawa" karin magana ne da ke wakilcin shugabanin Yahudawa da suka yi hamayya da Yesu. AT: "shugabanin Yahudawa sun faɗa a sakaninsu"
Wannan ya na nufin Yahudawa da aka baza su a duniyar Greek, a wujen Falistiyawa.
Wannan "kalma" magana ne da ya ke nufin sakon da Yesu ya bayar, wadda shugabanin Yahudawa sun kasa ganewa. AT: "Me ne ya na magana a kai a loƙacin da ya ce"
"babba" ce domin shi ne karshe, ko kuma muhimmin, ranar idi.
A nan kalmar "shi" magana ne da yake nufin yawan son abubuwan Allah, kamar yadda mutum yake "kishi" ruwa. AT: "Waddanda su ke son abubuwan Allah kamar yadda mutum mai kishi yake son ruwa"
Kalmar "sha" magana ne da yake nufin karɓan rai na ruhaniya da Yesu ya tanada. AT: "Ya zo wuri na don ya kashi ƙishirwa ta ruhaniya"
"kamar yadda littafi ya faɗi game da kowane mutum da ya gaskanta da shi"
"rafukan ruwa na rai za su bulbulo" magana da yake wakilcin rai da Yesu ya tanada wa waddanda suke "ƙishirwa" ta ruhaniya. AT: "rai na ruhaniya zai bulbulo kamar rafukan ruwa"
AT: 1) "ruwa da yake ba da rai" ko kuma 2) "ruwa da ya na sa mutane su rayu."
A nan ciki ya na wakilcin cikin mutum, musamman sashen mutum da ba ya bayyane. AT: "daga cikin shi" ko kuma " daga zuciyarsa"
A nan "ya" ya na nufin Yesu.
Yahaya ya na nufin cewa Ruhu zai zo daga baya don ya yi rayuwa a cikin wanda sun gaskanta da Yesu. AT: "Ruhu bai riga ya zo don ya yi rayuwa a cikin masubi ba"
A nan kalmar " daukaka" ya na nufin loƙacin da Allah zai girmama Ɗan bayan mutuwarsa da tashinsa.
Da faɗan wannan, mutanin su na nuna cewa sun gaskanta cewa Yesu ne annabi kamar Musa da Allah ya yi alkawari zai aiko. AT: "Wannan lallai annabi ne wadda yake kamar Musa da muke ta jira"
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya ne domin karin bayani. AT: "Almasihun ba zai iya zuwa daga Galili ba!"
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya ne domin karin bayani. AT: "Littafi ya koya cewa Almasihu zai zo daga layin Dauda kuma daga Baitalami, daga kauyen da Dauda ya fito!"
Ana maganar littafi kamar su na iya magana yadda mutum ya na magana. AT: "Annabawa sun rubuta a cikin littafi"
"inda Dauda ya yi rayuwa"
Taron ba su iya yarda da menene ko wanene Yesu ba.
Sa hanu a akan mutum karin magana ne da ke nufin a kama shi ko kuma jingina akan wani abu. AT: "amma ba bu wadda ya ƙwace shi don a kama shi"
"masu tsaron haikali"
Yan Jami'an sun zuguiguita domin su nuna farin cikinsu ga abin da Yesu ya ce. Za ku iys sa a bayyane cewa Jami'an ba su ce sun san komai da kowane mutum a dukkan loƙaci da wurare sun taɓa faɗa ba. "Ba mu taɓa gin wani ya faɗa irin wannan abin ban mamaki kamar wannan mutum ba!"
"Domin sun faɗa cewa, Farisawa"
"amsa Jami'an"
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya ne domin karin bayani. Farisawa sun yi mamakin amsan Jami'an. AT: "An karkatar da ku ma!"
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya ne domin karin bayani. AT: "Ba bu wani daga mahukunta ko Farisawa da sun gaskanta da shi!"
Wannan daga dokan Farisawa ne ba dokar Musa ba.
"Ga wannan taro da basu san doka ba, Allah zai sa su halaka!"
Yahaya ya ba da wannan bayani domin ya tunashar da mu game da Nikodimus. Harshen ku na iya samun wata hanyar nuna tushen bayani.
Wannan magana ya bayyana a matsayin tambaya domin karin bayani. AT: "shari'ar mu na Yahudawa bai yarda mana mu hukunta mutum ba ... abin da ya aikata!"
A nan Nikodimus ya yi maganan shari'a kamar mutum ne. Idan wannan ba ya al'adan harshenku, za ku iya fasara ta da wata kalma. AT: "Mu na hukunta mutum" ko "Ba mu hukunta mutum"
shugabanin Yahudawa sun san cewa Nikodimus ba daga Galili ba ne. Sun yi masa wannan tambaya don su yi masa ba'a. AT: "Kai daya daga cikin mutanin baya ne daga Galili!"
Wannan karin magana ne. Za ku iya sa bayani da ba bu a nan. AT: "Yi bincike da kyau a kuma yi karantun abin da an rubuta a cikin littatafe"
Mai yiwuwa wannan ya na nufin cewa an haife Yesu a cikin Galili.
Bai so ya shiga cikin Yahudiya ba domin Yahudawa suna shirin su kashe shi.
Sun sa shi ya je domin almajiransa su ga ayyukan da yake yi su ma kuma domin a gan shi a fili ga duniya.
Yesu ya ce wa 'yan'uwansa cewa, "loƙacin shi bai yi ba tukuna, kuma loƙacin shi bai cika ba.
Yesu ya ce duniya ta ƙi shi domin ya na fadin cewa ayyukansa ba su da kyau.
Yesu ya tafi bayan da 'yan'uwansa su ka tafi wurin idin, amma a asirce ba a fili ba.
Waɗansu suna cewa, "shi mutumin kirki ne." Waɗansu kuma suna cewa,"A'a yana karkatar da hankalin jama'a."
Ba wanda ya yi magana a fili a kan Yesu saboda suna jin tsoron Yahudawa.
Sa'anda aka kai rabin idin, sai Yesu ya shiga cikin haikali ya fara koyarwa.
Yesu ya ce idan wani ya na so ya yi nufin akan wanda ya aiko shi, zai san game da wannan koyarwan, ko ya zo ne daga Allah ko ba haka ba.
Yesu ya ce mutum mai gaskiya ne, kuma babu rashin adalci a cikin sa.
Yesu ya ce ba mai aikata dokokin.
Shaidar Yesu shi ne: Ku na yi wa mutane kaciya a ranar Asabar, domin kada a karya dokar Musa, don me kuka jin haushi na saboda na mai da mutum lafiyayye sarai ranar Asabar?
Yesu ya ce masu kada su yi shari'a ta ganin ido, amma su yi shari'a mai adalci.
Mutanen sun ce sun san inda Yesu ya fito, amma sa'anda Almasihu za ya zo, ba wanda zai san inda ya fito.
Manyan Firistoci da Farisawa suka aika jami'an tsaro su kama Yesu.
Maganganunsu ya nuna cewa basu fahimci maganar Yesu ba.
Yesu ya fadi haka a kan Ruhu, wanda waɗanda suka bada gaskiya gare shi za su karba.
Jami'an tsaron suka amsa, "Ba mutumin da ya taba yin magana kamar haka."
Nikodimus ya ce masu, "Shari'armu bata hana hukunta mutum ba, sai ta ji daga gare shi ta kuma san abin da ya aikata ba?"
1 Yesu ya je Dutsen Zaitun. 2 Da sassafe ya dawo Haikali, dukan mutane kuma suka zo wurin sa; yazauna koya masu. 3 Sai marubuta da Farisawa suka kawo mace wadda aka kama ta tana zina. Su ka sa ta a tsakiya. 4 Sai su ka ce da shi, "Malam, wannan mace an kama ta tana cikin yin zina. 5 A cikin shari'a, Musa ya bamu umurni mu jejjefe irin wandannan mutume, kai me ka ce game da ita?" 6 Sun fadi haka ne domin su gwada shi su sami abinda za su zarge shi da shi, amma Yesu ya sunkuya yayi rubutu da yatsansa a kasa. 7 Sa'adda suka cigaba da tambayar sa, ya mike tsaye yace masu, "shi wanda ba shi da zunubi a cikin ku, ya fara jifar ta da dutse." 8 Ya sake sunkuyawa, ya yi rubutu da yatsansa a kasa. 9 Da suka ji haka, sai suka fita dai-dai da dai-dai, kama daga babbansu. A karshe dai aka bar Yesu shi kadai, tare da matar wadda ta ke a tsakiyar su. 10 Yesu ya tashi tsaye ya ce da ita, "mace, ina masu zargin ki? Ba wanda ya kashe ki? 11 Ta ce, "Ba kowa, Ubangiji" Yesu ya ce, "Ni ma ban kashe ki ba. Ki yi tafiyar ki, daga yanzu kada ki kara yin zunubi." 12 Yesu ya kara yin magana da mutanen cewa, "Ni ne hasken duniya, shi wanda ya biyo ni, ba zai yi tafiya cikin duhu ba, amma za ya sami hasken rai. 13 Farisawa suka ce masa, "Kana bada shaida a kan ka, shaidarka ba gaskiya ba ce." 14 Yesu ya amsa ya ce masu, "Ko ma na bada shaida a kai na, shaidata gaskiya ce, na san daga inda na fito da inda zan tafi, amma ku baku san daga inda na fito ba, baku kuma san inda zan tafi ba. 15 Kuna shari'a ta son kai, ni ko ban yi wa kowa shari'a ba. 16 Ko ma da na yi shari'a, shari'ata gaskiya ce domin ba ni kadai ba ne, amma ina tare da Uba wanda ya aiko ni. 17 I, a cikin dokarku an rubuta cewa shaidar mutum biyu gaskiya ce. 18 Ni ne ni ke shaidar kaina, kuma Uba wanda ya aiko ni ya na shaida ta. 19 Su ka ce da shi, "Ina ubanka?" Yesu ya amsa ma su ya ce, "baku san ni ba balle Ubana, in da kun san ni da kun san Uba na kuma." 20 Ya fadi wadannan kalmomi a kusa da wurin ajiya sa'adda ya ke koyarwa a cikin haikali, kuma ba wanda ya kama shi saboda sa'arsa bata yi ba tukuna. 21 Ya kara cewa da su,"Zan tafi, za ku neme ni ba za ku same ni ba, za ku mutu cikin zunubinku. Inda ni ke tafiya, ba za ku iya zuwa ba". 22 Yahudawa su ka ce,"Zai kashe kansa ne, da ya ce inda ni ke tafiya ba za ku iya zuwa ba?" 23 Yesu ya ce masu ku daga kasa kuke, Ni kuwa daga bisa ni ke. Ku na wannan duniya ne, Ni kuwa ba na wannan duniya ba ne. 24 Shiyasa na ce maku za ku mutu cikin zunubanku. In ba kun bada gaskiya NI NE ba, za ku mutu cikin zunubanku. 25 Sai kuma suka ce da shi,"Wanene kai?" Yesu ya ce masu, "Abin da na gaya maku tun daga farko. 26 Ina da a bubuwa da yawa da zan gaya maku, in kuma hukunta ku a kai. Duk da haka, wanda ya aiko ni, mai gaskiya ne, abubuwan da naji daga wurin sa, wadannan abubuwan su ni ke gaya wa duniya." 27 Ba su gane ba yana yi masu magana a kan Uban. 28 Yesu ya ce, "Sa'adda kuka tada Dan Mutum sama sa'annan za ku gane NI NE, kuma ban yi komi domin kaina ba. Kamar yadda Uba ya koya mani, haka nike fadin wadannan abubuwa. 29 Shi wanda ya aiko ni, yana tare da ni kuma bai bar ni ni kadai ba, domin kullum ina yin abubuwan da suke faranta masa rai." 30 Sa'adda Yesu ya ke fadin wadannan abubuwa, dayawa suka bada gaskiya gare shi. 31 Yesu ya gayawa wadancan Yahudawa da suka bada gaskiya gare shi, "Idan kun tsaya a cikin magana ta ku almajiraina ne na gaskiya, 32 Kuma za ku san gaskiya, gaskiya kuwa zata 'yantar da ku." 33 Suka amsa masa, "Mu zuriyar Ibrahim ne kuma bamu taba yin bauta wurin kowa ba, yaya za ka ce, 'Za a 'yantar da ku'?" 34 Yesu ya ce masu, "Hakika, hakika, ina ce maku, dukan wanda ya ke aika zunubi bawan zunubi ne. 35 Bawa kuwa, ba ya zama a gida dindindin, da yana zama dindindin. 36 Saboda haka, idan Dan ya 'yantar da ku zaku zama 'yantattu sosai. 37 Na san ku zuriyar Ibrahim ne, kuna so ku kashe ni saboda kalma ta bata da wurin zama a cikin ku. 38 Na fadi abubuwan da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abubuwan da kuka ji daga wurin ubanku." 39 Suka amsa suka ce masa, "Ibrahim ne ubanmu" Yesu ya ce masu, "Da ku 'yayan Ibrahim ne da kun yi ayukan da Ibrahim ya yi. 40 Amma, yanzu kuna so ku kashe ni, mutumin da ya gaya maku gaskiyar da ya ji daga wurin Allah. Ibrahim bai yi haka ba. 41 Kuna yin ayyukan ubanku. Suka ce masa, "mu ba a haife mu cikin fasikanci ba, muna da Uba daya: Allah." 42 Yesu ya ce masu, "Inda Allah Ubanku ne, da kun kaunace ni, gama na zo daga wurin Allah kuma ga ni anan, gama ba domin kaina nazo ba, shine ya aiko ni. 43 Meyasa baku gane magana ta ba? Ai saboda ba za ku iya jin maganata ba ne. 44 Ku na ubanku, shaidan ne, kuma kuna so ku yi nufe-nufe na ubanku. Shi mai kisan kai ne tun daga farko kuma ba ya tsayawa gaskiya saboda da babu gaskiya a cikin sa. Sa'anda yake fadin karya, yana maganar halinsa ne domin shi dama makaryaci ne da uban karya kuma. 45 Dayake ina fadin gaskiya baku bada gaskiya gare ni ba. 46 Wanene a cikin ku ya kama ni da zunubi? Idan na fadi gaskiya don me ba ku gaskanta ni ba? 47 Shi wanda yake na Allah ya kan ji maganar Allah, ku ba kwa jin maganar Allah da yake ku ba na Allah bane," 48 Yahudawa suka amsa suka ce masa, "Bamu fadi gaskiya ba da muka ce kai Basamariye ne kuma kana da aljan?" 49 Yesu ya amsa, "Ni ba ni da aljan, ina girmama Ubana, ku kuma ba kwa girmama ni." 50 Ba na neman daraja domin kaina, akwai wanda ke nema yana kuma hukuntawa. 51 Hakika, hakika, iIna ce maku, dukan wanda ya kiyaye maganata, ba za ya ga mutuwa ba." 52 Sai Yahudawa su ka ce masa, Yanzu mun sani kana da aljan. Ibrahim da annabawa sun mutu, amma kai ka ce, ' dukan wanda ya yi biyayya da maganata ba zai dandana mutuwa ba'. 53 Ai baka fi ubanmu Ibrahim girma ba wanda ya mutu, ko ka fi shi? Annabawa kuma sun mutu. Wa kake daukar kanka ne?." 54 Yesu ya amsa, "Idan na daukaka kaina, daukaka ta banza ce, Ubana ne ya daukaka ni. Wanda kuka ce shi ne Allahnku. 55 Ku kuwa ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Idan na ce ban san shi ba, na zama kamar ku kenan, makaryaci. Sai dai, Ni na san shi ina kiyaye maganarsa. 56 Ubanku Ibrahim ya yi farinciki da ganin rana ta; ya gan ta kuma ya yi murna." 57 Yahudawa su ka ce masa, "Baka kai shekara hamsin ba tukuna, ka taba ganin Ibrahim?" 58 Yesu ya ce masu, "Hakika, hakika, ina ce maku, kafin a haifi Ibrahim, NI NE." 59 Suka dauki duwatsu za su jefe shi, amma Yesu ya boye kansa, ya fita daga haikali.
Sura ɗaya ya faɗa mana inda Yesu ya tafi a karshen Sura da ya rigaya wuce.
Sa'an da waddansu litattafe su ke da 7:53-8:1, litattafe na farko musa kyau ba su sa su ba.
Wannan ne ainahin yadda ana magana. Ya na nufin "mutane dayawa."
A nan jumlan "marubuta da Farisawa" karin magana ne da yake wakilcin waddansu mutanin wannan kungiyoyi biyu. AT: "Waddansu marubuta da Farisawa sun kawo" ko kuma "Waddansu mazaje wadda sun koya wa Yahudawa dokoki da waddansu da suke Farisawa"
Wannan jumla ce. AT: "macen da su ka samu ta ke yin zina"
"mutane irin haka" ko "mutane da suke yin haka"
"Don haka kun gaya mana. Me za mu yi game da ita?
Wannan ya na nufin yin amfani da wata tambaya.
Ana iya sa abin da za a zarge a bayyane. AT : "domin su iya yin zargin sa da faɗan abin da ba daidai ba" ko kuma "domin su iya zargin sa da rashin bin dokan Musa ko na Romawa"
Kalmar "su" ya na nufin marubuta da Farisawa.
Ana iya bayyana kalmar "zunubi." AT: "shi wanda bai taba yin zunubi a cikin ku ba" ko kuma "Idan wani a cikin ku bai taba yin zunubi ba"
"bari mutumin"
"ya durkusa"
"đaya bayan ɗaya"
A loƙacin da Yesu ya kira ta "mace," ba wai ya na sun ya sa ta ta ji kamar mara amfani bba ne. Idan mutane a harshenku za su yi tunani cewa ya na yin haka, ana iya fasara ba tare da kalmar "Mace" ba.
A nan "haske" misali ne na wahayin da ya ke zuwa daga Allah. AT: "Ni ne wadda na ke ba da haske a duniya"
Wannan magana ne na mutanin. AT: "mutanin duniya"
Wannan karin magana ne da ya ke nufin "kowane mutum da yake yin abin da ke daidai" ko "kowane mutum da ya ke biyayya da ni"
Yi "tafiya a cikin duhu" magana ne na yin rayuwan zunubi. AT: "ba zai yi rayuwa kamar ya na cikin duhun zunubi ba"
"Hasken rai" magana ne na gaskiya daga Allah wadda yake ba da rai na ruhaniya. AT: "gaskiya da yake kawo rai madawammi"
"Kana faɗan waddannan abubuwa game da kanka"
Farisawa su na nufin cewa shaidar mutum daya kadai ba gaskiya ba ne domin ba za a iya bincikawa ba. AT: "ba za ka iya zama shaidar kanka ba" ko " abin da ka faɗa game da kanka ba zai iya zama gaskiya ba"
"ko da na faɗa waddannan abubuwa game da ni"
"ma'aunin mutum da kuma dokokin mutane"
AT: 1) "ban yi wa kowa shari'a tukuna ba" ko 2) "ba zan yi wa kowa shari'a yanzu ba."
AT: 1) "idan na yi wa mutane shari'a" ko kuma 2) "duk loƙacin da na yi wa mutane shari'a"
AT: 1) "shari'ata zai zama daidai" ko "shari'ata daidai ne."
Yesu, Ɗan Allah, ya na da iko domin dangantaka na musamman da Ubansa.
Abin da bayanin ya ke nufi shi ne Yesu ba shi kadai ba ne a shari'an. AT: "ba ni kadai ba ne a yadda na ke yin shari'a" ko "ba na yin shari'a ni kadai"
Uba da Ɗa su na shari'ata tare. AT: "Uban ya na yin shari'a tare da ni" ko "Uban ya na yin shari'a kamar yadda na ke yi"
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah. Idan dole ne harshen ku zai faɗa Uban wa ne wannan, za ku iya ce " Uba na"
"kalmar "I" ya na nuna cewa Yesu ya na kara akan abin da dama ya na faɗa.
Wannan jumla ce. AT: "Musa ya rubuto"
hikiman a nan shi ne cewa mutum daya ya na iya duba kalmomin dayan mutumin. AT: "Idan mazaje biyu sun faɗa abu daya, mutane sun san cewa gaskiya ne"
Yesu ya shaida kansa. AT: "Na ba ku alamun kai na"
Uban kuma ya na shaida akan Yesu. Za ku iya sa a bayyane cewa wannan ya na nufin shaidar Yesu gaskiya ce. AT: "Uba na wadda ya aiko ni ya kuma kawo alamu game da ni. Don haka ku yarda cewa abin da mu na faɗa maku gaskiya ne"
Yesu ya nuna cewa saninsa, ya na nan kamar sanin Uban ne kuma. Ɗa da Uba Allah ne. "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah.
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
Kalmar "sa'a" magana ne na loƙacin da Yesu zai mutu. AT: "loƙaci bai kai da Yesu zai mutu ba"
A nan kalmar "mutu" ya na nufin mutuwa ta ruhaniya. AT: "mutu a loƙacin da ku na cikin zunubi" ko "za ku mutu a loƙacin da ku na yin zunubi"
"ba ku iya zuwa ba"
A nan "Yahudawa" magana ce na "shugabanin Yahudawa." AT: "shugabanin Yahudawa sun ce"
"An haife ku a cikin wannan duniya"
"na zo daga sama"
"Ku na wannan duniya ne"
"NI ba na wannan duniya ba ne"
"zu ku mutu da ba Allah ya yafe ku zunuben ku ba"
AT: 1) Yesu ya na bayyana kansa a kamar Yahweh, wadda ya ke nufin "Ni ne" ko 2) "Yesu ya so mutanin su gani cewa ya na nufin abin da ya rigaya ce shi ne: "Ina daga sama."
Kalmar "Su" ya na nufin shugabanin Yahudawa. (Dubi: John 8:22)
A nan "duniya" magana ne na mutanin da suke rayuwa a cikin duniya. AT: "waddannan abubuwa da na faɗa wa dukka mutane"
Wannan ya na nufin sa Yesu a kan giciye don a kashe shi.
Yesu ya yi amfani da wannan lakabin "Ɗan Mutum" wa kansa.
Kamar Allah Ɗa, Yesu ya san Allah Uba fiye da kowa. AT: 1) Yesu ya na bayyana kansa a mastayin Yahweh ta wurin cewa, "Ni ne Allah" ko 2) Yesu ya na cewa, "ni ne wadda na ke faɗa."
"Ina faɗan abinda Ubana ya koya mani in faɗa." Kalmar "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah.
Kalmar "shi" ya na nufin Allah.
"Sa'adda Yesu ya faɗa waddannan kalmomin"
"mutane dayawa sun yarda da shi"
Wannan karin magana ne da ya ke nufin "yin biyyaya da Yesu." AT: "yi biyyaya da abin da na faɗa"
"masu bi na"
Wannan karin magana ne. Yesu ya yi magana akan "gaskiyan" kamar mutum ne. AT: "Idan kun yi biyyaya da Allah, Allah zai yantar da ku"
Wannan ya na nufin abin da Yesu ya bayana game da Allah. AT: "abin da ke gaskiya game da Alla"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nuna mamakin shugabanin Yahudawa a abin da Yesu ya faɗa. AT: "Ba mu neman a cece mu!"
Dubi yadda an fasara wannan a cikin 1:51.
A nan kalmar "bawa" karin magana ne. Wannan ya na nufin cewa "zunubi" ya na nan kamar maigida ne ga wadda yake yin zunubi. AT: "ya na nan kamar bawan zunubi"
A nan "gida" magana ne na "iyali." AT: "A matsayin cikkaken dan iyalin"
Wannan karin magana ne. Za ku iya fasara shi ta amfani da kalmomin. AT: "ɗan dan gidan ne har abada"
Ya na nufin cewa Yesu ya na magana game da yanci daga zunubi, wadda magana ne na rashin iya yin zunubi. AT: "Idan Ɗan ya 'yantar da ku, zaku iya yantuwa daga zunubi"
"Ɗan" muhimmin lakabi ne na Yesu, Ɗan Allah. Yesu ya yi magana game da kansa ne. AT: "Idan Ni, Ɗan, ya yantar da ku"
A nan "kalma" magana ne na "koyarswa" ko "sakon" Yesu, wadda shugabanin Yahudawa ba karba ba. AT: "ba ku karbi koyarswa na ba" ko kuma "ba ku yarda sako na ta canza rayuwarku ba"
"Ina gaya maku game da abubuwan da na gani a loƙacin da ina tare da Uba na"
Shugabanin Yahudawa ba su gane cewa ta wurin "Ubanku" Yesu ya na nufin shaidan ne ba. AT: "kun kuma cigaba da yin abin da Ubanku ya gaya maku ku yi"
kakane
"Ibrahim bai taba gwada kashe wani da ya gaya mashi gaskiyan wahayi daga Allah ba"
Yesu ya na nufin cewa shaidan ne ubansu. AT: "a'a! Ku na yin abubuwan da ainahin ubanku ya yi"
A nan shugabanin Yahudawa su na nufin cewa Yesu bai san wa ne ainahin Ubansa ba. AT: "Ba mu san game da kai ba, amma ba mu ne ainahin 'ya'yan ba" ko kuma "An haife mu daga aurya da ya kamata"
A nan shugabanin Yahudawa sun amince cewa Allah ne Ubansu na ruhaniya. Wannan mihimmin lakabi ne wa Allah.
Wannan ne irin kauna da ya ke zuwa daga Allah kuma ya na kan kyauwawan mutane (tare da makiyanmu), ko bai amfane mutum ba.
Yesu ya na amfani da wannan tambaya domin ya tsauta wa shugabanin Yahudawa domin rashin jin su. AT: "Zan gaya maku dalilin da ba ku gane abin da na faɗa!"
A nan "magana" ya na nufin "koyarswan" Yesu. AT: "Ai saboda ba za ku yarda da koyarswa ta ba.
"ku na ubanku, shaidan"
A nan "uba" magana ne na wadda ya soma karya. AT: "shi ne wadda ya halittce dukka karya a farko"
"domin ina faɗa maku abubuwan gaskiya game da Allah"
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya domin ya bayana cewa bai taba yin zunubi ba. AT: "Ba bu wani a cikin ku da zai iya nuna cewa na taba yin zunubi!"
"Idan na faɗa abubuwan da suke gaskiya"
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya don ya tswata shugabanin Yahudawa domin rashin gaskanta. AT: "ba ku da dalilin rashin gaskanta da ni!"
A nan "maganar" ya na nufin "sakon" Allah. AT: "sakon Allah" ko kuma "gaskiya da ya ke zuwa daga Allah"
"Yahudawa" karin magana ne da ya ke wakilcin "shugabanin Yahudawa" da suke hamayya da Yesu. AT: "shugabanin Yahudawa"
shugabanin Yahudawa sun yi amfani da wannan tambaya domin su kushe Yesu su kuma ci masa mutunci. AT: "Hakika mun yi daidai da mu ka ce kai ba-Samariye ne kuma aljani ya na rayuwa a cikin ka!"
Wannan ya na nufin Allah.
A nan "magana" zance ne na "koyarwan" Yesu. AT: "yi biyayya da koyarwa na" ko "yi abin da na ce"
Wannan karin magana ne da yake nufin taba mutuwa. A nan Yesu ya na nufin mutuwa ta ruhaniya. AT: "mutu a ruhaniya"
A nan "Yahudawa" magana ne na "shugabanin Yahudawa" wadda suke hamayya da Yesu. AT: "shugabanin Yahudawa"
"Idan wani ya yi biyayya da koyarswata"
Wannan karin magana ne da yake nufin taba mutuwa. Shugabanin Yahudawa sun yi kuskure ta tunani cewa Yesu ya na magana akan mutuwa ta jiki ne kadai. AT: "mutu"
Shugabanin Yahudawa sun yi amfani da wannan tambaya domin su bayana cewa Yesu bai fi Ibrahim ba.AT: "Hakika ba ka fi Ubanmu Ibrahim wanda ya mutu ba!"
Yahudawa sun yi amfani da wannan tambaya don su kwaɓe Yesu domin ya na tunani cewa ya fi Ibrahim muhimmi. AT: "Kada ka yi tunani cewa ka na da muhimmi!"
Kalmar "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah. Ba bu wadda ya san Allah Uba kamar Yesu, Ɗan Allah. AT: "Uba na ne ya na daukaka na, sai kuma ku na ce shi ne Allahnku"
A nan "kalma" magana ne na abin da Allah ya ce. AT: "Ina biyayya da abin da ya ce a yi"
Wannan magana ne na abin da Yesu zai cika a loƙacin rayuwarsa. AT: "abin da zan yi a loƙacin rayuwata"
"ya gan zuwa na ta wurin wahayin Allah sai ya yi murna"
A nan "Yahudawa" magana ne na "shugabanin Yahudawa" wadda sun yi hamayya da Yesu. AT: "shugabanin Yahudawa sun ce masa"
Shugabanin Yahudawa sun yi amfani da wannan tambaya domin su bayana mamakin sun cewa Yesu ya ce ya gan Ibrahim. AT: "Ka na kasa da shekaru hamsin. Da ba ka iya ganin Ibrahim ba!"
Kamar Allah Ɗa, Yesu ya san Allah Uba fiye da kowa. AT: 1) Yesu ya na bayyana kansa kamar Yahweh ta wurin cewa, "Ni ne Allah" ko kuma 2) Yesu ya na cewa, kafin Ibrahim ya kasance, Na kasance."
Shugabanin Yahudawa sun yi fushi a abin da Yesu ya ce. A nan ya na nufin cewa sun so su kashe shi domin ya sa kanshi daidai da Allah. AT: "Sai sun dauki duwasu su kashe shi domin ya ce shi daidai ne da Allah"
Suka kawo mace wadda aka kama ta tana zina. Su ka sa ta a tsakiyarsu, suka tambaye Yesu game da abin da zai iya ce akanta (ya sharanta ta).
Sun kawo wannan matan wa Yesu domin su gwada shi su sami abin da za su zarge shi da shi.
Yesu yace masu, "shi wanda ba shi da zunubi a cikin ku, ya fara jifar ta da dutse."
Bayan Yesu ya yi magana, sai sun fita ɗaya bayan ɗaya, kama daga babbansu zuwa na karshen.
Yesu ya ce mata ta yi tafiyarta, daga yanzu kada ta kara yin zunubi.
Farisawan sun koka cewa Yesu ya na bada shaida a kan sa, kuma shaidarsa ba gaskiya ba ne.
Yesu ya faɗa cewa a cikin dokarsu an rubuta cewa shaidar mutum biyu gaskiya ce. Ni ne na ke shaidar kaina, kuma Uba wanda ya aiko ni ya na shaida ta.
Yesu ya sa maganannan akan sanin cewa su daga kasa suke, kuma shi kuwa daga bisa ni yake. Su na wannan duniya ne, shi kuwa ba na wannan duniya ba ne.
Yesu ya ce za su mutu a cikin zunubansu In ba su bada gaskiya cewa NI NE ba.
Yesu ya faɗa wa duniya abubuwan da yaji daga Uban.
Uban yana tare da shi kuma bai bar shi kadai ba, domin kullum ya na yin abubuwan da suke faranta masa rai.
Za su iya sanin cewa hakika su almajiran Yesu ta wurin tsaya a cikin maganarsa.
Waɗannan Yahudawan sun zata Yesu na maganar zama bawar, ko bauta ga mutane.
Yesu ya na nufin yantarwa daga bautar zunubi.
Suna so ku ƙashe shi saboda kalmar shi bata da wurin zama a cikin su.
Yesu ya ce su ba 'ya'yan Ibrahim ba ne domin ba su yin aikin Ibrahim amma, suna so ku ƙashe shi.
Yesu ya ce masu, "Inda Allah Ubanku ne, da kun ƙaunace ni, gama na zo daga wurin Allah kuma ga ni anan, gama ba domin kaina nazo ba, shine ya aiko ni.
Yesu ya ce Ibilis mai kisan kai ne tun daga farko kuma ba ya tsayawa gaskiya saboda da babu gaskiya a cikin sa. Sa'anda yake fadin karya, yana maganar halinsa ne domin shi dama makaryaci ne da uban karya kuma.
Yesu ya ce mahaifin su Ibilis ne.
Shi wanda yake na Allah ya kan ji maganar Allah.
Dukan wanda ya kiyaye maganarsa, ba za ya ga mutuwa ba.
Sun faɗa wannan domin Yesu ya ce, "Hakika, hakika, iIna ce maku, dukan wanda ya kiyaye maganata, ba za ya ga mutuwa ba."
Sun yi wannan tunani domin sun yi tunanin mutuwar jiki ne. Ibrahim da annabawa sun mutu (mutuwa ta jiki).
Yesu ya ce, "Hakika, hakika, ina ce maku, kafin a haifi Ibrahim, NI NE."
1 Da Yesu yana wucewa, sai ya ga wani mutum makaho tun daga haihuwa. 2 Sai almajiransa suka tambaye shi, "Mallam, wa yayi zunubi, mutumin ne ko iyayensa, har aka haife shi makaho?" 3 Yesu ya amsa, Ba mutumin ne ko iyayensa suka yi zunubi ba, amma domin aikin Allah ya bayyana a cikinsa. 4 Dole mu yi aikin wanda ya aiko ni tunda rana. Dare na zuwa inda ba mai iya yin aiki. 5 Yayinda ina duniya, ni ne hasken duniya." 6 Bayan da Yesu ya fadi wadannan abubuwan, ya tofa yawu a kasa, ya kwaba kasar da yawunsa, sai ya shafe idanun mutumin da kasar. 7 Ya ce masa, tafi, ka wanke a tafkin Siloam (ma'anarsa: aike)." Sai mutumin ya tafi, ya wanke, ya dawo yana gani. 8 Sai makwabtansa da mutanen da da suka gan shi tun can yana roko suka ce, "Ba wannan mutum ne wanda ya ke zaune yana roko ba?" 9 Wadansu suka ce, "shi ne." Wadansu suka ce, "A'a, amma yana kama da shi." Amma shi ya ce, "Ni ne wannan mutum." 10 Suka ce masa, "To yaya aka bude maka idanu?" 11 Sai ya amsa, "Mutumin da ake ce da shi Yesu shi ya kwaba kasa ya shafa mani a idanuna ya ce mani, 'je ka kogin Siluwam ka wanke.' Sai naje na wanke, sannan na samu gani." 12 Suka ce masa, "Ina yake?" Ya amsa, "Ban sani ba." 13 Suka kawo mutumnin da yake makaho a da wurin farisawa. 14 A ranar asabar ne kwa Yesu ya kwaba kasa ya bude masa idanu. 15 Har yanzu farisawan suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Ya ce masu, "Ya sa mani kasa a idanuna, na wanke, kuma yanzu ina gani." 16 Wadansu daga cikin farisawa suka ce, "Wannan mutum ba daga Allah yake ba domin ba ya kiyaye ranar Asabar. "Wadansu suka ce, "Yaya mai zunubi zai yi irin wadannan alamu?" Sai rabuwa ta shiga tsakanin su. 17 Sai suka tambayi makahon kuma, "Me kake cewa game da shi dashike ya bude maka idanu?" Makahon ya ce, "shi annabi ne." 18 Har yanzu kam Yahudawan basu yarda da makantarsa ba da ganin gari da ya samu, sai da suka kirayo iyayen shi wanda ya sami ganin garin. 19 Su ka tambayi iyayen, "Wannan shine yaronku da kuka ce an haife shi makaho? Yaya yanzu ya ke iya gani?" 20 Sai iyayen suka amsa masu, "Mun san wannan yaronmu ne kuma a makaho aka haife shi. 21 Yadda ya ke gani yanzu, bamu sani ba, kuma wanda ya bude masa idanu, bamu sani ba. Ku tambaye shi, ba yaro ba ne. Zai iya magana don kansa." 22 Iyayensa sun fadi wadannan abubuwan, domin suna ji tsoron Yahudawan. Gama Yahudiyawan sun rigaya sun yarda duk wanda yace Yesu Almasihu ne, za a fitar dashi daga majami'a. 23 Domin wannan ne, iyayensa suka ce, "Ai shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi." 24 Suka sake kiran mutumin dake makaho karo na biyu, suka ce masa, "Ka girmama Allah. Mu kam mun sani wannan mutum mai zunubi ne." 25 Sai wannan mutum ya amsa, "Ban sani ba ko shi mai zunubi ne. Abu guda daya na sani: da Ni makaho ne, amma yanzu ina gani." 26 Sai su ka ce masa, "Me ya yi maka? Ta yaya ya bude idanunka?" 27 Ya amsa, "Na rigaya na gaya maku, amma ba ku ji ba! Don me kuke so ku sake ji? Ko kuma kuna so ku zama almajiransa, haka ne? 28 Sai suka kwabe shi suka ce, "kai ne almajirinsa, amma mu almajiran Musa ne. 29 Mun sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum, bamu san ko daga ina ne ya zo ba." 30 Mutumin ya amsa masu ya ce, "Tirkashi, baku san inda ya fito ba, duk da haka shi ya bude mani idanu. 31 Mun san da cewa Allah baya jin masu zunubi, amma idan wani mai ibada ne yana kuma yin nufinsa, to yana jin sa. 32 Tunda duniya ta fara ba a taba jin cewa wani ya bude idanun wanda aka haifa makaho ba. 33 In mutumin nan ba daga Allah yake ba, ba zai iya yin komai ba." 34 Suka amsa suka ce masa, "an haife ka cikin zunubai, yanzu kana so ka yi mana koyarwa?" Sai suka fitar da shi. 35 Yesu ya ji cewa sun fitar da shi daga majami'a. Da ya same shi sai ya ce masa, "Kana bada gaskiya ga Dan Allah?" 36 Sai ya amsa masa yace, "Wanene shi, Ubangiji, da zan bada gaskiya gare shi?" 37 Yesu yace masa, "Ai ka gan shi, shine wanda yake magana da kai." 38 Mutumin ya ce, "Ubangiji, Na bada gaskiya." Sai ya yi masa sujada. 39 Yesu ya ce, "Don hukunci na zo wannan duniya domin wadanda ba su gani su gani, saboda kuma wadanda suke gani su zama makafi." 40 Wadansu Farisawa wadanda suke tare da shi suka ji wadannan abubuwan, suka tambaye shi, "Muma makafi ne?" 41 Yesu ya ce masu, "Inda ku makafi ne, da ba ku da zunubi, amma yanzu kun ce, 'Muna gani', don haka zunubinku ya tabbata.
Sa'ad da Yesu da almajiransa su na tafiya, sun haɗu da wani makaho.
Wannan kalma ya nuna cewa marubucin ya na so ya kwatanta sabon abu.
A nan "Yesu" magana ne na Yesu da almajiransa. AT: "sa'ad da Yesu da almajiransa suka wuce"
Wannan tambaya ya nuna tsohon amincewa na Yahudawa da cewa zunubi ne ya na sa dukka cituttuka da sauran mugun aibi ga jiki. Mallamai sun zata cewa yaro ya na iya yin zunubi daga cikin ciki. AT: "Mallam, mun san cewa zunubi ya na sa mutum makaho. Zunubin wa ne ya sa an haife wannan mutum makaho? Mutumin nan da kansa ne ya yi zunubi, ko iyayensa ne?"
Wannan "mu" ya na tare da Yesu da almajiran da yake magana da su.
A nan "rana" da "dare" karin magana ne. Yesu ya na kwatanta loƙacin da mutane su na iya yin aikin Allah har rana, loƙacin da mutane su na aiki, da kuma dare loƙacin da ba za su iya yin aikin Allah ba.
A nan "duniya" magana ne na mutanin da suke cikin duniya. AT: "yin rayuwa a sakanin mutanin wannan duniya"
A nan "haske" magana ne na gaskiyan wahayin Allah. AT: "wadda ya ke nuna abin da yake gaskiya kamar yadda haske ya na barin mutane su gani abin da yake cikin duhu"
Yesu ya yi amfani da yatsun shi ya kwaɓa datti da yawu. AT: "ya yi amfani da yasunsa ya kwaba dattin da yawu don ya yi laka"
Za ku iya sa a bayyane cewa Yesu ya so mutumin ya wanke lakan a idonshi a cikin tafkin kuma haka mutumin ya yi.
An sami dan yanka a cikin labarin don haka Yahaya zai iya bayana wa masu karatunsa abin da "Siloam" ya ke nufi. AT: "wadda yake nufin "aike"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya domin ya nuna mamakin mutanin. AT: "Wannan mutumin ne wadda ya saba zaune yana roko!"
maƙwabcin mutumin da ya taba makwace sun cigaba da magana da shi.
"To mai ne ya sa ka iya gani?" ko kuma "Ta yaya ka na iya gani yanzu?"
"yi amfani da yatsunsa don ya rufe mun idanu na da laka." Dubi yadda kun fasara irin wannan jumla a cikin 9:6.
Mutanin sun nace cewa sai mutumin ya tafi da su wurin Farisawa. Bu su tilasa shi da karfi ya je ba.
"Ranar hutun Yahudawa"
"Sai Farisawa sun kuma tambaye shi"
Wannan ya na nufin cewa Yesu ba ya kiyaye doka game da yin aiki a ranar hutun Yahudawa.
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nanata cewa alamun Yesu ya nuna cewa shi ba mai zunubi ba ne. "Mai zunubi ba zai iya yin wannan abu ba!"
Wannan wata kalma ne na abin al'ajibi. "Alamu" ya na ba da shaida cewa Allah shi ne mai dukka iko, kuma wadda yake da iko akan duniya.
"Ina tunani shi annabi ne"
A nan "Yahudawa" magana ne na "shugabanin Yahudawa" wadda suka yi hamayya da Yesu. AT: "Yanzu shugabanin Yahudawa ba su yarda ba.
"Su" ya na nufin shugabanin Yahudawa.
"shi na miji ne" ko "shi ba yaro ba ne kuma"
A nan "Yahudawa" ya na nufin shugabanin Yahudawa" wadda sun yi hamayya da Yesu. AT: "sun ji tsoron abin da shugabanin Yahudawa za su iya yi masu"
Wannan ya na nufin rashin daɗi da mutum ya ke da shi a loƙacin da akwai wata kurarin lahani a kansa ko waddansu.
"zai faɗa cewa Yesu Almasihu ne"
A nan "fitar daga majami'a" magana ne na rashin yarda a sake shiga majami'a kuma ba bu sake kasancewa a kungiyar mutane da suke zuwa sujada a majami'a. AT: "ba za a yarda masa ya shiga cikin majami'a ba" ko "ba zai cigaba da zama ɗan majami'a ba"
A nan "su" ya na nufin Yahudawa. ([Yahaya 9:18]
Wannan karin magana ne da mutane suke amfani da shi a loƙacin daukan rantsuwa. AT: "A gaban Allah, faɗa gaskiya" ko kuma "Faɗa gaskiya a gaban Allah"
Wannan ya na nufin Yesu.
Wannan ya na nufin mutumin da ada shi makaho ne.
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya bayana mamakin mutumin da cewa shugabanin Yahudawa sun ce masa ya gaya masu abin da ya faru kuma.
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin karin fasara a maganan mutumin. Ya san cewa shugabanin Yahudawa ba su so su bi Yesu. Ya na so ya yi masu ba'a anan. AT: "kamar ku na so ku zama almajiransa!"
"Ku na bin Yesu!"
Kalmar "mu" ya na a bayyane. shugabanin Yahudawa su na maganan kansu ne kadai. AT: "amma muna bin Musa"
"Mun tabata cewa Allah ya yi magana da Musa"
A nan shugabanin Yahudawa su na nufin Yesu. Suna nufin cewa ba shi da ikon kiran almajirai. AT: "ba mu san inda ya fito ba ko kuma inda ya sami ikonsa"
Mutumin ya na mamakin cewa shugabanin Yahudawa su na tuhunta ikon Yesu bayan sun san cewa ya na da ikon warkarwa. AT: "cewa ba ku san inda ya ke samu ikonsa ba"
"baya amsa addu'an masu zunubi ... Allah ya na amsa addu'ar sa"
Wannan jumla ne. AT: "ba bu wadda ya taɓa ji game da wani da ya taɓa warkar da mutum makaho tun daga haifuwa ba"
Wannan jumla ya yi amfani da hanyoyi dabam dabam. "Mutum daga Allah ne kadai zai iya yin abu irin wannan!"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin karin bayani. Ya na kuma nufin cewa an haife mutumin da makance domin zunuban iyayensa. AT: "An haife ka dalilin zunuban iyayenka. Ba ka kai ka koyar da mu ba!"
"suka fitar da shi daga majami'a"
Wannan ya na nufin "gaskanta da Yesu," gaskanta cewa shi ne Ɗan Allah, yarda cewa shi ne mai ceto, ku kuma yi rayuwa a hanyar da zai girmama shi.
Kalmar "duniya" ya na nufin "mutane da suke rayuwa a cikin duniya." AT: "zo ya yi rayuwa a sakanin mutanin wannan duniya"
A nan "gani" da "makanta" karin magana ne. Yesu ya banbanta mutane da su ke makance ta ruhaniya da makance na jiki. AT: "domin waddanda suka makance a ruhaniya, amma waɗɗanda su ke so su gan Allah, su na iya ganin shi, kuma waɗɗanda sun riga sun yi tunani cewa za su iya ganin Allah ne za su cigaba a cikin makantansu"
"Ka na tunani cewa mun makance a ruhaniya ne?"
A nan "makanta" magana ne na rashin sanin gaskiyar Allah. AT: "Inda ce kun so ku san gaskiyar Allah, za ku iya gani.
A nan "gani" magana ne na sanin gaskiyar Allah. AT: "Tunda ku na tunani cewa kun riga kun san gaskiyar Allah, za ku cigaba da makance"
Almajiran sun yi zaton cewa dalilin da an haifi mutumin a makance shi ne ko mutumin ne ko iyayensa su ka yi zunubi.
Yesu ya ce an haifi mutumin a makance domin aikin Allah ya bayyana a cikinsa.
Yesu ya tofa yawu a ƙasa, ya kwaba ƙasar da yawunsa, sai ya shafe idanun mutumin da ƙasar. Sai ya ce masa, tafi, ka wanke a tafkin Siloam.
Ya dawo yana gani.
Mutumin ya shaida cewa shi ne makaho mai rokon.
Sun kai mutumin wurin Farisiyawa.
Warkarwar makahon ya faru ne a ranar Asabar.
Farisawan suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari.
Waɗansu Farisawa suka ce Yesu ba daga Allah yake ba domin ba ya kiyaye ranar Asabar (ya yi warkarwa a ranar Asabar) kuma waɗansu Farisawan suka ce yaya mai zunubi zai yi irin waɗannan alamu.
Makahon ya ce, " shi annabi ne."
Sun kira iyayen mutumin domin har yanzu ba su yarda cewa mutumin ne wanda ya taba makanta ba.
Iyayen mutumin sun shaida cewa hakika mutumin ɗansu ne kuma an haife shi makaho.
Sun ce yadda ya ke gani yanzu, basu sani ba, kuma wanda ya buɗe masa idanu, basu sani ba.
Sun faɗa waɗannan abubuwan, domin suna jin tsoron Yahudawan. Gama Yahudiyawan sun rigaya sun yarda duk wanda yace Yesu Almasihu ne, za a fitar dashi daga majami'a.
Suka ce, "Ka girmama Allah. Mu kam mun sani wannan mutum mai zunubi ne."
Ya amsa, "Ban sani ba ko shi mai zunubi ne. Abu guda ɗaya na sani: da Ni makaho ne, amma yanzu ina gani."
Makahon ya amsa, "Don me kuke so ku sake ji? Ko kuma kuna so ku zama almajiransa, haka ne??
Makahon ya ce kowa ya san da cewa Allah baya jin masu zunubi.
Suka ce wa mutumin, an haife shi a cikin zunubi, yanzu kana so ka yi mana koyarwa. Sai suka fitar da shi daga cikin haikali.
Yesu ya tambaye mutumin ko ya gaskanta da Ɗan Mutum sai ya ce masa shi (Yesu) ne Ɗan Mutum.
Yesu ya je neman mutumin sai ya same shi.
Makahon Ya ce wa Yesu ya gaskanta ya kuma yi masa sujada.
Yesu ya ce masu, " Inda ku makafi ne, da ba ku da zunubi, amma yanzu kun ce, 'Muna gani', don haka zunubinku ya tabbata.
1 "Hakika, Hakika, ina ce maku, wanda bai shiga ta kofa zuwa garken tumaki ba, amma ya haura ta wata hanya, wannan mutum barawo ne da dan fashi. 2 Wanda ya shiga ta kofa shine makiyayin tumakin. 3 Mai gadin kofar zai bude masa. Tumakin suna jin muryarsa, ya na kuma kiran tumakinsa da sunayensu, ya kuma kai su waje. 4 Bayanda ya kawo su duka a waje, yana tafiya a gabansu, sai tumakin su bi shi, domin sun san muryarsa. 5 Ba za su bi bako ba amma sai dai su guje shi, domin basu san muryar baki ba." 6 Yesu ya yi masu magana da wannan misali, amma basu gane wadannan abubuwa da yake gaya masu ba. 7 Sai Yesu ya ce masu kuma, "Hakika, Hakika, Ina ce maku, Ni ne kofar tumaki. 8 Dukan wadanda suka zo kamin ni barayi ne da yan fashi, amma tumakin ba su ji su ba. 9 Ni ne kofa, In kowa ya shiga ta wurina, zai sami ceto, zai shiga ya fita ya kuma sami wurin kiwo. 10 Barawo ba ya zuwa sai don ya yi sata, ya kashe, ya kuma hallakar. Na zo ne domin su sami rai su kuma same shi a yalwace. 11 Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yana bada ransa domin tumakinsa. 12 Wanda yake dan sako kuma, ba makiyayi ba, wanda ba shine mai tumakin ba, in ya ga kyarkeci na zuwa sai ya saki tumakin ya gudu. Sai kyarkecin ya dauke su ya kuma warwatsa su. 13 Ya gudu domin shi mai aikin kudi ne kuma bai damu da tumakin ba. 14 Nine makiyayi mai kyau, na kuma san nawa, nawa kuma sun san ni. 15 Uban ya san ni, ni ma na san Uban, na kuma bada raina domin tumakin. 16 Ina da wadansu tumaki wadanda ba na wannan garken ba. Wadannan, kuma, dole in kawo su, su ma za su ji muryata saboda za su zama garke daya da makiyayi daya. 17 Domin wannan ne Uban yake kauna ta: Na bada raina domin in same shi kuma. 18 Babu wanda zai dauke shi daga wurina, amma ina bayar da shi da kaina. Ina da ikon bada shi, ina da iko in dauke shi kuma. Na karbi wannan umarnin daga wurin Ubana." 19 Tsattsaguwa ta sake tashi tsakanin Yahudawa domin wadannan kalmomin. 20 Dayawa a cikinsu suka ce, yana da aljani, kuma mahaukaci ne. Don me ku ke sauraronsa?" 21 Wadansu suka ce, wadannan ba kalmomin wanda yake da aljani ba ne. Ko mai aljani zai iya bude idanun makaho?" 22 Sai lokacin idin Tsarkakewa a Urushalima ya zo. 23 A lokacin damuna ne, Yesu kuwa yana tafiya a shirayi cikin haikalin Sulaimanu. 24 Sai Yahudawa suka zagaye shi suka ce masa, "Har yaushe ne za ka bar mu cikin shakka? In kai ne Almasihun, ka gaya mana dalla-dalla." 25 Yesu ya ce masu, "Na gaya maku, amma baku gaskata ba. Ayyukan da nake yi a cikin sunan Ubana, su ke yin shaida a kaina. 26 Duk da haka baku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne. 27 Tumakina suna jin murya ta; Na san su, suna kuma bi na. 28 Ina ba su rai na har abada; ba za su taba mutuwa ba, babu wanda zai kwace su daga hannu na. 29 Ubana, wanda ya bani su, ya fi kowa girma, kuma ba mai iya kwace su daga hannun Uban. 30 Ni da Uban daya ne." 31 Sai Yahudawa suka dauki duwatsu kuma domin su jajjefe shi. 32 Yesu ya amsa masu, "Na nuna maku kyawawan ayyuka masu yawa daga wurin Uban. Saboda wane daga cikin wadannan ayyukan kuke jefe ni?" 33 Sai Yahudawa suka amsa masa, "ba don wani aiki mai kyau muke son mu jefe ka ba, amma don sabo, domin kai, mutum ne, amma kana mayar da kanka Allah." 34 Yesu ya amsa masu, "Ba a rubuce yake a shari'arku ba, 'Na ce, "ku alloli ne"'?" 35 In ya kira su alloli, su wadanda maganar Allah ta zo gare su (kuma ba za a iya karya nassi ba), 36 kuna gaya wa wanda Uban ya kebe ya kuma aiko cikin duniya, 'Kana sabo', domin Na ce, 'Ni dan Allah ne'? 37 In ba na aikin Ubana, kada ku gaskata ni. 38 Amma, idan ina yin su, ko ba ku gaskata da ni ba, ku gaskata da ayyukan saboda ku sani, ku kuma gane cewa Uban yana ciki na, ni kuma ina cikin Uban." 39 Suka sake kokarin kama shi, amma ya yi tafiyarsa, ya fita daga hannunsu. 40 Ya yi tafiyarsa kuma har gaba da kogin Urdun zuwa inda Yahaya ke yin baftisma ada, ya kuma zauna a wurin. 41 Mutane masu yawa suka zo wurinsa, suka ce,"Hakika Yahaya bai yi wasu alamu ba, amma dukan abubuwan da Yahaya ya ce game da wannan mutum gaskiya ne." 42 Mutane dayawa suka bada gaskiya gare shi a wurin.
Yesu ya cigaba da magana da Farisawa. Wannan ne sashin labari wadda ya fara a cikin 9:35.
Yesu ya fara magana a cikin misalai.
Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 1:51.
Wannan wurin danga ne wadda makiyayi yana sa tumakinsa.
Wannan ya na nufin yadda ake amfani da kalmomi biyu makamanci domin karin nanaci.
"Mai gadin kofar ya na buɗe wa tumaki kofa"
Wannan mutum ne wadda an yi hayarsa domin ya duba kafar garken tumaki da dare a loƙacin da makiyayin ba ya nan.
"Tumakin ya gi muryan makiyayi"
"ya na tafiya a gabansu"
"domin sun gane muryarsa"
AT: 1) "almajiran ba su gane ba" ko 2) "taron ba su gane ba."
Wannan kwatanci ne daga aikin makiyayi, ta wurin amfani da karin magana. "Makiyayi" karin magana ne na Yesu. "Tumaki" su na wakilcin waɗɗanda suke bin Yesu, kuma "ɓaki" su ne shugabanin Yahudawa, haɗe da Farisawa, wadda sun gwada rudin mutane.
A nan "kofa" magana ne da yake nufin cewa Yesu ya tanada hanya zuwa garken tumaki, wurin da mutanin Allah suke zama a gabansa. AT: "Ina nan kamar kofa da tumaki suke amfani don su shiga cikin garken tumaki"
Wannan Ya na nufin waɗansu mallamai da su ka koyar da mutanen, tare da Farisawa da kuma waɗansu shugabanin Yahudawa. AT: "Dukan malaman da suka zo ba tare da iko na ba"
A nan "kofa" ƙarin magana ne. Ta wurin kiran kansa "kofa," Yesu ya na nuna cewa shi ne yake ba da hanyar gaskiya na shiga mulkin Allah. AT: "Ni da kai na ina nan kamar kofa"
Kalmar "kiwata"ya na nufin wuri mai ciyawa da tumaki ke ci.
Wannan biyu ne. A wadansu harshuna ya fi kyau a yi amfani da jumla mai kyau. AT: "zuwa don ya yi sata kadai"
Maganar a nan shi ne "tumaki," wadda ya na wakilcin mutanin Allah. AT: "sata, kashe, da kuma hallakar da tumaki"
Kalmar "su" ya na nufin tumaki. "Rai" ya na nufin rai madawami. AT: "domin su rayu, ba tare da rashi ba"
A nan "Makiyayi mai kyau" magana ne da yake wakilcin Yesu. AT: "Ina nan kamar Makiyayi mai kyau"
Ba da wani abu ya na nufin ka mika ranka. Wata hanya ne na mara tsanani da yake nufin mutuwa. AT: "mutu"
"mai aikin kudi" magana ne da ya na wakilcin shugabanin Yahudawa da kuma mallamai. AT: "wadda yake kamar mai aikin kudi"
A nan kalmar "tumaki" magana ne da ya na waklicin mutanin Allah. Kamar mai aikin kudi wadda ya saki tumakin, Yesu ya ce shugabanin yahudawa da mallamai ba su damu da mutanin Allah ba.
Allah Uba da Allah Ɗa sun san juna fiye da yadda wani ya san su. "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah.
Wannan karamin hanya ne da Yesu zai ce zai mutu domin ya kare tumakinsa. AT: "Na mutu don tumakin"
A nan "wadansu tumaki" karin magana ne na masu bin Yesu wadanda ba Yahudawa ba.
A nan "garke" da "makiyayi" karin magana ne. Dukka masubin Yesu, Yahudawa da waɗɗanda ba Yahudawa ba, za su zama kamar garkin tumaki. Zai zama kamar makiyayi wadda ya damu da dukkan su.
Madauwamin shirin Allah shi ne Allah Ɗa ya ba da rainsa domin ya biya zunuban 'yan Adam. Mutuwar Yesu a kan giciye ya bayyana kaunar Ɗan wa Uban kuma na Uban zuwa ga Ɗan.
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai abin da sun yi.
Wannan karamin hanya ne da Yesu zai ce zai mutu sai ya kuma rayu kuma. AT: "Na yarda in mutu domin in sake rayu"
An yi amfani da "kaina" a nan domin a nanata cewa Yesu ya ba da rainsa. Ba bu wadda zai karɓa daga wurinsa. AT: "Ni da kai na bayar"
"Wannan ne abin da Uba na ya umurce ni in yi." Wannan kalmar "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah.
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nanata maganar cewa kada mutane su saurare Yesu. AT: "Kada ku saurare shi!"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin karin bayani. AT: "Hakika aljani ba zai sa makaho ya iya gani ba!" ko kuma "Hakika aljani ba zai iya sa makafe gani ba!"
Wannan hutun ɗari ne na kwana takwas wadda Yahudawa suke amfani don tunawa da wata abin al'ajibi wadda Allah ya sa mai kadan ya cigaba da ba da haske a fitila har kwana takwas. Sun haska fitilar domin su tsarkake haikalin Yahudawa wa Allah. Tsarkaka abu ya na nufin yin alkawari cewa za ku yi amfani da shi a nufi mai kyau.
Wurin da Yesu ya yi tafiya wuri ne da yake wajen filin haikalin. AT: "Yesu ya na tafiya a cikin filin haikali"
Wannan abu ne da an kafa da ya ke a hade da kofan gini; ya na da jinka kuma ya na iya samu katanga ko ba bu.
A nan "Yahudawa" ya na nufin shugabanin Yahudawa wadda sun yi hamayya da Yesu. AT: "Sai shugabanin Yahudawa suka zagaye shi"
Wannan karin magana ne. AT: "sa mu mamaki" ko kuma "hana mu sanin takamaiman?"
A nan "suna" magana ne na ikon Allah. A nan "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah. Yesu ya yi abin al'ajibi ta wurin ikon Ubansa. AT: "ta wurin ikon Ubana" ko "da ikon Ubana"
Al'ajibinsa ya ba da shaida game da shi kamar yadda mutumin da yake yin shaida zai ba da shaida a kotun shari'a. AT: "ba da shaida game da ni"
Kalmar "tumaki" magana ne na masubin Yesu. AT: "ba masubina ba" ko "ba almajirai na ba"
Kalmar "tumaki" misali ce ta masubin Yesu. An bayyana Yesu kamar "makiyayi." AT: "Yadda tumaki su na bin muryan makiyayinsu na gaskiya, masu bi na su na jin murya na"
Kalmar "hanu" a nan magana ne da ya na wakilcin karewa da kula na Yesu. AT: "babu wadda zai sata su daga wuri na" ko kuma "za su kasance lafiya a kulawa na"
Kalmar "Uba" muhimmin lakabi ne wa Allah.
Kalmar "hanu" ya na nufin dukiya da kiyayewar Allah. AT: "Ba bu wadda zai sata su daga Ubana"
Yesu, Allah Da, da Allah Uba ɗaya ne. Kalmar "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah.
Kalmar "Yahudawa" ya na nufin shugabanin Yahudawa wadda suka yi hamayya da Yesu. AT: "Sai shugabanin Yahudawa suka fara dauka duwatsu kuma"
Yesu ya yi su abubuwan al'ajibi ta wurin ikon Allah. Kalmar "Uba" muhimmin lakami ne wa Allah.
Yesu ya san cewa shugabanin Yahudawa ba su so su jefe shi ba domin ya yi kyauwawan ayyaka.
Kalmar "Yahudawa" karin magana ne da ya na wakilcin shugabanin Yahudawa wadda suka yi hamayya da Yesu. AT: "gefen Yahudawan suka amsa" ko kuma "shugabanin Yahudawa sun amsa masa"
"cewa shi Allah"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin karin bayani. AT: "Ya kamata kun san cewa a rubuce ya ke a shari'ar ku cewa, 'ku alloli ne."
Yesu a nan ya yi magana daga nassi inda Allah ya kira masubinsa "alloli," watakila domin ya zabe su ne su wakilce shi a duniya.
Yesu ya yi maganar sakon Allah kamar mutum ne wanda ya maso kusa da wadanda sun ji shi. AT: "Allah ya faɗi sakonsa"
AT: 1) "ba bu wani da zai iya canza nassi" ko kuma 2) "a ko yaushe nassi yakan kasance gaskiya."
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya don ya tsawata abokan gabansa domin sun ce ya na sabo a loƙacin da ya kira kansa "Ɗan Allah." AT: "kada ku ce wa wanda Allah ya kebe don ya aika cikin duniya, 'kana sabo; a loƙacin da na ce ni ne Ɗan Allah!"
"ka na zagin Allah." Abokan gaban Yesu sun gane cewa a loƙacin da an ce shi ne Ɗan Allah, ya na nufin cewa shi daidai ne da Allah.
Wadannan muhimmin lakabi ne da ya na kwatanta dangantaka a sakanin Allah da Yesu.
A nan kalmar "gaskanta" ya na nufin amincewa ko kuma yarda cewa abin da Yesu ya faɗa gaskiya ne.
A nan "gaskanta da" shi ku yarda cewa ayyukan da Yesu ya yi daga Uban ne.
Wadannan karin magana ne da su na bayyana dangantaka na ƙwarai sakanin Allah da Yesu. AT: "Ni da Ubana ɗaya ne a haɗe"
Kalmar "hannu" magana ne da ya na wakilcin kula ko dukiyar shugabanin Yahudawa. AT: "tafi daga su kuma"
Yesu ya na gefen yamma na rafin Urdun. AT: "zuwa gabas na rafin Urdun"
Yesu ya tsaya ta gabas Urdun na dan loƙaci kadan. AT: "Yesu ya zauna na kuanaki dayawa a wurin"
"gaskiya ne cewa Yahaya bai yi wani alamu ba, haƙiƙa bai faɗa gaskiya game da wannan mutum ba, wadda yake yin alamu."
Wadannan abubuwan al'ajibi ne wadda ya ke nuna cewa wani abin gaskiya ne ko kuma ya na amince mutum.
A nan "gaskanta a" ya na nufin amince ko kuma yarda da abin da Yesu ya faɗa gaskiya ne.
Ya ce wanda bai shiga ta kofa zuwa garken tumaki ba, amma ya haura ta wata hanya, wannan mutum barawo ne da dan fashi.
Shi wanda ya shiga ta kofa shine makiyayin tumakin.
Suna bin shi domin sun san muryarsa.
A.a Ba za su bi bako ba.
Dukan waɗanda suka zo kamin ni barayi ne da yan fashi, amma tumakin ba su ji su ba.
Waɗanda sun shiga ta wurin Yesu, kofan, za su sami ceto, za su shiga su fita su kuma sami makiyayya.
Yesu, makiyayi mai kyau na bada ransa domin tumakinsa.
Yesu ya ce yana da waɗansu tumaki waɗanda ba na wannan garken ba. Waɗannan, kuma, ɗole ya kawo su, su ma za su ji muryasa domin za su zama garke ɗaya da makiyayi ɗaya.
Uban na ƙaunar Yesu domin ya bada ransa domin ya same shi kuma.
A'a. Ya na ba da shi da kansa.
Yesu ya ƙarbi wannan umarnin daga wurin Ubansa ne.
Dayawa a cikinsu suka ce, "yana da aljani, kuma mahaukaci ne. Don me ku ke sauraronsa?" Waɗansu kuma suka ce, "ẅaɗannan ba kalmomin wanda yake da aljani ba ne. Ko mai aljani zai iya buɗe idanun makaho?"
Suka ce masa, "Har yaushe ne za ka bar mu cikin shakka? In kai ne Almasihun, ka gaya mana dalla-dalla."
Yesu ya ce ya rigaya faɗa masu (cewa shi ne Almasihu), kuma basu gaskata ba domin su ba tumakinsa ba ne.
Yesu ya ce ya na ba su rai na har abada, ba za su taba mutuwa ba, babu wanda zai kwace su daga hannu sa.
Uban ya fi kowa.
Uban ne ya ba wa Yesu tumakin.
Saboda sun yarda cewa Yesu ya na yin sabo, ya na kuma mayar da kansa Allah ko dashike shi mutum ne.
Yesu ya yi shaidarkansa ta wurin faɗa cewa, "Ba a rubuce yake a shari'arku ba, 'Na ce, "ku alloli ne"'?" In ya kira su alloli, ga wanene maganar Allah ta zo gare su (kuma ba za a iya karya nassi ba), kuna gaya wa wanda Uban ya keɓe ya kuma aiko cikin duniya, 'Kana sabo', domin Na ce, 'Ni dan Allah ne'?
Yesu ya ce wa Yahudawan su dubi ayyukansa. Idan ba ya yin aikin Ubansa, kada su gaskanta da shi. Idan ya na yin ayyukan Ubansa, su gaskanta da shi.
Yesu ya ce za su iya sani su kuma fahimci cewa Uban na cikin Yesu kuma Yesu ya na cikin Uban.
Yahudawan sun so kuma su ƙama shi.
Yesu ya tafi gaba da kogin Urdun zuwa inda Yahaya ke yin baftisma ada.
Sun cigaba da ce, "Hakika Yahaya bai yi wasu alamu ba, amma dukan abubuwan da Yahaya ya ce game da wannan mutum gaskiya ne." Mutane dayawa suka bada gaskiya gare shi a wurin.
1 To wani mutum mai suna Li'azaru, yayi rashin lafiya. Shi mutumin Baitanya ne, wato kauyen su Maryamu da 'yar'uwarta Matta. 2 Wato wannan Maryamu da ta shafe Ubangiji da mur ta kuma share masa kafafunsa da gashin kanta, wadda dan'uwanta Li'azaru ke rashin lafiya. 3 'Yan'uwannan mata suka aika sako wurin yesu, cewa, "Ubangiji, duba, shi wanda kake kauna yana rashin lafiya". 4 Da Yesu ya ji, sai ya ce "Wannan ciwo ba zai kai ga mutuwa ba, amma domin daukakar Allah ne, domin Dan Allah ya sami daukaka tawurin ta". 5 Yesu yana kaunar Matta, da 'yar'uwarta da Li'azaru. 6 Da yaji cewa Li'azaru na rashin lafiya, sai ya tsaya kwana biyu a inda ya ke. 7 Bayan haka, sai ya ce wa almajiransa, "Bari mu je Yahudiya kuma." 8 Sai almajiransa suka ce masa, "Mallam, harwayau Yahudaya na neman ka domin su jefe ka da duwatsu, kuma kana son komawa can?" 9 Yesu ya amsa, "Ba sa'a goma sha biyu ce ta haske a rana guda ba? Idan mutum ya yi tafiya da rana, ba za ya yi tuntube ba, domin yana gani ta wurin hasken wannan duniya. 10 Amma idan mutum ya yi tafiya chikin dare, za ya yi tuntube domin haske ba ya tare da shi. 11 Ya fadi wadannan al'amura, kuma bayan wadannan abubuwa, sai ya ce masu, "Abokinmu Li'azaru ya yi barci, amma zan je don In tashe shi daga barci". 12 Sai almajirai suka ce masa, "Ubangiji, idan barci yake yi, ai za ya farka." 13 Yesu kuwa ya yi maganar mutuwar Li'azaru ne, amma su suna tsammani yana magana akan barci ne na hutu. 14 Sai Yesu ya yi masu bayani cewa, "Li'azaru ya mutu. 15 Ina farinchiki domin ku, da bani a wurin domin ku gaskata. Bari mu je wurinsa." 16 Toma wanda ake kira Dan tagwaye, ya ce wa sauran almajirai, "Bari mu tafi domin mu mutu tare da Yesu." 17 Da Yesu ya iso, sai ya tarar cewa Li'azaru ya rigaya ya yi kwana hudu a kabari. 18 Baitanya kuma tana kusa da Urushalima, 'yar tafiya marar nisa ce a tsakanin su. 19 Yahudawa dayawa sun zo wurin Maryamu da Matta domin su yi masu ta'aziyar mutuwar dan'uwansu. 20 Da Matta ta ji cewa Yesu na zuwa, sai ta tafi domin ta same shi, amma Maryamu na zamne a cikin gida. 21 Matta ta ce wa Yesu, "Ubangiji, da kana nan tare da mu, da dan'uwana baya mutu ba". 22 Ko yanzu na san cewa duk abinda ka roka a wurin Allah, za ya ba ka. 23 Yesu ya ce mata, "Dan'uwanki za ya rayu kuma. 24 Sai Matta ta ce masa, "Na san zaya rayu kuma a tashin mattatu na ranar karshe." 25 Yesu ya ce mata, "Ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai; wanda ya bada gaskiya gare ni, ko ya mutu, za ya rayu; 26 Kuma duk wanda yake raye, ya kuma bada gaskiya gare ni, ba zai mutu ba dadai. Kin gaskata da wannan?" 27 Sai ta ce masa, "I, Ubangiji, Na gaskata cewa kaine Almasihu, Dan Allah, wanda ke zuwa duniya. 28 Sa'adda ta fadi haka, sai ta koma ta kira yar'uwarta Maryamu gefe guda. Ta ce, "mallam ya iso, kuma yana kiran ki." 29 Da ta ji haka, sai ta tashi da sauri ta tafi wurin sa. 30 Yesu bai rigaya ya shiga kauyen ba, yana nan inda Matta ta zo ta same shi. 31 Da Yahudawan nan dake tare da Maryamu, wato wadannan da suka zo mata ta'aziya, suka ga ta fita daga chikin gida da sauri, sai suka bi ta, suna tsammanin cewa ta tafi ta yi kuka ne a kabari. 32 Da Maryamu ta kai inda Yesu ya ke, sai ta fadi gaban sawayensa, ta ce, "Ubangiji, inda kana tare da mu, da dan'uwana bai mutu ba". 33 Da Yesu ya gan ta tana kuka, da wadannan Yahudawa da suka bi ta, sai ya yi juyayi a ruhu ya damu kuma; 34 sai ya ce, "A ina kuka kwantar da shi?" Sai suka ce masa, "Ubangiji, zo ka gani." 35 Yesu ya yi kuka. 36 Sai Yahudawa suka ce, "Dubi yadda yake kaunar Li'azaru!" 37 Amma wadansun su suka ce, "Shi wannan mutum da ya iya ba makaho ganin gari, da bai iya hana wannan mutum mutuwa ba? 38 Yesu yana cikin juyayi kuma a cikin kansa, sai ya tafi kabarin. Kabarin a kogo ne an kuma rufe bakinsa da dutse. 39 Sai Yesu ya ce, "A kawar da dutsen." Matta yar'uwar Li'azaru wanda ya mutu, ta ce wa Yesu, "Ubangiji, Yanzu jikin ya ruba domin ya kai kwana hudu da mutuwa". 40 Yesu ya ce mata, "Ba na ce maki idan kin gaskata za ki ga daukakar Allah ba?" 41 Sai suka kawar da dutsen. Yesu ya daga idanunsa ya ce, "Uba, na gode maka domin kana ji na." 42 Na san kana ji na a kowane lokaci, amma domin wannan taro da ke tsaye kewaye da ni nike wannan magana, domin su bada gaskiya cewa kaine ka aiko ni." 43 Bayan ya yi wannan magana, sai ya daga murya ya ce, "Li'azaru, ka fito!" 44 Sai mataccen ya fito; kafafunsa da hannayensa na daure da likkafani, fuskarsa kuma na lullube da tsumma. Yesu ya ce masu, "Ku kwance shi, ya tafi". 45 To dayawa daga cikin yahudawan da suka zo wurin Maryamu suka kuma ga abinda Yesu ya yi, suka gaskata da shi; 46 amma wadansu suka koma wurin farisawa suka fada masu abubuwan da Yesu ya yi. 47 Sai manyan firistoci da farisawa suka tara majalisa wuri guda, suka ce, "menene za mu yi?" Mutumin nan yana alamu masu yawa. 48 Idan mun kyale shi haka, duka za su gaskata da shi; Romawa za su zo su kwace wurinmu da al'ummar mu. 49 Duk da haka, wani daga cikin su wato, Kayafas wanda shine babban firist a wannan shekara, ya ce da su, "baku san komai ba". 50 Ba ku lura cewa ya fi maku kyau mutum daya ya mutu domin mutane, a maimakon dukan al'umma ta hallaka." 51 Ya fadi wannan ne ba don kansa ba, amma sabo da shine babban firist, ya yi anabci ne cewa ya kamata Yesu ya mutu domin al'ummar; 52 kuma ba don alummar kawai ba, amma domin a tattara 'ya'yan Allah da suke warwatse ko'ina wuri daya. 53 Tun daga wannan rana suka fara neman hanyar da za su kashe Yesu. 54 Tun daga nan Yesu ya dena tafiya a sarari chikin Yahudawa, amma sai ya koma wani yanki kusa da jeji a wani gari da ake kira Ifraimu. A can kuma ya zamna da almajiransa. 55 Idin ketarewa na Yahudawa ya yi kusa, da yawa sun tafi Urushalima daga yankin kasar kamin ranar idi domin su tsarkake kan su. 56 Suka shiga neman Yesu, suna magana da junan su yayin da suke tsaitsaye a haikali, cewa "me kuke tunani? Ba za ya zo idin bane?" 57 Babban firist da farisawa sun rigaya sun ba da umurni cewa duk inda aka ga Yesu a zo a shaida domin su kama shi.
Wadannan Sura su na gabatar da labarin Lazarus da kuma ba da tushen bayana game da shi da kuma yar'uwarsa Maryamu.
Sa'adda Yahaya ya gabatar da Maryamu, yar'uwar Mata, ya ba da bayani game da abin da zai faru anjuma a cikin labarin.
"roke Yesu ya zo"
A nan "kauna" ya na nufin kaunar 'yan'uwa, ta halitta, kauna na mutum a sakanin abokai da dangi.
Yesu ya na nufin cewa ya san abin da zai faru da Li'azaru da ciwonsa. AT: "Mutuwa ba zai zama .karshen sakamakon wannan ciwo ba"
Wannan ya na nufin mutuwa ta jiki.
Yesu ya na nufin cewa ya san abin da zai faru. AT: "amma wannan nufin shi don mutane su gan girman Allah domin abin da ikonsa zai yarda min in yi"
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
Wannan tushen bayani ne.
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nanata cewa almajiran ba su son Yesu ya tafi Urushalima. AT: "Mallam, haƙiƙa ba ka so ka koma can! Yahudawa sun so su jefe ka a loƙacin da ka na wurin!"
Wannan magana ne na shugabanin Yahudawa wadda su ka yi hamayya da Yesu. AT: " shugabanin Yahudawa"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin karin bayani. AT: "kun san cewa rana ya na da sa'a sha biyu na haske!"
Mutane da suke tafiya a cikin hasken rana su na iya gani da kyau kuma ba su yin tuntuɓe. "haske" magana ne na "gaskiya." Yesu ya na nufin cewa mutane da suke rayuwa bisa gaskiya su iya yin abubuwan da Allah ya na so su yi"
Yesu ya cigaba da magana da almajiransa.
A nan "dare" magana ne da ya na nufin tafiyar mutum da babu hasken Allah.
AT: 1) "ba ya iya gani" ko "ba shi da hasken Allah."
A nan "barci" karin magana ne da ya na nufin Li'azaru ya mutu. Idan ku na da wata hanyar faɗa wannan a harshenku, za ku iya yin amfani da shi a nan.
Kalmomin " tashe shi daga barci" karin magana ne. Yesu ya na bayyana shirinsa na sa Li'azaru ya rayu kuma. Idan ku na da karin magana na wannan a harshen ku, za ku iya amfani da shi ana.
Da shike almajiran ba su fahimci abin da yesu ya na nufi ba, sun ce ko Li'azaru ya na hutawa ne kuma zai warke.
"Sai yesu ya gaya masu a kalmomin da za su iya gane"
"domin amfanin ku"
"da ba na wurin. Domin wannan za ku iya gaskanta da ni sosai."
AT: "wadda su ke kira Ɗan tagwaye"
Wannan sunan na miji ne wadda ya na nufin "yan biyu."
AT: "ya ji cewa mutane sun riga sun sa Li'azaru a cikin kabari har kwana hudu kafin"
"nisar kilomita uku." "filinwasanni" mita ɗari da tamanin da biyar.
Li'azaru kaninsu ne. AT: "game da kaninsu"
Li'azaru ne kanin. AT: "har yanzu kani na zai rayu"
Li'azaru ne kanin. AT: "kanin ki zai rayu kuma"
"zai rayu kuma"
A nan "mutu" ya na nufin mutuwa ta jiki.
A nan "rayu" ya na nufin rayuwa ta ruhaniya.
"waɗɗanda su na raye kuma sun gaskanta da ni ba za a raba su daga Allah har abada ba" ko "wadanda su na raye kuma sun gaskanta da ni za su rayu ta ruhaniya tare da Allah har abada"
A nan "mutu" ya na nufin mutuwa ta ruhaniya.
"Matta ta ce wa Yesu"
Matta ta gaskanta cewa Yesu Ubangiji ne, Almasihu, (Mai ceto), Ɗan Allah.
Maryamu kanuwar Matta ne. AT: "ta je ta kira kanuwarta Maryamu"
Wannan lakabi ne da ya na nufin Yesu.
"ya ce ki zo"
Yahaya ya ba da yanka a labarin domin ya ba da tushen bayani game da inda Yesu yake.
Maryamu ta kwanta ko ta durkusa a sawayen Yesu don ta nuna ladabi.
Yahaya ya hada wadannan jumloli masu ma'ana iri ɗaya domin ya bayyana tsananin wuya da kuma fushi mai yiwuwa da Yesu ya ji. AT: "hankalinsa ya tashi sosai"
Wannan wata hanyar tambaya, "A inane kuka binne shi?"
"Yesu ya fara kuka"
Wannan ya na nufin kaunar yan'uwa ko kaunar mutum wa aboki ko ɗan iyali.
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nuna mamakin Yahudawa da cewa Yesu bai warkad da Li'azaru ba. AT: "Ya iya warkad da makaho, ai da ya iya warkad da wannan mutum don kadda ya mutu!" ko "Tun da bai hana mutumin nan daga mutuwa ba, watakila bai warkad da mutumin da an haife shi makaho ba, kamar yadda sun ce ya yi!"
AT: "warkad da idanun"
Yahaya ya tsayar da labarin domin ya kwatanta kabarin da mutanin suka binne Li'aziru.
Matta da Maryamu yayun Li'azaru ne. AT: "Matta, yayar Li'azaru"
"Yanzu za a sami wari" ko "jikin ya na doyi"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nanata cewa Allah zai yi abin ban mamaki. AT: "Na gaya maki cewa indan kin yarda da ni, za ki gan abin da Allah zai yi!"
Wannan karin magana ne da ya na nufin duba sama. AT: "Yesu ya duba sama"
Yesu ya yi addu'a wa Allah domin wadanda suke akewaye da shi su ji addu'ar sa. "Uba, Na gode da ka ji ni" ko "Uba, Na gode da ka ji addu'a na"
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
"Ina so du gaskanta da cewa kaine ka aiko ni"
"bayan da Yesu ya yi addu'a"
"ya yi ihu"
Al'adan biso na wannan lokacin shi ne a ana nada gawa a cikin dogon likkafani. AT: "Wani ya naɗe likkafani a hannayensa da kafafunsa. Sun kuma daura likkafani a fuskarsa da tsumma"
Kalmar "masu" ya na nufin mutane da suke wurin kuma sun gan abin al'ajibin.
"Sai shugabanne a cikin firistoci"
Marubucin ya yi amfani da wannan kalma domin ya gaya wa mai karatun cewa abin da ya faru a farkon Aya 47 abin da ya faru ne 11:45-46.
Wannan ya na nufin cewa mutanin majalisa su na maganar Yesu ne. AT: "me nene za mu yi game da Yesu?"
Shugabanin Yahudawa sun ji tsoro cewa mutanin za su gwada sa Yesu ya zama sarkin su. AT: "kowa zai yarda da shi su kuma yi wa Romawa tawaye"
Wannan magana ne na sojojin Romawa. AT: "sojojin Romawa za su zo"
"halaka haikalinmu da al'ummar mu"
Wata hanya ne na gabatar da sabon mutum a cikin labarin. Idan ku na da yadda za ku yi shi a harshen ku, za ku iya amfani da shi anan.
Wannan zuguiguitawa ne da Kayafas ya yi amfani don ya zage masu sauraransa. AT: "ba ku gane abin da ya na faruwa ba" ko kuma "ku na magana kamar ba ku san komai ba"
Kayafas ya na nufin cewa sojojin Romawa za su kashe dukka mutanin al'ummar Yahudawa idan an yarda Yesu ya zauna ya kuma sa tawaye. Kalmar "al'umma" magana ne da ya na wakilcin dukkan mutanin Yahudawa. AT: "a maimakon Romawa su kashe dukkan mutanin al'ummar mu"
Kalmar "al'umma" magana ne da ya na nufin mutanin al'ummar Isra'ila.
Wannan karin magana ne. Kalmar "mutane" ya na a bayyane a mahallin. AT: "za a tara zuwa mutane ɗaya"
Wannan ya na nufin mutane da sun zama na Allah ta wurin bangaskiya a cikin Yesu kuma 'ya'yan Allah ne ta ruhaniya.
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa kuma "tafiya a sarari" ya na nufin "zama a inda kowa zai iya ganin shi." AT: "zamna a inda dukkan Yahudawa za su iya ganin shi" ko kuma "yi tafiya a sarari a sakanin shugabanin Yahudawa da su ka yi hamayya da shi"
kauyen da su na wujen gari da mutane kadan suke zama.
Yesu da almajiransa sun zamnaIfraimu na dan lokaci. AT: "A caan ya zamna da almajiransa na dan lokaci"
An yi amfani da jumlar "tafi" domin Urushalima ya na tudu fiye da sauran wuraran.
Kalmar "su" ya na nufin mutanin Yahudawa wanda sun tafi Urushalima.
Wadannan tambayoyi sun bayyana shakkan cewa Yesu zai zo idin ketarewa. Tambaya na biyu karin magana ne da ya bayyana "kuke tunani."Masu magana su na tunani ko Yesu zai zo idin tun da akwai alamar kamar shi. "Watakila Yesu ba zai zo idin ba. Ya na iya jin tsoro kar a kama shi!"
Wannan tushen bayani ne da ya na fasara dalilin da Yahudawa masubi sun yi tunani ko Yesu zai zo idin ko babu. Idan harshenku ya na da wata hanyar sa tushen bayani, sai ayi amfani da shi anan.
Li'azaru, mutumin Baitanya ne. 'Yan'uwanensa Maryamu ne da Matta. Wannan Maryamun ne za ta shafa Ubangiji da mur ta kuma share masa kafafunsa da gashin kanta.
Yesu ya ce, "Wannan ciwo ba zai kai ga mutuwa ba, amma domin daukakar Allah ne, domin Dan Allah ya sami daukaka tawurin ta".
Yesu ya tsaya kwana biyu a inda ya ke.
Almajiransa suka ce masa, "Mallam, harwayau Yahudawa na neman ka domin su jefe ka da duwatsu, kuma kana son komawa can?"
Yesu ya ce idan mutum ya yi tafiya da rana, ba za ya yi tuntuɓe ba, domin yana gani ta wurin hasken rana.
Idan mutum ya yi tafiya chikin dare, za ya yi tuntuɓe domin haske ba ya tare da shi.
Almajiran su suna tsammani Li'azaru yana barci ne don hutu.
A loƙacin da Yesu ya ce Li'azaru na barci, ya na maganar mutuwar Li'azaru ne.
Yesu ya ce, "Ina farinchiki domin ku, da bani a wurin domin ku gaskata."
Toma ya zata za su mutu.
Li'azaru ya rigaya ya yi kwana hudu a kabari.
Sa'ad da Matta ta ji cewa Yesu ya na zuwa, ta je ta same shi.
Matta ta ce "ko yanzu, duk abinda ka roka a wurin Allah, za ya ba ka."
Ta ce masa, "Na san zaya rayu kuma a tashin mattatu na ranar karshe."
Yesu ya faɗa cewa duk wanda ya bada gaskiya gare shi, ko ya mutu, za ya rayu kuma duk wanda yake raye, ya kuma bada gaskiya gare ni, ba zai mutu ba
Matta ta ce masa, "I, Ubangiji, Na gaskata cewa kaine Almasihu, Ɗan Allah, wanda ke zuwa duniya.
Maryamu za ta je ta sami Yesu.
Yahudawan da suke tare da ita sun yi tsammanin cewa ta tafi ta yi kuka ne a kabari.
Yesu ya yi nishi ya kuma damu a cikin Ruhu bayan ya gan Maryamu tana kuka, da Yahudawa da suke tare da ita.
Sun ce Yesu ya na ƙaunar Li'azaru.
Matta ta ce, "Ubangiji, Yanzu jikin ya ruba domin ya kai kwana hudu da mutuwa".
Yesu ya ce wa matta, "Ba na ce maki idan kin gaskata za ki ga ɗaukakar Allah ba?"
Yesu ya daga idanunsa ya yi addu'a ga Ubansa.
Ya yi addu'a da ƙarfi ya kuma faɗa abin da ya yi domin taron da suke tsaye a kewaye da shi, domin su bada gaskiya cewa Uban ne ya aiko shi.
Mataccen ya fito, kafafunsa da hannayensa na ɗaure da likkafani, fuskarsa kuma na lullube da tsumma.
Dayawa daga cikin yahudawan da suka ga abinda Yesu ya yi, suka gaskata da shi, amma waɗansu suka koma wurin farisawa suka fada masu abubuwan da Yesu ya yi.
Kayafas ya ce masu abu mai daɗi ne cewa mutum ɗaya ya mutu domin mutane, a maimakon dukan al'umma ta hallaka.
Sun shirya yadda za su ƙashe Yesu.
Yesu ya dena tafiya a sarari chikin Yahudawa, amma sai ya koma wani yanki kusa da jeji a wani gari da ake kira Ifraimu. A can kuma ya zamna da almajiransa.
Sun ba da umurni cewa duk wanda ya san inda Yesu yake, a zo a shaida domin su kama shi.
1 Kwana shidda kafin idin ketarewa, Yesu ya zo Baitanya inda Li'azaru yake, wato wannan da Yesu ya tada daga matattu. 2 Sai suka shirya masa abinci a wurin kuma Matta ce ke hidima, Li'azaru kuwa ya kasance cikin wadanda ke kan tebiri tare da Yesu. 3 Sai Maryamu ta dauki wani turare da aka yi da man nard, ta shafe kafafun Yesu da shi, ta kuma share kafafun nasa da gashin kanta. Sai gida ya cika da kamshin turaren. 4 Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin almajiransa, wanda zai bashe shi, ya ce, " 5 "Me yasa ba a sayar da wannan turare dinari dari uku a ba gajiyayyu ba?" 6 Ya fadi haka ba don ya damu da gajiyayyu ba, amma domin shi barawo ne: shi ne ma'aji, kuma yana sata daga jakkar kudi. 7 Yesu ya ce, "Ku kyale ta ta ajiye abinda ta tanada domin jana'iza ta. 8 Gajiyayyu suna tare da ku a koyaushe, ni kuwa ba zan kasance da ku koyaushe ba. 9 To babban taron Yahudawa sun ji cewa Yesu yana wurin, sai suka zo, ba don Yesu kawai ba amma domin su ga Li'azaru, wanda Yesu ya tada daga matattu. 10 Sai manyan firistoci suka kulla makirci akan yadda za su kashe Li'azaru shima; 11 domin saboda shi ne yahudawa dayawa suka je suka bada gaskiya ga Yesu. 12 Kashegari, babban taro suka zo idin. Da suka ji cewa Yesu na zuwa Urushalima, 13 Sai suka dauki ganyen dabino suka fita gari suka tare shi da kira mai karfi suna cewa, "Hosanna! Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji, Sarkin Isra'ila. 14 Yesu ya sami wani Aholakin jaki, ya hau kansa; kamar yadda aka rubuta, 15 "Kada ki ji tsoro ke 'yar Sihiyona; duba, ga Sarkinki na zuwa, zaune a kan danJaki". 16 Almajiransa basu fahimci wannan al'amari ba da farko, amma bayan da aka daukaka Yesu, sai suka tuna cewa an rubuta wadannan abubuwa game da shi, kuma sun yi masa wadannan abubuwa. 17 Sai taron da ke tare da Yesu a ranar da ya kira Li'azaru daga kabari ya kuma tashe shi daga matattu, suka bada shaida. 18 Domin wannan ne kuma taron suka zo domin su sadu da shi saboda sun ji cewa ya yi wannan alama. 19 Don haka, sai farisawa suka shiga magana a tsakanin su suna cewa "Duba, babu abinda zaku iya yi; kun ga, duniya ta gama bin sa. 20 Akwai wadansu Helinawa cikin wadanda suka je sujada a idin. 21 Wadannan suka tafi wurin filibus, mutumin Betsaida da ke Galili, suka ce masa, "Mallam, muna so mu ga Yesu. 22 Filibus ya tafi ya fadawa Andrawus; sai Andrawus ya tafi tare da Filibus, suka kuwa gaya wa Yesu. 23 Yesu ya amsa masu ya ce, "sa'a ta zo da za'a daukaka Dan mutum. 24 Hakika, hakika, Ina ce maku, in ba kwayar alkama ta fadi kasa ba ta mutu, za ta kasance ita kadai; amma idan ta mutu, za ta bada 'ya'ya masu yawa. 25 Duk wanda yake son ransa, zai rasa shi; amma wanda ba ya son ransa a duniyan nan za ya kiyaye shi domin rayuwa ta har abada. 26 Idan wani na bauta mani, to bari ya biyo ni; kuma duk inda nike, a can bawana zai kasance kuma. Duk wanda ke bauta mani, Uban zai girmama shi. 27 Yanzu raina na cikin damuwa, to me zan ce? 'Uba, ka cece ni daga wannan sa'a? Amma Saboda wannan dalili ne na zo wannan sa'a. 28 Uba, ka daukaka sunanka". Sai wata murya daga sama ta ce, "Na daukaka shi, zan kuma sake daukaka shi. 29 Daganan sai taron dake tsaye kuma suka ji muryar, suka ce an yi tsawa. Wasu suka ce, "Mala'ika ya yi magana da shi". 30 Yesu ya amsa ya ce, "wannnan murya ta zo ba saboda ni ba, amma domin ku." 31 Yanzu za'a shar'anta duniya. Yanzu za'a kori mai mulkin duniyan nan. 32 Sa, annan ni, idan an daga ni daga duniya, zan jawo dukan mutane zuwa gare ni". 33 Ya fadi wannan ne domin ya nuna irin mutuwar da za ya yi. 34 Taro suka amsa masa cewa, "Mun ji a cikin shari'a cewa Almasihu za ya kasance har abada. Yaya za ka ce, 'za'a daga dan mutum'? Wanene wannan dan mutum?" 35 Yesu ya ce masu, "Nan da lokaci kadan za ku kasance da haske, ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya mamaye ku. Wanda ke tafiya cikin duhu, bai san inda za shi ba. 36 Ku gaskata ga haske tun yana tare da ku domin ku zama yayan haske". Yesu ya fadi wadannan abubuwa sannan ya tafi ya boye masu. 37 Kodashike Yesu ya yi alamu da dama a gabansu, duk da haka ba su gaskata shi ba. 38 Saboda maganar annabi Ishaya ta cika, wadda ya ce, "Ubangiji, wa ya gaskata rahoton mu? Ga wa kuma hannun Ubangiji ya bayyana? 39 Saboda wannan dalili basu gaskata ba, gama Ishaya ya sake cewa, 40 ya makantar da su, ya kuma taurare zuciyarsu, saboda kada su gani da idanunsu, su kuma sami fahimta da zuciyarsu, su juyo wurina in warkar da su. 41 Ishaya ya fadi wadannan abubuwa ne domin ya hangi daukakar Yesu ya kuma yi magana game da shi. 42 Amma duk da haka, dayawa cikin shugabanni suka gaskata Yesu. Amma saboda farisawa, basu shaida shi a sarari ba, domin kada a kore su daga majami'a. 43 Suna son yabo daga mutane fiye da yabon dake zuwa daga Allah. 44 Yesu ya yi magana da babbar murya, ya ce, "Wanda ya gaskata ni, ba ni yake gaskatawa kadai ba, amma kuma yana gaskata wanda ya aiko ni, 45 kuma wanda ke gani na, yana ganin shi wanda ya aiko ni. 46 Na zo ne a matsayin haske a duniya, saboda duk wanda ya gaskata da ni ba za ya yi tafiya cikin duhu ba. 47 Duk wanda ya ji maganata baya gaskata ba, ba ni hukunta shi; gama ban zo in yi wa duniya hukunci ba, amma don in ceci duniya. 48 Wanda ya ki ni, ya kuma ki ya karbi magana ta, akwai wanda za ya yi masa hukunci. Kalmar da na fada, ita ce za ta yi masa hukunci a rana ta karshe. 49 Maganar da ni ke yi, ba ra'ayina ba ne. Amma Uba wanda ya aiko ni shi ke bani umarni game da abin da zan ce da abin da zan fadi. 50 Na san umarninsa rai ne madawwami, don haka na ce - kamar yadda Uba ya fada, haka ni ma nake fadi."
Yesu ya na cin abinci a Baitani a lokacin da Maryamu ta shafa kafafunsa da turare.
Marubucin ya yi amfani da wannan kalmomin domin ya nuna farawan sabon abu.
AT: "ya sa shi ya rayu kuma"
Za ku iya mai da wannan zuwa awu na zamani. "lita" kusan rabin kilo ne. Ko kuma ku yi amfani da wani abu da zai iya rike yawan turaran. AT: "rabin kilo na turare" ko "kwalbar turare"
Wannan wata ruwa-ruwan abu ne mai kamshi da kuma kyau ne da an yi shi daga man itace da fure mai kamshi.
Wannan turane ne da an yi shi daga wata fure a cikin duwasun Nepal, China da kuma India.
AT: "kamshin turarenta ya cika gidan"
"wadda ya sa an iya kama Yesu"
Wannan tambaya ne da ba ya neman amsa. Za ku iya fasara shi kamar babban jumla. AT: "za a iya sayar da wannan turare dinari dari uku a kuma yi amfani da kudin don a taimake talakawa!"
AT: "dinari ɗari uku"
Dainari kudin azurfa ne da ma'aikaci ya ke samuwa a rana ɗaya.
Yahaya ya bayyana dalilin da ya sa Judas ya yi tambaya game da talakawa. Idan harshen ku ya na da wata hanyar nuna tushen bayani, zaku iya yin amfani da shi a nan.
"ya faɗi haka domin shi barawo ne. Bai damu da talakawa ba"
Yesu Ya na nufin cewa ayukkan matan ya nuna cewa su na saurarar mutuwa da bisonsa. AT: "Bar ta ta nuna yadda take kauna na! A haka ne ta shirya biso na"
Yesu ya na nufin cewa akwai hanyoyi dayawa da za a iya taimakon talakawa. AT: "za a sami talakawa koyaushe a sakaninku, kuma za ku iya taimake su a duk loƙacin da ku na so"
A haka, Yesu ya na nufin zai mutu. AT: "Amma ba zan kasance tare da ku kayaushe ba"
An yi amfani da wannan kalma domin a sa layi a ainihin labarin. A nan Yahaya ya yi magana game da sabon kungiyar mutane da sun zo Betini daga Urushalima.
Rayuwar Li'azarus ne ya sa Yahudawa dayawa suka gaskanta da Yesu.
Wannan ya na nufin cewa mutanin Yahudawa dayawa sun na ba da gaskiya ga Yesu"
Marubucin ya yi amfani da waɗannan kalmomi domin ya fara sabon abu.
"babban taron mutane"
Wannan na nufin "Bari Allah ya cece mu yanzu"
Wannan ya bayyana yadda Allah ya na so ya sa abubuwa masu kyau su faru wa mutum.
A nan kalmar nan " suna" magana ne na karfi da ikon mutum. AT: "zuwa kamar wakilin Ubangiji" ko "zuwa a cikin sunan Ubangiji"
A nan Yahaya ya ba da tushen bayani cewa Yesu ya sami jaki. Ya na nufin cewa Yesu zai hawo jaki zuwa Urushalima. AT: "ya sami aholakin jaki sai ya zanna a kai, tafiya zuwa Urushalima"
AT: "yadda annabawa suka rubuta a cikin nassi"
"'Yar Sihiyona" ya na nufin mutanin Urushalima. AT: "ku mutanin Urushalima"
A nan kalmomin "wannan al'amari" ya na nufin kalmomin da annabi ya rubuta game da Yesu.
AT: "loƙacin da Allah ya ɗaukaki Yesu"
Kalmomin "wadannan abubuwa" ya na nufin abin da mutane sun yi a loƙacin da Yesu ya shiga cikin Urushalima a kan jaki (yabon shi da kuma nuna reshen giginya).
"sun ji wadansu su na ce ya yi wannan alama"
"Alama" abu ne ko abin da ya faru, wadda ya na nuna cewa abin gaskiya ne. A wannan magana, "Alamar" ta da Li'azaru ya nuna cewa Yesu ne mai ceto.
Farisawan su na nufin anan cewa ba za a iya hana Yesu ba. AT: "kamar ba za mu iya yin komai don mu hana shi ba"
Farisawa sun yi amfani da wannan zuguiguitawa domin su bayyana mamakin cewa mutane da yawa sun fito don su gan Yesu. AT: "kamar kowa ya na zama almajiransa"
A nan " duniya" magana ne da ya na wakilcin
Wannan jumla "Yanzu wadansu" ya nuna gabatarwar sabobin mutane a cikin labarin.
Yahaya ya na nufin cewa wadannan "helinawa" su na tafiya zuwa yabon Allah a loƙacin ketarewa. AT: "don a yabe Allah a idin ketarewa"
Wannan gari ne a yankin Galili.
Fillibus da Andrawas sun faɗa wa Yesu game da rokon da Helinawa sun yi don su gan shi. AT: "Sun gaya wa Yesu abin da Helinawan sun ce"
Yesu ya na nufin cewa yanzu ne daidan loƙaci da yakamata Allah ya ɗaukaki Ɗan Mutum ta wurin wahala mai zuwa, mutuwa da tashiwa. AT: "Allah zai ɗaukake ni a loƙacin da in na mutu da kuma tashi"
Fasara shi a yadda harshenku ya na nanata cewa abu na-biye ya na da muhiminci kuma gaskiya ne. Dubi yadda kun fasar "Hakika, hakika" a cikin 1: 51.
A nan "kwayar alkama" ko "iri" magana ne na mutuwa, biso, da kuma tashin Yesu.Yadda ana shuka iri kuma ya na girma zuwa shuka da zai ba da 'ya'ya, haka ne mutane dayawa za so gaskanta da Yesu a bayan an kashe shi, an binne shi, ankuma ta da shi daga mattatu.
A nan "son ransa" ya na nufin yadda ka na duba rai na jikinka da amfani fiye da rayukan wadansu. AT: "duk wadda ya na ɗaukakar ransa fiye da wadansu ba zai karɓi rai na har abada ba"
A nan wanda ya "ki ransa" ya na nufin wanda ya na son ran wadansu fiye da ransa. AT: "duk wanda ya ɗauki rayukan wadansu da muhiminci fiye da ransa zai rayu da Allah har abada"
Yesu ya na nufin cewa wadanda sun bauta masa ne za su kasance tare da shi a cikin sama. AT: "Bawa na zai kasance tare da ni a wurin, loƙacin da ina cikin sama"
A nan "Uba" muhimmin lakabi ne wa Allah.
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne. Kodashike Yesu ya so ya ki giciye, ya zaba ya yi biyyaya ga Allah a kuma kashe shi. AT: "Ba zan yi addu'a, 'Uba, ka cece ni gaga wannan sa'a!'"
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
A nan "wannan sa'a" magana ne da ya na wakilcin loƙacin da Yesu zai sha wahala ya kuma mutu a kan giciye.
A nan kalmar "suna" magana ne da ya na nufin Allah. AT: "sa ɗaukakar ka sananne" ko "bayyana ɗaukakar ka"
Wannan ya na wakilcin maganar Allah. Wadansu loƙaci, mutane su na kin kiran Allah domin suna daraja shi. AT: "Allah ya yi magana daga sammai"
A nan "wannan duniya" ya na nufin dukka mutane a cikin duniya. AT: "Yanzu ne loƙaci da Allah zai sharanta dukka mutane"
A nan "mai mulki" ya na nufin shaiɗan. AT: "Yanzu ne loƙacin da zan hukunta ikon shaiɗan da ya na mulkin wannan duniya"
Yesu ya na nufin giciyewarsa. AT: "A loƙacin da mutane sun daga ni sama a kan giciye"
Ta wurin giciyensa, Yesu zai tanada hanyar wa kowa don ya gaskanta da shi.
Yahaya ya fasara kalmomin Yesu cewa mutane za su giciye shi. AT: "Ya faɗi wannan domin ya sa mutanin su san yadda zai mutu"
Jumlar "daga" ya na nufin giciye. Za ku iya fasara shi da karin "a kan giciye." AT: "dole ne a daga dan mutum a kan giciye"
AT: 1) "Menene ainahin wannan Ɗan Mutum? ko kuma 2) "Wa ne irin Ɗan Mutum ne ka na magana a kai?"
A nan "haske" ya na nufin koyarswar yesu da ya bayyana gaskiyar Allah. Yi "tafiya cikin duhu" magana ne da ya na nufin yin rayuwa da ba tare da gaskiyar Allah ba. AT: "Magana ta ya na nan kamar haske ne a gareku, domin ya taimake ku ku fahimci yadda za ku yi rayuwa kamar yadda Allah ya na so ku yi. Ba zan kasance tare da ku sosai ba. Yakamata ku bi dokokina tun ina tare da ku. Idan kun ki magana ta, zai zama kamar tafiya ne a cikin duhu kuma ba za ku iya ganin inda za ku je ba"
"Haske" magana ne na koyarswar Yesu da ya bayyana gaskiyar Allah. "'ya'yan haske" magana ne na wadanda sun karɓa sakon Yesu kuma su na rayuwa a bisa gaskiyar Allah. AT: "Tun ina tare da ku, ku gaskanta da abin da ina koyar maku domin gaskiyar Allah ya kasance da ku"
AT: "domin a cika sakon annabi Ishaya"
Wannan ya bayyana kamar tambaya ne da baya neman amsa domin ya nuna tsoratawar annabin cewa mutanin basu gaskanta da sakon shi ba. AT: "Ubangiji, Da ker ne idan wanni ya gaskanta da sakon mu, kodashike sun gan cewa ka na da ikon cece su!"
Wannan magana ne da ya na nufin ikon ceton Ubangiji.
A nan "zuciya" magana ne na hankalin mutum. Jumlar "taurare zuciyarsu" magana ne na sa wani ya zama da taurin kai. Kuma, "fahimta da zuciyarsu" ya na nufin "fahimta sosai." AT: "ya sa su taurin kai ... fahimta sosai"
A nan "juyo" magana ne na "tuba." AT: "kuma za su tuba"
AT: "domin kada mutane su hana su daga tafiya zuwa majami'a.
"Sun so mutane su yaɓe su fiye da yadda sun so Allah ya yaɓe su"
A nan Yahaya ya na nufin cewa taron mutane sun taru domin su ji Yesu ya yi magana. AT: "Yesu ya yi wa taron da suka taru ihu"
A nan kalmar "shi" ya na nufin Allah. AT: "wanda ya gan ni ya gan Allah, wadda ya aike ni"
Yesu ya cigaba da magana da taron.
A nan "haske" magana ne na gurbin Yesu. AT: "Na zo ne in nuna gaskiyan"
A nan "duhu" magana ne na yin rayuwa a rashin sanin gaskiyar Allah. AT: "ba za ya cigaba da makanta a ruhaniya ba"
A nan "yi wa duniya hukunci" ya na nufin hukunci. Yesu bai zo don ya hukunta mutane ba. AT: "idan wani ya ji koyarswa ta ya kuma ki, ban hukunta shi ba. Ban zo don in hukunta mutane ba. Maimako, Na zo ne don in cece wadanda sun gaskanta da ni"
"a lokacin da Allah ya na hukunta zunuban mutane"
"Na san cewa kalmomin da ya umurce ni in fada kalmomi ne da ya na ba da rai na har abada"
Ya dawo kwana shidda kafin idin ketarewa.
Maryamu ta ɗauki litar wani turare da aka yi da man nard, ta shafe kafafun Yesu da shi, ta kuma share kafafun nasa da gashin kanta.
Yahuza ya faɗi haka ba don ya damu da gajiyayyu ba, amma domin shi barawo ne: shi ne ma'aji, kuma zai sata daga jakkar kuɗin wa kansa.
Yesu ya ce, "Ku kyale ta ta ajiye abinda ta tanada domin jana'iza ta. Gajiyayyu suna tare da ku a koyaushe, ni kuwa ba zan kasance da ku koyaushe ba."
Sun zo don Yesu kuma domin su ga Li'azaru, wanda Yesu ya tada daga matattu.
Sun so su ƙashe Li'azaru saboda akan shi ne yahudawa dayawa suka je suka bada gaskiya ga Yesu.
Suka ɗauki ganyen dabino suka fita gari suka tare shi da kira mai ƙarfi suna cewa, "Hosanna! Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji, Sarkin Isra'ila."
Annabcin cewa Sarkin Sihiyona zai zo, a zaune a kan ɗan Jaki ne ya cika.
Sun fita su sami Yesu domin sun ji daga masu shaidu cewa Yesu ya kira Li'azaru daga kabari, ya kuma ta da shi daga matattu.
Yesu ya amsa masu ya ce, "sa'a ta zo da za'a daukaka Dan mutum.
Yesu ya ce idan ta mutu, za ta ba da 'ya'ya dayawa.
Yesu ya ce duk wanda yake son ransa, zai rasa shi, amma wanda ba ya son ransa a duniyan nan za ya kiyaye shi domin rayuwa ta har abada.
Uban zai ɗaukaka shi.
Wata murya daga sama ta ce, "Na ɗaukaka shi, zan kuma sake ɗaukaka shi."
Yesu ya ce, "wannnan murya ta zo ba saboda ni ba, amma domin ku (Yahudawa)."
Yesu ya ce, "Yanzu za'a shar'anta duniya. Yanzu za'a kori mai mulkin duniyan nan."
Yesu ya faɗi wannan ne domin ya nuna irin mutuwar da za ya yi.
A'a, bai amsa tambayoyin kai tsaye ba.
Yesu ya ce, "Nan da loƙaci kadan za ku kasance da haske, ku yi tafiya tun kuna da haske ... "Ku gaskata ga haske tun yana tare da ku domin ku zama yayan haske".
Ba su gaskata ba saboda maganar annabi Ishaya ta cika, wadda ya ce, " Ubangiji, wa ya gaskata rahoton mu? Ga wa kuma hannun Ubangiji ya bayyana?
Basu iya gaskanta ba saboda yadda Ishaya ya ce, "ya makantar da su, ya kuma taurare zuciyarsu, saboda kada su gani da idanunsu, su kuma sami fahimta da zuciyarsu, kuma za su juyo wurina in warkar da su."
Ishaya ya faɗi waɗannan abubuwa ne domin ya hangi ɗaukakar Yesu.
Ba za su shaida shi domin suna tsoron Farisawa domin kada a ƙore su daga majami'a. Suna son yaɓo daga mutane fiye da yaɓon dake zuwa daga Allah.
Yesu ya ce, "Wanda ya gaskata ni, ba ni yake gaskatawa kadai ba, amma kuma yana gaskata wanda ya aiko ni, kuma wanda ke gani na, yana ganin shi wanda ya aiko ni."
Yesu ya zo don ya ceci duniya.
Kalmar da Yesu ya faɗa, ita ce za ta hukunta waɗanda sun ƙi shi a rana ta karshe.
A'a. Uba wanda ya aiko Yesu shi ke ba shi umarni game da abin da zai ce da abin da zai faɗi.
Yesu ya yi wannan domin ya san umarninsa rai ne madawwami.
1 Kamin bukin idin ketarewa, sa'adda Yesu ya san lokaci ya yi da zai tashi daga wannan duniya zuwa wurin Uba, da yake ya kaunaci nasa wadanda ke duniya- ya kaunace su har karshe. 2 Iblis ya rigaya ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti dan Saminu, ya bashe da Yesu. 3 Ya san cewa Uba ya bada kome a hannunsa, kuma ya zo daga wurin Allah, kuma zai koma wurin Allah. 4 Ya tashi daga cin abincin, ya tube tufafinsa, ya dauki tawul ya lullube kansa da shi. 5 Sa'an nan ya zuba ruwa a bangaji, ya fara wanke kafafun almajiran, yana shafe su da tawul din da ya lullube jikinsa da shi. 6 Ya zo wurin Bitrus Saminu, sai Bitrus ya ce masa,"Ubangiji, za ka wanke mani kafa?" 7 Yesu ya amsa ya ce, "Abin da nake yi ba za ka fahimce shi yanzu ba, amma daga baya za ka fahimta." 8 Bitrus ya ce masa, "Ba za ka taba wanke mani kafa ba." Yesu ya amsa masa ya ce, "In ban wanke maka ba, ba ka da rabo da ni". 9 Bitrus ya ce masa, "Ubangiji, ba kafafuna kadai za ka wanke ba, amma da hannayena da kaina." 10 Yesu ya ce masa, "Duk wanda ya yi wanka ba ya da bukata, sai dai a wanke kafafunsa, amma shi tsarkakakke ne baidaya; ku tsarkakakku ne, amma ba dukanku ba." 11 (Don Yesu ya san wanda zai bashe shi, shiyasa ya ce, "Ba dukanku ne ke da tsarki ba.") 12 Bayan Yesu ya wanke masu kafafu, ya dauki tufafinsa ya zauna kuma, ya ce masu, "Kun san abin da na yi muku? 13 kuna kirana, 'Malam, da Ubangiji,' kun fadi daidai, don haka Nake. 14 Idan ni Ubangiji da kuma mallam, na wanke maku kafafu, ya kamata kuma ku wanke wa junan ku kafafu. 15 Gama na baku misali, saboda ku yi yadda na yi maku. 16 Lalle hakika ina gaya muku, bawa ba ya fi mai gidansa girma ba; dan aike kuma ba ya fi wanda ya aiko shi girma ba. 17 Idan kun san wadannan abubuwa, ku masu albarka ne idan kun aikata su. 18 Ba ina magana akan dukanku ba; Na san wadanda na zaba. Amma domin Nassi ya cika: 'Shi Wanda ya ci gurasata, ya tayar mani'. 19 Ina fada maku wannan yanzu tun kafin haka ta faru domin sa'adda ta faru, ku gaskata Ni ne. 20 Hakika, hakika, Ina gaya maku, wanda ya karbi wanda na aiko, Ni ya karba, wanda kuma ya karbe ni, ya karbi wanda ya aiko ni. 21 Bayan Yesu ya fadi haka, ya damu a ruhu, ya yi shaida ya ce, "Lalle hakika, ina gaya muku cewa daya daga cikinku zai bashe ni." 22 Almajiran suka kalli juna, suna juyayin ko akan wa yake magana. 23 Daya daga cikin almajiransa, wanda Yesu yake kauna, yana a teburi, jingine a kirjin Yesu. 24 Siman Bitrus ya ce wa almajirin, "ka fada mana ko akan wa ya ke magana." 25 Sai ya sake jingina a kirjin Yesu, ya ce masa, "Ubangiji, wanene?" 26 Sannan Yesu ya amsa, "Shine wanda zan tsoma gutsuren gurasa in ba shi." Sannan bayan ya tsoma gurasar, sai ya ba Yahuza Dan Siman Iskariyoti. 27 To bayan gurasar, sai shaidan ya shige shi, sai Yesu ya ce masa, "Abinda kake yi, ka yi shi da sauri." 28 Babu wani a teburin da ya san dalilin dayasa ya fada masa wannan. 29 Wadansu sun yi tsamanin cewa, tun da Yahuza ne ke rike da jakkar kudi, Yesu ya ce masa, "Ka sayi abinda muke bukata don idin", ko kuma ya bada wani abu domin gajiyayyu. 30 Bayan Yahuza ya karbi gurasar, sai ya fita nan da nan. Da daddare ne kuwa. 31 Bayan Yahuza ya tafi, Yesu ya ce, "Yanzu an daukaka Dan mutum, kuma an daukaka Allah a cikinsa. 32 Allah zai daukaka shi a cikin kansa, kuma zai daukaka shi nan da nan. 33 'Ya'ya kanana, ina tare da ku na wani gajeren lokaci. Zaku neme ni, kuma kamar yadda na fadawa Yahudawa, 'in da zan tafi ba za ku iya zuwa ba.' Yanzu kuma na fada maku wannan. 34 Ina baku sabuwar doka, ku kaunaci juna; kamar yadda na kaunace ku, haka kuma ku kaunaci juna. 35 Ta haka kowa zai san ku almajiraina ne, idan kuna kaunar juna." 36 Siman Bitrus ya ce masa, "Ubangiji, ina za ka?" Yesu ya amsa ya ce, "Inda za ni, ba zaka iya bi na ba yanzu, amma zaka bini daga baya." 37 Bitrus ya ce masa, "Ubangiji, don me ba zan iya binka a yanzu ba? Zan bada raina domin ka." 38 Yesu ya amsa ya ce, "Za ka bada ranka domina? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara zaka yi musu na sau uku."
Ketarewa bai kai ba kuma Yesu ya na tare da almajiransa a abincin dare. Wadannan ayoyin sun bayyana shirin wannan labari, sun kuma ba da tushen bayani game da Yesu da Yahuza.
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai abin da sun yi
Jumlar "sa a zuciyar" karin magana ne da ya na nufin a sa wani ya yi tunanin wani abu. AT: "Iblis ya riga ya sa Yahuza Iskariyoti, dan Saminu, da yin tunanin cin amanar Yesu"
Aya uku ya cigaba da gaya mana game da tushen bayani game da abin da Yesu ya sani. Abin ya fara a aya hudu.
A nan "hannunsa" magana ne da ya na nufin iko da karfi. AT: "ya ba ni cikakken iko a komai"
Yesu ya saba kasancewa da Uban, kuma zai koma wurin bayan aikinsa a duniya ya kare.
Domin yankin na da kura, al'ada ne wa mai gidan da ya ba da abincin ya ba da bawan da zai wanke kafafun baki.
Tambayar Bitrus ya nuna cewa bai so Yesu ya wanke mashi kafa. AT: "Ubangiji, ba daidai ba ne ka wanke mani kafa na ba, mai zunubir!"
Yesu ya yi magana domin ya sa Bitrus ya yarda ya wanke mashi kafa. Yesu ya na nufin cewa dole Bitrus ya yarda Yesu ya wanke masa kafa idan ya na so ya cigaba da zama almajiransa. AT: "Idan na wanke ka, kullum za ka kasance nawa"
A nan "wanka" magana ne da ya na nufin cewa Allah ya wanke ruhaniyar mutum. AT: "Idan wani ya riga ya karbi yafewar Allah, yanzu ya kamata ya karbi wankewa daga zunubansa na kullum"
Yesu ya na nufin cewa wadda zai bashe shi, Yahuza, bai gaskanta da shi ba. Don haka Allah bai yafe masa zunubansa ba. AT: "Ba dukkan ku ne kun karbi yafewar Allah ba"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne don Yesu ya iya bayana muhimincin abin da ya na koyar wa almajiransa. AT: "Ya kamata ku fahimci abin da na yi maku!"
A nan Yesu ya na nufin cewa almajiransa su na da babban daraja masa. AT: "Kun nuna mani babban daraja a lokacin da kun kira ni "Mallam" da "Ubangiji."
Yesu ya na nufin cewa almajiransa su yarda su bi gurbinsa su kuma bauta wa junansu. AT: "ku kuma bauta wa junanku da ladabi"
Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 1:51.
wanin da yafi muhiminci ko iko, ko wanin da ya kamata ya sami saukin rayuwa ko dadin rayuwa sosai.
A nan "albarka" na nufin sa kyaun abubuwa su faru da mutum. AT: "Allah zai albakarkance ka"
AT: "wannan domin nassi ya cika"
Jumlar "ci gurasata" anan karin magana ne na wani da ya na yi kamar aboki. Jumlar "tayar" magana ne kuma daya na nufin mutum da ya zama abokin gaba. Idan ku na da karin magana a harshen ku da ke da wannan ma'ana, za ku iya yin amfani da shi anan. AT: "wadda ya yi kamar shi abokina ne ya koma ya zama makiya na"
"Inna gaya maku abin da zai faru yanzu kafin ya faru"
"Za ku iya gaskanta cewa ni ne wadda na ce ni ne" ko "Za ku iya gaskanta cewa ni ne mai ceto"
damu
"Almajiran sun kalli juna da mamaki: "Wa nene zai ci amanar Yesu?
Wannan ya na nufin Yahaya.
A zamanin Almasihu, Yahudawa su na yawan cin abinci tare kamar salon Greek, wadda suke zauna a gefe daya a kujeru kanana.
An dauke kukwance da kai a gefen wani mai cin abinci a salon Greek kamar nuna babban kauna ne a sakaninsu.
Wannan ya nuna cewa Yahuza daga kawyen Kerot ne.
An fahimci kalmomin "Yahuza ya dauke" a mahalli.
Wannan karin magana ne da ya na nufin shaiɗan ya dauki cikakken shugabancin Yahuza. AT: "Shaiɗan ya dauke shugabancinsa" ko "Shaiɗan ya fara umurce shi"
A nan Yesu ya na magana da Yahuza.
"Ya sauri da abin da ka ke shirin aikatawa!"
"je ka ba da kudade wa talakawa."
Yahaya ya so ya jawo hankali da cewa Yahuza zai aikata muguntarsa ko ayyukan "duhu" a cikin duhun dare. AT: "ya fita nan da nan cikin duhun dare"
AT: "Yanzu mutane za su ga yadda Ɗan Mutum zai karba daukaka kuma da yadda Allah zai karbi daukaka ta wurin abin da Ɗan Mutum ya ke yi"
Kalmar "shi" ya na nufin Ɗan Mutum. Wannan kalmar "kansa" magana ne da ya na nufin Allah. AT: "Allah zai ba da daukaka wa Ɗan Mutum nan da nan"
Yesu ya yi amfani da wannan magana "'Ya'ya kanana" domin ya nuna cewa ya na kaunar almajiransa kamar su 'ya'yan shi ne.
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa da su ka yi hamayya da Yesu. AT: "kamar yadda na faɗawa Yahudawa"
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai abin da sun yi
Za ku iya sa a bayyane cewa wannan zuguiguitawa ya na nufin mutane da suka gan yadda almajiran sun kaunace juna.
"ba da raina" ko "mutu"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin karin bayani game maganar Yesu. AT: "Ka ce za ka mutu domina, amma gaskiyan shi ne ba za ka yi ba!"
"za ka ce baka san ni sau uku kafin zakara ya yi cara"
Ya kaunace su har karshe.
Iblis ya rigaya ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti, ya bashe da Yesu.
Yesu ya zo daga wurin Allah, kuma zai koma wurin Allah.
Uba ya bada komai a hannun Yesu.
Ya tube tufafinsa, ya dauki tawul ya lullube kansa da shi. Sa'an nan ya zuba ruwa a bangaji, ya fara wanke kafafun almajiran, ya shafe su da tawul din da ya lullube jikinsa da shi.
Yesu ya ce, "In ban wanke maka ba, ba ka da rabo da ni".
10Yesu ya fada wannan domin ya san wanda zai bashe shi.
Yesu ya wanke wa almajiransa kafafu domin ya ya basu misali, saboda su yi yadda ya yi masu.
Bawa ba ya fin mai gidansa girma kuma dan aike ba ya fin wanda ya aiko shi girma ba.
Shi Wanda ya ci gurasasa, ya tayar masa.
Yesu ya fada masu wannan yanzu tun kafin haka ta faru domin sa'adda ta faru, su gaskata Ni ne.
Idan kun karbi Yesu, za ku karba duk wanda ya aiko kuma za ku karbi wanda ya aiko Yesu.
Siman Bitrus ya ce wa almajirin, "ka fada mana ko akan wa ya ke magana."
Yesu ya amsa, "Shine wanda zan tsoma gutsuren gurasa in ba shi." Sannan bayan ya tsoma gurasar, sai ya ba Yahuza Dan Siman Iskariyoti.
Bayan Yahuza ya karbi gurasar, Shaidan ya shige shi sai ya fita nan da nan.
Bayan Yahuza ya karbi gurasar, Shaidan ya shige shi sai ya fita nan da nan.
Za a ɗaukaka Allah ta wurin ɗaukaka Dan mutum. Sa'ad da an ɗaukaka Dan mutum, an ɗaukaka Allah.
A'a, Siman Bitrus bai fahimta ba domin ya tambayi Yesu, "Ubangiji, ina za ka?"
Sabon umarnen shi ne su ƙaunaci juna; kamar yadda ya ƙaunace su.
Yesu ya ce ta wurin yin biyayya da waɗannan umarnen, dukka mutane za su san cewa su almajiransa ne.
A'a, Siman Bitrus bai fahimta ba domin ya tambayi Yesu, "Ubangiji, ina za ka?"
Yesu ya amsa ya ce, " Za ka bada ranka domina? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara zaka yi musu na sau uku."
1 "Kada zuciyarku ta bachi. Kun gaskata da Allah, sai kuma ku gaskata da ni. 2 A gidan Ubana akwai wurin zama dayawa. Da ba haka ba, da na fada maku, domin zan tafi in shirya maku wuri. 3 In kuwa na je na shirya maku wuri, zan dawo in karbe ku zuwa wurina domin inda nake kuma ku kasance. 4 Kun san hanya inda zan tafi." 5 Toma ya ce wa Yesu, "Ubangiji, bamu san inda za ka tafi ba, yaya za mu san hanyar?" 6 Yesu ya ce masa, "Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne rai; Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina. 7 Da kun san ni, da kun san Ubana kuma. Amma daga yanzu kun san shi, kuma kun gan shi." 8 Filibus ya ce wa Yesu, "Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan za ya ishe mu." 9 Yesu ya ce masa, "Ina tare da ku da dadewa, amma har yanzu baka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ya ga Uban. Yaya za ka ce, 'Nuna mana Uban'? 10 Baka gaskata cewa Ina cikin Uban, Uban kuma yana ciki na ba? Maganganun da nake fada maku, ba da ikona nake fadi ba, amma Uban ne da yake zaune a ciki na yake yin ayyukansa. 11 Ku gaskata ni cewa ina cikin Uban, Uban kuma na ciki na, ko kuwa ku bada gaskiya domin ayyukan kansu. 12 "Lalle hakika, ina gaya maku, duk wanda ya gaskata ni zai yi ayyukan da nake yi, kuma zai yi ayyuka fiye da wadannan, domin zan tafi wurin Uba. 13 Duk abinda kuka roka da sunana, zan yi shi domin a daukaka Uban cikin Dan. 14 Idan kuka roke ni komai cikin sunana, zan yi shi. 15 "Idan kuna kaunata, za ku kiyaye dokokina. 16 Sa, annan zan yi addu'a ga Uba, zai kuwa baku wani mai ta'aziya domin ya kasance tare daku har abada. 17 Ruhun gaskiya. Wanda duniya ba zata iya karba ba, domin bata gan shi ba, ko ta san shi. Amma ku kun san shi, domin yana tare da ku, zai kuma kasance a cikin ku. 18 Ba zan barku ku kadai ba; zan dawo wurin ku. 19 Sauran dan gajeren lokaci, duniya kuma ba zata ka ra gani na ba, amma ku kuna gani na. Saboda ina raye, kuma zaku rayu. 20 A wannan rana zaku sani ina cikin Ubana, ku kuma kuna ciki na, ni ma ina cikin ku. 21 Shi wanda yake da dokokina yake kuma bin su, shine ke kauna ta, kuma shi wanda ke kauna ta Ubana zai kaunace shi, Ni ma kuma zan kaunace shi in kuma bayyana kaina gare shi." 22 Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce ma Yesu, "Ubangiji, meyasa za ka bayyana kanka a gare mu, ba ga duniya ba?" 23 Yesu ya amsa ya ce masa,"Kowa yake kauna ta, zai kiyaye maganata. Ubana kuwa zai kaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi. 24 Shi wanda baya kauna ta, ba ya kiyaye maganganuna. Maganar da kuke ji ba daga gareni take ba, amma daga Uba wanda ya aiko ni take. 25 Na fada maku wadannan abubuwa, sa'adda nake tare da ku. 26 Saidai, mai ta'aziyar- Ruhu Mai Tsarki wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya maku kome, kuma zai tunashe ku dukan abinda na fada maku. 27 Na bar ku da salama; ina ba ku salamata. Ba kamar yadda duniya ke bayarwa Nake bayarwa ba. Kada zuciyarku ta baci, kuma kada ku tsorata. 28 Kun ji dai na fada maku, 'zan tafi, kuma Zan dawo gare ku'. Idan kuna kaunata, za ku yi farinciki domin za ni wurin Uban, gama Uban ya fi ni girma. 29 Yanzu na fada maku kafin ya faru, domin idan ya faru, ku gaskata. 30 Ba zan kara magana mai yawa da ku ba, domin mai mulkin duniyan nan yana zuwa. Bashi da iko a kai na, 31 amma domin duniya ta san cewa ina kaunar Uban, Ina yin daidai abinda Uban ya Umarce ni. Mu tashi mu tafi daga nan.
An cigaba da sashin labarin daga Aya da ta wuce. Yesu ya ja baya a teburin da almajiransa sai ya cigaba da magana da su.
A nan "zuciya" magana ne na cikin mutum. AT: "daina damuwa"
"akwai wuraran zama dayawa a gidan Ubana"
Wannan ya na nufin sama, wurin da Allah ya na zama.
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
Kalmar "daki" ya na iya nufin daki ɗaya, ko babban wurin zama.
Yesu zai shirya wuri a sama wa kowane mutum da ya gaskanta da shi. "Ku" ya na nufin dukka almajiransa.
"ta yaya zamu san yadda za mu kai wurin?"
AT: 1) "hanya zuwa Allah" ko 2) "wadda ya ke kai mutane zuwa wurin Allah."
AT: 1) "mutumin gaskiyan" ko 2) "wadda ya ke fada kalmomin gaskiya game da Allah."
Wannan magana ne da ya na nufin cewa Yesu zai iya ba da rai wa mutane. AT: "Wadda zai iya san mutane su rayu"
Mutane za su iya zuwa wurin Allah su kuma yi rayuwa da shi idan sun gaskanta da Yesu. AT: "Babu wadda zai iya zuwa wurin Uba ya yi rayuwa da shi sai dai ta wurinsa"
"Uba" muhimmin lakabi ne wa Allah.
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin a kara nanata kalmomin Yesu. AT: "Filibus, Na kasance tare da ku almajirai na tsawon loƙaci. Ya kamata kun san ni yanzu!" zu
Ganin Yesu, wadda shi ne Allah, shi ne ganin Allah Uba. "Uba" muhimmin lakabi ne wa Allah.
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin a nanata maganar Yesu wa Filibus. AT: " Kada ku dinga ce, "nuna mana Uban!'"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin a nanata maganar Yesu wa Filibus. AT: "yakamata ka gaskanta ... ciki na."
"Abin da ina faɗa maku ba daga ni bane" ko "kalmomin da na faɗa ma ku ba daga ni ba ne"
Yanzu Yesu ya na magana da dukka almajiransa.
Wannan karin magana ne da ya na nufin Allah Uba kuma Yesu ya na da dangantaka da babu kamarsa. AT: "Ni ɗaya ne da Uba, kuma Uban ya na tare da ni" ko kuma "Ni da Uba na muna nan kamar ɗaya ne"
Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 1:51.
Wannan ya na nufin cewa Yesu ne Ɗan Allah.
A nan "suna" magana ne da ya na wakilcin ikon Yesu. AT: "Duk abin da kun roke ni, da amfani da iko na"
AT: "don in iya nuna wa kowa yadda Uba na yake"
Waɗannan muhimmin lakabi ne da ya na kwatanta dangantaka a sakanin Allah da Yesu.
A nan "suna" magana ne da ya na wakilcin ikon Yesu. AT: "Idan kun tambaye ni komai kamar masubi na, zan yi shi" ko kuma "Duk abin da kun tambaye ni, zan yi shi domin ku nawa ne"
Wannan ya na nufin Ruhu mai Tsarki.
Wannan ya na nufin Ruhu mai tsarki wadda ya na koya wa mutane abin da ya ke gaskiya game da Allah.
A nan "duniya" magana ne da ya na nufin mutane da su na hamayya da Allah. AT: "mutane da ba su gaskanta ba za su marabshe shi ba" ko kuma "Wadda su na hamayya da Allah ba za su karbe shi ba"
Anan yesu ya na nufin cewa ba zai bar almajiran shi kaɗai ba tare da wadda zai kula da su ba. AT: "barku kaɗai ba tare da wadda zai kula da ku"
A nan "duniya" magana ne da ya na wakilcin mutane da ba na Allah ba. AT: "marasa bi"
Allah Uba da Yesu sun zauna kamar mutum ɗaya. AT: "za ku san cewa Ubana da Ni ɗaya ne kamar mutum ɗaya"
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
"Ni da Ku muna nan kamar mutum ɗaya"
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai abin da sun yi
AT: "Ubana zai kaunace duk wadda ya kaunace ni"
Wannan ya na nufin wani almajiri wadda sunan sa Yahuza, ba ga almajiri wadda ya na daga ƙaukyen Keriot wadda ya ci amanar Yesu ba.
A nan kalmar "nuna" ya na nufin bayyana al'ajibin Yesu. AT: "Don me za ka bayyana kanka wa mu kadai" ko " Don me ba za ka bar mu mu gan al'ajibin ka ba?"
A nan "duniya" magana ne da ya na wakilcin mutane da suna hamayya da Allah. AT: "ba ga wadda ba su gaskanta da Allah ba"
"Wadda ya na kauna na zai yi abin da na gaya masa ya yi"
Uban da Ɗan za su yi rayuwa da waɗanda su na biyayya da abin da Yesu ya umurta. AT: "za mu zo mu zauna da shi, mu kuma samu dangantaka da shi"
"Abubuwan da na gaya maku ba abubuwan da na su in faɗa da kaina ba ne"
"sakon"
Loƙacin da Yesu ya ce "ku" ya na magana da dukkan almajiransa ne.
A nan kalmar "suna" magana ne da ya na wakilcin ƙarfi da ikon Yesu. AT: "saboda ni"
"duniya" magana ne da ya na wakilcin mutane da ba su kaunar Allah.
A nan "zuciya" magana ne da ya na wakilcin cikin mutum. AT: "Don haka ku daina damuwa, kuma kada ku ji tsoro"
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai ne abin da sun yi
A nan Yesu ya na nufin cewa zai koma wurin Uban shi. AT: "Zan koma wurin Uban"
A nan Yesu ya na nufin cewa Uban ya na da babban iko fiye da Ɗan sai kuma Ɗan ya na kan duniya. AT: "Uban ya na da babban iko fiye da yadda na ke da shi a nan"
A nan "mai mulki" ya na nufin Shaidan. Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 12:31. AT: "Shaidan da yake mulkin wannan duniya"
A nan Yesu ya na nufin cewa Shaidan ya na zuwa ya yi mashi hari. AT: "shaidan ya na zuwa ya yi mani hari"
A nan "duniya" magana ne wa mutane da ba na Allah ba ne. AT: "domin waɗanda ba na Allah ba su iya sani"
Wannan muhimmin laƙani ne wa Allah.
Kada zuciyarsu ta damu domin Yesu zai je ya shirya masu wuri, zai kuma sake dawo ya karbe su zuwa wurinsa domin inda yake kuma u kasance.
Akwai wurin zama dayawa a gidan Uban.
Yesu zai je ya shirya masu wuri.
Hanyar zuwa wurin Uba shi ne ta wurin Yesu.
Filibus ya ce wa Yesu, "Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan za ya ishe mu."
Yesu ba ya maganar ikonsa a maimako, Uban dake cikinsa ne ke yin ayyukar Uban.
Yesu ya ce su gaskanta wannan ba don wani dalili ba amma domin ayyukansa.
Yesu ya ce almajiran za su iya yin ayyuka fiye da shi domin zai tafi wurin Uba.
Yesu zai yi i shi domin a daukaka Uban cikin Dan.
Yesu ya ce za ku kiyaye dokokinsa.
Yesu ya ce Ruhun gaskiya zai kasance a cikin almajiran.
Yesu ya kira shi Ruhun Gaskiya.
Duniya ba za ta iya karban Ruhun Gaskiya ba domin bata gan shi ba, ko ta san shi ba.
Yesu zai kaunaci wadannan mutanen kuma shi da Ubansa za su bayyana kansu ga wadannan mutanen.
Mai ta'aziyar- Ruhu Mai Tsarki zai koya wa almajiran dukkan abubuwa ya kuma tunashe su dukan abinda ya fada masu.
Yesu ya su yi farinciki domin zai je wurin Uban, gama Uban ya fi shi girma.
Dalilin da Yesu ya bayar da wannan shi ne domin mai mulkin duniyan na zuwa.
1 "Nine itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomin. 2 Yakan cire duk wani rashe a cikina da ba ya bada 'ya'ya, mai bada 'ya'ya kuwa ya kan gyara shi domin ya kara bada 'ya'ya. 3 Kun rigaya kun tsarkaka saboda maganar da na yi muku. 4 Ku zauna ciki na, Ni kuma cikin ku. Kamar yadda reshe ba ya iya bada 'ya'ya shi kadai sai ya zauna cikin itacen, haka kuma ba za ku iya ba, sai kun zauna ciki na. 5 Ni ne itacen inabi, ku ne rassan. Wanda ya zauna ciki na, ni kuma cikin sa, yana bada 'ya'ya dayawa, gama in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba. 6 Wanda kuma bai zauna a ciki na ba, akan jefar da shi kamar reshe, ya bushe, kuma sukan tattara rassan su jefa a wuta, su kone. 7 In kun zauna a ciki na, maganata kuma ta zauna a cikin ku, sai ku roki duk abinda kuke so, za a kuwa yi maku. 8 Ta haka ake daukaka Ubana: cewa ku bada 'ya'ya dayawa, kuma cewa ku almajiraina ne. 9 Kamar yadda Ubana ya kaunace ni, haka Ni ma na kaunace ku; Ku zauna cikin kaunata. 10 Idan kun kiyaye dokokina, za ku zauna cikin kaunata kamar yadda Na kiyaye dokokin Ubana, na kuma zauna cikin kaunarsa. 11 Ina gaya maku wadannan al'amura domin farincikina ya kasance a cikin ku, kuma domin farincikinku ya zama cikakke. 12 "Wannan shine umarnina, cewa ku kaunaci juna kamar yadda na kaunace ku. 13 Babu wanda ke da kaunar da tafi haka, wato ya bada ransa domin abokansa. 14 Ku abokaina ne idan kuna yin abubuwan da na umarce ku. 15 Nan gaba ba zan kara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abinda Ubangijinsa ke yi ba. Na kira ku abokaina, domin na sanar da ku duk abinda na ji daga wurin Ubana. 16 Ba ku kuka zabe ni ba, amma Ni ne na zabe ku, na aike ku don ku je ku bada 'ya'ya, 'ya'yanku kuma su tabbata. Wannan ya zama domin duk abinda kuka roki Uba a cikin sunana, zai baku. 17 Na baku wannan umarni: domin ku kaunaci juna. 18 In duniya ta ki ku, ku sani cewa ta kini kafin ta ki ku. 19 Da ku na duniya ne, da duniya ta kaunace ku kamar nata. Amma saboda ku ba na duniya bane, na kuma zabe ku daga duniya, don haka duniya take kin ku. 20 Ku tuna da maganar da na yi muku, 'Bawa ba ya fi Ubangijinsa girma ba.' Idan sun tsananta mani, ku ma za su tsananta maku; Idan sun kiyaye maganata, za su kuma kiyaye maganarku. 21 Za su yi maku duk wadannan abubuwa saboda sunana, don basu san wanda ya aiko ni ba. 22 Da ban zo na yi masu magana ba, da basu da zunubi, amma yanzu, basu da wata hujja don zunubinsu. 23 Duk wanda ya ki ni ya ki Ubana. 24 Da ban yi ayyukan da babu wanda ya taba yinsu a cikin su ba, da basu da zunubi, amma yanzu sun gani, sun kuma ki ni da Ubana duka. 25 An yi wannan kuwa domin a cika maganar da ke rubuce a cikin shari'arsu, ' Sun ki ni ba dalili.' 26 Sa'adda Mai Ta'aziya- wanda zan aiko maku daga wurin Uban, wato, Ruhun gaskiya, wanda ke fita daga wurin Uban-ya zo, zai bada shaida a kai na. 27 Ku ma kuna bada shaida saboda kuna tare da ni tun daga farko.
An cigaba da sashin labarin daga Aya da ta wuce. Yesu ya ja baya a teburin da almajiransa sai ya cigaba da magana da su.
A nan "itacen inabi" karin magana ne. Yesu ya kwatanta kansa da itacen inabi. Shi ne tushen rai da ya na sa mutane su rayu a hany da ya cancanci Allah. AT: "ina nan kamar itacen inabi da yake ba da 'ya'ya mai kyau.
"manomin" karin magana ne. "Manomi" mutum ne wadda ya na kula da itacen inabi don ya gan ya ba da 'ya'ya. AT: "Ubana ya na nan kamar manomi"
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
A nan "duk wani rashe" ya na wakilcin mutane, kuma "'ba da 'ya'ya ya na wakilcin yin rayuwa a hanyar da Allah yake so.
"sare da cire"
"shirya kowane rashe"
Maganar da ana nufi a nan shi ne "tsarkakar reshe" wadda an riga an "gyara." AT: "Kamar an riga an gyara ku kuma ku tsarkakan reshe ne domin kun yi biyayya da abin da na koya maku"
Kalmar "ku" ya na nufin almajiran Yesu.
"Idan kun zauna a hade da ni, zan zauna a hade da ku"
Ta wurin zauna a cikin Almasihu, wadda sun zama na shi su na dogara akan shi don kokai. AT: "sa dai kun kasance a hade da ni ku kuma dogara da ni ma komai"
"itacen inabi" magana ne da ya na wakilcin Yesu. "rassan" magana ne da ya na wakilcin wadda su na gaskanta da Yesu sun kuma zama na shi. AT: "Ina nan kamar itacen inabi, kuma ku na nan kamar rassan da ya ke a haɗe da itacen inabi"
A nan Yesu ya na nufin cewa masubinsa su na a haɗe da shi kamar yadda ya na a haɗe da Allah. AT: "shi wadda ya zauna a haɗe da ni, kamar yadda ina zaune a haɗe da Ubana"
Maganan ana ya na nufi reshe mai ba da 'ya'ya wadda ya na wakilcin maibi da ya na sa Allah jin daɗi. Yadda reshe da ya na a haɗe da itacen inabi ya na ba da 'ya'ya dayawa, waɗanda sun kasance a haɗe da Yesu za su yi abubuwa dayawa da zai sa Allah ya ji dadi. AT: "za ku ba da 'ya'ya dayawa"
Maganan anan shi ne reshe mara ba da 'ya'ya da ya na wakilcin waɗanda ba su a haɗe da Yesu. AT: "mai gyaran itacen inabi ya na jefad da shi kamar reshe kuma ya na bushe"
AT: "wutan ya na kone su"
Yesu ya na nufin cewa dole masubi su roki Allah ya amsa adduwowinsu. AT: "roki Allah komai da ku ke so"
AT: "zai yi maku"
AT: "Ya na sa mutane su girmama Ubana"
A nan "ya'ya" magana ne na yin rayuwa don ku sa Allah ya ji dadi. AT: "loƙacin da kun yi rayuwa a hanya da zai ya na sa shi jin dadi"
"nuna cewa ku almajirai na ne"
Yesu ya ba da kaunar da Allah Uba ya na da shi mashi da kuma wadda su na kaunar sa. Anan "Uba" muhimmin lakabi ne wa Allah.
"cigaba amincewa da kuana ta"
Loƙacin da masubin Yesu sun yi masa biyayya, su na nuna kaunar su masa. AT: "loƙacin da kun yi abubuwan da na gaya maku ku yi, ku na zama a cikin kauna ta, kamar yadda ina yin biyayya ga Ubana da kuma zama a cikin kaunarsa"
"Na riga na gaya ma ku wannan abubuwa domin ku sami irin farinciki da ina da shi"
AT: "domin ku zama cikakke da farinciki" ko "domin farincikinku kada ya rasa komai"
Irin wannan kauna ya na zuwa ne daga Allah kuma ya na son amfanin sauran, ko bai amfane shi ba. Irin wannan kauna ya na lura da sauran, ko da me sun yi. AT: "Ba za ku samu babban kauna kamar wannan ba"
Wannan ya na nufin rai na jiki.
"Na gaya maku dukka abin da Uba na ya gaya ma ni"
Yesu ya na nufin cewa ba masubin sa ne suka zeɓa da kansu cewa za su zama almajiransa ba. AT: "Ba ku zaba cewa ku zama almajirai na ba"
A nan "'ya'ya" magana ne da ya na wakilcin rayuwa da ya na girmama Allah. AT: "yi rayuwar da zai girmama Allah"
"cewa abin da ku ka yi ya dadai har abada"
A nan "suna" magana ne da ya na wakilcin ikon Yesu. AT: "Domin ku nawa ne, duk abin da kun roke Uban, zai ba ku shi"
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
Yesu ya yi amfani da wannan kalmar "duniya" a waɗannan ayoyin kamar magana ne da ya na nufin mutane da ba na Allah ba kuma suna hamayya da shi.
Wannan ya na nufin kauna na mutum, kauna na 'yan'uwa ko kauna wa aboki ko ɗan gida.
A nan "maganar" sako ne na Yesu. AT: "Ku tuna da sakon da na faɗa ma ku"
A nan "saboda sunana" magana ne da ya na wakilcin Yesu. Mutane za su sa masubinsa su sha wahala domin su nashi ne. AT: "domin ku nawa ne"
Yesu ya na nufin anan cewa ya ba da sakon Allah tare da wadda ba su yarda da shi ba. AT: "Domin na zo in gaya masu sakon Allah, ba su da hudja a loƙacin da Allah zai hukunta su domin zunubansu"
Kin Allah Ɗan shi ne kin Allah Uba.
Wannan muhimmin laƙani ne wa Allah.
AT: "Domin na yi a cikinsu ayyukan da ba bu wani da ya yi. da basu da zunubi, kuma"
"ba su da wani zunubi." Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 15:22.
"Maganar" dukka sakon Allah. AT: "domin a cika annabci a cikin shari'arsu "
Wannan ya na nufin Tsohon Alkawari, wadda ya na da dukka dokokin Allah ga mutane.
Wannan ya na nufin Ruhu mai Tsarki. Dubi yadda an fasara wannan a cikin 14:16.
Allah Uba ya aiko Allah Ruhu don ya nuna wa duniya cewa Yesu shi ne Allah Ɗa.
Wannan lakabi ne wa Ruhu mai Tsarki. AT: "Ruhun da ya na faɗan gaskiya game da Allah da kuma ni"
A nan "shaida" ya na nufin gaya wa sauran game da Yesu. AT: "Ku kuma dole ne ku gaya wa kowa abin da kun sani game da ni"
A nan "farko" magana ne da ya na nufin farkon ranakun hidimar Yesu. AT: "Daga farkon ranakun da na fara koya wa mutane da kuma yin abubuwan a'lajibi"
Yesu ne itacen inabi na hakika.
Uban ne manomin.
Uban na cire duk wani rashe a cikinsa da ba ya bada 'ya'ya, mai bada 'ya'ya kuwa ya kan gyara shi domin ya kara bada 'ya'ya.
Sun tsarkaka saboda maganar da Yesu ya yi masu.
Mu ne rassan.
Domin ba da 'ya'ya, dole mu zauna a cikin Yesu.
Duk wanda bai zauna a cikin Yesu ba, za a jefar da shi kamar reshe, ya bushe.
Dole mu zauna a ciki Yesu, maganarsa kuma ta zauna a cikin mu, sai mu roki duk abinda muke so, za a kuwa yi mana.
Ana daukaka Uban idan mun bada 'ya'ya dayawa, kuma idan mu almajiransa ne.
Dole mu kiyaye dokokinsa.
Babu wanda ke da kaunar da tafi haka, wato ya bada ransa domin abokansa.
Mu abokan Yesu ne idan muna yin abubuwan da ya umarce mu.
Ya kira su abokai domin ya sanar da su duk abinda ya ji daga wurin Ubansa.
Duniya ta ki wadanda suna bin Yesu saboda su ba na duniya bane, kuma domin Yesu ya zabe su daga duniya.
Duniya ba ta da gafarar zunubai saboda Yesu ya zo ya kuma yi ayyukan da babu wanin da ya taba yi a cikinsu.
Mai Ta'aziya-wato, Ruhun gaskiya, da kuma almajiran Yesu za su shaida game da Yesu.
Za su bada shaida game da Yesu saboda suna tare da shi tun daga farko.
1 "Na fada maku wannan ne domin kada kuyi tuntube. 2 Zasu fitar da ku daga majami'u. Amma, sa'a tana zuwa, wadda idan wani ya kasheku, zai yi zaton aikin Allah yake yi. 3 Za suyi haka ne kuwa domin ba su san Uban ko ni ba. 4 Na fada maku wadannan abubuwa ne domin in lokacin da zasu faru yayi, ku tuna na fada maku." Ban fada maku wadannan abubuwa ba tun da farko, domin ina tare da ku. 5 Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, 'Ina za ka?' 6 Amma saboda na fada maku wadannan abubuwa, bakin ciki ya cika zuciyarku. 7 Amma ina gaya maku gaskiya: zai fi ye maku in na tafi. Domin in ban tafi ba, Mai Ta'aziyya ba zai zo gare ku ba, in kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku. 8 Idan kuwa ya zo, Mai Ta'aziyyar zai fadarkar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci. 9 Game da zunubi, domin basu gaskata da ni ba, 10 Game da adalci, domin za ni wurin Uba, kuma ba za ku sake ganina ba, 11 game da hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulki duniyan nan hukunci. 12 "Akwai abubuwa da yawa da zan gaya maku, amma ba za ku iya fahimta a yanzu ba. 13 Saboda haka, sa'adda Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku a cikin dukan gaskiyar, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai fada, zai kuma sanar da ku al'amuran da zasu faru. 14 Zai daukaka ni, domin zai dauko abubuwa dake nawa ya sanar da ku. 15 Duk abinda Uba yake da shi, nawa ne. Domin wannan ne nace zai dauko abubuwa da yake nawa ya sanar da ku. 16 "Bayan dan lokaci kadan, ba zaku kara ganina kuma ba. bayan dan lokaci kadan kuma, zaku gan ni." 17 Sai wadansu almajiransa sukace wa juna, "Me nene wannan da yake fadi mana, 'Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni?' da kuma, ' zan tafi wurin Uba'?" 18 Saboda haka sukace, "Me nene wannan da yake fada, 'Bayan dan lokaci kadan'? Bamu san abinda yake fada mana ba." 19 Yesu kuwa ya ga suna so su tambaye shi, sai ya ce masu, "Wato kuna tambayar juna ne abinda nake nufi da cewa, "Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni'? 20 Hakika, hakika, ina gaya maku, zaku yi kuka da makoki, amma duniya za ta yi farin ciki, zaku cika da bakin ciki, amma bakin cikinku zai koma farin ciki. 21 Mace takan ji zafi lokacin da take nakuda don lokacin haihuwa ya zo. Amma da zarar ta haifi jinjirin nan, ba ta kara tunawa da zafin, domin ta na fariciki an haifi mutum a duniya. 22 To yanzu dai kuna bakin ciki, amma zan sake ganinku, kuma ba wanda zai iya kwace maku wannan farin ciki. 23 A rannan, ba zaku tambaye ni komai ba. Hakika hakika, ina gaya maku, komai kuka roki Uba a cikin sunana zai ba ku shi. 24 Harwa yau, ba ku roki komai cikin sunana ba. Ku roka, zaku karba, domin farin cikin ku ya zama cikakke." 25 "Na fada maku wadannan abubuwa cikin karin magana. Amma sa'a tana zuwa da ba zan kara fada maku komai ba cikin karin magana, amaimakon haka zan gaya maku komai a sarari game da Uba. 26 A ranar nan, zaku yi roko a cikin sunana kuma bance maku zan yi addu'a ga Uba a madadinku ba, 27 domin Uba da kansa yana kaunarku, domin kun kaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito. 28 Daga wurin Uban na fito, kuma na shigo duniya. Har wa yau, kuma zan bar duniya in koma wurin Uba." 29 Almajiransa sukace, duba, "Yanzu kake magana a sarari, ba cikin karin magana ba! 30 Yanzu mun sani ka san komai, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito." 31 Yesu ya amsa masu yace, "Ashe, yanzu kun gaskata? 32 Duba, sa'a na zuwa, I, sa'ar ta yi, da za a warwatsa ku, kowa ya koma gidansa, kuma ku bar ni ni kadai. Duk da haka kuwa ba ni kadai nake ba, domin Ubana yana tare da ni. 33 Na fada maku wannan ne domin a ciki na ku sami salama. A duniya kuna shan tsanani, amma ku karfafa: na yi nasara da duniya,"
An cigaba da sashin labarin daga Aya da ta wuce. Yesu ya ja baya a teburin da almajiransa sai ya cigaba da magana da su.
A nan jumlar "tuntube" ya na nufin daina gaskantawa a cikin Yesu. AT: "ba za ku daina gaskanta da ni ba domin wahalan da za ku gani"
"zai faru wata rana cewa mutum zai kashe ku, zai kuma yi tunani cewa ya na yin abu mai kyau ne wa Allah."
Za su kashe waɗansu masubi domin ba su san Allah Uba ko Yesu ba.
Wannan muhimmin laƙani ne wa Allah.
A nan "loƙaci" magana ne da ya na nufin loƙacin da mutane za su tsananta masubin Yesu. AT: "a loƙacin da za su sa ku ku sha wahala"
Wannan magana ne da ya na nufin ranakun farko na hidimar Yesu. AT: "a loƙacin da kun fara bi na"
A nan "zuciya" magana ne na cikin mutum. AT: "yanzu ku na bakin ciki"
AT: "sadai in na tafi ne mai Ta'aziyya zai zo wurin ku"
Wannan lakabi wa Ruhu mai Tsarki wadda zai kasance da almajiran bayan ya tafi. Dubi yadda kun fasar wannan a cikin 14: 26.
Loƙacin da Ruhu mai Tsarki ya zo, ya fara nuna wa mutane cewa su masu zunubi ne.
Wannan magana ne da ya na nufin mutane a cikin duniya.
"su na da laifin zunubi domin ba su gaskanta da ni ba"
"Idan na koma wurin Allah, kuma ba su gan ni kuma ba, za su san cewa na yi abubuwa da ya kamata"
"Allah zai rike su da alhaki kuma zai hukunta su domin zunuban su, kamar yadda zai hukunta Shaidan, wadda yake mulki da wannan duniya"
A nan "mai mulki" ya na nufin Shaiɗan. Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 12:31. AT: "Shaiɗan da ya na mulki da wannan duniya"
"su sako maku" ko "kalmomi maku"
Wannan suna ne wa Ruhu mai Tsarki wadda zai gaya wa mutane game da Allah.
"Gaskiya" ya na nufin gaskiya ta ruhaniya. AT: "zai koya maku dukkan gaskiyar ruhaniya da za ku so ku sani"
Yesu ya na nufin cewa Allah Uba zai yi magana wa Ruhun. AT: "zai faɗa dukka abin da Allah ya gaya mashi ya faɗa"
A nan "abubuwan hankali" ya na nufin koyarwan Yesu da babban ayyuka. AT: "zai bayyana maku cewa abin da na faɗa, na kuma yi hakika gaskiya ne"
Ruhu mai Tsarki zai gaya wa mutane cewa magana da ayyukan Yesu gaskiya ne. AT: "Ruhu mai Tsarki zai gaya wa kowa cewa magana na da ayyuka na gaskiya ne"
"jim kaɗan" ko "kafin loƙaci dayawa su wuce"
"kuma, kafin loƙaci dayawa su wuce"
Wannan ɗan fashi ne a maganar Yesu a yayin da almajiran su ka tambaye juna game da abin da Yesu ya na nufi.
Almajiran ba su gane cewa wannan ya na nufin mutuwar Yesu a kan giciye ba.
AT: 1) Wannan na iya nufin tashiwar Yesu ko 2) Wannan na iya nufin zuwan Yesu a loƙacin karshe.
Wannan muhimmin laƙabi ne wa Allah.
Yesu ya yi amfani da wannan tambaya domin almajiransa su yi binbini da abin da ya gaya masu, domin ya iya fasara a gaba. AT: "Ku na tambayan junanku abin da ina nufi loƙacin da na ce, ... gan ni."
Fasara wannan a yadda harshenku na nanata cewa abin da yake bi ya na da muhiminci kuma gaskiya ne. Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 1:51.
A nan "duniya" magana ne wa mutane da suke hamayya da Yesu. AT: "amma mutane da suke hamayya da Yesu za su yi farin ciki"
AT: "amma bakin cikinku zai zama murna" ko "amma daga baya a maimakon yin bakin ciki za ku yi murna sosai"
A nan "zuciya" magana ne na cikin mutum. AT: "za ku yi murna sosai" ko "za ku yi farin ciki sosai"
A nan kalmar "suna" magana ne da ya na nufin mutuntaka da ikon Yesu. AT: "idan kun roki komai na Uban, zai ba ku domin ku nashi ne"
A nan "suna" magana ne da ya na nufin mutuntaka da ikon Yesu. Uban zai ɗaukaki rokon masubi domin dangantakar su da Yesu. AT: "domin ku masubi na ne" ko " a iko na"
AT: "Allah zai ba ku babban farin ciki"
"a harshen da babu sauƙin ganewa"
"ba da jumawa ba zai faru"
"gaya ma ku game da Uban a hanyar da za ku gane da kyau."
A nan "suna" magana ne na mutumtaka da ikon Yesu. AT: "za ko roka domin ku nawa ne"
idan mutum ya na kaunar Yesu, Ɗan, su na kuma kuanar Uban, domin Uban da Ɗan ɗaya ne.
Bayan mutuwarsa da tashin sa, Yesu zai koma wurin Allah Uba.
A nan "Uba" muhimmin laƙani ne wa Allah.
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nuna cewa Yesu ya yi mamaki cewa almajiran sa yanzu ne sun shirya su gaskanta da shi. AT: "don haka, yanzu ne kun gaskanta da ni!
AT: "sauran za su watsar da ku"
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
A nan salama" ya na nufin salama na ciki. AT: "domin ku samu salama na ciki don dangantakar ku da ni"
A nan "duniya" ya na nufin damuwowi da tsanantawa da masubi za su sha daga waɗanda suke hamayya da Allah. AT: "na yi nasara da damuwowin wannan duniya"
Yesu ya fada wadannan abubuwa domin kada suyi tuntube.
Za suyi haka ne kuwa domin ba su san Uban ko Yesu ba.
Yesu bai gaya masu tun farko ba domin ya na tare da su.
Zai fi Yesu ya tafi domin Mai Ta'aziyya ba zai zo gare su ba sai Yesu ya tafi; amma idan Yesu ya tafi, Yesu zai aiko da Mai Ta'aziyya gare su.
Mai Ta'aziyyar zai fadarkar da duniya a kan zunubi, adalci, da kuma hukunci.
Zai bishe ku a cikin dukan gaskiyar, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai fada, zai kuma sanar da ku al'amuran da zasu faru.
Zai daukaka Yesu ta wurin daukar abubuwar Yesu ya kuma sanar wa almajiran.
Ruhun Gaskiya zai dauki abubuwan Uban. Dukka abubuwan da Uban na da shi na Yesu ne.
Basu fahimci lokacin da Yesu ya ce, "Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni." kuma da ya ce, "domin zan tafi wurin Uba".
Zai koma farinciki.
Za su sake ganin Yesu kuma zuciyarsu zata yi farinciki.
Yesu ya ce su yii wannan domin farin cikin su ya zama cikakke.
Uban da na kaunar almajiran Yesu domin sun kaunace Yesu kuma sun gaskanta cewa ya fito daga Uban.
Yesu ya fito wurin Uban zuwa cikin duniya kuma zai bar duniya ya koma wurin Uban.
Uban zai kasance tare da Yesu.
Yesu ya ce almajiran za su warwatsu, kowa zuwa gidansa, kuma za u bar shi shi kadai.
Yesu ya ce wa almajiransa su karfafa domin ya yi nasara da duniya.
1 Da Yesu ya fadi wandannan abubuwa, sai ya tada idanunsa sama ya ce, ya Uba, sa'a ta zo; ka daukaka Danka, domin Dan shi ya daukaka ka, 2 kamar yadda ka ba shi iko akan dukkan 'yan adam, ya ba da rai madawwami ga duk wanda ka ba shi. 3 Wannan ne rai madawwami: wato su san ka, Allah makadaici na gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Almasihu. 4 Na daukaka ka a duniya, na gama aikin da ka ba ni in yi. 5 Yanzu, ya Uba, ka daukaka ni tare da kai da daukaka wadda ni ke da ita tare da kai tun kafin duniya ta kasanci. 6 Na bayyana sunanka ga mutunen da ka ba ni acikin duniya. Na ka suke, ka ba ni su, sun kuwa kiyaye maganarka. 7 Yanzu kuwa sun san duk iyakar abinda ka ba ni daga gare ka yake, 8 don kuwa maganganun da ka fada mani. Na fada masu, sun kuma karba, sun sani kuwa hakika na fito daga gareka ne, kuma sun gaskata kai ne ka aiko ni. 9 Ina yi masu addu'a. Ba domin duniya ni ke yin addu'a ba, amma domin wadanda ka bani gama na ka ne. 10 Gama dukan abinda ke nawa na ka ne, naka kuwa nawa ne, an kuma daukaka ni a cikinsu. 11 Ba na cikin duniya kuma, amma wadannan mutane suna cikin duniya, ni kuwa ina zuwa wurin ka. Ya Uba mai Tsarki, ka adanasu cikin sunanka da ka ba ni domin su zama daya, kamar dai yadda muke daya. 12 Lokacin da ina tare da su, na adanasu acikin sunanka da ka ba ni. Na kiyaye su, kuma ko daya kuwa daga cikinsu ba ya bace ba, sai dai dan hallakar nan, domin Nassi ya cika. 13 Amma yanzu ina zuwa wurinka, Ina fadar wadannan abubuwa tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu. 14 Na ba su maganarka, kuma duniya ta tsane su domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne. 15 Ba ina roko ka dauke su daga cikin duniya ba, amma domin ka tsare su daga mugun nan. 16 Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ba na duniya ba ne. 17 Ka kebe su domin kanka cikin gaskiya. maganarka gaskiya ce. 18 Kamar dai yadda ka aiko ni cikin duniya, haka kuma na aike su cikin duniya. 19 Na kebe kaina gareka sabili da su, domin su ma kansu a kebe su gareka cikin gaskiya. 20 Ina addu'a ba domin wadannan kadai ba, amma har da wadanda zasu gaskata da ni ta wurin maganarsu, 21 Domin su zama daya dukansu, kamar yadda kai, ya Uba, ka ke ciki na, ni kuma na ke cikin ka. Ina roko suma su kasance a cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa ka aiko ni 22 Daukakar da ka bani, ita nake basu, domin su zama daya, kamar yadda mu ke daya; 23 ni a cikinsu, kai kuma a ciki na. Domin su kammalu cikin zama daya, domin duniya ta sani cewa ka aiko ni, kuma ka kaunace su, kamar yadda ka kaunace ni. 24 Ya Uba, ina so wadanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, domin su dubi daukakata da ka yi mani. Domin ka kaunace ni tun kafin halittar duniya. 25 Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta sanka ba, amma ni na sanka; kuma wadannan sun sani kai ne ka aiko ni. 26 Na sanar masu da sunanka, zan kuma sanar da shi domin kaunar da ka yi mani ta kasance a cikinsu, ni kuma in kasance a cikinsu,
An cigaba da sashin labarin daga Aya da ta wuce. Yesu ya na ta magana da almajiransa, amma yanzu ya far addu'a ga Allah.
Wannan karin magana ne da ya na nufin duba sama. AT: "ya dubi sama ga sarari"
Wannan ya na nufin sarari.
Yesu ya roki Allah Uba don ya girmama shi domin ya iya ba da ɗaukaka wa Allah.
Waɗannan muhimmin lakabi ne da su na kwatanta dangantaka sakanin Allah da Yesu.
A nan kalmar "sa'a" magana ne da ya na nufin loƙaci ne wa Yesu da zai sha wahala ya kuma mutu. AT: "loƙaci ya kai da zan sha wahala in kuma mutu"
Wannan ya na nufin dukka mutane.
Rai madawwami shi ne sanin Allah makadaici na gaskiya, Allah Uba da Allah Ɗa.
A nan "aiki" magana ne da ya na nufin hidimar Yesu gaba ɗaya.
Yesu ya na da ɗaukaka da Allah "kafin a yi duniya" domin Yesu ne Allah Ɗan. "Uba, ka ba ni ɗaukaka ta wurin kawo ni zuwa gabanka kamar yadda muke kafin mu yi duniya"
Wannan muhimmin laƙani ne wa Allah.
A nan "suna" magana ne da ya na nufin Allah. AT: "Na koya masu game da kai da kuma abin da kake"
A nan "duniya" magana ne da ya na nufin mutanen duniya da sun yi hamayya da Allah. Wannan ya na nufin cewa Allah ya raba masubi ta ruhaniya daga mutanen da basu gaskanta da shi ba.
Wannan karin magana ne da ya na nufin biyayya. AT: "bi koyarswan ka"
A nan kalmar "duniya" magana ne da ya na nufin mutanen da sun yi hamayya da Allah. AT: "Ba na addu'a wa waɗanda ba na ka na"
Wannan magana ne da ya na nufin kasancewa a duniya da kuma kasancewa a cikin mutane da suka yi hamayya da Allah. AT: "a cikin mutane da ba na ka ba"
Yesu ya roki Uban ya adana waɗanda sun gaskanta da shi domin su iya samin dangantaka da Allah.
A nan kalmar "suna" magana ne na karfi da ikon Allah. AT: "ka adanasu da kyau a cikin karfi da ikonka, wadda ka ba ni"
A nan "suna" magana ne da ya na nufin karfi da kiyayewar Allah. AT: "Na adanasu da kiyayewarka"
"wadda an hallakar a cikin su shi ne ɗan hallaka kadai"
Wannan ya na nufin Yahuza, wadda ya bashe Yesu. AT: "wadda tun da dadewa ka zaba ka hallakar"
AT: "domin a cika annabci game da shi a cikin nassi"
AT: "domin ku iya basu babban farin ciki"
"Na faɗa masu sakon ka"
A nan "su" duniya" magana ne da ya na nufin mutanen da sun yi hamayya da Allah. AT: "Mutanen da sun yi hamayya da ku sun tsane masubi na domin su ba na waɗanda ba su gaskanta ba ne, kamar yadda ni ba na su ba"
A cikin wannan magana, "duniya" magana ne na mutane da suka yi hamayya da Allah.
Wannan ya na nufin Shaidan. AT: "kiyaye su daga Shaidan, mugun nan"
Ana iya sa a bayyane dalilin kebe su. Jumlar "ta gaskiya" anan ya na wakilcin ta wurin koyar da gaskiyan. AT: "Sa su su zama mutanen ka ta wurin koya masu gaskiyan"
"Sakon ka gaskiya ne" ko "Abin da ka faɗa gaskiya ne"
A nan cikin "duniya" magana ne da ya na nufin mutane da suke zama a cikin duniya. AT: "ga mutanin duniya"
AT: "domin su kebe kansu da gaskiye ma ka"
"waɗanda za su gaskanta da ni domin su na koyarswa game da ni"
Waɗanda sun gaskanta da Yesu sun zama daya da Uba da kuma Ɗan loƙacin da sun ba da gaskiya.
"Na ɗaukaka masubi na kamar yadda kun ɗaukaka ni"
AT: "domin ku hada su kamar yadda kun hada mu"
"domin su zama ɗaya cikakke"
A nan "duniya" magana ne da ya na nufin mutanin da ba su san Allah ba. AT: "domin dukka mutane su sani"
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai abin da sun yi
A nan "inda nake" ya na nufin sama. AT: "da ni a sama"
"domin su gan girma na"
A nan Yesu ya na nufin lokaci kafin halitta AT: "kafin halitta duniya"
A nan "Uba" muhimmin lakabi ne.
"duniya" magana ne na mutanin da ba na Allah ba. AT: "waɗanda ba naka ba ne ba su san yadda ka ke ba"
Kalmar "suna" ya na nufin Allah. AT: "Na bayyana maku yadda ka ke"
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai abin da sun yi
Uban ya yi wannan domin ya ba da rai madawwami ga duk wanda ka ba shi.
Rai madawwam shi sanin Allah makadaici na gaskiya, da shi kuma wanda ya aiko, Yesu Almasihu.
Ya yi wannan ta wurin yin aikin da Uban ya ba shi ya yi.
YYa na son ɗaukaka da ya ke da shi da Uban kafin hallitar duniya.
Yesu ya bayyana sunansa ga mutunen da Uban shi daga duniya.
Sun karbi maganar Yesu, sun sani kuwa hakika ya fito daga Uban ne, kuma sun gaskata Allah ne ya aiko shi.
Yesu ya ce ba ya addu'a wa duniya.
Yesu ya ce wa Uban ya sa su cikin sunar Uban domin su zama ɗaya, don ka kiyaye su daga mugu, don ka tsarkaka su a cikin gaskiya, domin su kasance a cikin Yesu da kuma Uban su kuma sami waɗanda Uban ya ba shi su kasance tare da shi inda yake.
Yesu ya adanasu.
Yesu ya ce wa Uban ya sa su cikin sunar Uban domin su zama ɗaya, don ka kiyaye su daga mugu, don ka tsarkaka su a cikin gaskiya, domin su kasance a cikin Yesu da kuma Uban su kuma sami waɗanda Uban ya ba shi su kasance tare da shi inda yake.
Yesu ya tsarkaka kansa domin waɗanda Uban ya ba shi su iya tsarkaka kansu cikin gaskiya.
Yesu ya na addu'a ba domin waɗanda zasu gaskata da shi ta wurin maganar waɗanda sun bi shi a wannan loƙacin.
Yesu ya ce wa Uban ya sa su cikin sunar Uban domin su zama ɗaya, don ka kiyaye su daga mugu, don ka tsarkaka su a cikin gaskiya, domin su kasance a cikin Yesu da kuma Uban su kuma sami waɗanda Uban ya ba shi su kasance tare da shi inda yake.
Uban na ƙaunar su kamar yadda ya na ƙaunar Yesu.
Yesu ya ce wa Uban ya sa su cikin sunar Uban domin su zama ɗaya, don ka kiyaye su daga mugu, don ka tsarkaka su a cikin gaskiya, domin su kasance a cikin Yesu da kuma Uban su kuma sami waɗanda Uban ya ba shi su kasance tare da shi inda yake.
Yesu ya yi kuma zai sa shi sananne domin ƙaunar da Uban ya ƙaunaci Yesu ya kasance a cikin su kuma Yesu ya kasance a cikinsu.
1 Bayan Yesu ya fadi wadannan maganganu, ya fita shi da almajiransa zuwa daya barayin kwarin Kidiron, inda wani lambu ya ke, ya kuma shiga da almajiransa. 2 Yahuza ma wanda zai bashe shi ya san wurin, domin Yesu ya saba zuwa wurin da almajiransa. 3 Yahuza kuwa, bayan ya dauko kungiyar soja daga manyan firistoci, da Farisawa, da 'yan majalisa, suka zo wurin, rike da fitilu, da cociloli, da makamai. 4 Sai Yesu, da ya san duk abinda ke faruwa da shi, yayiwo gaba, yace masu, "Wa kuke nema" 5 Suka amsa masa su ka ce, "Yesu Banazare" Yesu yace masu, Ni ne" Yahuza kuma, wanda ya bashe shi, yana tsaye tare da sojojin. 6 Sa'adda ya ce masu, "Ni ne", suka koma da baya, suka fadi a kasa. 7 Ya sake tambayarsu kuma, "Wa ku ke nema?" su ka ce, "Yesu Banazare." 8 Yesu ya amsa, "Ai, na gaya maku cewa, Ni ne. In kuwa ni ku ke nema, ku bar wadannan su tafi abinsu;" 9 Wannan kuwa domin maganar daya fada ta cika, "Daga cikin wadanda ka ba ni, ko daya bai bace mani ba." 10 Saminu Bitrus kuwa, da ya ke yana da takobi, ya zaro ya kai wa bawan babban firist sara, ya dauke masa kunnensa na dama, sunan bawan Malkus ne. 11 Yesu ya ce wa Bitrus, "Mai da takobin ka kubenta. Ba zan sha kokon da Uba ya ba ni ba.'? 12 Sai sojojin da hafsan, da 'yan majalisar Yahudawa, suka kama Yesu, suka daure shi. 13 Da fari suka tafi da shi wurin Hanana, don shi surukin Kayafa ne, wanda ya ke shi ne babban firist a shekaran nan. 14 Kayafa kuma shi ne ya ba Yahudawa shawara, cewa ya fiye masu mutum daya ya mutu domin mutane. 15 Saminu bitrus ya bi bayan Yesu, haka kuma wani almajirin yayi. Almajirin nan kuwa sananne ne ga babban firist, sai ya shiga har farfajiyar babban firist din tara da Yesu; 16 Amma bitrus kuwa ya tsaya a bakin kofa daga waje. Sai daya almajirin da ya ke sananne ga babban firist ya fita, yayi magana da macen da ta ke tsaron kofar, sa'an nan ya shigo da Bitrus. 17 Sai yarinyar mai tsaron kofar ta ce wa Bitrus, "kai ma ba kana cikin almajiran mutumin nan ba?" Yace "bani ba." 18 To, barorin da dogaran Haikali suna tsaye a wurin, sun kuwa hura wutar gawayi, suna jin dumi, gama ana sanyi. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin dumin. 19 babban firist ya tambayi Yesu game da almajiransa da koyarwarsa kuma. 20 Yesu ya amsa masa, Ai, na yi wa duniya magana a bayyane. Na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali in da Yahudawa duka sukan taru. Ban fadi komai a boye ba. 21 Don me kake tambaya ta? Ka tambayi wadanda suka saurare ni a kan abinda na fada, ai, sun san abinda na fada. 22 Sa'adda Yesu ya fadi wannan, wani daga cikin 'yan majalisar da ke tsaye a wurin ya nushi Yesu, yace, "Kana amsa wa babban firist haka." 23 Yesu ya amsa masa yace, "Idan na fadi mugun abu to, ka bada shaida kan hakan. In kuwa dai dai na fada, to, dan me za ka nushe ni?" 24 Sai Hanana ya aika daYesu a daure wurin Kayafa, babban firist. 25 To Saminu Bitrus yana tsaye yana jin dumin. Mutanen kuwa suka ce masa, "Anya kai ma ba cikin almajiransa ka ke ba?" Sai yayi musu yace, "A'a, ba na ciki." 26 Sai wani daga cikin bayin babban firist, wato dan'uwan wanda Bitrus ya fillewa kunne, yace, "Ashe, ban gan ka tare da shi a lambun ba? 27 Bitrus ya sake yin musu, nan da nan kuwa zakara yayi cara. 28 Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu fadar Gwamna. Da asuba ne kuwa, su kansu ba su shiga fadar Gwamnan ba, wai don kada su kazantu su kasa cin jibin Ketarewa. 29 Sai bilatus fa ya fita zuwa wurinsu, yace, "Wane zargi ku ke kawowa akan mutumin nan? 30 "Sai suka amsa suka ce, "idan da mutumin nan bai yi mugun abu ba, me zai sa mu yi kararsa a wurin ka" 31 bilatus yace masu, "Ku tafi da shi da kan ku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!" Sai Yahudawa su kace masa, "Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa akan kowa." 32 Sun fadi Wannan ne don a cika maganar da Yesu yayi, wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi. 33 Sai bilatus ya sake shiga cikin fadar Gwamnan, ya kira Yesu ya ce masa, "kai sarkin Yahudawa ne?" 34 Yesu ya amsa, "wannan fadarka ce, ko kuwa wadansu ne suka ce da ni haka a wurinka?" 35 Bilatus ya amsa "Ni ba Bayahude bane, ko kuwa?" Ai, jama'arka ne da manyan firistoci suka bashe ka gareni. "Me ka yi?" 36 Yesu ya amsa, "Mulkina ba na duniya nan ba ne. Da mulkina na duniyan nan ne da barorina za su yi yaki kada a bashe ni ga Yahudawa. To, mulkina ba daga nan ya ke ba." 37 Sai Bilatus yace masa, "Wato ashe, sarki ne kai?" Yesu ya amsa, "Yadda ka fada, ni sarki ne. Domin wannan dalili aka haife ni, domin kuma wannan dalili na zo cikin duniya, don in bada shaida game da gaskiya. Kowane mai kaunar gaskiya kuma yakan saurari muryata." 38 Bilatus yace masa, "Menene gaskiya?" Bayan da ya fadi haka, ya sake fitowa wurin Yahudawa, yace masu, "Ni kam, ban sami mutumin nan da wani laifi ba. 39 Amma dai kuna da wata al'ada, in Idin Ketarewa ya yi, na kan sakar maku mutum daya. To, kuna so in sakar maku sarkin Yahudawa?" 40 Sai suka sake daukar kururuwa suna cewa, "A; a, ba wannan mutum ba, sai dai Barabbas." Barabbas din nan kuwa dan fashi ne.
Aya 1-2 ya ba da tushen bayani na abin da zai faru. Aya 1 ya faɗa inda an yi, kuma Aya 2 ya ba da tushen bayani game da Yahuza.
Marubucin ya yi amfani da wannan kalmomi domin a nuna farkon sabon abu.
Kwarin ne a Urushalima da ya ke raba Dutsen haikali daga Dutsen Olives.
Wannan taron itacunan zaitun ne. AT: "inda akwai taron itacunan zaitun"
"Sai Yesu, wadda ya san komai da ya yi kusa ya faru da shi"
"Yesu, mutumin daga Nazare"
Kalmar "shi" bayani ne a wannan littafi. AT: "Ni ne shi"
"wadda ya ba da shi"
Mazan sun faɗi a kasa saboda ikon Yesu. AT: "faɗi a kasa saboda ikon Yesu"
A nan "duniya" ya na nufin kalmomin da Yesu ya yi addu'a. AT: "Wannan ya faru domin a cika kalmomin da ya faɗa a loƙacin da ya na yin addu'a wa Ubansa"
Malkus bawa ne na babban firist.
murfin wuka mai tsini, don wukan kar ya yanka mai shi
Wannan ya bayyana kamar tambaya ne domin a kara nanata jimlar Yesu. AT: "Dole ne in sha daga kokon da Uban ya ba ni!"
A nan "kokon" magana ne da ya na nufin wahala da dole ne Yesu ya jure.
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa wadda sun yi hamayya da Yesu. AT: "shugabanin Yahudawa"
Sojoji suka daure hanayen Yesu domin a hana shi kuɓucewa. AT: "sun kama Yesu sun kuma daura shi domin a hana shi kuɓucewa"
AT: "Yanzu babban firist din ya san wannan almajiran don haka ya iya ya shiga tare da Yesu"
AT: "Sai ɗayan almajirin, wadda babban firist ya sani"
Wannan ya bayyana kamar tambaya ne domin ya sa baiwan ta iya bayana maganar ta da hankali. AT: "Kai ma ɗaya ne daga almajiran mutumin nan da an kama! Ba kai ba ne?
Waɗannan su bayin babban firist ne da kuma dogaran haikali. AT: "An yi tsanyi, sai bayin babban firist da kuma dogaran haikali su yi shirya wutan gawayi sai sun tsaya su na ɗuma kansu a kewaye da shi"
An yi amfani da wannan kalma anan domin a sa fashi daga ainahin labarin domin Yahaya ya iya kara bayani game da mutane da suke ɗuma kansu a kewaye da wuta.
Wannan kefas ne. Dubi 18:13
A nan "koyarswansa" ya na nufin abin da Yesu ya yi ta koya wa mutane. AT: "game da almajiransa da abin da ya koya wa mutane"
Za ku iya sa wannan a bayyane cewa kalmar "duniya" magana ne na mutane da sun ji koyarswan Yesu. Anan zuguiguitawar "duniya" ya nanata cewa Yesu ya yi magana a bayyane. e.
A nan "dukka Yahudawa" zuguiguitawa na da ya na nanata cewa Yesu ya yi magana a inda duk wadda zai ji zai iya jin shi.
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin a kara bayani a abin da Yesu ya na faɗa. AT: "Kadda ku dinga yi mun wannan tambaya!"
Wannan ya bayyana kamar tambaya ne domin karin nanaci. AT: "ba haka ne ya kamata ka amsa babban firist ba!"
"gaya mani abin da na faɗa da ba daidai ba"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin a kara nanata abin da Yesu ya na faɗa. AT: "Inda na faɗa abin da daidai ne kadai, kada ku dinga nushe na!"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin a kara nanatawa. AT: "Kai ma ɗaya daga cikin almajiransa ne!"
Wannan magana ya bayyana ne kamar tambaya domin karin nanaci. A nan "shi" ya na nufin Yesu. AT: "Na gan ku tare da mutumin da an kama a cikin taron itacen zaitun! ko ba haka?"
A nan Ya na nufin cewa Bitrus ya yi musan sanin da kuma zama tare da Yesu. AT: "Bitrus ya kuma musanta cewa ya san Yesu ko ya yi zama tare da shi"
A nan ana zaton cewa mai karatun zai tuna cewa Yesu ya ce Bitrus zai musanta shi kafin zakara yayi cara. AT: "yadda Yesu ya ce zai faru"
A nan ya na nufin cewa su na kai Yesu gidan Kafaya. AT: "Sai suka tafi da Yesu daga gidan Kayafa"
Bilatus ba Bayahude ba ne, don haka indan shugabanin Yahudawa sun shiga cikin faɗar sa, za su kazantu. Da wannan ya hana su yin hidimar ketarewa. AT: "su kansu sun tsaya a wajen faɗar Bilatus domin Bilatus ɗan Al'umma ne. Ba su so su zama da kazanta"
AT: "Wannan mutumin nan ya na aikata mugun abu, shi ya sa mun kawo maka don hukunci"
Wannan jumla ya na nufin ba ma makiya.
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa da suka yi hamayya da Yesu sun kuma kama shi. AT: "Su shugabanin Yahudawan suka ce masa"
Bisa ga dokan Romawa, Yahudawa ba su iya kashe mutum. AT: "Bisa ga dokan Romawa, ba za mu iya kashe mutum ba"
AT: "domin a cika abin da Yesu ya faɗa a farko"
"bisa ga yadda zai mutu"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin Bilatus ya iya nanata cikakken rashin son abubuwan al'adun mutanen Yahudawa. AT: "To, hakika ni ba Bayahude ba ne, kuma ban damu da waɗannan zancen ba!"
"'yan'uwanka Yahudawa"
A nan "duniya" magana ne na mutane da sun hamayya da Yesu. AT: 1) "Mulki na ba na duniya ba ne" ko kuma 2) "Ba na son umurnin wannan duniya domin in yi mulki kamar sarkinsu" ko kuma "Ba daga wannan duniya ne ina da ikon zaman sarki ba."
AT: "a kuma hana shugabanin Yahudawa daga kama ni"
A nan "duniya" magana ne da na nufin mutanen da suke cikin duniya.
A nan "gaskiya" ya na nufin game da Allah. AT: "gaya wa mutane gaskiya game da Allah"
Wannan karin magana ne da ya na nufin kowane mutum da ya na kaunar gaskiya game da Allah.
A nan "murya" magana ne da ya na nufin kalmomin da Yesu ya yi. AT: "abubuwan da na faɗa" ko "ni"
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin ya nuna yadda Bilatus ya yarda da cewa ba bu wadda ya san gaskiya. AT: "Ba bu wadda zai san menene gaskiya!"
Wannan karin magana ne. AT: "Ba bu! Kada ku sake wannan mutum! Ku sake Barabbas a maimako"
A nan Yahaya ya ba da tushen bayani game da Barabbas.
Ya tafi shi da almajiransa zuwa kwarin Kidiron, inda wani lambu ya ke, ya kuma shiga.
Ya san game da shi domin Yesu ya saba zuwa wurin da almajiran.
Yahuza, kungiyar soja daga manyan firistoci, da Farisawa, da 'yan majalisa sun kuma zo lambun.
Yesu ya ce masu, ''Wa kuke nema?"
Sojojin da waɗansu suka koma da baya, suka faɗi a ƙasa.
Yesu ya faɗa wannan kuwa domin maganar ta cika wanda ya ce, ''Daga cikin wadanda ka ba ni, ko daya bai bace mani ba.''
Yesu ya ce wa Bitrus, ''Mai da takobin ka kubenta. Kada in sha kokon da Uba ya ba ni ne.'?
Sun fara kai shi wurin Hanana.
Hanana shi ne surukin Kayafa, wanda shi ne babban firist a wannan shekara.
Sai ɗaya daga cikin almajirin da ya ke sananne ga babban firist ya fita, yayi magana da macen da ta ke tsaron kofar, sa'an nan ya shigo da Bitrus.
Mace mai tsaron kofar, barorin babban firist da dogaran Haikali, wanda ɗan'uwan wanda mutumin da Bitrus ya yanka mashi kunne, dukka suka tambayi Bitrus ko ya na tare da Yesu ko shi almajirin sa ne.
Yesu ya ce ya yi wa duniya magana a bayyane. Ya ce wa babban firist ya tambayi waɗanda sun ji game da abin da ya ce.
Hanana ya aika da Yesu wurin Kayafa, babban firist.
Zakara yayi cara nan da nan bayan Bitrus ya musanci Almasihu sau uku.
Ba su shiga fadar ba, don kada su kazantu su kasa cin jibin Ketarewa.
Suka amsa suka ce, ''idan da mutumin nan bai yi mugun abu ba, me zai sa mu yi kararsa a wurin ka''
Yahudawa sun so su ƙashe Yesu kuma ba su da ikon zartar da hukuncin kisa akan kowa ba tare da umarne daga manyan Romawa ba (Bilatus).
Bilatus ya ce masa ko shi ne Sarkin Yahudawa, ya kuma tambayi Yesu game da abin da ya yi.
Yesu ya ce wa Bilatus mulkinsa ba na duniya nan ba kuma bai zo daga nan ba.
An haifi Yesu domin ya zama Sarki.
Bilatus yace wa Yahudawan,"ban sami mutumin nan da wani laifi ba."
Yahudawa suka ta da murya da cewa, ''A'a, ba wannan mutum ba, sai dai Barabbas.''
1 Sai Bilatus yayi wa Yesu bulala. 2 Sojojin kuwa suka saka rawanin kaya. Suka kuwa dora wa Yesu a kai suka sa mashi kaya irin na saurata. 3 Suka zo wurin sa sukace, "Ranka ya dade, sarkin Yahudawa! sai suka nushe shi. 4 Sai Bilatus ya sake fita waje yace masu, "Dubi, zan kawo maku mutumin domin ku sani ban same shi da wani laifi ba", 5 Yesu kuwa ya fito, da rawanin kaya da kaya irin na sarauta. Sai Bilatus yace "Ga mutumin nan". 6 Da manyan firistocin tare da yan majalisar suka ga Yesu, sai suka yi ta ihu suna cewa "A gicciye shi, A gicciye shi" Sai Bilatus yace masu, "ku dauke shi ku gicciye shi, ni kam ban same shi da wani laifi ba". 7 Sai Yahudawan sukace mashi, "Ai muna da shari'a, kuma bisa ga shari'ar ya cancanci mutuwa domin ya mai da kansa Dan Allah". 8 Da Bilatus ya ji wannan zance sai ya tsorata kwarai. 9 Sai ya sake shiga fadar Gwamna, yace wa Yesu, "Daga ina ka fito?" amma Yesu bai amsa mashi ba. 10 Sai Bilatus yace masa "Ba zaka yi mani magana ba? Baka san ina da iko in sake ka ba, kuma in gicciye ka? 11 Yesu ya amsa masa, "Ai ba ka da iko a kaina sai dai in an baka daga sama, Saboda haka, wanda ya mika ni a gare ka shine mafi zunubi". 12 Da jin haka, sai Bilatus yayi kokari a sake shi, amma sai Yahudawa suka tada murya sukace, "In ka saki mutumin nan, kai ba abokin Kaisar bane, duk wanda ya maida kansa sarki, ya sabawa Kaisar". 13 Da Bilatus ya ji irin maganganunsu sai ya fito da Yesu waje ya kuma zauna akan kujeransa a inda ake kira "Dakalin shari'a," a Yahudanci kuma, "Gabbata." 14 To a ran nan ana shirye shiryen idin ketarewa, da misalin sa'a ta shidda kenan, wato tsakar rana, Bilatus yace wa Yahudawan "Ga sarkin ku!" 15 Su kuwa suka yi ihu, a tafi da shi, a tafi da shi, a gicciye shi, Bilatus yace masu "In gicciye sarkin ku? Sai manyan firistocin sukace "Ba mu da wani sarki sai Kaisar". 16 Sai Bilatus ya mika Yesu domin su gicciye shi. 17 Sai suka tafi da Yesu, ya fito yana dauke da gicciyen zuwa wurin da ake kira "Wurin kwalluwa" da Yahudanci kuma "Golgota". 18 Suka gicciye Yesu a wurin, tare da wasu mutum biyu, daya a kowane gefe, Yesu kuwa na tsikiya. 19 Bilatus kuwa ya rubuta wata alama a kan gicciyen, "YESU BANAZARE, SARKIN YAHUDAWA". 20 Yahudawa da yawa kuwa suka karanta wannan alama domin wurin da aka gicciye Yesu yana kusa da Birnin. Alamar kuwa an rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da Helenanci. 21 Sai manyan firistocin yahudawa sukace wa Bilatus, kada ka rubuta sarkin Yahudawa, amma kace, 'wannan yace "Ni ne sarkin Yahudawa"'. 22 Bilatus kuwa ya amsa, "Abinda na rubuta na rubuta kenan." 23 Bayan da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka yayyaga rigarsa kashi hudu, kowane soja da nasa, kashin, sai kuma alkyabbar. Alkyabbar kuwa bata da dinki an saka tane daga sama har kasa. 24 Sai sukace wa junansu, "Kada mu yaga alkyabbar, amma kuzo mu jefa kuri'a a kan ta mu gani ko wanene zai dauke ta, anyi haka ne domin a cika nassi cewa "Sun raba rigata a tsakaninsu, sun kuwa jefa kuri'a domin alkyabbata. 25 Sojojin suka yi wadannan abubuwa. Uwar Yesu, da 'yar'uwarta, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya. Wadannan mataye suna tsaye kusa da gicciyen Yesu. 26 Da Yesu ya ga mahaifiyarsa da almajirin nan da yake kauna tsaye kusa da juna, yace, "Mace, dubi, dan ki!" 27 Sai yace wa almajirin, "Dubi, mahaifiyarka!" Daga wannan sa'a almajirin ya dauke ta zuwa gidansa. 28 Bayan wannan Yesu, saboda ya san yanzu komai ya kammala, domin a cika nassin, sai yace "Ina jin kishi. 29 A gefensu kuma akwai gora cike da ruwan inabi mai tsami, sai suka tsoma soso a cikin ruwan inabin mai tsami suka daura a wata sanda sai suka mika masa a baki. 30 Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin, sai yace "An gama" Sai ya sunkuyar da kansa ya kuwa saki ruhunsa. 31 Sai Yahudawan, domin ranar shirye shirye ne, domin kada a bar jikunansu akan gicciye har ranar asabacin (domin asabacin rana ce mai muhimmanci), suka roki Bilatus ya kakkarye kafafunsu kuma ya saukar da su. 32 Sai sojojin suka zo suka karya kafafun mutum na farko da kuma mutum na biyun wadanda aka gicciye tare da Yesu. 33 Da suka iso kan Yesu sai suka tarar ya riga ya mutu, sai basu kuwa karya kafafunsa ba. 34 Duk da haka daya daga cikin sojojin ya soki kuibin shi da mashi, nan da nan sai jini da ruwa suka fito. 35 Wanda ya ga wannan, shi ya zama shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya sani cewa abinda ya fada gaskiya ne saboda ku ma ku gaskata. 36 Wadannan sun faru ne domin a cika nassi, "Babu ko daya daga cikin kasusuwansa da za'a karya". 37 Kuma wani nassin yace, "Zasu dube shi wanda suka soka." 38 Bayan wadannan abubuwa, Yusufu mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne (amma a boye saboda tsoron Yahudawa) ya roki Bilatus izini domin ya dauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya bashi izini, sai Yusufu yazo ya dauki jikin. 39 Nikodimu ma ya zo, wanda da farko ya zo wurin Yesu da daddare, ya kawo hadin man kamshi na mur da al'ul wajen nauyin awo dari. 40 Sai suka dauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lillin tare da kayan kamshin nan, domin jana'iza bisa ga al'adar Yahudawa. 41 To a wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu, a cikin lambun kuma akwai sabon kabari wanda ba'a taba sa kowa ba. 42 Da yake ranar shirye shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuwa na kusa, sai suka sa Yesu a ciki.
An cigaba da sashin labarin daga Aya da ta wuce. Yesu ya na tsaye a gaban Bilatus a yayin da Yahudawa suke zargin shi.
Bilatus bai duke Yesu da kansa ba. Anan "Bilatus" magana ne na sojojin da Bilatus ya umurta su duki Yesu. AT: "Sai Bilatus ya sa sojoin su duke Yesu"
A nan amfani da gaisuwan "ranka ya daɗe" da hanu a sama a gaishe da Caesar ne kadai. A yayin da sojojin su na amfani da kayoyi da kaya irin na sarauta su na yi wa Yesu ba'a, da mamaki ne cewa ba su gane wai a hakika shi sarki ne ba.
Bilatus ya faɗi wannan so biyu domin ya nu na bai yarda cewa Yesu ba shi da laifi ba. Bai so ya hukunta shi. AT: "ban gan dalilin hukunta shi ba"
Rawanin da kaya irin na sarauta kaya ne da sarakuna ne kadai suke sa. Sojojin su yi wa Yesu sutura haka domin su yi mashi ba'a. Dubi 19: 2.
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa da suka yi hamayya da Yesu. AT: "Shugabanin Yahudawa suka amsa Bilatus"
An hukunta Yesu har ga mutuwa a kan giciye domin ya ce shi ne "Ɗan Allah."
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
Wannan magan ya bayyana kamar tambaya ne. A nan Bilatus ya bayyana mamakinsa cewa Yesu bai yi amfani da loƙacin don ya kare kansa ba. AT: "Ban iya yarda cewa kana kin magana da ni ba!" ko "Amsa ni!"
Wannan magana ya bayyana domin karin nanaci. AT: "Ya kamata ka san cewa zan iya sake ka ko kuma in umurce sojoji na su giciye ka!"
A nan "iko" magana ne da ya na nufin iya yin wani abu ko kuma sa abu ya faru.
AT: "kun na iya aikata ba da son rai na ba saboda Allah ya sa ku"
Wannan hanya ne na daraja Allah.
Wannan jumla anan na nufin mika wa makiya.
A nan " jin haka" na nufin amsar Yesu. AT: "A loƙacin da Bilatus ya ji amsar Yesu"
"yi kokari" a asali ya nuna cewa Bilatus ya yi kokari " ƙwarai ko kuma "sake" don a saki Yesu. AT: "ya yi kokari ƙwarai don a sake Yesu" ko "ya yi ta kokari don a sake Yesu"
A nan "Yahudawa" magana ne da ya na nufin shugabanin Yahudawa da suka yi hamayya da Yesu. A cikin ainahin, " tada murya" ya na nuna cewa sun yi ta ihu. AT: "amma shugabanin Yahudawa suka cigaba da yin ihu"
"kana hamayya da Kaisar"
"ya ce shi na sarki"
A nan "shi" na nufin Bilatus kuma magana ne na "Bilatus ya umurce sojojin." AT: " ya umurce sojojin su kawo Yesu waje"
Mutane masu daraja kamar Bilatus su ke zaune a loƙacin da su na yin aiki, sai mutane da ba su da daraja sosai su na tsaye.
Wannan kujera ne na musamman da mutum mai daraja kamar Bilatus ya ke zauna akai a lokacin da ya na yin hukunci. Idan harshenku ya na da yadda za a kwatanta wannan abu, za ku iya yin amfani da shi a anan.
Wannan dakalin dutse ne da mutane masu daraja ake yarda su je. AT: "a wurin da mutane sun kira Dakalin shari'a, amma"
Wannan ya na nufin harshen da mutanen Israi'la suke yi.
Wannan magana ya sa fashi a cikin labarin domin Yahaya ya iya ba da bayani game da idin ketarewa mai zuwa da rana.
"kusan tsakar rana"
A nan "Yahudawa" magana ne da ya na nufin shugabanin Yahudawa wadda sun yi hamayya da Yesu. AT: "Bilatus ya ce wa shugabanin Yahudawan"
A nan "in" magana ne da ya na nufin sojojin Bilatus wadda zai yi gicciyewan. AT: "Ku na so in gaya wa sojoji na cewa su gicciye sarkin ku a kan gicciye?"
A nan Bilatus ya ba da umurni da sojojin don su gicciye Yesu. AT: "Bilatus ya sa sojojin su gicciye Yesu"
AT: "zuwa wurin da mutane suke kira "Wurin kwakwalluwa,"
Yahudanci harshen mutanene Isra'ila ne. AT: "wadda ake kira a Yahudanci "Golgota."
Wannan karin magana ne. AT: "sun kuma gicciye shi da waɗansu barayi a kan su gicciyensu"
A nan "Bilatus" magana ne na mutumin da ya yi rubutu a kan alaman. A nan "a kan gicciye" ya na nufin gicciyen Yesu. AT: "Bilatus ya kuma umurce wani ya rubuta a alama ya kuma sa shi a kan gicciyen Yesu"
AT: "Sai mutumin ya rubuto kalmomin: Yesu Banazare, sarkin Yahudawa"
AT: "wurin da sojojin suka gicciye Yesu"
AT: "wadda ya shirya alama ne ya rubuto kalmomin a harshuna uku: Yahudanci, da Romanci, da Helenanci"
Wannan harshe ne na gwamnatin Romawa.
Manyan firistocin sun koma zuwa wurin faɗan Bilatus don su yi zangazanga game da maganganun a alaman. AT: "Manyan firistocin sun koma wurin Bilatus sai ya ce"
Bilatus ya na nufin cewa ba zai canza kalmomin a kan alaman ba. AT: "Na riga na rubuto abin da na ke so in rubuta, kuma ba zan canza ta ba"
A karshen aya 24 an yi fashi daga ainahin labari a yayin da Yahaya faɗa yadda wannan abu ya ciika nassi.
sun kuma dauke alkebbarsa." Sojojin sun ajiye alkebbar dabam, ba su raba shi ba. AT: "sun ajiye alkebbar dabam"
Sojojin za su yi caca da alkebbar kuma wadda ya ci ne zai dauka rigan. AT: "mu yi caca da alkebbar sai wadda ya ci ne zai samu ya ajiye"
AT: "Wannan ya cika nassi da ya ce" ko "Wannan ya faru ne domin ya sa nassi ya zama gaskiya"
Hakane sojojin su ka raba kayan Yesu a sakaninsu. AT: "sun yi caca"
Wannan Yahaya ne, marubucin wannan bishara.
A nan kalmar "ɗan" karin magana ne. Yesu ya na son almajiransa, Yahaya, ya zama kamar ɗa wa uwarsa. AT: "Mace, ga mutumin da zai zama kamar ɗa maki"
A nan kalmar "uwa" karin magana ne. Yesu ya na son uwarshi ta zama kamar uwa wa almajiransa, Yahaya. AT: "Yi tunanin wannan macen kamar uwarka ce"
"daga wannan loƙaci"
AT: "ya san cewa ya yi komai da Allah ya aike shi ya yi"
AT: "Wani ya ajiye awurin gorar ruwan inabi mai tsami"
"ruwa mai ɗaci"
A nan "su" na nufin masu gadin Romawa.
karamin abu wadda na iya jikuwa har ya kuma rike ruwa
"a kan rashe a tushe da ake kira hissop"
Yahaya ya na nufin cewa Yesu ya ba da Ruhunsa wa Allah. AT: " ya sunkuyar da kansa ya kuwa ba wa Allah ruhunsa" ko kuma "ya sunkuyar da kansa ya mutu"
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa da suka yi hamayya da Yesu. AT: "shugabanin Yahudawa"
Wannan lokaci ne kafin idin ketarewa da mutane su na shirya abinci don idin ketarewa.
AT: "kakkarye kafafun mutanen da an yi masu hukunci an kuma saukar da jikunansa daga su gicciye"
AT: "wadda an gicciye shi kusa da Yesu"
Wannan jimla ya ba da tushen bayani ga labarin. Yahaya ya na faɗa wa masu karatu cewa ya na wurin kuma za mu iya gaskanta abin da ya rubuto.
"Shaida" ya na nufin faɗa abin da wani ya gani. AT: "ya faɗa gaskiya game da abin da ya gani"
A nan "gaskanta" ya na nufin sa yardan mu a Yesu. AT: "domin ku sa yardan ku a Yesu"
AT: "ciki magana ne da wani ya rubuto a cikin nassi"
Wannan magana ne daga Zabura 34. AT: "ba bu wadda zai karya kasusuwansa"
Wannan magana ne da Zechariah 12.
Arimatiya karamin gari ne. AT: "Yusufu daga garin Arimatiya"
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa da suka yi hamayya da Yesu. AT: " saboda tsoron shugabanin Yahudawa"
Yahaya ya na nufin cewa Yusufu na Arimatiya ya na so ya binne jikin Yesu. AT: "izini don a ɗauke jikin Yesu daga gicciye"
Nikodimu ɗaya ne daga cikin Firistoci wadda sun gaskanta da Yesu. Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 3:1.
Waɗannan abubuwan kamshi ne da mutane na shirya gawa don biso.
Za ku iya sa wannan a awu na zamani. "lita" na nan kamar rabin kilo. AT: "kamar kilo 33 a nauyi"
"100"
A nan Yahaya ya sa fashi a cikin labarin domin a ba da tushen bayani game da inda kabarin da za a binne Yesu yake.
AT: "Yanzu a wurin da an gicciye Yesu akwai lambu"
AT: "wadda mutane ba su binne kowa ba"
Bisa shari'an Yahudawa, ba bu wadda zai yi aiki bayan rana ya fadi ranar Juma'a. Farkon Asabar da kuma ketarewa. AT: "An yi kusa a fara idin ketarewa a yamman"
Sojojin suka murza kayoyi suka rawanin kaya wa Yesu, suka kuwa dora wa Yesu a kai suka sa mashi kaya irin na saurata. Sai suka zo wurin sa sukace, "Ranka ya dade, sarkin Yahudawa! sai suka nushe shi.
Bilatus ya fitar da Yesu wa mutanen domin su sani bai same shi da wani laifi ba.
Yesu kuwa ya fito, da rawanin kaya da kaya irin na sarauta.
Suka ta da murya suna cewa "A gicciye shi, A gicciye shi"
Yahudawan sukace wa Bilatus, "Ai muna da shari'a, kuma bisa ga shari'ar ya cancanci mutuwa domin ya mai da kansa Dan Allah".
Yesu bai amsa Bilatus ba.
Yesu ya ce, "Ai ba ka da iko a kaina sai dai in an baka daga sama."
Yahudawa suka tada murya sukace, "In ka saki mutumin nan, kai ba abokin Kaisar bane, duk wanda ya maida kansa sarki, ya sabawa Kaisar".
Manyan firistocin sukace "Ba mu da wani sarki sai Kaisar".
An gicciye Yesu a Golgota wanda ke nufin wurin kwalluwa.
A'a. Wasu mutum biyu, ɗaya a kowane gefe, Yesu kuwa na tsikiya.
An rubuta akan alamar, "YESU BANAZARE, SARKIN YAHUDAWA".
An rubuta alamar da Yahudanci, Romanci, da Helenanci.
Sojojin suka yayyaga rigarsa kashi hudu, kowane soja da nasa, kashin. Sun jefa kuri'a domin su gan ko wanene zai ɗauke alkyabbarsa wanda bata da dinki.
Wannan ya faru ne domin a cika nassi cewa, "Sun raba rigata a tsakaninsu, sun kuwa jefa kuri'a domin alkyabbata."
Mahaifiyar Yesu, 'yar'uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, Maryamu Magadaliya, da kuma almajirin da Yesu ya na ƙauna sosai.
Yesu ya ce mata, "Mace, dubi, ga ɗan ki!"
Daga wannan sa'a almajirin da Yesu yake ƙauna ya ɗauke mahaifiyar Yesu zuwa gidansa.
Yesu ya faɗa wannan domin a cika nassin.
Bayan da Yesu ya sha ruwan inabi mai tsami, ya ce "Ya kare." Sai ya sunkuyar da kansa ya kuwa saki ruhunsa.
Ranar shirye shirye ne, domin kada a bar jikunansu akan gicciye har ranar asabacin (domin asabacin rana ce mai muhimmanci), Yahudawan suka roki Bilatus ya kakkarye kafafunsu kuma ya saukar da su.
Basu karya kafafun Yesu ba domin sun gan cewa ya rigaya mutu.
Ɗaya daga cikin sojojin ya soki kuibin shi da mashi.
Ya shaida waɗannan abubuwa ne saboda ku ma ku gaskata.
Waɗannan sun faru ne domin a cika nassi, "Babu ko daya daga cikin kasusuwansa da za'a karya". Kuma "Zasu duɓe shi wanda suka soka."
Yusufun Arimatiya, ya roki Bilatus izini domin ya ɗauke jikin Yesu.
Nikodimu ya zo tare da Yusufu Arimatiya.
Suka ɗauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lillin tare da kayan kamshin nan. Sai suka sa jikin Yesu a cikin sabon kabari da yake cikin lambu.
1 To da sassafe ranar farko ta mako, da sauran duhu, Maryamu Magadaliya ta zo kabarin, ta tarar an kawar da dutsen daga kabarin. 2 Sai ta ruga da gudu zuwa wurin Saminu Bitrus tare da almajirin nan da Yesu ke kauna, tace masu, "Sun dauke Ubangiji daga kabarin, bamu kuwa san inda aka sa shi ba." 3 Sai Bitrus tare da almajirin nan suka fita, kuma suka tafi kabarin, 4 dukansu suka ruga da gudu tare, amma daya almajirin ya riga Bitrus isowa kabarin, 5 Sai ya sunkuya ya leka ciki, ya ga likkafanin lillin a wurin, amma fa bai shiga ciki ba. 6 Sai Saminu Bitrus ya iso daga bayansa sai ya shiga kabarin, ya tarar da likkafanin lillin a ajiye. 7 sai fallen kuma da yake kansa. Ba'a ajiye tare da likkafanin ba amma aka linkeshi aka ajiye shi daban. 8 Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga ya gani, sai ya ba da gaskiya. 9 Har ya zuwa wannan lokacin basu san nassin daya ce zai tashi daga matattu ba. 10 Sai almajiran suka sake komawa gida kuma. 11 Amma Maryamu tana tsaye a bakin kabarin tana kuka. Yayin da take kuka, sai ta sunkuya ta leka cikin kabarin. 12 Sai ta ga mala'iku guda biyu cikin fararen kaya zaune, daya ta wurin kai daya kuma ta wurin kafafu inda aka kwantar da Yesu. 13 Sukace mata, "Uwargida don me kike kuka? Sai tace masu, "Domin sun dauke Ubangijina, ban kuwa san inda suka ajiye shi ba. 14 Bayan ta fadi haka, ta juya sai ta ga Yesu tsaye a wurin. Amma bata san cewa Yesu bane, 15 Yesu yace mata, "Uwargida, me yasa kike kuka? Wa kuma kike nema? Domin tana zaton shine mai kula da lambun, sai tace masa, "Maigida in kaine ka dauke shi, gaya mani inda ka sa shi, ni kuwa in dauke shi." 16 Yesu yace mata, "Maryamu". Sai ta juya, tace masa da Armaniyanci "Rabboni!" wato mallam. 17 Yesu yace mata, kada ki taba ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna, amma kije wurin 'yan'uwana kice masu, zan je wurin Ubana da Ubanku, Allahna da kuma Allahnku". 18 Maryamu Magadaliya ta je tace wa almajiran, "Na ga Ubangiji" Ta kuma ce ya fada mata wadannan abubuwa. 19 Da yamma a wannan rana, a rana ta farko ta mako, almajiran suna kulle a daki saboda tsoron Yahudawa, Yesu yazo ya tsaya a tsakaninsu, yace "Salama Agareku". 20 Bayan ya fadi haka, sai ya nuna masu hannuwansa da kuibinsa. Da almajiran suka ga Ubangiji, sai suka yi farin ciki. 21 Yesu ya sake ce masu, "salama agareku. "Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka Ni ma na aike ku". 22 Da Yesu ya fadi haka, sai ya hura masu lumfashinsa, yace masu, "Ku karbi Ruhu Mai Tsarki. 23 Duk wanda kuka gafarta wa zunubai, an gafarta masa; kowa kuka rike zunubansa, an rikesu." 24 Toma, daya daga cikin sha biyun, wanda ake kira Dan Tagwai, baya tare dasu lokacin da Yesu ya bayyana. 25 Sauran almajiran sukace masa "Mun ga Ubangiji". Sai yace masu, "In ban ga gurbin kusoshi a hannuwansa ba, in sa yatsana a gurbin kusoshin ba, in kuma sa hannuna cikin kuibinsa ba, ba zan bada gaskiya ba. 26 Bayan kwana takwas har wa yau almajiran na cikin gida, Toma ma na tare dasu, kofofin suna kulle, sai ga Yesu a tsakaninsu yace, "Salama agareku". 27 Sa'an nan yace wa Toma, "Iso nan da yatsanka, dubi hannuwana. Miko hannunka kuma kasa a kuibina, kada ka zama marar bada gaskiya, sai dai, mai bada gaskiya". 28 Toma ya amsa yace "Ya Ubangijina da Allahna!" 29 Yesu yace masa, "Wato saboda ka gan ni, ka bada gaskiya? Albarka ta tabbata ga wadanda basu gani ba, amma kuwa sun bada gaskiya. 30 Yesu yayi wadansu alamu da yawa dabam dabam a gaban almajiransa, wadanda ba'a rubuta a littafin nan ba. 31 Amma an rubuta wadannan ne, domin ku bada gaskiya Yesu shine Almasihu, Dan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai cikin sunansa.
Wannan ne ranar ta mako bayan da an binne Yesu.
"Lahadi"
AT: "ta tarar cewa wani ya kawar da dutsen"
Wannan jumla ya bayyana a yadda Yahaya kira kansa a cikin littafinsa. Anan kalmar "kauna" ya na nufin kaunar yan'uwa ko kauna wa abokai ko ɗan iyali.
Maryamu Magadaliya ta yi tunani cewa wani ya sata jikin Ubangiji. AT: "Wani ya riga ya ɗauka jikin Ubangiji daga kabari"
Yahaya ya nuna kaskancin shi ta wurin kiran kansa a nan "ɗayan almajirin," a maimakon saka sunansa.
Yahaya ya na nufin cewa waɗannan almajiran su na tafiya zuwa wurin kabarin. AT: "ruga daga kabarin"
Waɗannan kayakin bison Yesu ne da mutane sun kinsa jikin Yesu.
A nan "kansa" na nufin Yesu." AT: "kayan da wani ya rufe fuskan Yesu da shi"
AT: "amma wani ya riga ya linkeshi ya kuma sa a gefe, dabam daga likkafanin lillin"
Da ya gan cewa ba komai a kabarin, ya ba da gakiya cewa Yesu ya tashi daga matattu. AT: "ya gan waɗannan abubuwa sai ya fara gaskantawa cewa Yesu ya tashi daga matattu"
A nan kalmar "su" ya na nufin almajiran da ba su fahimci nissin da ya ce Yesu zai tashi kuma ba. AT: "Har yanzu almajiran ba su fahimci nassin ba"
zama rayeye kuma
Daga dukka waɗanda sun riga sun mutu. Wannan magana ya kwatanta dukka matattu a cikin duniya.
Almajiran sun cigaba da zama a Urushalima. AT: "sun koma inda suke zama a cikin Urushalima"
Mala'ikun sun sa fararen kaya. AT: "ta ga mala'iku guda biyu cikin fararen kaya"
"Sun tambaye ta"
"Domin sun dauke jikin Ubangijina"
"ban kuwa san inda suka ajiye shi ba"
"Yesu ya tambaye ta"
A nan kalmar "shi" na nufin Yesu. AT: "idan ka dauke jikin Yesu"
"gaya mani inda ka sa shi"
Maryamu Magadaliya ta na so ta samu jikin Yesu don ta binne kuma. AT: "zan samu jikin in kuma binne kuma"
Kalmar "Rabboni" ya na nufin mallam a Aramaik, harshen da Yesu da almajiran sa suke yi.
Yesu ya na nufin almajiransa ne da ya yi amfani kalmar "'yan'uwa."
Yesu ya tashi daga matattu ya kuma faɗi cewa zai je sama, zuwa wurin Ubansa, wadda shi ne Allah. AT: "Na yi kusa in koma sama domin in kasance da Ubana da kuma Ubanku, zuwa wadda shi ne Allahna da kuma Allahnku"
Waɗannan muhimmin lakabi ne da ya kwatanta dangantaka a sakanin Yesu da Allah, da kuma masubi da Allah.
Maryamu Magadaliya ta je inda almajiran suke zama sai ta faɗa masu abin da ta gani ta kuma ji. AT: "Maryamu Magadaliya ta je inda almajiran suke sai ta gaya masu"
Wannan na nufin Lahadi.
AT: "almajiran sun kulle kofofin inda suke"
A nan "Yahudawa" magana ne na shugabanin Yahudawa wadda za su iya kama almajiran. AT: "domin sun ji tsoron cewa shugabanin Yahudawa za su kama su"
Wannan sanannan suna ne da ke nufin "Bari Allah ya ba ku salama".
AT: "ya nuna masu rauni a hannuwansa da kuibinsa"
Allah Uba ya aiko Allah Ɗa wadda yanzu ya ke aikan masubi a cikin ikon Allah Ruhu mai Tsarki.
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
AT: "Allah zai gafarta masu"
"Idan ba ku gafarta zunuban wani ba"
AT: "Allah ba zai gafarta maku ba"
Wannan sunan na miji ne da ke nufin "'yan biyu." Dubi yadda kun fasar wannan a cikin 11:15.
Kalmar "shi" nanufin Toma.
AT: "Zan gaskanta idan na gan ... kuibinsa"
Kalmar "shi" na nufin Yesu.
Kalmar "shi" ya na nufin Yesu.
AT: "loƙacin da sun kulle kofofi"
Yesu ya yi amfani da wadannan maganganu "kada ka zama mara bada gaskiya" domin ya nanata kalmomin na biye, "amma ka bada gaskiya." Idan harshen ku bai yarda da abu biyu da ke a karkaceba, ko mai karatun ba zai gane cewa Yesu ya na nanata kalmomin da ka biye, ba sai kun fasara wannan magana. AT: "Wannan ne ma fi muhimmi a gare ku: dole ne ku gaskanta"
A nan "gaskanta" na nufin ba da gaskiya ga Yesu. AT: "ba da gaskiyan ku ga Yesu"
Toma ya gaskanta cewa Yesu ya na da rai domin ya gan shi. AT: "ka gaskanta cewa ina da rai"
Wannan ya na nufin "Allah ya na ba da babban farin ciki ga waɗanda."
Wannan na nufin waɗanda ba su san Yesu ba. AT: "waɗanda basu gan shi da rai ba"
Kalmar "alamu" ya na nufin abin al'ajibi da ya nuna cewa Allah ne mai dukka karfi wadda ya ke da cikakken iko a duniya.
AT: "alamun da marubucin bai rubuta akai ba a cikin wannan littafi"
AT: "amma marubucin ya rubuta game da waɗannan alamun"
Wannan muhimmin lakabi ne wa Allah.
A nan "rai" magana ne da ya na nufin Yesu ya ba da rai. "za ku iya sami rai saboda Yesu"
Wannan ya na nufin rai na ruhaniya.
Ta zo kabarin da sassafe ranar farko ta mako.
Ta gan an kawar da dutsen daga kabarin.
Ta ce masu, "Sun ɗauke Ubangiji daga kabarin, bamu kuwa san inda aka sa shi ba."
Dukansu suka ruga da gudu zuwa kabarin.
Bitrus ya gan likkafanin lillin a ajiye. Fallen kuma da yake kansa ba'a ajiye tare da likkafanin ba amma ta linkeshi ta kuma ajiyu da kanta.
Ya gani ya kuma ba da gaskiya.
Ta ga mala'iku guda biyu cikin fararen kaya zaune, ɗaya ta wurin kai ɗaya kuma ta wurin kafafu inda aka kwantar da Yesu.
Sukace mata, "Uwargida don me kike kuka?"
Ta ga Yesu a tsaye a wurin, amma bata san cewa Yesu bane.
Ta zata shine mai kula da lambu ne.
Ta gane Yesu ne a loƙacin da yace mata, "Maryamu".
Yesu ya ce wa Maryamu kada ta taba shi domin har yanzu bai hau wurin Uba ba tukuna ba.
Yesu ya ce wa Maryamu ta faɗa wa 'yan'uwansa cewa zai je wurin Ubansa da Ubanku, Allahnsa da kuma Allahnku".
Yesu yazo ya tsaya a tsakaninsu.
Ya nuna masu hannuwansa da kuibinsa.
Ta gudu ta zo wurin Saminu Bitrus da kuma ɗayan almajirin da Yesu ya na ƙauna.
Yesu ya kamar yadda Uba ya aiko shi, haka shi ma ya aike su.
Ya ce masu, "Ku ƙarbi Ruhu Mai Tsarki. Duk wanda kuka gafarta wa zunubai, an gafarta masa; duk wanda kuka rike zunubansa, an rikesu."
Toma, ɗaya daga cikin sha biyun, wanda ake kira Dan Tagwai, baya tare dasu lokacin da Yesu ya bayyana.
Toma ya ce idan bai ga gurbin kusoshi a hannuwansa ba, ya sa yatsansa a gurbin kusoshin ba, ya kuma sa hannunsa cikin kuibinsa ba, ba zas bada gaskiya ba.
Bayan kwana takwas, Tomana tare da almajiran a loƙacin da Yesu ya zo sa'ad da kofofin suna kulle, sai ya tsaya a tsakaninsu.
Yesu ya ce wa Toma ya iso da yatsansa, ya dubi hannuwansa ya kuma miko hannunsa kuma kasa a kuibin Yesu, Yesu ya ce wa Toma kada ya zama marar bada gaskiya, sai dai, mai bada gaskiya.
Toma yace "Ya Ubangijina da Allahna."
Yesu ya ce, " Albarka ta tabbata ga wadanda basu gani ba, amma kuwa sun bada gaskiya."
I, Yesu yayi waɗansu alamu da yawa dabam dabam a gaban almajiransa, waɗanda ba'a rubuta a littafin nan ba.
An rubuta waɗannan ne, domin ku bada gaskiya Yesu shine Almasihu, Ɗan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai cikin sunarsa.
1 Bayan wadannan abubuwa, Yesu ya sake bayyana kansa ga almajiran a bakin tekun Tibariya. Ga yadda ya bayyana kansa: 2 Saminu Bitrus na tare da Toma wanda ake kira Dan Tagwai, da Natana'ilu daga Kana ta kasar Galili, da 'ya'yan nan na Zabadi, da kuma wadansu almajiran Yesu biyu. 3 Saminu Bitrus yace masu, "Zani su." sukace masa "Mu ma za mu je tare da kai." Sai suka fita suka shiga jirgi, amma a daren nan basu kama komai ba. 4 To, gari na wayewa, sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran basu gane cewa Yesu bane. 5 Sai Yesu yace masu, "Samari, kuna da wani abinda za a ci?" Suka amsa masa sukace "A'a". 6 Yace masu, "Ku jefa taru dama da jirgin zaku samu wasu." Suka jefa tarunsu har suka kasa jawo shi don yawan kifin. 7 Sai almajirin nan da Yesu yake kauna yace wa Bitrus, "Ubangiji ne fa!" Da Saminu Bitrus yaji, Ashe, Ubangiji ne, yayi damara da taguwarsa, (don a tube yake), ya fada a tekun. 8 Sauran almajiran kuwa suka zo a cikin karamin jirgi, (domin basu da nisa da kasa, kamar kamu dari biyu zuwa sama), janye da tarun cike da kifi. 9 Da isowarsu gaci, sai suka ga garwashin wuta a wurin da kifi akai, da kuma gurasa. 10 Yesu ya ce masu "Ku kawo wandansu daga cikin kifin da kuka kama yanzu". 11 Sai Saminu Bitrus ya hau, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku (153). Amma duk da yawansu, tarun bai tsage ba. 12 Yesu yace masu, "Ku zo ku karya kumallo". Daga cikin almajiran kuwa babu wanda yayi karfin halin tambayarsa "Ko shi wanene?" Domin sunsani Ubangiji ne. 13 Yesu zo ya dauki gurasar ya ba su, haka kuma kifin. 14 Wannan shine karo na uku da Yesu ya bayyana ga almajiransa bayan tashinsa daga matattu. 15 Da suka karya kumallon, Yesu yace wa Saminu Bitrus, "Bitrus dan Yahaya, kana kaunata fiye da wadannan?" Bitrus yace masa "I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka" Yesu yace masa "Ka ciyar da 'ya'yan tumakina". 16 Ya sake fada masa karo na biyu, "Saminu Dan Yahaya, kana kaunata?" Bitrus Yace masa "I ya Ubangiji, ka sani ina kaunarka". Yesu yace masa, "Ka lura da Tumakina". 17 Ya sake fada masa, karo na uku, "Bitrus Dan Yahaya, kana kaunata? Sai Bitrus bai ji dadi ba domin Yesu ya fada masa karo na uku, "Kana kaunata" Yace masa, "Ubangiji ka san komai duka, ka sani ina kaunarka." Yesu yace masa "Ka ciyar da tumaki na. 18 Hakika, hakika, Ina gaya maka, lokacin da kake kuruciyarka, kakan yi wa kanka damara, ka tafi inda ka ga dama. amma in ka tsufa, zaka mike hannuwanka wani yayi maka damara, ya kai ka inda baka nufa ba." 19 To Yesu ya fadi haka ne domin ya nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi ga daukakar Allah. Bayan ya fadi haka, sai yace wa Bitrus, ka biyo ni. 20 Bitrus ya juya sai ya ga almajirin da Yesu yake kauna yana biye dasu; wanda ya jingina a kirgin Yesu lokacin cin jibin nan da yace "Ya Ubangiji, wanene zai bashe ka?" 21 Da Bitrus ya gan shi, yace wa Yesu "Ya Ubangiji, Me mutumin nan zai yi?" 22 Yesu yace masa, "Idan ina so ya zauna har in dawo ina ruwanka? Ka biyo ni." 23 Wannan zance ya yadu cikin 'yan'uwa cewa, wannan almajirin ba zai mutu ba. Alhali Yesu bai cewa Bitrus, wannan almajirin ba zai mutu ba, Amma "Idan ina so ya zauna har in dawo ina ruwanka?" 24 Wannan shine almajirin da yake shaida wadannan abubuwa, wanda ya rubuta su, kuma mun tabbata shaidarsa gaskiya ne. 25 Akwai kuma sauran abubuwa da yawa wanda Yesu yayi. Idan da an rubuta kowannensu daya bayan daya, ina gaya maku, ko duniya bazata iya daukar litattafan da za a rubuta ba.
Yesu ya nuna kansa kuma ga almajiran a Tekun Tibariya. Aya 2 da 3 ya faɗa mana abin da zai faru a cikin labarin kafin Yesu ya bayyana.
"Bayan waɗansu loƙaci"
AT: "da Toma wanda ake kira Ɗan Tagwai"
Wannan sunan na miji ne da ya na nufin "yan biyu." Dubi yadda an fasara wannan suna a cikin 11:15.
Wannan magana ne na kalma mai daɗi da ya na nufin "Abokai na na ƙwarai."
A nan "wasu" na nufin kifi. AT: "za ku kama wasu kifi a cikin taru ku"
"jawo taru ciki
Wannan irin kauna ya na zuwa daga Allah ne ya na bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba. Irin wannan kauna ya na kula da mutane, ko mai abin da sun yi
"ya tsare taguwarsa a kewaye da shi" ko "ya sa kayansa"
Wannan tushen bayani ne. Bitrus ya cire kayakin shi domin ya iya yin aiki, amma yanzu da zai gai da Ubangiji, ya so ya kara sa kaya. AT: "don ya tube waɗansu kayakin shi"
Bitrus ya yi tsalle a cikin ruwa sai ya yi yanƙayi zuwa gaɓa. AT: "tsalle zuwa cikin tekun sai ya yi yanƙari zuwa gaɓa"
Wannan karin magana ne da ya na nufin cewa Bitrus ya yi tsalle a cikin ruwa da sauri.
Wannan tushen bayani ne.
"mita 90." Kamu kaɗan ne da rabin mita.
A nan "hau sama" na nufin Saminu Bitrus ya koma wurin kwalekwalen. AT: "Sai Saminu Bitrus ya kuma wurin kwalekwalen"
"jawo taru zuwa gaci"
AT: "basu karye ba"
"cike da manyan kifaye, dari da hamsin da uku." Akwai kifi 153.
abincin safe
Za ku iya fasara wannan maganan adadin jerantawa "uku" kamar "loƙaci 3."
A nan "kauna" na nufin irin kauna dake zuwa daga Allah, wadda ya ke bisa kyaun mutane, ko bai amfani wani ba.
A loƙacin da Bitrus ya amsa, ya yi amfani da kalmar "kauna" wadda yake nufin kaunar 'yan'uwa ko kaunar aboki ko kuma ɗan iyali.
A nan "tumaki" magana ne na mutanen da suke kaunar Yesu kuma suna bin shi. AT: "ka ciyar da mutanen da ina kula da su"
A nan "tumaki" magana ne na mutanen da suke kaunar Yesu kuma suna bin shi. AT: "lura da mutanen da ina kula da su"
Kalmar "shi" ya na nufin Yesu. A nan "na uku" na nufin "loƙaci na uku." AT: "Yesu ya ce mashi na uku"
Wannan loƙacin da Yesu ya yi wannan tambaya ya yi amfani da kalmar "kauna" wadda ya ke nufin kaunar 'yan'uwa ko kaunar aboki ko kuma ɗan iyali.
A nan "tumaki" magana ne da ya na wakilcin waɗanda sun zama na Yesu kuma suna bin shi. AT: "lura da mutanen da ina kula da su"
Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 15: 51.
Yahaya ya yi amfani da wannan kalma domin ya nuna cewa ya na ba da tushen bayani ne kafin ya cigaba da labarin.
A nan Yahaya ya na nufin cewa Bitrus zai mutu a kan gicciye. AT: "don ya nuna cewa Bitrus zai mutu a kan gicciye domin ya ɗaukaka Allah"
A nan kalmar "biyo" na nufin "zaman Almajiri." AT: "cigaba da zama almajiran"
Yahaya ya kira kansa haka a duk lokaci a littafin, a maimakon kiran sunansa.
Wannan ya na nufin abincin dare na karshe. (Dubi: John Chapter 13)
A nan "shi" na nufin "almajirin da Yesu yake kauna."
Bitrus ya na so ya san abin da zai faru da Yahaya. AT: "Ya Ubangiji, me nene zai faru da wannan mutum?"
"Yesu yace wa Bitrus"
A nan "shi" ya na nufin ""almajirin da Yesu yake kauna" a cikin 21:20.
Wannan ya na nufin zuwan Yesu na biyu, dawowar sa duniya daga sama.
Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne don ya bayana tsawa mara tsanani. AT: "ka da ku damu da wannan."
A nan "'yan'uwa" na nufin dukka masubin Yesu.
" almajirin Yahaya"
A nan "shaida" ya na nufin cewa shi da kansa ya na gannin abubuwa. AT: "wadda ya gan dukka waɗannan abubuwa"
A nan "mu" ya na nufin waɗanda sun gaskanta da Yesu. AT: "mu da mun gaskanta da Yesu mun san"
AT: "Idan wani ya rubuto dukkansu"
Yahaya ya zuguiguita domin ya nanata cewa Yesu ya yi abin al'ajibi dayawa fiye da abin da mutane na iya rubutawa a kai a cikin wannan littatafan.
AT: "litattafan da mutane na iya rubutawa game da abin da yi"
Almajiran suna bakin tekun Tibariya a loƙacin da Yesu ya sake bayyana masu kansa.
Saminu Bitrus, Toma wanda ake kira Dan Tagwai, da Natana'ilu daga Kana ta kasar Galili, da 'ya'yan na Zabadi, da kuma wadansu almajiran Yesu biyu.
Waɗannan almajiran su tafi kamar kifi amma ba su kama komai a daren ba.
Yesu ya ce wa almajiran su jefa taru a dama da jirgin zasu samu wasu kifi.
Sun kasa jawo tarun don yawan kifin.
Ya yi damara da taguwarsa, sai ya fada a cikin tekun.
Sauran almajiran kuwa suka zo a cikin jirgi sua jawo tarun cike da kifi.
Yesu ya ce wa almajiran su kawo wanɗansu kifin kifin da suka kama.
Wannan shine karo na uku da Yesu ya bayyana ga almajiransa bayan tashinsa daga matattu.
Yesu ya tambayi Saminu Bitrus ko ya na ƙaunar shi fiye da waɗannan.
A karo ta uku Yesu yace masa, "Ka ciyar da tumaki na."
A karo na uku da aka tambaye Bitrus, ya ce, "Ubangiji ka san komai duka, ka sani ina ƙaunarka."
Yesu ya faɗa wa Saminu Bitrus cewa a loaƙcin da zai tsufa, zai mike hannuwansa wani yayi masa damara, ya kai shi inda bai so ba.
Yesu ya faɗi haka ne domin ya nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi ga ɗaukakar Allah.
Bitrus ya tambayai Yesu, "Ubangiji, Menene mutumin nan zai yi?"
Yesu ya ce wa Bitrus, "Ka biyo ni."
Almajirin da Yesu yake ƙauna ne ya rubuto wannan littafi ya kuma shaida cewa abubuwan da an bayyana a ciki gaskiya ne.
1 Littafin da na rubuta da farko, Tiyofilos, ya fadi abubuwan da Yesu ya fara yi ya kuma koyar, 2 har zuwa ranar da aka karbe shi zuwa sama. Wannan kuwa bayan da ya ba da umarni ga zababbun manzanninsa ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 3 Bayan ya sha wahala, ya bayyana kan sa da rai a garesu, da alamu da dama masu gamsarwa. Kwana arba'in ya baiyana kansa a garesu yana yi masu magana game da mulkin Allah. 4 Yayin da yana zaune tare da su ya basu umarni cewa kada su bar Urushalima, amma su jira alkawarin Uban, wanda ya ce, "Kun ji daga gare ni, 5 cewa Yahaya babu shakka ya yi baftisma da ruwa, amma ku za a yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki nan da kwanaki kadan." 6 Sa'adda suna tare suka tambaye shi, "Ubangiji, a wannan lokaci ne za ka maido da mulki ga Isra'ila?" 7 Ya ce masu, "Ba naku bane ku san lokaci ko sa'a wanda Uba ya shirya ta wurin ikonsa. 8 Amma za ku karbi iko, idan Ruhu Mai Tsarki ya zo bisanku, sa'annan za ku zama shaidu na cikin Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, har ya zuwa karshen duniya." 9 Lokacin da Ubangiji Yesu ya fadi wadannan abubuwa, yayin da suna kallon sama, sai aka dauke shi zuwa sama, kuma girgije ya boye shi daga idanunsu. 10 Da suka dinga kallon sama yayin da ya tafi, nan da nan, mazaje biyu suka tsaya a gabansu cikin fararen tufafi. 11 Suka ce, "Ku mazajen Galili me yasa ku ke tsaye a nan kuna kallon sama? Wannan Yesu wanda ya hau zuwa sama zai dawo kamar yadda kuka gan shi yana tafiya zuwa sama." 12 Da suka dawo Urushalima daga dutsen Zaitun, wanda ke kusa da Urushalima, tafiyar Asabaci daya ne. 13 Da suka iso, sai suka haye zuwa cikin bene inda suke da zama. Sune su Bitrus, Yahaya, Yakubu, Andarawus, Filibus, Toma, Bartalamawus, Matiyu, Yakubu dan Alfa, Siman mai tsattsauran ra'ayi, kuma da Yahuza dan Yakubu. 14 Dukansu kuwa suka hada kai gaba daya, yayin da suka ci gaba da naciya cikin addu'a. Tare da su kuma akwai mata, Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma 'yan'uwansa. 15 A cikin wadannan kwanaki Bitrus ya tashi tsaye a tsakiyar 'yan'uwa, kimanin mutane dari da ashirin, ya ce, 16 " 'Yan'uwa, akwai bukatar Nassi ya cika, wanda Ruhu Mai Tsarki ya fada a baya ta bakin Dauda game da Yahuza, wanda ya jagoranci wadanda suka kama Yesu 17 Domin yana daya daga cikinmu kuma ya karbi rabonsa na ladan wannan hidima," 18 (Wannan mutum fa ya sai wa kansa fili da cinikin da ya yi na muguntarsa, kuma a nan ya fado da ka, cikinsa ya fashe, hanjinsa suka zubo waje. 19 Duka mazaunan Urushalima suka ji wannan, saboda haka suka kira wannan fili da harshensu "Akeldama" wato, "Filin Jini.") 20 "Domin an rubuta a littafin Zabura, 'Bari filinsa ya zama kufai, kada a bar kowa ya zauna wurin,'kuma, 'Bari wani ya dauki matsayinsa na shugabanci.' 21 Saboda haka ya zama dole, daya daga cikin wadanda suke tare da mu tun lokacin da Ubangiji Yesu yana shiga da fita, a tsakaninmu, 22 farawa daga baftismar yahaya har zuwa ranar da aka dauke shi daga wurinmu zuwa sama, ya zama daya daga cikin mu wurin shaidar tashinsa." 23 Suka gabatar da mutum biyu, Yusufu wanda ake kira Barsabbas, wanda kuma aka yiwa suna Justus, da kuma Matayas. 24 Su ka yi addu'a suka ce, "Ubangiji, kai ka san zuciyar dukan mutane, ka bayyana mana wanda ka zaba cikin su biyun nan 25 Domin ya dauki gurbin da kuma manzancin daga inda Yahuza ya kauce zuwa nashi waje" 26 suka jefa kuri'a a kansu; zabe ya fada kan Matayas kuma suka lissafta shi tare da manzanni sha dayan.
Litafin forkon shi ne Bishara ta hannun Luka.
Luka ya rubuto wannan litafi zuwa ga wani mai suna Tiyofilos. Ma'anan Tiyofilos shi ne "abokin Allah"
Wannan na nufin haurawar Yesu zuwa cikin sama. AT: "har zuwa ranar da aka karɓe shi zuwa sama"
Ruhu Mai Tsarki Ya bishe Yesu ya umurci manzanensa game da wasu abubuwa.
Wannan na nufin wahalar Yesu da mutuwar sa bisa kan giciye.
Yesu ya bayana kansa ga manzanensa da kuma sauran almajirensa da dama.
Waɗannan abubuwan sun faru ne a lokacin kwanaki 40 da Yesu ya bayyana kansa wa almajirensa bayan ya tashi daga matattu.
Anan kalmar "shi" na nufin Yesu.
Yayin da yana zama tare da manzanninsa"
Wannan na nufin Ruhu Mai Tsarki. AT: Ruhu Mai Tsarkin, wadda Uban Ya yi alƙawari cewa zai aika.
Idan kun fasara jimla na baya a haɗe da Kalamun na "Ruhu Mai Tsarki," za ku iya canja kalmar "wanda" zuwa "wadda." AT: "game da wadda Yesu ya ce"
Yesu yana nuna bambancin yadda Yahaya na yi wa mutane baptisma da ruwa da yadda Allah zai yi wa masubi baptisma da Ruhu Mai Tsarki.
"Yahaya hakĩka ya yi wa mutane baftisma da ruwa"
Ana iya faɗin wannan a siffar aiki. AT: Allah zai yi maku baftisma"
"za ka sake mayar da Isra'ila babban masarauta kuma"
Yana iya yiwuwa wannan na nufin 1) kalamun "lakatai" da "sa'o'i" na nufin lokaci iri daban-daban. AT: " duka lokaci ko takamaimain rana ko kuma 2) kalamu biyun a takaice na da ma'ana guda. AT: "takamaimain lokaci"
Manzannin za su karɓi ikon da zai iza su su zama shaidun Yesu. AT: "Allah zai inganta ku ... ku zama shaidu na"
Yana iya yiwuwa wannan na nufin 1) "dukan duniya" ko 2) "zuwa wurare a duniya mafi nisa kwarai"
"da suke duba." Manzannin'' na kallon sama" ga Yesu domin ya tashi zuwa sararin sama" AT: "yayin da suke kallon sama" .
Anan iya faɗin wannan a siffar aiki. AT: ya tashi zuwa cikin sama" ko kuma "Allah ya ɗauke shi zuwa sama"
"girgijen ya tare su har basu iya cigaba da ganin sa kuma ba"
"zuba ido sama" ko kuma "ƙura idon su suma"
Mala'ikun sun kira manzannin a matsayin mutanen da ke daga Galili.
Yesu zai dawo daga sama, kamar yadda girgijen sun rufe shi yayin da ya taso zuwa sama.
"Manzannin sun komo"
Wannan na nufin tsawon tafiya wadda, bisa ga al'adun Malaman Yahudawa, ana iya barin mutum yayi tafiya a ranan asabar. AT: " kilomita ɗaya daga nan"
"Da suka kai masaukinsu." Aya 12 ya ce suna komowa Urushalima.
"ɗakin da ke sama a gidan"
Wannan na nufin Manzannin da masubin duk sun haɗa kai da alkawari da manufa ɗaya, kuma babu jayayya a cikin su.
Wannan na nufin almajiran sun saba yin addu'a tare a kullum kuma akai-akai.
Waɗannan kalamun na ba da alamar wata sabuwan sashin labarin. Suna nufin bayan da Yesu Ya hauro sama yayin da almajiren suna haɗuwa a wata ɗaki da ke sama. AT: "A wancan loƙacin"
"ɗari da ashirin"
Anan kalmar "'yan'uwa" na nufin 'yan'uwa masubi, maza da mata.
Ana iya faɗin wannan a siffar aiki. AT: Lallai ne abubuwan da muka karanta a Nassi sun cika"
Kalmar "baki" anan na nufin kalamun da Dauda ya rubuto. AT: "ta kalamun Dauda"
Kalamun "wannan mutum" na nufin Yahuza Iskariyoti.
"kuɗin ladan muguntar da yayi". Kalamun "muguntarsa" na nufin Yahuza Iskariyoti ya basher da Yesu wa mutanen da suka kashe shi.
Wannan na ba da ra'ayin cewa Yahuza ya faɗo daga wani wurin mai tsayi, ba wai ya bi ya faɗo kawai ba. Faɗin ya isa yasa cikin sa ya fashe. Wasu ayoyin nassi sun ce ya ratiye kansa.
Da mutanen da ke zama a Urushalima sun ji yadda Yahuza ya mutu, sun sake wa filin suna.
Ana iya faɗin wannan a siffar aiki. AT: "Domin Dauda ya rubuta a littafin Zabura"
Wadannan jimla biyun suna nufin abu ɗaya ne atakaice. Na biyun yana nanata ma'anan na forkon ta wurin maimaita ra'ayi ɗaya da kalamu daban-daban.
Yana iya yiwuwa wannan na nufin 1) cewa kalmar "fili" na nufin fillin da Yahuza ya mutu Ko Kuma 2) cewa kalmar "fili" na nufin wurin mazaunin Yahuza kuma magana ce da ke nufin zuriyansa.
"ya zama ba kowa a ciki"
Bisa ga nasosin da ya ambato da kuma bisa ga abinda da Yahuza ya yi, Bitrus ya faɗa wa ƙungiyar abinda za su yi.
Bitrus ya ba da jerin halayen da sun cancanta a samu mutumin da zai maye gurbin Yahuza da shi a matsayin manzo.
tafiya ciki da wajen a tsakanin wata taron mutane magana ce da ke nufin kasancewa ɗaya daga cikin taron. AT: "Ubangiji ya zauna a tsakaninmu"
"A nan iya fasara sunan "baftisma" zuwa kalman aiki. Yana iya yiwuwa ma'anan shine 1) "tun daga lokacin da Yahaya yayi wa Yesu baftisma" ko kuma 2) "tun daga lokacin da Yohanna ya yi wa mutane baftisma"
Ana iya faɗin wannan a siffar aiki. AT: "har ranan da Yesu ya bar mu ya kuma haura sama" ko kuma har ranan da Allah ya ɗauke shi daga wurinmu"
A nan kalmar "su" na nufin dukan masubin da ke wurin. AT: "Suka ba da sunayen mutane biyu da suka cika duk halayen da ake bukata da Bitrus ya jera"
Ana iya sanar da wannan a siffar aiki. AT: "Yusufu, wadda mutane ke kira Barsabbas da Justus"
A nan kalmar "su" na nufin dukan masubin, amma dai yana iya yiwuwa ɗaya daga cikin manzanen ne ya furta wadanan kalamun. AT: "Masubin sun yi addu'a tare sa'anan ɗaya daga cikin manzanen ya ce"
A nan kalmar "zukata" na nufin tunani da kuma manufofi. AT: "Ubangiji, kai ka san tunani da kuma manufofin kowa"
A nan kalmar "manzanci" na ba da ma'anar irin "hidimar" da ke akwai. AT: "ya karbi gurbin Yahuza cikin wannan hidimar manzancin" ko kuma "ya karbi gurbin Yahuza cikin bauta a matsayin manzo"
A nan wannan furcin "ƙauce" na mufin cew Yahuza ya daina yin wannan hidimar. AT: "wadda Yahuza ya daina cikawa"
Jimlar nan na nufin mutuwar Yahuza, kuma ya yiwu shari'ar sa bayan mutuwa. AT: "ya je wurin da yakamãta"
Manzannin suka jefa kuri'a domin su yanke shawara tsakanin Yusufu da matayas.
Zaɓen ya nuna cewa Matayas ne wanda zai maye gurbin Yahuza.
Ana iya faɗin wannan a siffar aiki. AT: "masubin sun ɗauke shi ya zama manzo tare da sauran sha-ɗayan"
Luka ya rubuta wannan littafin zuwa ga Tiyofalas.
Yesu ya bayyana da rai ma almajiran sa, yana ce abubuwa akan mulkin Allah.
Yesu ya gaya ma almajirain sa su jira ma alkawarin Uban.
Almajirian za su yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki.
Yesu ya gaya masu cewa ba nasu bane su san lokacin.
Yesu ya ce manzanin zasu same iko.
Yesu ya ce manzanin zasu zama shaidu a Yahudiya, Samariya, da kuma iyakar duniya.
An tayar da Yesu sama kuma majimare ya boye shi daga idanun su.
Mala'ikun sun ce Yesu zai dawo a hanya daya da ya je sama
Sun nace da addu'a.
Nassin ya cika da Yahuza.
Yahuza ya sayi fili, ya fadi da kai fari, jikin sa ya fashe, kuma duk kayan cikin sa su zuba.
Zabura ta ce wurin shugabancin Yahuza ya kammata ya cika da wani daban.
Mutum mai dauka wurin dole ne ya raka manzanin daga lokacin baftisman Yahaya, kuma dole ya shaida tashin matattu na Yesu.
Manzanin sun yi addu'a cewa Allah ya nuna ra'ayin sa, kuma sun yi kuri'a.
An sa Matiyas a cikin manzannin nan goma sha daya.
1 Da ranar Fentikos ta zo, dukansu suna tare wuri daya. 2 Nan da nan sai ga wata kara daga sama kamar ta babbar iska, kuma ta sauko ta cika duka gidan inda suke zaune. 3 Sai ga wasu harsuna kamar na wuta sun bayyana a garesu aka rarraba su, kuma suka zauna bisa kowannensu. 4 Dukansu suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka fara magana da wadansu harsuna, yadda Ruhu ya ba su iko su yi magana. 5 A lokacin akwai Yahudawa dake zaune a Urushalima, mutanen Allah, daga kowace kasa karkashin sama. 6 Da suka ji wannan kara jama'a duk suka taru suka rude saboda kowannensu ya ji suna magana da harshensa. 7 Suka yi mamaki matuka; suka ce, "Lallai, wadannan duka ba Galiliyawa ba ne? 8 Yaya mu ke jinsu duka, kowannensu na magana a cikin harshen da aka haife mu? 9 Fisiyawa da Mediyawa da Elimawa, da Yahudawa da Kafadokiya, cikin Fontus da Asiya, 10 cikin Firgia da Bamfiliya, cikin Masar da yankunan Libiya ta wajen Sur, da baki daga Roma, 11 Yahudawa da tubabbun cikin Yahudanci, Kiretawa da Larabawa, duk munji su suna fadi a harshenmu game da manyan ayyukan Allah." 12 Dukansu suka yi mamaki suka rikice; suka ce da junansu, "Menene ma'anar wannan?" 13 Amma wasu suka yi ba'a suka ce, "Sun bugu ne da sabon ruwan inabi." 14 Amma Bitrus ya tashi tare da sha dayan, ya daga murya ya ce da su, "Mutanen Yahuda da dukanku dake zaune a Urushalima, bari ku san wannan; ku saurari maganata. 15 Domin wadannan mutanen ba buguwa suka yi ba yadda kuke zato, domin yanzu karfe tara ne na safe kawai. 16 Amma wannan shine abinda aka fada ta wurin annabi Yowel. 17 Allah ya ce, 'Haka zai kasance a kwanakin karshe, zan zubo Ruhuna a kan dukan mutane, 'ya'yanku maza da mata za su yi anabci, kuma samarinku za su ga wahayoyi, kuma tsofaffinku za su yi mafarkai. 18 Haka kuma a bisa bayi na maza da mata, a kwanakin nan zan zubo da Ruhuna, kuma za su yi anabci. 19 Zan nuna al'ajibai a sararin sama da kuma alamu a bisa duniya, jini da wuta, da girgije. 20 Rana zata juya ta koma duhu kuma wata ya koma jini, kafin Babbar ranan nan ta Ubangiji ta zo. 21 Zai kuma zama dukan wanda ya kira ga sunan Ubangiji zai sami ceto. 22 Mutanen Isra'ila, ku saurari wadannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar da shi gareku ta wurin manyan ayyuka da ban mamaki da alamu da Allah ya yi ta wurinsa a tsakiyarku, kamar yadda ku da kanku kuka sani. 23 Saboda tabbataccen shiri da riga sani na Allah, aka bayar dashi, ku kuma, ta hannun mutane 'yan tawaye, kuka gicciye shi kuma kuka kashe shi. 24 Wanda Allah ya tayar, bayan ya cire zafin mutuwa daga gareshi, saboda ba zai yiwu ba ta rike shi. 25 Gama, game da shi, 'Ina ganin Ubangiji a gabana ko yaushe, domin yana gefen hannun damana saboda kada in firgita. 26 Saboda haka zuciyata na farin ciki harshena yana yin murna. Kuma, jikina zai zauna gabagadi. 27 Gama ba za ka watsar da raina a lahira ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka ya ga ruba ba. 28 Ka bayyana mani hanyar rai; da fuskarka zaka cika ni da farin ciki. 29 'Yan'uwa, zan yi magana da ku gabagadi game da baba Dauda: ya mutu kuma aka bizne shi, kuma kabarinsa na nan tare da mu har yau. 30 Domin haka, don shi annabi ne kuma ya san Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa daga cikin zuriyarsa zai sanya wani bisa kursiyinsa. 31 Ya hango wannan al'amari kuma ya yi magana game da tashin Almasihu, 'Ba ayi watsi da shi ba a lahira, kuma jikinsa bai ga rubewa ba.' 32 Wannan Yesun - Allah ya tashe shi, wanda dukanmu shaidu ne. 33 Saboda haka yadda aka tashe shi zuwa hannun dama na Allah kuma ya karbi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, shine ya zubo mana wannan da kuke gani kuma kuke ji. 34 Dauda bai hau zuwa sama ba, amma ya ce, "Ubangiji ya ce wa Ubangijina, "Zauna hannun dama na, 35 har sai na maida makiyanka abin takawar sawunka.'" 36 Saboda haka, bari gidan Isra'ila su sani tabbas wannan Yesun wanda kuka gicciye, Allah ya maishe shi Ubangiji da kuma Almasihu. 37 Da suka ji haka sai suka soku a zukatansu, suka cewa Bitrus da sauran manzanni, '"Yan'uwa me za mu yi?" 38 Sai Bitrus ya ce masu, "Ku tuba ayi wa kowannenku baftisma, cikin sunan Yesu Almasihu domin gafarar zunubanku, kuma za ku karbi baiwar Ruhu Mai Tsarki. 39 Domin alkawarin a gareku ne da 'ya'yanku da duk wadanda ke nesa, dukan iyakar mutanen da Ubangiji Allahnmu zai kira." 40 Da maganganu da yawa ya ba da shaida kuma ya karfafa su; ya ce, "Ku ceci kan ku daga wannan muguwar tsara." 41 Sai suka karbi maganar sa kuma aka yi ma su baftisma, a wannan rana kuma aka sami karin rayuka wajen dubu uku. 42 Su ka cigaba cikin koyarwar manzanni da zumunta, cikin kakkaryawar gurasa da kuma cikin addu'o'i. 43 Tsoro ya sauko bisa kowane rai, kuma aka yi abubuwan ban mamaki da alamu da yawa ta wurin manzannin. 44 Duka wadanda suka ba da gaskiya suna tare kuma komai nasu na kowanensu ne, 45 kuma suka saida kadarorinsu da mallakarsu kuma suka rarrabawa kowa, bisa ga irin bukatar da kowannensu yake da ita. 46 A kowace rana suka cigaba tare da nufi daya a cikin haikali, suna kakkarya gurasa a gidaje, kuma suna raba abinci tsakaninsu cikin farin ciki da tawali'u a zuciya; 47 Suna yabon Allah kuma suna da tagomashi a gaban dukan mutane. Ubangiji kuma kullum yana kara masu wadanda suke samun ceto.
Wannan wata sabuwar abu ce; yanzu ranar Fentikos ne, kwanaki 50 bayan Idin ketarewa.
Wannan na nufin abin da ya faru ba zato ba tsammani
Yana iya yiwuwa ma'anan shi ne 1)"sama" na nufin Wurin da Allah yake zama. AT: "wata ƙara ta fito daga sama" ko kuma 2) "sama" na nufin sararin sama. AT: "wata ƙara daga sararin sama"
"wata hayaniya kamar ƙaran wata iska mai ƙarfin gaske na hurawa"
Wannan na iya yiwuwa gidan ko ginin babba ne sosai.
Ba lallai ne waɗanan su zama ainihin harsuna ko wuta ba, amma wani abu ne dai yayi kama da su. Yana yiwuwa ma'anan sune 1) harsuna da sun yi kamar anyi su da wuta ko kuma 2) kananan wuta da sun yi kamar harsuna. Idan wuta na ƙona wa, kamar a fitilla, wutan na daukan kamanin harshe.
Wannan na nufin "harsuna kamar wuta" sun warwatsa yadda akwai daya bisa kowane mutum.
Ana iya faɗin wannan a siffar aiki. AT: Ruhu Mai Tsarki ya cika dukan waɗanda suke wurin sa'anan suka"
Waɗanan harsuna ne da basu taba saninsu ba.
A nan "Mutanen Allah" na nufin mutanen da sun mika kai cikin yi wa Allah sujada kuma suna kokarin biyayya da dukan shari'ar Yahudawa.
"kowace ƙasa a duniya." Kalmar "kowace" ƙari ne da ke nanata cewa mutanen daga ƙasashe da dama ne daban-daban kuma. AT: ƙasashe da dama daban-daban"
Wannan na nufin ƙaran da ya yi kama da na wata iska mai ƙarfi.
"babban taron jama'a"
An yi amfani da kalamai biyu a turance masu ma'ana guda domin a nanata tsananin mamakinsu. AT: "Sun yi mamaƙi ƙwarai"
Mutanen sun yi wannan tambayan ne domin su nuna mamakinsu. Anan iya canza tambayan zuwa furcin ban mamaki. AT: Ai waɗanan Galaliyawan ba za su iya sanin harsunanmu ba!"
Yana iya yiwuwa wannan na nufin 1) wannan tambayan ganganci ne da ke bayyana sananin mamakin su ko muma 2) wannan ainihin tambaya ne da mutanen ke buƙatan amsa.
"a cikin harsunan mu da muka koya tun daga haifuwa"
Wannan ya ba da jerin wasu ƙasashe, yankuna, da jahohi da suka fito.
tubabbun cikin Yahudanci
adanan kalamu biyun suna da ma'ana kusan ɗaya. Dukkansu na nanata cewa mutanen basu iya gane abin da ke faruwa ba. AT: "yi mamaki suka rikice"
Wasu mutanen sun zarge masubin da buguwa da sabon ruwan inabi. AT: "Sun bugu"
Wannan na nufin ruwan inabin da ya fara tsami.
Bitrus ya fara maganarsa wa Yahudawan da suke wurin a ranan Fentikos.
Duk manzannin sun tsaya suna goyon bayan jawabin Bitrus.
Wannan karin magana ne da ke nufin "ya yi magana da ƙarfi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)
Wannan na nufin cewa Bitrus zai yi bayyanin ma'anan abin da mutanen ke gani. Ana iya sanar da wannan a siffar aiki. AT: "ku san wannan" ko kuma "bari in bayyana muku wannan"
Bulus na nufin abinda yake faɗi. AT: "ku kasa kunne sosai ga magana ta"
Bulus na sa rai cewa yakamata masu sauraron su san cewa mutane basu buguwa da safe.
Ana iya faɗin wannan a siffar aiki. AT: "wannan shine abinda Allah ya gaya wa annabi Yowel ya rubuta" ko kuma "wannan shine abinda annabi Yowel ya faɗa"
"Ga abinda zai faru" ko kuma "Ga abinda Ni zan yi"
A nan kalaman nan "zubo" na nufin a bayar a da matukar yawa a yalwace. AT: Zan ba da Ruhuna sosai ga dukan mutane"
"dukan bayi na maza da mata." Wadannan kalamun na nanata cewa Allah zai zubo da Ruhunsa bisa dukan bayin sa, wato maza da mata.
A nan kalaman nan "zubo" na nufin a bayar da matuƙar yawa a yalwace. Duba yadda kun fasara wannan a [Ayyukan Manzanni 2:17]. AT: "Zan ba da Ruhuna a yalwace ga dukan mutane"
"hayaƙi mai ƙauri" ko kuma "hazon hayaƙi"
Wannan na nufin cewa rana zai fito da duhu maimakon hasƙe. AT: Rana zai zama duhu"
Wannan na nufin wata zai fito ja kamar jini. AT: wata zai fito ya zama ja"
Kalamun nan "babba" da "ƙwarai" na da ma'ana kusan ɗaya kuma suna nanata muhimmin ranar. AT: "wannan babbar ranan"
babba kuma ƙyaƙyawa
Ana iya faɗin wannan a siffar aiki. AT: "Ubangiji zai ceci dukan wanda ya kira gare shi"
"ku ji abinda zan faɗa"
Wannan na nufin cewa ya tabbatar cewa shi ne ya zaɓi Yesu domin aikinsa, ya kuma tabbatar da wannan ta wurin al'ajibai.
Ana iya fasara "shiri" da "riga-sani" zuwa kalmar aiki.
AT: "kun bayar da Yesu zuwa ga abokan gabansa" ko kuma 2) Yahuza ya bashe Yesu zuwa gareku.
Ko da shike 'yan tawaye" ne suka giciye Yesu, Bitrus yana ɗorawa taron laifin kashe Yesu domin sun nema ya mutu.
A nan "hannun" na nufin ayyukan 'yan tawaye. AT: "ta wurin ayyukan 'yan tawaye" ko kuma "ta wurin abubuwan da 'yan tawaye suka yi"
AT 1) Yahudawan da basu gaskanta ba sun ba wa Yesu laifuka ko 2) Sojojin Roma da suka yi kisan Yesu.
A nan a tayar karin maganane da ke sa wanda ya mutu ya dawo da rai kuma. AT: "Amma Allah ya sa shi ya rayu kuma"
Bitrus yana maganan mutuwar kamar wani mutum ne da ke ɗaura mutane da igiyoyi masu zafi ya riƙe su. Yana maganar yadda Allah ya cire zafin mutuwar Almasihu kamar Allah ya yanke igiyoyin da suka riƙe Almasihu ya kuma yantas da shi. AT: "ƙãre zafin mutuwa"
AT: "mutuwa ta riƙe shi"
AT: "a kasancewa ta" ko "tare da ni"
Kasancewa a "hannun daman" mutum kan iya nufin kasancewa a wani matsayin taimako ko rayawa. AT: "dap da ni" ko kuma "tare da ni ya taimake ni"
Anan kalmar "jijjigu" na nufin firgita. AT: "mutane ba za su iya sa in firgita ba" ko "ba abin da zai firgitar da ni"
Mutanen kan ɗauka "zuciya" itace cibiyar shauki sa'anan "harshe" ne muryar wanɗanan shaukin. AT: "na yi farin ciki na kuma yi murna"
"jiki" na nufin 1) mutum dai zai mutu AT: ko da shike ni mutum ne, ina da gaba gaɗi ga Allah. ko 2) yana nufin mutum gabaki ɗaya. AT: "Zan yi rayuwa da gaba gaɗi"
Almasihu, Yesu na nufin shi da kansa ne da "Mai Tsarkinka" AT: ba kuwa za ka bar ni, Mai Tsarkinka, in ga ruɓa ba"
A nan Kalmar "ga" a nan na nufin a ɗanɗana abu. Kalmar "ruɓa" na nufin bazuwar jiki bayan mutuwa. AT: "ta ruɓa"
"hanyoyin da ke kai ga rai"
A nan "Fuska" na nufin kasancewar Allah. AT: "mutuƙar farin ciki da na ganka" ko "matuƙar farin ciki da ina gabanka"
murna, jin daɗi
"'Yan'uwana Yahudawa, Ni"
AT: "ya mutu kuma mutane sun bisne shi"
"Allah zai sanya ɗaya daga cikin zuriyan Dauda bisa Kursiyin Dauda." AT: "Allah za zaɓa ɗaya daga cikin zuriyan Dauda ya zama sarki a wurin Dauda
A nan wani daga jikinsa na nufin wani da zai haifa. AT: "wani dan zuriyansa"
AT: "Allah bai ƙyale shi zuwa lahira ba"
A nan Kalmar "ga" na nufin a ɗandana abu. Kalmar "ruɓa" na nufin bazuwar jiki bayan mutuwa. Dubi yadda aka fasara wannan a [Ayyukan Manzanni 2:27] AT: "ko kuwa jikinsa ya ruɓa" ko kuma "ko kuwa ya bar shi ya daɗe a mace har jikinsa ya ruɓe"
Wannan karin magana ne. AT: "Allah ya sa shi ya rayu kuma"
AT: saboda Allah ya daukaka shi zuwa hannun damarsa"
A nan "zubo" na nufin cewa Yesu, wanda shi ne Allah, ya sa waɗanan abubuwan su faru. Abin fakaici ne cewa ya yi wannan ta wurin ba da Ruhun sa Mai Tsarki ga masubi. AT: "ya sa waɗanan abubuwan da"
A nan kalmar nan "zubo" na nufin a bayar da matukar yawa a yalwace. Duba yadda ku fasara irin wannan jimlar a [Ayyukan Manzani 2:17]. AT: "bayar a yalwace"
Zauna a "hannun damar Allah" alama ce na karɓan girmamawa da iko daga Allah. AT: Zauna a wurin daraja a gefena"
Wannan na nufin cewa Allah zai ya sa makiyan Almasihu gaba daya su sha kashi ya kuma sa su a karkashin sa. AT: "sai Na baka nasara bisa duk makiyanka"
Wannan na nufin Kasan Isra'ila. AT: "kowane ba Isra'ila"
"Da mutanen suka ji abinda Bitrus ya faɗa"
AT: "Maganar Bitrus ya soki zukatansa"
Wannan na nufin sun gane cewa su masu laifi ne sai suka yi bakin ciki kwarai. AT: "damu kwarai"
AT: "ku bar mu mu yi muku baftisma"
"a cikin sunan" anan na nufin "ta wurin ikon" AT: ta wurin ikon Yesu Almasihu"
Wannan na nufin 1) "dukan waɗanda ke zama da nisa" ko 2) "dukan mutanen da ke da nisa da Allah."
Anan kalamumin nan "shaida" da kuma "karfafa" na da ma'ana kusan ɗaya kuma suna nanata cewa Bitrus ya karfafa su sosai ne su amince da abinda yake faɗi. AT: "ya karfafasu sosai"
Abin shi ne Allah zai hukunta "wannan muguwar tsaran" AT: "Ku ceci kanku daga hukuncin da waɗanan mugayen mutanen za su sha"
A nan kalmar nan "karɓi" na nufin cewa sun gaskanta da abinda Bitrus na faɗi. AT: "sun gaskanta abinda bitrus ya ce"
AT: "mutane sun yi musu baftisma"
AT: "rayuka kusan dubu uku suka haɗa kai da masubi a wannan rana"
" A nan kalmar "rayuka" na nufin mutane. AT: kusan mutane 3000"
Gurasa na cikin abincin da suke ci. Wannan na iya nufin 1) kowane abincin da suke ci tare. AT: "cin abinci tare" 2) za su ci abinci tare domin tunawa da mutawa da tashiwar Almasihu. AT: "cin jibi tare"
A nan "tsõro" na nufin sun girmama Allah. Kalmar "rai" na nufin mutum gaba ɗaya. AT: "Kowane mutum ya girmama Allah sosai"
AT: 1) "manzanen sun yi abubuwan ban mamaki da alamu da yawa" 2) Allah ya yi abubuwan ban mamaki da alamu da yawa ta wurin manzannin"
"ayyukan mu'ujjizai da aukuwan allahntaka" (Duba yadda kun juya wannan a [Ayyukan Manzani 2:22].
AT: "Dukan su sun gaskanta da abu ɗaya" ko 2) Dukan su sun gaskanta cewa suna wuri ɗaya"
"sun raba mallakarsu da juna"
"fili da abubuwan da suke da su"
A nan "su" na nufin ribar da sukayi daga siyar da kadarorinsu da mallakarsu. AT: "rarraba riban wa kowa"
Sun rarraba raban da suka samu daga siyar da kadarorinsu da mallakarsu ga duk mai bi da ke da bukata.
AT: 1) "sun ci gaba da saduwa tare ko kuma 2) dukansu sun cigaba da hali ɗaya."
Gurasa na cikin abincin da suke ci. AT: "sun ci abinci tare a cikin gidanjensu"
Anan "zuciya" na nufin "shauki". AT: "da farin ciki da kaskanci"
"suna yabon Allah. Dukan mutane kuma sun amincewa da su"
AT: "waɗanda Ubangiji ke basu ceto"
Almajirian sun taru a ranar Fentikos.
Almajirian sun fara magana da wadansu harsuna.
Akwai Yahudawa masu ibad daga kowane kasa karkashin sama.
Taron sun rude domin kowa da kowa sun ji su suna magana a harshen su.
Almajiran suna magana a kan ayyukan Allah masu girma.
Wasu sun yi ba'a kuma suka yi tsammani sun cika da sabon ruwan inabi.
Bitrus ya ce annabcin Yowel na cika wanda ya ce Allah zai zubo Ruhun sa akan duka naman jiki.
Kowa da kowa wadanda ke kira a sunan Ubangiji su ne wadanda suka cetu.
Allah ya ingantar da hidiman Yesu ta ayyuka masu girma da kuma abubuwan al'ajibi da kuma almamo.
An gicciye Yesu ta kayyada shirin Allah.
Sarki Dauda ya ce Allah bazai yadda mai Tsarkin shi Daya ya gan lalata ba.
Sarki Dauda ya ce Allah ba zai yadda mai Tsarkin shi Daya ya gan lalata ba.
Allah ya yi alkawari da Sarki Dauda cewa daya daga zuriyar sa zai zauna akan kursiyin
Sarki Dauda ya ce Allah bazai yadda mai Tsarkin shi Daya ya gan lalata ba.
Annabcin na Yesu ne Mai Tsarki kuma Sarki.
Allah ya sa Yesu duk Ubangiji da kuma Almasihu.
Taron sun tambaya menene su yi.
Bitrus ya gaya ma taron su tuba kuma su yi baftisma a cikin sunan Yesu Almasihu don gafarar zunuban su.
Bitrus ya ce alkawarin Allah ma taron ne, 'ya'yan su, kuma duk wanda suna da nisa.
An yi ma kamar mutane dubu uku baftisma.
Sun cigaba a cikin koyarwar almajirai da zumunci, in karyawan gurasa kuma a cikin addu'a.
Sun sar da dukiyan su da mallakan su sun kuma rarraba musu duka, kamar yadda duk na da bukata.
Masubin suna haduwa a Haikalin.
Ubangiji ya kara rana da rana wanda suna same ceto.
1 Sa'adda Bitrus da Yahaya suna hanya zuwa haikali a lokacin addu'ar karfe uku. 2 Wani mutum, gurgu ne tun daga haihuwa, ana daukar sa kulluyomi zuwa kofar haikali da ake kira Kyakkyawa, domin bara gun mutanen da ke shiga haikalin. 3 Da ya ga Bitrus da Yahaya suna shiga haikalin, sai ya roke su sadaka. 4 Bitrus da Yahaya kuwa suka zuba masa ido, Bitrus ya ce, "Ka dube mu." 5 Gurgun nan kuwa ya dube su, yana tsammanin zai sami wani abu a wurin su. 6 Amma Bitrus ya ce, "Azurfa da Zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, zan baka. A cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, Yi tafiya" 7 Bitrus ya kama hannun damarsa, ya daga shi; nan da nan kafafunsa da kashin idon sawayensa suka samu karfi. 8 Da gurgun ya yunkura, ya mike tsaye sai ya fara takawa; ya shiga haikali tare da Bitrus da Yahaya, yana takawa, yana tsalle, yana kuma girmama Allah. 9 Dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana kuma yabon Allah. 10 Sun lura cewa, shine mutumin da ke zama yana bara a Kyakyawar kofar haikali; sai suka cika da mamaki domin abin da ya faru. 11 Yayin da yake rike da Bitrus da Yahaya, dukan jama'a suka matso wurinsu, a gefen dakalin Sulaimanu, suna ta mamaki kwarai. 12 Da Bitrus ya ga haka ya amsa wa jama'ar, "Ya ku mutanen Isra'ila, don me ku ke mamaki?" Don me ku ka zura mana ido, kamar mu ne muka sa shi ya yi tafiya da ikon kanmu ko adalcin mu? 13 Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allah na iyayenmu ya girmama bawansa Yesu. Shi kuka ki kun kuma bashe shi a gaban Bilatus da ya so ya sake shi. 14 Kuka ki Mai Tsarkin nan, Mai Adalcin, maimakon haka kuka ce a sakkar maku mai kisan kai. 15 Kun kashe mai ba da rai, wanda Allah ya tayar daga matattu, mu kuwa shaidu ne ga wannan al'amari. 16 Yanzu, ta bangaskiya ga sunansa - wannan mutum da kuke gani kuma kun san shi - ta wurin wannan sunan ne ya sami karfi. Bangaskiya cikin Yesu ta ba shi cikakkiyar lafiya, a gabanku duka. 17 Ya ku 'yan'uwa, na san kun yi haka ne cikin rashin sani, yadda shugabaninku suka yi. 18 Amma duk abubuwan da Allah ya fada ta bakin dukan anabawansa, cewa Almasihunsa zai sha wahala, yanzu ya cika. 19 Saboda haka, Ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, domin lokacin sabuntuwa daga wurin Ubangiji ya zo; 20 domin a aiko maku da Almasihu wanda aka kaddara wato, Yesu. 21 Shine wanda dole sama ta karbe shi har zuwa lokacin komo da dukan abubuwa, game da abubuwan da Allah ya fada tun da ta bakin annabawansa tsarkaka. 22 Musa hakika ya ce, 'Ubangiji Allah zai tayar maku da wani annabi kamar ni daga cikin, 'yan'uwanku. Za ku saurari dukan abin da zai fada maku. 23 Zai kasance kowanne mutum da bai saurari annabin nan ba za a kau da shi gabadaya daga cikin mutanensa.' 24 I, dukan annabawa tun daga Sama'ila da wadanda suka zo bayansa, sun yi magana sun ambaci wadannan kwanaki. 25 Kune 'ya'yan annabawa da na alkawari wanda Allah ya yi da kakanninku, yadda ya ce wa Ibrahim, 'Daga zuriyarka dukan al'uman duniya za su sami albarka.' 26 Bayan da Allah ya ta da bawansa, a gareku ne ya fara aiko shi, domin ya albarkace ku tawurin juyadda kowannenku daga muguntarsa."
Wata rana Bitrus da Yahaya sun tafi Haikali.
Aya 2 ya bada hoton baya game da gurgun.
Basu je cikin ginin haikalin inda firistoci ne kaɗai ake bari su je ba. AT: "zuwa tsakar haikalin" ko kuma "zuwa yankin haikali"
A kowace rana, mutane na ɗauƙan wanan mutum, gurgu tun daga haihuwa, sai su ajiye shi kusa da wata kofar haikali
yana kasa iya tafiya
Bitrus da Yahaya sun kalle shi, amma Bitrus ne kadai yayi magana.
wannan na iya nufin 1) "yana kallon shi kai tsaye" ko kuma 2) "yana kallon shi da duk niyarsa"
A nan kalmar "duba" na nufin sa hankali ga wani abu. AT" Gurgun ya sa hankalin sa a kan su"
Waɗannan na nufin kuɗi.
An iya gane cewa Bitrus yana damar iya warkas da mutumin.
A nan kalmar "suna" na nufin ƙarfi da iko. AT: "Da ikon Almasihu Yesu"
...
"Bitrus ya sa shi ya tsaya"
Bai je cikin ginin haikalin inda firistoci ne kaɗai ake bari su je ba. AT: "ya shigo ... yankin haikalin" ko kuma "ya shigo ... zuwa tsakar haikalin"
"sun ɗago cewa mutumin ne" ko kuma "sun gane cewa mutumin ne"
Wannan ne sunan ɗaya dage cikin kofofin haikalin. Duba yadda kun fasara wannan a irin wannan jimla a [Ayyukan Manzanni 3:2]
A nan kalamun nan "mamaki da al'ajibi na nufin kusan abu ɗaya kuma suna nanata mamakin mutanen ne. AT: "sun yi mamaki ƙwarai"
"gefen dakalin Sulaimanu." Wannan wata gefe ne da ke kunshe da layukan ginshiƙai da ke riƙe jinkan, toh shine mutane ke kira sa sunan sarki Sulaimanu.
"tsananin mamaki"
A nan kalmar nan "haka" na nufin mamakin mutanen.
"'yan'uwa ba Isra'ila" Bitrus yana wa taron magana.
Bitrus yana wannan tambayan ne domin ya nanata cewa bai kamata su yu mamakin abinda ya faru ba. AT: "kada ku yi mamaki"
Bulus yana wannan tambayan ne domin ya nanata cewa bai kamata mutanen su ga kamar shi da Yahaya ne sun warkas da mutumin da iyawan su ba. AT: "kada ku zuba mana idanu. Bamu muka sa shi ya yi tafiya da ikon kanmu ko adalcin mu ba.
Wannan na nufin cewa sun kalle su da duk niya ba iyaka. AT: "zuba mana ido" ko kuma "kalle mu"
AT: "ƙin shi a wurin Bilatus"
"da Bilatus ya so ya sake Yesu"
"cewa Bilatus ya sake muku mai kisan kai"
wato Yesu. Wannan na nufin 1 "mai ba wa mutane rai na har abada" ko 2) "mai mulkin rayuwa" ko 3) "mai ba da rai" ko 4) "wadda ke kai mutane ga samun rai"
AT: "wandan Allah ya sa ya rayu kuma"
Wannan kalmar "yanzu" na jan hankalin masu sauraro zuwa kan gurgun.
A nan "suna" na nufin Yesu. Wannan na iya nufin 1) "domin wannan mutumin ya gaskanta da Yesu" ko 2) "domin Yahaya da Ni mun gaskanta da Yesu"
"ya sa shi ya warke"
Wannan na nufin 1) cewa mutanen basu san cewa Yesu ne Almasihu ba ko 2) cewa basu fahimci muhimmancin abinda suka yi ba.
Idan manzanin sun yi magana, yana kamar Allah ne da kansa ke maganan domin shi ne yake faɗa musu abinda za su ce. AT: "Allah ya annabta ta wurin gaya wa annabawa abin da su faɗa"
"Allah ya faɗa tun da sauran loƙaci" ko kuma "Allah ya faɗa kafin su faru"
A nan kalmar "baki" na nufin maganganun da annabawa sun faɗa ko sun rubuto. AT: "maganganun dukan annabawa"
"ku kuma juyo." Anan "juyo" na nufin fara yi wa Ubangiji biyayya. AT: "sai ku fara biyayya da Ubangiji"
A nan "shafe" na nufin gafartawa. An yi maganar zunubi kamar an rubuta su a wani littafi ne da Allah ke gogewa daga littafin a lokacin da ya gafarta su. AT: saboda Allah ya gafarta maku zunuban da kuka yi mishi
"loƙacin taimako daga wurin Ubangiji." Wannan na nufin 1) "loƙacin da Allah zai karfafa ruhunku" ko 2) loƙacin da Allah zai farfaɗo da ku"
A nan kalamun nan "wurin Ubangiji" na nufin Ubangiji da kansa. AT" "daga Ubangiji"
"domin ya aiko maku da Almasihu kuma." Wannan na nufin zuwan Almsihu kuma"
AT: "wadda aka naɗa domin ku"
"shine wanda dole sama ta marabta." Bitrus yana maganar sama kamar wani mutum ne wanda ke marabtan Yesu zuwa gidansa.
Wannan na nufin cewa lallai ne Yesu ya cigaba da zama a sama domin abinda Allah ya shirya kenan.
Wannan na nufin 1) har zuwa loƙacin da Allah zai komo da dukan abubuwa 2) "har loƙacin da Allah zai cika komai da ya anabta."
Da annabawa suka yi magana, yana kamar Allah ne da kansa ke maganan domin shi ne yake faɗa musu abinda za su ce. AT: "game da abubuwan da Allah ya yi magana da ta wurin cewa annabawansa tsarkaka su yi magana game da su"
A nan kalmar "baki" na nufin maganganun da annabawa sun faɗa ko sun rubuto. AT: "maganganun dukan annabawansa tsarkaka"
"za sa ɗaya daga cikin 'yan'uwanku ya zama annabin gaskiya, kuma kowa zai san da shi"
"kasanku"
AT: "shi annabin, Allah zai hallakar da shi gaba ɗaya"
"A gaskiya, dukan annabawa." A nan kalmar "I" na nanata abinda ya biyo.
"tun daga Sama'ila aka cigaba har zuwa dukan annabawan da suka zo a bayansa"
"waɗannan sau" ko kuma "abubuwan da ke faruwa yanzu"
A nan kalmar "'ya'ya" na nufin magadan da za su karɓi abinda annabawa da kuma alkawari ta alkawarta. AT: Kune magadan annabawa da kuma magadan alkawari"
"saboda zuriyanka"
Al'umma na nufin taron mutane ko kasashe. AT: "Zan albarkaci dukan taron mutanen duniya"
"Bayan da Allah ya sa Yesu ya zama bawansa ya kuma sa shi ya zama sananne"
Wannan na nufin Almasihu, Yesu.
"juyawa ... daga" na nufin sa wani ya daina yin wani abu. AT: "sa kowane ɗayanku ya daina yin mugunta" ko kuma "sa kowane ɗayanku ya tuba daga muguntarsa"
Bitrus da Yahaya sun gan wani gurgun mutum daga haifuwa wanda na roko a kofar Haikalin.
Bitrus bai ba wa mutumin azurfa da zinariya ba.
Bitrus ya ba ma mutumin iyawan tafiya.
Mutumin ya shiga Haikalin da tafiya, da tsalle, da kuma yabon Allah.
Mutanen sun cika da mamaki da al'ajabi.
Bitrus ya tunashi mutanene cewa sun kashe Yesu.
Bitrus ya ce bangaskiya a sunan Yesu ya sa mutumin ya warke.
Bitrus ya gaya ma mutanen su tuba.
Bitrus ya ce har lokacin sabuntawar duk abubuwa, za karbi Yesu a sammai.
Musa ya ce Ubangiji Allah zai tasar da wani annabi kamar kansa wanda mutanen za su saurari.
Mutum da bai saurari Yesu zai hallaka duka.
Bitrus ya tunashe mutanen cewa sune 'ya'yan alkawarin da Allah ya yi da Ibrahim a lokacin da ya ce, "Ta zuriyarka ne za a wa dukan kabilan duniya albarka".
Allah ya yi marmarin ya albarkaci Yahudawa ta aiko da Yesu masu da farko ya juye su daga muguntan su.
1 Yayin da Bitrus da Yahaya suna kan magana da mutanen, sai firistoci da shugaban masu tsaron Haikali da kuma Sadukiyawa suka afko masu. 2 Sun damu sosai domin Bitrus da Yahaya suna koyar da mutane game da Yesu kuma suna shelar tashinsa daga matattu. 3 Suka kama su suka jefa kurkuku sai washegari, domin yamma ta riga ta yi. 4 Amma mutane da yawa da suka ji sakon suka ba da gaskiya; kimanin mazaje dubu biyar ne kuwa suka ba da gaskiya. 5 Washegari, da shugabaninsu, da dattawansu, da Marubuta suka taru a Urushalima. 6 Anas babban firist, yana nan, da Kayafa, da Yahaya da Iskandari, da dukan dangin babban firist 7 Da suka kawo Bitrus da Yahaya a tsakiyarsu sai suka tambaye su, "Da wanne iko, ko cikin wanne suna k ka yi haka?" 8 Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya ce, "Ku shugabanni da dattawan jama'a, 9 idan mu yau ana tuhumarmu saboda aikin kirki da aka yi ga wannan mara lafiya - ta yaya wannan mutum ya sami lafiya? 10 Bari ku da dukan mutanen Isra'ila, ku san wannan, cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda kuka giciye, wanda Allah ya tayar daga matattu ta dalilinsa ne wannan mutumin yake tsaye a gaban ku lafiyayye. 11 Yesu Almasihu ne dutsen da ku magina kuka ki, amma an mai da shi kan gini. 12 Babu ceto daga kowanne mutum, domin babu wani suna da aka bayar karkashin sama, a cikin mutane wanda ta wurinsa za a iya samu ceto." 13 Sa'adda, suka ga karfin halin Bitrus da Yahaya, suka gane mutane ne talakawa marasa ilimi, sai suka yi mamaki, suka kuma lura suka gane Bitrus da Yahaya sun kasance tare da Yesu. 14 Da yake suna ganin mutumin nan da aka warkar tare da su, sai suka rasa abin yi. 15 Amma bayan sun fitar da manzannin daga majalisa sai suka tattauna a tsakaninsu. 16 Suka ce, "Yaya za mu yi da wadannan mutane? Babu shakka aikin al'ajibi ya faru ta wurinsu, kuma sananne ne ga dukan mazauna Urushalima, kuma ba mu da iko mu musanci haka. 17 Amma saboda kada ya cigaba da yaduwa cikin mutane, bari mu yi masu kashedi kada su kara magana da kowa cikin wannan suna." 18 Suka kira Bitrus da Yahaya suka dokace su kada su kara magana ko kuma koyarwa ko kadan a cikin sunan Yesu. 19 Amma Bitrus da Yahaya suka amsa suka ce, "Ko ya yi daidai a gaban Allah mu yi maku biyayya fiye da shi, ku hukunta. 20 Baza mu iya daina magana game da abubuwan da muka ji kuma muka gani ba." 21 Bayan sun sake yi wa Bitrus da yahaya kashedi, sai suka sake su, su tafi. Domin ba su iya samu wata hujja da za su hore su a kai ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru. 22 Mutumin da ya sami wannan al'ajibi na warkarwa yana sama da shekara arba'in. 23 Bayan an sake su, Bitrus da Yahaya suka zo cikin mutanensu suka ba da rahoton duk abin da manyan firistoci da dattawa suka fada masu. 24 Da suka ji haka, suka daga muryarsu tare ga Allah suka ce, "Ubangiji, kai da ka yi sama da duniya da teku da duk abin da ke cikinsu, 25 kai wanda ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin ubanmu Dauda bawanka, ya ce, 'Me ya sa al'ummai suka tunzura, kuma mutane suke tunanin abubuwan banza? 26 Sarakunan duniya sun hada kansu tare, kuma shugabanninsu sun taru don su yi gaba da Ubangiji, da kuma Almasihunsa.' 27 Hakika, Hiridus da Buntus Bilatus, tare da al'ummai da mutanen Isra'ila, sun taru a wannan birni domin su yi jayayya da bawanka mai tsarki Yesu, shafaffe. 28 Sun taru domin su aiwatar da dukan abin da hannunka da nufinka ya shirya zai faru. 29 Yanzu, Ya Ubangiji ka dubi kashedin su, ka ba bayin ka ikon furta maganar ka gabagadi. 30 Sa'adda ka mika hannunka domin warkarwa, alamu da al'ajibai su faru ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu." 31 Bayan sun gama addu'a, wurin da suka taru ya girgiza, suka cika da Ruhu Mai Tsarki, suka furta maganar Allah gabagadi. 32 Babban taron da suka ba da gaskiya kansu hade yake; kuma ba wanda ya ce da abinda ya mallaka nasa ne; maimakon haka, komai na su daya ne. 33 Da iko mai karfi manzannin suka yi shelar shaidarsu game da tashin Yesu Ubangiji daga matattu, babban alheri kuma na bisansu. 34 Babu wani a cikinsu wanda ya rasa komai, domin masu filaye da gidaje suka sayar suka kawo kudin abin da suka sayar 35 sai suka kawo kudin gaban manzanni. Aka rarraba wa kowanne mutum bisa ga bukatarsa. 36 Yusufu, Balawi, mutumin tsibirin Kubrus, wanda manzannisu ka yi wa lakani da suna Barnaba. (wato, mai karfafa zuciya). 37 Yana da fili sai ya sayar da shi ya kawo kudin gaban manzanni.
Bayan da Bitrus da Yahaya sun warkas da mutumin nan da aka haife shi gurgu, Malaman addini sun kama su.
"kusance su" ko kuma "zo wurinsu"
"Sun yi fushi kwarai." Sadukiyawa, musamman, za su fi yin fushi game da abinda Bitrus da Yohanna ke faɗa domin basu gaskanta da tashin mattatu ba.
Bitrus da Yohanna suna cewa Allah zai tayar da mutane daga matattu kamar yadda ya riga ya tayar da Yesu daga cikin matattu. A fasara wannan yadda "tashin matattun" zai nuna cewa ana nufin tashinwar Yesu daga matattu ne da kuma tashiwar kowa ne gabaɗaya.
Daga dukan waɗanda sun riga su mutu. Wannan furcin na bayyana dukan mutane gaba ɗaya da ke cikin karkashin duniya. A dawo daga cikinsu na maganar zama da rai kuma.
"Firistocin, shugaban masu tsaron haikalin, da kuma Sadukiyawan sun kamo Bitrus da Yahaya"
Basu saba tuhurmar mutane da dare ba
Wannan na nufin mazaje kadai kenan, baya haɗe da kimanin mataye da 'ya'ya ba da suka ba da gaskiya ba.
"ta karu zuwa wajen dubu biyar"
A nan kalmar "nasu" na nufin mutanen Yahudawa gabaki ɗaya.
An yi amfani ne da wannan jimlar ne domin a nuna wurinda aka fara ɗauka matakin. Idan harshenku tana da wata hanyar yin haka, za ku iya duban yadda za ku yi amfani da shi anan.
Wannan na nufin majalisar, kotun Yahudawa, wadda ta kunshi waɗannan kungiyoyin mutane kashi ukun.
Waɗanan mazaje biyun 'yan iyalin babban firist ɗin ne. Wannan ba Yahaya manzo ba ne.
"Wa ya baku iko"
A nan kalmar nan "suna" na nufin iko. AT: da ikon wa"
Duba yadda kun juya wannan a [2:4]. AT: Ruhu Mai Tsarki ya cika Bitrus sa ya"
Bitrus yayi wannan tambayar ne domin ya nuna a fili cewa dalilin da ya sa fitinansu kenan. AT: "Kunan tambayan mu a yau ... ta yaya wannan mutumin ya sami lafiya"
"kuna tuhumarmu a yau"
AT: "ta yaya muka sa wannan mutum ya sami lafiya"
AT: Bari dukan ku da kuke mutanen Isra'ila ku san wannan
"ku da kuke tuhumar mu da kuma dukan sauran mutanen Isra'ila"
A nan kalmar "suna" na nufin iko. AT: ta wurin ikon Yesu Almasihu Banazere"
Wannan karin magana ce da ke sa wanda ya mutu ya zama da rai kuma. AT: "wadda Allah ya sa ya rayu kuma"
Bitrus ya ruwaito wannan daga Zabura ne. Wannan na nufin cewa shugabanen addini, kamar magina, sun ki Yesu, amma Allah zai mai da shi mafi amfani a cikin mulkinsa, kamar yadda dutsen kan gini na da amfani"
A nan kalmar "kan" na nufin "mafi amfani"
"ku da magina suka ki" ko kuma "ku a matsayin magina kuka ki shi ba a bakin kome ba"
Ana iya fasara sunan "ceto" anan zuwa kalmar aiki. Kuna iya faɗin wannan haka AT: "Shine kaɗai mutumin da ya iya ceto"
AT: "babu wani suna a karkashin sama da Allah ya bayar a cikin mutane"
Jimlar "suna ... bayar a cikin mutane" na nufin mutumin nan Yesu. AT: "babu wani mutum a karkashi sama, wanda aka ba shi a cikin mutane, ta wadda"
Wannan wata hanya ne da ke nufin ko ina a cikin duniya. AT: "a cikin duniya"
AT: "da za ta cecemu" ko kuma "wanda zai iya ceton mu"
A nan "karfin hali" na nufin yadda Bitrus da Yahaya suka amsa wa shugabanen Yahudawan. AT: "yadda Bitrus da Yahaya suka yi magana da karfin hali" ko kuma "karfin halin da Bitrus da Yahaya suke da shi"
ba wani tsoro
Shugabanen Yahudawan su "gane" saboda yadda Bitrus da Yahaya suka yi magana"
"kuma sun fahimci"
Kalman nan "talakawa" da kuma "marasa ilimi" na da ma'ana kusan ɗaya. Suna nanata cewa Bitrus da Yahaya basu samu wata ƙwararren horoswa cikin shari'ar Yahuwada ba.
AT: mutumin da Bitrus da Yahaya sun warkas"
"babu abin faɗi game da warkar da wannan mutumin da Bitrus da Yahaya suka yi." Anan kalmar "wannan" na nufin abinda Bitrus da Yahaya suka yi.
Wannan nufin Bitrus da Yahaya
Shugabanen Yahudawan sun yi wannan tambayan saboda basu iya tunanin abinda za su iya yi wa Bitrus da Yahaya. AT: Babu abin da za mu iya yi wa waɗannan mutanen"
AT: "Gama duk mazaunan Urushalima sun san cewa sun yi aikin al'ajibi"
ba lallai haka yake ba. Wannan na iya zamanto cewa an yi shi ne domin a nuna cewa shugabanen suna ganin cewa wannan babban damuwane. AT: "mutane da dame da ke zama a Urusahlima" ko kuma "mutanen da ke zama a ko'ina a Urushalima"
A nan kalmar "ya" na nufin kowani al'ajibi ko kuma koyarwar Bitrus da Yahaya za su iya cigaba da yi. AT: "saboda kada labarin wannan al'ajibin ya cigaba da yaduwa" ko kuma "saboda kada mutane su kara jin game da wannan al'ajibin"
A nan kalmar "suna" na nufin mutuminan Yesu. AT: "kar ko ku kara magana da kowa game da wannan mutumin, Yesu"
A nan jimlar "a gaban Allah" na nufin ra'ayin Allah. AT: Ko Allah na ganin hakan daidaine"
Shugabannin Yahudawan sun sake yin barazanan horas da Bitrus da Yohanna.
Ko dashike Shugabannin Yahudawan sun yi wa Bitrus da Yahaya barazana, ba su iya samun wata dalilin horas da su har ba tare da sa mutane su ta da hargitsi ba.
AT: "saboda abin da Bitrus da Yahaya suka yi"
"Mutum wadda Bitrus da Yahaya suka warkar ta al'ajibi"
Jimlar nan "mutanensu" na nufin sauran masubi. AT: "je wuring sauran masubi"
A daga murya karin maganane da ke nufin yin magana. "suka farin yin magana tare ga Allah" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)
Wannan na nufin ce Ruhu Mai Tsarki ya sa Dauda ya faɗi ko kuwa ya rubuta abin da Allah ya faɗa.
kalmar nan "baki" na nufin maganar da Dauda ya faɗi ko ya rubuto. AT: "ta wurin maganar bawanka, ubanmu Dauda
A nan "uba" na nufin "kakani"
Wannan tambayan ganganci ne da ke nanata azancin gãba da Allah. AT: "Kasashen Al'ummai baza su yi fushi ba, kuma mutanen baza su yi tunanin abubuwan banza ba"
Waɗannan "abubuwan banzan" na kunshe da shirin gãba Allah. AT: "mutanen suna tunanin abubuwan banza na gãba da Allah"
...
Waɗannan jimla biyun na nufin kusan abu ɗaya. Dukan su suna nanata cewa ƙoƙarin duk shugabannin duniya su yi hamaya da Allah.
Waɗannan jimla biyun na nufin sun haɗa rundunar soja domin faɗa da yaƙi
A nan kalmar nan "Ubangiji" na nufin Allah. A cikin Zabura, kalmar "Almasihu" na nufin shafaffe na Allah
"wannan birni" na nufin Urushalima
Yesu wadda ke bauta maka da aminci"
A nan an yi amfani da kalmar nan "hannu" mai nufin ikon Allah. Bugu da ƙari, jimlar nan "hannunka" da nufinka da ka shirya" na nuna ikon Allah da shirinsa. AT "aiwatar da duk abin da ka shirya domin kai mai iko ne kuma kã yi dukan abinda ka shirya"
A nan kalmar "dubi" roko ne ga Allah ya lura da yadda shugabannin Yahudawan na yi wa masubi barazana. AT: "lura da yadda suke barazana su hore mu"
Kalmar "magana" anan na nufin sakon Allah. AT: "furta maganarka da gabagaɗi" ko kuma "zama da gabagaɗi da muke furta sakonka"
A nan kalmar nan "hannu" na nufin ikon Allah. Wannan roƙo ne ga Allah ya nuna ikonsa. AT: A yayin da kake nuna ikon ka ta wurin warkas da mutane"
A nan kalmar nan "suna" na nufin iko. AT: ta wurin ikon bawanka mai tsarki Yesu"
...
Duba yadda kuka fasara wannan a
AT: "suna tunani ta hanya ɗaya kuma suna son abubuwa ɗaya"
"sun rarrraba mallakarsu da juna" Duba yadda kun fasara wannan a [2:44]
Wannan na iya nufin 1) cewa Allah yan sa wa masubin albarka sosai ko kuma 2) cewa mutanen da ke Urushalima su na ganin masubin da girma sosai.
AT: "Mutane da dama da ke da filaye ko gidaje" ko kuma "mutane masu filaye ko gidaje" Dubi:
...
AT: "kuɗaɗen da suka samu da abubuwan da sun sayar"
AT: "suka miko wa manzannin" ko "sun ba wa manzannin"
A nan iya fasara sunan nan "bukata" da kalmar aiki. AT: suka rarraba kudaden go kowane mai bi da ke bukatarsa"
Manzannin sun yi amfani da wannan suna ne domin su nuna cewa Yusufu mutum ne da ya karfafa sauran mutane. "Ɗan " karin magana ne da ke bayyana yanayi ko halin mutum. AT: "mai karfafawa" ko kuma "wanda ke karfafawa"
Bitus da Yahaya sun koyar a kan Yesu da tashiwan sa daga matattu.
Sun kama Bitrus da Yahaya sun kuma sa su a gidan wakafi.
Mutane dayawa sun bada gaskiya, kamar dubu biyar.
Bitrus ya ce a cikin sunan Yesu Almasihu ya warkar da mutumin a Haikalin.
Bitrus ya ce ba wata suna in banda na Yesu ta wanda zamu iya sami ceto.
Shugabannin basu iya ce komai ba domin mutumin da an warkar na tsaye da Bitrus da Yahaya
Shugabannin Yahudawa sun umurne Bitrus da Yahaya kadda su yi magana ko koyar akan Yesu.
Bitrus da Yahaya sun ce wai baza su taimaka idan basu yi magana akan abubuwa da sun gani da kuma ji.
Masubi sun tambaya wa magana da karfin hali, kuma a yi alamu da abubuwan al'ajabi a sunan Yesu.
Bayan masubi sun gama addu'a, wurin da sun hadu ya girgiza, sun cika da Ruhu Mai Tsarki, da kuma sun yi magana gabagadi.
Masubin suna da kome na kowa, kuma ma su dukiya sun sayar suka kuma bayar da kudin a rarraba bisa ga bukata.
Masubin suna da kome na kowa, kuma ma su dukiya sun sayar suka kuma bayar da kudin a rarraba bisa ga bukata.
Mutum ma suna "Dan karfafa" ne Barnaba.
1 Sai wani mai suna Hananiya da matarsa Safiratu, suka sayar da filinsu, 2 Hananiya kuwa ya boye wasu daga cikin kudin filin, (kuma da sanin matarsa), sa'annan suka kawo ragowar kudin a gaban manzannin. 3 Amma Bitrus ya ce, "Hananiya don me shaidan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki karya? Har ka boye wasu daga kudin filin? 4 Sa'adda ba ka sayar da filin ba, ba mallakarka bane? Bayan da ka sayar ma, ba naka bane? Don me kayi irin wannan tunanin a zuciyarka? To ba mutane ka yi wa karya ba, Allah ka yi wa." 5 Nan take da jin haka, Hananiya ya fadi ya ja numfashinsa na karshe. Dukan mutanen da suka ji labarin kuwa tsoro mai girma ya afko masu 6 Matasa suka zo suka nannade gawarsa, suka fitar da shi waje suka binne shi. 7 Bayan wajen sa'a uku, sai matarsa ta iso, ba tare da sanin abin da ya faru ba. 8 Sai Bitrus ya ce mata, "ki gaya mini ko nawa kuka sayar da filin?" Sai ta amsa, "ta ce kaza ne." 9 Sa'annan Bitrus ya ce mata, "Don me kuka shirya wannan makidar tare da mijinki don ku gwada Ruhun Ubangiji? Kiji tafiyar wadanda suka bizne mijinki a bakin kofa, kuma za su dauke ki yanzu." 10 Nan take sai ta fadi a gabansa, ta ja numfashinta na karshe, matasan kuwa suka zo suka same ta ta mutu; sai suka dauki gawarta suka kai waje suka kuma bizne ta kusa da mijinta. 11 Tsoro mai girma kuwa ya afko wa iklisiyar gaba daya da dakan wadanda suka ji wadan nan al'amura. 12 Ayyukan alamu da ban mamaki masu yawa kuwa sun faru ga mutane, ta hannun manzannin. Dukansu kuma suna nan tare a dakalin Sulaimanu, 13 Sai dai babu mai karfin halin ya hada kai tare dasu; amma suna da kwarjini sosai a gaban jama'a. 14 Har wa yau aka rika samun karin masu ba da gaskiya, dinbin jama'a, maza da mata, 15 har sukan dauki marasa lafiya su kai su bakin titi, suna kwantar da su a bisa gadaje da shinfidu, domin idan Bitrus ya zo wucewa ko da inuwarsa ma ta taba wasunsu. 16 Mutane dayawa kuwa sukan zo daga garuruwan da ke kewaye da Urushalima, suna kuma kawo masu rashin lafiya, da wadanda aljannu ke damunsu, aka kuma warkar da su duka. 17 Amma babban firist ya taso tare da duk wadanda ke tare da shi (wato 'yan darikar Sadukiyawa); suka cika da kishi matuka 18 suka kama manzannin suka kuma jefasu a kurkuku. 19 A cikin dare sai mala'ikan Ubangiji ya bude kofofin kurkukun ya kuma fito da su waje, ya ce, 20 "Kuje ku tsaya a gaban haikali ku kuma gaya wa mutane maganar wannan rai." 21 Sa'adda suka ji haka, sai suka tafi haikalin da wayewar gari suka yi koyarwa. Amma babban firist da jama'arsa suka zo suka kuma kira taro da kuma dukan yan majalisa, da dattawan jama'ar Isra'ilawa suka fito suka kuma ba da umarni, a fito masu da manzannin. 22 Amma ma'aikatan da suka je kurkukun basu sami kowa, a kurkukunba, sai suka dawo suka ba da rahoto, 23 Su ka ce kurkukun a rufe gam da masu gadi suna nan a tsaye a bakin kofar amma da muka shiga, bamu sami kowa a ciki ba. 24 Yanzu sa'adda shugaban haikalin da manyan firistoci suka ji wadannan kalamai, sai suka rikice sosai game da su, suka ce yanzu me wannan zai haifar. 25 Sai wani ya zo ya ce masu, "Wadannan mutanen da kuka jefa a kurkuku suna can a cikin haikali suna koyar da jama'a." 26 Sai shugaban haikalin ya je da ma'aikatansa suka kawosu, ba tare da tashin hankali ba, domin gudun kada jama'a su jejjefesu. 27 Da suka kawo su, sai suka gabatar da su gaban majalisa, babban firist kuwa ya tuhume su, 28 cewa "Ba mun yi maku kashedi da karfi kada ku yi koyarwa cikin wannan sunan ba? Amma ga shi duk kun cika Urushalima da koyarwarku, kuna kuma neman kusa jinin mutumin nan ya sauko kanmu." 29 Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, "Dole mu yi wa Allah biyayya ba mutane ba. 30 Allah na ubanenmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe, ta wurin rateye shi a bisa itace, 31 Allah kuwa ya daukaka shi a hannun damarsa, domin ya zama sarki da kuma mai ceto, ya ba Isra'ila tuba da gafarar zunubai. 32 Mu kuwa shaidu ne ga wadannan al'amura, haka ma Ruhu Mai Tarki, wanda Allah ya bayar ga dukan wadanda suka yi biyayya a gareshi." 33 Da yan majalisa suka ji haka sai suka fusata kwarai da gaske, har suka nemi su kashe manzannin. 34 Amma wani Bafarise mai suna Gamaliel, malami ne kuma na attaura wanda dukan jama'a suna martabawa, sai ya mike ya ba da umarni cewa a fid da manzannin waje na dan lokaci. 35 Sai ya ce masu "Ya ku mutanen Isra'ila, ku lura sosai da a binda kuke niyyar yi wa mutanen nan, 36 A kwanakin baya wani ya zo mai suna Tudas ya dauki kansa wani abu, kimanin mutane dari hudu ne suka bishi, amma da aka kashe shi jama'arsa baki daya sai suka watse, ba wanda ya kara jin labarinsu. 37 Bayansa kuma, aka yi wani mai suna Yahuza na Galili wanda a kwanakin kidaya, ya zo ya rinjayi mutane da yawa, shima ya lalace, duk wadanda suka bi shi kuwa suka watse. 38 Don haka ina gaya maku ku rabu da mutanen nan, domin idan shirinsu ko kuma ayyukansu na mutane ne za su lalace. 39 Amnma idan abin nan daga Allah yake baza ku iya lalata su ba; kada ya zama kuna gaba da Allah." Sai suka rinjayu. 40 Da suka kira manzannin ciki suka yi masu duka, sai suka umarce su da cewa kada su sake koyarwa a cikin sunan Yesu, sai suka barsu suka tafi. 41 Suka fita daga cikin majalisar, suna murna domin sun cancanta su sha wulakanci saboda sunan. 42 Bayan haka kullayomin suna zuwa haikali, suna bi gida gida, suna wa'azi, suna kuma koyarwa ba fasawa cewa Yesu shine Almasihu.
Luka ya cigaba da labarin yadda sabobin masubi sun raba mallakarsu da sauran masubi. Sa'annan ya faɗi yanda masubi guda biyu, Hananiya da Safiratu.
An yi amfani da wannan kalman anan don a sa alamar yanke ainihin labarin a faɗi wata sabuwan bangaren labarin.
"matarsa ma na da sanin cewa ya ajiye sauran kuɗin"
Wannan na nufin sun ba wa manzannin kuɗin. AT: "ba da shi wa manzannin" ko kuma "ba wa manzannin"
Idan harshen ku ba ta amfani da tambayoyin ganganci, za ku iya canza waɗannan zuwa zance.
Bitrus ya yi amfani da wannan tambayan ne don ya sauta wa Hananiya. AT: "'da baka bar shaiɗan ya cika zuciyarka har ka yi karya ... gona."
A nan kalmar nan "zuciya"na nufin nufi ko shauƙi. Jimlar nan "Shaiɗan ya cika zuciyarka" karin magana ne da ke iya nufin 1) "Shaiɗan ya shawo kanna dabaɗaya" ko kuma 2) "shaiɗan ya rinjaye ka"
Wannan na nufin cewa Hananiya ya faɗa wa manzannin cewa ya bayar da dukan yawan kuɗin da ya karɓo ne daga sayar da gonarsa.
Bitrus na amfani ne da wannan tambayan don ya sautar wa Hananiya. AT: "Sa'adda ba ka sayar da filin ba, ai naka ne ..."
"Sa'adda baka sayar da shi ba"
Bitrus yana amfani da wannan tambayan ne don ya sautawwa Hananiya. AT: "bayan da ka sayarma, kana da mulki a kan kuɗin da ka karɓa"
AT: bayan da ka sayar da shi"
Bitrus yayi amfani ne da wannan tambayan ya sauta wa Hananiya. Anan kalmar nan "zuciya" na nufin nufi da shauƙi. AT: "Da ba ka yi tunanin yin haka ba"
A nan "ja nufashinsa na ƙarshe" wata hanyar ɗa'a ne na faɗin cewa ya mutu. Hananiya ya fãɗi ya mutu, ba wai ya mutu don ya fãɗi bane. AT: "mutu sai ya fãda kasa"
"Matar Hananiya ta shigo" ko kuma "Safiratu ta shigo"
"cewa mijinta ya mutu"
"ko nawa kuɗin." Wannan na nufin yawan kuɗin da Hananiya ya bawa manzannin.
Bitrus ya yi wannan tambayan ne don ya sauta wa Safiratu. AT: "Da ba ki yarda ba da mijinki ku gwada Ruhun Ubangiji tare!"
"kun yarda tare ku biyu"
A nan kalmar nan "gwada" na nufin a kalubale ko a jarrabta. Suna kokarin gani ko za su iya wa Allah ƙarya su tafi ba tare da samun hukuncinsa ba.
A nan kalmar na "tafiyar" na nufin mutanen. AT: "mutanen da suka bizne mijinki"
Wannan na nufin cewa da ta mutu, ta faɗi a kasa a gaban Bitrus. Kada a rikice wannan furci da faɗiwar mutum kasa mai nuna alamar kaskance.
A nan "ja nufashinta na ƙarshe" wata hanyar ɗa'a ne na faɗin cewa ta mutu. Duba yadda kun fasara irin wannan jimlar a [5:5]
ko "Ayyukan alamu da ban mamakisun faru a cikin mutanen ta hannun manzannin." AT: "Manzannin sun yi ayyukan alamu na ban mamaki a tsakanin mutanen"
"aukuwar allahntaka da ayyukan mu'ujizai." Duba yadda kun fasara wannan kalamun a [2:22].
Anan kalmar nan "hannun" na nufin manzannin. AT: ta wurin manzannin"
"gefen dakalin Sulaimanu." Wannan wata gefe ne da ke kunshe da layukan ginshiƙai da ke riƙe jinkan, wadda shine mutane ke kiran sa sunan sarki Sulaimanu. Duba yadda kuka fasara "dakalin da a ke ce da ita na Suleimanu" a [3:11]
AT: "mutanen sun ba wa masubin girma sosai"
Duba yadda kun fasara "aka sami" a [2:41]. AT: Karin masubi cikin Ubangiji"
Ana nufin cewa Allah zai warkar da su idan inuwar Bitrus ya taɓa su.
"waɗanda ruhuhi mara tsarki suka damesu"
AT: Allah ya warkar da su duka" ko kuma "manzannin sun warkar da su duka"
Wannan na fara wata labari ne da ya bambanta. Za a iya fasara wannan a wata hanyar da harshen daku ke gabatar da labarin da ya bambanta.
A nan kalmar nan "taso" na nufin cewa babban firist ya dauki mataki, ba wai ya tsaya daga wurin zamansa ba. AT: babban firist ɗin ya ɗauki mataki"
AT: "suka zama da kishi sosai"
Wannan na nufin cewa sun cafke su da ƙarfi. Da sun umurce masugadi su yi haka. AT: "sa masugadin su kãmã manzannin"
Basu je cikin ginin haikalin inda firistoci ne kaɗai ake bari su je ba. AT: "zuwa tsakar haikalin" ko kuma "zuwa yankin haikalin"
Kalmar nan "magana" na nufin sakon da manzannin sun riga sun shela. Wannan na iya nufin 1) "dukan sakon rai na har abada" ko kuma 2) " gabaɗayar sakon wannan sabuwar hanyar rayuwa"
"da wuri ya fara haske." Kodashike mala'ikan ya fito da su waje da dare, amma rana tana kan haurowa a loƙacin da manzannin suka kai tsakar haikalin.
Wannan na nuna cewa wani ya je kurkukun. AT "aike wannan zuwa kurkukun ya kawo manzanannin.
Kalmar nan "kowa" na nufin manzannin. Wannan na nuna cewa babu kowa a kurkukun in ba manzannin ba. AT: ba mu same su a ciki ba"
"sun yi mamaki sosai" ko kuma "sun ruɗe sosai"
"game da maganar da suka fito ji" ko kuma "game da waɗannan abubuwan"
"menene zai zama sakamakon wannan"
Basu je cikin ginin haikalin inda firistoci ne kaɗai ake bari su je ba. AT: suna koyarwa a zuwa tsakar haikalin"
...''sai suka ji tsoro''
A nan kalmar nan "suna" na nufin Yesu da kansa. Duba yadda kuka fasara wannan a [4:17]. AT: faɗa wa kowa game da mutumin nan, Yesu"
An yi maganar koyar wa mutane masu yawa a birnin kamar suna cika birnin ne da koyarwa. AT: "Kun koyar wa mutane da yawa a Urushalima game da shi" ko kuma "kun yi koyarwa game da shi a Urushalima gaba ɗaya"
A nan kalmar nan "jini" na nufin mutuwa, kuma a sa jinin wani a kan mutane na nufin cewa sune da laifin mutuwar mutumin. AT: "neman sa man alhakin mutuwar wannan mutum"
Bitrus ya yi magana a maɗadin manzannin da ya faɗi waɗannan kalaman"
A nan "ta da" karin magana ne. AT: "Allahn Ubannen mu ne ya sa Yesu ya sake rayuwa kuma"
Zama a "hannun damar Allah" alama ce na samun baban martaba da iko daga wurin Allah. AT: "Allah ya ɗaukaka shi zuwa wurin martaba a gefensa"
A nan "Bitrus" yana amfani ne da kalmar nan "bishaya" ya nuna giciyen da aka yi shi da katako. AT: "ta wurin rateye shi a bisa giciye
Ana iya fasara kalamun nan "tuba" da "gafara" zuwa kalmar aiki. AT: ya ba wa mutanen Isra'ila damar tuba su kuma samu sa Allah ya gafarta zunubansu"
Kalmar nan "Isra'ila" na nufin mutanen Yahudawa.
Waɗandan sun mika kanzu ga ikon Allah"
Luka ya gabatar da Gamaliel, sai ya bayar da tarihinsa.
AT: "wanda dukan mutanen ke martabawa"
AT: Umurce masugadin su fid da manzannin waje"
"yi tunani da kyau da" ko kuma "yi hankali da." Gamaliel yana masu gargaɗi ne kada su yi wani abinda za su yi baƙin cikinsa nan gaba.
Wannan na iya nufin 1) "Tudas yayi tawaye" ko kuma 2) "Tudas ya ɓullo"
"ɗauki kansu wani mai muhimmanci"
AT: "mutane suka kashe shi"
AT: "dukan mutanen da suke binsa suka watse" ko kuma "jama'ar da suke binsa suka kama hanyan su daban-daban"
Wannan na nufin cewa basu yi abinda suka shirya su yi ba.
"Bayan Tudas"
"loƙacin ƙiɗaya mutanen ƙasa"
Wannan na nufin ya rinjayi wasu mutane tare da shi kuma suka yi wan gwamnatin Roma tawaye. AT: sa mutane da yawa sun bi shi" ko kuma "sa mutane da yawa sun haɗa kai da shi a tawaye"
Gamaliel yana gaya wa shugananen Yahudawa cewa kada su kara hores da manzannin kuma ko su mayar da su kurkuku kuma .
"idan mutane ne sun kirkiro wannan shirin ko sun yi wannan aikin"
AT: wani zai lalace su"
A nan kalmar nan "abin" na nufin "shirin ko aikin." AT: "idan Allah ne ya kirkiro wannan shirin ko ya umurta waɗannan mutanen su yi wannan aikin"
AT: Sai Gamaliel ya rinjaye su"
Kungiyan majilisan na iya dokaci masu gadin haikalin su aikata waɗannan abubuwan.
A nan "suna" na nufin ikon Yesu. Duba yadda kun fasara inrin wannan jimlar a [4:18]. AT: "su kara koyarwa a cikin ikon Yesu"
Manzannin san yi murna domin Allah ya martaba su ta wurin barin shugabannen Yahudawan su wulakantasu. AT" "Allah ya lisaftasu cikin waɗanda sun cancanta su sha wulakanci saboda Sunan"
A nan "Sunan" na nufin Yesu. AT: "saboda Yesu"
Bayan wannan ranan, kowace rana." Wannan jimlar na nuna alamar abinda manzannin suka yi kowace rana har zuwa kwanakin da sun biyo baya.
Basu je cikin ginin haikalin inda firistoci ne kaɗai ake bari su je ba. AT: "a cikin haikalin da kuma cikin gidajen mutane daban-daban"
Hananiya da Safiratu sun yi karya, cewa suna bayar da duka farashi da sun samu daga dukiyan su, amma zahirin sun baya da sashin farashin.
Bitrus ya ce Hananiya da Safiratu sun yi karya ma Ruhu Mai Tsarki.
Allah ya kashe Hananiya.
Allah ya kashe Safiratu.
Baban tsoro ta zo akan ikklisiyan da duk wanda sun ji akan Hananiya da Safiratu.
Wasu na dauke mara lafiya cikin tituna don inuwan Bitrus ya fadi a kan su, kuma wasu sun kawo mara lafiya daga wasu garuruwa zuwa Urushalima.
Sadukiyawa sun cika da kishi kuma sun sa manzannin a kurkuku.
Malaika ya zo ya bude kofofin kurkukun ya kuma fitar da su.
Jami'an sun samu kurkukun tam a kule, amma ba kowa a ciki.
Jami'an sun ji tsoro cewa mutanen zasu iya jefe su.
Manzannin sun ce, "Tilas ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum".
Manzannin sun ce baban firistoci da mambobin majalisa na da alhakin kashe Yesu.
Mambobin majalisan sun yi fushi sun kuma so su kashe manzannin.
Bagalile ya shawarce majalisan su bar manzannin kadai.
Majalisan sun duke su kuma sun umurce su kada su yi magana a sunan Yesu, sun kuma bar su su tafi.
Manzannin sun yi farin ciki cewa an kirga su da kirki su sha wahala qyamar don sunan Yesu.
Manzannin sun yi wa'azi sun kuma koyar kowani rana cewa Yesu ne Almasihu.
1 A wadannan kwanaki, yawan almajiran ya ci gaba da ribanbanya, sai Yahudawan da suke zama a kasar Helanawa suka fara gunaguni game da Yahudawan Isra'ila, domin basu damu da gwamrayensu, wajen raba abinci da ake yi kullum. 2 Manzannin nan sha biyu suka kira taron almajiran suka ce masu, "Bai kamata mu bar maganar Allah mu shiga hidimar rabon abinci ba. 3 Don haka ku zabi 'yan'uwa maza daga cikinku, mutane bakwai wadanda a ke ganin su da daraja, cike da Ruhu da kuma hikima, wadanda za mu zaba suyi wannan hidima. 4 Mu kuwa mu ci gaba da da addu'a da kuma hidimar kalmar." 5 Maganar su kuwa ta farantawa dukan jama'a rai sosai. Sai suka zabi Istifanus, shi kuwa mutum ne cike da bangaskiya kuma da Ruhu Mai Tsarki da Filibus, da Birokoros, da Nikanar, da Timan, da Barminas, da kuma Nikolas, mutmin Antakiya wanda ya yi tuban Yahudanci. 6 Masu bin kuwa suka gabatar da wadannan mutanen a gaban manzannin, su kuwa suka yi masu addu'a suka kuma dora hannuwansu a kansu. 7 Sai maganar Allah ta yawaita; yawan almajiran kuwa ya rubanbanya matuka a Urushalima; firistoci da yawa na Yahudawa suka bada gaskiya. 8 Sai Istifanus, cike da alheri da iko, ya rika yin ayyukan ban mamaki da alamu a cikin jama'a. 9 Amma sai ga wadansu mutane daga wata majami'a da ake kira majami'ar Yantattu, wato su Kuramiyawa da Iskandariyawa, da kuma wasu daga kasar Kilikiya da Asiya. Wadannan mutanen kuwa suna muhawara da Istifanus. 10 Amma suka kasa yin tsayayya da Istifanus, saboda irin hikima da Ruhun da Istifanus ya ke magana da shi. 11 Sai a asirce suka zuga wasu mutane su je su ce, "Ai munji Istifanus yana maganganun sabo game da Musa da kuma Allah." 12 Sai suka zuga mutanen, har da dattawa da marubuta suka tunkari Istifanus, suka kama shi, suka kawo shi gaban majalisa. 13 Suka kawo masu shaidar karya suka ce, "Wannan mutumin har yanzu bai dena maganganun gaba akan wannan wuri mai tsarki da kuma shari'a ba. 14 Domin kuwa mun ji shi, yana cewa wannan Yesu Banazarat zai rushe wannan wuri zai kuma canza al'adun da muka gada daga wurin Musa." 15 Dukan wadanda suke zaune a majalisar suka zuba masa ido, sai suka ga fuskarsa kamar ta mala'ika.
Wannan shine forkon wata bangaren labarin. Luka yana ba da muhummin bayyanin tarihin da zai tamaka a fahimtar labarin.
Duba yadda ake gabatar da sabuwar bangaren labari a harshen ku.
"na karuwa kwarai da gaskiya"
Waɗannan su ne Yahudawa da sun yi rayuwarsu mafi yawa a wata yankin Roma waje da Isra'ila, kuma sun tashi suna yin Grika. Harshen su da al'adan su na da banbanci da wa na waɗanda suka tashi a Isra'ila.
Waɗannan sune Yahudawa da suka taso a Isra'ila suna yin Yahudanci. A wannan loƙacin Ikkilisiyar ta kunshi yahudawa ne da kuma tubabbu da addinin Yahudanci kawai.
matayen da mazajensu sun mutu
AT: "Yahudawa masubin ba su damu da gwamrayen Halenawan ba"
"kyale su" ko "manta da su." An manta da mutane da dama da da suke buƙatan taimako
Kuɗaden da ake ba wa manzannin wanda ake amfani da raguwansa a siya abinci wa gwamrayen ikkilisiya na farko.
Wannan na nufin a haɗe da Matiyas, wadda aka zaba a [1:26]
"dukan almajira" ko "dukan masubi"
An faɗi wannan ne domin a nanata muhimmancin hidimar su na koyar da maganar Allah. AT: "daina wa'azi da koyar da maganar Allah"
Wannan jimlar na nufin a raba wa mutanen abinci"
Wannan na iya nufin 1) mutanen na da halaye uku-- a ke ganin su da daraja, suna cike da Ruhu Mai Tsarki, kuma da hikima ko kuma 2) Mutanen suna da halaye biyu-- cike da Ruhu Mai Tsarki, da kuma cike da hikima.
"Mutanen da aka san su da kirki" ko kuma "mutanen da an yarda da su"
"ɗauki nawayan wannan aiki"
Zai zama da amfani sosai a yi karin bayani a kan wannan. AT: "hidimar koyar wa da wa'azin sakon"
"Dukan jama'ar sun so shawarwarinsu"
Waaɗnnan sunayen Grika ne, kuma suna ba da ra'ayin cewa dukan mutanen da aka zaba daga taron Yahudawa ne masu jin Halenanci ne.
Bahalane da ya tuba zuwa addinin Yahudawa
Wannan na nufin zuba albarku da kuma ɗaura nawaya da ikon aiki ga mutane bakwai din.
AT: "mutanen da sun gaskanta da maganar Allah sun ƙaru" ko kuma "kimamun mutanen da sun gaskata da sakon Allah sun ƙaru"
"ke bin wannan sabuwar koyaswa"
Wannan na iya nufin 1) sakon bisharar amincewa da Yesu ko kuma 2) koyaswar ikkilisiya ko kuma 3) koyaswar bi.
Wannan itace ce forƙon wata sabuwar bangaren labarin.
Wannan na gabatar da Istifanus a matsayin ainihin mai jan hankali a wannan labarin.
Kalamun nan "alheri" da "iko" anan na nufin ikon Allah. Anan iya kãrin bayani game da wannan. AT: Allah na ba wa Istifanus ikon yin"
"Yantattu" na nufin mutanen da ke bayi ne dama daga wurare daban-daban. Ba a san ko mutanen da aka jera suna cikin majami'ar ko kuma sun bi sun shiga muhawara da Istifanus ba ne.
"suna musu da Istifanus"
Wannan na nufin cewa ba za su iya ƙaryata abinda shi ya faɗa ba. AT: "ba za su iya musanta ba"
wannan na nufin Ruhu Mai Tsarki
An basu kuɗi su ba da shaidar ƙarya. AT: "wasu mutane so yi ƙarya su ce"
"abubuwan da ba kyau game"
"sa mutanen, da dattawan, da marubuta su yi fushi kwarai da Istifanus"
"cafke shi suka kuma riƙe shi yadda ba zai iya kubucewa ba"
"cigaba da magana"
Jimlar nan "gãɗa" na nufin "an miƙo" AT: "koyas da kakanninmu"
Wannan karin maganar na nufin sun kalle shi da kyau. Anan "ido" na nufin kallo. AT: "kalle shi da sosai" ko kuma "sun gan shi"
Wannan jimlar na nufin kwatanta fuskar sa da na mala'ika amma ba tare da ya faɗi abinda ya haɗa su ba.
Yahudawa masu ji Helenanci sun yi gunaguni cewa ba'a kula da gwanrayen su a rabawan abincin kulayomi.
Almajiran ('yan'uwa)sun zabi mutane bakwai.
Mutane bakwai suna da suna mai kyau, cike da Ruhu da hikima.
Almajirain zasu ci gaba a addu'a kuma a hidiman kalma.
Manzannin sun yi addu'a sun kuma saka hanaye a kan su.
Lamban almajirain ya karu kwarai, duk da lamban firistoci ya karu kwarai.
Yahudawa marasa bi basu iya tsaya gaba da hikima da Ruhu wanda Istafanas ya yi magana.
Shaidu masu karya sun yi da'awa cewa Istafanas ya ce Yesu zai halakar da wurin kuma ya canza kwastan na Musa.
Sun gan cewa fuskarsa na nan kamar fuskar mala'ika.
1 Sai babban firist ya ce, "Wadannan al'amura gaskiya ne?" 2 Sai Istifanus ya amsa ya ce, "Ya 'yan'uwa da ubanni, ku saurare ni, Allah Madaukaki ya bayyana ga ubanmu Ibrahim tun yana can kasar Mesofotamiya, kafin ma ya zauna a kasar Haran; 3 ya ce masa, 'Ka bar kasarka da danginka, ka tafi kasar da zan nuna maka.' 4 Sa'annan ya bar kasar Kaldiyawa ya zo ya zauna a Haran; daga can, bayan rasuwar mahaifinsa, sai Allah ya kira shi zuwa wannan kasa da kuke ciki. 5 Amma Allah bai ba shi kasar gado ba tukuna, ko da misalin tafin sawunsa. Amma ya alkawarta - ko da yake bai riga ya haifi da ba tukuna - wanda zai ba shi kasar gado, shi da zuriyarsa, a bayansa. 6 Allah ya yi magana da shi kamar haka, cewa zuriyarsa za su yi bakonci a wata kasa wadda ba tasu ba, mutanen wannan kasar kuwa za su gwada masu bakar azaba su kuma bautar da su har shekaru dari hudu. 7 'Kuma zan hukunta wannan al'umma da ta bautar da su,' Allah ya ce, 'Bayan haka za su fito daga wannan kasa su bauta mini a wannan wuri.' 8 Allah ya ba Ibrahim alkawarin kaciya, sai Ibrahim ya haifi Ishaku ya yi masa kaciya a rana ta takwas; Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu kuma ya haifi ubanni Isra'ila su goma sha biyu. 9 Wadannan 'yan'uwa suka yi kyashin danuwansu Yusifu suka sayar da shi bauta zuwa Masar. Amma Allah na tare da shi. 10 Ya kuwa cece shi daga dukan sharin da yan uwansa suka kulla masa, Allah kuwa ya ba shi tagomashi da hikima a gaban Fir'auna, sarkin Masar. Fir'auna kuwa ya mai da shi mai mulki a dukan kasar Masar da kuma dukan mallakarsa. 11 Sai aka yi babbar yunwa a dukan kasar Masar da ta Kan'ana, iyayenmu suka sha wuya saboda rashin abinci. 12 Amma lokacin da Yakubu ya ji akwai hatsi a kasar Masar, sai ya aiki ubannimu a karo na farko. 13 Da suka je a karo na biyu, sai Yusifu ya bayyana kansa ga yanuwansa; a wannan lokaci ne Fir'auna ya gane da yanuwan Yusufu. 14 Yusufu ya aiki yanuwansa su kawo Yakubu ubansu da dukan mallakarsu da iyalansu zuwa Masar, Dukansu mutane saba'in da biyar ne. 15 Yakubu ya tafi ya zauna a Masar; shi da zuriyarsa har mutuwar su. 16 Aka dauke su zuwa Shekem aka binne su a kabarin da Ibrahim ya saya da kudin azurfa daga hannun yayan Hamor a Shekem. 17 Yayin da alkawarin Allah ya kusato wanda Allah ya fada wa Ibrahim, mutanen suka karu suka hayayyafa kwarai a Masar, 18 Sai a ka yi wani sarki a Masar wanda bai san Yusifu ba, 19 Wannan sarki ya yaudari kakkaninmu ya yi masu mugunta kwarai da gaske, har ma ya kai ga suna barin jariransu cikin hasari don su ceci rayukansu. 20 A wannan lokaci ne aka haifi Musa, kuma kyakkyawan yaro ne sai aka yi renon sa tsawon wata uku a gidan mahaifinsa a asirce. 21 Yayin da aka jefar da shi, sai diyar Fir'auna ta dauke shi ta rene shi kamar danta. 22 Aka ilimantar da Musa da dukan ilimi irin na Masar; kuma ya shahara cikin fasahar magana da kuma ayyukansa. 23 Amma lokacin da yakai shekara arba'in, sai ya yi niyyar ya ziyarci 'yan'uwansa, Isra'ilawa. 24 Sai ya ga wani na cin zalin Ba Isra'ile, Musa kuwa ya taimaki wanda ake kwara ta wurin murkushe Bamasaren: 25 zaton Musa 'yan'uwansa za su fahimci taimakon Allah ne ya zo masu amma ina! Basu gane ba. 26 Washegari ya ga wasu Isra'ilawa na fada da junansu; ya yi kokari ya raba su; sai ya ce masu, 'Malamai, ku 'yan'uwan juna ne; don me kuke fada da junanku?' 27 Amma shi wanda ake kwarar makwabcinsa ya ture Musa a gefe guda, ya ce, 'Wa ya nada ka shugaba ko alkali akanmu? 28 Kana so ka kashe ni ne, kamar yadda ka kashe Bamasaren nan jiya?' 29 Da jin haka sai Musa ya gudu, zuwa kasar Midinawa, a matsayin dan gudun hijira. Anan ya haifi "ya'ya biyu maza. 30 Bayan da shekaru arba'in suka wuce, sai mala'ika ya bayyana gare shi a jeji, kusa da dutsen Sinai, a cikin harshen wuta a cikin jeji. 31 Sa'adda Musa ya ga wutar, mamaki ya kama shi; sai ya maso kusa don ya kara dubawa, sai ya ji muryar Ubangiji na cewa, 32 'Nine Allah na ubanninka, Ibrahim, da na Ishaku, da na Yakubu.' Musa ya razana har ma bai sake daga kai ya duba ba. 33 Ubangiji ya ce masa, 'Tube takalminka, domin in da kake tsaye wuri mai tsarki ne. 34 Ba shakka na ga wahalar da mutane na ke sha a Masar, kuma na ji nishinsu, don haka na zo in cece su, yanzu fa sai ka zo, in aike ka zuwa Masar.' 35 Wannan fa shine Musan da suka ki, harma da cewa, 'Wanene ya nada ka alkali ko shugaba a kanmu?' Shine kuma wanda Allah ya aiko masu a matsayin shugaba da kuma mai ceto. Allah ya aiko shi ta hannun mala'ikan da ya gani a daji. 36 Bayan alamu da al'ajibai iri-iri a Masar da kuma Baharmaliya, Musa ya fito da su daga Masar da kuma cikin jeji, a lokacin da suka yi tafiya shekara arbain. 37 Wannan shine Musan da ya cewa Isra'ilawa, 'Ubangiji zai tayar maku da wani annabi kamar ni daga cikin Yan'uwan ku.' 38 Wannan shine mutumin da ke tare da mutane a jeji. Karkashin jagorancin mala'ikan da ya yi magana da shi a dutsen Sinai. Wannan ne mutumin da ke tare da ubannen mu, wannan shi ne mutumin da ya ba mu maganar Allah mai rai. 39 Wannan shine mutumin da ubannenmu suka ki su yi masa biyayya; su ka fitar da shi daga cikinsu, suka kudurta a zuciyarsu za su koma masar. 40 A lokacin ne suka cewa Haruna, 'ya yi masu allolin da za su jagorance su zuwa masar. Domin kuwa ga zancen Musan nan da ya fito da mu daga Masar, ba mu san abin da ya faru da shi ba.' 41 Sai suka kera dan maraki suka kawo wa gunkin hadaya, suka yi murna da abin da hannayensu suka kera. 42 Allah ya bashe su su bauta wa tauraran sama, kamar yadda yake a rubuce cikin littattafafan annabawa, 'Kun mika mani hadayu na yankakkun dabbobi a jeji ne a shekaru arba'in din nan ya ku Isra'ilawa?' 43 Kun yarda da haikalin Molek da kuma tauraron allahn nan Rafem, da kuma siffofin nan da kuka kera don ku yi masu sujada; don haka zan kai ku bauta har gaba da Babila.' 44 Kakkaninmu suna da alfarwa ta sujada domin shaida a cikin jeji, kamar yadda Allah ya umarta yayin da ya yi magana da Musa, cewa ya yi shi bisa ga salon da aka nuna mashi. 45 Wannan shine Alfarwar da kakkaninmu suka zo da shi, a lokacin Joshuwa. Wannan ya faru ne yayin da suka mallaki wannan kasa ta al'ummai da Allah ya kora a gaban kakkaninmu. Haka abin yake har ya zuwa zamanin Dauda, 46 wanda ya sami tagomashi a wurin Allah; don ya gina masujada domin Allah na Yakubu. 47 Amma Sulaimanu ne ya gina Gidan Allah. 48 Sai dai Madaukaki ba yakan zauna a gidan da hannaye suka gina ba, kamar yadda annabin ya ce, 49 'Sama kursiyina ce, duniya kuwa wurin ajjiye sawayena ne. To wane irin gida za ku gina mani? inji Ubangiji: ko kuwa ina ne wurin da zan huta? 50 Ko ba hannayena ne suka yi dukan wadannan ba?' 51 Ku mutane masu taurin kai masu zuciya mara kaciya da kunnuwa marasa ji, kullum kuna gaba da Ruhu Mai Tsarki, kuna aikata abin da kakkaninku suka aikata. 52 Wane annabi ne kakkaninku ba su tsanantawa ba? Sun kashe annabawan da suka rigayi zuwan Mai Adalcin nan, kuma kun zama wadanda suka kasance masu bashe shi da masu kashe shi, 53 kune mutanen da kuka karbi shari'a wadda mala'iku suka bayar, amma ba ku kiyaye ta ba". 54 Yayin da majalisar suka ji wannan, sai ransu ya baci kwarai, har suna cizon hakoransu don gaba da Istifanus. 55 Amma shi, cike da Ruhu Mai Tsarki, sai ya daga idonsa sama, ya ga daukakar Allah; ya kuma hango Yesu na tsaye a hannun daman Allah. 56 Istifanus ya ce, "Duba, ina ganin sama ta bude, ga Dan Mutum na tsaye a hannun dama na Allah." 57 Amma yan majalisar suka daga murya da karfi, suka yi ihu, suka kuma toshe kunnuwansu, gaba dayansu suka afka masa; 58 suka fitar da shi bayan gari, suka jejjefe shi da duwatsu, don shaida sai suka tube manyan rigunansu suka ajiye a gaban wani matashi da ake ce da shi Shawulu. 59 Lokacin da suke kan jifan Istifanus, ya dinga kira yana cewa, "Ya Ubangiji Yesu, ka karbi ruhu na." 60 Ya durkusa ya daga murya da karfi, ya ce, "Ya Ubangiji, kada ka rike wannan zunubi a kansu." Yayin da ya fadi wannan, sai ya yi barci.
Bangaren labarin Istifanus da aka fara a [6:8] ya cigaba. Istifanus ya fara amsa wa babban firist da majalisar sa ta wurin magana game da abubuwan da suka faru a tarihin Isra'ila. Yawancin wannan tarihin ya fito ne daga rubuce-rubucen Musa.
Kalmar nan "na mu" ya haɗa da Istifanus, majalisar Yahudawa wadda yake wa magana, da kuma masu sauraro duka. Kalmar nan "ka" wa mutum ɗaya ne kuma yana nufin Ibarahim ne.
Istifanus matukar ba wa majalisar girma ne ta wurin gaishe su a matsayin 'yan'uwa gaba ɗaya.
"Bai ba da shi ba ko kaɗan"
Wannan na iya nufin 1) wurin da zai ishe shi tsayawa ko kuma 2) wurin da zai ishe shi ya taka. AT: "wata matuƙar kankanin filin"
"domin Ibrahim ya mallaka ya ba wa zuriyarsa"
Zai zama da taimako a ce wannan ya faru kamun wannan maganar a aya da ke baya. AT: "Daga baya Allah ya ce wa Ibrahim"
"shekaru 400"
"al'umma" na nufin mutanen da ke kasar. AT: "Zan hukunta mutanen kasar"
"wannan al'umma da za su wa bauta"
Yahaduwa za su fahimci cewa wannan alkawalin zai bukaci Ibrahim ya yi wa duk mazajen iyalinsa kaciya. AT: "Ya yi alkawali da Ibrahim ya yi wa 'ya'yan iyalinsa maza kaciya"
Labarin ya komo kan zuriyan Ibrahim.
Yakubu ya zama mahaifin." Istifanus ya takaita haka.
"manyan 'ya'yan Yakubu" ko kuma "yayun Yusufu"
Yahudawan sun san cewa kakanin su, sun sayar da Yusufu zuwa bauta a Masar. AT: "suka sayar da shi zuwa Masar a matsayin bawa"
Wannan wata karin magana ne da ke nufin taimakon mutum. AT: ya taimake shi"
Wannan na nufin dukan mutanen kasar Masar. AT: "dukan mutanen kasar Masar"
Wannan na nufin dukiyansa. AT: "komai da yake da shi"
"ƙarancin abinci ta zo." Kasa ta daina ba da abinci.
Wannan na nufin Yakubu da 'ya'yansa, kakkanin mutanen Yahudawa duka.
Hatsi ne abincin kowa a wancan loƙacin.
Duka jimla biyun na nufin 'ya'uwansa Yusufu manya.
"da suka ƙara tafiya kuma"
Yusufu ya bayyana kansa ga 'yan'uwansa a matsayin ɗan'uwansu.
AT: "ya sani da cewa su 'yan iyalin Yusufu ne"
"ya aiki 'yan'uwansa su koma kan'ana" ko kuma "ya aiko su gida"
...
"Yakubu da 'yan'uwansa da suka zama kakkaninmu a yau"
AT: "Zuriyar Yakubu sun ɗauko jikin Yakubu da na 'ya'yansa zuwa ... suka binne sa"
"da kuɗi"
A wasu harsuna, yana iya zama da amfani a ce mutanen sun karu a yauwa kamar ace alkawarin ya zo.
Loƙacin da Allah zai cika alkawalin sa wa Allah ya yi kusa.
"wani saiki ya fara mulki"
"Yufufu" na nufin halin Yusufu. AT: "wanda ba san yadda Yusufu ya taimake Masar ba"
Haka ne labarin Musa ya shigo cikin wannan labarin.
Wannan karin magana ne da ke nuna cewa Musa kyakkyawa ne sasai.
AT: "iyayensa suka yi renon sa" ko kuma "iyayensa sun kula da shi"
An jefar da Musa saboda umarnin da Fir'auna ya bayar. AT: "Yayin da iyayensa suka jefar" ko kuma "Da iyayensa suka yar da shi"
Ta mashi dukan abinda uwa na kwarai ke iya yi wa ɗan cikinta. Yi amfani da ainihin kalmar harshen ku da kuke mora ku bayyana abinda uwa ke yi domin ta tabbatar cewa ɗan ta ya yi girma da ƙyau sosai.
AT: "Masarawan suka ilimintar da Musa"
An kara nanata wannan ne don a nuna cewa musa ya horu a makarantu mafi kyau da ke Masar.
"inganci cikin magana da ayyukansa" ko kuma "ya zama da rinjayaa cikin abinda yake faɗi da aikatawa"
Wannan jimlar "ya yi niyyar" na nufin ya kudura a zuciyar sa. AT: "ya zo tunaninsa"
Wannan na nufin mutanensa, ba ma iyalin kawai ba. AT: "ya ga yadda mutanensa, 'ya'yan Isra'ila suke"
AT: Da ya ga Bamasaran na cin mutuncin Ba Isra'ile, Musa ya taimaki Ba Isra'ile ta wurin murkushe Bamasaran da ke sananta wa"
Musa ya bugi Bamasaran da ƙarfi har ya kashe shi.
"ya yi tunanin"
AT: "na taimakon su ta wurin abinda Musa ya yi" ko kuma "na amfani da abinda musa ke yi ya yantad da su"
Yakamata masu sauraron sun sani daga tarihin da ke Fitowa cewa mutane biyu ne amma Istifanus bai saka shi haka ba.
"sa su daina faɗa"
Musa ya magana ne da Isra'ilawan da ke faɗa.
Musa ya yi wannan tambayan ne don ya ƙarfafa su su daina faɗa. AT: "ku daina faɗa da juna!"
Mutumin ya yi amfani ne da wannan tambayan ya tsauta wa Musa. AT: "ba ka da iko a kan mu!"
Mutumin ya yi amfani ne da wannan tambayan ya yi wa Musa ƙashedin cewa shi maiyuwa da wasu sun san cewa Musa ya ƙashe wani Bamasaren.
Wannan na ba da tabbacin cewa Musa ya fahimci cewa Isra'ilawan sun sa da cewa ya ƙashe wani Bamasaren kwana ɗaya kamun [7:28]
"Bayan da shekaru arbain suka wuce." Wannan shi ne yawan kwanakin da Musa ya yi a Midina. AT: "shekaru arbain bayan da Musa ya gudu daga Masar"
Masu sauraron Istifannus sun san da cewa Allah ya yi magana ta wurin mala'ika.
Musa ya sha mamakin cewa jejin ba ta kone wa da wuta, Dama masu sauraron Istifanus sun san da wannan. AT: "domin jejin ba ta kone wa ba"
Wannan na nufin cewa dama musa ya maso kusa ne ya bincika, amma sai ya komo baya don tsoron da ya ji muryar.
"Nine Allahn da kakkaninku sauka yi wa sujada"
Musa ya firgita don tsoro. AT: "Musa ya razana da tsoro"
Allah ya gaya wa Musa wannan ne don ya girmama Allah"
Wannan na nuna wurin da Allah yake kasancewa, Ana ɗaukan dai dai yankin da Allah yake yã zama ko kuma yã zama da tsarki.
"na ga da tabbaci." Ba shakka na kara nanata ganin.
Kalmar nan "na" na nanata cewa waɗannan mutanen sun zama na Allah. AT: "zuriyar Ibrahim, Ishaku, da Yakubu"
"da kaina zan yantad da su"
"ka shirya." Allah ya ba da umurni ne anan.
Wannan na mayar da mu zuwa ga abubuwan da suka aiku da aka rubuta a [7:27-28]
Sun yi amfani ne da wannan tambayan su tsauta wa Musa. Duba yadda kuka fasara wannan tambayan gangancin a [7:27]. AT: "Ba ka da iko a kan mu!"
...
Hannun na nufin abinda mutum ya yi. A wannan zancen, Mala'ikan ya umuci Musa ya koma kasar Masar. Istififanus na magana kamar mala'ikan na da hannu ne da za a iya gani. Kuna iya buƙaci ko kara bayyana abinda mala'ikan ya yi. AT: "ta wurin abinda mala'ikan ya yi" ko kuma "ta wurin samun mala'ikan ... daji umurce shi ya koma Masar"
Masu sauraron Istifanus sun san game da shekaru arbain da Isra'ilawa suka yi a cikin jeji. AT: loƙacin ... shekara arbain da mutanen Isra'ila suka rayu a cikin jeji"
"sa wani ia zama annabi"
"daga cikin mutanenku"
Musa ne wannan mutumin da ke tare da Isra'ilawa"
Jimlar nan "wannan shine mutumin" a wannan nassin na nufin Musa.
Allah ne ya bayar da maganan. AT: "wannan shi ne mutumin da Allah ya bashi maganar rai ya ba mu"
Wannan na iya nufin 1) "sakon da ke jurewa" ko kuma 2) "maganar da ke ba da rai"
Wannan na nufin kiyayyan da suka yi wa Musa. AT: "suka ki shi a matsayin shugaban su"
Anan "zuciya" na nufin tunanin mutane. Ayi abu a zuciya na nufin a yi marmarin aikata abin.AT: "suka yi marmari su koma"
"Da suka yi marmari su koma Masar"
Masu sauraron Istifanus sun san cewa ɗan marakin da suka ƙera gunki ne. AT: "suka ƙera wata gunki a sifar ɗan maraki"
Waɗannan su jimlar na wannan gunkin ɗan marafin ne.
"Allah ya juya musu baya." Wannan matakin na nuna cewa Allah bai ji daɗin mutanen ba kuma bai cigaba da taimakon su ba. AT: "Allah ya daina gyara su"
"ya yi watsi da su"
Daga ainihin jimlar, wannan na iya nufin 1) tauraran kawai ko kuma 2) rana, wata, da tauraro
Wannan ba shakka na nufin tarin rubuce-rubuce da dama na annabawan Tsohon Alkawali da aka haɗa a gungura ɗaya. Wannan na iya ma haɗe da rubuce-rubucen Amo.
Allah ya yi wannan tambayan ne don ya nuna masu cewa basu yi masa sujada ta wurin haɗayun su ba. AT: "ba ku ko daraja ni ba sa'an da kuke miko yankakkun dabbobi da haɗayu ... Isra'ilawa"
Wannan na nufin kasar Isra'ila gabaki ɗaya. AT: "dukanku Isra'ilawa"
Wannan na nufin cewa sun ɗauki gumakai da suna tafiya a cikin jeji. AT: "kun ɗauke su da ku zuwa wurare"
gidan bukkan da wani allah mai suna molek ke zama
tauraron da an fi gane ta da wani allah mai suna Rafem
Sun ƙera gumakai da sifofi alloli Molek da Rafem don su yi masu sujada.
"zan cire ku zuwa wurare har ma gaba da Babila." Wannan zai zama shari'ar Allah.
Wata bukka da sanduki (akwati) ke zama a ciki tare da dokoki goma (10) da aka ƙera a kan dutse a cikin ta.
jimlar nan "a loƙacin Joshuwa" na nufin cewa kakkaninsu sun yi waɗannan abubuwan bisa ga bishewar Joshuwa. AT: "kakkaninmu, bisa ga umarni daga Joshua sun karbi wannan alfarwa suka zo da shi"
Wannan jimlan na nuna dalilin da ya sa kakanin su iya kwace kasar ya zama na su. AT: "Allah ya tilasta al'umman su bar kasar a gaban kakkaninmu"
Wannan na iya nufin 1) "Yayin da kakkaninmu na kallo, Allah ya kwaci kasar daga al'ummai ya kuma kore su" 2) "Da kakkanin mu suka zo, sai Allah ya kwaci kasar daga al'ummai ya kuma kore su"
Wannan na nufin mutanen da ke zama a kasan kamun Isra'ila. AT" "mutanen da ke zaune dã a wurin"
"ya tilasata su su bar kasar"
"gidan domin sanduki wurin da Allahn Yakubu zai iya zama" Dauda ya buƙaci wurin zama na dindindim domin sandukin ya zauna a Urushalima, ba a buƙa ba.
Hannaye na nufin mutane. AT: "da mutane suka gina"
Shi annabin yana kwatanta girman darajar kasancewar Allah ne da yadda ba shi yiwuwa mutum ya gina wa Allah wurin da zai huta a duniya tun da shike duniyan gaba ɗaya wurin ajiye sawun sa ne kawai.
Allah ya yi wannan tambayan ne domin ya nuna cewa aikin banza ne kokarin mutum ya kula da Allah. AT: "Ba za ku iya gina mani gida daidai yadda zai ishe ni ba!"
Allah ya yi wannan tambayan ne don ya nuna cewa mutum ba zai iya tanada wa Allah wurin hutu ba. AT: "Babu wani wurin hutu da ya mani kyau!"
Allah ya yi wannan tambayan ne don ya nuna cewa mutum bai halice kome ba. AT: "Hannayena ne suka yi dukan kome!"
Istifanus ya daina haɗa kai da malamen Yahudawan ya koma sauta musu.
Wannan baya nufin cewa kawunansu na da tauri ba, amma yana nufin cewa su "basu ji."
Yahudawa na ɗaukan marasa kaciya a matsayin marasa yi wa Allah biyayya. Istifanus yana amfani ne da marasa kaciya da kunnuwa marasa ji" a maɗɗaɗin malaman Yahudawa da suke yi kamar al'ummai suke yi loƙacin da basu biyayya da Allah. AT: "kun ki ku yi biyayya ku kuma ji"
Wannan na nufin Almasihu, shafeffen.
Istifanus yana wannan tambayan ne don ya nuna musu cewa basu koya kome daga kuskuren kakkaninsu ba. AT: "Kakkaninsu sun tsanantawa kowane annabi!"
"ku ma kun bashe shi kun kuma kashe shi"
"masu ƙashe Mai Adalcin" ko kuma "masu ƙashe Almasihu"
"shari'un da Allah ya sa mala'iku su bawa kakkaninku
Labarin ya juya anan; hadisin ya zo ga ƙarshe anan, sai majalisar suka ɗauki mataki.
"ransu ya baci" na nufin suka yi fushi kwarai da gaskiya. AT: "sai suka yi fushi kwarai da gaskiya" ko kuma "sa suka yi fushi sosai"
Wannan matakin na nuna matukar bakin cikinsu da Istifanus ko kuma matukar kiyayyar su da Istifanus. AT: "suka yi fushi ƙwarai da gaskiya har ya kai su ga cizon hakora" ko kuma "suka motsa hakoransu yayin da suke kallon Istifanus"
"ya zuba idon sa sama." Yana yi kamar Istifanus ne kaɗai ya ga wannan wahayin banda suran jama'ar da ke taron.
Mutane sukan ga ɗaukakar Allah a matsayin hasken wuta. AT: "ya ga wata hasken wutar Allah"
A tsaya a "hannun damar Allah" alama ce na samun daukaka da ikon Allah. AT: "sai ya hango Yesu a wurin ɗaukaka da iko a gefen Allah" Dubi:
Istifanus na nufin Yesu kenan.
"suka sa hannayensu bisa kunuwansu." Sun yi haka ne domin su nuna cewa basu so su ji abin da Istifanus yake faɗi.
"suka kãmo shi suka jawo shi da ƙarfi bayan gari"
Waɗannan manyan tufafi ne da ake sako wa domin tare sanyi. Suna kamar su suweita ne ko kwot.
Sun ajiye su a wurin domin Shawulu ya rika duba su.
Shawulu yana irinsu shekaru 30 ne a lokacin.
"ga ruhu na." Zai zama da taimako idan aka nuna cewa wannan roƙo ne. AT: "ina roƙo, ka karbi ruhu na"
Wannan alamar biyayya ne ga Allah
Ana iya sanar da wannan a tabbacecciyar sifa. AT: "ka gafarta masu wannan zunubin"
Yin barci anan na nufin mutuwa. AT: "mutu"
Istafanas ya fara tarihin sa ta magana akan alkawuran Allah ma Ibrahim.
Allah ya yi alkawarin kasar zuwa ga Ibrahim da zuriyar sa.
Alkawarin Allah ya yi kamar ba zai yiwu ba ya cika domin Ibrahim ba shi da yara.
Allah ya ce zuriyar Ibrahim zasu zama bayi a kasashen waje ma shekaru dari hudu.
Allah ya ba wa Ibrahim alkawarin kaciya.
'Yan'uwan sa suna kishin sa sun kuma sayar da shi cikin Masar.
Allah ya ba ma Yusufu yarda da kuma hikima a gaban Fir'auna
Yakubu ya aike 'ya'yan sa zuwa Masar domin ya gi akwai hatsi a wurin.
Yusufu ya aika yan'uwan sa su gaya ma Yakubu ya zo Masar.
Lambar Isra'ilawa a Masar ya yi girma ya kuma yawaita.
Sabon sarkin Masar ya tilasta Isra'ilawa su jefa da jarirain su don kadda su rayu.
'Yar Fir'auna ta dauki Musa ta kuma tayar da shi kamar dan ta.
Musa ya sami karantar a dukan ilimi Masarawa.
Musa ya kare dan Isra'ila ya kuma buga dan Masarawa.
Musa ya gudu zuwa Madayana.
Musa ya gan mala'ika a cikin harshen wuta a cikin jeji.
Ubangiji ya umurce Musa ya je Masar, domin Allah zai je ya ceta Isra'ilawa.
Musa ya bi da Isra'ilawa a cikin jeji har shekaru arba'in.
Musa ya annabce ma Isra'ilawa cewa Allah zai ta da annabawa kamar sa daga tsakanin 'yan'uwan su.
Isra'ilawan sun yi maraki sun kuma yi hadaya wa gumkin.
Allah ya juya wa Isra'ilawa baya ya kuma mika su ga rundunar sama.
Allah ya ce zai kai Isra'ilawa Babila.
A cikin jejin, Isra'lawan sun gina alfarwar shaidar.
Allah ya kore al'ummain gaba da Isra'ilawan.
Dauda ya tambaya ya gina wurin mazauni wa Allah.
Suleiman ya gina wa Allah gida.
Ma Daukaki na da sama kamar kursiyin sa.
Istafanas ya la'anta mutanen ma tsayayya da Ruhu Mai Tsarki.
Istafanas ya ce mutanen sun ci amanarsa sun kuma kashe Mai Adalcin.
Membobin majalisan suka husata ƙwarai da gaske kuma suka ciji baki don haushin Istafanas
Istafanas ya ce ya gan Yesu tsaye a hanun dama na Yesu.
Membobin majalisan sun aukar masa, sun fitar da shi a bayan gari, suka kuma jefe sa.
Shaidun sun ajiye tufafin wajen su a ƙafan wane saurayi mai suna Shawulu.
Istafanas ya tambaye Allah kada ya ɗora ma mutanen wannan zunubi.
1 Bulus ya amince da mutuwarsa. A wannan rana tsanani mai zafi ya fara tasowa akan Iklisiya da take a Urushalima, sai masu bangaskiya duka suka bazu ko ina a cikin garuruwan Yahudiya da Samariya, sai manzannin kadai aka bari. 2 Amintattun mutane suka bizne Istifanus suka yi babban makoki game da shi. 3 Amma Shawulu ya yi wa Iklisiya mugunta kwarai, ya dinga shiga gida gida yana jawo mutane maza da mata, kuma yana kulle su cikin kurkuku. 4 Duk da haka masu bangaskiyar nan da suka warwatsu suka tafi suka dinga yada wa'azin maganar. 5 Filibus ya tafi can Samariya ya yi shelar Almasihu. 6 Da taron mutane suka ji kuma suka ga alamun da Filibus yake yi, sai suka mai da hankali dukansu domin su ji abinda yake fadi. 7 Domin kazaman ruhohi sun fito daga cikin mutane da yawa da suka saurare shi suna kuka da kururuwa; nakasassun mutane dayawa da guragu suka warke. 8 Kuma aka yi farin ciki mai girma a birnin. 9 Amma akwai wani mutum a cikin birnin da ake kira Siman, wanda tun farko shi masafi ne da kuma dan dabo, yana yi wa mutanen Samariya abubuwan ban mamaki, yayin da yake kiran kansa wani mai muhimmanci. 10 Dukan Samariyawa, manya da yara, suna sauraronsa, su kan ce, "Wannan mutum shine ikon Allahn nan wanda ake kira mai girma." 11 Suna sauraron sa, domin ya dade yana yi masu abubuwan mamaki da tsafe-tsafensa. 12 Amma da suka yi bangaskiya da wa'azin bisharar da Filibus yake yi game da mulkin Allah da sunan Yesu Almasihu, sai aka yi masu Baftisma dukansu maza da mata. 13 Har shima Siman da kansa ya ba da gaskiya. Bayan an yi masa Baftisma ya cigaba da bin Filibus, da ya ga ana nuna alamu da manyan ayyuka, sai ya yi mamaki. 14 Da manzannin da ke Urushalima suka ji labarin Samariya ta karbi maganar Allah, sai suka aika masu Bitrus da Yahaya. 15 Da suka iso, suka yi masu addu'a, domin su karbi Ruhu Mai Tsarki. 16 Domin har wannan lokaci, Ruhu Mai Tsarki bai sauko kan kowannensu ba; an dai yi masu baftisma ne kadai cikin sunan Ubangiji Yesu. 17 Sai Bitrus da Yahaya suka dora masu hannuwansu, sai suka karbi Ruhu Mai Tsarki. 18 Sa'adda Siman yaga ana bayar da Ruhu Mai Tsarki ta wurin dorawar hannuwan manzanni, ya basu kudi. 19 Ya ce, "Ku bani wannan iko, ni ma, don duk wanda na dora wa hannu ya karbi Ruhu Mai Tsarki." 20 Amma Bitrus yace masa, "Azurfarka ta lalace tare da kai, saboda kana tunanin za ka malaki baiwar Ubangiji da kudi. 21 Baka da wani rabo a wannan al'amari, domin zuciyarka ba daidai take da Allah ba. 22 Saboda haka ka tuba daga wannan muguntarka, ka kuma yi addu'a ga Ubangiji, domin mai yiwuwa ya gafarta maka game da manufar zuciyarka. 23 Domin na gane kana cikin bacin rai da kuma cikin daurin zunubi." 24 Siman ya amsa ya ce, "Kayi addu'a ga Ubangiji domina, kada wani daga cikin abubuwan nan da ka fada ya faru da ni." 25 Sa'anda Bitrus da Yahaya suka bada shaida kuma suka fadi maganar Ubangiji, sun koma Urushalima; akan hanya, suka yi wa'azin bishara a kauyukan samariyawa da yawa. 26 Yanzu kuwa Mala'ikan Ubangiji ya yi wa Filibus magana cewa, "Tashi ka tafi ta kudu da hanyar da ta yi kasa daga Urushalima zuwa Gaza" (wannan hanyar yana cikin hamada.) 27 Ya kuwa tashi ya tafi. Sai ga wani mutum daga Habasha, baba ne mai babban matsayi a karkashin Kandakatu, sarauniyar Habasha. Shine yake mulkin dukan dukiyarta. Ya zo Urushalima domin ya yi ibada. 28 Yana komawa zaune cikin karussarsa, kuma yana karanta Littafin annabi Ishaya. 29 Ruhun ya ce wa Filibus, "Ka je kusa da karussar nan." 30 Sai Filibus ya gudu ya same shi, kuma ya ji shi yana karanta littafin annabi Ishaya, sai ya ce, "Ka fahimci abin da kake karantawa?" 31 Bahabashen ya ce. "Yaya zan iya, idan ba wani ya bishe ni ba?" Ya roki Filibus ya shigo cikin karussar ya zauna tare da shi. 32 Wannan kuwa shine nassin da Bahabashen yake karantawa, "An kai shi kamar tunkiya zuwa mayanka; shiru kuma, kamar dan rago a hannun masu sosayarsa, bai bude baki ba. 33 Cikin kaskancinsa aka yi masa shari'a da rashin adalci: Wa zai bada tarihin tsararsa? Domin an dauke ransa daga duniya." 34 Sai baban ya tambayi Filibus, ya ce, "Na roke ka, gaya mani, game da wa annabin yake magana? Da kansa, ko kuwa wani mutum dabam?" 35 Filibus ya fara magana; akan littafin Ishaya, ya kuwa yi masa wa'azi akan Yesu. 36 Yayin da suke tafiya akan hanya, sai suka iso bakin wani kogi; Baban ya ce, "Duba, ga ruwa anan; me zai hana ayi mani baftisma?" 37 Filibus ya ce," Idan ka gaskanta da zuciya daya, ana iya yi maka baftisma." Sai Bahabashen ya ce, "Na gaskata Yesu Almasihu shine Dan Allah." 38 Sai Bahabashen ya umarta a tsai da karussar. Sai suka zo wurin ruwa dukan su biyu, Filibus da baban, Filibus kuwa yayi masa baftisma. 39 Yayin da suka fito daga cikin ruwan, Ruhun Ubangiji ya dauke Filibus; baban bai sake ganin shi ba, sai ya ci gaba da tafiyar sa yana murna. 40 Amma Filibus ya bayyana a Azotus. Ya ratsa wannan yankin yana wa'azin bishara a dukan garuruwan, har sa'anda ya iso Kaisariya.
Labarin ya maso daga kan Istifanus zawa Bulus a waɗannan ayoyi.
Yana iya zama da taimako wa masu sauraro a masar da bangaren labarin Istifanus gaba ɗaya kamar yadda UDB ta yi
Wannan bangaren aya 1 na ba da bayyanin tsanantawa da ya taso bayan rasuwan Istifanus. Wannan ya bayyana dalilin da ya sa Bulus yana tsananta wa masu bi a aya 3.
Wannan na nufin ranar da Istifanus ya rasu. (Dubi: [7:59-60]
Kalmar na "duka" na nufin cewa masubi da yawa suka bar Urushalima saboda tsanantawa.
Wannan na nufin cewa manzannin ne suka rege a Urusalima ko da yake su ma sun ɗandana matukar tsanantawa.
"Mutane masu tsoron Allah" ko kuma "Mutanen da ke da tsoron Allah"
suka yi babban makokin mutuwarsa"
Bulus ya ɗauki masubi Yahudawa da ƙarfi daga gidajen su ya jefa su a kurkuku.
"gidaje ɗaya bayan ɗaya"
Wannan na nufin maza da mata da suka gaskata da Yesu.
Dalilin warwatsuwan nan fa tsanantawa ne kamar yadda aka ambata a baya. AT: "wadda suka gudu wa babban tsanantawar, suka kuma tafi"
"maganar" anan na nufin "sakon." AT: suka dinga wa'azin sakon Allah"
...Wannan karin magana ''tafi can'' an yi amfani da shi anan don samariya na kasa da isra'ila.
Wannan na iya nufin 1) Luka ya sammanin cewa masu karatunsa za su san birnin da yake rubutu a kai. AT: "babbar garin birnin Samariya" ko kuma 2) Luka bai zaci masu karatunsa su san wace gari ne yake rubutu a kai ba. AT: "wata birni a Samariya"
Laƙabin nan "Almasihu" na nufin Yesu. AT: "faɗi musu cewa Yesu shi ne Almasihu"
"Da mutane masu yawa a birnin Samariya." An kayyade wurin a baya. (Dubi: [8:5]
Sun mai da hankalinsu ne saboda dukan warkaswan da Filibus yayi.
"waɗanda ke da su" ko kuma "waɗanda kazaman ruhohi ke mulki da su"
Jimlar nan "wannan birnin" na nufin mutanen da ke murna. AT: "Kuma mutanen birnin suna murna"
Haka ake gabatar da sabun mutum zuwa cikin labarin. Harshen ku na iya moran wasu kalamu daban don gabatar da sabuwar mutum zuwa cikin labarin.
"birnin Samariya" (Dubi: [8:5])
Kalmar nan "duka" na nufin masu yawa. AT: "Samariyawa ma su yawa" ko kuma "Samariyawan da ke birnin"
Waɗannan jimla da nufin mutane daga kowane bangare. AT: "komen muhimmancinsu"
Mutane suna cewa Siman ne wannan ikon Allahn da ake ce da shi "Iko Mai girma."
Wannan na iya nufin 1) Wakilin Allah mai iko ko kuma 2) Allah ko kuma 3) mutum mafi iko 4) malaika. Da shike ba bayyana kamar a fili ba, ya fi a fasara ta da "ikon Allah mai girma"
AT: "Filibus ya masu baftisma" ko kuma "Filibus ya yi wa sabobbin tuban baftisma"
An yi amfani ne da wannan kalmar "da kansa" don a nanata cewa Siman ya ba da gaskiya. AT: "Siman ma yana cikin waɗanda suka ba da gaskiya"
AT: "Filibus ya yi wa Siman baftisma"
Ana iya faɗin wannan a wata sabuwan jimla. AT: "Da ya ga"
Wannan na fara wata sabuwan bangaren labarin yadda Samariyawa suka fara zama masubi.
Wannan na nufin mutane masu yawa, da sun zama masubi a yankin Samariya.
"suka ba da gaskiya" ko kuma "suka yarda"
"da Bitrus da Yahaya suka isa"
...
"Bitrus da Yahaya suka yi wa masubi Samariyawa addu'a"
"domin masubi Samariyawa su karɓi Ruhu Mai Tsarki"
AT: Filibus ya dai yi wa Masubi Samariyawa baftisma ne kadai"
A nan "suna" na nufin iko, kuma yin baftisma a cikin sunan nan na a madaddin baftisma domin kasancewa a karkashin ikonsa. AT: "an dai yi masu baftisma ne kadai domin su zama almajiran Yesu"
"su" anan na nufin mutanen Samariya da suka gaskata da sakon bisharan da Istifanus ya yi.
Wannan alama ce da ke nuna cewa Bitrus da Yahaya suna so Allah ya ba wa masubi Ruhu Mai Tsarki.
AT: "manzannin suka ba su Ruhu Mai Tsarkin ta wurin dorawar hannuwan manzanni"
"don in ba da Ruhu Mai Tsarki ga duk wanda na dora wa hannu"
"bari kai da kuɗinka ku hallaka"
Wannan na nufin iya ba da Ruhu Mai Tsarki ta wurin ɗora hannaye a kan mutane.
AT: "ba za ka iya haɗa hannu a wannan aikin ba"
A nan "zuciya" na nufin tunani ko manufofin. AT: "manufofinka ba daidai suke ba"
A nan "zuciya" na nufin tunanin mutum. AT: "domin abinda ka yi niyar yi" ko kuma "domin abinda kake tunanin yi"
"waɗannan mugayen tunani"
"ma yiwuwa yana shirye ya gafarta"
A nan "cikin bacin rai" na nufin matukar kishi. AT: "matukar kishi"
Ana maganar "ɗurin zunubi" kamar zunubi na iya hana Siman ya kuma ɗaure shi. Yana nufin cewa Siman ba zai iya daina yin zunubi da kansa ba. AT: "domin kã cigaba da zunubi kamar wadda ke ɗaure" ko kuma "kana kamar ɗaurere ne ga zunubi"
AT: "abubuwan da ka faɗa ... kada su faru da ni"
Bitrus da Yahaya sun faɗi abinda suka sani da kansu game da Yesu wa Samariyawan.
"magana" anan na nufin "sako." Bitrus da Yahaya sun ba da bayanin Yesu wa Samariyawa.
A nan "kauyuka" na nufin mutanen da ke cikinsu. AT: "zuwa da mutanen da ke cikin kauyukan Samariyawa da yawa" (Dubi:
Wannan ya sa alamar canjin yanayin labarin ne.
Waɗannan kalamun aikin na aiki tare ne domin nanata cewa ya shirya ya fara tafiya mai nesa da zai ɗauki ɗan loƙaci. AT: "Shirya don tafiya"
An yi amfani ne da wannan jimlar "yi ƙasa" domin Urushalima na sama da Gaza.
Masu ilimi sun yarda cewa Luka ya ƙara wannan maganar domin ya bayyana yankin da Filibus zai tafi.
Kalmar nan "sai" na jan hankalinmu zuwa ga wani sabon mutum da ya shigo labarin. Yana iya yiwuwa harshenku tana da wata hanyar yin haka.
Nanacin "bãbã" anan na game da matsayin da mutumin Habasha ke da shi a gwamnati, ba kawai domin yanayin sa na fiɗiya ba.
Wannan wata lakani ne da ake kiran duk sauraniya a Habasha. Yana kamar yadda ake amfani da kalmar Fir'auna wa duk sarki a Masar.
Wannan na nuna cewa shi ba'alummi ne wadda ya gaskata da Allah, ya kuwa zo ya yi wa Allah ibada a haikali. AT: "ya zo ne ya yi wa Allah ibada a haikalin da ke Urushalima"
Mai'yiwuwa "keken doki" za ta fi shiga da wannan yanayin. An fi ambata karusarsa a matsayin abin hawa zuwa yaƙi, ba lallai abin hawa domin tafiya mai nesa ba. Kazalika, mutane na iya tuƙin karusarsa a tsaye.
Wato littafin Ishaya da ke Tsohon Alkawali. AT: "yana karatu daga littafin Ishaya"
Filibus ya gane cewa wannan na mufi ya zai je kusa da mutumin da ke tukin karussarsa. AT: "ka raka mutumin da ke cikin wannan karussarsa"
Wato littafin Ishaya da ke Tsohon Alkawali. AT: "yana karutu daga littafin Ishaya"
Shi Habashan na da basira kuma yana iya karatu, amma ya rasa fahimi na ruhaniya. AT: "Kana fahimtar ma'annan abinda kake karantawa?"
Ana wannan tambayan ne domin a nuna cewa hakika ba zai iya fahimtar abida yake karantawa ba idan ba tare da an taimake shi ba. AT: "ba zan iya fahimtar haka ba sai dai idan wani ya bishe ni"
A nan sammanin cewa Filibus ya yarda ya yi tafiya da shi a hanyan domin ya fassara masa nassosin
Masu soyarsa sune masu aske gashin rago domin a iya amfani da shi.
AT: "Aka wulakãntashi kuma ba masa shari'a da adalci ba" ko kuma "ya bar masu masa zargin sa suka ci mutuncinsa ya kuma sha wahalan rashin adalci"
Ana amfani ne da wannan tambayan domin a nanata cewa babu tsararsa. AT: "Babu wanda zai iya magana akan tsararsa, gama ba za a samu ko ɗaya ba"
Wannan na nufin mutuwarsa. AT: "Mutane ne suka kashe shi" ko kuma "mutane ne suka ɗauki ransa daga duniya"
"Don Allah ka fạɗa mani"
Wannan na nufin rubuce rubucen Ishaya da ke cikin Tsohon Alkawali. AT: "a cikin rubuce rubucen Ishaya"
"ya koya wa baban bisharar Yesu.
"suka cigaba da tafiya a hanya"
Baban ya yi wannan tambaya ne domin Filibus ya bashi damar yin baftisma. AT: "no roke ka bari in yi baftisma"
"ya ce wa ma tukin karussarsa ya tsaya"
"baban bai sake ganin Filibus ba"
Wannan alama ce cewa Filibus na tafiya tsakanin wurin da ya wa Habashan baftisma da Azotus. Filibus ya bi ya ɓace a hanyar Gaza ya sake fitowa a birnin Azotus.
Wannan na nufin yankin da ke kewaye da birnin Azotus.
"a dukan garuruwan da ke wannan yankin"
Shawulu ya yadda da mutuwan Istafanas.
Babbantsanani ya auko wa ikkilisiyar da take Urushalima ta fara a ran da an jefe Istafanas.
Masu bi a Urushalima warwatsa a lardin Yahudiya da Samariya.
Mutanen sun saurara a loƙacin da sun gan alamomin da Filibus ya yi.
Mutanen sun saurara da sun gan sihirin sa.
Saminu ya yi ĩmãni, a ka kuma yi masa baftisma.
Masu bi a Samariya sun samu Ruhu Mai Tsarki.
Saminu ya mika wa manzannin kudi ma musaya ma iko na bayar da Ruhu Mai Tsarki ta ɗora hannu.
Bitrus ya ce Saminu na cikin guba haushi da kuma shaidun zunubi.
Mala'ika ya gaya wa Filibus ya je kudu zuwa hanyar hamada ta Gaza.
Filibus ya hadu da băbă, mai babban matsayi daga Habasha wanda na zama a cikin karusai sa yana karantun littafin Annabi Ishaya.
Filibus ya tambaye mutumin, "Ka gane abin da kana karanta?"
Mutumin ya tambaye Filibus ya zo cikin karusai kuma ya bayana abin da yana karanta.
An ja mutumin kamar tumaki zuwa mayanka, amma bai bude bakin sa ba.
Mutumin ya tambaye Filibus in annabawan na magana akan kansa ko akan wane mutum daban.
Filibus ya bayyana cewa mutumin cikin littafi daga Ishaya Yesu ne.
Filibus da kuma băbă duk sun je cikin ruwa kuma Filibus ya yi masa baftisma.
Da Filibus ya fita daga ruwan, Ruhun Ubangiji ya ɗauki Filibus daga nan.
A loƙacin da băbăn ya fito daga ruwan, ya je hanyan sa da farin ciki.
1 Amma Shawulu, ya cigaba da maganganun tsoratarwa har ma da na kisa ga almajiran Ubangiji, ya tafi wurin babban firist 2 kuma ya roke shi wasiku zuwaga majami'un da ke Dimashku, domin idan ya sami wani da ke na wannan hanya, maza ko mata, ya kawo su Urushalima a daure. 3 Yayin da yana tafiya, ya kasance da ya iso kusa da Dimashku, nan da nan sai ga wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi; 4 Sai ya fadi a kasa kuma yaji wata murya na ce da shi, "Shawulu, Shawulu, me yasa kake tsananta mani?" 5 Shawulu ya amsa, "Wanene kai, Ubangiji?" Ubangiji ya ce, "Nine Yesu wanda kake tsanantawa; 6 amma ka tashi, ka shiga cikin birnin, kuma za a gaya maka abinda lallai ne kayi. 7 Mutanen da ke tafiya tare da Shawulu suka tsaya shiru sun rasa abin fada, suna sauraron muryar, amma ba su ga kowa ba. 8 Shawulu ya tashi daga kasa, kuma daga ya bude idanunsa, baya ganin komai; sai suka kama hannuwansa suka yi masa jagora suka kawo shi cikin birnin Dimashku. 9 Har kwana uku ba ya kallo, kuma ba ya ci balle sha. 10 Akwai wani almajiri a Dimashku mai suna Hananiya; sai Ubangiji ya yi magana da shi cikin wahayi, ya ce, "Hananiya." Sai ya ce, "Duba, gani nan Ubangiji." 11 Ubangiji ya ce masa, "Tashi, ka tafi titin da ake kira Mikakke, kuma a gidan wani mai suna Yahuza ka tambaya mutum daga Tarsus mai suna Shawulu; gama yana addu'a; 12 kuma ya gani cikin wahayi mutum mai suna Hananiya na shigowa kuma ya daura masa hannu, domin idanunsa su bude." 13 Amma Hananiya ya amsa, "Ubangiji, na ji labari daga wurin mutane da yawa game da mutumin nan, da irin muguntar da ya aikata ga tsarkakan mutanenka da ke Urushalima. 14 An bashi izini daga babban firist domin ya kama dukan wanda ke kira bisa sunanka." 15 Amma Ubangiji ya ce masa, "Jeka, gama shi zababben kayan aiki na ne, wanda zai yada sunana ga al'ummai da sarakuna da 'ya'yan Isra'ila; 16 Domin zan nuna masa irin wahalar da zai sha sabo da sunana." 17 Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Ya dora masa hannu a kai, ya ce, "Dan'uwa Shawulu, Ubangiji Yesu, wanda ya bayyana a gareka a hanya sa'adda kake zuwa, ya aiko ni domin ka sami ganin gari ka kuma cika da Ruhu Mai Tsarki." 18 Nan take wani abu kamar bawo ya fado daga idanun Shawulu, kuma ya sami ganin gari; ya tashi aka yi masa baftisma; 19 kuma ya ci abinci sai aka karfafa shi. Ya zauna tare da almajirai a Dimashku kwanaki da yawa. 20 Nan take ya fara shellar Yesu cikin haikali, yana cewa shine dan Allah. 21 Dukan wadanda suka saurare shi suka yi mamaki suka ce "Ba wannan mutumin ne yake hallaka mutanen Urushalima da ke kira bisa ga wannan suna ba? Ya kuma zo nan domin ya ba da su a daure ga manyan firistoci." 22 Amma Shawulu kuwa ya sami iko sosai, kuma yana haddasa damuwa tare da rinjaya tsakanin Yahudawan dake zama a Dimashku ta wurin tabbatar da Yesu shine Almasihu. 23 Bayan kwanaki da yawa, sai Yahudawan suka yi shiri domin su kashe shi. 24 Amma shirin su ya zama sananne ga Shawulu. Suna fakkon sa ta wurin tsaron kofar birnin dare da rana domin su kashe shi. 25 Amma da tsakar dare almajiransa suka daukeshi a kwando, suka zurara shi ta katanga. 26 Sa'adda ya zo Urushalima, Shawulu ya yi niyyar hada kai da almajirai, amma dukansu suna tsoronsa, domin ba su yarda cewa shima ya zama almajiri ba. 27 Amma Barnaba ya dauke shi ya kawo shi wurin manzannin. Ya kuwa gaya musu yadda Shawulu ya sadu da Ubangiji a hanya, har Ubangiji ya yi magana da shi, kuma yadda Shawulu ya yi wa'azi cikin sunan Yesu gabagadi a Dimashku. 28 Ya sadu da su lokacin shigar su da fitar su a Urushalima. Ya yi wa'azi gabagadi cikin sunan Ubangiji Yesu 29 kuma yana muhawara da Yahudawan Helenanci; amma sun ci gaba da kokarin kashe shi. 30 Da 'yan'uwa suka gane haka, sai suka kawo shi Kaisariya, suka kuwa tura shi zuwa Tarsus. 31 Sa'annan iklisiya dake dukan kasar Yahudiya, Galili da kuma Samariya suka sami salama da kuma ginuwa; suka kuwa ci gaba da tafiya cikin tsoron Ubangiji, da kuma ta'aziyar Ruhu Mai Tsarki, iklisiyar kuwa ta karu da yawan mutane. 32 Har ta kai, yayin da Bitrus ya zaga dukan yankin kasar, ya dawo wurin masu bi dake zama a garin Lidda. 33 A can kuwa ya sami wani mutum mai suna Iniyasu, wanda yake shanyayye ne, yana kwance har tsawon shekara takwas a kan gado. 34 Bitrus ya ce masa, "Iniyasu, Yesu Almasihu ya warkar da kai. Tashi ka nade shimfidarka." Nan take sai ya mike. 35 Sai duk mazauna kasar Lidda da kasar Sarona suka ga mutumin, suka kuma juyo ga Ubangiji. 36 Yanzu kuwa a Yafa akwai wata almajira, mai suna Tabita, ma'ana "Dokas." Wannan matar kuwa tana chike da ayyukan nagarta da halin tausayi da take yi ga mabukata. 37 Ya kai ga cewa a kwanakin can ta yi rashin lafiya har ta mutu; da suka wanke gawar ta suka kwantar da ita a bene. 38 Da shike Lidda na kusa da Yafa, almajiran kuma sun ji cewa Bitrus yana can, suka aika mutane biyu wurinsa. Suna rokansa, "Ka zo garemu ba tare da jinkiri ba." 39 Bitrus ya tashi ya tafi da su, da isowar sa, suka kai shi benen. Sai dukan gwamrayen suka tsaya kusa da shi suna kuka, sai suka dauko riguna da sutura da Dokas ta dinka lokacin da take tare da su. 40 Bitrus ya fitar da su duka daga cikin dakin, ya durkusa, ya yi addu'a; sai, ya juya wurin gawar, ya ce, "Tabita, tashi." Ta bude idanunta, da ta ga Bitrus ta zauna, 41 Bitrus kuwa ya mika hannunsa ya tashe ta; sa'annan ya kira masu bi da gwamrayen, ya mika ta a raye garesu. 42 Wannan al'amari ya zama sananne cikin dukan Yafa, kuma mutane da yawa suka bada gaskiya ga Ubangiji. 43 Ya kasance, cewa, Bitrus ya zauna kwanaki da dama a Yafa tare da wani mutum mai suna Saminu, majemi.
Labarin ya komo kan Bulus da samun cetonsa.
Waɗannan ayoyin suna ba da tarihin abubuwan da Bulus ya rika yi tun daga mutuwar Istifanus.
AT: cigaba da maganganun tsoratarwa, har ma da kisan almajiran"
Wannan na nufin mutanen da ke majami'un. AT: "zuwaga mutanen da ke majami'un" ko kuma "zuwaga shugabanin da ke majami'un"
...''in ya sami wani'' ko ''har ya sami wani''
"da ke bin koyarwar Yesu Almasihu"
Wannan wata lakani ce da aka san masu bi da shi a wancan loƙaci.
"ya kawo su a matsayin yan gidan kurkuku a Urushalima." Za a iya kara bayanin manufan Bulus idan aka kara cewa "domin ya shugabanin Yahudawa su masu shari'a su kuma yanka masu hụkunci"
Shawulu ya bar Urushalima za shi Dimashku
Wannan furcin na ba da alamar canji a labarin cewa wani abu da na zai faru.
"wani wuta daga sama ya haska kewaye da shi"
Wannan na iya nufin 1) sama, wurin da Allah ke kasancewa ko kuma 2) sararin sama. Ma'anan na forkon ya fi gaskiya. Yi amfani da wannan ma'anan idan harshen ku ta na da wata kalma daban masa.
Wannan na iya nufin cewa 1)"Shawulu ya yi tsalle zuwa ƙasa" ko kuma "Haken ya sa shi ya fada ƙasa" ko kuma "Shawulu ya faɗi ƙasa kamar wanda ya sume." Faduwar Shawulu dai ba hatsari ba ne.
Wannan tambayan ganganci ne na sauta wa Shawulu. A wasu harsuna ana iya faɗin sa ba da tambaya ba
Ba wai Shawulu yana amicewa da cewa Yesu Ubangiji ba ne. Ya yi amfani ne da wannan lakani domin ya fahimci cewa yana magana ne da wata iko na allahntaka.
"ta shi ka je cikin birnin Dimashku"
AT: "wani zai faɗa maka"
"sun ji muryar amma basu ga kowa ba"
A fili yake cewa Bulus ne kadai ya dandana wannan hasken.
Wannan na nuna cewa ya rufe idanunsa saboda yawan hasken.
"bai iya ganin komai ba." Shawulu ya makance.
"na makance" ko kuma "ba ya iya ganin komai"
Ba a bayyana ko shi ne ya zaɓa kada ya ci ko ya sha ba saboda ibada, ko kuma bai ma ji marmarin haka saboda halin da yake ciki. Ya fi kada ma aba da wata takamemmenn dalili.
Wannan na gabatar da wani sabuwar mutum a cikin labarin.
"Hananiya ya ce"
"ka je Mikakkiyar titi"
Ba wannan Yahuza ne ya bashe Yesu ba. Wannan Yahuza shi ne mai gidan da ke Dimashku in da Shawulu yake zama.
"wani mutum daga birnin Tarsus mai suna Shawulu" ko kuma "shawulu da ke Tarsus"
Wannan alama ce na ba wa Shawulu albarku na ruhaniya."
"ya iya gani kuma"
A nan "tsarkaka people" na nufin Masubi. AT: "mutanen da ke Urushalima da sun gaskanta da kai"
A nan daukan cewa iyakar iko da izini da aka ba wa Shawulu ya tsaya ne kan mutanen Yahudawa a wannan loƙaci.
A nan "sunanka" na nufin Yesu.
"zababben kayan aiki" na nufin wani abin da aka kebe domin wata hidima. AT: "na zabe shi ya bauta mini"
Wannan furci ne na gana wa ko kuma sanar da Yesu. AT: "domin ya sanar da ni"
Wannan furcin na nufin "sanar wa mutane game da ni"
Zai zama da taimako idan a sanar cewa Hananiya ya je gidan kamun ya shigo ciki. AT: "Sai Hananiya ya tafi, da ya samo gidan da Shawulu yake, sai ya shigo"
AT: "ya aiko ni domin ka sami ganin gari Ruhu Mai Tsarki ya kuma cika ka"
...
"ya iya ganin gari kuma"
AT: ya tashi sai Hananiya ya masa baftisma"
Wannan wata laƙaɓi ne ma muhimanci na Yesu.
AT: "Waɗanda suka saurare shi" ko kuma "Da daman su da suka saurare shi"
Wannan tambayan ganganci ne da ke nanata cewa lallai Shawulu ya tsananta wa masubi. AT: "Ai wannan ne mutumin da ya hallaka mutanen da ke Urushalima da ke kira bisa ga sunan Yesu!"
"A nan "suna" na nufin Yesu. AT: "sunan Yesu"
Suna damuwa ƙwarai domin ba su iya samun wata hanya na ƙaryata muhawarar Shawulu cewa Yesu Almasihu ne.
Wato shugabanin Yahudawan. AT: "Shugabanin Yahudawan"
AT: "Amma wani ya faɗa wa Shawulu game da shawaransa" ko kuma "Bulus ya san game da shirinsu"
Birnin yana da katanga kewaye da shi. Mutane na iya shiga ko fita daga birnin ta kofofin ne kawai.
mutanen da suka ba da gaskiya ga sakon Shawulu game da Yesu kuma sun bin koyaswansa.
"suka yi amfani da igiyoyi suka sauke shi a wata babban kwando ta wata rami a katangan.
A nan "dukansu" na iya yiwuwa ya hada da kowannensu, AT: "amma suna tsoronsa"
Wannan wata hanya ne na cewa ya yi wa'azi bishara ko koyar da sakon Yesu Almasihu ba tsoro. AT: "ya yi wa'azin bisharan Yesu a fili"
Wato Bulus kenan. Kalmar nan "su" kuma na iya nufin manzannin da kuma sauran almajiran da ke Urushalima.
Wannan na iya nufin 1) wannan na iya zama Ubangiji Yesu wadda Bulus ke magana akai. AT: "game da Ubangiji Yesu" ko kuma 2) "suna" na nufin iko. AT: "karkashin ikon Ubangiji Yesu" ko kuma "da ikon da Ubangiji Yesu ya ba shi"
Shawulu ya yi koƙarin tattaunawa da Yahudawan da ke Halenanci.
"Kalmar nan 'yan'uwan' na nufin masubi da ke Urushalima.
Kaisariya na kasa da Urushalima d tadawa.
Kaisariya kuwa tashan saukan jiragen ruwa ne. Mai yiwuwa 'yan'uwan sun turo shi Tarsus ta jirgin ruwa ne.
Wannan ne forƙon kiran ikkilisiyoyi fiye da ɗaya a matsayin ikkilisiya guda. Anan yana nufin dukan masubi a dukan kungiyoyin da ke Isra'ila gabaɗaya.
"suka zauna lafiya." Wannan na nufin cewa tsanantawar da aka fara daga kisan Istifanus ya kare.
Maginan na kuma Allah ne ko kuma Ruhu Mai Tsarki. AT: "Allah ya taimake su sun yi girma" ko kuma "Ruhu Mai Tsarki ya gina su"
"tafiya" anan magana ce da ke nufin "rayuwa". AT: "suna rayuwar biyayya ga Ubangiji" ko kuma " suka cigaba da girmama ubangiji"
Wannan jimlar na nuna alamar wata sabuwan bangaren labarin.
"tare da samun karfawa da taimakon Ruhu Mai Tsarki"
Wannan na nufin cewa Bitrus ya ziyarce masubi da ke wurare da dama a yankin Yahudiya, Galili, da Samaria.
Lidda na kasa da sauran wuraren ta yake tafiya.
Lidda wata birni ne da ke kilomita 18 gabas maso kudancin Yafa. Anan kiran wannan birni Lod a Tsohon Alkawali da kuma Isra'ila ta yau.
Bitrus ba fito nema wani shanyayyen mutum da gangan ba ne, ya dai faru hake ne dai da shi. AT: "A can kuwa ya sadu da wani mutum"
Wannan na gabatar da Iniyasu ne a matsayin wani sabon mutum a labarin.
Wannan dai tarihin Iniyasu kenan.
ba iya tafiya ba, mai yiwuwa ma ba ya iya motsi daga kwankwasonsa.
"ka kintsa taburmarka"
Wannan na nufin mutane masu yawa da ke wurin. AT: "waɗanda ke kasar Lidda da kuma kasar Sarona" ko kum "mutane da yawa da ke kasar Lidda da kuma kassar Sarona"
Birnin Lidda a sararin Sarona ya ke.
Yana iya zama da taimako a sanar cewa sun ga mutumin a warke. AT: "suka ga mutumin da Bitrus ya warkar"
A nan "juyo ga Ubangiji" na nufin suka fara biyayya ga Ubangiji. AT: "sai suka tuba daga zunubansu suka fara yi wa Allah biyayya"
Tabita shi ne sunan ta a Harshen Yahudanci, sa'annan Dokas shine sunan ta a harshen Hallenanci. Duka sunaye biyun dai na nufin "barewa." AT: "sunanta a Hallenaci ita ce Dokas"
"tana yin abubuwa da yawa masu kyau"
Wannan na mayar da mu zuwa ga loƙacin da Bitrus ke Yafa. AT: "Ya kai ga loƙacin da Bitrus yana kusa"
Wannan wankin domin shirin bizne ta ne.
Wannan dai nuna jikin mamaci ne na ɗan loƙaci yayin jana'izi.
"almajiran suka aiko mutane biyu wurin Bitrus"
"wata dakin sama wurin da jikin Dokas yake a kwanciye"
Yana iya yiwuwa dukan gwamrayen garin suna kasace a waurin tunda ba babbar gar ba ce.
Matayen da mazan su sun mutu kuma suna buƙatan taimako
"loƙacin da take da rai tare da almajiran"
"ya ce masu su bar dakin." Bitrus ya fitar da su duka daga dakin domin ya kasance shi kadai a wurin ya yi wa Tabita addu'a.
Bitrus ya kama hannun ta ya taimake ta tsayawa.
Gwamrayen na iya zama masubi su ma amma ba ambaci hakan ka tsaye ba domin Tabita ta na da muhimanci sosai a garesu.
Wannan na nufin abin al'ajibin da Bitrus yayi na tayar da Tabita daga matattu. AT: Mutane da ke Yafa duka sun ji wannan al'amarin"
"suka ba da gaskiya ga bisharar Ubangiji Yesu"
Wani mai suna Saminu, da ke yi fata daga jikin dabbobi"
Shawulu ya tambaye ma wasiƙu don ya iya tafiya zuwa Dimashƙu kuma ya zo da su ɗaure kowane wanda ya mallakar Hanyan.
Da Shawulu ya yi kusa da Dimashƙu, ya gan haske daga sama.
Muryan ya ce, "Shawulu, Shawulu, don me kake tsanata mini".
Amsan shine, "Ni ne Yesu wanda kake tsanata wa".
Da Shawulu ya taso daga kasa, bai iya gan kome ba.
Shawulu ya je Dimashƙu kuma bai ci ko sha ba ma kwana uku.
Ubangiji ya gaya ma Hananiya ya je ya kuma sa hannun sa a Shawulu, Soboda Shawulu ya iya gani.
Hananiya ya yi damuwa domin ya san Shawulu ya zo daga Dimashƙu ya kama kowa wanda yana kira akan sunan Ubangiji.
Ubangiji ya ce Shawulu zai ɗauka sunan Ubangiji gaban al'ummai, sarakuna, da kuma 'ya'yan Isra'ilawa.
Ubangiji ya ce Shawulu zai yi wuya ƙwarai sabilin sunan Ubangiji.
Bayan Hananiya ya sa hannun sa a kan Shawulu, Shawulu ya same gani, an yi masa baftisma, ya kuma ci abinci.
Shawulu nan da nan ya fara shelar Yesu a majami'u, yana cewa shi ne Dan Allah.
Da Yahudawan sun shirya su kashe shi, Shawulu ya gudu ta zura shi ta wata taga a jikin garu cikin kwando.
A Urushalima, manzannin sun ji tsoron Shawulu.
Barnaba ya kai Shawulu ya kuma bayyana abin da ya faru da Shawulu a Dimashƙu.
Shawulu ya yi magana gabagadi a cikin sunan Ubangiji Yesu.
Ikkilisiyar Yahudiya, Galili, da ta Samariya ta sami zaman lafiya kuma ta ingantu, ta yi girma a lamba.
A Lidda, Bitrus ya yi magana da mutum mai shanyeyye wanda Yesu ya warkar.
Bitrus ya yi addu'a ma mata da ta mutu mai suna Tabita, wanda an tayar da itta daga matatu.
1 An yi wani Mutum a birnin Kaisariya, mai suna Karniliyas, shugaban sojoji ne na kungiyar da ake kira Italiya. 2 Mutum ne mai ibada, wanda ya mika kansa da iyalinsa ga bautar Allah; ya kan bada taimakon kudi mai yawa ga Yahudawa, kuma yana addu'a ko yaushe ga Allah. 3 Wajen sa'a ta tara ga yini, an bayyana masa cikin wahayi mala'kan Ubangiji na zuwa gare shi sai mala'ikan ya ce masa, "Karniliyas!" 4 Karniliyas ya zuba wa mala'ikan ido a tsorace ya ce "Menene, mai gida?" mala'ikan ya ce masa, "Addu'ar ka da taimakon ka ga talakawa ya kai sama matsayin sadaka abin tunawa a gaban Allah, 5 "Yanzu ka aika mutane zuwa birnin Yafa su kawo mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus. 6 Yana zama tare da Saminu majemi, wanda gidansa ke bakin teku. 7 Da mala'ikan da ya yi magana da shi ya tafi, Karniliyas ya kira biyu daga barorin gidansa, da kuma soja guda mai bautar Allah daga cikin sojojin da suke masa hidima. 8 Karniliyas ya fada masu dukan abin ya faru sai ya aike su Yafa. 9 Washe gari wajen sa'a ta shida (tsakar rana) suna cikin tafiya da suka yi kusa da birni, Bitrus ya hau kan bene don ya yi addu'a. 10 Sai ya ji yunwa kuma yana bukatar wani abinda da zai ci, amma a yayin da mutanen na dafa abinci, sai ya ga wahayi. 11 Sai ya ga sararin sama ya bude kuma wani tasa na saukowa, wani abu kamar babban mayafi yana saukowa zuwa duniya, ana zuro shi ta kusuryoyinsa hudu. 12 A cikinsu kuwa akwai dukan halitun dabbobi masu kafa hudu da kuma masu rarrafe a duniya da tsunstayen sama. 13 Sai murya ta yi magana da shi; "Tashi, Bitrus, yanka ka ci " 14 Amma Bitrus ya ce "Ba haka ba, Ubangiji, gama ban taba cin abu mara tsarki ko mai kazanta ba." 15 Amma muryar ta sake zuwa masa karo na biyu kuma; "Abinda Allah ya tsarkake, kada ka kira shi kazantacce." 16 Wannan ya faru sau uku; nan da nan sai aka dauki tasar zuwa sama. 17 A yayin da Bitrus na cikin rudani game da ma'anar wahayin da ya gani, sai ga mutanen da Karniliyas ya aika suna tsaye a bakin kofar gidan, bayan sun tambayi hanyar zuwa gidan, 18 Kuma suka yi sallama suna tambaya ko Saminu wanda ake kira Bitrus ya sauka a nan. 19 A yayin da Bitrus yana kan tunani akan wahayin, Ruhu ya ce masa, "Duba, mutane uku na neman ka." 20 Tashi ka sauka ka tafi tare da su. Kada ka yi jinkirin tafiya tare da su, domin Nine na aike su." 21 Bitrus kuwa ya sauko wurin mutanen ya ce, "Ni ne wanda kuke nema. Me ya sa kuka zo?" 22 Suka ce, "Shugaban soja mai suna Karniliyas, adalin mutum kuma mai bautar Allah, yana da kyakkyawar shaida a dukan al'umman Yahudawa, shi ne wanda mala'ika mai tsarki na Allah ya aika domin ka zo gidansa, ya ji sako daga wurinka." 23 Sai Bitrus ya gayyace su su zo ciki kuma su zauna tare da shi. Washegari sai ya tafi tare da su, kuma wadansu 'yan'uwa daga Yafa suka raka shi. 24 Kashegari suka shiga Kaisariya, Karniliyas kuwa yana jiran su; har ma ya gayyaci 'yan'uwansa da kuma abokansa na kusa. 25 Ya kasance sa'adda Bitrus ya shiga, Karniliyas ya sadu da shi kuma ya durkusa ya yi masa sujada. 26 Amma Bitrus ya tashe shi yana cewa, "Tashi tsaye! Ni ma mutum ne." 27 A lokacin da Bitrus yake magana da shi, ya shiga ciki sai ya tarar da mutane da yawa sun taru a wuri daya. 28 Ya ce masu, "Ku da kanku kun sani bai dace Bayahuden mutum ya yi ma'amulla ko ya ziyarci wani ko wata kabila ba. Amma Allah ya ce da ni kada in ce da kowa mara tsarki ko kazantacce. 29 Wannan shine yasa na zo ba tare da musu ba, a lokacin da kuka kira ni. Don haka na tambaye ku me ya sa kuka aika in zo." 30 Karniliyas ya ce "Kwanaki hudu da sun wuce a daidai wannan lokaci, ina addu'a da cikin sa'a na tara (karfe uku) a gidana, sai na ga mutum tsaye a gabana da tufafi mai haske. 31 Ya ce, "Karniliyas, Allah ya ji addu'ar ka, kuma taimakon ka ga talakawa ya tuna ma Allah da kai. 32 Saboda haka ka aika da wani Yafa, ya kira maka mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus. Yana zama a gidan Saminu majemi, da ke bakin teku. [1]33 Don haka nan da nan na aika a kira ku. Kuna da kirki da kuka zo. Yanzu haka, duk muna nan a gaban Allah, don jin duk abin da Ubangiji ya umarce ku da ku faɗi.” [2]34 Sai Bitrus ya bude bakinsa ya ce, "Gaskiya, na fahimci Allah baya nuna bambanci. 35 Maimakon haka, cikin kowace al'umma duk mai ibada kuma mai aikata adalci karbabbe ne a gare shi. 36 Ku kun san sakon da ya aika wa mutanen Isra'ila, a lokacin da ya sanar da labarin mai kyau na salama ta wurin Yesu Kristi, wanda shine Ubangiji na duka. 37 Ku da kanku kun san al'amuran da suka kasance, wanda ya faru cikin Yahudiya, farawa daga Galili, bayan sanarwar baftismar da Yahaya ya yi. 38 Al'amura game da Yesu Banazare, yadda Allah ya kebe shi da Ruhu Mai Tsarki da iko kuma. Ya kuma ci gaba da aikin alheri da warkarwa ga dukan wadanda shaidan ya daure, domin Allah yana tare da shi. 39 Mu shaidu ne ga dukan abubuwan da ya yi a kasar Yahudawa da cikn Urushalima, wannan Yesu wanda suka kashe, ta wurin giciye shi a akan itace. 40 Wannan mutumin, Allah ya ta da shi rana ta uku ya kuma maishe shi sananne, 41 ba ga dukan mutane ba, amma ga shaidun da Allah ya zaba tun da farko - mu kanmu, wadanda muka ci muka sha tare da shi bayan tashin sa daga matattu, 42 Ya umarce mu mu yi wa mutane wa'azi mu kuma tabbatar cewa shine wanda Allah ya zaba ya yi shariya bisa masu rai da matattu. 43 Gareshi ne dukan annabawa suka yi shaida, domin dukan wanda ya bada gaskiya gareshi ya sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.` 44 Sa'adda Bitrus yana kan magana game da wadannan abubuwa, Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan dukan wadanda suke sauraron wa'azin sa. 45 Mutanen da ke kungiyar masu bi da suka yarda da kaciya, dukan wadanda suka zo tare da Bitrus suka yi mamaki, domin baiwar Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan al'ummai. 46 Domin sun ji al'umman nan suna magana da wasu harsuna suna yabon Allah. Sai Bitrus ya amsa, 47 "Ko akwai wanda zai hana wa wadannan baftisma ta ruwa, da shike suma sun karbi Ruhu Mai Tsarki kamar mu?" 48 Sai ya ba da umarni a yi masu baftisma cikin sunan Yesu Kristi. Sai suka roke shi ya kasance da su na wasu kwanaki.
Wannan ne forƙon bangaren labarin Karniliyas.
Waɗannan ayoyin suna ba da tarihi game da Karniliyas.
Wannan wata hanya ne na gabatar da sabuwar mutum a wannan sashin tarihin.
"sunan sa Karniliya. Shugaban sojoji ne da ke da sojoji 100 a karkashinsa daga sojojin Roma da ke bangaren Italiya.
"Ya gaskata da Allah yana kuma neman ya girmama ya kuma mika kansa ga Allah muddin ransa."
Kalmar nan "mika kai" a nan na nuna matuƙar bangirma datsoron Allah.
Wannan na nufin yawancin loƙaci. AT: yana wa Allah addu'a sosai" ko kuma ""yana wa Allah addu'a kulayomi"
"da karfe uku na rana." Wannan ne daidai loƙacin da Yahudawa sukan yi addu'a.
"an bayyana wa Karniliyas"
A nan iya cewa taimakonsa da addu'oinsa sun sami karba a wurin Allah. AT: "Allah yana jin dadin addu'oi da sadakarka ... abin karma a wurin sa"
mutumin da ke yin fata daga jikin dabbobi
"Da wahayin Karniliyas game da malaikan ya kare."
"ɗaya daga cikin sojojin da ke bauta masa, da ke wa Allah sujada kuma." Wannan sojan mai bi ne. Hakan yana da wuya a samu a cikin sojojin Roma, saboda haka yana iya yiwuwa ma cewa sauran sojojin Karniliyas ba masubi ba ne.
...
Karniliyas ya yi bayyanin wahayinsa ga bayinsa, ɗaya daga cikin sojojinsa.
"ya aiko bayinsa biyu, ɗayan su kuma soja ne kuma an aiko shi Yafa ne
"tsakar rana"
Kan gidajen shimfiɗaɗɗe ne, kuma mutane sun kan ya abubuwa da dama a bisan su.
"kamin mutanen su gama dafa abincin"
"Allah ya nuna masa wahayi"
Wannan ne forƙon wahayin Bitrus. Za a iya fara ta da wata sabuwan jimla.
...
...
Daga amshin Bitrus a aya na gaba, za a iya tunanin cewa shari'ar Musa bai umurce Yahudawan su ce wasu dabbobin ba. AT: "dabbobi da tsuntsayen da shari'ar Musa ya hana Yahudawa ci"
Ba ambaci mai maganan ba. Yana iya yiwuwa "muryar" nan na Allah ne, ko da shike ya na iya ma ya zama muryar Malaikan Allah ne.
"Ni ba zan yi haka ba"
Ana ɗaukan cewa shari'ar Musa bai ba wa masubin da ke rayuwa kamun mutuwar Almasihu daman cin wasu dabbobi da ke mayafin domin su ƙazantacecce na.
Idan Allah ne mai magana, yana magana game da kansa kamar shi ne mutum na uku a wurin. AT: "Abinda Ni, Allah, na tsarkake"
Ba lallai kome ne da Bitrus ya gani ya faru sau uku ba. Wannan jimlar na iya nufin, "Abinda Allah ya tsarkaka, kada ka ce da shi kazantatce" ne aka maimaita sau uku. Ko da shika, ya fi kyau a ce "Wannan ya faru sau uku" da a yi ta koƙarin ba da wasu bayyani.
Wannan na nufin cewa Bitrus ba iya gane abinda wahayin ke nufi ba.
Kalmar nan "sai" na jan hankalin mu zuwa ga bayyani na ban mamaki da ya biyo baya a wannan sha'anin, mutan biyun da ke tsaye a ƙofar.
"suka tsaya a bakin kofar gidan." Ana dauƙan cewa wannan gidan na da bango da kuma kofa wadda ake bi a shigo ta.
Hakan ya faru kamin su iso gidan. Ana iya sanar da wannan a ayan da ke kamin wannan kamar yadda aka yi a UDB.
Mutanen Karniliyas suna kasance a kofa, a waje yayin da suna tambayan game Bitrus.
"yana kan tunanin ma'anar wahayin"
"Ruhu Mai Tsarki"
"ka kasa kunne daomin abinda nake so in gaya maka gaskiya ne kuma mai muhimanci ne: mutane uku"
Wasu nasosi na da suna da kimamun mutane daban-daban.
"sauka daga saman gidan"
Ya na da sauki Bitrus ya ki yin marmarin tafiya tare da su, domin su baƙi ne, kuma Al'ummai ne.
"Ni ne mutumin da kuke nema"
(Dubi: )
kalmar "bautar Allah" anan nu nufin mutuƙar ban girma da tsoron Allah.
Ana moran kalmar nan "dukan" domin a nanata yadda Yahudawa da yawa sun san da shi.
Tafiya Kaisariya na da nesa su bi su kama hanya da rana haka.
...
Wannan na nufin masubi da ke Yafa.
Wato bayan da suka bar Yafa kenan. Tafiyar Kaisariya na ɗaukansu fiya da ini ɗaya.
...
"sa'adda Bitrus ya shigo gidan"
"ya durkusa ya sa fuskarsa kusa da karfa Bitrus." Ya yi haka ne domin ya girmama Bitrus.
Ya yi haka ne musamman don ya nuna cewa yana sujada.
Wannan wata ɗan tsauta wa ne ko kuma gyara ne wa Karniliyas don kada ya yi wa Bitrus sujada. AT: "Ka daina yin haka! Ni ma fa mutum ne kamar ka"
"Al'ummai da yawa sun taru a wuri ɗaya." Ana ɗaukan cewa mutanen nan da Karniliyas ya gayyata Al'ummai ne.
Bitrus yana magana ne da Karniliyas da kuma gayyatattun baƙinsa.
"an hana Bayahuden mutum." Wannan na nufin shari'ar adinin Yahudanci.
Wannan na nufin mutanen da ba Yahudawa ba lallai wurin da suke zama ba.
Karniliyas yana nufin yini ɗaya kamun dare a uku kamun ya fara magana da Bitrus. Bisa ga kirgen Littafi Mai Tsarki ana kirga ranar da ake ne, don haka kamun dare uku da suka wuce shi ne "kwanaki huɗu da suka wuce." Da shike al'adun Yammaci a yau ba su kirge da kwanan da ake ciki, masu juyi da yawa sukan rubuta "kwanaki uku da suka wuce.
Wasu mannyan ma su karatu sun ce "azumi da addu'a" suke yi, a maimakon "addu'a" kawai.
Daidai lokacin da Yahudawa ke yi wa Allah addu'a da rana.
.lokaci ne da rana da Yahudawa suke yin sujada ga Allah.
"ya jawo da hankalin Allah zuwa kanka." Wannan bai nuna cewa Allah ya manta ba ne.
"fada wa Saminu wadda a ke kira Bitrus ya zo gare ka"
"da sauri"
Wanna furcin wata hanya ne na gode wa Bitrus da zuwa. AT: "Hakika na gode sosai da zuwa"
...
AT: da Ubangiji ya ce ka faɗa"
"Bitrus ya fara masu magana"
Wannan na nufin cewa abinda zai fada masu yana da muhimmanci sosai su sani.
...
"yana karaban duk wanda ke masa ibada mai aikata adalci"
Kalmar nan "ibada" anan na nuna matuƙar ban girma da tsoron Allah."
An takaita tsawon wannan jimlar zuwa wasu gajerun jimla a UDB.
A nan "duka" na nufin "dukan mutane"
AT: "Yahudiya gabakiɗaya" ko kuma "a wurare da dama cikin Yahudiya"
"bayan da Yahaya ya yi wa mutanen wa'azi su tuɓa ya masu baftisma"
an yi maganan Ruhu mai tsarki da ikon Allah kamar wanni abu ne wanda za a zuba a kan mutum
AT: "waɗanda shaiɗan ya daure" ko kuma "mutane da dama da shaiɗan ya ɗaure"
Wannan karin maganan "yana tare da shi" na nufin "yana taimakonsa."
Wannan na nufin Yahudiya ne a wannan loƙacin.
AT: "giciye shi a bisa giciyen katako"
A nan a tayar karin magana ne da ke nufin a sa mutum da ya mutu ya tashi kuma. AT: "Allah ya rayar da shi kuma"
"rana ta uku bayan ya mutu"
"ya bar mutane da dama su ganshi bayan ya ta da shi daga matattu"
Daga dukan waɗanda suka mutu. Wannan furcin na bayyana cewa dukan matattu gabaɗaya suna karkashin duniya.
"Allah ya zabe shi Yesu"
Wannan na nufin mutanen da suke da rai da kuma muutanen da sun riga sun mutu. AT: "mutanen da ke da rai da kuma mutanen da sun riga sun mutu"
"Dukan annabawa sun ba da shaida akan Yesu"
AT: "Allah za gafarta zunuban duk wanda ya ba da gaskiya ga Yesu domin abinda Yesu ya yi"
Anan "sunansa" na nufin abinda Yesu ya yi. Ma'anan "sunansa" shi ne Allah mai ceto. AT: "ta wurin abinda Yesu ya yi masu"
A nan kalmar nan "sauko" na nufin "ya faru da sauri." AT: "Ruhu Mai Tsarki ya bi ya zo"
A nan "duka" na nufin dukan Al'ummai da ke a gidan suna sauraron Bitrus.
Wannan wata hanya ce da ke nufin Yahudawa masu bi.
Wannan na nufin Ruhu Mai Tsarki da kansa da aka ba su.
AT: "Allah ya sauko da Ruhu Mai Tsarki"
AT: "bayar a yalwace"
kyautar baiwar
A nan "ma" na nuna cewa an riga an ba da Ruhu Mai Tsarki ga masubi Yahudawa.
Waɗannan sanannun harsuna ne da suka sa Yahudawa suka amince cewa lalle Al'umman suna yabon Allah.
Bitrus ya yi amfani ne da wannan tambayan ya karfafa Yahudawa masu bi da cewa a yi wa Al'ummai masu bi baftisma. AT: "Kada wani ya hana waɗannan mutanen da ruwa! Mu yi masu baftisma domin sun karbi ... mu!"
Ana ɗaukan cewa Yahudawa masubi ne za su yi masu baftisma. AT: "Bitrus ya umarce Al'ummai masubi su bar Yahudawa masubi su yi masu baftisma" ko kuma "Bitrus ya umarce Yahudawa masu bi su yi masu baftisma"
Anan "cikin sunan Yesu Kiristi" na nuna cewa dalilin baftismar su shi ne domin sun gaskanta da Yesu. AT: "a yi masu baftisma a mastayin masu bi a cikin Yesu Kristi"
Karniliyas mutum mai ibada ne mai tsoron Allah, yana ba da sadaka, kuma yana addu'a ga Allah a kai a kai.
Mala'ikan ya ce addu'oi Koneliyus da kyautai da yana ba wa matalauta ya tunãtar da Allah akan Karniliyas.
Mala'ikan ya gaya ma Koneliyus ya aika mutane Yoffa su kira Bitrus.
Bitrus ya gan babban mayafi cike da kowace irin dabba, da masu jan ciki, da tsuntsaye.
Murya ya ce ma Bitrus, "Tashi, Bitrus, kashe ka kuma ci".
Bitrus ya ki, yana ce bai taba cin wani abu marar tsarki ko mai ƙazanta ba.
Muryan ta ce, "Abin da Allah ya tsarkake, kada ka ce da shi marar tsarki".
Ruhun ya gaya ma Bitrus ya sauka ya kuma je da su.
Mutane daga Karniliyas sun zata Bitrus ya zo ya ba da sako a gidan Karniliyas
Bitrus ya gaya ma Karniliyas ya tashi, shi ma ɗan Adam ne.
Bitrus na tarayya da mutane daga wani al'uma, domin Allah ya nuna mashi cewa kadda ya kira wani mutum marar tsarki ko mai ƙazanta.
Bitrus ya ce ko wane da na tsoron Allah mai kuma aikata adalci, abin karɓuwa ga Allah.
Mutanen sun riga sun ji cewa Ruhu Mai Tsarki ya shafe Yesu da iko, kuma cewa ya warkar da duk waɗanda ke danne, don Allah na tare da shi.
Bitrus ya sanad cewa Allah ya tasar da Yesu a rana na uku, kuma cewa Bitrus ya ci abinci da Yesu bayan tashin sa daga matattu.
Yesu ya umurce su su yi wa'azi cewa Allah ya zabi Yesu ya zama hukunta rayayyu da matattu.
Bitrus ya ce kowa da ya gaskanta a Yesu zai sami gafarar zunubai.
Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan duk wanda suna saurare Bitrus.
Masu bin wanda suke tare da rukuni ma su kaciya sun nuna mamaki domin zubo masu baiwar Ruhu Mai Tsarki har akan al'ummai.
Mutanen suna magana a wadansu harsuna, suna ta ɗaukaka Allah wanda ta nuna cewa Ruhu Mai Tsarki ta zubo a kan su.
Bitrus ya umarni cewa a yi ma mutanen baftisma a cikin sunan Yesu Almasihu.
1 Yanzu Manzani da 'yan'uwa wadanda suke cikin Yahudiya suka ji cewa al'ummai ma sun karbi maganar Allah 2 Lokacin da Bitrus ya je Urushalima, wadanda suke na kaciya suka zarge shi; 3 suka ce, "Ka hada kai tare da mutane marasa kaciya kana ci tare da su!" 4 Amma Bitrus ya fara bayyana masu dalla-dalla; ya ce, 5 Ina addu'a a cikin birnin Yafa, sai na ga wahayi game da taska yana saukowa, kamar babban mayafi da aka saukar daga sama ta kusurwan nan hudu. Ya sauko gabana. 6 Na zura masa ido kuma na yi tunani a kansa, na ga dabbobi masu kafa hudu na duniya, miyagun dabbobi, da masu rarrafe, da tsuntsayen sama. 7 Sai na ji murya tana ce da ni, "Tashi, Bitrus, yanka ka ci." 8 Na ce, "Ba haka ba, Ubangiji: gama babu abu mara tsarki ko mai kazanta da ya taba shiga bakina." 9 Amma murya ta amsa kuma daga sama cewa, "Abin da Allah ya kira mai tsarki, kada ka kira shi mara tsarki." 10 Wannan ya faru sau uku, sai dukan komai ya koma sama. 11 Nan da nan sai ga mutane uku tsaye a gaban gidan da muke; an aike su daga Kaisariya zuwa gare ni. 12 Ruhun ya umurce ni in tafi tare da su, ba tare da nuna banbanci game da su ba. Yan'uwan nan shida sun tafi tare da ni, sai muka shiga gidan mutumin. 13 Ya fada mana yadda ya ga mala'ika tsaye a cikin gidansa yana cewa "Aiki mutane zuwa Yafa, su kirawo Saminu wanda ake kira Bitrus. 14 Zai gaya maku sakon da za ku sami ceto kai da dukan gidanka." 15 Da na fara magana da su, Ruhu Mai Tsarki ya sauko akansu kamar yadda ya sauko mana tun da farko. 16 Sai na tuna da maganar Ubangiji, yadda ya ce,"Hakika Yahaya ya yi baptisma da ruwa, amma ku za a yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki." 17 To, idan Allah ya yi masu baiwa kamar yadda ya yi mana yayin da muka bada gaskiya ga Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni da zan yi jayayya da Allah? 18 Da suka ji wadannan abubuwa, suka rasa ta cewa, amma suka daukaka Allah suka ce "Ga al'ummai ma Allah ya basu tuba zuwa rai." 19 Sai wadanda suka warwatsu saboda tsananin da ya bi bayan mutuwan Istifanas, suka yadu har zuwa Finikiya, Kuburus da Antakiya, amma suka yi wa'azin Yesu ga Yahudawa kadai. 20 Amma wadan sunsu, mutane daga Kuburus da Kurane, suka zo Antakiya suka yi magana da hellenawa, suna yi masu wa'azin Ubangiji Yesu. 21 Kuma ikon Ubangiji yana tare da su, har mutane da yawa suka gaskata kuma suka juyo wurin Ubangiji. 22 Labari game da su ya iso kunnen ikilisiya da ke Urushalima: sai suka aika da Barnaba zuwa can Antakiya. 23 Da ya iso kuma ya ga kyautar Allah, sai ya yi farinciki; ya karfafa su dukka su kafu cikin Ubangiji da dukan zuciyar su. 24 Domin shi mutumin kirki ne, cike kuma da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, sai mutane da yawa suka karu ga Ubangiji. 25 Sai Barnaba ya tafi Tarsus domin ya nemi Shawulu. 26 Da ya same shi, ya kawo shi Antakiya. Ya kasance, shekara guda suna taruwa tare da ikilisiya suka koyar da mutane da yawa. A Antakiya ne aka fara kiran almajiran Krista. 27 A cikin kwanakin nan wadansu annabawa daga Urushalima suka zo Antakiya. 28 Daya daga cikinsu, mai suna Agabas ya mike tsaye yayi magana da ikon Ruhu cewa za a yi tsanani fari ko'ina a duniya. Wannan ya faru ne a zamanin Kalaudiya. 29 Sai, almajiran, suka dau niyya kowa gwargwadon karfinsa, su aika wa 'yan'uwa da ke Yahudiya da taimako. 30 Suka yi haka; sun aika wa dattawa da kudi ta hanun Barnaba da Shawulu.
Bitrus ya iso Urushalima ya fara wa Yahudawa da ke wurin magana.
Wannan farƙon wata sabuwar hali ne a labarin.
Wannan na sa alamar wata sabuwar bangaren labarin.
Wato "'yan'uwa" na nufin masubi da ke cikin Yahudiya.
"waɗanda ke cikin yankin Yahudiya"
Wannan furci na nuna gaskiyar cewa Al'ummai ma sun gaskanta da sakon Yesu. AT: "sun gaskanta da sakon Allah game da Yesu"
...
Wannan na nufin wasu Yahudawa da sun gaskanta cewa dole ne a yi wa kowane mai bi kaciya. AT: "wasu Yahudawa masu bi a Urushalima da ke so dukan masubin Almasihu ya yi kaciya"
jimlar nan "mutane marasa kaciya" na nufin Al'ummai.
Al'addun Yahudawa ba su yarda Yahudawa su ci tare da Al'ummai ba.
Biitrus bai zarga abinda Yahudawa suka gaskanta da shi ba amma ya amsa masu ne a hanyar da za su gane.
"daidai abinda ya faru"
... Duba yadda aka juya wannan a [10:11]
"da kursuwansa guda huɗu a dakace" ko kuma "da kursuwansa huɗu a sama da sauransu" Duba yadda aka juya wannan a [10:11]
Daga amshin Bitrus, ya a iya ɗaukan cewa shari'ar Musa ya umarce Yahudawa kada su ci wasun su. Duba yadda aka fasara irin wannan jimlar a [10:12]. AT: "dabbobi da sunsaye da shari'ar Musa ya hana Yahudwa ci"
Wannan na iyan nufin dabbobi da mutane ba su iya kiwonso ko kuma bi da su ba.
Wato hallitu masu rarrafe kenan
Ba a ambaci mai maganan ba. Maiyiwuwa "muryar" kuwa na Allah ne, kodashike yana ma kuma iya zama mala'ikar Allah ne. Duba yadda aka fasara "murya" a [10:13]
"Ba zan yi haka ba" Duba yadda fasara wannan a [10:14]
Wannan a fili yake cewa dabbobin da ya gani dabbobi ne da dokar Yahudawa a Tsohon Alkawali ya hana Yahudawa ci. AT: "Ina cin naman tsarkakku da tsabatattun dabbobi ne kawai"
Bisa ga shari'ar Yahudawa na Tsohon Alkawali, mutum na iya zama "marar tsarki" ta hanyoyi da dama, kamar su cin haramtaccen dabbobi.
wato dabbobin da ke a mayafin kenan.
ka lallai ne cewa kome ya sake faruwa ne sau uku ba. Wannan na iya nufin "Abinda Allah ya tsarkake, kada ka kira shi mara tsarki. Kodashike, ya fi ma a saukake a ce "Hakan ya faru ne sau uku" a maimakon koƙarin bada dukkan labaran. Duba yadda aka fasara wannan a [10:16]
Wannan kalmar na jan hankalin mu ne zuwaga sabobin mutane a labarin. Mayiwuwa harshenku tana da wata hanyar yin haka.
"ba da batan lokaci ba" ko kuma "a dai dai lokacin"
AT: "wani ya aike su"
"cewa kada in damu da da cewa su Al'ummai ne"
"'Yan'uwan nan shida sun tafi tare da ni zuwa Kaisariya"
Waɗannan Yahudawa shida masubi"
Wato gidan Karniliyas.
...
AT: "Allah zai cece ku"
Wato dukkan mutanen da ke gidanka. AT: "kowan da ke gidanka"
Wannan na nufin cewa Bitrus bai gama magana ba, amma yana da da sauran magana.
Bitrus ya bar wasu abubuwa domin ya takaita labarin. AT: "Ruhu Mai Tsarkin ya sauko akan Al'ummai masubin, kamar yadda ya sauko akon Yahudawa masubi a ranar Fentikos"
Bitrus na nufin ranar Fentikos"
AT: "Allah zai yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki"
Bitrus na amfani ne da wannan tambayan don yă nanata cewa shi dai biyayya da Allah yake yi. AT: "Dashike Allah ya basu ... na zaɓi kada in yi gãba da Allah!"
Bitrus na nufin baiwar Ruhu Mai Tsarki.
"basu yi jayayya da Bitrus ba"
"Allah ya ba da tuɓa da ke kai ga rai wa Al'ummai suma." A nan "rai" nan nufin rai na har'abada. AT: "Allah ya bar Al'ummai su ma su tuɓa su rayu har'abada"
Yahudawa sun fãra sananta wa masubin Yesu domin Istifanus ya faɗi ya kuma aikata abubuwan da Yahudawa basu so ba. Saboda wannan tsanantawa, mabiyan Yesu da yawa sun bar Urushalima suka warwatsu zuwa wurare dabam dabam.
"suka tafi hanyoyi dabam dabam"
AT: "wanda Yahudawa ke tsananta masu saboda haka suka bar Urushalima"
tsanin da ya faru saboda abinda Istifanus ya faɗa ya kuma yi
Masubin sun ɗauka cewa maganar Allah domin Yahudawa ne kawai, ba domin Al'ummai ba.
Waɗannan Hallenawan Al'ummai ne, ba Yahudawa ba. AT: "suka yi magana da Al'ummai da suke Hallenanci ma"
Ikon Allah na nufin ikon taimakonsa. AT: "Allah yana iza waɗannan masubi su yi wa'azi"
A nan "juyo wa Ubangiji" karin magana ne da ke nufin fãra yi wa Ubangiji biyayya. AT: "sai suka tuɓa daga zunubansu suka fãra yi wa Ubangiji biyayya"
A nan "kunne" na nufin labarin abubuwan da suka faru da masubi sun ji. AT: "masubin da ke ikkilisiya"
"ga yadda Allah ya motsa cikin ƙauna domin masubi"
"ya riƙa ƙarfafasu"
"su kafu da aminci ga Ubangiji" ko kuma "su cigaba da dogara ga Allah"
A nan "zuciya" na nufin abinda mutum ke so ko marmarin. AT: "da dukkan son so" or "da mika kai gabaƙiɗaya"
Ruhu Mai Tsarki ne ya bi da Barnaba ya yi da yake biyayya da Ruhu Mai Tsarki.
A nan "karu" na nufin cewa sun gaskanta da Ubangiji kamar yadda sauran mutane. AT: "mutane masu yawan gaskiye su ma sun gaskata da Ubangiji"
"tafi birnin Tarsus"
Waɗannan kalamun na nufin cewa sun ɗauki lokaci sun kuma yi koƙari domin Barnaba ya same Shawulu.
Wannan na bada wata sabuwar abu da ya faru cikin labarin.
Barnaba da Shawulu suka taru tare da ikkilisiyar"
Wannan na nufin cewa sauran mutane suna kiran masubi da wannan suna. AT: "Mutanen Antakiya suka kira almajiran Kirista." Wato masu bin Yesu
"na farƙo a Antakiya"
Urushalima na sama da Antakiya ne a tadawa. Don haka, 'yan Isra'ila ma suna iya maganar haurowa zuwa Urushalima ko kuma saukowa da wurin.
"sunansa Agabus ne"
"Ruhu Mai Tsarki ya bishe shi yă yi anabci"
"za a yi wata babbar karancin abinci"
Wannan na nufin a yankin duniya da suka sani. AT: "a dukkan yankin duniya da mutane ke ciki" ko kuma "a Ɗaular Romawa gabaƙiɗaya"
Masu sauraron Luka za su san cewa Kaladiya shi ne sarkin Ɗaular Roma a wannan lokaci. AT: "a lokacin da Kalaudiya yana mulkin Ɗaular Roma"
Wannan kalma na nuna alamar abinda ya faru ta dalilin wani abinda ya faru tukuna. A wannan hali, sun turo koɗi domin anabcin Agabus ko kuma karancin abincin.
Waɗanda sun fi arziki suka aika da mai yawa, marasa arziki kuma suka aiko da kadan.
"masubin da ke Yahudiya"
Hannu wata karin magana ne da ke nufin abinda mutumin ya yi gabaƙiɗaya. AT: "ta wurin raƙiyar Barnaba da Shawulu"
Manzannin da 'yan'uwa a Yahudawa sun ji cewa al'ummai ma sun same maganar Allah.
Wanda suna rukunin masu kaciya sun yi zargi Bitrus ma cin abinci da al'ummai.
Bitrus ya gabatar da tabbataci cewa Ruhu Mai Tsarki ya zo akan al'ummai.
Sun ɗaukaka Allah kuma sun kammala cewa Allah ya ba su tuba zuwa rai ma al'ummai ma.
Mafi yawa masu bi sun fada sako akan Yesu ma Yahudawa kadai.
A loƙacin da sun yi wa'azin Ubangiji Yesu ma Girika, mutane dayawa sun ba da gaskiya.
Barnaba ya karfafa mutanen Girika to kasance da Ubangiji da duka zuciyarsu.
Barnaba da Shawulu sun tsaya ma duk shekara a ikkilisiya a Antakiya.
A Antakiya ne aka fara kiran almajirai Kirista.
Agabas ya hango cewa za a yi wata babbar yunwa a duniya duka.
Almajirai suka aika taimako zuwa 'yan'uwa a Yahudiya ta hannun Barnaba da Shawulu.
1 A lokacin nan Sarki Hiridus ya sa wa wasu masu bi hannu domin ya musguna masu. 2 Ya kashe Yakubu dan'uwan Yahaya da takobi. 3 Bayan da ya ga hakan ya gamshi Yahudawa, sai ya kama Bitrus ma. 4 Bayan ya kama shi, sai ya tsare shi a kurkuku ya kuwa sa sojoji hudu su dinga tsaron sa; yana niyyar kawo shi gaban mutanen a bayan Idin katarewa. 5 To, Bitrus na tsare a kurkuku, amma 'yan'uwa na iklisiya suna yin addu'a ga Allah sosai domin sa. 6 Ana kamar gobe Hiridus zai fitar da shi, a wannan daren, Bitrus yana barci a tsakanin sojoji biyu, daure da sarkoki biyu; sojoji kuma na gadi a bakin kurkukun. 7 Ba zato, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gareshi, haske ya haskaka dakin. Ya taba Bitrus a gefe ya tashe shi kuma ya ce, "Tashi da sauri." Sai ga sarkokin suka zube daga hannunsa. 8 Mala'ikan ya ce masa, "Yi damara ka sa takalmanka." Bitrus kuwa yayi haka. Mala'ikan ce ma sa, "Yafa mayafinka, ka biyo ni." 9 Bitrus kuwa ya bi mala'ikan suka fita waje. Bai gane abin da mala'ikan ke yi zahiri ne ba. Yana zaton ko yana ganin wahayi ne. 10 Bayan da suka wuce masu tsaron fari da na biyu, sun kai kofar da aka yi da karfe wadda ta mike zuwa cikin gari; ta bude masu da kanta. Suka fita sun bi titin, kuma nan take kuma sai mala'ikan ya bar shi. 11 Da Bitrus ya komo hayyacin sa, ya ce, "Hakika yanzu na gane Ubangiji ya aiko da mala'ikansa don ya kubutar da ni daga hannun Hiridus da abin da Yahudawa suke zato." 12 Da ya gane haka, ya zo gidan Maryamu mahaifiyar Yahaya wanda sunan mahaifinsa Markus; masu bi da yawa sun taru a can suna addu'a. 13 Da ya kwankwasa kofar gidan, sai baiwar gidan mai suna Roda ta zo don ta bude kofar. 14 Da ta gane muryar Bitrus, don farin ciki ta kasa bude kofar; maimakon haka, ta koma daki a guje, don ta basu labari Bitrus na tsaye a bakin kofa. 15 Suka ce mata, "Kin haukace." Amma ta nace da cewa haka ne. Suka ce, "Mala'ikansa ne." 16 Amma Bitrus ya ci gaba da kwankwasawa, da suka bude kofar, sai suka ga ai shine, suka sha mamaki kwarai. 17 Bitrus kuwa ya yi masu hannu yana, masu alama su yi shuru. Sai ya gaya masu labarin yadda Ubangiji ya kubutar da shi daga kurkukun. Ya ce, "Ku gaya wa Yakubu da dukan 'yan'uwa abin da ya faru." Sai ya bar su, ya tafi wani wuri. 18 Sa'anda gari ya waye ba karamar hargowa ce ta tashi a cikin sojojin ba, game da abin da ya faru da Bitrus. 19 Bayan da Hiridus ya neme shi kuma bai same shi ba, sai ya tambayi masu tsaron kuma ya bada umarni a kashe su. Sai ya gangara daga Yahudiya zuwa Kaisariya ya yi zamansa a can. 20 Yanzu kuwa Hiridus ya yi fushi sosai da mutanen Taya da Sidon. Suka tafi wurinsa tare. Suka roki Bilastasa, mataimakin sarkin, ya taimake su. Sai suka nemi sasantawa don suna samun abinci daga kasarsa ne. 21 A ranan da aka kayyade, Hirudus ya sha damara da kayan saurata kuma ya zauna akan kursiyi; ya yi masu jawabi. 22 Mutanen suka yi ihu, "Wannan muryar allahce, ba ta mutum ba!" 23 Nan take mala'ika Ubangiji ya buge shi don bai ba Allah daukaka ba, nan take tsutsotsi suka cinye shi har ya mutu. 24 Maganar Allah ta yadu tana ta ribabbanya. 25 Bayan Barnaba da Shawulu sun gama aikin su a Urushalima. Suna dawowa, suka zo tare da Yahaya wanda sunan mahaifinsa Markus ne.
Wannan na ba da wata tsanantawa da aka fara da kisan Yakubu, sa'annan da ɗaurin Bitrus a kurkuku, da kuma sakin sa.
Wannan tarihi ne na Kisan Yakubu da Hiridus yayi.
Wannan na ba da wata sabuwar sashin labarin.
Wato lokacin babban yunwar.
Wannan na nufin cewa Hiridus ya kamo masubi. Duba yadda aka fasara wannan a [5:18] AT: "aike sojoji su kama"
Yakubu da Bitrus ne kawai aka ambata, wannan na nuna kenan cewa su ne shugabanen ikkilisiyar da ke Urushalima
"domin ya ba wa masubi su wahala"
Wannan na nuna yadda aka ƙashe Yakubu.
Wannan na iya nufin 1) Hiridus da kansa ne ya ƙashe shi ko kuma 2) Hiridus ne ya ba da doka cewa a ƙashe shi. AT: "Hiridus ne ya ba da doka sai suka ƙashe shi"
"Da Hiridus ya dago cewa kisan Yakubu ya gamshi shugabanin Yahudawa"
"ya sa shugabanin Yahudawa farin ciki"
"Hiridus ya yi haka" ko kuma "Hakan ya faru ne"
Wannan na nufin lokacin idin adinin keterewa na adinin Yahudawa. AT: "idin lokacin da mutanen Yahudawa sukan ci abinci marar yisti"
sojoji kashi huɗu." ko wane kashi suna na sojoji huɗu da suka yi tsaron Bitrus, kashi ɗaya bayan ɗaya. Suka raba yini ɗaya sau huɗu. A kowane lokaci, sijoji biyu na iya kasacewa da shi a ciki, sai sauran biyun a kofar shiga.
"Hiridus ya shirya ya yanke wa Bitrus hukunci a gaban jama'a" ko kuma "Hiridus ya shirya yanke wa Bitrus hukunci a ganan mutanen Yahudawa"
Wannan na nuna cewa sojojin sun ci gaba da tsare Bitrus a kurkuku. AT: "sojojin suka cigaba da tsaron Bitrus a kurkuku"
AT: "taron masu bi da ke Urushalima suka yi wa Allah addu'a sosai dominsa"
cigaba kuma tare da miƙa kai
Ana iya kara bayyana cewa Hiridus ya yi niyya yă ƙashe shi. AT: "Hakan ya faru ne kamar gobe Hiridus zai fitar da Bitrus daga kurkuku domin hukunci, sa'annan ya ƙashe shi"
"a kafe da sarƙoki biyu." Yana iya zaman cewa kowane sarka na haɗe a hannun masu tsaro da ke tsaye a hago da manar Bitrus.
"na tsaron kofofin kurkukun"
Wannan kalma na jan hankalin mu ne mu kassa hankalin mu ga abin ban mamaki da ke biye da shi.
"kusa da shi" ko kuma "a gefensa"
"cikin ɗakin kurkukun"
"Mala'ikan ya tashe Bitrus" ko kuma "Mala'ikan ya zungure Bitrus." Ba shakka Bitrus yana wata matuƙar barci ne da ya zama lallai mala'ikan ya tashe shi.
Mala'ika ya sa sarkokin suka zuɓe daga hannayen Bitrus ba tare da ya taɓa su ba.
"Bitus kuwa ya yi abinda mala'ikan ya ce yă yi" ko kuma "Bitrus ya yi biyayya"
"Bai fahimci"
AT: "abinda mala'ikan ya yi ya faru da gaske ne ba"
Wannan na nuna cewa sojojin basu iya ganin Bitrus da mala'ikan yayin da suke wucewa su ba. AT: "Masu tsaron kofa na fari da na biyu basu gansu yayin da suke wuce su ba, sa'annan
...
Ana iya fahimci kalmar nan "masu tsaro" daga jimla da ke baya. AT: "da kuma masu tasro na biyun"
"Bitrus da malaikan suka iso ƙofar ƙarfe"
"wanda ke buɗe zuwa cikin birnin" ko kuma "wanda ya miƙe daga gidan kurkukun zuwa cikin garni"
A nan "da kanta" na nufin tsakanin Bitrus da mala'ikan ba wanda ya buɗe ƙofan. AT: "kofar ta yi lilo ta buɗu da kanta" ko kuma "kofar ta buɗe kanta domin su"
"suka yi tafiya a wata titi"
"ya barshi nan da nan" ko kuma "ya ɓace nan da nan"
Wannan karin magana ne. "Da Bitrus ya komo hankalinsa" ko kuma "Da Bitrus ya tuna cewa abinda ya faru zahiri ne"
A nan "hannun Hiridus" na nufin "riƙon Hiridus" ko kuma "shirin Hiridus." AT: "ya cire ni daga mummunan shirin da Hiridus ke da shi dominna.
"ya cece ni"
A nan "Yahudawa" na iya nufin shugabanin Yahudawa. AT: "dukkan abinda Yahudawa sun aza zai faru da ni"
Ya zo ga sanin cewa Allah ya cece shi.
A nan kiran Yahaya ma Markus. AT: "Yahaya, wadda mutane ke kiransa Markus"
"Bitrus ya ƙwanƙwasa." Taɓa ƙofa wata al'ada ne na yau da kullum a Yahudanci da ke sa mutane su san cewa an zo masu fatan ziyara. Kuna iya canza wannan ya yi daidai da al'adan ku.
"ƙofar shiga gidan" ko kuma "ƙofar shiga daga kan titi zuwa hařabar gidan"
Ta zo ƙofar ta tambaya wa ke ƙwanƙwasawa"
"saboda matuƙar farin ciki" ko kuma "cike da farin ciki"
"bata buɗe kofar ba" ko kuma "ta manta ta buɗe kofar"
Ka iya so ma ce "wurga da gudu zuwa cikin ɗaki da ke gidan"
"ta faɗa masu" ko kuma "ta ce"
"tsaye a wajen ƙofar." Har yanzu Bitrus na nan tsaye a waje.
Mutanen ba kadai sun ƙi yarda da ita ba, amma suka tsauta mata cewa tana hauka. AT: "kina hauka"
"ta nace cewa abinda ta faɗa gaskiya ne"
"suka amsa"
"Abinda kin gani, malaikan Bitrus ne." Wasu Yahudwa sun gaskanta da mala'iku masu tsaro, saboda haka me yiwuwa suna ɗaukan cewa mala'ikan Bitrus ne ya zo wurinsu.
Kalmar nan "ci gaba" na nufin cewa Bitrus ya riƙa ƙwanƙwasawa duk loƙacin da mutanen cikin nan suna ta magana.
"faɗa masu waɗannan abubuwan"
"sauran masubi"
"da safe"
A nan amfani ne da wannan jimlar don a nanata zahirin abinda ya faru. AT: "an samu wata babbar hargowa a cikin sojojin game da abinda ya faru da Bitrus"
"Bayan da Hiridus ya neme Bitrus bai iya samun shi ba"
Wannan na iya cewa 1) "da Hiridus ya ji cewa Bitrus ya bata, ya je da kansa ya neme shi a kurkuku" ko kuma 2) "da Hiridus ya ji cewa Bitrus, ya aike sauran sojojin su duba kurkukun."
A mulkin Roma, hukuncin da ake ba wa masu taron kurkuku idan wani daga kurkuku ya gudu shi ne a ƙashe masu gadin gidan kurkukun.
An yi amfani ne da wannan kalmar "ya gangara" domin Kaisariya yana kasa da Yahudiya.
Ba lallai ne ake nufin dukkan mutanen Taya da Sidon sun tafi wurin Hiridus. AT: "Wakilai na mutanen Taya da Sidon sun tafi tare domin su yi tattauna da Hiridus"
"Waɗannan mutanen sun roƙi Bilastasa"
Wannan mataimaki ne ko kuma wani babban jami'in soji na Sarki Hiridus"
"waɗannan mutanen sun nema zaman lafiya"
Mai yiwuwa suna sayan abincin ne ma. AT: "mutanen Taya da Sidon suna sayan dukkan abincin su daga wurin mutanen da Hiridus ke sarautar su ne"
A nan ɗaukan cewa Hiridus ya hana masu abincin ne domin yana fushi da mutanen Taya da Sidon.
Wannan na iya nufin ranan da Hiridus ya sa domin haɗuwa da wakilan. AT: "A ranar da Hiridus ya sa don ya haɗu da su"
tufafi ne masu yawan sada da za su nuna cewa shi ne sarkin.
wato wurin da Hiridus ya shirya ya yi wa mutanen da suka zo ganin sa Jawabi.
"ba da jimawa ba" ko kuma "Yayin da mutanen suna kan yabon Hiridus, mala'ika"
"ya wa Hiridus hari" ko kuma "sa Hiridus ya zama da rashin lafiya sosai"
Hiridus ya bar mutanen nan su yi yi masa sujada a maimakon ya ce masu su yi wa Allah sujada.
A nan "tsutsotsi" na nufin tsutsotsin da ke cikin jiki, maiyiwuwa tsutsosin hanji. AT: "tsutsotsi suka cinye cikin Hiridus har ga mutuwa"
AT: "Maganar Allah kuwa ta bazu zuwa wurare da dama kuma mutane da yawa sun gaskanta da shi."
"sakon da Allah ya aika game da Yesu"
Wannan na nufin lokacin da suka kawo kuɗi daga masu bi da ke Antakiya a [11:29-30]. AT: "suka danka kuɗaden zuwa ga shugabanin ikkilisiyar da ke Urushalima
Suka komo Antakiya daga Urushalima. AT: "Barnaba da Shawulu suka komo Antakiya"
Sarki Hirudus ya kashe Yakubu dan'uwan Yahaya da takobi.
Hirudus ya kama ya kuma sa Bitrus a kurkuku, da niyyar ya kawo shi gaban jama'a bayan Idin.
Taron ta yi naciya da addu'a wa Bitrus.
Bitrus ya bi mala'ika ya wuce masu gadi, kuma ƙofar ta bude da kanta.
Wata baranya mai suna Roda ta amsa ƙofar kuma ta ba da rahoto cewa Bitrus na tsaye a ƙofar, amma ba ta buɗe ƙofar ba.
Da farko sun tsammani Roda mahaukaciya ce.
Bitrus ya gaya masu su fada abubuwan nan ma Yakubu da 'yan'uwan.
Hirudus ya tuhume masu gadin ya kuma yi umurni a kashe su.
Mutane sun yi ihu, "Wanan muryan wani allah, ba ta mutum ba"!
Domin Hirudus bai ɗaukaka Allah ba, mala'ika ya buge shi kuma tsutsotsi suka ta cin sa har ya mutum.
Maganar Allah ta yi girma ta kuma yi yawaita a loƙacin nan.
Barnaba da Shawulu sun ɗauki Yahaya wanda ake kira Markus da su.
1 A cikin iklisiyar da take Antakiya, akwai annabawa da malamai. Sune su Barnabas, Saminu (wadda ake kira Baki) da Lukiya Bakurame da Manayin (wanda aka yi renon su tare da sarki Hiridus mai mulki) da Shawulu. 2 Sa'adda suke bauta wa Allah tare da azumi, sai Ruhu Mai Tsarki ya ce, "Ku kebe mani Barnaba da Shawulu domin aikin da na kiraye su". 3 Bayan taron sun yi addu'a da azumi, sai suka sa masu hannu, su suka sallame su. 4 Sai Shawulu da Barnabas suka yi biyayya da Ruhu Mai Tsarki suka tafi Sulukiya; daga nan suka ketare zuwa tsibirin Kuburus. 5 Sa'adda suke garin Salami, suka koyar da maganar Ubangiji a majami'un Yahudawa, suna kuma tare da Yahaya Markus mai taimakonsu. 6 Bayan sun zaga tsibirin duka har Bafusa, nan suka iske wani Bayahude mai suna Bar-yeshua mai tsafi kuma annabin karya. 7 Wannan mai tsafin wanda ke tare da Makaddas, shi Sarjus Bulus mutum mai basira ne. Wannan kuwa ya kira Shawulu da Barnaba domin yana so ya ji maganar Allah. 8 Amma Elimas "mai tsafi" (fasarar sunansa kenan) ya yi adawa da su; yana so ya baudar da Makaddashin daga bangaskiya. 9 Amma Shawulu wanda ake ce da shi Bulus yana cike da Ruhu Mai Tsarki ya kafa masa ido. 10 Sai ya ce, "Kai dan iblis, kana cike da kowace irin yaudara da mugunta. Kai abokin gabar kowanne irin adalci ne. Ba za ka daina karkata mikakkakun hanyoyin Ubangiji ba? 11 Yanzu ga hannun Ubangiji bisa kanka, zaka zama makaho. Ba za ka ga rana ba nan da dan lokaci." Nan take kuwa sai wani hazo da duhu suka rufe shi ya fara yawo yana neman mutane su yi masa jagora. 12 Bayan da Makaddashin ya ga abin da ya faru ya ba da gaskiya saboda ya yi mamakin koyarwa game da Ubangiji. 13 Bulus da abokansa suka shirya suka ketare a jirgin ruwa daga Bafusa zuwa Firjiya a Bamfiliya. Amma Yahaya ya bar su ya koma Urushalima. 14 Bulus da abokansa suka tafi daga Firjiya zuwa Antakiya na kasar Bisidiya. Nan suka shiga majami'a ran Asabaci suka zauna. 15 Bayan karatun dokoki da annabawa, shugabanin iklisiyar suka tura sako cewa, "'Yan'uwa, idan kuna da wani sakon karfafawa ga jama'a ku fadi." 16 Bulus kuwa ya tashi ya yi alama da hannunsa ya ce, "Mutanen Isra'ila da ku wadanda kuke girmama Allah, ku ji. 17 Allahn Isar'ila ya zabi kakkaninmu ya kuma ribabbanya su sa'adda suke kasar Masar da kuma madaukakin iko ya fito da su daga cikinta. 18 Ya yi hakuri da su a jeji har na tsawon shekara arba'in. 19 Bayan ya hallaka kasashe bakwai a kasar Kan'ana, ya ba kakkaninmu kasar nan gado. 20 Duk wadanan abubuwan sun faru shekaru dari hudu da hamsin da suka wuce. Bayan wadannan, Allah ya ba su alkalai har sai da annabi Sama'ila ya zo. 21 Sai jama'a suka roka a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Saul dan Kish, mutumin kabilar Binyamin ya zama sarki har na tsawon shekara arba'in. 22 Allah kuwa ya cire shi daga kan kujerar sarauta, ya daga Dauda ya zama sarkinsu. A kan Dauda ne Allah ya ce, 'Na sami Dauda dan Yessi, mutumin da zuciyata ke so; zai yi duk abin da nake so'. 23 Daga zuriyar mutumin nan Allah ya fito da mai ceto, Yesu, kamar yadda aka alkawarta zai yi. 24 Wannan ya faru kafin Yesu ya zo, Yahaya ya yi shelar baftimar tuba ga jamma'ar Isra'ila. 25 Sa'adda Yahaya ya gama aikin sa, sai ya ce, 'Wanene ni a tsamanin ku? Ba nine shi ba. Amma ku saurara, akwai wani mai zuwa bayana wanda maballin takalminsa ban isa in kwance ba.' 26 Yan'uwa 'ya'ya daga zuriyar Ibrahim, da wadanda ke bautar Allah a cikinku, saboda mune aka turo sakon ceto. 27 Saboda wadanda ke zaune cikin Urushalima, da masu mulkinsu, ba su gane shi ba, kuma sun cika fadin annabawa da a ke karantawa kowace ranar Asabaci ta wurin kashe shi. 28 Duk da cewa ba su sami dalilin mutuwa a kansa ba, suka roki Bilatus ya kashe shi. 29 Bayan sun gama duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka sauke shi daga giciye suka sa shi a cikin kabari. 30 Amma Allah ya tashe shi daga matattu. 31 Mutanen da suka zo tare da shi daga Galili da Urushalima kuwa suka yi ta ganinsa har kwanaki da yawa. Wadanan mutane kuma sune shaidunsa ga jama'a a yanzu. 32 Mun kawo maku labari mai dadi game da alkawaran da aka yi wa kakkaninmu. 33 Ubangiji ya bar mana alkawaran. Don haka ya ta da Yesu daga matattu. Kamar yadda ya ke a littafin zabura ta biyu: "Kai da na ne yau na zama mahaifinka." 34 Kuma dalilin tayar da shi daga matattu shine saboda kada jikinsa ya rube, ya yi magana kamar haka: "Zan baku albarkun Dauda masu tsarki tabatattu." 35 Wannan shine dalilin da ya yi magana kuma a wata Zabura, 'Ba za ka bar Mai Tsarkinka ya rube ba.' 36 Bayan Dawuda ya yi wa Allah bauta a cikin zuciyarsa da kuma abin da Allah yake so, ya mutu, aka binne shi tare da kakkaninsa, ya kuma ruba, 37 amma wanda Allah ya tayar bai ga ruba ba. 38 'Yan'uwa, ku sani cewa ta wurin mutumin nan aka yi maku wa'azin gafarar zunubai. 39 Ta wurinsa ne duk wanda ya ba da gaskiya zai kubuta daga dukan abin da dokar Musa bata 'yantar da ku a kai ba. 40 Saboda haka ku yi hankali da abubuwan da annabawa suka fada kada su faru a kanku: 41 'Ku masu reni, za ku rude don mamaki, ku kuma shude; saboda ina aiki a cikin kwananakinku, aikin da ba za ku yarda ba ko da wani ya gaya maku." 42 Da Bulus da Barnaba suna fita kenan, sai jama'a suka rokesu, su sake yin irin wannan magana ranar Assabaci mai zuwa. 43 Bayan da sujadar ta kare, Yahudawa da yawa da kuma wadanda suka shiga addinin Yahudanci suka bi Bulus da Barnaba, sai suka gargade su da su cigaba da aikin alherin Allah. 44 Da Asabaci ta kewayo, kusan dukan garin suka taru domin su ji maganar Ubangiji. 45 Sa'adda Yahudawa suka ga taron jama'a, sai suka cika da kishi suna karyata abubuwan da Bulus ya fada suka kuma aibata shi. 46 Amma Bulus da Barnaba sun yi magana gabagadi suka ce, "Dole ne a fara fada maku maganar Allah. Amma da yake kun ture ta, kun nuna baku cancanci rai madawwami ba soboda haka zamu juya ga al'ummai. 47 Don haka Ubangiji ya umarce mu, cewa, 'Na sa ku haske ga al'ummai, saboda ku kawo ceto ga iyakar duniya.'" 48 Da al'ummai suka ji haka, sai suka yi murna suka kuma yabi kalmar Ubangiji. Dukan wadanda aka kaddarawa samin rai madawwami suka tuba. 49 Kalmar Ubangiji kuwa ta bazu a kowanne bangaren yankin. 50 Amma Yahudawan suka zuga wadansu mata masu sujada, masu daraja da kuma shugabannin mazan garin. Wannan ya tayar da tsanani ga Bulus da Barnaba har suka fitar da su daga iyakar garinsu. 51 Amma Bulus da Barnaba suka kade masu kurar kafarsu. Suka tafi garin Ikoniya. 52 Amma almajiran suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.
Luka ya fara faɗin aikin tafiye tafiye da ikkilisiyar Antakiya sun turo Barnaba da Shawulu su je.
Aya 1 na ba da tarihin mutanen da ke ikkilisiyar Antakiya.
"A wannan lokacin a ikkilisiyar da take Antakiya"
Waaɗannan sunayen maza ne
Maniyan mai yiwuwa abikin wasane na Hiridus ko kuma abokin na kusa da suka yi girma tare.
"Zaɓa domin su yi mani aiki"
Wannan na nufin cewa Allah ya zaɓe su domin su yi wannan aiki.
"suka sa wa mutanen nan da Ubangiji ya keɓe domin hidimarsa hannu." Hakan ya nuna cewa shugabanin su amnice cewa Ruhu Mai Tsarki ne ya kiraye Barnaba da Shawulu su yi wannan aiki.
"suka sallame waɗannan mutanen" ko kuma "suka sallame waɗannan mutanen so je su yi aikin da Ruhu Mai Tsarki ya ce su yi"
Wannan kalmar tana sa alamar wani abinda ya faru ne ta dalilin abinda ya bi baya. A wannan hali, Barnaba ne da Shawulu Ruhu Mai Tsarki ya keɓe.
Sulukiya tana kasa da Antakiya.
wata gari ne kusa da teku
Garin salamis tana kan tsibirin Kuburus.
"Maganar Allah" anan karin magana ne da ke nufin "sakon Allah" AT: "Shelar maganar Allah"
Wannan na iya nufin cewa 1) "akwai majami'u da yawa a birnin Salami wurin da Barnaba da Shawulu suka yi jawabi" ko kuma "2) "Barnaba da Shawulu sun fara daga majami'a da ke Salami ne kamun suka ci gaba da bishara a dukkan majami'un da sun samu yayin da suka yi tafiyi a yankin tsibirin Kuburus"
"Yahaya Markus ya je tare da su yana kuma taimakon su"
...
Sun haye daga ɗayan hayin tsibirin suka yada bishara a kowane gari da suka bi.
wata babar birnin da ke tsibirin Kuburus inda muƙaddas suke
A nan "iske" na nufin sun zo wurin ba tare da shirin neman sa ba. AT: "suka haɗu" ko kuma "suka same"
"wani mutum mai yin maita" ko kuma "wani mutum mai da ya gwaninta a yin sihiri"
Bar-yeshua" na nufin "Ɗan Yesu." Babu wani dangartaka tsakanin wannan mutumin da Yesu Almasihu. Ba wuya a samu masu suna Yesu a wannan lokaci.
...
Wato shugaban da ke mulkin lardin Roma. AT: "shugaba"
Wannan ita ce tarihin Sajus Bulus.
"Maganar Allah" wata karin magana ce mai nufin "sakon Allah" AT: "yana so ya ji sako daga Allah"
Wato Bar-Yeshua kenan da akan ce da shi "mai tsafi"
"haka ake kiransa a Hallenanci"
"ya yi gãba da su, ta wurin ƙokarin bauɗar" ko kuma "ya yi ko kuma "ya yi ƙokarin hana su ta wurin"
A nan "bauɗar ... daga" karin magana ne da ke nufin a rinjaye mutum kada ya yi wani abi. AT: "yi ƙokarin rinjayan shugaban ya ki gaskata da wa'azin bishara"
"Shawulu" ne sunar sa a Yahudanci, kuma "Bulus" itace sunar sa a harshen Roma. Dashike yana magana ne da ma'aikacin gwamnatin Roma, ya yi amafani ne da sunarsa a harshen Roma. AT: "Shawulu da ke kiran kansa Bulus"
"ya zuba masa ido"
Bulus yana cewa mutumin yana yi kamar ibilis. AT: "Kai kamar ibilis ne" ko kuma "Kana yi kamar ibilis"
"kana da niyyar sa mutane su gaskanta da abinda ba gaskiya ba ta wurin ƙarya da riƙa aikata abinda ba daidai ba"
A wannan hali na nufin kyuya da rashin rashin ƙwazon bin maganar Allah"
Bulus yana kasa Elimas da ibilis ne. Yadda ibilis yana gãba da Allah, da kuma adalci, haka ma Elima.
Bulus yana amfani ne da wannan tambayan domin ya tsauta wa Elima saboda yin gãba da Allah. AT: "kana riƙa musunta gaskiya game da Ubangiji Allah cewa ƙarya ne"
A nan "miƙaƙƙun hanyoyi" na nufin hanyoyi masu gaskiya. AT: "hanyoyin gaskiya na Allah"
A nan "hannu" na nufin &&&&&&&&&&
AT: "Allah zai sa ka makance"
Elizama zai zama makaho gabaɗaya da ko rana ba zai iya gani ba. AT: "Ko rana ba za ka iya gani ba"
"ba ɗan lokaci" ko kuma "har lokacin da Allah ya zaɓa"
"idanun Elimas suka zama wani iri har sun yi duhu" ko kuma "Elimas ya fara gani kadan kadan har bai iya ganin kome kuma ba"
"Elimas ya ɓata"
"ya ba da gaskiya ga Yesu"
AT: "koyarwa game da Ubangiji ya bashi mamaki kwarai"
Wannan na nuna wata sabuwar bangaren labarin.
"suka yi tafiya a jirgin ruwa daga Paphos"
"iso Firjiya da ke Bamfiliya"
"Amma Yahaya ya bar Bulus da Barnaba"
"birnin Antakiya yana lardin Bisidiya"
"dokoki da annabawa" na nufin bangaren litattafan Yahudawa da aka karana. AT: "Bayan wani ya yi karatu daga litattafan attaura da kuma rubuce rubucen annabawa"
"suka ce wa wani ya faɗa" ko kuma "suka gaya wa wani ya ce"
Mutanen majami'a suna amfani ne da wannan kalma "'yan'uwa" don su nuna cewa Bulus da Barnaba suma Yahudawa ne.
"idan kuna da wani abun faɗi ku ƙarfafa mu"
"muna roƙo ku faɗi" ko kuma "muna roƙo ku gaya mana"
Wannan na iya nufin cewa ya motsa hannun sa yă nuna cewa ya yi shirin yin magana. AT: "ya motsa hannunsa yă nuna cewa zai yi magana"
Wannan na nufin Al'ummai da suka tuɓa zuwa adinin Yahudanci. AT: "ku da ba Isra'ilawa ba amma kuna wa Allah ibada"
"Allah, ku saurare ni" ko kuma "Allah, ku saurare abinda zan faɗa"
"Allahn da mutanen Isra'ila ke bauta wa"
...
"ya sa sun kara yawa sosai"
Wato ƙarfin ikon Allah.
"ya fito da su daga Kasar Masar"
Wannan na nufin "ya jure da su." Wasu juyi suna da wata kalma daban da ke nufin "ya kula da su." AT: "Allah ya jimre da rashin biyayyan su" ko kuma "Allah ya kula da su"
A nan kalmar nan "kasashe" na nufin kungiyoyin mutane dabandaban ba yanki ko iyakar kasa ba.
"ɗauki sama da shekaru 450 da ƙarewa.
"har zuwa lokacin annabi Samaila"
"zama tsarkinsu har na tsawon shekara arba'in"
Wannan ambacin na nufin Allah ya sa Shawulu ya daina zama sarki. AT: "ya ƙi Bulus daga zama sarki"
"sarkin Isra'ila" ko kuma "sarki a bisa Isra'ilawa"
"Allah ya ce game da Dauda"
"na na gãne da cewa"
Wannan furcin na nufin cewa "mutum ne da ke son abinda Ni ma ina so."
"Daga Zuriyan Dauda." An saka wannan a farkon jimalan ne domin a nanata cewa lallai ne mai ceton ya zama wani daga zuriyan Dauda. (Dubi: [13:22])
Wato jama'ar Isra'ila kenan. AT: "ba wa jama'ar Isra'ila"
"kamar yadda Allah ya alkawarta zai yi"
AT: "baftismar yin tuba" ko kuma "baftismar da mutane ke roƙa a masu idan suna so su tuba daga zunubansu"
Yahaya ya yi wannan ta tambayan ne domin ya sa mutane su yi tunanin ko shi wanene. AT: "Yi tunani ko ni wanene"
Yahaya yana magana ne game da Almasihu, wadda a ke zaton zuwansa. AT: "Ba nine Almasihu ba"
Wannan yana nanata muhimmancin maganar da zai biyo baya.
Wato Almasihu kenan. AT: "Almasihu zai zo ba da jimawa ba"
"Ni ban isa in kwance takalminsa ba." Shi Almasihu ɗin ya fi Yahaya daraja har ma bai ji ya isa ya yi mafi kaskancin abu masa ba.
Bulus yana ba da wannan jawabin ga masu sauraronsa tubabbun Yahudawa da Hallenawa ne domin ya tunashe su game da masayinsu ta musamman a matsayin masu bauta wa Allah na gaskiya.
AT: "Allah ya turo da sakon wannan ceton"
AT: "cewa Allah zai cece mutane"
"ba su gãne cewa wannan mutumin Yesu shi ne wanda Allah ya turo yă cece su"
A nan "faɗin" na nufin sakon annabawan. AT: "rubuce rubucen annabawa" ko kuma "sakon annabawan"
AT: "da mutum ke karantawa"
"sun kuwa yi daidai abinda annabawan sun ce za su yi a cikin litattafan annabawan"
"ba su sami wani dalilin da za sa s kashe Yesu ba"
Kalmar "roƙi" anan kalma ne mai ƙarfi da ke nufin a nuna buƙata, roƙo, neman izini.
"Bayan da sun gama yi wa Yesu dukkan abubuwan da annabawa suka ce za su faru da shi"
Za zama da taimako a ce Yesu ya mutu kamun hakan ya faru. AT: "suka kashe Yesu sa'annan suka sauke shi daga giciyen bayan da ya mutu"
...
"Amma" na nuna wata babbar banbanci tsakanin abinda mutanen suka yi da abinda Allah ya yi.
"ya tashe shi daga cikin waɗanda sun mutu." "Yă kasance da mattu na nufin cewa Yesu ya riga ya mutu.
A nan, a tashe shi karin magana ne na sa wanda ya mutu yă rayu kuma. AT: "ya sa shi ya rayu kuma"
Daga cikin dukkan waɗanda sun riga sun mutu. Wannan furucin na bayyana dukkan matattu gabaɗaya da ke karkashin kasa. A tayar da mutum daga cikin su na maganar cewa mutumin na da rai kuma.
AT: "Almajiran da suka yi tafiya tare da Yesu daga Galili zuwa Urushalima suka ga Yesu har kwanaki da yawa"
Mu dai sani daga wasu rubuce rubuce cewa wannan kwanaki 40 ne. Fasara "kwanaki da yawa" da kalmar da zai yi daidai da wannan tsawon lokacin.
"su ne yanzu suna shaida wa mutane game da Yesu" ko kuma "sune yanzu suna gaya wa mutane game da Yesu"
Allah ya cika mana waɗannan alkawaran da ya yi wa kakkanninmu"
"mu" waɗanda muke 'ya'yan kakkanin mu." Bulus yana magana ne da tubabbun Yahudawa da Al'ummai da ke majami'ar da ke Antakiya na garin Pisidiya. Waɗannan su ne kakkanin Yahudawa na jiki, da kuma kakkanin tubabbun a ruhu.
A nan tayar wa wata karin magana ne na sa mutumin da ya mutu ya tashi kuma. AT: "taurin sa Yesu ya tashi kuma"
"Haka aka rubuta a cikin Zabura ta biru"
"Zabura 2"
Waɗanan wasu laƙabi ne da ke bayyana dangartakan da ke tsakanin Yesu da Allah.
"Allah ya yi magana haka game da rayar da Yesu kuma ne domin kada ma yă sake mutuwa kuma"
"tabbacin albarku"
Masu sauraron Bulus na iya fahimtar cewa wannan Zaburan na magane ne game da Almasihu. AT: "A wata Zaburan Dauda, ya yi magana game da Almasihu"
"Dauda ya kuma ce." Dauda ne marubucin Zabura 16 inda aka ruwaito wannan.
AT: "Ba za ka bar jikin Mai Tsarkinka ya ruɓa ba"
Dauda yana magana da Allah ne anan.
"a lokacin da yake ruyuwa"
"ya yi abinda Allah ya so yayi" ko kuma "ya yi abinda ya gamshi Allah"
...
"aka binne shi tare da kakkaninsa da suka mutu"
Wannan jimlar "ya kuma ruɓa" na nufin "jikinsa ya ruɓa." AT: "jikinsa kuwa ya ruba"
"amma Yesu wanda"
A nan a tayar wata karin magana ne da ke sa wanda ya mutu ya yi rai kuma. AT: "Allah ya sa ya rayu kuma"
Wannan jimlar "bai ga ruɓa ba" wata hanya ce na cewa "bai ruɓa ba"
"ku san wannan" ko kuma "wannan na da muhimmanci ku sani"
AT: "cewa mun fada maku cewa ana iya gafarta maku zunuban ku ta wurin Yesu ne"
AT: "cewa Allah na iya gafarta zunubanku"
"Ta wurinsa ne duk mutumin da ya ba da gaskiya" ko kuma "Duk wanda ya ba da gaskiya gare shi"
AT: "Yesu yana kubutar da duk wanda ya ba da gaskiya"
"dukan zunubai"
A nan daukan cewa abinda za su yi hankali da shi itace sakon Bulus. AT: "ku ba da hankalinku ga abinda na faɗa maku"
"saboda abinda da annabawa sun yi magana akai"
"ku 'yan adawa"
...
"ku kuma mutu"
"ina yin wani abu" ko kuma "ina wata hidima"
"a zamaninku"
"In yin wani abu wanda"
"ko da wani ya faɗa maku game da shi"
"Da Bulus da Barmaba suna fitowa kenan"
...
A nan "magana" na nufin jawabin da Bulus ya yi. AT: "wannan jawabin"
Wannan na iya nufin 1) wannan na ƙarin bayyani akan "Da Bulus da Barnaba suna fita kenan" a aya 42 ko kuma 2) Bulus da Barnaba sun bar taron kamun a tashi, sa annan wannan ya faru ne nan gaba.
Waɗannan ba Yahudawa ba ne amma sun tuba zuwa adinin Yahudanci.
"sai Bulus da Barnaba suka yi magana da su suka gargaɗe su"
Ana ɗaukan cewa sun gaskanta ne da jawabin Bulus cewa Yesu Almasihu ne. AT: "da su cigaba da gaskanta cewa Allah yana gafarta zunuban mutane saboda abinda Yesu ya yi ne"
"garin" anan na madadin jama'ar da ke garin. Wannan jimlar na nuna matukar shigar kalmar Ubangiji a wannan gari. AT: "kusan duka mutanen garin"
Ana ɗaukan cewa Bulus da Barnaba ne suka yi maganar Ubangiji. AT: "domin su saurare Bulus da Barnaba suna magana game da Ubangiji Yesu"
A nan "Yahudawa" na nufin shugaban Yahudawa. AT: "shugaban Yahudawa"
A nan ana maganar kishi kamar wani abu ne da ke iya cika mutum. AT: "suka zama da kishi"
"musunta" ko kuma "yi gãba"
...
Ana ɗaukan cewa Allah ya umarta ayi haka. AT: "Allah ya Umarta"
AT: "maganar Allah" anan na nufin "sako daga Allah" AT: "mu fara faɗa maku wannan sako daga Allah tukuna" ko kuma "mu fara faɗa maka wannan maganar Allah tukuna"
"kun nuna baku cancanci rai na har abada ba" ko kuma "kuna yi kamar baku cancanci rai madawwami ba"
"za mu tafi gun Al'ummai" Bulus da Barnaba suna cewa za su kai wa Al'ummai bishara. AT: "za mu bar ku mu fara wa Al'ummai bishara"
Ana maganar gaskiya game da Yesu ne kamar wani hasken wuta ne da mutane ke iya gani.
Kalmar nan "iyaka" na nufin ko ina. AT: "gaya wa mutane da ke ko ina a cikin duniya cewa ina so in cece su"
Kalmar nan "iyaka" na nufin ko ina. AT: "gaya wa mutane da ke ko ina a cikin duniya cewa ina so in cece su"
A nan "kalmar" na nufin sako game da Yesu da suka gaskata da shi. AT: "suka kuma yabi Allah don sakon da suka ji game da Ubangiji Yesu"
AT: "Dukan waɗanda Allah ya kaddarawa samin rai na har abada sun gaskata" ko kuma "Dukan waɗanda Allah ya zaɓa su sami rai madawammi"
A nan "kalmar" na nufin sako game da Yesu. AT: "Waɗanda sun gaskanta suka yada kalmar Ubangiji zuwa ko ina a yankin" ko kuma "Waɗanda sun gaskanta suka tafi ko ina a yankin suna gaya wa mutane sakon Yesu"
"shawo kan" ko kuma "yaudare"
"mutane mafi daraja"
"Suka shawo kan shugabannin maza da mata su tsananta wa Bulus da Barnaba"
"suka fitar da Bulus da Barnaba daga garinsu"
Wannan alama ce na nuna wa marasabin cewa Allah ya ƙi si kuma zai hukunta su.
Wannan na iya nufin sabobin tuɓa da ke garin Antakiya a garin Fisidiya wurin da Bulus da Sila suka fito bari.
Taron a Antakiya suna yi wa wa Ubangiji ibada da yin azumi da Ruhu Mai Tsarki ya yi magana da su.
Ruhu Mai Tsarki ya gaya masu su keɓe Barnaba da Shawulu su yi aiki wanda Ruhu na kiran su a kai.
Taron su yi azumi, da addu'a, sun kuma sa hannu a Barnaba da Shawulu, suka kuma salleme su.
A Kubrus, Yahaya Markus na nan da su kamar mataimakin su.
Bar-yashu'a Bayahude ne, annabi mai karya wani maƙaddas.
Maƙaddas ya kira Barnaba da Shawulu domin ya so ya ji maganar Allah.
An san Shawulu kuma da Bulus
Bulus ya gaya ma Bar-yashu'a cewa zai makance har wani loƙaci.
Maƙaddas din ya ba da gaskiya.
Yahaya Markus ya bar Bulus da abokansa ya koma Urushalima.
A Antakiya ta ƙasar Basidiya, an tambai Bulus ya yi magana a majami'an Yahudawa.
A jawabin Bulus, Bulus ya ce Allah ya zaɓi Isra'ilawa.
Daga Sarki Dauda Allah ya kawo ceto ma Isra'ila.
Bulus ya ce Yahaya ma Baftisma ya shirya hanya ma Ceto mai zuwa.
Mutanen da kuma shugabanni a Urushalima sun cika saƙonnin annabawa ta hukuntar da Yesu zuwa mutuwa.
Mutanen da sun gan Yesu bayan da ya tashi daga matattu sun zama shaidun sa yanzu.
Allah ya nuna cewa ya cika alkawarinsa da Yahudawa da ya ta da Yesu daga matattu.
Allah ya yi alkawari cewa Mai Tsarki ba zai gan ruɓa ba.
Bulus ya yi shelar gafarar zunubai ma kowa da ya ba da gaskiya a cikin Yesu.
Bulus ya gargaɗi masu sauraran sa kadda su zama kamar wanda annabawa sun yi maganar a kai wanda sun ji sanarwar aikin Allah, amma ba su ba da gaskiya ba.
Kusar duk birnin suka hallar su ji maganar Allah a Asabar da ta kewayo.
Yahudawan sun cika da kishi sun kuma yi musun sakon Bulus, suna zaginsa.
Bulus ya ce Yahudawan suna tura maganar Allah da an yi masu.
Al'ummai suka yi murna, sun kuma yabi maganar Ubangiji.
Waɗanda aka ƙaddara wa samun rai madawwami su ka ba da gaskiya
Yahudawa suka haddasa tsanani ga Bulus da Barnaba, suka kore su daga ƙasarsu.
Bulus da Barnaba suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaida a kan ƙarsar Antakiya waɗanda suka kore su.
1 A lokacin da Bulus da Barnaba sun shiga garin Ikoniya suka shiga majami'an Yahudawa suka yi wa'azi yadda har mutane da yawa daga cikin Yahudawa da Hellinawa suka ba da gaskiya. 2 Amma Yahudawa da basu yi biyayya ba, suka zuga al'umman har suka yi fushi da 'yan'uwan. 3 Suka zauna a wurin na tsawon lokaci, suna yni maganarsu gabagadi da ikon Ubangiji, yana kuma shaidar sakon alherinsa. Ya yi wannan ta wurin alamu da al'ajibai ta hannun Bulus da Barnaba. 4 Saboda haka mutanen garin sun rabu: wadansun su suka bi ra'ayin Yahudawa, wasu kuwa sun bi manzannin. 5 Al'umman garin da Yahudawa sun nemi jan hankali shugabanninsu, don su wulakanta Bulus da Barnaba, su jajjefe su, 6 da suka gane haka suka gudu zuwa biranen Likoniya, Listira da Darbe, da garuruwa wadanda ke kewaye da su, 7 a can suka yi wa'azin bishara. 8 A Listira akwai wani wanda ke zaune bai taba tashi da kafafunsa ba, don shi gurgu ne tun daga haihuwa. 9 Wannan mutumin ya ji Bulus yana magana. Bulus ya kafa masa ido, ya gane mutumin na da bangaskiya da za a warkar da shi. Sai ya ce masa da murya mai karfi, "Tashi ka tsaya akan kafafunka" 10 Sai mutumin ya yi tsalle ya fara tafiya da kafafunsa, yana yawo. 11 Da jama'an garin sun ga abin da Bulus ya yi, suka tada muryarsu suna cewa da Likoniyanci, "Ai alloli sun ziyarce mu daga sama, da kamanin mutane." 12 Suna kiran Barnaba da sunan "Zafsa," Bulus kuwa suka kira shi da sunan "Hamisa" domin shine yafi yin magana. 13 Sai firist din zafsa wanda dakin yin masa sujada na kofar birni; ya kawo bijimai biyu da furannin da aka saka su kamar gammo; shi da jama'arsa suna so su yi masa hadaya. 14 Amma da manzannin, wato Barnaba da Bulus, su ka ji labarin, suka yage rigunansu, suka hanzarta zuwa gun taron mutanen. 15 Suna ta cewa, "Kuji! Ku mutane don me kuke wannan abin? Mu fa mutane ne kamarku. Mun kawo maku labari mai dadi ne, da cewa, ku rabu da abubuwa marar amfani, ku koma ga Allah mai rai, wanda ya hallici sama da kasa da teku da dukan abubuwa da ke cikinsu. 16 A da dai ya bar mutane su yi abinda suka ga dama. 17 Duk da haka, bai bar kansa ba tare da shaida ba, don yana bada abubuwa masu kyau, yana ba ku ruwan sama, lokatai masu albarka, ya cika ranku da abinci da farin ciki." 18 Duk da wadannan kalmomin da kyar, Bulus da Barnaba suka iya tsayar da su daga yi masu hadaya. 19 Amma wasu Yahudawa daga Antakiya da wasunsu daga Ikoniya suka rinjayi tarun jama'ar. Suka jajjefi Bulus suka ja shi zuwa wajen garin, suna ganin kamar ya mutu. 20 Duk da haka da almajirai suka kewaye shi a tsaitsaye, sai ya tashi ya koma cikin garin. Washegari, ya tafi Darba tare Barnaba. 21 Bayan sun yi wa'azin bishara a wannan birnin suka kuma sami almajirai da yawa, suka dawo Listira, da Ikoniya da Antikiya. 22 Suna karfafa zuciyar almajiran su rike bangaskiyarsu, su ci gaba da ita, suna ce masu, "Ta wurin jimrewa mai yawa zamu shiga mulkin Allah, don haka dole ne mu sha wahala." 23 Da suka zabar masu dattawa a kowace iklisiya, sai suka yi addu'oi da azumi, suka mika su ga Ubangiji, ga wanda suka gaskanta a gareshi. 24 Sa'annan sun bi ta Bisidiya suka kai Bamfiliya. 25 Da suka yi maganarsu a Biriya, sun wuce zuwa har Italiya. 26 Ta jirgin ruwa zuwa Antakiya, a nan ne aka mika su ga alherin Allah don aikin da suka gama a yanzu. 27 Da isowarsu Antakiya sun tara 'yan iklisiya a wuri daya, sun ba da labarin dukan abin da Allah ya yi ta wurinsu. Da yadda Ya bude kofa a wurin al'ummai ta bangaskiya. 28 Sun zauna tare da almajiran na tsawon lokaci.
An cigaba da ba da labarin Bulus da Barnaba a Ikoniya.
Wannan na iya nufin 1) "Sai ya kasance a garin Ikoniya cewa" 2) A garin Ikoniya kamar yadda aka saba"
"suka yi magana da ƙarfi sosai" Yana da taimako idan a sanar da cewa sun yi magane ne game da Yesu. AT: "suka yi magane game da Yesu sosai"
Wannan na nufin wasu Yahudawa da basu gaskanta da bisharar Yesu ba.
suka sa su fushi da abinda ake faɗi
aka zuga al'umman
A nan "'yan'uwan na nufin Bulus da Barnaba da kuma sabobin tuba.
"Duk da haka sun zauna a wurin" Bulus da Barnaba sun zauna a Ikoniya sun taimaki jama'a da dama da suka ba da gaskiya a [14:1]. Idan "Duk da haka" zai kawo wani rikicewa a harshen ku, ana iya cire shi kawai.
"ya nuna cewa sakon alherinsa gaskiya ne"
"game da sakon alherin Ubangiji"
AT: "ta wurin iza Bulus da Barnaba su yi alamu da al'ajibai"
A nan "hannu" na nufin ta koƙarin mutane biyun nan bisa ga bishewar Ruhu Mai Tsarki. AT: "ta hiddimar Bulus da Barnaba"
AT: "yawancin mutanen garin sumka raɓu" ko kuma "yawancin mutanen garin basu yařda da juna ba"
"suka goyi bayan Yahudawa" ko kuma "suka yarda da Yahudawa." Taron farin da aka ambata basu karɓi sakon alherin ba.
Taron na biyun da aka ambata sun karɓi sakon alherin. AT: "suka goyi bayan manzaninnin"
Wato Bulus da Barnaba kenan. Anan ana iya ce da "manzannin" "waɗanda aka aiko"
"su yi koƙarin rinjayan shugabannin Ikoniya." Anan "nemi" na nufin cewa basu iya jan hankalin su gabaɗaya kamun manzannin suka bar garin ba.
"don su daka Bulus da Barnaba su kuma ƙashe su ta wurin jefin su da wuwatsu"
Wata lařdi a Ƙaramar Asiya
Wata birni a Karamar Asiya kudancin Ikonoya kuma arewacin Darbe
Wata birnin a Karamar Asiya kudancin Ikoniya da listira
Bulus da Barnaba ma sun yi wa'azzin bishara a can"
Bulus da Barnaba suna kasar Listira yanzu.
Wannan na gabatar da wata sabuwar mutum kenan a labarin.
"ba ya iya motsa ƙafofinsa" ko kuma "ba ya iya tafiya da ƙafafunsa ba"
"an haife shi shi gurgu ne"
mutumin da ba ya iya tafiya da ƙafafu
"Bulus ya zuba masa ido"
Ana iya fasara "bangaskiya" anan da "gaskanta." AT: "ya gaskanta cewa Yesu zai iya warkar da shi" ko kuma "ya gaskanta cewa Yesu zi iya ba shi lafiya" (Dubi: and
"ya tashi sama." Wannan na nufin cewa ƙafafunsa sun warke sarai.
Wato warkar da gurgun kenan.
A tada murya na nufin a yi magana da ƙarfi. AT: "suka yi magan da ƙarfi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)
Jama'an da yawa suka gaskanta cewa Bulus da Barnaba allolin al'ummai ne suka sauka musu daga sama.AT: "Ai alloli sun Sauka mana daga sama"
a nasu harshen Likoniya." Mutanen Listira suka iya yin Likoniyanci da kuma Girka.
Waɗannan mutanen sun gaskanta cewa lallai ne allolin sun canza kamanin su domin su zama kamar sauran mutane.
Zasfa shi ne tsarki bisa dukkan sauran allolin al'ummai.
Hamisa shi ne wani allahn al'ummai da ke kawo saƙonni daga wurin Zasfa da sauran alloli.
Zai zama da taimako a kara takamaimain bayani akan wannan firist. AT: "Akwai wata haikali da mutane ke ɓautar Zasfa a ƙofar shiga garin. Da wannan firist da ke hidima a haikalin ya ji abinda Bulus da Barnaba suka yi, ya kawo"
Bijimain na hadaya ne. Furannin na na yi wa Bulus da Barnaba kamar gammo ne akai ko kuma a sa a bisa bijimain hadayan.
"Ƙofofin birane sukan zama wurin taron mutanen gari ne gaba ɗaya.
"suna so su yi wa Bulus da Barnaba hadaya a madadin alloli Zasfa da Hamisa"
Maiyiwuwa Luka anan yana moran "manzannin" kamar yadda akan moranshi wa "ɗan aika."
Wannan alama ce na nuna matuƙar bakin ciki da rashin gamsuwar su cewa taron suna so su yi masu hadaya.
Barnaba da Bulus suna tsauta wa mutanen ne saboda hadaya da suke so su yi masu. AT: "Ku Mutane, kada ku ya haka!"
"mana sujada"
Da haka, Barnaba da Bulus suna cewa su ba alloli ba kenan. AT: "Ai muma 'yan adam ne kamarku. Mu ba alloli ba ne!"
"kama da ku ta kowane yanayi"
A nan "rabu da ... ga" na karin maganan ne da ke nufin a daina yi wani abu, a kuma fara yin wani abu dabam. AT: "ku daina ɓauta wa allolin ƙarya da ba za su iya taimakonku ba, a maimakon haka, ku fara bauta wa Allah mai rai
"Allag da ke rayayye da gaske"
"a lokatai da suka wuce" ko kuma "har sai yanzu"
Wato su yi rayuwar kansu. AT: "su yi rayuwa yadda ya gamshe su" ko kuma "su yi duk abinda suke so su yi"
AT: "Allah ya bar shi da shaida" ko kuma "Allah ya shaida"
"kamar yadda yakke a fili"
A nan "ranku" na nufin mutanen. AT: "yana baku isheshen abubuwan ci da kuma sa kawo farin ciki"
Bulus da Barnaba suka hana taron daga yi masu hadaya, amma basu same hakan da sauki ba.
"sun sha wuya a tsayar da su"
Zai zama da taimako a faɗi abinda suka rinjayi taron su yi. AT: "suka rinjayi jama'ar don kada su gaskanta da Bulus da Barnaba, amma su yi masu tawaye.
Ba lallai ne wannan su zama wannan taron da aka yi maganar su a iya da ta gabata ba. Domin akwai ɗan banbancin lokaci a tsakani, kuma wannan na iya zama su wani taro ne dabam gabaɗaya.
"domin suna gani kamar ya riga ya mutu"
Wato sabobin tuɓa kenan da ke garin Listira.
"Bulus suka sake shiga garin Listira tare da masubin"
"Bulus da Barnaba suka tafi garin Darba"
"Darba" (Dubi: [Acts 14:20])
A nan "zuciyar" na nufin almajiran. Wannan na nanata yadda suke ji da kuma imaninsu. AT: "Bulus da Barnaba sun ƙarfafa masubin su cigaba da gaskanta da sakon Yesu" ko kuma "Bulus da Barnaba suka ƙarfafa masubin su cigaba da girma ƙwarai a ɗangartakarsu da Yesu"
"da ƙarfafa masubin su cigaba da dogara ga Yesu"
"Da Bulus da Barnaba suka zaɓa shugabanni a kowace sabuwar taron masubi"
Wannan na iya nufin 1) "Bulus da Barnaba suka miƙa dattawa da suka zaɓa" ko kuma 2) "Bulus da Barnaba suka ɗanka shugabannin da sauran masubi"
"su" anan ya ɗangarta ga zaɓin da kun yi na ma'annar "na su" a jimlar da ta gabata na abinda ake nufi (ko dattawa ko shugabanni, da kuma sauran mutane)
"Magana" anan na nufin "Maganar Allah." AT "Da suka yi maganar Allah a Bariyata"
Ataliya yana kasa da Bariyata.
AT: a nan ne masubi da ke garin Antakiya suka miƙa Bulus da Barnaba ga alherin Allah" ko kuma "anan ne mutanen Antakiya suka yi addu'a Allah ya kiyaye ya kuma tsare Bulus da Barnaba"
"suka kirkiro masubi suka taru a haɗu tare"
Ana maganar yadda Allah ya ba wa Al'ummai zarafi su gaskanta kamar ya buɗe wata ƙofa ne da tun can yana hana su shiga cikin bangaskiya. AT: "Allah ya mai da shi abu mai yiwuwa Al'ummai su gaskanta"
Yahudawa marar bi sun zuga zuciyar al'ummai suka kuma ɓata tsakanin su da 'yan'uwa.
Allah ya ba da shaida a kan sakon alherin sa ta bayar da alamun da abubuwan al'ajabi ta hannun Bulus da Barnaba.
Waɗansu Al'ummai da Yahudawa suka tasar wa shugabanninsu su wulakanta su, su kuma jejjefe Bulus da Barnaba.
Bulus ya warkar da wane mutum wanda gurgu ne tun aka haife shi.
Barnaba da Bulus sun kyekketa tufafinsu, suka ruga cikin taron, sun daga murya suna cewa mutanen su juyo daga abubuwan banza zuwa Allah mai rai.
Allah ya ba al'ummai ruwan sama da damuna mai albarka, yana ƙosar da zuciyar su da abinci da kuma murna.
Mutanen so yi hadaya ta wurin firistoci Rhea ma Bulus da Barnabas.
Taron da suna Listira sun jejejfe Bulus suka kuma ja shi bayan gari daga baya.
Bulus ya tashi ya shiga birnin.
Ta hanyar shan wuya ne Bulus ya ce almajirai tilas su shiga cikin mulkin Allah.
A kowaee toro, Bulus da Barnabas sun zaɓa dattawa, addu'a da azumi, suka danƙa masu bi ga Ubangiji.
Da suka dawo Antakiya, suka ba da rahoto duk abubuwan da Allah ya yi da su, da kuma yadda ya buɗe ƙofar bangaskiya ma Al'ummai.
1 Wadansu mutane suka zo daga Yahudiya suka koyar da 'yan'uwa, cewa, "Idan ba yi maku kaciya bisa ga al'addar Musa ba, ba za ku sami ceto ba." 2 Da Bulus da Barnaba suka tunkare su da mahawara, sai 'yan'uwa suka yanke shawara Bulus da Barnaba da wasu su je Urushalima wurin manzanni da dattawa a kan wannan magana. 3 Da shike iklisiya ce ta aike su, sai suka bi ta Finikiya da ta Samariya suka sanar da tuban al'ummai. Ya kawo murna mai yawa a wurin 'yan'uwa. 4 Bayan sun zo Urushalima, sai iklisiya da manzanni da dattawa, suka marabce su, sai suka fada masu abin da Allah ya yi ta wurinsu. 5 Amma wadansu mutane wadanda suka ba da gaskiya daga cikin Farisawa, suka tashi suka ce, "Dole ne a yi masu kaciya a kuma umarce su su kiyaye dokar Musa." 6 Sai manzanin da dattawan suka taru don su duba wannan lamari. 7 Bayan mahawara mai tsanani, sai Bitrus ya tashi ya ce masu, "'Yan'uwa, kun san lokacin baya da ya wuce, Allah ya yi zabi a cikinku, cewa ta bakina ne al'ummai za su ji bishara, su kuma ba da gaskiya. 8 Allah, wanda ya san zuciya, ya yi masu shaida, ya kuma basu Ruhu Mai Tsarki kamar yadda ya yi mana; 9 kuma bai bambanta mu da su ba, ya tsabtace zuciyarsu ta wurin bangaskiya. 10 To, saboda haka don me kuke gwada Allah, kuna sa wa almajirai nauyi a wuya wanda ubanninmu duk da mu ba mu iya dauka ba? 11 Amma mun gaskanta za mu samu ceto ta wurin alherin Ubangiji Yesu, kamar yadda suke." 12 Dukan taron jama'ar suka yi shiru sa'adda suke sauraron sakon shaidar da mamakin abin da Allah ya yi ta wurin Bulus da Barnaba a cikin al'ummai. 13 Bayan sun gama magana, Yakubu ya amsa, ya ce, "'Yan'uwa, ku ji ni. 14 Saminu ya fada yadda Allah ya fara nuna jinkai ga al'ummai domin ya dauke jama'a daga cikinsu domin sunansa. 15 Maganar annabawa ta yarda da wannan, kamar yadda yake a rubuce, 16 'Bayan wadannan abubuwa zan dawo, zan gina gidan Dauda wanda ya fadi kasa; in sake gina bangonsa, in tsayar da shi, 17 saboda sauran jama'a su nemi fuskar Ubangiji, har da al'ummai da ake kira da sunana. 18 Wannan shine abin da Ubangiji ya fadi, shi wanda ya yi wadannan abubuwa da aka sani tun zamanin da. 19 Saboda haka, a gani na kada mu matsa wa al'umman da suka juyo gun Allah; 20 amma zamu rubuta masu da cewa, su guje wa gumaka da zina da faskanci da maye da cin mushe. 21 Tun zamanin da akwai mutane a kowanne birni wadanda suke wa'azi da karatun Musa a majami'u kowanne Asabaci." 22 Sai ya yi wa manzanin kyau su da dattawa da dukan iklisiyar su zabi Yahuza da Barnaba da Sila da dattawan iklisiya a tura su Antakiya tare da Bulus da Barnaba. 23 Sai suka rubuta wasika, "Manzani da dattawa da 'yan'uwa zuwa ga al'ummai 'yan'uwa a Antakiya da Suriya da Kilikiya, gaisuwa mai yawa. 24 Mun ji cewa wasu mutane daga cikinmu wadanda ba mu umarce su ba, sun fita daga cikinmu sun yi maku koyarwar da ta daga maku hankali. 25 Ya yi kyau da dukanmu, muka amince mu zabi wadansu mutane mu tura su wurinku tare da Bulus da Barnaba, 26 mutane wadanda suka sadaukar da ransu domin sunan Ubangiji Yesu Almasihu. 27 Mun aika Yahuza da Sila su gaya maku wadannan abubuwa. 28 Saboda haka ya yi kyau Ruhu Mai Tsarki da mu, kada mu sa maku nauyi fiye da wadannan abubuwan: 29 ku bar yi wa gumaka hadaya, ku bar cin mushe da shan kayan maye da zina da faskanci, in kun kiyaye wadannan abubuwa za ku zauna lafiya. Ku huta lafiya." 30 Da aka sallame su, sai suka je Antakiya. Bayan sun tara jama'a sai suka ba su wasikar. 31 Bayan da suka karanta ta, sai suka yi murna sosai saboda karfafawa. 32 Yahuza da Sila, da shike su annabawa ne, suka karfafa 'yan'uwa da kalmomi masu yawa. 33 Bayan sun yi kwananki a wurin, sai aka sallame su zuwa wurin 'yan'uwa wadanda suka aiko su. 34 Amma ya gamshe Sila ya zauna a wurin. 35 Amma Bulus da Barnaba suka tsaya a Antakiya da sauran 'yan'uwa, suna koyar da maganar Ubangiji. 36 Bayan kwanaki kadan Bulus ya ce ma Barnaba, "Mu koma yanzu mu ziyarci dukan 'yan'uwa da muka yi masu bisharar Ubangiji, mu ga yadda suke. 37 Barnaba yana so su dauki Yahaya wanda kuma ake kira Markus. 38 Amma Bulus ya yi tunanin bai kamata a tafi da Markus ba, tun da ya bar su a Bamfiliya bai ci gaba da su ba. 39 Nan jayayya ta tashi tsakaninsu, har suka rabu da juna sai Barnaba ya tafi tare da Markus suka ketare zuwa Kuburus. 40 Amma Bulus ya zabi Sila suka tafi, bayan 'yan'uwa sun yi masu addu'ar alherin Allah ya kiyaye su. 41 Bulus ya tafi ya zazzaga Suriya da Kilikiya yana ta karfafa iklisiyoyin.
Bulus da Barnaba suna nan a garin Antakiya yayin da aka samu wata jayayya game da Al'ummai da kaciya.
"waɗansu mutane." Ana iya kara bayyana wannan a fili cewa waɗanan mutanen Yahudawa ne da suka gaskanta da Yesu.
Yahudiya yana ɗan sama da Antakiya.
A nan 'yan'uwa na matsayin masubin Almasihu. Ana ɗaukan cewa suna Antakiya ne. AT: "suka koyar wa masubi da ke Antakiya" ko kuma "suna koyar da masubi a Antakiya"
AT: "saida an yi maku kaciya bisa ga al'adar Musa, Allah ba zai cece ku ba" ko kuma "Allah ba zai cece ku daga zunubanku ba sai kun yi kaciya bisa ga shari'ar Musa"
Ana iya kara bayannin kalamun nan "ƙaramar gardama" da "muhawara" a fili. AT: "suka tunkare su da muhawara tare da Mutanen Yahudiya"
Urushalima yana sama da kusan ko wane wuri a Isra'ila, saboda haka, daidai ne Isra'ilawan su yi maganar haurowa zuwa Urushalima.
"wannan zancen"
A nan kalaman nan "Su", "su", sa kuma "na su" na nufin Bulus, Barnaba, da dai irin sauransu. (Dubi: [Acts 15:2])
AT: "Da shike taron masubi ne suka aike su daga Antakiya zuwa Urushalima"
A nan "ikkilisiya" tana nufin jama'ar ikkililsiya.
Kalamun nan "suka bi" da "suka nanar" na nuna cewa sun ɗan zauna na wasu lokatai a a wurare daban daban suna ba da bayyani filla-filla na abinda Allah ke yi.
Kalmar nan "tuɓa" na nuna cewa Al'ummain sun fara ƙin allolin su na ƙarya suna gaskanta da Allah. AT: suka sanar wa taron masubi a waɗannan wurare cewa Al'ummai ma suna gaskanta da Allah"
Ana maganar yadda sakonsu ya sa 'yan'uwan murna ne kamar ita "murna" ɗin wata abu ne da ake iya ɗauko suka kawo wa 'yan'uwan. AT: "Abinda suka faɗa ya sa masubin su yi farin ciki"
wato masubi.
AT: "manzannin, dattawa, sa sauran taron masubi suka marabace su"
"ta wurinsu"
A nan, Luka yana bambanta waɗanda sun gaskanta cewa ana iya samun ceto ta wurin Yesu ne kadai da kuma waɗanda suka gaskanta cewa ceto ta wurin Yesu ne da kuma kaciya kamun a sami ceto.
"su yi biyayya da dokar Musa"
Shugabannin Ikkilisiyar suka tattauna ko Al'ummai ɗin suna buƙatar a yi masu kaciya da kuma su kiyaye dokar Musa kamun Allah ya ceci su daga zunubansu.
Bulus yana magana ne da dukkan masubi da ke kasancewa a wurin.
A nan "baki" na nufin Bitrus. AT: "daga gareni" ko kuma "ta wurina"
"yakamata al'ummai su ji"
AT: "bisharar Yesu"
A nan "zuciya" na nufin "ainihin tunanin 'yan'adam." AT: "wanda ya san tunanin 'yan'adam" ko kuma "wanda ya san abinda mutane ke tunani"
"ya yi wa Al'ummai shaida"
"ya sa Ruhu Mai Tsarki ya sauko a kan su."
Allah bai bi da Yahudawa masubi da dabam da Al'ummai masu bi ba.
Ana maganar gafarar zunuban da Allah ya yi wa Al'ummai ne kamar yadda ake tsabtace wani abu. A nan "zuciya" na nufin ainihin tunanin mutum. AT: "ya gafarta masu domin sun gaskanta da Yesu"
Wannan bata nufin "a daidai wannan lokaci," amma ana amfani ne da ita domin a jawo hankalinmu zuwa ga wat abu mai muhimmanci da ya biyo baya.
Bitrus yana amfani ne da wannan tambayan domin ya gaya wa Yahudawa masubi cewa kada su buƙaci waɗanda ba Yahudawa ba su yi kaciya kamun su samu ceto. AT: "Kada ku gwada Allah ta wurin nauyaya wa masubi da ba Yahudawa ba da nauyi da mu Yahudawa ba iya ɗuka ba!"
Wato kakkaninsu Yahudawa.
AT: "Amma mun gaskanta cewa Ubangiji Yesu zai cece mu ta wurin alherinsa, kamar yadda ya cece waɗanda ba Yahudawa ba."
"Kowa" ko kuma "Kungiyar gaba ɗaya" (See: [Acts 15:6])
"Allah ya sa"
"'yan'uwa masubi, ku ji." Mai yiwuwa Yakubu yana magana da Maza ne kadai.
"saboda yă zaɓi jama'a daga cikinsu"
"domin sunan Allah." Anan "suna" na nufin Allah. AT: "domin kansa"
A nan "magana" na nufin sakon. AT: "Abinda annabawa sun faɗa ta yarda" ko kuma "Annabawa sun yarda"
"tabbata da wannan gaskiyar"
AT: "kamar yadda suka rubuta" ko kuma "kamar yadda Annabi Amoz ya rubuta tun da daɗe wa"
Wannan na maganar zabe da Allah zai sãke yi daga zuriyar Dauda domin ya yi mulki a bisa mutanensa kamar yana sãke shirya wata gida ne da ya riga ya rushe.
A nan "gida" na nufin Iyalin Dauda.
Wannan na magana ne game da yadda mutane ke son yi wa Allah biyayya da kuma kara koya game da shi kamar suna neman sa ne.
A nan "jama'a" sun haɗa da maza da mata. AT: "sauran mutane"
Allah yana magana game da kansa ne, amma ya yi kamar akwai mutum na uku da yake magana akai. AT: "su nemi fuska ta, Ubangiji"
AT: "a haɗe da dukkan Al'ummai da suke nawa"
A nan "sunana" na nufin Allah.
AT: "da jama'a sun sani"
Ana iya kara bayyanan a fili dalilin da ya sa Yakubu ba ya so a matsa wa Al'umman. AT: "kada mu umarci Al'umman su yi kaciya su kuma kiyaye dokokin Musa"
Ana maganar mutumin da ya fara biyayya da Allah ne kamar anan iya ganin yadda mutumin ya juya ga Allah.
Zina da fasikanci, cin abinda aka maƙure, da kuma cin nama tare da jini suna cikin bukukkuwan bautar gunakai da allolin ƙarya.
Wannan na iya nufin cin namar wata dabba da wani ya miƙa hadaya ga wata gunki ko wani abinda ya shafe bautar gumaka.
Allah bai yarda Yahudawa su ci nama da ke da jini a cinkinta ba. Haka ma, ko Musa daga rubuce rubucen sa a littafin Farawa, Allah ya haramta shan jini. Sabodahaka, ba za su iya cin wata dabba da wani ya maƙure ba domin ba a janye jini daga namar dabban yadda ya kamata ba.
Yakubu na nufin cewa Al'ummai sun san muhimmancin waaɗnnan dokokin domin Yahudawa sun yi jawabin su a kowani birnin da ke da majami'a. Anan ɗaukan cewa Al'ummai ma suna iya zuwa gun malamain majami'u don karin bayyani game da waɗannan dokokin.
A nan "Musa" na nufin littattfen shari'ar Musa. AT: "An yi shelar shari'ar Musa" ko kuma "Yahudawa sun koyar da shari'ar Musa"
kalmar nan "kowanne" anan na nufin wurare da dama. AT: "a birane da dama" )
Musa a nan na nufin shari'ar. AT: "kuma ana karanta shari'ar" ko kuma "kuma sun karanta shair'ar"
A nan "ikkilisiyar" na nufin jama'ar da ke ikkilisiyar Urushalima. AT: "ikkilisiyar Urushalima" ko kuma "al'umman masubi gabaɗaya da ke Urushalima"
Sunan mutumin kenan. "Barsaba" dai wani suna ne kuma da mutane kam kiransa da shi.
Wannan itace gabatarwar wasikar. Harshen ku na iya samun wata hanyar gabatar da marubucin wasika da kuma wadda aka rubuta masu. AT: "Ga wasika daga 'yan'uwan ku, manzanni da dattawa. Muna rubuta maki Al'ummai masubi da ke Antakiya, Suriya, da Kilikiya. Gaisuwa mai yawa a gare ku" ko kuma "Zuwa ga 'yan'uwan mu Al'ummai da ke Antakiya, Suriya, da Kilikiya. Gaisuwa mai yawa daga manzanni da dattawa, 'yan'uwanku"
A nan kalmar nan "'yan'uwa" na nufin sauran masubi. Manzannin da dattawa suna amfani ne da wannan kalmar don su tabbatar wa Al'umma masubi da cewa sun karɓe su a matsayin 'yan'uwa masubi.
Wannan dai sunan wata lardi ne da ke Karamar Asiya arewacin tsibirin Kuburus.
"wasu mutane"
"ƙodashike ba mu umarce su su je ba"
A nan "hankali" na nufin mutane. AT: "sun koya maku abubuwan da suka dame ku"
Mutanen da suka aika su ne Yahuza da ake kira Barsaba da kuma Sila. (Dubi:[15:22])
A nan "suna" na nufin mutum gabaɗaya. AT: "domin sun ba da gaskiya ga Ubangijinmu Yesu Almasihu" ko kuma "domin suna bauta wa Ubangijinmu Yesu Almasihu"
Wannan jimlar na nanata cewa Yahuza da Sila za su faɗi abu ɗaya da manzanni da dattawa sun rubuta. AT: "wanda da kansu za su yi maku magana game da abubuwan da muka rubuta"
Wannan na maganar dokokin da mutane ke buƙatar kiyaye wa ne kamar sun zama wasu kayayyaki e=ne da mutane za su ɗaɗɗauka a bisa kafaɗansu.
Wannan na nufin cewa ba yarda su ci naman wata dabba da wani ya miƙa wa gumaka hadaya ba.
Wannan na nufin shan jini ko cin naman da ba a janye jinin sa ba.
Dabba da aka musƙure ya mutu, amma ba janye jinin sa ba.
Wannan na sanar da ƙarshen wasikar. AT: "Wassalam" ko kuma "Ku zamna lafiya" ko kuma "Allah ya bishe ku"
Kalmar nan "su" na nufin Bulus, Barnaba, Yahuza, da Sila. AT: "Don haka da aka sallame su, sai suka tafi Antakiya"
AT: "Da aka sallame manzannin da dattawa huɗun" ko kuma "Da masubi da ke Urushalima suka aiko su"
Antakiya tana kasa da Urushalima a tadawa.
"masubi da ke Antakiya sun yi murna sosai"
AT: "saboda abinda manzanni da dattawan sun rubuta ya ƙarfafasu"
Annabawa malamai ne da ke da izini daga Allah su yi magana a madadin sa. AT: "da shike su annabawa ne" ko kuma "ga su ma annanbawa ne"
An yi maganar taimaka wa wani ya dogara sosai ga Yesu kamar an ƙara masu ƙarfin jiki
Kalmar nan "sun" na nufin Yahuza da Sila. AT: "Bayan sun zauna a wurin na ɗan lokaci. AT: "Bayan sun zauna a wurin na ɗan lokaci"
AT: "'yan'uwan suka sallame Yahuza da Sila sun koma lafiya"
"'zuwa wurin masubi da ke Urushalima da suka aike Yahuza da Sila" (Dubi: (See: [Acts 15:22]))
Kalmar nan "su" anan na nufin Bulus da Barnaba kenan.
A nan "maganar" na nufin sako. AT: "sakon Ubangiji"
"Ina mai shawaran cewa yanzu mu koma"
"kula da 'yan'uwa" ko kuma "yi koƙarin tallafe wa masubi"
Suna so su ga yanayin 'yan'uwan da kuma yadda suna kan riƙe da gaskiyar maganar Allah.
"su ɗauki Yahaya, wadda ake kira Markus"
Kalmar nan "bai kamata" ba na nufin ba daidai ba ne. AT: "Bulus ya yi tunanin cewa tafiya da Marku ba zai yi kyau ba"
Wannan wata lardi ne a Karamar Asiya. Duba yadda aka fasara wannan a [2:10]
"bai ci gaba da aiki tare da su ba a lokacin" ko kuma "bai cigaba da hidima tare da su ba"
A nan iya sanar "jayayya" anan ta da "rashin amincewa." AT: "Suka ƙi amincewa da juna"
AT: "bayan da masubi da ke Antakiya suka danƙa Bulus ga alherin Ubangiji" ko kuma "da masubi da ke Antakiya suka yi addu'a ga Ubangiji don ya kiyaye Bulus yă kuma ƙaunace shi"
Jamlar da da wannan ke bi na nuna cewa Sila yana tare da Bulus. AT: "sun tafi" ko kuma "Bulus da Sila suna tafe" ko kuma "Bulus ya ɗauki Sila sun tafe
Waɗannan su ne lardodin da ke Karamar Asiya kusa da tsibirin Kuburus.
Kalmar nan "ikkilisiyoyin" na nufin taron masubi da ke Suriya da Kilikiya. AT: "ta ƙarfafa masubin da ke ikkilisiyoyin" ko kuma "suna taimaka wa taron masubi su ƙara dangana ga Yesu"
Wasu maza daga Yudiya sun koyar cewa sai dai idan yan'uwa suna da kaciya, ba za su samu ceto ba.
Yan'uwan sun yanke cewa Bulus, Barnabas, da kuma wasu ya kamata su je Urushalimao zuwa ga manzanni da dattawa
Bulus da abokan tafiyarsa sun sanad da juyowar al'ummai.
Kungiyar Farisiyawa sun gaskanta cewa dole ne a yiwa al'ummai kaciya kuma dole ne su ajiye dokokin Musa.
Bulus ya fadi cewa Allah ya riga ya ba wa A'ummai Ruhu Mai Tsarki kuma ya riga ya maida zuciyarsu da tsabta ta wurin bangaskiya.
Bulus ya fadi cewa dukka Yahudawa da al'ummai sun samu ceto ta wurin alherin Ubangiji Yesu
Bulus da Barnabas sun kai rahoton alamu da abubuwan al'ajabi da Allah yayi a tsakanin al'ummai.
Anabcin ya fadi cewa Allah zai sake gina alfarwar Dauda da ta fadi, kuma cewa zai hada da al'ummai
Yakub ya bada shawara cewa a ba wa al'ummai sabobin tuba umurni su gudu daga gumaka, daga fasikanci, daga abun da ke maqura,kuma daga jini
An ce marubutan wasikar da kuma Ruhu Mai Tsarki suna cikin yarjejeniya tare da yanke shawara
Al'umman sun yi farin ciki domin karfafawar dake a cikin wasikar
Bulus da Barnabas sun yi koyi kum sun yi wa'azin kalmar Ubangiji
Bulus ya ce wa Barnabas cewa ya so ya koma kuma ya ziyarce yan'uwa a kowane birni da suka zayyana kalmar Ubangiji
Akwai bambancin ra'ayi kadan a tsakanin su, da ya sa suka rabu daga junansu.
1 Bulus ya kuma isa Darbe da Listira, in da akwai wani almajiri mai suna Timoti a wurin, dan wata Bayahudiya wadda ta ba da gaskiya; ubansa kuwa Baheline ne. 2 Ana maganar kirki a kansa ta bakin 'yan'uwa da ke Listira da Ikoniyan. 3 Bulus ya yi wa Timoti kaciya, domin yana so su yi tafiya tare, domin kuma saboda Yahudawan da ke wurin, sun san cewa ubansa Baheline ne. 4 Suna shiga cikin biranen, suna yi wa iklisiyoyi gargadi da su yi biyayya da umurnan da Manzanni da dattawa suka rubuta a Urushalima. 5 Bangaskiyar iklisiyoyi kuwa ta karu, ana kuma samun karuwa na wadanda suke ba da gaskiya kowace rana. 6 Bulus da abokan aikin sa sun shiga cikin lardin Firigiya da Galatiya, tun da Ruhu Mai Tsarki ya hana su wa'azin kalmar a cikin yankin Asiya. 7 Sun zo kusa da Misiya, da nufin shiga cikin Bitiniya, Ruhun Yesu ya hana su. 8 Da suka ratse ta cikin Misiya, sai suka shiga birnin Taruwasa. 9 Bulus ya ga wahayi cikin dare, wani mutumin Makidoniya na kiransa, yana cewa. "Ka zo Makidoniya ka taimake mu". 10 Bulus, da ganin haka, ya kama hanya zuwa Makidoniya, da tunanin Allah ne ya ke so su kai wa mutanen Makidoniya bishara. 11 Da barin Taruwasa, Bulus da kungiyarsa sun shiga jirgin ruwa zuwa Samutaraki, da gari ya waye kuma sun tafi Niyafolis; 12 Daga nan kuma suka tafi Filibi, birni na Makidoniya, mai muhimmanci ne a yankin Roma, in da mun yi zango kwanaki da dama. 13 Ranar Asabaci mun je kofar gari, gefen rafi, da tunanin samun wurin addu'a. Mun zauna mun kuma yi magana da matan da sun taru a wurin. 14 Wata mace mai suna Lidiya, 'yar kasuwa ce a birnin Tiyatira, mai bautar Allah ce, ta saurare mu. Ubangiji ya bude zuciyarta, ta mai da hankali ga maganar da Bulus ke fadi. 15 Sa'anda da aka yi mata Baftisma tare da mutanen gidanta, ta ce da mu, "Idan kun dauke ni mai bautar Allah, ku zo gidana ku zauna." Sai ta rinjaye mu. 16 A daidai wannan lokaci, muna tafiya wurin addu'a, wata yarinya mai ruhun duba ta hadu da mu. Iyayen gijinta na arziki da ita sosai. 17 Tana bin Bulus, tare da mu, tana fadi da murya mai karfi cewa, "Wadannan mutanen, bayin Allah mafi daukaka ne, suna sanar maku hanyar ceto ne". 18 Ta dauki kwanaki tana haka. Amma Bulus ya yi fushi da ita ainun, ya juya ya umarci ruhun, ya ce, "Na umarce ka, ka rabu da ita a cikin sunan Yesu Almasihu". Ruhun ya yi biyayya ya rabu da ita nan take. 19 Da iyayengijinta suka ga cewa hanyar shigar kudinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila, suka ja su cikin kasuwa suka kai su gaban mahunkunta. 20 Da suka kai su Kotu, suka ce, "Wadannan mutane Yahudawa ne, suna kawo tashin hankali a birninmu. 21 Suna koyar da abubuwa da ba su karbuwa a gare mu, balle mu aikata, a matsayinmu na Romawa." 22 Sai jama'a gaba daya sun tayar wa Bulus da Sila; alkalan kuma sun yage rigunansu, sun ba da umarni a duki Bulus da Sila da bulala. 23 Bayan dukan, an jefa su Bulus a kurkuku, an ba mai tsaron kurkukun umurni ya kulle su da kyau, kada su gudu. 24 Shi kuma ya yi hakanan, ya sa masu sarkoki a kafafun su, kamar yadda aka umurce shi. 25 Da tsakar dare, Bulus da Sila suna yin adu'a, su na raira wakoki ga Allah, sauran 'yan sarkar su na jin su. 26 Nan da nan sai ga wata girgizar kasa, wadda ta sa ginshikan kurkukun sun kadu, nan da nan kofofin kurkukun sun bude, 'yan sarka kuma, sarkokin su sun karkatse. 27 Mai tsaron kurkukun ya tashi daga barci ya ga kofofin kurkukun a bude, ya zaro takobi, zai kashe kan sa, a tunanin sa, 'yan sarkar sun gudu. 28 Amma Bulus ya ta da murya da karfi, ya ce, "kada kayi wa kanka barna, domin dukan mu muna nan". 29 Mai tsaron kurkukun ya aika a kawo fitila, ya shiga ciki a gurguje da rawan jiki, ya fadi a gaban Bulus da Sila, 30 ya fitar da su waje ya ce, "Shugabanni, me ya kamata in yi domin in tsira?" 31 Sun ce masa, "ka ba da gaskiya ga Yesu Ubangiji, da kai da gidan ka, za ku sami tsira". 32 Bulus da Sila suka fada masa maganar Ubangiji, tare da iyalinsa. 33 Shi mai tsaron kurkukun ya dauke su cikin daren, ya wanke raunukansu, an kuma yi masa Baftisma nan da nan tare da iyalinsa. 34 Ya kai Bulus da Sila gidansa, ya ba su abinci. Murna ta cika gidan mai tsaron kurkukun, domin iyalin sa duka sun ba da gaskiya ga Allah. 35 Da gari ya waye, alkalai sun ba da sako a saki Bulus da Sila. 36 Mai tsaron kurkukun kuwa ya sanar wa Bulus wannan magana ta alkalan, saboda haka ya ce wa Bulus, "Ku tafi cikin salama". 37 Amma Bulus ya ce masu, "Sun yi mana duka a fili a gaban mutane mu da muke Romawa, ba a kashe mu ba, sun kuma sa mu a kurkuku; suna koran mu a asirce? Su zo da kansu su fitar da mu. 38 Masu tsaron kurkuku sun mayar da maganar Bulus ga alkalan, wanda ya sa sun firgita, da jin cewa Bulus da Sila Romawa ne. 39 Alkalai da kansu sun zo sun roki Bulus da Sila; da suka fitar da su daga kurkukun, sun ce wa Bulus da Sila su bar birnin. 40 Da hakanan ne Bulus da Sila suka fita daga kurkuku, sun je gidan Lidiya. Da Bulus da Sila sun ga 'yan'uwa, sun karfafa su, sa'annan suka bar birnin.
Wannan ya cigaba da tafiye-tafiyen bisharar Bulus tare da Sila.
An gabatar da Timoti a wannan labarin, ya kuma haɗa kai da Bulus da Sila. Aya 1 da 2 na bada takamaimain tarihin Timoti.
Ana iya fasara "isa" da "je"
Wannan sunan wani gari ne a karamar Asiya. Duba yadda aka fasara wannan a [14:16].
Wannan kalmar "sai ga" na jan hankalin mu ne ga wani sabon mutum a labarin. Harshen ku na iya samun wata hanyar yin haka.
Ana fahimtar "ga Almasihu". AT: "wadda ta ba da gaskiya ga Almasihu"
AT: "'yan'uwan suna maganar kirki a kansa" ko kuma "Timoty yana da shaida mai kyau a gaban 'yan'uwan" ko kuma "'yan'uwan suna faɗin abubuwa masu kyau game da shi"
A nan "'yan'uwan" na nufin masubi. AT: " ta wurin masubi
Mai yiwuwa Bulus ne kansa ya yi wa Timoti Kaciya, amma ya fi yi kamar Bulus ya sa wani ne dabam ya yi wa Timoti kaciya.
"domin Yahudawan da suke zama a waɗannan wuraren da Bulus da Timoti za su je"
Dashike Halenawa basu yi wa 'ya'yan su kaciya, Yahudawa za su san cewa Timoti ba shi da kaciya, kuma za su ki Bulus da Timoti kafin ma su saurare bisharar su game da Almasihu.
"da 'yan ikkilisiya su yi biyayya" ko kuma "da masubi su yi biyayya"
AT: "da Manzanni da dattawa da ke Urushalima suka rubuta"
AT: "Masubin sun kara ƙarfi a bangaskiyarsu, kuma ana kuma samun karin mutane da suke tuba zuwa bi kowace rana"
Ana maganar taimakon mutum ya gaskanta da gabadadi kamar karin kuzari ne.
A nan wannan na nufin masubi da ke ikkilisiyoyin.
Wato lardin Asiya. Duba yadda aka fasara wannan sunan a [2:10]
AT: "Ruhu Mai Tsarki ya hana su" ko kuma "Ruhu Mai Tsarki bai yarda masu ba"
A nan "kalma" na nufin "sako." AT: "sakon almasihu"
A nan ana iya fasara "zo" da "je" ko kuma "iso"
Waɗannan wasu lardodi biyu ne kuma da ke Asiya.
"Ruhu Mai Tsarki"
Taruwasa yana kasa da Misiya a tadawa.
A nan ana iya fassara "shiga" da "je"
"Bulus ya ga wahayi daga Allah" ko kuma "Bulus ya samu wata wahayi daga Allah"
"na roƙonsa" ko kuma "yana gayyatansa"
Akwai wata taiku tsakanin Makidoniya da Taruwasa. AT: "Ka ƙetaro zuwa ƙasar Makidoniya"
A nan kalamun nan "mu" da kuma "na mu" na nufin Bulus ne da abokan tafiyarsa a haɗe da Luka, wanda shi ne marubucin Ayyukan Manzanni.
Waɗannan birane ne da ke gaɓar teku a kusa da Filibi a Makidoniya.
A nan ana iya juya wannan kalmar "zo" zuwa "je" ko kuma "iso."
Wannan wata gari ce a wajen Italiya da mutanen suka zo daga Roma ke zama. Jama'ar da ke a wannan wurin ma suna da dama da 'yanci ɗaya da waɗanda ke biranen Italiya. Suna iya mulkin kansu kuma ba lallai ne su biya haraji ba.
A nan "wata mace" na gabatar mana da wata sabuwar mutum kenan a wannan labarin. AT: "Akwai waa mace mai suna Lydia"
A nan "tufafi" ne aka fahimta. AT: "'yar kasuwa ce mai sayar da tufafi masu jan launi"
Wato sunar garin kenan.
Mai yi wa Allah ibada shi ne ba Al'ummi da ke yabon Allah, yana kuma binsa, amma baya biyayya da dukkan dokokin Yahudawa.
Wato Allah ya sa ta gaskanta da sakon kenan. AT: "Ubangiji ya sa ta ta saurara da kyau ta kuma ba da gaskiya"
A nan "zuciya" na nufin hankalin mutum. Kuma marubucin wannan wasika na maganar "zuciya" da "hankali" kamar wata akwati ne da mutum ke iya buɗe wa idan anyi shirin cika ta da abubuwa.
AT: "maganar da Bulus yayi"
AT: Da aka yi wa Lidiya da mutanen gidanta baftisma"
A nan "gida" na nufin mutanen da ke zama a gidanta. AT: "mutanen gidanta" ko kuma " 'iyalin ta da ma'aikatan gidanta"
Wannan jimlar na sa alammar wata sabuwar bangare ne a labarin. Idan harshen ku na da wata hanya ta musamman na yin haka, ana iya yin amfani da shi anan.
Wannan jimla "wata yarinya" na gabatar mana ne da wata sabuwar mutum a labarin. AT: "akwai wata yarinya"
Wani ruhun miyagu yakan yi magana da ita game da abinda zai faru da mutane nan ba da jimawa sosai ba.
Ana maganar yadda mutum na iya samun ceto ne anan kamar wata hanya ne da mutum ke iya wuce wa ko ya bi. AT: "yadda Allah zai cece ku"
AT: "Amma ta sa Bulus ya ji fushi da ita ƙwarai, sai ya juya"
A nan "suna" na nufin yin magana da iko ko a matsayin wakilin Yesu Almasihu.
"ruhun ya rabu da ita nan da nan"
"wato masu yarinyar"
Ana iya sanar da wannan a fili dalilin rashin sammanin samu kuɗinsu ya toshe. AT: "Da iyayengijinta suka ga cewa ba za ta iya tara masu kuɗi kuma da ta wurin yin duba"
"zuwa cikin jama'a" Wato wurin da ake kasuwanci kenan, inda ake siya da sayar da kayaki, shanu, ko hařkoki na tafiya.
ko kuma "domin mahukuntan su yanke masu hukunci"
"Da suka kawo su ga mahukunta"
masu mulki ko mahukunta
A nan "kalmar nan "mu" na nufin jama'ar garin a haɗe da Alƙalan da ke mulkinta.
"gaskanta ko biyayya" ko kuma "karɓa ko ma a yi"
AT: "umarce sojojin su duke su da bulala"
"aka buge su sosai da bulala"
"an faɗi wa mai tsaron kurkukun ya tabbatar cewa basu tsira daga kurkukun ba"
mutumin da ke da hakin kula da dukkan mutanen da ke ɗaure a kurkuku.
"shi kuma yayi na'am da wannan umarni"
"ɗaura kafafunsu da kyau a cikin turu""
wata katako ne ki itace ne mai rami da ke hana kafar mutum iya motsi.
AT: "girgizar ƙasar ta sa ginshikin kurkun suna kaduwa"
Da ginshikin ta kadu, kurkukun gabaɗaya ya kadu.
AT: "duk kofofin suka buɗu"
AT: "sarkokin kowa suka ɓalle"
AT: "Mai tsaron kurkukun ya farfado"
"ya yi shirin kashe kansa." Mai tsaron kurkukun ya gumaci ya ɗauki ransa a maimakon gamuwa da sakamakon barin ya kurkukun su gudu.
Ana iya bayyana a fili dalilin da ya sa mai tsaron kurkukun ya bukaci wuta. AT: "ya aika a kawo mas wuta domin yă iya ganin wanda ke cikin kurkun har yanzu"
Kalmar nan "wuta" na nufin abu mai iya ba da haske. AT: "tocila" ko kuma "fitulu"
"ya shiga kurkukun da sauri"
Mai tsaron Kurkukun ya kaskantar da kansa ta wurin durkusawa a gaban Bulus da Sila.
"ya fitar da su wajen kurkuku"
AT: "me nake buƙata in yi domin Allah ya cece ni daga zunubaina"
AT: "Allah zai cece ka" ko kuma "Allah zai cece ka daga zunubanka"
A nan "gida" na nufin mutanen da ke gidan. AT: "dukkan 'yan gidanka" ko kuma "iyalinka"
A nan "magana" na nufin sako. AT: "Sai suka faɗa masa sakon Ubangiji Yesu"
AT: "Bulus da Sila suka yi wa mai tsaron kurkukun baftisma tare da dukkan iyalinsa"
Ana amfani ne da wannan kalmar a sa alamar dakatawa daga ainihin labarin. Anan Luka yana faɗin abu na ƙarshe a labarin da aka fara a [16:16]
A nan "sako" na nufin "kalma" ko kuma "umarni." AT: "suka aika da sako ga masu tsaron" ko kuma ""suka ba da umarni ga masu tsaron"
A nan "aika" na nufin cewa hukumomin su aike wani yă kai wa masu tsaron sakonsu.
"Ku sake mutanen nan" ko kuma "Ku bar mutanen nan su tafi"
"ku fita daga kurkuku"
Mai yiwuwa Bulus yana magana da mai tsaron kurkukun, amma yana nufin cewa mai tsaron kurkukuun ya gaya wa hukumomin abinda ya faɗa. AT" ya ce wa mai tsaron kurkuku"
A nan "Su" na nufin hukumomin da sun umarci sojoji su yi masu duka. AT: "Hukumomin sun umarci sojojinsu su yi mana duka a fili a gaban jama'a"
mu da muke Romawa ne, sun kuma sa sojojin su suka sa mu a kurkuku ba tare da wata shaida a kotu cewa muna da laifi ba"
Bulus yana amfani ne da wannan tambayan don ya nanata cewa ba zai bar hukumomin su fitar su daga garin a asirce ba bayan da sun yi wa Bulus da Sila ba dadi. AT: "Ba zan taɓa bar su su fitar mu daga garin nan a asirce ba!"
A nan an yi amfani ne da "da kansu" domin nanatawa.
Zaman 'ɗan Roma na nufin zaman tabbaceccen dangari Lardin. Yangarinci na ba da yanci daga tsanantawa da kuma yanci a sauare mutum kamun hukunci. Shugabanen garin na tsoron cewa, shugabani mafi muhimmanci na gaba da su na iya sanin yadda yan garin suka yi wa Bulus da Sila ba dadi.
A nan ana iya juya "zo" zuwa "je"
...
A nan "'yan'uwa" na nufin masubi, ko maza ko mata. AT: "sun ga masubin"
Bulus ya yi wa Timoti kaciya domin Yahudawa a wuraren sun san uban Timoti Girika ne.
Bulus ya isar da umarni wanda manzannin da dattawa sun rubuta a Urushalima.
Bulus ya same wahayin wane mutumin Makidoniya na kiran shi ya zo ya taimake su.
Bulus ya tsammani akwai wurin yin addu'a a wurin.
Ubangiji ya bude zuciyar Lidiya ta saurare abubuwan wanda Bulus na yi magana a kai.
Ta na samun kudi wa uban gijinta ta wurin tuba
Bulus ya juya kuma ya umurci ruhohin, a cikin sunan Yesu Almasihu, su fita daga cikin ta.
Sun zargi Bulus da Sila cewa suna koyar da abubuwa da basu halatta wa Romawa to karba ko tsayar ba.
An buge su da sanda, aka jefa su a kurkuku, kuma aka sa su a hannun jari.
Suna addu'oi da raira wakokin yabon Allah.
Anyi girgizar kasa, duka kokofin kurkukun suka bude, kuma kowa da ke a sarka suka kwance.
Mai Tsaron kurkukun ya tambaye Bulus da Sila, "Yallabai, menene ya zama dole in yi domin in samu ceto"?
Bulus da Sila suka amsa masa cewa, "Ka yi imani da Ubangiji, kuma za ka samu ceto, kai da gidanka.
Mai tsaron kurkukun da kuma dukan iyalinsa aka yi wa baptisma da daren nan.
Masu yanke hukunci a kotun sun ji tsoro domin sun gane cewa sun yi wa 'yan kasar Roma wadanda ba la'ance su ba dukan tsiya a fili.
Bulus da Sila sun je gidan Lidiya, suka karfafa yan'uwan, kuma sai suka tafi daga Filibi.
1 Bayan sun wuce biranen Amfibolis da Aboloniya, sun iso birnin Tasalunika, in da akwai wata majami'ar Yahudawa a wurin. 2 Bulus, kamar yadda ya saba, ya nufi wurinsu, yana tattaunawa da su har Asabaci uku, daga cikin littattafai. 3 Bulus ya bude littattafai yana bayyana masu cewa, dole ne Almasihu ya sha wahala, ya kuma tashi daga matattu. Ya ce, "Wannan Yesu kuwa da nake sanar maku, shine Almasihu". 4 Wasu Yahudawa sun yarda, sun bi Bulus da Sila, da wadansu Helenawa, da Shugabannin Mata da jama'a da yawa. 5 Yahudawan da basu ba da gaskiya ba suka cika da kishi, suka dauki wadansu 'yan ta'adda daga cikin kasuwa, suka tada tarzoma cikin birnin, mutane da yawa na bin su. Sun kai hari a gidan Yason, da niyyar fitar da Bulus da Sila a gaban jama'a. 6 Amma da ba su ga Bulus da Sila ba, suka ja Yason da wasu 'yan'uwa masu bi zuwa gaban mahukuntar birnin, suna cewa, "Wadannan ne fa masu ta da zaune tsaye, gashi sun zo mana. 7 Wadannan mutane da Yason ya marabta, sun saba wa dokokin Kaisar; Suna cewa akwai wani sarki mai suna - Yesu." 8 Da taron jama'a, da mahukuntan birnin suka ji haka, sun damu. 9 Bayan da sun amshi kudi daga wurin Yason da sauran 'yan'uwan, sai suka sake su. 10 A wannan daren, 'yan'uwa masu bi suka fitar da Bulus da Sila, suka aike su garin Biriya. Da isar su can, su ka nufa majami'ar Yahudawa. 11 Mutanen Biriya daban suke da na Tasalunika, sun yarda da sakon Bulus da zuciya daya, suna kuma binciken littattafai kowace rana domin su tabbatar da sakon Bulus, ko gaskiya ne. 12 Saboda haka mutane da yawa cikin su sun ba da gaskiya, tare da wadansu sannanun mata Helenawa da maza da yawa. 13 Amma da Yahudawan Tasalunika suka ji cewa Bulus yana wa'azin kalmar Allah a Biriya, sun haura can, sun tada hankulan jama'a. 14 Nan da nan, masu bi na Biriya sun dauki Bulus sun aika shi zuwa teku, an bar Sila da Timoti a Biriya tukuna. 15 Wadanda sun fitar da Bulus, sun kai shi har zuwa birnin Atina. Bulus ya ba su sako, su fada wa Sila da Timoti suyi hanzari su same shi. 16 Sa'anda Bulus yana jiran zuwan Sila da Timoti a Atina, ya yi fushi a ransa, da ya ga birnin cike da gumakai. 17 Ya tattauna da Yahudawa a cikin majami'a tare da masu yin sujada ga Allah, da kuma wadanda yake samu a kowace rana, a kasuwa. 18 Amma wadan su Abikuriyawa da masana sun yi karo da shi. Wadansun su na cewa, "Menene wannan sakaren ke cewa?" Wadansu kuma sun ce, "Da alama mai wa'azi ne na wasu alloli dabam," domin yana wa'azin Yesu da tashin sa daga matattu. 19 Suka dauki Bulus zuwa Tudun Arasa, suna cewa, "Ko za ka sanar mana da wannan sabuwar koyaswar taka? 20 Abubbuwan da kake fadi, baki ne a gare mu. Muna so mu san ma'anar su." 21 (Atiniyawa da bakin da ke cikinsu, suna ba da lokacin su ga fadin sabobbin abubuwa da sauraron su). 22 Bulus ya tsaya a tsakiyar Tudun Arasa ya ce, "Ku mutanen Atiniya na lura masu kwazon addini ne ku. 23 Na lura da abubuwan sujadar ku yayin da nake zagawa, amma na ga wani bagadi da rubutu a kansa mai cewa, "Ga Allah wanda ba a sani ba." Abin da kuke bauta wa cikin rashin sani, shi nake sanar maku. 24 Allahn da ya yi duniya da kome da ke cikinta, tun da ya ke shine Ubangijin sama da kasa, ba ya zama a haikalin da mutane suka gina da hannu. 25 Ba ya neman taimakon kowa, babu kuma wanda ya isa ya ba shi. Shine ke ba da rai, da numfashi da kowanne abu. 26 Daga mutum daya ya hallici dukan al'umman duniya, ya rarraba, ya kuma sanya kowa a inda ya shirya masa. 27 Domin su nemi Allah ko za su iya kaiwa zuwa gareshi su same shi, ga shi kuwa ba ya nesa da kowannenmu. 28 A cikinsa muke rayuwa, muna walwala, kamar yadda wani daga cikin masananku yace, 'Mu 'ya'yansa ne'. 29 Idan mu 'ya'yan Allah ne, bai kamata mu danganta Allah da zinariya ko azurfa, ko kuma duwatsu da itatuwa da an sassaka ba. 30 Saboda haka ne, Allah ya kawar da kwanakin jahilci, amma ya ba da umarni kowa a ko'ina ya tuba. 31 Akwai ranar da ya shirya zai yi wa duniya shari'a cikin adalci, ta wurin mutumin da ya zaba. Allah ya nuna wannan mutumin, ta wurin ta da shi daga matattu". 32 Da mutanen Atina sun ji batun tashi daga matattu, wadansu suka yi wa Bulus ba'a; amma wadansu kuma sun ce, "Za mu saurare ka kuma, a kan wannan maganar." 33 Bayan haka, Bulus ya bar su. 34 Amma wasu maza a cikinsu sun yarda da bisharar, sun ba da gaskiya, hade da Diyonisiyus dan Majalisar Tudun Arasa da wata mace mai suna Damaris, da wadansu tare da su.
Wannan na cigaba da labarin tafiyar bishara ne na Bulus, Sila, da Timoti. Sun isa garin Tasalonica, da saukin ganewa ba tare da Luka ba, tun da ya ce "su" ba "mu" ba.
A nan kalmar nan "su" na nufin Bulus da Sila.Ƙwatanta [16:40] Kalmar nan "su" na kuma nufin Yahudawa da ke majami'a a Tasalonica. check: them and they
A nan amfani ne da wannan kalmar a nuna kauchewa daga ainihin labarin. Anan Luka, marubucin, ya fara faɗin wata sabuwar bangaren labarin.
"sun yi tafiya ta"
Waɗannan su ne biranen da ke gaɓar teku a Makidoniya.
A nan ana iya juya kalmar nan "zo" zuwa "je" ko kuma "iso." AT: "suka iso birnin" ko kuma "suka iso garin"
"kamar yadda halinsa yake" ko kuma "kamar yadda ya saba yi." Bulus ya saba zuwa majami'a a ranar Asabar lokacin da Yahudawa za su kasance.
"a kowace rasar Asabar ha makonni uku"
Bulus yana masu bayanin abinda Littattafain ke nufi domin ya hakikanta wa Yahudawa da cewa Yesu shafaffe na Allah ne
"yana basu dalilai" ko kuma "yana muhawara da su" ko kuma "yana bincikawa da su"
Wannan na iya nufin 1) Ana maganar faɗin ma'anar littattafai a yadda mutane za su iya fahimtar ne kamar Bulus yana buɗe wani abu ne da mutane na iya ganin abinda ke cikinsa ko kuma 2) Bulus yana ainihim buɗe wata littafi ne sa'annan yana karatu daga cikinta.
"yana cikin shirin Allah"
"yă dawo da rai"
Daga cikin waɗanda sun mutu. Wannan bayyanin na bayyana dukkan matattun mutane gabaɗaya da ke ƙarƙashin duniya. Dawuwa daga cikinsu na maganar zama rayayye kuma.
AT: "Yahudawa sun gaskanta" ko kuma "Yahudawa sun fahimta"
"sun haɗa hannu tare da Bulus"
Wato Halenawa da ke yi wa Allah ibada amma ba su juya zuwa ga addinin Yahudanci ta wurin kaciya ba.
Wannan ma bai ka ma a nanata ba cewa shugabanin mata da yawa sun bi su. AT: "Shugabannin mata da yawa"
Ana maganar yin kishi kamar wani abu ne da ake iya cika da shi. AT: "cika da kishi sosai" ko kuma "yi matuar fushi"
Ana iya bayana a fili cewa waɗannan Yahudawan sunsa kishi cewa wasu yahudawa da Girkawa sun gaskanta da jawabin Bulus.
A nan "ɗauki" bai nuna cewa Yahudawan sun ɗauke su da ƙarfi ba ne. Amma yana nufin cewa Yahudawan su rinjaye su su taimake su.
"wasu mugayen mutane." Kalmar nan "mutane" na nufin musamman maza ne.
"daga cikin garin." Wato wurin da ake harkokin siya da sayay da abubuwa, shanike, da ayyuka daban daban kenan.
A nan "birni" na nufin mutanen da ke garin. AT: "suka sa mutane garin suka ta da hargitsi" ko kuma "suka sa mutanen garin suka ta da faɗa"
Wannan na iya nufin cewa mutanen suka riƙa jefa duwatsu a gidan domin su balle kofar gidan.
Wannan dai sunan wani mutum ne.
Wannan na iya nufin ko kuma "jama'a" 1) shugabanin ƙasa ko taron masu yanke shari'a ko ɗaukan shari'a ko kuma 2) taron 'yan banza ko 'yan iska.
AT: "wasu masubi"
"gaban ma'aikatan hukuma"
Mutanen Yahudawa kenan suna magana, kuma wannan jimlar "Waɗannan" na nufin "Bulus da Sila."
Wannan jimlar wata hanya ne na cewa Bulus da Sila suna ta da hargitsi duk inda sun je. Shugabannin Yahudawa suna kara gishri ga albarkacin da Bulus da Sila ke da shi da koyarwarsu. AT: "suna ta da rikici a ko ina a duniya" ko kuma "suna ta da rikici duk inda sun je"
Wannan jimlar na ba da alamar cewa Yason ya amince da jawabin manzannin mai ta da hargitisi.
"sun damu"
Yason da sauran mutanen sun biya ma'aikatan hukumar garin kuɗi a matsayin ɗaukan alkawarin zaman lafiya; ana iya mayar masu da wannan kuɗin idan kome ya yi daidai ko kuma ana iya amfani da shi a gyara abubuwan da suka lalace saboda hargitsin da ya faru.
Kalmar nan "sauran" na nufin sauran masubi da Yahudawan suka kawo gaba ma'aikatan hukuma.
,"ma'aikatan hukumar sun bar Yason da sauran masubin sun tafi"
Kalmar nan "'yan'uwa masubi" na nufin maza da mata masubi. AT: "masubin"
Waɗannan mutane ta musamman suna da marmarin bimbini da tunani sosai game da sabobin koyarwa fifye da sauran mutane. AT: "sun fi shirya zukatansu" ko kuma "suna da marmarin kasa kunne"
A nan "sakon" na nufin koyarwar. AT: "su saurare koyarwar"
Waɗannan mutanen Biriyan suna shirye su bincika koyarwar Bulus daga Littafi Mai Tsarki.
"suna karatun littafai suna kuma kintata ta a kowace rana"
"abubuwan da Bulus ke koyarwa gaskiya"
AT: "sun je can sun hanzuga" )
sai sun tada jama'an" ko kuma "suka sa mutanen sun zama da firgaba da tsõro"
Wato maza da mata masu bi. (Dubi:
"zuwa gaɓar teku." Dagan nan mai yiwuwa Bulus zai yi tashi ya yi wata tafiya zuwa wata gari.
"masu wa Bulus rakiya" ko kuma "waɗanda suke tafiya tare da Bulus"
"ya faɗa masu cewa su gargadas da Sila da Timoti."
A nan "ransa" na nufin Bulus da kansa. AT: "hankalinsa ya tashi domin ya ga cewa garin yana cike da gumakai ko ta ina" ko kuma "ganin gumakai a ko ina a garin ya tayar masa da hankali"
ya yi muhawwara" ko kuma "ya yi shawara" Wato akwai hulda da masu sauraro, ba wai Bulus yana ta jawabi shi kaɗai ba. Su ma suna magana da shi.
Wato Al'ummai (wanda ba Yahudawa ba) da ke Yabon Allah suna kuma bin sa, amma ba su kiyaye duka dokokin Yahudawa.
"a cikin taron jama'a." Wurin harkokin siya da sayarwa.
Waɗannan mutanen sun gaskanta cewa dukkan abubuwa sun dai kasance haka ne kawai kuma allolin suna fama da farin ciki, don haka, ba su damu da yin mulki a bisa duniya ba. Sun musunce tashin mattatu, don suna son annashuwa ne kurum.
Waɗannan mutanen sun gaskanta cewa ana samun 'yanci ta wurin yin murabus da ƙaddara. Sun ƙi cewa akwai wani Allah mai ƙaunar kowane mutum, da kuma tashin mattatu.
"sun saɗu da shi"
"Waɗansu masanan sua cewa"
A nan amfani ne da kalmar nan "sakare" wa sunsaye da ke cin hatsi a masayin abincinsu. Yana nufin mutumin da ke da karancin sani game da wani abu. Masanan suna cewa Bulus yana da karancin sani wanda basu isa su sa a saurare shi ba. AT: "Menene wanna mutum marar ilimi"
"Waɗansu masanan kuma sun ce"
"Ga alama kamar shi mai shelar" ko kuma "Kamar yana da nufin tarin mutane ne su gaskanta sa nasa irin sani"
Ba wai wannan tana nufin "bare" ba ne, amma yana nufin "bãƙi", wato, Allolin da Girkawa da Romawa ba su masu sujada ba ko basu san da su ba.
Ba wai sun ɗaura Bulus ba. Masanan sun gayyace Bulus ya yi magana da shugabanninsu bisa ga ka'ida.
A "Tudun Arasa" ne shugabannin sukan haɗu. AT: "zuwa wurin shugabannin da ke haɗuwa a Arasa"
A nan shugabannin Tudun Arasa ne ke magana. Ana iya sanar da wannan a wata sabuwar jimala. AT: "Tudun Arasa. Shugabannin sun ce wa Bulus"
Wannan wata sanannen dutse ne mai tudu a Atiniya da kotun kolin Atiniya suka hadu.
Ana maganar koyarwar Bulus game da Yesu da kuma tashin mattatu kamar wani abu ne da iya kai shi ga wani. AT: "Domin kana koyar da wasu abubuwa ne da bamu taba jin su ba"
Ana amfani ne da waɗannan kalmomin a datsa aya ga ainihin labarin. Anan, Luka yana ba da takaitaccen tarihin mazaunan Atiniya ne da kuma marmarin da suke da shi na koyan sabobin abubuwa"
Wannan kalmar "dukkan" na nufin masu yawa. AT: "yanzu Atiniyawa masu yawa da bãƙin da ke cikinsu" ko kuma "yanzu mafi yawan Atiniyawa da bãƙin da ke cikinsu"
"Atiniyawa" na nufin mutane daga Atiniya, wata gari kusa da gaɓar teku kasa da Makidoniya (ƙasar Helas ayau" )
"'yan wasu ƙasashe da ban"
Ana maganar "lokaci" ne anan kama wani abu ne da mutume ke iya ba wa wani. AT: "suna amfani da lokacinsu ga faɗi ko sauraro" ko kuma "basu yin komai ba illa faɗi ko sauraro"
"tattauna sabobin sani" ko kuma "suna faɗin abubuwa da ke sabobi ne a gare su"
Bulus yana nufin yadda Atiniyawa suke nuna wa allolinsu girma a fili ta wurin adduo'i, gina bagadi, da kuma ba da hadayu"
"Domin da nake wucewa" ko kuma "da nake tafiya"
Wannan na iya nufin 1) ga wani Allah ta musamman da ba a sani ba" ko kuma 2) ga wani allag da ba sani ba" Wannan ita ce wata rubutu ne ta musamman ko kuma alama da aka sa a wannan bagadi.
A hanya mafi dacewa, "duniya" na nufin sama da duniya da kamai a cikinsu.
"domin shi ne Ubangiji" Anan "shi" yana nufin allahn da ba sani ba da aka ambata a [17:23] da Bulus ke yin bayani shi ne Ubangiji Allah.
A nan amfani da kalamun nan "sama" da "duniya" gabadaya a nuna cewa dukkan abubuwa da ke sama da duniya.
A nan "hannaye" na nufin mutane. AT: "gina da hannayen mutane" ko kuma "da mutane suka gina"
A nan "taimako" na nan kamar yadda likita ke taimake mutum marar lafiya har ya samu lafiya kuma. AT: "Hannayen mutane basu taimake shi ba"
A nan "hannaye" na nufin mutum gabaɗaya. AT: "gun 'yan adam"
"domin shi da kansa." An kara kalmar nan "kansa" ne domin nanatawa.
Wato Adamu, mutumi na farko da Allah ya halita. A nan iya sanar da wanna a haɗe da Hauwa'u. Ta wurin Adamu da Hauwa'u ne Allah ya yi dukkan sauran mutane. AT: "iyali ɗaya"
AT: "ya kuma rarraba lokatai da wurare da za su kasance"
A nan "su nemi Allah" na nufin su yi marmarin sanin shi, haka kuma "kaiwa zuwa gareshi su same shi" na nufin yi masa addu'a da samun dangartaka da shi. AT: "domin su yi marmarin sanin Allah su kuma iya yi masa auud'a har ma su kasance a cikin mutanensa"
AT: "Ga shi kuwa yana kurkusa da kowane ɗayanmu"
"Saboda shi ne"
Da shike Allah ne ya hallice kowa, ana maganar dukkan mutane ne kamar su 'ya'ya ne na jiki ga Allah.
A nan "Allah" na nufin assalin Allah ko kuma halayarsa. AT: "cewa Allah"
AT: "wadda mutum ya yi amfani da gwanintarsa zuwa wani abu da ya kera" ko kuma "kamanni da mutane suka sassaka ta wurin dabararsa su"
"Domin abinda na faɗa maku gaskiya be"
"Allah ya bi ya ƙi hukunta mutane a lokacin jahilci"
Wannan na nufin kamun Allah ya bayyana kansa cikakke ta wurin Yesus Almasihu da kuma kamun mutane su san yadda za su yi sahihiyar biyayya da Allah.
Wato jama'a dukka, maza da mata. AT: "jama'a dukka"
da mutumin da ya zaɓa zai yi wa duniya shari'a cikin adalci"
A nan "duniya" na nufin mutane dagaɗaya. AT: "zai yi wa dukkan mutane shari'a"
"cikin gaskiya" ko kuma "daida"
"Allah ya nuna zaɓin sa da ya yi na wannan mutumin"
Waɗannan ne mutanen da ke nan a Tudun Arasa suna sauraron Bulus.
"waɗansu suka yi wa Bulus zuliya" ko kuma "waɗansu suka yi wa Bulus Dariya." Waɗannan din basu yarda cewa abu mai yiwuwa ne mutum da ya mutu yă dawo da rai kuma ba."
Diyonisiyus sunar wani mutum ne. Majalisar Tudun Arasa ɗaya daga cikin alkalai ne da ke majalisar Tudun Arasa.
Wannan sunar wata mata ne.
Bulus ya fara zuwa haikalin Yahudawa domin ya yi magana daga nassosi game da Yesu.
Bulus ya nuna cewa ɗole ne Almasihu ya sha wahala, ya kuma tashi daga matattu.
An yi zargin Bulus da Sila cewa sun saba wa dokokin Kaisar; Suna cewa akwai wani sarki mai suna - Yesu.
Bulus da Silas suka shiga cikin haikalin Yahudawa.
'Yan Biriya sun ƙarbi kalmar sun kuma yi binciken littattafan domin su gan ko abin da Bulus ya na faɗa haka ne.
Bulus ya bar Biriya domin Yahudawan Tasalunika suka tada hankalin jama'a, sai Bulus ya tafi Atina.
Bulus ya je haikalin Yahudawa da wurin kasuwa domin su tattauna daga nassosi.
An kawo Bulus zuwa Tudun Arasa, domin ya kara bayana koyarwansa.
Bulus ya sami wani bagadi da an rubutu a kansa cewa, ''Ga Allahn da ba a sani ba." wanda yake sanar masu.
Bulus ya ce Allahn da ya yi komai na ba mutane rai da numfashi da kuma komai.
Daga mutum ɗaya ne Allah ya hallici dukan al'umman mutane.
Bulus ya ce Allah ba shi da nisa da kowa.
Bulus ya ce kada mu ɗauki Allah kamar zinariya ko azurfa, ko kuma duwatsu da itatuwa da mutum ya sassaka ba.
Yanzu Allah na kiran dukka mutane a ko ina ga tuba.
Allah ya nuna cewa an zaɓi Yesu a matsayin mai shari'ar duniya ta wurin ta da shi daga matattu.
Allah ya shirya wani ranar da Yesu zai shari'ar duniya cikin adalci.
Wadansu suka yi wa Bulus ba'a sa'ad da sun ji ya yi magana game da tashi daga matattu
I, wasu mutane sun gaskanta da Bulus, da waɗansu tare da su.
1 Bayan haka sai Bulus ya tafi Antakiya daga nan, ya wuce Korinti. 2 A can ya sadu da wani Bayahude mai sunan Akila, dan kasar Buntus ne; bai dade da zuwa garin ba, daga Italiya ya zo da matarsa mai suna Balkisu, saboda Kalaudiyas ya ba da umarni dukan Yahudawa su bar Roma; sai Bulus ya je wurinsu. 3 Bulus ya zauna a gidansu don sana'arsu daya ce, wato, masu aikin Tanti ne. 4 Saboda haka Bulus na zuwa majami'a, yana yin nazari tare da su a kowace Asabaci. Yana kokari ya rinjayi Yahudawa da Helinawa. 5 Amma a lokacin da Sila da Timoti suka iso Makidoniya, Ruhu ya matsa Bulus ya shaida wa Yahudawa cewa Yesu Almasihu ne. 6 Lokacin da Yahudawa suka tayar masa suna zarginsa. Bulus ya kakkabe rigansa a gabansu yana cewa, "Alhakin jininku yana kanku; daga yanzu zan koma wurin al'ummai." 7 Da ya bar wurinsu, ya tafi gidan Taitus Yustus mai wa Allah sujada. Gidansa na kusa da majami'a. 8 Kiristus shine shugaban majami'a, sai shi da dukan iyalin gidansa sun ba da gaskiya ga Ubangiji. Korantiyawa da yawa suka ji jawabin Bulus suka ba da gaskiya, aka yi masu Baftisma. 9 Da dare Ubangiji ya ce wa Bulus a cikin wahayi, "Kada ka ji tsoro, amma ka yi magana kada kuma ka yi shuru. 10 Gama ina tare da kai, ba wanda zai cutar da kai, gama ina da mutane anan garin." 11 Bulus ya zauna a nan tsawon shekara daya da wata shida, yana koyar masu da maganar Allah. 12 Amma da Galiyo ya samu zaman gwamnan Akaya, sai Yahudawa suka tayar wa Bulus har suka kai shi gaban dakalin shari'a. 13 Suna cewa, "Wannan mutumin yana kokarin rinjayar mutane su yi sujadar da ta saba wa dokarmu." 14 Duk da haka kafin Bulus ya yi magana, Galiyo ya ce wa Yahudawa, "Ku Yahudawa in da karar ku ta wani babban laifi ce wanda ya aikata, da sai in hukunta. 15 Amma tun da ya ke akan al'amurar, kalmomi ne, da ta sunaye da dokokin ku, ku je ku sasanta al'amuran ku." 16 Galiyo ya kore su daga dakalin shari'a. 17 Saboda haka sai suka kama Sastanisu, suka yi masa duka sosai a gaban dakalin shari'a. Amma Galiyo bai damu da yadda suka karasa ba. 18 Bulus kuwa, bayan ya zauna tare da su na wasu kwanaki masu yawa, ya bar 'yan'uwan zuwa Suriya ta jirgin ruwa, tare da Balkisu da Akila. Kafin ya bar tashar jiragen ruwa da ke a Sankuriya, ya tafi saboda ya aske kansa, domin ya dauki alkawarin Banazare. 19 Da suka iso Afisa, Bulus ya bar Balkisu da Akila anan. Shi kuwa ya shiga majami'ar Yahudawa yana nazari tare da su. 20 Da suka roki Bulus ya zauna da su na tsawon lokaci, bai yarda ba. 21 Ya kama hanyarsa ya bar su ya ce, "In Allah ya yardar mani zan dawo wurinku wata rana." Sai ya shiga jirgin ruwa daga Afisa. 22 Daga saukar su a Kaisariya, sai ya haura zuwa Urushalima ya gai da iklisiya daga nan ya tafi Antakiya. 23 Bayan ya zauna na dan lokaci a wurin, Bulus ya kama hanyarsa zuwa yakin Galatiya da Firjiya anan ya karfafa almajirai. 24 A nan dai akwai wani Bayahude mai suna Afolos, dan asalin Iskandariya ne da haihuwa, ya zo Afisa. Shi masani ne a maganar Allah. 25 Afolos dai ya sami horo daga maganar Ubangiji. Shi mai kokari ne a ruhu, yana wa'azi da koyarwa daidai game da Yesu. Amma ya san da Baftismar Yahaya ne kadai. 26 Afolos ya fara wa'azinsa da gabagadi a cikin majami'a. Da Balkisu da Akila suka ji shi sai suka yi abokantaka da shi, suka kara bayyana masa game da labarin hanyar Allah mafi daidai. 27 Da ya so ya wuce zuwa cikin Akaya 'yan'uwa suka karfafa shi, sun rubuta wa almajiran da ke a Akaya, don su karbe shi da hannu biyu. Da ya iso wurinsu, ya kuwa karfafa 'yan'uwa da sun ba da gaskiya ta wurin alheri. 28 Afolos ya ba Yahudawa mamaki da irin ikon da yake da shi da gwanintarsa, yadda yake nunawa daga nassoshi cewa Yesu shine Almasihu.
Wannan wata bangare ne labarin tafiye tafiyen Bulus yayin da ya tafi Korintus.
Ana gabatar da Akila da Bilkisu ne a labarin a ayoyi 2 da 3 da kuma takaitaccen tarihinsu.
"Bayan da waɗannan abubuwa sun faru a Atina"
Atina itace ce wata birni mafi muhimmanci a Hellas. Duba yadda aka juya wannan a [17:15]
Wannan na iya nufin 1) Bulus ya bi ya same ko kuma 2) Bulus ya yi niyyar samun.
A nan jimlar nan "wani" na gabatar da wani sabon mutum kenan a labarin,
Buntua wata lardi ce da ke kudancin gaɓar tekun baƙin Teku.
Wannan na iya nufin a shekaran da ta gabata.
Wannan sunar wata ƙasa ne. Roma itace cibiyar garin Italiya.
Kalaudiyas ne shugaban Roma a wannan lokacin. Duba Yadda aka juya wannan a [11:28]
"yana irin aikin da suke yi"
"Saboda haka Bulus yayi muhawara" ko kuma "Saboda haka Bulus ya tattauna." Ya ba da dalilai. Wato a maimakon wa'azi kawa, Bulus yayi magana ya kuma hulda da su.
Wannan na iya nufin 1) "Ya sa Yahudawa da Halinawa su gaskanta" ko kuma 2) "Yana ta ƙoƙarin rinjayar Yahudawa da Halinawa."
AT: "Ruhu ya tilasta Bulus"
Wannan wata alama ce da ke nuna cewa Bulus ba zai cigaba da koya wa Yahudawan game da Yesu. Yana barinsu ga hukuncin Allah.
Ana "alhaki" na nufin alhakin laifinsu. "kanku" kuma anan yana nufin mutum gabaɗaya. Bulus yana faɗi wa Yahudawan cewa su ne da hakin hukuncin da za su fuskanta domin rashin jinsu idan su ƙi tuɓa. AT: "Ku ne da ɗaukan hakin hukuncin zunubinku"
Waɗannan sunayen maza ne.
Mai yi wa Allah sujada Bahaline da ke yabon Allah yana kuma binsa amma ba lallai ne yana kiyaye dukkan dokokin Yahudawa ba.
Wani jahili mai da ke tallafa wa tafiyar da majami'a, ba lallai malamin ba.
A nan "gida" na nufin mutanen da ke zama tare. AT: "mutanen da ke zama tare da shi a gidansa"
AT: "sun samu yin baftisma"
Ubangiji yana ba da umarni ɗaya a hanyoyi biyu don ya nanata wa Bulus cewa lallai yă cigaba da wa'azi. AT: "Kada ka kuskura ka ji tsoro, a maimakon haka, ka cigaba da magana kuma kada ka yi shiru"
Ubangiji yana ba da umarni ɗaya a hanyoyi biyu daban daban don yă umarce Bulus da babban murya cewa ya cigaba da magana. AT: "lallai ne ka ci gaba da magana"
Ana iya sanar a fili abinda Ubangiji ke so Bulus yă faɗa. AT: "kada ka daina yin bishara"
"akawai mutane da yawa a wannan garin sa sun sa bangaskiyar su a gareni" ko kuma " mutane da yawa a wannan garin za su sa bangaskiyar su gareni"
Wannan ne maganar ne ke kammala wannan bangaren labarin. "maganar Allah" anan na nufin Littafi Mai Tsarki gabaɗaya. AT: "Bulus ya zauna a wurin ... yana koyar masu da Littafi Mai Tsarki"
Wannan sunan wani mutum ne.
Wannan na nufin shugabannin Yahudawan da basu gaskanta da Yesu ba.
"suka taru" ko kuma "suka haɗu"
Yahudawan sun ɗauki Bulus da ƙarfi ne zuwa gaban kotu. A nan "dakalin shari'a" na nufin wurin da Galiyo ke zama lokacin yanke hukunci a kotu. AT: "suka kai shi domin gwamna yă yanke masa hukunci a dakalin shari'a"
Galiyo shi ne gwamnar Roma na wannan lardin.
A nan "doka" na nufin dokar Musa da kuma al'adun Yahudawa na zamanin Bulus.
"Ni ba zan yanke hukuncin waɗanna zantukan ba"
"Galiya ya sallame su daga dakalin shari'a." Anan "dakalin shari'a" na nufin wurin da Galiyo ke zama lokacin yanke hukunci a kotu. AT: "Galiyo ya sa sun tashi a gabansa a kotu" ko kuma "Gaiyo ya sa sun bar kotun"
Wannan na ƙara nanata yadda mutanen ke ji. AT: "jama'a da yawa suka kama" ko kuma "da yawan su sun raruma"
Wannan na iya nufin 1) Haleniyawan sun dũke Sastanisu a kotun a gaban dakalin shari'ar domin shi shugaban Yahudawa ne ko kuma 2) mai yiwuwa Sastanisu mai bi ne cikin Almasihu, don haka, Yahudawa suka masu dũka a gaban kotu.
"Sastanisu" shi ne shugaban Yahudawa da majami'ar da ke Korintus.
"suka riƙa bubbuge shi" ko kuma "suka riƙa naushinsa"
Kalmar nan "'yan'uwan" na nufin masubi, maza da mata. AT: "ya bar 'yan'uwa masubi"
Bulus ya shigo wata jirgi ruwa da ya tashi zuwa ƙasar Suriya. Balkisu da Akila suka je tare da shi.
Wannan wata alamace da ke nuna cikar wa'adin. AT: "ya sa wani yă aske hashi kansa"
"yana tattaunawa tare" ko kuma "yana muhawara tare"
"da yake yi masu ban kwana"
"isowar su Kaisariya." Anyi amfani ne da wannan kalmar "sauka" domin nuna cewa sun iso a jirgin ruwa ne.
Ya yi tafiya zuwa birnin Urushalima. An yi amfani ne da jimlar nan "ya haura" domin Urushalima yana sama da Kaisariya a tadawa.
A nan "ikilisiya" na nufin masubi da ke Urushalima. AT: "ya gai da jama'ar ikilisiyar Urushalima"
Antakiya yana ƙasa da Urushalima a tadawa.
"Bulus ya yi gaba" ko kuma "Bulus ya tafi"
AT: Bayan da ya ɗan zauna a wurin kaɗan"
Wannan na nuna sun kauce daga ainihin labarin.
Jimlar nan "wani" na nuna cewa Luka yana gabatar da wani sabon mutum a wannan labarin.
"mutumin da aka haifa a garin Iskandariya." Wannan wata gari ne a Masar a arewacin gabarr tekun Afirka.
"ya iya magana"
"ya san maganar Allah sosai." Ya fahimci rubuce rubucen Tsohon Alkawali da kyau.
Wasu masubi sun koya wa Afolos yadda Ubangiji Yesu yake son mutane su yi rayuwa"
A nan "ruhu" na nufin shi Afolos da kansa. AT: "Shi mai aminci ne ƙwarai"
"Baftismar da Yahaya ya yi." Wannan kwatanci ne na baftismar Yahaya da yayi da ruwa da kuma baftismar Yesu wadda yake yi ne da Ruhu Mai Tsarki.
Ana maganar yadda Allah ya ke so mutane su yi rayuwa ne kamar wata hanya ne da mutum ke iya bi yă yi tafiya.
"cikakke"
"yă je yankin Akaya." Anyi amfani ne da kalmar nan "wuce" domin Afolos ya ketere Tekun Aijiya don ya kai Akaya daga Afisus.
Kalmar nan "'yan'uwa" anan na nufin masubi, maza da mata. Anan iya bayana a fili cewa waɗannan masubi ne a Afisus. AT: "'yan'uwa masubi da ke Afisus"
"sun rubuta wasika zuwa ga masubi da ke Akaya"
"da sun gaskanta cewa samun ceto ta wurin alherin ne" ko kuma "da ta wurin alherin Allah suka gaskanta da Yesu"
"A muhawara cikin Jama'a, Afolos da iƙo da gwaninta ya nuna wa Yahudawa kuskurensu"
"yayin da Yesu yake nuna masu ta wurin nassohi cewa Yesu ne Almasihu"
Bulus ya yi aikin gyara tanti domin ya riƙe kanshi..
Bulus ya shaida wa Yahudawa cewa Yesu shi ne Almasihu.
Bulus ya faɗa wa Yahudawan cewa alhakin jininsu yana kansu; daga nan ya tafi wurin al'ummai.
Ubangiji ya ce wa Bulus ya cigaba da magana, gama babu wanda zai cũtar da shi a wurin.
Yahudawa sun yi zargin Bulus domin koya wa mutane su yi sujada da ta saba wa dokarsu.
Gwamna ya faɗa cewa bai so ya zama mai hukunta al'amurar da ta kansa dokar Yahudawa ba.
Akila da Balkisu sun yi tafiya tare da Bulus zuwa Afisa?
Bayan ya bar Afisa, Bulus ya yi tafiya zuwa Urushalima daga nan sai Antakiya.
Afolos ya fahimci abubuwa game da Yesu sosai, amma a san da Baftismar Yahaya ne kadai.
Balkisu da Akila sun zama abokai da Afolos sun kuma bayana masa game da labarin hanyar Allah da kyau.
Afolos ya ba Yahudawa mamaki a bayyana, da cewa Yesu shine Almasihu.
1 Sa'adda Afolos yake a Koranti, Bulus ya zagaya kasar tudu ya zo birnin Afisa, a nan kuma ya sami wadansu almajirai. 2 Bulus ya ce masu, "Ko kun karbi Ruhu Mai Tsarki sa'anda kuka ba da gaskiya?" Suka amsa, "A'a bamu taba jin labarin Ruhu Mai Tsarki ba. 3 Bulus ya ce, "Wacce irin baftisma aka yi maku?" Suka ce, "Baftismar Yahaya" 4 Bulus ya amsa ya ce, "Yahaya ya yi wa mutane baftismar tuba, ya ce su ba da gaskiya wanda zai zo bayansa, wato, Yesu kenan." 5 Da mutanen suka ji haka, sai aka yi masu baftisma cikin sunan Ubangiji Yesu. 6 Sa'adda Bulus ya dibiya hannu a kansu, Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauka a kansu suka yi magana da harsuna da kuma annabci. 7 Su wajen mutum goma sha biyu ne. 8 Bulus ya shiga majami'a ya yi ta koyarwa gabagadi misalin tsawon wata uku. Yana bi da su cikin nazarin maganar yana fahimtar da mutane su gaskanta game da abubuwa da suka shafi mulkin Allah. 9 Amma sa'adda wadansu Yahudawa suka taurare, suka ki yin biyayya, sai suka fara bata hanyar Almasihu a gaban taron. Saboda haka sai Bulus ya janye daga wurinsu tare da wadanda suka ba da gaskiya. Ya fara koyarwa a makarantar Tiranus. 10 Haka ya cigaba shekaru biyu har duk mazaunan Asiya suka ji maganar Ubangiji, Yahudawa da Helenawa. 11 Allah ya yi manyan al'ajibai ta hannun Bulus, 12 har marasa lafiya suka warke, mugayen ruhohi suka fito daga cikin mutane, sa'adda suka karbi kyallaye da mayafai daga jikin Bulus. 13 Amma akwai Yahudawa masu tsubu da suka biyo ta wajen, suka dauka wa kansu su yi amfani da sunan Yesu. Suka ce, "Mun dokace ku cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa'azinsa, ku fita." 14 Wadanda suka yi wannan su bakwai ne 'ya'yan wani babban firist Bayahude mai suna Siba. 15 Mugun ruhun ya amsa ya ce, "Na san Yesu, na san Bulus, amma ku, su wanene?" 16 Sai mugun ruhun da ke cikin mutumin ya fada a kan matsubatan ya fi karfinsu ya kuma bubuge su. Suka runtuma da gudu suka fice daga dakin tsirara da raunuka. 17 Wannan ya zama sanannen abu ga dukan mutane, Yahudawa da Helenawa mazaunan Afisa. Suka ji tsoro kwarai, sunan Ubangiji Yesu ya sami daukaka. 18 Masu bi da yawa kuma, suka zo suka furta mugayen ayyukan da suka aikata. 19 Masu sihiri suka kawo littattafansu suka kona a gaban mutane. Da aka yi jimilar tamaninsu, aka samu sun kai dubu hamsin na azurfa. 20 Sai maganar Ubangiji ta yadu da iko ta hanyoyi da yawa. 21 Da Bulus ya kammala aikinsa na bishara a Afisa, Ruhu ya bishe shi sai ya bi ta Makidoniya da Akiya a kan hanyarsa zuwa Urushalima. Ya ce, "Bayan na je can, dole in je Roma." 22 Bulus ya aiki almajiransa biyu Timoti da Irastus zuwa Makidoniya, wadanda suka taimake shi. Amma shi da kansa ya jira a Asiya na dan lokaci. 23 A wannan lokacin sai aka yi babban tashin hankali a Afisa game da wannan Hanyar. 24 Wani Makeri mai suna Damatrayus wanda ke kera sifoffin gunkin azurfa na Dayana, wanda sana'a ce mai kawo wa makera riba sosai. 25 Ya tattara makera ya ce da su, "Kun sa ni da wanan sana'a ne muke samun kudi mai yawa. 26 Kun gani kun kuma ji cewa, ba a Afisa kadai ba, amma har da fadin kasar Asiya wannan Bulus ya rinjayi mutane da yawa. Yana cewa babu alloli da ake kerawa da hannu. 27 Ba sana'ar mu kadai ke cikin hatsari ba, amma har da haikalin allahnmu Dayana babba zai zama mara amfani. Ta haka za ta rasa girmanta, ita da dukan kasar Asiya da duniya ke wa sujada." 28 Da suka ji haka sai suka fusata kwarai, suka yi kira mai karfi suna cewa "Mai girma ce Dayana ta Afisa." 29 Gari gaba daya ya rude, jama'a kuma sun hanzarta zuwa wurin taron. Kafin wannan lokaci, sun riga sun kama abokan tafiyar Bulus, wato Gayus da Aristakas wadanda suka zo daga Makidoniya. 30 Bulus ya yi niyya ya shiga cikin taron jama'ar, amma almajiran suka hana shi. 31 Haka nan ma wadansu abokan Bulus da ke shugabanin yankin al'umma Asiya sun aika masa da roko mai karfi kada ya shiga dandalin. 32 Wadansu mutane na kirarin wani abu, wadansu kuma na kirarin wani abu dabam, domin jama'a sun rude. Da yawa daga cikinsu ma ba su san dalilin taruwarsu ba. 33 Yahudawa suka kawo Iskandari ya tsaya a gaban taruwan jama'a. Iskandari ya mika hannunsa sama domin ya yi bayani ga jama'a. 34 Amma da suka gane shi Bayahude ne, sai dukansu suka kwala ihu wajen sa'a biyu, "Mai girma ce Dayana ta Afisa." 35 Da magatakardar garin ya sha kan jama'a, sai ya ce, "Ya ku mutanen Afisa, wanene bai san cewa birnin Afisa cibiya ce na allahn nan Dayana mai girma da na sifar da ta fado daga sama ba? 36 Tun da ba a karyata wadannan abubuwa ba, ya kamata ku yi shuru don kada ku yi wani abu a gaggauce. 37 Gama kun kawo wadannan mutane a wannan dakin sharia ba a kan su mafasa ne na haikali ba ko kuma masu sabo ga allahnmu ba. 38 Saboda haka idan Damatrayas da makeran da ke tare da su na da wata tuhuma a kan wani, kotuna suna nan a bude masu shari'a kuma suna nan. Ba ri su kai karar junansu. 39 Amma idan akwai maganganu na dubawa, za a daidaita su a taronmu na lokaci lokaci. 40 Domin hakika muna cikin hatsarin zargi game da hargitsin yau. Babu dalilin wanan yamutsi domin ba mu da bayani a kansa." 41 Da ya fadi haka, sai ya sallami taron.
Bulus ya tafi Afisus.
"Ƙasar tudu" wata yanki ne a Asiya da ake ce da ita a yau Turkey zuwa arewacin Afisus. Mai yiwuwa Bulus ya tafiya ta kasa ne a bisa tekun Aijiya zuwa Afisus (wato Turkey a yau) wadda ke gabacin Korintus ta teku.
Wannan kalmar na nuna alamar wata sabuwar bangaren labarin. Idan harshenku tana da wata hanya ta musamman na yin haka, kuna iya amfani da ita anan.
"ya yi tafiya ta"
Wato ko Ruhu Mai Tsarki ya sauko masu.
"bamu taɓa jin game da Ruhu Mai Tsarki ba"
AT: "wace irin baftisma aka yi maku?"
A nan iya juya wannan zuwa kammalallen jimla. AT: "An yi mana baftismar da Yahaya ke koyarwa akai"
AT: "baftismar da mutane ke roƙa a masu yayin da suka zo tuba"
A nan "wanda" na nufin Yesu kenan.
Wato wadda zai zo bayan Yahaya mai Baftisma nan gaba, ba wai mai binsa a jiki ba.
A nan "mutane" na nufin almajiran da ke magana da Bulus a Afisus. [19:1]
AT: "suka yi baftisma"
A nan "suna" na nufin iƙon da izinin Yesu. AT: "as matasyin masubin Ubangiji Yesu"
"ya dora hannayensa a bisa kansu." Mai yuwuwa ya dora hannayensa a bisa kafadan su ko a kansu. AT: "ya dora hannayensa a bisa kansu ya masu addu'a"
Ba kamar yadda yake a [2:3-4] ba. babu takamaimian bayani game da waɗanda sun fahimci abubuwan da suke faɗi.
Wannan na nuna kimamun mutanen da aka masu baftisma.
"mutum 12"
"Bulus yakan shiga taron majami'a na kimamun wata uku kuma a can yana magana da gabagadi"
"yana kawar masu da shakka da tabbacecen koyarwa"
A nan "mulki" na nufin shugabacin Allah a matsayin sarki. AT: "game da mulkin Allah a matsayin sarki" ko kuma "game da yadda Allah zai nuna kansa a matsayin sarki"
wato suka ƙi su ba da gaskiya. AT: "wasu Yahudawa sun ƙi su karɓa su kuma yi biyayya da sakon"
Ana maganar abinda Almasihu ke so mutane su gaskkanta da shi ne kamar wani hanya ne da mutum ae iya tafiya a cikinta. Kamar kalmar nan, "hanyar" wani laƙabi ne na Masubi a wannan lokacin. AT: "suka fara faɗin mugayen abubuwa wa taron game da bi" ko kuma "suka fara faɗa wa taron mugayen abubuwa a kan mabiyaen Almasihu da kuma mabiyan koyarwarsa game da Allah" (Dubi: and 9:2)
"suka fara faɗin mugayen abubuwa game da"
"a babbar ɗakin da Tiranus ke koyar da mutane"
Wannan sunan wani ne.
Wannan na iya nufin 1) Bulus ya yi wa'azin bishara ga jama'a da dama a dukkan Asiya ko kuma 2) Bisharar Bulus ya fito zuwa dukkan Asiya daga Afisus ta wurin Afisawan da kuma jama'ar da suka ziyarci Afisus da suka zo daga dukkan Asiya.
A nan "maganar" na nufin sakon. AT: "sakon Ubangiji"
A nan "hannu" na nufin Bulus da kansa. AT: Allah yana sa Bulus yă yi mu'ajizai ko kuma "Allah yana yin mu'ajizai ta wurin Bulus"
AT: "har man yayin da a kai wa marasa lafiya adikansa da kuma rigar aikin da suka taɓa Bulus"
Wannan na iya nufin 1) kayayyakin aiki da Bulus ya taɓa ko kuma 2) kayayyakin da Bulus ya saka ko ya yi amfani da su.
tufafu da ake iya sawa a kai
tufafin sa ake sawa a ayi aiki don su tare ainihin tufafun da mutum ya sa.
"marasa lafiya sun samu lafiya"
Wato mutanen da basu da lafiya. AT: "mutanen da ba lafiya" ko kuma "waɗanda basu da lafiya"
masu korin aljannu daga mutane ko wurare
A nan "suna" na nufin iƙon da izini
"Yesu" suna ne na yau da kullum a wannan lokacin, don haka masu tsubu suna son mutane su san wanda suke magana akai.
Wato iƙo da izininYesu. AT: "da izinin Yesu" ko kuma "da iƙon Yesu"
Wannan sunan wani ne.
"Na san Yesu da kuma Bulus" ko kuma "Na san Yesu, na Kuma san Bulus"
Ruhun ya yi wannan tambayan ne don yan nanata cewa matsubutan ba su da iƙo ko izini a kan mugayen ruhohi. AT: "amma ni ban san ku ba!" ko kuma "amma ku, baku da iƙo akai na!"
Wannan na nufin cewa mugun ruhin yake cikinsa ya dira akan matsubutan.
Matsubutan sun runtuma da gudu da jikunansu a tuɓe.
AT: "sun ɗaukaka sunan Ubangiji Yesu" ko kuma "sun ɗauki sunan Ubangiji Yesu da girma"
Wato iƙo da izinin Yesu.
"suka tattara litattafansu." Kalaman nan "litattafai" na nufin litattafan da ke ɗauke da ka'idodin sihiri.
"a gaban kowa da kowa"
"tumanin litattafan"
"50,000"
Kowane "azurfa" yana kusan kuɗin da ake biyan mai koduga a kowace rana.
"saboda waɗannan mannyan ayyuka, mutane masu yana sun ji bisharar Ubangiji Yesu"
An yi amfani ne da wannan kalmar don a sa alamar kaucewa daga ainihin labarin. Anan, Luka ya fãra faɗin wata sabuwar bangaren labarin.
"Bulus ya kammala aikin da Allah ke da shi dominsa a Afisa"
Wannan na iya nufin 1) Bulus ya zaɓa da taimakon Ruhu Mai Tsarki ko kuma 2) Bulus ya zaɓa a ransa, wato ya kudura a zuciyansa.
Akiya itace lardin Roma wurin da Korintus yake. Itace babbar birnin da ke ƙasar Helas kuma cibiyar lardin. Duba yadda aka juya wannan a [18:12].
"dole in kama hanya zuwa Roma"
Wannan sunan wani ne.
An ƙara bayyana a fili a ayoyin da ke gaba cewa Bulus ya tsaya a Afisus.
An maimaita wannan ne domin nanaci.
Wannan dai itace takaitaccen bayanni na farkon zancen.
"zuciyar mutanen ya ɓace ƙwarai" Duba yadda aka juya wannan a [12:18].
Wato na adinin Kirista kenan. Duba yadda aka juya wannan a [9:1]
Yadda aka yi amfani da kalmar nan "wani" yana gabatar da wani sabon mutum kenan a wannan labarin.
maƙerin tagula ne da ke aiki da su azurfa don yă kera kayan ado kamar su zinariya da sauransu.
Wannan dai sunan wani mutum ne. Damatrayus maƙerin azurfa ne a Afisus kuma yana gãba da Bulus da kuma ikkilisiyar da ke wurin.
"yana kawo kuɗi sosai ga duk masu ƙeran gumakai"
Sana'a itace aiki da mutum ke yi. AT: "sauran masu yin irin wannan aikin"
"kun zo ga sani da kuma fahimtar cewa"
Wato yadda Bulus ke hana mutane bautar gumakai kenan. AT: "ya sa mutanae da yawa suka daina bautar gumakai"
A nan "hannu" na nufin mutum gabaɗaya. AT: "Yana cewa gumakai da mutane ke ƙerawa ba ainihin alloli bane"
AT: "cewa mutane ba za su siya gumakan mu kuma ba"
AT: "mutane ba za su ga amfanin zuwa haikali don bautar allahnmu Artimas babba"
Girmar artimas yana samowa ne daga abinda mutane ke sammani da ita.
Wannan na nufin cewa jama'a masu yawa kenan domin a nuna cewa ita sananne ne a ko ina. A nan kalmomin nan "Asiya" da "duniya" na nufin jama'ar da ke Asiya da dukkan wuraren da aka sani a duniya. AT: "ita da jama'a da masu yawa a Asiya da sauran wurare a duniya ke bauta wa"
Wato maƙeran kena. AT: "suka yi fushi ƙwarai"
"suka daga murya sosai" ko kuma "suka yi ihu sosai"
Ana "gari" na nufin mutanen. AT: "Sai hankalin mutanen garin gabaɗaya ya tashi suka fara ihu"
Wannan dai taron 'yan banza ne ku kuma dai a ce na hargitsi ne.
Dandalin Afisus wuri ne da jama'a sukan taru domin tarurruka da kuma nishaɗi kamar su wasanni da kuma waƙoki da kaɗe-kaɗe. Wuri ne da ke waje da kujeru masu iya ɗaukan mutane dubbai.
Mutanen da ke tare da Bulus.
Waɗannan sunayen mutane ne maza
Dandalin Afisus wuri ne da jama'a sukan taru domin tarurruka da kuma nishaɗi kamar su wasanni da kuma waƙoki da kaɗe-kaɗe. Wuri ne da ke waje da kujeru masu iya ɗaukan mutane dubbai. Duba yadda aka juya "dandali" a [19:29]
Wannan sunan wani mutum ne.
Ana iya bayyani a fili cewa Iskandari yana nu na wa mutane ne da cewa ya son su yi shiru. AT: "ya motsa ga taron don su yi shiru"
"yana so ya yi wata bayyani"
Ana maganar ta da muryar mutane a lokaci ɗaya ne kamar suna ihun da murya ɗaya ne. AT: "cikin ɗaya" ko kuma "tare"
Wato "marubuci" ko kuma "sakatare" kenan.
Magatakardan ya yi wannan tambayan ne domin yă tabbatar wa taron cewa suna da gaskiya yă kuma karfafa su. AT: "kowa ya san cewa garin Afisus cibiya ce da ke kula da haikalin ... sama."
Magatakardan garin yana amfani ne da "bai" don ya nanata cewa dukkan mutane sun san da haka.
Jama'ar Afisa ne suna kula da kuma tsere haikalin Artimas.
Akwai sifar wata allah a cikin haikalin Artimas. An sifanta ta ne daga wata dutse ne da ta faɗo daga sararin sama. Mutane suka sammanain cewa dutsensa ta faɗo ne daga Zafsa, mai mulkin allolin Halenanwa (gumakai).
"Da shike kun san da waɗannan abubuwa"
"kada ku yi wani abu kamun ku zo kuna tunani aka"
ba tare da tunani sosai
Kalmomin nan "waɗannan mutane" na nufin Gayus da Aristakas ne, abokan tafiyar Bulus. (Dubi: [19:29])
"Domin abina nan da na faɗa maku gaskiya ne." Shi magatakardan garin ya faɗa a [19:37] cewa Gayus da Aristakas ba barayi bane ko masu zagin sha'anin addina ba.
Ana iya sanar da kalmar nan "ƙara" na zuwa "zargi" AT: "su na son su zargi wani"
Wakilan hukumar Romawa masu yanke hukuncin kiyaye doka a kotu
Wannan bata nufin cewa Dimitiriyas da waɗanda ke tare da sh zasu zargi juna. Yana nufin cewa wannan wuri ne da mutane gabaɗaya na iya faɗi zarginsu. AT: "Waɗannan mutane na iya zarge junansu"
"Amma idan kuna da wasu maganganu daomin tattaunawa"
AT: "sai mu daidaita a taron mu na lokaci lokaci"
Wannan na nufin taron jama'an gari gabaɗaya wanda shi magatakardar yake shugabancinsa.
AT: "cikin hatsarin zargi daga hukumar Romawa akan hargitsin da ta taso a yau.
Almajiran basu taba ji game da Ruhu Mai Tsarki ba.
Yahaya ya ce wa mutanen su gaskanta da wanda zai zo a bayansa.
Baftismar Yahaya baftisma na tuba ne.
Bulus ya yi masu baftisma cikin sunar Ubangiji Yesu.
Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauka a kansu suka yi magana da harsuna da kuma annabci.
Bulus ya janye daga wurinsu tare da wadanda suka ba da gaskiya sai ya fara koyarwa a makarantar Tiranus.
Sa'adda suka karbi kyallaye da mayafai daga wurin Bulus, suna warkad da marsa lafiya su na kuma fitar da mugayen ruhohi.
Mugun ruhun ya duke matsubatan sai suka runtuma da gudu suka fice tsirara da raunuka.
Yawancin masu sihiri a Afisa suka kona littattafansu a gaban mutane.
Bulus ya ce zai tafi Roma bayan je Urushalima.
Damatrayus ya damu cewa Bulus ya na koya wa mutane wai babu alloli da ana kera da hannu, kuma ana iya ganin gunkin Dayana banza.
Mutanen sun yi fushi sun kuma yi kuka da cewa Dayana mai girma ce, sun kuma cika duka garin da rudewa.
Almajiran da wasu shugabanin ba su bar Bulus ya yi wa jama'a magana ba.
Magatakarda ya ce wa mutanen su kawo zarginsu kotu.
Magatakarda ya ce mutanen suna cikin dauwan argi game da hargitsi kuma babu wani abin bayani.
1 Bayan da rikici ya kare, Bulus ya aika a kira al'majiran, ya karfafa su. Sa'annan ya yi bankwana da su, ya tashi zai tafi Makidoniya. 2 Bayan ya ratsa cikin lardunan yana yi wa masu bi gargadi sosai, sai ya zo kasar Helenawa. 3 Sa'adda ya yi wata uku a wurin, Yahudawa suka kulla masa makirci, yayin da yake shirin hawa Jirgi zuwa Suriya, sai ya canza ra'ayi ya koma ta Makidoniya. 4 Masu yi wa Bulus rakiyar zuwa yankin Asiya sun hada da Sobatarus dan Burus daga Biriya; Gayus mutumin Derbe; Timoti da Aristakus da Sakundus, dukansu masu bi ne daga Tasalonika; da Tikikus da Trofimus daga Asiya. 5 Amma wadansu har suka rigaye mu, suka jira mu a Taruwasa. 6 Da muka shiga Jirgi daga Filibi bayan kwanakin Gurasa mara yisti; bayan kwanaki biyar muka iske su a Taruwasa; kwananmu bakwai a wurin. 7 A rana ta fari ga mako, da muka taru domin karya gurasa. Bulus ya yi wa masubi jawabi, don ya yi niyyar ya tafi da wayewar gari; jawabinsa ya kai har tsakar dare. 8 A benen da suka taru akwai fitilu da yawa. 9 Wani matashi mai suna Aftikos yana zaune a kan taga, barci mai nauyi ya dauke shi; da shike Bulus ya tsawaita jawabinsa, saurayin da shike barci mai nauyi ya dauke shi sai ya fado daga kan bene na uku aka dauke shi matacce. 10 Sai Bulus ya sauka ya mike a bisansa ya rungume shi, sa'annan ya ce, "Kada kowa ya damu; domin yana darai bai mutu ba." 11 Sa'annan ya hawo kan bene domin cin gurasa tare da su, ya yi magana da su har gari ya waye daga nan ya bar su. 12 Suka kawo saurayin da rai, sun sami ta'aziya ba kadan ba. 13 Amma mu, da muka riga Bulus zuwa gun Jirgin, muka shiga zuwa Asos, mun shirya mu dauki Bulus a jirgi amma shi ya kudurta ya yi tafiya a kasa. 14 Da muka sadu a Asos, mun dauke shi a Jirgin ruwa zuwa Mitilitus. 15 Bayan tashin mu daga can, washegari muka zo tsibirin Kiyos. Washegari kuma muka zo birnin Militus. 16 Amma Bulus ya kudurta wucewa Afisa a Jirgi, don kada ya bata lokaci a Asiya, don yana sauri in ya yiwu ranar Fentekos ta same shi a Urushalima. 17 Daga Militus ya aika a kira masa dattawan iklisiyar Afisa. 18 Da suka zo wurinsa sai ya ce masu, "Ku da kanku kun san tun daga ranar da na sa kafata a Asiya, irin zaman da muka yi da kasancewar mu tare. 19 Na bauta wa Ubangiji da tawaliu har da hawaye, da wahalun da na sha saboda makircin Yahudawa. 20 Kun sani ban ji nauyin sanar da ku kowanne abu mai amfani ba, na bi ku gida gida ina koyar da ku abubuwa a sarari. 21 Kunsan yadda na gargadi Yahudawa da Hellenawa game da tuba ga Allah da bangaskiya ga Ubangiji Yesu. 22 Yanzu fa, gashi, zan tafi Urushalima, Ruhu Mai Tsarki ya nuna mani a fili dole in je, ban san abin da zai faru da ni a can ba. 23 Sai dai Ruhu Mai Tsarki ya nuna mani a kowanne gari cewa, sarkoki da wahalu suna jira na. 24 Amma ban dauka cewa raina yana da wani amfani gare ni ba, domin in cika tsere da hidimar da na karba daga wurin Ubangiji Yesu, ta shaidar bisharan alherin Allah. 25 Yanzu fa, duba, na san dukanku, wadanda na yi wa wa'azin mulkin Allah, ba za ku kara gani na ba. 26 Don haka na shaida maku a wannan rana, ba ni da alhakin jinin kowanne mutum. 27 Don banji nauyin sanar maku da dukan nufin Allah a gare ku ba. 28 Saboda haka ku kula da kanku, da masubi da Ruhu Mai Tsarki ya sanya ku shugabanni. Ku kula ku yi kiwon iklisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa. 29 Na sani cewa bayan tafiyata, kyarketai masu zafi za su shiga tsakaninku, kuma baza su rangwanta wa masubi ba. 30 Na sani har daga cikinku wadansu mazaje za su zo su fadi gurbattatun zantattuka, domin su janye almajirai zuwa gare su. 31 Saboda haka ku yi lura. Ku tuna da cewa shekara uku ban fasa yi wa kowannenku gargadi da hawaye dare da rana ba. 32 Yanzu ina mika ku ga Allah, da maganar Alherinsa, wadda take da ikon gina ku ta kuma ba ku gado tare da dukan wadanda ke cikin kebabbu na Allah. 33 Ban yi kyashin azurfa, ko zinariya, ko tufafin wani ba. 34 Ku da kanku kun sani na yi aiki da hannuwana, na biya bukatu na da na wadanda ke tare da ni. 35 Na zama maku abin koyi a kowace hanya game da yadda za ku taimaka wa nakasassu ta wurin aiki, da yadda za ku tuna da maganar Ubangiji Yesu, maganar da shi da kansa ya ce: "Bayarwa tafi karba albarka." 36 Bayan da ya yi magana haka, ya durkusa ya yi addu'a tare da su duka. 37 Dukansu kuwa suka yi kuka mai tsannani, suka rungume shi kuma suka sunbace shi. 38 Suka yi bakin ciki musamman domin abin da ya ce masu, ba za su kara ganinsa ba. Sai dukansu suka yi masa rakiya zuwa wurin jirgin ruwa.
Bulus ya bar Afisa ya cigaba da tafiye tafiyensa.
"Bayan hargitsin"
"ya yi masu sallama"
"ya ƙarfafa masubin sosai" ko kuma "ya faɗi maganganun ƙarfafawa sosai ga masubi"
"Bayan da ya kasance a waurin na wata uku." Ana maganar lokaci anan kamar wani abu ne da mutum ke iya yi
AT: "Yahudawa suka kulla masa makirci a ɓoye"
Wannan na nufin wasu Yahudawa. AT: "Wasu Yahudaw"
"yayin da ya gama shirin hawa jirgi zuwa Suriya"
A nan kalmar nan "shi" yana nufin Bulus ne. (Dubi: [21:1])
"Masu tafiya da shi"
Waɗannan duka sunayen mutane ne, maza.
Duk waɗannan sunayen wurare ne.
Waɗannan sunayen mutane ne, maza. Duba yadda aka juya waɗannan sunayen a [19:29].
"waɗannan mutane duk sun tafi kamun mu"
Wannan na nufin lokacin idin adinin keterewa na adinin Yahudawa. Duba yadda aka juya wannan a [12:3]
Gurasa yana cikin cin abincin su na kullum. Wannan nu iya nufin 1) Wato cin abinci tare kurum. AT: "ci abinci" ko kuma 2) wato abinci da za su ci tare domin tunawa da mutuwa Yesu da tashinsa. AT: "domin cin Jibin Ubangiji"
"ya cigaba da jawabi"
Mai yiwuwa wannan itace hawa ta uku a gidan.
Wannan wata buɗadden wuri ne a bango da ke da wata dakali da zai ishe mutum zama.
Wannan sunan wani mutum ne.
Ana maganar barci ne kamar wani abu ne mai nauyi da ke iya ɗaukan mutum. AT: "ya shiga barci da kyau" ko kuma "ya gaji sosai sosai har a ƙarshe ya shiga barci sosai"
Da suka sauko su duba yanayin da yake ciki, sai samu ya riga ya mutu. AT: "bene na uku; da suka ɗauke shi, sun samu ya riga ya mutu"
Wato bene biyu daga bene da ke ƙasa. Idan al'adan ku ba ta kirga bene na ƙasa, ana iya sanar da wannan a matsayin "bene na biyu"
Gurasa wata abinci ne na yau da kullum a lokacin cin abinci. A nan "gutsuttura gurasa na iya nufin cewa rarraba wasu abincin ci ba gurasa kadai ba.
"ya tafi"
Wato Aftikos kenan [20:9]. Wannan na iya nufin 1) shi saurayi ne wanda ya fi shekara 14 ko kuma 2) shi saurayi ne tsakanin 9 da 14 ko kuma 3) kalmar nan "sauayi" na iya nufin cewa shi bara ne
Kalmar nan "kanmu" na ƙara nanaci ne sa'annan yana bambanta Luka da abokan tafiyarsa da Bulus, wadda bai yi tafiyar sa ta jirgin ruwa ba.
Asus wata gari ne ƙasa da Beram a ƙasar Turkey a baƙin Tekun Aijiya.
An ce da kanshi ne domin a nanata cewa abinda Bulus ya kudurta a zuciyar sa kenan.
"yayi tafiya ta ƙasa"
Mitilini wani gari ne da ke garin Mitilini a ƙasar Turkey a baƙin Tekun Aijiya.
"kusa da tsibirin" daga ƙetaren tsibirin"
Kiyos wata tsibiri ne da ba ta baƙin tekun ƙasar Turkey a yau a Tekun Aijiya.
"muka iso tsibirin Samas"
Samas wata tsibiri ne a kudancin Kiyos a Tekun Aijiya a baƙin tekun Turkey a yau.
Militas wata gari ne da ke da tashan jirgi a yamma da ƙaramar Asiya kusa da baƙin Kogin Miyanda.
Bulus ya kamo hanya a jirgin ruwa suka wuce tashan jirgi da ke Afisa, gaba da kudu domin su sauka a ƙasar Militini.
A nan maganar "lokaci" ne kamar wani abu ne da mutum ke iya amfani da shi ko ƙashewa. AT: "domin kada yă cigaba da tsayawa a wurin na 'yan lokaci" ko kuma "domin kada yă makara"
Militini tashin jirgi ne da ke yammacin ƙaramar Asiya kusa da kogin Miyanda. Duba yadda aka juya wannan a [20:15]
Ana amfani ne da kalmar nan "da kanku" ne domin nanata maganar.
A nan "kafa" na nufin mutumin gabaɗaya. AT: "Na shigo Asiya"
AT: "yadda na riƙa bi da kaina lokacin da nake tare da ku"
AT: "ƙasƙanci" ko kuma "halin ƙasƙanci"
A nan "hawaye" na nufin rashin jin daɗi da kuma kuka. AT: "Da kuka yayin da nake bauta wa Ubangiji"
Wannan ba ta nufin dukkan Yahudawa. Amma yana nuna mana ne waɗanda suka ƙulla haka. AT: "wasu Yahudawa"
"Kun san yadda ban taɓa yin shiru ba, amma na riƙa sanar da ku"
Bulus ya koya wa mutane a cikin gidajen su. An fahimci kalmomin nan "na koyar". AT: "Kuma na koyar da ku a lokacin da nake gidajenku"
AT: "cewa akwai buƙata su tuba a gaban Allah, su kuma gaskanta ga Ubangiji Yesu Almasihun mu"
AT: "domin Ruhu Mai Tsarki ne ya iza ni in tafi can"
"kuma ban san abinda zai faru da ni a wurin ba"
A nan "sarkoki" na nufin kamu da ɗaurin Bulus a kurku. AT: "za a ɗaura ni a kurku a sa ni in sha wuya"
Ana maganar hidima da tsere ne kamar wasu abubuwa ne da Yesu ya bayar sa'annan Bulus ya karɓa. Anan "tsere" da "hidima" abu ɗaya ne. Bulus ya maimaita su ne domin nanaci. AT: "domin in kammala aikin da Ubangiji Yesu ya umarta in yi"
Bulus yana maganar kammala aikin Yesu ya umarce shi ya yi ne kamar gudun tsere ne.
"ta gaya wa mutane bisharan alherin Allah." Wannan itace hidimar da Bulus ya karɓa daga wurin Yesu.
"Yanzu, ku mayar da hankali domin na san"
"na san cewa dukkanku"
A nan "mulki" na nufin shugabancin Allah a matsayin sarki". AT: "ga waɗanda na yi masu jawabin shugabancin Allah a matsayin sarki" ko kuma "ga waɗanda na yi masu jawabin yadda Allah zai bayyana kansa a matsayin sarki"
AT: "ba za ƙu ƙara gani na a wanna duniyan kuma ba"
A nan "jini" na nufin mutuwar mutum, wadda, a wannan yanayin, ba mutuwar jiki ba ne amma mutuwa a ruhu yayin da Allah ya furta cewa mutum yana da alhakin zunibi. Bulus ya gaskiya na Allah. AT: "Ni na na da alhakin kowa da Allah ya shar'anta da hakin zunubi ta dalilin ba da gaskiya ga Yesu"
A nan, wannan na nufin kowane mutum, miji ko mace. AT: "kowane mutum"
"Don ban yi shiru in ƙi faɗa maku ba" AT: "Domin haƙiƙa na faɗa maku"
"Dashike nan da na faɗa maku gaskiya ne," na nufin dukkan abinda Bulus ya faɗa a maganar sa game da barin su.
Shugabannin Ikkilisiya na da hakin kula da al'umman masubi kamar yadda makiyayin tumaki ke tsare garkensa daga ƙyarkeci. AT: "taron masubi da Ruhu Mai Tsarki ya ɗanka maku. Ku tabbatar kun kula da ikilisiyar Allah"
Ana kamanta zuɓar da "jinin" Yesu anan a matsayin biyar Allah ne saboda zunubanmu. AT: "jama'ar da Almasihu ya cetas da zunubansu ta wurin zuɓar da jininsa a bisa giciye"
A nan "jini" na nufin mutuwar Almasihu.
Ana ba da misalin masu ƙoyarwar ƙarya ne da kuma masu kawo illa ga taron masubi kamar su ƙyarketai ne da ke cin tumaki a garke. AT: "abokan gãba da yawa za su shiga cikinku don su yi wa taron masubi illa"
Ana maganar masu koyarwar ƙarya su rinjaye masubi su fara bin koyarwar sa ne kamar yana rinjayar tumaki ne daga garke zuwa wurinsu. AT: "domin su rinjaye mutane wadda suke almajirai su zama almajiransu"
"ku zama a faɗake ku kuma tuna" ko kuma "ku zama a faɗake kuna tuna"
"ku zama a farke da lura kuma" ko kuma "ku yi shirya." Ana maganar shirin shugabannin masubi domin duk wanda yana son ya yi wa taron masubi barna kamar yadda sojoji masu tsaro ne ke tsaro da kyau domin abokan gãba.
"Ku cigaba da tuna cewa" ko kuma "Kada ku manta cewa"
Ba cewa ake wai bulu ya koyar masu kowane rana har shekara uku ba, amma ya ɗauki lokaci cikin tsawon shekara uku.
"Ban daina faɗakad da ku ba"
Ana "magana" na nufin jawabi. AT: "Ina addu'a Allah yă cigaba da kula da ku yă kuma taimake ku ku da gaskanta da jawabin da na yi maku game da alherinsa"
a ba wa wani dabam hakin kula da wani ko wani abu.
Ana maganar bangaskiyar mutum ne kamar wani ganuwa ne da ake ginata sama da karfi kuma. AT: "wadda ke da ikon sa ku ƙara zama da ƙarfi a bangaskiyanku"
Ana maganar "maganar alherinsa" ne kamar Allah ne da kansa zai ba wa masubi gãdo. AT: "Allah zai ba ku gãdo"
Ana magana albarkun da Allah ke ba wa masubi ne kamar kuɗi ne ko kuma wasu dukiya da ɗa na iya gãda daga mahaifinsa.
"Ban yi marmarin kuɗin wani ba" ko kuma "Ban yi marmarin kuɗin wani don kaina ba"
Tufafi ma dukiya ne; yawansu shi ne yawan arzikin mutum.
Kalmar nan "hannu" a nan na nufin mutumin da kansa. AT: "Ina yin aiki ne da kaina in samu kuɗi in biya bukatuna"
"ku yi aiki domin ku samu kuɗi ku taimaka wa mutanen da ba su iya samo wa kansu"
AT: nakasassun mutane" ko kuma "waɗanda ba su da ƙarfi"
"marar lafiya"
A nan "magana" na nufin abinda Yesu ya faɗa.
Wato mutum yana samun tagomashin Allah yana kuma ɗandana farin ciki mai yawa idan ya ba wa sauran mutane fiye da yawan karɓawa daga wurin wasu.
Al'ada ne na yau da kullum a durkusa yayin da ake yin addu'a. Alama ce na kaskanci a gaban Allah.
...
Sumbacin mutum a kumatu alama ce na nuna ɗayantaka ku kuma ƙauna a Gabas ta tsakiya.
AT: "ba za ku ƙara ganina a duniyan nan kuma ba.
Bulus ya canza shirinsa dominYahudawa sun yi shiri akansa kuma ya yi kusan tafiya zuwa Suriya.
A rana ta fari na mako, Bulus da masubi suka taru domin karya gurasa.
Saurayin ya faɗo daga kan bene na uku aka ɗauke shi matacce amma Bulus ya mika hannunsa a kansa sai rayu kuma.
Bulus ya na sauri zuwa Urushalima domin ya kai saboda ranar Fentakus.
Bulus ya ce ya kwaɓe Yahudawa da Hellenawa game da tuɓa ga Allah da kuma bangaskiya ga Ubangiji Yesu.
Ruhu Mai Tsarki ya na shaida wa Bulus cewa sarkoki da wahalu suna jiransa.
Bisharar Bulus shi ne ya shaida bisharar alherin Allah.
Bulus ya ce ba shi da alhakin jinin kowanne mutum domin ya sanar masu da dukan nufin Allah a gare.
Bulus ya umarce dattawan su bi da garken da kyau.
Bulus ya faɗa cewa wasu dattawa za su zo su faɗi gurbattatun zantattuka, domin su janye almajirai zuwa gare su.
Bulus ya danka dattawan Afisawa wa Allah.
Bulus ya yi aiki domin bukatarsa da na waɗanda ke tare da shi, ya kuma taimaka wa nakasassu.
Dattawan Afisawa sun yi bakin ciki musamman domin abin da Bulus ya ce ba za su kara ganinsa ba.
1 Da muka rabu da su, muka shiga jirgin ruwa muka mike hanya zuwa birnin Kos, washegari sai birnin Rodusa, daga nan sai kuma zuwa birnin Batara. 2 Da muka sami jirgi mai hayewa zuwa Fonisiya sai muka shiga. 3 Da muka hango tsibirin Kubrus muka bar shi a hagun mu muka nufi Suriya, muka sauka a birnin Taya domin a nan ne jirgin ruwan zai sauke kayansa. 4 Bayan mun sami almajirai sai muka zauna can kwana bakwai. Al'majiran suka ce ma Bulus, ta wurin Ruhu, kada ma ya je Urushalima. 5 Bayan 'yan kwanaki muka cigaba da tafiyarmu. Dukansu da matansu da 'ya'yansu suka raka mu har bayan birnin. Sa'annan muka durkusa a bakin gacci muka yi addu'a muka yi sallama da juna. 6 Sai muka shiga jirgin ruwa, su kuma suka koma gida. 7 Da muka gama tafiyarmu a Taya muka iso Talamayas. A nan ne muka gaisa da 'yan'uwa, muka zamna kwana daya da su. 8 Washegari muka tashi muka tafi Kaisariya. Muka shiga gidan Filibus mai shaida bishara, daya daga cikin bakwai din, muka zauna da shi. 9 Wannan mutum yana da 'ya'ya hudu mata, budurwai masu yin annabci. 10 Sa'anda muka zauna can 'yan kwanaki, wani annabi ya zo daga Yahudiya mai suna Agabus. 11 Ya zo wurinmu ya dauki damarar Bulus ya daure tasa kafar da hannayensa ya ce, "Ruhu Mai Tsarki ya ce, 'Haka Yahudawa za su daure mai wannan damarar, zasu kuma bashe shi ga al'ummai.'" 12 Da muka ji wannan sakon, sai dukanmu da mazaunan wurin muka roki Bulus kada ya tafi Urushalima. 13 Sai Bulus ya amsa ya ce, "Me kuke yi, kuna kuka kuna karya mani zuciya? Bama a shirye don dauri kadai nake ba har ma da mutuwa a Urushalima, sabili da sunan Ubangiji Yesu." 14 Tun da Bulus bashi da niyyar a rinjaye shi, muka daina kuka muka ce, "Bari nufin Ubangiji ya tabbata." 15 Bayan wadannan kwanaki, muka dauki jakkunanmu muka haura Urushalima. 16 Wadansu almjirai daga Kaisariya suka bi mu. Sun zo ne tare da wani ana ce da shi Manason, mutumin Kuburus mai bi na farko, wanda za mu zauna da shi. 17 Da muka isa Urushalima, 'yan'uwa suka marabce mu da farin ciki. 18 Washegari Bulus ya tafi tare da mu zuwa wurin Bitrus, dukan dattawa kuma suna nan. 19 Bayan ya gaishe su, sai ya shaida masu daya bayan daya abubuwan da Allah ya yi cikin al'ummai ta wurin hidimarsa. 20 Da suka ji haka, suka yabi Ubangiji suka ce masa, "Ka gani, dan'uwa, dubban Yahudawa sun bada gaskiya suna kuma da niyyar kiyaye shari'a. 21 An kuma gaya masu a kanka cewa, kana koya wa Yahudawan da suke zaune cikin al'ummai su yi watsi da Musa. Kana koya masu kada su yi wa 'ya'yansu kaciya, kada kuma su bi tsofaffin al'adu. 22 Me ya kamata mu yi? Hakika za su ji ka zo. 23 Sabo da haka ka yi abin da muka fada maka yanzu. Muna da maza hudu da suka dauki wa'adi. 24 Tafi da wadannan ka tsarkake kanka tare da su, ka dauki dukan dawainiyar su dana askin kai. Ta haka kowanne mutum zai sani abubuwan da ake fadi a kanka karya ne. Za su sani cewa kai mai kiyaye shari'a ne. 25 Game da al'umman da suka bada gaskiya mun yi masu wasika, mun bada umarni su kaurace kansu daga sadakokin da aka mika wa gumaku, da jini, da abin da aka makare da kuma fasikanci. 26 Sai Bulus ya dauki mazannan, washegari ya tsarkake kansa tare da su, suka shiga haikali, domin ya sanar da cikar ranakun tsarkakewarsu, wato ranar ba da sadaka domin kowanne dayansu. 27 Da kwanakin nan bakwai suka yi gab da cika, wadansu Yahudawa daga Asiya suka ga Bulus a haikali, sai suka zuga taro, suka danke shi. 28 Suna ta kururuwa, "Mutanen Isra'ila ku taimaka mana. Wannan shine mutumin da ke koya wa dukan mutane ko'ina abubuwa gaba da mutane, da shari'a da kuma wannan wurin. Banda haka ya kawo Helenawa cikin haikalin nan ya kazantar da wannan wuri tsatsarka." 29 Domin dama sun ga Tarofimas mutumin Afisa tare da Bulus cikin birni, suka yi zaton ya kawo shi cikin haikali. 30 Sai duk gari ya rude, mutane suka runtuma suka danke Bulus. Suka ja shi waje daga cikin haikalin, nan da nan aka rufe kofofin. 31 Suna kokarin kashe shi kenan, sai labari ya kai wurin hafsan sojoji cewa Urushalima duk ta yamutse da tarzoma. 32 Nan take ya dauki mayaka da jarumawa, suka sheka da gudu wurin taron. Da mutane suka ga hafsan sojoji da rundunansa sai suka daina dukan Bulus. 33 Sai hafsan ya tafi ya danke Bulus ya sa aka daure shi da sarkoki biyu. Ya tambaya ko shi wanene da kuma laifinsa. 34 Wadansu cikin taron suna ta kururuwa wadansu su ce wannan, wadansu su ce, wancan. Tunda hafsan bai fahimci abin da suke fadi ba, sabo da ihunsu, ya dokaci a shigar da Bulus farfajiyar sojoji. 35 Da suka kai matakala, sojoji suka dauki Bulus sabo da tsananin husatar taron jama'a. 36 Domin taron suka biyo baya suna ihu suna cewa, "A kashe shi." 37 An kusa shigar da shi farfajiyan kenan sai Bulus ya ce wa babban hafsan, "Ko ka yarda inyi magana da kai?" Hafsan ya ce, "Ka iya Helenanci? 38 Ashe ba kai ne Bamasaren nan da kwanakin baya ka haddasa tawaye, ka dauki 'yan ta'adda dubu hudu ka kai su jeji ba?" 39 Bulus ya ce, "Ni Ba'ibrane ne daga birnin Tarsus a Kilikiya. Ni dan kasar babban birni ne. Ka amince mani in yi magana da mutanen." 40 Da hafsan ya bashi izni, Bulus ya mike a kan matakala ya daga hannayensa sama ya yi nuni su yi shuru. Da wuri ya yi tsit, Bulus ya yi masu magana da Ibraniyanci. Ya ce,
Marubucin Luka, Bulus da abokan tafiyansu sun cigaba da tafiye tafiyensu.
A nan kalmar nan "mu" na nufin Luka, Bulus, da waɗanda ke tafiya tare da su, amma ba masu karatu ba.
"muka tafi birnin Kos" ko kuma "muka wuce zuwa garin Kos"
Kos wata tsibiri ne na Hellas daban da baƙin Turkey a yau da ke kudancin tekun jaha Aijiya.
Rodusa tsibirin Hallas ne da ke daban da tsibirin Turkey a yau a kudancin Tekun Aijiya a jiha kuduncin Kos dakuwa arewa ta gaba na Karita.
Batara wata birni ne a baƙin kogin kudu ta yamma na Turkey a yau kudancin Tekun da ke Tekun Bahar Rum.
A nan "jirgin mai hayewa" na nufin ƙungiyar da ke tafiya a jirgin. AT: "Da muka sami jirgin a da ƙungiyar da ke hayewa zuwa Fonisiya"
A nan dai "hayewa" ba ta nufin cewa jirgin tana kan hayewa ba amma tana nufin cewa jirgin za ta haye Fonisiya ba da jimawa ba. AT: "jirgi da za ta ketere ruwa" ko kuma "jirgin da za ta tashi"
"muka wuce tsibirin a gefen hagu" hagun itace gefen "masukin" jirgin ruwan.
A nan "jirgin" na nufin ƙungiyar da ke tafiya a jirgin ruwan. AT: "ƙungiyar da ke tafiya a jirgin za su sauke kayansa"
"Waɗannan masubi suka gaya wa Bulus abinda Ruhu Mai Tsarki ya bayyana masu. Suka "ta ce masa sau da dama"
AT: "Bayan kwanaki bakwai" ko kuma "Da lokacin tafiya ya kai"
Hali ne na yau da kullum a durkusa yayin da ake yin addu'a. Yin haka alama ce na kaskanci a gaban Allah.
"muka koma gida"
Talamayas wata gari ne a Taya ta kudu, Lebanon. Talamayas itace Akir, Isra'ila a yau.
"'yan'uwa masubi"
"bakwai" ɗin na nufin mutanen da aka zaɓa su raɓa abinci su kuma taimake gwamraye a 6:5.
"Filibus" daga aya 8.
mai bishara
A nan amafani ne da wannan kalmar anan don a sa alamar kauchewa daga ainihin labarin. Anan, Luka yana faɗin tarihin Filibus ne da 'ya'yansa, mata.
"budurwai huɗu mata da sukan karɓan maganar Allah su kuma ba da shi ga mutane.
Wannan na gabatar da wani sabon mutum ne a labarin.
Agabus mutumin Yahudiya ne.
"ya ciro ɗamarar Bulus daga ƙudun Bulus"
Ana sanar da sakon wani da cikin sanar da furcin wani. AT: "Ruhu Mai Tsarki ya ce haka ne Yahudawan Urushalima za su ɗaure ... ga al'ummain.
Wannan na nufin Yahudawan da za su aikata wannan, ba wai dukkan Yahudawa ba. AT: "shugabannin Yahudawa" ko kuma "wasu Yahudawan"
"miƙa shi"
AT: "ga masu yanke shari'a na al'ummai"
Wato masu iƙo a cikin al'ummai. AT: "al'ummai masu iƙo"
Bulus ya yi wannan tambaya ne domin yă nuna wa masubi cewa su daina ƙoƙarin jawo hankalinsa. AT: "Ku daina wannan abinda kuke yi. Kuka da kuke yi yana ƙarya mani zuciya"
Ana maganar sa mutum yin baƙin ciki ne kamar zuciya ne da ke ƙarye wa. A nan "zuciya" na nufin yadda mutum ke ji. AT: "sanyaya mini gwiwa" ko "baƙanta mini rai"
AT: "bama kadai don su ɗaure ni kawai ba"
A nan "suna" na nufin Yesu da kansa. AT: "sabili da Ubangiji Yesu" ko kuma "domin na ba da gaskiya ga Ubangiji Yesu"
AT: "ba ya so mu rinjaye shi ya je Urushalima"
AT: "Bari komai ta kasance yadda Aallah ya shirya ta"
"Akwai wani tare da su"
Manason wani ne daga tsibirin Kuburus"
Wato, Manason yana ɗaya daga cikin waɗanda suka fara gaskanta da Yesu.
A nan "'yan'uwa" na nufin masubi da ke Urushalima, ko miji ko mace. AT: "'yan'uwa masubi suka marabce mu"
"ya ba da ƙwaƙwaran labarin su duka"
A nan "ɗan'uwa" na nufin "ɗan'uwa mai bi"
Yana nan a bayyane cewa akwai wasu Yahudawa da ke ɓata koyarwar da Bulus ke yi. Shi bai hana Yahudawa kiyaye shari'ar Musa ba. Sakon sa dai shi ne basu buƙatan kaciya da wasu al'adu kamun Yesu yă iya cetonsu. Ana iya ƙara bayyana cewa shugabannim Yahudawa masubi da ke Urushalima na da sanin cewa koyarwar Bulus gaskiya ne.
AT: "Mutane sun gaya wa Yahudawa masubin"
A nan "Musa" na nufin shari'ar Musa. AT: "su daina kiyaye shari'un da Musa ya ba mu"
A nan maganar biyayya da tsofofin al'adu ne kamar al'adun ne suke jagora yayin da mutanen ki bi a baya. AT: "kada su yi biyayya da tsofofin al'adu" ko kuma "kada su gwaninta a tsofofin al'adu"
"al'adun da Yahudawa suka saba kiyayewa"
"maza huɗu da suka yi wa Allah alkawari." Wato irin alkawarai wanda mutum ba zai sha ruwan inabi ba ko kuma yă aske gashin kansa har sai bayan wasu lokatai da aka keɓe.
Sai sun tsarkake kansu kamun su iya shiga sujada a haikalli.
"ka biya masu dukkan buƙatunsu." Kashe kanshen za su tafi dukka wajen siyan ɗan tinkiya na mace da na miji, rago, da kuma hatsida baye bayen sha.
Wannan alama ne cewa mutum ya kammala alkawarin da ya yi wa Allah.
AT: "abubuwan da mutane ke faɗi a kanka"
Ana maganar kiyaye shari'a ne kamar shari'ar shugaba ne da mutane ke iya bi a baya. AT: "yi biyayya da shari'a" ko kuma "yi rayuwa da ta dace da shari'ar Musa da kuma sauran al'adun Yahudawa"
Waɗannanduka ka'idodi ne game da abinda za su iya ci. An hana su cin naman dabbobin da aka sadaukad wa gunki, nama da ke da jini a cikinta, da kuma naman dabban da aka maƙure domin akwai jini a cikinta. Duba yadda aka juya irin wannan jimlar a [15:20].
AT: "su guje naman dabba da wani ya sadaukad ga gunki"
Ana iya ƙara bayyani akan dabbobin da aka muƙure. AT: "daga dabbobin da wani ya maɍƙure" ko kuma "daga dabbobin da wani ya maƙure do a ci amma ba tare da an janye jininsa ba.
Wato mutane huɗun nan da suka ɗauki wa'adi.
Kamun ya shiga gefen haikali inda ake buƙatar Yahudawa su tsarkake kansu tukuna. Wannan tsarkakewar ya shafe ma'amalan da Yahudawa ke yi da Halenawa.
Basu shigo cikin wurin da babban firist ne kawai ke iya shiga a haikalin ba. Sun shiga harrabar haikali. AT: "suka shigo harrabar haikali"
Wannan wata hanyar tsarkakewa ne da ake buƙata su cika domin su iya shiga harrabar haikali.
AT: "har sai sun miƙa dabba domin sadaka"
Wato kwanaki bakwai na tsarkakewa kenan.
Ba wai Bulus yana cikin haikalin ne ba. Yana harraban haikalin ne. AT: "a harrabar haikali"
Ana maganar hanzuga mutane su yi matuƙar fushi da Bulus kamar sun zuka hankalin taron ne. AT: "suka sa mutane da yawa a cikin taron sun yi fushi ƙwarai da Bulus"
A nan "suka ɗanke shi" na nufin a "kama" ko kuma "riƙe." Duba yadda aka juya "suka ɗanke" a [5:18] AT: "suka riƙe Bulus"
"mutanen Isra'ila, da shari'ar Musa, da kuma haikali"
Yahudawa ne kawai akan bari shi shigo wasu wurare a cokon harrabar haikalin da ke Urushalima.
wannan karin bayyani ne. Luka yana bayyana dalilin da ya sa Yahudawa daga Asiya suna ɗaukan cewa Bulus ya kawo Bahalene cikin haikali.
Wannan shi ne mutumin da ake zargin Bulus cewa ya shigo da shi haikali wurinda Yahudawa ne kadai su ke shiga. Duba yadda aka juya sunan sa a [20:4]
Kalmar nan "duk" na nufin masu yawa. Kalmar nan "gari" na nufin Urushalima. AT: "Mutane masu yawa a barin suka yi fushi da Bulus"
"suka kama Bulus" ko kuma "suka riƙo Bulus"
An rufe kofofin domin kada a yi hargitsin a harrabar haikali. AT: "Nan da nan sai wasu Yahudawa suka rufe kofofin haikali. ko kuma " Nan da nan sai masu tsaron haikalin suka rufe kofofin"
A nan "labari" na nufin ɗan aika da ya je ya faɗi labarin. AT: "mai ba wa babban hafsan sojoji labari"
Ana amfani da jimlar nan "ya kai wurin" ne domin babbar hafsan yana wata sansani ne da ke haɗe da haikali a sama da harrabar haikali.
Wato shugaban sojojin Roma da ke shugabantar sojoji 600
Kalmar nan "Urushalima" na nufin Urushalima. Kalmar nan "duk" na nufin hankalin mutane masu yawa zai tashi. AT: "mutane da yawa a Urushalima suna yamutase"
Akwai mataka na sauka daga sansanin zuwa harrabar.
AT: "ya umarci sojojinsa su ɗaura shi"
Wannan na nufin cewa sun ɗaure Bulus kusa da sojojin Roma biru, ɗaya a kowane gefensa.
Ana iya sanar da wannan a matsayin ambacin abinda wani ya faɗa. AT: "Ya tambaya, 'Wanene wannan mutumin? Menene laifinsa?"
Babbar hafsan sojojin yana magana da taron ne, ba da Bulus ba.
Ana iya fahimtar kalaman nan "suna kururuwa" a jimla na baya. AT: "sai wasu suna kururuwa wani daban" ko kuma "sai wasu kuma a cikin taron na kururuwar wani abu daban"
Wato shugaban sojojin Roma da ke shugabantar sojoji 600.
AT: "ya dokaci sojojinsa su sgigar da Bulus"
Wannan sansanin yana haɗe sa wajen harrabar haikali.
AT: "Da Bulus ya shigo matakan sansanin, sojojin sun ɗauke shi"
Taron suka amfani ne da wata hanya mai sauki da kuma wata hanya daban na roƙo a ƙashe Bulus. AT: "Ku ɗauki ransa" ko kuma "Ku ƙashe shi"
AT: "Da sojojin suka yi shirin kawo Bulus"
Wannan sansanin yana haɗe sa wajen harrabar haikali.
Babban hafsan sojojin yana tambaya domin ya nuna mamakinsa cewa Bulus ba wanda yake tunanin shi ne ba. AT: "Ashe ka iya Halenanci. Ina tsammanin ko kai ne Bamasaren da ke haddasa tawaye a jeji ba, tare da 'yan ta'adda dubu huɗu"
Ba da jimawa ba kamun zuwa Bulus, wani mutum da masar wanda ba ambaci sunansa ba, ya haddasa tawaye ga Roma a Urushalima. Jim kaɗan sai ya tsere da gudu zuwa jeji, sai kuma shugaban sojojin yana mamamki ko Bulus ne wannan mutumin.
AT: "sa mutane suka tayar wa mulkin Roma"
"'yan ta'adda 4,000"
Wato taron Yahudawa masu tawaye da mulkin Roma da duk wanda ke goyon bayan Romawa.
"Na roƙe ka" ko "I na roƙon ka"
"don Allah ka amince mini" ko kuma "don Allah ka yarda mini"
AT: "hafsan ya amince wa Bulus ya yi magana"
Kalmar nan "matakala" a nan na nufin mataka zuwa sansanin.
Ana iya karin bayyanin dalilin da ya sa Bulus ya daga hannayensa. AT: "ya daga hannayensa domin mutanen su yi shiru"
Da mutanen suka yi tsit gabaƙiɗaya"
Almajirai a Taya suka ce wa Bulus ta wurin Ruhun cewa kada ya je Urushalima.
Filibus yana da 'ya'ya hudu mata, budurwai masu yin annabci.
Agabus ya faɗa wa Bulus cewa Yahudawa za su ɗaure shi su kuma bashe shi ga al'ummai.
Bulus ya faɗa cewa ya na shirye domin a ɗaura shi ya kuma mutu a Urushalima sabili da sunar Ubangiji Yesu.
Bulus ya sadu da Yakubu da kuma dukan dattawa.
Yahudawa sun yi wa Bulus zargin koya wa Yahudawa da suke zama a cikin al'ummai cewa su bar Musa.
Sun so kowa ya san cewa Bulus Ba-Yahuda ya na rayuwa domin ya kiyaye doka.
Yakubu ya ce al'ummai su kaurace kansu daga sadakokin da aka mika wa gumaku, da jini, da abin da aka makare da kuma fasikanci.
Yahudawa sun yi wa Bulus zargin koyarwa da ba daidai a doka ba, yana kuma kazantar da haikali ta wurin kawo Helenawa ciki.
Yahudawan sun jawo Bulus daga cikin haikali sun kuma so su ƙashe shi.
Hafsan sojoji ya danke Bulus ya sa aka ɗaure shi da sarkoki biyu, ya tambaya ko shi wanene da kuma da abin da ya yi.
Taron suna ihu suna cewa, "A kashe shi."
Bulus ya roka cewa a bar shi ya yi wa mutanen magana.
Bulus ya yi wa mutanen magana da Ibraniyanci.
1 "Yanuwa da Ubanni, ku saurari kariya ta zuwa gare ku yanzu." 2 Da taron sun ji Bulus na magana a harshen Ibraniyawa sai sun yi tsit. Ya ce, 3 Ni Bayahude ne daga garin Tarwasa na Kilikiya, amma a karkashin Gamaliyal aka ilimantar da ni. An horar da ni sosai bisa ga bin hanyar dokokin kakkaninmu. Ina da himma ga bin Allah kamar yadda ku ma kuna da ita. 4 Na tsananta wa wannan Hanyan har ga mutuwa; na daure maza da mata sa'annan na jefa su cikin gidan yari. 5 Hakannan ma babban firist da dukan dattawa za su ba da shaida cewa na karbi izini daga wurinsu domin 'yan'uwa da ke a Dimashku, saboda in tafi can. Haki na shine in daure mabiyan Hanyan nan, in kawo su Urushalima domin a hukunta su. 6 Sa'anda ina cikin tafiya, ina kuma kusa da Dimashku, da tsakar rana sai farat daya ga babban haske daga sama ya haskaka kewaye dani. 7 Na fadi kasa sa'anan na ji murya na ce da ni, 'Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani?' 8 Na amsa, 'Wanene kai, Ubangiji?' Ya ce mani, 'Nine Yesu Banazarat wanda kake tsananta wa.' 9 Wadanda ke tare da ni sun ga hasken, amma ba su gane muryar wanda ya yi magana da ni ba. 10 Na ce, 'Me zan yi ya Ubangiji?" Ubangiji ya ce mani, 'Tashi ka tafi cikin Dimashku, a can za a fada maka abinda wajibi ne ka yi. 11 Ban iya ganin wuri ba domin walkiyar hasken, sai na tafi cikin Dimashku ta wurin jagorancin wadanda ke tare da ni. 12 A can na sami wani mai suna Ananiya, mai tsoron Allah bisa ga sharia, da kyakyawan suna kuma a gaban Yahudawa da ke zama a can. 13 Ya zo gare ni ya ce, 'Dan'uwa Shawulu, karbi ganin gari.' A daidai wannan sa'a na gan shi. 14 Sa'annan ya ce, 'Allah na kakkaninmu ya zabe ka ka san nufinsa, ka ga Mai Adalcin nan, ka kuma ji muryar da ke fitowa daga bakinsa. 15 Gama za ka zama mashaidinsa ga dukan mutane game da abinda ka gani da wanda ka ji. 16 A yanzu me ka ke jira? 'Tashi a yi maka baftisma a wanke zunubanka, kana kira bisa sunansa.' 17 Bayan da na dawo Urushalima, sa'anda ina addu'a a cikin haikali, sai na karbi wahayi. 18 Na gan shi ya ce mani, 'Gaggauta ka bar Urushalima yanzu, domin ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.' 19 Na ce, 'Ubangiji, su da kansu sun san yadda na sa su a kurkuku na kuma doddoke wadanda suka gaskanta da kai a kowacce masujada. 20 A sa'anda a ke zubar da jinin mashaidinka Istifanus, ina nan tsaye ina goyon baya, ina kuma lura da rigunan wadanda suka kashe shi.' 21 Amma ya ce mani, 'Tafi, domin zan aike ka can wurin Al'ummai.' 22 Mutanen sun bar shi yayi magana har zuwa ga wannan lokacin. Amma sai suka ta da murya suna cewa, 'A kawar da wannan dan taliki daga duniya: don bai kamata ya rayu ba.' 23 Sa'anda suke tadda muryarsu, suna jefar da tufafinsu da kuma baza kura a iska, 24 babban hafsan ya umarta a kawo Bulus a farfajiyan. Ya umarta da cewa a bincike shi da bulala, domin ya san dalilin da suka ta da ihu gaba da shi haka. 25 Bayan da suka daure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa Jarumin da ke kusa da shi, "Ko daidai ne bisa ga doka a yi wa Barome wanda ma sharia ba ta kashe shi ba bulala?" 26 Da Jarumin ya ji haka, ya tafi wurin babban hafsan, yana cewa, "Me kake so ka yi? Gama wanan mutumin dan asalin Roma ne." 27 Babban hafsa ya zo ya ce masa, "Gaya mani, kai dan asalin Roma ne?" Bulus ya ce, "Haka ne." 28 Babban hafsan ya amsa masa, "Da kudi masu yawa na sayi yancin zama dan kasa." Amma Bulus ya ce, "An haife ni dan kasar Roma. 29 "Sai mutanen da sun zo su tuhume shi sun bar shi nan da nan. Babban hafsa shi ma ya tsorata da ya gane Bulus dan asalin Roma ne, domin ya riga ya daure shi. 30 Washegari, babban hafsan ya so ya san gaskiyar tuhuma da Yahudawa suke yi a kan Bulus. Sai ya kwance shi daga sarka, ya kuma umarci babban firist da dukan majalisa su sadu. Sai ya kawo Bulus ya sa shi a tsakiyarsu.
Bulus yana magana da taron Yahudawa a Urushalima.
Aya 2 yana ba da karin bayyani.
Wannan wata hanya ne mai sauki na yi wa tsaran Bulus da 'yan gaba da shi a tsakanin mas sauraro.
"yanzu zan yi maku bayyanin" ko kuma "yanzu zan zan gabatar maku"
Harshen Ibraniyawa itace harshen Yahudawa da.
AT: "Amma ni dalibin malam Gamaliyal ne a nan Urushalima"
A nan "kařkashi" na nufin yadda mutum zai zauna yayin da yake koyo daga malami. AT: "ta wurin Gamaliyal"
Gamaliyal wani sanannen malamin dokar Yahudawa ne sosai. Duba yadda aka juya wanna a [5:34]
AT: "Ya horar da shi a hanyar da zai iya kiyaye kowane dokar kakkaninmu" ko kuma "Horaswar da na samu sun bi daki daki yadda dokokin kakkaninmu"
"dokokin kakkaininmu." Wato dokokin da Allah ya ba jama'ar Isra'ila ta wurin Musa.
"Na miƙa kai in yi biyayya da Allah" ko kuma "Ina da marmarin yi wa Allah hidima"
"daidai yadda kuma kuke a yau." Bulus yana ƙwatanta kansa da taron jama'ar.
A nan "wannan hanyan" na nufin mutanen da ke na wannan taron mutanen da ake ce da su "hanyar." AT: "Na tasananta wa mutanen da ke na wannan hanya"
Haka a ke ce da adinin Kirist ko kuma masu bi a da. Duba yadda aka juya "wannan Hanyan" a [9:2].
Ana iya juya kalmar nan "mutuwa" zuwa "kisa" ko kuma "mutu". AT: "kuma na nema hanyoyin kasahe shi su" ko kuma "har ma na sa suka mutu"
"ina ɗaure mutane maza da mata ina sa su a kurkuku"
"za su iya shaida" ko kuma "za su iya faɗa maku"
babbar firist da dattawa sun bani wasiku"
Ana "'yan'uwa" na nufin "'yan'uwa Yahudawa."
Sun bani umarni na ɗaura da sarkoki waɗanda ke 'yan hanya in mayar da su Urushalima"
AT: "domin su karɓi hukuncinsu" ko kuma "domin hukumar Yahudawa su hukunta su"
Ana amfani ne da wannan jimlar don a nuna wurin da zancen ya fara. Idan harshenku tana da wata hanya ta musamman na yin haka, kuna iya moransa anan.
A nan "murya" na nufin mai magana. AT: "Na ji wani ya ce mini"
A nan "murya" na nufin mutumin da yake magana. AT: "basu fahimci abinda mai magana da ni ke cewa ba"
AT: "a can wani zai faɗa maka" ko kuma "a wurin za ka san"
"Na zama makahu saboda tsananin walkiyar hasken"
A nan "jagoranci" na nufin waɗanda ke bi da Bulus. AT: "waɗanda suka bi da ni zuwa Damishku"
Wannan Hananiya daban ne da wanda ya mutu dama [5:3], kuna iya juya wannan yadda kuka yi a [5:1]
Hananiya na da ƙwazo ƙwarai game da kiyaye shari'ar Allah.
AT: "Yahudawa da ke zama a wurin suna ba da kyakyawar shaida a kansa"
A nan "Ɗan'uwa" wata hanya ne may kyau na yaba wa mutum. AT: "Abokina Shawulu"
AT: "fara gani kuma"
Wannan wata hanya ne na nuna cewa abu ya faru nan da nan. AT: "nan take" ko kuma "nan da nan" ko kuma"
"abinda Allah ke shiryawa yana kuma sa yă faru"
Da "murya" da "baƙi" duka suna nufin mai magana. AT: "ka kuma ji shi yana magana da kai kai tsaye"
A nan "mutane" na nufin jama'a maza da mata. AT: "ga dukkan jama'a"
Ana amfani ne da kalmar nan "yanzu" a nan ba wai don yana nufin "a daidai wannan sa'a" ba, amma domin a jawo hankali ne ga wata muhimmin zance da ke bin wannan.
An yi amfani ne da wannan tambaya domin a gargaɗe Bulus ya yi baftisma. AT: "Kada ka jira" ko kuma "Kada ka ɓata lokaci"
AT: "bari in yi maka baftisma" ko kuma "karɓi baftisma"
Kamar yadda wanke jiki ke cire datti, kira ga sunan Yesu domin gafarrar zunubai yana tsabtacce zukatan mutum daga zunubi. AT: "ka roƙa gafarrar zunubanku"
A nan "suna" na nufin Ubangiji. AT: "kana kira bisa Ubangiji ko kuma "kana dogara ga Ubangiji"
AT: "na samu wani wahayi" ko kuma "Allah ya bani wata wahayi"
"Na gan Yesu yana ce mini"
"waɗanda suke Urushalima ba za su yarda da abinda za ka faaɗ masu akai na ba"
Ana amfani ne da kalmar nan "da kansu" domin nanaci.
"Bulus ya je masujadai da dama yana neman Yahudawa da suka gaskanta da Yesu.
A nan "jini" na nufin rai na Istifanus. A zuɓar kuma na nufin a ƙashe. AT: "sun ƙashe Istifanus mai ba da shaida a kanka.
Wannan jimlar "daga duniya" na kara nanata ne da cewa a kawar da irin mutumin. AT: "Ƙasheshi"
"Yayin da suka." Ana amfani ne da jimlar nan "Sa'anda suke" domin a sa alamar abubuwa biyu da ke aukuwa a lokaci ɗaya.
Wannan na nuna cewa Yahudawa da ke wurin sun yi fushi domin Bulus ya saɓa wa Allah ta wurin maganarsa.
hafsan sojojin Roma ko kuma shugabana sojojin kusan 600
AT: "ya umurce sojojinsa su kawo Bulus"
Wannan sansanin yana haɗe sa wajen harrabar haikali. Duba yadda aka juya wannan a [21:34]
Shi shugaban sojojin yana so Bulus ya sha azaba ne ta wurin yi masa duka domin ya tabbatar cewa Bulus ya faɗa masu gaskiya. AT: "Ya umarce sojojinsa su bulali Bulus don su tilasta shi ya faɗa masu gaskiya"
Ana amfani ne da kalmar nan "kansa" domin nanaci.
wato tsirkiyar laida ko kuma na fatan dabba.
Bulus yana amfani ne da wannan tambayan domin yă sa Shugaban yă bincike ko daidai ne da aka sa sojoji su bulali Bulus. AT: "Ba daidai ba ne bisa ga doka a bulali mutumin da ke Baome ba tare da an yi masa bincike ba!"
An yi amfani ne da wannan tambaya domin a sa shugaban ya ƙara tunani shirinsa yă bulali Bulus. AT: "Kada ka yi haka!"
A nan ana iya juya "zo" zuwa "je"
"Bayan da na biya hukumar Roma kuɗi masu yawa ne." Shi hafsan ya yi wannan magana ne domin ya san cewa yana da wuya ƙwarai mutum ya zama Barome, yana kuma ɗaukan cewa ba gaskiya ne Bulus ke faɗi ba.
"Na sami yancin zama ɗan ƙasa." AT: "na zama ɗan ƙasa"
Muddin Uban mutum ɗan ƙasa Roma ne, to lallai ne 'ya'yansa su zamanto 'yan ƙasar Roma daga haihuwa.
"mutanen da suka yi shirin tuhumar" ko kuma "mutanen da suke shirin su tuhume"
Mai yiwuwa "babbar hafsan" na nufin babbar hafsan sojojin. AT: "Don haka, babbar hafsan ya umurce sojojin su kwance sarkokin Bulus"
Daga sansanin, akwai wani matakala saukowa daha harrabar haikalin.
A loƙacin da taron suka ji Bulus na magana da Yahudanci, suka yi tsit.
Bulus ya karatu a Urushalima kuma Gamaliyal ne malaminsa.
Bulus ya tsananta wa waɗanda suke bin hanyan har ga mutuwa, ya kuma jefa su cikin kurkuku.
Murya daga sama ya ce, 'Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani?
Bulus ya na tsananta wa Yesu Banazarat.
Bulus bai iya gani kuma ba saboda hasken da ya gani sa'ad da ya yi kusa da Dimashku.
Mutum mai tsoron Allah ya zo ya tsaya a gefen Bulus ya ce, "Dan'uwa Shawulu, karbi ganinka."
Ananiya ya ce wa Bulus ya tashi a yi masa baftisma don a wanke zunubansa.
Yesu ya faɗa cewa Yahudawa ba za su karba shardar Bulus game da shi ba.
Yesu ya aike Bulus wurin Al'ummai.
Mutanen suke tadda muryarsu, suna jefar da tufafinsu da kuma baza kura a iska.
Bulus ya yi tambaya ko daidai ne bisa ga doka a yi wa Barome wanda sharia ba ta kashe shi ba bulala?
An haife Bulus dan kasar Roma ne.
Babban hafsan ya kwance shi daga sarka, ya kuma umarci babban firist da dukan majalisa su sadu da Bulus a tsakiyarsu.
1 Bulus ya kura wa yan majalisa ido yace, '"Yan'uwa, na yi rayuwa tare da Allah da lamiri mai kyau har wannan ranan." 2 Babban firist Hannaniya ya ba wandanda suke tsaye tare da shi urmarni su buge bakinsa. 3 Bulus ya ce, "Allah zai buge ka, kai munafiki. Kana zama domin ka shari'anta ni da shari'a, kuma ka umarce a buge ni, gaba da sharia?" 4 Wanda suka tsaya a gefe suka ce, "Kada ka zage babban firis na Allah." Bulus yace, "Ban sani ba, 'yan'uwa, cewa shi babban firis ne. 5 Domin a rubuce yake, Ba za ku zargi shugaban mutanenku ba." 6 Da Bulus ya ga cewa, daya bangaren Sadukiyawa ne dayan kuma Farisawa, ya yi magana da karfi a majalisa, '"Yan'uwa, ni Bafarise ne, dan Farisawa. Don tabbacin tashin matattu ne kuna shari'anta ni." 7 Daya fadi haka, mahawara ta fara a tsakanin Farisawa da Sadukiyawa, sai taron ya rabu kashi biyu. 8 Don Sadukiyawa suka ce babu tashin matattu, babu mala'iku, babu kuma ruhohi, amma Farisawa suka ce dukan abubuwan nan sun kasance. 9 Sai mahawara ta tashi, wadansu marubutan Farisawa suka tashi da mahawara cewa, "Ba mu same mutumin nan da laifi ba sam. Ko mala'iku da ruhohi ne suka yi masa magana?" 10 Da jayayya ta tashi, babban hafsa ya ji tsoro kada su yayaga Bulus, sai ya umarce sojoji suje su kwato shi da karfi daga 'yan majalisa, su tafi da shi farfajiya. 11 Da dare Ubangiji ya tsaya kusa da shi yace, "Kada ka ji tsoro, kamar yadda ka ba da shaida game da ni a Urushalima, dole zaka sake zama shaida a Roma." 12 Da gari ya waye, wadansu Yahudawa sun yi yarjejeniya suka dauka wa kansu la'ana: suka ce ba za su ci ba ba za su sha ba sai sun kashe Bulus. 13 Mutane fiye da arba'in suka kulla wannan makirci. 14 Suka je wurin manyan firistoci da dattawa suka ce, "Mun sa wa kanmu la'ana, ba za mu ci ba, ba za mu sha ba sai mun kashe Bulus. 15 Yanzu, bari majalisa ta ba wa babban hafsa izini a kawo shi a gaba, kamar zai yanke hukunci. Mu kam, a shirye muke mu kashe shi kafin ya iso nan. 16 Amma dan yar'uwan Bulus ya ji suna labe, sai ya tafi ya shiga farfajiyar ya fada wa Bulus. 17 Bulus ya kira daya daga cikin jarumai yace, "Dauki saurayin nan ka kai shi wurin babban hafsa, don yana da abin da zai fada masa." 18 Jarumin ya dauke saurayin ya kai shi wurin babban hafsa yace, "Bulus dan sarka ne yace in kawo saurayin nan a gaban ka. Yana da abin da zai fada maka." 19 Babban hafsa ya kai shi wani lungu, sai ya tambaye shi, "Menene kake so ka fada mani?" 20 Saurayin yace, "Yahudawa sun yarda su roke ka ka kawo Bulus gobe a majalisa, kamar zasu kara bincike a kan al'amarin. 21 Amma kada ka yarda da su, mutane fiye da arba'in suna jiransa. Sun sa wa kansu la'anna, ba za su ci ba ba za su sha ba sai dai sun kashe shi. Yanzu a shirye suke; suna jira ka ba su izini." 22 Sai babban hafsa yace wa saurayin ya tafi, da ya gama masa magana, "Kar ka fada wa wani al'amuran." 23 Sai ya kira jarumai biyu yace, "Ku shirya sojoji dari biyu, yan dawakai saba'in, masu daukar mashi dari biyu su tafi kaisariya karfe uku na dare." 24 Ya umarta a shirya dabbobin da Bulus zai hawo da zasu kai shi lafiya wurin Filikus gwamna. 25 Sai ya rubuta wasika a misalin haka: 26 Gaisuwa zuwa Kuludiyas Lisiyas zuwa ga mai martaba gwamna Filikus. 27 Yahudawa sun kama wannan mutumin suna shirin kashe shi, na abko masu da sojoji na kwace shi, bayan da na ji shi Barome ne. 28 Inna son sani dalilin zarginsa, sai na kai shi majalisa. 29 Na gane cewa ana zarginsa ne a kan tambayoyi game da shari'ansu, amma ba wani zargi da ya cancanci dauri ko mutuwa. 30 Da aka sanar da ni shirin makircin, sai na tura shi wurinka ba da bata lokaci ba, na umarce masu zarginsa su kawo zarginsu wurinka. Huta lafiya." 31 Sai sojoji suka yi biyayya da umarni da aka basu: suka dauki Bulus suka kawo shi dadare a wurin Antibatris. 32 Da gari ya yawe, yan dawakai suka tafi tare da shi kuma sauran sojoji suka koma farfajiya. 33 Bayan da yandawakan suka isa Kaisiririya sun mika wasika ga gwamna, suka kuma danka Bulus a hanunsa. 34 Da gwamna ya karanta wasikar, sai ya tambaye su daga wani yanki ne Bulus ya fito; da ya ji daga yankin kilikiya ne, 35 Yace zan saurare ka sosai lokacin da masu zargin ka sun zo. Sai ya umarta a tsare shi a fadar Hiridus.
Bulus yana gaban babban firist da kuma majalisarsa. (Dubi: [22:30])
Wannan na nufin "'Yan'uwa Yahudawa"
"Na san cewa har wa yau na yi abinda Allah yake so in yi"
Sunan mutumin kenan. Kodashike wannan sunan daban ne da Hananiya da ke a [5:1]), da kuma wanda ke a [9:10]).
Bulus yana nuna wa Hananiya ne cewa kodashike, ya fita kamar mutumin kirki, amma yana nan cike da mugun tunani a zuciyansa. AT" ...
Bulus yana amfani ne da wannan tambayan domin ya nuna munafincin Hananiya. AT: "Ka zauna a nan ka shar'anta ... gãba da shari'a."
AT: "ka umarci mutane su buge ni"
Mutanen suna amfani ne da wanna tambayan domin su yi wa Bulus tsawa domin abinda ya faɗa a [23:3]. AT: "Kada ka zage babban firis na Allah!"
Bulus zai furta abinda Musa ya rubuta kenan a cikin Shari'a. AT: "Gama Musa ya rubuta a cikin shari'a"
A nan "ɗa" na nufin shi ainihin ɗan Bafarisi ne da kuma zuriyar Farisiyawa. AT: "kuma mahaifi na da kakkani na farisiyawa ne"
A nan iya sanar da wannan kalmar "tashi" zuwa "dawuwa da rai." Ana kuma iya sanar da kalmar nan "mutuwa" zuwa "waɗanda suka mutu." AT: "waɗanda suka mutu za su samu rai kuma, ... ni"
AT: "kuna shar'a'anta ni"
"mutanen da ke taron suka ƙi yarda da juna sam"
Wannan yana kara ba da hasken bayyani ne game da Sadukiyawa da Farisiyawa
"Sai suka fara yi wa juna ihu." Kalmar nan "sai" yana nuna abin da ya faru domin wani abu daban da ya faru a baya. A wannan hali, abinda ya faru a baya shine Bulus ya furta gaskantawar shi da tashin matattu.
Farisiyawan suna sauta wa sadukiyawan ta wurin tabbatar masu cewa akwai ruhohi da mala'iku kuma suna iya magana da mutane. AT: "Mai'yiwuwa wani ruhu ko mala'ika ya yi magana da shi!"
A nan iya mayar da waɗannan kalmomi "jayayya mai tsanani" zuwa "gardama mai tsanani." AT: "Da suka fara wata gardama mai tsanani"
wani shugaban sojojin Roma mai mai shugabancin sojoji 600
Jimlar nan "a yi kaca kaca da Bulus" na maganar yadda mutanne za su iya yi wa Bulus illa. AT: "za su iya yayyaga Bulus kaca kaca" ko kuma "za su yi wa Bulus wata babbar rauni a jiki"
"su yi amfani da ƙarfin jiki su tafi da shi"
Wannan sansanin yana haɗe sa wajen harrabar haikali. Duba yadda aka juya wannan a [21:34]
Wato bayan daren da Bulus ya je gaban majalisa. AT: "A Daren nan"
A nan iya fahimtar waănnan kalmomin "game da na". AT: "ba da shaida a kai na a Roma" ko kuma "ka shaide ne a Roma"
"suka shirya kansu da manufa ɗaya" andn, domin su ƙashe Bulus.
A nan iya kara bayyana dalilin da zai sa la'ana ya bi su. AT: "sun roƙi Allah ya la'antasu idan basu yi abinda sun alkawarta su yi ba"
"mutum 40"
"suka haɗa wannan shiri" ko kuma "suka yi shirya su ƙashe Bulus"
A nan kalmar nan "Su" na nufin Yahudawa arba'in da ke [23:13] ne
A nan maganar ɗaukan alkawari ne da kuma roƙon Allah ya la'anta su idan basu cika alkwarinsu ba kamar wani abu ne da za su ida sa wa a bisa kapaɗansu. AT: "Mun ɗauki rantsuwa cewa ba za mu ci kome ba har sai mun kashe Bulus. Mun roƙi Allah ya la'anta mu idan ba mu cika wannan alkwarin ba"
"Da shike abin nan da muka faɗa gaskiya ne, ko kuma "Da shile mun sa wa kanmu a wannan la'ana"
Ba "a dai dai wannan lokaci" ake nufi ba, amma ana amfani ne da wanna domin a jawo hankali mutane a akan wani abu mai muhimmanci da ke bi a baya.
"kawo Bulus daga sansanin domin yă same ku"
"kamar kuna so ku ƙara sani game da abinda Bulus ya yi"
"suna bagon Bulus" ko kuma "suna jira su kashe Bulus"
Sansanin yana haɗe ne da harrabar wajen haikali. Dubia yadda aka juya wannan a [21:34]
"Bulus ɗan sarka ne ya ce in zo in yi magana da shi"
Da shike Babban hafsan ya kai saurayin, ya kuma ce da shi saurayi, wannan na nufin cewa, ɗan ƙanen Bulus yana iya zama mai shekara 12 zuwa 15.
Wannan bai shafe dukkan Yahudawa ba, amma dukkan taron Yahudawa da ke wurin. AT: "Wasu Yahudawan sun yarda"
"ka kawo Bulus daga sansanin"
"suna son su ƙara sani game da laifin da Bulus ya yi"
"sun shirya bagon Bulus" ko kuma "sun shirya su kashe Bulus"
"Sun rantse cewa ba za su ci ko su sha komai ba har sai sun kashe Bulus. Sun ce ma Allah ya la'anta su idan basu cika alkawarin yin abinda sun ce za su yi ba"
"ya kira gareshi"
"jarumai 2"
'yan dawakai 70"
"sojoji dari biyu da aka masu ɗamarar yaƙi da mashi"
wato 9:00 p.m. da dare.
Wannan ce gabatarwa ta musumman a wasikar. Babbar hafsan ya fara da kansa. Ana iya gane wannan da "ina rubutowa". AT: "Ni, Kuludiyas Lisiyas, ina rubutowa zuwa gareka, mai martaba, gwamna Filikus. Gaisuwa mai yawa zuwa gareka"
"zuwa ga gwamna Filikus da ya cancanci dukkan girma"
A nan "Yahudawa" na nufin "wasu Yahudawa." AT: "wasu Yahudawa sun kama wannan mutum"
AT: "sun yi shirin kashe Bulus"
"Ni da sojoji na muka iso wurin d a Bulus da Yahudawan suke"
AT: "cewa suna zarginsa a kan tambayoyi game da"
AT: "amma ba wanda ya zarge shi da wani abu da zai sa hukumomin Romawa su kashe shi ko su ɗaure shi ba"
AT: "Daga baya na gane"
Kalmar nan "sai" na nuna alama ne cewa hakan ya faru ne ta dalilin wani abu da ya faru a baya. A wannan karo, abinda ya faru a baya shi ne umarnin da babbar hafsan ya bayar cewa sojoji su raka Bulus.
A nan ana iya juya "kawo" zuwa "kai." AT: "Suka samo Bulus sai sun kai shi da dare"
A nan iya sanar da wannan a matsayin furci. AT: "Ya tambaye Bulus, 'daga wani yanki ka fito?' Da
AT: "Bulus ya ce, 'Ni daga Kilikiya ne.' Sai gwamna ya ce"
"Zan saurare duk maganan da kake da shi"
AT: "ya umurci sojoji su tsare shi" ko kuma "ya umarci sojoji su masa tsaro"
Babban firist ya yi fushi domin Bulus ya ce ya yi rayuwa tare da Allah da lamiri mai kyau.
Bulus ya ce za a hukunta shi domin tabbacin tashin matattu da yake da shi.
Mahawara ta fara domin Farisawa suka ce akwai tashin matattu amma Sadukiyawa suka babu tashin matattu.
Babban hafsa ya ji tsoro kada 'yan majalisa su yayaga Bulus.
Ubangiji ya ce wa Bulus kada ya ji tsoro domin zai yi shaida a Urushalima da a Roma.
Kusan mutane arba'in suka yi yarjejeniya cewa ba za su ci ko su sha ba sai sun kashe Bulus.
Sun ce wa babban firist da dattawa cewa a kawo Bulus wurin majalisa domin su iya ƙashe shi kafin ya isa.
Ɗan yar'uwan Bulus ya ji game da shirin sai ya faɗa wa Bulus.
Babban Kyaftin ya umarce manyan sojoji su kai Bulus lafiya wurin Filikus gwamna a sa'a ta ukun ɗare.
Babban hafsan ya ce Bulus bai cancanci ɗauri ko mutuwa ba, amma wai zargin game da tambayoyi ne akan dokar Yahudawa.
Filikus yace zai saurare Bulus sosai loƙacin da masu zargin shi sun zo.
An ajiye Bulus a fadar Hiridus sai ranar shari'arsa.
1 Bayan kwanaki biyar, sai Ananiyas babban firist, Wasu dattawa da wani masanin shari'a mai suna Tartilus, sun tafi can. Suka kai karar Bulus gaban gwamna. 2 Lokacin da Bulus ya tsaya gaban gwamna, Tartilus ya fara zarginsa yace wa gwamnan, "Saboda kai mun sami zaman lafiya; sa'annan hangen gabanka ya kawo gyara a kasarmu; 3 don haka duk abin da ka yi mun karba da godiya, ya mai girma Filikus. 4 Domin kada in wahalsheka, ina roko a yi mani nasiha don in yi magana kadan. 5 An iske mutumin nan yana barna irir iri, yana kuma zuga jama'ar Yahudawa a dukan duniya su yi tayarwa. 6 Har ma ya yi kokarin kazantar da haikali; saboda haka muka kama shi. [1]7 Amma Lisiyas jami'i ya zo ya kwace shi da karfi daga hannunmu. 8 Idan ka binciki Bulus game da wadannan al'amura, kai ma, zai tabbatar maka abin da muke zarginsa a kai. 9 Dukan Yahudawa suna zargin Bulus cewa wadannan abubuwa gaskiya ne. 10 lokacin da gwamnan ya alamta wa Bulus ya yi magana sai yace, "Yanzu na fahimci cewar da dadewa kana mulkin kasarnan, don haka da farin ciki zan yi maka bayani. 11 Zaka iya tabbatarwa cewa bai kai kwana sha biyu ba tun da nake zuwa Urushalima don yin sujada. 12 Da suka same ni a haikali, ban yi jayayya ko kawo rudami a tsakanin jama'a ba. 13 Don haka ba su da tabbas akan abinda suke zargina a kansa yau. 14 Amma na sanar da kai, bisa ga abin da suke kira darika, haka ni ma nake bautawa Allah na kakanninmu. Na yi aminci wajen kiyaye dukan abin da ke a rubuce a Attaurat da litattafan annabawa. 15 Ina sa bege ga Allah, kamar yadda za a yi tashin matattu, masu adalci da miyagu; 16 a kan haka kuma, nake kokarin zama mara abin zargi a gaban Allah da mutane ina yin haka cikin dukan al'amura. 17 Bayan wadansu shekaru na zo in kawo wasu sadakoki da baikon yardar rai. 18 Cikin kudurin yin haka, sai wasu Yahudawa daga kasar Asiya suka iske ni a cikin ka'idodin tsarkakewa a haikali, ba da taro ko ta da hargitsi ba. 19 Yakamata wadannan mutanen su zo gabarka a yau, har idan suna da wani zargi a kai na. 20 In kuwa ba haka ba bari mutanennan su fada in sun taba iske ni da wani aibu a duk lokacin da na gurfana a gaban majalisar Yahudawa; 21 sai dai ko a kan abu daya da na fada da babbar murya sa'adda na tsaya a gabansu, 'Wato batun tashin matattu wanda ake tuhumata ake neman yi mani hukunci yau.'" 22 Filikus yana da cikakken sanin tafarkin Hanyar, shi yasa ya daga shari'ar. Yace da su, "Duk sa'anda Lisiyas mai ba da umarni ya zo daga Urushalima, zan yanke hukunci." 23 Sa'annan ya umarci jarumin ya lura da Bulus, amma ya yi sassauci, kada ya hana abokansa su ziyarce shi ko su taimake shi. 24 Bayan wadansu kwanaki, Filikus da mai dakinsa Druskila, ita Bayahudiya ce, ya kuma aika a kira Bulus ya saurare shi game da bangaskiya cikin Kristi Yesu. 25 Amma sa'adda Bulus yake bayyana zancen adalci, kamunkai, da hukunci mai zuwa, Filikus ya firgita ya ce, "Yanzu ka tafi. Amma idan na sami zarafi an jima, zan sake neman ka." 26 A wannan lokacin, yasa zuciya Bulus zai bashi kudi, yayi ta nemansa akai-akai domin yayi magana da shi. 27 Bayan shekaru biyu, Borkiyas Festas ya zama gwamna bayan Filikus, domin neman farin jini a wurin Yahudawa, ya ci gaba da tsaron Bulus a gidan yari.
A nan gwada Bulus a Kaisariya. Tartilus ya miƙa wa Gwamna Filikus ƙarar da ke kan Bulus.
A nan kalmar nan "kai" na nufin Filikus, gwamna.
"bayan kwanaki biyar da sojojin Roma suka kai Bulus Kaisariya"
Wannan sunan wani mutum ne.
Wannan sunan wani mutum ne. Wannan Hananiya daban ne da wanda aka yi maganarsa a [5:1], da kuma Hananiya da ke [9:10]. Duba yadda aka juya wannan a 23:1
"wani lauya." Tartilus wani shaharren Masanin shari'ar Romawa ne, ya kasance a kotu ne musamman domin ya zargi Bulus.
"tafi Kaisariya inda Bulus yake dama"
"gaban gwamna wanda shi ne alkali a kotun"
"Ya fara ƙarar a gaban gwamna cewa Bulus ya ƙarye doka."
Ana "mu" na nufin 'yan gari da ke karkashin mulkin Filikus. AT: "mu, jama'a da kake mulkimu, muna zaman lafiya"
"sa'annan shirin da ka yi ya ƙara ƙyau ƙasarmu"
"Filikus gwamna wanda ya cancanci dukkan girma" Filikus ne gwamnar Roma da ke mulkin dukkan yankin. Duba yadda aka juya irin wannan jimlar a [23:25]
Wannan na iya nufin 1) "domin kada in ci maka lokaci" ko kuma "domin kada in gajiyad da kai"
"yi hakuri ka ɗan saurare maganar da zan yi"
Ana maganar Bulus kamar wani aloba ne da ke yaduwa daga wannan mutim zuwa wancan mutum. AT: "mutumin nan fitinanne ne"
Wannan dai karin magana ne domin a jaddada zargin da ke kan Bulus.
Jimlar nan "ɗariƙar Nazarawa" wata suna ne na masubi. AT: "Yana kuma shugabantan taron jama'a da ake ce da su mabiyan Nazarawa"
Wanna wata ƙaramar ƙungiya a cikin manyan ƙungiyoyi. Tartilus yana ganin masubi a matsayin wata ƙaramar ƙungiya a cikin adinin Yahudanci.
"ka gane ko waɗannan zargin da muka kawo a kansa gaskiya ne" ko kuma "ka gane ko yana da laifin abubuwan da muka zarge shi akai"
Wannan na nufin shugabannin Yahudawa da ke wurin da ake gwada Bulus.
"gwamnan ya motsa"
A nan "ƙasa" na nufin mutanen ƙasar Yahudawa. AT: "mai shari'ar mutanen ƙasar Yahudawa"
"bayana maka yanayina"
"kwana 12 tun"
"ta da hargitisi" anan karin magana ne da ke nufin ta da hankulan mutane. AT: "ban ta da hankalin taron ba"
"ɗaukan laifofin munana ayyukansu" ko kuma "zargin laifofi
"Na shaida maka wannan" ko kuma "Na furta maka wannan"
Jimlar nan "hanyar" wata laƙabi ne da ke nufin masubi a zamanin Bulus.
Wanna wata ƙaramar ƙungiya a cikin manyan ƙungiyoyi. Tartilus yana ganin masubi a matsayin wata ƙaramar ƙungiya a cikin adinin Yahudanci. Duba yadda aka juya "ɗariƙa" a [24:5]
Bulus yana amfani ne da wannan kalmar "haka" don yă nuna cewa shi, a matsayinsa na maibin Yesu, yana bauta wa Allah yadda kakkaininsu na Yahudawa suka yi. Yana shugabantar wata "ɗariƙa" ko kuma yana koyar da wata sabuwan abu da ke gãba da addininsu na zamanin dã.
"kamar yadda waɗannan mutanen suka yi" Anan "waɗannan" na nufin Yahudawa masu zargin Bulus a kotu.
Ana iya sanar da kalmar nan "tashin" zuwa "ta da" AT: "cewa Allah zai ta da dukkan waɗanda suka mutu, da masu adalci da marasa adalci"
Wannan na nufin mutane masu adalci da mugayen mutane. AT: "mutane masu adalci da mutane marasa adalci" ko kuma "waɗanda suka aikata abinda ke daidai da waɗanda suka aikata abinda ba daidai ba"
"nake himma kullum" ko kuma "ina iya ƙoƙari"
A nan "lamiri" nan nufin tunani ko kuma hankalin mutum da ke iya sanin abinda ke daidai da wanda ba daidai ba. AT: "zama marar laifi" ko kuma "in riƙa aikata abinda ke daidai"
"a gaban Allah"
Wannan kalmar na nuna dabara a muhawarar Bulus. Ana ya bayyana yanayin Urushalima a lokacin da wasu Yahudawa suka kama shi.
"bayan wasu shekaru nesa da Urushalima"
A nan ana iya juya kalmar nan "na zo" zuwa "na je." AT: "Na je in tallafawa wa mutane na ta wurin kawo masu gudumawar kuɗi"
"a cikin haikali bayan na gama ka'idodin tsarkake kaina"
Ana iya sanar da wannan a wata sabuwar jimla. AT: "Ban hada taro ba, ba ma ina ƙoƙarin ta da hargitisi ba
"Yahudawa daga Asiya"
"idan suna da wani abin faɗi"
Wato mutanen majalisar da ke nan a Urusahlima a lokacin shari'ar Bulus.
"su faɗi abinda na yi wanda ba daidaiba da za su iya su hakikanta"
A nan iya sanar da kalmar nan "tashin matattu" zuwa "Allah zai tashe su da rai" AT: "Wato saboda na gaskanta cewa Allah zai ta da matattu ne
AT: "kana yi mini shari'a a yau"
Wannan wata laƙabi ne na Masubi. Duba yadda aka juya shi wannan [9:2]
"sa'anda Lisiyas mai ba da umarni ya ko kuma "in Lisiyas ma ba da umarni ya zo"
Wannan ne sunan babban hafsan. Duba yadda aka juya wannan sunan a [23:26]
Urushalima yana tudu fiye da Kaisariya, don haka ana iya ce mutum ya sauko daga Urushalima.
"zan yanke maka hukunci game da zargin da ke a kanka" ko kuma "zan shar'anta ko kana da laifi"
"ba wa Bulus yanci kadak wanda ba a ba sauran 'yan kurkuku"
"Bayan kwanaki da dama"
Wannan sunan wata mace ce.
Wato mace a Yahudawa. AT: "wadda Bayahudiya ce"
Mai yiwuwa Filikus ya ji tabbacin zunubansa"
"a daidai wannan lokaci"
Filikus yana sa zuciya Bulus zai bashi toshiya don a sake shi.
"don haka Filikus yakan aika ya gan Bulus akai akai don yă yi magana da Bulus"
Wannan shi ne sabon Gwamnar Roma wanda ya maye gurbin Filikus.
A nan "Yahudawa" na nufin shigabannin Yahudawa. AT: "domin yana so shugabannin Yahudawa so so shi"
"ya bar Bulus a Kurkuku"
Tertullus ya yi wa Bulus zargin cewa ya na sa Yahudawa su yi tawaye da kuma kazantar da haikali.
Tertullus ya ce Bulus ne shugaban ɗariƙar Nazarawa.
Bulus ya ce bai yi jayayya da kowa ba kuma bai kawo rudami a tsakanin jama'a ba.
Bulus ya ce ya na da aminci ga dukan abin da ke a rubuce a Attaurat da litattafan annabawa.
Su na da bangaskiya ga Allah game da tashin matattu masu adalci da marasa adalci.
Bulus ya ce ya zo ya kawo taimako ga al'ummansa da kuma ƙyautar kuɗi.
Bulus ya ce ya na cikin bikin tsarkakewa a loƙacin da an same shi.
Gwamna Filikus yana da cikakken sani game da Hanyar.
Filikus ya ce zai yanke hukuncin Bulus a loƙacin da Lisiyas mai ba da umarni ya zo daga Urushalima.
Bulus ya faɗa wa Filikus game da bangaskiya cikin Almasihu Yesu, adalci, kamunkai, da kuma hukunci mai zuwa.
Filikus ya ji tsoro sai ya ce wa Bulus ya tafi daga gabansa.
Filikus ya bar Bulus a kurkuku domin neman farin jini a wurin Yahudawa.
1 Da Festas ya shiga lardin, kuma bayan kwana uku, ya tashi daga Kaisariya ya tafi Urushalima. 2 Sai babban firist da manyan Yahudawa suka kawo wa Festas sara a kan Bulus. 3 Suka roki tagomashi wurin Festas ya kira Bulus zuwa Urushalima domin su kashe shi a hanya. 4 Amma Festas ya amsa masu cewa, Bulus dan sarka ne a Kaisariya, kuma ba da dadewa ba shi da kansa zai koma can. 5 "Saboda haka duk wadanda za su iya, su biyo mu. Idan akwai wani laifi game da mutumin, sai ku zarge shi." 6 Bayan kwana takwas ko goma, sai ya gangara zuwa Kaisariya. Washegari ya zauna bisa kursiyin shari'a ya bada umarni a kawo Bulus a gabansa. 7 Da Bulus ya iso, Yahudawa daga Urushalima suka tsaya kusa, suka yi ta kawo kararraki, amma basu iya tabbatar da su ba. 8 Bulus ya kare kansa ya ce, "Ban yi wa kowa laifi ba, ko Yahudawa, ko haikali, ko kuma Kaisar." 9 Amma Festas yana neman farin jini wajen Yahudawa, sabo da haka ya tambayi Bulus ya ce, "Kana so ka je Urushalima in shari'anta ka a can game da wadannan abubuwa?" 10 Bulus ya ce, "Ina tsaye a Ddakalin Shari'ar Kaisar inda dole a shari'anta ni. Ban yi wa Yahudawa laifi ba, kamar yadda ka sani sosai. 11 Idan lallai na yi laifi kuma na yi abin da ya chanchanci mutuwa, ban ki ba in mutu. Amma idan zarginsu karya ne, kada kowa ya bashe ni gare su. Ina daukaka kara zuwa ga Kaisar." 12 Bayan Festas ya tattauna da majalisa ya amsa ya ce, "Kana kira ga Kaisar; za ka tafi wurin Kaisar." 13 Bayan wadansu kwanaki, sarki Agaribas da Barniki suka iso Kaisariya domin su ziyarci Festas. 14 Da ya kasance kwanaki da yawa, Festas ya fada wa sarki labarin Bulus ya ce, "Akwai wani mutum dan sarka da Filikus ya bari a kurkuku. 15 Sa'anda nake a Urushalima, babban firist da dattawan Yahudawa suka kawo kararsa gare ni, suka roka a kashe shi. 16 Game da wannan na amsa na ce masu, ba al'adar Romawa ba ce a ba da mutum tagomashi; sai wanda ake kararsa an bashi zarafi ya kare kansa a gaban masu kararsa, ya kuma bada hujjojinsa game da kararakin. 17 Saboda haka, da duk suka taru ban bata lokaci ba, washegari na zauna a kujerar shari'a, na ba da umarni a kawo mutumin. 18 Da masu karar suka fadi kararsu, sai na fahimci karar ba wani muhimmin abu a cikinta. 19 Sai dai na ga cewa jayayya ce tsakanin su ta addini a kan wani Yesu da ya mutu, wanda Bulus ya ce yana da rai. 20 Na rasa yadda zan bincike wannan al'amarin, sai na tambaye shi ko zai je Urushalima a shari'anta shi kan wadannan abubuwa. 21 Amma da Bulus ya nemi a lura da shi, Kaisar ya shari'anta shi, sai na ba da umarni a ajiye shi har sai na aika shi wurin Kaisar." 22 Agaribas yace wa Festas. "Zan so ni ma in saurari mutumin nan." "Gobe za ka ji shi," in ji Fostus. 23 Washegari Agaribas da Barniki suka zo tare da kasaitaccen taro suka shiga dakin taro tare da hafsoshi da shugabanin gari. Da Festas ya ba da umarni, aka fito da Bulus wurinsu. 24 Festas ya ce, "Sarki Agaribas da dukanku da kuke tare da mu a nan, kun ga mutumin nan, dukan Yahudawa sun gana da ni a Urushalima da nan kuma. Suna mani ihu cewa, bai chanchanta a bar shi da rai ba. 25 Na gane bai yi wani abin da ya chanchanci mutuwa ba; amma saboda ya daukaka kara zuwa Kaisar, na yanke shawara in aika shi. 26 Amma ba ni da wani dalili na musamman da zan rubuta wasika ga Kaisar. Saboda wannan dalili na kawo shi gabanku, masamman kai ya sarki Agaribas. Domin in sami karin abin da zan rubuta game da shi. 27 Gama a ganina wauta ce in aika dan sarka ba tare da na rubuta laifi a kansa ba."
Bulus ya cigaba da zama a ɗaure a Kaisariya.
Festas ya Zama Gwamnar Kaisariya. Dubi yaka aka juya wannan a [24:27]
Wannan kalmar na nuna alamar wani sabon abin da ya faru a labarin.
Wannan na iya nufin 1)Festas ya fito fara mulki a yankin. ko kuma 2) Festas dai ya iso yankin.
An yi amfani da jimlar nan "ya tashi" domin Urushalima yana sama da Kaisariya a tadawa.
Ana maganar ƙara kamar wani abu ne da mutum ke iya kawo wa wani. AT: "Sai babban firist da shugabanin Yahudawa suka kawo karan Bulus ga Festas"
A nan kalmar nan "sa" na nufin Festas.
Wato Festas zai umarci su su kai Bulus zuwa Urushalima. AT: "cewa yă umarci sojojinsa su kai Bulus zuwa Urushalima"
"za su yi bagon Bulus.
Ana iya sanar da wannan a matsayin furci. AT: "Amma Festas ya ce, 'Bulus ɗan sarka ne a Kaisariya, kuma ni da kai na zan koma can ba da dadewa ba."
Ana iya fara jimlar waɗannan kalmomin "ya ce". AT: "Amma ya ce, "Saboda haka, waɗanda za su iya zuwa Kaisariya su biyo mu"
"Idan Bulus yana da wani laifi"
"sai ku zarge shi da laifin ƙetere doka" ko kuma "sai ku kawo karansa"
Urushalima yana sama da Kaisariya bisa ga labarin ƙasa. Don haka, yana da sauki a ce mutum ya sauko daga Urushalima.
A nan "kursiyin shari'a na nufin zaman Festas a matsayin alkalin da ke binciken maganar Bulus. AT: "ya zauna a kursiyin yanke hukunci" ko kuma "ya zauna a matsayin mai yanke hukunci"
AT: "sojojinsa su kawo Bulus gabansa"
"Da ya zo ya tsaya gaban Festas"
Ana maganar mugun laifi kamar wani abu ne da mutum ke iya kawo kotu. AT: "sun zargi Bulus da laifuffuka masu nauyi da yawa"
Bulus ya ce shi bai ƙetere wani doka game da wanda za su iys shiga haikalin da ke Urushalima ba"
A nan "Yahudawa" na nufin shugabannin Yahudawa. AT: "yana so ya gamshi shugabannin Yahudawa"
Urushalima yana sama da Kaisariya bisa ga labarin ƙasa. Don haka, yana da sauki a ce mutum ya sauko daga Urushalima.
AT: "inda ni zan shar'anta ka a game da waɗannan ƙararraki.
"dakalin shari'a" na nufin ikon da Kaisar ke da shi na shar'anta Bulus. AT: "Na roƙa in saya a gaban Kaisar don ya shar'anta ni ne"
Bulus yana magana ne idan maganar da za a kawo a kansa gaskiya ne. Idan yana da laifi, zai karɓi hukuncin, amma shi ya tabbatar cewa ba shi da laifi.
"idan na aikata laifin da ya cancanci mutuwa ne ya zama hukunci na"
"idan ƙararraki da aka yi a kaina ba gaskiya ba ne"
Wanna na iya nufin 1) Festas bashi da iko bisa ga shari'a ya bashe Bulus ga waɗannan masu zargin ko kuma 2) Bulus yana cewa idan ba shi da laifin komai, kada gwamna ya amince da roƙon Yahudawa.
"Ina roƙo a kai ni gaba Kaisar don ya shar'anta ni"
Ba wannan Majalisar bane ake ta maganar su a matsayin "majalisa" a Ayyukan Manzanni gabaɗaya. Wannan ne majalisar siyasa da ke gwamnatin Roma. AT: "da nasa mashawarta"
don su ziyarci Fe stas game da zancnen aikin hukuma"
AT: "Da Filikus ya bar nan, ya bar wani mutum a nan kurkuku"
Filikus ne gwamnar Roma na wannan yankin kuma yana zama ne a Kaisariya. Duba yadda aka juya wannan a [23:24]
Ana maganar ƙarar mutum a kotu ne kamar wani abu ne da mutum ke iya kai kotu. AT: "ya yi magana da ni game da mutumin nan"
Wannan na nufin cewa suna roƙo a ƙashe Bulus. AT: "sun roƙe ni in ƙashe shi" ko kuma "sun roƙe ni in tabbatar mishi da laifin da zai kai shi ga mutuwa"
A nan "ba da" na nufin a kai wani wurin wasu don su hukunta ko kuma su ƙashe shi. AT: "bari wani yă hukunta ko ma wa" ko kuma "bari ku hukunta wani da mutuwa"
Wannan na nufin su hadu da masu ƙararrakin sa. AT: "a gaban mutumin da aka zarge shi da laifi ya haɗu da masu zarginsa fuska da fuska"
"Da shike abinda na faɗa maku gaskiya ne." Festas ya fito ce gaya masu cewa duk mutumin da aka kai ƙaransa zai bayyana a gaban masu ƙaran don ya yi nasa magana akan ƙaran.
"da shugabannin Yahudawan sun zo sun same ni anan"
A nan "kujerar sheri'a" na nufin shari'ar da Festas yake kan yi akan Bulus. AT: "na zauna a bisa kujerar in yanke shari'a" ko kuma "na zauna a matasyin alkali"
AT: "na umarci sojojin su kawo Bulus gabana"
A nan "addini" na nufin ra'ayin mutane akan rayuwa da kuma abinda ya wuci ikon ɗan Adam.
A "shar'anta" karin magana ne da ke nufin a yanke wa mutum hukunci don a san ko mutumin yana da laifi ko babu. AT: "ya je yi masa shari'a a akan waɗannan laifuffuka" ko kuma "don mai yanke shari'a yă san ko waɗannan ƙararraki a kansa gaskiya ne ko ba gaskiya ba ne"
AT: "Amma Bulus ya nace a bar shi da masu tsaron Romawa har zuwa loƙacin da sarki zai zo yă shar'anta shi"
AT: "Sai na umarci sojoji su ajiye shi a wurinsu" ko kuma "Sai na ce wa sojoji su tsare shi"
"Ana iya fara jimlar da kalmomin nan "Festas ya ce" AT: "Festas ya ce, 'zan ba ka lokaci ka saurare Bulus gobe'"
"tare da kasaitaccen taro su basu girma"
Wannan wata babban ɗaki ne da jama'a kan taru domin bukukkuwa, da shari'u, da kuma wasu abubuwa.
AT: "sojojin sun fito da Bulus ya bayyana a gabansu"
Ana amfani ne da kalmar nan "dukkan" domin a nanata cewa Yahudawa masu yawa sosai suna son Bulus yă mutu. AT: "Yahudawa masu yawa sosai" ko kuma "shugabaninnin Yahudawa da dama"
"suna yi mani magana da ƙarfi"
Ana iya juya wannan a wata hanya daban. AT: "A ƙashe shi nan yanzu yanzu"
"domin ya ce yana so sarki ne ya yanke masa shari'a"
Sarkin shi ne mai mulƙin ƙasashen da ke yankin Roma. Ya mulƙe ƙasashe da lardodi masu yawa.
"Na kawo Bulus a gaban ku dukka, musamman kai, ya Sarki Agaribas."
"domin in sami wani abu kuma da zan rubuta" ko kuma "domin in san abinda zan rubuta"
Ana iya juya kalmar nan "wauta" da kuma "ba tare da" a wata hanya daban. AT: " a yana da kyau idan na aika da aɗn sarka, in rubuta"
Wannan na iya nufin 1) zargin da Shugabannin Yahudawa suka kawa a kansa ba ko kuma "ƙararrakin dokar Romawa da sun shafe Bulus.
Sun roƙi Festas ya kira Bulus zuwa Urushalima domin su ƙashe shi a hanya.
Festas ya ce masu su je Kaisariya, inda za shi, kuma wai za su iya zargin Bulus a wurin.
Festas ya yi wa Bulus wannan tambaya domin ya yi farin jini a wajen Yahudawa.
Festas ya tambayi Bulus ko ya na so ya tafi Urushalima a hukunta shi a wurin.
Bulus ya ce ya na tsaye a Dadakalin Shari'ar Kaisar inda ɗole a shari'anta shii.
Festas ya shirya cewa tun da Bulus ya kira ga Kaisar, zai tafi wurin Kaisar.
Festas ya faɗa cewa Romawa suna ba mai laifi zarafi ya kare kansa a gaban masu zarginsa, ya kuma bada hujjojinsa game da su zargin.
Festas ya faɗa cewa laifin ya kunsa jayayya game da addini a kan wani Yesu da ya mutu, amma Bulus ya ce yana da rai.
Festas ya so Sarki Agarbas ya taimake shi rubuta wani abu game da zancen Bulus ga Kaisar.
Festas ya ce ba zai dace ya aika Bulus zuwa Kaisar ba tare da rubuta laifi a kansa ba.
1 Sai Agaribas ya ce wa Bulus, "Za ka iya kare kan ka." Sai Bulus ya daga hannunsa ya fara kare kansa. 2 "Ina farinciki, ya sarki Agaribas, game da saran da Yahudawa ke kawowa a kaina yau; 3 musamman ma don kai masani ne game da al'adun Yahudawa da al'amuransu. Don haka, ina rokanka ka yi hakuri ka saurare ni. 4 Hakika, dukan Yahudawa sun san yadda na yi rayuwa ta daga kurciyata a kasa ta, da kuma Urushalima. 5 Sun san ni tun farko, kuma yakamata su yarda cewa na yi rayuwa kamar Bafarase, darikan nan mai tsatsauran ra'ayi ta addininmu. 6 Yanzu ina tsaye a nan dominn a shari'anta ni, saboda alkawalin da Allah ya yi wa ubanninmu. 7 Domin wannan shine alkawalin da kabilunmu goma sha biyu suka sa zuciya su karba, yayin da suke yin sujada da himma ga Allah dare da rana. Saboda wanan bege, Sarki Agaribas, Yahudawa ke tuhuma ta. 8 Me ya sa wani zai yi tunani cewa abin mamaki ne Allah ya ta da mattatu? 9 Da, na yi tunanin yin abubuwa gaba da sunan Yesu Banazarat. 10 Na yi wadanan a Urshalima. Na kulle masu bi da yawa a kurkuku, sanadiyar iko da na samu daga wurin manyan firistoci, kuma da ake kashe su ma, ina ba da goyon baya. 11 Na wahalshe su sau dayawa a cikin dukan majamiu ina kuma yin kokari in tilasta masu su yi sabo. Na yi gaba mai zafi da su kuma na tsananta masu har zuwa birane na wadansu kasashe. 12 A sa'anda nake yin wannan, na tafi Dimashku da izinin manyan firistoci; 13 a cikin tafiyata kuma, da tsakar rana, ya sarki, na ga haske daga sama da ya fi rana sheki, ya haskaka kewaye da ni da kuma wadanda ke tafiya tare da ni. 14 Da dukanmu muka fadi kasa, na ji wata murya na magana da ni a harshen Ibraniyawa tana cewa, 'Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani? Yana da wuya ka hauri abin da ke mai tsini.' 15 Sai na ce, 'Wanene kai ya Ubangiji?' Ubangiji ya amsa, 'Ni ne Yesu wanda kake tsanantawa. 16 Yanzu ka tashi tsaye domin saboda wannan dalili ne na bayyana gare ka in sanya ka, ka zama bawa da mashaidi na game da abubuwan da ka sani a kaina yanzu da wadanda zan bayyana maka daga bisani; 17 Zan kubutar da kai daga wurin mutane da kuma al'ummai da zan aike ka wurinsu, 18 domin ka bude idanunsu ka juyo su daga duhu zuwa haske da daga ikon Shaidan zuwa ga Allah, domin su karbi gafarar zunubai da gado da zan ba wadanda na kebe wa kaina ta wurin bangaskiya gare ni.' 19 Saboda haka, sarki Agaribas, ban yi rashin biyayya da wahayin da na gani daga sama ba; 20 amma, da farko ga wadanda ke a Dimashku, sa'annan a Urushalima da kasar Yahudiya gaba daya, da dukan Al'ummai, na yi wa'azi domin su tuba su kuma juyo ga Allah, su yi ayyukan da suka chanchanci tuba. 21 Domin wannan dalili ne Yahudawa suka kama ni a cikin haikali kuma suke kokari su kashe ni. 22 Allah ya taimake ni har wa yau, domin in iya tsayawa gaban mutane kanana da manya, in bada shaida game da iyakar abin da annabawa da Musa suka fada zai faru; 23 wato lallai Almasihu zai sha wahala, ya kuma zama na farko da za'a rayar daga matattu ya kuma yi shelar haske zuwa ga mutanen Yahudawa da Al'ummai." 24 Da Bulus ya gama kare kansa, Festas ya yi magana da babban murya, "Bulus, kana hauka; yawan iliminka yasa ka hauka." 25 Amma Bulus ya ce, "Ba na hauka, ya mai girma Festas; amma da karfin zuciya nake fadi kalmomin gaskiya da na natsuwa. 26 Saboda sarkin ya san wadannan abubuwa duka; shi ya sa nake magana gabagadi, don na hakikance cewa, ba abin da ke a boye gare shi; gama ba a yi wadannan abubuwa a boye ba. 27 Ko ka gaskanta da annabawa, Sarki Agaribas? Na sani ka gaskanta." 28 Agaribas ya ce wa Bulus, "A cikin karamin lokaci kana so ka rinjaye ni ka mai da ni Krista?" 29 Bulus ya ce, "Ina roko ga Allah, domin ko a karamin lokaci ko a dogon lokaci, ba kai kadai ba, amma har da wadanda ke sauraro na yau su zama kamar ni, amma ban da wadannan sarkokin." 30 Sai sarki ya tashi tsaye tare da gwamna da Barniki da dukan wadanda ke zaune tare da su; 31 da suka bar dakin taron, suka ci gaba da magana da juna suna cewa, "Wannan mutum bai yi wani abin da ya chanchanci mutuwa ko kuma dauri ba." 32 Agaribas ya ce wa Fastos, "Da mutumin nan bai daukaka kara zuwa ga Kaisar ba da an sake shi."
Festas ya kawo Bulus gaban Agaribas. A aya 2, Bulus ya ƙare kansa game da ƙarar da aka kawo a kansa.
Agaribas ne sarkin da ke kan mulki a Palastini, ko da shike yana mulkin kananan ƙasashe ne. Duba yadda aka juya wannan sunan a [25:13].
"miƙa hannunsa" ko kuma "ya yi motsi da hannunsa"
AT: "ya fara ƙare kansa daga masu zarginsa"
Bulus yana farin ciki domin ya ɗauki bayyanawarsa a gaban Agaribas yă zama wani zarafi ne mai na yin bishara.
Wannan jimlar na nufin mutum yă bayyana halin da yake ciki, don jama'a da ke kotu su tattauna su kuma yanke hukunci. AT: "in ƙari kaina"
A nan iya sanar da kalmar nan "ƙararraki" zuwa ƙara." AT: "ga dukkan ƙararrakin da Yahudawa ke yi a kaina"
Wannan bai haɗa da kowane Bayahuɗe ba. AT: "shugabannin Yahudawa"
Ana iya ƙara bayani akan irin al'amuran da ake magana a kai. AT: "al'amuran addini"
Wato ana nufin masu yawa kenan. Wannan na iya nufin 1) Wannan na nufin Yahudawa dai da sun san game da Bulus. AT: "Yahudawan" ko kuma "2) wato Yahudawan da sun san Bulus. AT: "shugabannin Yahudawa"
Wannan na iya nufin 1) a cikin mutanensa, ba lallai a zancen ƙasar Isra'ila ba ko kuma 2) in ƙasar Isra'ila.
"ɗarikar addinin Yahudawa da ta fi kiyaye kowace ka'ida"
A nan "ku" na nufin jama'ar da ke sauraron Bulus.
Wannan na nuna alamar ƙaucewar Bulus daga maganar da yake yi na abubuwan baya zuwa maganar abubuwan kansa a lokacin da ake ciki.
AT: "ga ni a nan, in da suna mini bahasi"
Ana maganar alkawalin ne anan kamar wani abu ne da mutum ke iya nema har yă gani. AT: "Ina jira, ina kuma sa zuciya ga Allah zuwa ga cikar alkawarin da ya yi wa kakkaninmu"
Jimlar nan "kabilanmu goma sha biyu" na nufin mutanen waɗannan kabilu. AT: "Wannan shi ne 'yanuwanmu Yahudawa na kabilu goma sha biyu ke jira"
Ana maganar alkawali kamar wani abu ne da mutum ke iya karɓa.
Waɗannan matsanancin kalmomin "dare" da "rana" na nufin suna "wa Allah sujada akai akai."
Ba dukkan Yahudawa aka nufi ba. AT: "Shugabannin Yahudawa ke"
Bulus yana amfani ne da wannan tambayan yă kalubalanci Yahudawan da ke wurin. Sun gaskanta cewa Allah na iya ta da matattu amma ba su yarda cewa Allah ya ta da Yesu ba. Ana iya sanar da wannan cikin jimla. AT: "Ba wanin ku da bai gaskanta cewa Allah yana ta da matattu ba"
A nan a tayar wata karin magana ce ta sa wanda ya mutu ya tashi kuma. AT: "yana sa matattu su tashi kuma"
Bulus yana amfani ne da wannan jimlar yă matsowa zuwa wani bangaren ƙare kansa. Yanzu ya fara bayanin yanda shi ma a dã ya tsananta wa Mutanen Yesu.
Kalmar nan "suna" na nufin koyarwa akan mutumin. AT: "in hana mutume koyarwa game da Yesu"
AT: "Na amince da sauran shuganannin Yahudawan cewa su yanke wa masubi hukuncin mutuwa"
Wannan na iya nufin 1) Bulus ya wahalshe wasu masubi da sau da dama ko kuma 2) Bulus ya wahalshe masubi daban daban sau da dama.
Bulus yana amfani ne da wannan jimlar domin yă dasa wata aya a kare kansa da yake yi. Yanzu yana maganar lokancin da ya gan Yesu har ya zama almajirinsa.
Wannan kalmar na ba da alamar abubuwa biyu da ke faruwa a lokaci guda. A wannan sa'a, Bulus ya tafi Damisku lokacin da yake sananta wa masubi.
Bulus yana riƙe da wasiku daga Shugabannin Yahudawa, wanda ke bashi izini ya sananta wa Yahudawa masubi.
A nan "murya" na nufin mai magana. AT: "na ji wani yana magana da ni cewa"
Wato ana maganar yadda Bulus yă ki karɓin Yesu ne amma yă sananta wa masubi kamar shi wani takarkari ne da ke hauri sanda mai tsini da mutum ke amfani da shi yana kiwon dabba. Wannan na nufin cewa Bulus ya yi wa kansa ne rauni. AT: "Kana dai yi wa kanka ne rauni kamar yadda takarkari ke hauri sanda mai tsihi"
Ana maganar taimakon mutum yă fahimci gaskiya ne kamar taimakon mutum ne ya buɗe idanunsa.
Ana maganar taimaka wa mutum yă daina aikata mugunta ne yă kuma fãra dogara ga Allah yana kuma yi masa biyayya kamar mutumin yana jagoran wani daga wuri mai duhu zuwa wuri mai haske.
Ana maganar tamaka wa mutum yă daina yi wa shaidan biyayya ne yă kuma fãra biyayya Ga Allah kamar mutumin yana juyo wa ne daga wurin da shaidan ke mulki ana kuma jagoransa zuwa wurin da Allah ke mulki.
AT: "domin Allah yă gafarce zunubansu"
Ana iya juya wanna kalmar gãdo zuwa gãda. AT: "domin su gãda abinda zan bayar
Ana maganar albarkun da Yesu ke ba wa waɗanda sun gaskanta da shi ne kamar wasu kayan gãdo ne da 'ya'ya ke samu ne na mahaifinsu.
Ana maganar zaɓen da Yesu ya yi wa wasu su zama na shi kamar ya keɓe su ne daga sauran mutane.
"domin sun gaskanta da ni." Anan, Bulus ya gama furcin maganar Allah.
"Da shike abinda na faɗa gaskiya ne." Bulus ya fito yin bayanin abinda Ubangiji ya umarce shi a wahayin.
AT: "na yi biyayya"
Wato abinda mutumin ya faɗa wa Bulus a wahayin. AT: "abinda mutum na sama ya faɗa mani a wahayin"
Ana maganar fara dogara ga Allah ne kamar mutum ya juya ne ya fãra tafiya zuwa wurin Allah." AT: "dogara ga Allah"
AT: "su kuma fãra ayyukan da za su hakikanci cewa sun tuba"
AT: "game da daidai abinda"
Bulus na nufin rubuce rubucen annabawan Tsohon Alkawali gaba ɗaya.
Ana iya karin bayyani anan cewa lallai ne Almasihu ma yă mutu. AT: "wato lallai ne Almasihu yă sha wahala har ma yă mutu"
yă sake rayuwa
Jimlar nan "matattu" na nufin ruhohin waɗanda sun mutu. A rayu daga cikinsu na nufin a sake samun rai kuma.
zai yi shelar sakon hasken." Ana maganar yadda Allah ke ceto ne kamr mutum yana maganar gaskiya ne. AT: "zai yi shelar sakon yadda Allahe ke ceton mutane"
"kana maganan banza ne" ko kuma "kai mahaukaci ne"
"iliminka yayi yawa har a shi yanzu ka haukache"
AT: "ina cikin hankali na ... kuma" ko kuma "ina iya tunani da kyau ... kuma"
"Festas, wanda ya cancanci dukkan daraja"
Har yanzu Bulus yana magana da Sarki Agariba ne, amma yana magana da shi a matsyin mutum na uku. AT: "Saboda kai ... da kai ... gare ka"
Bulus bai ji tsoron faɗa wa sarkin game da Almasihu ba. AT: "nake magana da gabagaɗi"
AT: "na tabbata"
AT: "cewa ya san da haka" ko kuma "cewa kana da sanin wannan"
"ba su faru a ɓoye ba"
Wato, yin abu a asirce kammar mutum ya shigo wani wuri ne da ba a iya ganinshi. AT: "a cikin duhu" ko kuma "a asirce"
Bulus yana wannan tambayan ne domin ya tunashe Agaribas da cewa Agaribas ya riga ya gaskanta da abinda annabawa sun faɗa game da Yesu. AT: "Ai ka riga ka gaskanta da abinda annabawan Yahudawa suka faɗa, Sarki Agaribas."
Agaribas yana amfani ne da wannan tambayan do ya nuna wa Bulus cewa ba zai iya ya rinjaye shi da sauke haka ba tare da kara wasu shaidu ba. AT: "Lallai fa, a ganinka za ka iya rinjaya na in gaskanta da Yesu a saukakke haka!"
A nan "sarkoki" na nufin zama ɗaurarre. AT: "amma, alhali ma, ba na son ka zama ɗaurarre kaman ni"
"Sai Sarki Agaribas ya tashi tsaye, tare da Gwamna Festas"
Wannan wata babban daki ne na bukukkuwa, sauraron kararraki da sauron taro.
Ana iya sanar da kalmar nan "mutuwa" zuwa "mutu". AT: "Wannan mutum bai chanchanci ya mutu ko a rufe shi a ɗaure shi a kurkuku ba"
AT: Da wannan mutum ya samu 'yanci" ko kuma "Da na sake mutuminan"
Bulus ya yi farincikin kare kansa a gaban Agaribas domin shi masani ne game da dukka al'adun Yahudawa da al'amuransu.
Bulus ya yi rayuwa kamar Bafarase, darikan nan mai tsatsauran ra'ayi ta addini.
Bulus ya faɗa cewa shi da Yahudawa suna begen kai ga alkawarin tashin mattatu.
Bulus ya na kulle masu bi da yawa a kurkuku, ya na amince ranar da za a ƙashe su, ya kuma tsananta masu har zuwa birane na waɗansu kasashe.
Bulus ya ga haske daga sama da ya fi rana haskakawa.
Bulus ya ji murya tana cewa, "Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani?"
Yesu ya na magana da Bulus a hanya zuwa Dimashku.
Yesu ya naɗa Bulus ya zama bawa da kuma mai shaida ga al'ummai.
Yesu ya ce ya so Al'ummai su ƙarba gafarar zunubai da gado daga Allah.
Bulus ya ce ya yi wa'azi domin mutanen su tuɓa su kuma juyo ga Allah, su yi ayyukan da ta chanchanci tuba.
Annabawa da Musa sun ce lallai na Almasihu zai sha wahala, za a ta da shi daga matattu ya kuma yi shelar haske zuwa ga mutanen Yahudawa da Al'ummai.
Festas ya zata Bulus na hauka.
Bulus ya so Sarki Agaribas ya zama mai bi.
Sun amince cewa Bulus bai yi komai da ya chanchanci mutuwa ko kuma ɗauri ba, kuma da bai kai kara zuwa ga Kaisar ba da an sake shi.
1 Bayan da aka amince zamu tafi Italiya, sun mika Bulus tare da wadansu daurarru a hanun wani jarumi mai suna Yuliyas, daga batalian Agustas. 2 Muka shiga Jirgin ruwa daga Adramatiya, wanda ke shirin tashi zuwa kusa da gefen tekun Asiya. Sai muka je teku. Aristakus mutumin Tasalonika a Makidoniya ya tafi tare damu. 3 Washegari muka sauka birnin Sidon, inda Yuliyas ya nuna wa Bulus karamci ya kuma yarda abokansa su bi shi don ya kula da su. 4 Daga wurin, muka bi teku muka tafi ta Tsibirin Kubrus, domin matsananciyar iska da ke gaba damu. 5 Sa'adda muka ketare ruwa zuwa sassan Kilikiya da Bamfiliya, muka zo Mira ta birnin Lisiya. 6 Anan, jarumin ya sami jirgin ruwa daga Iskandariya wanda za shi Italiya. Ya samu cikinsa. 7 Kwana da kwanaki muna tafiya a hankali a karshe da kyar muka sauka kusa da Sinidus, iska ta hana mu tafiya, sai muka ratsa ta Karita, kusa da Salmina. 8 Da wahala muka bi ta makurda har muka zo wani wuri da ake kira Mafaka Mai Kyau wanda ke kusa da birnin Lasiya. 9 Yanzu mun dauki dogon lokaci, gashi lokacin azumin Yahudawa ya wuce, tafiyar kuma ta zama da hatsari. Bulus ya gargade su, 10 ya ce, "Jama'a, na gane tafiyarmu zata zamar mana da barna da asara mai yawa, ba ga kaya da jirgin kadai ba amma har da rayukan mu." 11 Amma jarumin ya fi mai da hankali ga maganar shugabansa da mai jirgin ruwan, fiye da abubuwan da Bulus ya fadi. 12 Da shike tashar ba za ta yi dadin zama da hunturu ba, mafi yawa sun ba da shawara a bar wurin, in maiyiwuwa ne muga mun kai birnin Finikiya, don mu yi hunturu a can. Finikiya tashar jirgin ruwa ce a Karita, tana fuskantar arewa maso gabas da kudu maso gabas. 13 Sa'adda iska daga kudu ta huro a hankali, sun tsammaci bukatarsu ta biya. Sai suka janye linzamin jirgin ruwan sukabi ta Karita kusa da gaba. 14 Amma bayan wani dan lokaci sai iska mai karfi da ake kira Yurokilidon, ta fara bugun mu daga tsibirin. 15 Sa'adda Jirgin ruwan ya kasa fuskantar iskar, sai muka bi inda iskar ta nufa. 16 Sai muka bi ta inda muka sami kariya kusa da wani dan tsibiri wanda ake kira Kauda; kuma da wahala muka daure karamin jirgin a jikin babban. 17 Bayanda suka daga shi, sun yi amfani da igiyoyi don su daure jirgin don gudun fadawa kan yashin Sirtis, suka bar jirgin yana ta korarsu. 18 Mun yi ta fama da hadari ba kadan ba, da gari ya waye ma'aikatan jirgin suka fara zubar da kaya daga jirgin. 19 A rana ta uku, ma'aikatan jirgi suka jefar da kaya daga cikin jirgin da hannuwansu. 20 Kwanaki dayawa ba mu ga hasken rana da taurari a bisan mu ba. Babban hadari kadai ke dukanmu, duk mun fidda zuciya zamu tsira. 21 Sa'adda sun dade basu ci abinci ba, sai Bulus ya tashi a gaban ma'aikatan jirgi yace, "Jama'a, da kun saurare ni, da bamu tashi daga Karita ba, balle mu fuskanci wannan barna da asarar. 22 Yanzu fa ina karfafa ku kuyi karfin hali, domin ba wanda zai rasa ransa a cikinku, sai dai jirgin kadai za a rasa. 23 Domin daren da ya gabata mala'ikan Allah wanda ni nasa ne, wanda kuma nake bautawa -mala'ikansa ya tsaya kusa dani 24 ya ce, "Kada ka ji tsoro, Bulus, dole ka tsaya gaban Kaisar, duba kuma, Allah cikin jinkansa ya baka dukan wadannan da ke tafiya tare da kai. 25 Domin haka, jama'a, kuyi karfin hali, domin na gaskanta da Allah, kamar yadda aka fada mani haka zai faru. 26 Amma lallai dole ne a jefa mu kan wani tsibiri". 27 Sa'adda dare na goma sha hudu ya yi, ana ta tura mu nan da can a cikin tekun Adriyat, wajen tsakar dare, ma'aikatan jirgin sun tsammaci sun kusanci wata kasa. 28 Da suka gwada sai suka iske kamu ashirin; bayan dan lokaci kadan, sun sake aunawa sai suka iske kamu sha biyar ne. 29 Tsoro ya kama su ko watakila a jefar da mu kan duwatsu, sai suka jefa linzami hudu daga karshen jirgin suka yi addu'a don gari ya waye da sauri. 30 Ma'aikatan jirgin ruwan suna neman hanyar da za su rabu da jirgin kuma sun jefa karamin jirgin a cikin teku. Suka yi kamar zasu jefa wasu linzamai daga gaban jirgin. 31 Amma Bulus ya ce ma jarumi da sojojin, "Idan mutanen nan ba zasu tsaya cikin jirgin ba, ba zaku tsira ba". 32 Sai sojojin suka yanke igiyoyin jirgin suka kuma barshi ya fadi. 33 Da gari ya fara wayewa, Bulus ya roke su duka su dan ci abinci, ya ce, "Yau kwana goma sha hudu kenan ba ku ci kome ba. 34 Saboda haka na roke ku ku ci abinci, domin wannan saboda lafiyarku ne; kuma ko gashin kanku daya baza ku rasa ba". 35 Da ya fadi haka sai ya dauki gurasa ya yi godiya ga Allah a idanun kowa. Sai ya gutsutsura gurasa ya fara ci. 36 Sai dukansu suka karfafu suka kuma ci abinci. 37 Mu mutane 276 (dari biyu da saba'in da shida) ne cikin jirgin. 38 Da suka ci suka koshi, suka zubar da alkamar cikin teku domin su rage nauyin jirgin. 39 Da gari ya waye, basu fahimci kasar ba, amma suka hangi wani lungu a gacci, sai suka yi shawara tsakaninsu ko su tuka jirgin zuwa cikin lungun. 40 Sai suka yanke linzaman suka bar su cikin tekun. Cikin lokaci guda suka kwance igiyoyin da ke juya jirgin, suka saki filafilan goshin jirgi suka nufi gabar tekun. 41 Da suka iso inda ruwa biyu suka hadu, sai jirgin ya tsaya kasa. Gaban jirgin ya kafe a nan, ba damar matsawa, sai kuma kurar jirgin ta fara kakkaryewa saboda haukan rakuman ruwa. 42 Shirin sojojin ne su kashe 'yan kurkukun domin kada su yi iyo su tsere. 43 Amma shi hafsan ya so ya ceci Bulus, sai ya tsai da shirin su, ya ba da umarni, duk masu iya iyo su yi tsalle su fada ruwa su kai gacci. 44 Sa'annan sauran mazajen su biyo baya, wadansu a kan karyayyun katakai, wadansu akan abubuwan da ke a jirgin. Ta haka ne dukanmu muka kai gacci lafiya.
Bulus, ɗaurarre, ya kama hanyarsa zuwa ƙasar Roma.
Kalmar nan "mu" ya shafe marubucin Ayyukan Manzanni, Bulus, da sauran mutanen da ke tafiya da Bulus, banda masu karatu.
AT: "Bayan da sarki da gwamna suka amince"
Italiya sunar wata yanki ne da ƙasar Roma take. Duba yadda ake juya "Italiya" a [18:2]
AT: "aka sa wani jarumi mai suna Yiliyas, na batalian Agustas, a matsayin mai lura da Bulus sa wasu ɗaurarru"
Wannan na iya nufin: 1) "su" na nufin gwamna da sarkin ko kuma 2) "su" na nufin "suran ma'aikatan Roma.
"Yuliyas sunan wani mutum ne.
Wannan shi ne sunar batalia ko soja da jarumin ya fito. Wasu.
A nan "jirgi ...wanda ke shirin tashi" na nufin ƙungiyar ma'aikatan jirgin. AT: "Muka shiga jirgin ruwa ... wanda ma'aikatan jirgin na shirin tashiwa"
Wannan na iya nufin 1) Jirgin ruwa da ta fito daga Adramatiya ko kuma 2) Jirgin ruwa da aka yi rajistanta ko mai aiki da takardan izinin aiki daga Adramatiya.
"nan da nan zai tashi" ko kuma "zai tafi nan da nan"
"muka fara tafiyar mu a teku"
Aritakus mutumin Makidoniya ne amma ya riƙa aiki da Bulus a ƙasar Afisus. Duba yadda aka juya wannan a [19:29]
"Yuliyas ya nuna wa Bulus halin abokin ƙwarai." Duba yadda aka fasara "Yuliyas" a [27:1]
AT: je wurin abokansa don su kula da shi" ko kuma "je wurin abokansa don su taimaka masa da duk abubuwan da yake bukata"
"muka fara tashi a jirgin ruwa muka tafi"
"tsibirin Kuburus" wate gefen Tsibirin ne da ke tare iska mai ƙarfi, don haka jiragen ruwa masu tafiya basu iya ƙauce wa daga fagen su.
Wannan wata yanki ne a Ƙaramar Asiya. Duba yadda aka juya wannan a [2:10]
Ana iya karin bayyani cewa sun suka daga jirgin ruwan a Mira. AT: "suka zo Mira, ta birnin Lisiya, inda suka sauka daga jirgin ruwan"
Mira sunar wata birni ce.
Lisiya wata yankin Roma ne, da ke tsibirin kudanci ta yamma na ƙasar Turki a yau.
Ana ɗaukan cewa ƙungiyar ma'aikata jirgin ruwan za su tashi zuwa Italiya. AT: "sami wata jirgin ruwan da ƙungiyar ma'aikatanta suka taso daga Iskandariya kuma za suna kokarin tasowa zuwa Italiya"
Wannan sunan wata birni ce.
Ana iya bayyana a fili dalilin da ya sa suka yi ta tafiya a hankali da kuma wahala da suka sha saboda iska da ke ɓullowa daga ɗayan gefensu ne.
Wannan at tsohon mazauni ne da ke ƙasar Turki a ya.
"muka kasa tafiya ta wancan gefen saboda iska mai ƙarfi"
"sa muka ratsa ta Karita wurin da ba iska sosai"
Wannan wata birni ce mara laushi a Karita.
Ana iya bayyana a fili cewa ko da shike iskan ba ta da ƙarfi kamar na da, amma har yazu ta kai ta sa tafiya ta zama da wahala.
Wannan wata tasha ce kusa da Lasiya, a tsibirin da ke kudancin Karita.
Wannan wata wata birni ce mara laushi da Karita.
Tafiyansu daga Kaisariya zuwa Mafaka Mai Kyau ya ci masu lokaci fiye da yadda suka shirya saboda gefen da iska ke ɓullowa.
Marubicin yan haɗa kansa, da Bulus, da kuma masu tafiya tare da su, amma banda mai karatu.
Ana wannan azumin ne a Ranar yin Kafara, wanda yakan zo a ƙarshen watan tara ko a farkon watan goma bisa ga kalanda na ƙasashen Yammaci. Bayan wannan lokaci, akwai hatsarin lokacin iska mai ƙarfi.
"idan mun yi tafiya yanzu, za mu sha barna da asara masu yawa"
Bulus ya haɗa kansa da masu sauraronsa, don haka wannan ya shafe su dukka.
A nan "asara" na nufin barna a zancen abubuwa sa'annan hallaka a zancen mutane.
Kaya anan na nufin kaya waɗanda jirgin ruwa ke ɗauka. AT: "ba jirgin kadai ba, har na dikiyan da ke jirgin"
AT: "da Bulus ya ce"
Ana iya faa a fili dalilin da ya sa tashar ba za ta yi dadin zama da hunturun ba. AT: "tashan ba ta tsare wurin tsayan jirgin ruwa yadda yakamata a lokacin da hunturu na fita da hadari
wani wuri ne a kusa da kasa da ya fi kyau ga jiragen ruwa
Finikiya wata garin tasha ne da ke kudancin tsibirin Karita.
Ana maganar lokacin hunturu kamar wani abu ne da mutum ke iya yi. AT: "don mu zamna a can saboda lokacin sanyi"
A nan "fuskantar arewa maso gabas da kudu maso kudu" na nufin mabudin tashar suna waɗannan gefen. AT: "ya budu zuwa ta arewa maso gabas da kudu maso gabas"
Waɗannan kwatancen na bisa ga haura.war rana da fitanta. Arewa maso gabas tana ɗan kusa da gefen hago na fitar rana. Kudu maso gabas tana ɗan kusa da gefen dama na fitar rana. Wasu juyin na cewa "arewa maso yamma da kudu maso yamma."
A nan "Janye" na nufin a ja daga cikin ruwa. Linzamin jirgin ruwa wani abu ne ma nauyi da ke a haɗe da wani igiya da ke tsare jirgin ruwar. Ana jefa linzamin jirgin ruwan zuwa cikin ruwan yă lume zuwa kasan tekun don yă tsare jirgin ruwan daga kaucewa.
"bayan ɗan karamin lokaci"
"wani iska mai ƙarfi, mai hatsari kuma"
"ake kira iska mai ƙarfi daga arewa maso gabas." Wannan kalmar "Yurokilidon" ya zo ne daga ainihin harshen da aka rubuta littafi. Kuna iya juya wannan kalmar yadda zai yi dai dai da harshen ku.
"ta huro daga tsibirin karita, ta bugo jirgin mu da ƙarfi"
"Sa'adda iskan ta bugo da ƙarfi ƙwarai a gaban jirgin har ma muka kasa tafiya"
AT: "muka kasa tafiya gaba, sai muka bar iskan ta bi da mu inda ta nufa"
"Sai muka bi gefen tsibirin, inda iskar ba ƙarfi sosai"
Wannan tsibirin yana kudancin tsibirin Karita.
Wannan wata ƙaramin jirgi ne da akan ja shi a bayan jirgin kuma wani lokaci akan shigo jirgin a ɗaura a kasan. Ana amfani ne da wanns jirgin domin dalilai da yawa, har ma a haɗe da tsira daga lumewar jirgi.
"suka daga karamin jirgin" ko kuma "suka jawo karamin jirgin daga babban jirgin"
Sun ɗaure jirgin don kar jirgin ba zai raɓu sa'adda iskan ya huro.
yashin Sirtis wurare ne masu zurfi inda jirage suna iya maƙalewa a yashin. Sirtis yana tsibirin Libiya, a arewacin Africa.
Suka jefa sarkokin jirgin a ruwan don ya rage gudun jirgin zuwa wurin da iskan zai iya ƙorarsu. Ana sake sarkan zuwa cikin ruwan ne don ya tsare jirgin daga kauche na da can. Duba yadda aka juya wannan a [27:13]
AT: "yana tafiya ta kowani gefen da iskan ke huramu"
AT: "Iskan ya hura mu barkatai gaba da baya har muka ji raunuka muka kuma gurje saboda iskan"
"su" wato ma'aikatan jirgin kenan. Sun yi haka ne don su rage nauyin jirginsu hana shi daga lumewa
Kayayyakin da ake tafiya da su a jirgin ruwan kenan. Duba yadda aka juya wannan a [27:10]. AT: "su amfanin da ke jirgin"
A nan "kaya" na nufin kayakin da ma'aikatan jirgin na buƙata don su yi tafiya da jirgin; su magance, hau, tsakiyar katsko, a toshe a magance, igiyoyin, filafilai da dai sauransu. Wannan na nuna alamar yadda yanayin gaggawa da suka shiga yake.
Ba su iya ganin rana da taurari ba saboda iskar haɗari. Ma'aikatan jirgin suna bukatar rana da taurari ne don su san inda suke da inda suka nufa.
"Babban haɗari yana dukanmu gaba da baya"
AT: "kowa ya daina sa zuciya cewa za mu tsira"
A nan "su" na nufin ma'aikatan jirgin. Ana ɗaukan cewa, Luka, Bulus, da waɗanda ke tare da asu ba su ci abinci dama ba. AT: "Sa'ad da muke daɗe na sawon lokaci ba cin abinci"
"a cikin mutanen"
"har kuma hakan ya sa mu fuskanci wannan lahani da asarar"
"Bulus yana magana ne da ma'aikatan jirgin. A nan ɗaukan cewa, Bulus nna nufin shi da waɗanda ke tare da shi ma ba za su mutu ba. AT: "babu wanninmu da zai mutu"
Ana amfani ne da "rasa" anan a matsayin hallaka. AT: "amma iskan zai hallakar da jirgin"
Jimlar nan "tsaya a gaban Kaisar" na nufin Tafiyar Bulus kotu da yardarsa Kaisar ya shar'anta shi. AT: "Lallai ne ka bayyana a gaban Kaisar don yă shar'anta ka"
"ya zaɓa ya bar dukkan waɗanda ke tare da kai su rayu"
AT: "kamar yadda mala'ikan ya faɗa mini"
"Lallai ne mu tuƙa jirginmu don ya jujjugu a bisa wani tsibiri"
Ana iya sanar da wannan jerin lamba "goma sha huɗu" zuwa "sha huɗu." AT: "Bayan ƙwana 14 da iskan ya fara, da daren"
AT: "da tekun ke hura mu gaba da baya"
Wannan ita ce tekun da ke tsakanin Italia da Ƙasar Hellas.
"Suka gwada zurfin ruwan tekun." Sun gwada durfin ruwan ta wurin jefa wata igiya da abu mai nauyi zuwa ƙarshen ruwan"
"Kamu" ɗaya itace ce rabo ɗaya a ma'aunan auna zurfin ruwa. AT: suka iske mita 40"
"Kamu" ɗaya itace ce rabo ɗaya a ma'aunan auna zurfin ruwa. Kamu ɗaya tana kai kusan mita biyu. AT: "suka iske mita 30"
Linzami wani abu ne mai nauyi da ake haɗa shi da wani igiya domi a sare jirgi. Akan jefa linzamin a ruwa har ya sauka kansa tekun, don yă hana tekun masowa nan da can. Duba yadda aka juya wannan a [27:13]
"daga bayan jirgin"
Wannan wata ƙaramin jirgi ne da akan ja shi a bayan jirgin kuma wani lokaci akan shigo jirgin a ɗaura a kasan. Ana amfani ne da wanns jirgin domin dalilai da yawa, har ma a haɗe da tsira daga lumewar jirgi. Duba yadda kun juya wannan a [27:16]
"daga gaban jirgin"
"Ai sai waɗannan mutanen sun tsaya a jirgin kamun mu tsira"
"Da gari ya kussan wayewa"
Jerin lamba "goma sha huɗu" anan na iya zama "sha huɗu." AT: "ƙwana 14"
Wannan wata hanya ce na cewa babu wata illa da zai same su. AT: "dukkan ku za ku rayu daga wannan bala'in lafiya"
"ya tsinka gurasa" ko kuma "ya diba gutsurin gurasa"
AT: "Wannan ya ƙarfafa su dukka"
mu ɗari biyu da saba'in da shida a jirgin." Wannan ne bayyanin tarihin.
Wata babbar yankin ruwa da ke saurauta ke kewaye da kasa
"suka ga ƙasar amma basu fahimce shi kamar wani wurin da suka sani ba"
"yanke igiyoyin suka bar su a baya"
"Wata gungumen Itace da ke bayan jirgin ruwan da ake tuka jirgin da shi.
"kyallen da aka rataya su a gaban jirgin." Kyallen wata babban yaɗi ne da ke tsare hana iska matsar da jirgin.
"suka tuka jirgin zuwa gabar tekun"
Wato ruwa da ke tafiya a gefe ɗaya ba tsayawa. Wani lokaci, ana iya samun ruwa da ke ketere ɗaya. Wannan na iya sa ƙasar da ke ƙarkashin ruwar yă taru har ya sa ruwa ya kara zama na bisa-bisa.
"Gaban jirgin "
"bayan jirgin"
"Sojojin suna shirin"
"sa ya hana su yin abinda suka yi shirin yi"
"su yi tsalle daga jirgin ruwan zuwa ruwa"
"waɗansu a kan katakai"
Yuliyas ya nuna wa Bulus karamci ya kuma yarda ya bi abokansa don su kula da shi.
Jirgin ya yi tafiya ta tsibirin Karita da kyar.
Yuliyas bai bi gargaɗin Bulus ba domin ya mai da hankali fiye ga mai jirgin ruwan.
Bayan farawa a hankali, wata iska da ake kira Yurokilidon, ta fara buga jirgin.
Bayan kwanaki dayawa, ƙungiyan sun bar duk begen da ya kamata su tsira.
Mala'ikan ya faɗa wa Bulus cewa shi da wanda suna cikin jirgin za su tsira.
Masu jirgin su zata jirgin na kusanta da wata kasa.
Masu jirgin suna neman hanyar da za su rabu da jirgin.
Bulus ya ce wa jarumi da sojoji cewa idan masu jirgi ba zasu tsaya cikin jirgin ba, jarumin da sojojin ba zasu tsira ba.
Bulus ya roki kowa ya ci abinci.
Ƙungiyan sun kai jirgin zuwa rairayin bakin teku, amma gaban jirgin ya kafe a kasa, sai kuma kurar jirgin ta fara kakkaryewa.
Sojojin za su kashe 'yan kurkukun domin kada su tsira.
Jarumin ya hana shirin sojojin domin ya so ya ceci Bulus.
Waɗanda suka iya iyo sun yi tsalle su fada a ruwa suka kai gacci, sa'annan sauran su biyo baya a kan karyayyun katakai ko akan abubuwan da ke a jirgin.
1 Sa'adda muka sauka lafiya, sai muka ji cewa sunan tsibirin Malita. 2 Mutanen garin sun nuna mana alheri matuka don sun hura wuta don mu ji dimi, saboda ruwan sama da sanyin da ake yi. 3 Amma sa'adda Bulus ya tara kiraruwa don hura wuta, sai maciji saboda zafin wuta, ya fito ya nade hannuwansa. 4 Da mazaunan garin suka ga maciji ya nade hannuwansa, sai suka cema junansu, "Ba shakka wannan mutumin mai kisan kai ne, koda shike ya tsira daga Teku, sharia baza ta barshi da rai ba". 5 Amma ya karkade macijin cikin wuta ba tare da ya cutar da shi ba. 6 Sun saurara su gani ko zai kumbura ko ya fadi matacce. Amma da suka jira dan lokaci basu ga wata matsala ta same shi ba sai suka canza tunaninsu sukace shi wani allah ne. 7 A kusa da wannan wurin tsibirin akwai wasu gonakin wani babban mutumin tsibirin, mai suna Babiliyas. Ya karbe mu ya biya bukatun mu har kwana uku. 8 Ana nan ashe mahaifin Babiliyas yana fama da zazzabi da atuni. Bulus ya shiga, yayi masa addu'a, ya dibiya masa hannu, ya sami warkarwa. 9 Sa'adda wannan ya faru, sauran marasa lafiya da ke tsibirin sun zo sun sami warkarwa. 10 Mutanen sun mutunta mu kwarai. Yayin da muke shirin tafiya, sun bamu duk abinda muke bukata. 11 Bayan watanni uku, mun shiga jirgin Iskandariya wanda tun da hunturu yake a tsibirin mai zane kamannin Tagwaye Maza. 12 Bayan saukar mu a birnin Sirakus, mun yi kwana uku a wurin. 13 Daga nan sai muka tafi, har muka zo birnin Rigiyum. Bayan kwana daya iska mai karfi daga kudu ta taso, a cikin kwana biyu muka iso Butiyoli. 14 A can muka iske wasu 'yan'uwa suka roke mu mu zauna tare da su har kwana bakwai. Ta wannan hanyar ce muka zo Roma. 15 Daga can da 'yan'uwa suka ji labarin mu, suka fito don su tarbe mu tun daga Kasuwar Abiyas da kuma Rumfuna Uku. Da Bulus ya gan su, ya yi wa Allah godiya ya kuma sami karfafawa. 16 Sa'adda muka shiga Roma, aka yardar wa Bulus ya zauna shi kadai tare da sojan da ke tsaronsa. 17 Ana nan bayan kwana uku, Bulus ya kira shugabannin Yahudawa. Bayan da suka taru, sai ya ce masu, "Yan'uwa, ko da shike ban yi wa kowa laifi ko keta al'adun Ubanninmu ba, duk da haka an bashe ni daurarre tun daga Urushalima zuwa ga hannunwan mutanen Roma. 18 Bayan tuhumata, sun yi kudirin saki na, domin ban yi laifin da ya cancanci mutuwa ba. 19 Amma da Yahudawa suka tsaya a kan ra'ayin su, ya zama dole in daukaka kara zuwa ga Kaisar, ba domin ina da wani dalilin da zan yi karar al'ummata ba ne. 20 Saboda wannan ne na bukaci ganinku in yi magana da ku. Saboda begen da Isra'ila suke da shi ya sa nake daure da wannan sarkar". 21 Sai suka ce masa, "Bamu karbi wasiku daga Yahudiya game da kai ba, babu kuma wani daga cikin 'yan'uwa wanda ya kawo mana wani rahoto ko wata magana game da kai. 22 Amma muna so mu ji daga gare ka abin da kayi tunani ka kuma gani game da wannan darikar, gama mun sani ana kushenta a ko'ina." 23 Sa'adda suka sa masa rana, mutane da dama suka same shi a masaukinsa. Ya gabatarda zantattukan a gare su, yana tabbatar da bayyanuwar mulkin Allah. Har ya nemi ya rinjaye su a kan zancen Yesu, tun daga attaurat ta Musa zuwa litattafan annabawa, ya yi wannan tun daga safiya har yamma. 24 Wasu sun kawar da shakkar abin da aka fada, amma wadansu basu gaskanta ba. 25 Da shike ba su yarda da junansu ba, sai suka tafi bayan da Bulus ya fadi kalma daya, "Ruhu Mai Tsarki ya yi magana ta bakin annabi Ishaya zuwa ga kakanninku. 26 Ya ce, 'Jeka wurin al'umman nan ka ce, cikin ji zaku ji amma ba zaku fahimta ba; zaku gani amma ba zaku gane ba. 27 Amma zuciyar mutanen nan ta yi kanta, kunnuwansu sun ji da kyar, sun rufe idanunsu; don kada su gani su gane, su kuma ji da kunuwansu, kuma su fahimta da zuciyarsu, domin su juyo ni kuma in warkar da su." 28 Saboda haka, sai ku sani cewa wannan ceto na Allah an aikar da shi zuwa ga Al'ummai, za su kuma saurara." 29[1]30 Bulus ya zauna shekaru biyu a cikin gidan hayarsa, yana marabtar duk wadanda suka zo wurinsa. 31 Yana wa'azin mulkin Allah, yana koyarwa da al'amuran Ubangiji Yesu Kristi gaba gadi. Ba wanda ya hana shi.
Bayan aukuwar haɗarin jirgin ruwar, Jama'ar da ke tsibirin Malita sun taimaka wa Bulus da kowa da kowa da ke jirgin. Suka yi zama a wurin har na wata 3.
A nan kalmar nan "mu" na nufin Bulus, marubucin, da kuma waɗanda suake tafiya tare da su, ammam ba masu karatu ba.
AT: "Sa'adda muka iso lafiya"
Bulus da Luka suka ji sunan tsibirin. AT: "muka ji daga baƙin mutanen" ko kuma "muka ji daga mazaunan wurin"
Malita wata tsibiri ce da ke kudancin tsibirin Sicily a yau.
"Ainihin 'yan wurin"
Ana maganar alheri kamar wani abu ne musamman da ake iya nunawa. AT: "ba ƙaramin alheri suka nuna mana ba"
"nuna mana baban alheri matuka"
"sun haɗa ƙirare da su reshe suka ƙone su"
Wannan na iya nufin 1) "suka marabci dukkan mutanen da ke jirgin ruwan" ko kuma 2) "suka marabci Bulus da dukkan abokan tafiyansa."
"sai maciji mai dafi sosai ya fito daga tarin itatuwan"
"ya cije Bulus a hannu ya kuma ɗafa hannun"
"Haƙikka, wannan mutumin mai kisan kai ne" ko kuma "Lallai wannan mutumin mai kisan kai ne"
kalmar nan "shari'a" sunan wani allah ne da suke bauta wa. AT: "allah da ake kira "shari'a"
"ya karkaɗe hannun sa don macijin ya faɗi daga hannunsa cikin wuta"
"Bai ji ma Bulus ba ko sam"
Wannan na iya nufin 1) jikinsa ya kumbura saboda defin macijin ko kuma 2) zai yi zafi ƙwarai da zazzabi.
AT: "kome akansa yana yadda yakamata"
Ana maganar yin wata tunani daban aka yanayi ne kamar mutum yana canza tunanisa. AT: "suka sãke tunani kuma"
AT: "cewa, 'lallai wannan wani allah ne"
Mai yiwuwa akwai wata bangaskiya da suke da shi cewa mutumin da har ya rayu bayan cizon maciji mai dafi sosai allah ne ko kuma na allah ne shi.
Ana amfani ne da wannan do a gabatar da wani sabon mutum ko abinda ya faru a labarin.
Wannan na iya nufin 1) ainihin shugaban mutanen ko kuma 2) wani mafi muhimmanci a tsibirin, mai yiwuwa domin dukiyarsa"
Wannan sunan wani mutum ne.
Wannan na ƙarin bayani ne game da mahaifin Babiliyas da zai zama da muhimmanci ƙwarai a fahimtar labarin.
yana fama da "rashin lafiya"
Atini wani ciwa ne da ke kama hankin mutum.
"ya taɓa shi da hannayensa"
AT: "ya warkar da su ma"
Mai yiwuwa sun mutunta Bulus da waɗanda ke tare da shi ta wurin ba su kyautai.
"wanda ƙungiyar ma'aikatan jirgin sun bari a tsibirin don lokacin sanyi"
Wannan na iya nufin 1) wata jirgi da ta zo daga Iskandariya, ko kuma 2) wata jirgi da aka yi mata rajista ko kuma aka ba ta takardin izinin aiki a Iskandariya.
A sashin gaba da jirgin ruwan, akwai siffar gumakai biyu da ake ce da su "tagwaye maza." Sunayen su na Kasto da Pollus.
Siracus wata gari ne a tsibirin kudu maso gabas na tsibirin Sikili a yau, daidai kudu maso yamma na Italiya.
Wannan wata gari ne na tsaha da ke kudu maso yammacin ƙareshen ƙasar Italiya.
"iskan ta fara tasowa ne daga kudu"
Butiyoli yana garin Napalis tsibirin yamma na ƙasar Italiya.
"A can muka sadu"
Wato masubin Yesu kenan, a haɗe da maza da mata. AT: "''yan'uwa masubi"
AT: "suka gayacce mu"
Da zara Bulus ya isao Butiyoli, sauran tafiyarsa zuwa ƙasar Roma a kasa ne dukka. AT: "Sa'annan bayan da mun yi ƙwana bakwai da su, sai mun tafi ƙasar Roma"
"da suka ji cewa muna zuwa"
Ana maganar samun ƙarfafawa ne kamar wani abu ne da mutum ke iya ɗaukawa. AT: "wannan ya ƙarfafa shi, sa'annan ya yi wa Allah godiya"
AT: "Da muka iso ƙasar Roma, sai hukumar Roma suka ba wa Bulus izinin"
Ana amfani ne da wanna jimlar don a dasa aya ga wata sabuwar bangaren labarin. Idan harshenku tana da wata hanya ta musamman na yin haka, kuna iya amfani da shi anan.
Wato shugabannin ma'aikatan gwamnati ko kuma na addini da ke Roma.
"yi wa mutanen mu laifi" ko kuma "yi wa Yahudawa laifi"
AT: "wasu Yahudawa sun kama ni a Urushalima suka da ni a hannuwan hukumar Romawa"
A nan "hannuwan" na nufin iko ko kuma mulki.
"ban yi wani abinda zai sa su su ƙashe ni ba"
Wannan bai shafi Yahudawa dukka ba. AT: "shugabannin Yahudaw"
"suka yi gardama da abinda hukumar Roma suke son si yi"
AT: "ya zama lallai ne in roƙa Kaisar yă yanke mini shari'a"
Ana iya juya kalmar nan "kara" zuwa "zargi." Anan "al'umma" na nufin jamar. AT: "amma ba wai don ina so in zarge al'ummata a gabar Kaisar bane.
Wannan na iya nufin 1) mutanen Isra'ila suna bidan zuwan Almasihu da gabagadi ko kuma 2) jama'ar Isra'ila
A nan "Isra'ila" na nufin mutanen. AT: "mutanen Isra'ila" ko kuma "Yahudawa"
A nan "ɗaure da wannan sarkar" na nufin zaman ɗaurarre. AT: "cewa ni ɗaurarre ne"
A nan "'yan'uwa" na nufin 'yan'uwa Yahudawa. AT: "babu kuma wani daga cikin 'yan'uwan mu Yahudawa"
Wata ƙaramar taro ne a tsakanin wata babban taro. Anan wanna na nufin waɗanda suka gaskanta da Yesu. AT: "kayi tunani game da darikar da kake"
AT: "domin mun sani"
AT: "Yahudawa da yawa a dukkan kasashen da ke cikin ikon Roma na faɗin munanan abubuwa akasa"
"suka zaɓa wani lokaci da zai yi magana da su"
A nan "mulkin Allah" na nufin mulkin Allah a matsayin mai sarauta. AT: "ya faɗa masu game da sarautar Allah a matsayinsa na sarki" ko kuma "ya faɗa masu yadda Allah zai nuna masu kansa a matsayin sarki"
A nan " litattafan annabawa" na nufin abinda suka rubuta. AT: "daga abinda annabawa suka rubuta"
AT: "Bulus ya samu ya ƙarfafa wasun su"
A nan "kalma" na nufin sako ko bayani. AT: "bayan da Bulus ya ƙara faɗi wani abu" ko kuma "Bulus ya yi wannan bayani"
AT: "Ruhu Mai Tsarki ya yi magana mai kyau ta wurin baƙin annabi Ishaya zuwa ga kakanninku sa'ad da Ruhu ya ce wa Ishaya yă gaya masu cewa za su ji amma ba za su fahimta ba; za su kuma gani amma ba za su gane ba"
Ana maimaita kalmomin nan "ji" da "gani" ne domin nanaci. "Za ku ji kam da kyau ... za ku kuma gani sosai"
Duk waɗannan a takaice na nufin abu ɗaya ne. Suna nanata ne cewa Mutanen Yahudawa ba za su fahimci shirin Allah ba.
Ana maganar mutanen da sun ƙi su fahimci abinda Allah ke cewa ne ko yi kamar zuciyar su ne ta yi kanta. Ana "zuciya" na nufin hankalin.
Ana maganar mutanen da sun ƙi su fahimci abinda Allah ke cewa ne ko yi kamar ba su iya ji kuma suna rufe idanunsu don su gani.
A nan "zuciya" na nufin hankali.
Ana maganar fara biyayya da Allah kamar mutum ne da ake iya ganinsa yana juyo wa zuwa ga Allah.
Wannan na nufin ba a jiki kadai Allah zai warkar da su ba. Amma zai warkar da su a ruhaniya ta wurin gafarta masu zunubansu.
Ana maganar yadda Allah yana ceton mutane ne kamar wani abu ne da aka aika. AT: "Allah yana aikan bayinsa zuwa ga Al'ummai su faɗa masu game da yadda zai cece su"
"wasunsu kuma za su saurara." Wannan amsa da Al'ummai za su yi ya banbanta da yadda Yahudawa suka amsa a wancan lokaci.
A nan "mulkin Allah" na nufin sarautar Allah a matsayin Sarki. AT: "Yana wa'azi akan sarautar Allah a matsayin Sarki" ko kuma "Yana wa'azin akan yadda Allah zai nuna kansa a matsayin sarki"
Mutanen sun nuna masu alheri matuka.
Mutanen sun zata cewa Bulus mai kisan kai ne, wanda ba a yarda masa ya rayu ba.
Mutanen sun zata ko Bulus wani allah ne.
Sauran mutane marasa lafiya da ke tsibirin sun zo sun sami warkarwa.
Bulus da ƙuniyan suka zauna a tsibirin Malita har watanni uku.
Da Bulus ya gan su, ya yi wa Allah godiya ya kuma sami karfafawa.
An yardar wa Bulus ya zauna shi kadai tare da sojan da ke tsaronsa.
Bulus ya faɗa wa shugabanin Yahudawa cewa an ɗaura shi da sarka saboda begen Isra'ila.
Shugabanin Yahudawa a Roma sun san cewa ana magana akan ƙungiyan a ko'ina.
Bulus ya yi kokarin rinjaye su game da Yesu daga dokar Musa da kuma annabawa.
Wasu shagabanin Yahudawa sun amince, wasu kuma basu gaskanta ba.
Nassi na karshe da Bulus ya ambata ya faɗa cewa waɗanda basu ganskanta ba, ba za su fahimta ko su ji abin da suka ji ko gani ba.
Bulus ya ce an aika sakon ceton Allah ga Al'ummai, za su kuma saurara.
Ba wanda ya hana shi.
Bulus ya yi wa'azin mulkin Allah, ya kuma yi koyarwa game da Ubangiji Yesu Almasihu da gabagadi.
1 Bulus, bawan Yesu Almasihu, kirayayye ya zama manzo, kuma kebabbe domin bisharar Allah. 2 Wannan itace bisharar da ya alkawarta tuntuni ta wurin annabawansa ta wurin tsarkakakkun littattafan sa. 3 Game da Dansa ne, haifaffe daga zuriyar Dauda ga zancen jiki. 4 Ta wurin tashinsa daga mattatu aka aiyana shi ya zama Dan Allah ta wurin ikon Ruhu na tsarkakewa. Yesu Almasihu Ubangijimu. 5 Ta wurinsa muka karbi alheri da manzanci sabo da biyayyar imani a cikin dukkan al'ummai, domin darajar sunansa. 6 cikin wadannan al'ummai kwa, ku ma an kiraku ku zama na Yesu Almasihu. 7 Wannan wasika ga dukkanku ne da kuke cikin Roma, kaunatattu na Allah, kirayayyun mutane tsarkakakku. Bari alheri ya kasance tare daku, da salama daga Allah Ubanmu, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu. 8 Abu na farko dai ina yi wa Allah na godiya ta wurin Yesu Almasihu domin ku duka, domin kuwa ana labarta bangaskiyarku ko ina a cikin dukkan duniya. 9 Domin kuwa Allah shi ne shaida ta, wanda nake bautawa a cikin ruhuna a cikin bisharar Dansa, yadda a koyaushe na ke ambaton ku. 10 A kullum ina roko cikin addu'o'ina domin ta kowanne hali in yi nasarar zuwa gare ku da izinin Allah. 11 Gama ina marmarin ganin ku, domin in baku wata baiwa ta ruhaniya, domin in karfafa ku. 12 Wato ina dokin in sami cikakkiyar karfafawa a cikin ku, ta wurin bangaskiyar junanmu, wato tawa da taku. 13 Yanzu fa bana so ku rasa sani, yan'uwa, sau da yawa nake yin niyyar zuwa wurinku, amma har yanzu hakan din bata samu ba. Na so yin hakan din ne don in sami 'ya'ya na ruhu a cikinku kamar dai yadda ya ke a sauran Al'ummai. 14 Ina dauke da nawayar Hellinawa da ta sauran jama'a, masu hikima da marasa hikima. 15 Don a shirye na ke in sanar da bishara a gare ku, ku da kuke cikin Roma. 16 Don kuwa ni ba na jin kunyar yin bishara, don ita ce ikon Allah don samun ceto ga duk wanda ya gaskata, da farko dai Yahudawa kana kuma Hellinawa, 17 Domin a cikin ta adalcin Allah ya bayyana daga bangaskiy zuwa bangaskiya, kamar yadda yake a rubuce, "Mai adalci zai rayu ne tawurin bangaskiya." 18 Domin fushin Allah ya bayyana ne daga sama gaba da rashin ibada da rashin adalci na yan'adam, wadanda suke danne gaskiya ta wurin rashin adalcin su. 19 Dalili kuwa abinda yakamata a sani game da Allah a bayyane ya ke a gare su. Domin kuwa Allah ya bayyana masu shi a zahiri. 20 Domin al'amuransa da ba'a iya gani a bayyane suke tun halittar duniya. A na iya gane su ta wurin halitatattun abubuwa. Wadannan al'amura kuwa sune madawwamin ikonsa da Allahntakarsa. Sakamakon haka, wadannan mutane ba su da hujja. 21 Dalili kuwa, koda suna jin sun san Allah, amma basu darajanta shi a matsayin Allah ba, ko kuma su nuna masa godiya. Maimakon haka, suka zama wawaye a cikin tunaninsu, zukatansu marasa tunani sun duhunta. 22 Suna daukar kansu akan masu hikima ne su, amma sai ga su sun zama wawaye. 23 Sun musanya daukakar Allah madawwami da ta kamannin abubuwan da basa dawwama, kamar mutum, da tsuntsaye, da dabbobi masu kafafu hurhudu, da masu jan ciki. 24 Saboda haka Allah ya bashe su ga sha'awoyin kazantar zukatansu, su wulakantar da jukunansu a junansu. 25 Sune suka musanya gaskiyar Allah da karya, Kuma suke sujada da bauta ga halittaccen abu, maimakon Mahaliccin, Wanda yake abin yabo har abada. Amin. 26 Saboda haka Allah ya bashe su, ga sha'awowin su na lalata da wulakanci, har matansu suka canza ka'idar jima'i da aka saba zuwa madigo mace da mace. 27 Mazajensu ma suka sauya ka'idar jima'i tsakanin mace da miji zuwa namiji da namiji suna yin aikin lalata. Maza su na kwana da maza suna aikata aikin ban kyama, suna kuwa girbe sakamakon aiknsu na ban kyama. 28 Tunda shike ba su amince da Allah a cikkin al'amuransu ba, Allah ya bashe su ga bataccen hankalinsu, su aikata wadannan munanan abubuwa. 29 Suna cike da dukkan rashin adalci, mugunta, kyashi, keta, kuma cike da kishi, kisan kai, tarzoma, makirci, da kuma munanan manufafofi. 30 Masu gulma da kage, makiyan Allah. Masu tada zaune tsaye, masu taurin kai, da ruba, masu kaga kowadanne miyagun abubuwa, kuma masu kin yin biyayya ga iyayensu. 31 Masu duhun zuciya; masu cin amana, marasa soyayya, da kuma rashin tausayi. 32 Suna sane da tsarin Allah cewa masu yin irin wadannan al'amura sun cancanci hukuncin mutuwa. Ba kuwa yin wadannan abubuwan ka dai suke yi ba, harma goyon bayan masu yinsu suke yi.
Mai yiwuwa harshen ku na da wata hanya da take gabatar da marubucin wasika. Yana iya yiwuwa ku bayyana wadanda Bulus ya rubuto masu wasikar a ayan nan ta fari
AT: "Allah ya kira ni don in zama manzo ya kuma zaɓe ni in shaida wa mutane bishara"
Wannan na nufin cewa Allah ya naɗa ko ya zaɓe mutane su zama 'ya'yan sa, su zama bayin sa da kuma masu shaida sakon ceto ta wurin Yesu.
Allah ya yi wa mutanen sa alkawari cewa zai kafa mulkin sa. Ya ce wa annabawa su rubuta waɗannan alkawaran cikin littattafai.
Wannan na nufin "bisharar Allah", Labari mai kyau da Allah ya alkawarta cewa zai aiko da Ɗan sa cikin duniya.
Wannan laƙabi ce mai muhimmanci na Yesu, Ɗan Allah.
A nan kalman nan "jiki" na nufin jiki nan ta duniya. AT: "shi wanda ke daga zuriyar Dauda bisa ga halitan jiki" ko "wanda ke haifaffe daga iyalin Dauda"
A nan Bulus ya yi maganar takalifin sa don wa'azi.
Kalman nan "shi" na nufin Yesu Almasihu. AT: "Da iƙo Allah ya ce da shi Ɗan Allah"
"tawurin tashe sa da aka yi daga cikin su mutanen da suka mutu." Wannan na maganar dukan mutanen da suka mutu har ma da duniya ta mugayen ruhohi, kuma tashiwa da rai faɗaɗɗe ne kamar tashin mattatu daga cikin su.
Wannan na nufin Ruhu Mai Tsarki.
Allah ya ba wa Bulus kyautar zaman manzo. AT: "Allah ya mai da ni manzo." Wannan gatanci ne ta musamman"
Kalman nan "mu" anan na nufin Bulus ne da kuma manzanin nan dake mabiyan Yesu amma banda masubi dake ikkilisiyar da take a Roma.
Bulus ya yi amfani da wannan kalman "suna" kamar wata kalma ce da ake amfani da ita a maɗadin ainihin abin da ake magana a kai wanda anan tana nufin Yesu. AT: "Domin koyar da dukan al'ummai su yi biyayya saboda bangaskiyar su a gare shi"
AT: "Ina rubuta wannan wasikar ga ku da ke a Roma waɗanda Allah ya ƙaunace su ya kuma zaɓa don su zama mutanensa"
AT: "Bari Allah ya baku alheri da salama" ko "Bari Allah ya albarkace ku ya kuma baku salamar zuciya"
Kalman nan "Uba" lakani ce mai muhimmanci na Allah.
yankin Roma itace duniyan da Bulus da masu karanta wasikar sa sun sani kuma suna iya tafiye-tafiye ciki
Bulus ya nanata cewa yana yi musu addu'a kuma Allah ya gan shi a sa'adda yana yi masu addu'a. Kalman nan "don" yawancin lokatai ba a juya shi.
Ruhun mutum wata bangare ce tasa da ke iya sanin Allah da kuma gaskatawa cikin sa.
Labari mai kyau (bishara) ta Littafi Mai Tsarki ita ce Ɗan Allah ya bada kansa domin ceton duniya.
"Na yi magana da Allah game da ku"
"Ina addu'a a kowace lokaci , Ina roƙon Allah don ... in yi nasara ... cikin zuwa ziyartan ku"
"ta kowace hanyan da Allah ya bari"
"daga baya" ko "daga karshe"
"saboda muradin Allah"
"Domin lailai ina so in gan ku"
Bulus na so ya karfafa runahaniyar kristocin ta Romawa. AT: "waɗansu baiwa da za su taimake ku ku yi girma cikin ruhaniya"
AT: "Ina nufin cewa so nake mu karfafar Juna ta wurin bayyana bangaskiyar mu cikin Almasihu"
Bulus ya nanata cewa yana so su samu sanin wannan labari. Zaka iya juya wannan nau'i biyu cikin tabbatacen tsari. AT: "Ina so ku sani"
A nan wannan na nufin Krista ne, haɗe maza da mata.
AT: "ko wace lokaci wani abu kan hana ni"
Kalman "amfani" kwatanci ne da ke a madaɗin mutane da ke a Roma waɗanda Bulus ke so su gaskata da bishara. AT: "don mutane cikin ku su iya sa begensu cikin Yesu"
Al'ummai cikin waɗansu yanki ta inda ya riga ya je.
Yin amfani da kwatancin nan "bashi," Bulus ya yi magana a kan aiki bautar Allah kamar wata bashi ne ta kuɗi da Allah ke bin sa. AT: "Lailai ne in kai bishara zuwa ga"
Kuna iya juya wannan cikin tabbatacen tsari. AT: "Na sa begen dungum cikin bishara"
A nan "bada gaskiya" na ma'anan cewa mutum ya sa begen sa cikin Almasihu. AT: "gama ta wurin bishara ce Allah cikin ikonsa ya cece duk wanda suka sa begen su cikin Almasihu"
"ga mutanen Yahudawa sa'anan kuma Al'ummai"
A nan "farko" na ma'anan zuwa kafin sauran bisa ga lokaci.
A nan "ta" na nufin bishara. Bulus ya bayyana dalilin sa begen sa dungum cikin bishara.
Bulus ya yi maganar sakon bishara kamar wani abu ta duniya ne da Allah zai iya nuna wa mutane a fili. Ku na iya juya wannan cikin tsari mai aiki. AT: "Allah ya fada mana cewa ta wurin bangaskiya ne mutane su kan zama adalai tun farko har zuwa karshe"
AT: "kamar yadda wani ya rubuta cikin litattafai"
A nan "adalai" na nufin waɗanda su ka sa begen su ga Allah. AT: "ai mutanen da suka sa begen su ga Allah su ne ya dube su a matsayin waɗanda aka daidaita da shi, su kuma za su rayu har abada"
AT: "Gama Allah ya nuna fushin sa"
Bulus ya yi anfani da Kalman nan "gama" don ya nuna wa mutane cewa abin da ya fada cikin Romawa 1:17 gaskiya ne.
kalmomin nan "rashin bin Allah" da "rashin adalci" suna ce mai tsamo da ake iya bayyana ta tawurin amfani da kalma kamar "rashin bin Allah" ta na kamanta mutane, "rashin adalci" kuma kamanin ayyukan su ne. Sunayen nan kalma ce da ke nuna mutanen da Allah ke fushi da su. Ku na iya juya wannan cikin sifar aiki. AT: "Allah ya bayyana fushin sa daga sama ga mutane domin rashin bin Allahn su da kuma ayyukan duhu"
"gaskiya" anan na nufin gaskiyar labarin game da Allah. AT: "boye labari ta gaskiya game da Allah"
AT: "su na iya sanin Allah saboda abubuwan da suna iya gani a fili"
A nan "bayyana masu" na ma'anan cewa Allah ya nuna musu gaskiyar game da kansa. AT: "domin Allah ya bayyana wa kowa yadda yake"
Bulus ya yi maganar fahimtar al'amuran Allah marasa gănuwa ga mutane kamar mutane sun gan al'amuran. AT: "Gama mutane sun fahimci al'amuran Allah marasa gănuwa kamar haka, madawamiyar iƙon sa da allahntakarsa"
"dukan al'amura da kuma halin Allah" ko "abubuwa game da Allah da ya nuna cewa shi Allah ne"
Wannan na nufin sammai da duniya da kuma dukan abin da ke cikin su.
AT: "saboda abubuwan da Allah ya halita" ko "domin mutane sun gan abubuwan da Allah ya halita"
"wannan mutanen ba su da hujjan cewa ba su sani ba"
AT: "suna tunanin munanan abubuwa"
A nan "duhu" kalma ce da ke a misalin rashin fahimtar mutane. Anan "zuciya" wata kalma ce da ke misalin tunanin mutum ko kuwa rayukan. AT: "sun zama marasa fahimtar abin da Allah ke so su sani ba"
"A sa'ada suke da'awa wai su masu hikima, sun zama wawaye"
mutanen bisa ga Romawa 1:18
"sauya gaskiyar cewa Allah maɗaukaki ne kuma ba zai mutu ba" ko "ba su gaskata cewa Allah shine maɗaukaki kuma ba zai taɓa mutuwa ba"
"maimakon haka sun zabi su bauta wa gumaka da ke kamanin"
"waɗansu mutane da za su mutu"
"kamar tsuntsaye, dabbobi ko abubuwa masu rarrafe"
"domin abin nan da na fada gaskiya ce"
"Allah ya bar su ga shiga cikin"
"yan' adam" bisa ga Romawa 1:18
A nan "sha'awace-sha'awacen zukatansu" adaɗin magana ne da ke a madaɗin mugayen abubuwan da suke so su aikata. AT: "halin kazanta ita ce babbar muradin su "
Wannan daddin magana ce da ke nufin aikata lalata. AT: "sun aikata lalata da kuma abubuwa masu banƙyama"
A nan "halita" na nufin abubuwan da Allah ya halita. AT: "Sun yi sujada ga abubuwan da Allah ya halita"
"maimakon"
"saboda bautar gumaka da kuma zunubin lalata"
"sha'anin sha'awace-sha'awace ta kunya"
"domin matansu"
AT: "yin jima'i ta hanyar da ba shirin Allah ba"
A nan "ma'amalarsu ta halal" adaɗin magana ce da ke nuna ɗangantakan mace da miji cikin juma'i. AT: "maza dayawa sun bar ma'amalarsu ta halal da mata"
"kasance da sha'awar waɗansu maza"
"sun yi abubuwan da ya kamata su ji kunya, amma basu ji kunya ba"
"maza, kuma Allah ya hukunta su da ãdalci bisa ga kuskuren da suka yi"
halin da ba daidai ba, ba kuskure game da gaskiya
"Ba su yi tunanin cewa yana da muhimmanci su san Allah ba"
Waɗannan kalmomi na nufin "yan' adam" cikin [Romawa 1:18]
A nan "battacen hankalinsu" na ma'anan zuciya mai tunanin abubuwa ta haram. AT: "Allah ya bar zuciyar su da ke cike da halin banza da kuma haramtaccen tunani ta mulke su"
"abin kunya" ko "zunubi"
AT: "Su na da muradi mai karfi na" ko "Su na cike da muradin mai karfi na yin ayyuka na" (Dubi:
AT: "Kullayomi yanwanci suna kishin suaran mutane... yawanci muradin kullayomi ita ce kisan kai ... suna sa gardama da kuma hargitsi tsakanin mutane ...don rudin waɗansu ... suna magana ta rashin jituwar su game da waɗansu"
mai ɓatanci ya kan faɗa abin da ba daidai ba game da wani don ya ɓata masa suna.
"tunanin sabuwar hanyar yin mugunta ga wadansu"
"Suna sane da yadda Allah yake so su yi rayuwa"
A nan "aikata" na nufin cigaba da yi ko halin yin mugayen abubuwa. AT: "kuma dukan wanɗanda suka cigaba da aikata mugayen abubuwa"
"cancanci mutuwa"
"irin waɗannan mugayen abubuwa"
A nan kalman nan "aikata" na nufin cigaba da aikata mugayen abubuwa. AT: "waɗanda suka cigaba da aikata mugayen abubuwa"
Allah ya yi alkawarin bishara a dă kafin annabawa a cikin littafi mai tsarki.
An haife Ɗan Allah a zuriyar Dauda ne bisa ga jiki.
An bayyana Yesu Ɗan Allah ta wurin tashi daga matattu.
Bulus ya karbi alheri da kuma almajiranci domin biyayyansa na bangaskiya daga cikin dukka kasashe.
Bulus na yi wa Allah godiya domin suna shellar bangaskiyarsu ko ina a cikin dukkan duniya.
Bulus ya na marmarin ganin su domin ya basu wasu kyauta na ruhu domin ya ƙaddamad da su.
Bulus bai iya ziyartar su ba domin hakan bai samu ba sai yanzu.
Bulus ya ce bishara ikon Allah ne domin ceton dukka wanda ya bada gaskiya.
Bulus ya sa farashin littafin da ya ce ''Sălihai za su yi rayuwar bangaskiya''.
Mugaye da marasa adalci suna kin gaskiya ko da shike dukka abubbuwan da ke sane game da Allah ya na a bayyane garesu.
Abubbuwan da suke a boye game da Allah suna a bayyane ta wurin abubbuwan da aka halitta.
Ikon Allah na har abada da kuma siffar Allah suna nan a bayyane.
Allah ya na ba da su ga sha'awar jikin su da na zuciyarsu domin rashin tsabta, domin jikinsu ta kaskantad dasu a cikin su.
Matan nan suna ƙwadayin sha'awar jikin juna, mazajen kuma suna ƙwadayin sha'awar jikin juna.
Allah ya na ba da su ga muguwar hankalinsu, domin su yi abubbuwan da basu dace ba.
Wadanda suke da mugayen hankali suna cike da hassada, da kisan kai, da husuma, da yaudara, da kuma mugayen nufi.
Wadanda suke da mugayen hankali suna gane cewa wadanda suke yin wadannan abubuwa sun cancanci mutuwa.
Sun cigaba da yin abubuwa marasa adalci, sun kuma amince da ma su yin su.
1 Saboda da haka baka da hujja, kai mutum, kai mai shara'antawa, domin kuwa abinda kake shara'antawa akan wasu kana kada kanka da kanka. Domin kuwa kai mai shar'antaawa kana aikata wadannan abubuwa. 2 Amma mun san cewa shari'ar Allah ta gaskiya ce sa'adda zata fado wa masu aikata wadannan irin abubuwa. 3 Amma ka lura da wannan, ya kai mutum, mai shara'anta masu aikata wadannan ababuwa. Duk da shike kaima kana aikatawa. Kana jin zaka kubucewa hukuncin Allah? 4 Ko kana raina falalar alheransa da yake yi ta wajen jinkirin hukuncinsa, da hakurinsa? Baka san cewa alheransa musanman domin su kai ka ga tuba bane? 5 Amma saboda taurin kanka da zuciyarka marar tuba, kana tanadarwa kanka fushi, a ranar fushi, wato ranar bayyanuwar shari'ar adalci ta Allah. 6 Zai baiwa kowanne mutum daidai sakamakon ayyukansa: 7 Ga wadanda kuma suka nace da yin ayyukan alheri ba fasawa, sun samarwa kansu, yabo da daraja, da rai na har'abada. 8 Amma ga masu son kai, wadanda suka ki yin biyayya ga gaskiya, suka yiwa rashin adalci biyayya, fushi da hasala mai zafi zai afko masu. 9 Allah kuma zai sauko da bala'i da bakin ciki ga dukkan rayukan da suka aikata mugunta, ga Yahudawa da fari, sannan kuma Hellinawa. 10 Amma yabo daraja da salama zasu kasance ga dukkan wadanda suka aikata ayukan alheri, ga Yahudawa da fari sannan Hellanawa. 11 Domin kuwa Allah ba mai tara bane. 12 Ga wadanda suka yi zunubi batare da shari'aba, zasu hallaka ba tare da shari'a ba, ga wadanda suka yi zunubi cikin shari'a kuma za'a hukunta su bisa ga shari'a. 13 Domin kuwa ba masu jin shari'ar ne masu adalci agaban Allah ba, amma masu aikatawa ne zasu samu barata. 14 Gama al'umai da basu san shari'a ba, bisa ga dabi'a sun yi abinda ke na shari'a, sun kuma zame wa kansu shari'a, koda shike basu da shari'ar. 15 Dalilin haka kuwa sun nuna cewa ayukan da shari'a take bukata na nan a rubuce a zuciyarsu. lamirinsu kuma na yi masu shaida, tunanainsu kuma, ko dai yana kashe su, ko kuma yana karesu. 16 hakanan kuma ga Allah. Wannan zai faru ranar da Allah zai shara'anta asiran boye na dukkan mutane, bisa ga bishara ta cikin Yesu Almasihu. 17 Da shike kana kiran kanka Bayahude, kana zaune akan shari'a, kana alfahari cikin Allah, 18 ka san nufinsa, ka kuma san abubuwan da suka bambanta da hakan, ka kuma sami koyarwa cikin shari'ar. 19 Da shike kana da gabagadi akan cewa kai jagora ne ga makafi, haske ga wadanda suke cikin duhu, 20 mai horo ga marasa hikima, mai koyar da jarirai, kuma a cikin shari'ar kana da abin da ya shafi sani da kuma gaskiya. 21 ku da kuke koyar da wadansu, ba ku koyar da kanku? ku da kuke wa'azi kada ayi sata, ba ku yin sata? 22 Ku da ke wa'azi kada ayi zina, ba ku yin zina? ku da ke hana bautar gumaka, ba ku yin sata a haikali? 23 ku masu murna da tinkaho cikin shari'ar, ba kwa wulakanta Allah cikin kurakuranku na rashin bin shari'a? 24 "Domin kuwa an wulakanta sunan Allah cikin Al'umai sabili da ku," kamar yadda aka riga aka rubuta. 25 Lallai kuwa kaciya tana da riba a gare ku, idan kuka kiyaye doka, amma idan ku marasa bin doka ne kaciyarku ta zama rashin kaciya. 26 domin kuwa idan mutum marar kaciya zai kiyaye dukkan bukatun doka, baza'a iya daukan rashin kaciyarsa a matsayin mai kaciya ba? 27 Sannan idan mutum marar kaciya ta jini zai kiyaye dukkan dokoki, ba zai iya shara'anta ku masu kaciya ta shari'a ba? Haka kuma ya kasance ne domin kuna da shari'a a rubuce da kuma kaciya amma ba kwa bin doka! 28 Domin shi kuwa ba Bayahude bane a waje; ba kuwa mai kaciyar da aka tsaga fata ba. 29 Amma Bayahude ne ta ciki, sanna kuma mai kaciyar zuciya da kuma ruhu ba wasika ba, irin wanna mutumin yabonsa ba daga wurin mutane yake zuwa ba, amma daga Allah.
Bulus ya tabbatar cewa dukan mutane masu zunubi ne, ya kuma tunashe su cewa dukan mutane mugaye ne.
Kalman nan "saboda haka" na nuna sabon bangaren wasikar. Ta kuma kawo ga karshen maganar bisa ga abin da Bulus ya faɗa cikin [Romawa 1:1-32]. AT: Dashike Allah zai hukunta waɗanda sun cigaba da yin zunubi, hakika ba zai bar zunubin ka ba"
Bulus yana rubutu anan kamar yana magana da bayahuden da ke muhawara da shi. Bulus yana yin wannan domin ya koyawa masu sauraronsa cewa Allah zai hukunta duk wanda ya cigaba da yin zunubi, ko Bayahude ko kuwa Ba'al'ummi.
A nan wakilan sunan nan "kai" mufuradi ne. (Dubi:
Bulus ya yi amfani da kalman nan "mutum" anan don ya sautawa wanda zai iya tunanin shara'anta sauran mutane kamar Allah. AT: "Kai ma ɗan adam ne amma kana shara'anta sauran mutane sa'annan kana cewa sun cancanci hukuncin Allah" Dubi:
"Amma kana shara'anta kanka domin kaima ka yi mugayen abubuwa kamar yadda suka yi"
A nan wakilin sunan nan "mu" na iya yiwuwa ya shafe krista da kuma Yahudawa waɗanda ba masubi ba.
Bulus yai maganar "shari'ar Allah" anan kamar rayayye ce kuma zata iya "faɗo" kan mutane. AT: "Allah zai shara'anta waɗannan mutanen da gaskiya da kuma adalci"
"mutane masu aikata mugayen abubuwan nan"
"don haka, ku lura da wannan" ko "Saboda haka, ku lura da wannan"
"yi tunani game da abin nan da zan faɗa maka"
Yi amfani da kalman nan ta ɗan adam "ko kai waye ne"
"Kai mai cewa wani ya cancanci hukuncin Allah amma kana yin mugayen abubuwa daidai da su"
Wannan furuci ta bayyana cikin sifar tambaya don a kara nanatawa. Ka na iya juya wannan tambaya a matsayin magana da ba tabbaci. AT: "Haƙika baza ka tsira da ga shari'ar Allah ba!"
Wannan furuci ta bayyana cikin sifar tambaya don a kara nanatawa. Ka na iya juya wannan tambaya a matsayin tabbataccen magana. AT: Kada ka yi kamar bata da muhimmanci cewa Allah nagari ne kuma yana hakurin jira na sawon loƙaci kafin ya hukunta mutane don adalcinsa zai sa su su tuba"
"duba falalar ... hakurin mara muhimmanci" ko "duba ... mara kyau"
Wannan furuci ta bayyana cikin sifar tambaya don a kara nanatawa. Ka na iya juya wannan tambaya a matsayin tabbataccen magana. AT: Lalle ne ka sani cewa Allah ya nuna maka cewa shi nagari ne don ka iya tuba!"
Bulus ya yi amfani da maganar don ya kwatanta mutum da ya ki yin biyayya ga Allah da wani abu mai karfi kamar dutse. Ya kuma yi amfani da kalman nan "zuciya" a maɗaɗin zuciyar mutum ko kuwa rai. AT: "Domin kun ƙi ku kasa kunne kun kuma ki tuba"
Wannan hanya biyu ce da za ka iya haɗa kamar "zuciya mara tuba" AT: "taurin zuciya"
Maganar nan "ajiya" na nufin misali da yakan nufin mutum na tara dukiyoyinsa ya na kuma sa su a wuri mai kyau. Bulus ya ce a maimakon dukiya, mutumin yana tara hukuncin Allah. kamar yadda suka daɗe cikin rashin tuba haka ma tsanancin hukuncin. AT: ka na sa hukuncin ka ta zama mafi muni"
Dukan wannan maganar nan na nufin ranan nan ɗaya. AT: "Sa'ada Allah ya nuna fushinsa ga kowa kuma yana sharanta dukan mutane da adalci"
"bada sakamako daidai ko hukunci"
"kowane mutum bisa ga abinda da mutumin ya yi"
wannan na nufin cewa sun yi aiki cikin hanyar da zai kai ga daidaitawa mai kyau daga Allah a ranar shari'a.
Suna so Allah ya yabe su ya kuma girmama su, kuma ba su so su mutu.
Wannan na nufin ruɓewa na jiki, ba hali ba.
"son kai" ko "damuwa da abin da ke sa su kadai farin ciki"
Waɗannan maganganun na nufin abu ɗaya. Na biyun ya ƙara zurfin farkon.
Kalmomin nan "fushi" da "hasala mai zafi" na nufin abu daya ne ya kuma nanata fushin Allah ne. AT: "Allah zai nuna mummunan fushinsa"
A nan kalman nan "fushi" karin magana ne da ke nufin hukuncin Allah mai tsanani ga mugayen mutane. (Dubi:
Kalmomin nan "tsanani" da "wahala" a takaice na nufin abu ɗaya ne anan kuma ta nanata yadda munin hukuncin Allah zai zama. AT: "hukunci mai ban tsoro za ta auku zuwa ga"
A nan Bulus yayi amfani da kalman nan "rai" a matsayin karin magana ne da ke nufin mutum. AT: " bisa kan kowane mutum"
"cigaba da aikata mugayen abubuwa"
"Allah zai sharanta mutanen Yahudawa da farko sa'annan waɗanda ba mutanen Yahudawa ba"
Ma'ana mai iya yiwuwa suna kamar haka 1) "farko bisa ga loƙaci" ko 2) "lailai haƙĩƙa"
"Amma Allah zai bada yabo, girma da salama"
"cigaba da aikata abin da ke nagari"
Ku na iya juya wannan cikin tabbataciyar sifar. AT: "Gama Allah yana yi wa dukan mutane daidai yadda ya kamata"
"Don waɗanda suka yi zunubi"
Bulus ya maimaita "rashin shari'a" don nanata cewa ko mutum bai san dokan Musa ba. In sun yi zunubi, Allah zai sharanta su. AT: "a rashin sanin shari'ar Musa haƙika duk da haka za su mutu a ruhaniya"
"duk waɗanɗa suka yi zunubi"
Allah zai sharanta masu zunubi bisa shar'arsa. AT: "kuma ku da kun san shari'a Musa, Allah zai sharantasu bisa ga ita shari'ar" (Dubi: and activepassive)
Aya 14 da 15 sun tura asalin maganar da Bulus ya ba wa masu karanta wasikarsa don ƙara sanar da su. In kuna da wata hanya da ke nuna tura magana ciki kamar wannan a harshenku, kuna iya amfani da ita anan.
A nan "shari'an" na nufin shari'an Musa. AT: "ba waɗanda suka ji shari'an Musa kawai ba"
"waɗanda Allah ya tube su a matsayin adalai"
"amma waɗanda ke biyayya da shari'ar Musa"
AT: "waɗanda Allah zai ƙarbe"
Maganar nan "shari'an wa kansu" karin magana ne da ke nufin mutanen nan suna biyayya ga shari'an Allah. AT: "suna da shari'an Allah cikin zukatansu"
A nan "shari'ar" na nufin shari'ar Musa. AT: "basu da shari'an da Allah ya ba wa Musa"
"Tawurin yin biyayya ga shari'ar ya nu"
A nan "zukata" karin magana da ke nu tunani ko kuwa cikin mutum. Maganan nan "a rubuce a zuciyarsu" karin magana ne ta sanin abu cikin zuciyar su. AT: "cewa Allah ya rubuta cikin zukatansu abin da shari'ar ke buƙata su yi" ko "cewa sun san abin da Allah yana so su bisa ga shari'ansa"
A nan "yin shaida" na nufin sanin da suka samu tawurin shari'ar da Allah ya rubuta a zukatansu. AT: "ta fada musu ko suna rashin biyayya ko kuwa biyayya ga shari'ar Allah"
Wannan ta karasa maganar Bulus daga [Romawa 2:13]. "Wannan zai faru ne a sa'anda Allah zai sharanta"
"tundashike kana kiran kanka Bayahudi"
Maganar nan "dogara akan shari'an" na misalin gaskatawar cewa baza su iya zama adalai ba tawurin biyayya ga shari'an. AT: "dangan kan shari'an Musa"
"da kuma sane da nufin Allah"
AT: "domin mutane sun koyar da kai abin da ke daidai bisa ga shari'an" ko "domin ka koya daga shari'an"
A nan "makafi" da "waɗanda suke tafiya cikin duhu" wakilcin mutane ne wadda ba su fahimcin shari'ar ba. AT: "cewa domin ka koyar da shari'ar, kai da kan ka kana kamar ja gora ne ga makafi, kai kuma kana kamar haske ne ga mutanen da sun ɓata cikin duhu"
"ka horad da waɗanda suka yi abin da ba daidai ba"
A nan Bulus ya kwatanta waɗanda basu san shari'an ba da kananan 'ya'ya. AT: "kuma ka koyar da waɗanda ba su san shari'an ba"
Sanin gaskiya dake cikin shari'ar na zuwa ne daga wurin Allah. AT: "domin ka tabbata cewa ka fahimci gaskiyar da Allah ya bayar cikin shari'an"
Bulus yana amfani da tambaya domin ya kwaɓe masu sauraronsa. AT: "Kana koyawa waɗansu, amma ba ka koyar da kanka!" ko "kana koyawa waɗansu amma ba ka aikata abin da kake koyarwa!"
Bulus yana amfani da tambaya domin ya kwaɓe masu sauraronsa. AT: "Kana cewa mutane kada su yi sata, amma kai kana sata!"
Bulus yana amfani da tambaya domin ya kwaɓe masu sauraronsa. AT: "Kana cewa mutane kada su yi zina, amma kai kana zina!"
Bulus yana amfani da tambaya domin ya kwaɓe masu sauraronsa. AT: "Kana cewa wai kana ƙyamar gumaka, amma kana sata a ɗakin gunki!"
Ma'ana mai iya yiwuwa suna kamar haka 1) "satan abubuwa daga ɗakin gunkin al'umma su kuma sayar don su sami riba" ko 2) "kada ku aika kuɗi dake na Allah zuwa haikalin da ke a Urushalima."
Bulus yana amfani da tambaya domin ya kwaɓe masu sauraronsa. AT: "ai mugunta ne in kana taƙama da shari'ar, sa'annan a lokaci guɗa kana rashin biyayya da ita, ta haka kuma kana kawo kunyatawa ga Allah!"
AT: "Al'ummai da yawa sun yi saɓon sunan Allah"
Kalman nan "suna" kalma ce da ke nufin Allah, ba sunan shi kawai ba.
Na faɗi wannan duka domin kaciya bata da riba a gareku"
"in baku yi biyayya ga dokokin da ke cikin shari'ar ba"
"kamar ba a yi muku kaciya ba"
"mutum da ba a iy masa kaciya ba"
"biyayya da abinda Allah ya umurta cikin shari'an"
Bulus ya yi tambayoyi biyu anan domin ya nana cewa ba kaciya ne ke daidaita mutum da Allah ba. Ba lailai a juya wannan cikin tambaya ba. AT: "Allah zai dube shi a matsayin wanda ya yi kaciya. Wanda ba ayi masa kaciya ta jiki ba zai sharanta ku ... shari'an."
Wannan na nufin al'adun Yahudawa, karmar kaciya, wanda mutane ke iya gani.
Wannan na nufn canji ta jikin mutum a sa'ada an yi masa kaciya.
Wannan na nufin jiki. AT: "jiki"
Waɗannan kalmomin suna da ma'ana kusan iri daya. ta farkon "shi bayahude ne wadda a ciki," ta bayyana ta biyun, "kaciyar ta zuci ne."
Wannan na nufin daraja da kuma muraɗin wannan mutum da Allah ya sake she yana da shi.
A nan "zuciya" na nufin cikin mutum.
A nan "wasika" na nufin Littafi Mai Tsarki. AT: "Tawurin aikin Ruhu Mai Tsarki, ba domin ku san Littafi Mai Tsarki ba"
Wannan na nufin cikin, ruhun mutum wanda "Ruhun Allah" ya canza shi"
Wasu mutane ba su da uzuri a cikin hukuncin da su ke yi domin abubuwan da suke hukuntawa a wasu suma suna yin wannan abubuwa da kansu.
Allah ya na hukunci sa a hanyar gaskiya a lokacin da yake hukunta wadanda ba su yin adalci.
Hakurin Allah da alherinsa ya kamata ya kai mutum ga tuba.
Wadanda suke da taurin kai, da zuciya marasa tuba suna ajiye wa kansu fushi domin ranar shari'an adalci ta Allah.
Wadanda suke ayukkan adalci a ko yaushe za su sami rai na har abada.
Wadanda suke biyayyan rashin adalci za su sami fushi, tsanani da wuya.
Allah ba ya nuna son kai domin wadanda suka yi zunubi, Yahudawa ko 'yan Giriki za su halakka.
Masu bin doka suna da wajaba a gaban Allah.
Al'ummai suna nuna cewa suna da doka na kansu a lokacin da suke yin ayuka na doka bisa ga dabi'an su.
Bulus ya kalubalence su yana cewa idan suna koya wa wasu doka, suma su koya wa kansu.
Bulus ya na ambatan zunuban sata, zina, da kuma sata a haikali.
Ana ƙasƙantad da sunan Allah domin mallaman Yahudaawa na doka suna karya dokar.
Bulus ya ce kaciyar mutum tana iya zaman rashin kaciya idan mutumin mai karya doka ne.
Bulus ya ce rashin kaciyar mutumin al'umme ya na iya zaman kaciya idan wannan mutumin ya na ajiye umarnin doka.
Bulus ya ce bayahude na gaskiye bayahude ne a zuciya wanda ya ke da kaciyar zuciya.
Bayahude na gaskiye ya na karban yabo da ga wurin Allah.
1 To ina fifikon da bayahude yake dashi? Kuma ina ribar kaciya? 2 Akwai muhimmancinsu ta kowacce hanya. Tun farko dai, yahudawa ne aka dankawa wahayi daga Allah. 3 Idan wasu yahudawa basu bada gaskiya ba fa? Rashin bangaskiyarsu zai hana amincin Allah aiki? 4 Bazai taba zama haka ba. Maimakon haka, bari Allah ya zama mai gaskiya, ko da kowanne mutum makaryaci ne. Kamar yadda aka rubuta, "Domin a nuna kai mai adalci cikin maganganunka, kuma kayi nasara a lokacin da aka kawo ka gaban shari'a." 5 Amma idan rashin adalcinmu ya nuna adalcin Allah, to me zamu ce? Allah ba marar adalci ba ne, wanda ke aiwatar da fushinsa, ko kuwa? Ina magana bisa ga tunanin mutuntaka. 6 Bazai taba zama haka ba. Domin idan haka ne ta yaya Allah zai shar'anta duniya? 7 Amma idan gaskiyar Allah ta wurin karyata ta habaka yabonsa, To me yasa ake shar'anta ni a matsayin mai zunubi? 8 To me zai hana ace kamar yadda ake fadin zancen karya a kanmu, wasu kuma sun dauka cewa mun fadi hakan, "Bari muyi mugunta, domin nagarta tazo?" Hukuncin su halal ne. 9 To me kenan? Zamu ba kanmu hujja ne? ko kadan. Domin mun riga munyi zargin yahudawa da hellinawa, da cewar dukkansu, suna karkashin zunubi. 10 Kamar yadda aka rubuta, babu wani mai adalci, babu ko daya. 11 Babu wani mai fahimta. Babu wani mai neman Allah. 12 Dukansu sun kauce hanya, dukansu gaba daya sun zama marasa amfani. Babu mai aikin nagarta, a'a, babu ko da guda daya. 13 Makogwaronsu a bude yake kamar kabari. Harsunansu na dauke da cuta. Dafin macizai na karkashin lebunansu. 14 Bakunansu cike suke da la'ana da daci. 15 Sawayensu na saurin zuwa zubar da jini. 16 Tafarkinsu wahala ce da lalacewa. 17 Wadannan mutane basu san hanyar salama ba. 18 Babu tsoron Allah a idanunsu." 19 To mun san dai duk abin da shari'a tace, shari'a na magana ne da wadanda ke karkashinta, domin a rufe kowanne baki, domin dukan duniya ta bada amsa a gaban Allah. 20 Domin a gabansa babu wanda zai barata ta wurin ayukan shari'a. Domin ta wurin shari'a ne sanin zunubi yazo. 21 Amma yanzu ba tare da shari'a ba an bayyana sanin adalcin Allah, wanda shari'a da annabawa suke shaidawa. 22 Wato, adalcin Allah ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ga dukkan wadanda ke bada gaskiya. Domin babu bambanci: 23 Domin duk sun yi zunubi sun kuma kasa kaiwa ga darajar Allah, 24 Da alherinsa an baratar da mu ta wurin fansar dake cikin Yesu Almasihu. 25 Amma Allah ya bayar da Yesu Almasihu wanda yake hadayar fansa ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya mika Almasihu a matsayin tabbacin hukuncinsa, sabo da kuma ketarewar zunubanmu na baya 26 cikin hakurinsa. Duk wannan ya faru ne domin a bayyana adalcinsa cikin wannan zamani, domin ya tabbatar da kansa mai hukunci, kuma ya nuna shine mai baratar da kowa saboda bangaskiya cikin Yesu. 27 To ina fahariya? An fitar da ita. A kan wane dalilin? Don ayyuka? A'a, amma ta dalilin bangaskiya. 28 Domin wannan muka kammala cewar ana baratar da mutum ta wurin bangaskiya ba tare da ayyukan shari'a ba. 29 Ko kuwa Allah Allahn yahudawa ne kadai? Shi ba Allahn al'ummai bane? I, na al'ummai ne kuma. 30 Idan dai lallai Allah daya ne, zai baratar da mai kaciya ta wurin bangaskiya, da marar kaciya kuma ta wurin bangaskiya. 31 Mun kawar da shari'a kenan ta wurin bangaskiya? ba zai taba kasancewa haka ba. Maimako ma, muna inganta shari'a kenan.
Bulus ya shaida ribar da Yahudawa su na da shi ta dalilin shari'ar da Allah ya ba su.
Bulus ya mika ra'ayin da mutane za su iya samu bayan sun ji abin da ya rubuto a sura 2. Ya yi wannan ne domin ya faɗa musu a aya ta 2. AT: "Waɗansu na iya cewa, 'To menene ribar Bayahude? kuma menene amfanin kaciya?" ko "waɗansu na iya cewa, 'in gaskiya ce, to bayahude ba shi da wata riba, kuma babu wata amfani cikin yin kaciya."'
Bulus ya amsa batun da aka kawo a aya ta 1. Anan "akwai" na nufin zama ɗaya daga cikin mutanen Yahudawa. AT: "Amma akwai babbar riba a zaman Bayahude"
Ma'ana mai iya yiwuwa suna kamar haka 1) "Da farko dai bisa ga lokaci" ko 2) "Lailai Hakika" ko 3) "Mafi muhimmanci."
A nan "wahayi" na nufin maganar Allah da kuma alkawarensa. AT: "Allah ya bada waɗannan maganganun da ta kunshi alkawarinsa zuwa ga Yahudawa"
Bulus ya yi amfani da wannan tambayoyin domin ya sa mutane su yi tunani. AT: "Waɗansu Yahudawa ba su yi aminci ga Allah ba. To, sai mu ce, bisa ga wannan, cewa Allah ba zai cika alkawarinsa ba?"
Wannan maganar na bayyan cewa wannan ba zai faru ba. Yana iya yiwua kuna da wata hanya a harshen ku da za ku iya yin amfani da ita. "Wannan ba mai yiwuwa bane!" ko "haƙika ba haka ba!"
"maimakon haka sai mu ce, bari"
Allah zai zama mai gaskiya a koyaushe kuma zai cika alkawarensa. AT: "Allah a koyaushe yana aikata abin nan da ya alkawarta"
Kalmomin nan "kowane" da "maƙarya" don a kara nanata cewa Allah ne kadai mai gaskiya ga alkawarensa a koyaushe. AT: "in kowane mutum maƙaryaci ne"
AT: "Litattafai kansu sun yarda da abinda nake faɗi"
Waɗannan maganganun na da ma'ana kusan iri daya. AT: "Dole kowa ya amince cewa abinda da kun faɗa gaskiya ne, kuma za ku yi nasara a koyaushe in wani ya zargi ku"
Bulus ya yi amfani da wannan tambaya don ya nuna abin da waɗansu mutane suna jayayya a kai sa'annan kuma ya sa masu karatunsa su yi tunani game da abin da yake faɗi gaskiya ne ko ba gaskiya. AT: "Waɗansu sun ce tundashike rashin adalcin mu ta nuna adalcin Allah, to Allah ba mai adalci bane in ya hukuntamu"
A nan "fushi" na nufin hukunci. AT: "aiwatar da hukuncinsa a kan mu" ko "hukunta mu"
"abinda waɗansu mutane ke faɗa shine nake faɗi" ko "wannan shine abin da waɗansu mutane ke fada"
Bulus ya yi amfani da wannan tambayar don ya nuna cewa muhawarar da ke gãba da bisharar mara amfani ne, tundashike Yahudawa ma sun gaskanta cewa Allah zai shara'anta dukan mutane. AT: "Mun sani cewa Allah zai shara'anta duniya!"
"duniya" na nufin dukan mutane da ke rayuwa cikin duniya. AT: kowa dake cikin duniya"
A nan Bulus na tunanin cewa wani na iya cigaba da ƙin bisharar. Cewa abokin gãba na muhara saboda zunubinsa ta nuna adalcin Allah, don haka Allah kada ya maishe shi mai zunubi a ranar shari'a in, a misali, ya yi ƙarya.
Anan Bulus ya yi tambaya don ya nuna yadda ba'ar muhawarar abokan gãban da yake tunaninsu take. AT: "Ni ma zan iya cewa ... zo!"
"Waɗansu sun yi ƙarya cewa wannan shine abin da muna faɗa"
Zata zama daidai a sa'ada Allah ya hukunta waɗannan abokan gãban Bulus, don ƙarya game da abin da Bulus ya yi ta koyarwa.
Bulus ya yi waɗannan tambayoyin don nanata ainihin nufinsa. AT: "Mu Yahudawa kada mu yi tunanin zamu guje wa hukuncin Allah, wai don mu Yahudawa ne!"
Waɗannan kalmomin sun fi ƙarfin "a'a" kawai, amma bai kai ƙarfin "cikakken a'a!" ba
AT: "Kamar yadda annabawa suka rubuta cikin Litattafai"
Babu wani wanda ya fahimci abin da ke daidai AT: "Lailai, babu wani wanda ya fahimci abin da ke daidai"
A nan "biɗan Allah" na nufin samun ɗangantaka da Allah. AT: "Babu wani mai ƙoƙarin samun sahilin ɗangantaka mai kyau da Allah"
Wannan karin magana ne da ke nufin mutane basu so su yi tunani game da Allah. Suna so kauce masa. AT: "Dukan su sun juya baya ga Allah"
Tundashike babu wani wanda ke yin abu mai kyau, sun marasa amfani ne ga Allah. AT: "Kowa ya zama mara amfani ga Allah"
Kalman nan "su" na nufin "Yahudawa da kuma Helenawa" ta [Romawa 3:9]
Kalman nan "maƙogwaro" na nufin dukan abin da mutane suke cewa dake mara adalci da kuma ƙyama. Anan "buɗaɗɗen kabari" na nufin ɗoyin kalmomi marasa kyau na mutanen.
Kalman nan "harsuna" na nufin kalmomin karya da mutanen ke faɗa. AT: Mutane na faɗan karya"
A nan "dafin macizai" na a maɗaɗɗin babbar hastarin miyagun kalmomin da mutanen na faɗi. Kalman nan "leɓuna" na nufin kalmomin mutanen. AT: "Miyagun kalmominsu na cutar da mutane daidai kamar dafin maciji" )
A nan "bakuna" na a maɗaɗɗin miyagun kalmomin mutanen. Kalman nan "cike" na nufin sau da yawa mutanen na maganar la'ana da kuma magana mai daci. AT: "Sau da yawa sukan faɗi la'ana da kuma mugayen kalmomi"
Waɗannan kalmomin na nufin Yahudawa ne da kuma Helenawa cikin [Romawa 3:9]
A nan "Sawaye" na nufin mutanen da kansu. Kalman nan "jini" na nufin kashe mutane. AT: "Su na hanzarin yin lahani da kisan mutane"
A nan "lalacewa da wahala" na nufin lahanin da mutanen nan ke sa waɗansu su sha. AT: "ƙoƙarinsu shine su rushe waɗansu su kuma sa su su sha wahala"
"yadda za su yi zaman cikin salama da sauran mutane." "hanyar" ita hanya ce ko kuma tafarki.
A nan "tsoro" na nufin girmama Allah da kuma yarda a daraja shi. AT: "Kowa ya ki ya ba Allah darajar da ya cancanci shi"
Bulus ya yi maganar shari'ar kamar da rai kuma tana da muryarta. AT: "dukan abin da shari'ar ta ce mutane su yi don" ko "duk dokokin da Musa ya rubuta cikin shari'ar ne don"
"waɗanda lailai ne su yi biyayya ga shari'ar"
A nan "baki" na nufin kalmomin da mutane ke faɗi. AT: "domin babu wasu wanda za su iya ce wani abu ƙarɓaɓɓe don kare kanssu"
A nan "duniya" na nufin dukan mutanen da ke cikin duniya. AT: "cewa Allah ya iya ce da kowa dake cikin duniya mai laifi ne."
A nan "jiki" na nufin dukan 'yan adam.
Wannan na iya nufin 1) "Don Haka" ko 2) "Wannan domin"
"a sa'ada wani ya san shari'ar Allah, sai ya gane cewa ya yi zunubi"
kalman nan "yanzu" na nufin tun loƙacin da Yesu ya zo cikin duniya.
AT: "Allah ya bayyana hanyar daidaitawa tare da shi ba tare da yin biyayya ga shari'ar ba"
Kalman nan "shari'an da kuma annabawa" na nufin bangaren litattafan da Musa da kuma annabawa sun rubuta cikin litattafan Yahudawa. Bulus ya bayyana su anan kamar su mutane ne da ke shaida a kotu. AT: Abinda Musa da Annabawa sun rubuta ta tabbatar da wannan"
A nan "adalci" na nufin daidaitawa ga Allah. AT: "daidaitawa ga Allah na kai ga dogara ga Yesu Almasihu"
Bulus na nufin cewa Allah ya karɓi kowa ta hanya ɗaya. AT: "Babu wata bambanci tsakanin Yahudawa da Al'ummai"
A nan "darajar Allah" na nufin siffar Allah da kuma dabi'ar sa. AT: "sun ƙãsa zama kamar Allah"
Anan "baratar" na nufin daidaitawa da Allah. AT: "Allah ya yi musu kyautar daidaitasu da kansa, domin Almasihu Yesu ya yantar da su"
Wannan na nufin cewa an daidaita su ba tare da sun tãrã ko kuma sun cancanci a daidaita su ba. A kyauta Allah ya daidaita su. AT: "an daidaita su ga Allah ba tare da sun samu ita ba"
Wannan na nufin mutuwar Yesu hadaya ce domin zunubai. AT: "cikin mutuwarsa hadaya ce domin zunubai"
Ma'ana mai iya yiwuwa na kamar haka 1) ƙyale ko 2) yafewa.
"Ya yi wannan ne don ya nuna yadda Allah yana daidaita mutane da kansa"
"Ta haka ya nuna cewa shi mai hukunci ne da kuma mai ce da kowane mai bada gaskiya ga Yesu, mai adalci"
Bulus ya yi wannan tambaya don ya nuna cewa babu wata dalilin da mutane za su yi fahariya game da biyayyarsu ga shari'ar. AT: "Saboda haka babu wata hanyar cewa Allah ya yi mana alheri don mun yi biyayya ga shari'ar. An fid the fahariya"
Bulus ya yi tambaya ya kuma bada amsa tambayar don nanata cewa duk abin nan da ya faɗa haƙika gaskiya ne. Kuna iya juya wannan har da kalmomin da Bulus ke nufi. AT: "A kan wace dalili za mu fid da fahariya? shine mu fid da fahariay saboda kyawawan ayyuka? A'a, ko dai, mu fid da ita saboda bangaskiya"
A nan "bangaskiya" na nufin bada gaskiyar mutumin ga Allah. "mutum" anan na nufin kowane mutum. AT: "Allah na daidata kowane mutum mai gaskantawa ga Allah" ko "Sa'ada Allah ya daidaita mutum, ya yi wannan ne domin mutumin ya gaskanta ga Allah"
"ko bai yi ayyukan shari'ar ba"
Bulus ya yi wannan tambaya don ya nanatawa ne. AT: "Haƙika ku da ku ke Yahudawa kada ku yi tunanin cewa ku kadai ne Allah zai karɓe ku!"
Bulus ya yi wannan tambayar don nanata abin da yake ƙoƙorin faɗa. AT: "Zai karbi waɗanda ba Yahudawa ba, wato Al'ummai"
A nan "masu kaciya" na nufin Yahudawa, "marasa kaciya" kuwa na nufin waɗanda ba Yahudawa ba. AT: "Allah zai daidaita Yahudawa duk da waɗanda ba Yahudawa ba ga kansa ta wurin bangaskiyarsu cikin Almasihu"
Bulus ya yi tambayar da yana iya yiwuwa wani mai karatu yana da shi. AT: "wani na iya cewa za mu iya kawar da shari'ar don muna da bangaskiya."
"muna biyayya ga shari'ar"
Wannan na nufin Bulus, sauran masubi, da masu karatu.
Daga farko dukka abubuwan masu amfani na bayahude shine an danƙa masu da bayyanuwa na Allah.
Ko da shike kowane mutum mai karya ne, an sami cewa Allah mai gaskiya ne.
Domin Allah mai adalci ne, ya na iya hukunta duniya.
Hukunci yana zuwa a kan wadanda suke cewa, '''mu yi mugunta , domin idan mai yiwuwa ne adalci ya zo''.
Yana rubuce cewa babu kowane da ya ke da adalci , ko daya.
Bisa ga abin da ya ke a rubuce, ba wanda ya gane ya kuma nemi Allah.
Babu wani da za a wajaba ta wurin ayukkan doka.
Sanin zunubi yana zuwa ta wurin doka.
Ta wurin saidun doka da kuma annabawa na da adalci ba tare da sa sanin doka yanzu ba.
Adalci mara doka itace adalci na Allah ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Almasihu domin dukkan wadanda suka yi ĩmanĩ.
Mutum ya kan sami adalci a kyauta a gaban Allah ta wurin fansa da ya ke cikin Almasihu Yesu
Allah ya yi tanadin Almasihu Yesu domin gafara ta wurin bangaskiya a cikin jininsa.
Allah ya nuna cewa shine wanda ya ke wajaba kowa domin bangaskiya a cikin Yesu.
Mutum ya kan sami barata ta wurin bangaskiya ne ba tare da ayukkan doka ba.
Allah ya na wajaba su dukka ta wurin bangaskiya.
Muna inganta doka ta wurin bangaskiya.
1 Me kenan zamu ce game da Ibrahim, kakanmu a jiki, me ya samu? 2 Domin idan Ibrahim ya sami kubutarwa ta wurin ayuka, ai da ya sami dalilin fahariya, amma ba a gaban Allah ba. 3 Kuma fa me nassi ke fadi? "Ibrahim ya bada gaskiya ga Allah, sai aka lisafta ta adalci gare shi." 4 Yanzu fa shi dake yin ayyuka, ladansa ba a lisafta shi alheri ba ne, amma abun da ke nasa. 5 Amma kuma shi da bai da ayyuka kuma maimakon haka ya gaskanta ga wanda ke kubutar da masu zunubai, bangaskiyarsa an lisafta ta a misalin adalci. 6 Dauda ya yi furcin albarka bisa mutumin da Allah ya lisafta mai adalci da rashin ayyuka. 7 Sai ya ce, "Masu albarka ne wadanda aka yafe laifofinsu, kuma wadanda zunubansu a rufe suke. 8 Mai albarka ne mutumin da ko kadan Ubangiji ba zaya lisafta zunubin sa ba." 9 To albarkar da aka fadi ko a bisansu wadanda aka yi wa kaciya ne kadai, ko kuwa a bisan su ma marasa kaciya? Domin mun yi furcin, "Bangaskiyar Ibrahim an lisafta ta adalci ce agare shi." 10 Yaya aka lisafta ta? Bayan Ibrahim ya yi kaciya, ko kuwa a rashin kaciya? Ba a cikin kaciya ba, amma a rashin kaciya. 11 Ibrahim ya amshi alamar kaciya. Wannan shi ne hatimin adalcin bangaskiyar da ya ke da ita tun cikin rashin kaciyarsa. Albarkacin wannan alama ce, ta sa shi ya zama uban dukkan wadanda suka badagaskiya, ko da shike ba su da kaciya. Wato ma'ana, adalci za a lisafta masu. 12 Wannan kuma yana da ma'anar cewa Ibrahim ya zama uban kaciya ga wadanda suka fito ba domin masu kaciya kadai ba, amma kuma domin wadanda ke biyo matakin ubanmu Ibrahim. Kuma wannan itace bangaskiyar da ya ke da ita a rashin kaciya. 13 Domin ba ta wurin shari'a aka bada alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim da zuriyarsa ba, wannan alkawarin da ya ce zasu gaji duniya. Maimako, a ta wurin adalcin bangaskiya ne. 14 Domin idan su da ke na shari'a magada ne, bangaskiya bata da komai, kuma alkawarin an wofintar da shi kenan. 15 Domin shari'a ta kan jawo fushi, amma ta wurin rashin shari'a, babu karya umarni. 16 Saboda wannan dalili haka ta faru ta wurin bangaskiya, domin ya zama bisa ga alheri. Kamar haka, alkawarin ya tabbata ga dukkan zuriya. Kuma wannan zuriya ba zata kunshi wadanda suke da sanin shari'a ba kadai, har ma da wadanda ke daga bangaskiyar Ibrahim. Saboda shi ne uban dukkan kowa, 17 kamar yadda aka rubuta, "Na maishe ka uba ga kasashe masu yawa." Ibrahim na gaban aminin sa, wato, Allah, mai bada rai ga mattatu kuma ya kan kira abubuwan da basu da rai su kuma kasance. 18 Duk da halin da ke a bayyane, Ibrahim ya gaskata ga Allah kai tsaye game da abubuwan da ke nan gaba. Sai ya zama uba ga kasashe masu yawa, kamar yadda aka ambata, "... Haka zuriyarka zata kasance." 19 Ba ya karaya a bangaskiya ba. Ibrahim ya yarda da cewa jikinsa ya rigaya ya tsufa (shekarun sa na misalin dari). Ya kuma yarda da cewa mahaifar Saratu bata iya bada 'ya'ya ba. 20 Amma domin alkawarin Allah, Ibrahim bai ji nauyin rashin bangaskiya ba. Maimakon haka, ya sami karfafawa a bangaskiyarsa sai ya daukaka Allah. 21 Ya na da cikakkiyar gamsuwa cewa idan Allah ya yi alkawari, shi mai iya kammalawa ne. 22 Haka nan ne kuma aka lisafta masa wannan a matsayin adalci. 23 To ba'a rubuta kawai damin amfaninsa kadai ba, da aka lisafta dominsa. 24 A rubuce yake domin mu, domin wadanda za'a lisafta su, mu da muka bada gaskiya gare shi wanda ya tada Yesu Ubangijinmu daga matattu. 25 Wannan shi ne wanda aka bashe shi domin zunubanmu kuma an tada shi saboda fasar mu.
Bulus ya tabbatar da cewa ko a zamanin dã an daidaita masubi da Allah ta wurin bangaskiya ba ta wurin shari'ar ba.
Bulus ya yi amfani da tambayan don ya kama hankalin masu karatunsa ya kuma fara magana game da wani abu sabo. AT: "Wannan shine abin da Ibrahim kakan kakaninmu na jiki ya samu"
Bulus ya yi amfani da wannan tambayar domin ya kara nanatawa. Ya yi maganar littafin kamar tana da rai kuma ta iya magana. AT: "Gama za mu iya karantawa cikin littafin"
AT: Allah ya dubi Ibrahim a matsayin mutum mai adalci"
AT: "babu wanda ke lisafta abin da mai daukan aiki ya biya shi a matsayin kyauta daga mai ɗaukan aiki"
AT: "amma abin yake bin mai ɗaukan sa aiki"
"ga Allah, wanda ke daidaita"
AT: "Allah ya dubi bangakiyar mutumin a misalin adalci" ko "Allah ya dubi adalcin mutumin saboda bangaskiyar sa"
Dauda kuwa ya rubuta game da albarkan Allah ga mutumin da Allah ya mai da shi adali ba tare da ayyuka ba"
An bayyan abu ɗaya ta hanyoyi uku dabam dabam. AT: "Ubangijin ya yafe waɗanda sun karye shari'ar ... waɗanda zunubansu Ubangiji ya rufe ... waɗanda zunubansu Ubangiji ba zai lisafta ba"
Wannan furucin ta bayyana cikin sifar tambaya don kara nanaci. AT: Shin, Allah ya albarkaci masu kaciya ne kawai, ko kuwa da waɗanda ma ba su yi kaciya ba?"
Wannan na nufin mutanen Yahudawa. AT: "Yahudawa"
Wannan na nufin mutane wanda ba Yahudawa ba. AT: "Al'ummai"
AT: "Allah ya dubi bangaskiya Ibrahim a matsayin adalci"
Bulus ya yi wannan tambayoyi don ya kara nanata maganarsa. AT: "Yaushe Allah ya dubi Ibrahim a matsayin mai adalci? Shin, kafin kaciyar sa ne, ko kuwa bayan kaciyar?"
Ta faru ne kafin a yi masa kaciya, ba bayan kaciyarsa ba"
A nan "adalcin bangaskiya" na nufin cewa Allah ya dubi shi a matsayi mai adalci. AT: "alama da za a iya ganin cewa Allah ya dubi shi a matsayin mai adalci saboda ya riga ya gaskanta ga Allah tun kafin a yi mada kaciya"
"ko ba a yi musu kaciya ba"
AT: "Wannan na nufin cewa Allah zai dube su a matsayin masu adalci"
A nan "kaciyan" na nufin masu gaskantawa da Allah na gaske, duk da Yahudawa da Al'ummai.
A nan "bin cikin matakin bangaskiyar" na nufin bin gurbin wani. AT: "wanda sun bi gurbin bangaskiyar ubanmu Ibrahim"
an yi magana game da mutanen da Allah ya yi masu alkawari sai ka ce za su gaji kaya da arziki daga wani daga cikin iyali.
Kalmomin nan "alkawaein ta zo" an fahimci su daga maganar fari ne. za ku iya juya wannan ta wurin kara waɗannan kalmomin da ke nufin abu kamar haka. AT: "amma alkawarin ta zo ne tawurin bangaskiya, wadda Allah ya dubi a matsayin adalcin"
A nan "rayuwa ta wurin shari'ar" na nufin biyayya ga shari'ar. AT: "idan waɗanda ke biyayya ga shari'ar ne za su gaji duniya"
"bangaskiya ba ta da daraja, kuma alkawarin bata da ma'ana"
Ana iya bayyana wannan in an cire sunan nan "karya umarnin." AT: "ba bu wanda ya isa ya ketare shari'ar" ko "ba shi yiwuwa a ketare shari'ar"
"don haka"
Kalman nan "shi" na nufin samun abin da Allah ya alkawarta. AT: "ta wurin bangaskiya ne muka sami alkawarin" ko "mun sami alkawarin ta wurin bangaskiya"
A nan "alkawarin zai zama bisa ga alheri" na wakilcin cewa Allah ya da da abin da ya alkawarta saboda alherinsa. AT: "domin abin da ya alkawarta ya zama kyauta" ko "don alkawarinsa ya zama saboda alherinsa"
AT: "dukkan zuriyar Ibrahim haƙika za su ƙarbi abin da Allah ya alkawarta zai bayar"
Wannan na nufin mutanen Yahudawan, wanda takalifin yin biyayya ga dokar Musa.
Wannan na nufin waɗanda suke da bangaskiya kamar Ibrahim kafin ya yi kaciya. AT: "waɗanda suka bada gaskiya kamar yadda Ibrahim ya yi"
A nan kalman nan "mu" na nufin Bulus da kuma dukkan Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba da suka gaskanta da Almasihu. Ga jiki Ibrahim kakan mutanen Yahudawa ne, amma shi kuma uban waɗanda ke da bangaskiya ne cikin ruhaniya.
Ana iya bayyana inda aka rubuta. AT: "kamar yadda aka rubuta cikin nasin"
A nan kalman nan "ka" mufuradi ne kuma na nufin Ibrahim.
Anan "ga shi wanda ya dogara" na nufin Allah. AT: "Ibrahim na gaban Allah wanda ya dogara a gare shi, wato shi wanda ya ba da rai ga waɗanda suka mutu"
"daga ba komai ya halici kowane abu"
Wannan karin maganan na nufin cewa Ibrahim ya dogara ga Allah kodashike bai nuna masa cewa zai iya samu ɗa ba. AT: Kodashike ba zama mai yiwuwa a gare shi ya samu zuriya ba, amma ya gaskanta da Allah"
AT: "kamar yadda Allah ya ce wa Ibrahim"
Ana iya bayyana cikakken alkawarin da Allah ya ba wa Ibrahim. AT: "za ka kasance da zuriya da ba za ka iya kidaya ba"
AT: "Ya kasance da ƙarfi cikin bangaskiyar sa, kodashiƙe"
Ku na iya juya wannan cikin tabbatacciya sifa. AT: "cigaba da aiki cikin bangaskiya"
AT: "ya kasance da ƙarfi cikin bangaskiyarsa"
"Ibrahim ya tabbata"
"Allah zai iya yin"
AT: "Saboda haka Allah ya lisafta bangasikiya Ibrahim a matsayin adalci" ko "Saboda haka Allah ya dubi adalcin Ibrahim don Ibrahim ya bada gaskiya gare shi"
"yanzu" an yi amfani da ita anan don a haɗa daidaita Ibrahim da aka yi ta wurin bangasikiya da kuma daidaita masubi na yanzu ta wurin bangaskiya cikin mutuwa da tashin Almasihu.
"ga Ibrahim kaɗai"
AT: "da Allah ya lisafta masa adalci" ko "Allah ya dube shi a matsayin mai adalci"
Kalman nan "mu" na nufin Bulus tare da duk masubi cikin Almasihu.
AT: "don amfanin mu ne kuwa, domin Allah zai dube mu a matsayin masu adalci kuma inda mun bada gaskiya"
"Tashe ... daga mattattu" anan na nufin "sa wani ya rayu kuma." AT: "shi wanda ya sa Yesu Ubangijimu ya rayu kuma"
AT: wanda Allah ya bashe shi ga masu gãbã don zunubanmu da kuma wanda Allah ya rayar don ya daidaita mu da shi"
Ibrahim zai iya samin dalilin yin alfahari idan ya samu barata ta wurin ayukka.
Littafi ya ce Ibrahim ya yi ĩmanĩ da Allah , aka kuma lissafta masa kamar adalci.
Allah yana wajaba mugaye.
Bisa ga Dauda, mai albarka ne mutum da ya sami gafarar zunubai wanda kuma Ubangiji ba ya lissafta zunubansa.
An lissafta bangaskiyar Ibrahim kamar adalci kafin a yi masa kaciya.
Ibrahim Uba ne ga dukkan wanda suka yi ĩmanĩ, marasa kaciya da masu kaciya dukka.
An yi wa Ibrahim da zuriyar sa alkawari cewa za su zama magadan duniya.
Idan da alkawarin ya zo ta wurin doka ne, da bangaskiya ya zama fanko kuma alkawarin ya zama karya.
Ana bada alkawarin daga bangaskiya saboda ya zama daga alheri , saboda kuma ta zama tabbatacce.
Bulus ya ce Allah ya na ba da rai ga matattu ya kuma kira abubuwan da ba su da rai su kuma kasance.
Ibrahim ya amince da Allah bai kuma yi shakka da rashin yarda ba.
A lokacin da Allah ya yi wa Ibrahim alkawari, Ibrahim yana da shekaru dari a duniya kuma mahaifan Saratu ya riga ya mutu.
Ibrahim ya amince da Allah bai kuma yi shakka da rashin yarda ba.
An yi rubutun nan a kan Ibrahim domin amfanin sa, da kuma amfanin mu.
Mun yi ĩmanĩ Allah ya tashi Yesu da ga matattu, wanda aka mika shi domin zunuban mu aka kuma tayar da shi domin gaskatawan mu.
1 Tun da shike mun sami barata, sabili da bangaskiya, mun sami salama tare da Allah ta wurin Yesu Almasihu. 2 . Ta wurin sa kuma mun sami iso zuwa ga alheri inda muke tsayawa albarkacin bangaskiyarmu. Muna murna da gabagadin da Allah ya ba mu game da abin da zai faru, gabagadin da zamu dandana nan gaba cikin daukakar Allah. 3 Ba kuwa haka kadai ba, amma muna murna da shan wahalolinmu. Mun san cewa shan wuya na haifar da 4 Jimiri, Jimiri kuma na kawo amincewa, amincewa na kawo gabagadi game da abin da zai zo nan gaba. 5 Wannan gabagadi wato begen da muke da shi baya kunyatarwa, domin kuwa an kwarara mana kaunar Allah a cikin zuciyarmu ta wurin Ruhu Mai Tsarki, da aka ba mu. 6 Domin kuwa ko yayin da muke raunana, Almasihu ya mutu a lokacin da ke dai dai domin marasa ibada. 7 To ai kuwa yana da wuya kwarai wani mutum ya yarda ya mutu don mutumin kirki ma. Watakila, wani na iyayin kasada ya yarda ya mutu don nagarin mutum. 8 Amma Allah ya tabbatar mana da kaunarsa a gare mu, don kuwa tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu domin mu. 9 Balle ma yanzu, da muka barata ta wurin jininsa, za mu sami tsira daga fushin Allah. 10 Domin kuwa, in tun muna makiya, aka sulhunta mu da Allah ta wurin mutuwar Dansa, balle ma, yanzu da muka sami sulhu, zamu sami tsira ta wurin ransa. 11 Bama haka kadai ba, amma muna murna a cikin Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurinsa ne muka sami wannan sulhu. 12 Saboda haka, kamar yadda ta wurin mutum daya zunubi ya shigo cikin duniya, ta haka mutuwa ta shigo ta dalilin zunubi. 13 Domin kuwa tun kafin a bada shari'a, zunubi na nan a duniya, amma ba' a lissafin zunubi in da ba shari'a. 14 Duk da haka, mutuwa ta mallake tun daga Adamu har Musa, har ma wadanda basu yi zunubin keta umarni irin na Adamu ba, wanda yake misalin mai zuwan nan a gaba. 15 Amma kyautar ba kamar keta umarnin take ba. Domin in sabo da laifin mutum dayan nan ne, da yawa suke mutuwa, haka ma alherin sa da baiwarsa ta wurin mutum dayan nan, Yesu Almasihu, sai baiwar ta wadata zuwa ga masu yawa. 16 Domin kyautar ba kamar sakamakon wannan da yayi zunubin bace. Ta haka din nan ne, hukuncin nan mai tsanani ya zo sabo da zunubin mutum dayan. Har yanzu dai, wannan baiwa ta yanci ta zo ne bayan laifuffuka masu yawa. 17 Domin, idan sabo da laifin mutum dayan nan ne, mutuwa ta mallake, saboda dayan, haka ma wadanda suka karbi alheri mai yawa da kuma baiwar adalci ta wurin ran, Yesu Almasihu. 18 Don haka, kamar yadda zunubin dayan ya sa hukunci ya zo kan dukka, haka ma aikin adalci na dayan zai kawo barata da rai ga mutane masu yawa. 19 Kuma kamar yadda rashin biyayyar dayan ta sa mutane masu yawan gaske su zama masu zunubi, haka ma ta biyayyar dayan mutane da yawan gaske za su sami adalci. 20 Amma shari'a ta zo, inda ta sa zunubi ya habaka. Amma inda zunubi ya habaka, alheri ma ya habaka ribin ribi. 21 Wannan ya faru ne, don kamar yadda zunubi yai mallaka zuwa mutuwa, haka kuma alheri ya mallaka zuwa adalci da rai na har abada ta wurin Yesu Almasihu Ubangijin mu.
Bulus ya fara faɗin abubuwa dabam dabam da zai faru sa'adda Allah ya daidai masubi da kansa.
"domin an daidaita mu"
Duk aukuwar "mu" da "na mu" na nufin dukkan masubi kuma ya kamata a sanya su.
"saboda Ubangijinmu Yesu Almasihu"
A nan "Ubangiji" na nufin cewa Yesu Allah ne.
A nan "albarkacin bangaskiyar" na nufin dogarar mu ga Yesu, wanda ta yaddar mana mu tsaya a gaban Allah. AT: "Domin mun dogara ga Yesu, Allah ya ba mu yancin zuwa gabansa"
Kalman nan "wannan" na nufin ra'ayin da aka bayyana [Roman 5:1-2]
duk aukuwar "mu" na nufin dukkan masubi kuma ya kamata a haɗa su.
Wannan tabbatacin cewa Allah zai cika dukkan alkawaransa ga waɗanda suka dogara ga Almasihu.
Bulus ya yi magana game da "gabagadi" sai ka ce ta na da rai. AT: "muna da gabagadin cewa za mu ƙarbi abubuwan da muna jira"
A nan "zukatan" na a maɗaɗɗin tunanin mutum, ji, ko cikin mutum. Maganan na "an kwarara mana ƙaunar Allah a cikin zukatan mu" nufin ƙaunar Allah ga mutanen sa. AT: "domin ya ƙaunace mu sasai" ko "domin Allah ya nuna mana yadda yake ƙaunar mu"
Kalman nan "mu" anan na nufin dukkan masubi kuma ya kamata a haɗa su.
"yana da wuya a samu wani da zai yarda ya mutu ko saboda mutum mai adalci.
"Amma za a iya samun wani wanda zai yarda ya mutu saboda mutum nagari"
Za ku iya juya wannan aikataun jimlar da ta shige ta wurin yin amfani da "nuna."
Duk aukuwar "mu" na nufin dukkan masubi haɗe.
A nan "daidaitawa" na nufin cewa Allah ya sa mu cikin ɗanganta mai kyauda kansa. AT: "me kenan Allah zai yi mana yanzu da ya daidaita mu da kansa saboda mutuwar Yesu a kan giciye"
Wannan na nufin mutuwar haɗaya da Yesu ya yi a kan giciya.
Wannan na nufin cewa ta wurin mutuwar haɗayar da Yesu ya yi a kan giciye, Allah ya yafe mana mana ya kuma cece mu daga hukuncin nan ta jahannama domin zunubanmu.
A nan "fushi" na nufin hukunci Allah a kan waɗanda suka yi masa zunubi. AT: "hukuncin Allah"
Duk aukuwar "mu" na nufin dukkan masubi haɗe.
"Ɗan Allah ... ran Ɗan Allah"
Mutuwar Ɗan Allah ta ba mu rai madawwamiyar yafe ta kuma sa mu mun zama abokai da Allah, wato ga waɗanda suka bada gaskiya ga Yesu. AT: "Allah ya bar mu mu sami ɗangantaka ma salama da shi saboda ɗansa ya mutu domin mu"
Wannan lakani ne mai muhimmanci ta Yesu Ɗan Allah.
AT: "yanzu kam Allah ya maishe mu abokan sa kuma"
Bulus ya bayyana zunubi kamar wani abu ne mai hatsari da ta shigo cikin duniya ta wurin aikin "mutum ɗayan nan" wato Adamu. Wannan zunubi kuwa ta zama kofa wadda mutuwa, wadda ke nuna hoton wani abu kuma mai hatsari, ta shigo duniya.
Wannan na nufin cewa mutane su na zunubi tun kafin Allah ya bada shari'ar. AT: "Mutanen suna zunubi tun kafin Allah ya ba wa Musa shari'ar"
Wannan na nufin cewa Allah bai lisafta wa mutane zunubansu ba kafin a ba da shari'ar. AT: Amma Allah bai rubuta zunubi gaba da shari'ar ba kafin ya bada shari'ar"
"Ko da shiƙe abin nan da na faɗa gaskiya ne, mutu" ko kuma "Babu rubutacciyar shari'a tun daga loƙacin Adamu zuwa loƙacin Musa, amma mutuwa." (Dubi: [Romans 5:13])
Bulus yana magana game da mutuwa sai ka ce sarki ne da ke mulki. AT: "mutane sun cigaba da mutuwa tun loƙacin Adamu har zuwa loƙacin Musa a matsayi sakamakon zunubansu"
"har ma mutanen da zububansu dabam ne da na Adamu sun cigaba da mutuwa"
Adamu misalin Alamsihu ne wanda ya bayyana a gaba. Shi kusan iri ɗaya ne da shi.
Anan "ɗaya" na nufin Adamu. AT: "Domin in ta wurin zunubin mutun ɗayan nan da yawa su mutu"
A nan "alheri" na nufin kyatar Allah da ke samamme ga kowa ta wurin Yesu Almasihu. AT: "har ma ta wurin mutumin nan Yesu Almasihu, wanda ya mutu domin dukkan mu, Allah ya ba mu kyauta rai madawwani, ƙodashiƙe ba mu cancance ta ba"
A nan "kyautar" na nufin cewa Allah a yalwace ya shafe zunubanmu. AT: "Kyautar ba kamar sakamakon zunubin Adamu ba ne"
A nan Bulus ya bada dalilai biyu da "kyautar ba kamar sakamakon zunubi Adamu bane." "hukuncin halaka" na nufin cewa mun cancanci hukuncin Allah saboda zunubanmu. AT: "Domin a wannan bangare, Allah ya ce dukkan mutane sun cancanci hukunci saboda zunubin mutum ɗayan nan, amma a wata bangare dabam kuwa"
Wannan na nufin yadda Allah ya daidaita mu da kansa ko da shike ba mu cancanci a daidata mu ba. AT: "irin kyautar Allah don ya daidaita mu tare da kansa"
"bayan zunuban mutane dayawa"
Wannan na nufin zunubin Adamu.
A nan Bulus ya yi magana game da "mutuwa" kamar sarki ne wanda ke mulki. "Mulkin" mutuwa ta kan sa kowa ya mutu. AT: "kowa ya mutu"
"ta wurin zunubin nan ɗaya da Adamu ya aikata" ko kuwa "saboda zunubin Adamu"
A nan "hukunci" na nufin hukuncin Allah. AT: "dukan mutane sun cancanci hukuncin Allah saboda zunubi"
hadayan Yesu Almasihu
A nan "kuɓuta" na nufin cewa Allah zai iya daidaita mutane zuwa gare shi. AT: "Allah ya daidaita dukan mutane wa kansa"
rashin biyayyar Adamu
AT: "mutane da yawa sun yi zunubi"
biyayyar Yesu
AT: Allah zai daidaita mutane dayawa wa kansa"
Anan Bulus ya yi magana game da shari'ar sai ka ce mutum. AT: "Allah ya ba wa Musa shari'ar"
"zunubi ta karu"
A nan "alheri" na nufin albarkun Allah da ba a cancanci ta ba. AT: "Allah ya cigaba a yin kirki gare su, a ta hanyar da bai cancance su ba"
A nan Bulus ya yi magana game da mutuwa sai ka ce sarki ne da ke mulki. AT: "kamar yadda zunubi ta jawo mutuwa"
Bulus ya yi magana game da "alheri" anan sai ka ce wani sarkin ne da ke mulki. AT: "alheri ta ba wa mutane rai madawwami ta wurin adalcin Yesu Alamasihu Ubangijin mu"
Bulus ya yi magana game da "alheri" anan sai ka ce sarkin ne da ke mulki. Kalman nan "adalci" na nufin ikon Allah don daidaita mutane wa kansa. AT: "ha kama Allah zai ba da kyatar sa a yalwace ga mutane don ya daidaita su wa kansa"
Bulus ya haɗa da kansa, masu karatunsa, da dukkan masubi.
Domin an baratar da su zuwa ga bangaskiya, masubi suna da salama da Allah ta wurin Ubangiji Yesu Almasihu.
Wahala yana samar da jimiri, amincewa, da kuma amana.
Allah ya na tabbatar da kaunarsa zuwa gare mu, domin yayin da muke masu zunubi, Almasihu ya mutu domin mu.
A kasancewan gaskatawan mu daga jinin Almasihu, ma su bi suna samin ceto daga fushin Allah.
Marasa bi abokan gaba ne na Allah kafin su sami sulhu da Allah ta wurin Yesu.
Domin zunubin mutum daya, zunubi ya shigo duniya, mutuwa ya shigo ta wurin zunubi, mutuwa kuma ta bazu zuwa mutane duka.
Adamu ne wannan mutum daya wanda ta wurin sa zunubi ta shigo duniya.
Ta wurin zunubin Adamu dayawa sun mutu, amma ta wurin kyautar Allah dayawa sun yawaita.
Shari'ar hukunci ne sakamakon zunubin Adam, amma gaskatawa itace sakamakon kyautan Allah.
Mutuwa ta yi mulki sakamakon zunubin Adamu, wadanda kuma suka karba kyautar Allah sun yi mulki ta wurin rayuwan Yesu Almasihu.
Da yawa sun zama masu zunubi ta wurin rashin biyyayan Adamu, da yawa kuma za su sami adalci ta wurin biyayyan Almasihu.
Shari'a ta shigo tare domin mai yiwuwa laifi ya yawaita.
Alherin Allah ta yawaita fiye da laifi.
1 Me kuwa zamu ce yanzu? Sai mu ci gaba da yin zunubi domin Alheri ya yawaita? 2 Ba zai taba faruwa ba. 'Yaya za'ace mu da muka mutu cikin zunubi mu ci gaba da rayuwa cikin sa? 3 Ba ku san cewa duk wadanda aka yi masu baftisma cikin Almasihu Yesu an yi masu baftisma har ya zuwa mutuwarsa ne ba? 4 An kuwa binne mu tare da shi, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa. Haka kuma ya kasance ne domin kamar yadda Almasihu ya tashi daga matattu cikin daukakar Uba. Sakamakon haka muma zamu yi tafiya cikin sabuwar rayuwa. 5 Domin kuwa idan muna tare dashi cikin kamannin mutuwarsa zamu kuwa zauna tare dashi har ga kamannin tashinsa. 6 Mun kuma san cewa, an giciye wannan tsohon mutunmin nan namu tare dashi, domin a hallaka jikin zunubi. wanna kuwa ya kasance ne domin kada mu ci gaba da bautar zunubi. 7 Duk kuma wanda ya mutu an ambace shi a matayin adali akan zunubi. 8 Amma idan muka mutu tare da Almasihu, mun bada gaskiya zamu yi rayuwa tare dashi. 9 Muna da sanen cewa an tada Almasihu daga matattu, don haka kuwa ba matacce yake ba. Mutuwa kuma bata da iko a kansa. 10 Game da mutuwar da yayi ga zunubi yayi sau daya kuma domin dukka. Rayuwar da yake yi kuma yana yi wa Allah ne. 11 Don haka ku ma sai ku dauki kanku a matsayin matattu ga zunubi amma rayayyu ga Allah cikin Almasihu Yesu. 12 Sabili da haka kada ku bar zunubi yayi mulki a cikin jikinku, har ku yi biyayya ga sha'awarsa. 13 Kada ku mika gabobin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin rashin adalci. Amma ku mika kanku ga Allah rayayyu daga mutuwa. Ku kuma mika gabobin jikinku ga Allah a matsayin kayan aiki na adalci. 14 kada ku ba zunubi dama yayi mulki a kanku, domin ba karkashin doka kuke ba, amma karkashin alheri kuke. 15 To sai me? Sai mu yi zunubi wai don ba a karkashin doka muke ba amma alheri. ba zai taba faruwa ba. 16 Ba ku san cewa duk ga wanda kuka mika kanku a matsayin bayi, a gareshi ku bayi ne ba? Wannan fa gaskiya ne, ko dai ku bayi ne ga zunubi wanda kaiwa ga mutuwa ko kuma bayi ga biyayya wanda ke kaiwa ga adalci. 17 Amma godiya ta tabbata ga Allah! domin da ku bayin zunubi ne, amma kun yi biyayya daga zuciyarku irin salon koyarwar da aka baku. 18 An 'yantar daku daga bautar zunubi, an kuma maishe ku bayin adalci. 19 Ina magana da ku kamar mutum, domin kasawarku ta nama da jini. Kamar yadda kuka mika gabobin jikinku ga kazamta da miyagun ayyuka, haka ma yanzu ku mika gabobin jikinku a matsayin bayi na adalci. 20 Domin a lokacin da kuke bayin zunubi, ku yantattu ne ga adalci. 21 A wannan lokacin wanne amfani kuka samu na ayyukan da yanzu kuke jin kunyarsu? Domin kuwa sakamakon wadannan ayyuka shine mutuwa. 22 Amma yanzu da da aka yantar daku daga zunubi aka mai da ku bayin Allah, amfaninsa ku kuwa shine tsarkakewarku. Sakamakon kuwa shine rai na har abada. 23 Don kuwa sakamakon zunubi mutuwa ne. Amma kyautar Allah itace rai madauwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.
A karkashin alheri, Bulus ya faɗa wa waɗanda suka gaskanta da Yesu cewa su yi sabon rayuwa kamar su mattattu ne ga zunubi da kuma rayayyu ne ga Allah.
Bulus ya yi waɗannan tambayoyi nan don ya jawo hankalin masu karatunsa ne. AT: "To, me za mu ce game da duk wannan? Haƙika ba za mu cigaba da yin zunubi ba wai don Allherin Allah ya yawaita ba!
kalman nan "mu" na nufin Bulus, masu karatun sa da sauran mutane.
A nan "mutu cikn zunubi" na nufin cewa masubi Yesu su na kamar mattattun mutane ne wanda zunubi ba za ta iya shafe su ba. Bulus ya yi amfani da wannan tambayar don nanaci ne. AT: "Muna kamar mutanen da zunubi ba ta shafe su ba! Don haka ba za mu cigaba da zunubi ba!"
Bulus ya yi amfani da wannan tambaya don ya kara nanaci. AT: "Tuna fa, a sa'adda an yi mana baftisma don a nuna cewa muna da ɗangantaka da Almasihu, wannan kuma na nuna cewa mun mutu tare da Almasihu a kan giciye!"
Anan Bulus ya yi magana game da baftimar masubi sai ka ce mutuwa ne da kuma biso. AT: "A sa'adda aka yi mana baftisma, ya na nan kamar an binne mu ne cikin kabari tare da Almasihu"
A ta da wani daga matattu na nufin a sa wani ya sake rayuwa kuma. Wannan na kwatanta sabuwar rayuwar ruhaniya na masubi da dawowar Yesu da rai kuma cikin jiki. Sabuwar rayuwa ta ruhaniya na masubi na ba mutumin ikon yin biyayya ga Allah. AT: "kamar yadda Uban ya tashe shi da matattu bayan mutuwarsa, mu ma mun sami sabuwan rayuwa ta ruhaniya mu kuma yi biyayya ga Allah"
Daga cikin dukan waɗanda suka mutu. Wannan maganar ta bayyana dukan mutanen da suka mutu tare da karkashi duniya. A tashe mutum daga cikin su na magana ne game da sake rayuwa kuma.
Bulus ya kwatanta haɗa mu da aka yi da Almasihu da mutuwa. Waɗanda suna tare da Almasihu cikin mutuwar sa za su kuwa tashi tare da shi. AT: "mutu tare da shi...dawo da rai tare da shi"
"tsohon mutumin" na nufin mutumin kafin ya ba da gaskiya ga Yesu. Bulus ya bayyana tsohon mutumin nan na mu mai zunubi kamar mutuwa kan giciye tare da Yesu a sa'adda muka bada gaskiya ga Yesu. AT: "mutumin nan namu mai zunubi ya mutu kan giciye tare da Yesu"
Wannan na nufin mutumin nan na da, amma yanzu kam ba ya a raye.
Wannan na nufin gabadayan mai zunubi. AT: "halin mu na zunubi"
AT: "zai mutu"
AT: "kada zunubi ta mashe mu bawan ta" ko "kada mu zama bayi ga zunubi"
A nan "adali" na nufin ikon Allah ya daidaita mutane wa kansa. AT: "A sa'adda Allah ya daidaita mutum wa kansa. wannan mutumin zunubi ba ta shugabantan sa"
A nan "mutu" na nufin cewa zunubi ba ta shugabantan masubi.
A nan a tashe, na nufin a sa wani wanda ya mutu ya rayu kuma. AT: "mun sani da cewa tun da shiƙe Allah ya dawo da Almasihu da rai kuma bayan ya mutu"
A nan "mutuwa" an bayyanata kamar sarki ko mai mulki da ke da iko bisa mutane. AT: "ba Zai sake mututwa ba" Dubi:
Maganar "sau ɗaya domin dukka" na nufin a gama wani abu gabaɗaya.Ku na yi bayyan ma'anar wannan a juyin ku. AT: "Gama a sa'adda ya mutu, ya ƙarye ikon zunubi gabaɗaya"
"Saboda wannan dalili ku dauke"
"yi tunanin kanku kamar" ko kuwa "dubi kanku kamar"
Kamar yadda ba za a yi sa gawa dole ya yi wani abu ba, zunubi ba ta da ikon sa masubi su yi rashin biyayya ga Allah. AT: "sai ka ce kun mutu ga ikon zunubi"
mutu ga iƙon zunubi, amma rayayyu don girmama Allah"
"rayu don girmama Allah ta wurin iƙon da Almasihu Yesu ya ba ku"
Bulus ya yi magana game da zunubin da mutane ke yi sai ka ce zunubi maigida ko sarki ne da ke mulkin su. AT: "Kada ku bar sha'awace sha'awace ta zunubi ta yi mulkin ku"
Wannan magana na nufin gabobin jikunan mutum, wanda zai mutu. AT: "ku"
Bulus ya yi magana game da muguwar sha'awace sha'awacen mutum sai ka ce zunubi maigida ne da ke da muguwar sha'awace sha'awace
Hoton mai zunubi ne da ke miƙa "gabobin jikinsa" ga maigidansa ko sarki. "gabobin jiki" na nufin gabadiyar mutum. AT: "Kada ku miƙa kanku ga zunubi don yi abin da ba daidai ba"
A nan "rayayyu" na nufin sabon rai ta ruhaniyan masubi. AT: "Amma ku miƙa kanku ga Allah, domin ya ba ku sabon rayuwa ta ruhaniya" ko kuwa "Amma ku miƙa kanku ga Allah kamar waɗanda suka mutu amma yanzu su na raye"
A nan "gabobin jiki" na nufin gabaɗayan mutum. AT: "bari Allah ya yi amfani da ku don jin daɗin ran sa"
Bulus ya yi magana game da "zunubi" anan sai ka ce sarkin ne da ke mulki bisa mutane. AT: "Kada ku bar sha'awace sha'awace ta zunubi ta bi da ku ci abin da kuke yi" ko kuwa "Kada ku bar kanku ku yi mugayen abubuwan da kuke so ku yi"
Zama "ƙarƙashin shari'ar" na nufin miƙa kai ga matuƙa da rashin ƙarfin ta. Kuna iya bayyana ma'ana wannan a juyinku. AT: "Gama ba a ɗaure ku ga shari'ar Musa ba wanda ba ta iya ba ku iƙon barin zunubi ba"
Zama "ƙarkashin alheri" na nufin kyautar Allah ta ba ku iƙon barin yin zunubi. Kuna iya bayyana ma'anar wannan a juyin ku. AT: "amma kuna ɗaure bisa alherin Allah wanda ke ba ku iƙon barin zunubi"
Bulus yana amfani da tambaya don ya nanata cewa rayuwa ƙarƙashin alheri dalilin zunubi ba ne. AT: "Duk da haka, ba domin muna ɗaure ga alherin maimakon shari'ar Musa sai ya zama cewa an ce mu yi zunubi ba"
"Ba za mu taba so hakan ya faru ba" ko "Ina roƙon Allah ya taimake ni kada in aikata wannan! "Wannan magana na nuna muradi ta musamman cewa wannan bai faru ba. Yana iya yiwuwa ku na da magana makamancin haka a harshen ku da za ku iya amfani da ita anan. Dubi yadda ku ka juya wannan cikin [Romawa 3:31].
Bulus ya yi amfani da wannan tambayar da on ya kwaɓe du wanda zai iya tunanin cewa Allah ya ba da alherinsa ta zama dalilin yi zunibi. AT: "Ku sani cewa ku bayi ne ga maigidan da kun zaɓa ku yi wa biyayya!"
A nan, Bulus ya yi magana game da "zunubi" da kuma "biyayya" sai ka ce su iyayengiji ne da bayi za su yi masu biyayya. AT: "ko dai ku kamar bayi ne ga zunubi ... ko kuwa kamar bayi ne ga biyayya" ko kuwa "ko dai ku bayi ne ga zunubi ... ko ku bayi ne ga biyayya"
"wanda sakamakon ta mutuwa ... wanda sakamakon ta adalci ne"
"Amma na gode wa Allah!"
Bayin zunubi na nufin samu sha'awar mai ƙarfi ta yi zunubi da ka kasa hana kanka yin zunubi. Yana nan ne kamar zunubi ne ke mulkin mutumin. AT: "kuna kamar bayin zunubi ne" ko kuwa "zunubi ne ke mulkin ku"
A nan kalman nan "zuciya" na nufin muradi yin abu daga sahili ko kuwa muradi na gaskiya. AT: "Amma kun yi biyayya da gaske"
A nan "salo" na nufin wata hanyar rayuwa da ke kai ga adalci. Masubin sun canza tsohon hanyar rayuwa don ya yi daidai da wannan sabon hanyar rayuwar da shugabanen masubi sun ƙoya masu. AT: "ƙoyarwar da shugabanen masubi sun ba su"
AT: "Almasihu ya 'yantar da ku daga zunubi"
Bayin adalci na nufin samun sha'awa mai ƙarfi don yi abin da ke daidai. Wato sai kace adalci na mulkin mutumin. AT: "an maishe ku kamar bayin adalci" ko "adalci ne ke mulkin ku yanzu"
Bulus mai yiwuwa na tsamanin cewa masu karatunsa su na mãmãki, me ya sa Bulus na magana game da 'yanci da kuma zama bawa. Anan yana cewa ya na amfani da waɗannan ra'ayin daga rayuwar su ta kowace rana don ya taimake su su fahimci cewa zunubi ko adalci na mulkin mutane. AT: "Ina magana game da wannan cikin kalmomin mutane" ko "Ina amfani da misalin rayuwar kowace rana"
Sau da yawa Bulus ya yi amfani da kalma nan "jiki" kamar kishiyar "ruhu". AT: "domin ba ku fahimci gabaɗayan abubuwan ruhaniya ba"
A nan "gabobin jiki" na nufin gabaɗayan mutum. AT: "miƙa kan ku a matsayin bayi ga kowace abu da ke miyagu kuma ba ta faranta wa Allah rai"
A nan "gabobin jiki" na nufin gabadayan mutum. AT: "miƙa kanku a matsayin bayi ga abin da ke daidai a gaban Allah don ya keɓe ku ya kuma ba ku iƙon bauta masa"
A nan "yantattu ne ga adalci" na nufin ba abin da ya haɗa ku da adalci. Mutanen su rayuwa kamar ba abin da ya haɗa su da abin da ke daidai. AT: "Wato kamar dã ku 'yantattu ne ga adalci" ko "ku na yi kamar ba lallai ne ku yi abinda da ke daidai ba" ko
"amfani" na nufin "sakamako" ko "abin da ya fito." Bulus ya yi wannan tambayar don ya nanata cewa sakamakon zunubi ba abu mai kyau ba ne. AT: "Babu abu mai kyau da ta zo daga waɗannan abubuwan da ke sa ku kunya yanzu" ko "Ba ku sami kome ba ta wurin aikata waɗannan abubuwan nan da ke sa ku kunya yanzu"
AT: "Amma yanzu da ku 'yantattu ne daga zunubi kun kuma zama bayin Allah" ko "Amman yanzu da Allah ya 'yantar da ku daga zunubi ya kuma maishe ku bayinsa"
Zaman "'yantattu daga zunubi" na nufin ikon ta rashin yin zunubi. AT: "Amma yanzu da Allah ya ba ku iƙon rashin yin zunubi"
Zaman "mai da ku bayin" ga Allah na nufin iƙon bauta da kuma biyayya ga Allah. AT: "Allah ya ba ku iƙon bauta masa"
A nan "amfani" na nufin "sakamako" ko kuwa "amfani." AT: "amfaninsa kuwa ita ce tsarkakewarku" ko "amfaninsa kuwa shine ku yi rayuwar tsarki"
"Sakamakon duk wannan ita ce za ku yi rayuwa har abada tare da Allah"
Kalman nan "haki" na nufin ladan aikin da aka ba wa wabi don aikin su. "Gama in kun bautawa zunubi, za ku karɓi mutuwar ruhaniya a matsayin lada" ko "Gama in kun cigaba da yin zunubi, Allah zai hukunta ku da mutuwar ruhaniya"
"amma Allah ya bada rai madawwamin ga waɗanda ke na Almasihu Yesu Ubangijinmu"
Ka da shi yiwu ya taba zama haka.
Masu bi ya kamata su yi tafiya a cikin sabon rayuwa.
Masubi suke haɗaɗɗe da Almasihu a cikin mutuwarsa da kuma tashin sa daga matattu.
An giciye tsohon mutumin mu da Almasihu, saboda mu dena zaman bayin zunubi.
Mun sani cewa mutuwa ta dena mulkin Almasihu domin an tayar da Almasihu daga matattu.
Almasihu ya mutu sau daya ga mutuwa domin dukkan mutane.
Mai bi yana yin rayuwarsa domin Allah.
Mai bi ya kamata ya yi tunanin kansa kamar matacce ga zunubi.
Mai bi ya kamata ya mika jikinsa zuwa ga Allah kamar kayan aikin adalci.
Mai bi yana rayuwa a karkashin alheri, wanda ya ke yarda masa ya yi mulkin zunubi.
karshen sakamakon mutum mai mai da kansa bawan zunubi itace mutuwa.
Karshen sakamakon mutum da ya ke mai da kansa bawan Allah itace adalci.
Karshen sakamakon mutum da ya ke mai da kansa bawan Allah itace adalci.
Karshen sakamakon mutum da ya ke mai da kansa bawan Allah itace adalci.
karshen sakamakon mutum mai mai da kansa bawan zunubi itace mutuwa.
Bayin Allah suna samin 'ya'yan su domin tsarkakewa.
Kyautar Allah itace rai na har abada.
Hakkin zunubi shine mutuwa.
1 'Yan'uwa, ko baku sani ba (domin ina magana da wadanda suka san shari'a), cewar shari'a na mulkin mutum muddin ransa? 2 Domin ta wurin shari'a matar aure a daure take muddin mijinta nada rai, amma idan mijinta ya mutu, ta kubuta daga shari'ar aure. 3 To don haka idan, mijinta na da rai, sai ta tafi ta zauna da wani mutumin, za'a kirata mazinaciya. Amma idan mijin ya mutu, "yantarciya ce daga shari'a, domin kada ta kasance mazinaciya idan ta auri wani mutum. 4 Domin wannan, 'yan'uwana, ku ma an sa kun mutu ga shari'a ta wurin jikin Almasihu, saboda a hada ku aure da wani, wato, ga wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu haifawa Allah 'ya'ya. 5 Domin sa'adda muke cikin jiki, ana motsa dabi'armu ta zunubi dake cikin jikunan mu ta wurin shari'a domin mu haifi 'ya'ya zuwa mutuwa. 6 Amma yanzu an kubutar damu daga shari'a, mun mutu daga abin da ya daure mu, domin mu yi bauta cikin sabuntuwar Ruhu, ba cikin tsohon rubutun shari'a ba. 7 To me zamu ce kenan? ita shari'ar kanta zunubi ce? ba zai taba faruwa ba. Duk da haka. Idan ba ta wurin shari'a ba, ba zan taba sanin zunubi ba, in ba ta wurin shari'a ba. Ba zan taba kyashin abin wani ba, har sai da shari'a tace, "Kada kayi kyashi." 8 Amma zunubi, sai ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya jawo dukkan sha'awa dake cikina. Domin in da babu shari'a, zunubi matacce ne. 9 Ada na rayu sau daya ba tare da shari'a ba, amma da dokar ta zo, sai zunubi ya farfado, ni kuma na mutu. 10 Dokar wadda ta kamata ta kawo rai, sai na same ta matacciya. 11 Domin zunubin, ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya rude ni, kuma ta wurin dokar ya kashe ni. 12 Domin haka, shari'ar na da tsarki, dokar na da tsarki, adalci da kuma kyau. 13 To abu mai kyau ya zamar mani mutuwa kenan? ba zai taba zama haka ba. Amma zunubi, domin ya nuna shi zunubi ne ta wurin abin da ke mai kyau, sai ya kawo mutuwa a cikina. Wannan ya kasance haka ne domin ta wurin dokar, zunubi ya zama cikakken zunubi. 14 Domin mun san shari'a mai Ruhaniya ce, amma ni ina cikin jiki. An sai da ni karkashin bautar zunubi. 15 Domin ni ma ban fahimci abin da nake aikatawa ba. Domin abin da nake so in aikata, ba shi nake aikatawa ba, kuma abin da bana so, shi nake aikatawa. 16 Amma idan na aikata abin da bana so, na amince da shari'a kenan, cewar shari'a nada kyau. 17 Amma yanzu ba ni ke aikata abin ba, amma zunubi da ke zaune a cikina. 18 Domin na san a cikina, wato cikin jikina, babu wani abu mai kyau. Domin marmarin aikata abu mai kyau na tare da ni, amma ba ni iya aikatawa. 19 Domin abu mai kyau da na ke so in aikata bana iyawa, amma muguntar da ba na so ita na ke aikatawa. 20 To idan na yi abin da ba ni so in aikata, wato kenan ba ni bane ke aikatawa, amma zunubin da ke zaune a cikina. 21 Don haka, sai na iske, akwai ka'ida a cikina dake son aikata abu mai kyau, amma kuma ainihin mugunta na tare dani. 22 Domin a cikina ina murna da shari'ar Allah. 23 Amma ina ganin wasu ka'idoji daban a gabobin jikina, su na yaki da wannan sabuwar ka'idar da ke cikin tunanina, suna kuma sanya ni bauta ta wurin ka'idar zunubi wadda ke cikin gabobin jikina. 24 Ni wahalallen mutum ne! wa zai kubutar dani daga wannan jiki na mutuwa? 25 Amma godiya ga Allah ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Domin haka ni kaina a wannan hannu bisa ga tunani na ina bautawa shari'ar Allah. Duk da haka, ta wani gefen ina bautawa ka'idar zunubi da ke tare da jikina.
Bulus ya bayyana yadda shari'ar ke mulkin waɗanda ke rayuwa ƙarƙashi shari'ar.
Bulus ya yi wannan tambayar do ya ƙara nanaci. AT: "haƙika kun sani cewa dole ne mutane su yi biyayya ga shari'ar in dai suna raye"
A nan wannan na nufin masubi, duk tare da maza da mata.
Bulus ya bada misalin wannan a [Romawa 7:2-3]
A nan "ɗaura take ga mijinta bisa ga shari'ar" na nufin an gama mace da mijinta bisa ga dokar aure. AT: "bisa ga shari'a, macen da ta yi aure an gama ta da mijinta"
Wannan na nufin macen da ta yi aure.
AT: "Allah zai dube ta a matsayin mazinaciya" ko "mutane za kira ta mazinaciya"
A nan yanciya daga shari'ar na nufin ba lallai a yi biyayya ga shari'ar ba. Cikin wannan yanayi macen ba ta bukatan yin biyayya ga shari'ar da ta ce mata ma'aurata ba za su iya auran wani mutum ba. AT: "ba ta bukata ta yi biyayya ga shari'ar"
Ɗangantakan wannnan ta kai mu baya zuwa [Romawa 7:1]
AT: "ku kuma kun mutu ga shari'ar a don ta wurin Almasihu kun mutu a kan giciye"
"Tashe" a nan na nufin "a sa wani ya sake rayuwa kuma." AT: "ga shi wanda aka sa shi ya sake rayuwa kuma" ko "ga shi wanda Allah ya tashe shi daga matattu" ko "ga shi wanda Allah ya sa shi ya sake rayu kuma"
A nan "'ya'ya" na nufin ayyukan da ke faranta wa Allah rai. AT: "mu iya yin abubuwan da zasu faranta wa Allah"
A nan "'ya'ya" na nufin "sakamakon ayyukan wani" ko "abin da ta fito ta dalilin ayyukan." AT: "wanda ke kai ga mutuwa cikin ruhu" ko "sakamoko wanda ita ce mutuwar mu ta ruhaniya"
AT: "Allah ya kubutar da mu daga shari'ar"
Wannan na nufin Bulus da kuma masubi.
Wannan na nufin shari'ar. AT: "ga shari'ar da ta ɗaure mu"
Wannan na nufin shari'ar Musa. AT: "shari'ar Musa:
Bulus na gabatar da sabon kan magana ne.
"I mana, wannan ba gaskiya bane!" Wannan magana na bada amsar tambayar da ke baya. Mai yiwuwa kuna da magana makamancin haka a harshen ku da za ku iya amfani da ita anan. Dubi yadda ku ka juya wannan cikin [Romawa 9: 14]
Bulus ya kwatanta zunubi da mutumin da ya iya ƙwaiƙoyo
"sha'awa ta ta yin zunubi"
Wannan kalman na tare da sha'awar samun abin da ke na wasu mutane da kuma sha'awa ta sha'anin jiki da ba daidai ba.
"inda babu shari'ar, babu karya dokan saboda haka babu zunubi"
Wannan na nufin 1) "na gane cewa ina zunubi" ko 2) "ina da sha'awa mai karfi ta yi zunubi"
Bulus ya yi magana game da umurnin Allah sai ka ce ta na kai ga mutuwa cikin jiki. AT: "Allah ya ba ni dokar don in rayu, amma a maimakon haka ta kashe ni"
Kamar yadda take cikin [Romawa 7:7-8], Bulus na bayyana zunub kama mutum wanda zai iya yin abubuwa uku: ɗauki zarafi, ruɗe, da kuma kisa. AT: "Domin ina so in yi zunubi, na ruɗe kai na ta wurin yin tunanin cewa zan iya yin zunubi in kuma yi biyayya ga doƙar a loƙaci ɗaya, amma Allah ya hukunta ni saboda rashin biyayya ta ga doƙar ta wurin raba sakani na da shi"
Bulus ya kwatanta zunubi da mutumin da ke ƙwaiƙoyo. Dubi yadda kun juya wannan cikin [Romawa 7:8]
Bulus ya yi magana game da kayes da mai zunubi sai ka ce ta na kai ga mutuwa ta jiki. AT: "ta raba ni da Allah"
cikakke, babu zunubi
Bulus na gabatar da sabon kan magana ne.
Bulus ya yi amfani da tambaya don kara nanaci ne.
Wannan na nufin shari'ar Allah.
"sa ni in mutu"
Bulus na duban zunub kamar ita mutum ne da zai iya yin wani abu.
"raba ni da Allah"
"domin na yi rashin biyayya ga doƙar"
"ban da tabbacin dalilin da ya sa ina yi wasu abubuwan da nake yi"
"domin abin da na yi"
Kalmomin nan "ba shi nake aikatawa ba" na nanata cewa Bulus ba ya yi abin da yake so yayi a kai a kai kamar yadda ya ke so ko kuwa cewa yana aikata abin da ba ya so ya aikata sau da yawa"
kalmomin nan "na aikata" da ke nufin cewa ya cika yin abin ba ya so ya yi, nanaci ne cewa Bulus na aikata abinda ba ya so ya aikata sua da yawa. AT: "abubuwan da na san cewa ba su da kyau su ne abubuwan da na ke aikatawa wani loƙaci"
"amma dai, in na aikata"
"na san cewa shari'ar Allah na da kyau"
Bulus ya bayyana zunubi kamar abu mai rai ne da ke da iƙon shi zuciyar sa.
A nan "jiki" na nufin hali mutuntaka na zunubi. AT: "halin zunubi na"
"abubuwa masu kyau" ko kuwa "ayyuka masu kyau"
"muguwar abubuwa" ko kuwa "muguwar ayyuka"
Bulus ya yi magana game da "zunubi" sai ka ce ta na da rai kuma ta rayuwa cikin sa.
Bulus ya yi magana game da "mutunta" anan sai ka ce ta na da rai ta na kuma rayuwa cikin sa.
Wannan ruhu mutumin da ya dogara ga Almasihu ne da aka farkar.
"Ina yi aikata abin da tsohon hali ya faɗa mini in yi ne kadai, ba ga sabon rayuwa ta hanyar da Ruhun ya nuna mini ba"
Wannan sabon halin ruhaniya ne da ke raye.
Wannan tsohon hali ne. yadda mutane suke a sa'adda aka haife su.
"hali na ta zunubi"
Bulus ya yi amfani da tambaya don ya bayyana babbar shauƙinsa. In harshen ku na da wata hanyan nuna babbar shauƙin ta wurin amfani da maganar da ke nuna motsin rai ko kuwa tambaya, to yi amfani da ita anan. AT: "Ina so wani ya kubutar da ni daga ikon abin da jiki na ke sha'awar ta!"
"cece ni"
Wannan na nufin jikin nan mai mutuwa ta duniya.
Wannan ita ce amsar tambayar da ke cikin 7:24.
Tunani da kuma jiki an yi amfani da su anan do a nuna yadda aka kwatanta bautar shari'ar Allah ko kuwa ƙa'idar zunubi. Da tunanin ko iyawa, wani zai iya zaɓan faranta da yi wa Allah biyayya da kuma jikin ko halin mutuntaka a bauta wa zunubi. AT: "Tunani na ta zaɓa ta faranta wa Allah rai, amma jiki na ta zaɓa ta yi biyayya ga zunubi"
Doka ta kan kula da mututm har tsawon lokacin da ya ke raye.
Mace mai aure tana karkashin dokan aure har sai mijin ta ya mutu.
A lokacin da ta sami yanci daga dokan aure, mata za ta iya yin wani aure.
Ana mai da masubi matattu ga doka ta wurin jikin Almasihu.
Bayan da aka mai da su matattu ga doka, masu bi suna iya zama haɗadu da Almasihu.
Doka ta na sa a san menene zunubi.
A'a, doka ba zunubi ba ce.
Zunubi, ta wurin umarnin doka tana kawo sha'awar jiki a daga cikin kowani mutum.
Doka tana da tsarki, umarnin kuma tana da tsarki, adalci da kuma kyau.
Bulus ya ce zunubi, ta wurin doka, ya na kai ga mutuwa a cikinsa.
A lokacin da Bulus ya na yin abubwan da ba ya so ya yi, ya na amincewa da dokar cewa tana da kyau.
Zunubin da ke zama a cikin Bulus ke yin abaubuwan da shi baya so ya yi.
Abubuwa marasa kyau ke zama a cikin jikin Bulus.
Bulus ya sami ka'idodi in cikin shi da yake so su yi abun da ke mai daidai, amma mugunta zahiri na ckin shi.
Mutum na cikin jikin Bulus na murna a dokar Allah
Bulus ya yi wa Allah godiya ta wurin Yesu Almasihu don kubutarsa
1 Saboda haka babu kayarwa yanzu ga wadanda ke cikin Almasihu Yesu. 2 Domin ka'idar ruhun rai a cikin Almasihu Yesu ta maishe mu 'yanttatu daga ka'idar zunubi da mutuwa. 3 Saboda abin da shari'a bata iya aikatawa ba domin kasawa ta wurin jiki, Allah ya yi. Ya aiko da dansa a kamanin jiki mai zunubi domin ya zama hadaya domin zunubi, sai ya yi Allah wadai da zunubi a cikin jiki. 4 Ya yi haka domin bukatar shari'a ta sami cika a cikinmu, mu da muke tafe ba ta gwargwadon jiki ba, amma ta gwargwadon ruhaniya. 5 Wadanda ke rayuwa gwargwadon jiki sukan lura da al'amuran jiki, amma su da ke rayuwa a gwargwadon Ruhu sukan mai da hankali ga al'amuran Ruhu. 6 To kwallafa rai ga jiki mutuwa ce, amma kwallafa rai ga Ruhu rai ne da salama. 7 Haka yake domin kwallafa rai ga jiki gaba yake da Allah, gama baya biyyaya ga shari'ar Allah, balle ma ya iya. 8 Wadanda ke a jiki ba su iya faranta wa Allah zuciya. 9 Duk da haka, ba ku cikin jiki amma a cikin Ruhu, idan gaskiya ne, Ruhun Allah na rayuwa cikinku. Amma idan wani ba shi da Ruhun Almasihu, shi ba na sa bane. 10 In Almasihu na cikinka, jikin ka fa matacce ne ga zunubi, amma ruhu na rayuwa bisa ga adalci. 11 Idan Ruhun wanda ya tada Yesu daga matattu na raye a cikinku, to shi wanda ya tada Almasihu da ga matattu za ya bada rai ga jikinku masu matuwa ta wurin Ruhunsa, da ke rayuwa a cikin ku. 12 To, 'yan' uwa, muna da hakki amma ba bisa jiki ba, da za mu yi rayuwa bisa ga dabi'ar jiki. 13 Gama idan kun yi rayuwa gwargwadon jiki, za ku mutu kenan, amma idan ta wurin Ruhu ku ka kashe ayyukan jiki, za ku rayu. 14 Gama duk wadanda Ruhun Allah ke bishe su, su 'ya 'yan Allah ne. 15 Gama ba ku karbi ruhun bauta da ke sa tsoro ba. Maimakon haka, kun karbi ruhun diyanci, ta wurinsa muke tadda murya muna kira, "Abba, Uba!" 16 kansa na bada shaida tare da namu ruhun cewa mu 'ya'yan Allah ne. 17 Idan mu 'ya'ya ne, ai mu magada ne kenan, magadan Allah. Kuma mu magada ne tare da Almasihu, hakika idan mun sha wahala tare da shi za a kuma daukaka mu tare da shi. 18 Gama na yi la'akari cewa wahalonin zamanin nan ba su isa a kwatanta su da daukakar da za'a bayyana mana ba. 19 Saboda yadda halitta ke marmarin bayyanuwar 'ya'yan Allah. 20 Gama an kaskantar da halitta ga banza, ba da nufin ta ba, amma na shi wanda ya kaskantar da ita. Ta na cikin tabbacin alkawarin. 21 Cewa halitta kanta za ta kubuta daga bautar rubewa, kuma za a kawo ta zuwa ga 'yantarwa na yabon daukakar 'ya'yan Allah. 22 Gama mun sani dukan halitta na nishi da zafin nakuda tare har ya zuwa yanzu. 23 Ba haka kadai ba, amma ko mu kanmu, da ke nunar farko na Ruhu--mu kanmu muna nishi acikin mu, muna jiran diyancinmu, wato ceton jikinmu kenan. 24 Gama ta wanan hakikancewa aka cece mu. Amma dai abin da muke da tabbacin zai faru ba mu gan shi ba tukuna, domin wanene wa ke begen tabbatacce abin da yake gani? 25 Amma idan muna da tabbacin abin da ba mu gani ba tukuna, to sai mu jjira shi da hakuri. 26 Hakanan, Ruhu kuma ke taimako a kasawarmu. Gama ba mu da san yadda zamu yi addu'a ba, amma Ruhu kansa na roko a madadinmu da nishe-nishen da ba'a iya ambatawa. 27 Shi da ke bidar zuciya yana sane da tunanin Ruhu, domin yana roko a madadin masu badagaskiya ta wurin nufin Allah. 28 Mun san cewa ga wadanda ke kaunar Allah, yakan aikata dukan al'amura domin su zuwa ga alheri, ga duk wadanda aka kira bisa ga nufinsa. Dukan abubuwa sukan zama alheri. 29 Saboda wadanda ya sani tuntuni su ne ya kardara su zama da kamanin dansa, domin ya zama dan fari a cikin 'yan'uwa masu yawa. 30 Su da ya kaddara, ya kiraye su. Wadanda ya kira, su ya kubutar. Su da ya kubutar, sune kuma ya daukaka. 31 Me zamu ce game da wadannan al'amura? Idan Allah na tare da mu, wake gaba da mu? 32 Shi da baya hana dansa ba, amma ya bada shi a madadinmu dukka, me zai hana shi bamu dukkan abubuwa a yalwace tare da shi? 33 Wa zaya kawo wata tuhuma ga zababbu na Allah? Allah ne ke "yantarwa. 34 Wanene ke hukumtawa? Almasihu ne da ya mutu sabili da mu har ma fiye da haka, shi wanda kuma aka tasar. Yana mulki tare da Allah a wuri mai daukaka, shi ne kuma ya ke roko sabili da mu. 35 Wa za ya raba mu da kaunar Allah? Kunci, ko bacin rai, ko tsanani, ko yunwa, ko tsiraci, ko hadari, ko takobi? 36 Kamar yadda aka rubuta, "Saboda kai ake kisanmu dukkan yini. An mai da mu kamar tumaki yanka." 37 A dukan al'amuran nan mun fi karfi a ce da mu masu nasara ta wurin shi da ke kaunar mu. 38 Gama na tabata cewa ko mutuwa, ko rai, ko mala'iku, ko mulkoki, ko al'amuran yanzu, ko al'amura masu zuwa, ko iko, 39 ko tsawo, ko zurfi, kai ko wace irin halitta, ba su isa su raba mu da kaunar Allah, da ke a cikin Almasihu Yesu Ubangijin mu ba.
Bulus ya bada amsa ga gwagwarmayar sa da zunubi da nagarta.
A nan "kayarwa" na nufin a hukunta mutane. AT: "Allah ba zai kayar ko hukunta waɗanda suke tare da Almasihu Yesu ba"
"saboda wannan dalili" ko kuwa "saboda abin nan da na faɗa maku yanzun nan gaskiya ne"
Wannan na nufin Ruhun Allah. AT: "Ruhun Allah cikin Almasihu Yesu"
'Yantuwa daga ka'idar zunubi da mutuwa na nufin cewa ka'idar zunubi da mutuwa ba da mulki. AT: "ya sa ka'idar zunubi da mutuwa ba su mulkin ku a yanzu kuma"
Ma'ana mai yiwuwa su ne cewa wannan na nufin 1) ka'idar da ke sa mutane su yi zunubi, zunubin su kuwa na sa su su mutu. AT: "ka'idar da take da zunubi da mutuwa" ko kuwa 2) ka'idar cewa mutane sun yi zunubi sun kuma mutu.
Shari'ar anan an bayyana ta kama mutum wanda bai iya karya ikon zunubi ba. AT: "Gama shari'ar bata da ikon hana mu yi zunubi saboda ikon zunubi tsakanin mu na da karfi sosai. Amma Allah ya hana mu yin zunubi"
"saboda halin zunubi na mutane"
Ɗan Allah har'abada ya biya bukatar fushin Allah mai tsarki gãbã da zunubi ta wurin bada jikinsa da rayuwarsa ta mutuntaka a matsayin madawwamiyar hadaya don zunubi.
Wannan lakani ne mai muhimmanci na Yesu, Ɗan Allah.
"wanda ke kama da kowane mutum mai zunubi"
"saboda ya iya mutuwa a matsayin hadaya don zunuban mu"
"Allah ya karye ikon zunubi ta wurin jikin Ɗansa"
AT: "mu iya cika abin da shari'ar ke buƙata"
Tafiya a tafarkin na nufin yadda mutane ke rayuwa. Jiki karin magana ne ta halin zunubin 'yan adam. AT: "mu da ba mu yin biyayya ga sha'awace sha'awacen zunubi ba"
"amma wanda ke biyayya ga Ruhu Mai Tsarki"
A nan Bulus ya yi magana game da "jiki" da kuma "ruhu" sai ka ce mutane ne da ke raye. AT: "yadda mutane masu zunubi suke tunani ... yadda mutane da ke kasa kunne ga tunanin Ruhu Mai Tsarki"
A nan wannan na nufin raba mutum da Allah.
Wannan na nufin mutanen da ke yin abin da halin zunubi ya gaya musu su yi.
aiki bisa ga haili ku na zunubi" Dubi yadda kun juya "jiki" cikin [Romawa 8:5]
"aiki bisa ga Ruhu Mai Tsarki"
Waɗanan duk na nufin Ruhu Mai Tsarki.
Wannan magana ba ta nufin cewa Bulus ya na shakka cewa wasun su suna da Ruhun Allah. Bulus ya na so su gane cewa Dukkan su suna da Ruhun Allah. AT: "tundashiƙe" ko kuwa "saboda"
Za a iya bayyana yadda Almasihu ke rayuwa cikin mutum. AT: "In Almasihu na rayuwa cikinku ta wurin Ruhu Mai Tsarki"
Ma'ana ma yiwuwa suna kamar haka 1) mutum ya mutu ga iƙon zunubi a ruhaniya ko kuwa 2) jikinsa wanda muke iya gani za ta mutu saboda zunubi.
Ma'an mai yiwuwa suna kamar haka 1) mutum na da rai cikin ruhun saboda Allah ya ba shi ikon aikata abin da ke daidai ko kuwa 2) Allah zai dawo da mutumin zuwa rai bayan ya mutu saboda Allah mai adalci ne, ya kuma ba wa masubi rai madawwami.
Bulus na tsammanin cewa Ruhun Mai Tsarki na raye cikin masu karantun sa. AT: "Tundashiƙe Ruhu ... na raye a cikin ku"
"Allah, wanda ya tada"
A nan "tada" na nufin sa wani wanda ya mutu ya rayu kuma. AT: "sa Yesu ya rayu kuma"
"jikun ta duniya" ko kuwa "jikin, wanda zai mutu wata rana"
"saboda abin nan da na faɗa maku gaskiya ne"
A nan wannan na nufin masubi maza da mata dukka.
Bulus yana magana game da biyayya sai ka ce biyan wata hakki ne. AT: "ya kamata mu yi biyayya"
Haka kuma Bulus ya yi magana game da biyayya sai ka ce biyan wata hakki ne. Za ku iya sa abin da kalman "hakki" ta nufi. AT: "amma mu ba masu biyan hakki ga jiki bane, kuma ba lallai ne mu yi biyayya ga sha'awace sha'awacen mu ta zunubi ba"
"domin in kun yi rayuwa don ku faranta wa sha'awace sha'awacen ku ta zunubi kawai"
"haƙikia za a raba ku da Allah"
Bulus ya yi magana game da "tsohon mutum" cewa an giciye ta da Almasihu kamar mutumin da ke da nawayan sha'awace sha'awacen sa ta zunubi. AT: "amma in ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki kun bar yin biyayya ga sha'awace sha'awacen ku ta zunubi"
AT: Gama duk mutanen da Ruhun Allah ke bishe su"
A nan na nufin dukkan masu bada gaskiya ga Yesu, sau da yawa ana juya shi "'ya'yan Allah."
"wanda ya samu mu ta da murya mu kira"
"Abba" "Uban" ne a harshen Aramiyanci
Bulus ya yi magana game da masubi sai ka ce za su gaji wata kaya da dukiya daga ɗaya daga cikin iyali. AT: "mu kuma wata rana za mu karbi abin da Allah ya alkawarta mana"
Bulus ya yi magana game da masubi sai ka ce za su gaji kaya da dukiya daga ɗaya daga cikin iyali. Allah zai ba mu abin nan da ya ba wa Almasihu. AT: "za mu kuma karɓi abin da Allah ya alkawarta mana kuma tare da Almasihu"
Allah zai ɗaukaka masubi a sa'adda ya ɗaukaka Almasihu. AT: "cewa Allah zai ɗaukaka mu tare da shi"
Wannan na nanata "na yi la'akari." ba ta nufin "saboda"
AT: "ba zan iya kwatanta wahalolin mu ta yanzu da"
AT: "Allah zai bayyana" ko kuwa "Allah zai sa a sani"
Bulus ya bayyana dukkan abin da Allah ya halita kamar mutum ne wanda ke marmarin jiran wani abu.
AT: "loƙacin da Allah zai bayyana 'ya'yan sa"
AT: "Gama Allah ya sa abin da ya halita ta zama da rashin iƙon cimma burinsa" (Dubi:
A nan Bulus ya bayyana "halita" kamar mutum wanda ke da muradi. AT: "ba wai domin abin da halitattun abubuwa ke so ba ne, amma domin abin da Allah ke so ne"
AT: "Domin Allah ya san da cewa zai cece halita"
A nan bautar ruɓewa na nufin haƙika zai ruɓe. AT: daga zama kamar bayi zuwa ga ruɓewa"
"'Yantarwa" anan na da bambanci da zama bawa zuwa ga ruɓewa. wannan na nufin cewa halita ba za ta ruɓe ba. AT: "cewa za ta samu ɗaukakar 'yanci daga ruɓewa kamar 'ya'yan Allah"
Halitan an kwatanta ta da macen da ke nakuda a sa'adda ta ke haihuwa. AT: Gama mun san cewa dukkan abubuwan da Allah ya halita na so ta sami yanci kuma suna nishin ta kamar macen da ke haihuwa"
Bulus ya kwatanta karbar Ruhu Mai Tsarki na masubi da nunan fari da kuma kayan lambu ta loƙacin da ke girma. Wannan na nanata cewa Ruhu Mai Tsarki farkon abin da Allah zai ba wa masubi ne. AT: "wanda suka sami farkon kyautar da Allah ya ba mu, wato, Ruhu Mai Tsarki"
A nan "dayancinmu" na nufin sa'adda muka zama cikakken 'yan iyalin Allah kamar 'ya'yan da aka karbe su. Kalman nan "ceto" ba nufin sa'ada Allah ya cece mu. AT: "jiran sa'adda za mu zama cikakkun 'yan iyalin Allah kuma ya cece jikunan mu daga ruɓewa da kuma mututwa"
AT: "Gama Allah ya cece mu saboda begen mu na cikin sa"
Bulus ya yi wannan tambaya don ya taimake masu sauraron sa su fahimci mecece "bege". AT: "Amma in muna jira da gabagadi, ai wannan na nufin cewa ba mu riga mun sami abin da muke so ba kenan. Babu wanda ke da gabagadi in har ya riga ya sami abin da yake so"
"nishe-nishe da ba za mu iya bayyana ta ba cikin kalmomin"
A nan "Shi" na nufin Allah. Anan "zuciya" na nufin tunanin mutum da kuma shauƙi. Maganar "bidar zuciya" na nufin jaraba tunanin da shauƙi. AT: "Allah, wanda ya san dukkan tunani da kuma yadda suke ji"
AT: "ga waɗanda Allah ya zaɓe su"
"waɗanda ya sani tun kafin ya halici duniya"
"ya kuma sa ta ta zama hanyar da ya kadara" ko kuwa "ya kuma shirya tun da wurin"
Allah ya shirya tun daga farko halita ya sa waɗanda suka bada gaskiya ga Yesu, Ɗan Allah su yi girma cikin mutanen wanda suna kamar Yesu. AT: "zai canza su su zama kamar Ɗansa"
domin Ɗansa ya zama ɗan fari"
A nan "'yan'uwa" na nufin masubi mata da maza dukka. AT: "a cikin 'yan'uwa maza da mata masu yawa wanda ke na iyalin Allah"
"Waɗanda Allah ya yi musu shiri tundawuri"
A nan "kubutar" na nanata cewa wannan lallai zai faru. AT: "waɗannan da ya daidaita su ga kansa" Dubi:
Kalman "ɗaukaka" na nanata cewa wannan lallai zai faru. AT: " waɗannan ne ya kuma ɗaukaka"
Bulus ya yi amfani da wannan tambayar don ya nanata ainihin nufin abin da ya faɗa a baya. AT: "Wannan ita ce abin da ya kamata mu sani daga duk wannan: tundashiƙe Allah na taimakon mu, babu wanda zai ci nasara a kanmu" Dubi:
Allah Uban ya aiko da Allah Ɗan, Yesu Almasihu zuwa giciyen a matsayin hadaya mai tsarki, mara matuka wanda ake bukata don biya bukatar Allah mara iyaka, halin sa na tsarki gaba da zunubin 'yan adam. Anan "Ɗa" lakani ne ma muhimanci na Yesu, Ɗan Allah.
"amma ya sa shi karkashin iƙon abokan gabansa"
Bulus ya yi amfani da tambaya fon ya nanaci. AT: "haƙika shi zai ba mua kome kyauta!"
"bamu dukkan abubuwa"
Bulus ya yi amfani da tambaya don nanaci. AT: "Babu wanda zai zarge mu a gaban Allah saboda shine wanda ke daidaita mu wa kansa"
Bulus ya yi amfani da tambayar don nanaci. Ba ya bukatar amsa. AT: "Babu wanda zai hukunta mu!"
A nan a ta da na nufin a sa wani wanda ya mutu ya rayu kuma. AT: "wanda kodashiƙe mafi muhimanci, Allah ya tashe shi faga matattu" ko kuwa "wanda kodashiƙe mafi muhimanci ya tashi da rai"
Zama a "hannun daman Allah" alama ce ta karbar daraja da iko daga wurin Allah. AT: "wanda ke wurin mai daraja tare da Allah"
Bulus ya yi wannan tambayar don ya koya cewa babu abin da ta isa ta raba mu da ƙaunar da Almasihu ke yi mana. AT: "babu wanda zai raba mu da ƙaunar ƙaunar da Almasihu ke yi mana!" ko kuwa "Babu abin da zai raba mu daga ƙaunar da Almasihu ke yi mana!"
Kalman nan "zai raba mu daga ƙaunar da Almasihu ke yi mana" an fahimci ta faga tambayar da ke a baya. AT: "shin Kunci, ko bacin rai, ko tsananin, ko yunwa, ko tsiraici, ko hatsari, ko takobi ne za ta raba mu da ƙaunar da Almasihu ke yi mana?"
Waɗannan kalmomin su na nufin abu ɗaya ne.
A nan "kai" na nufin Allah ne. AT: "domin ka"
A nan "mu" na nufin shi wanda ya rubuto wannan sashin Nassin ba mai sauraro wato Allah. Maganar nan "yini zubur" na nanata hatsarin da suke cikin ne. Bulus ya yi amfani da wannan sashin Nassin don ya nuna cewa dukkan wanda ke na Allah, to sai ya sammaci loƙacin wahala. AT: "abokan gaban mu su koƙarin kashe mu"
A nan Bulus ya kwatanta dabbobi da waɗanda mutane ke kashe su saboda biyayyar su ga Allah. AT: "ran mu ba ta daraja kuma a gare su da tumakin da suke kashe"
"mu na da cikakken nasara"
Ku na iya bayyana irin ƙaunar da Yesu ya nuna mana. AT: "saboda Yesu, wanda ya ƙaunace mu sosai har ma yana shirye ya mutu domin mu"
"ba ni da shakka" ko kuwa "ina da gabagadi"
Wannan na iya nufin 1) aljanu ko 2) sarakuna da masu mulki.
Wannan na iya nufin1) ruhohi da ke da iƙo ko 2) mutane da ke da iƙo.
ƙa'idar Ruhun mai ba da rai da yake ga Almasihu Yesu ya 'yantar da Bulus daga ƙa'idar zunubi da mutuwa.
Shariyar ta kasa domin shariyar ta wurin mutumtaka ta raunana.
Waɗanda suke tafiya ta Ruhu na ƙwallafa ransu ga abubuwan Ruhu.
Halin mutumtaka na gãba da Allah kuma ba ya bin Shariyar.
Mutanen da ba na Allah ba ne, ba su da Ruhun Almasihu a raye cikin su.
Allah na ba wa mai ba da gaskiya rai ta wurin Ruhunsa da ke rayuwa a cikin mai bin.
Ruhun Allah na bishe 'ya'yan Allah.
Mai bi na zama ɗan iyalin Allah ta wurin karɓan shi a matsayin ɗa.
A matsayin 'ya'yan Allah, masu bi magadan Allah ne kuma magada ne tare da Almasihu.
Masu bi su jimre wahalar wannan zamani domin a daukaka su tare da Almasihu a bayyanuwar 'ya'yan Allah.
Za a cece hallita zuwa ga 'yancin daukakar 'ya'yar Allah.
Hallitar na karkashin bautar lalacewa a wannan zamanin.
Masu bi su jira fansar jiki da yarda da kuma hakuri.
Ruhun da kan shi na roƙo a madadin tsarkaka ta nufin Allah.
Allah na aikata abu dukka zuwa alheri ga waɗanda suke ƙaunar Allah, su ke kirayayyu kuma bisa ga nufinsa.
Allah ya zaɓe waɗanda bisa ga ri ga saninsa su ɗauke kamannin Ɗansa sa.
Waɗanda ya ri ga ya zaɓa, Allah ya kira, ya kuma kuɓutar, da kuma ɗaukakasu.
Masu bi sun san cewa Allah zai zai ba su dukka komai hannu sake domin ya ba da Ɗansa a madadin masubi dukka.
Almasihu Yesu na hannun damar Allah yana roƙo a madadin tsarkaka.
Masubi sun zarce masu nasara ta wurin shi wanda yake ƙaunar su.
Bulus na da tabbacin cewa ba wani halitta da zai iya raba masu bi daga ƙaunar Allah.
1 Gaskiya ne nake gaskiya nake fada cikin Almasihu. Ba karya nake yi ba. Lamirina, na shaida a cikin Ruhu Mai Tsarki. 2 cewa ina da matukar bakin-ciki da takaici marar karewa a zuciyata. 3 Dama ace, a la'anta ni, in rabu da Almasihu saboda 'yan'uwana, wato dangina da suke zuriyata bisa ga jiki. 4 Sune Isra'ilawa, sun sami karbuwa, da daukaka, da baiwar shari'a, da yi wa Allah sujada, da alkawarai. 5 Dukkan ubanni nasu ne daga cikinsu Almasihu ya fito bisa ga jiki- wanda shi ke Allah bisa kowa. Yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin. 6 Amma ba wai alkawarin Allah ya kasa ba ne, ba dukkan Isra'ilawa ne suke Isra'ilawa na gaskiya ba. 7 Haka nan, ba dukkan zuriyar Ibrahim ne 'ya'yansa ba. Amma "ta wurin Ishiyaku ne za'a kira zuriyarka." 8 Yana nuna mana cewa ba 'ya'yan jiki su ne 'ya'yan Allah ba. Amma 'ya'yan alkawari ne ake kirga su, kuma aka kebe su. 9 Wanna ce kalmar alkawari, "badi warhaka zan dawo, Saratu kuwa zata sami da." 10 Amma ba wannan kadai ba, bayan Rifkatu ta dauki ciki daga gun mijinta, ubammu Ishiyaku. 11 Yaran nan kafin ma a haife su, balle ma a ce sun yi wani abu mai kyau ko laifi, saboda zaben da Allah yayi, bai danganta da abin da suka yi ba, ko don aiki ba, amma don shine mai kira-- 12 kamar yadda Ya ce, mata, "babban zaya yiwa karamin bauta," haka nassi yace, 13 "Kamar yadda aka rubuta: "Yakubu na ke kauna, amma Isuwa na ki shi." 14 To me zamu ce kenan? Allah ya yi rashin adalci kenan? Ko kadan. 15 Gama ya ce wa Musa, "Ina nuna jinkai ga wanda zan yi wa jinkai, zan ji tausayi ga wanda zan tausaya masa." 16 Saboda haka, ba don wanda ke da aniya ba ne, ko kuwa wanda yake kokari ba, amma saboda Allah mai nuna jinkai. 17 Gama nassi ya ce da Fir'auna, "Saboda wannan dalilin ne, na tada kai, don in nuna ikona mai karfi a kanka, don sunana ya yadu ga dukkan duniya." 18 Ta haka Allah ya nuna jinkansa ga wanda ya so, ya taurarar da zuciyar wanda ya ga dama. 19 Za kuce mani, to don me, "Yake kama mu da llaifi? Wa ya taba yin jayayya da nufinsa?" 20 In ma mun duba, kai mutum wanene kai da zaka ja da Allah? Ko abin da aka gina zai ce wa magininsa, "Don me yasa ka ginani haka?" 21 Ko maginin ba shi da iko akan yimbu daya da zai gina tukunya mai daraja, wata kuma tukunyar don kowanne irin aiki? 22 In ace Allah, dake niyyar nuna fushinsa da ikonsa, ya sanu, sai ya jure da matukar hakuri mai yawa da tukwanen fushi da ya shirya don hallakarwar fa? 23 To ko ma ya yi haka don ya nuna yalwar daukakarsa da take dauke da alheri, wanda ya shirya don daukakarsa tun farko? 24 Zai yiwu ma ya yi haka ne domin mu, mu da ya kira, ba ma daga cikin Yahudawa kadai ba, amma har ma daga cikin al'ummai? 25 Kamar yadda ya ce a cikin littafin Yusha'u: "zan kira wadanda ba mutanena ba mutanena, da kuma kaunatattunta wadanda ba kaunatattu ba. 26 Zai zama kuma a inda aka ce da su, "ku ba mutanena bane, za a kisa su 'ya'yan Allah mai rai."' 27 Ishaya ya yi kira game da Isra'ila, "in a ce yawan 'ya'yan Isra'ila zasu zama kamar yashi a bakin teku, ragowarsu ne kawai za su sami ceto. 28 Ubangiji zai tabbatar da cikar kalmarsa a duniya, ba kuwa da dadewa ba. 29 Yadda Ishaya ya rubuta ada, "In da ba Ubangiji mai runduna bai bar mana zuriya ba, da zamu zama kamar Saduma, da kuma an maida mu kamar Gomarata. 30 To me za mu ce kenan? Ko al'ummai, da ba sa neman adalci, sun samu adalci ta wurin bangaskiya. 31 Amma Isra'ila, wadanda suka nemi adalcinsu ta wurin shari'a, ba su kai ga gaci ba. 32 To don me? don ba su neme shi da bangaskiya ba, amma ta ayyuka. Sun yi tuntube a kan dutse da zai sa laifi. 33 Kamar yadda aka rubuta, "Ga, shi na ajiye dutse a kan Sihiyona dutsen tuntube mai sa laifi. Ga wanda ya bada gaskiya gare shi ba zai ji kunya ba."
Bulus ya bayyana muradin sa cewa al'uman Israila su sami ceto. Sa'annan ya nanata bambamcin hanyar da Allah ya shiryar musu don su gaskanta.
Waɗannan maganganu biyun na nufin abu ɗaya ne. Bulus ya yi amfani da su don ya nanata cewa ya na faɗin gaskiya ne.
"Ruhu Mai Tsarki na mulkin lamirina kuma ya tabbata cewa abin nan da na faɗa"
A nan "takaici mara karewa a zuciyata" karin magana ne da Bulus ya yi amfani da ita don matsanancin baƙin cikin sa. AT: "ina gaya mu cewa ina matukar juyayi sosai da kuma zurfin"
Waɗannan maganganu biyun na nufin abu ɗaya ne. Bulus ya yi amfani da su tare don ya nanata matukar shauƙinsa take.
AT: "Ni kaina san so Allah ya la'anta ni ya kuma raba ni da Almasihu har'abada in wannan zau taimake 'yan'uwana Isra'ilawa, mutane na, su gaskanta da Almasihu"
A nan wannan na nufin masubi maza da mata dukka.
"Su, Isra'ilawa ne kamar ni. Allah ya zaɓe su su zama zuriyar Yakub"
A nan Bulus ya yi amfani da "karɓuwa" don ya nuna cewa Isra'ilawa suna kamar 'ya'yan Allah ne. AT: "Su na da Allah a matsayin Ubansu"
A nan "Almasihu ya fito bisa ga jiki" na nufin cewa Almasihu ga jiki daga zuriyar ubannin Isra'ila ne. AT: "Almasihu ya zo cikin jiki a matsayin zuriya ne daga ubannin su"
"Amma Allah bai kãsã cika alkawarensa bane" ko "Allah ya cika alkawarensa"
Allah bai yi alkawarensa ga dukan zuriyar Isra'ila (ko Yakub) ga jiki ba, amma ga zuriyarsa ta ruhaniya, wato, waɗanda suka dogara ga Yesu.
"Haka kuma ba dukkansu bane 'ya'yan Allah kawai wai don du zuriyar Ibrahim ne ba"
A nan "'ya'yan ta jiki" na nufin zuriyar Ibrahim ta jiki. AT: "ba dukkan zuriyar Ibrahim"
Wannan na nufin mutane da ke zuriyar ne cikin ruhaniya, wato waɗanda ke da bangaskiya cikin Yesu.
Wannan na nufin mutane wanda za su gaji alkawaren da Allah ya ba wa Ibrahim.
"waɗannan ne kalmomin da Allah ya yi amfani da ita a sa'adda ya yi alkawarin"
Kuna iya juya wannan cikin sifar aiki don bayyana cewa Allah zai ba wa Saratu ɗa. AT: "Zan ba wa Saratu ɗa"
Yana iya yiwuwa a al'adan ku kuna bukatan sa 9:11 bayan 9:12 don saukin fahimta. AT: "ubanmu Ishaku, an ce mata, 'babban zai bauta wa karamin.' Yanzu kam ba a haifi 'ya'yan ba tukuna ... domin shi wanda ya kira. Kamar yadda aka"
Bulus ya dubi Ishaku a matasyin "ubanmu" domin Ishaku kakan kakan Bulus ne da kuma Yahudawa masubi da ke a Roma.
"ta sami ciki"
"kafin ma a haifi 'ya'yan kuma kafin ma su yi wani abu, ko mai kyau ko mummuna"
saboda abin da Allah ke so ta faru bisa ga nufinsa za ta faru"
"kafin ma a haifi 'ya'yan"
"ba wai domin wani abin da suka yi ba"
domin Allah
"Allah ya cewa Rifkatu, 'babban ɗan zai bauta wa karamin ɗan"
Kalman nan "ƙi" zuguiguici ne. Allah yana ƙaunar Yakub fiye da yadda yake ƙaunar Isuwa. Ba wai a zahiri ya ƙi Isuwa ba ne.
Bulus ya yi amfani da wannan tambayar don ya jawo hankalin masu karatunsa.
"Wannan ba mai yiwuwa bane!" ko "haƙika ba haka ba!" Wannan maganar ta yi matukar musu cewa wannan zai iya faru. yana iya yiwuwa kuna da wata magana makamanci haka a harshen ku da za ku iya amfani da ita anan.
Bulus yi yi magana game da maganar Allah tare da Musa sai ka ce yana faru ne a wannan zamanin. AT: "Gama Allah ya ce wa Musa"
"ba don abin mutane ke so ko kuwa saboda suna ƙoƙarin sosai"
Bulus ya yi magana game da mutum wanda ke yi abubuwa masu kyau don ya sami tagomashi daga wurin Allah sai ka ce mutum da ke tsere.
A nan yadda nasin yake sai ka ce Allah na magana ne da Fir'auna AT: "an rubuta a nasin cewa Allah ya ce"
Allah na nufin shi kansa ne.
mufuradi
"Tada" anan karin magana na "a sa abu ta zama abin da ita ce." AT: "Na mai da kai mutum mai iko"
AT: "don mutane su iya yin shelar sunana"
Wannan na nufin ko 1) Allah cikin dukkan Allahntakansa. AT: "wanene ni" ko 2) ga sunan sa. AT: "yadda na ke da girma"
"ko'ina da akwai mutane"
Allah ya sa wanda ya ga da ma, taurin kai.
Bulus na magana da masu zurfin tunani game da koyarwar sa kamar yana magana ne da mutum ɗaya. Mai yiwuwa kun bukaci yi amfani da jam'i anan.
Waɗannan tambayoyi da Bulus ya yi amfani da su na kara nanaci ne. Za ku iya juya wannan cikin magana ma nauyi.
kalmomin nan "shi" da "na shi" anan na nufin Allah.
Bulus ya yi amfani da iƙon da magini tukwane ke da shi don yin kowane abu da ya ke so daga yumbu don nuna makamacin abu game da iƙon mahalici ya yi kowane abu da ya ke so da halitarsa. Bulus ya yi waɗannan tamɓayoyin don ya nanata abin da ya ke ƙoƙarin faɗa.
Kalman nan "ka" anan na nufin Allah ne. Bulus ya yi amfani da wannan tamɓayar don ya kara nanatawa ne. Kuna iya juya wannan kamar magana na na kwarai. AT: "Ya Allah, bai kamata ka ginani haka ba!"
Bulus ya yi magana game da mutane sai ka ce su tukwane ne. AT: "mutanen da suka cancanci hukunci ... mutanen da suka cancanci jinƙan"
Bulus ya kwatanta ayyukan Allah na ban mamaki da babbar "dukiya." AT: "ɗaukakarsa, wanda ke da daraja na kwarai, kan"
A nan "ɗaukaka" na nufin rayuwa cikin sama tare da Allah. AT: wanda ya shirya tun da wurin don su yi rayuwa da shi"
Kalman nan "mu" anan na nufin Bulus da 'yan'uwa masubi.
A nan "kira" na nufin cewa Allah ya naɗa ko ya zaɓe mutane su zama 'ya'yansa, su zama bayinsa da kuma masu shelar saƙon cetonsa tawurin Yesu.
A nan "ya" na nufin Allah. "kamar yadda Allah ya faɗa kuma cikin litaffin cewa Yusha'u ya rubuto"
Yusha'u annabi ne a dã.
"Zan zaɓa wa mutane na waɗanda ba mutane ba"
A nan "ta" na nufin ma Yusha'u, Gomer, wanda ke a maɗaɗɗin al'umar Isra'ila. AT: "Zan zaɓe ta ita wanda ban ƙaunace ta ba ta zama wanda ina ƙauna"
Kalman nan "rayayye" mai yiwuwa na nufin gaskiyar cewa Allah shine Allah na gaskiya, kuma shi ba kamar allolin karya bane. AT: "'ya'yan Allah na gaskiye"
"kira"
A nan Bulus ya kwatanta yawan mutanen Isra'ila da yashin teku. AT: "yawan da ba za a iya kirgawa ba"
Bulus ya yi amfani da kalman nan "ceto" a fannin ruhaniya. Idan Allah ya cece mutum, wannan na nufin cewa ta wurin gaskantawa ne da mutuwar Yesu a kan giciye, Allah ya yafe masa ya kuma kubutar da shi daga hukuncin zunubansa. AT: "Allah zai cece"
Anan kalman nan "mu" da "mu" na nufin Ishaya da waɗanda ya yi magana game da su. (Dubi:
A nan "cikar kalmarsa" na nufin yadda ya shirya cewa zai hukunta mutane. AT: "Ubangiji zai hukunta mutane a duniya bisa ga yadda ya faɗa"
Allah ya hallaka mutanen Saduma da Gomarata saboda zunubansu. AT: "da an hallaka mu kamar mutanen Saduma da Gomarata" ko "da Allah ya hallaka mu dukka kamar yadda ya hallaka birnin Saduma da Gomarata"
Bulus ya yi amfani da wannan tambayar do ya kama hankalin masu karatunsa. AT: "Wannan ita ce abin da lallai ne mu faɗa"
"za mu ce cewa Al'ummai"
waɗanda ƙoƙarin faranta wa Allah rai"
A nan "ta wurin bangaskiya" na nufin dogarar wani ga Almasihu. Za ku iy bayyana wannan cikin juyin ku. AT: "domin Allah ya daidaita su da kansa a sa'adda sun dogara ga Almasihu"
Wannan na nufin cewa Isra'ilawa ba su iya faranta wa Allah rai ba ta wurin yi ƙoƙarin bin shari'ar. Kuna iya bayyana wannan cikin juyin ku. AT: "ba su iya faranta wa Allah rai ba ta wurin bin shari'ar don ba su iya bin ta ba"
Wannan magana ce da bai cika ba. Kuna iya bayyana kalmar a juyin ku. Bulus ya yi wannan tambayar don ya sami hankalin masu karatunsa. AT: "Me ya za ba su iya kai ga adalci ba?"
Wannan na nufin abubuwan da mutane ke ƙoƙarin yi don su farantawa Allah. AT: "ta wurin aikata abubuwan da zai farantawa Allah rai" ko kuwa "ta wurin bin shari'an"
Za ku iya nuna cewa Ishaya ya rubuto wannan. AT: kamar yadda annabi Ishaya ya rubuto"
A nan Sihiyona na misalin Isra'ila. AT: "a Isra'ila"
Duka maganganu biyun na nufin abu ɗaya ne, kuma na nufin Yesu da mutuwarsa a kan giciye. wato sai kace mutane sun yi tuntuɓe a kan dutse domin sun yi ƙyamar ta sa'adda sun dubi mutuwar Yesu a kan giciye.
Domin dutse na a maɗaɗɗin mutum, mai yiwuwa ku bukaci juya "gaskanta da shi."
Bulus na shirye Allah ya la'ance shi saboda 'ya'uwansa.
Isra'ilawa na da alkawari, Shariya, bautar Allah, daukaka, da kuma maishewa 'ya'ya.
Bulus ya ce ba dukka waɗanda suke a Isra'ila ba ne asalin Isra'ilawa, kuma ba dukka 'yan zuriyar Ibrahim ba ne 'ya'yansa na asali.
'Ya'yan mutumtaka ba a kirga su a matsayin 'ya'yan Allah.
'Ya'yan alkawari ne ake kirga su a matsayin 'ya'yan Allah
Nufin Allah ta zaɓensa ne ya kawo wannan maganar wa Rebeka.
Zaɓen Allah ne dalilin kyautarsa na rahama da tausayi.
Dalilin da ya kawo kyautar Allah na rahama da tausayi ba ya a zaɓe ko ayyukan mutumin da ke karɓar kyautan.
Bulus ya ce, "Wane ne kai ka yi jayayya da Allah?"
Allah ya haƙura, matuƙar haƙuri da waɗanda aka shirya domin hallaka.
Allah bayyana masu yalwar ɗaukakarsa .
Allah ya kira daga cikin Yahudawa da al'ummai tare waɗanda ya nuna masu jinkai.
Daga dukka 'ya'yan Isra'ila, akwai raguwar da zasu sami ceto.
Al'umman sun samu ta wurin adalci da ke a bangaskiya.
Isra'ilawa sun yi tuntuɓe a dutsen tuntuɓe da kuma dutseb laifi.
Isra'ilawa ba su samu ba domin sun nema ta wurin ayyuka ne ba ta wurin bangaskiya ba.
Waɗanda ba su yi tuntuɓe be, kuma sun gaskata ba su kunyata ba.
1 'Yan'uwana, muradin zuciyata da dukkan addu'oi na ga Allah dominsu shine don su sami ceton. 2 Domin na shaida game da su cewa suna da kwazo game da Allah, amma ba a kan sani ba. 3 Don, ba su da sani akan adalcin Allah, suna kokarin tabbatar da adalcin kansu. Ba su bada kan su ga adalcin Allah ba. 4 Gama Almasihu shi ne cikar doka zuwa ga adalci ga dukkan wadanda suka gaskata. 5 Musa kam ya rubuta game da adalci da zai samu ta shari'a: "mutumin da ya aikata adalcin shari'a, zai rayu ta wurin wannan adalcin." 6 Amma adalcin da ya zo ta wurin bangaskiya yace, "Kada ku ce a zuciyarku, wa zai hau zuwa sama?"(don ya sauko da Almasihu kasa). 7 Kada ku ce, "Wa zai gangara zuwa kasa?" (Wato wa zai fito da Almasihu daga cikin matattu). 8 Amma me yake cewa? "kalmar tana kusa da kai a cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka." Wato kalmar bangaskiya, wadda muke shaidawa. 9 Don idan da bakinka, ka shaida Yesu Ubangiji ne, kuma ka gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto. 10 Don da zuciya ne mutum yake gaskatawa zuwa ga adalci, da kuma baki ne yake shaida zuwa ga ceto. 11 Don nassi na cewa, "Duk wanda ya gaskata da shi ba zai ji kunya ba," 12 Gama ba bambanci tsakanin Bayahude da Ba'al'ume. Gama dukkansu Ubangijinsu daya ne, Shi mayalwaci ne ga dukkan wanda ya kira shi. 13 Duk wanda ya kira sunan Ubangiji zai sami ceto. 14 To ta yaya zasu kira ga wanda basu gaskata ba? Kuma ta yaya zasu gaskata ga wanda ba su taba jin labarinsa ba? 15 Kuma ta yaya zasu ji in ba ayi masu wa'azi ba? Kuma ta yaya zasu yi wa'azin in ba an aike su ba? - Kamar yadda yake a rubuce, "Ina misalin kyau na kafafun wadanda ke shaida labarin farin ciki na abubuwa masu kyau!" 16 Amma ba dukkansu ne suka ji bishara ba. Gama Ishaya ya ce, "Ubangiji, wa ya gaskata da sakon? 17 Saboda haka bangaskiya na zuwa ta wurin ji, jin kuwa daga maganar Almasihu. 18 Amma na ce, "ko basu ji ba ne? I, tabbas" muryarsu ta kai dukkan duniya, kuma kalmominsu sun kai har karshen duniya." 19 yau, na ce, "Ko Isra'ila basu sani ba ne?" Da farko Musa ya ce, "Zan sa kuyi fushi da kishi da abin da ba al'umma ba. Abin da nake nufi nan shine al'ummar da basu da fahinta, zan more su, in tayar maku da hankali." 20 Amma Ishaya da karfin hali ya ce, "Ga wadanda basu neme ni ba suka same ni. Na bayyana ga wadanda basu nemi ni ba. 21 "Amma ga Isra'ila kam ya ce, "na mika hannu na ga masu rashin biyayya dukkan tsawon rana, domin su mutane ne masu taurin kai."
Bulus ya cigaba da bayyana muraɗinsa saboda Isra'ila su gaskanta amma ya nanata cewa duk waɗanda ke Yahudawa har ma da kowane mutum zai iya samun ceto ta wurin bada gaskiya ga Yesu ne.
Anan wannan na nufin Masubi, maza da mata dukka.
Anan "zuciya" na nufin shauƙin mutumin ko kuwa cikinsa. AT: "babbar muraɗi na"
"ita ce Allah zai cece Yahudawa"
"Na yi shela cikin gaskiya game da su"
A nan "adalcin" na nufin hanyar da Allah ke daidaita mutane wa kansa. Ku na iya bayyana wannan cikin juyin ku. AT: "Gama ba su san yadda Allah ke daidaita mutane da kansa ba"
"Ba su yarda da hanyar da Allah ke daidaita mutane wa kansa ba"
"Gama Almasihu ya cika bukatar shari'ar gabaɗaya"
A nan "bada gaskiya" na nufin "dogara." AT: "don ya daidaita dukkan wanda ya dogara a gare shi a gaban Allah"
Bulus ya yi magana game da "adalci" sai ka ce ta na raye kuma na iya tafiya. AT: "yadda shari'ar ke daidaita mutum a gaban Allah"
Don a daidaita ga Allah ta wurin shari'ar, lallai ne mutumin ya kiyaye shari'ar daidai, hakan kuwa ba mai yiwuwa bane. AT: "Mutumin da ya kiyaye shari'ar babu kuskure zai rayu saboda shari'ar zata daidaita shi a gaban Allah"
Kalmomin nan "zai rayu" na iya nufin 1) rai madawwami ko kuwa 2) rayuwar mutum da ke zumunta da Allah.
A nan "adalci" an bayyana ta kamar mutumin da ke iya magana. AT: "Amma Musa ya rubuta wannan game da yadda bangaskiya ke daidaita mutum da Allah"
Musa na magana da mutane sai ka ce yana magana da mutum ɗaya ne. Anan "zuciya" na nufin zuciyar mutum ko mutum na ciki. AT: "Kada ku ce wa kanku"
Musa ya yi amfani da wannan tambayar don ya koyawa masu sauraronsa. Umurninsa na baya cewa "Kada ku ce" na bukatan amsar da ke nuna cewa "babu". kuna iya juya wannan tambayar zuwa maganar da ba tambaya ba. AT: "Babu wanda zai iya hau zuwa sama"
"don su sa Almasihu ya sauko zuwa duniya"
Musa ya yi amfani tambaya don ya koyawa masu sauraron sa. Umurnin sa na baya "Kada ku ce" na bukatan amsar da ke nuna cewa "babu." Kuna iya juya wannan tambayar zuwa maganar da ba tambaya ba. AT: "Bubu wani mutum da zai iya gangarowa ya shiga wurin da ruhohin mutanen da suka mutu suke" (Dubi:
Daga cikin duk waɗanda suka mutu. Wannan furcin na bayyan dukkan mutanen da suka mutu cikin karkashin ƙasa. A fid da wani da cikin su na nufin sake rayuwa kuma.
Wannan kalman na magana game da mutuwa ta jiki.
Kalman nan "yake" na nufin "adalcin" ta [Romawa 10:6]. Anan Bulus ya bayyana "adalci" kamar mutum da zai iya magana. Bulus ya yi amfani da tambaya don ya nanata amsar da yake ƙoƙarin bayarwa. AT: " Amma wannan ita ce abin da Musa ya faɗa"
Bulus ya yi magana game da saƙon Allah sai ka ce mutum ne da ke iya tafiya. AT: "Ka riga ka ji saƙon"
Kalman "baki" na nufin abin da mutu ya faɗa. AT: "Ka san yadda za ka yi magana ... saƙon Allah"
Wannan kalmomin "cikin zuciyarka" na nufin abinda mutum ya yi tunaninsa ya kuma bada gaskiya. AT: "ka san abin ... saƙon Allah na nufi"
"Saƙon Allah na faɗa mana cewa lallai ne mu bada gaskiya a gare shi"
"In ka shaida cewa Yesu Ubangiji"
A nan "zuciya" na nufin hankali ko kuwa cikin mutum. AT: "gaskanta cikin tunani ka" ko kuwa "gaskanta da gaske"
"Tashe" anan na nufin "a sa wani ya sake rayuwa kuma." AT: "sa shi ya sake rayuwa kuma"
AT: "Allah zai cece ka"
A nan "zuciya" na walkilcin tunan ko son rai. AT: "Gama da Zuciya mutum ke dogara kuma a daidaita shi a gaban Allah, da baki kuma mutum ke shaidawa, Allah kuwa ya cece shi"
A nan "baki" na wakilcin iya magana ta mutum.
Bulus ya yi magana game da Nassin sai ka ce ya na a raye kuma yana da murya. Ku na iya bayyana a fili wanda ya rubuta Nassin da Bulus ya yi amfani da ita ana. AT: "Gama Ishaya ya rubuta a cikin Nassin"
Wannan daidai ne da : "Dukkan wanda ba gaskanta ba zai kunyata." An yi amfani da wannan don a nanaci ne. AT: "Allah zai daraja dukkan wanda ya gaskanta da shi"
Bulus na nufin cewa Allah zai yi da dukkan mutanen daidai. Ku na iya bayyana wannan a fili cikin juyin ku. AT: "daidai haka Allah ke yi da Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa"
A nan "shi mayalwaci" na nufin cewa Allah zai zuɓo da yalwar albarkarsa. Ku na iya bayyana wannan a juyin ku. AT: "a yalwace ya albarkaci duk wanda ya dogara a gare shi"
Anan kalman "suna" na nufin Yesu. AT: "Ubangiji zai cece duk wanda ya dogara a gare shi"
Bulus ya yi wannan magana don ya nanata muhimancin kai bisharar Almasihu ga waɗanda ba su ji ba. Kalman nan "su" na nufin waɗanda ba na Allah ba tukuna. AT: "Waɗanda ba su gaskanta da Allah ba, ba za su iya kira bisan sa ba!"
Bulus ya yi amfani da wata tambayar kuma ta dalili iri ɗaya. AT: "Kuma ba za su iya gaskanta da shi ba in har ba su ji saƙonsa ba!" ko kuwa "Kuma ba za su iya gaskanta da shi ba in ba su ji saƙo game da shi ba!"
A nan wannan na nufin yardar cewa abin da wannan mutum ya faɗa gaskiya ne.
Bulus ya yi amfani da wata tambaya kuma don dalili iri ɗaya ne. AT: "Kuma ba za su iya jin saƙon ba in wani ba gaya musu ba!"
Bulus ya yi amfani da wata tambay kuma don dalili ɗaya. Kalman nan "su" na nufin waɗanda ke na Allah. AT: "Haka kuma ba za su iya faɗa wa wasu mutane saƙon ba sai dai in wani ya aike su!"
Bulus ya yi amfani da "ƙafafu" na wakilcin waɗanda ke matafiye kuma suna kawo saƙon ga waɗanda ba su ji ba. AT: "Ta na da kyau inda masu kai saƙo suka zo don su gaya mana saƙon Bishara"
A nan "su" na nufin Yahudawa. "Amma ba dukkan Yahudawa suka kasakunne ba"
Bulus ya yi amfani da wannan tambayar don ya nanata cewa Ishaya ya yi annabci cikin Nassi cewa Yahudawa dayawa ba za su gaskanta da Yesu ba. Ku na iya juya wannan kamar wata magana. AT: "Ubangiji, yawancinsu ba su gaskanta da saƙon mu ba"
A nan "mu" na nufin Allah da Ishaya.
A nan "bangaskiya" na nufin "bada gaskiya ga Almasihu"
"ji tawurin kasakunne ga saƙo game da Almasihu"
Bulus ya yi amfani da tambaya don nanaci. kuna iya juya wannan kamar magana. AT: "Amma, na ce hakika Yahudawa sun ji saƙon game da Almasihu" (Dubi: and
Waɗannan maganganu biyun na nufin abu ɗaya ne, kuma Bulus ya yi amfani da su don nanaci. Kalman nan "tasu" na nufin rana, wata da tauraru. Anan an bayyana su kamar masu saƙo zuwa ga 'yan adam da ke gaya wa mutane game da ALlah. Wannan na nufin cewa kassancewar su na nuna iko da ɗaukakan Allah. Kuna iya bayyana cewa Bulus ya faɗi daga Nassi Anna. AT: "Kamar yadda take a Nassi, 'rana, wata da tauraru abib shaida ce iko da ɗaukakan Allah, kowa kuwa a duniya na ganinsu ya kuma san gaskiya game da Allah.'"
Bulus ya yi amfani da tambaya don nanaci. Kalman nan "Isra'ila" na nufin mutanen da ke kasar Isra'ila. AT: "Kuma ina gaya muku, mutanen Isra'ila ba su san saƙon"
Wannan na nufin cewa Musa ya rubuta abin da Allah ya ce. "Ni" na nufin Allah, "Ku" na nufin "Isra'ila. AT: "Da farko Musa ya ce cewa Allah zai sa ku fushi ... Allah zai motsa su"
ta wurin waɗanda kuke duban su a matsayin al'umma ta gaske" ko kuwa "tawurin mutane wanda ba zu ciki wata al'umma ba"
A nan "rashin fahimta" na nufin cewa mutane ba su dan Allah ba. AT: "Ta wurin mutanen da ba sun san ni ba ko umurni na"
"Zan sa ku fushi" ko kuwa "zan sa ku ku yi fushi"
Wannan na nufin banin Isra'ila.
A nan kalman nan "Ni," "-na" na nufin Allah.
Wannan na nufin Annabi Ishaya ya rubuta abin da Allah ya ce.
Annabawa sun cika magana game da abubuwan da ke gaba sai ka ce sun riga sun faru. Wannan na nanata cewa anabcin haƙika zai cika. AT: "Kodashiƙe al'ummai ba za su neme ni ba, za su same ni"
"Na maishe kaina sananne"
"Ya" na nufin Allah, wanda ke magana da Ishaya.
Wannan jimla an yi amfani da ita don a nanata cewa Allah ya cigaba da ƙoƙarin . "cigaba"
"Na yi ƙoƙarin marabtan ku, in kuma taimake ku, amma kun ƙi taimakon da na ba ku, kun cigaba da rashin biyayya"
Muradin zuciyar Bulus shine ceton Isra'ilawa.
Isra'ilawa suna nema su kafa nasu adalcin.
Isra'ilawa basu san game da adalcin Allah ba.
Almasihu shi ne cikamakin Shariya domin kowane mai ba da gaskiya yă sami adalci.
Kalmar bangaskiya na kusa, a baki da kuma cikin zuciya.
Bulus ya ce lalle ne mutum ya amince da bakinsa Yesu Ubangiji ne, ka kuma gaskata a zuciya cewa Allah ya tashe shi daga matatu.
Duk wadda ya kira ga sunan Ubangiji zai sami ceto.
Bulus ya ce, a farko dai ana aikan mai bishara, sai a ji a kuma gaskata da bisharar, domin a iya kira ga sunan Ubangiji.
Ana jin kalmar Almasihu, wadda yake kawo bangaskiya.
I, Isra'ilawa sun ji bisharar.
Allah ya ce zai sa Isra'ila ta fusata da kishi ta wurin bayyana ga waɗanda basu fahimta ba.
Da Allah ya miƙa hannunwansa ga Isra'ila, ya ga jama'a marasa biyayya da masu tsayayya.
1 Sai na ce, Allah ya ki mutanensa ne? Ba zai taba yiwuwa ba. Domin ni ma ba-Isra'ile ne, na zuriyar Ibrahim, a kabilar Bilyaminu. 2 Allah bai ki mutanen sa da ya ke da rigyasaninsu ba. Ko kun san abin da nassi ya ce game da Iliya, yadda ya kai karar Isra'ila a gaban Allah? 3 Ya ce, "Ubangiji, sun kashe annabawanka, sun rushe alfarwanka kuma, Ni kadai ne na rage, ga shi suna neman su kashe ni." 4 Amma wacce amsa ce Allah ya ba shi? Ya ce, "Ina da mutane dubu bakwai da na kebe don kaina, da ba su taba rusuna wa Ba'al ba." 5 Ban da haka ma, ban da haka ma a wannan lokacin akwai sauran zabe na alheri. 6 Amma tun da ta wurin alheri ne, ba ga ayyuka ba. In ba haka ba, alheri ba zai zama alheri ba kenan. 7 Sai kuma me? Abin da Isra'ila ke nema, ba su samu ba, amma zababbun sun same shi, saura kuma sun taurare. 8 Kamar yadda yake a rubuce, "Allah ya ba su ruhun rashin fahimta, ga idanu amma ba za su gani ba, ga kunnuwa amma ba za su ji ba, har zuwa wannan rana." 9 Dauda kuma ya ce, "bari teburinsu ya zama taru, da tarko, ya zama dutsen tuntube da abin ramako a gare su. 10 Bari idanunsu ya duhunta domin kada su gani; bayansu kuma a duke kullum." 11 Na ce, "sun yi tuntube domin su fadi ne?" Kada abu kamar haka ya faru. A maimakon haka, juyawa baya da suka yi ya sa, ceto ya zo ga Al'ummai, domin ya sa su kishi. 12 Idan yanzu juyawa baya da sun yi ya zama arziki ga duniya, rashin su kuma arziki ga Al'ummai, yaya kwatancin girmansa zai kasance in sun zo ga kammala? 13 Yanzu ina magana da ku ku da ke Al'ummai. Tunda yake ni ne manzo ga Al'ummai, ina kuma fahariya cikin hidimata. 14 Yana yiwuwa in sa "yan'uwa na kishi, domin mu ceci wadansu su. 15 Idan kinsu ya kawo sulhuntawa ga duniya, Karbarsu kuma zata zama yaya? Zata zama rai ne daga mutuwa. 16 'ya'yan farko sunan haka ma kakkabensu yake, Idan saiwar itace na nan, haka ma rassan za su zama. 17 Amma idan an karye wasu daga cikin rassan, idan ku rassan zaitun na ainihi ne, da aka samu daga cinkinsu, kuma idan kuna da gado tare da su, acikin saiwar itacen zaitun din. 18 Kada ku yi fahariya a kan rassan. Amma idan kuka yi fahariya to ba ku bane masu karfafa saiwar amma saiwar ce ke karfafa ku. 19 Kana iya cewa, "An karye rassan domin a same ni a ciki." 20 Wannan gaskiya ne! Saboda rashin bangaskiyarsu ne ya sa aka karye su daga rassan, amma ku tsaya da karfi acikin bangaskiyarku. Kada ku dauki kanku fiye da yadda ya kamata, amma ku ji tsoro. 21 Domin idan Allah bai bar ainihin rassan ba, to ba zai bar ku ba. 22 Ku duba yadda irin ayyuka masu tsananni na Allah. Ta daya hannun kuma, tsanannin kan zoa kan Yahudawa wadanda suka fadi. Har 'ila yau jinkai Allah ya zo maku, idan kun cigaba cikin alherinsa baza a sare ku ba. Amma in kun ki za a sare ku. 23 Hakanan, idan ba su ci gaba cikin rashin bangaskiyarsu ba, za a maida su cikin itacen. Domin Allah zai iya sake maida su. 24 Idan an yanke ka daga itacen zaitun da ke na jeji, har ya yiwu an hada ka cikin itacen zaitun na ainihi, yaya kuma wadannan Yahudawa wadanda sune ainihin rassan, da za'a maido cikin zaitun da ke na ainihi? 25 Yan'uwa, ba na so ku kasance cikin duhu a game da wannan asirin, domin kada ku zama da hikima cikin tunaninku. Wannan asirin shine cewa wannan taurarewa ta faru a Isra'ila, har sai da Al'ummai suka shigo ciki. 26 Ta haka dukan Isra'ila za su tsira, kamar yadda yake a rubuce: "Daga cikin Sihiyona mai Kubutarwa zai fito; Zai kawar da kazanta daga cikin Yakubu. 27 Wannan zai zama alkawarina da su, sa'adda na kawar da zunubansu." 28 A wani bangaren kuma game da bishara, su makiya ne amamadinku, ta wani fannin kuma bisa ga zabin Allah su kaunattatu ne saboda ubanni. 29 Domin baye-baye da kiran Allah basa canzawa. 30 Domin ku ma da ba ku yin biyayya ga Allah, amma yanzu kun sami jinkai saboda rashin biyayyarsu. 31 Ta wannan hanyar dai, wadannan Yahudawan sun zama marasa biyayya. Sakamakon haka shine ta wurin jinkan da aka nuna maku, suma su samu jikai yanzu. 32 Domin Allah ya rufe kowa ga rashin biyayya, domin ya nuna jinkai ga kowa. 33 Ina misalin zurfin wadata da kuma hikima da sani na Allah! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban a bincika, hanyoyinsa kuma sun fi gaban ganewa! 34 Don wanene ya san tunanin Ubangiji? Wanene kuma ya zama mai bashi shawara? 35 Ko kuma, wanene ya fara ba Allah wani abu, domin a biya shi?" 36 Daga wurinsa ne, ta wurinsa ne kuma, a gare shi ne kuma dukan abu suka fito. A gare shi daukaka ta tabbata har abada. Amin.
Ƙodashiƙe Isra'ila a matsayin al'umma sun ƙi Allah, Allah yana so su fahimci ceto da ke samuwa tawurin alheri ba tare da ayyuka ba.
"Ni Bulus, na ce"
Bulus ya yi wannan tambaya don ya iya amsa tambayar wasu Yahudawa wanda sun yi fushi cewa Allah ya haɗa al'ummai cikin mutanensa, tundashiƙe mutanen Yahudawa sun taurara zuciyarsu.
"Wannan ba mai yiwuwa ba!" ko kuwa "Haƙika ba haka!" Wannan maganan ta ba da tabbacin cewa wannan ba zai faru ba. Mai yiwuwa kuna da magana makamancin haka a harshen ku da za ku iya amfani da ita ana. Dubi yadda kuka juya wannan cikin [Romawa 9: 14].
Wannan na nufin kabilar da ke daga Biliyaminu, ɗaya daga cikin kabilu 12 cikin wanda Allah ya raba mutanen Isra'ila.
"wanda ya sani tun kafin loƙaci"
AT: "Haƙika kun san Abin da Nassin ta faɗa game da sa'adda Iliya ya yi roƙo game da Isra'ila"
Bulus ya yi magana game da Nassin sai ka ce suna iya yin magana.
"su" na nufin mutanen Isra'ila.
"Ni" anan na nufin Iliya.
"son su kashe ni"
Bulus na amfani da wannan tambayar don ya kai masu karatunsa zuwa ga abin da zai faɗa a gaba. AT: "Ta yaya Allah ya amsa shi?"
"shi" na nufin Iliya.
"Mutane 7,000"
A nan wannan na nufin ƙaramin bangare mutane wanda Allah ya zaɓa su sami alherinsa.
Bulus ya cigaba da bayana yadda jinkan Allah ke aiki. AT: Amma dashike jinkan Allah na aiki tawurin alheri"
"Me za mu ce kenan?" Bulus ya yi wannan tambayar don ya kai masu karatunsa nufinsa na gaba. Ku na iya juya wannan cikin furuci. AT: "Wannan ita ce abin da ya kamata mu tuni"
Wannan na nufin cewa mutanen ba su fahimta a ruhaniyar su. Ba su iya ji ko su karɓi gaskiyar ruhaniya ba.
A nan wannan na nufin "samun halayen," kamar "ruhun hikima."
Ra'ayin cewa, a gani da idanu, ana duban ta daidai ne da samun fahimta.
Ra'ayin cewa, a ji da kunnuwa, a duban ta daidai ne da yin biyayya.
"Tebur" anan na wakilcin shagalgalin, kuma "raga" da "tarko" na wakilcin hukunci. AT: "Ya Allah ka maishe da shagalgalinsu kamar tarko da zata kama su"
"sanadin tuntuɓe" wani abu ne da ke sa mutum ya faɗi. Anan ta na wakilcin abu da ke gwada mutum do ya yi zunubi. AT: "wani abu da ke gwadasu su yi zunubi"
"wani abu ne da ke bada zarafin yin ramako a kansu"
A nan "tanƙwara bayansu" wata karin magana ne na sa bayi a dole su ɗauka kaya mai nauyi a bayansu. Wannan na nufin a sa mutum ya sha wahala. AT: "sa su shan wahala kamar mutane da ke ɗauke da kaya mai nauyi"
Bulus ya yi amfani da wannan tambaya do ya kara nanaci. AT: "Shin, Allah ya ƙi su har abada domin sun yi zunubi ne?
Dubi yadda kuka juya wannan jimla cikin [Romawa 10:19]
Waɗannan jimla biyun na nufin abu ɗaya ne a takaice. In lallai ne, to za ku iya haɗa su cikin juyin ku. AT: "Sa'adda Yahudawa suka faɗi a ruhaniya, sakamakon ita ce Allah ya albarkaci wanda ba Yahudawa ba a yalwace"
Domin Yahudawa sun ƙi Almasihu, Allah ya sa wa Al'ummai albarka a yalwace ta wurin ba su zarafi su karɓi Almasihu.
A nan "duniya" na nufin mutane wanda ke rayuwa cikin duniya musamman Al'ummai.
Dubi yadda kuka juya wannan jimla cikin [Romawa 10:19]
Wannan na nufin "'yan'uwana Yahudawa"
Allah zai cece waɗanda sun gaskanta. AT: "Maiyiwuwa wasu za su gaskanta, Allah kuma zai cece su"
"Domin in saboda Allah ya ƙi su, shi zai sulhunta duniya wa kansa"
"su" na nufin Yahudawa waɗanda ba su gaskanta ba.
Bulus ya yi wannan tambayar don ya nanata cewa sa'adda Allah ya karɓi Yahudawa, zai zama abin al'ajibi ne. AT: "yaya za ta zama a sa'adda Allah ya karɓe su? Zai zama kamar sun tashi ne daga cikin matattu!" ko kuwa "Sa'adda Allah ya karɓe su, zai zama kamar sun mutum sai suka dawo da rai kuma!"
Wannan kalman na magana ne game da dukkan mutane da suka mutu cikin ƙarƙashin kasa.
Bulus ya yi magana game da Ibrahim, Ishaku da Yakub, kakkanin Isra'ila, sai ka ce su ne tsaba na farƙo ko kuwa "'ya'yan fari" da za a girɓe. Yana kuma magana game da Isra'ila wanda ke zuriyar waɗanna mutane sai ka ce "kakkaben yake" da ke samuwa daga tsaba. AT: "Idan Ibrahim shine na farko da aka lisafta cikin abin da aka mika wa Allah, dukkan kakkaninmu wanda suke bi, su ma sai a lisafta a matsayin dukiyan Allah"
Bulus na magana a kan Ibrahim, Ishaku da Yakub, kakanin Isra'ila sai ka ce su saiwar itace ne, Isra'ila wanda su ne zuriyar waɗannan mutane, sai ka ce su "rassan" itacen ne."
Mutane a kullum su kan miƙa wa Allah amfanin gona na farko da suka girbe. Anan "'ya'yan fari" na a maɗaɗɗin mutane da suka fara gaskantawa da Almasihu.
"ku" da kuma jimla "rassan zaitun na jeji ne," na nufin Al'ummai wanda sun karɓi ceto tawurin Yesu.
A nan Bulus ya dubi Yahudawa wanda suka ƙi Yesu kamar "rassan da aka karye." AT: "Amma in wani ya karye wasu rassan"
A nan Bulus ya yi magana game da Al'umma masubi sai ka ce su "rassan da aka ɗaura aure mata aure ne." AT: "Allah ya haɗa ku da itacen da ke cikin sauran rassan"
A nan "saiwar itacen" na nufin alkawaren Allah
A nan "rassan" na nufin mutane Yahudawa. AT: "Kada ku ce kun fi Yahudawa mutanen da Allah ya ƙi"
Haka kuma Bulus na nufin Al'umma masubi sune rassan. Allah ya cece su kawai domin alkawaren da ya yi wa Yahudawa.
Anan "rassan" na nufin Yahudawa wanda sun ƙi Yesu kuma wanda Allah ya ƙi yanzu. AT: "Allah ya sare rassan nan"
Bulus na nufin Al'umma masubi wanda Allah ya karɓe su a wannan jimlar da ya yi amfani da ita. AT: "don ya ɗaura ni a kai"
"tasu" da "su" na nufin mutane Yahudawa wanda ba su gaskanta ba.
Bulus ya yi magana game da adalcin Al'umma masubi sai ka ce suna kafe ne kuma babu wanda zai iya tura su. AT: "Amma ku, ku na nan saboda bangaskiyarku"
A nan "asalin rassan" na nufin mutanen Yahudawa wanda sun ƙi Yesu. AT: "Dashiƙe Allah bai bar waɗannan Yahudawa wanda ba su bada gaskiya ba, wanda ke girma kamar asalin rassan itace da ke daga gigiyan, to ka sani, in ba ka bada gaskiya ba, ba zai bar ka ba"
Bulus yana tuna wa Al'umma masubi cewa ƙodashiƙe Allah ya yi masu alheri, ba zai yi jinkirin yi musu shari'a da kuma hukunci ba.
Za a iya bayana wanna in an cire "tsanani" da kuma "alheri." AT: "Allah ya tsananta wa Yahudawa da suka faɗi ... amma Allah ya yi muku alheri"
An yi magana game da yin abin da ba daidai ba sai ka ce faɗiwa ne. AT: "Yahudawan da suka yi abin da ba daidai ba" ko kuwa "Yahudawan da sun ƙi su dogara ga Almasihu"
Ana iya sake faɗin wannan in an cire sunan nan "alheri." AT: "in kun cigaba da yi abin da ke daidai don ya cigaba da yin muku alheri"
Bulus ya sake amfani da misalin reshe wanda Allah zai iya "sarewa" in ya na bukata ya sare. Anan "sarewa" na nufin ƙi ƙarbar wani. AT: "In ba haka ba Allah zai sare ku" ko kuwa "In ba haka ba Allah zai ƙi karɓa ku"
Fi'ilin maganar nan "ba su cigaba cikin rashin badagaskiya ba" korau biyu. AT: "Idan Yahudawan su fara gaskanta da Almasihu"
Bulus ya yi magana game da Yahudawa sai ka ce su rassa ne da za ɗaura musu aure da itace in sun fara gaskantawa da Yesu. AT: "Allah zai komar da su zuwa"
Wannan abin da ya cika faruwa ne wato reshe da bai bushe ba na itace an haɗa wani itacen don sabuwar rassan ta cigaba da girma a cikin wannan itace.
Bulus ya cigaba da magana game da Al'umma masubi da Yahudawa sai ka ce rassa itace ne. AT: "Gama idan Allah ya sare ku wanda ainihin itace zaitun na jeji ne, har ya yiwu ya haɗa ku cikin itacen zaitun mai kyau, yaya kuma Yahudawa wanda su ne ainihi rassan, za haɗa su cikin itace zaitun da ke na ainihi?"
Bulus ya yi magana game da Yahuda da kuma Al'ummai kamar su rassa ne. "ainihin rassan" na wakilcin Yahudawa, "rassa da aka ɗaura musu aure da itace" na wakilcin Al'umma masubi.
Dukkan bayyanuwa "ku" ko "su" na nufin Yahudawa ne.
Bulus anan ya yi amfani da korau biyu. AT: "Ina so ku sani"
A nan "'yan'uwa" na nufin Masubi mazaje da mataye dukka.
"Ni" na nufin Bulus.
"ku" da "naku" na nufin Al'umma masubi.
Bulus baya so Al'umma masubi su yi tunanin cewa suna da hikima fiye da Yahudawa masubi. AT: "don kada ku yi tunani kuna da hikima fiye da yadda kuke"
Bulus ya yi magana game da "taurarewa" ko kuwa taurin kai kamar taurin wani abu na jiki. wasu Yahudawa sun ƙi su karɓi ceto ta wurin Yesu. AT: "mutane daya na Isra'ila sun cigaba da taurarewa"
Kalman nan "har sai" anan na nufin cewa wasu Yahudawa za su gaskanta bayan Allah ya gama kawo al'umma zuwa cikin Ikkilisiya.
AT: "Ta haka Allah zai cece Isra'ila
AT: "Kamar yadda yake rubuce a nassin"
An yi amfani da "Sihiyona" anan ma dawamammen wurin ne na Allah. AT: "Daga wurin da Allah yake a tsakanin Yahudawa:
"shi wanda ya kowa mutanensa ga ceto"
Bulus ya yi magana game da rashin bin Allah sai ka ce wani abu ne da wani ke iya cirewa, mai yiwuwa kamar wani ya fid da tufa.
An yi amfani da "Yakub" a matsayin Isra'ila. AT: "daga mutanen Isra'ila"
Bulus ya yi magana game da zunubi sai ka ce wani abu ne da a iya kawar da shi. AT: "Zan kawar da nawayar zunubansu"
Ku na iya bayyana dalilin da ya sa Bulus ya ambata bisharan. AT: "Domin Yahudawa sun ƙi bisharan"
Ku na iya bayyana ko su maƙiyan wa ne su a fili, da yadda ta zama saboda Al'ummai ne. AT: "su maƙiyan Allah ne saboda da ku" ko kuwa "Allah mashe su maƙiya don ku ma ku ji bisharan"
Ku na iya bayyana dalilin da ya sa Bulus ya ambata zaɓe. AT: "domin Allah ya zaɓe Yahudawa" ko kuwa "saboda Allah ya zaɓe Yahudawa"
Ku na iya bayyana wanda ya ƙaunaci Yahudawa a fili da kuma dalilin da ya sa Bulus ya ambata kakkaninsu. AT: "Har wa yau, Allah yana ƙaunarsu saboda abin da ya yi alkawari zai yi wa kakkaninsu"
Bulus ya yi magana game da albarkar ruhaniya da ta jiki da Allah ya alkawarta zai ba wa mutane sai ka ce wata kyauta ne. Kiran Allah na nufin cewa Allah ya kira Yahudawa su zama mutanensa. AT: "Gama Allah bai canza zuciyarsa ba game da abin nan da ya yi alkawari zai ba su, game da yadda ya kira su su zama mutanen sa kuma"
"a dã ba ku yi biyayya ba"
A nan jinkai na nufin albarkar Allah da ba ta cancanci wani ba. AT: "Domin Yahudawa sun ƙi Yesu, ku kun sami albarkar da ba ta cancance ku ba"
Wannan na nufin Al'umma masubi, kuma jam'i ne
Allah ya yi da mutanen da suka yi masa rashin biyayya kamar 'yan kurkuku wanda ba su iya gudwa daga kurkuku ba. AT: "Allah ya mashe su 'yan kurkuku wato su waɗanda suka yi masa rashin biyayya. Yanzu kam ba za su iya bar yi wa Allah rashin biyayya ba"
A nan "hikima" da "sani" a takaice na nufin abu ɗaya ne. AT: "Dubi yadda amfanin hikimar Allah da saninsa take da ban mamaki!"
"Mu kam gabaɗaya mun kasa fahimta abubuwa da ya shirya, mun kuma kasa gane hanyoyinsa a gare mu"
Bulus ya yi amfani da wannan tambayar don ya nanata cewa babu wani wanda yake da hikima kamar Ubangiji. AT: "Babu wanda ya taɓa sani zuciyar Ubangiji, babu kuma wanda ya taɓa zama mashawarcinsa."
A nan "zuciya" na nufin sanin abubuwa ko kuwa yin tunani game da abubuwa. AT: "dukkan abin da Ubangiji ya sani" ko kuwa "abin da Ubangiji na tunani game da su"
Bulus ya yi amfani da wannan tambayar don ya nanata ainihin abin da yake so ya faɗa. AT: "babu wanda ya taɓa ba wa Allah wani abu da bai fara samuwa da wurin Allah ba" * Daga wurinsa ... tawurinsa ...masa - Anan, duk aukuwar "sa" na nufin Allah.
Bulus ya yi amfani da wannan don muradinsa ne dukkan mutane su ɗaukaka Allah. Ku na iya bayyana wannan a fili cikin juyin ku. AT: "Bari dukkan mutane su girmama shi har abada"
Allah ya sauƙe
Bulus ya ce akwai raguwan da aka keɓe domin zaɓen alheri.
Zaɓabu a cikin Isra'ilawa ne suka sami ceto, an kuma taurara sauran.
ruhun toshen basira ya hana idonsu gani, kunensu kuma ba ya iya ji.
Ceton Al'ummai zai ta da fushin kishi a gare Isra'ilawa.
Ceto ya zo ga Al'ummai.
Tushin ita ce Isra'ila. rassan jeji kuma su ne Al'ummai.
Tushin ita ce Isra'ila. rassan jeji kuma su ne Al'ummai.
Bulus ya ce tilas ne rassan jejin ka da su yi taƙama a kan asalin rassan da a aka yanke.
Bulus ya gargaɗe rassan jeji cewa idan Allah bai bar rassan asalin ba, hakama ba zai bar rassan jejin ba in sun faɗi daga bangaskiya.
Allah zai iya kafa rassan asalin a itace zaitun in ba su ci gaba a rashin bangaskiya ba.
Taurarawan da ba mai dawama zai kasance har sai iyakar Al'ummai sun shiga ciki.
Allah ya ci gaba da ƙaunar Isra'ilawa domin kakaninsu, kuma kirar Allah ba ya canja wa.
Allah ya nuna jinkai ga marasa biyayya da kuma Yahudawa da Al'ummai tare.
Ya nuna cewa Yahudawa da Al'ummai tare na da rashin biyayya.
Ba wanda zai iya bincikan huƙuncin Allah ko ya ba shi shawara.
Dukka abubuwa daga Allah ne, ta wurin Allah ne, kuma zuwa Allah ne.
1 Ina rokon ku 'yan'uwa, saboda yawan jinkan nan na Allah, da ku mika jikunanku hadaya mai rai, mai tsarki kuma abar karba ga Allah. wannan itace hidimarku ta zahiri. 2 Kada ku kamantu da wannan duniya, amma ku sami canzawa ta wurin sabunta tunaninku, kuyi haka don ku san abin da ke nagari, karbabbe, kuma cikakken nufin Allah. 3 Don ina cewa, saboda alherin da aka bani, ka da waninku ya daukaka kansa fiye da inda Allah ya ajiye shi; a maimakon haka ku kasance da hikima, gwargwadon yadda Allah yaba kowa bangaskiya. 4 Domin muna da gababuwa da yawa a jiki daya, amma ba dukansu ne ke yin aiki iri daya ba. 5 haka yake a garemu, kamar yadda muke da yawa haka cikin jikin Almasihu, dukkanmu gabobin juna ne. 6 Muna da baye-baye dabam-dabam bisa ga alherin da aka bayar a gare mu. Idan baiwar wani anabci ne, yayi shi bisa ga iyakar bangaskiyarsa. 7 In wani yana da baiwar hidima, sai yayi hidimarsa. Idan baiwar wani koyarwa ce, yayi koyarwa. 8 Idan baiwar wani karfafawa ce, yayi ta karfafawa; Idan baiwar wani bayarwa ce, yayi ta da hannu sake; Idan baiwar wani shugabanci ne, yayi shi da kula; Idan baiwar wani nuna jinkai ne, yayi shi da sakakkiyar zuciya. 9 Ku nuna kauna ba tare da riya ba. Ku Ki duk abin da ke mugu ku aikata abin da ke nagari. 10 Akan kaunar 'yan'uwa kuma, ku kaunaci juna yadda ya kamata; akan ban girma kuma, ku ba juna girma. 11 Akan himma kuma, kada ku yi sanyi; akan ruhu kuma, ku sa kwazo; Game da Ubangiji kuma, ku yi masa hidima. 12 Akan gabagadi kuma, ku yi shi da farin ciki; akan tashin hankali kuma, ku cika da hakuri; akan adu'a kuma, ku nace. 13 Ku zama masu biyan bukatar tsarkaka, ku zama masu karbar baki a gidajenku. 14 Ku albarkaci masu tsananta maku, kada ku la'anta kowa. 15 Ku yi farinciki tare da masu farinciki; Ku yi hawaye tare da masu hawaye. 16 Tunanin ku ya zama daya. Kada tunaninku ya zama na fahariya, amma ku yi abokantaka da matalauta. Kada wani a cikin ku ya kasance da tunanin yafi kowa. 17 Kada ku rama mugunta da mugunta. Ku yi ayukan nagarta a gaban kowa. 18 Ku yi duk abin da za ku iya yi domin ku yi zaman salama tare da kowa. 19 'Yan'uwa, kada ku yi ramako, ku bar Allah ya rama maku. A rubuce yake, "'Ramako nawa ne; zan saka wa kowa,' in ji Ubangiji." 20 "Amma idan makiyin ka na jin yunwa, ba shi abinci ya ci. Idan yana jin kishin ruwa, ba shi ruwan sha. Idan kun yi haka, garwashin wuta ne za ku saka akan duk makiyi." 21 Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta ta wurin yin aikin nagarta.
Bulus ya faɗi yadda ya kamata rayuwar maibi ta kasance da yadda ya kamata masubi su yi bauta.
A nan "'yan'uwa" na nufin 'yan'uwa masubi maza da mata. AT: "'yan'uwa masubi, saboda da matuƙar jinkain da Allah ya ba ku, Ina so ku"
A nan Bulus ya yi amfani da kalman nan "jikuna" don ya na nufin mutum gabaɗayasa. Bulus na kwatanta maibi cikin Alamsihu wanda ke matuƙar biyayya ga Allah da dabbobin da Yahudawa kan yanka su kuma miƙa wa Allah. AT: "miƙa kanku gabaɗaya ga Allah tun kuna raye kamar hadayar da ta mutu a kan bagadin haikali"
Wannan na iya nufin 1) haɗaya wanda ka ba wa Allah kai kaɗai kuma wanda ya faranta masa rai" ko kuwa 2) abar karɓa ga Allah domin mai tsarki ne"
"Wannan hanya ce da ke daidai na yi wa Allah sujada"
Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) "Kada ku yi hali kamar yadda duniya ke yi" ko kuwa 2) "Kada ku yi tunani yadda duniya ke yi"
Wannan na iya nufin 1) "Kada ku bar duniya ta gaya muku abin da za ku yi da kuma tunani" ko kuwa 2) "Kada ku bar kanku ku aikata abin da duniya ke yi."
Wannan na nufin marasa bi da ke rayuwa a wannan duniya.
AT: "amma bar Allah ya canza yadda kuke tunani da kuma halinku"
A nan "alheri" na nufin zaɓen da Allah ya yi wa Bulus ya zama manzo da kuma shugaban ikkilisiya. Ku na iya bayyana wannan a fili cikin juyin ku. AT: "domin Allah ya zaɓe ni in zama manzo"
"cewa kada wani a tsakanin ku ya yi tunani cewa ya fi sauran mutane"
"Amma ku zama da hikima a yadda kuke tunani game da kanku"
Bulus na nufin cewa masubi na ba iyawa daban dabam daidai bisa ga bangaskiyarsu ga Allah. AT: "dashiƙe Allah ya ba wa kowanen ku iyawa daban dabam domin dogararku a gare shi"
Bulus ya yi amfani da wannan kalman don ya nuna cewa yanzu ka zai bayyana dalilin da ya sa kada masubi su yi tunani sun fi sauran mutane.
Bulus ya dubi dukkan masubi cikin Almasihu kamar su gabobi ne na jikin ɗan'adam. Ya yi wannan ne domin ya yi misali cewa ƙodashiƙe masubi na iya yi bautar Almasihu ta hanya daban dabam, kowan mutum na Almasihu ne kuma yana bauta a hanya mai muhimmanci.
Waɗannan abubuwa ne kamar idanu, ciki, da hannaye.
Bulus ya yi magana game da masubi kamar Allah ya haɗa su a gu ɗaya kamar gabobin jikin ɗan'adam. AT: "Allah ya haɗa kowane maibi tare da dukkan masubi"
Bulus ya yi magana game da iyawar daban dabam na masubi kamar kyauta ce daga Allah a yalwace. AT: "Allah ya ba kowanenmu iya na yi abubuwa daban dabam domin sa"
Wannan na iya nufin 1) "sai ya yi annabce annabce ba fiye da bangaskiyar da Allah ya ba shi ba" ko kuwa 2) "sai ya yi annabce annabce da ta yarda da koyarwa ta bangaskiyarmu."
A nan "bayaswa" na nufin ba da kuɗi da wasu abubuwa ga mutane. Ku na iya bayyana ma'anar wanna a fili cikin juyin ku. AT: "In wani na da baiwar bayaswa ta kuɗi ko kuwa wasu abubuwa ga mutanen da cikin bukata"
AT: "Lallai ne ku yi sahilin ƙaunaci mutane da kuma gaskiya"
Kalman da Bulus ya yi amfani da ita anan na nufin irin ƙaunar da ke zuwa daga wurin Allah da ke mayar da hankali ga amfani wasu ko mutum bai sami riba ba.
A nan Bulus ya fara bada tsarin sunayen abubuwa tara, kowanne da sifar "Game da ... zama" don ya gaya wa masubi irin mutane da ya kamata zu zama. Yana iya yiwuwa kuna bukantan juya wasu daga cikin abubuwan kamar "Game da ... yi." Sunayen sun cigaba har zuwa [Romawa 12: 13]
"game da yadda kuke ƙaunar 'yan'uwa masubi"
AT: "nuna ƙauna ga juna"
"Ku daraja da kuma girmama juna" ko kuwa "Ku daraja 'yan'uwan ku masubi ta wurin girmamasu"
"Kada ku zama ragwaye ciki aikin ku, amma ku himmantu ga bin Ruhu da kuma bautar Ubangiji"
"Jira cikin hakuri a duk sa'ad da kuna da damuwa"
Wannan ita ce abu na karshe cikin sunayen abubuwan da ya fara cikin [Romawa 12:9]. "A sa'ad da 'yan'uwa masubi na cikin matsala, ku taimake su da abin da suke bukata"
"Ku marabce su a cikin gidanku a kullayaumi sa'ad da suke bukatan wurin zama"
Wannan wata karin magana ne da nufin rayuwar ɗayantaka. AT: "Ku yarda da juna" ko kuwa "Ku yi rayuwar ɗayantaka da juna"
"Kada ku nuna cewa kun fi wasu muhimmanci"
"ku marabci mutanen da kamar basu da muhimmanci"
"kada ku yi tunani kamar kuna da hikima fiye da kowa kuma"
"Kada ku yi mugayen abubuwa ga wanda ya yi muku mugayen abubuwa"
"Ku yi abubuwan da kowa da duba a matsayin abu nagari"
"ku yi kowane abin da za ku iya yi don ku zauna lafiya da kowa"
A nan "fushi" na nufin hukuncin Allah. AT: "ku bar Allah ya hukunta cu"
AT: "Domin wani ya rubuta"
Waɗannan jimla biyun na nufin abu ɗaya ne a takaice, na kuma nanata cewa Allah zai rama wa mutanensa. AT: "Hakika zan rama maku"
Duk "ka" da "-ka" ga mutum ɗaya ne.
Cikin 12:20 Bulus ya faɗi daga wata bangare ne a Nassin. AT: "Amma Nassin ma ya ce, 'In maƙiyanka na jin yunwa ... kansa'"
"ba shi abinci"
Bulus ya yi magana game da albarkun da miyagu za su samu kamar an zuba garwashin wuta ne a kansu. Wannan na iya nufin 1) "sa mutum da ya yi muku mugunta ya ji ba daɗi game da yadda ya muzguna muku" ko kuwa 2) "ba wa Allah dalilin masananciyar shari'a ga maƙiyinku."
Bulus ya bayana "mugunta" kamar sai ka ce mutun. AT: "Kada ku bar waɗanda ke mugaye su yi nasara da ku, amma ku yi nasara da waɗanda ke mugaye ta wurin aikata nagargarun ayyuka"
Ibada ta ruhaniya na masu bi shi ni miƙa jiki hadaya rayayyiya ga Allah.
Hankalin da ya sãke na sa mai bi ya san abu mai kyau, abun karɓa, da kuma cikaken abin da Allah ya ke so.
Ya kamata kada mai bi ya ɗauke kan shi fiye da yadda ya kamata.
Masu bi jiki ɗaya ne cikin Almasihu, kuma kowanne gaɓar ɗan'uwansa ne.
Kowani mai bi ya yi amfani da baiwar sa gwargwadon bangaskiyarsa.
Masu bi su kasance da ƙaunar juna gaya, da bawa juna girma.
Masu bi su agaji tsarkaka.
Masubi su sa wa masu tsananta musu albarka ba la'ana ba.
Masu bi su karɓe kaskantattun mutane.
In mai yiwuwa ne, mas bi su yi zama lafiya da dukka mutane.
Kada masu bi su ɗau ma kansu ramako, domin ramako na Ubangiji ne.
Masu bi su rinjaye mugunta da nagarta.
1 Bari kowa yayi biyayya da hukuma, saboda babu wata hukuma sai dai in tazo daga Allah; mahukunta da suke nan kuwa daga Allah ne. 2 Saboda da haka duk wanda ya ja hukuma ya ja da dokar Allah; kuma dukan wadanda suka ki hukuma za su sha hukunci. 3 Don kuwa mahukunta ba abin tsoro ne ga masu nagarta ba, amma ga masu aikata laifi. Kuna so ku zama marasa tsoron hukuma? Kuyi abu nagari, zaku sami yabo daga yin hakan. 4 Saboda shi bawan Allah ne a gare ku don nagarta. Amma in kun yi abu mara kyau, kuyi tsoro, saboda ba ya dauke da takobi ba tare da dalili ba. Don shi bawan Allah ne mai saka wa mugu da fushi. 5 Saboda haka dole kuyi biyayya, ba don fushi ba, amma saboda lamiri. 6 Saboda wannan ne kuke biyan haraji. Don masu mulki bayin Allah ne, wadanda suke yin haka kullum. 7 Ku bawa kowa hakkinsa; haraji ga mai haraji; kudin fito ga mai fito; tsoro ga wanda ya cancanci tsoro; girma ga wanda cancanci girmamawa. 8 Kada ku rike bashin kowa, sai dai ku kaunaci juna. Domin duk wanda ya kaunaci dan'uwansa ya cika doka. 9 To, "Kada kuyi zina, kada kuyi kisa, kada kuyi sata, kada kuyi kyashi, idan har akwai wata doka kuma, an takaita ta a wannan jimlar: "Ka kaunaci dan'uwanka kamar kanka." 10 Kauna bata cutar da makwabci. Domin haka, kauna tace cikar shari'a. 11 Saboda wannan, kun san lokaci yayi, ku farka daga barci. Domin cetonmu yana kusa fiye da yadda muke tsammani. 12 Dare yayi nisa, gari ya kusan wayewa. Don haka, sai mu rabu da ayyukan duhu, mu yafa makaman haske. 13 Sai muyi tafiya yadda ya kamata, kamar da rana, ba a cikin shashanci ko buguwa ba. Kada kuma muyi tafiya cikin fasikanci da muguwar sha'awa, ba kuma cikin husuma ko kishi ba. 14 Amma ku yafa Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuwa ku tanadi halin mutumtaka, don biye wa muguwar sha'awarsa.
Bulus ya ga ya wa masubi yadda za su yi rayuwa a karkashin masu mulkinsu.
A nan "rai" na nufin gabaɗayan mutum. "Dukkan maibi ya yi biyayya" ko kuwa "Kowa ya yi biyayya"
"ma'aikatan gwamnati"
domin
"Dukkan iƙo na zuwa daga wurin Allah"
AT: "Mutane masu mulki sun kassancea wurin domin Allah ya sa su a wurin"
"mahukuntan gwamnati" ko kuwa "muhukuntan da Allah ya sa a wurin iƙo"
AT: "Allah zai hukunta waɗanda ke rashin biyayya ga mahukuntan gwamnati"
Masu mulki ba sa sa mutane nagari su ji tsoro.
Ana iya gane mutane ta wurin "nagargarun ayyuka" ko kuwa "mugayen ayyuka"
Bulus ya yi amfani da wannan tambayar don ya ja hankalin mutane su yi tunani game da abin da suna bukata su yi don kada su ji tsoron mahukunta. AT: "Bari in gaya muku yadda za ku zama marasa tsoron mahunta."
Gwamnati sa su faɗa nagargarun abubuwa game da mutanen da ke aikata abu nagari.
AT: "ya na ɗauke da takobi ta dalili nagari" ko kuwa "ya na da iƙon hukunta mutane, kuma shi zai hukunta mutane"
Gwamnatin Romawa na ɗauke da guntun takoni a matsayin alamar ikonsu.
A nan "fushi" na wakilcin hukuncin da mutane za su samu in sun yi mugayen ayyuka. AT: "mutum da ya hukunta mutana na kamar fushin gwamnatin gaba da mugu"
"ba domin kada gwamnati su hukunta ku ba, amma kuwa domin ku samu lamiri mai kyau a gaban Allah"
"Saboda gwamnati na hukunta masu aikata mugunta"
Bulus na magana da masubi ne anan.
"Wannan ita ce dalilin da ya sa ya kamata ku biya haraji: mahukunta"
"tafiyad da" ko kuwa "aiki a kan"
kalman na "biya" an fahimci ta daga jimla na baya. AT: "Biya haraji ga mai haraji, da fito ga mai fito. Wanda suka cancanci ladabi, ladabi da girma ga wanda ya cancanci girmamawa"
A nan biyan tsoro da girma na nufin ladabi da girmamawa ga waɗanda sun cancanci tsoro da girma. AT: "Yi tsoro ga waɗanda sun cancanci tsoro, da girma ga waɗanda sun cancanci girmamawa" ko kuwa "Ladabi ga waɗanda sun cancanci ladabi, da girma ga waɗanda sun cancanci girmamawa"
Wannan wani irin haraji ne.
Wannan korau biyu ne. AT: "Ku biya dukkan bashin da kowa ke bin ku, ku kuma ƙaunaci juna"
Wannan aikatau jam'i ce kuma na nufin dukkan masubi ta Roma.
Wannan ita ce bashi ɗayan da ke nan kamar yadda aka rubuta a baya.
Wannan na nufin irin ƙaunar da ke zuwa daga Allah da ke mayar da hankali ga amfani wasu ko mutum kansa bai sami riba ba.
yi sha'awa samun ko kuwa karban abin da ke na wani
Wannan jimla na ba da hoton ƙauna kamar mutum da ke nuna kirki ga sauran mutane. AT: "Mutanen da ke ƙaunar maƙwabcinsu ba sa cutuar su"
Bulus ya yi magana game da bukatan masubi da ke Roma su canza halinsu, kamar suna bukantan su tashi daga barci ne.
Bulus ya yi magana game da lokaci da mutane ke aikata miyagun ayyuka kamar dare. AT: "Lokacin zunubi ta kusan kai ga karshe" ko kuwa "Ta na nan kamar dare ta kusan kai ga karshe"
Bulus ya yi magana game da lokaci da mutane ke aikata abin da ke daidai kama rana. AT: "lokacin adalci zata fara jim kaɗan" ko kuwa "wato kamar rana za ta yi jim kaɗan"
Bulus ya yi magana game da "ayyukan duhu" kamar sutura ne da mutum ya ajiye a gefe. Anan "rabu da" na nufin cewa a bar yin wani abu. Anan "duhu" na nufin mugu. AT: "Don haka, sai mu bar aikata miyagun abubuwa da mutane ke yi a cikin duhu"
A nan "haske" na nufin abi nagari da kuma daidai. Bulus ya yi magana game da aikata abin da ke daidai kamar yafa makami ne don tsaron mutum da kansa. AT: "Sai mu fara yi abin da ke daidai. Yin haka kuwa zai tsare mu daga abin da ke mugu kamar yadda makami ke tsaron soja"
Bulus ya haɗa da masu karatunsa da sauran masubi tare da kansa kuma.
Bulus ya yi magana game yin rayuwa kamar masubi na gaskiya kamar wani na tafiya ne da rana. AT: "Sai mu yi tafiya cikin haske da sanin cewa kowa na iya ganin mu"
Waɗannan ra'ayin a takaice na nufin abu ɗaya ne. Za ku iya haɗa su a juyin ku. AT: "ayyuka na shashanci"
Wannan na nufin shirya mugunta da kuma musu tare da mutane.
Wannan na nufin jin bacin rai game da wanim nasarar wani ko riba fiye da wasu.
Bulus ya yi magana game da bin halin Almasihu kamar mayafi ne da mutane ke iya gani.
Idan harshen ku na da jam'i na umurni, to sai a yi amfani da ita anan.
A nan "jiki" na nufin halin ta jiki na mutum wanda ke gaba da Allah. Wannan halin zunubi ne na 'yan adam. AT: "ko kaɗan kada ku bar tsohon muguwar zuciyar ku ta samu zarafin aikata muyagun abubuwa"
Allah ne ya naɗa mahukunta a duniya, kuma daga wurin Allah ne suka samu ikonsu.
Waɗanda suke gãba da mahukunta na duniya za su samu hukunci akan su.
Bulus ya ce masu bi su aikata abu mai kyau don haka ba za su ji tsoron masu mulki ba.
Allah ya ba masu mulki iko su yiƙe takobin hukunta masu mugunta.
Allah ne ya ba su ikon karɓar haraji.
Bulus ya ce masu bi su riƙe hakin ƙaunar juna.
Mai bi na cika Shariya ta wurin ƙaunar maƙwabcinsa.
Bulus ya ambata ka da ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kuma kada ka yi ƙyashi, a sashin Shariya.
Bulus ya ce masu bi su kauce wa ayyukan duhu, su kuma ɗauki ɗamarar haske.
Masu bi bai kamata su yi tafiya cikin shashanci da buguwa ba, ko fasikanci da fajirci ba, ko jayayya da kishi ba.
Kada mai bi ya ba da zarafi ga muguwar sha'awa ta jiki.
1 Ku karbi duk wanda yake da rarraunar bangaskiya, ba tare da sukar ra'ayinsa ba. 2 Wani yana da bangaskiyar yaci komai, wani wanda yake da rauni yakanci ganye ne kawai. 3 Kada wanda yake cin komai ya raina wanda baya cin kowanne abu. Kada kuma wanda baya cin kowanne abu ya shara'anta sauran da suke cin komai. Saboda Allah ya karbe shi. 4 Kai wanene, kai wanene da kake ganin laifin bawan wani? Tsayawarsa ko faduwarsa ai hakin maigidansa ne, amma Ubangiji yana da ikon tsai da shi. 5 Wani yakan daukaka wata rana fiye da sauran. Wani kuma yana daukan ranakun daidai. Kowa ya zauna a cikin hakakkewa akan ra'ayinsa. 6 Shi wanda ya kula da wata rana, ya kula da ita don Ubangiji. Kuma wanda yaci, yaci ne domin Ubangiji, domin yana yi wa Allah godiya. Shi wanda bai ci ba, yaki ci ne domin Ubangiji. Shima yana yi wa Allah godiya. 7 Domin babu wanda yake rayuwa don kansa a cikinmu, kuma babu mai mutuwa don kansa. 8 Domin in muna raye, muna raye don Ubangiji. Kuma in mun mutu, mun mutu ne don Ubangiji. Ashe, ko muna raye, ko a mace mu na Ubangiji ne. 9 Domin wannan dalilin Almasihu ya mutu ya kuma tashi, saboda ya zama Ubangiji ga matattu da rayayyu. 10 Amma ku don me kuke shara'anta yan'uwanku? kai kuma don me kake raina dan'uwanka? Dukan mu zamu tsaya gaban kursiyin shari'ar Allah. 11 Domin a rubuce yake, "Na rantse, "inji Ubangiji", kowacce gwiwa zata rusuna mani, kowanne harshe kuwa zai yabi Allah." 12 Domin kowannenmu zai fadi abin da shi yayi da bakinsa a gaban Allah. 13 Saboda da haka kada muyi wa juna shari'a, amma maimakon haka ku dauki wannan kudduri, don kada kowa ya zama sanadin tuntunbe ko faduwa ga dan'uwansa. 14 Na sani na kuma tabbata tsakani na da Ubangiji Yesu, ba abin da yake mara tsarki ga asalinsa. Sai dai ga wanda ya dauke shi marar tsarki ne yake zama marar tsarki. 15 Idan har abincinka na cutar da dan'uwanka, ba ka tafiya cikin kauna. Kada ka lalata wanda Yesu ya mutu domin sa da abincinka. 16 Saboda haka, kada abubuwan da aka dauka kyawawa su zama abin zargi ga wadansu. 17 Saboda mulkin Allah ba maganar ci da sha ba ne, amma game da adalci ne, salama, da farin ciki a cikin Ruhu Mai Tsarki. 18 Domin wanda yake bautar Almasihu a wannan hanya, karbabbe ne ga Allah, kuma jama'a sun yarda da shi. 19 Don haka, mu nemi abubuwa na salama da abubuwan da zasu gina juna. 20 Kada ku lalata aikin Allah don abinci. Komai yana da tsarki, amma kaiton mutumin da yake cin abin da zai sa shi ya fadi. 21 Bashi da kyau a ci nama ko a sha ruwan inabi, ko duk abin da zai jawo faduwar dan'uwanka. 22 Wannan bangaskiyar da kuke da ita, ku adana ta tsakaninku da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa bata da laifi akan abin da hankalinsa ya ga daidai ne. 23 Duk wanda yayi shakka amma kuma yaci, ya sani yayi laifi kenan, domin ba tare da bangaskiya bane. Duk abin da ba na bangaskya bane zunubi ne.
Bulus ya karfafa masubi su tuna cewa amsa wa Allah.
Wannan na nufin waɗanda ji kamar suna da laifi game da ci da kuma shan wasu abubuwa.
"kuma kada ku shara'anta su saboda ra'ayinsu"
A nan "bangaskiya" na nufin yin abin da mutum ya gaskanta cewa Allah ya faɗa masa ya yi.
Wannan na bayana mutumin da ya gaskanta cewa Allah ba ya so ya ci nama.
Bulus ya yi amfani da tambaya don ya sauta wa waɗanda ke shara'anta wasu. Kuna iya juya wannan cikin magana. AT: "Kai ba Allah ba ne, saboda haka ba ba ka izinin shara'anta wani bawansan ba!"
"kai" anan ba mutum fiye da daya ba ne.
Bulus ya yi magana game da Allah sai ka ce shi maigida ne da ke da bayi. AT: "Ai maigidan ne kaɗai ke da iƙo yanke shawara ko zai karbi bawan ko kuwa"
Bulus ya yi magana game da bawan da ke karɓaɓɓe ga Allah kamar kamar an "tsai da shi ne" a maimakon ya faɗi. AT. "Amma Ubangiji zai karɓe shi domin ya na da iƙon mayar da bawan ya zama karɓaɓɓe"
"Wani na tunani rana guda ya fi muhimanci fiye da sauran, amma wani kuma na tunanin dukkan ranaku ɗaya ne"
Ku na iya bayana ma'anar wanna a fili. AT: "Bari kowane mutum ya tabbata cewa abin da yake yi don girmama Ubangiji ne"
A nan "kula" na nufin yin sujada. AT: "Mutumin da ke sujada a rana ta musamman yana yi haka don girmam Ubangiji ne"
kalman nan "kowane abu" an fahimci ta ne daga [Romawa 14: 03]. Ana iya sake nanata ta anan. AT: "mutumin da ke cin kowane irin abinci"
ya ci don girmama Ubangiji" ko "ya ci ta wannan hanyar don ya girmama Ubangiji ne"
Kalman nan "kowane abu" an fahimci ta ne daga [Romawa 14:03]. Anan iya sake nanata ta anan. AT: "Shi wanda ba ya ci kowane abu" ko "Mutumin da ba ya cin wasu iri abinci"
"ya ƙi cin waɗannan abincin don ya girmama Ubangiji ne" ko "ya ci ta haka don ya girmama Ubangiji ne"
A nan "rayuwa don kansa" na nufin rayuwa don faranta wa kansa rai. AT: "Kada mu yi rayuwa don kawai mu farantawa kanmu rai"
Wannan na nufin mutuwar wani ya shafe sauran mutane. AT: "kada mu yi tunanin cewa in mun mutu, mutuwar mu za ta shafe mu kawai ne"
Bulus ya haɗa da masu karatunsa ne.
Ta wurin amfani da waɗannan tambayoyin, Bulus na nuna yadda yana bukata ya sauta wa wasu daga cikin masu karatunsa. AT: "ba daidai ne ka shara'anta ɗan'uwanka ba, kuma ba daidai ne ka raina ɗan'uwanka ba!" ko "ka shara'anta da kuma raina ɗan'uwanka!"
A nan wannan na nufin 'yan'uwa masubi, maza ko kuwa mata.
"Kursiyin shari'a" na nufin iƙon Allah don shari'a. AT: "Gama Allah zai shara'anta mu dukka"
AT: "Gama wani ya rubuta cikin Nassin: 'kamar"
An yi amfani da maganannan don a fara ransuwa ko kuwa alkawari. AT: "Ku tabbata cewa wannan gaskiya ne"
Bulus ya yi amfani da kalmomin nan "gwiwa" da "harshe" do yana nufin mutum gabaɗayansa. Haka kuma, Ubangiji ya yi amfani da kalman nan "Allah" don ya na nufin kansa. AT: "kowane mutun zai rusuna ya kuma miƙa yabo zuwa a gare ni"
"lallai ne ya yi bayanin halayensa ga Allah"
A nan "sanadin tuntuɓe" da "faduwa" a takaice na nufin abu ɗaya ne. AT: "maimakon haka bari ya zama maƙasudinku kada ku yi ko ku faɗa wani abin da zai iya sa ɗan'uwa maibi ya yi zunubi"
A nan kalmomin nan "sani" da "na tabbata" a takaice na nufin abu ɗaya ne; Bulus ya yi amfani da su don ya nanata tabbacinsa ne. AT: "Na hakikance saboda ɗangantakana da Ubangiji Yesu"
Za a iya juya wannan cikin tabbataciyar magana. AT: "kowane abu kanta mai tsarki ne"
"ga asalin ta" ko kuwa "saboda abin da ta ke"
A nan Bulus na nufin cewa mutum ya yi nesa da kowane abin da yake tunani marar tsarki ne. Kuna iya bayana wannan a fili cikin juyin ku. AT: "Amma in mutum na tunanin cewa wani abu marar tsarki, to ga wannan mutum abin marar tsarki ne saboda haka sai ya yi nesa da shi"
"Idan ka cutar da bangaskiyar ɗan'uwanka mai bi a kan zancen abinci." Anan kalman nan "ka" na nufin waɗanda ke da ƙarfi cikin bangaska "'ɗan'uwa" na nufin waɗanda ke raunana cikin bangaskiya.
Bulus ya yi magana game da halin masubi kamar tana tafiya. AT: "saboda haka ba ka nuna ƙauna"
"Idan wani na tunani cewa wani abu na zargi ne, to kada ka aikata shi, ko ka ɗauka kyakkyawa ne"
Bulus na cewa Allah ya kafa mulkinsa don ya ba mu ɗangantaka mai kyau da kansa, ya kuma yi tanaɗin salama da farin ciki. AT: "Gama Allah ba kafa mulkinsa saboda ya yi mulki kan abin da muke ci ko sha ba. Ya kafa mulkinsa ne saboda mu samu ɗangantaka ma kyau da shi, ta haka kuma zai ba mu salama da farin ciki"
AT; "mutane za su amince da shi" ko kuwa "mutane za su ba shi girma"
A nan "gina juna" na nufin taimakon juna don girma cikin bangaskiya. AT: "Sai mu nemi rayuwan zaman salama tare da kuma taimakon juna don girma da ƙarfi cikin bangaskiya"
Ku na iya bayana ma'anar wannan jimlar a fili. AT: "Kada ka warware abin da Allah ya yi wa ɗan'uwa maibi wai domin ka na so ka ci wani irin abinci"
A nan abin da ke "sa shi tuntuɓe" na nufin ta na sa ɗan'uwa raunana ya yi abin da lamirinsa bai amince da shi ba. AT: "amma zai zama zunubi in wani ya ci abincin da wani ɗan'uwa ke tunanin cewa ba daidai ne a ci ba, idan ta wurin ci wannan ya sa ɗan'uwa raunana ya yi abinda lamirinsa ba amince ba"
"Zai fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuwa ka yi wani abu da zai iya sa ɗan'uwanka zunubi"
Wannan na nufin mai ƙarfin cikin bangaskiya, "ɗan'uwa" na nufin raunana cikin bangaskiya.
Wannan na nufin imani game da ci da sha.
mufuradi. Domin Bulus na magana da masubi, mai yiwuwa ya zama lallai ku juya wannan ta wurin amfani da jam'i.
"Albarka ta tabbata ga waɗanda ba sa zargin kansu don abin da sun amince za su aikata"
AT: "Allah zai ce da wannan mutum ya yi abin da ba daidai ba in har bai tabbata ko daidai ne ya ci wani irin abinci ba, amma ya ci" ko kuwa "Mutumin da bai tabbata ko daidai ne a ci wani irin abinci ba, amma ya ci ko ta wace hanya zai sami damuwa cikin lamirinsa"
Kowane abin da "ba daga bangaskiya ba" wannan abu ne wanda Allah ba ya so ka yi. Ku na iya bayana ma'anar wannan a fili anan. AT: "Allah zai ce da cewa ba yi daidai ba domin yana ci abin da ya bada gaaskiya Allah ba ya son sa da ci"
kowane abin da "ba na bangaskiya ba" abu ne wanda Allah ba ya so ka yi. Ku na iya bayana ma'anar wannan a fili anan. AT: "ka na zunubi idan ka yi wani abin da ba ka gaskanta cewa Allah na so ka yi ba"
Mutum mai bangaskiya mai karfi na cin komai, amma mutu wanda na da rarrauna bangaskiya na cin kayan gona.
Kada masu bi da suka bambanta wajen abun da suke ci su raina ko shariyartar da juna.
Allah ya ƙarɓe wanda yana cin komai da wanda yana cin iyakar kayan gona kadai.
Bulus ya yi magana game da amincewa wani wai wani rana ya fi wani ko dukka ranaku ɗaya ne.
Masu bi na rayuwa har da mutuwa domin Ubangiji ne?
Dukka masu bi za su tsaya a gaban kursiyin shariya r Allah.
Kada wani ɗan'uwa ya sa dutsen tuntuɓe ko tarko wa wani game da abun da ya amince.
Bulus ya tabbata cewa ba wani abinci da mara tsarki.
Mulkin Allah na game da adalci, salama, da kuma farin ciki cikin Ruhu mai Tsarki.
Bulus ya ce zai yi kyau kada ɗan'uwan nan ya ci nama ko sha ruwan inabi a gaban wani ɗan'uwan da baya ci.
Kowani ayyuka zunubi ne idan ba tare da bangaskiya.
1 Yanzu mu da muke da karfi ya kamata mu dau nauyi raunana, kuma bai dace mu nuna son kai ba. 2 Bari kowannenmu ya faranta wa makwabcinsa rai, domin wannan yana da kyau, don a gina shi. 3 Domin Almasihu bai faranta wa kansa rai ba. Kamar yadda aka rubuta, "zagin da wadansu suka yi masa ya sauka a kaina." 4 Don abin da aka rubuta a baya an rubuta ne domin a gargade mu, domin ta hakuri da karfafawar litattafai mu sami karfi. 5 Yanzu Allah mai hakuri da karfafawa ya baku zuciya daya ta zaman tare da juna bisa ga halin Yesu Almasihu. 6 Domin ya yi haka ne da zuciya daya domin ku yi yabo da bakinku daya. 7 Domin ku karbi juna, kamar yadda Yesu ma ya karbe ku domin a daukaka Allah. 8 Saboda na ce an mai da Almasihu bawan kaciya a madadin gaskiyar Allah. Ya yi wannan ne don a tabbatar da alkawarai da aka ba kakanin kakaninmu. 9 Domin Al'umai su daukaka Allah saboda jinkansa, kamar yadda ya ke a arubuce, "Domin ta haka zan yabe ka cikin Al'umai in yi wakar yabon sunanka." 10 Kuma an ce. "Ku yi faranciki, ku Al'ummai tare da mutanensa." 11 Kuma." Ku yabi Ubangiji, ku dukan Al'ummai; bari dukan mutane su yabe shi." 12 Kuma, Ishaya ya ce "Za a sami tsatson Yessi, wanda zai tashi ya yi mulki a kan Al'umai, Al'umai za su sami karfin hali a cikinsa." 13 Yanzu Allah mai karfafawa ya cika ku da dukkan farin ciki salama, saboda da bangaskiyarku, domin ku sami cikkakiyar karafafawa, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki. 14 Ni kaina na amince da ku, yan'uwa. Kuma na amince cewa ku da kanku kuna cike da alheri, cike da dukkan sani. Na amince cewa za ku sami zarafi ku gargadi juna. 15 Amma ina rubuta maku da gabagadi kan wadansu abubuwa, domin in tunasheku, saboda baiwar da aka bani daga wurin Allah. 16 Cewa baiwar ta sa na zama bawan Almasihu Yesu da aka aika ga Al'ummai, limami na bisharar Allah. Zan yi wannan saboda baikon Al'ummai ya zama karbabbe, kuma kebbabe ga Allah ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 17 Don haka ina jin dadi cikin Yesu Almasihu da abubuwa na Allah. 18 Domin ba ni da abin da zan ce, sai abin da Yesu ya aikata ta wurina, domin Al'ummai su yi biyayya ta magana da aiki. 19 Ta wurin alamu, da al'jibai, da ikon Ruhu Mai Tsarki. Daga Urushalima, da kewaye har zuwa Ilirikum, an kai bisharar Almasihu ko'ina dukka. 20 A cikin hanyar nan, burina in sanar da bishara, amma a inda ba a san Yesu ta wurin sunansa ba, don kada in sa gini akan harshashi wani. 21 Kamar yadda yake a rubuce."Wadanda ba a taba fada wa labarinsa ba, su gane. Wadanda ba su taba jin labarinsa ba su fahimta." 22 Saboda an hana ni zuwa wurin ku a lokatai da dama. 23 Amma yanzu bani da sauran wani wuri a lardin nan, kuma cikin shekaru masu yawa ina da marmarin in zo wurin ku. 24 Duk lokacin da zan tafi Asbaniya ina begen ganin ku yayin wucewa, don ku raka ni bayan na ji dadin zama da ku na dan lokaci. 25 Amma yanzu ina tafiya Urushalima don in yi wa tsarkaka hidima. 26 Domin abin farinciki ne ga mutanen Makidoniya da Akaya su yi bayarwa domin gajiyayyu masu bada gaskiya wadanda suke a Urushalima. 27 Suna jin dadi domin hakika kamar bashi ne a kansu. Domin Al'ummai sun yi tarayya da su cikin ayyukan ruhaniya, ya zama hakki a kansu su ma su taimake su da abubuwa. 28 Domin lokacin da na gama basu kudin, zan zo gareku a hanyata ta zuwa Asbaniya. 29 Na san cewa lokacin da na zo gareku, zan zo da cikakkun albarku na Almasihu. 30 Yanzu ina rokonku, yan'uwa, ta wurin Ubangiji Yesu Almasihu, da kaunar Ruhu Mai Tsarki, ku yi ta fama tare da ni a cikin yin addu'o, inku ga Allah saboda ni. 31 Kuyi haka saboda in tsira daga wadanda suke masu biyayya ga Yahudiya, domin kuma hidimata saboda Urushalima ta zama karbabbiya. 32 Ku yi addu'a cewa in zo wurinku da farinciki ta wurin nufin Allah, cewa tare da ni da ku, mu sami hutu. 33 Allah na salama ya kasance tare da ku duka. Amin.
Bulus ya gama wannan sashin game da rayuwar masubi don wasu ta wurin tunashe su yadda Almasihu ya yi rayuwa.
Ku juya wannan ta wurin yin amfani da kalmomin da ake amfani da shi a harshen don gabatar sabuwar zance.
Anan "karfi" na nufin mutanen da ke da karfi cikin bangaskiyarsu. Sun gaskanta cewa Allah ya ba su iznin cin kowane irin abinci. AT: "mu da muke da karfin cikin bangaskiya"
Wannan na nufin Bulus, masu karatunsa da kuma sauran masubi.
A nan "raunanan" na nufin mutanen da ke raunana cikin bangaskiyar. Sun gaskanta cewa Allah bai yarda musu su ci wasu irin abinci. AT: "waɗanda ke raunana cikin bangaskiya"
Ta wurin wannan, Bulus na nufin karfafa bangaskiyar wani. AT: "a karfafa bangaskiyarsa"
A nan Bulus na nufin nassin da Almasihu
Zagin da waɗansu suka yi wa Allah ya sauka a kan Almasihu.
AT: "Don a dã, annabawa sun rubuta kome cikin Nassosin don su koya mana"
Bulus ya haɗa masu karatunsa da suaran masubi.
A nan "sami gabagadi" na nufin cewa masubi za su san cewa Allah zai cikata alkawarensu. Za ku iya bayana ma'anar a fili cikin juyin ku. AT: "ta haka nassosin za su karfafa mu mu sa sammanin cewa Allah zai yi mana kowane abin da ya alkawarta"
"addu'a ta ita ce ... Allah ... zai yi"
A nan zama da "zuciya ɗaya" na nufin a yarda da juna. AT: "yarda da juna" ko "zama ɗaya"
Wannan na nufin a zama ɗaya cikin yabon Allah. AT: "yabe Allah tare cikin ɗayantaka kamar baki ɗaya ke magana"
"karɓi juna"
Kalman "na" na nufin Bulus.
A nan "mai kaciya" na nufin Yahudawa. AT: "Yesu Almasihu ya zama bawan Yahudawa"
Waɗannan ne makasuɗi biyu da ya sa Almasihu ya zama bawa ga masu kaciya. AT: "domin a tabbatar da alkawaren ... da kuma domin Al'umai su ɗaukaka Allah saboda jinkansa"
A nan "ubannin" na nufin kakkanin mutanen Yahudawa. AT: "alkawaren da Allah ya ba wa kakkanin Yahudawa"
AT: "kamar yadda wani ya rubuta cikin nassosin"
A nan "sunanka" na nufin Allah. AT: "yi maka wakar yabo"
"Kuma nassin ya ce"
Wannan na nyfin mutanen Allah. Ku na iya bayana wannan a fili cikin juyinku. AT: "tare da mutenen Allah"
"yabe Ubangiji"
Yessi uban Sarki Dauda ne a jiki. AT: "zuriyar Yessi"
A nan "sa" na nufin zuriyar Yessi, Mai Ceton. Waɗanda ba Yahudawa za su yarda cewa shi zai cika alkawarensa. AT: "Mutanen da ba Yahudawa ba ba za su iya yarda da shi cewa zai yi abin da ya alkawarta"
Bulus ya zuguiguta anan don ya nanana nufinsa. AT: "cika ku da matuƙar farin ciki da salama"
Bulus ya tabbata cewa masubi a Roma na girmama juna cikin halayensu. AT: "Ni kaina na tabbata babu shakka cewa ku kanku kun yi wa juna abu mai kyau ta hanya mai kyau"
A nan wannan na nufin 'yan'uwa masubi, duk mazaje da mataye.
Bulus anan ya nanata ainihin nufinsa. AT: "cika da cikakkiyar sani don bin Allah"
A nan "gargaɗi" na nufin a koyar. AT: "kuma iya koyar da juna"
Bulus ya yi magana game da alheri kamar kyauta a jiki da Allah ya ba shi. Allah ya zaɓi Bulus ya zama manzo ko dashiƙe ya tsanantawa masubi kafin ya zama mai bin Yesu. AT: "alherin da Allah ya ba ni"
Bulus ya yi magana game da wa'azin bisharasa kamar shi, a matsayin firist, yana mika baiko ga Allah. AT: "Al'ummai sun farantawa Allah rai a sa'ad da sun yi masa biyayya"
A nan "Waɗanan abubuwan" na nufin abin da Almasihu ya yi ta wurin Bulus. AT: "Saboda biyayyar Al'ummai, zan yi magana game da abin da Almasihu ya yi ta wurin na cikin furuci da aikatawa da kuma ta wurin iƙon alamu da al'ajibai ta wurin iƙon Ruhu Mai Tsarki"
Waɗannan kalmomin biyu a takaice na nufin abu ɗaya na kuma nufin iri iri al'ajibai.
Wannan daga birnin Urushalima har zuwa nesa da lardin Ilirikum, wani wuri kusa da Italiya.
Bulus na so ya yi wa'azi ga mutanen da ba su taba ji game da Almasihu ba. AT: "Saboda wannan, ina so in yi wa'azin bishara a wuraren da mutane ba su taba ji game da Almasihu ba"
Bulus ya yi magana game da aikinsa kamar yana gini ne kan harshashi. AT: "don kada in cigaba da aikin da wani ya riga ya fara. Ba na so in zama kamar mutum wanda ya yi ginin gida kan harshashin wani"
A nan Bulus na nufin abin da Ishaya ya rubuta cikin nassosin. Ana iya bayyana ma'anar wannan a fili. AT: "Abin da ke faru daidai ne kamar abin da Ishaya ya rubuta cikin nassosin"
A nan Bulus ya yi magana game da "bushăra" ko sako game da Almasihu kamar rayayye ne kuma na iya tafiya da kanta. AT: "Waɗanda ba wanda ya taɓa faɗa wa labari game da shi"
AT: "sun kuma hana ni" ku kuwa "mutane kuwa sun hana ni"
Bulus na nufin cewa babu wani wurin a waɗannan yankunan da mutane ke rayuwa da ba su ji game da Almasihu ba. AT: "babu waɗansu wuraren cikin waɗannan yankunan da mutane ba su ji game da Almasihu ba"
Wannan lardin roma ne ta yammancin Roma inda muraɗin Bulus ne ya yi ziyara.
"a sa'ad da Ina wucewa cikin Roma" ko kuwa "a sa'ad da ina hanya ta"
A nan Bulus na nufin cewa yana so masubi da ke Roma su yi masa tanaɗin wasu kuɗi don tafiyarsa"
"na ji daɗin zama da ku na dan lokaci" ko kuwa "na ji daɗin ziyartanku"
A nan kalmomin nan "Makidoniya" da "Akaya" na nufin mutanen da ke rayuwa a waɗannan wurare. AT: "masubi a lardin Makidoniya da Akaya sun yi murna"
"Masubi da ke a Makidoniya da Akaya sun ji daɗin aikata ta"
"haƙika mutanen Makidoniya da Akaya su kamar bashi ne ga masubi da ke Urushelima"
"dashiƙe Al'ummai sun yi tarayya da su cikin ayyukan ruhaniyan masubi da ke Urushalima, Al'ummai na da bashin bauta ga masubi da ke Urushalima.
Bulus ya yi magana game da kuɗin da zai kai Urushalima kamar 'ya'yan itace ne da ya karɓa daga wurin su. AT: "cikin koshin lafiya ya kai wannan baikon zuwa gare su"
Wannan magana na nufin cewa Almasihu zai albarkaci Bulus da Masubi da ke Roma. AT: "Na kuma sani cewa sa'ad da na ziyarce ku, Almasihu zai albarkace mu a yalwace"
"Ina karfafa ku"
"ku nace" ko "ku yi gwagwarmaya"
AT: "Allah zai kubutar da ni daga waɗanda suke rashin biyayya" ko "Allah zai sa waɗanda suke rashin biyayya su yi nesa don kada su yi mini lahani"
Anan Bulus ya bayana muraɗin sa cewa masubi da ke Urushalima za su karɓe kuɗin da ya kawo daga masubi da ke Makidoniya da Akaya da farin ciki. AT: "addu'a ta ita ce masubi da ke Urushalima za su karɓi kuɗin da na kawo musu da farin ciki"
"Allahn na salama" na nufin Allahn da ke sa masubi su sami salamar zuci. AT: "Ina addu'a cewa Allah wanda ya sa dukkanmu mu sami salamar zuci"
Masu bi da suke ƙarfafa su ɗauki nauyin waɗanda suke rarrauna cikin bangaskiya domin su gina su.
Almasihu bai yi rayuwa domin kanshi ba, sai dai yi wa wasu hidima.
An rubuta nassi a baya domin umurninmu.
Bulus na so masu bi su kasance da zuciya ɗaya da juna.
Almasihu bai yi rayuwa domin kanshi ba, sai dai yi wa wasu hidima.
Nassoshin sun ce Al'ummai zasu yi murna su kuma yabe Ubangiji.
Masu bi zasu cika da murna da salama, za su kuma kasance da aminci.
Hidimar Bulus shi ne ya zama bawan da AlmasihuYesu zuwa ga Al'ummai
Almasihu ya yi amfani da Bulus ta wurin kalma da ayyuka, ta wurin ikon al'ajabai da mu'ajuzai, da kuma ta wurin ikon Ruhun Mai Tsarki.
Bulus na so ya yi shelar bishara a inda ba san Almasihu ba.
Bulus na shirin tafiya zuwa Andalus, ta wannan ne zai samu damar zuwa Roma.
Yanzu Bulus na tafiya Urshalima ne domin yi wa masu bi hidima.
Al'ummai masu bi na da haƙin Yahudawa masu bi na kaya jiki a kansu domin Al'ummai masu bi sun samu daga cikin kayan ruhaniya na Yahudawa masu bi.
Bulus na so a cece shi daga waɗanda suke rashin biyayya a Yahudia.
1 Ina gabatar muku da fibi 'yar'uwarmu, wanda take hidima a Ikilisiya dake cikin Kankiriya. 2 Domin ku karbe ta cikin Ubangij. A hanyar da ta dace ga masu bada gaskiya, ku tsaya tare da ita cikin kowacce bukata. Domin ita da kanta ta zama da taimako ga masu yawa, har da ni ma. 3 Ku gai da Bilkisu da Akila abokan aiki cikin Yesu Almasihu. 4 Wadanda sabo da ni suka sadaukar da ransu. Ina godiya garesu, ba ni kadai ba, amma kuma da dukan Ikilisiyoyin Al 'mmai. 5 Gaida Ikilisiya da ke gidansu. Ku gai da Abainitas kaunataccena. Wanda shi ya fara bada gaskiya ga Almasihu a Asiya. 6 Ku gai da Maryamu, wadda ta yi maku aiki tukuru. 7 Ku gai da Andaranikas da Yuniyas, yan'uwana da abokan kurkukuna. Su sanannu ne cikin manzani, wadanda suke cikin Almasihu kafin ni. 8 Ku gai da Amfiliyas kaunatace na cikin Ubangiji. 9 Ku gai da Urbanas abokin aikinmu cikin Almasihu, da Istakis kaunataccena. 10 Ku gai da Abalis amintacce cikin Almasihu. Ku gai da wadanda su ke gidan Aristobulus. 11 Ku gai da Hirudiya, dan'uwa na, da wadanda ke gidan Narkissa, wadanda ke cikin Ubangiji. 12 Ku gai da Tarafina daTarafusa, masu aikin Ubangiji. 13 Ku gai da Barsisa kaunatacciya, wadda ta yi aikin Ubangiji da yawa. Ku gai da Rufas zababbe cikin Ubangiji da mamarsa da ni. 14 Ku gai da Asinkiritas da Filiguna da Hamis da Baturobas da Hamisu da kuma yan'uwa da ke tare da su. 15 Ku gai da Filolugus daYuliya da Niriyas da yan'uwansa, da Ulumfas da kuma dukan tsarkaka da ke tare su. 16 Ku gaggai da juna da tsatsarkar sumba. Dukan Ikilisiyoyin Almasihu na gaishe ku. 17 Yanzu ina rokon ku, yan'wa, ku yi tunani fa game da masu kawo rabuwa da tuntube. Sabanin koyarwar da ku ka koya. Ku yi nesa da su. 18 Domin irin mutanen nan ba sa bauta wa Ubangiji Yesu, sai dai tumbinsu. Ta dadin bakinsu suke rudin zuciyar marasa laifi. 19 Domin rayuwar biyayyarku takai ga kunnen kowa, na yi farin ciki da ku, amma ina so ku zama da hikima game da abin ya ke mai kyau, ku zama marasa laifi ga abin da ke na mugunta. 20 Allah na salama zai sa ku tattake Shaidan da sauri kalkashin sawayen ku. Alherin Ubangijin mu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku. 21 Timoti abokin aikina, yana gaishe ku, haka Lukiyas da Yason da Susibataras da kuma yan'uwana. 22 Ni Tartiyas wanda ya rubuta wasikan nan, na gaisheku cikin Ubangiji. 23 Gayus mai masaukina da kuma dukan Ikilisiya, suna gaishe ku. Arastas ma'ajin birni na gaishe ku, da Kwartus dan'uwanmu. 24 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku dukka. Amin. 25 Yanzu ga wanda ke da Ikon karfafa ku bisa ga bisharata da wa'azin Yesu Almasihu, wanda ta gare shi ne aka bayyana asiran nan da suke boye tun da dadewa, 26 amma yanzu sanannu ne ta wurin litattafan Annabawa bisa umarnin Allah madauwami, domin biyayyar bangaskiya cikin Al'ummai dukka. 27 Ga Allah mai hikima kadai, ta wurin Yesu Almasihu daukaka ta tabbata har abada. Amin.
Bulus ya gaishe da masubi da yawa dake Roma ta wurin ambata suna.
"Ina so ku ba wa Fibi girma"
Wannan suna ce na ta mace.
Kalman "mu" na nufin Bulus da dukkan masubi. AT: "'yar'uwarmu cikin Almasihu"
Wannan a dă wurin jirgin ruwa ne a birnin Hellas.
Bulus ya karfafa masubi da ke Roma da su marabci Fibi kamar 'yar'uwa maibi. AT: "marbce ta domin dukkan mu na Ubangiji ne"
"Ta hanyar da masubi ya kamat su marabci sauran masubi"
Bulus ya karfafa masubi da ke a Roma cewa su ba wa Fibi kowane abu da take bukata. AT: "taimake ta tawurin ba ta kowane abin da take bukata"
"taimake mutane da yawa, ta kuma taimake ni"
Biriska matan Akila.
"abokan aikin" Bulus mutane ne wanda suna gaya wa mutane game da Yesu. AT: "wanda muke aikin gaya wa mutane game da Almasihu Yesu tare"
"Gaida masubi da ke taruwa su yi sujada a gidansu"
Wannan sunan na miji ne.
Bulus ya yi magana game da Abainitas kamar shi 'ya'yan itace ne da aka girba. AT: "mutum na farko a ƙasar Asiya da ya bada gaskiya da Yesu"
Wannan sunan mace ce.
Waɗannan sunayen maza ne.
Wannan na iya zama 1) Yuniyas sunan mace ce, ko, ba kamar haka ba, 2) Yuniyas, sunan na miji ne.
AT: "Manzannan sun san su kwarai da gaske"
"abokai na ƙaunatattu da 'yan'uwa masubi"
Waɗannan sunayen maza ne.
Kalman nan "amintacce" na nufin wani wanda aka gwada shi an kuma tabbatar cewa shi na ƙwarai ne. AT: "wanda Almasihu ya amince"
Wannan na nufin waɗanda sun dogara ga Yesu. AT: "wanda ke masubi" ko "wanda ke na Ubangiji"
Waɗannan sunayen mata ne.
Waɗannan sunayen maza.
AT: "wanda Ubangiji ya zaɓa"
Bulus ya yi magana game da uwar Rufas karma uwarsa ce. AT: "uwa tasa, wanda ni ma ina tunanin ta kamar uwa ta" (Dubi:
A nan wannan na nufin 'yan'uwa masubi, mazaje da mataye dukka.
Waɗannan sunayen maza ne.
Sunan mace ce. Yuliya mai yiwuwa matar Filolugus.
nuna so ga 'yan'uwa masubi
A nan Bulus ya yi magana ta gabaɗaya game da Ikkilisiyoyin Almasihu. AT: "Masubi cikin dukkan ikkilisiyoyin fa ke wannan yanki na mika sakon gaisuwarsu zuwa gare ku"
"yi hankali da"
Wannan na nufin waɗanda ke musu suna kuma hana wasu dogara ga Yesu. AT: "masu sa masubi musu da juna da kuma rashin bada gaskiya ga Allah"
"Su na koyar da abubuwan da bai yi daidai da gaskiyar da kuka koya ba"
"Yi Nesa" anan na nufi "ƙin kassa kunne." AT: "Kada ku kassa kunne a gare su"
Kalmomin nan "suna bautawa", an fahimci ta daga magana da ke a baya. Wannan ana iya bayana ta cikin wata jimla dabam. AT: "Maimakon haka, su na bauta wa cikinsu"
Kalmomin nan "romon" da "flattering" a takaice na nufin abu ɗaya ne. Bulus na nanata yadda waɗannan mutane de ruɗin masubi. AT: "Ta wurin faɗin abubuwan da ke kamar mai kyau da kuma gaskiya"
A nan "zuciya" na nufin tunanin mutum ko kuwa cikin sa. AT: "sun ruɗe masubi marasa laifi"
Wannan na nufin waɗanda ke da sauƙin kai, marasa azanci da butulci. AT: "marasa azancin da suka dogara a gare su" ko "waɗanda ba su sani cewa waɗannan malaman na ruɗin su ba"
A nan Bulus ya yi magana game da biyayyar masubi da ke a Roma kamar mutum ne da zai iya zuwa wurin mutane. AT: "Don kowa ya ji yadda ku ke biyayya ga Yesu"
Maganar nan "tattake ... a karkashin sawayen ku" na nufin matuƙar nasara kan maƙiyi. Anan Bulus ya yi magana game da nasara kan Shaidan kamar masubi da ke Roma na tattake maƙiyi da karkashin sawayensu. AT: "Allah zai ba ku salama da matuƙar nasara kan Shaidan ba da jimawa ba"
"ba haɗa kai da miyagun abubuwa"
Waɗannan sunayen mazaje ne.
Tartiyas shine wanda ya rubuta abin da Bulus ya faɗa.
"gaisheku kamar ɗan'uwan maibi"
Waɗannan sunayen mazaje ne.
Wannan na nufin Gayus, mutumin da Bulus da 'yan'uwa masubi na taruwa don sujada a gidansa.
Wannan mutum ne wanda ke kula da kuɗaɗen kungiya.
A nan kalman nan "yanzu" alamace ta ƙarshen bangaren wasiƙa. Idan ku na da wata hanya na yin wannan a harshen ku, kuna iya amfani da ita ana.
Bulus ya yi magana game da samun bangaskiya mai karfi kamar mutum ne da ke tsaye a maimakon faɗiwa. AT: "a sa bangaskiyarku ta yi karfi"
"ta wurin bisharar da na yi wa'azinta game da Yesu Almasihu"
Bulus ya ce cewa Allah ya bayyana gaskiyar da aka ɓoye a dă ga masubi. Ya yi magana game da waɗannan gaskiyar kamar wata asiri ne. AT: "somin Allah ya bayyana asirin da ya ajiye tun dă ga masubi"
Aikatau nan "sananne" da "bayyana" a takaice na nufin abu ɗaya. Bulus ya yi amfani da su dukka don ya nanata ainihin maganarsa. Ku na iya haɗa waɗannan kalmomin. AT: "amma yanzu Allah madawwami ya sa ta ta zama sananne ga dukkan Al'ummai ta wurin rubuce rubucen annabawa"
A nan "biyayya" da "bangaskiya" sunaye ne. Ku na iya amfani da aikatau na "biyayya" da "dogara" cikin juyin ku. Ya kamata ku bayyana shi wanda zai yi biyayya ya kuma dogara. AT: "domin dukkan Al'ummai za su yi biyayya ga Allah domin sun dogara a gare shi"
A nan "ta wurin Yesu Almasihu" na nufin abin da Yesu ya yi. A bada "ɗaukaka" na nufin yabo ga Allah. AT: "Saboda abin da Yesu Almasihu ya yi mana, za mu yabe shi kaɗai wanda shi ne Allah, shi kaɗai kuma mai hikima. Amin"
'Yar'uwa Fibi ta zama mataimakiya na Bulus da sauran mutane dayawa.
A baya, Bilkisu da Akila sun kasai da ransu domin Bulus.
Masu bi a ROma da haduwa a gidan Bilkisu da Akila.
A baya, Andaranikas da Yuniyas na tare da Bulus a kurkuku.
Masu bi suna gai da juna da tsattsarkar sumba.
Bulus ya ce wa Masu bi su rabu da masu kawo tsatsaguwa da sa tuntunɓe.
Wasu su saɓanin koyarwar da kuka koya, suke yaudarar masu sauƙin kai.
Bulus na so masu su kasance da hikima wajen nagarta, ya kuma ba ruwansu da mugunta.
Allah mai ba da salama zai tattaka Shaiɗan a karkashin kafafun masu bi.
Tartiyas ne asalin wadda rubuto wannan wasika.
Arastas shi ne ma'ajin garin.
Yanzu Bulus na wa'azin bayyanuwae bisharar Yesu Almasihu.
Bulus na wa'azin biyayya na bangaskiya a cikin Al'ummai.
1 Bulus, kirayayye daga Almsihu Yesu don zama manzo ta wurin nufin Allah, da dan'uwanmu Sastanisu, 2 zuwa ga Ikilisiyar Allah da ke korinti, zuwa ga wadanda aka kebe su cikin Almasihu Yesu, wadanda aka kira domin su zama al'umma maitsarki. Muna kuma rubuta wa dukan masu kira bisa sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a ko'ina, wato Ubangijinsu da Ubangijinmu kuma. 3 Bari alheri da salama su zo gare ku daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu. 4 Kodayaushe ina gode wa Allahna domin ku, saboda alherin Allah da Almasihu Yesu ya yi maku. 5 Ya ba ku arziki ta kowace hanya, cikin dukkan magana da dukkan ilimi. 6 Kamar yadda shaida game da Almasihu ta tabbata gaskiya a tsakaninku. 7 Saboda haka baku rasa wata baiwa ta ruhaniya ba yayinda kuke marmarin jiran bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 8 Zai kuma karfafa ku zuwa karshe, saboda ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 9 Allah mai aminci ne shi wanda ya kira ku zuwa zumunta ta Dansa, Yesu Almasihu Ubangijimu. 10 Ina rokon ku, yan'uwa, cikin sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku yarda da juna, kada tsattsaguwa ta kasance tsakanin ku. Ina rokon ku ku zama da zuciya daya da kuma nufi daya. 11 Gama mutanen gidan Kulowi sun kawo kara cewa akwai tsattsaguwa a cikin ku. 12 Ina nufin: kowannen ku na cewa, "Ina bayan Bulus," ko " Ina bayan Afollos," ko "Ina bayan Kefas," ko "Ina bayan Almasihu." 13 Almasihu a rarrabe yake? An gicciye Bulus domin ku? Ko an yi maku baftisma a cikin sunan Bulus? 14 Na godewa Allah domin ban yi wa wanin ku baftisma ba, sai dai Kirisfus da Gayus. 15 Na yi wannan saboda kada wani ya ce an yi maku baftisma a cikin sunana. 16 (Na kuma yi wa iyalin gidan Sitifanas baftisma. Banda haka, ban sani ko na yi wa wani baftisma ba.) 17 Gama Almasihu bai aiko ni domin yin baftisma ba, amma domin yin wa'azin bishara. Bai aiko ni domin in yi wa'azi da kalmomin hikimar mutum ba, saboda kada giciyen Almasihu ya rasa ikonsa. 18 Gama wa'azin gicciye wauta ne ga wadanda su ke mutuwa. Amma cikin wadanda Allah ke ceto, ikon Allah ne. 19 Gama a rubuce yake, "Zan watsar da hikimar masu hikima. Zan dode fahimtar masu basira." 20 Ina mai hikima? Ina masani? Ina mai muhawara na duniyan nan? Allah bai juya hikimar duniya zuwa wauta ba? 21 Tunda duniya cikin hikimarta bata san Allah ba, ya gamshi Allah ta wurin wautar wa'azi ya ceci masu bada gaskiya. 22 Gama Yahudawa suna bidar al'ajibai, Helinawa kuma suna neman hikima. 23 Amma muna wa'azin Almasihu gicciyayye, dutsen tuntube ga yahudawa da kuma wauta ga Helinawa. 24 Amma ga wadanda Allah ya kira, Yahudawa da Helinawa, muna wa'azin Almasihu a matsayin iko da kuma hikimar Allah. 25 Gama wautar Allah tafi mutane hikima, kuma rashin karfin Allah yafi mutane karfi. 26 Dubi kiranku, yan'uwa. Ba dukkan ku ke da hikima a ma'aunin mutane ba. Ba dukkan ku ke da iko ba. Ba dukkan ku ke da haifuwa ta sarauta ba. 27 Amma Allah ya zabi abubuwan da suke wofi na duniya domin ya kunyatar da masu hikima. Allah ya zabi abin da ke marar karfi a duniya domin ya kunyatar da abinda ke mai karfi. 28 Allah ya zabi abinda ke marar daraja da kuma renanne a duniya. Ya ma zabi abubuwan da ake dauka ba komai ba, domin ya wofinta abubuwan da ake dauka masu daraja. 29 Ya yi wannan ne domin kada wani ya sami dalilin fahariya a gabansa. 30 Domin abinda Allah ya yi, yanzu kuna cikin Almasihu Yesu, wanda ya zamar mana hikima daga Allah. Ya zama adalcinmu, da tsarkinmu da fansarmu. 31 A sakamakon haka, kamar yadda nassi ya ce, "Bari mai yin fahariya, ya yi fahariya cikin Ubangiji."
Bulus da Sastanisu sun rubuto wannan wasikar ne zuwa ga masubi da ke ikilisiya a Koronti.
Harshen ku na da wata hanya ta musamman na gabatar da marubucin wasika da kuma masu sauraro. AT: "Ni, Bulus, na rubuta maku wannan wasika ku a Koronti da kuke ba da gaskiya ga Allah"
Wannan ya na nuna cewa Bulus da korontiyawan sun san Sastanisu. AT: "Sastanisu ɗan'uwa da ni da ku mun sani"
Anan "keɓe" na nufin mutane wanda Allah ya shirya domin su ɗaukakka shi. AT: "ga waɗanda Yesu Almasihu ya keɓe su wa Allah" ko "ga waɗanda Allah ya keɓe ma kansa saboda su na cewa Almasihu Yesu ne"
AT: "waɗanda Allah ya kira su zama sarkaken mutane"
"sunan" na nufin Yesu Almasihu da kansa. AT: "masu kira bisa Ubangiji Yesu Almasihu"
Kalman "namu" na haɗe da masu sauraran Bulus. Yesu ne Ubangijin Bulus da Korontiyawan da kuma Ubangijin dukkan ikilisiyoyi.
Bulus ya kwatanta matsayin maibi da kuma zumunta cikin Almasihu yayin da suke jiran zuwan sa.
Bulus na magana game da bangaskiya kaman wani abu ne a bayyane wanda Yesu ya ba wa masubi kyauta. AT: "saboda Almasihu Yesu ya sa shi yiwuwa ma Allah ya yi ma ku kirki"
AT:1) "Almasihu ya ba ku arziki" ko kuma 2) "Allah Ya ba ku arziki"
Bulus ya na magana a muhimmin kalmomi. AT: "ya ba ku arziki da dukkan irin albarku na ruhaniya"
Allah ya sa ku ku gaya wa sauran game da sakon Allah a hanyoyi dayyawa.
Allah ya sa ku, ku gane sakon Allah a hanyoyi dayyawa
AT: 1) "kun gani wa kanku cewa abin da muke cewa game da Almasihu gaskiya ne" ko kuma 2) "sauran mutane sun gani daga ganin yadda yanzu ku ke rayuwa saboda abun da mu da ku muka faɗa game da Almasihu gaskiya ne."
"domin abin da na riga na faɗa gaskiya ne"
Ana iya bayana wannan da kyau. AT: "ku na da kowane baiwa ta ruhaniya"
AT 1) "lokacin da Allah zai bayyana Ubangiji Yesu Almasihu" kokuwa 2) "lokacin da Ubangijinmu Yesu Almasihu zai bayyana kan sa."
Babu wata dalilin da Allah zai hukunta ku.
"Allah zai yi komai da ya ce zai yi"
Wannan muhimmin laƙabi ne ma Yesu, Ɗan Allah.
Anan wannan na nufin su masubi, tare da maza da mata.
"sunan" na nufin Yesu Almasihu da kansa kenan. AT: "ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu"
"cewa ku yi rayuwa a cikin jituwa da juna"
"cewa kadda a samu rabe rabe a tsakaninku"
"rayuwa cikin zaman ɗaya"
Wannan na nufin 'yan gida, bayi, da sauran da ke sashin iyalin na Kulowi, mace, ne shugaba.
"ku na cikin ƙungiya da ke faɗa da junan ku"
Bulus yana bayyana yawancin halin raɓuwa yake
Bulus ya so ne ya nanata gaskiyan cewa Alamsihu ɗaya ne ba a rarrabe yake ba. "ba mai yiwuwa bane a raɓa Almasihu a yadda kuke yi ba!"
Bulus ya so ne ya nanata cewa Almasihu ne an gicciye ba Bulus ko Apollos ba. AT: "haƙiƙa ba Bulus bane wanda suka sa a mutuwa akan gicciye domin ceton ku ba!"
Bulus ya so ya nanata cewa dukkan mu mun yi baftisma a cikin sunan Almasihu. AT: "Ba a cikin sunan Bulus ne aka yi maku baftisma ba!"
"kaɗai"
Dama shi shugaban ikilisiya da ya zama mai bi.
Ya yi tafiya tare da Manzo Bulus.
"Suna" na wakilcin "iƙo." Wannan na nufin cewa Bulus bai yi ma wasu baftisma ba domin za su iya ce sun zama almajiran Bulus. AT: "waɗansunku suna gani cewa na yi maku baftisma domin ku zama almajirai na"
Wannan na nufin iyalin gidan da kuma bayi a cikin gidan da Sitifanas, na miji, ne shugaba.
Wannan na nufin cewa baftisma ba ainahin maƙasudin bisharar Bulus ba ne.
Bulus na maganan "kalmomin hikimar mutum" kaman mutane ne, gicciyen kaman kunshi, da kuma ƙarfi kaman abun da na bayyane da Yesu zai iya sa a cikin kunshi. AT: "kalmomin hikimar mutum ... kadda waɗancan kalmomin hikimar mutum su wofintar da karfin gicciyen Almasihu " ko kuma "kalmomin hikimar mutum ... kadda mutane su daina gaskanta da sako game da Yesu su kuma fara tunani cewa ina da muhimmanci fiye da Yesu"
"wa'azi a kan giciyewar" ko "sako akan mutuwan Almasihu a kan giciye"
"mara hankali" ko "wawa"
A nan "mutuwa" na nufin yanayin mutuwa ta ruhaniya.
"Allah ne na aiki da iko a cikin mu"
"Zan rikita mutane masu basira" ko kuma " Zan sa shirin da mutane masu basira suke yi ya kasa"
Bulus na nanata cewa gaskiya babu mutane masu hikima. AT: "A kwatance da hikimar bishara, babu mutane masu hikima, babu masani, babu muhawara!"
Mutumin da an ɗauke shi kaman wanda ya yi karatu sosai
Mutum da ke yin muhawara a kan abin da ya sani ko wanda de ke gwani a cikin muhawaran
Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya nanata abin da Allah ya yi ma hikimar duniyan nan. AT: "Allah ya nuna cewa dukkan abin da sun kira hikma, wauta ne ta ainahi"
AT: 1) "dukkan waɗanda sun bada gaskiya a sakon" ko 2) "dukkan waɗanda sun bada gaskiya ga Almasihu."
"game da Almasihu, wanda ya mutu a bisa gicciye"
Sakon ceto ta wurin gicciyen Almasihu ya hana Yahudawa daga gaskanta da Yesu, kaman yadda mutum ke iya tuntuɓe a kan dutse a hanya. AT: "ba ƙarbabe ba" ko "laifi sosai"
"ga mutanen da Allah ya kira"
"muna koyarwa game da Almasihu" ko kuma "mu na gayawa dukkan mutane game da Almasihu"
AT: 1) "Allah ya yi hikima da iko ta wurin aika Almasihu ya mutu domin mu" ko "Ta wurin Almasihu, Allah ya nuna iko dakarfinsa"
AT: "Almasihu na da iko kuma ta wurin Almasihu ne Allah ya cece mu"
AT: "Allah ya nuna abin da ke cikin hikimar sa ta wurin Almasihu."
AT: 1) Bulus na maganar zance game da wautar Allah. Bulus ya san cewa Allah ba wawa ba ne ko na da rashin ƙarfi. AT: "Abin da ke da alaman wautar Allah tafi mutune hikima, kuma abin da ke da alaman rashin ƙarfin Allah yafi karfin mutanen" ko 2) Bulus na magana daga fanin mutanen Girka wadda su na iya tunani cewa Allah wawa ne ko mara ƙarfi. AT: "Abin da mutane ke kira wautar Allah ta fi abin da mutane ke kira hikima, kuma abin da mutane ke kira rashin ƙarfin Allah ta fi ƙarfin na mutane"
Ana iya bayana wannan da kyau. AT: "ku ƙadan"
"Abin da yawancin mutane za su kira hikima"
"musamman domin gidan ku na da muhimmi"
Bulus ya mamaita kalmomin iri ɗaya a jimla biyu da ke nufin abu ɗaya sau da dama don ya nanata bambanci sakanin yanda Allah na yin abubuwa da kuma yanda mutane ke tunani ya yi.
"Allah ya zaɓi ya yi amfani da waɗanda duniya ke gani suke da wofi don ya kunyatar da masu gani su na da hikima"
"Allah ya zaɓi ya yi amfani da waɗanda duniya ke gani mara ƙarfi domin ya kunyatar da masu gani su na da ƙarfi"
Mutanen da Allah ya ƙi su. AT: "mutane masu tawali'u da an ki su"
AT: "wanda mutane ke ɗauka da rashin daraja"
"ba komai ba. Ya yi haka domin ya nuna cewa abubuwan da a ke ɗauka da daraja wofi ne"
AT: "abubuwan da mutane sun ɗauka na da kuɗi" ko kuma "abubuwan da mutane sun ɗauka ne da girma"
"Allah ya yi wannan"
Wannan na nufin aikin almasihu a kan gicciye.
Wannan kalmomin na nufin Bulus, wanda na tare da shi, da kuma Korontiyawa.
AT: 1) "Almasihu Yesu, wanda ya bayana mana hikimar Allah" ko kuma 2) "Almasihu Yesu, wanda ya ba mu hikiman Allah."
"Idan mutum na fahariya, ya yi fahariya don girman Almasihu"
Yesu ya kira Bulus domin ya zama manzo.
Bulus ya so su sami alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu.
Allah ba su arziki ta kowace hanya, cikin dukkan magana da dukkan ilimi.
Basu rasa wata baiwa ta ruhaniya.
Zai yi haka saboda ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
Bulus ya ce masu su yarda da juna, kada tsattsaguwa ta kasance tsakanin su, kuma su zama da zuciya ɗaya da kuma nufi ɗaya.
Mutanen Kulowi sun kawo kara wa Bulus cewa akwai tsattsaguwa a Koronti.
Bulus na nufin: kowannen ku na cewa, " Ina bayan Bulus," ko " Ina bayan Afollos," ko "Ina bayan Kefas," ko "Ina bayan Almasihu."
Bulus ya goɗe wa Allah domin wannan ba zai sa su yi ce an yi maku baftisma a cikin sunar Bulus.
Almasihu ya aiki Bulus ya yi wa'azin bishara.
Wa'azin gicciye wauta ne ga waɗanda su na mutuwa.
Ikon Allah ne a cikin waɗanda Allah ke cetowa.
Allah ya juya hikimar duniya zuwa wauta.
Ya gamshi Allah ya yi haka domin duniya cikin hikimarta bata san Allah ba.
Allah bai kira waɗanda suke haka dayawa ba.
Allah ya zaɓi abubuwan da suke wofi na duniya domin ya kunyatar da masu hikima.
Allah ya zaɓi abinda ke mara daraja da kuma renanne a duniya, ya kuma zaɓi abubuwan da ake ɗauka ba komai ba.
Masubi su na cikin Almasihu Yesu domin abinda Allah ya yi.
Ya zama mana hikima daga Allah-adalcinmu, da tsarkinmu da fansarmu.
Bari mai yin fahariya, ya yi fahariya cikin Ubangiji.
1 Lokacin da na zo wurin ku, yan'uwa, ban zo da gwanintar magana ko hikima ba yayinda na yi shelar boyayyun bayanai game da Allah. [1]2 Domin na kudura a zuciyata kada in san komai lokacin da nake tare da ku, sai dai Yesu Almasihu, gicciyayye. 3 Ina tare da ku cikin kasawa, da tsoro, da fargaba mai yawa. 4 Kuma sakona da shelata basu tare da kalmomin hikima masu daukar hankali. Maimakon haka, sun zo da bayyanuwar Ruhu da iko, 5 saboda kada bangaskiyarku ta zama cikin hikimar mutane, amma cikin ikon Allah. 6 Yanzu muna maganar hikima ga wadanda suka ginu, amma ba hikima ta duniyan nan ba, ko ta masu mulkin wannan zamani, wadanda suke shudewa. 7 Maimakon haka, muna maganar hikimar Allah ta boyayyar gaskiya, boyayyar hikima da Allah ya kaddara kafin zamanin daukakarmu. 8 Babu wani mai mulki na zamanin nan da ya san wannan hikimar, domin inda sun gane ta a wancan lokacin, da basu gicciye Ubangijin daukaka ba. 9 Amma kamar yadda yake a rubuce, "Abubuwan da babu idon da ya gani, babu kunnen da ya ji, babu zuciyar da ta yi tsammanin sa, abubuwan da Allah ya shirya wa wadanda suke kaunarsa. 10 Wadannan ne abubuwan da Allah ya bayyana mana ta wurin Ruhu. Gama Ruhu yana bincika komai, har ma abubuwa masu zurfi na Allah. 11 Gama wanene ya san tunanin mutum, sai dai ko ruhun mutumin da ke cikinsa? Haka ma, babu wanda ya san abubuwa masu zurfi na Allah sai dai Ruhun Allah. 12 Ba mu karbi ruhu na duniya ba, amma Ruhun da ya zo daga wurin Allah, domin mu san abubuwan da aka bamu a sake daga wurin Allah. 13 Muna maganar wadannan abubuwa da kalmomin da hikimar da mutum baza ta iya koyarwa ba, amma wadanda Ruhu ke koyar da mu. Ruhu yana fassara kalmomi na ruhaniya da hikima ta ruhaniya. 14 Mutum marar ruhaniya ba ya karbar abubuwan da suke daga Ruhun Allah, gama wauta suke a gareshi. Ba zai iya sanin su ba domin Ruhu ne yake bayyana su. 15 Shi wanda yake mai ruhaniya yana shari'anta dukan abubuwa, amma shi baya karkashin shari'ar sauran mutane. 16 "Wa zai iya sanin zuciyar Ubangiji, da zai iya ba shi umarni?" Amma mu muna da lamiri irin na Almasihu.
Bulus ya bambanta hikimar mutum da hikimar Allah. Ya nanata cewa hikima ta ruhaniya na zuwa daga Allah.
Wannan anan na nufin yan'uwa masubi, tare da maza da mata.
A lokacin da Bulus ya ce "na kudura kada in san komai " ya zuguiguita don ya nanata cewa ya kudura ya natsu da kuma koyar game da Yesu Almasihu. AT: "na kudura in koyar da komai ... sai dai Yesu Almasihu" ko "na kudura kada in koyar da komai ... sai dai Yesu Almasihu"
"Ina ziyara tare da ku"
AT: 1) "kasawan jiki" ko kuma 2) "ji kaman bazan iya yin abin da na so in yi ba."
kalmomi da na da hikima wanda mai magana na bege yasa mutane su yi ko kuma su ba da gaskiya a wani abu
Bulus ya katse ainahin muhawarar sa don ya bayana abin da ya ke nufi da "hikima" ga wanda ya so ya yi magana.
An yi amfani da kalman "Yanzu" domin a sa alama a ainahin koyarwan. Bulus ya fara bayana cewa hikiman Allah, hikiman gaskiya ne.
"Hikima" magana mai zuzzurfar ma'ana ne da ana iya bayana a siffa "dabara." AT: "yi maganan kalmomin dabara" or "yi maganan sakon dabara"
"masubi da sun ginu"
"Kafin Allah ya halice komai"
"domin a tabatar da ɗaukarmu nan gaba"
"Yesu, Ubangijin da ya isa alfarma"
Wannan ba cikakken jumla ba ne ama wadansu fasaran na sa ta cika. "abubuwan da babu idon da ya gani ... yi tsammanin; wannan ne abubuwan ... wadanda suke kaunarsa." Waɗansu ba su karasawa ama su na nuna cewa ba cikakke ba ne ta wurin amfani da su aya da waƙafi da kuma fara da aya mai zuwa kamar cigabawan wannan aya: "Abubuwan da babu idon da ya gani ... yi tsammanin ... abubuwan ... waɗanda suke kaunarsa'-"
Wanda aka riɓanya sau uku na nufin dukan sashin mutum domin a nanata cewda babu mutum da ya taba sanin abin da Allah ya shirya.
Ubangiji ya halicci abin ban mamaki a cikin sama ma wanda suke ƙaunrsa.
Bulus ya yi magana game da gaskiya akan Yesu da giccye. Idan an yi amfani da 2:9 kaman jumla da bai cika, "waɗannan ne abubuwan."
Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya nanata cewa ba wanda ya san abin da mutum ke tunani sai mutumin da kansa. AT: "Ba bu wanda ya san abin da mutum yake tunani sai Ruhun mutumin"
Wannan na nufin cikin mutumin, halittar ruhaniyan sa.
AT: "Ruhu mai Tsarki ne kadai ya san zurfin abubuwan Allah"
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "wanda Allah ya bamu a sake" ko "wanda Allah ya bamu ta alheri"
Ruhu mai Tsarki na bayana gaskiyar Allah ga masubi a cikin kalmomin Ruhu na kuma basu hikimar sa.
mutum da ba mai bi ba, wanda bai karɓa Ruhu mai Tsarki ba
"domin gane wannan abubuwa na neman taimakon Ruhu"
"Mai bi da ya riga ya karɓi Ruhun"
Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya nanata cewa ba wanda ya san zuciyar Ubangiji. Ba wanda ke da hikima kaman Allah. AT: "Ba wanda zai iya sanin zuciyar Ubangiji, don haka ba bu wanda zai iya koya ma shi abin da bai riga ya sani ba"
Bulus bai zo da gwanintar magana ko hikima a loƙacin da yi shelar ɓoyayyar gaskiyar game da Allahba.
Bulus ya so kada ya san komai sai dai Yesu Almasihu, gicciyayye.
Saboda kada bangaskiyarsu ta zama cikin hikimar mutane, amma cikin ikon Allah.
Sun yi maganar hikimar Allah ta boyayyar gaskiya-boyayyar hikima da Allah ya kaddara kafin zamanin ɗaukakarmu.
Inda shugabanin sun san hikimar Allah da basu gicciye Ubangijin ɗaukaka ba.
Allah ya bayyana waɗannan abubuwa ta wurin Ruhu.
Ruhun Allah ne kadai ya san zurfin abubuwan Allah.
Sun karba Ruhun da ya zo daga wurin Allah, domin su san abubuwan da aka bamu a sake daga wurin Allah.
Mutum marar ruhaniya ba zai iya karbar su ba saboda wauta ne a gareshi kuma ba zai iya sanin su ba domin Ruhu ne yake bayyana su.
Bulus ya ce suna da lamiri na Almasihu.
1 Amma ni, yan'uwa, ba zan iya magana da ku kamar mutane masu ruhaniya ba, amma kamar mutane masu jiki, kamar jarirai cikin Almasihu. 2 Na shayar da ku da Madara ba da nama ba, don baku isa cin nama ba, kuma ko yanzu ma baku isa ba. 3 Gama har yanzu ku masu jiki ne. Muddin akwai kishi da jayayya a tsakaninku, ashe, ku ba masu jiki ba ne, kuma kuna tafiya bisa magwajin mutane? 4 Domin in wani ya ce, "Ina bayan Bulus," wani kuma ya ce, "Ina bayan Afollos," ashe, ba zaman mutuntaka kuke yi ba? 5 To wanene Afollos? Wanene kuma Bulus? Bayi ne wadanda kuka bada gaskiya ta wurin su, kowannen su kuwa Allah ya bashi ayyuka. 6 Ni nayi shuka, Afolos yayi banruwa, amma Allah ne ya sa girma. 7 Don haka, da mai shukar da mai banruwan, ba komi bane. Amma Allah ne mai sa girman. 8 Da mai shukar, da mai banruwan, duk daya suke, kuma kowannen su zai sami nasa lada, gwargwadon aikinsa. 9 Gama mu abokan aiki ne na Allah. Ku gonar Allah ne, ginin Allah kuma. 10 Bisa ga alherin Allah da aka bani a matsayin gwanin magini, na kafa harsashi, wani kuma yana dora gini a kai. Sai dai kowane mutum, ya lura da yadda yake dora ginin. 11 Gama ba wanda ke iya kafa wani harsashin daban da wanda aka rigaya aka kafa, wato, Yesu Almasihu. 12 Yanzu fa in wani ya dora gini a kan harashin da zinariya, ko azurfa, ko duwatsu masu daraja, ko itace, ko ciyawa, ko tattaka, 13 aikinsa zai bayyanu, domin ranar nan zata tona shi. Gama za a bayyana shi cikin wuta. Wutar kuwa zata gwada ingancin aikin da kowa ya yi. 14 Duk wanda aikinsa ya tsaya, zai karbi lada; 15 amma duk wanda aikinsa ya kone, zai sha Asara, amma shi kansa zai tsira, sai dai kamar ta tsakiyar wuta. 16 Ashe, baku san ku haikalin Allah ne ba, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikin ku? 17 Idan wani ya lalata haikalin Allah, Allah zai lalata shi. Gama haikalin Allah mai tsarki ne, kuma haka ku ke. 18 Kada kowa ya rudi kansa. Idan wani a cikin ku na ganin shi mai hikima ne a wannan zamani, bari ya zama" wawa" domin ya zama mai hikima. 19 Gama hikimar duniyar nan wauta ce a gun Allah. Gama a rubuce yake, "Yakan kama masu hikima a cin makircin su." 20 Har wa yau, "Ubangiji ya san tunanin masu hikima banza ne." 21 haka ba sauran fariya akan mutane! Domin kuwa kome naku ne, 22 Ko Bulus, ko Afollos, ko kefas, ko duniya, ko rai, ko mutuwa, ko abubuwa na yanzu, ko abubuwa masu zuwa. Duka naku ne, 23 Ku kuwa na Almasihu ne, Almasihu kuma na Allah ne.
Bulus ya tunashar da masubi na Korontiyawa game da yanda suke rayuwa maimakon nuna halin zaman su a gaban Allah. Ya kuma tuna masu cewa mutumin da ya koyar da su, ba shi da muhimmi kaman Allah da ya ba da girman su.
A nan na nufin yan'uwa masubi tare da maza da mata.
mutane masu bin ruhaniya
mutane masu bin sha'awan su
An kwatanta Korantiyawa da jarirai da suna kanana da kuma fahimta. AT: "kamar ƙaramin mai bi a cikin Almasihu"
Korantiyawan na iya fahimtan gaskiya mai sauki kaman jarirai da na iya shan madara kadai. Ba su shirya sosai don su gane baban gaskiyan ba kaman jarirai masu shekaru wanda su iya cin abinci mai kauri yanzu.
Na nufin cewa ba su shirya su fahimci koyarswa mai wuya ba. AT: "haryanzu ba ku shirya ku fahimci koyarswa mai wahala game da bin Almasihu ba"
nuna hali har yanzu bisa zunubi ko sha'awa na duniya
Bulus ya na kwaɓe Korontiyawa domin halin zunubin su. Ana "tafiya" magana ne game da "hukuncin halin ku," zaban abin da ke da kyau ko mar kyau. AT: "Ya kamata ku ji kunya domin ku na yin hali bisa sha'awan zunubi kuma ku na amfani da ma'aunin mutum don ku shirya ko halin ku na da kyau ko ba bu kyau!"
Bulus ya na kwaɓen Korontiyawan. AT: "Ya kamata ku ji kunya domin ku na rayuwa irin yanda mutane marasa Ruhu su ke yi"
Bulus na nanata cewa kada Korotiyawa su bi su domin shi da Afollos ba ainahin tushen bisharan ba. AT: "ba daidai ba ne ku kafa kungiyoyi don ku bi Afollos da Bulus!" ko
Bulus na maganan kansa kaman yana magana game da wani ne. AT: "ba ni da amfani!" ko kuma "Wa ne ne ni?"
Bulus ya amsa tambayansa da cewa shi da Afollos bayin Allah ne. AT: "Bulus da Afollos bayin Allah ne, kuma kun gaskanta da Almasihu domin muna bauta ma shi"
Ana iya bayana wannan da labarin da an fahimta. AT: "Mu bayi ne ta wurin wanda ku gaskanta. Mu mutane ne kadai da Allah ya ba da aiki"
An kwatanta sanin Allah da iri da yakamata dole a shuka domin ya yi girma. AT: "Ina nan kaman wani da na shuka iri a lambu, a lokacin da na yi maku wa'azin kalmar Allah.
Kaman yadda iri na son ruwa, bangaskiya na buƙatar karin koyarswa domin ya yi girma. AT: "ya na nan kaman wanda yana banruwa a lambu, a lokacin da Afollos ya cigaba da koya maku maganar Allah"
Yadda shuke-shuke na ci gaba, haka ne bangaskiya da sani a cikin Allah na girma, na kuma zama da zurfi da kuma karfi. AT: "Amma Allah ya sa ku ku yi girma" ko "amma yanda Allah ya na sa shuke-shuke su yi girma, ya na sa ku ku yi girma ta ruhaniya"
Bulus ya ce lallei ba shi ko Afollos ne ke da alhakin girman ruhuniyan masubi ba, Ama yin Allah ne.
Anan bayar da girma na nufin sa girma. Ana iya bayana "girma" mai zuzzurfar ma'ana da fi'ilin magana. AT: "Allah ne na sa ku ku mutu"
Bulus ya yi magana game da gayawa mutane labari mai kyau da kuma koya ma wanda sun amince kamar su na shuka da yin banruwa.
AT: 1) "hadadden manufa" ko 2) "daidan muhimmanci."
adadin kuɗi da ma'aikaci na karɓa domin aikinsa.
Wannan na nufin Bulus da Afollos ba ikilisiyoyin Koronti ba.
Bulus ya ɗauki kansa da Afollos a matsayin masu yin aiki tare.
Wannan na iya nufin 1) kasancewa lambun Allah na nufin na Allah. AT: "ku na nan kaman lambu na Allah" ko kuma 2) kasancewa lambun Allah na nufin yadda Allah na sa mu mu yi girma. AT: "ku na nan kamar lambun da Allah ya na sa shi girma"
Wannan na iya nufin 1) kasancewa ginin Allah na wakilcin na Allah. "ku na nan kaman gini na Allah" ko kuma 2) kasancewa ginin Allah na wakilcin yadda Allah na sa mu mu yi zama abin da yake so. AT: "ku na nan kamar gini da Allah ya na ginawa"
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "Bisa ga aikin da Allah ya bani in yi"
Bulus ya daidaita koyarwan bangaskiyansa da ceto cikin Yesu Almasihu zuwa ga kafa harsashi don gini.
Bulus na nufin mutum ko mutane da su ke koyar da Korontiyawa a lokacin kaman sun zama kafinta wanda suke gina gini a bisa harsashi
Wannan na nufin muhimmin ma'aikatan Allah. AT: "bari kowane mutum da ke bautan Allah"
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "ba wanda ke iya kafa wani harsashin daban da wanda, ni Bulus, na kafa" ko kuma "na riga na kafa harsashin da kowa zai iya fafa"
Ma su gini su amfani da zinariya, ko azurfa, ko duwatsu masu daraja kamar ado a su gini. Bulus ya yi maganan abin da masu gin sukan yi a lokacin gini domin ya kwatanta abin da malamai a Korontiyawa su ke yi.
An kwatanta kanyan aiki da ana amfani a gina sabon gini da darajan ruhania da ake amfani domin gina halin mutum da kuma ayuka a zaman sa a duniya. AT: "ko mutum ya yi gini da kaya masu daraja da za su daɗe ko kuma da kaya masu arha da za su ƙone da sauri"
"duwatsu masu tsada"
AT: "Allah zai nuna wa kowa abin da mai ginin ya yi"
"Ranar" magana ne na lokacin da Allah zai yi shari'a. Zai zama kaman rana ta zo domin ta bayana abin da ya faru da dare, a lokacin da Allah ya nuna ma kowa abin da mallaman nan su yi.
Wutan Allah zai hukuta ayukan mutum da kokarin sa, kaman yanda wuta ya ke bayana ƙarfin gini ko kuma bata rashin ƙarfin sa. AT: "Allah zai yi amfani da wuta don ya nuna ingancin aikinsa"
"aiki ya daɗe" ko "aiki ya haye"
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "idan wuta ya lalatar da aikin wani" ko kuma " idan wuta ya ɓata aikin wani"
Ana iya bayana isimin nan "asara" da fi'ilin "rasa." AT: "zai rasa ladan sa"
AT: "Amma Allah zai cece shi"
Bulus na kwaɓan Korontiywa. AT: "ku na yi kaman ba ku san cewa ku haikalin Allah ba ne, kuma Ruhun Allah na zaune a cikin ku!"
kada kowa ya yarda da karya cewa shi kansa na da hikima a cikin duniyan nan.
bisa ga yanda mutanen da ba su gaskanta ke yanke abin hikima
"domin mutumin ya yarda ya samu mutanen da ba su gaskanta ba su kira shi wawa"
Allah na kama mutanen da su na tunani cewa su na da fasaha na kuma amfani da dabarun su domin ya kama su.
"Ubangiji ya san cewa abinda mutanen sa masu tunani cewa suna da wayo suna shirin yi banza ne"
mara amfani
"kun zama na Almasihu, Almasihu kuma ya zama na Allah"
Bulus ya ce har yanzu suna cikin jiki domin akwai kishi da jayayya a tsakaninsu.
Su bayi ne wanda ta wurin su ne Korontiyawa sun gaskanta da Almasihu.
Allah ne mai sa girman.
Yesu Almasihu ne harsashin.
Aikinsa zai bayyanu a rana da kuma cikin wuta.
Wutar kuwa zata gwada ingancin aikin da kowa ya yi.
Mutumin nan zai karbi lada.
Mutumin zai sha asara, amma shi kansa zai tsira, kamar tsira ta tsakiyar wuta.
Mu ne haikalin Allah kuma Ruhun Allah na zaune a cikin mu.
Allah zai hallaka mutumin da ya hallaka haikalin Allah.
Bulus ya ce, "... bari ya zama "wawa" domin ya zama mai hikima.
Ubangiji ya san tunanin masu hikima banza ne.
Ya ce masu su daina yin fahariya, "Gama dukka abubuwa naku ne," ... ku kuwa na Almasihu ne, Almasihu kuma na Allah ne"...
1 Ga yadda za ku dauke mu, kamar bayin Almasihu da kuma masu rikon asiran Allah. 2 Hade da wannan, ana bukatar wakilai su zama amintattu. 3 Amma a gare ni, karamin abu ne ku yi mani shari'a, ko a wata kotu irin ta mutane. Gama bani yi wa kaina shari'a. 4 Ban sani ko akwai wani zargi a kaina ba, amma wannan bai nuna cewa bani da laifi ba. Ubangiji ne mai yi mani shari'a. 5 Sabili da haka, kada ku yanke shari'a kafin lokaci, kafin Ubangiji ya dawo. Zai bayyana dukkan boyayyun ayyuka na duhu, ya kuma tona nufe-nufen zuciya. San nan kowa zai samu yabonsa daga wurin Allah. 6 Yan'uwa, ina dora wadannan ka'idoji a kaina da Afollos domin ku, yadda ta wurin mu za ku koyi ma'anar maganar nan cewa, "kada ku zarce abin da aka rubuta." Ya zama haka domin kada waninku ya kumbura yana nuna fifiko ga wani akan wani. 7 Gama wa yaga bambanci tsakanin ku da wasu? Me kuke da shi da ba kyauta kuka karba ba? Idan kyauta kuka karba, don me kuke fahariya kamar ba haka ba ne? 8 Kun rigaya kun sami dukkan abubuwan da kuke bukata! Kun rigaya kun zama mawadata! Kun rigaya kun fara mulki- kuma ba tare da mu ba! Hakika, marmarina shine ku yi mulki, domin mu yi mulki tare da ku. 9 A tunanina, mu manzanni, Allah ya sa mu a jerin karshe kamar mutanen da aka zartar wa hukuncin mutuwa. Mun zama abin kallo ga duniya, ga mala'iku, ga mutane kuma. 10 Mun zama marasa wayo sabili da Almasihu, amma ku masu hikima ne a cikin Almasihu. Mu raunana ne, amma ku masu karfi ne. Ana ganin mu marasa daraja, ku kuwa masu daraja. 11 Har zuwa wannan sa'a, muna masu yunwa da kishi, marasa tufafi masu kyau, mun sha kazamin duka, kuma mun zama marasa gidaje. 12 Mun yi fama sosai, muna aiki da hanuwanmu. Sa'adda an aibata mu, muna sa albarka. Sa'adda an tsananta mana, muna jurewa. 13 Sa'adda an zage mu, muna magana da nasiha. Mun zama, kuma har yanzu an dauke mu a matsayin kayan shara na duniya da abubuwa mafi kazamta duka. 14 Ban rubuta wadannan abubuwa domin in kunyata ku ba, amma domin in yi maku gyara kamar kaunatattun yayana. 15 Ko da kuna da masu riko dubu goma a cikin Almasihu, ba ku da ubanni da yawa. Gama ni na zama ubanku cikin Almasihu Yesu ta wurin bishara. 16 Don haka, ina kira gare ku da ku zama masu koyi da ni. 17 Shiyasa na aiko Timoti wurin ku, kaunatacce da amintaccen dana cikin Ubangiji. Zai tunashe ku hanyoyina cikin Almasihu, kamar yadda nake koyar da su ko'ina da kowace Ikilisiya. 18 Amma yanzu, wadansun ku sun zama masu fahariya, suna yin kamar ba zan zo wurinku ba. 19 Amma zan zo gare ku ba da dadewa ba, idan Ubangiji ya nufa. Sannan zan san fiye da maganar masu fahariya, amma kuma zan ga ikonsu. 20 Gama Mulkin Allah ba magana kadai ya kunsa ba, amma ya kunshi iko. 21 Me kuke so? In zo wurin ku da sanda ne ko kuwa da kauna da ruhun nasiha?
Bayan da ya tuna wa mutunen cewa kada su yi takama da wadda ya koya masu game da Almasihu da kuma wadda ya yi masu baftisma, Bulus ya tunashar da masubi na Koronti cewa yakamata dukan masubi su zama bayi masu tawali'u.
Bulus ya na magana game kansa kaman ya na magana akan waɗansu mutane. AT: "Ana bukata mu zama"
Bulus ya na kwatanta bambanci sakanin hukuncin mutum da hukuncin Allah. Hukuncin mutum ba shi da muhimanci idan aka kwatanta shi da gaskiyar hukuncin Allah akan mutum.
"Ban ji wannan ya kushe ni cewa ina yin abu da ba daidai ba"
"rashin zargi bai nuna cewa bani da laifi ba. Allah ya san ko bani da laifi ko ina da laifi"
"Domin abin da na fada gaskiya ne"
Anan "bayyana dukkan boyayyun ayyuka na duhu" magana ne da na sa abubuwan da an aikata a boye sananne ga kowa. Anan "zuciya" zance ne akan tunani da nufin mutum. AT: "Kamar haske da ya na haskaka a kan abubuwa a cikin duhu, Allah zai bayyana abin da mutane sun aikata a duhu da kuma abin da sun shirya a asirce"
Wannan na nufin masubi, tare da maza da mata.
"domin amfanin ku"
Bulus ya na magana da Korontiyawa kamar sun zama mutum daya.
Bulus ya na tsawata wa Korontiyawa da suke tunani cewa sun fi wadanda sun ji bishara daga wani dabam. AT: "Gama babu bambamci a sakanin ku da wadansu." ko kuma "Gama ba ku gaba da waɗansu mutanen."
Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya nanata cewa basu samu abin da suke da shi don ladan aikinsu ba. AT: "Dukan abin da kuke da shi, kyuata ne da kun karɓa." ko kuma "Allah ya ba ku komai da kuke da shi kyauta!"
Bulus ya na tsawata masu domin yin fahariya da abin da suke da shi. AT: "kadda ku yi fahariya kaman ba ku yi haka ba." ko kuma "ba ku da iƙon yin fahariya!"
Jumlan "yi haka" na nufin karɓan abin da suke da shi a kyauta. AT: "kamar yadda ba ku karɓa a kyauta ba" ko kuma "kamar kun samu don ladan aikin ku"
Bulus ya yi magana anan domin ya kunyatar da Korontiyawan, ya kuma sa su su gane cewa zunubi ne su na yi a loƙacin da suna takama da junansu da kuma mallamansu.
Bulus ya bayana hanyoyi biyu da Allah ya sa manzannin sa a gwaji domin duniya su gani.
Allah ya gwada manzanninsa kamar yadda fursuna a karshen farati na sojojin Romawa, wadda a na ci masu mutunci da su kafin a yi masu kisa.
Allah ya sa manzannin a gwaji kamar wadda za a ci masu mutunci.
AT: 1) "duniya" na da abin da ya wuce iƙon ɗan-adam
Bulus ya yi amfani da maganan domin ya kunyatar da Korontiyawan don su yi tunanin abin da yake faɗa.
"Mutuane suna na yi maku Korontiyawa kaman ku mutane masu muhimmanci"
"Mutane na kunyatar da mu manzanni"
"Har yanzu"
Wannan na nufin bugawa da hanu, ba da bulala ko kulki ba. AT: "mutane sun duke ne"
Bulus na nufin cewa su na da wuraran zama, amma sun kewaye wurare dabam dabam. Ba su da kafaffiyar gida.
AT:"Loƙacin da mutane na aibata mu, mun sa masu albarka" ko kuma " "Loƙacin da mutane na raina mu, mun sa masu albarka"
AT: "Loƙacin da mutane ke tsananta mu"
AT: "Loƙacin da mutane ke kushe mu"
"Mutane sun fara ɗaukan mu--kuma har yanzu su na ɗaukan mu--zama datti na duniya"
"Ban yi niya in kunyata ku ba, amma domin in kara gyara ku" ko kuma "ba wai ina kokarin kunyatar da ku bane, amma ina so in gyara ku ne"
faɗa ma wani cewa abin da suke aikatawa ba daidai bane kuma zai sa mugun abu ya faru
Wannan magana ne akan lamban mutanen da ke lura da su, domin a nanata muhimmin Uba daya na ruhaniya.AT: "yawan wakilai" ko kuma "babban tarun wakilai"
Domin Bulus ya bi da su zuwa ga Almasihu, ya na nan kamar Uba ne a wurin Korontiyawan
A farko, Bulus na natata cewa ɗangantakansa da Korontiyawa na da muhimmi a "cikin Almasihu", na biyu domin ya zo saboda ya faɗa masu game da bisharan, na uku na cewa shine a wadda yake kamar Uba a gare su. "saboda Allah ya hada ku ga Almasihu a loƙacin da na faɗa maku game da labari mai kyau cewa ni ne na zama Uban ku"
"Wadda ina ƙauna, wadda na koyar game da Almasihu kaman dana ne"
Wannan kalma na nuna cewa Bulus ya na canja batunsa domin ya tsautawa halin girman kai na masubi a Koronti.
"zan ziyarce ku"
Bulus ya na yin roko na karshe ga Korontiyawa, yadda ya saba tsautawa masu game da kuskuren da sun yi. AT: "fada mani abin da ku na so ya faru yanzu"
Bulus ya na ba wa Korontiyawa halaya biyu da suke gaba da juna wanda zai iya yin amfani da shi a gabatar da su. AT: "Idan ku na so, zan iya zuwa in hukunta ku, ko kuma zan iya zuwa don in nuna maku yadda ina kaunar ku ta kasancewa da hankali da ku"
"na alheri" ko kuma "na taushi"
Korontiyawa su ɗauke su kamar bayin Almasihu da kuma wakilan ɓoyeyyar gaskiyar Allah.
Dole waƙilai su zama amintattu.
Bulus ya ce Ubangiji ne mai yi masa shari'a.
Zai bayyana dukkan boyayyun ayyuka na duhu, ya kuma tona nufe-nufen zuciya.
Bulus ya yi wannan ta dalilin masubi na Korontiyawa domin su koya ma'anar maganar nan cewa, "kada ku zarce abin da aka rubuta," domin kada wani ya nuna fifiko ga wani akan wani.
Bulus ya so su yi mulki, domin shi da abokan aikinsa su yi mulki tare da su.
Bulus ya ce, "Mun zama marasa wayo sabili da Almasihu, amma ku masu hikima ne a cikin Almasihu. Mu raunana ne, amma ku masu karfi ne. Ana ɗaukarku da daraja amma ana ɗaukar ma marasa daraja.
Bulus ya ce sun ji yunwa da kishi, da rashin tufafi masu kyau, sun sha kazamin duka, kuma sun zama marasa gidaje.
Sa'adda aka kai masu hari, sun sa albarka. Sa'adda an tsananta masu, sun jure. Sa'adda an zage su, sun yi magana da nasiha.
Ya rubuta su domin ya yi masu gyara kamar ƙaunatattun yayansa.
Bulus ya ce masu su yi koyi da shi.
Bulus ya aiko Timoti zuwa Korontiyawa domin ya tunashe masubi a wurin game da hanyoyinsa a cikin Almasihu.
Waɗansu sun zama masu fahariya, suna yi kamar Bulus ba ya zuwa wurinsu.
Mulkin Allah ya kunshi iko.
1 Mun ji cewa akwai lalata mai kazanta a cikin ku, irin lalatar ba ba a yarda da ita ba ko a cikin al'ummai. Labarin da na samu shine, wani daga cikin ku yana kwana da matar mahaifinsa. 2 Kuma kuna fahariya sosai! Ba bakinciki ya kamata ku yi ba? Shi wanda ya yi haka, dole a fitar da shi daga cikin ku. 3 Gama Kodashike ba ni tare da ku cikin jiki, amma ina tare daku a ruhu, na rigaya na hukunta wanda yayi wannan, tamkar ina wurin. 4 Lokacin da ku ka taru a cikin sunan Ubangijinmu Yesu, ruhuna yana nan tare da ku cikin ikon Ubangiji Yesu, na rigaya na hukunta wannan mutum. 5 Na yi haka ne domin in mika wannan mutum ga Shaidan domin a hallaka jikin, don ruhunsa ya tsira a ranar Ubangiji. 6 Fahariyarku bata yi kyau ba. Ko baku sani ba yisti dan kadan ya kan bata dukan dunkule? 7 Ku tsarkake kan ku daga tsohon yisti domin ku zama sabon dunkule, wato gurasar da ba ta da yisti. Gama an yi hadayar Almsihu, dan ragonmu na idi. 8 Don haka, bari mu yi idinmu ba da tsohon yisti ba, wato yisti irin na rashin tabi'a da mugunta. Maimakon haka, bari muyi bukin idi da gurasa marar yisti ta aminci da gaskiya. 9 Na rubuta maku a cikin wasikata cewa kada ku yi hudda da fasikan mutane. 10 Ba ina nufin fasikan mutane na wannan duniya ba, ko masu zari, ko 'yan'damfara, ko masu bautar gumaka, tunda kafin ku rabu da su sai kun bar wannan duniya. 11 Amma yanzu ina rubuta maku cewa kada ku yi hudda da duk wanda ake kira dan'uwa amma yana zama cikin fasikanci, ko zari, ko bautar gumaka, ko in shi mai ashar ne, ko mashayi, ko dan'damfara. Kada ko abinci ku ci da irin wannan mutum. 12 Domin ta yaya zan iya shar'anta wadanda ba 'yan Ikklisiya ba? Maimakon haka, ba ku ne zaku shar'anta wadanda ke cikin ikilisiya ba? 13 Amma Allah ke shar'anta wadanda ke waje. "Ku fitar da mugun mutumin daga cikin ku."
Bulus ya bayana game da irin zunubansu da ya ji, da kuma yadda masubi na Korontiyawan su na fahariya da amincewan su game da mutumin nan da zunubinsa.
AT: "cewa, ko Al'ummai ba su yarda ba"
"kwana da" magana ne na "yin zina da" AT: wani daga cikin ku na yin zina da"
matar Ubansa, amma mai yuwuwa ba Uwarsa ba
Ana amfani da wannan tambayan domin a tsawta Korontiyawan. AT: "maimako ku yi bakinci akan wannan!"
AT: "Dole ne ku fitar da wanda ya yi wannan a sakaninku"
"ina nan da ku a ruhu." Zama tare da su a ruhu na wakilcin kula da su ko kuma son zama tare da su. AT: "Ina kula da ku" ko kuma "Ina so in zauna da ku"
AT: 1) "na riga na yanke abin da za ku yi ma wadda ya yi wannan" ko kuma 2) "na samu mutumin da ya yi wannan laifin"
"loƙacin da ku na tare" ko kuma "loƙacin da kun hadu tare"
suna iya nufin 1) sunan Ubangiji Yesu magana ne da ke walkincin ikon sa. AT: "da iƙon Ubangiji Yesunmu" ko kuma 2) taruwa a cikin sunan Ubangiji na nufin saduwa domin yin masa sujada. AT: "domin yin sujada wa Ubangijinmu Yesu"
miƙa mutumin ga Shaidan na wakilcin rashin yarda wa mutumin ya kasance a kungiyan su domin shaidan ya iya yin masa lahani. AT: "sa wannan mutumin ya bar kungiyan ku domin Shaidan ya iya yi masa lahani"
Suna iya nufin 1) na nufin "jikin" sa. AT: "domin Shaidan ya lahata jikinsa" ko kuma 2) "jiki" magana ne na halin mutuntaka. AT: "domin a halaƙar da halin mutuntakansa" ko kuma "domin kada ya ci gaba da rayuwa a bisa halin mutuntakarsa"
AT: "domin mai yiwuwa, Allah ya cece ruhunsa a ranar Ubangiji"
"Fahariyarku babu kyau"
yadda ana shafa yisti dan kadan a dukan dukulen burodi, haka ne zunubi kadan na shafi duka zumuntar masubi.
Kamar yadda ragon idi na rufe zunuban Isra'ila ta wurin bangaskiya a kowane shekara, haka ne mutuwar Almasihu ya rufe zunuban dukan wadanda sun gaskanta da shi ta wurin bangaskiya na madauwami. AT: "Ubangiji ya yi hadayar Almasihu, ragon idinmu"
Wannan na nufin mutanen da sun gaskanta da Almasihu amma su na wannan ayukan.
mutanen da sun zaba su yi rayuwan fasikanci, wadda ba masubi ba
"waɗanda su ke da haɗama" ko kuma "waɗanda su ke so su zama marasa adalci domin su samu abin da wadansu ke da shi"
Wannan na nufin mutanen da suke yaudara don su samu kayan wadansu.
"yakamata ku guje duka mutane"
"duk wanda ya kira kansa"
Wannan na nufin maibi, namiji ko na mace.
Bulus ya na nanata cewa ba shi ne zai shar'anta mutanen wadanda ba 'yan Ikklisiya ba. AT: "Ba ni ba ne yakamata in shar'anta mutane waɗanda ba na Ikklisiya ba"
Bulus ya na yi ma Korontiyawan tsawa. "ku san cewa ku ne yakamata ku shar'anta wadanda ke cikin ikilisiya"
Bulus ya ji cewa akwai lalata mai kazanta a wurin. Ɗaya daga cikin su yana kwana da matar mahaifinsa.
Shi wanda ya yi zunubi da matar mahaifinsa, ɗole a fitar da shi daga cikin ku.
Sa'ad da Ikilisiya a Koronti sun taru a cikin sunar Ubangiji Yesu, za su mika mutum mai zunubi ga Shaidan don hallakar jiki saboda ruhunsa ya tsira a ranar Ubangiji.
Bulus ya yi amfani da sabon gurusa mara yisti wa aminci da gaskiya.
Bulus na ƙwatanta su da yisti.
Bulus ya rubuta masu cewa kada su yi hudda da fasikan mutane.
Bulus ba ya nufin masu faskanci na wannan duniya. Za ku fita daga duniya don ku raɓu da su.
Ya na nufin cewa kada su yi hudda da duk wanda ake kira ɗan'uwa amma yana zama cikin fasikanci, ko zari, ko bautar gumaka, ko yin ashar, ko mashayi, ko ɗan'damfara.
Ya kamata su shar'anta waɗanda suke cikin ikilisiya .
Allah ke shar'anta waɗanda ke wajen Ikilisiya.
1 Idan wani a cikin ku yana jayayya da wani, to sai ya tafi kotu gaban alkali marar bada gaskiya, a maimakon gaban masu bi? 2 Ko ba ku sani ba, masubi ne za su yiwa duniya shari'a? Kuma idan ku za ku yi wa duniya shari'a, sai ku kasa sasanta al'amura marasa mahimmanci? 3 Baku sani ba mu za mu yiwa mala'iku shari'a? Balle shari'ar al'amuran wannan rai? 4 Idan kuna shar'anta al'amuran yau da kullum, don me ku ke kai irin wadannan matsaloli gaban wadanda ba 'yan ikilisiya ba? 5 Na fadi wannan domin ku kunyata. Babu wani mai hikima a cikin ku ko daya da zai iya sasanta gardama a tsakanin 'yan'uwa? 6 Amma kamar yadda yake, mai bi ya na kai karar mai bi a kotu, kuma a gaban mai shari'a wanda ba mai bi ba! 7 Kasancewar rashin jituwa a tsakanin Kirista na nuna cewa kun rigaya kun gaza. Don me ba za ka shanye laifi ba? Don me ba za ka yarda a kware ka ba? 8 Amma kun yi wa wadansu laifi kun kuma cutar su, su kuwa 'yan'uwanku ne! 9 Ba ku sani ba marasa adalci ba za su gaji Mulkin Allah ba? Kada ku gaskata karya. Da fasikai, da masu bautar gumaka, da mazinata, da karuwai maza, da masu ludu, 10 da barayi, da masu zari, da mashaya, da masu zage-zage, da 'yan damfara - ba waninsu da zai gaji Mulkin Allah. 11 Kuma da haka wadansu a cikinku suke, amma an tsarkake ku, an mika ku ga Allah, an maida tsayuwar ku dai-dai a gaban Allah a cikin sunan Ubangji Yesu Almasihu, kuma ta wurin Ruhun Allahnmu. 12 Dukkan abu halal ne a gare ni", amma ba kowanne abu ne mai amfani ba. "Dukan abu halal ne a gare ni," amma ba zan yarda wani abu ya mallake ni ba. 13 "Abinci don ciki ne, kuma ciki don abinci ne", amma Allah za ya kawar da su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba. Maimakon haka, jiki don Ubangiji ne, kuma Ubangiji zai yi wa jiki tanaji. 14 Allah ya tada Ubangiji, kuma za ya tashe mu ta wurin ikonsa. 15 Ba ku sani ba jikunanku gabobi ne na Almasihu? Na dauki gabobin Almasihu in hada su da karuwa? Allah ya sawwake! 16 Ko baku sani ba dukan wanda yake hade da karuwa, ya zama jiki daya da ita kenan? 17 Kamar yadda Littafi ya fadi, "Su biyun za su zama nama daya." Amma wanda yake hade da Ubangiji ya zama ruhu daya da shi kenan. 18 Ku gujewa fasikanci! Kowane zunubi mutum yake aikatawa a waje da jikinsa yake, amma mutum mai fasikanci yana zunubi gaba da jikinsa. 19 Ba ku sani ba jikinku haikali ne na Ruhu Mai-tsarki, wanda yake zaune a cikinku, wanda ku ka samu daga wurin Allah? Ba ku sani ba cewa ku ba na kanku ba ne? 20 An saye ku da tsada. Don haka, ku daukaka Allah da jikin ku.
Bulus ya kuma bayana yadda masubi za su shirya saɓani da suaran masubi.
saɓani ko kuma muhawara
Bulus ya na nanata cewa dole ne masubi su tsai da saɓani a sakanin su. AT: "kar ya yi karfin halin tafiya ... masubi!" ko kuma "ya ji tsoron Allah, kadda ya tafi ... masubi!"
wurin da alkalin karamar hukuman gwamnati na duba magana da kuma tsai da mai daidai.
Bulus ya na kunyatar da Korontiyawan domin yadda su na aikatawa kamar basu sani ba .
Domin za a basu baban aiki nan gaba, yakamata su dauki nauyin abubuwa kadan yanzu. AT: "za ku yi wa duniya shari'a a loƙaci gaba, yakamata ku sasanta wannan al'amura yanzu."
"daina muhawara game da abubuwan wannan rai"
Bulus ya na mamaki cewa ba su da alaman sani. AT: "kun san cewa za mu yiwa mala'iku shari'a."
Bulus ya sa kansa da Korontiyawan.
Domin za a basu baban aiki nan gaba, yakamata su dauki nauyin abubuwa kadan yanzu. AT: "Domin za mu yi wa mala'iku shari'a, ya kamata mu san cewa Allah zai sa mu mu yi shari'ar a'lamarin wannan rai."
AT: 1) " wannan tambayane ko kuma 2) wannan bayani ne, "a loƙacin baya da kun sasanta al'amura da ke da muhimminci a wannan rayuwan, ba ku watsar da gardama a sakanin masubi da ya kamata marasabi ne sun sasanta ba" ko kuma 3) wannan umurni ne, "loƙacin da kun sasanta al'amura da suke da muhiminci a wannan rayuwan, na waɗanda ba su da ...a cikin ikilisiya cewa wai ku sasanta al'amuran!"
"Idan an kira ku domin ku daidata game da rayuwa na kulum" ko kuma "Idan dole ne ya kamata ku sasanta al'amuran da ke da muhiminci a wannan rayuwan"
Bulus ya na sawta ma Korontiyawa game da yadda suke sasanta maganganun nan. AT: 1) "ku daina ba da maganganun nan ga mutanen da yan ikilisiya ba." ko kuma 2) "za ku iya ba da maganganun nan wa membobin ikilisiya wadda sauran masubi ba su dauke su komai ba."
"domin rashin mutuncin ku" ko kuma "domin ya nuna yadda kun kasa a wannan al'amarin"
Bulus ya na kunyatar da Korontiyawan. AT: "yakamata ku ji kunyar domin ba ku iya samu mai bi da hikiman da zai sasanta jayayya a sakanin masubi"
Anan na nufin 'yan'uwa masubi tare da maza da mata.
"Ama yadda yake yanzu" ko kuma "Ama maimako"
"masubi wadda suna da gardama da junansu su na tambayan mai shari'a wanda ba mai bi ba ya yi masu hukunci"
AT: "mai bi ya yarda da maganan"
"ya na da rashin cin nasara"
Bulus ya cigaba da kunyatar da Korontiyawan. AT: "zai zama mafi kyau idan kun bar waɗansu su yi maku laifi da kuma cuce ku, da ku kai su kotu."
Dukan masubi a cikin Almasihu 'yan'uwan juna ne. "'yan'uwanku masubi"
Bulus ya nanata cewa yakamata su san wannan gaskiyar. AT: "kun riga ku san cewa"
Karɓan abin da Allah ya yi ma masubi alkawari na nan ne kamar gaje kaya da dukiya daka ɗan iyali.
Allah ba zai hukunta su kamar masu adalci a shari'an ba, kuma ba za su shiga rai mai dawami ba.
AT: 1) "magana ne game da ayukan ludu ko kuma 2) "Bulus ya na sa sunayen ayuka dabam dabam ne.
AT: 1) mazaje da suke yarda wadansu mazaje su kwana da su ko kuma 2) mazaje da suke yarda wadansu mazajen su biya su domin su kwana da su ko kuma 3) mazaje da suke yarda waɗansu mazaje su kwana da su a masayin ayukan addini.
mazaje da suke kwuna da waɗansu mazajen
mutanen da suke sata daga waɗansu
mutanen da suke da niyan yin amfani da mugun hanya domin su ɗauki kayan waɗansu
mutanen da suke sata daga waɗanda sun yarda da su
AT: "Allah ya wanke ku"
AT: "Allah ya keɓe ku wa kansa"
AT: "Allaha ya daidaita ku da shi"
Anan "suna" magana ne game da ƙarfi da ikon Yesu Almasihu. AT: "ta wurin ƙarfi da ikon Ubangji Yesu Almasihun mu"
AT: 1) Bulus ya na amsa abin da waɗansu Korontiyawan za su iya yin tunani, "waɗansu sun ce, 'zan iya in yi komai" ko kuma 2) Bulus ya na faɗan abin da ya ke tunani cewa daidai ne, "Allah ya yarda ma ni in yi komai."
Bulus ya na amsa wadda a ce, "kowanne abu halal ne a gare ni." AT: "amma ba kowanne abu ne ya ke da kyau a gare ni ba"
AT: "ba zan yarda wadanan abubuwa su yi mulki a kai na kamar maigida ba"
AT: 1) "Bulus ya na gyara abin da waɗansu Korontiyawan za su iya yin tunani, "abinci don ciki, kuma ciki don abinci ne," ta wurin amsa cewa Allah zai kawar da cikin da kuma abincin duka ko kuma 2) Bulus ya yarda cewa "abinci don ciki, kuma ciki don abinci ne," amma ya kara cewa Allah zai kawar da su duka.
Wannan na iya nufin cewa mai maganan na magana game da jiki da kuma jima'i, amma ku fasara wannan kamar "ciki" da "abinci."
"hallaƙa"
"sa Ubangiji ya rayu kuma"
Kalman da an fasara kamar "gabobi" na nufin sashi na jiki. An yi maganan kasancewan mu da Almasihu kaman muna cikin jikinsa. Mun zama na shi sosai, har jikinmu ya zama na shi. Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya tuna wa mutanin game da abin da yakamata sun sani. AT: "Ku san cewa jikin ku na Almasihu ne"
Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya nanata yadda ba kyau wanin da ya zama na Almasihu ya je wurin karuwa. AT: "Ina cikin Almasihu. Ba zan ɗauka jiki na in hadda da karuwa ba!" ko kuma "Mu na cikin jikin Almasihu. Ba lalai ba ne mu ɗauki jikinmu mu hadda da karuwa ba!"
"Kadda wancan ya faru!" ko kuma "kadda mu yi haka!"
Bulus ya fara koyar da Korontiyawan ta wurin nanata gaskiyan da sun riga sun sani. "Ina so in tuna maku cewa ... ita."
AT: "a loƙacin da na miji a haɗa jikinsa da jikin karuwa, yana nan kamar jikinsu ya zama jiki ɗaya"
AT: "a loƙacin da Ubangiji ya hada ruhunsa da ruhun mutum, yana nan kamar ruhohin sun zama ruhu ɗaya"
Bulus na magana game da mutum da ke kin zunubin fasikanci kamar mutumin ya na gudun hatsari. AT: "tashi daga"
Su na iya nufin 1) Bulus ya na nuna cewa zunubin fasikanci ba bu kyau domin yana gaba da jikin mai zunubi da kuma waɗansu. ko kuma 2) Bulus ya na faɗan abin da waɗansu Korontiyawan suke tunani. AT: "fasikanci! Waɗansunku na ce, 'kowane zunubin da mutum ya yi na wajen jiki; amma na ce"
"mugun ayuka da mutum yake yi"
Bulus ya cigaba da koyar da Korontiyawan ta wurin nanata abin da sun riga sun sani. AT: "Ina so in tuna maku ... Allah, cewa ku ba na kanku ba ne."
jikin kowane mai bi haikali ne na Ruhu mai Tsarki
Wani haikali aka sadaukar domin Allahntaka, kuma wurin ne suke zama. A haka, jikin kowane mai bi na Koronti ya na nan kamar haikali ne domin Ruhu mai Tsarki na nan a sakaninsu.
Allah ya biya wa yancin Korontiyawa daga bautar zunubi. AT: "Allah ya biya wa yancinku"
"domin abin da na faɗa daidai ne"
Bulus ya ce za su iya shar'anta jayayya sakanin tsarkaku bisa ga al'amurar duniya na wannan rayuwa.
Tsarkaku za su shar'anta duniya da mala'iku.
Mai bi ya na kai karar mai bi a kotu, kuma a gaban mai shari'a wanda ba mai bi ba.
Na nuna cewa wannan rashin cin nasara ne a garesu.
Marasa adalci masu fasikanci, da masu bautar gumaka, da mazinata, da karuwai maza, da masu ludu, da barayi, da masu zari, da mashaya, da masu zage-zage, da 'yan damfara - ba za su gaji Mulkin Allah ba.
An tsarkake su, an mika su ga Allah, an mai da tsayuwar su dai-dai a gaban Allah a cikin sunan Ubangji Yesu Almasihu, kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.
Bulus ya ce abinci ko faskanci ba za su mallake shi ba.
A'a. Allah ya sawwake!
Jikunansu gabobi ne na Almasihu.
Ya zama jiki ɗaya da ita.
Ya zama ruhu ɗaya da shi
Su na yin zunubi wa jikunarsu a loƙacin da suke yin fasikanci.
Ya kamata masubi su ɗaukaka Allah da jikunarsu domin jikinsu haikali ne na Ruhu Mai-tsarki kuma don an saye su da farashi.
1 Game da abubuwan da kuka rubuto: "Yayi kyau ga mutum kada ya taba mace." 2 Amma Saboda jarabobi na ayyukan fasikanci masu yawa, ya kamata kowane mutum ya kasance da matarsa, kowace mace kuma ta kasance da mijinta. 3 Kowanne maigidanci ya ba matarsa hakin ta, kuma kowace mace ta ba maigidan ta hakinsa na saduwa da juna. 4 Matan ba ta da iko akan jikin ta amma maigidan ne. Haka ma, maigidan bashi da iko akan jikinsa amma matar ce. 5 Kada ku hana wa junanku saduwa, sai dai da yardar junanku domin wani dan lokaci. Kuyi haka domin ku bada kanku ga addu'a. Daganan sai ku sake saduwa, domin kada Shaidan ya jarabce ku saboda rashin kamun kanku. 6 Amma ina fada maku wadannan abubuwa ne a matsayin nuni, ba a matsayin umurni ba. 7 Na so da kowa da kowa kamar ni yake. Amma kowa na da baiwarsa daga wurin Allah. Wani na da irin wannan baiwar, wani kuma waccan. 8 Ga marasa aure da gwamraye, Ina cewa, yana da kyau a garesu su zauna ba aure, kamar yadda nike. 9 Amma idan baza su iya kame kansu ba, ya kamata su yi aure. Gama yafi masu kyau su yi aure da su kuna da sha'awa. 10 Ga masu aure kwa, ina bada wannan umarni- ba ni ba, amma Ubangiji: "Kada mace ta rabu da mijinta." 11 Amma idan har ta rabu da mijinta, sai ta zauna ba aure ko kuma ta shirya da shi. Haka kuma " Kada miji ya saki matarsa." 12 Amma ga sauran ina cewa-Ni, ba Ubangiji ba-idan wani dan'uwa yana da mata wadda ba mai bi ba, kuma idan ta yarda ta zauna da shi, to kada ya sake ta. 13 Idan kuwa mace tana da miji marar bi, idan ya yarda ya zauna tare da ita, to kada ta kashe aure da shi. 14 Gama miji marar bada gaskiya ya zama kebabbe saboda matarsa, sannan mata marar bada gaskiya ta zama kebbiya saboda mijinta mai bi. In ba haka ba 'ya'yanku za su zama marasa tsarki, amma a zahiri su kebabbu ne. 15 Amma idan abokin aure marar bi ya fita, a bar shi ya tafi. A irin wannan hali, dan'uwa ko 'yar'uwa ba a daure suke ga alkawarinsu ba. Allah ya kira mu da mu zauna cikin salama. 16 Yaya kika sani, ke mace, ko za ki ceci mijinki? ko yaya ka sani, kai miji, ko za ka ceci matarka? 17 Bari dai kowa ya yi rayuwar da Ubangiji ya aiyana masa, kamar yadda Allah ya kirawo shi. Wannan ce ka'idata a dukkan ikilisiyu. 18 Mutum na da kaciya sa'adda aka kira shi ga bada gaskiya? Kada yayi kokarin bayyana kamar marar kaciya. Mutum ba shi da kaciya sa'adda aka kira ga bangaskiya? To kada ya bidi kaciya. 19 Gama kaciya ko rashin kaciya ba shine mahimmin abu ba. Mahimmin abu shine biyayya da dokokin Allah. 20 Kowa ya tsaya cikin kiran da yake lokacin da Allah ya kira shi ga bada gaskiya. 21 Kai bawa ne lokacin da Allah ya kirawo ka? Kada ka damu da haka. Amma idan kana da zarafin samun 'yanci, ka yi haka. 22 Domin wanda Ubangiji ya kira shi lokacin da yake bawa, shi 'yantacce ne na Ubangiji. Hakanan kuma, wanda shike 'yantacce lokacin da aka kira shi ga bada gaskiya, Bawan Almasihu ne. 23 An saye ku da tsada, donhaka kada ku zama bayin mutane. 24 Yan'uwa, a kowace irin rayuwa kowannenmu ke ciki lokacin da aka kira mu ga bada gaskiya, bari mu tsaya a haka. 25 Game da wadanda basu taba aure ba, ba ni da wani umarni daga wurin Ubangiji. Amma ina bada ra'ayina kamar mutum wanda, ta wurin jinkan Allah, yake yardajje. 26 Don haka, Ina ganin saboda yamutsin dake tafe ba da jimawa ba, ya yi kyau mutum ya zauna yadda yake. 27 Kana daure da mace? Kada ka nemi 'yanci daga gare ta. Baka daure da mace? Kada ka nemi auren mace. 28 Amma idan ka yi aure, ba ka yi zunubi ba. Kuma idan mace marar aure ta yi aure, bata yi zunubi ba. Saidai su wadanda suka yi aure za sha wahalhalu iri-iri a yayinda suke raye, kuma ina so in raba ku da su. 29 Amma wannan nike fadi ya'nuwa: lokaci ya kure. Daga yanzu, bari wadanda suke da mata suyi rayuwa kamar basu da su. 30 Masu kuka su zama kamar marasa kuka, masu farinciki kamar marasa farinciki, masu sayen abubuwa kamar marasa komai. 31 Wadanda suke harka da duniya kamar ba su harka da ita, domin ka'idar duniyan nan tana kawowa ga karshe. 32 Ina so ku kubuta daga damuwa mai yawa. Mutum marar aure yana tunani akan al'amuran Ubangiji, yadda zai gamshe shi. 33 Amma mai aure yana tunani akan al'amuran duniya, yadda za ya gamshi matarsa, 34 hankalinsa ya rabu. Mace marar aure ko budurwa tana tunanin al'amuran Ubangiji, yadda za ta kebe kanta a jiki da ruhu. Amma mace mai aure tana tunanin al'amuran duniya, yadda za ta gamshi mijinta. 35 Ina fadar wannan domin amfaninku ne, ba domin in takura ku ba. Na fadi wannan domin abinda ke daidai, yadda zaku bi Ubangiji ba tare da hankalinku ya rabu ba. 36 Amma idan wani yana tunani da cewa baya yin abinda ya dace ga budurwarsa- idan ta wuce shekarun aure, kuma hakan ya zama dole- sai yayi abinda yake so. Ba zunubi yake yi ba. Sai suyi aure. 37 Amma idan ya tsaya da karfi a zuciyarsa, idan baya shan wani matsi kuma yana iya kame kansa, har ya kudurta a zuciyarsa yayi haka, wato ya kiyaye budurwarsa da yake tashi, to hakan ya yi daidai. 38 Don haka, shi wanda ya auri budurwarsa yayi daidai, sannan shi wanda ya zabi yaki yin aure yafi yin daidai. 39 Mace tana a daure ga mijinta a duk tsawon rayuwarsa. Amma idan mijin ya mutu, tana da 'yanci ta auri duk wanda take so ta aura, amma a cikin Ubangiji. 40 Amma a ganina, za ta fi farinciki idan za ta zauna yadda take. Kuma ina tunanin ni ma ina da Ruhun Allah.
Bulus ya ba masubi takamaiman dokoki game da aure.
Bulus ya na gabatar da sabon batu a cikin koyaswarsa.
Korontiyawa sun rubuto wasika wa Bulus don su tambaye shi game da amsoshi akan waɗansu tambayoyin.
AT: 1) Bulus ya na faɗan abin da Korontiyawa sun rubuto, "game da: kun rubuto, ' 'Yayi kyau wa na miji kada ya taɓa mace.' gaskiya ne, amma saboda" ko kuma 2) Bulus ya faɗa abin da ya na tunani, "game da: amsa na shi ne i, ya na da kyau kaɗa na miji ya taɓa mace. Amma Saboda"
"ya na da taimako sosai"
AT: 1) "na miji" na nufin na miji mai aure. AT: "mai gida" ko kuma 2) "na miji na nufin kowane mutum.
Su na iya nufin 1) "taɓa mace" magana ne game da yin jima'i. AT: "kada ya yi jima'i da matar sa a dan loƙaci" ko kuma 2) "taba mace" magana ne game da aure. AT: "kada ya yi aure"
"Amma saboda Shaidan yana jarabtan mutane don su yi fasikanci, kowane" ko kuma "Amma mu na so mu yi fasikanci saboda zunubi, don kowane"
An umurta cewa ya kamata mazaje da mataye su ringa kwuana da abokan aurensu.
An riga an gane kalmomin "ya ba" da "hakin saduwa da juna" a jumla da ya wuce. AT: "haka kuma, kowace mace ta ba maigidan ta hakinsa na saduwa da juna"
Kalman "ƙi" na nufin hana wani abin ya ke da yancin karbawa. "Kada ku ki saduwa da abokan aurenku"
domin ku iya samu loƙacin addu'a mai zurfi
"danƙa kanku"
"kwana tare kuma"
"domin bayan wadansu kwanaki, sha'awar ku zai fi karfin ku"
AT: Bulus ya na faɗa wa Korotiyawan cewa ya na barin su ne, ba wai ya na umurtasu ba ne, 1) don yin aure da kuma kwana tare ko kuma 2) don daina kwana tare na dan loƙaci.
Ko Bulus bai taɓa aure ba ko kuma matanshi ta mutu. Da shakka ne idan ya taba yin saki.
"Allah ya na sa mutane su yi abubuwa dabam dabam. Ya na sa mutum daya ya yi abu ɗaya, ya na kuma sa wani ya yi wani abu dabam"
"wannan waɗanda ba su yi aure ba ne"
"ga matayen da mazajensu sun mutu"
"domin rayuwa a cikin son marmarin kwana da wani kullum"
Ma su sauraran Bulus ba su san bambancin rabu wadda saki ba. Daina zama da wani na nufin kashe aure. AT: "kaɗa ku saka"
AT: "ta sasanta da mijinta, ta kuma koma mashi"
Ma su sauraran Bulus ba su san bambancin rabu wada saki ba. Aikata wannan shi kashe aure. AT: "kada ku rabu daga"
"isa"
AT: 1) "Gama Allah ya kebe miji marar bada gaskiya wa kansa saboda matarsa da ta bada gaskiya" ko kuma 2) "Allah ya na yi ma miji mara bada gaskiya kamar yadda zai yi wa ɗa saboda matarsa wadda ta bada gaskiya"
waɗannan ne kalmomin Greek na "miji" da "mace."
Su na iya nufin 1) "Allah ya keɓe mata marar bada gaskiya wa kansa saboda mijinta da ya bada gaskiya" ko kuma 2) "Allah ya na yi ma mata mara bada gaskiya kamar yadda zai yi wa 'ya saboda mijinta wadda ya bada gaskiya"
na miji ko mai gida da ya ba da gaskiya
AT: 1) Allah ya kebesu wa kansa" ko kuma 2) "Allah ya yi masu kamar yadda zai yi wa 'ya'yansa"
Anan "ɗan'uwa" da "'yar'uwa" na nufin mata da miji masubi. Anan "ɗaure suke ga alkawarinsu" magana ne da ke nufi cewa ba a tilas'a mutumin ya yi abin da sun yi alkawari cewa za su yi ba. AT: "A irin wannan halin, Allah ba ya bukutan mai aure da ya gaskanta ya cigaba da bin alkawarin aure"
Bulus ya na magana da Korontiyawan kamar su mutane daya ne, duka misalai na "ku" daya ne.
Bulus ya yi amfani da tambayan domin ya sa mata su yi tunani da zurfi game da abin da yake faɗa. AT: "baza ki san ko za ki cece mijin ki da bai gaskanta ba."
Bulus ya yi amfani da tambayan domin ya sa maza su yi tunani da zurfi game da abin da yake faɗa. AT: "baza ka san ko za ka cece matar ka da bata gaskanta ba."
"ko wane mai bi"
Bulus ya na koyar da masubi a dukkan ikilisiyu don su aikata a wannan hanya.
Bulus yana magana da masu kaciya
Yanzu Bulus yana magana da marasa kaciya. AT: "Ga marasa kaciya, A loƙacin da Allah ya kira ku ku gaskanta, ba ku yi kaciya ba"
Anan, kalmomin "mu" na nufin dukan masubi tare da masu sauraran Bulus.
Anan " kira" na nufin aiki ko masayi da ku ke ciki. AT: "yi rayuwa da aiki yadda ku ke yi"
Bulus ya na magana da Korontiyawa kaman su ɗaya ne, duka misalai na "ku" da umurnin "zama" daya ne.
AT: "ga waɗanda su bayi ne a loƙacin da Allah ya kira ku ku gaskanta, na faɗa wannan: kada ka damu"
Allah ya yafe wannan 'yantaccen mutum, don haka yana da salama daga Haidan da zunubi.
AT: "Almasihu ya saye ku ta wurin mutuwa domin ku"
Anan, wannan na nufin yanuwa masubi tare da maza da mata.
AT: "A loƙacin da Allah ya kira mu mu gaskanta da shi"
Bulus bai san koyarwa game da Yesu da ya yi magana akan yanayin nan ba. AT: "Allah bai umurce ni in faɗa wani abu game da mutanin da basu taba yin aure ba"
"Na faɗa maku abin da nake tunani"
"domin, ta wurin jinkan Ubangiji, Ina yardajje"
Bulus ya na magana da Korontiyawan kaman ya na magana ne da kowane mutum, waɗannan misalai "ku" da " da kuma umurnin "kadda ku nema" daya ne. Ka na auren mata ne? Kada ... Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya bayana yanayi mai yiwuwa. Ana iya fasara tambayan kamar jumla tare da "idan."Idan kun yi aure, kada"
"kada ka kuskura ka sake ta" ko kuma "ka gwada rabuwa da ita"
"kada ka kuskura yin aure"
Kalman"wannan" na nufin irin damuwa ta duniya da masu aure ke iya samu. AT: "Ina so in taimake ku don kada ku samu damuwa ta duniya"
"Akwai ƙanƙanin loƙaci" ko kuma "Loƙaci ya yi kusan tafi"
yi kuka ko bakin ciki da hawaye
"waɗanda suke harka kullum da marasa bi"
"su nuna ta wurin ayukan su cewa sun sa begensu ga Allah"
"kubuta" karin magana ne da ke nufin yin rayuwa ba tare da tunani kulum ba."
"sa hankali a"
"ya na so ya sa Allah ya ji dadin sa, ya na kuma so ya sa matansa ta ji dandin sa a loƙaci daya"
ƙuntata
"iya duƙufa a"
"ba kirki" ko kuma "ba darajawa"
AT: "macen da ya yi alkawari ya aura" ko kuma 2) "budurwan 'yar shi."
AT: 1) "ya aure budurwansa" ko kuma 2) "ya bar 'yar shi ta yi aure."
Anan "tsaya da karfi" magana ne na shirya abu ba shaka. Anan "zuciya" magana ne game da hankalin ko tunanin mutum. AT: "Amma idan ya shirya da karfi a zuciyarsa"
Anan "ɗaure" magana ne game da ɗangantaka a sakanin mutane da suke taimakon juna ta ruhaniya, ayuka da kauna. Anan na nufin saduwan aure. AT: "mace ta na aure da mijinta" ko kuma "mace ta na a haɗe da mijinta"
"sai ya mutu"
"duk wanda take bukata"
"idan sabon mijin mai bi ne"
"fahintana na maganan Allah"
mafi yawan wadata, mafi yawan murna
"kasance ba aure"
Saboda jarabobi na ayyukan fasikanci masu yawa, ya kamata kowane mutum ya kasance da matarsa, kowace mace kuma ta kasance da mijinta.
A'a. Mai gida na da iko akan jikin matarsa haka kuma mace ta na da iko akan jikin mai gidanta.
Daidai ne idan miji da mata sun yarda sun kuma shirya loƙaci domin su iya duƙufa kansu ga addu'a.
Bulus ya ce na da kyau su zauna ba aure.
Su yi aure indan suna kuna da sha'awa kuma ba za su iya kama kansu.
Kada mace ta rabu da mijinta, Amma idan har ta rabu da mijinta, sai ta zauna ba aure ko kuma ta shirya da shi. Haka kuma Kada miji ya saki matarsa.
Idan mijin ko matar da ba mai bi sun yarda su zauna da abokan aurensu, kada mai bi ya saki wanda ba mai bi ba.
Mai bin ya bar abokin aurensa da ba mai bi ba ya tafi..
Dokan ita ce: Bari kowa ya yi rayuwar da Ubangiji ya aiyana masa, kuma wanda Allah ya kirawo shi.
Bulus ya ce kada marasa kaciya su yi kaciya kuma kada masu kaciya su so su cire alamun kaciyarsu.
Idan su biwa ne a loƙacin da Allah ya kira su, kada ku damu, amma idan za su iya sami 'yanci, su yi kokari. Idan su bayi ne, su 'yantattun mutumin Ubangiji ne. Kada su zama bayin mutane.
Bulus ya gan cewa saboda hargitsi da ke zuwa, ya yi kyau mutum ya zauna babu aure.
Kada su nemi 'yanci daga alkawarinsu na aure macen.
Ya faɗa wannan domin ya so ya cece su daga wahalhalu iri-iri da waɗanda sun yi aure zasu samu a yayinda suke raye.
Su yi haka domin ka'idar duniyan nan tana kawowa ga karshe.
Ya na da wuya domin miji ko mace mai bi na tunani akan al'amuran duniya, yadda za ya gamshi matarsa ko maigidanta.
Shi wanda ya ƙi yin aure yafi yin daidai.
Za ta iya aure wanda take so ta aura, amma a wanda ke cikin Ubangiji.
Mace tana a ɗaure ga mijinta a duk tsawon rayuwarsa.
1 Game da abinci da ake yiwa gumakai hadaya: Mun sani cewa, "Dukanmu muna da ilimi." Ilimi ya kan kawo takama, amma kauna tana ginawa. 2 Idan wani yana tunanin ya san wani abu, wannan mutumin bai rigaya ya san abinda ya kamata ya sani ba. 3 Amma idan wani yana kaunar Allah, to ya san da wannan mutum. 4 Game da abincin da aka yiwa gumakai hadaya: Mun san cewa, "Gunki a duniyan nan ba wani abu bane," kuma cewa" Babu wani Allah sai guda daya." 5 To wata kila ma a ce wadanda ake kira alloli sun kasance, ko a cikin sama ko duniya, kamar yadda akwai wadanda ake ce dasu "alloli dabam dabam a duniya ko a sama," kamar yadda akwai "alloli da iyayengiji" da yawa. 6 "Amma a wurin mu, Allah daya ne, Uban dukan duniya, daga wurinsa aka halita dukan abu, domin sa muke rayuwa, Ubangiji Yesu Almasihu daya, wanda ta wurin sa kome ya kasance, mu kuma daga wurinsa muke." 7 Amma ba kowa ke da wannan ilimi ba. Shi ya sa tun da, wadan su na bauta wa gunki, kuma suna cin wannan abincin kamar abin da aka mika wa gunki. Lamirin su ya kazantu sabo da yana da rauni. 8 Amma ba abinci ke bamu tagomashi a wurin Allah ba. Ko mun ci, bamu kara karbuwan mu ba, ko ba mu ci ba, ba mu rage karbuwan mu ba. 9 Amma, ka yi hatara kada 'yancin ka ya zama sanadiyar tuntuben wani mai rarraunar bangaskiya. 10 Anar misali, idan wani mai rarraunar lamiri ya hango ka mai ilimi, kana cin abincin da aka mika wa gunki, ai ba ka bashi kwarin gwiwa kenan yaci abincin da aka mika wa gunki ba? 11 Sabili da ganewar ka akan yanayin gumaka, dan'uwa rarrauna wanda Yesu ya mutu domin sa ya hallaka. 12 Saboda haka, idan ka saba wa 'yan'uwa masu raunin a lamiri, ka yi zunubi a gaban Almasihu. 13 Idan abinci zai sa dan'uwa na yayi tuntube, zan huta cin nama, domin kada in jawo wa 'yan'uwana faduwa.
Bulus ya tuna wa masubi cewa ƙodashike gumakai ba su da iƙo, yakamata masubi su yi hankali kadda su taɓa wadanda ba su yi karfi a bi ba, wadda su na iya tunani cewa sun damu da gumakai. Ya faɗa wa masubi cewa su yi hankali da yancin da suke da shi a cikin Almasihu.
"Mu" na nufin Bulus, ƙodashike ya na rubutu musamman wa masubi na Korontiyawa, da dukkan masubi.
Bulus ya yi amfani da wannan jumla domin ya yi gaba game da tambayan da Korontiyawan sun tambaye shi.
Al'ummai masu sujada zasu mika hatsi, kifi, kaza, ko nama wa allolinsu. Firis zai kona wani kashin a kan tebur a cikin Majami'a. Bulus ya na magana game da kashin da firis zai ba wa masu sujada domin su ci ko kuma su sayad a kasuwa.
"Ilimi ya kan kawo takama wa mutane." Anan "takama" magana ne game da sa wani girman kai. Ana iya bayana "Ilimi" da "sani." AT: "Ilimi na sa mutane girman kai" ko kuma "Mutanin da suke tunani cewa sun sani sosai suna zama da girman kai"
Ana iya bayan kalmar "kauna". AT: "amma a loƙacin da mun kaunace mutane, muna ginasu"
Gina mutane na wakilcin taimaka masu su yi girma da karfi a cikin bangaskiyansu. AT: "ƙauna na karfafa mutane" ko kuma "a loƙacin da mun kaunace mutane, mu na karfafasu"
"ya gaskanta cewa ya san komai game da wani abu"
AT: "Allah ya san wancan mutumin"
Mia yiwuwa Bulus ya na fadan jumlan da wadansu Korontiyawan su yi amfani. Zaman "komai" na wakilcin rashin iƙo. AT: "Mun sani, kamar yadda ku na son faɗa, cewa gunki a wannan duniya ba shi da iƙo kuma babu wani Allah sai guda ɗaya"
"abubuwan da mutane ke kira alloli"
Bulus bai yarda cewa akwai alloli dayawa da kuma iyayengiji da yawa ba, amma ya yarda cewa kafirai sun gaskanta akwai.
"Amma mun san cewa Allah ɗaya ne"
"dukkan mutane ... waɗansu mutanen da sun zama masubi yanzu"
lahani ko illa
Bulus ya yi magana game da abinci kamar mutum ne da zai iya sa Allah ya marabce mu. AT: "abinci ba ya ba mu tagomashi da Allah" ko kuma "abincin da muke ci ba ya sa Allah ya ji dadinmu"
AT: "Waɗansu mutane na iya tunani cewa idan bamu ci wadansu abubuwan ba, Allah zai ƙaunace mu kadan. Basu yi daidai ba. Wadanda suke tunani cewa Allah zai ƙaunace mu sosai idan mun ci waɗancan abubuwa, basu yi daidai ba"
masubi da ba su da karfi a bangaskiyansu
Bulus ya na magana da Korontiyawan kaman su mutum daya ne, kalmomin nan ɗaya ne.
abin da ya gane cewa daidai ko ba daidai ba ne
"ƙarfafa ya ci"
Bulus ya na magana da Korontiyawa kamar su mutum daya ne, kalmar "ku" anan daya ne.
ɗan'uwa ko 'yar'uwa da ba shi da karfi a bangaskiyansa zai yi zunubi ko ya rasa bangaskiyansa.
"Domin abin da na faɗa daidai ne"
Anan "abinci" magana ne game da mutum da yake cin abinci. AT: "idan na sa ta wurin cin" ko kuma "idan na, domin abin da na ci, sa"
Ilimi na sa takama, amma ƙauna tana ginawa.
Bulus ya yi maganar abinci da ake yiwa gumakai hadaya.
A'a Gunki a duniyan nan ba wani abu bane, kuma babu wani Allah sai ɗaya.
Akwai Ubangiji Yesu Almasihu, ta wurin wanda dukka abubuwa sun kasance, kuma ta wurin wanda muke rayuwa.
Akwai Allah Uba ɗaya kadai. Daga wurinsa akwai dukka abubuwa, kuma muna rayuwa dominsa.
Lamirin su ya kazantu sabo da yana da rauni.
Abinci ba zai bamu tagomashi a wurin Allah ba. Ko mun ci, bamu kara karbuwan mu ba, ko ba mu ci ba, ba mu rage karbuwan mu ba.
Mu yi hatara kada 'yancin mu ya zama sanadiyar tuntuben wani mai rarraunar bangaskiya.
Ana iya hallaka ɗan'uwa ko 'yar'uwa mai lamiri mai rauni.
Mun yi zunubi ga ɗan'uwa ko 'yar'uwa da an sa su tuntuɓe mun kuma yi zunubi a gaban Almasihu.
Bulus ya ce zai yi idan abinci ya sa ɗan'uwansa ko 'yar'uwarsa tuntuɓe, ba zai sake cin nama kuma ba.
1 Ni ba yantacce bane? Ni ba Manzo ba ne? Ban ga Ubangijinmu Yesu ba? ba ku ne aikin hannuna cikin Ubangiji ba? 2 Idan ni ba Manzo ba ne ga wadansu, hakika ni Manzo ne a gare ku. Ai kune shedar manzanci na cikin Ubangiji. 3 Ga kariya ta zuwa masu zargi na, 4 Ba mu da 'yanci mu ci mu sha? 5 Ba mu da 'yanci mu dauki mace mai bada gaskiya kamar sauran manzanni da Kefas da 'yan'uwan Ubangiji? 6 ko ni da Barnabas ne kawai muka cancanci aiki? 7 Wake aikin soja daga aljihunsa? Wake shuka gonar inabi baya ci daga 'ya'yan ta ba? Ko kuwa wake kiwon tumaki ba ya shan madarasu? 8 Ina wannan zance da ikon mutum ne? Doka bata fadi haka ba? 9 Gama a rubuce yake a attaura ta Musa cewa, Takarkari mai tattake hatsi kada a sa masa takunkumi. Amma shanu ne Ubangiji ke zance a kai? 10 Ba don mu yake magana ba? An rubuta domin mu ne. Domin wanda yake noma, yayi cikin bege. mai tattake hatsi kuma yayi da begen samu. 11 Idan mun yi shuka ta ruhaniya a rayuwarku, mai wuya ne mu girbi kayan ku na jiki? 12 Idan wadansu sun mori wannan 'yanci a gurin ku, ba mu fi su cancanta ba? duk da haka bamu yi amfani da wannan 'yancin ba, maimakon haka, mun yi jimriya da duk abin da zaya hana bisharar Yesu Almasihu. 13 Baku sani ba masu bauta a haikali suna samun abincinsu ne daga haikalin? Baku sani ba masu bauta a bagadi, suna da rabo daga abin da ake kawowa kan bagadin? 14 Haka kuma Ubangiji ya umarta masu aikin bishara zasu ci abincinsu ta hanyar bishara. 15 Amma ban yi amfani da wannan 'yanci ba, ba kuma ina rubuta maku domin ayi mani wani abu bane, na gwanmace in mutu maimakon wani ya hana ni wannan fahariya. 16 Ko nayi shelar bishara, ba ni da dalilin fahariya domin ya zama dole in yi. Kaito na idan ban yi shelar bishara ba 17 Idan na yi hidimar nan da yardar zuciyata, ina da sakamako, idan kuma ba da yaddar zuciyata ba, harwa yau akwai nauwaya akai na. 18 To menene sakamako na? shi ne in yi shelar bishara kyauta, da haka ba zan yi amfani the 'yanci na cikin bishara ba 19 Ko da shike ni 'yantacce ne ga duka, amma na mai da kaina bawan kowa domin in ribato masu yawa, 20 Ga yahudawa, na zama bayahude, domin in ribato yahudawa, ga wadanda ke karkashin shari'a, na maishe kaina kamarsu, domin in ribato wadanda ke karkashinta. Na aikata wannan ko da shike bana karkashin shari'a 21 Ga wadanda basu karkashin shari'a, na maishe kaina kamar su. Ko da shike ban rabu da shari'ar Allah ba. Amma ina karkashin dokar Almasihu. Na yi haka ne domin in ribato wadanda ba sa karkashin shari'a. 22 Ga marasa karfi, na maishe kaina kamar marar karfi, domin in ribato raunana. Na mai da kaina dukan abu ga dukan mutane domin in sami zarafin da zan ribato wadansu zuwa ceto. 23 Ina dukan abu sabili da bishara, domin kuma in sami albarkar da ke cikinta 24 Baku sani ba mutane da dama suna shiga tsere amma daya neke karbar sakamakon, saboda haka ku yi tsere domin ku karbi sakamako. 25 Dan wasa yana motsa jiki da kame kansa. Yana yi saboda ya karbi wannan sakamako mai lalacewa, amma muna tsere domin mu karbi sakamako marar lalacewa. 26 Saboda haka ba na tsere ko fada haka nan kamar mai bugun iska. 27 Amma ina matse jiki na in maishe shi bawa, kada bayan na yi wa wadansu wa'azi ni kuma a karshe a fitar da ni.
Bulus ya bayana yadda yake amfani da yancin da yana da shi a cikin Almasihu.
Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya tuna wa Korontiyawan game da iƙon da yake da shi. AT: "Ni yantaccen mutum ne."
Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya tuna wa Korontiyawan game da kansa da kuma iƙon da yake da shi. AT: "ni Manzo ne."
Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya tuna wa Korontiyawan game da kansa. AT: "na ga Ubangijinmu Yesu."
Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya tuna wa Korontiyawan game da dangantakansu da shi. AT: "kun ganskanta da Almasihu domin na yi aiki yadda Ubangiji yake so in yi.
"shedar" a nan na nufin magana game da alamu da ake so domin a hakikanta wani abu. AT: "ku shedu ne da zan iya yin amfani domin in hakikanta cewa Ubangiji ya zaɓe ni don in zama manzo"
AT: 1) kariyan Bulus ne kalmomin da suke bi ko kuma 2) kalmomin cikin 9:1-2 kariyan Bulus ne, "Ga kariya ta ...ni. Ba."
Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya nanata cewa ya san Korontiyawan sun amince da abin da yake faɗa. AT: "mu na da tabacecen iƙon mu karɓa ci da sha daga ikilisiyoyi."
Anan "mu" na nufin Bulus da Barnabas.
Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya nanata cewa ya san Korontiyawan sun amince da abin da yake faɗa. AT: "idan mu na da mataye da sun ganskanta, mu na da iko mu ɗauke su kamar yadda sauran mazannin sun yi, da yan'uwanin Ubangiji, da Kafas."
Bulus ya na kunyatar da Korontiyawan. AT: "ku na tunani da alama cewa mutuanen da yakamata su yi aiki domin su samu kuɗi shine ni da Barnabas."
Bulus ya yi amfani da tambaya domin ya nanata cewa ya san Korontiyawan sun amince da abin da yake faɗa. AT: "Mun san cewa babu sojan da zai saya guzurinsa." ko kuma "Mun san cewa kowane soja ya na karɓan guzurinsa daga gwamnati ne."
Bulus ya yi amfani da tambaya domin ya nanata cewa ya san Korontiyawan sun amince da abin da yake faɗa. AT: "Mun san cewa wadda ya shuka gona ne zai ci 'ya'yansa." ko kuma "Mun san cewa ba wadda ya ke tsammani cewa wadda da ya shuka gona ba zai ci 'ya'yansa ba."
Bulus ya yi amfani da tambaya domin ya nanata cewa ya san Korontiyawan sun amince da abin da yake faɗa. AT: "Mun san cewa waɗanda suke kiwon tumaki na samu sha daga tumakin."
Bulus yana kunyatar da Korontiyawan. "ku na tsammani cewa ina ina faɗan abubuwa bisa iƙon mutum."
Bulus yana kunyatar da Korontiyawan. AT: "ku na yi kamar ba ku san cewa wannan ne abin da an rubuta a doka ba."
Musa yana magana da Isra'ilawa kaman su mutum ɗaya ne, wannan dokan daya ne.
Bulus ya yi tambaya domin Korontiyawan su yi tunani game da abin ya ke faɗa ba sai ya faɗa ba. AT: "Ya kamata ku sani ba sai na faɗa maku cewa ba shanu ne Allah ya fi damu da shi ba."i
Bulus ya yi tambaya domin ya nanata jumlan da yake yi. AT: "maimako, haƙiƙa Allah ya na magana game da mu."
Anan "mu" na nufin Bulus da Barnabas.
Bulus ya yi tambaya domin Korontiyawan su yi tunani game da abin da yake faɗa ba sai ya faɗa ba. AT: "Ya kamata ku sani ba sai na faɗa maku cewa taimakun ba zai yi mana yawa in mun karɓa ba."
Bulus ya yi tambaya domin Korontiyawan su yi tunani game da abin da yake faɗa ba sai ya faɗa ba. Anan "mu" na nufin Bulus da Barnabas. AT: "Waɗansu sun mori ... ku, Kun sani ba sai na faɗa maku cewa mu na da wannan iƙo fiye."
Bulus da Korontiyawan su sani cewa waɗansu sun mori iƙon. "tunda wadansu sun mori wannan iƙo"
wadansu ma'aikata na bishara
iƙon da zai sa masubi na Koronti su tanada abubuwa wa waɗanda sun faɗa masu game da bishara
"zama nauyi" ko kuma " daina baza"
Bulus ya na tuna wa Korontiyawan game da abin da sun sani domin ya kara waɗansu bayanen. AT: "Ina so in tuna ma ku cewa wadanda su na bauta a haikali suna samun abincinsu ne daga haikalin."
Bulus ya na tuna wa Korontiyawan game da abin da sun sani domin ya kara waɗansu bayanen. AT: "Ina so in tuna ma ku cewa waɗanda su na bauta a bagadi suna samun abincinsu ne daga bagadi."
Kalmar "bishara" anan magana ne game da 1) mutanen da aka gaya masu game da bisharan, sun karɓa abinci da waɗansu kayakinsu da suna so daga waɗanda suka koya masu game da bisharan," ko kuma 2) shaidan aikin bishara, "sun karba abinci da waɗansu kayakinsu da suke so domin sun yi aikin shelar bisharan."
"wannan abubuwan da na chanchanci"
AT: "domin ku yi mani wani abu"
"ɗauka wannan zarafin, zan yi fahariya"
"dole ne in yi wa'azin bishara"
"in sha wahalan rashin sa'a idan"
"idan na yi wa'azi ba da yarda ba" ko kuma "idan na yi wa'azi domin ina so"
An fahimci kalmomin "na yi wannan" a jumla da ya wuce. AT: "Amma idan na yi wannan ba da yarda ba" ko kuma " Amma idan na yi wannan ƙodashiƙe ba na so" ko kuma "Amma idan na yi wannan domin an sa ni dole in yi"
AT: "Dole ne in yi wannan aikin da Allah ya amince ma ni in karasa"
Bulus ya na shirya su domin sabon bayani da zai ba su. AT: "wannan ne lada na"
"ladan wa'azi na shi ne zan iya yin wa'azi ba da karɓan kuɗi ba"
"yi wa'azin bishara"
"ba zan roke mutane su taimake ni sa'ad da ina tafiya da wa'azi ba"
"ni 'yantacce ne ga duka" karin magana ne da ke nufin yin rayuwa ba tare da yin tunanin abin da zaku yi wa waɗansu ba. AT: "zan iya yin rayuwa ba ba tare da bauta wa waɗansu ba"
"rinjaye waɗansu su gaskanta" ko kuma "taimake waɗansu su san Almasihu"
"ina yi kamar Bayahude" ko kuma "ina yin al'adan Yahudawa"
"Na zama kamar wadda ya miƙa kansa ga bin bukatun shugabancin Yahudawan, yarda da fahimtar su game da litatafan Yahudawan"
"waɗanda ba su biyayya da dokokin Musa"
Bulus ya na tuna wa Korontiyawan game da abin da sun sani domin ya iya kara sabon bayani. AT: "Bari in tuna muka cewa ƙodashiƙe masu tseren su na tserewa, mai tsere daya ne ya ke karɓan lada."
Bulus yana kwatanta zaman rayuwan mai bi da yin aiki ma Allah da tserewa da zama ɗan wasan guje-guje. Kaman tserewa, rayuwa da aikin mai bi na bukatan horo mai tsanani a gefen mai tseren, kuma mai bi na da maƙasudi.d
Bulusya na magana game da ladan da Allah zai ba wa amintaccen mutanensa kamar kyauta ne da a ke ba wa masu wasannin guje-guje.
Sakamako taren ganye ne da an murɗa tare. An ba da sakamako a amtsayin kyauta wa masu yin wasanni da guje-guje. Bulus ya na magana game da rai madawami kamar sakamako ne da ba zai taɓa bushe ba.
Anan "tserewa" da "bugu" zance ne game da yin rayuwa da bauta wa Allah. AT: "Na san dalilin da na ke gudu sosai, kuma na san abin da nake yi a loƙacin da nake bugu"
Hukuncin tsere ko kuma gasa magana ne game da Allah. AT: "mai shari'an ba zai hana ni ba" ko kuma "Allah ba zai ce na kasa bin dokokin ba"
Bulus ya faɗa cewa saboda masubi na Korontiyawa su ne aikin hannu na cikin Ubangiji, su da kansu shaida ne na manzancin Bulus a cikin Ubangiji.
Bulus ya ce su na da 'yanci su ci su sha, da kuma 'yancin ɗaukar mace mai bi.
Bulus ya ambaci soja, mai shuka gonar inabi da kuma wanda ke kiwon tumaki kamar misalan waɗanda sun ƙarbi amfani ko biya daga aikinsu.
Bulus ya umarce cewa, "Takarkari mai tattake hatsi kada a sa masa takunkumi" domin ya goyi bayan maganarsa.
Bulus da abokan aikinsa ba su yi amfani da 'yancinsu ba domin kada ya hana bisharar Yesu Almasihu.
Ubangiji ya umarta cewa masu aikin bishara su ci abincinsu ta hanyar bishara.
Bulus ya ce bai iya yin fahariya game da wa'azin bishara ba domin ɗole ne zai yi wa'azin bishira.
Bulus ya zama bawa ga dukka domin ya iya cin nasarar mutane ɗayawa wa Allah.
Bulus ya zama kamar Yahudawa domin ya ci nasara da Yahudawa.
Bulus ya zama kamar waɗanda suke wajen shari'a domin ya ci nasara da waɗanda suke wajen shari'a.
Ya yi wannan domin ya iya hallarci albarkun bishara.
Bulus ya ce a yi tsere domin a ƙarbi sakamako.
Bulus na tserewa domin ya ƙarbi sakamako mara lalacewa.
Bulus ya yi haka domin kada bayan ya yi wa waɗansu wa'azi shi kuma a karshe a fitar da shi.
1 Ina son ku sani, 'yan'uwa, cewa ubaninmu duka suna karkashin gajimarai kuma sun bi ta cikin teku. 2 Dukansu an yi masu baftisma cikin gajimarai da kuma teku, 3 kuma dukansu sun ci abincin ruhaniya iri daya. 4 Dukansu sun sha abin sha na ruhaniya iri daya. Gama sun sha daga wani dutsen ruhaniya da ya bisu, kuma wannan dutsen Almasihu ne. 5 Amma Ubangiji bai ji dadin yawancinsu ba, saboda haka gawawakin su suka bazu a jeji. 6 Wadan nan al'amura, an rubuta mana su domin muyi koyi da su, kada mu yi sha'awar miyagun ayyuka kamar yadda suka yi. 7 Kada ku zama masu bautar gumaka kamar yadda wadansun su suka yi. Wannan kamar yadda aka rubuta ne, "Mutanen sukan zauna su ci su sha kuma su tashi suyi wasa." 8 Kada mu shiga zina da faskanci kamar yadda yawancin su suka yi, a rana guda mutane dubu ashirin da uku suka mutu. 9 Kada mu gwada Almasihu kamar yadda yawancinsu suka yi, macizai suka yi ta kashe su. 10 kada kuma ku zama masu gunaguni kamar yadda suka yi, suka yi ta mutuwa a hannun malaikan mutuwa. 11 Wadannan abubuwa sun faru dasu ne a matsayin misalai a garemu. An rubuta su domin gargadinmu - mu wadanda karshen zamanai yazo kanmu. 12 Saboda haka, bari duk wanda yake tunanin shi tsayyaye ne, to yayi hattara kada ya fadi. 13 Babu gwajin da ya same ku wanda ba a saba da shi ba cikin dukan mutane. A maimako, Allah mai aminci ne. Da ba zaya bari ku jarabtu ba fiye da iyawarku. Tare da gwajin zai tanadar da hanyar fita, domin ku iya jurewa. 14 Saboda haka ya kaunatattu na, ku guji bautar gumaka. 15 Ina magana da ku kamar masu zurfin tunani, domin ku auna abin da ni ke fadi. 16 Kokon albarka da muke sa wa albarka, ba tarayya bane cikin jinin Almasihu? Gurasa da muke karyawa ba tarayya bane cikin jikin Almasihu? 17 Domin akwai gurasa guda, mu da muke dayawa jiki daya ne. Dukanmu munci daga gurasa daya ne. 18 Dubi mutanen Isra'ila: ba wadanda ke cin hadayu ke da rabo a bagadi ba? 19 Me nake cewa? gunki wani abu ne? Ko kuma abincin da aka mika wa gunki hadaya wani abu ne? 20 Amma ina magana game da abubuwan da al'ummai suke hadaya, suna wa aljannu ne hadaya ba Allah ba. Ba na son kuyi tarayya da al'janu! 21 Ba zaku sha daga kokon Ubangiji ku kuma sha na Al'janu ba, ba za kuyi zumunta a teburin Ubangiji ku yi a na Al'janu ba. 22 Ko muna so mu sa Ubangiji kishi ne? Mun fi shi karfi ne? 23 "Komai dai dai ne," amma ba komai ke da amfani ba, "Komai dai dai ne," amma ba komai ke gina mutane ba. 24 Kada wani ya nemi abinda zaya amfane shi. A maimako, kowa ya nemi abinda zaya amfani makwabcinsa. 25 Kana iya cin duk abin da ake sayarwa a kasuwa, ba tare da tamboyoyin lamiri ba. 26 Gama "duniya da duk abin da ke cikin ta na Ubangiji ne." 27 Idan marar bangaskiya ya gayyace ka cin abinci, kana kuma da niyyar zuwa, ka je ka ci duk abinda aka kawo maka, ba tare da tamboyoyin lamiri ba. 28 Amma idan wani ya ce maka, "Wannan abinci an yi wa gumaka hadaya da shi ne" To kada ka ci. Wannan za ka yi ne saboda wanda ya shaida maka, da kuma lamiri (gama duniya da dukan abinda ke cikin ta na Ubangiji ne). 29 Ba ina nufin lamirin ka ba, amma lamirin wanda ya fada maka. Don me za a hukunta 'yanci na domin lamirin wani? 30 Idan na ci abincin tare da bada godiya, don mi za a zage ni don abin da na bada godiya a kansa? 31 Saboda haka, ko kana ci ko kana shi, ka yi komai domin daukakar Allah. 32 Kada ka zama sanadiyyar tuntube, ga Yahudawa, ko Helenawa, ko ikilisiyar Allah. 33 Na yi kokari in farantawa dukan mutane rai cikin dukan abubuwa. Ba riba nake nema wa kaina ba, amma domin kowa. Na yi wannan ne domin su sami ceto.
Bulus ya tuna ma su game da misalin tsohon Ubannin Yahudawa da yadda sun ji da fasikanci da kuma bautan gumakai.
Bulus ya na nufin zamanin Musa a cikin littafin Fitowa a loƙacin da Isra'ilawa sun bi ta Jan Teku a yayin da sojojin Masarawa sun bi su. Kalman "mu" na nufin kansa tare da Korontiyawan.
An san wannan tekun da sunaye biyu, Jan Teku da kuma Tekun Iwa.
"tafiya ta cikin"
"Duka sun bi sun kuma mika kansu ga Musa"
ta gajimarai da su ka wakilci hallarar Allah, sun kuma bi da Isra'ilawa da rana
"sha ruwan ruhaniya iri ɗaya wadda Allah ya kawo ta ruhaniya daga dutse ... dutsen ruhaniya"
"dutse", na nufin dutse wadda ana iya gani. Idan harshen ku ba za ta iya ce dutse "ne" sunan mutum ba, ku ɗauki kalman "dutse" a matsayin magana game da iƙon Almasihu da ke aikia a cikin dutsen. AT: "Almasihu ne ya yi aiki a cikin wancan dutsen"
"rashin jin dadi" ko kuma "fushi"
ubannin Isra'ilawa
"Allah ya baza gawawakin su a kewayen" ko kuma "Allah ya kashe su ya kuma baza gawawakinsu"
filin daji a sakanin Masar da Isra'ila wadda Isra'ilawa sun ragaita na shekaru 40
mutanen da suke bauta wa gumakai
"zauna su ci abinci"
Bulus ya na magana daga al'adun Yahudawa. Yakamata masu sauraran sa sun gane daga wannan kalma cewa mutanen su na bautan gumaka ta wakoki da rawa da kuma yin ayukan faskanci, ba bu jin dadi.
"Allah ya kashe mutane 23,000 a rana daya"
"domin sun aikata waɗancan ayyuka mara daidai na faskanci"
AT: "yi. Sakamakon ita ce, macizai suka kashe su duka"
yi kara
AT: "yi. Sakamakon ita ce, malaika na mutuwa ya kashe su"
"Allah ya hukunta kakaninmu"
Anan " mu" na nufin masubi.
AT: "Allah ya sa Musa ya rubuta domin mu koyi yin abin da yakamata"
"karshen zamani"
kada ya yi zunubi ko kuma ki Allah
AT: "gwajin da yake taɓa ku, gwaji ne da mutane sun ji"
"zai bari a gwada ku a hanyar da za ku iya tsare"
AT: "ba zai bar wani ya gwada ku ba"
Bulus ya na magana game da ayukan bautar gumakai kaman abin da ya ke a bayyane kamar mugun dabba. AT: "ku yi abin da za ku iya domin ku kare kunku daga bautar gumakai"
Bulus ya na magana game da albarkan Allah kamar kokon da ake amfani a hidiman abincin Almasihu.
"wadda muke gode wa Allah"
Bulus ya na tuna wa Korontiyawa game da abin da sun sani, cewa kokon da muke rabawa na wakilcin tarayyanmu a jinin Almasihu. AT: "mu na tarayya a cikin jinin Almasihu."
Bulus ya na tuna wa Korontiyawa game da abin da sun sani. AT: "mu na tarayya a cikin jikin Almasihu a loƙacin da muke raɓa gurasan."
"aikatawa"
gasheshen gurasa guda daya da aka yanka ko kuma gutsure kamin a ci.
Bulus ya na tuna wa Korontiyawan game da abin da sun sani domin ya iya ba su sabon bayani. AT: "waɗanda su ke cin hadayu, su na tarayya a ayuka da albarku na bagadi"
Bulus ya na tuna wa Korontiyawan game da abin da sun sani domin ya iya ba su sabon bayani. AT: "bari in sake duba abin da ina faɗa." ko kuma "ga abin da ina nufi."
Bulus ya na so Korontiyawan su amsa tambayan a zuciyar su domin kadda ya sake faɗa masu. AT: "kun san cewa ba wai ina ce gumki abin gaskiya ba ne."
Bulus ya na so Korontiyawan su amsa tambayan a zuciyar su domin kadda ya sake faɗa masu. AT: "kun san cewa ba wai ina ce wai abincin da ake hadaya wa gumakai na da muhimmi ba."
Bulus ya na magana game da mutum da ya ke sha daga koko daya da al'janu kamar shaida ne cewa mutumin abokin al'janu ne. AT: "ba mai yiwuwa ba ne ku zama abokan gaskiya da Almasihu da kuma al'janu ba"
"ba zai yiwu ku zama daya da mutanen Almasihu da kuma na al'janu ba"
Bulus ya na so Korontiyawan su amsa wannan tambayan a zuciyar su. AT: "Yakamata ku sani ba sai na faɗa ma ku cewa ba kyau ku sa Ubangiji kishi ba."
ga fush ko kiyama
Bulus ya na so Korontiyawan su amsa wannan tambayan a zuciyar su. AT: "Yakamata ku sani ba sai na faɗa ma ku cewa ba mu fi Allah karfi ba."
AT: 1) Bulus ya na amsa abin da waɗansu Korontiyawan za su iya tunani, "wadansu su na ce, 'zan iya yin komai" ko kuma 2) Bulus yana faɗan abin da yake tunani daidai ne, "Allah ya bar ni in yi komai." A fasara wannan a cikin 6:12
"waɗansu abubuwan ba su da amfani"
Gina mutane na wakilcin taimaka masu don su yi girma da karfi a cikin bangaskiyansu. Dubi yadda ake fasara "gina" a cikin 8:1. AT: "ba komai ne yake karfafa mutane ba" ko kuma "waɗansu abubuwan ba su karfafa mutane"
"ku. Allah ya na so ku ci abinci ba tare da shaka ba"
An sa waɗansu fasaran a bayyane 1) siffar "ku" da "ci" daya ne annan, amma Bulus ya yi amfani da su, 2) kalmomin "don me za a hukunta yanci na da lamirin wani?" ya kafa a kan "ci kowane abin da an baku, ba tare da yin tambayoyin lamiri ba" 10:27 ba tare da "lamirin dayan mutumin ba."
Bulus ya na magana da Korontiyawa kamar su mutane daya ne, kalmomin "ku" da umurnin "kada ka ci " daya a nan.
AT: "kalmar "don" na nufin koma zuwa 10: 27, "bai kamata in yi tambayoyin lamiri, don haka me ... lamiri? Idan na ci ... bada godiya?" ko kuma 2) Bulus yana fadan abin da waɗansu Korontiyawan su na tunani, "kamar yadda waɗansunku za su ta yin tunani, "Don me ... lamiri? Idan na ... gade?"
Mai magana ya na son mai sauraransa ya amsa tambayan a cikin zuciyarshi. AT: "yakamata ku sani ba sai na faɗa maku cewa kadda wani ya ce ban yi daidai ba domin ya na da sanin daidai da ba daidai ba da sun bambanta daga nawa.
Mai magana ya na son mai sauraransa ya amsa tambayan a cikin zuciyarshi. AT: "Na ci abincin da godiya, don haka kada wani ya zage ni."
Idan Bulus ba ya fadan abin da Korontiyawan su ke iya tunani, "na" ya na wakilcin waɗanda suke cin nama da godiya. "Idan na ci" ko kuma "Idan mutum ya ci"
"ku kuma gode wa Allah don shi" ko kuma "ku kuma gode wa mutumin da ya ba ni"
"kada ku bata da Yahudawa ko Girkawa" ko kuma "kada ku sa Yahudawa ko Girkawa fushi"
"sa duka mutane murna"
"ba na yin abin da na ke so wa kai na"
yawan mutane
Duka suna ƙarƙashin gajimarai kuma sun bi ta cikin teku. Dukansu an yi masu baftisma cikin gajimarai da kuma teku, kuma dukansu sun ci abincin ruhaniya iri ɗaya, kuma dukansu sun sha abin sha na ruhaniya iri ɗaya.
Almasihu ne ɗutsen da ya bi su.
bai ji dadin ubannensu a da domin mugayen abubuwa.
Allah ya hallaka su da macizai da kuma mala'ikar mutuwa.
Sun faruwa a matsayin misalai a garemu kuma an rubuta su domin gargadinmu.
Babu gwajin da ya same mu wanda ba a saba da shi ba cikin dukan mutane.
Ya tanada hanyar fita domin mu iya jimre gwaji.
Ya ƙwabe su su guji bautar gumaka.
ƙokon tarayya ne cikin jinin Almasihu. Gurasan tarayya ne cikin jikin Almasihu.
Suna mika waɗannan abubuwa ga aljannu ne ba Allah ba.
Bulus ya ce masu ba zasu sha daga kokon Ubangiji su kuma sha na Al'janu ba, ba za suyi zumunta a teburin Ubangiji su kuma yi a na Al'janu ba.
Muna sa Ubangiji ƙishi.
A'a. Maimakon haka, kowa ya nemi abinda zaya amfani makwabcinsa.
Ka ci duk abinda aka kawo maka, ba tare da tamboyoyin lamiri ba.
Kada ku ci saboda wanda ya fada maku da kuma lamirinsa.
Mu yi komai, tare da ci da sha ga ɗaukakar Allah.
Kada mu ba su laifi domin su sami ceto.
1 Ku yi koyi da ni, kamar yadda nake koyi da Almasihu. 2 Yanzu ina yaba maku ne, don kuna tunawa da ni cikin abu duka. Ina kuma yaba maku wajen bin al'adun da na ba ku daidai yadda na ba ku. 3 Amma fa ina son ku fahimta da cewa, shugaban kowane mutum Almasihu ne, shugaban kowace mace mutumin ne, shugaban Almasihu Allah ne. 4 Kuma duk mutumin da ya yi addu'a ko annabci kansa a rufe, ya wulakanta shugabansa. 5 Amma duk macen da ta yi addu'a ko annabci kanta a bude, ta wulakanta shugabanta. Gama yayi dai dai da idan tayi aski. 6 Gama idan mace ba zata rufe kanta ba, to ta yanke gashinta ya zama gajere. Idan abin kunya ne mace ta yanke gashinta ko ta aske kanta, bari ta rufe kanta. 7 Bai kamata na miji ya rufe kansa ba, tun da yake shi siffa ne da daukakar Allah. Amma mace daukakar namiji ce. 8 Don kuwa namiji ba daga jikin mace yake ba. A maimako, matar daga jikin namiji take. 9 Ba a kuma halicci namiji don mace ba. A maimako, an halicci mace don namiji. 10 Shi ya sa mace za ta kasance da alamar iko a kanta, saboda mala'iku. 11 Duk da haka, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, haka kuma namiji ba a rabe yake da mace ba. 12 Kamar yadda mace take daga namiji, haka ma namiji kuma haihuwar mace ne. Amma dukkan abubuwa daga Allah suke. 13 Ku hukunta da kanku: Daidai ne mace ta yi addu'a ga Allah kanta a bude? 14 Ashe, ko dabi'a bata nuna maku cewa abin kunya ne namiji, ya kasance da dogon gashi ba? 15 Ba dabi'a ta koya maku cewa idan mace tana da dogon gashi, daukakar ta ne ba? Gama domin rufewa aka yi mata baiwar gashin. 16 To idan wani yana da niyyaryin gardama game da wannan, mu dai bamu da wata al'adar, ikilisiyoyin Allah kuma haka. 17 Amma game da umarnin dake biye, ban yaba maku ba, taruwarku ba ta kirki ba ce, ta rashin gaskiya ce. 18 Farko dai sa'adda kuke, taron ikklisiya, na ji har akwai rarrabuwa tsakaninku, har na fara amincewa da maganar. 19 Dole ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya gane wadanda suke amintattu a cikinku. 20 Domin, in kun taru a wuri daya, ba jibin Ubangiji kuke ci ba! 21 Ya yin da kuke ci, kowa na cin abincinsa ne kamin sauran Wani yana jin yunwa, wani kuma ya zarin ci, har ya bugu. 22 Baku da gidajen da zaku ci ku sha, kuna raina ikkilisiyar Allah, kuna kuma wulakanta wa wadanda basu da komai? To, me zan ce maku? Yaba maku zan yi? Ba zan yaba maku ba akan wannan. 23 Amma abin da na karba a gun Ubangiji shi nake baku cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi ya dauki gurasa. 24 Bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, "wanna shi ne jikina wanda yake saboda ku, ku yi domin tunawa da ni." 25 Ta wannan hanya kuma, sai ya dauki kokon, ya ce, "kokon nan na sabon alkawari ne, da aka tabbatar da shi da cikin jinina. Ku yi haka kuna sha don tunawa da ni." 26 Duk sa'adda kuke cin gurasar nan, kuna kuma sha cikin kokon nan, kuna bayyana mutuwar Ubangiji ke nan, har sai ya dawo. 27 Saboda haka duk wanda ya ci gurasar nan, ko ya sha a cikin kokon nan, na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulakanta jikin Ubangiji da jininsa. 28 Sai kowa ya fara auna kansa, kafin ya ci gurasar, ya kuma sha a cikin kokon nan. 29 In kowa ya ci, ya sha ba tare da rarrabewa da jikin Ubangiji ba, lalle ya jawowa kansa hukunci, ta wurin ci da sha da ya yi. 30 Shi ya sa da yawa a cikin ku suke raunana, kuma suna fama da rashin lafiya, har ma wasun ku da dama suka yi barci. 31 Amma, in mun auna kanmu, ba a za a hukunta mu ba. 32 In kuwa Ubangiji ne ya ke hukunta mu, To, muna horuwa ke nan, don kada a kayar damu tare da duniya. 33 Saboda haka, ya ku 'yan'uwana, idan kuka tattaru don cin abinci, sai ku jira juna. 34 Idan kuwa wani yana jin yunwa, ya ci a gida, kada ya zama taronku ya jawo maku hukunci. Batun sauran abubuwan da kuka rubuta kuwa, zan ba da umarni a kai sa'ad da na zo.
Bayan da ya tuna masu cewa su bi shi yadda yake bin Almasihu, Bulus ya ba da umurni game da yadda maza da mata za su yi rayuwa a matsayin masubi.
"kuna tunawa da ni a kowane loƙaci" ko kuma "kullum ku na kokarin aikata kamar yadda ina so ku aikata" Korontiyawan ba su mata da ko waye ne Bulus ko kuma abin ya koya masu ba.
AT 1) "Domin wannan, Ina so ko kuma 2) "ƙodashiƙe, Ina so."
na da iƙo akan
AT 1) "yakamata mazaje su samu iƙo akan mataye" ko kuma 2) "yakamata maigidan ya kasance da iƙo akan matan"
"yi haka bayan ya saka mayafi a kanshi"
AT: 1) "na kawo kunya wa kansa" ko kuma 2) "na kawo kunya a Almasihu, wadda shi ne shugaba."
AT: 1) "macen da ta yi addu'a ... ta na kawo rashin kunya wa kanta" ko kuma 2) "matan da ta yi addu'a ... kawo rashin kunya wa mijin ta."
Cewa da rashin kayan da aka sa a saman kai, kuma ya na rufe suma da kuma kafaɗa.
kaman ta cire duka suma a kanta da raiza
Alamar kunya ne ko wulakanci wa mace ta yanka suman ta.
Sa a kanta rigan da an sa a saman kai wadda yake rufe suma da kafaɗa.
AT: 1) "ba dole ne ya rufe kansa ba" ko kuma 2) "ba lallai ne ya rufe kansa ba"
Yadda mutum yake nuna iƙon Allah, haka ne macen ta na nuna halin mijin.
Allah ya yi mace ta wurin cire ƙashi daga na miji. AT: "Allah bai yi na miji daga mace ba. A maimako, ya yi mace daga na miji"
Ana iya bayyana waɗannan kalmomin a 11:8 domin mai karatun ya iya ganin kalman "wannan" cikin "wannan ne dalilin ... mala'iku" na nufin kalmomincan "mace ne ɗuakakar namiji" a cikin 11:7.
AT: 1) "don nuna alamar cewa ta na da miji a matsayin shugabanta" ko kuma 2) " don nuna alamar cewa ta na da iƙon yin addu'a ko kuma annabci."
"Dashiƙe abin da na faɗa duka gaskiya ne, abu ma fi muhimmi shi ne wannan: cikin Ubangiji"
AT: 1) "a sakanin masubi, wadda sun kasance na Ubangiji" ko kuma 2) "a cikin duniya, da Allah ya halita."
AT: "mace ta na dogara akan namiji, kuma namiji ya na dogara akan mace"
"Allah ya halicci komai da komai"
"ku hukunta wannan zance bisa ga al'adu da ayukan ikilisiyan da kun sani"
Bulus ya so Korontiyawa su yarda da shi. AT: "mace ta rufe kanta a addu'a ga Allah, domin ta ɗaukaka Allah."
Bulus ya so Korontiyawa su yarda da shi. AT: "dabi'a da kansa ya koya maku ... domin shi."
AT: "Domin Allah ya hallicci mace da gashi"
AT: "Ya yin da na ba ku wannan umarni, a kowai abin da ba zan iya yabon ku ba : A loƙacin"
"umarnin da ina so in yi magana game da"
"tara tare" ko kuma "haɗu"
"ba ku taimake junanku ba; maimako, ku na yi wa junanku illa"
"a matsayin masubi." Bulus ya magana game da kasancewa a cikin gini.
"ku na raɓa kanku zuwa kungiyoyin hamayya"
Suna iya nufin 1) Kalmar "dole" na nuna cewa wannan yanayi na iya faruwa. AT: "Mai yiwuwa za a iya samun tsattsaguwa a tsakaninku" ko kuma 2) Bulus ya yi amfani da maganan nan don ya kunyatar da su domin su na da tsattsaguwa. AT: "kamar ku na tunani cewa dole ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku" ko kuma "kamar ku na tunani cewa dole ne ku raɓa kanku"
kungiyoyin hamayya na mutane
AT: 1) "don mutane su san masubi da suke da martaba sosai a sakaninku" ko kuma 2) "don mutane su iya nuna wannan yabo ga sauran mutane a sakaninsu." Mai yiwuwa Bulus ya yi ta amfani da wannan magana, a faɗan abin da ya ke so Korontiyawan su gane, don ya kunyatar da su.
AT: 1) "wadda Allaha ya amince" ko kuma 2) "wadda ku, ikilisiya, ku ka amince."
"za ku iya gaskanta cewa ku na cin abincin Ubangiji, amma ba ku yin shi da daraja"
"wadda za a tara ma abinci"
tsana ko kuma da rashin mutunci da kuma rashin ladabi
ruɗa ko kuma sa jin kunya
Bulus ya na kwaɓan su Korontiyawan. AT: "Ba zan iya ce abu mai kyau game da wannan ba. Ba zan iya yabon ku ba."
"Amma daga Ubangiji ne na ji abin da na faɗa maku, cewa wannan ne: Ubangiji"
AT: "a daren da Yahuda Iskarioti ya bashe shi"
"ya cire gutsure daga shi"
"Gurasan da nake riƙe da shi, jikina ne"
Ya na da kyau a bayana wannan. Korontiyawan sun san kokon da ya ɗauka, don haka ba "kwaf" bane ko "waɗansu kwaf" ko kuma "kowane kwaf ba." AT: 1) kokon ruwa da mutum ze so ya yi amfani da shi ko kuma 2) kokon na uku ko na huɗu na ruwa da Yahudawa sun sha a abincin Idin ketarewa.
"sha daga wannan kokon, kuma a yadda ku na sha daga shi"
koyar game da giciyewa da kuma tashiwa
Anan iya bayyana wurinda Yesu zai zo. AT: "sai Yesu ya dawo duniyannan"
"ci gurasar Ubangiji ko kuma sha kokon Ubangiji"
Bulus ya na magana game da mutum da yana duba tafiyarsa da Allah da kuma yadda ya ke rayuwarsa kamar mutumin ya na neman abin da zai saya. Dubi yadda an fasara "gwada kyau" a cikin 3:13.
AT: 1) "kuma bai yarda cewa ikilisiya ne jikin Ubangiji ba" ko kuma 2) "kuma bai duba cewa yana rike da jikin Ubangiji ba."
Waɗannan kalmomin su na nufin abu iri daya kuma ana iya hada su, kamar a cikin UDB.
"barci" magana ne game da mutuwa. AT: "kuma waɗansunku sun mutu" .
Idan wannan zai nuna kamar Bulus yana magana da wadda sun mutu ne, za ku iya sa shi a bayyane cewa ba haka ba ne. AT: "waɗansu mutanen kungiyanku"
AT: "Allah ba zai hukunta mu ba"
AT: "Ubangiji ya na hukunta mu, ya na horas da mu, domin kadda ya kayar da mu"
an taru domin a ci abinci tare kafin a yi yabon abincin Ubangiji
"ku jira sauran su zo kafin ku fara abincin"
"ya ci kafin zuwa wannan taru"
"ba zai zama rana ne da Allah zai yi maku horo ba"
Bulus ya ce masu su yi koyi da Bulus.
Bulus mai yin koyi da Almasihu ne.
Bulus ya yaɓe su don suna tunawa da shi cikin abu duka da kuma wajen bin al'adun da ya ba su daidai yadda ya ba su.
Almasihu ne shugaban kowane mutum.
Allah ne shugaban Almasihu.
Mutum ne shugaban mace.
Ya wulakanta kansa idan ya yi addu'a da kansa a rufe.
Duk macen da ta yi addu'ac da kanta a buɗe, ta wulakanta shugabanta.
Kada ya rufe kanshi domin shi siffa ne da ɗaukakar Allah.
An halicci mace don namiji.
Al'adun su ne mata su rufe kansu a addu'a.
Mace ta zo daga namiji, haka ma namiji kuma haihuwar mace ne.
Al'adun su ne mata su rufe kansu a addu'a.
Ɗole ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya gane waɗanda suke amintattu a cikinsu.
Ya yin da kuke ci, kowa na cin abincinsa ne kamin sauran. Wani yana jin yunwa, wani kuma ya zarin ci har ya bugu.
Ya ce, "wanna shi ne jikina wanda yake saboda ku, ku yi wannan domin tunawa da ni."
Ya ce, "kokon nan na sabon alkawari ne, da aka tabbatar da shi da cikin jinina. Ku yi haka kuna sha don tunawa da ni."
kuna shelar mutuwar Ubangiji, har sai ya dawo.
Yin haka na sa ku yin laifin wulakanta jikin Ubangiji da jininsa. Ku na ci da kuma shan hukunci a kanku.
Dayawa a cikinsu sun raunana da kuma rashin lafiya har wasunsu sun mutu.
Ya ce masu su jira juna.
1 Game da baye bayen Ruhu Mai Tsarki 'yan'uwa, bana so ku zama da jahilci. 2 Kun san cewa lokacin da ku ke al'ummai, an rude ku da alloli marasa magana ta hanyoyi dabam dabam marasa kan gado. 3 Saboda haka ina so ku sani babu wanda ya ke magana da Ruhun Allah da zai ce, "Yesu la'ananne ne." Babu kuma wanda zaya ce, "Yesu Ubangili ne," sai dai ta Ruhu Mai Tsarki. 4 Akwai bay bye iri iri, amma Ruhu daya ne. 5 Akwai hidimomi iri iri, amma Ubangiji daya ne. 6 Akwai aikace aikace iri iri, amma Allah daya ke bayyanawa kowane mutum yadda zai aiwatar da su. 7 To ga kowanne an bayar da ikon nuna ayyukan Ruhu a fili domin amfanin kowa. 8 Ga wani ta wurin Ruhu an bayar da baiwar hikima, kuma ga wani kalmar sani ta wurin Ruhu daya. 9 Ga wani an ba shi baiwar bangaskiya ta wurin Ruhun nan, ga wani kuwa an ba shi baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhun. 10 Ga wani yin ayyukan iko, ga wani kuwa annabci. Ga wani kuwa an ba shi baiwar bambance ruhohi, ga wani harsuna daban daban, kuma ga wani fassarar harsuna. 11 Dukan wadannan Ruhu daya ne ya ke iza su, ya kuma rarraba baye bayen ga kowannen su yadda ya nufa. 12 Kamar yadda jiki daya ne amma da gabobi da yawa kuma duk gabobin na jiki daya ne, haka nan Almasihu yake. 13 Gama ta Ruhu daya aka yi wa kowa baftisma cikin jiki daya, ko Yahudawa ko al'ummai, ko bayi ko 'ya'ya, dukan mu kuwa an shayar da mu Ruhu daya. 14 Gama jiki ba daya ba ne sungun, amma gabobi ne da yawa. 15 Idan kafa ta ce, "tun da dai ni ba hannu ba ne to ni ba fannin jikin bane," wannan baya rage masa matsayin sa a jikin ba. 16 Kuma da kunne zaya ce, '"Da yake ni ba ido ba ne, ai, ni ba gabar jiki ba ne," fadar haka ba za ta raba shi da zama gabar jikin ba. 17 Idan dukan jikin ya kasance ido ne da me za a ji? Da dukan jikin kunne ne, da me za a sunsuna? 18 Amma Allah ya shirya gabobin jiki bisa ga tsarin sa. 19 Amma da duk jiki gaba daya ce, da ina jikin zai kasance? 20 Ga shi akwai gabobi da yawa, kuma jiki daya ne. 21 Ba da ma ido ya fadawa hannu, "Bana bukatar ka," ko kuma kai ya fadawa kafafu, "Ba na bukatar ku." 22 Amma, sai ma gabobin da ake gani kamar raunannu su ne masu humimmanci, gabobin jiki kuwa da ake gani kamar sun kasa sauran daraja, mu kan fi ba su martaba. 23 Ta haka gabobinmu marasa kyan gani, akan kara kyautata ganinsu. Gabobin mu masu kyan kuma ba sai an yi masu ado ba. 24 Amma Allah ne da kansa ya hada jiki, yana bada mafificiyar martaba ga kaskantacciyar gaba. 25 Yayi haka ne domin kada a sami tsattsaguwa a cikn jikin, amma domin gabobin su kula da juna da matsananciyar lura. 26 Kuma idan gaba daya na wahala, dukan gabobin suna wahala tare. ko kuma idan an girmama gaba daya, dukan gabobin na farin ciki tare. 27 Yanzu ku jikin Almasihu ne, saboda haka kuma kowannen ku gabarsa ne. 28 A cikin ikilisiya, Allah ya sa wasu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin ayyukan iko, sai masu aikin warkarwa, da masu bayar da taimako, da masu aikin tafiyar da al'amura, da masu harsuna daban daban. 29 To kowa manzo ne? ko kuwa duka annabawa ne? ko kuma duka masu koyarwa ne? Kowa ne ke yin manyan ayyukan iko? 30 Ko kuwa dukan su ne suke da baiwar warkarwa? Dukan su ne ke magana da harsuna? ko kuma dukan su ne ke fassara harsuna? 31 Amma bari ku himmantu ga neman baiwa mafi girma. Kuma zan nuna maku wata hanya mafificiya.
Bulus ya nuna masu cewa Allah ya ba wa masubi kyauta na musamman. Waɗannan kyautane za su taimaka wa taron masubi.
AT: "Ina so ku sani"
Anan "ruɗi" magana ne game da kawas da shakan yin abin da ba daidai ba. Rudawa ga gumakai na wakilcin rashin kawas da shaka ga bautar gumakai. Ana iya bayana wannan zance a cikin siffa "an ruɗe" da "sun ruɗe ku". AT: "kun riga kun kawas da shaka a wadansu hanyoyin bautar gumakai da ba su iya magana ba" ko kuma "kun yarda da karya shi ya sa kun bauta wa gumakai da ba su iya magana ba"
AT: 1) "ba bu mai bi wadda yana da Ruhun Allah a cikinsa zai iya ce" ko kuma 2) "ba bu wadda yake yin annabci da iƙon Ruhun Allah da zai iya ce."
"Allah zai hukunta Yesu" ko kuma "Allah zai sa Yesu ya sha wahala"
"sa kowa ya kasance da su"
Ana iya bayyana wannan a cikin sifar aiki. Allah ne mai yin bayarswa 12:6. AT: "Allah yana ba wa kowane daya"
AT: Ta wurin Ruhu, Allah ya na ba mutum daya kalmar"
"sakon"
Allah ya na ba da kyautani ta wurin aikin Ruhu.
Bambancin kalmominnan a nan ba su da amfani domin Allah ne ya ba da su ta Ruhu daya.
Bulus yana bayyana wata ra'ayi ta wurin kalmomi biyu. AT: "kalmomin hikima"
Bulus yana bayyana wata ra'ayi ta wurin kalmomi biyu. AT: "kalmomin da suke nuna sani"
Ana iya bayyana wannan a cikin sifar aiki. Dubi yadda an fasara wannan a cikin 12:8. AT: "Allah ya bayar"
An fahimci kalmomin "an bayar" a jumla da ya wuce. AT: "ga wani kuwa an ba shi baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhun"
An fahimci jumlan "an bayar ta Ruhu daya" a jumla da ya wuce. AT: "ga wani kuwa an ba shi annabci ta wurin wannan Ruhun"
An fahimci jumlan "an bayar ta Ruhu daya" a jumla da ya wuce. AT: "ga wani harsuna daban daban ta wurin wannan Ruhun"
Anan "harsuna" na wakilcin yararruka. AT: "baiwar fassarar harsuna dabam dabam"
An fahimci jumlan "an bayar ta Ruhu daya" a jumla da ya wuce. AT: "ga wani fassarar harsuna ta wurin wannan Ruhun"
Wannan baiwan jin abin da wani ya faɗa a wata harshe domin a iya fasara wa mutane a wata harshe abin da wannan mutumin yake faɗa. AT: "baiwar fasara abin da ana faɗa a waɗansu harshen"
Allah ya na ba da kyautan nan ta wurin aikin Ruhu mai Tsarki kadai. Dubi yadda an fasara wannan a cikin 12:8.
AT: 1) Ruhu mai Tsarki ne yake yi mana baftisma, "Don Ruhu daya ne ke yi mana baftisma " ko kuma 2) Ruhun, kamar ruwar baftisma, shi ne abin da ake yi mana baftisma zuwa cikin jiki, "Gama ta Ruhu daya aka yi wa mana baftisma"
"dauri" magana ne game da "bayi." AT: "ko bayin mutane ko 'ya'yan mutane"
AT: "Allah ya bamu Ruhu iri daya, muna raɓa Ruhun kamar yadda mutane na iya raɓa abin sha"
Ana iya sa wannan a jumla. AT: "ba ku iya jin komai ba ... ba ku iya sunsuna komai ba"
Kalmar "gabibi" kalma ne game da sashin jiki, kaman kai, hamata ko gwiwa. AT: "irin sashin jiki ɗaya"
Ana iya sa wannan a jumla. AT: "ba za a sumu jiki ba"
"ba na bukatanku"
"mara amfani"
Wannan na iya nufin sashin siri na jikin mu wadda mutane ke rufewa.
"ana iya hadda jikin , kuma"
AT: "wani ya na daraja gabobi daya"
Ana amfani da kalmar "yanzu" anan domin a jawo hankali zuwa ga muhimmin magana.
AT: 1) "Kyauta na farko cda zan faɗa shi ne manzanni" ko kuma 2) "Kyauta muhimmi shi manzanni."
"masu tanada taimako wa sauran masubi"
"waɗanda suke bi da ikilisiya"
mutumin da na iya magana a harshe daya ko biyu na wata kasa da bai taba koya ba.
Bulus yana tuna wa masu sauraransa game da abin da sun riga sun sani. AT: "Waɗansunsu ne kadai manzanni. Waɗansunsu ne kadai annabawa. Waɗansunsu ne kadai masu koyarwa. Waɗansunsu ne kadai ke yin manyan ayyukan iƙo."
Wannan na iya zama jumla. AT: "Ba dukan su ba ne ke da baiwar warkarwa ba."
Wannan na iya zama jumla. AT: "Ba dukan su ba ne ke magana da harsuna ba."
Wannan na iya zama jumla. AT: "Ba dukan su ba ne ke fassara harsuna ba."
Wannan na nufin gayawa wadansu abin da wani ya faɗa a harshen da basu gane. Dubi yadda an fasara wannan a cikin 2:13
AT: 1) "Dole ne ku bida da marmari kyauta daga Allah da ke taimakon ikilisiya." ko kuma 2) "Ku na nema da marmari kyautanni da ku ke tunani sun fi domin ku na tunani sun fi kyau."
Bulus ya na so su san game da baye bayen Ruhu Mai Tsarki.
Ba ya iya ce, "Yesu la'ananne ne."
Mutum na iya ce, "Yesu Ubangili ne," ta wurin Ruhu mai Tsarki.
Ya na sa yiwuwa a kowane mai bi baiwa iri iri, hidimomi iri iri, da kuma ayuka iri iri.
An bayar domin amfanin kowa.
Wasu baiwar su ne bangaskiya, baiwar warkarwa, ayyukan iko, annabci, baiwar bambanta ruhohi, harsuna dabam dabam da kuma fassarar harsuna.
Ruhun na ba wa kowa baiwa yadda ya zaɓa.
Ta Ruhu ɗaya aka yi wa kowa baftisma cikin jiki ɗaya, kuma dukan mu kuwa an shayar da mu Ruhu ɗaya.
Allah ya shirya kowane gabobin jiki bisa ga tsarin sa.
A'a. Gabobin da ake gani kamar raunannu su ne masu muhimmanci.
Allah ya hada gabobin tare, ya kuma bada mafificiyar martaba ga waɗanda sun rasa.
Yayi haka ne domin kada a sami tsattsaguwa a cikn jikin, amma domin gabobin su kula da juna da matsananciyar lura.
A cikin ikilisiya, Allah ya sa wasu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin ayyukan iko, sai baiwar warkarwa, da masu bayar da taimako, da masu aikin tafiyar da al'amura, da masu harsuna daban daban.
Ya ce zai nuna masu wata hanya mafificiya.
Ya ce masu su nema baiwa mafi girma.
1 Koda ya zamanto ina magana da harsunan mutane, har ma da na mala'iku, amma kuma ba ni da kauna, na zama kamar kararrawa mai yawan kara, ko kuge mai amo. 2 Ko da ya zamanto ina da baiwar annabci kuma na fahimci dukkan boyayyar gaskiya, da dukkan ilimi, ko ina da matukar bangaskiya, har ma zan iya kawar da duwatsu. muddin ba ni da kauna, ni ba komai ba ne. 3 Ko da ya zamanto na bayar da dukan mallakata domin a ciyar da matalauta, in kuma mika jikina domin a kona. Amma in ba ni da kauna, ban sami ribar komai ba. (Na bayar da jikina ne domin inyi fahariya). 4 Kauna na da hakuri da kirki. kauna bata kishi ko fahariya. kauna ba ta girman kai 5 ko fitsara. Bata bautar kanta. Bata saurin fushi, kuma bata ajiyar lissafin laifuffuka. 6 Bata farin ciki da rashin adalci. A maimako, tana farin ciki da gaskiya. 7 Kauna tana jurewa cikin dukan abubuwa, tana gaskata dukan abubuwa, tana da yarda game da dukan abubuwa, tana daurewa dukan abubuwa. 8 Kauna ba ta karewa. Idan akwai anabce anabce, zasu wuce. Idan akwai harsuna, zasu bace. Idan akwai ilimi, zaya wuce. 9 Domin muna da sani bisa - bisa kuma muna anabci bisa - bisa. 10 Sa'adda cikakke ya zo, sai marar kammalar ya wuce. 11 Da nake yaro, nakan yi magana irinta kuruciya, nakan yi tunani irin na kuruciya, nakan ba da hujjojina irin na kuruciya. Da na isa mutum na bar halayen kuruciya. 12 Gama yanzu muna gani sama - sama kamar ta madubi, amma a ranar fuska da fuska, yanzu na sani bisa - bisa, amma a lokacin zan sami cikakken sani kamar yadda aka yi mani cikakken sani. 13 To, a yanzu abubuwan nan uku sun tabbata: bangaskiya, da gabagadi mai zuwa, da kuma kauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce kauna.
Bayan da Bulus ya gama magana game da kyautanni da Allah ya ba wa masubi, Bulus ya nanata abin da ke da muhimmi.
AT: 1) Bulus yana zuguiguitawa don fahimta ne kuma be yarda cewa mutane na yin harshen da mala'iku ke amfani ba, ko kuma 2) "Bulus yana tunani cewa waɗansun da suke magana a harsuna ne masu magana a harshen mala'iku.
na zama kama kayan kiɗe-kiɗe dake yin yawan kara, kara mai bata rai
Baban, tsiriri, mulmulallen kuwanon ƙarfe da ake bugawa da sanda domin ya yi kara mai yawa
gongoni biyu, mulmulallen kuwanon ƙarfe da ake buga wa tare domin ya yi kara
Ana iya bayyana wannan jumla " domin a kona". AT: "Na bar wadda sun hukunta ni su ƙone ni har ga mutuwa"
Anan, Bulus yana magana game da kauna kamar mutum ne.
AT: "Ba bu wadda zai iya sa shi fushi da sauri"
AT: "Ya na farinciki a adalci ne kadai da kuma gaskiya"
Madubi a zamanin Bulus an a yin su da karfe mai kyau maimakon glass kuma ya na nuna abu ba da haske sosai ba.
AT: 1) "yanzu mun ga Almasihu" ko kuma 2) "yanzu mun ga Allah."
"amma za mu gan gan Almasihu fuska da fuska". Wannan na nufin cewa za mu kasance a gaban Almasihu.
An fahimci kalmar "Almasihu". AT: "Zan san Almasihu cikakke"
AT: "Kamar yadda Almasihu ya san ni cikakke"
Ana iya bayana wannan magana. AT: "Dole ne mu gaskanta da Ubangiji, ku sani da gabagadi cewa zai yi abin da ya yi alkawari, ƙaunacee shi da waɗansun"
Zai zama kamar kararrawa mai yawan kara, ko kuge mai amo.
Zai zama shi ba komai ba ne.
In ba shi da ƙauna, ba zai sami ribar komai ba ko da ya yi sauran waɗannan abubuwa.
Ƙauna na da hakuri da kirki; ƙauna bata kishi ko fahariya; ƙauna ba ta girman kai ko fitsara. Bata bautar kanta, bata saurin fushi, kuma bata ajiyar lissafin laifuffuka. Bata farin ciki da rashin adalci, a maimako, tana farin ciki da gaskiya. Tana jurewa cikin dukan abubuwa, tana gaskata dukan abubuwa, tana da yarda game da dukan abubuwa, tana daurewa dukan abubuwa.
Ƙauna ba ta karewa.
Anabce, ilimi da kuma abin da bai cika ba zai wuce kuma harsuna za su bace.
Bulus ya ce a loƙacin da ya isa mutum ya bar halayen kuruciya.
Bangaskiya, da gabagadi mai zuwa, da kuma kauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.
1 Ku dafkaci kauna kuma ku himmatu domin baye bayen ruhaniya, musamman domin kuyi anabci. 2 Domin wanda yake magana da harshe bada mutane yake magana ba amma da Allah. domin babu mai fahimtarsa saboda yana zancen boyayyun abubuwa ciki Ruhu. 3 Amma wanda yake anabci da mutane yake magana domin ya gina su, ya karfafa su, kuma ya ta'azantar dasu. 4 Wanda yake magana da wani harshe, kansa yake ginawa, amma mai yin annabci kuwa, ikilisiya yake ginawa. 5 To, fatana ace dukan ku kuna magana da harsuna. Amma fiye da hakama, fatana ace kuyi anabci. Wanda yake anabci yafi wanda yake magana da harsuna (sai dai idan wani ya fassara domin ikilisiya ta ginu). 6 Amma yanzu, 'yan'uwa, in na zo wurin ku ina magana da harsuna, ta yaya zaku karu dani? ba zaya yiwu ba, sai idan nayi maku magana da wahayi, ko sani, ko anabci, ko koyarwa. 7 Idan kayan kida marasa rai suna fitar da sauti - kamar su sarewa da algaita - kuma basu fitar da amo daban daban, ta yaya wani zaya san irin amon da sarewar da algaitar suke kadawa? 8 Domin idan aka busa kaho da sauti marar ma'ana, ta yaya wani zaya san lokacin da ya dace ya shirya zuwa yaki? 9 Haka yake game da ku. Idan kuka furta zance marar ma'ana, ta yaya wani zaya fahimci abinda kukace? zaku yita magana, kuma babu wanda zaya fahimce ku. 10 Babu shakka akwai harsuna daban daban a duniya, kuma babu wanda baya da ma'ana. 11 Amma idan ban san ma'anar wani harshe ba, zan zama bare ga mai maganar, kuma mai maganar zaya zama bare a gareni. 12 haka yake gare ku. Tun da kuna da dokin bayyanuwar Ruhu, ku himmatu da habaka cikin gina ikilisiya. 13 To wanda yake magana da harshe yayi addu'a domin ya iya fassarawa. 14 Domin idan nayi addu'a da harshe, ruhuna yayi addu'a, amma fahimtata bata karu ba. 15 To, me zan yi? Zan yi addu'a da ruhuna, in kuma yi addu'a da fahimtata. Zan yi raira waka da ruhuna, kuma in raira waka da fahimtata. 16 In ba haka ba, idan ka yi yabon Allah da ruhu kawai, ta yaya wanda yake waje zai ce, "Amin" a kan godiyar da kake yi in bai san abin da kake fada ba? 17 Babu shakka kayi godiya sosai, amma wanin baya ginu ba. 18 Nagodewa Allah ina magana da harsuna fiye da ku duka. 19 Duk da haka dai a taron ikilisiya na gwammace in yi magana da kalmomi biyar cikin fahimta saboda inganta wadansu fiye da dubu goma da harshe. 20 'Yan'uwa, kada ku zama yara cikin tunani, sai dai a wajen aikin mugunta, ku yi halin jarirai, amma a tunaninku ku girma. 21 A rubuce yake a shari'a cewa, "zan yi magana da mutanen nan ta wurin mutane masu bakin harsuna, da kuma lebunan baki. Duk da haka kuwa ba za su saurare ni ba", in ji Ubangiji. 22 Amma harsuna alamu ne, ba ga masu bada gaskiya ba, sai dai ga marasa ba da gaskiya. Annabci kuwa alama ce ga masu ba da gaskiya, amma ba don marasa bangaskiya ba. 23 Saboda haka, in dukan ikilisiya ta taru, kowa kuwa yana magana da wasu harsuna, wadansu na waje da kuma marasa ba da gaskiya suka shigo, ashe, ba sai su ce kun haukace ba ba? 24 In kuwa kowa yana yin annabci, wani kuma marar ba da gaskiya ko wani daga waje ya shigo, maganar kuwa zata ratsa shi. Za a ma hukanta shi a kan maganar, 25 asiran zuciyarsa kuma za su tonu. Sakamokon haka, sai ya fadi ya yi wa Allah sujada, zaya furta cewa lallai Allah yana tare da ku. 26 Sai me kuma 'yan'uwa? idan kuka tattaru, wani yana da zabura, koyarwa, wahayi, harshe, ko fassara. Kuyi komai domin gina ikilisiya. 27 Idan wani yayi magana da harshe, bari a sami mutum biyu ko uku a yawansu, kuma kowa yayi daya bayan daya. Sai wani ya fassara abinda aka fada. 28 Amma idan babu wanda zaya fassara, bari dukansu suyi shiru a ikilisiya. Bari kowa yayi wa kansa maganar a gida shi kadai da kuma Allah. 29 Bari annabawa biyu ko uku suyi magana, bari sauran su saurara tare da bambance abinda ake fada. 30 Idan kuma anba wani fahimta wanda yana zaune a cikin sujadar, bari wanda yake ta magana kafin yanzu yayi shiru. 31 Dukanku kuna iya yin annabci daya bayan daya, domin kowannen ku yayi koyi, a kuma samu karfafawa. 32 Gama ruhohin annabawa suna karkashin annabawa, 33 domin Allah ba Allahn rudu ba ne, na salama ne. Haka yake kuwa a duk ikllisiyoyin masu bangaskiya. 34 Mataye suyi shiru a ikilisiyoyi. Domin ba a basu dama ba suyi magana. A maimako, su zama masu sadaukar da kansu, kamar yadda doka ta ce. 35 Idan akwai abinda suke so su koya, bari su tambayi mazajen su a gida. Domin abin kunya ne mace tayi magana a ikilisiya. 36 Daga wurinku maganar Allah ta zo ne? ko kuwa a gare ku kadai ta iso? 37 In wani yana zaton shi ma annabi ne, ko kuwa mai ruhaniya, to, sai ya fahimta, abin nan da nake rubuta maku umarni ne daga wurin Ubangiji. 38 In kuwa wani ya ki kula da wannan, shi ma kada a kula da shi. 39 Saboda haka, 'yan'uwa, ku yi marmarin yin annabci sosai, sa'an nan kada ku hana kow yin magana da harsuna. 40 Sai dai a yi komai ta hanyar da ta dace bisa ga tsari.
Bulus yana so su sani cewa ƙodashiƙe koyarwa ya na muhimminci sosai don yana umurta mutane, yakamata a yi shi a cikin kauna.
Bulus ya na magana game da kauna kamar mutum ne. "ku bi bayan kauna" ko kuma "yi aiki sosai domin ku ƙaunace mutane"
"yi aiki sosai domin ku iya yin anabci"
Gina mutane na wakilcin taimaka ma su domin su yi girma da karfi a cikin bangaskiya. Dubi yadda kun fasara "ginawa" a cikin 8:1. AT: "domin a karfafa su"
Gina mutane na wakilcin taimaka ma su domin su yi girma da karfi a cikin bangaskiya. Dubi yadda kun fasara "ginawa" a cikin 8:1. AT: "karfafa mutane"
Bulus ya na nanata cewa kyautar anabci ya fi kyautar magana da harsuna. AT: "Wanda yake anabci, ya ke da babban kyauta"
Wannan na nufin faɗa wa wadansu abin da wani ya ce a a harshen da basu gane ba. Dubi yadda an fasara wannan a cikin 2:13.
Wannan na iya zama jumla. AT: "Ba zan amfane ku ba." ko kuma "Da ban yi abin da zai taimake ku ba."
Wannan na nufin karan jifa dabam dabam da suke yin launin waƙa, ba ba bambaci a sakanin karan galgaita da sarewa ba.
Bulus yana son Korontiyawan su amsa wannan tambayan da kansu. AT: "ba wadda zai san irin amon da sarewar da algaitar suke kadawa."
launin ko waƙa
Bulus yana son Korontiyawan su amsa wannan tambayan da kansu. AT: "ba wadda zai san lokacin da ya dace a shirya wa yaƙi."
AT: "su na da ma'ana"
"yin abin da ke nuna cewa Ruhu ne na bi da ku"
Bulus ya yi magana game da ikilisiya kamar gida ce da wani zai iya gina, da kuma aikin gina ikilisiya kamar abu ne da mutum zai iya girba. AT: "domin cin nasara sosai a sa mutanen Allah su bauta masa"
Wannan na nufin gaya wa wadansu abin da wani ya ce a a harshen da basu gane ba. Dubi yadda an fasara wannan a cikin 2:13.
An yi maganar rashin fahimtar zuciya game da abin da ake yin addu'a, don haka, maganar rashin karban riba daga addu'a na kamar "hankalin da bata karu ba." AT: "A cikin hankalina da ban gane ba" ko kuma "hankalina ba shi da riba a addu'an, domin ban gane kalmomin da na ke faɗa ba"
Bulus ya na gabatar da kalmasawarsa. AT: "Ga abin da zan yi."
Dole ne addu'a da waƙoki su kasance a harshen da mutanin da sun hallaru su iya ganewa.
"da kalmar da zan gane"
Ƙodashiƙe "ku" anan daya ne, Bulus ya na magana da kowane mutum da ke addu'a a cikin ruhu kadai, amma ba tare da zuciya ba.
Wannan na iya zama jumla. AT: "wanda yake waje ba zai iya ce, 'Amin' ba ... faɗa ba."
AT: 1) "wani mutum" ko kuma "mutane da su sabobi ne a kungiyan ku."
"iya yarda"
Bulus ya na magana da Korontiyawan kamar su mutum daya ne, kalmar "ku" daya ne anan.
Gina mutane na wakilcin taimaka masu su yi girma da karfi a cikin bangaskiya. Dubi yadda za ku fasara "ginu" a cikin 8:1. AT: "dayan mutumin bai karfafu ba" ko kuma" abin da ku ka faɗa ba ya karfafa bare da zai iya ji ba"
Ba kirgen kalmomi ne Bulus yake yi ba, amma ya yi amfani da maganan domin ya nanata cewa kalmomi kadan da ana iya fahimta ya fi daraja fiye da lamban kalmomi a cikin harshen da mutane ba za su iya fahimta ba. AT: "kalmomi 10,000" ko kuma "yawan kalmomi"
Bulus ya faɗa masu cewa manzo Ishaya ya yi magana game da magana a cikin harsuna dabam dabam a shekaru dadama ta ta wuce kafin magana a waɗansu harsuna ya faru a farkon ikilisiyan Almasihu.
Anan "yara" magana ne game da rashin girma a ruhaniya. AT: "kada ku yi tunani kamar yara"
AT: "Manzo ne ya rubuta waɗannan kalmomi a cikin shari'a:"
Waɗannan jumlan na nufin abu iri daya kuma domin nanatawa, an yi amfani da su.
Ana iya bayyana a kuma hada wannan jumla da kyau. AT: "ga masubi ne kadai"
AT: "za su ce ku na hauka."
A takaice, Bulus ya faɗa abu biyu domin nanata. AT: "zai gane cewa yana da laifin zunubi domin ya na ji abin da kuke faɗa"
Anan "zuciya" magana ne game da tunanin mutum. AT: "Allah zai bayyana ma sa asiran da yake cikin zuciyar shi" ko kuma "zai gane asirin zurfin tunanin sa"
"fadi" karin magana ne da ke nufin durkusawa. AT: "zai durkusa ya yi wa Allah yabo"
Bulus ya yi amfani da tambaya domin ya gabatar da sakon sa. AT: "Domin komai da na faɗa maku gaskiya ne, ga abin da ya kamata ku yi, yan'uwana masubi."
"kuma su yi magana daya bayan daya"
AT: "fasara abin da sun faɗa"
Wannan na nufin gaya wa waɗansu abin da wani ya ce a a harshen da basu gane ba. Dubi yadda an bayana "fassara" a cikin 2:13.
AT: 1) annabawa biyu ko uku suke yin magana a taro. ko kuma 2) annabawa biyu ko uku ne suke magana a loƙacin da ya kamata.
AT: "ga abin da sun ce"
AT: "Idan Allah ya ba wani fahimta"
mutum daya ne kadai zai yi annabci ɗai bayan ɗai.
AT: "za ku iya karfafa duka"
Allah ba ya halitan yanayin rudu ta wurin sa mutane su yi magana a loƙaci ɗaya ba.
AT: 1) daina magana, 2) daina magana a loƙacin da wani yake yin anabci, ko kuma 3) ku yi shiru a loƙacin sujada.
Bulus ya nanata cewa ba Korontiyawa kadai ba ne suka fahimci abin da Allah ya ke so masubi su yi ba. AT: "maganar Allah bai zo daga wurin ku a Koronti ba; ba ku ne kadai mutanen da sun fahimci nufin Allah ba."
"maganar Allah" zance ne game da sako daga Allah. AT: "sakon Allah"
Manzon gaskiya ko mutum mai ruhun gaskiya ne zai karba rubutun Bulus yadda ya zo daga Allah.
AT: "kada ku kula da shi"
Bulus ya bayyana cewa an amincecce ne da kuma karbabbe ne magana a cikin harsuna a taron ikilisiya.
Bulus ya na nanata cewa a dinga yin taron ikilisiya a hanyar da ta ɗace. AT: "Amma ku yi komai ta hanyar da ta dace bisa ga tsari" ko kuma "Amma ku yi komai ta hanya da ta ɗace, hanya mai kyau"
Bulus ya ce mu yi himma ta musamman ga anabci.
Bada mutane yake magana ba amma da Allah.
Wanda yake magana da wani harshe, kansa yake ginawa, amma mai yin annabci kuwa, ikilisiya yake ginawa.
Ya kwatanta kayan kida kamar su sarewa da algaita da basu fitar da amo dabam dabam, da kuma busa kaho da sauti marar ma'ana.
Ya ce su himmatu da habaka cikin gina ikilisiya.
Ya yi addu'a domin ya iya fassarawa.
Bulus ya ce idan yayi addu'a da harshe, ruhunsa yayi addu'a, amma fahimtarsa bata karu.
Bulus ya ce zai yi addu'a da waka ba da ruhunsa kadai ba amma da hankalinsa.
Bulus ya ce ya gwammace ya yi magana da kalmomi biyar cikin fahimta saboda inganta waɗansu.
Harsuna alamu nega marasa bi kuma annabci kuwa alama ce ga masu bi.
Su na iya ce masubi sun haukace.
Bulus ya ce maganar zai ratsa marar ba da gaskiya ko wani ɗan waje. za a kuma hukanta shi da duk abin da an ce.
Zai faɗi ya yi wa Allah sujada, zaya kuma furta cewa lallai Allah yana tare da su.
Ya ce mutum biyu ko uku a yawansu za su yi magana, kuma kowa yayi daya bayan daya. Amma idan babu wanda zaya fassara, bari dukansu suyi shiru a ikilisiya.
Bulus ya ce a bar annabawa biyu ko uku suyi magana, sa'anan sauran su saurara tare da bambance abinda ake fada. Idan kuma wani anabin na da basira, bari wanda yake ta magana kafin yanzu yayi shiru.
Bulus ya ce ba a amince wa mata su yi magana a ikilisiyu ba.
A na ganin shi bin kunya ne.
Bulus ya ce masu su tambayi mazajen su a gida.
Bulus ya ce su fahimci cewa abubuwan da ya rubuta wa masubi na Korontiyawa umarne ne na Ubangiji.
Za a yi komai ta hanyar da ta dace bisa ga tsari.
1 Yanzu ina tunashshe ku 'yan'uwa, game da bisharar nan da nake shelarwa, wadda kuka karba kuke kuma dogara da ita. 2 Da wannan bishara aka yi maku ceto, idan kuka rike wa'azi da na yi maku da karfi, sai in dama kun gaskanta a banza. 3 Domin na baku muhimmin sako kamar na farko da na karba: cewa Almasihu ya mutu domin zunubanmu, bisa ga nassosi, 4 cewa kuma an bizne shi, ya kuwa tashi daga matattu a rana ta uku bisa ga nassosi. 5 Cewa kuma ya bayyana ga Kefas, sa'an nan ga sha biyun. 6 Daga nan ya bayyana ga 'yan'uwa sama da dari biyar a lokaci guda. Wadanda mafi yawan su na da rai har yau, amma wasun su sun yi barci. 7 Daga nan ya bayyana ga Yakubu, da kuma ga manzannin duka. 8 A karshe, sai ya bayyana a gare ni, kamar dan da aka haifa bakwaini. 9 Gama ni ne mafi kankanta a cikin manzanni. Ban cancanci a kira ni manzo ba, domin na tsanantawa ikklisiyar Allah. 10 Amma saboda alherin Ubangiji ina matsayin da nake a yau, kuma alherin sa da ke ciki na ba a banza yake ba. A maimako, nayi aiki tukuru fiye da su duka. Amma duk da haka ba ni bane, amma alherin Allah da ke tare da ni. 11 Saboda haka ko nine ko Su, haka mukayi wa'azin, haka kuma kuka gaskata. 12 To idan anyi shela a matsayin cewa Yesu ya tashi daga matattu, tayaya wadansunku su ke cewa babu tashin matattu? 13 Amma idan babu tashin matattu, Almasihu ma ai ba a tashe shi ba kenan. 14 idan kuwa ba a tashi Almasihu ba, wa'azin mu ya zama banza kenan, haka kuma bangaskiyar ku ta zama banza. 15 Mun kuma zama shaidun karya game Allah kenan, muna shaida akan Allah cewa ya tashi Almasihu daga matattu alhali ko bai tashe shi ba. 16 Domin idan babu tashin matattu, kai, ko Almasihu ma ba a tashe shi ba kenan. 17 Idan har ba a tashi Almasihu ba, bangaskiyar ku a banza take, har yanzu kuma, kuna cikin zunuban ku. 18 To wadanda suka mutu cikin Almasihu kuma sun hallaka kenan, 19 idan a wannan rayuwa ce kadai muke da bege cikin Almasihu, to cikin dukkan mutane munfi kowa zama abin tausayi. 20 Amma yanzu, Almasihu ya tashi daga matattu, wanda ya sa shi ya zama nunar fari cikin tashi daga matattu. 21 Domin yadda mutuwa ta shigo duniya ta hanyar mutum guda, hakkan nan ma tashi daga matattu. 22 Gama kamar yadda a cikin Adamu duka suka mutu, haka kuma a cikin Almasihu za a rayar da duka. 23 Amma kowanne da tsarinsa: Almasihu, nunan fari, sannan su wadanda ke na Almasihu za a rayar da su lokacin zuwansa. 24 Sa'an nan karshen zai gabato, lokacin da Almasihu zai mika mulkin ga Allah Uba. sa'an nan ne zaya kawar da dukkan mulki, martaba da iko. 25 Gama mulkinsa zai habaka har sai ya sa dukkan makiyansa a karkashin sawayen sa. 26 Mutuwa kuwa, ita ce makiyi na karshe da za'a hallaka. 27 Domin " yasa dukkan komai a karkashin ikonsa," Amma da aka ce" yasa dukkan komai a karkashin ikonsa," a sarari yake cewa wannan baya hada da wanda yasa dukan komai a karkashin ikonsa ba. 28 Idan dukan abu na karkashin mulkinsa, to Dan da kansa zaya kasance a karkashin ikon shi wanda yasa komai a karkashin ikonsa. Wannan zaya kasance ne saboda Allah Uba ya zama dukkan komai cikin dukkan komai. 29 ko kuma me zai faru da wadanda ake yi wa baftisma domin matattu? Idan kuwa babu tashin matattu sam sam, ina amfanin yi masu baftisma domin su? 30 Kuma me yasa muke cikin hadari kowace sa'a? 31 Ina mutuwa kullum. Wannan nake furtawa ta wurin fahariya, 'yan'uwa, wadda nake da ita cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu. 32 Menene ribata, a idanun mutane, idan nayi kokowa da bisashe a Afisa, idan babu tashin matattu? "bari mu ci mu sha, domin gobe zamu mutu." 33 Kada fa a yaudare ku, domin " tarayya da mugaye takan bata halayen kirki." 34 "Ku natsu! kuyi zaman adalci! kada ku cigaba da zunubi. Domin wasunku basu da sanin Allah. Ina fadar wannan domin in baku kunya. 35 Amma wani zaya ce, "Yaya za'a yi tashin matattu? Wane irin jiki kuma zasu tashi da shi? 36 Ku jahilai ne sosai! Abinda ka shuka ba zaya fara girma ba sai ya mutu. 37 Abinda ka shuka ba jikin da zaya kasance bane, amma kwayar irin ne kawai. Wanda zaya zama alkama ko wani abu daban. 38 Amma Allah zaya bashi jiki yadda ya zaba, ga kowane kwayar iri da nashi jikin. 39 Ba duka jiki ne yake iri daya ba. A maimako, akwai jiki irin na mutane, akwai kuma wani irin na dabbobi, kuma wani jikin irin na tsuntsaye, kuma da irin na kifi. 40 Akwai kuma jikina na samaniya da jikina na duniya. Amma daukakar jikin samaniya wata daban ce kuma daukakar jikin duniya daban ce. 41 Akwai daukaka irin ta rana, da kuma wata daukakar irin ta wata, da kuma wata daukakar irin ta taurari. Domin wani tauraron ya bambanta da wani wajen daukaka. 42 Haka yake a tashin matattu. Abinda aka shuka mai lalacewa ne, wanda aka tayar marar lalacewa ne. 43 An shuka shi cikin rashin daraja; an tayar da shi cikin daukaka. An shuka shi cikin rauni; an tayar da shi cikin iko. 44 An shuka shi jiki na zahiri; an tayar da shi jiki na ruhaniya. Idan akwai jiki na zahiri, to akwai jiki na ruhaniya. 45 Haka kuma aka rubuta, "Adamu na farko ya zama rayayyen taliki." Adamu na karshe ya zama Ruhu mai bayar da rai. 46 Amma na ruhaniyar ba shine ya fara zuwa ba amma na zahirin, daga nan na ruhaniyar. 47 Mutumin farkon ai daga turbaya ya fito, wato na duniya. Amma shi na biyun daga sama yake. 48 kamar yadda mutumin ya fito daga turbaya haka ma wadanda aka halitta da turbaya. kamar yadda mutumin yake daga sama haka ma wadanda ke na sama. 49 Kamar yadda muke dauke da jiki mai kamannin turbaya, haka ma zamu kasance da kamannin mutumin sama. 50 To wannan na fada, 'yan'uwa, cewa nama da jini ba za su gaji mulkin Allah ba. Haka kuma mai lalacewa ba za ya gaji marar lalacewa ba. 51 Duba! ina gaya maku asirtacciyar gaskiya: Ba dukanmu zamu mutu ba, amma dukanmu za a canza mu. 52 Za a canza mu nan da nan, cikin keftawar ido, a kaho na karshe. Domin za a busa kaho, kuma za a tada matattu marasa lalacewa, kuma za a canza mu. 53 Domin wannan jiki mai lalacewa dole ya sanya jiki marar lalacewa, kuma wannan jiki mai mutuwa dole ya sanya marar mutuwa. 54 Amma idan wannan jiki mai lalacewa ya sanya marar lalacewa, kuma wannan jiki mai mutuwa ya sanya marar mutuwa, sai abinda aka rubuta ya cika, "An hadiye mutuwa cikin nasara." 55 "Mutuwa, ina nasararki? Mutuwa, ina dafinki?" 56 Gama dafin mutuwa zunubi ne, kuma ikon zunubi shari'a ce. 57 Amma godiya ga Allah, wanda ya bamu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu! 58 Saboda haka, ya ku 'yan'uwana kaunatattu, ku dage kuma kada ku jijjigu. Ko yaushe ku habaka da aikin Ubangiji, domin kun san cewa aikinku cikin Ubangiji ba a banza yake ba.
Bulus ya tuna masu cewa bishara ne ta cece su ya kuma faɗa masu abin da bisharan ke nufi. Ya ba su dan darasin tarihi, wadda ya kamala da abin da zai faru.
"taimake ku tunawa"
Bulus ya na magana game da Korontiyawa kamar su gini ne da kuma bishara kamar ita ce tushen da gidan ya ke dogara a kai.
AT: "Allah zai cece ku"
"sakon da nake iya maku wa'azin"
AT: 1) kamar mafi muhimincin abubuwa dayawa ko kuma 2) kamar na farko a cikin lokaci.
"biya domin zunubanmu" ko kuma "domin Allah ya iya yafe zunubanmu"
Bulus ya na nufin rubutun Tsohon Alkawari.
AT: "sun bizne shi"
AT: "Allah ya tashe shi"
"an sa shi ya rayu kuma"
"nuna kansa wa"
500
"barci" anan magana ne game da mutuwa. AT: "waɗansu sun mutum"
"A karshe, bayan ya bayyana ga wadansun"
Wannan magana ne da Bulus na iya nufin cewa ya zama mai bi a bayan sauran manzanin. ko kila ya na nufin cewa, ba kamar sauran manzanin ba, bai gan hidimar Yesu na shekara uku ba. AT: "wani da ya rasa ayukan waɗansu"
Alherin Allah ko kauna ne ya sa Bulus a yadda yake yanzu.
Bulus ya na nanatawa ta wurin magana cewa Allah ya yi aiki ta wurin Bulus. AT: "domin ya yi mun kirki, na iya yin aiki mai kyau"
Bulus ya yi magana game da aiki da ya iya yi domin Allah ya yi masa kirki, kamar Alherin ne ya ke yin aikin. AT: 1) Wannan gaskiya ne, kuma Allah ya yi aikin ya kuma yi amfani da Bulus da kyau a matsayin kayan aiki ko kuma 2) Bulus ya na amfani da magana, da cewa Allah ya so Bulus ya yi aikin ya kuma sa aikin Bulus ya sami sakamako mai kyau.
Bulus ya na amfani da wannan tambayan domin ya fara sabon batu. AT: "ku daina faɗa cewa babu tashin matattu!"
Bulus yana amfani da wannan magana domin ya tabbatar da cewa akuwai tashin matattu. Ya san cewa Almasihu ya tashi, shi ya sa ya bayyana cewa akuwai tashin matattu. Faɗa cewa babu tashin matattu na nan kamar cewa Almasihu bai tashi ba, amma wannan karya ne domin Bulus ya gan Almasihun da ya tashi 15:8.
AT: "Allah bai tashe Almasihu ba"
sa rayayye kuma
Bulus ya na bayyana cewa idan Almasihu bai tashi daga matattu ba, ya zama su na shaida karya ko kuma suna karya game da zuwan Almasihu kuma.
AT: "kowa za su gane cewa mu"
bangaskiyar su na kan Almasihu da ya tashi daga mattatu, da haka bai faru ba, da bangaskiyar su ya zama ba bu amfani.
"na kowa, tare da masubi da kuma marasa bi"
"mutane su ji tuasayin mu fiye da yadda suke ji ma waɗansu"
"kamar yadda yake, Almasihu" ko kuma "wannan ne gaskiyan: Almasihu"
Anan "nunar fari" magana ne da ke kwatanta Almasihu da girbin farko, da ke biye da sauran girbin. Almasihu ne na farko da ya tashi daga matattu. AT: "wadda yake kamar na farkon a girbi"
"tashi" karin magana ne game da "sa ya rayu kuma." AT: "Allah ya tashe Almasihu, wanda shi ne nunar fari na wadda sun mutu"
Ana iya bayyana kalmar "mutuwa." AT: mutane na mutuwa domin mutum daya"
Ana iya bayyana kalmar "tashi." AT: "mutane na tashi daga matattu saboda wani mutum"
Anan kalmomin "shi" da "na shi" na nufin Almasihu.
"zai hana mutanen da suke mulki, wadda suke da iƙon aikata abin da su ke aikatawa"
Sarakuna da sun ci yaƙi za su sa ƙafafunsu a wuyan wadanda sun yake su. AT: "sai Allah ya hallaƙa dukka maƙiyan Almasihu gabadaya"
Bulus ya yi magana game da mutuwa kamar mutum ne wadda Allah zai kashe. AT: "mutuwa ce maƙiya na karshe wadda Allah zai hallaƙa"
Sarakuna da sun ci yaƙi za su sa ƙafafunsu a wuyan waɗanda sun yake su. Dubi yadda an fasara "sa ... a karkashin iƙonsa" a cikin 15:25. AT: "Allah ya hallaƙa dukka maƙiyan Almasihu gabadaya"
AT: "Allah ya sa komai a karkashin iƙon Almasihu"
AT: "Ɗan da kansa zai yi zama a karkashi"
A cikin ayoyin da suka wuce, an kira shi "Almasihu." AT: "Almasihu, Ɗan da kansa"
Wannan lakami ne na muhimmi da ke kwatanta ɗangantaka a sakanin Yesu da Allah.
Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya koya wa Korontiyawa. AT: "in ba haka ba zai zama da rashin amfani wa masubi su karbi baftisma wa matattu."
Bulus ya yi amfani da wata yanayi domin ya bayana cewa ana tashin matattu. Faɗa cewa ba bu tashin matattu na nan kamar faɗan cewa kada mutane su yi baftisma domin matattu. Amma waɗansu mutane, watakila waɗansu mutanin ikilisiyan Koronti, sun yi baftisma domin matattu, don haka ya na zata cewa waɗanan mutanin sun yi baftisma domin matattu don sun gaskanta cewa akowai tashin matattu.
AT: "Allah baya tashin matattu"
"ba a sa ya rayu kuma"
Bulus ya yi amfani da wannan tambaya domin ya koyar da Korontiyawan. AT: "basu da dalilin da mutane za su yi ma su baftisma a madadin matattu ba."
Bulus ya yi amfani da wannan tambaya domin ya koyar da Korontiyawan. Dalilin da shi da sauran sun shiga hadari shine waɗansu mutane sun yi fushi cewa suna zato Yesu zai tashe mutane daga matattu. AT: "Idan mutane baza su tashi daga matattu ba, bamu da riban komai a kasancewan mu a cikin hadarin kowace sa'a na koya cewa mutane za su tashi."
Anan "fuskanta mutuwa" na wakilcin sanin cewa zai mutu jim kaɗan. Ya san cewa waɗansu mutane sun so su kashe shi domin ba su so abin da yake koyarwa ba. AT: "Kullum ina yin kasada da rai na!"
Bulus ya yi amfani da wannan jumlan domin ya nuna cewa ya na fuskanta mutuwa kullum. AT: "Zan ku iya sani cewa wannan gaskiya ne, domin kun san game da fahariya ta a cikin ku" ko kuma "Zan ku iya sani cewa wannan gaskiya ne, domin kun san yadda na ke fahariya a cikin ku"
Bulus ya yi fahariya a cikin su domin abin da Almasihu Yesu ya yi masu. AT: "fahariya ta a cikin ku, wadda nake yi domin abin da Almasihu Yesu Ubangijinmu ya yi maku"
"yadda nake faɗa wa waɗansu mutane game da kirkin ku"
Bulus ya na so Korontiyawa su gane ba sai ya gaya masu ba. Wannan na iya zama jumla. AT: "Ban samu riban komai ba ... ta wurin kokowa da bisashe a Afisa ... tashi ba."
Bulus ya na nufin abin da ya yi. 1) Bulus ya na magana game da jayayyan sa da kafirai masani da kuma mutane da sun so su kashe shi ko kuma 2) an sa shi a filin da zai yaki mugayen dabbobi.
Bulus ya kalmasa da cewa idan akowai rai bayan mutuwa, zai yi mana kyau idan mun more wannan rai, domin gobe rain mu zai kare da rashin wata fata.
Idan kun yi rayuwa da mugayen mutane, za ku aikata kamar su. Bulus ya na faɗan karin magana ne.
"Dole ne ku yi tunani game da wannan"
Suna iya nufin 1) mutumin na tambaya da gaskiya ko kuma 2) mutumin ya na amfani da tambayan domin ya yi ba'a game da maganan tashin matattu. AT: "Amma waɗansu za su ce ba su san yadda Allah zai tayar da matattu ba, da kuma irin jiki da Allah zai ba su a tashin matattu."
"wani zai yi tambaya"
Zai zama jiki na ruhaniya ne ko jiki wadda ana iya gani? Wace irin halitta ne jikin za ta kasance da shi? Yi amfani a fasara tambaya na muhimmi wadda wani da zai so ya san amsoshi game da wannan tambayoyin zai iya tambaya.
Bulus ya na magana da Korontiyawa kamar su mutum daya ne, don haka misalin "ku" a nan daya ne.
"Ba ku san game da wannan ba"
Iri ba zai yi girma ba sai an binne a karkashin kasa. Haka kuma, sai mutum ya mutu kafin Allah ya tashe shi.
Bulus ya yi amfani da maganan iri kuma domin ya faɗa cewa Allah ya tayar da mutatcen jikin masubi, amma jikin ba zai bayyana kamar yadda yake ba.
Bulus ya na magana da Korontiyawa kaman su mutum daya ne, don haka kalmar "ku" anan daya ne.
"Allah zai zaɓi irin jiki da zai kasance da shi"
Game da dabbobi, an na iya fasara "jiki" kamar "fata" ko kuma "nama."
AT: 1) rana, wata, tauraru, da sauran haske a cikin sarari ko kuma 2) mutane na samaniya, kamar mala'iku da sauran mutane da sun wuce ikon ɗan Adam.
Wannan na nufin mutane.
"ɗaukaka da jikin samaniya ke da shi dabam ne da ɗaukaka na jikin mutane"
Anan "ɗaukaka" na nufin gwargwadon haske ga idon mutum a sarari.
Marubucin ya yi magana game da jikin mutum da an binne kamar ya zama iri da aka shuka a kasa. Ya kuma yi magana game da tashin jikin mutum daga matattu kamar shuka da yake girma daga irin. AT: "Abin da ya nufi kasa ... Abin da ke fata daga kasa ... ya na nufa cikin kasa ... ya fito daga kasa" ko kuma "Abin da mutane suka binne ... Abin da Allah ya tayar ... Mutane sun binne ... Allah ya tayar"
"an sa shi ya rayu kuma"
"zai iya ruɓa ... ba zai iya ruɓa ba"
"mutum na zahiri ne ya zo da farko. Mutum na ruhaniya daga Allah ne kuma ya zo daga baya ne."
halittace daga hanyoyi ta duniya, da baya a haɗe da Allah
Allah ya yi mutum na farko, Adamu, daga ƙura duniya.
ƙazanta
Yesu Almasihu
"waɗanda sun zama na Allah"
"ya kasance kamar ... zai kuma kasance kamar"
Suna iya nufin 1) jimla biyu nan na nufin abu ɗaya ne. AT: "mutane da za su mutu ba za su gaji mulkin Allah mai dauwama ba" ko kuma 2) jimla na biyu ya karasa tunani da na farkon ya fara. AT: "mutanin da ba su da ƙarfi ba za su gaji mulkin Allah ba. Ko kuma waɗanda za su mutu ne ma su gaji mulkin har'abada"
Waɗanda sun zauna a jikin da an ƙaddara ya mutu.
An yi maganar karɓan abin da Allah ya yi wa masubi alkawari kamar ya na gaji kaya da dukiya daga ɗan iyali.
AT: "Allah zai canza mu dukka"
AT: "Allah zai canza mu"
Zai faru da sauri kamar yadda mutum ya na kefta idonshi ko idonta.
"loƙacin da kaho na karshe ya yi kara"
AT: "Allah zai tada matattu"
"a hanyar da ba zai ruɓa ba ... jikin nan da ba zai iya ruɓa ... ba zai iya ruba ba." Dubi yadda an fasara jumla irin wannan a cikin 15:42
Bulus ya na magana game da yadda Allah ya na sa jikinmu kada su mutu kamar Allah ya na sa ma na sabon kaya.
Anan an yi maganar jiki kamar mutum ne. AT: "loƙacin da wannan jiki mai lalacewa ya zama marar lalacewa" ko kuma "loƙacin da wannan jikin da na iya rubawa ba zai iya ruba kuma ba"
Anan an yi maganar jiki kamar mutum ne. AT: "a loƙacin da wannan jiki mai mutuwa ya zama mara mutuwa" ko kuma "loƙacin da wannan jikin da na iya mutuwa ba zai iya mutuwa ba"
Bulus ya yi magana kamar mutuwa mutum ne, ya kuma yi amfani da wannan tambaya domin ya yi wa iƙon mutuwa gori. AT: "Mutuwa ba shi da nasara. Mutuwa ba shi da dafinki."
Wannan daya ne.
Ta wurin zunubi ne an ƙaddara ma na mutuwa.
Shari'a Allah da Musa ya kawo ne ya bayyana zunubi, ya kuma nuna mana yadda muke zunubi a gaban Allah.
"ya yaƙi mutuwa domin mu"
Bulus ya yi magana game da wani da be bar komai ya hana shi yin abin da ya yi niya ba. AT: "ku ƙudura"
Bulus ya yi magana game da ƙoƙarin da ake yi a aikin Ubangiji kamar sun zama kayan da mutum na iya samu. AT: "Ko yaushe ku yi wa Ubangiji aiki da aminci"
Ya tunashe su game da bisharar da yake yi masu shela.
Bulus ya faɗa masu cewa za su tsira idan suka rike wa'azi da ya yi masu da ƙarfi.
Sashin bisharar da su ke da mafi muhimminci su ne cewa Almasihu ya mutu domin zunubanmu, bisa ga nassosi, kuma an binne shi, ya kuma tashi daga matattu a rana ta uku bisa ga nassosi.
Bayan ya tashi daga matattu, Almasihu ya bayyana wa Kefas, ga sha biyun, ga 'yan'uwa maza da mata fiye da dari biyar a loƙaci ɗaya, ga Yakub, ga dukka manzanni da kuma Bulus.
Ya faɗa haka domin ya tsanantawa ikklisiyar Allah.
Ya na nufin cewa waɗansunsu su na cewa babu tashin matattu.
Bulus ya faɗa cewa idan kuwa haka ne, Almasihu bai tashi daga matattu ba, kuma wa'azin Bulus da wasu kamar sa ya zama banza kenan, kuma bangaskiyar Korontiyawa ta zama banza.
Sun hallaka kenan.
Idan wannan haka ne, cikin dukkan mutane munfi kowa zama abin tausayi.
Ya na kiran Almasihu, "nunar fari cikin tashi daga matattu".
Adamu ya kawo mutuwa cikin duniya kuma ta wurin Almasihu za a rayar da duka.
Wannan zai faru a loƙacin da Almasihu zai zo.
Almasihu zai mika mulkin ga Allah Uba, sa'an nan ne zaya kawar da dukkan mulki, martaba da iko.
Ɗole mulkinsa zai habaka har sai ya sa dukkan makiyansa a ƙarƙashin sawayen sa.
Mutuwa kuwa, ita ce makiyi na karshe da za'a hallaka.
Wanda ya sa komai cikin ikon Ɗan (kansa) ba a hada shi kamar ya na karkashin ikon (Ɗan) ba.
Ɗan da kansa zaya kasance a ƙarƙashin ikon shi wanda yasa komai a ƙarƙashin ikonsa.
Bulus ya ce, "bari mu ci mu sha, domin gobe zamu mutu."
Ya umarce su su natsu, suyi zaman adalci, kuma kada su cigaba da zunubi.
Ya ce wasunsu basu da sanin Allah.
Ya kwatanta shi da irin da an shuka.
Ɗole ya mutu.
Abinda ka shuka ba ya kama da jikin da zaya kasance ba.
A'a. Ba dukka jiki ne ɗaya ba, Jiki irin na mutane, dabbobi, tsuntsaye, da kifi dukka dabam dabam ne.
Akwai kuma jikina na samaniya da jikina na duniya.
Akwai ɗaukaka ɗaya na rana, da kuma wani ɗaukakar irin ta wata, da kuma wata ɗaukaka irin ta taurari kuma wani tauraron ya bambanta da wani wata a ɗaukaka.
An shuka shi cikin rashin daraja da cikin rauni.
Wanda aka tayar marar lalacewa ne; an tayar da shi cikin ɗaukaka da iko.
Adamu na farko ya zama rayayyen taliki.
Ya zama Ruhu mai bayar da rai.
Mutumin farkon daga turbaya ya fito, wato na duniya. Mutum na biyun daga sama yake.
Kamar yadda muke ɗauke da jiki mai kamannin turbaya, haka ma zamu kasance da kamannin mutumin sama.
Nama da jini ba za su gaji mulkin Allah ba.
Dukanmu za a canza mu.
Za a canza mu nan da nan a loƙacin da an yi busan kaho na karshe, a cikin keftawar ido.
Za a hadiye mutuwa cikin nasara.
Dafin mutuwa zunubi ne, kuma ikon zunubi shari'a ce.
Allah ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu!.
Ya gaa masu su yi wannan domin sun san cewa aikinsu cikin Ubangiji ba a banza yake ba.
1 Yanzu game da zancen tattara gudunmuwa ga masu bi, kamar yadda na umurci ikilisiyun Galatiya, haka za ku yi. 2 A ranar farko ga mako, kowannen ku ya ajiye wani abu, yana tarawa bisa ga iyawarku. Ku yi haka don in na zo ba sai an tattara ba. 3 Sa'adda na zo, zan aiki duk wadanda kuka yarda da su da wasiku don su kai sakonku Urushalima. 4 Sannan idan ya dace nima in tafi, sai su tafi tare da ni. 5 Zan zo wurinku sa'adda na ratsa Makidoniya. Domin zan ratsa ta makidoniya. 6 Meyuwa in jima a wurinku, har ma in yi damuna, domin ku taimaka mani game da tafiyata, duk inda za ni. 7 Gama ba na so in yi maku gani na gajeren lokaci. Don ina so in dau lokaci tare da ku, idan Ubangiji ya yarda. 8 Amma zan tsaya Afisus har ranar Fentikos. 9 Gama an bude mani kofa mai fadi, kuma akwai magabta da yawa. 10 Sa'adda Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa acikinku, tun da aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi. 11 Kada fa kowa ya rena shi. Ku tabbata kun sallame shi lafiya, domin ya komo gare ni, don ina duban hanyarsa tare da yan'uwa. 12 Game da zancen dan'uwanmu Afollos kuwa, na karfafa shi ya ziyarce ku tare da 'yan'uwa. Sai dai baya sha'awar zuwa yanzu. Amma zai zo sa'adda lokaci ya yi. 13 Ku zauna a fadake, ku tsaya daram cikin bangaskiya, kuna nuna halin maza, ku yi karfin hali. 14 Bari dukan abinda kuke yi ayi shi cikin kauna. 15 Kun dai sani iyalin gidan Sitefanas su suka fara tuba a Akaya, kuma sun bada kansu ga yi wa masu bi hidima. Yanzu ina rokonku, 'yan'uwa, 16 kuyi biyayya da irin wadannan mutane da duk wanda ke taimakawa a cikin aikin, yana kuma fama tare da mu. 17 Na yi farinciki da zuwan Sitefanas, da Fartunatas, da Akaikas. Sun debe mini kewarku. 18 Gama sun wartsakar da ruhuna da naku kuma. Don haka, Sai ku kula da irin wadannan mutane. 19 Ikilisiyoyin kasar Asiya suna gaishe ku. Akila da Bilkisu, tare da ikilisiyar da take taruwa a gidansu, suna gaishe ku cikin Ubangiji. 20 Dukan 'yan'uwa masu bi na gaishe ku. Ku gaida juna da sumba maitsarki. 21 Ni Bulus, nake rubuta wannnan da hannuna. 22 Duk wanda ba ya kaunar Ubangiji bari ya zama la'ananne. Ubangijinmu, Ka zo! 23 Alherin Ubangiji Yesu ya kasance tare da ku. 24 Bari kaunata ta kasance tare da ku duka a cikin Almasihu Yesu. [1]
A rubutunsa na rufewa, Bulus ya tuna wa masubi na Korontiyawa da cewa su karɓa kuɗi wa musubi da suke da bukatu a Urushalima. Ya tuna masu da cewa Timoti zai zo masu kafin ya je wurin Bulus.
Bulus ya na karɓan kuɗi daga ikilisiyoyi domin talakawan Yahudawa masubi a cikin Urushalima da kuma Yahudiya.
"kamar yadda ina ba da su takamaiman umurni"
AT: 1) ajiye shi a gida ko kuma 2) "bar shi tare da ikilisiyan"
"domin ba sai kun sake karban kuɗi kuma ba a loƙacin da ina tare da ku"
Bulus ya na faɗa wa ikilisiyan da cewa su zabi daga cikin mutaninsu wadda za su kai baikonsu a Urushalima. "waɗanda ku ka zaba" ko kuma "mutanin da ku ka naɗa"
AT: 1) "Zan aika da wasikun da zan rubuta" ko kuma 2) "Zan aika da wasikun da za ku rubuta."
Wannan na nufin cewa za su iya ba wa Bulus kuɗi ko kuma wadansu abubuwa da ya na bukata domin shi da 'yan'uwansa na bishara su iya cigaba da tafiya.
Bulus ya na bayyana cewa ya na so ya yi ziyara na tsawon loƙaci, ba na ƙaramin loƙaci ba.
Bulus zai tsaya a Afisus sai wannan ranar idi, wadda ya zo a May ko kuma June, a kwana hamsin a bayan Idin ketarewa. Zai kuma yi tafiya ta Makidoniya, sai ya kuma sauka a cikin Koronti kafin rani ya fara a watan goma sha ɗaya.
Bulus ya yi magana game da loƙacin da Allah ya bashi domin ya rinjaye mutane zuwa ga bishara. Kamar kofa ce da Allah ya buɗe domin ya iya tafiya a cikinsa.
"ku tabbata cewa ba shi da tsoron kasancewa da ku"
Domin Timoti ya fi Bulus ƙarami, wani loƙaci ba a girmama shi yadda ya kamata a matsayin mai koyarwan bishara.
Anan kalmar "mu" na nufin Bulus da ma su sauraransa.
Bulus ya na kwatanta abin da yake son Korontiyawan su yi kamar ya na ba wa soja umurni hudu a yaki. Wannan umurni hudun na nufin abu ɗaya kuma ana amfani da su domin nananci.
Bulus ya yi magana game da mutanin da sun san abin da ke faru kamar sun zama masu tsaro da ke tsaron gari ko kuma lambu. AT: "Yi hankali da wadda kun amince da shi" ko kuma "ku yi hankali da haɗari"
Bulus ya yi magana game da yadda mutane sun cigaba da bin Almasihu bisa koyarwansa kamar sun zama sojojin da sun ƙi su ja da baya a harin makiya. AT: 1) "ku gaskanta da karfi a abin da mun koya maku" ko kuma 2) "ku amince da Almasihu da karfi"
A garin da Bulus da masu sauraransa suke, mazaje su na tanada wa iyalin su ta wurin yin aiki mai karfi da faɗa da masu shigan gari da hari. AT: "ku zama da takalifi"
"Dukkan abin da ku ke yi ya nuna wa mutane cewa ku na kaunan su"
Sitefanas daya ne daga cikin farkon masubi ikilisiyan Koronti.
Wannan sunan lardi a cikin Girka.
Waɗannan mazajen, masubi ne na farko a Korontiya ko kuma dat'tawan ikilisiya da suke aiki tare da Bulus.
"sun shirya da shike ba ku nan."
Bulus ya na cewa ya karfafu da ziyarar su.
Bulus ya fadi a bayyane da cewa umurnin da ke a wasikannan daga gare shi ne, ko da shike ɗaya daga cikin ma'aikatan sa ya rubuta abin da Bulus ke faɗi a sauran wasikun. Bulus ya rubuta na karshen da hannun sa.
"Bari Allah ya la'anta shi." Dubi yanda "la'ananne" an bayana a cikin 12:1.
Bulus ya umurci ikilisiyun Galatiya kamar yadda yake a ikilisiya a Koronti.
Ya ce masu a ranar farko ga mako, kowannen su ya ajiye wani abu, yana tarawa bisa ga iyawarsu, domin kada a yi wani tari a loƙacin da Bulus zai zo.
Zai je wurin masubi a Urushalima.
Zai zo wurinsu sa'adda ya ratse Makidoniya.
Bulus ya so ya ziyarce su na tsawon lokaci, idan Ubangiji ya yarda.
Bulus ya tsaya a Afisus domin kofa mai fadi ya buɗe masa, kuma akwai magabta da yawa.
Timoti na aikin Ubangiji kamar yadda Bulus yake.
Bulus ya faɗa wa ikilisiya a Koronti cewa su tabbata Timoti ya sami sakewa acikinsu. Bulus ya ce masu kada kowa ya rena shi kuma su tabbata sun sallame shi cikin salama.
Bulus ya karfafa Afollos don ya ziyarce masubi a Koronti.
Iyalin gidan Sitefanas sun ba da kansu ga yin hidima wa tsarkaku.
Bulus ya ce masu su yi biyayya da irin waɗannan mutane.
Sun debe kewar tsarkakun Korontiyawa, sun kuma wartsakar da ruhun Bulus.
Ikilisiyoyin Asiya, Akila da Bilkisu, da dukan 'yan'uwa maza da mata masu bi sun aika gaisuwarsu ga ikilisiya a Koronti.
Bulus ya ce,"Idan wani ba ya ƙaunar Ubangiji, bari ya zama la'ananne"
1 Bulus, manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah, da kuma Timoti dan'uwan mu, zuwa ga Ikilisiyar Allah da ke a Korantus, da kuma dukan 'yan'uwa da ke yankin kasar Akaya. 2 Bari alheri ya kasance tare da ku da kuma salama ta Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Almasihu. 3 Bari yabo ya tabbata ga Allah da kuma Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu. Shine Uba na dukan jiyejiyenkai, da kuma Allah na dukan ta'aziya. 4 Allah yana ta'azantar da mu a cikin dukan wahalarmu, domin mu iya ta'azantar da wadanda ke cikin kowace wahala. Muna ta'azantar da wasu da irin ta'aziyar da Allah ke ta'azantar da mu. 5 Gama kamar yadda wahalhalun Almasihu suka karu domin mu, haka kuma ta'aziyarmu ta yawaita cikin Almasihu. 6 Amma fa idan muna shan wuya, domin ta'aziyarku ne da cetonku. Haka kuma in mun ta'azantu, domin ta'aziyarku ne. Ta'aziyarku tana aiki ne sosai yayinda kuka jure da irin shan wuyar da mu ma muke sha. 7 Kuma gabagadinmu game da ku tabbatacce ne. Mun kuwa sani kamar yadda kuke tarayya cikin shan wahalhalun, haka kuma za ku yi tarayya cikin ta'aziyyar. 8 Gama ba mu so ku rasa sani, 'yan'uwa, game da tsananin da ya same mu a Asiya. An murkushe mu gaba daya har fiye da karfin mu, har ma mun fidda zuciya za mu rayu. 9 Hakika, mun ji hukuncin mutuwa akan mu. Amma wannan ya faru ne domin kada mu dogara ga kanmu, sai dai ga Allah, wanda ke tada matattu. 10 Ya kubutar da mu daga wannan mummunan hatsari na mutuwa, kuma zai sake kubutar da mu. Mun kafa begenmu gare shi cewa zai sake kubutar da mu. 11 Zai aikata wannan yayinda kuka taimake mu da addu'ar ku. Sa'an nan da dama za su bada godiya a madadin mu don tagomashin alheri da aka yi mana ta wurin addu'o'in mutane masu yawa. 12 Muna kuwa alfahari da haka: wato shaidar lamirinmu. Gama da kyakkyawan nufi da aminci da ke zuwa daga Allah muka tafiyar da rayuwarmu a Duniya. Mun yi wannan ne musamman tare da ku-ba kuwa cikin hikimar Duniya ba, amma ta wurin alherin Allah. 13 Bamu rubuta maku abinda ba za ku iya karantawa ko fahimta ba. Ina fata za ku fahimce mu baki daya, 14 kamar yadda kuka fahimce mu kadan yanzu. Daganan a ranar Ubangijinmu Yesu za mu zama dalilinku na alfahari, kamar yadda za ku zama namu. 15 Saboda gabagadin da nake da shi game da haka, naso in zo gare ku da farko, domin ku amfana da ziyara sau biyu. 16 Ina da shirin ziyaratar ku a kan hanyata ta zuwa Makidoniya. Daga nan kuma ina da yi niyyar in sake ziyartar ku, a tafiya ta daga Makidoniya, domin ku aike ni a hanyata ta zuwa Yahudiya. 17 Yayinda nake irin wannan tunani, ina shakka ne? Ina shirya abubuwa ne bisa ga magwajin mutum, ta yadda har zan ce "I, i" da "A, a, a, a" a lokaci guda? 18 Amma kamar yadda Allah yake amintacce, ba ma fadin "I" da "A'a" a lokaci guda. 19 Gama Dan Allah, Yesu Almasihu, wanda Silbanus da Sila, da Ni muka shaida maku, ba "I" da "A, a" ba ne. Maimakon haka, Shi "I" ne a kodayaushe. 20 Gama dukan alkawaran Allah 'I' ne a cikin sa. Haka kuma ta wurin sa muna cewa "Amin" zuwa ga daukakar Allah. 21 Yanzu dai Allah ne ya tabbatar da mu da ku a cikin Almasihu, ya kuma kebe mu. 22 Ya sa hatiminsa a kan mu ya kuma ba mu Ruhu a zuciyar mu a matsayin tabbacin abinda zai bamu daga baya. 23 Maimakon haka, na yi kira ga Allah ya zama shaida domina, cewa dalilin dayasa banzo Korintis ba domin in kare ku ne. 24 Ba muna kokarin mu sarrafa yadda bangaskiyar ku za ta zama ba ne. Maimakon haka, muna aiki tare da ku ne domin farincikinku, yayinda kuke tsaye cikin bangaskiyarku.
Bayan gaisuwan Bulus zuwa ga Ikilisiyar da ke Korantus, ya rubuta kuma game da azaba da kuma ta'aziya da ke samu ta wurin Yesu Almasihu
Harshen ku, ya iya yuwa kuna da yadda kuna gabatar da marubucin wasika da kuma masu sauraro. AT: " Ni, Bulus... na rubuto muku wannan wasika, Ikilisiyar Allah dake a Korantus"
wannan na nuna cewa Bulus da Mutanen Korantus sun san Timoti, suna kuma ɗaukansa dan'uwansu cikin ruhaniya.
Wannan sunace yankin gabacin Roma wanda a yau itace Girka.
wannan gaisuwace da Bulus ya saba amfani da ita a wasikarsa
Wannan ana iya bayyana ta kamar haka. AT: Bari mu ɗaukaka Allah da kuma Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu"
"Allah, Wanda shine Uban"
Waɗannan Maganganu biyu suna bayyana abu ɗaya ne a hanyoyi biyu. Dukan maganan suna nufin Allah.
Anan "mu" da "namu" na nuna tare da Korantus.
Bulus ya yi maganan wahalhalun Almasihu kamar wani abu ne wanda za ta iya karu kuma a kidaya. AT: "Gama kamar yadda Almasihu ya sha wahala sosai domin mu"
Ma'anar da ke iya yuwa suna kamar haka 1) wato wahalan Bulus da Timoti sun sha domin sun yi wa'azin sako game da Almasihu ko kuwa 2) wahalan da Almasihu ya sha a madadin su.
Bulus ya yi magana game da ta'aziya kamar wani abu ne wanda zai iya girma.
A nan kalmanan "mu" na nufin Bulus da Timoti, amma ba yan Korantiyawa ba. Ana iya bayyana wannan haka. AT: "Amma in mutane sun wahalal da mu"
Ana iya bayyana wannan haka. AT: "in Allah ya ta'azantar da mu"
"Kuna samun ta'aziya yadda ya kamata"
Wannan za a iya bayanna shi a kalmomi kamar haka. AT: "muna so ku sani"
Bulus da Timoti suna nufin kujewa karma abu mai nauyi da sun dauka.
Bulus da Timoti suna misalin yadda suke ji da wanda an yi masa hukuncin mutuwa. AT: "mun ji kamar wanda aka yanke wa hukuncin kisa"
Kalmomin nan "sa begen mu" an cire su daga maganan. AT: "amma dai, mu sa begen mu ga Allah"
A nan, a ta da, wanin karin magana ne wanda ke nuna cewa wanda ya mutu ya dawo da rai. AT: "wanda ya sa matattu su rayu kuma"
Bulus ya kwatanta yadda ya fid da zuciyarsa saboda damuwar da yake fuskanta da mummunan hatsari na mutuwa ko kuwa hadari mai ban soro. AT: "fid da zuciya"
"shi zai cigaba da ceton da mu"
"Allah zai kubutar da mu daga hadari a sa'alin da, ku mutanen ikilisiyar da ke a Korantus kun kuma taimake mu"
Wannan ana iya bayayana shi karma haka. AT: "tagomashin alheri wanda Allay ya riga da ya ba mu"
Kalman nan ta "takama" da kuma "alfahari" anan an yi amfani ne da su don nufin yadda aka ji lailai an biya bukata da kuma murna domin wani abu.
Bulus yayi maganar alhalin laifi kamar Lamirin shi mutum ne wanda zai iya magana. AT: "mun sani tawurin lamirin mu"
A nan "jiki" na yin misalin dan Adam. AT: "ba mu jigina ga hikimar da adam ba, amma ga alherin Allah
Ana iya bayana wannan cikin kalmomi kamar haka. AT: "kun iya karanta da kuma fahimtar dukan abubuwan da muka rubuta muku"
Bulus ya bayyana sahilin tsammanin sa da muradin mai kyau domin ya zo ya ga masubi da ke a Korantus bayan wasikar sa ta fari.
Kalman nan "wannan" ta na nufin maganar da Bulus ya yi game the Korantiyawa
"kun iya amfana daga ziyarata sau biyu"
"taimaka mini a hanya ta zuwa Yahudiya"
Bulus yayi wannan tambaya domin ya nuna nauyin lafazi cewa yana tabbacin game da shirin ziyarsa zuwa Korantus. sammacin amsar tambayar itace a'a. AT: "dama ba na shakka" ko kuwa "ina da gabagadi cikin shiri na."
Bulus ya yi amfani da wannan tambaya ne domin ya nuna nauyin lafazin sa da cewa shirin sa domin ziyartan Korantiyawa sahili ce. AT: "Ban shirya abubuwa bisa ga ma'aunin ɗan adam ba...a lokaci guda"
Wannan na nufin Bulus bai ce wai zai ziyarci ko kuwa ba zai yi ziyara ba a lokaci guda. Kalmomin nan "i" da "a'a" an maimaita shi domin nuna nauyin lafazi. AT: "ban shirya abubuwa... domin in ce 'I, zan yi ziyara' da 'a'a, hakika ba zan yi ziyara ba' a lokaci guda!"
Yesu ya ce "I" game da alkawarin Allah, ma'ana kuwa itace tabbaci cewa duka gaskiya ce. AT: "Gama Dan Allah... bai ce "I" da "a'a" game da alkawarin Allah ba. Maimakon haka, shi ya kan ce "I" a ƙodayaushe.
Wannan suna ce mai mahimmanci na Yesu da ke bayana ɗangantakarsa da Allah.
Wannan na nufin Yesu shi ne tabbacin dukan alkawarai na Allah. AT: "dukan alkawarai na all ta na tabbaci cikin Yesu Almasihu"
Kalman nan "sa" na nufin Yesu Almasihu.
mana masu yiwuwa suna kamar haka 1) " Allah wanda ya tabbatar da ɗangantakar mu da juna domin muna cikin Almasihu" ko 2) "Allah wanda ya tabbatar da mu kuma da dangantakar ku da Almasihu."
mana masu yiwuwa suna kamar haka 1) "ya aike mu mu yi wa'azin bishara" ko 2) "ya zabe mu mu zama mutanen sa."
Bulus ya yi magana game da Allah ya nuna mu nasa ne kamar Allah ya sa alama a kan mu domin ya nuna alaman cewa mu nasa ne. AT: "she ya sa alamar shaidar ce nasa ne a kan mu" ko "ya nuna cewa mu nasa ne"
A nan Kalman nan "zukata" na nufin
An yi maganar Ruhun Kamar shi wani ne wanda bai isa cikakkiyar biyar rai madawwami ba.
Maganar nan "zama shaida" na nufin mutum na fadin abin da ya gani ko ji domin ya sasanta mahawara. AT: "Na roki Allah ya nuna cewa abin da nake fadi gaskiya ne"
"domin kada in kara sa wahalar da ku"
"muna aiki da ku domin may yiwuwa ku sami farinciki"
Kalman nan "tsaya" na iya nufin abun da ba ya canzawa. AT: "tsaya da karfi cikin bangaskiyar ku"
An rubuto zuwa ga Ikilisiyar Allah da ke a Koronti, da kuma dukan 'yan'uwa da ke yankin kasar Akaya.
Bulus da Timoti ne sun rubuto wannan wasika.
Bulus ya kwatanta Allah a matsayin Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uban dukan jinƙai, da kuma Allahn dukan ta'aziya.
Yana ta'azantar da mu a cikin dukan wahalarmu, domin mu iya ta'azantar da waɗanda ke cikin kowace wahala, da irin ta'aziyar da Allah ke ta'azantar da mu.
An murkushe su gaba ɗaya har fiye da karfin su. An yi masu hukuncin mutuwa.
Hukuncin kisa ya sa su kada su dogara ga kansu, amm sai dai ga Allah.
Bulus ya faɗa cewa ikilisiyar Korontiyawa za su iya taimakon su ta wurin addu'an.
Sun yi fahariya shaidar lamirinsu, wand suka tafiyar da rayuwarsu a duniya-kuma musamman tare da ikilisiyar Korontiya-tare da tsarkaka da aminci da ke zuwa daga Allah, ba kuwa bisa hikimar duniya ba, amma ta wurin alherin Allah.
Yana da gabagadi cewa a ranannan, shi da abokan aikinsa za su zama dalilin fahariyar masubi na Korontiya.
Ya yi shirin ziyartarsu sau biyu.
Ya ba da Ruhun a matsayin tabbacin abinda zai bamu daga baya.
Bai zo Koronti ba domin ya kare su ne.
Bulus ya ce ba suna kokarin su sarrafa yadda bangaskiyar su za ta zama ba ne, amma suna aiki tare da ikilisiyar Korontiya domin farincikinsu.
1 Don haka na yanke shawara daga bangarena, ba zan sake zuwa wurin ku cikin yanayi mai tsanani ba. 2 Idan na bata maku rai, wa zai karfafa ni, in ba shi wanda na bata wa rai ba? 3 Na rubuto maku kamar yadda na yi domin idan na zo gareku kada in sami bacin rai a wurin wadanda ya kamata su faranta mani rai. Ina da gabagadi game da dukan ku, cewa farincikin da nake da shi, shine kuke da shi duka. 4 Domin kuwa na rubuto maku cikin kunci da bacin rai da kuma hawaye mai yawa. Ba zan so in sake bata maku rai ba. Maimakon haka, na so ku san zurfin kaunar da nake da ita domin ku. 5 Idan wani ya kawo sanadin bacin rai, ba ni kadai ya kawo wa wannan abin ba, amma ta wani fannin- domin kada a tsananta- har a gare ku duka. 6 Hukuncin nan da galibinku kuka yi wa mutumin nan ya isa. 7 Don haka, yanzu a maimakon hukunci, ku gafarta masa, ku kuma ta'azantar da shi. Ku yi haka domin kada bakinciki mai yawa ya danne shi. 8 Don haka ina karfafa ku da ku nuna irin kaunar da kuke yi masa a fili. 9 Wannan shine dalilin da ya sa na rubuto maku, domin in gwada ku, ko kuna biyayya cikin komai. 10 Duk mutumin da kuka gafarta wa, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta-idan na gafarta wani abu-an gafarta ne domin ku a gaban Almasihu. 11 Wannan ya zama haka ne domin kada shaidan ya yaudare mu. Don ba mu jahilci irin makircinsa ba. 12 Na samu budaddiyar kofa daga wurin Ubangiji yayin da nazo birnin Tarwasa, in yi wa'azin bisharar Almasihu a can. 13 Duk da haka, raina bai kwanta ba, domin ban ga dan'uwana Titus a can ba. Sai na bar su a can, na dawo Makidoniya. 14 Amma godiya ta tabbata ga Allah, wanda cikin Almasihu yake kai mu ga nasara a koyaushe. Ta wurin mu ya baza kamshi mai dadi na saninsa ko'ina. 15 Gama mu, kamshi ne mai dadi na Almasihu ga Allah, a tsakanin wadanda ake ceton su, da kuma tsakanin wadanda suke hallaka. 16 Ga mutanen da suke hallaka, kamshi ne daga mutuwa zuwa mutuwa. Ga wadanda suke samun ceto kuma kamshi ne daga rai zuwa rai. Wanene ya cancanci wadannan abubuwan? 17 Gama mu ba kamar sauran mutane muke ba, masu sayar da maganar Allah domin samun riba. Maimakon haka, da tsarkakkiyar manufa, muke magana cikin Almasihu, kamar yadda Allah ya aiko mu, a gaban Allah.
Saboda matukar ƙaunarsa gare su, Bulus ya bayyana cewa tsawtawar sa a wasikarsa ta farko zuwa gare su (tsawtarwa domin yaddarsu da zunubin fasikanci) ta sa shi bai ji dadi ba kamar yadda ta sa mutanen ikilisiyar da take a Korantus da kuma mutum mai rashin adalci
" Na yi shirin"
cikin yanayi da za ta sa ku cikin saka mai wuya"
Bulus ya yin amfani da tambaya da bata bukatan amsa domin ya dada nu muhimincin maganarsa cewa ko shi ko su, ba wanda zai karu in zuwan sa wurinsu zai kawo musu bacin rai. AT: "Idan na bata maku rai, ku waɗanda ke karfafani wa zai karfafa ni, in ba shi wanda ya samu bacin rai daga ni ba"
wanan ana iya bayyana ta cikin kalmomi masu kuzari. AT: "she wanda ya samu bacin rai daga ni"
wannan na nufin wata wasika da Bulus ya rubuto zuwa ga krista da suke a Korantus wanda ba ta nan a yau. AT: " Na rubuto kamar yadda na yi a wasikar wanda na rigaya na rubuto"
Bulu na magana ne game da wata irin halin masubi da suke a Korantus wanda za ta sa shi jin zafi cikin zuciyarsa. Wannan ana iya sa shi cikin magana mai kuzari. AT: " waɗanda ya kamata su faranta mini rai watakila kada su sani bacin rai"
"abin da ke faranta mini rai shi ne abida ke faranta muku rai kuma"
A nan Kalman na "kunci" na nufin jin zafi cikin zuci.
A nan Kalman nan "zuciya" na nufin inda zafin rai take. AT: "da matsanancin bakin ciki"
"da kuka sosai"
"zuwa ga wani iyaka"
Wannan na iya nufin 1) Bana so in fadi shi cikin Tsananci sosai" ko 2) "Bana son in zuguiguita."
Wannan ana iya bayyana ta kalmomi masu kuzari. Kalman nan "hukunci" na iya juya shi ta wurin amfani da aikatau. AT: " Yadda yawanci su suka hukunta mutumin ya isa."
"ya isa"
Wannan na nufin jin zafin zuci mai yawa bai sa shi bakin ciki sosai ba. Wannan ana iya bayyana ta kalmomi masu kuzari. AT: "bakin ciki mai yawa bai danne shi ba."
Wannan na nufin cewa su tabbatar the ƙaunar su ga wannan mutum a gaban dukan masubi.
Wannan na iya nufin 1) "kuna biyayya ga Ubangiji cikin dukan kome" ko 2) kuna biyayya cikin dukan kome da na koyas da ku"
wannan ana iya bayyana ta cikin kalma mai kuzari. AT: "Na gafarce shi domin ku"
Wannan na iya nufin 1) "gafartawa saboda ɗaunar da nake yi muku" ko 2) "gafartawa
Bulus yayi amfani da waɗanan kalmomi domin ya dada bayyan maganar. AT: "Don mun san makircinsa sarai"
Bulus ya yi maganar zarafin da ya samu domin yin wa'azin bishara kamar wat kofa ce da aka barshi ya shiga. wannan ana iya bayyana shi cikin kalmomi masu kuzari. AT: Ubangiji ya bude mini kofa ... in yi wa'azin bishara" ko "Ubangiji ya bani zarafi ... in yi wa'azin bishara"
"Zuciyata ta birkice" ko " Na damu"
Bulus ya yi magana game Titus da nufin shi dan'uwans ne cikin ruhaniya.
"Sai na bar mutanen Tarwasa"
Bulus ya yi magana game da Allah kamar shi wani shugaba mai nasara wanda ke shugabantar farati da shi da kuma abokan aikinsa kamar wanda suke farati. Wannan na iya nufin 1) Allah, wanda cikin Almasihu kan sa muyi tarayya cikin nasararsa a ƙoyaushe" ko 2)"Allah, wanda cikin Almasihu a ƙoyaushe ya na shugabantarmu cikin nasara kamar waɗanda tawurinsu ya sami nasara"
Bulus ya yi maganar sanin Almasihu kamar wata kamshi mai dadi. AT: "Ya sa sanin Almasihu ta bazu ga kowan da ya ji su, sai ka ce wata kamshin turare da ke bazuwa ga duk wanda ke kusa"
"ya baza... ko'ina muka je"
Bulus ya yi maganar aikinsa kamar wata hadayar ƙonawa wanda wani ya miƙa ga Allah.
Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) "kamshi mai dadi wanda ita ce sanin Almasihu" ko 2) "kamshi mai dadi wanda Almasihu ya mika."
Ana iya bayyana wannan cikin kalmomi da ke nuna kuzari. AT: "waɗanda Allah ya ceta"
"sanin Almasihu kamshi ce." Wannan ya komar damu zuwa [2 Korantiyawa 2:14]
Ma'an mai yiwuwa suna kamar haka 1) wato kalman nan "mutuwa" an sake maimaita ta domin nauyi lafazi, kuma maganar tana nufin "kamshi mai sa mutuwa" ko 2) "kamshin mutuwa da ke sa mutane su mutu"
Wannan ana iya bayyana ta cikin kalmomi da ke nuna kuzari. AT: "Wanɗanda Allah ke ceta"
Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) wato kalman nan "rai" an sake maimaita ta domin nauyi lafazi, kuma maganar tana nufin "kamshi mai bada rai" ko 2) "kamshin rai mai ba da rai ga mutane"
Bulus ya yi amfani da wannan tambaya domin ya dada nayin maganarsa cewa babu wanda cancanci yin aikin da Allah ya kira su. AT: "Babu wanda ya cancanci waɗannan abubuwa"
"Kalma" anan kalma ce mai nuna "sako". AT: "masu sayar da sakon Allah"
"manufa mai tsarki"
"muke magana kamar mutanen da ke tare da Almasihu" ko "muke magana da ikon Almasihu"
Wannan ana iya bayyana ta cikin kalmomi da ke nu kuzari. AT: "kamar mutanen da Allah ya aiko"
Bulus da abokanayen aikinsa sun yi wa'azin bishara da sanin cewa Allah na kallon sun. AT: "mun yi magana a gaban Allah"
Bulus ya na gudan zuwa ikilisiyar Korontiya a cikin yanayi mai tsanani.
Ya rubuto kamar yadda ya yi domin idan ya zo garesu kada ya sami bacin rai a wurin waɗanda ya kamata su faranta masa rai.
Ya rubuto masu domin ya so su san zurfin ƙaunar da yake da ita domin su.
Ya na cikin ƙunci da bacin rai da kuma hawaye mai yawa.
Bulus ya ce su gafarta masa, su kuma ta'azantar da shi.
An yi haka ne domin kada bakinciki mai yawa ya danne wanda sun hukunta.
Bulus ya rubuto masu domin ya gwada su, ko suna biyayya cikin komai.
Wannan ya zama haka ne domin kada shaidan ya yauɗare su.
Bai sami salama a zuciyarsa ba domin bai ga ɗan'uwansa Titus a Tarwasa ba.
Ta wurin Bulus da abokan aikinsa Allah ya baza kamshi mai daɗi na sanin Almasihu a ko'ina.
Bulus da abokan aikinsa sun banbanta domin sun bada tsarkakkiyar manufa, suke magana cikin Almasihu, kamar yadda Allah ya aiko su, a gaban Allah.
1 Muna fara sake yabon kanmu ne? Ba mu bukatar wasikun shaida daga gare ku ko zuwa gare ku, kamar wadansu mutane, ko ba haka ba? 2 Ku da kanku kune wasikar shaidarmu, wadda aka rubuta a zukatanmu, wadda Kuma dukan mutane suka sani suke kuma karantawa. 3 Kuma kun nuna ku wasika ne daga Almasihu, wadda muka isar. Ba da tawada aka rubuta ta ba amma da Ruhun Allah mai rai. Ba bisa allunan duwatsu aka rubuta ta ba, amma bisa allunan zukatan mutane. 4 Gama wannan ne gabagadin da muke da shi cikin Allah ta wurin Almasihu. 5 Ba mu da wata gwanintar kanmu da za mu yi takamar wani abu ya zo daga gare mu. Maimakon haka, gwanintar mu daga Allah take. 6 Allah ne ya maishe mu kwararrun bayi na sabon alkawari. Wannan alkawari ne ba na rubutu ba amma na Ruhu. Gama rubutu kisa yake yi, amma Ruhu rai yake bayarwa. 7 To hidimar da ta haifar da mutuwa- wadda aka rubuta bisa duwatsu- ta zo cikin irin wannan daukaka da har Israila ba su iya kallon fuskar Musa kai tsaye ba. Wannan kuwa saboda daukakar da ke fuskarsa ne, daukaka mai shudewa. 8 Ina misalin girman daukakar hidimar da Ruhu ke yi? 9 Gama idan hidimar kayarwa tana da daukaka, ina misalin yalwatar daukaka da hidimar adalchi za ta yi! 10 Babu shakka, abin da aka maishe shi mai daukaka a da, ba ya da sauran daukaka a wannan fanni, saboda irin daukakar da ta zarce shi. 11 To idan har mai shudewar nan ya na da daukaka, ina misalin daukakar da abu na dindindin zai samu! 12 Dashike muna da wannan tabbaci, muna da gabagadi sosai. 13 Ba kamar Musa muke ba wanda ya sa mayafi ya rufe fuskarsa, ta yadda mutanen Isra'ila basu iya kallon karshen daukaka mai shudewa ba kai tsaye. 14 Amma tunaninsu ya zama a rufe. Har yau kuwa mayafin na nan sa'adda ake karanta tsohon alkawari. Ba a bude shi ba, saboda a cikin Almasihu ne kadai ake kawar da shi. 15 Amma har yau, duk lokacin da ake karanta littafin Musa, akwai mayafi shimfide a zukatansu. 16 Amma sa'adda mutum ya juyo wurin Ubangiji, an kawar da mayafin. 17 To Ubangiji shine Ruhun. Inda Ruhun Ubangiji yake, akwai 'yanci. 18 Dukan mu yanzu, da fuskoki marasa mayafi, muna ganin daukakar Ubangiji. Muna samun sakewa zuwa cikin irin wannan daukaka, daga wannan mataki na daukaka zuwa wani matakin, kamar dai daga wurin Ubangiji, wanda shine Ruhun.
Bulus ya tunashe da cewa baya fahariya a sa'ada ya yi musu magana game da abin da ya yi tawurin Almasihu.
Bulus ya yi amfani da wannan tambayar domin ya nuna nauyin maganarsa cewa ba su fahariya da kan su. AT: "Mu ba fara yabon kan mu muke yi kuma ba"
Bulus ya fadi wannan maganar cewa Korantiyawa sun riga sun san game da halin kirki na Bulus da Timoti. Tambayar ta nema amsa. AT: "Haƙika ba mu bukatar wasikun shaida daga gare ku ko zuwa gare ku, kamar waɗansu mutane"
Wannan wasika ce da mutum ke rubutawa domin ya gabart da kuma bada izinin su ga wani dabam.
Bulus ya yi magana game da Korantiyawa kamar su wasikar shaida. da shike sun zama masubi wannan ta zama abin da ta inganta aikin bisharan Bulus ga wanɗansu. AT: "Ku da kanku kuna kamar wasikar shaidarmu"
A nan Kalman nan "zukata" na nufin tunanin su da kuma yadda suke ji. Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1)Bulus da abokan aikinsa sun tabbata cewa Korantiyawa wasikar su ne ta shaida ko 2) Bulus da abokan aikinsa suna lura da Korantiyawa sosai.
Wannan ana iya bayyana shi cikin kalmomi masu kuzari. AT: "cewa kowa na iya sani da karantawa"
Bulus ya bayyana cewa Almasihu ne wanda ya rubuta wannan wasika. AT: "ku wasika ce wanda Almasihu ya rubuta"
"muka kawo"
Bulus ya bayyana cewa Korantiyawa suna kamar wasikun ruhaniya ba kamar wasika bace da mutane ke rubutawa da abubuwan rubutu na jiki.
Wannan ana iya bayyana ta cikin kalmomi masu kuzari. AT: "Ba wasika bace da mutane suka rubuta da tawada amma wasika wanda Ruhun Allah mai rai ya rubuto"
Wannan ana iya bayyana ta cikin kalmomi masu kuzari. AT: "Ba wasika bace da mutane suka zana a allun duwasuba amma wasika da Ruhun Allah mai rai ya rubuto a allunan zukatan mutane"
Bulus ya yi maganar zukatan su kamar wata dutse ko kuwa yumbu da mutane ke iya rubuta wasiku.
Wannan na nufin abida Bulus ya fada yanzun nan. Samin gabagadin sa ta zo ne daga sanin cewa Korantiyawa sune karfin aikinsa gaban Allah.
"cancanta a kanmu" ko "mu kanmu mun isa"
Anan kalman nan "wani abu" na nufin wani abu game da aikin manzoncin Bulus. AT: "takamar cewa wani abu da mu ka yi domin aikin ta zone daga kokarin mu"
"Allah ne ya bamu iyawa"
A nan kalman nan "wasika" na da ma'anan haruffa ta kuma nufin kalmomi da mutane ke rubutawa. Wannan magana ta na nufin dokokin Tsohon Alkawari. AT: "alkawari wanda ba bisa dokokin da mutane suka rubuta ba"
Ruhu Mai Tsarki she ne wanda ya kafa alkawarin Allah da mutane. AT: "amma alkawarin bisa ga abin da Ruhun ya yi ne"
Bulus ya yi maganar dokokin Tsohon Alkawari kamar wani mutum wanda ke kisa. Bin dokokin na kai ga mutuwa cikin ruhu. AT: "rubutaciyar dokokin tana kai ga mutuwa"
ƙodashiƙe doka na kai ga mutuwa, Bulus ya nanata cewa har yanzu ta na fifiko.
"the ministry of death." Wannan na nufin dokokin Tsohon Alkawarin wanda Allah ya bayar tawurin Musa. AT: "aikin da ke sa mutuwa domin tana nan bisa ga dokoki"
"goge dutse zuwa ga haraffai." Wannan ana iya bayyana ta cikin kalmomi masu nuna kuzari. AT: "cewa Allah ya goge dutse zuwa ga haraffi"
"cikin ɗaukaka mai yawa"
"Ba su iya gani ba saboda"
Bulus yayi wannan tambayar domin ya nuna nauyi maganarsa cewa "hidimar da Ruhu ya yi" dole ne ta fi ɗaukaka fiye da "hidimar da an haifa" domin ta kan kai ga rai. AT: "Saboda haka hidimar da Ruhun ke yi dole ne ta fi daukaka"
"aikin Ruhun." Wannan na nufin sabon alkawari wanda Bulus ma'aikaci ne. AT: "aikin da ke bada rai domin ta na bisa Ruhun ne"
"aikin kayarwa." Wannan na nufin doka da ke Tsohon Alkawari. AT: "aikin da ke kayar da mutane domin ta bisa dokan"
A nan Kalman nan "ta yaya" tana nuna alamar maganar kamar maganar motsin rai ba tambaya ba. AT: "sa'an nan hidimar adalci dole ta yelwata fiye da ɗaukaka!"
Bulus ya yi maganar "hidimar adalci" kamar wani abu ne da za ta iya haifuwa ko ta yaɗu. Ya na nufin "hidimar adalci" ya fi ɗaukaka sosai fiye da doka wanda tana da ɗaukaka ita ma.
"aikin adalci." Wannan na nufin sabon Alkawari ce wanda Bulus ma'aikaci ne. AT: "aikin da ke sa mutane su zama da adalci domin bisa ga Ruhun ta ke.
Dokokin Tsohon Alkawarin bata kuma da ɗaukaka in an kwatanta ta da Sabon Alkawari wanda tana da ɗaukaka fiye.
wannan ana iya bayyana ta cikin kalmomi masu nuna kuzari. AT "alkawarin wanda Allah ya maishe ta mai ɗaukaka a da"
"cikin wannan hanya"
Wannan na nufin "hidimar kayeswa," wanda Bulus ya yi maganar ta kamar wani abu mai iya ɓacewa. AT: "abin da ke zuwa ga rashin amfani"
Wannan na nufin abin da Bulus ya gama fada. Begen sa ta zo daga sanin cewa sabon alkawari ta zo ne da madawamiyar daukaka.
"wannan gabagadi"
Wannan na nufin ɗaukakar da ta hakaka fuskar Musa. AT: "ɗaukakar da ke fuskar Musa a sa'alin da take shuɗewa gaba ɗayan ta.
"Amma sun taurara zukatan su." Bulus ya yi magana game da zukatan Israila kamar wani abu ne da zai iya rufuwa ko kuwa tauri. Wannan na nufin ba su iya fahimtar abin da suka gani ba. AT: "Amma Isa'ila ba su iya fahimtar abin da suka gani ba"
Waɗannan na maganganu na nufin lokacin da Bulus ke rubutun sa zuwa ga Korantiyawa.
kamar yadda Israila basu iya ganin fuskar Musa ba domin ya rufe fuskar sa da mayafi, akwai wani mayafi na ruhu da ke hana mutane fahimtar tsohon alkawarin a sa'ada suka karanta.
"a sa'ada sun ji wani na karanta tsohon alkawari"
A nan bayyanuwan kalman nan "ita" na nufin "mayafin." Wannan ana iya bayyana ta cikin kalmomi ma su nuna kuzari. AT: "Babu wanda ke cire mayafin domin tawurin Almasihu ne kadai Allah ke cire ta"
A nan kalman nan "Musa" na nufin dokokin Tsohon Alkawari. Wannan ana iya bayyana ta cikin Kalmomi masu nuna kuzari. AT: duk sa'ada wani ya karanta dokokin Musa"
A nan Kalman nan "Zukata" na misalin tunanin mutane, da kuma an yi maganar rashin fahimtar tsohon Alkawarin ga mutanen kamar wata mayafine da ta rufe zukatan su kamar yadda mayafi zai rufe idan su. AT: "ba su iya fahimtar abin da suka ji ba"
A nan "juyo wurin" na da ma'anan biyayya ga wani. AT: " sa'ada mutun ya fara sujada ga Ubangiji" ko "sa'ada mutum ya fara amince da Ubangiji"
Allah ya ba su iyawa don su fahimta. Wannan maganan ana iya bayyana ta cikin kalmomi masu nuna kuzari. AT: "Allah ya cire mayafin" ko "Allah ya basu iyawa don su fahimta"
A nan kalman nan "mu" na nufin dukan masubi har da Bulus da kuma Korantiyawa.
Ba kamar Israila ba wanɗanda ba su iya ganin ɗaukakař Allah kamar yadda ta bayyana a fuskar Musa ba domin ya rufe ta da mayafi, babu wani abu da zai hana masubi ganin ɗaukakar Allah da kuma fahimtar ta.
Ruhun na sake masubi su zama da ɗaukaka kamar shi. Wannan ana iya bayyana ta cikin kalmomi masu nuna kuari. AT: "Ubangiji na sake mu cikin ɗaukaka kamar sa"
"daga wata yawan ɗaukaka zuwa ga wata yawan ɗaukaka." Wannan na nufin Ruhun na cingaba da kara ɗaukakan masubi.
"kamar dai wannan ta zo daga wurin Ubangiji"
Masubi a Korontiya sune wasikar shaidarsu, wadda Kuma dukan mutane suka sani suke kuma karantawa.
Gabagadinsu ba ya bisa gwanintarsu amma a mayalwaci da Allah ya tanada masu.
Sabon alkawarin na bisa Ruhun da ke ba da rai, ba rubutu dake kisa ba.
Basu iya kallon shi a faska ba saboda ɗaukakar da ke fuskarsa, ɗaukaka mai shudewa.
Hidimar adalchi za ta yawaita a ɗaukaka.
Sai Isra'ila ta juyo wurin Ubangiji, sai hankalinsu ya buɗe kuma a kawar da mayafin.
Damuwarsu shi ne hankalinsu na rufe kuma akwai mayafi shimfiɗeɗɗe a zukatansu.
Inda Ruhun Ubangiji yake, akwai 'yanci.
Suna samun sakewa zuwa cikin irin wannan ɗaukaka, daga wannan mataki na ɗaukaka zuwa wani matakin.
1 Don haka, domin muna da wannan hidima, da kuma yadda muka karbi jinkai, ba mu karaya ba. 2 Maimakon haka, sai muka rabu da dukan hanyoyin da ke na kunya, kuma na boye. Ba mu rayuwar makirci, kuma bamu yiwa maganar Allah rikon sakaci. Ta wurin gabatar da gaskiya, muna mika kanmu ga lamirin kowa a gaban Allah. 3 Amma, idan bishararmu a rufe take, tana rufe ne ga wadanda ke hallaka. 4 A al'amarinsu, allahn wannan duniya ya makantar da zukatansu marasa bada gaskiya. A sakamakon haka, ba su iya ganin hasken bisharar daukakar Almasihu ba, wanda shine surar Allah. 5 Gama ba mu yin shelar kanmu, amma Almasihu Yesu a matsayin Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu. 6 Gama Allah shine wanda ya ce, "Haske zai haskaka daga cikin duhu." Ya haskaka cikin zukatanmu don ya bada hasken sanin daukakar Allah a gaban Yesu Almasihu. 7 Amma muna da wannan dukiya a randunan yunbu, yadda zai zama a bayyane cewa mafi girman iko na Allah ne ba namu ba. 8 Muna shan tsanani ta kowace hanya, ba a ci mu dungum ba. Mun rikice amma ba mu karaya ba, an tsananta mana amma ba a watsar da mu ba. 9 Ana tsananta mana amma ba a yashe mu ba. Aka doddoke mu amma ba mu lalace ba. 10 Mu dai a kullayaumin muna dauke da mutuwar Yesu a jikkunanmu, saboda a bayyana rayuwar Yesu a jikkunanmu kuma. 11 Mu da muke a raye kuwa a kulluyaumin ana mika mu ga mutuwa saboda Yesu, domin rayuwar Yesu ta zama a bayyane a jikunanmu na mutuntaka. 12 Saboda haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, amma rai na aiki a cikinku. 13 Amma dai muna da wannan Ruhu na bangaskiya kammar yadda aka rubuta: "Na gaskata, saboda haka na furta." Mu ma mun gaskata, haka kuwa muke fada. 14 Mun sani cewa wanda ya tada Ubangiji Yesu daga matattu za ya sake tada mu tare da Yesu. Mun san cewa zai gabatar da mu tare da ku a gabansa. 15 Dukan abubuwa sabili da ku suke domin, yayin da aka baza alheri ga mutane dayawa, bada godiya ta karu ga daukakar Allah. 16 Don haka ba mu karaya ba. Kodashike daga waje muna lalacewa, daga ciki ana sabunta mu kulluyaumin. 17 Domin wannan 'yar wahala ta dan lokaci tana shirya mu zuwa ga nauyin madauwamiyar daukaka wadda ta wuce gaban aunawa. 18 Domin ba muna kallon abubuwan da ake gani bane, amma abubuwan da ba a gani. Abubuwan da muke iya gani ba masu dawwama ba ne, amma abubuwan da ba a gani madawwama ne.
Bulus ya rubuta gaskiyar hidimar sa ta wurin wa'azin Almasihu ba ya kuma yabon kansa. Ya bayyana mutuwa da rayuwar Yesu ta yadda ya yi rayuwa saboda rai ta yi aiki cikin masubi da ke Korantus
Kalman nan "mu" na nufin Bulus da abokan aikin sa, amma banda Korantiyawa.
Wannan maganan ta bayyana yadda Bulus da abokan aikinsa sun "sami wannan hidimar." Kyauta ce wanda Allah ya basu tawurin jinkansa. AT: "domin Allah ya nuna jinkansa gare mu" (Dubi:")
Wannan na nufin Bulus da abokan aikinsa sun ki su yi abin "kunya da kuma abin da ke boye). Bai nuna cewa sun yi waɗannan abubuwa a da ba.
Kalman nan "boye" ta bayyana abubuwan da mutane ke yi a boye. Abin kunya ya kamata ta sa su su ji kunya. AT: "abubuwan da mutane ke yi a boye domin ta na sa kunya"
"zaman yaudara"
"Kalman Allah" a nan ta nufin wata kalma da za a yi amfani da sakon daga Allah a maɗadin ta. Wannan maganan na amfani da abu biyu
Ma'anan wannan shi ne sun tanada shaida ga kowane mutum mai jin su domin ya zaba ko sun yi daidai ko kuwa ba daidai ba.
Wannan na nufin a gaban Allah. Fahimtar Allah da kuma amincewar sa game da gaskiyar Bulus na nufin Allah na iya ganin su. AT: "gaban Allah" ko "da Allah wanda shi ne shaida"
Wannan na mai da mu baya zuwa [2 Korantiyawa 3:14-16]
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "idan mayafi ta rufe bisharar mu, wannan mayafin ta rufe ta"
"bishara da muke wa'azin"
Bulus ya maganar zukantans kamar suna da idanu da kuma rashin iya fahimtarsu kamar zukantansu bata iya gani ba. AT: "allahn wannan duniya ya hana marasa bada gaskiya fahimta"
"allahn da ke mulkin wannan duniyan." Wannan na nufin Shaidan.
Israila ba su iya ganin ɗaukakar Allah da ta haskaka fuskan Musa ba saboda ya rufe she da mayafi. (Dubi: 2 Korantiyawa 3:13), haka nan marasa bada gaskiya ba su iya ganin ɗaukakan Almasihu da ke haskaka wa cikin bishara ba. Wannan na nufin ba us iya fahimtar "bisharar ɗaukakan Almasihu ba"
"hasken da ke zuwa daga bisharan"
"bishara game da ɗaukakan Almasihu"
za ku iya sa kalma ta aikatau a waɗannan maganganun. AT: "amma mu kam shelar Almasihu Yesu a matsayin Ubangiji muke yi da kuma shelar kan mu a matsayin bayin ku"
"saboda Yesu"
Da wannan jumlar, Bulus na nufin Allah mahalincin haske kamar yadda aka bayyana cikin littafin Farawa.
A nan kalman nan "haske" na nufin iya fahimta. Kamar yadda Allah ya halici haske, haka nan ya halici masubi da fahimta. AT: " Ya riga ya nuna ... don mu iya fahimtar ɗaukakar Allah"
A nan kalman nan "zukata" na nufin zuciya da tunani. AT: "cikin zuciyar mu"
"hasken itace sanin ɗaukakar Allah"
"ɗaukakar Allah a fuskan Yesu Almasihu." Kamar yadda daukakar Allah ta ke a fuskar Musa (Dubi: 2 Korantiyawa 3:7), haka nan take haskakawa a fuskar Yesu. Ma'anar wannan kuwa ita ce a sa'ada Bulus na wa'azin bishara, mutane kuwa sun iya gani da kuma fahimtar sakon game da ɗaukakar Allah.
A nan kalmar nan "mu" na nufin Bulus da abokan aikinsa badan Korantiyawa.
Bulus ya yi magana game da bishara kamar wata dukiya, jikin mu kuma kamar randuna da aka yi da yumbu da zata iya fashewa. Nauyi wannan itace suna da daraja kadan ne in an kwatanta da darajar bishara da ka yi wa'azin ta.
"yadda zai zama a bayyane ga mutane" ko "don mutane su sani ba shakka"
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "Mutane sun wahala da mu ta kowace hanya"
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "Mutane na tsananta man amma Allah bai yashe mu ba"
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "Mutane sun doddoke mu amma ba su hallaƙa mu ba"
"Aka ji mana mumunar ciwo"
Bulus ya yi maganar wahalar sa kamar ya taba jin yadda mutuwan Yesu ta ke. AT: "Kullum muna cikin haɗarin mutuwa yadda Yesu ya mutu" ko "kullayaumi muna shan wahala a wani yanayi da mu kan ji kamar mutuwar Yesu"
Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) "jikunan mu zata sake rayuwa domin Yesu na raye" ko 2) "rayuwar ruhu da Yesu ya bayar ta kuma nuna cikin jikinmu."
Ɗaukar mutuwan Yesu tana misalin zama cikin haɗarin mutuwa saboda biyayya ga Yesu. AT: "Ga mu da muke raye, Allah ya kan bishe mu mu fuskanci mutuwa domin muna tare da Yesu" ko "Mutane a kullayaumi kan sa mu cikin haɗarin mutuwa mu da muke raye saboda muna tare da Yesu"
Allah na son rayuwar Yesu ta bayyana cikin mu. Ma'ana mai yiwuwa suna kamar haka 1) "jikunan mu zata rayu kuma domin Yesu yana raye" ko 2) "rayuwar ruhu da Yesu ya bayar ta bayyana cikin jikunan mu." (Dubi yadda kun juya wannan magana cikin 2 Korantiyawa 4:10.
Bulus ya yi maganar mutuwa da rai kamar wani mutum ne da zai iya aiki. Wannan na nufin suna cikin haɗarin mutuwar jiki saboda Korantiyawa su iya samun rai ta ruhaniya.
"hali ɗaya ta bangaskiya." Anan Kalman nan "ruhu" na nufin halin mutum da kuma hali.
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "shi wanda ya rubuta waɗannan kalmomi"
Wannan nasi ce daga Zabura.
A nan tada karin magana ce na sa wani wanda ya mutu ya tashi da rai kuma. AT: "cewa shi wanda ya sa Ubangiji Yesu ya rayu kuma zai" ko " Allah wanda ya tada Ubangiji Yesu zai"
A nan kalman nan "dukan abubuwa" na nufin dukan wahalar da Bulus ya yi misalin su a ayoyi kafin wadannan.
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "sa'ada Allah ya yaɗa alherinsa ga mutane masu yawa"
Bulus ya yi maganar bada godiya kamar kamar wani abu ne da zata iya karuwa da kanta. AT: "mutane dayawa su mika godiya"
Ana iya bayyana wannan kamar tabbaci. AT: "Don muna da gabagadi"
Wannan na nufin jikunan su mai ruɓe wa da kuma mutuwa. AT: "jikunan mu tana kara zama mara karfi tana kuma mutuwa"
Wannan na nufin daga ciki rayuwarsu ta ruhaniya na samun karfi. AT: "ruhaniyan mu tana samun karfin kulluyaumi"
Bulus ya yi maganar wahalarsa da kuma ɗaukaka da Allah zai ba shi kamar waɗansu abubuwa da za a iya gwada nauyin ta. Daukakan ta fi wahalan sosai.
Nauyin ɗaukakar da Bulus zai ji ba za a iya aunawa ba. AT: "wanda ba mai iya aunawa"
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "abubuwan da muna iya gani...abubuwan da ba mu iya gani"
Za ku iya sa aikatau a wannan maganar. AT "amma muna duban abubuwan da ba a gani"
Basu karaya ba domin suna da wannan hidima da kuma yadda suka karbi jinkai.
Sun musanci hanyoyin da ke na kunya da kuma na ɓoye. Ba su yi rayuwar makirci ba, kuma basu yi wa maganar Allah rikon sakaci ba.
Sun yi haka ta wurin gabatar da gaskiya.
Tana rufe ne ga waɗanda ke hallaka.
Tana rufe saboda allahn wannan duniya ya makantar da zukatansu marasa bada gaskiya don ba su iya ganin hasken bisharan.
Sun yi shelar Almasihu Yesu a matsayin Ubangiji, su kuma bayin ikilisiyar Korontiyawa sabili da Yesu.
7Amma muna da wannan dukiya a randunan yunbu, yadda zai zama a bayyane cewa mafi girman iko na Allah ne ba namu ba.Suna da wannan dukiya a randunan yunbu domin zai zama a bayyane cewa mafi girman iko na Allah ne ba nasu ba.
Sun ɗauke mutuwar Yesu a jikkunarsu domin rayuwar Yesu ya bayyana a jikkunarsu.
Za a kawo Bulus da abokan aikinsa da kuma masubi na Korontiyawa ga wanda ya tada Ubangiji Yesu daga matattu.
Yayin da aka baza alheri ga mutane dayawa, godiya ta karu ga ɗaukakar Allah.
Basu karaya ba domin daga ciki ana sabunta su kulluyaumin. Kuma domin wannan 'yar wahala ta dan loƙaci tana shirya su zuwa ga nauyin madauwamiyar ɗaukaka wadda ta wuce gaban aunawa. A karshe, suna ganin abubuwan da ba a gani madawwame.
Suna da dalilin karaya domin daga waje suna lalacewa.
1 Mun san cewa idan wannan gidan da muke zaune a ciki ya rushe, muna da wani ginin daga wurin Allah. Gida ne wanda ba hannuwan mutane suka gina ba, amma madawwamin gida ne a cikin sama. 2 Domin a cikin wannan jiki muna gurnani, muna jira a suturta mu da wurin zaman mu na samaniya. 3 Muna jiran wannan ne domin ta wurin suturtar da mu ba za a same mu tsirara ba. 4 Gama babu shakka yayinda muke cikin wannan alfarwa, muna gurnani, muna nawaita. Ba mu so muyi zaman hutanci. Maimakon haka, muna so a suturtar da mu, domin rai ya hadiye abu mai mutuwa. 5 Wanda kuwa yake shirya mu domin ainihin wannan abu Allah ne, wanda ya ba mu Ruhu a matsayin alkawarin abinda ke zuwa. 6 Domin wannan mu zama da gabagadi koyaushe. Mu lura da cewa yayinda muka shagala cikin jiki, muna nesa da Ubangiji. 7 Gama bisa ga bangaskiya muke tafiya, ba bisa ga ganin ido ba. 8 Don haka muna da gabagadi. Mun gwammace mu rabu da jiki domin mu zauna tare da Ubangiji. 9 Sai muka maishe shi burinmu, ko muna cikin jiki ko nesa, mu gamshe shi. 10 Domin tilas dukanmu mu hallara a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, saboda kowa ya karbi sakamakon abubuwan da yayi cikin jiki, ko masu kyau ne ko marasa kyau. 11 Don haka, domin mun san tsoron Ubangiji, muna rinjayar mutane. Allah na ganin yadda muke a fili. Ina fatan hakan a fili take ga lamirinku. 12 Ba muna kokarin mu rinjaye ku domin ku kalle mu a matsayin amintattun mutane ba. Maimakon haka, muna ba ku dalilin yin takama da mu, domin ku sami amsar da za ku bada ga wadanda ke fahariya da kasancewarsu amma ba game da abinda ke zuciya ba. 13 Gama idan mun fita daga hankulanmu, saboda Allah ne. Kuma idan muna cikin hankalinmu, domin ku ne. 14 Domin kaunar Almasihu ta tilas ta mu, domin mun tabbatar da wannan: cewa mutum daya ya mutu domin kowa, kuma domin wannan duka sun mutu. 15 Kuma Almasihu ya mutu domin kowa, domin wadanda ke raye kada su sake rayuwa domin kansu. A maimakon haka, su yi rayuwa domin shi wanda ya mutu kuma aka tashe shi. 16 Domin wannan dalili, daga yanzu ba za mu kara shar'anta kowa bisa ga ma'aunin 'yan'adam ba, ko da yake a baya mun taba duban Almasihu a haka. Amma yanzu mun daina shar'anta kowa ta haka. 17 Saboda haka, duk wanda ke cikin Almasihu, sabon halitta ne. Tsofaffin al'amura sun shude. Duba, sun zama sababbi. 18 Dukan wadannan abubuwa daga Allah ne. Ya sulhunta mu da kansa ta wurin Almasihu, ya kuma ba mu hidimar sulhu. 19 Wato, cikin Almasihu, Allah na sulhunta duniya zuwa gare shi, ba tare da lissafin zunubansu a kansu ba. Yana damka mana sakon sulhu. 20 Don haka an zabe mu a matsayin wakilan Almasihu, kamar dai Allah na kira ga mutane ta wurin mu. Muna rokon ku, saboda Almasihu: "ku sulhuntu ga Allah!" 21 Shi ya maida Almasihu ya zama hadaya domin zunubinmu. Shine wanda bai taba zunubi ba. Ya yi haka ne don mu zama adalchin Allah a cikin sa.
Bulus a ciga da nuna bambanci tsakanin jikunan masubi ta wannan duniya da kuma na sama wanda Allah zai bayar.
A nan "gida ta duniya" zuwa wani lokaci ƙayadadde kwatanci ce ta jikin mutum. Anan dauwamammen "gini daga wurin Allah" kwatanci ce ta sabon jiki da Allah zai ba wa masu gaskantawa da shi bayan sun mutu.
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "in mutane sun rushe gidan mu ta duniya wanda muke ciki" ko "in mutane sun kashe jikunan mu"
Ma'ana "gidan" anan abu daya da "gini daga Allah." "Hannu" anan misali ce dake nufin gabadayan mutum. Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "Gida ce wanda ba mutane ne suka yi ba"
"wannan Bukka" na nufin abu daya ne da "gidan da muke ciki a wannan duniya." Kalman nan nishi wata ƙara ce wanda wani kan yi a sa'ada su na sa begen samun wani abu mai kyau.
Kalmomin nan "gidan mu na samaniya" na nufin abu daya ne da "gida ne daga Allah." Bulus yayi maganar sabon jiki da masubi za su samu bayan mutuwar su kamar wata gini da kuma sutura da mutum zai iya sa wa.
"ta wurin sa gidanmu na samaniya"
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. "baza mu zauna tsirara ba" ko " Allah ba zai same mu tsirara ba"
Bulus ya yi maganar jikin kamar wata "bukka."
Kalman nan "alfarwa" na nufin "gidan nan ta duniya da muke zama ciki." Kalman nan nishi wata ƙara ce wanda wani kan yi a sa'ada su na sa begen samun wani abu mai kyau. Dubi yadda kun juya wannan cikin 2 Korantiyawa 5:2.
Bulus na nufin shan wahala da jiki ke ji kamar wata abu ne mai nauyi da ke da wuyar ɗaukawa.
Bulus ya yi maganar jikin kamar wata sutura. "Rashin sutura" anan na nufin nutuwar jiki; "sa sutura" na nufin samun jiki na tashin mattatu da Allah zai bayar.
"zama da rashin sutura" ko "zama tsirara"
Bulus ya yi maganar rai kamar wata dabba ce da ke cin "abu mai mututwa." Dawamammen Jiki na tashin mattatu za ta cika gurbin jiki da zai mutu
An yi maganan Ruhun kamar shi ba cikakken fansa ne zuwa ga samun rai madawami. Dubi yadda ka juya magana mai kama cikin 2 Korantiyawa 1:22.
Bulus ya yi maganar jikin kamar wata wuri ne da mutum ke zama. AT: " a yayinda muna zama cikin jiki ta duniya"
"ba mu gida tare da Ubangiji" ko "ba mu cikin sama tare da Ubangiji"
Anan "tafiya"kwatanci ne na "zama" ko "nuna hali." AT: "Muna zama bisa ga bangaskiya ba bisa abinda muke gani ba"
Kalman nan "jiki" anan na nufin jikin ta duniya.
"a gida tare da Ubangiji cikin sama"
Ana iya sa kalman nan "Ubangijin" daga ayoyi dake baya. AT: "ko muna gida tare da Ubangiji ko nesa da Ubangiji"
" faranta wa Ubangiji"
"gaban Almasihu domin shari'a"
"kowane mutun zai karbi abin da ya cancanci shi"
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "abubuwan da ya yi ciki jikin nan ta duniya"
"ko abubuwa nan masu kyau ko mara kyau
"mun san abin da ake nufi da tsoron Ubangiji"
Ma'ana mai iya yiwuwa suna kamar haka 1) "mun rinjaye mutane game da gaskiyar bishara" ko 2) "mun rinjaye mutane da cewa mu ainihin manzanai ne."
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "Ba shakka Allah na ganin wani irin mutane ne muke"
"cewa kun tabbatar da ita"
"don ku iya samun abin fada ga"
Kalman nan "bayyanuwa" anan na nufin abubuwa kamar iyawa da matsayi. "zuciya" kalma ce dake nufin hali na cikin mutum. AT: "waɗanda suke yabon ayukansu amma basu damu da abin da suke a rayukansu na ciki ba"
Bulus ya yi magana game da yadda waɗansu suke tunani game da su da abokan aikin sa. AT: "in mutane na tunani mu mahaukata ne... in mutane na tunani mu masu hankali ne"
Ma'ana mai iya yiwuwa na kamar haka 1) "ƙaunar mu ga Almasihu" ko 2) "Almasihu na ƙaunar mu"
"mutu domin dukan mutane"
"shi wanda ya mutu saboda su wanda Allah ya rayar da shi kuma" ko "Almasihu wanda ya mutu saboda su wanda Allah ya tashe shi"
Ma'ana mai iya yiwuwa suna kamar haka 1) waɗannan kalmomin na nufin "mutu" kawai ko 2) waɗannan kalmomin na nufin duka biyun da "mutu" da kuma "an tashe."
Wannan na nufin abin da Bulus ya gama fada game da rayuwa don Almasihu maimakon rayuwa don jiki.
Bulus ya yi magana a kan mutum da gaskanta da Almasihu kamar sabon mutum wanda Allah ya halici. AT: "sabon mutun ne"
A nan "tsofaffin al'amura" na nufin abubuwa da ke nuna halin mutum kafin sun amince da Almasihu.
Kalman nan "Duba" tana shiryamu mu mai da hankali ga sanarwa mai ban mamaki da ke zuwa.
"Allah ya yi duk waɗannan abubuwa." Wannan na nufin abin da Bulus ya gama fada a ayoyin da ke baya game da sabon abubuwa sun cika gurbin tsohon abubuwa.
Ana iya juya wannan da sashen magana da ke da aikatau. AT: "aikin sulhunta mutane gare shi"
"Wannan na ma'ana"
Kalman nan "duniya" anan na nufin mutane dake cikin duniya. AT: "cikin Almasihu Allah na sulhunta yan Adam wa kansa"
Allah ya ba wa Bulus alhakin baza sako cewa Allah na sulhunta mutane wa kansa.
"sakon game da sulhu"
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "Allah ya naɗa mu wakilan Almasihu"
"waɗanda suna magana a maɗadin Almasihu"
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "Bari Allah ya sulhunta ku zuwa gare shi"
"Allah ya mai da Almasihu hadayan don zunubi"
Kalman nan "namu" da "mu" anan suna haɗe na kuma nufin dukan masubi.
"Almasihu ne wannan da bai taɓa yin zunubi ba"
"Allah ya yi wannan ... adalcin Allah cikin Almasihu"
Maganar nan "adalcin Allah" na nufin adalcin da Allah na bukata kuma wanda ta zo ne daga Allah. AT: " domin mu iya samun adalcin Allah cikin mu ta wurin Almasihu"
Bulus ya ce muna da wani ginin daga wurin Allah, gida ne wanda ba hannuwan mutane suka gina ba, amma madawwamin gida ne a cikin sama.
Bulus ya faɗa wannan domin yayinda muke cikin wannan alfarwa, muna so a suturtar mu, domin rai ya hadiye abu mai mutuwa.
Allah ya ba mu Ruhu a matsayin alkawarin abinda ke zuwa.
Bulus ya ce, "Mun gwammace mu rabu da jiki domin mu zauna tare da Ubangiji".
Bulus ya maishe shi burinsa domin ya gamshe Ubangiji.
Bulus ya maishe shi burinsa domin tilas dukanmu za mu hallara a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, saboda kowa ya ƙarbi sakamakon abubuwan da yayi cikin jiki, ko masu kyau ne ko marasa kyau.
Su na rinjayar mutane domin sun san cewa suna tsoron Ubangiji.
Suna ba masubi na Korontiyawa dalilin yin takama da su, domin su sami amsar da za su bada ga waɗanda ke fahariya da kasancewarsu amma ba game da abinda ke zuciya ba.
Kada su yi rayuwa domin kansu, amma domin shi wanda ya mutu kuma aka tashe shi.
Masubi ba su shar'anta kowa bisa ga ma'aunin 'yan'adam.
Shi sabon halitta ne. Tsofaffin al'amura sun shuɗe; sun zama sababbi.
Allah ba ya lissafa zunubansa a kansu kuma ya damka masu sakon sulhu.
Rokon su ga Korontiyawa shi ne su sulhuntu ga Allah saboda Almasihu.
Allah ya yi haka ne don a cikin Almasihu mu zama adalcin Allah.
1 haka, tundashike muna aiki tare, na roke ku kar ku yi watsi da alherin Allah. 2 Domin ya ce, "A lokacin alheri na saurare ku, kuma a ranar ceto na agaje ku." Yanzu ne fa, lokacin alheri. Duba, yanzu ne ranar ceto. 3 Ba mu sa sanadin faduwa a gaban kowannen ku, domin ba mu so hidimarmu ta zama marar amfani. 4 Maimakon haka, mun tabbatar da kan mu ta wurin dukan ayyukanmu, cewa mu bayin Allah ne. Mu bayinsa ne ta wurin yawan jimiri, azaba, kunci, wahala, 5 duka, kurkuku, tarzoma, cikin aiki tukuru, cikin rashin barci yawancin dare, cikin yunwa, 6 cikin tsarki, ilimi, hakuri, kirki, cikin Ruhu Mai tsarki, da sahihiyar kauna. 7 Mu bayinsa ne cikin kalmar gaskiya, cikin ikon Allah. Muna kuma da makamai na adalci, a hanun dama da hagu. 8 Muna aiki cikin daraja da rashin daraja, kushe da yabo. Ana zargin mu a kan mu mayaudara ne, duk da haka mu masu gaskiya ne. 9 Muna aiki kamar ba a san mu ba, gashi kuwa mu sanannu ne. Muna aiki kamar masu mutuwa-duba! -har yanzu muna raye. Muna aiki kamar wadanda aka hukunta, amma ba hukuncin kisa ba. 10 Muna aiki kamar muna bakinciki, amma a koyaushe muna farinciki. Muna aiki kamar matalauta, amma muna azurta mutane dayawa. Muna aiki kamar ba mu da komai, amma mun mallaki komai. 11 Mun fada maku dukan gaskiyar, Korantiyawa, kuma zuciyar mu a bude ta ke. 12 Ba mu kange zukatan ku ba, ku ne kuka kange zukatanku a gare mu. 13 Yanzu a sabanin haka-Ina magana da ku kamar yara-ku bude mana zukatanku. 14 Kada ku yi cudanya da marasa bangaskiya. Wace tarayya ke tsakanin adalci da take shari'a? Ko kuma wace zumunta ce ke tsakanin haske da duhu? 15 Wace yarjejeniya ke tsakanin Almasihu da Ibilis? ko kuma me ya hada masu bangaskiya da marasa bangaskiya? 16 ko wace yarjejeniya ce a tsakanin haikalin Allah da gumaka? Domin kuwa mu haikali ne na Allah mai rai, kamar yadda Allah ya ce: "Zan zauna a cikin su, in kuma yi tafiya a tsakanin su. Zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena." 17 Sabili da haka, "Ku fito daga cikin su, kuma ku zama kebabbu," in ji Ubangiji. "Kada ku taba kazamin abu, zan kuma karbe ku. 18 Zan zama Uba a gare ku, ku kuma za ku zama 'ya'ya maza da mata a gare ni," in ji Ubangiji Mai iko duka.
Bulus ya takaita yadda tafiya tare ya kamata ya zama don Allah.
cikin aya 2 Bulus ya rubuta da sashin annabi Ishaya.
Bulus na nufin shi da Timoti suna tafiya tare da Allah. AT: Tafiya tare da Allah"
Bulus ya roƙe su sun bar alherin Allah ta yi aiki rayuwar su. Ana iya bayana wannan kalmomi masu nuna tabbaci. AT: "muna rokon ku, ku yi amfani da alherin da kuka karɓa daga wurin Allah"
"Don Allah ya ce." Wannan ya gabatar da nassi daga annabi Ishaya ya faɗa. AT: "Allah ya ce cikin littafi"
Kalmar na "Duba" anan na shirya su da su kassa kunne ga labari mai ban mamaki dake biyowa.
Bulus ya yi maganar abin da zai hana mutum sa begen sa ga Almasihu kamar wani abu da mutumin zai iya yin tuntuɓe ya fadi. AT: "Ba mu so mu yi wani abu da zai hana mutane gaskantawa da sakon mu"
"Kalmar nan "aibata" na nufin mutane ba faɗin abu mara kyau game da aikin Bulus da kuma găba da sakon da ya shaida. Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "ba mu son mutane su iya yin magana mara kyau game da aikin mu"
"Mun haƙikanta cewa mu bayin Allah ne tawurin dukan abin da muke yi"
Bulus ya ambaci iririn yanayi masu wuya wanda a cikin ta sun haƙikanta cewa sun bayin Allah ne.
Bulus ya ambaci waɗansu halin kirki da dama don ya nuna cewa cikin yanayi ma wuya haƙika su bayin Allah ne.
Mika kansu wurin wa'azin bishara cikin iƙon Allah ya nuna cewa haƙika su bayin Allah ne.
"ta wurin maganar sakon Allah game da gaskiya" ko "ta wurin maganar gaskiyar sakon Allah"
"ta wurin nuna ikon Allah ga mutane"
Bulus ya yi maganar adalcin su kamar wata makami da ake amfani da ita a yi yakin ruhaniya.
"adalci kamar sulkin mu" ko "adalci kamar makamin mu"
Ma'ana mai iya yiwuwa suna kamar haka 1) akwai makami a hannu daya da kuma garkuwa a dayan hannun ko 2) suna shirye domin yaki don su iya tsare kowace hari daga kowace hanya.
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "Mutane sun zargi mu wai mu masu yaudara"
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "kamar mutane ba su san mu ba da kuma haƙika mutane sun san mu kwarai"
Kalman nan "Duba" anan na shirya mu mu saurari labari ta ban mamaki zai biyo baya.
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "Muna aiki kamar mutane sun tsananta mana ta dalilin aikin mu amma ba kamar an yi mana hukunci kisa ba"
"sahilin maganar gare ku"
Bulus ya yi maganar ƙaunarsa ga korantiyawa kamar samun zuciya da ke a buɗe. Anan "zuciya" wata magana ce da ake amfani da ita a maɗadin abin da mutum ke ji. AT: "muna kanar ku sosai"
Bulus ya yi maganar rashin ƙaunar Korantiyawa zuwa gare shi kamar zukantan da aka matse ta don shiga matsesen wuri. Anan "zuciya" wata magana ce da ake amfani da ita a maɗadin abin da mutum ke ji.
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "Ba mu kange ku ba" ko " Ba mu ba ku wata dalilin da zai sa ku ki ƙaunar mu ba"
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "zukatan ku tana kange ku" ko "kun bar ƙaunar mu ta dalilin kanku"
"kamar amsar da ta dace"
Bulus ya yi magana da Korantiyawa kamar 'ya'yan sa na ruhaniya. AT: "Na yi magana kamar ni uban ku ne"
Bulus ya karfafa Korantiyawa su ƙaunace shi kamar yadda ya ƙaunace su. AT: "ku ma ku ƙaunace mu" ko "ku ƙaunace mu sosai kamar yadda mun ƙaunace ku"
Ana iya bayyana wannan cikin kalmomi masu nuna i. AT: "sai dai ku yi cudanya da masubi"
Bulus ya yi maganar aiki tare domin manufa ɗaya kamar dabbobi biyu da aka ɗaure don jan keken shanu ko noma. AT: "
Wannan tambaya ce da ke jiran amsa ta a'a. AT: "Don adalci ba ta iya taraya da take shari'a"
Bulus ya yi wannan tambayar domin ya nanata cewa haske da duhu ba za su iya zama tun da shiƙe haske kan kori duhu. Kalmomin nan "haske" da "duhu" na nufin hali da kuma nau'i ta ruhaniya na masubi da marasabi. AT: "Haske ba za ta iya samu ɗangantaka da duhu ba"
Wannan tambaya ce da ke jiran amsa ta a'a. AT: "Babu wata yarjejeniya tsakanin Almasihu da Ibilis?
Wannan wata suna ce ta ibilis.
Wannan tambaya ce da ke jiran amsa ta a'a. AT: " Ba abinda da ya hada mai bada gaskiya da mara bada gaskiy"
Wannan tambaya ce da ke jiran amsa ta a'a. AT: "Babu wata yarjejeniya tsakanin haikalin Allah da gumaka"
Bulus na nifin dukan Krista siffa ce ta haikalin da Allah ke zama ciki. AT: mu na kama da haikali wanda ke mazaunin Allah mai rai"
Wannan nasi ce daga Tsohon Alkawari dake magana akan Allah na tare da mutane a hanyoyi biyu dabam dabam. Kalmomin nan "zaune tsakanin" na magana rayuwa in da wadansu ke rayuwa, kalmomin nan "tafiya tsakanin" kuma na nufin zama tare da su a sa'ada suke rayuwar su. AT: "Zan zama tare da su in kuma taimake su"
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "ku kebe kanku" ko "ku bari in keɓe ku"
Ana iya bayyana wannan cikin kalmomi dake nuna. AT: "Taba abu mai tsabta"
Sun roke Korontiyawan da cewa kar su yi watsi da alherin Allah.
Yanzu ne loƙacin alheri. Yanzu ne ranar ceto.
Ba su sa dutsen faduwa a gaban kowa domin ba su so hidimarsu ta zama marar amfani ba.
Ayukansu ya nuna cewa su bayin Allah ne.
Sun jimiri, azaba, kunci, wahala, kurkuku, tarzoma, cikin aiki tukuru, cikin rashin barci yawancin dare, da yunwa.
An yi zargin su a kan yaudara.
Bulus ya ce zuciyarsu a buɗe ta ke ga Korontiyawa kuma musaya, Bulus ya so masubi na Korontiyawa su buɗe zuciyarsu ga shi da abokan aikinsa.
Bulus ya bayar da waɗannan dalilai: Wace tarayya ke tsakanin adalci da take shari'a? Wace zumunta ce ke tsakanin haske da duhu? Wace yarjejeniya ke tsakanin Almasihu da Ibilis? Me ya hada masu bangaskiya da marasa bangaskiya? Wace yarjejeniya ce a tsakanin haikalin Allah da gumaka?
Ubangiji ya ce zai karbe su. Zai zama Uba a gare su, su kuma za su zama 'ya'ya maza da mata a gare shi.
1 Kaunatattu, da shike muna da wadannan alkawura, bari mu tsaftace kanmu, daga dukan abubuwan da ke kazantar da jikinmu da ruhunmu. Bari mu bidi tsarki cikin tsoron Allah. 2 Ku ba mu dama! Bamu bata wa kowa rai ba. Ba mu cutar da kowa ko mu zambaci kowa ba. 3 Ba domin in kayar da ku na fadi haka ba. Domin kuwa na riga na fada muku, cewa kuna zuciyar mu, domin mu mutu tare mu kuma rayu tare. 4 Ina da muhimmin gabagadi a cikin ku, Ina fahariya da ku. Ina cike da ta'aziya. Farincikina ya cika makil duk da wahalhalunmu. 5 Yayin da muka zo Makidoniya, jikinmu bai samu hutu ba. A maimakon haka, mun shiga matsaloli ta ko wace hanya ta wurin tashin hankali a waje tsoro kuma a ciki. 6 Amma Allah, mai ta'azantar da raunana, ya ta'azantar da mu ta wurin zuwan Titus. 7 Ba ta wurin isowar sa kadai Allah ya yi mana ta'aziyya ba. Amma kuma ta wurin ta'aziyyar da Titus ya samu daga wurin ku. Ya gaya mana irin matsananciyar kaunarku, bakincikinku, da zurfin kulawarku a kaina. Na kuwa yi farinciki sosai. 8 Kodashike wasikata, ta bata maku rai, ban yi da na sanin haka ba. Amma sa'adda na ga wasika ta ta bata maku rai, na yi da na sani. Sai dai bacin ranku, na dan lokaci ne. 9 Yanzu kuwa, ina farinciki, ba domin bacin ranku ba, amma domin bacin ranku ya kawo ku ga tuba, kun fuskanci bakinciki na ibada, donhaka ba ku yi rashi ba sabili da mu. 10 Domin bakinciki daga Allah ya kan kai ga tuba da ke kammala ceto ba tare da-da na sani ba. Bakinciki na duniya kuwa ya kan kai ga mutuwa. 11 Ku dubi irin kyakkyawar niyya da bakincikin nan daga Allah ya haifar a cikin ku. Ina misalin girman niyyar nan taku ta nuna cewa baku da laifi. Ina misalin girman fushinku, tsoronku, da sa zuciyarku, himmar ku, da marmarin ku na ganin cewa an yi adalci! A cikin komai, kun nuna kanku marasa laifi a cikin wannan al'amari. 12 Kodayake na rubuto maku, ban rubuto saboda mai laifin ba, ko kuma saboda wanda aka yi wa laifin. Na rubuto ne domin himmarku gare mu ta sanu gare ku a gaban Allah. 13 Dalilin haka ne muka samu karfafawa. Baya ga ta'aziyyar mu, mun kuma yi murna sosai saboda farin cikin Titus, domin ruhunsa ya wartsake ta wurin ku duka. 14 Domin kuwa idan na yi fahariya da ku a gaban sa, ban ji kunya ba. A sabanin haka, kamar yadda kowane abu da muka fada maku gaskiya ne, fahariyarmu a kan ku ga Titus ta zama gaskiya. 15 Kaunarsa a gare ku tana da girma, kamar yadda ya rika tunawa da biyayyarku duka, yadda kuka karbe shi da tsoro da rawar jiki. 16 Ina farinciki matuka domin ina da cikakken gabagadi a cikin ku.
Bulus ya cigaba da tunashe su da su rabu da zunubi su kuma biɗi zaman tsarki da nufi daya.
"Ku wanda nake ƙauna" ko "Abokai na na kwarai"
Bulus na cewa ana da su yi nesa daga kowace irin zunubi da zai bata dangantakansu da Allah.
"mu yi ƙoƙarin zaman tsarki"
"Tawurin girmama Allah kwarai"
Wannan na nufin abin da Bulus ya ce [2 Korantiyawa 6:11-13]
"Ban faɗi wannan domin zambar ku cewa kun yi wata laifi ba." Kalman nan "wannan" na nufin abin da Bulus ya faɗa yanzu cewa bai yi wa kowa laifi ba.
Bulus ya yi maganar ƙaunar da shi da abokan aikin sa suke yi wa Korantiyawa kamar sun rike su cikin zukatan su. AT: "ku ƙaunatattun mu ne"
Wannan na nufin Bulus da abokan aikin za su ciga da ƙaunar Korantiyawa a ko wace yanayi. AT: "ko muna raye ko mun mutu"
"mu" na nufin duk da masubi na Korantiyawa
Ana iya bayyana wannan a cikin nau'i mai aiki. AT: "Kun cika ni da ta'aziya"
Bulus ya yi maganar farincikinsa kamar wata ruwa da ya cika shi har lokacin da ta fara zuɓe wa. AT: "Ina da matukar farinciki "
"duk da dukan wahalar mu"
Kalman nan "mu" anan na nuf Bulus da Timoti amma bada Korantiyawa ko Titus.
"Jiki" anan na nufin gabadayan mutumin. AT: "ba mu sami hutu ba" ko "mun gaji kwarai"
Ana iya bayyana wannan cikin nau'i mai aiki. AT: "muna shan wahala ta kowace hanya"
Ma'ana mai iya yiwuwa ta "waje" suna kamar haka 1) "wajen jikunan mu" ko 2) "wajen ikilisiya." kalman nan "ciki" na nufin yadda suke ji a cikin su. AT: "ta wurin tashin hankali tare da mutane da kuma tsoro a cikin mu"
Bulus ya sami ta'aziya tawurin sanin cewa Korantiyawa sun ta'azantar da Titus. AT: "Ta wurin sanin cewa Titus ya sami ta'aziay daga gare ku"
Wannan na nufin wasikar Bulus ta da zuwa ga masubi na Korantiyawa wanda a cikin ta ya tsauta musu don sun karbi cewa maibi na iya yin fasikanci da matan uban sa.
"sa'ada na sani cewa wasika ta"
Ana iya bayyan wannan cikin nau'i mai aiki. AT: "ba domin abin da na faɗa cikin wasika ta ya bata muku rai ba"
"Baku rasa kome ba domin mu tsauta maku." Wannan na nufin ƙodashiƙe wasikar ta sa su baƙin ciki, sun karu ta wurin wasikar domin ta kai su ga tuba. AT: "don haka ba mu yi muku lahani a ko wata hanya ba"
Kalman nan "tuba" ana iya nanata ta don bayyana dangantakan abin da ta bi baya da kuma wanda ke biye da shi. AT: "Gama baƙin ciki wanda Allah ke sa wa na kai ga tuba, tuba kuwa na kai ga ceto"
Ma'ana mai iya yiwuwa suna kamar haka 1) Bulus bai yi 'da na sani' ba saboda baƙin ciki domin baƙin ciki ta kai ga tuban da kuma ceton su ko 2) Korantiyawa ba za su yi 'da na sani' ba don baƙin cikin su ba don ta kai ga tuban da kuma ceton su.
Irin wannan baƙin ciki tana kai ga mutuwa ba ceto ba domin ba ta kai ga tuba. AT: "Baƙin ciki ta duniya tana kai ga mutuwa cikin ruhaniya"
"Duba ka gani don kan ka kyakkyawar ƙuduri"
Anan Kalman nan "Ina misalin" ta sa wannan maganar ta zama kamar maganar motsin rai. AT: "ƙudurin ku don nuna cewa ba ku da laifi kyakyawa ce!"
"fushin ku"
Ana iya bayyana wannan cikin nau'i mai aiki. AT: "cewa wanin ya yi adalci"
"shi wanda ya yi laifi"
Ana iya bayyana wannan cikin nau'i mai aiki. AT: "don ku sani cewa himmarku zuwa gare mu sahili ce"
Wannan na nufin a gaban Allah. Sannin Allah da kuma yardan gaskiyar Bulus na kamar cewa Allah ya iya ganin su. Dubi yadda kun juya wannan cikin [2 Korantiyawa 4:2]
Kalman nan "wannan" anan na nufin yadda Korantiyawa sun karbi wasikar Bulus, kamar yadda ya bayyana a ayan da ke baya. Ana iya bayyana wannan cikin nau'i mai aiki. AT: Wannan ne ta karfafa mu"
Anan kalman nan "ruhu" na nufin yanayin mutum da kuma halinsa. Ana iya bayyana wannan cikin nau'i mai aiki. AT: "kun wartsake ruhun sa dukan ku" ko "dukan ku kun sa shi ya daina damuwa "
"Don ƙodashiƙe na yi fahariya daku a gaban sa"
"ba ku ba ni kunya ba"
"kun hakikanta cewa fahariyarmu game da ku zuwa ga Titus gaskiya ce"
Wannan "biyayya" ana iya bayyana ta da aikatau, "biyayya." AT: "yadda dukan ku ku yi biyayya"
A nan "tsoro" da "rawar jiki" suna da ma'ana mai kama kuma suna nanata karfin tsoro. AT: "kun marabce shi da girmamawa kwarai"
Ma'ana mai iy yiwuwa suna kamar haka 1) "da babban girmamawa wa Allah" ko 2) "da babba girmamawa wa Titus."
Mu tsaftace kanmu, daga dukan abubuwan da ke kazantar da jikinmu da ruhunmu.
Bulus ya na so su "ba su dama!"
Bulus ya faɗa wa masubi na Korontiyawa cewa suna zuciyarsa da abokan aikinsa, domin su mutu tare su kuma rayu tare. Yana da muhimmin gabagadi a cikin su, Yana fahariya da su.
Allah, ya ta'azantar da su ta wurin zuwan Titus. Kuma ta labarin ta'aziyyar da Titus ya samu daga wurin masubi na Korontiyawa, da kuma matsananciyar ƙaunarsu, bakincikinsu, da zurfin kulawarsu wa Bulus.
Masubi na Korontiyawa sun fuskanci bakinciki, bakinciki na ibada ga amsar wasikar Bulus na baya.
Bakinciki ya na kai ga tuba a cikinsu.
Bulus ya ce ya rubuta domin naciyar masubi na Korontiyawa saboda shi da abokan aikinsa su zama sananne ga masubi na Korontiyawa a gaban Allah.
Ya na farin ciki domin ruhunsa ya wartsake ta wurin masubi na Korontiyawa.
Ƙaunar Titus ga masubi na Korontiyawa ya yi girma sa'ad da ya rika tunawa da biyayyarsu kamar yadda suka ƙarbe shi da tsoro da rawar jiki.
1 Muna so ku sani, 'yan'uwa, game da alherin Allah da aka bayar ga Ikkilisiyoyin Makidoniya. 2 A lokacin babban gwajin wahala, yalwar farincikinsu da tsananin talaucinsu ya haifar da yalwar bayarwa hannu sake. 3 Domin ina shaida, sun yi bayarwa iya kokarinsu, fiye da abinda ma suke iyawa. Cikin yaddar ransu 4 da roko mai yawa suka nace da a ba su zarafi su yi tarayya a wannan hidima ga masu bi. 5 Haka ya auku ba kamar yadda muka yi zato ba. A Maimakon haka, sai da suka fara bada kansu ga Ubangiji. Kuma suka bada kansu gare mu bisa ga nufin Allah. 6 Sai muka karfafa Titus, wanda ya rigaya ya fara wannan aiki, domin ya kammala wannan aiki na bayarwa ta fannin ku. 7 Amma kun habaka cikin komai-cikin bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin aiki tukuru, cikin kaunarku dominmu. Don haka, ku tabbata kun habaka a wannan aiki na bayarwa. 8 Na fadi haka ne ba kamar ina umurtar ku ba. A maimakon haka, na fadi haka ne in gwada sahihancin kaunarku ta wurin kwatanta ta da himmar sauran mutane. 9 Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu. Kodashike shi mai arziki ne, amma ya zama matalauci, domin ta wurin talaucinsa ku yi arziki. 10 A wannan al'amari zan ba ku shawarar da za ta taimake ku. Shekarar da ta wuce, ba fara wani abu kawai kuka yi ba, amma kun yi marmarin ku yi shi. 11 Yanzu ku kammala shi. Kamar yadda kuke da niyya da marmarin yin haka a lokacin, bari ku yi kokari ku kawo shi ga kammalawa iyakar iyawar ku. 12 Idan kuna niyya ku yi wannan aiki, abu mai kyau ne karbabbe kuma. Tabbas ya zama dai-dai da abinda mutum ke da shi, ba abinda ba ya da shi ba. 13 Domin wannan aiki ba domin a nawaita maku sannan wadansu su samu sauki ba ne. A maimakon haka, ya kamata a sami daidaituwa. 14 Yalwar ku a wannan lokaci za ta zama abin biyan bukatarsu. Haka nan kuma domin yalwar su ta iya biyan bukatarku, domin a sami daidaituwa. 15 Yana nan kamar yadda aka rubuta: "Wanda ke da shi dayawa bai samu raguwar komai ba, kuma wanda yake da kadan bai rasa komai ba." 16 Amma godiya ga Allah, da yasa a zuciyar Titus marmarin kulawa da ku kamar wadda nake da ita domin ku. 17 Gama ba rokon mu kadai ya karba ba, amma ya yi da gaske akan haka. Ya zo gare ku ne da yardar kan sa. 18 Mun aiko tare da shi dan'uwa da ake yaba masa a tsakanin dukan Ikkilisiyoyi domin ayyukansa a cikin shelar bishara. 19 Ba domin wannan kadai ba, amma Ikkilisiyoyi ne suka zabe shi ya tafi tare da mu a cikin yin wannan hidima ta alheri. Wannan domin girmama Ubangiji ne kansa da kuma domin aniyarmu ta taimakawa. 20 Muna gudun kada kowa ya sa mana laifi game da wannan alheri da muke dauke da shi. 21 Niyyar mu ce mu yi kyakkyawan abu, ba a gaban Ubangiji kadai ba, amma a gaban mutane ma. 22 Mun kuma aiki wani dan'uwan tare da su. Mun sha gwada shi, kuma mun same shi da himma wajen ayyuka da dama. Yanzu kuma ya kara himma, saboda amincewa mai girma da yake da ita gare ku. 23 Game da Titus, shi abokin tafiyata ne, kuma abokin aikina domin ku. Game da yan'uwanmu, an aiko su ne daga Ikkilisiyoyi. Su kuwa daraja ne ga Almasihu. 24 Don haka, ku nuna masu kaunarku, ku kuma nuna wa Ikilisiyoyi dalilin fahariyarmu game da ku.
Bayan da ya yi bayanin canjin shirin sa da kuma na salon hidimansa, Bulus yayi magana a kan bayaswa.
AT: "alherin Allah da ya ba ikkilisiyoyin Makidoniya"
Bulus ya yi maga game da "farinciki" da "talauci" kaman abu mai rai ne da zai iya bayar da hannu sake. AT: "saboda yawar farincikin mutanen da kuma tsananin talauci, sun zama da bayarwa"
Bulus ya yi maga game da farinciki kaman abun da ana iya gani wadda yana iya yaduwa.
ko da shike ikkilisiyar Makidoniya sun sha gwaji mai tsanani da talauci, ta wurin alherin Allah, sun iya tara kuɗi domin masubi a Urushalima.
"yawan yalwar hannu sake." Kalmar nan "yalwar" na bayyana yalwar bayarwarsu hannu sake.
Wannan na nufin ikkilisiya a Makidoniya.
"da son rai"
Bulus na nufin tanadin kuɗi wa masubi a Urushalima. AT: "Wannan hidima na tanadi wa masubi da ke Urushlima"
Bulus na maganar karban kuɗi daga wurin Korantiyawa domin masubi da ke Urushalima. AT: "wanda ya karfafa bayaswanku tun daga farko"
Ya kamata Titus ya taimakawa Korantiyawa domin su kammala tarin kuɗin. AT: "domin a karfafa ku ku kammala karba da kuma yalwar bayarwa ku"
Bulus ya yi magana game da masubi na Korantiyawa kaman su kaya ne da ke a bayyane. AT: "kun yi koƙari ta hanyoyi da yawa"
AT: "ku tabbata cewa kun yi koƙari a bayaswan ku ga masubi da ke Urushalima"
Bulus na karfafa Korantiyawa cewa su yi yalwar bayarwa ta wurin kwatanta yalwar bayarwar su da na ikklisiyar Makidoniya.
A wannan halin, kalmar nan "alheri" na nanata yalwar bayarwa wanda Yesu ya albarƙaci Korantiyawa da su.
Bulus ya yi magana game da Yesu kamin zuwansa a jiki ne a matsayin mai arziki, da kuma ɗaukan jikin mutum da yayi a mastayin zaman talaka.
Bulus ya yi magana cewa Korantiyawa sun zama da arziki ta ruhania ta dalilin bayyanuwar Yesu a jikin mutum.
Wannan na nufin karban kuɗi domin a ba wa masubi da ke Urushalima. AT: "game da tarin"
AT: "kun yi marmari kun kuma yi niyya ku yi shi"
"kammala shi" ko "kare shi"
A nan kalamun nan "kyau" da kuma "karɓabbe" na da ma'ana iri guda kuma suna nanata kyaun abu . AT: "Abu mai kyau sosai"
"Dole ne bayarwa ya zama dai-dai da abinda mutum ke da shi"
Wannan na nufin karban kuɗi wa masubi da ke Urushalima. AT: "Domin wannan aikin karban kuɗi"
AT: "domin ku saukaka wa wasu ku kuma nawaita wa kanku".
"ya kamata a kasance daidai"
Da shike Korantiyawan suna aiki a wannan zamani yana nuna cewa masubi da ke Urushalima za su kuma taimaka masu a wata loƙaci nan gaba. AT: "Domin nan gaba yalwar su ta iya biyan buƙattarku"
Anan Bulus ya ɗauko wannan daga Fitowa. Ana iya bayana wannan cikin sifar aiki. AT: "yadda Musa ya rubuto"
AT: "na da komai da yake buƙata"
Anan, kalmar "zuciya" na nufin motsin ta ƙauna. Wannan na nufin cewa Allah ya sa Titus ya ƙaunace su. AT: "da ya sa Titus ya kula da ku kamar yadda nake yi"
"irin babar sha'awa" ko "kwakwaran damuwa"
Bulus na nufin yanda ya ce wa Titus ya koma korantus don ya kammala karban bayaswan. AT: "Gamma ba amince wa roƙon mu kadai ya yi don ya taimaka da karɓan bayaswanba"
" tare da Titus"
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT:"ɗan'uwa da masubi ke yaba a sakanin dukan iklisiya"
"Ba kadai ne masubi a cikin dukkan iklisiyoyi ke yabon sa ba"
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "iklisiyoyi sun kuma zaɓe shi"
" don gudanar da wannan aiki yalwar bayaswa." Wannan na nufin kai baikon Urshalima
" domin nuna kwazonmu don taimakawa"
Wannan na nufin kai baiko ga Urushalima. Ana iya bayana wannan maganan "yalwar bayarwa" da siffa. AT: "Game da yadda muke ɗauke da yelwar kyauta"
" Muna hankali da yadda muke rike wannan kyauta ta hanya mai daraja"
"a ra'ayin Ubangiji... a ra'ayin mutane"
Kalmar "su" na nufin Titus da kuma dan'uwan da aka ambata daga farko
"shi amini na ne wanda ke aiki tare da ni domin taima ma ku"
Wannan na nufin mutane biyu da za su raka Titus.
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "Ikkilisiyoyi sun aiko su"
Ana iya bayana wannan magan. AT: "Za su sa mutane su daraja Almasihu"
Bulus ya so su san game da alherin Allah da aka bayar ga Ikkilisiyoyin Makidoniya.
Sun haifar da yalwar bayarwa hannu sake.
Bulus ya karfafa Titus cewa ya kammala wannan aiki na alheri ta fannin masubi na Korontiyawa.
Sun habaka bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin aiki tukuru, cikin kuma ƙaunarsu domin Bulus.
Bulus ya ce abu mai kyau ne kuma karɓaɓɓe ne wa masubi na Korontiyawa su yi niyya a yin wannan aiki.
A'a. Bulus ya ce yalwar Korontiyawa a wannan loƙaci za ta zama abin biyan bukatarsu. Haka nan kuma domin yalwar su ta iya biyan bukatar masubi na Korontiyawa, da kuma domin a sami daidaituwa.
Titus ya amince rokon Bulus, ya yi da gaske akan haka, Ya kuma zo gare su da yardar kansa.
Bulus ya na gudun kada kowa ya same shi da laifi game da ayukarsa.
Bulus ya faɗa wa ikilisiyar Korontiyawa cewa su nuna masu ƙauna, su kuma nuna masu dalilin da Bulus ya yi fahariya game da ikilisiyar Korontiyawa a cikin sauran ikilisiyoyi.
1 Game da hidima domin tsarkaka, ya dace in rubuta maku. 2 Na san marmarinku, wanda na yi fahariya da shi a gaban mutanen Makidoniya. Na gaya masu Akaya sun riga sun shirya tun bara. Kwazon ku ya sa yawancin su sun shiga aiki. 3 To na aiko maku da 'yan'uwa saboda kada fahariyarmu akanku ta zama a banza, domin kuma ku zauna a shirye, kamar yadda na ce za ku yi. 4 Idan kuwa ba haka ba, idan wani cikin makidoniyawa ya biyoni kuma ya tarar da baku shirya ba, za mu ji kunya-ba ni cewa komai game da ku-domin ina da gabagadi a kan ku. 5 Sai na ga ya dace in turo 'yan'uwa su zo wurin ku kafin lokaci yayi suyi shirye shirye game da gudummuwar da kuka yi alkawari. Wannan ya zama haka ne domin a shirya shi a matsayin bayarwar albarka, ba wani abin kwace ba. 6 Batun shine: wanda ya shuka kadan zai girbi kadan, wanda kuma ya shuka da manufar albarka zai girbi albarka 7 Bari kowa ya bayar bisa ga yadda ya yi niyya a zuciyarsa. Kada ya bayar da bacin rai ko kamar dole. Gama Allah yana kaunar mai bayarwa da dadin rai. 8 Allah na da ikon ya sa kowace albarka ta ribanbanya domin ku, domin, a koyaushe, a cikin dukan abubuwa, ku sami duk abinda kuke bukata. Hakan zai kasance domin ku ribabbanya kowanne kyakkyawan aiki. 9 Kamar yadda aka rubuta, "Ya rarraba arzikinsa, ya bada shi ga matalauta. Adalcinsa ya dawwama har abada." 10 Shi wanda ke bayar da iri ga mai shuka da gurasa domin abinci, zai bayar ya kuma ribabbanya maku iri domin shuka. Zai sa girbin adalcinku ya karu. 11 Za ku wadata ta kowace hanya domin ku zama masu bayarwa, wannan kuwa zai sa a yi wa Allah godiya ta wurin mu. 12 Aiwatar da wannan hidima ba biyan bukatun tsarkaka kawai take yi ba. Tana kuma ribanbanya zuwa ayyuka masu yawa na bada godiya ga Allah. 13 Domin an gwada ku an tabbatar da ku akan wannan hidima, za ku kuma daukaka Allah ta wurin biyayyar ku ga shaidar bisharar Almasihu. Za ku kuma daukaka Allah ta wurin yalwar bayarwarku gare su da kowa duka. 14 Suna marmarin ganin ku, suna kuma yi maku addu'a. Suna yin haka saboda alherin Allah mai girma da ke bisan ku. 15 Godiya ga Allah domin kyautarsa wadda ta fi gaban bayyanawa.
Bulus ya cigaba da zancen bayaswa . Yana so ya tabbatar da an yi bayaswa domin masubi dake bukata a Urushalima kafin ya zo saboda da kada ya zama kamar ya ci zarafin su. Ya yi magana game da yanda bayarwa ke albarcance mai bayarwa da kuma daukaki Allah.
Yayin da Bulus ke ambata Akaya, ya na nufin lardin Romawa da ke a kudancin Greece inda Korontus yake.
Wannan na nufin karban kuɗi domin a ba wa masubi a Urushalima. Ma'anan wannan zance na a bayyane. AT: "hidiman bishara ga masubi a Urshalima"
Anan kalmar "Akaya" na nufin mutane da suke zama a wannan lardin, masamman mutane na iklisiyar Koronti. AT: "mutanen Akaya su na ta shiri"
Wannan na nufin Titus da mutane biu da suka raka shi.
Bulus ba ya so waɗansu su yi tunani cewa karya ne abubuwan da ya yi fahariya game da korontiyawa.
"tarar da baku shirya kubayar ba"
Bulus ya yi anfani da korau zance don ya nanata cewa abu iri guda ne ke gaskiya game da korontiyawa. AT: "za ku kuma fin shan kunya"
Daga fahimtar Bulus, 'yan'uwan na tafiya. AT: " 'yan'uwa su tafi wurin ku"
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "ba kaman abun da mun tilasta maku ku bayar ba"
Bulus ya yi kwatanci da manomi mai shuki don ya yi bayanin sakamokon bayaswa. kamar da girbin manoma na nan bisa yan da ya shuka, haka ne albarkun Allah ze kasance da yawa ko da kadan bisa Yalwar bayaswar korontiyawa.
A nan kalmar "zuciya" na nufin tunani da motsin zuciya. AT: "bayar kamar yadda ya yi nia"
Ana iya bayana wannan maganan. AT: "ba domin ya zargu ko domin wani yanna tilas'a shi ba"
Allah yana son mutane su bayar da zuciya daya domin su taimake 'yan'uwa masubi.
An bayana alheri kaman abu ne na jiki da mutum na iya samu fiye da yanda zai yi amfani. Yadda mutum ya ke ba da kudi wa masubi, Allah na kuma ba mai bayarwan dukan abin da ya ke so. AT: "Allah na iya baku fiye da ku ke bukata"
Wannan na nufin abin da ke na jiki wanda maibi ke bukata, ba don bukatan Allah ya cece shi daga zunubinsa ba.
"domin ku iya yin kyakyawan ayuka mai yawa"
"Haka yake kaman yadda aka rubuta." Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "Haka yake kamar yadda marubucin ya rubuta"
"Allah mai bayar"
A nan kalmar "gurasa" na nufin abinci muhinmi. AT: "abinci don ci"
Bulus yayi magana game da malakar Korontiyawa kamar iri ne da na bayaswa ga waɗansu kaman su na shuki. AT: "Allah zai albarkance ku don "
Bulus ya kwatanta riɓar da korontiyawa za su samu daga Yalwar bayarwansu da na girbi. AT: "Allah zai albarkance ku domin adalcin ku"
"girbin da ke zuwa daga ayukan adalcin ku." A nan kalmar "adalci" na nufin adalcin ayukan Korontiyawa a bayaswan malakar su ga masubi a Urushalima.
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "Allah zai wadatar da ku"
"Wannan" na nufin yalwar bayaswar korontiyawa. AT: "Wanda sun karbi kyautanen da mun kawo za su gode wa Allah, domin yalwar bayaswar ku" ko "idan mun ba da kyautar ku ga wanda suke so, za su yi wa Allah godiya"
A nan kalmar "hidima" na nufin Bulus da abokan tafiyarsa da sun kawo taimakon ga masubi a cikin Urushalima. AT: "Domin yin wannan hidima ma masubi a Urushalima"
Bulus ya yi magana game da hidimar masubi na Korontiya kaman abu ruwa ruwa ne wanda abu ba zai iya ɗauka ba. AT: "na sa ayuka mafiyawa da mutane za su gode wa Allah"
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "Domin wannan hidiman ya tabbatar da ku"
Bulus ya ce Korontiyawa za su daukaka Allah ta wurin aminci da Yesu da kuma yalwar bayarswa ga saura masubi da suke da bukata.
"domin kyautarsa , wadda kalma bazata iya kwatanta ba." ma'anan su na kamar haka1) wannan kyauta na nufin "kyakyawar alheri" da Allah ya ba wa Korantiyawa, wanda ya sa su yalwanta ko 2) wannan kyauta na nufin Yesu Almasihu, da Allah ya ba ma masubi.
Bulus ya ce bai dace ya rubuta masu game da hidimar masubi ba.
Ya aiko 'yan'uwa saboda kada fahariyarsa akansu Korontiyawa ta zama a banza, domin kuma su zauna a shirye, kamar yadda ya ce za su yi.
Bulus ya ga ya dace domin shi da abokan aikinsa ba za su kunyata idan wani ɗan Makadonia ya zo da Bulus sai ya same su ba a shirye ba. Bulus ya so Korontiyawan su shirya ƙyautansu a matsayin bayarwar albarka, ba wani abin ƙwace ba.
Bulu ya ce batun shine: "Wanda ya shuka kadan zai girbi kadan, wanda kuma ya shuka da manufar albarka zai girbi albarka."
Kowa ya bayar bisa ga yadda ya yi niyya a zuciyarsa-Kada ya bayar da ɗole ko ya yi bakinciki sa'ad da ya na bayar.
Zai bayar ya kuma ribabbanya masu iri domin shuka zai kuma sa girbin adalcinsu ya karu. Za su wadata ta kowace hanya domin su zama masu bayarwa.
Sun ɗaukaka Allah ta wurin biyayyar su ga shaidar bisharar Almasihu da kuma ta wurin yalwar bayarwarsu.
Sun yi marmarin ganin su saboda alherin Allah mai girma da ke bisa Korontiyawan.
1 Ni, Bulus, da kaina nake rokon ku, ta wurin tawali'u da nasihar Almasihu. Ina da saukin kai yayinda nake gaban ku, amma ina da gabagadi a gare ku yayinda ba na tare da ku. 2 Ina rokon ku, yayinda nake gabanku, ba ni so in zama mai tsaurin hali. Amma ina ganin zan bukaci zama mai gabagadi sa'adda nake tsayayya da su wadanda ke zaton muna zama bisa ga jiki. 3 Kodashike dai muna tafiya bisa jiki, ba ma yin yaki bisa jiki. 4 Domin makaman da muke yaki da su ba na jiki ba ne. Maimakon haka, makamai ne na Allah da ke da ikon rushe ikokin shaidan. Suna kawar da dukan gardandamin da ke kawo kaucewa. 5 Muna kuma rushe duk wani abinda ke gaba da sanin Allah. Muna kuma kama kowanne tunani zuwa biyayya ga Almasihu. 6 Muna kuma shirye mu hukunta kowanne irin aiki na rashin biyayya, da zarar biyayyarku ta tabbata. 7 Dubi abin da aka sa a bayyane a gaban ku. In har wani ya tabbata shi na Almasihu ne, bari fa ya tunatar da kansa cewa kamar yadda shi na Almasihu ne, hakanan muma muke. 8 Ko da zan yi fahariya da ikon da muke dashi, wanda Ubangiji ya ba mu domin mu inganta ku, ba domin mu rushe ku ba, ba zan ji kunya ba. 9 Ba na so ya zama kamar ina firgita ku ne da wasikuna. 10 Domin wadansu mutane na cewa, "Wasikunsa na da iko da firgitarwa, amma in ka gan shi kumama ne. Kalmominsa ba abin saurare ba ne." 11 Bari wadannan mutane su sani cewa abinda muke fadi a kalmomin wasikunmu lokacin da ba mu nan, haka za mu yi in muna nan. 12 Mu dai ba mu hada kanmu da kowa, ko kuma mu kwatanta kanmu da wadanda ke yabon kansu. Amma yayin da suke gwada kansu da junansu, suke kuma kwatanta kansu da junansu, ba su da ganewa. 13 Saidai, ba za mu yi fahariya fiye da yadda ya kamata ba. Maimakon haka, za mu yi haka ne gwalgwadon iyakar abinda Allah ya sa muyi, iyakar da takai gareku. 14 Gama bamu yi zarbabi ba sa'adda muka kai gareku. Mune na farko da muka kai gare ku da bisharar Almasihu. 15 Ba mu yi fahariya fiye da kima game da aikin wasu ba. Maimakon haka, muna fatan bangaskiyar ku ta karu domin bangaren aikin mu ya kara fadada kwarai, kuma a daidai iyakarsa. 16 Muna fatan haka, domin mu kai bishara zuwa yankunan da ke gaba da naku. Ba za mu yi fahariya akan aikin da aka yi a yankin wani ba. 17 "Amma bari duk wanda zai yi fahariya, ya yi ta cikin Ubangiji." 18 Domin ba wanda ya ke shaidar kansa shine yardajje ba. Maimakon haka, sai dai wanda Ubangiji ke shaidarsa.
Bulus ya chanja zancen daga bayaswa zuwa tabatar da ikon shi na koyarswa kamar yada ya saba.
Ana iya furta kalmar "tawali'u" da "nasiha" ta wani hanya. AT: " Ina tawali'u da nasiha, domin Almasihu ya riga ya yi ni haka"
"wanda ke tunani"
Kalmar "jiki" na nufin sifar zunubi. "muna kwoikwayo daga ni'yar mutum"
A nana"tafiya" magana ne na "mai rai" da kuma "jiki" da na nufin rayuwa ta jiki AT: "muna rayuwa a cikin jiki "
Bulus na kokakarin rinjayan korontiyawa domin su gaskanta da shi ba da masu koyaswar karya kaman su na yaki a cikin jiki. Yakamata a bayana wannan kalmomi.
AT: 1) kalmar "jiki" na nufin rayuwa ta jiki. AT: "yi fada da abokan gabanmu ta yin anfani da makamai na jiki" ko kuwa 2) kalmar "jiki" na nufin sifar mutum na zunubi. AT: " yin yaki a hanyar zunubi"
Bulus ya yi magana game da hikima ta Allah dake bayana hikimar mutum ta zama karya kamar shi ne makami da yake rushe gagararran gidan makiya. AT: " makaman da muke yaki da su ... na nuna wa mutane cewa abun da makiyan mu sun fada ba daidai ba ne."
AT: 1) kalmar "jiki" magana ne ta jiki. AT: "ba na jiki ba ne" kokwa 2) kalmar "jiki"na nufin sifar mutum na zunubi. AT: "ba na zunubi ba ne" kokwa " kada ku yarda manna mu yi abun da ba daidai ba"
Bulus na kan magana game da yaki kaman "sanin Allah" rundunan yaƙi ne kuma " dukan abubuwa da ke sama" katanga ne da mutane su ka yi domin su kare mai sarau. AT: "ko wane jayayyan karya da mutane masu girman kai su na tunani karen kansu"
"duk abin da mutane masu girman kai su na yi"
Bulus ya yi magana game da jayayya kaman katanga ne da ke kare rundunar yaƙi. Kalman "gaba da" na nufin "tash tsaye" ba "abin da ke gaba" na kwanta a kan iska. AT: "mutane na haka domin kada su iya sanin wa ne ne Allah" "
Bulus na magana game da tunanin mutane kaman su ne makiyan soja wadda ya kama a fada.AT: "mun nuna masu yadda dabarun da mutanen ke da shi ba daidai bane mu kuma koya wa mutanen su bi umurnin Almasihu"
Kalmomin "aiki na rashin biyayya" magana ne na mutanen da ke ayukan can. AT: "hukunta kowanen ku da ya yi mana rashin biyayya"
AT: 1) wannan doka ne ko 2) wannan zance ne, "kuna duba abunda kuke iya gani da idanunku." Wadansu na tunani cewa wannan a takaice ne da ake iya rubuta a zancen. AT: "kuna duba abinda ke sarai a gaban ku?" kokwa "Kamar ba ku iya gani abun da ke sarai a gabanku ba."
"ya kamata ya tuna"
"cewa kamar yadda mu na Almasihu ne kaman yadda yake"
Bulus na maganan taimaka wa Korontiyawa domin su san Almasihu da kyau kaman ya na kan aikin gini. AT: "domin a taimake ku ku zama ainahin masubin Almasihu ba don a hana ku binsa ba"
"Ina gwada firgita ku"
"bukaci da ƙarfi"
"Ina so waɗannan mutane su sani"
"zamu sake yin irin abin da mun rubuta a cikin wasikun mu a lokacin da ba mu na tare da ku in muna nan "
Duka kwatancin wannan kalmar na nufin kungiyar bishara na Bulus ba Korontiyawa ba.
"kimar mu ta kai ga"
Bulus ya na kara maimaitawa sau biu
Bulus na maganar kyau kaman abun da mutane ke iya gwado tsawon sa. AT: "suka kali junansu ko za su iya tantace"
"sun nuna wa kowa cewa ba su san komai ba"
Bulus ya yi magana da iƙo da yake dashi kamar kasa da yake da mulki, waɗanan abubbuwa da yake da mulki a kan su suna a sakanin iyaka . ko kuwa "inda ta tsaya" na ƙasar sa, sai abubuwan da basu a karkashin iƙonsa su wuce wanan "iyaka."
AT: "ba zan yi fahariya da abubuwan da ba mu da iƙo a kansu ko kuwa zan yi fahariya da abubuwan da muke da iƙo a kansu.
"A kan abubuwan da na karkashin iƙon da Allah"
Bulus ya yi magana da iƙo da yake da shi kamar kasa ne da yake mulki. AT: " kuma kuna cikin iyakan iƙon mu"
"ba mu fita a iyakar mu ba"
AT: "yi fahariya akan abubuwa wanda bamu da iƙo a kai" ko kuwa "yi fahariya kadai akan abubuwa wanda muke da iƙo a kai." Dubi yada aka fasara kalmar a cikin 10:13.
AT: "Allah zai kara buɗe bangaren aikin mu kwarai"
"yankin da Allah ya ba wa wani"
"fahariya akan abun da Allah ya yi"
Wannan na nufin cewa ya tanada kowane mutum da ya ji shi ya kuma duba ko ya yi daidai ko bai yi daidai ba. Dubi yadda "shaidar kanmu" aka fasara a nan 4:2.
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "wanda Ubangiji ya yarda"
za ku iya bayana wannan zancen. AT: "wanda Ubangiji ya yi shaidar sa shi ne Ubangiji ya yardajje"
Bulus ya rake cewa yayinda yake gabansu, ba ai ya zama mai tsaurin hali.
Bulus ya yi tunani cewa zai zama mai tsaurin hali a loƙacin da ya yi tsayayya da waɗanda ke zaton suna zama bisa ga jiki.
Bulus da abokan aikinsa basu yi amfani da makamai na jiki a loƙacin da suke yaki ba.
Makaman da Bulus ya yi amfani da shi na da ikon rushe ikokin Shaidan.
Ubangiji ya ba Bulus da abokan aikinsa iko domin su inganta masubi na Korontiyawa, ba domin su rushe su ba.
Waɗansu mutane na cewa, Wasikunsa na da iko da firgitarwa, amma in ka gan shi kumama ne kuma kalmominsa ba abin saurare ba ne.
Bulus ya faɗa cewa abin da ya faɗa a wasika a loƙacin da ba ya nan zai zama yadda zai yi idan ya na tare da masubi na Korontiyawa.
Suna nuna ba su da ganewa saboda suna auna kansu da junansu, suna kuma kwatanta kansu da junansu.
Bulus ya ce fahariyarsu zai zauna a yankin da Allah ya sa su, har ya kai ga Korontiyawa. Bulus ya ce ba za su yi fahariya da aikin wasu ba, akan aikin da aka yi a yankin wani ba.
Bulus ya ce fahariyarsu zai zauna a yankin da Allah ya sa su, har ya kai ga Korontiyawa. Bulus ya ce ba za su yi fahariya da aikin wasu ba, akan aikin da aka yi a yankin wani ba.
Wanda aka amince da shi ne wanda Ubangiji ke shaidarsa.
1 Ina fatan za ku jure da ni cikin wauta kadan. Ko da yake lallai kuna jurewa da ni! 2 Domin ina kishi sabili da ku. Kishi na kuwa irin na Allah ne domin ku. Tun da na alkawartar da ku a cikin aure ga miji daya. Na kuma yi alkawarin in gabatar da ku kamar budurwa mai tsarki ga Almasihu. 3 Gama ina fargaba a kan ku, ko watakila, kamar yadda macijin ya yaudari Hauwa'u ta wurin kissarsa, Ya zamana tunaninku ya kauce daga sahihiyar sadaukarwa ga Almasihu. 4 Anar misali idan wani ya zo ya kawo shelar wani Yesu daban da wanda muka yi maku wa'azinsa. Ko kuma kun karbi wani ruhu daban da wanda muka karba. Ko kuma kun karbi wata bishara daban da wadda muka karba. Amincewar da kuka yi wa wadannan abubuwa ta isa! 5 Don kuwa ina tsammanin ba a baya nake ba ga sauran wadanda ake kira manyan manzanni. 6 To ko ma ba a ilimantar da ni ba akan yin jawabi, ban rasa horarwar ilimi ba. Ta kowace hanya kuma cikin abubuwa duka mun sanar da ku wannan. 7 Na yi zunubi ne da na kaskantar da kai na domin a daukaka ku? Domin na yi maku wa'azin bisharar Allah kyauta. 8 Na yi wa sauran Ikilisiyoyi kwace ta wurin karbar gudummuwa daga wurin su domin inyi maku hidima. 9 Lokacin da ina tare da ku kuma na sami kai na cikin bukata, ban dora wa kowa nauyi ba. Domin 'yan'uwa da suka zo daga Makidoniya sun biya bukatuna. A cikin komai na kebe kaina daga zama nawaya a gare ku, kuma zan cigaba da yin haka. 10 Kamar yadda gaskiyar Almasihu ke ciki na, ba zan yi shiru da wannan fahariya tawa ba a cikin dukan kasar Akaya. 11 Don me? Saboda ba na kaunar ku? Allah ya sani. 12 Amma abinda na ke yi, zan cigaba da yi. Zan yi haka ne domin in yanke zarafin wadanda ke son samun zarafi kamar mu akan abubuwan da suke fahariya da shi. 13 Don irin wadannan mutane manzannin karya ne masu aikin yaudara. Suna badda kama kamar manzannin Almasihu. 14 Wannan ba abin mamaki ba ne, domin shaidan ma yakan badda kama ya fito kamar mala'ikan haske. 15 Ba wani babban abin mamaki ba ne idan bayin sa sun badda kamanninsu don a dauka bayin adalci ne su. Karshen su zai zama sakamakon abin da suka aikata. 16 Ina kara fadi: Kada wani ya yi zaton ni wawa ne. Idan kun yi zaton hakan, to ku dauke ni kamar wawan don inyi fahariya kadan. 17 Abinda nake fadi game da wannan gabagadi mai fahariya ba bisa ga amincewar Ubangiji ba ne, amma ina magana a matsayin wawa. 18 Tun da mutane dayawa suna fahariya bisa ga jiki, ni ma zan yi fahariya. 19 Gama kuna murnar tarayya da wawaye. Ku masu hikima ne! 20 Kuma kuna hakuri da wanda zai bautar da ku, idan ya tauye ku, yana amfani da ku don ribar kansa, idan ya dauki kansa fiye da ku, ko ya mammare ku a fuska. 21 Ina mai cewa mun kunyata da muka rasa gabagadin yi maku haka. Duk da haka idan wani zai yi fahariya-Ina magana kamar wawa-Ni ma zan yi fahariya. 22 Su yahudawa ne? Ni ma haka. Su Isra'ilawa ne? Nima haka. Su zuriyar Ibrahim ne? Nima haka. 23 Su bayin Almasihu ne? (Ina magana kamar ba ni cikin hankalina) na fi su ma. Na ma yi aiki tukuru fiye da su duka, shiga kurkuku fiye da kowa, a shan duka babu misali, a fuskantar haduran mutuwa da yawa. 24 Daga hannun yahudawa sau biyar na sha bulala "Arba'in ba daya". 25 Sau uku na sha dibga da sanduna. Sau daya aka jejjefe ni da duwatsu. Sau uku na yi hadari a jirgin ruwa. Na yi tsawon dare da yini guda a tsakiyar teku. 26 Ina shan tafiye tafiye, cikin hadarin koguna, cikin hadarin 'yan fashi, cikin hadari daga mutane na, cikin hadari daga al'ummai, cikin hadarin birni, cikin hadarin jeji, cikin hadarin teku, cikin hadarin 'yan'uwan karya. 27 Na sami kaina ina aiki tukuru cikin mawuyacin hali, cikin yin dare dayawa ba barci, cikin yunwa da kishin ruwa, cikin yawan azumi, cikin sanyi da tsiraici. 28 Baya ga wadannan duka, akwai nauyi a kaina kullayaumin saboda damuwata akan Ikkilisiyoyi duka. 29 Waye kumama, wanda ban zama kumama akan shi ba? Wanene aka sa yayi tuntube, kuma ban kuna ba? 30 Idan zan yi fahariya, zan yi fahariya akan abinda ke nuna kasawata. 31 Allah kuma Uba na Ubangijinmu Yesu, wanda ya isa yabo har abada, ya san ba karya nake yi ba! 32 A Damasku, gwamnan da ke mulki karkashin sarki Aritas yasa aka yi tsaron birnin Damasku domin a kama ni. 33 Amma ta taga cikin kwando aka ziraro ni bayan ganuwar birni, na kuwa kucce daga hannunsa.
Bulus ya ciba da amince cewa shi monzo ne.
"ku bar ni inyi wauta"
Waɗannan kalmomi na maganan kyaun sha'awa mai karfi ne da Korontiyawa su yi imani da Almasihu, da cewa kadda a tilisa su su barshi.
Bulus na maganar kiyayer masubi na Korontiyawa kamar ya yi wa wani mutum alkawari cewa zai shirya ɗiyar sa domin ta aure shi kuma ya damu cewa mutmin ya iya rike alkawarin. AT: "I na nan kamar uba da ya yi alkawari don ya gabatar da ɗiyar sa ga miji guda. Na kuma yi alkawari in riƙe ku kamar budurwa mai tsarki domin in miƙa ku ga Almasihu"
"Gama ina fargaba kila tunanin ku na iya kauce ga halaka daga gaskiya da kauna mai sarki zuwa ga Almasihu yadda ibilis ya yaudare hauwa'u da wayon sa"
Bulus ya yi maganan tunani kaman dabbobi ne da mutane ke iya kai wa hanyan halaka. AT: "wani na iya sa ku gaskanta karya"
"in wani ya zo da"
"wani ruhu dabam da ba ruhu mai Tsarki ba ko kuwa wani bishara dabam da ku ka karɓa a wurin mu"
"yi da wanan abubuwa." Duba yadda an fasara wannan kalamar 11:1.
Bulus ya yi amfani da maganan nan domin ya nuna cewa mallaman nan ba su da amfani kaman yanda mutanen na fada. AT: "wanɗancan mallamai da suke tunani sun fi kowa goni"
Wannan zancen da ba daidai ba na nanata kyaun gaskiya cewa ya yi horo a cikin ilimi. "ilimi" magana ce da za a iya bayana. AT: "Haƙika ina horo a cikin ilimi"
Bulus ya fara ɗauka da cewa ya lura da korontiyawa da kyau. Ana iya fasara wannan zancen, in da bukata. AT: "Ina tunani mun yadda cewa ban yi zunubi ta wurin kaskanta da kaina na domin a ɗaukaka ku"
"yi maku wa'azin bisharar Allah ba da niyan samun abu ba"
Wannan karuwan zance ne don ya nanata cewa Bulus ya karɓa kuɗi daga ikilisiyoyin da bai kamata su ba shi ba. AT: "Na karɓa kuɗi daga sauran Ikilisiyoyi"
Ana iya bayyana wannan. AT: "Ina iya yin muku hidima ba don komai ba"
"Ban taba zama maku da nawayan kuɗi ba." Bulus na maganan wani wanda wani zai kashe kuɗi kaman wani nauyi abu ne da mutane ke dauka. Ma'anan wannan na a bayyane. AT: "Na yi abin da zan iya domin in tabatar cewa ba ku kashe kuɗi ba domin in iya zama tare da ku"
Watakila waɗannan "'yan'uawa" maza ne duka.
"Ba zan zama ma ku da nawaya ba"
Bulus na nanatawa cewa saboda masu sauraran sa su fahinci cewa yana fadan gaskiya game da Almasihu. Za su sani cewa yana fadan gaskiya ne. "Tun da kun san da cewa na san gaskiyan kuma ina shelar gaskiyan game da Almasihu, za ku iya sani ko abin da zan faɗa gaskiya ne. Wannan"
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. "Ba wanda da zai iya hana ni in yi fahariya har in tsaya shuru.
Wannan na nufin abin da Bulus ya yi magana a 11:7-9.
"yankin Akaya." Kalmar "gaba" na magana wurin kasa, ba rabuwan siyasa ba ne.
Bulus ya yi magana a fakaice don ya nanata kauna ga Korontiyawa. Ana iya hada waɗannan tamboyoyin ko a mai da shi zance. AT: "saboda bana kaunan ku ne ya sa ba na bukatan in nawaita maku?" ko kuwa "zan ci gaba da hana ku biyan bukatu na domin wanan ya nuna wa sauran da cewa ina ƙauna ku."
kuna iya fahimtan sadarwan bayani. AT: " Allah ya sani ina ƙaunar ku."
Bulus ya yi magana akan karya da maƙiyansa sun faɗa ne kamar wani abu ne da ya ɗaukawa. AT: "Domin in iya sa shi mara yiwuwa"
Bayan fahariyan Bulus shine "ya yi wa'azin bishara kyauta" (11:7), abokan gabansa sun yi fahariya cewa su iya yin magana da kyau (11:5).
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "Don mutanen su yi tunanin cewa su nan kaman mu"
" Ina yin abinda na ke yi domin mutane na son su"
"masu aikin rashin gaskiya"
"Ba manzanne ba , ama su na kokari su mai da kansu kaman manzannin"
Da farin wanan a kamanin korou Bulus na nanatawa da cewa Korontiyawa da su shirya saduwa da "monzon karya" masu yawa
"shaidan ba mala'ikan haske ba ne, ama yana kokarin ya mai da kansa kamar mala'ikan haske"
Anan "haske" zance ne na adalci. AT: "mala'ikan haske"
"Bayinsa ba bayin adalci ba ne, ama suna kokarin mai da kansu kamar bayin adalci"
"karbe ni kamar yadda za ku karɓe wawa: Bari in yi magana, ku kuma maida fahariya kalaman wawa"
A nan maganan "jiki" na nufin mutum a cikin sifar zunubi da riɓa sa. AT: "Game da riban mutumtakansu"
"ku karɓe ni in na yi kwoikoyo kaman wawa" Dubi yadda an fasara zance irin wannan a 11:1.
Bulus na kunyatas da Korontiyawa ta wurare dayawa. AT: "Kuna samani cewa kuna da wayo, ama babu"
Bulus ya yi amfani da abubuwa dabam dabam game da yanda wadansu mutane ke tilisa waɗansu su yi biyaya da dokoki kaman su na tilasa su su zama bayi. AT"sa ku ku bi dokoki dan ba daidai ba".
Bulus ya yi maganan game da manyan manzani masu ɗaukan abubuwan mutane kamar suna cin mutanen ne da kansu. AT: "ya dauki dukan malakan ku"
Mutum na amfani da zarafin wani ta wurin sanin abinda wancan bai sani ba da kuma yin amfani da sanin don ya taimake kansa ya kuma jawo ma wacan mutum lahani.
"Na yarda da kunya cewa ba mu iya riƙe ku ba." Bulus yana amfani da magana dabam dabam don ya fada wa Korontiyawa cewa ba don rashin karfin sa ne ya sa ya riƙe su da kyau ba. AT: " Ba na kunya in ce muna da iƙon yin ma ku mugunta ba, ama mun riƙe ku da kyau"
"Ni ma zan yi fahariya da Kowane abinda wani ya yi fahariya"
Bulus ya yi tambayan da Korontiyawa na iya tambay da kuma amsawa domin ya nanata cewa shi dan Yahudawa ne fiye da su manyan-manzanen nan. In ya yiwu ku riƙe tambayan da amsan. AT: "Su na so ku yi tunani cewa suna da amfani kuma ku bada gaskiya akan abinda su ke ce domin su Yahudawa ne da Israilawa daga zuriyar Ibrahim. To, haka nake. Sun ce su bayin Almasihu ne -ina magana kaman ba na cikin hankalina-ama ina fiye"
"kaman bana iya tunani da kyau"
Kuna iya fahimtar da bayanin na sasai. AT: "Ni bawan Almasihu ne fiye da su"
"Na yi aiki tukuru"
"na shiga kurkuku so dayawa"
Wannan karin magana ne, an zuguiguita ta domin a nanata cewa an duke shi so dayawa. AT: "An duke ni so dayawa" ko "An duke so dayawada ya wuce kirge"
"kuma na yi kusan mutuwa so dayawa"
Wannan sanannen magana ne na shan duka sau 39. A dokan Yahudawa ainahin yadda ake yarda a duke mutum a lokaci shi ne tsula arba'in. Sun saba bulalan mutum so talatin da tara domin su zama da laifin bulalan wani so dayawa idan an kirga ba daidai ba.
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "mutane sun dibga ni da sanduna a itace"
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "mutane sun jejejefe ni da duwatsu san da sun zata na mutu"
Bulus na nufin ya kwanta a cikin ruwa bayan da jirgin ta nutse.
Ana iya bayana cikaken ma'anan wannan zancen. AT: "A cikin hatsari daga mutanen da su ka dauke mu yan'uwa a Almasihu, ama sun ci amanar mu"
Bulus ya wuce ne domin ya nuna bukatan suturan sa. AT: "rashin ishashen sutura da zai sa ni dumi"
Bulus ya sani cewa Allah zai kama shi da alhakin yadda ikilisiyoyi su na biyayya da Allah ya kuma yi magana akan wancan sanin kaman abu mai nauyi ne da na tura shi kasa. AT"na san cewa Allah zai tambaye ni don girman ruhanian ikilisiyoyin, Ina yawan ji kaman abu mai nauyi na tura ni kasa"
Ana iya fasara afakaice wannan zancen. AT: "Duk lokacin da wani na kumama, ina jin wanan kumaman ni ma."
Ana iya fasara afakaice wannan zancen. Bulus ya yi amfani da tambayan nan don ya nanata fushin sa a lokacin da an sa dan'uwa maibi yin zunubi. AT: "Ina fushi a duk lokacin da wani ya sa ɗan'uwa yin zunubi."
Bulus ya yi magana game da zunubi kaman yana tuɓe akan abu na kuma fadiwa. AT: "aka kai shi ga zunubi" kokuwa "ya yi sam'mani cewa Allah zai yarda ma shi ya yi zunubi domin abinda wani dabam ya aikata."
Bulus ya yi magana akan jin fushi da zunubi kaman yana da wuta a cikin jikin sa. AT: "Ban na fushi akan sa"
"abinda ke nuna kasawa na"
Bulus na nanata cewa gaskiyane yake fada. AT: "Ina fadin ainahin gaskiyan"
"gwamna wanda sarkin Aritas ya zabi ya fadi wa mazajen su yi tsaron garin"
"domin su rike da kuma kama ni"
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "waɗansu mutane sun sa ni a kwando suka ziraro ni a kasa"
Bulus ya yi anfani da hanuwan gwamnan domin kwatanci na gwamna. AT: "daga gwamna"
Ya na yi masu ƙishi domin ya yi alkawarin gabatar da su kamar budurwa mai tsarki ga Almasihu.
Bulus ya ji tsoro kada tunaninsu ya ƙauce daga sahihiyar sadaukarwa ga Almasihu.
Sun jure wanin da ya zo ya kawo shelar wani Yesu daban da wanda Bulus da abokan aikinsa suka yi masu wa'azinsa.
Bulus ya yi wa Korontiyawa wa'azin bishara a kyauta.
Ya yi masu "kwace" ta wurin karbar gudummuwa daga wurin su domin ya yi wa Korontiyawa hidima.
Bulus ya kwatanta irin waɗannan mutane kamar manzannin ƙarya masu aikin yaudara. Suna sake kama kamar manzannin Almasihu.
Ya na sake kama kamar mala'ikan haske.
Bulus ya ce masu su ƙarbe shi kamar wawa domin ya iya yin fahariya kadan.
Bulus ya ce suna murnar tarayya da wawaye, da kuma wanda zai bautar da su, da wanin da ke sa tsattsaguwa a sikinku, da wanin da ke tauye ku, yana amfani da ku don ribar kansa, ko ya mammare ku a fuska.
Bulus ya yi fahariya cewa shi ba-yahuɗe ne, ɗan Isra'ila kuma zuriyar Ibrahim kamar waɗanda sun so su zama daidai da shi. Bulus ya ce shi bawan Almasihu fiye da su, ya kuma yi aiki tukuru fiye da su duka, ya shiga kurkuku fiye da kowa, a shan duka babu misali, a fuskantar haɗuran mutuwa da yawa.
Daga hannun yahudawa sau biyar Bulus ya sha bulala ''Arba'in ba ɗaya''. Sau uku ya sha dibga da sanduna. Sau ɗaya aka jejjefe shi da ɗuwatsu. Sau uku ya yi haɗari a jirgin ruwa. Ya yi tsawon ɗare da yini guda a tsakiyar teku. Ya na shan tafiye tafiye, cikin haɗarin koguna, cikin haɗarin 'yan fashi, cikin haɗari daga mutane na, cikin haɗari daga al'ummai, cikin haɗarin birni, cikin haɗarin jeji, cikin haɗarin teku, cikin haɗarin 'yan'uwan karya. Ya na kuma cikin haɗarin gwamnan Damasku.
Wanda ke sa wani tuntuɓe ne na sa Bulus kuna.
Bulus ya ce zai yi fahariya akan abinda ke nuna kasawarsa.
Daga hannun yahudawa sau biyar Bulus ya sha bulala ''Arba'in ba ɗaya''. Sau uku ya sha dibga da sanduna. Sau ɗaya aka jejjefe shi da ɗuwatsu. Sau uku ya yi haɗari a jirgin ruwa. Ya yi tsawon ɗare da yini guda a tsakiyar teku. Ya na shan tafiye tafiye, cikin haɗarin koguna, cikin haɗarin 'yan fashi, cikin haɗari daga mutane na, cikin haɗari daga al'ummai, cikin haɗarin birni, cikin haɗarin jeji, cikin haɗarin teku, cikin haɗarin 'yan'uwan karya. Ya na kuma cikin haɗarin gwamnan Damasku.
1 Dole ne in yi fahariya, ko dashike bata da ribar komai. Amma zan ci gaba da wahayoyi da ruyoyi daga Ubangiji. 2 Na san wani mutum cikin Almasihu, wanda shekaru goma sha hudu da suka wuce-ko a cikin jiki ne ko ba a jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani-an dauke shi zuwa sama ta uku. 3 Kuma na san wannan mutumin-ko cikin jiki ko kuma ba cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ya sani- 4 an dauke shi zuwa Firdausi ya kuma ji madaukakan al'amura wadanda ba mai iya fadi. 5 A madadin irin wannan mutumin zan yi fahariya. Amma a madadin kaina ba zan yi fahariya ba, sai dai game da kumamancina. 6 Idan ina so inyi takama, ba zai zama wauta ba, domin gaskiya zan rika fada. Amma zan guje wa fahariya, domin kada wani ya dauke ni fiye da abinda ya gani ko ya ji daga gare ni. 7 Zan kuma gujewa fahariya saboda irin wadannan gagaruman ruyoyi. Domin kada in cika da girman kai, an ba ni kaya cikin jikina, manzon shaidan ya wahalshe ni, domin kada in yi girman kai dayawa. 8 Na roki Ubangiji har sau uku domin ya kawar mini da wannan. 9 Amma ya ce mani, "Alherina isasshe yake a gare ka, domin ta wurin kumamanci karfi yake cika." Don haka zan gwammace takama a akan kasawata, domin ikon Almasihu ya zauna a ciki na. 10 Sabili da haka a gamshe nake ta dalilin Almasihu, cikin kumamanci, ko raini, ko matsaloli, ko jarabobi, ko kuma nawaya. Don ko dayaushe na raunana, ina da karfi kuma. 11 Na zama wawa! Amma ku ne kuka tilasta mani haka, ya kamata ku yabe ni, domin ban kasa ga wadan da ake kira manyan manzanni ba, ko da shike ni ba komai ba ne. 12 Cikakkun alamun mazanni sun faru a tsakanin ku, da cikakken hakuri, alamu da abubuwan ban mamaki da manyan ayyuka. 13 Ta yaya kuka zama da rashin muhimmanci akan sauran Ikkilisiyoyin, sai dai don ban zama matsala a gare ku ba? Ku gafarce ni a kan wannan laifin. 14 Duba! A shirye nake domin in zo gare ku karo na uku. Ba zan so in zamar maku nawaya ba, domin ba kayanku nake so ba. Amma ku nake so. Domin ba 'ya'ya ne ya kamata su yi wa iyaye tanadi ba. Amma iyaye ne ya kamata su yi wa 'ya'ya tanadi. 15 Zan yi murnar biyan bukatunku, ko ya kai ga in bada rai na. Idan ni na kaunace ku, sosai, sai ni za a kaunata kadan? 16 Amma kamar yadda yake, ban nawaita maku ba. Amma, da shike ni mai dabara ne, Ni ne na kama ku da yaudara. 17 Ko na cutar da ku ta wurin wadanda na turo maku? 18 Rokar Titus na yi domin ya zo gare ku, sa'an nan na turo shi da wani dan'uwa. Ko da na turo Titus, ya cutar da ku ne, ba cikin hanya daya muka yi tafiya ba? Ba a sawu daya muka yi tafiya ba? 19 Kuna tsammanin a dukan wannan lokaci muna kare kan mu a gaban ku ne? A gaban Allah, a cikin Almasihu muke fadin komai domin ku sami karfi. 20 Ina tsoro domin idan na zo ba zan same ku yadda nake zato ba. Ina tsoro kuma ba za ku same ni kamar yadda ku ke zato ba. Ina tsoron cewa za a sami gardandami, kishi, barkewar fushi, buri na son kai, gulma, girman kai da yamutsi. 21 Ina tsoron cewa bayan na dawo, Allahna zai iya kaskantar da ni a gaban ku. Ina tsoron cewa zan yi bakinciki domin mutane dayawa da suka yi zunubi kafin yanzu, wadanda kuma ba su tuba daga rashin tsarki da zina da fasikanci da ayyukan sha'awa da suka aikata ba.
Bulus ya cigaba da fadan abubuwa da suka faru da shi tun da ya zam mai bi, a tsaren manzoncin sa daga Allah.
"zan cigaba da magana, ama ba yanzu ba"
AT: 1) Bulus ya yi amfani da kalmomin "ruyoyi" da "wahayoyi" don nufin abu ɗaya a handiyadiyas domin nanatawa. AT: "abubuwan da Ubangiji ya yarda kadai ni in gani" kokuwa 2) Bulus na magana game da abubuwa biyu dabam. AT: "asirtacen abubuwa da Ubangiji ya yadda mani in gani da idanu na da wasu abubauwan asiri da ya yi mani magana akai"
Bulus na magana ne akansa kaman yana yi ne da wani dabam, in ya yiwu a fasara wannan a bisa kalma.
Bulus ya cigaba da yin bayani game da kansa kaman wannan ya faru ne da wani mutum ne. "Ban sani ko wannan mutum yana cikin wannan jiki ne ko kuma jikin ruhaniya ba"
"Allah ne kadai ya sani"
Wannan na nufin mazaunin Allah ba sama ko sarari ba (duniya, tamraru, da duniya).
Bulus ya chigaba da magana game da kan sa kaman yana maganan wani ne dabam.
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: 1) "Allah ya ɗauke wannan mutum ... cikin firdausi" kokuwa 2) malaika ya ɗauke wannan mutum ... chikin firdausi." In ya yu, bai zai kyautu a bada sunan wanda ya ɗauke mutumin ba: "wani ya ɗauki ... firdausi"kokuwa "sun ɗauki ... firdausi."
ba zato ba tsammani da karfi an kamo an ɗauko
AT: 1) sama ko 2) sammai na uku 3) wuri na musamman a sama.
"na wanan mutum"
Ana iya bayana wannan a cikin kyaun aiki. AT: "zan yi fahariya don raunawa na"
"babu wani da zai ba ni amana fiye da abinda ya gani ko ya ji daga gare ni"
"saboda waɖannan ruyoyi suna fiye da kowane abu da wani ya taɓa gani"
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "Allah ya ba ni kaya a cikin jikin" ko kuma "Allah ya barni in sami kaya a cikin jikin"
An kwatanta al'amarin Bulus a bayane kaman kaya da ke huda jiki. AT: "azaba" ko kuma "bayanannan al'amari"
"bawan Shaiɗan"
"su bani azaba"
"girman kai sasai"
A farkon jumla, Bulus ya sa kalmomin nan domin ya nanata cewa yayi addu'a so da yawa domin wannan "ƙaya". (12:7).
"Ubangiji domin wannan ƙayan a cikin jiki," ko kuma " Ubangiji domin wannan wahalan"
"zan yi maka tagomashi, gama abin da ku ke buƙata kenan"
"gama iƙo na ya fi aiki yayin da kuke kumamanci"
Bulus ya yi magana game da iƙon Almasihu kaman rumfa ce da aka gina a kansa. AT: 1) "mutane na iya ganin cewa ina da iƙon Almasihu" ko kuma 2) "Ina iya samu ikon Almasihu."
AT: 1) "a gamshe nake a cikin kumamanci, raini, matsaloli, jarabobi, da kuma mawiyancin yanayi idan wadannan abubuwa sun zo domin ni na Almasihu ne." kokuwa 2) " a gamshe nake cikin kumamanci ... idan wannan abubuwan ya sa mutane su san Almasihu."
"lokacin da ina kumanci"
"lokacin da mutane na kokarin sa ni fushi ta wurin cewan ni mutum ne mara azanci"
"lokacin da ina shan wuya"
"lokacin da akwai husuma"
Bulus na cewa, lokacin da ba shi da karfi sosia domin yin abin da ya kamata, Almasihu, wadda yake da cikakken iko fiye da Bulus, zai yi aiki ta Bulus domin yin abin da ya kamata. Ko da shike, zai fi kyau a fasara kalmomin dalla-dalla, idan yaren ku ta amince.
"Ina yi kaman wawa"
"Kun tilasta mani in yi magana a haka"
Ana iya bayana waanan a cikin sifar aiki. AT: "ya kamata da yabo ne kun bani"
AT: 1) "yabo" (3:1) kokuwa 2) "shaida" (4:1).
Ta wurin anfani da wata hanya, Bulus yana fada da karfi cewa Korantiyawa da su ke tunani cewa bai isa ba sun yi kuskure. AT: "gama ina da kyau kaman"
Bulus ya yi amfani da maganan nan domin ya nuna cewa mallaman nan ba su da mahimmanci kaman yadda mutane na fadɖa. Dubi yadda wannan an yi fasarar sa a 11:5.AT: "mallaman nan da waɗansu ke tunani cewa sun fi kowa"
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki, a kan "alamun." AT: "alamun gaskiya ne ina yi"
yi amfani da kalman a lokaci daya.
Waɗannan su ne "alamun gaskiya na manzo" da Bulus ya yi "da cikaken hakuri"
Bulus na nanata cewa Korontiyawa sun yi kuskure ta wurin zargin shi cewa ya na so ya yi masu lahani. Ana iya fasara zancen atacaike. AT: "Na yi muku kamar yadda na yi wa sauran iklisiyoyi, sai dai ... ku."
"Ban roƙe ku kuɗi ko sauran abubuwa da na ke buƙ ata ba"
Bulus ya yi zance haka ne domin ya kunyatar da Korontiyawa.Shi da su duk sun sani cewa bai yi masu laifi ba, amma suna yi ta masa kaman wadda ya yi masu laifi su.
rashin tambayan su kuɗi da kuma sauran abin da ya ke buƙata
Cikakken ma'anar wannan na a bayyayane. AT: "Abinda nake so shine ku ƙaunace ni ku kuma karɓe ni"
Ba raganar 'ya'ya ne su tara kudi ko wasu abubuwa domin su ba wa lafiyayun iyayen su ba.
Bulus na maganan aikin sa da kuma rayuwar sa kamar kudin ne da shi ko Allah na iya kashewa. AT: "Zan yi ko wace aiki da murna, da kuma murna in yadda Allah ya amince wa mutane su kashe ni"
Kalmar "rayukanku" na matsayin mutane da kan su. AT: "sabili da ku" ko kuma "domin ku zauna lafiya"
Ana iya fasara wannan maganan kaman zance. AT: "idan ina ƙaunan ku sosai, kadda ku ƙaunace ni kadan." ko kuwa "idan ... sosai, ku ƙaunace ni fiye da ku ke yi."
Ba a bayyane ya ke ba cewa kaunar Bulus yana nan "sosai" fiye. Zai fi kyau idan an yi amfani da "mai yawa" ko kuwa "da yawa" za a iya kamantawa da "kankani" a maganan.
Bulus ya yi amfani da wannan zance domin ya kunyatar da Korontiyawa da suke tunani ya yi masu kariya ko da shike bai roƙe su kuɗi ba. AT: "Amma waɗansu na tunanin na yaudaresu kuma na yi amfani da dabara"
Bulus da Korontiyawa sun san amsan kariya ce. Ana iya fasarar wannan maganan kaman zance.AT: "Babu wani da na aiko wurin ku da ya zalunce ku!" )
Bulus da Korontiyawan su san cewa ansar a'a ne. Ana iya fasara wannan magana kaman zance. AT: "Titus bai zalunce ku ba."
Bulus na maganan rayuwa kaman tafiya a kan hanya.Bulus da Korontiyawa sun san amsan tambayan gaskiya ne. Ana iya fasra wannan magana kaman zance. AT: "Dukan mu muna da irin hali iri daya kuma muna rayuwa iri daya."
Bulus ya yi maganan rayuwa kaman tafiya a kan hanya.Bulus da Korontiyawa sun san amsan tambayan i ne. Ana iya fasara wannan magananar kamar zance. AT: "Mu na yin abu iri ɗaya."
Bulus ya yi amfani da wannan tambayan domin ya nuna wani abu da mutanen ke ta tunani. Ya yi wannan domin ya tabatar masu cewa ba gaskiya bane. AT: "watakila kuna tunani dukkan wannan lokaci da cewa muna kare kanmu daga gare ku n."
Bulus yayi magana game da sanin komai na Allah da Bulus ya ke yi kaman Allah na nan a bayyane kuma ya na duban komai da Bulus ya ke faɗa da kuma aikata. AT: "A gaban Allah" ko koma "Da Allah mai shaida" ko kuma "A gaban Allah"
"Don karfafa ku." Bulus yayi maganan sanin yadda za'a bi Allah da kuma marmarin binsa kaman girma ta jiki ne. AT: "Saboda ku san Allah ku kuma yi bi shi da kyau"
"ba zan so abinda na samu ba" ko kuma "ba zan so abin da na gan ku na yi ba"
"ba za ku so abin da kun gani a kai na ba"
kwatancin gardandami, kishi, barkewar fushi, buri na son kai, gulma, girman kai da yamutsi" ana iya fasara su ta yanyer ayuka. AT: 1) "waɗansun ku za su yi gardama da mu, su ji kishin mu, nan da nan su yi fushi da mu, yin magana game da rayuwan mu na girman kai, da kuma jayayya da mu yayin da muke kokarin jagorantar ku" kokuwa 2) "wadan sun ku za su yi gardama da juna, suna maganar tsirin rayuwar juna, da girman kai, da kuma jayayya da waɗanda Allah ya zabe su yi jagora"
"zan yi bakin ciki domin yawancin su ba su bar tsoƒoƒin zunuban su ba"
AT: 1) Bulus na fadin kusan abu daya son uku domin nanatawa. AT: "Ba su bar aikata zunubin zina da suke yi ba" ko kuwa 2) Bulus na maganan zunubai kashi uku.
Anan iya bayana kalman tsarki kaman "abubuwan da ba su gamshi Allah ba." AT: "na yin tunani a tsirance game da sha'awan abubuwan da ba za su gamshi Allah ba"
Maganan "fasikanci" ana iya fasara ta kaman "ayuka mara kyau." AT: "na yin ayukan zina da fasikanci"
Ana iya fasara Kwatancin "aikata" ta wata kalma. AT: "na ... yin abubuwan da ze sa jin dadin fasikanci"
Bulus ya ce zai cigaba da fahariya game da wahayoyi da ruyoyi daga Ubangiji.
An dauke shi zuwa sama ta uku.
Bulus ya ce ba zai zama wauta idan ya yi fahariya ba domin gaskiya zai rika faɗa.
An ba Bulus kaya cikin jikinsa, manzon Shaidan domin ya wahalshe shi.
Bulus ya ce ya gwammace yin takama a akan kasawarsa, domin ikon Almasihu ya zauna a ciki sa.
Ubangiji ya ce wa Bulus, "Alherina isasshe yake a gare ka, domin ta wurin kumamanci ƙarfi yake cika."
Alamu da abubuwan ban mamaki da manyan ayyuka, cikakkun alamun mazanni sun faru a tsakanin ku, da cikakken hakuri.
Bulus ya faɗa wannan domin ba kayansu yake so ba. Su yake so.
Bulus ya ce zai yi farincikin biyan bukatunsu, ko ya kai ga bada ransa.
Bulus ya faɗa dukka waɗannan abubuwa domin ya gina masubi na Korontiyawa.
Bulus ya ji tsoro cewa zai iya sami gardandami, ƙishi, barkewar fushi, buri na son kai, gulma, girman kai da yamutsi.
Bulus ya ji tsoro cewa ba su tuba daga rashin tsarki da zina da fasikanci da ayyukan sha'awa da suke aikata ba.
Bulus ya na tsoro cewa Allah zai iya ƙasƙantar da shi a gaban masubi na Korontiyawa.
1 Wannan ne karo na uku da nake zuwa gare ku, "Ana tabbatar da kowanne zargi ta bakin shaidu biyu ko uku." 2 Na riga na yi magana a baya da wadanda suka yi zunubi da kuma sauran a lokacin da ina tare da ku karo na biyu, kuma ina sake fadi: Idan na sake zuwa, ba zan raga masu ba. 3 Ina fadi maku wannan ne domin kuna neman shaida ko Almasihu na magana ta bakina. Shi ba kasashshe bane zuwa gare ku. Maimakon haka, Shi mai iko ne a cikin ku. 4 Domin an gicciye shi cikin kasawa, amma yana da rai ta ikon Allah. Don mu ma kasassu ne a cikin shi, amma za mu rayu tare da shi cikin ikon Allah dake cikinku. 5 Ku auna kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya. Ku yi wa kanku gwaji. Ba ku lura da cewa Yesu Almasihu yana cikin ku ba? Yana cikin ku, sai dai in ba a amince da ku ba. 6 Gama ina da gabagadin cewa za ku iske an amince da mu. 7 Ina addu'a ga Allah cewa ba za a same ku da laifi ba. Ba wai ina rokon mu bayyana kamar mun ci gwadawar ba. Maimakon haka, ina addu'a ku yi abinda ke dai dai, ko dayake mun yi kamar mun fadi gwadawar. 8 Domin bamu iya yin wani abu na tsayayya da gaskiya ba, sai dai mu yi domin gaskiya. 9 Muna farin ciki idan mun kasa ku kuma kun yi karfi. Muna addu'a kuma domin ku kammalu. 10 Na rubuta wadannan abubuwa yayinda ba ni tare da ku, saboda yayin da zan kasance da ku ba zan zamar maku mai fada ba. Ba na so inyi amfani da ikon da Ubangiji ya bani in tsattsaga ku, sai dai in gina ku. 11 A karshe, 'yan'uwa, ku yi farinciki, ku yi aiki don sabuntuwa, ku karfafa, ku yarda da juna, ku zauna cikin salama. Kuma Allahn kauna da salama zai kasance tare da ku. 12 Ku gai da juna da tsattsarkar sumba. 13 Masu bi duka suna gaishe ku. 14 Bari alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da kaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.
Bulus ya shinfida da cewa Almasihu na magana ta wurin sa, da kuma cewa Bulus yana son ya tsada su, ya karfafa su da kuma sa su yi zamantakewa.
Ana iya iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "Ku gaskanta cewa wani ya yi abu mummuna bayan mutum biyu ko uku sun fada abu iri ɗaya"
"ya ku dukkan sauran mutane"
Ana iya sa wannan a aiki. AT: "sun gicciye shi"
Allah ya ba mu iƙo da hikimar don mu yi rayuwa a ciki da kuma tare da shi.
Bulus ya yi tambaya domin ya nanata zancen sa AT: " ku san cewa Yesu Almasihu yana cikin ku" ko kuma "Yesu Almasihu yana cikin ku. Ya kamata kun riga kun sani!"
AT: 1) rayuwa a cikin kowane mutum 2) "tsakani ku," sakani da muhimmin mutum na kungiya.
"cewa ba za kuyi zunubi ko kadan" ko kuma" cewa ba za ku ki jin mu a lokacin da muke kwaɓe ku ba." Bulus yana nanata bambam zancen sa. AT "cewa za ku yi dukkan kamai daidai"
"zama kwararan mallamai da yin rayuwan gaskiya"
"bamu iya yin abun da ze hana mutane koyan gaskiya ba"
"gaskiya; dukkan abun da muke yi zai sa mutane su koyi gaskiyar"
"domin ku yi girma a cikin ruhania"
"idan na yi amfani da iƙo na"
Bulus ya yi maganan taimaka wa Korontiyawa don su san Almasihu da kyau kaman yana aikin gini. Dubi yanda an fasara irin wannan magana a 10:8 AT: " domin a taimake ku ku zama ainahin mabiyan Almasihu ba a sa ku fit da rai don ku daina binsa ba."
"yi aikin kaiwa ga girma"
"yi rayuwar jituwa da junna"
"da ƙauna ta Masubi"
" waɗanda Allah ya kabe wa kansa"
Bulus ya rigaya zo masu sau biyu a loƙacin da an rubuta Korontiyawa ta 2.
Bulus ya faɗa masu wannan domin masubi na Korontiyawa su neman shaida ko Almasihu na magana ta wurin Bulus.
Bulus ya ce masu su auna kansu su gani ko suna cikin bangaskiya.
Bulus ya amince cewa masubi na Korontiyawa za su san cewa an yarda da su.
Bulus ya ce ba su iya yin wani abu na tsayayya da gaskiya ba, sai dai mu yi domin gaskiya.
Bulus ya so ya yi amfani da ikon da Ubangiji ya bashi domin ya gina masubi na Korontiyawa ba kuwa ya tsattsage su ba.
Bulus ya yi haka saboda yayin da zai kasance da su ba zai zama masu mai fada ba.
Bulus ya na so su yi farinciki, su yi aiki don sabuntuwa, su karfafa, su yarda da juna, su zauna cikin salama, su kuma gai da juna da tsattsarkar sumba.
Bulus ya so su sami dukka alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki.
1 Wannan Bulus manzo ne. Manzancina kuwa, bai zo daga mutane ba ko mutum, amma ta wurin Yesu Almasihu da Allah Uba wanda da ya tashe shi daga matattu. 2 Ni da dukan 'yan'uwa da nake tare da su a nan, ina rubuto maku ku iklisiyoyi da ke a Galatiya. 3 Alheri zuwa gare ku da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangjinmu Yesu Almasihu, 4 wanda ya ba da kansa domin zunubanmu saboda ya kubutar da mu daga wannan mugun zamani, bisa ga nufin Allah da Ubanmu. 5 Daukaka ta tabbata a gare shi har abada abadin. 6 Na yi mamaki kwarai yadda kuka juya da sauri zuwa wata bishara daban. Na yi mamakin cewa kuna juyawa daga shi wanda ya kira ku ta wurin alherin Almasihu. 7 Ba wata bishara, amma akwai wadansu mutane da suke kawo maku rudani kuma suna so su gurbata bisharar Almasihu. 8 Amma, ko da mu ne ko mala'ika daga sama ya yi maku shelar wata bishara ta daban da wadda muka yi shelar ta, la'ananne ne. 9 Kamar yadda muka fadi maku a da, yanzu kuma ina sake fada, "Idan wani ya yi maku shelar wata bishara ta daban da wadda kuka karba, la'ananne ne." 10 To yanzu ina neman shaidar mutane ne ko Allah? Ina neman in gamshi mutane ne? Idan har yanzu ina kokarin in gamshi mutane ne, ni ba bawan Almasihu ba ne. 11 Ina son ku sani fa 'yan'uwa, cewa bisharar da nake shelar ta ba daga mutane take ba. 12 Ban karbe ta daga mutum ba, ba ma wanda ya koyar mani A maimakon haka, ta wurin wahayin Yesu Almasihu ne zuwa gare ni. 13 Kun riga kun ji game da rayuwa ta a da cikin Yahudanci, yadda da nake da kwazon tsananta wa iklisiyar Allah fiye da misali kuma ina lalatar da ita. 14 Ina gaba-gaba cikin Yahudanci fiye da yawancin tsararrakina. A kwazo kuwa fiye da kima game da al'adun ubannina. 15 Amma ya gamshi Allah ya zabe ni daga cikin mahaifiyata. Ya kira ni ta wurin alherinsa. 16 Ya bayyana dansa a gareni, saboda in yi shelar sa cikin al'ummai. Nan da nan, ban nemi shawarar nama da jini ba 17 kuma ban tafi Urushalima ba wurin wadanda suka zama manzanni kafin ni. Maimakon haka sai na tafi Arebiya, daga nan sai na dawo Dimashku. 18 Bayan shekara uku na je Urushalima don in san Kefas, na zauna da shi na kwana goma sha biyar. 19 Amma ban ga ko daya daga cikin manzannin ba sai Yakubu kadai, dan'uwan Ubangiji. 20 Duba, a gaban Allah, ba karya nake yi ba cikin abin da na rubuta maku. 21 Daga nan sai na je lardin Suriya da Kilikiya. 22 Har a lokacin babu wanda ya san ni a fuska a iklisiyoyin Yahudiya da suke cikin Almasihu, 23 amma sai labari kawai suke ji, "Wanda a da yake tsananta mana yanzu yana shelar bangaskiyar da a da yake rusarwa." 24 Suna ta daukaka Allah saboda ni.
Bulus, wani manzo ya rubuta wannan wasika zuwa ga ikkilisiyu da ke yankin Galatiya.
"wanda ya sa shi ya rayu kuma"
Nan, wannan na nufin 'yan'uwanmu Krista maza da mata, tunda shike a cikin Kristi duk masubi 'yan iyali daya ne a ruhaniya, kamar yadda Allah shi ne Ubansu na samaniya. AT: "ɗan'uwa da yar'uwa"
"Zunubai" na iya ba da ra'ayi cewa hukuncin zunubi. AT: "ɗaukar hukunci da ya cancanci zunuban mu"
A nan "wannan ... zamani" na bayana iƙokin da ke aiki a cikin zamanin. AT: "domin ya kawo mu ga kariya daga mugayen iƙoki da ke aiki a cikin duniya ta yau"
Wannan yana nufin "Allah Ubanmu". Shi ne Allahnmu da Ubanmu.
Bulus ya ba da dalilin rubuta wannan wasika: yana tunashe su cewa su ci gaba da fahimtar bishara.
" Na yi mamaki" ko kuma "Na gigice." Bulus ya ji kunyan abin da su ke yi.
A nan "juyawa...daga gareshi" na siffanta fara shakka ko kuma rashin dogara ga Allah. AT: "kuka fara saurin shakkan sa"
"Allah, wanda ya kira ku"
A nan wannan na nufin Allah ya nada ko kuma ya zabi mutane su zama yayansa, su bauta masa, da kuma shela kalmarsa na ceto ta wurin Yesu.
"saboda Alherin Almasihu" ko kuma "saboda hadayan alherin Almasihu"
A nan "juyawa zuwa" na siffanta fara gaskanta ga wani abu. AT: "kun kuma fara gaskanta wata bishara daban"
"wasu mutane"
Wannan na bayana abin da bai faru ba kuma ka da ya faru. AT: "da shela" ko kuma "zai shela"
"daban daga bishara" or "daban daga sakon"
"Allah ya hukuta wannan mutumin har abada. "idan akwai yadda aka saba la'ance wani a harshen Hausa, za a iya mora anan.
Waɗannan tambayoyi a takaice na buƙatar amsan "a'a." AT: "bana neman shaidar mutane, amma ina bidar shaidar Allah. Bana neman in gamshi mutane?."
kalmomin nan "idan" da kuma "to" na nuna abin da ba gaskiya ba. "har yanzu bana kokari in gamshi mutane; Ni bawan Almasihu ne" ko kuma "Idan har yanzu ina kokarin gamshi mutane, to ba zan zama bawan Almasihu ba"
Yin amfani da wannan kalmar bai nuna wai Bulus na kokarin cewa Yesu Almasihu da kansa ba mutum bane. Domin Almasihu mutum ne kuma Allah me, duk da haka shi ba mutum mai zunubi bane. Bulus na rubutu game da inda bishara ta fito; da cewa ba daga wasu mutane masu zunubi bane, amma daga Yesu Almasihu.
Zai yiwu ana nufin 1) "Yesu Almasihu da kanshi ne ya bani wahayin bishara" ko kuma 2) "Allah ya sa mun sannin bishara lokacin da ya nuna mun ko wanene Yesu Almasihu."
"hali a wata lokaci" ko kuma "rayuwa kafin yanzu" ko kuma "farkon rayuwa"
Wannan wuri na bada hutun Bulus ya kasance a gaba da Yahudawa da suka tsaran shi wanda suke da manufan zama cikakkun Yahudawa.
"Yahudawa da suke tsara ɗaya da ni
"kakanina"
Zai yiwu ana nufin 1) "Allah ya kira ni in bauta masa domin alherensa" ko kuma 2) "Ya kira ni ta hayar alherinsa."
Zai yiwu ana nufin 1) "bani damar sannin Ɗan sa ko kuma 2) nuna wa duniya ta wurina cewa Yesu Ɗan Allah ne."
Wannan muhimmin lakabi ne na Yesu, Ɗan Allah.
"shelar cewa shi Ɗan Allah ne" ko kuma "wa'azin bishara game da Ɗan Allah"
Wannan furci ne da ke nufin magana da waɗansu. AT: "tambayar mutane su taya ni fahimtar sakon"
"tafi Urushalima." Urushalima na yakin tudai masu tsawo, ya zama wajibi ne a hau tudai da yawa domin a iya isa, shi yasa an saba bayyana tafiya zuwa Urushalima kamar " hauwa zuwa Urushalima."
Wannan musu da ke da baki biyu na haddada cewa Yakubu ne kadai manzon da Bulus ya gani. AT: "manzon da na iya gani kawai shi ne Yakubu"
Bulus na son Galatiyawa su gane cewa ba karya yake yi ba, kuma ya san cewa Allah na jin abin da ya faɗi kuma zai hukunta shi idan bai faɗi gaskiya ba.
Bulus yayi amfani da irin kalmonin nan domin ya nanata cewa abin da yake faɗi gaskiyace. AT: "ba karya na ke yi maku ba a sakon da na rubuta ma ku" ko kuma "game da abubuwan da na rubuta ma ku gaskiya ne na ke faɗi"
"sashin duniya da ake kira"
"amma sun san iyakan abin da suka ji wasu na faɗa game da ni"
"cikin mutane ikilisiyun Yahudiya da suke cikin Almasihu babu wanda ya taɓa saduwa da ni"
Bulus ya zama manzo ta wurin Yesu Almasihu da kuma Allah Uba.
An kubutar da masubi a cikin Yesu Almasihu daga wannan mugun zamani.
Bulus ya na mamaki cewa sun juya da sauri zuwa wata bishara daban.
Akwai bisharan gaskiya ɗaya kadai, bisharar Almasihu.
Bulus ya ce a la'anta duka wanda ya yi shelar wata bishara daban.
Ɗole bayin Allah su fara neman amincewar Allah.
Bulus ya ƙarbi bisharar Almasihu ta wurin wahayin Yesu Almasihu zuwa gare shi.
Bulus na bin Yahudanci da ƙwazo, da tsananta wa iklisiyar Allah.
Ya gamshe Allah ya zaɓe Bulus daga cikin mahai'fiyarsa don ya zama manzo.
Allah ya zaɓi Bulus ya zama manzonsa saboda ya yi shelar Almasihu a cikin al'ummai.
A karshe, Bulus ya je Urushalima ya kuma sadu da manzo Kefas da Yakub.
Ikilisiyoyi a Yahudiya su na jin cewa wai Bulus wanda a da yake tsananta wa ikilisiya, yanzu yana shelar bangaskiyan.
1 Daga nan, bayan shekara goma sha hudu na koma Urushalima tare da Barnaba. Na kuma dauki Titus tare da ni. 2 Na koma ne domin Allah ya nuna mani in koma. Sai na gabatar masu shelar bisharan da nake yi a cikin al'ummai. (Amma a kebe na yi magana da wadanda aka dauka muhimman shugabanni). Na yi haka ne domin in tabbatar da cewa ba gudun banza nake yi ba, ko kuma na yi gudun banza. 3 Amma ko Titus wanda yake tare da ni, Baheline, ba wanda ya tilasta masa ya yi kaciya. 4 Wannan maganar ta taso ne daga 'yan'uwan karya da suka zo cikinmu a boye su ga 'yancin mu a cikin Yesu Almsihu. Sun yi marmarin su maishe mu bayi ga doka. 5 Ba mu mika kanmu biyayya gare su ba ko da na sa'a daya, domin gaskiyar bishara ta kasance babu canzawa domin ku. 6 Amma su wadanda a ke ganin su da muhimmanci ba su taimaka mani da komai ba. Ko su wanene su bai dame ni ba. Allah ba ya karbar wanda mutane suka fi so. 7 Maimakon haka, suka ga an danka mani shelar bishara ga wadanda ba su da kaciya. Kamar yadda aka ba Bitrus shelar bishara ga masu kaciya. 8 Gama Allah wanda yake yin aiki a cikin Bitrus domin manzanci zuwa ga masu kaciya, haka kuma yake aiki ciki na zuwa ga al'ummai. 9 Da Yakubu, Kefas, da Yahaya, wadanda a ke gani masu gina ikilisiya, suka fahimci alherin da aka ba ni, suka bamu hannun dama na zumunci ni da Barnaba, Sun yi haka ne kawai domin mu mu tafi zuwa wurin al'ummai, su kuma su je wurin masu kaciya. 10 Suna kuma so mu tuna da matalauta. Ni ma ina da aniyar yin haka. 11 Da Kefas ya kai Antakiya, na yi tsayayya da shi a gabansa domin shine ke da kuskure. 12 Da ma Kefas yana cin abinci tare da al'ummai kafin zuwan wasu mutane daga wurin Yakubu. Amma da wadannan mutane suka iso, sai ya dena kuma ya ware kansa daga al'umman. Yana jin tsoron wadannan mutanen da ke bukatar kaciya. 13 Hakannan ma sauran Yahudawa da suke tare da shi sun bi munafurcin sa. A sakamakon haka Barnaba ma ya bi munafurcin su. 14 Da na ga basu bin gaskiyar da take cikin bisharar, na gaya wa Kefas a gaban su duka, "Idan kai Bayahude ne kana rayuwar ka ta al'ummai a maimakon rayuwar Yahudawa, to ta yaya za ka tilasta wa al'ummai su yi zaman Yahudawa?" 15 Mu da muke Yahudawa daga haihuwa, ba "Al'ummai masu zunubi ba." 16 Ku sani fa, babu wanda za a baratar ta ayyukan shari'a. A maimakon haka an baratar da su ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu. Mun zo ga cikin Almasihu Yesu domin mu samu baratarwa ta bangaskiya cikin Almasihu, kuma ba ta ayyukan shari'a ba. Domin ta ayyukan shari'a babu wanda zai samu baratarwa. 17 Amma idan mun nemi Allah ya baratar da mu cikin Almasihu, mun samu kanmu masu zunubi kenan, Almasihu ya zama bawan zunubi ne? Ko kadan! 18 Idan na sake gina dogara ta a kan shari'a, dogarar da na juya wa baya, na nuna kai na mai karya shari'a kenan. 19 Ta wurin shari'a na mutu ga shari'a, domin in yi rayuwa irin ta Allah. 20 An giciye ni tare da Almasihu, ba nine ke rayuwa ba kuma, amma Almasihu ke rayuwa a cikina. Rayuwar da nake yi a yanzu a cikin jiki, ina yin ta ne, ta wurin bangaskiya ga dan Allah, wanda ya kaunace ni ya ba da kansa domina. 21 Ban yi watsi da alherin Allah ba, domin idan adalci ya wanzu ta wurin shari'a, ashe Almasihu ya mutu a banza kenan.
Bulus ya cigaba da bayas da tarihin yada ya koyi bishara daga Allah ba manzane ba.
"tafiya." Urushalima wuri ne mai tudai a kasan. Yahudawa kuma suna ganin Urushalima wuri ne a kasa da yafi kusa da sama, zai yiwu Bulus na bada misali ne, ko kuma bada huton wuyan hauwa tudu, a tafiya don a isa Urushalima.
" mafi muhimmancin shugabanni a cikin masubi"
Bulus yayi amfani da kalmar gudu a manufar aiki, kuma ya yi amfani da kalmar musu mai baki biyu domin ya nanata cewa aikin da ya yi na da riɓa. AT: "Na dinga yi, ko kuma da na yi, aikin riɓa ce"
"da ba amfani" ko kuma "ba na kome ba"
za a iya bayyana wannan a ... AT: "a sami wani ya masa kaciya"
"mutanen da suke yaudaran kansu wai su masubi ne su ka shi go Iklisiya", ko kuma "mutane da suke yaudaran kansu wai su masubi ne sun zo cikin mu"
duban mutane a boye don a ga yadda suke zaman 'yanci
'yanci
"Waɗannan masu duba a boye sun yi marmarin" ko kuma "waɗannan 'yan'uwan karya na son"
" a maishe bayi ga doka." Bulus na magana game da tilasawa ga bin al'adun yahudanci da doka ya umurta. Ya na magana game da wannan kamar bauta. al'adan da ya fi muhimminci shi ne kaciya. "tilastamu mu yi biyyaya da doka"
"biyyaya" ko kuma "saurara"
kalmar "ni" anan na bayyani abin da Bulus ke koyaswa. AT: "bai kara komai ba a abin da na koyas" ko kuma "bai gaya mun in kara wani abu ba a abin da na koyas"
"maimako" ko kuma "gwamma"
za iya ambatan wannan cikin aiki, AT: "Allah ya ɗanka mani"
Su mutane ne wanda suka koyas game da Yesu kuma suka tabbatar da mutane su gaskanta cikin Jesus.
za a iya fasara wannan kalmar "Alheri" a kalmar aikatau "yin kirki." AT: "fahimci cewa Allah ya yi mani kirki"
za a iya ambacin wannan cikin aiki. AT: "Alherin da Allah ya ba ni"
riƙe hannun dama kankan alamar zumunci ne. AT: "marabta ...kamar abokan aiki" ko kuma "marabta ...da daraja"
"hannun damar su"
Zai iya buƙace ka bayyana abin da zai tuna game da matalauta. AT: "tuna a lura da bukatun matalauta"
kalmomin nan "a fuskar sa" na bada ra'ayin "wurin da zai iya gani ya kuma ji shi." AT: "Na fuskance shi da kanshi" ko kuma "Na yi tsayaya da ayyukan sa da kaina"
ɗangane da lokaci
"ya dena ci tare da su"
za a iya bayyana dalilin da ya sa Kefas ya ji tsoro haka. AT: "Yana tsoron cewa waɗannan mutane da suke buƙatan kaciya za su sha'ranta shi da yin abin da ba daidai ba" ko kuma " Yana tsoron waɗannan mutane da suke buƙatar kaciya za su bashi laifi domin abubuwan da ya ke yi ba daidai ba" Dubi:
Yahudawan da suka zama masu bi, amma su na buƙatan waɗanda su ka ba da gaskiya cikin Almasihu su yi zama bisa ga al'adun Yahudawa
"zauna baya daga" ko kuma "ƙauce wa"
Anan aka "ciwo" na bayyana rinjaya a yin abin da ba daidai ba. Ana iya bayyana wannan kalmar "ciwo" cikin aiki. AT: "Har Barnaba ya yi kamar su a yin abin da ba daidai ba"
"ba sa rayuwa kamar mutanen da suka gaskanta da bishara" ko kuma "suna rayuwa kamar ba su gaskanta da bishara ba"
Wannan tambaya ne da baya buƙatar amsa tsautawa ne kuma za a iya fassara kamar sanarwa. kalman "ka" na nufin Bitrus. AT: " ba ka yi daidai ba da tilasta Al'ummai su yi rayuwa kamar Yahudawa."
Ya ka iya nufin 1) tilasta ta wurin amfani da kalmomi ko kuma 2) rinjayi.
"ba waɗanda Yahudawa su ke kiran su Al'ummai masu zunubi ba"
"mun gaskanta cikin Almasihu Yesu"
Wannan na nufin mai yiwuwa Bulus ne da wasu amma ba Galatiyawa ba, wanda su da farko Al'ummai ne Dubi:
Kalman "ɗan adam" na nufin gabadayan mutum. AT: "ba mutum"
kalman "baratawa cikin Almasihu" na nufin baratawa domin muna tare da Almasihu aka barata da mu ta dalilin Almasihu.
Kalmomin "an tarar da" na nanata cewa "mu na" lalle ne da zunubi. AT: "mun ga cewa mu ma lallai musa zunubi ne"
"i mana, wannan ba gaskiya ba!" Wannan magana na ba da karfin musun amsa ga tambaya da aka riga yi "Almasihu ya zama bawar zunubi ne? za ku iya amfani da yadda ake yin irin wannan magana a harsha da ku ke amfani da ita.
Wannan lakabi ne mai muhimmanci na Yesu.
Bulus ya ambata kalmar musu domin ya nanata gaskiyar. AT: "Na tabbatar da darajan"
Bulus na bayyana yanayin da bai taɓa faruwa ba.
"inda mutane za su iya zama adalai ta wurin biyyaya da shari'a"
"ashe da Almasihu bai cika komai ba tawurin mutuwa"
Bulus ya yi magana da shugabannin ikilisiya a ɓoye, da bayana masu shelar bisharan da yake yi.
Ba a so Titus ya yi kaciya.
Maƙaryatan 'Yan'uwan suna so su maishe Bulus da abokansa ɓayi ga doka.
A'a, basu kara komai a sakon Bulus ba.
Da farko, an aika Bitrus ya yi shelar bishara ga waɗanda suka yi kaciya don.
Shugabanin Urushalima sun ba Bulus da Barnaba hannun dama na zumunci don su nuna yardansu.
Bitrus ya dena cin abinci da al'ummen domin ya ji tsoron mutanen da suka yi kaciya.
Bulus ya tambaye Kefas yadda ya tilasta al'umman su yi zama kaman Yahudawa bayan Kefas na rayuwa kamar ɗan al'umma.
Bulus ya ce babu wanda ake baratarwa ta wurin ayukan doka.
Mutum na barata ne a gaban Allah ta wurin bangaskiya a Almasihu Yesu.
Bulus ya ce ya nuna kanasa mai karya shari'a.
Bulus ya ce yanzu Almasihu ne ke rayuwa a cikinsa.
Bulus ya ce Ɗan Allah ya ƙaunace shi ya kuma ba da kansa domin Bulus.
1 Ku Galatiyawa marasa wayo! Wanne mugun ido ya cuce ku? Ashe, ba Yesu Almasihu gicciyayye aka nuna a gaban idon ku ba? 2 Ina so in gane wannan daga wurin ku ne kawai. Kun karbi Ruhun ta wurin ayyukan doka ne ko ta wurin ba da gaskiya ga abin da kuka ji? 3 Rashin wayonku ya yi yawa haka ne? Kun fara da Ruhu, sai kuma yanzu ku karasa a cikin jiki? 4 Kun fuskanci abubuwa da yawa a banza ne - har idan a banza ne? 5 To, shi wanda ya ba ku Ruhun, da ayyuka masu iko a tsakanin ku, ya yi ne ta wurin ayyukan shari'a ko ta wurin ji tare da bangaskiya? 6 Ibrahim "ya ba da gaskiya ga Allah, kuma an lisafta mashi wannan a matsayin adalci." 7 Ta wannan hanya ku fahimta su wadanda suka ba da gaskiya, 'ya'yan Ibrahim ne. 8 Nassi ya riga ya hangi gaba cewa, ta wurin bangaskiya Allah zai baratar da Al'ummai. An yi wa Ibrahim shelar bishara tuntuni: "A cikinka ne dukan al'ummai za su yi albarka." 9 Saboda haka, wadanda suka ba da gaskiya, masu albarka ne tare da Ibrahim wanda ke da bangaskiya. 10 La'ana na kan wadanda sun dangana ga ayyukan shari'a. Gama a rubuce yake, "La'ananne ne kowanne mutum da bai tsaya ga duk abin da ke a rubuce cikin littafin shari'a ba, ya kuma aikata shi duka."' 11 Yanzu a sarari yake, Allah ba ya baratar da kowa ta wurin shari'a, domin "Mai adalci zai rayu ta bangaskiya." 12 Doka ba daga bangaskiya take ba, 'Amma a maimakon haka, "Shi wanda ke yin wadannan abubuwa cikin shari'a, zai yi rayuwa ta wurin shari'a." 13 Almasihu ya fanshe mu daga la'anar shari'a da ya zama la'ananne saboda mu. Kamar yadda yake a rubuce, "La'ananne ne duk wanda aka sargafe a bisa itace." 14 Dalilin shine, albarkan da ke bisan Ibrahim ta zo ga al'ummai cikin Almasihu Yesu, domin mu samu karban alkawarin Ruhu ta wurin bangaskiya. 15 'Yan'uwa, ina magana bisa ga ka'idojin mutane. Idan mutane sun yi yarjejeniya, babu mai kawar da shi ko a kara shi. 16 Yanzu fa, an fada alkawaran nan ne ga Ibrahim da zuriyarsa. Bai ce, "ga zuriya ba" da manufar masu yawa; amma a maimakon haka ga daya kadai, "ga zuriyar ka," wanda shine Almasihu. 17 Yanzu na fadi wannan. Shari'a, wadda ta zo shekaru 430 daga baya, ba ta kawar da alkawarin da Allah ya tabbatar da shi ba tun a baya. 18 Domin idan da gadon ya zo ta dalilin shari'a ne, da ba za ya zo kuma ta dalilin alkawari ba. Amma Allah ya ba da shi ga Ibrahim kyauta ta wurin alkawari. 19 Me ya sa kenan aka ba da shari'a? An kara ta ne saboda laifuffuka, har sai zuriyar Ibrahim din nan ta zo ga wadanda aka yi masu alkawarinta. An kaddamar da ikon shari'ar ta wurin mala'iku, ta hannun matsakaici. 20 Yanzu dai matsakanci yana nufin mutum fiye da daya, duk da haka Allah daya ne. 21 Shari'a tana tsayayya da alkawaran Allah kenan? Ko kadan! Domin idan da an ba da shari'a da ke iya bayar da rai, babu shakka da adalci ya zo ta wurin wannan shari'a. 22 A maimakon haka, nassi ya kulle abubuwa duka a karkashin zunubi. Allah ya yi wannan domin alkawarin sa na ceton mu ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu ya samu a ba da shi ga wadanda suka gaskanta. 23 Amma kafin bangaskiya cikin Almasihu ta zo, an kulle mu kuma aka tsare mu da shari'a har zuwa ga wahayin bangaskiya. 24 Daga nan shari'a ta zama mana jagora har sai da Almasihu ya zo, domin mu samu baratarwa ta wurin bangaskiya. 25 Yanzu da bangaskiya ta zo, ba mu kuma a karkashin jagora. 26 Domin dukanku 'ya'yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Almasihu Yesu. 27 Dukanku da aka yi wa baftisma cikin Almasihu, kun suturce kanku da Almasihu. 28 Babu Bayahude ko Baheline, bawa ko 'yantacce, babu na miji ko mace, domin dukanku daya ne cikin Almasihu Yesu. 29 Idan ku na Almasihu ne, ku zuriyar Ibrahim ne kenan, magada bisa ga alkawarin.
Bulus ya tunashe masu bi a Galatiya da cewa Allah ya basu Ruhun sa a lokacin da suka gaskanta da bishara ta wurin bangaskiya, ba ta wurin aikata shari'ar Allah ba.
Bulus na tsauta wa Galatiyawa ta wurin tambayoyi da suke kamar sanarwa ba su bukatan amsa.
Bulus na amfani da habaici da tambaya da baya bukatan amshi cewa Galatiyawa suna ayuka kamar wani ya sa ma su sihiri. Ba wai ya gaskata wani ya sa ma su sihiri ba ne. AT: "kuna hali kamar wani ya sa ma ku sihiri!"
"ya yi mu ku tsafi" ko kuma "an yi mu ku maita"
Bulus na magana game da sararin koyaswarsa game da Yesu gicciyeyye kamar ya sa hoton kasancewar Yesu a giciye ga jama'a. ya kuma yi magana game da Galatiyawa da su ka ji koyarwar sa kamar sun ga hoton. AT: "ku da kanku kuka ji koyarwar sarai game da kasancewar Yesu a giciye"
Wannan ya cigaba the magana a habaici da ke aya 1. Bulus ya san amsan tambayoyin da ya ke so ya yi.
Fassara wannan tambaya a matsayin tambaya in za ku iya, domin mai karatun za yi tsammanin tambaya ne anan. Kuma, ka tabbata wai mai karatu ya san amsan tambayan nan cewa 'ta wurin gaskatan abin da ka ji," ba "ta wurin yin abin da shari'a ta ce." AT: "kun sami Ruhu, ba ta wurin aikata abin da shari'a ta ce ba, amma ta wurin gaskata abin da kun ji."
Wannan tambaya na nuna cewa Bulus na mamaki kuma har yayi fushi da rashin wayon Galatiyawa. AT: "kuna da wauta sosai!"
kalman "jiki" na ba da ra'ayin kokari. AT: "ta wurin kokarin ku" ko kuma "ta wurin aikin ku"
Bulus na amfani da tambaya ya tunashe Galatiyawa da cewa lokacin da suke wahala, sun gaskata cewa za su sami wasu amfani. AT: "Haƙika ba ku yi tsammanin cewa kuna shan wahalan abubuwa dayawa a banza ba ne ...! ko kuma "Haƙika kun sanni cewa akwai wasu kyawawan shiri domin wahalar abubuwa da yawa ..."
za a iya bayyana a fili cewa sun fuskace wahalar wannan abubuyan domin mutane da suke adawan bangaskiyar su cikin Almasihu. AT: " a banza ne kuka fuskace wahalar abubuwa dayawa daga ma su yi mu ku adawan bangaskiyar ku cikin Almasihu" ko kuma "Kun gaskata cikin Almasihu, da kuma wahalar abubuwa dayawa da kuka sha daga wanda suke adawan Almasihu. Kasancewar bangaskiya da wahalar ku a banza ne"
"mara amfani" ko kuma "ba tare da begen samun wani abu mai kyau ba"
Zai yiwu a nufin 1) Bulus na amfani da wannan irin tambaya ya gargade su kar su bari kwarewansu ya zama a banza. AT: "Kada ku bari ta zama a banza!" ko kuma "Ka da ku daina gaskata cikin Yesu Almasihu kuma barin wahalar ku ta zama a banza." AT: "haƙika ba a banza ba ne!"
Bulus ya tambaya wani tambaya ya tunashe Galatiwaya yada mutane ke samun Ruhu. AT: "Ya ... yi ba ta wurin aikin shari'a ba; yayi ta wurin ji tare da bangaskiya."
Wannan na wakilci mutane da suke aikata abin da shari'a ke bukata. AT: "domin kuna aikata abin da shari'a ta ce mu yi"
harshe ku na iya bukatar cewa abin da mutane suka ji da wanda suka amince a bayyana sosai. AT: "domin kun ji sakon ku ka gaskata cikin Yesu ko kuma "domin kun saurari sakon ku ka kuma amince cikin Yesu"
Allah ya ga bangaskiyar Ibrahim cikin Allah, sanan Allah ya ga Ibrahim a matsayin adali.
"wanda suke da bangaskiya." Manufar wannan kalma "bangaskiya" akan iya bayyana shi cikin aiki "yin imani da." AT: "wanda suka yi imani da"
Wannan na wakilce mutane wanda Allah na kalon su kamar yadda yana kalon Ibrahim. AT: " adali ta hanya ɗaya kamar Ibrahim"
Domin Allah ya yi alkawari wa Ibrahim, suka kuma rubuta kafin alkawarin ta zo ta wurin Almasihu, nassi na kamar wani wanda ya san gobe kafin ta faru. AT: "annabta " ko kuma "gani kafin ta faru"
"ta dalilin abin da ka yi" ko kuma "domin na riga na albarkace ke." kalmar "ka" na nufin Ibrahim ne.
"dukan mutane a cikin duniya." Allah na nanata cewa bai fi son Yuhadawa kadai ba, zababun sa. Shirin sa domin ceto wa Yayudawa da kuma wanda ba Yayudawa.
kasancewa a karkashin la'ana na nufin kasance la'anane. Anan ana nufin kasancewa a madawwamiyar azaba. "Waɗanda suka dogara ga ... shari'a la'anannu ne" ko kuma "Allah zai hukunta har abada wanda suke dogara ga ...shari'a"
Abin da ya ke a sarari za a iya bayyana haka. AT "a sarari Nassin ta ke" ko kuma "Nassi ya koyar a sarari"
za a iya bayyana wannan cikin aiki. AT: "Allah ba zai baratar da kowa ba ta wurin bin shari'a"
wannan kalman "adalci" na nufin adalan mutane. AT: "adalan mutane za su rayu ta wurin bangaskiya"
"abin da shari'a ta ce dole mu aikata"
Zai yiwu ana nufin 1) dole ayi biyaya da su duka" ko kuma 2) "za a hukunta shi ta wurin iya yin abin da shari'a ke bukatar."
kalmar "la'ananne" ana iya bayyana ta cikin aiki da "la'ana." AT: daga kasancewa cikin la'ana domin shari'a" ko kuma "daga kasancewar la'anane ta wurin rashin bayayya da shari'a"
kalman nan "La'ana" za a iya bayyana shi cikin aiki "la'anane," AT: "ta wurin kasance la'ananne domin mu" ko kuma "lokacin da Allah ya la'ance shi maimakon mu"
Kalman "la'ana" anan na bada ra'ayin hukuncin Allah ga mutumin da ya la'anta. AT: "daga gare mu Allah ya hukunta mu domin mun karya shari'a ... da sa Allah ya hukunta shi a maimakon mu...Allah ya hukunta kowa da kowa"
Bulus na sa ran masu sauraro sa su fahimci cewa yana nufin Yesu aka kafa bisan giciye.
"domin Almasihu ya zama la'ananne domin mu, albarkan Ibrahim za ta zo"
domin Almasihu ya zama la'ananne domin mu, ta wurin bangaskiya za mu samu"
kalman "mu" ya hada da mutanen da za su karanta wasikar.
Dubi yadda ku/ka fassara wannan a Galatiyawa 1:2.
"a yadda mutum" ko kuma " da abubuwa mafi yawan mutane sun fahimta"
Wannan kalman na nufin cewa Bulus ya bayyana manufar, yanzu yana fara gabatar da wani muhimmin zance.
"na nufin zuriya masu yawa"
kalman "ka" na nufin wani mutum musamma, wanda shi musamman zuriyar Ibrahim
"shekaru dari hudu da talatin"
Bulus na magana gama da yanayin da ba ta taba kasancewa ba don ya nanata cewa gadon na zuwa wurin alkarine ne kadai. AT: "gadon ya zo gare mu ta wurin alkawari ne, domin ba mu iya kiyaye buƙatar shari'ar Allah ba"
karɓan abin da Allah ya alkawarta wa masubi ne a ke maganar ta kamar wani gadon dukiya ne daga wani dan iyali, da madawwamiyar albarku da kuma fansa.
Bulus ya yi amfani da tambaya da ba ta buƙatar amsa ya gabatar da zancen da zai tattauna a gaba. za a fassara wannan maganar kamar. AT: "Zan gaya mu ku menene manufar shari'a." ko kuma "Bari in gaya mu ku dalilin da ya sa Allah ya bayar da shari'a."
ana iya bayyana wannan cikin aiki. AT: "Allah ya kara ta" ko kuma "God ya kara shari'a"
Ana iya bayyana wannan cikin aiki. AT: "Allah ya bayar da shari'a ta wurin taimakon mala'iku, sai matsakanci ya tilasta ta"
"mai wakilci"
Allah ya ba da alkarinsa ga Ibrahim ba tare da matsakanci ba, amma ya bayar da shari'a ga Musa tare da matsakanci. Ta dalilin haka, ma su karatun wasikar Bulus za su iya yin tsammani cewa shari'an ta wata hanya dai ta sa alkarin ba ta cika ba. Bulus na bayyana abin da masu karatu za iya yin tsammani anan, da kuma zai amsa mu su a cikin aya da ke bi.
"na găba da alkawaran" ko kuma "cikin saɓani da alkawaran"
Wannan anan iya bayyana cikin aiki, da kuma suna "rai" ana iya fassaran aiki "rayuwa." AT: "in da Allah ya bayar da shari'a da ke ba da dama ga wanda suka kiyaye ta su rayu"
"da mun zama adalai ta wurin yin biyyaya da shari'a"
Ana iya ba da wasu ma'ana 1) domin kowa yayi zunubi, Allah ya sa komai a karkashin mulkin shari'a, kamar kulle su a kurkuku, ta haka ne abin da ya alkawarta ga wanda suka gaskata cikin Almasihu Yesu zai iya bayar ga masu gaskatawa. 2) domin mu yi zunubi, Allah ya sa komai a karkashin mulkin shari'a, kamar kulle su a kurkuku. ya yi haka ne domin abin da alkawarta ga wanda suka gaskata cikin Almasihu Yesu ya bayar ga masu gaskatawa."
Bulus na yi da nassi kamar wani mutun ne da yake magana ga da Allah, wanda ya rubuta nassi. AT: "Allah"
za a iya bayyana wannan cikin aiki. AT: "shari'an ta riƙe mu ƙangi, muna cikin kurkuku" ko kuma "shari'an ta riƙe mu ƙangi cikin kurkuku"
wannan ana iya bayyana cikin aiki, da wanda wannan bangaskiya ke ciki na iya bayyana a sarari. AT: " kafin Allah ya bayyana cewa ya kuɓutar da wanda suke da bangaskiya cikin Almasihu" ko kuma " kafin Allah ya bayyana cewa ya kuɓutar da wanda suke dõgara cikin Almasihu
Fiye da jagora kawai "wani da ya ke ba da dubawa ga yaro," a yawanci wannan bawa ne wanda aikinsa tilasta umurni da halin da iyaye suka bayar, ya kuma kai rahoto ga iyaye game da halin yaron.
"kafin lokacin da Almasihu ya zo"
kafin zuwan Almasihu, Allah ya yi shirin kuɓutar da mu. lokacin da Almasihu ya zo, ya cika shirin sa na kuɓutar da mu. ana iya bayyana wannan ciki aiki. AT: "sabõda haka Allah ya bayyana mu adalai"
" domin dukanku wanda aka yi muku baftisma cikin Almasihu"
Ana iya nufin 1) wannan nafin kamar an hada su da Almasihu. AT: "kun zama a haɗe da Almasihu" ko kuma "na Almasihu" ko kuma 2) wannan na nufin kamar cewa sun zama kamar Almasihu. AT: " a zama kamar Almasihu"
Allah baya ganin bambanci tsakanin Bayahude da Ba'al'umme, bawa da 'yantace, namiji da mace"
mutanen da Allah ya yi ma su alkari su ake magana akai kamar za su gãji dukiya daga wani ɗan iyali.
Ibrahim ya ba da gaskiya ga Allah, kuma an lisafta mashi wannan a matsayin adalci.
Wadanda suka ba da gaskiya ga Allah, su ne 'ya'yan Ibrahim.
Nassi ya hangi gaba cewa ta wurin bangaskiya, Al'ummai za su barata.
Waɗanda suka dogara ga ayyukan shari'a su na barata a karkashin la'ana.
Babu wanin da aka baratar ta wurin ayyukan shari'a.
Almasihu ya fanshe mu daga la'anar shari'a ta wurin zama la'ananne saboda albarkan da ke bisa Ibrahim ta zo ga al'ummai.
"Zuriyar" da aka yi maganarsu a kan alkawari zuwa Ibrahim shi ne Almasihu.
A'a, dokan bai kawar da alkawarin da aka yi wa Ibrahim ba.
Dokan ya zo saboda laifuffuka, har sai zuriyar Ibrahim ta zo.
Dokan cikin nassi ya kulle kowa a karkashin zunubi.
An yantad da mu daga ɗaurin kurkukun doka ta wurin bangaskiya a cikin Almasihu Yesu.
Duka waɗanda suka yi baftisma a cikin Almasihu sun suturce kansu a Almasihu.
Yahudawa, Heliniyawa, bayi, 'yantacce, na miji da mace, ɗaya ne cikin Almasihu Yesu.
1 Ina cewa muddin magaji yaro ne, babu bambancin sa da bawa, ko da yake shine mai mallakan dukan kadarorin. 2 A maimakon haka, yana karkashin masu jagora da amintattu har sai lokacin da mahaifinsa ya ajiye. 3 Hakannan mu ma, lokaci da muke yara, an rike mu cikin kangi na tushin ka'idojin wannan duniya. 4 Amma da lokacin ya yi daidai, Allah ya aiko da dansa, haihuwar mace, haihuwar karkashin shari'a. 5 Ya yi haka ne domin ya fanshi wadanda ke a karkashin shari'a, domin mu karbi diyanci a matsayin 'ya'ya. 6 Domin ku 'ya'ya ne, Allah ya aiko da Ruhun Dansa cikin zuciyarmu, Ruhun wanda ke kirar, "Abba, Uba." 7 Saboda wannan dalilin kai ba kuma bawa ba ne amma da. Idan kai da ne, hakannan kuma kai ma magaji ne ta wurin Allah. 8 Duk da haka a da, da ba ku san Allah ba, bayi ne ku ga alloli wadanda ainihi ba alloli ba ne ko kadan. 9 Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma, yanzu da Allah ya san ku, me ya sa kuke sake komawa zuwa ga tushen ka'idodin nan mara karfi da amfani? Kuna so ku sake komawa zaman bayi kuma daga farko? 10 Kuna kiyaye ranaku na musamman, sabobin watanni, lokatai, da shekaru. 11 Ina ji maku tsoro. Ina tsoro cewa kamar na yi aiki cikinku a wofi. 12 Ina rokon ku 'yan'uwa, ku zama kamar yadda nake, domin ni ma na zama kamar ku. Ba ku yi mani laifin komai ba. 13 Amma kun sani cewa saboda rashin lafiya ne na yi maku shelar bishara da farko. 14 Ko da yake halin da nake ciki cikin jiki a zahiri ya sa ku cikin gwaji, ba ku raina ni ba ko kuma kuka watsar da ni. A maimakon haka, kun karbe ni kamar mala'ikan Allah, kamar ni Almasihu Yesu ne da kansa. 15 Saboda haka, yanzu ina murnar taku? Domin ina shaidar ku, idan mai yiwuwa ne, da kun kwakulo idanunku, kun ba ni. 16 To kenan, na zama makiyin ku ne saboda na gaya maku gaskiya? 17 Suna neman ku da himma ba domin wani alheri ba ne. Suna so su raba ni da ku domin ku bi su. 18 Yana da kyau ko yaushe a yi himma domin dalilai masu kyau, ba kuma kawai sa'adda ina tare da ku ba. 19 'Ya'yana kanana, sabili da ku ina cikin zafin nakuda kuma sai Almasihu ya samu kafuwa cikinku. 20 Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canza muryata, domin ina damuwa a kanku kwarai. 21 Ku gaya mani, ku da kuke marmarin ku zo karkashin shari'a, ba ku ji abin da shari'ar ta ce ba? 22 A rubuce yake cewa, Ibrahim yana da 'ya'ya maza biyu, daya dan baiwa ne, dayan kuma dan 'yantaciyar mace ne. 23 Abin lura anan, dan baiwar an haife shi ta hanyar mutuntaka ne, amma dan 'yantaciyar macen, an haife shi ta wurin alkawari ne. 24 Ana iya bayyana abubuwan nan a hanyar kwatanci kamar haka, wadannan mata na kama da alkawarai ne guda biyu. Dayan alkawarin daga dutsen Sinayi ne. Ta haifi 'ya'ya da ke bayi ne su. Ita ce Hajaratu. 25 Yanzu fa, Hajaratu ita ce dutsen Sinayi da ke Arebiya. Misali ce na Urushalima na yanzu, domin tana cikin bauta tare da 'ya'yanta. 26 Amma Urushalima da ke bisa 'yantacciya ce, ita ce mahaifiyarmu. 27 Kamar yadda yake a rubuce, "Ki yi murna, ke bakarariya, ke da ba ki taba haihuwa ba. Ki yi shewa na farinciki, ke da ba ki dandana haihuwan da ba. Domin 'ya'yan bakarariya da yawa suke, fiye da ta mace mai miji." 28 Yanzu fa, 'yan'uwa, kamar yadda Ishaku yake, haka muke, wato 'ya'yan alkawari. 29 A lokacin can, shi wanda aka haife shi ta hanyar mutuntaka ya tsananta wa wanda aka haife shi ta hanyar Ruhu. Haka yake har yanzu. 30 Amma menene nassi ya ce? "Ka kori baiwar nan tare da danta. Domin dan baiwar nan ba za ya ci gado tare da dan macen nan da ke 'yantacciya ba." 31 Saboda haka 'yan'uwa, mu ba 'ya'yan baiwa ba ne, a maimakon haka, mu 'ya'yan macen nan ne da ke 'yantacciya.
Bulus ya ci gaba da tunashe masubi a Galatiya cewa Almasihu ya zo ya fanshi wanda suke karkashi shari'a, ya kuma mayar da su 'ya'ya ba bayi kuma ba.
"ɗaya da"
mutane da suke da iƙon lura da 'ya'ya bisa ga umurnin hukuma
mutanen da wasu ke amince da su waje lura da muhimman abubuwa
kalman "mu" anan na nufin dukan masubi, harda masu karatu wasikar Bulus.
A nan " 'ya'ya" na nufin kamar kasance rashin girma a ruhaniya. AT: "sa'ada mu ke kamar 'ya'ya"
A nan "bauta" na ba da misalin rashin iya hana kaina daga yin wani abu. Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "ƙa'idodin farko na duniya na mulkin mu" ko kuma " mun yi biyayya da ƙa'idodin farko na duniya kamar mun kasance bayi"
Ya yiwu ana nufin 1) wannan na nufin dokoki ko kuma ƙa'idodin halin duniya, ko 2) wannan na nufi da iƙokin ruhu wanda waɗansu ke tunani na mulkin abin da ke faruwa a duniya.
Bulus yayi amfani da misãlin mutun da ke sayan dukiyan da ya ratsa, ko sayan 'yancin wani bawa kamar hoton yadda Yesu ke biya domin zunuban mutanesa ta wurin mutuwa a kan giciye.
Wannan muhimmin lakabi ne na Yesu, Ɗan Allah.
Bulus ya yi amfani da kalmar yaro namiji anan domin zancen game da gado ne. A al'adan shi da masu karatun shi, an saba ba gado ga 'ya'ya maza, ko da yake ba ko yaushe ba. ba wai yana tanatance ko kuma ware 'ya'ya mata ba ne anan.
Ta kiran "Abba, Uba" Ruhun na tabbatar da mu 'ya'ya Allah ne kuma yana kaunar mu.
zuciya anan a nufin bangare a mutum da ke tunani ko ji. AT: "aika Ruhun Ɗan sa ya nuna mana yadda za mu yi tunani da zama"
Wannan muhimmin lakabi ne na Yesu, Ɗan Allah.
Ruhu shi ne wanda ke kira.
Ta wannan hanya ne yaro ke martaba mahaifinsa a harshen gidan Bulus, amma ba a harshen Galatiyawa masu karatu ba. domin ci gaban harshen waje, fassara wannan kalman "Abba" kamar yadda harsha ku ke yi.
Bulus na magana da masu karatun sa kamar mutum daya ne.
ana magana game da mutanen da Allah yayi wa alkawarai kamar za su gaji wani dukiya ne da ga wani ɗan iyali.
"waɗannan abubuwan da suke" ko kuma "waɗannan ruhohin wanda suke"
ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: Allah ya san ku"
A nan "juya baya ga" na kamar fara mayar da hankali ga wani abu kuma. AT: "ka da ku fara mayar da hankalinku ga... ƙa'idodi." ko kuma "ka da ku damu da ... ƙa'idodi."
dubi yadda ku ka fassara wannan magana cikin Galatians 4:3.
Bulus na amfani da wannan tambaya ya tsauta wa mutanen domin suna wani hali kamar bayi. AT: "da alama kuna so ku za bayi kuma." ko kuma "kuna hali kamar kuna so ku sake zama kamar bayi."
Bulus na magana game da aminci da hankalinsu wajen kiyaye lokatan idi, da tunanin cewa kiyaye wannan ne zai daidaita su da Allah. AT: "kun kansanci da hankali a kiyaye idin ranaku da sabobin watanni da na shekaru"
"iya kassance banza" ko kum "ba bu wani sakamako"
A nan wannan na nufin tambaya ko kuma izawa da karfi. Wannan ba kalmar da ake amfani wajen tambayan kuɗi ko abinci ko kuma wasu kaya da ake iya gani ba.
Dubi yadda kuka fassara wannan cikin (Galatiyawa 1:2) (../01/01.md).
ana iya bayyana wannan a tabbataceyar sifa. "kun bi da ni da kyau" ko kuma "kun lura da ni a yadda yakamata"
"ko da yake ya yama mu ku da nauyi ku kalle ni ciki rashin lafiya ta jiki"
ƙiyayya sosai
"a shawo ku ga hada kai da su"
"a raɓa ku da ga gare mu" ko kuma "su sa ku daina kassance da biyyaya da mu"
"himmantu da abin da suka ce da ku ku yi"
Wannan na ba da ra'ayin almajirai ko kuma masu bi. AT: "ku da kuke almajirai domina"
Bulus na amfani da nakuda ya bayyana damuwar sa game da Galatiyawa. AT: " Ina cikin zafi kamar ni wata mace ce da taka haifan ku, kuma zan ci gaba da zama a cikin zafin har sai Almasihu mulkance ku da gaske"
"Ina so in yi wani tambaya" ko kuma "Ina so in gaya mu ku wani abu"
Bulus na gabatar da abin da ce a gaba. AT: "kuna bukatar ku koyi abin da shari'ar ta ce." ko kuma "bari in gaya muku gaskiyar abin da shari'a ta ce."
Wannan labarin 'ya'ya maza biyu na kamar hoton da zan gaya muku yanzu"
"misali" labari ce wanda mutane da abubuwan cikin ta na nufin wasu abubuwa. a misalin Bulus, mata biyu na Galatiyawa 4:22 na nufin alkawarai biyu.
"mata na ba da hoton ... ita hoton"
"Dutsen Sina'i" anan na matsayin shari'an da Musa ya bayar ga 'Israi'lawa a wurin. AT: "Dutsen Sina'i, wajen da Musa ya bayar da shari'a ga Israi'la"
Bulus na magana game da shari'a kamar wani mutum ne. AT: "mutanen da suke karkashin wannan alkawarin na kamar bayi ne wanda ya kammata su yi biyyaya da shari'a"
Hajara baiwa ce, 'ya'yan ta ma bayi ne da ita. AT: "Urushalima, kamar Hagara, baiwa ce, 'ya'yan ta kuma bayi ne da ita"
"ba a ɗaure ba" ko kuma "ba bawa ba"
yi murna
Anan "ke" na nufin bakarãriya mace.
Ana iya nufin cewa Galatiyawa sun zama 'ya'ya Allah 1) ta wurin gaskata alkawarin Allah, ko kuma 2) domin Allah yayi aikin mu'ujizai domin ya cika alkawaren sa ga Ibrahim, farko ya ba Ibrahim ɗa sannan ya mayar da Galatiyawa 'ya'yan Ibrahim wato 'ya'yan Allah.
Wannan na nufin Ibrahim ya zama uban Isma'ilu ta daukan Hajaratu ta zama matarsa. AT: "ta wurin aikin mutuntaka" ko kuma "ta dalilin abin da mutane suka yi"
"domin wani abin da Ruhu ya yi"
kalmomin nan "mu 'ya'ya ne"an fahimce su a maganar baya. Ana iya fassarar wannan kamar wata magana dabam. AT: "amma, mu 'ya'yan 'yantacciyar macen ne"
Magajin ya na karkashin masu jagora da amintattu har sai lokacin da mahaifinsa ya sa.
Allah, a loƙacin da ya dace, ya aiko da Ɗansa, don ya fanshi waɗanda su ke karkashin shari'a.
Ya yi haka ne domin ya fanshi wadanda ke a karkashin shari'a, domin mu karbi diyanci a matsayin 'ya'ya. Allah ya ƙarɓe 'ya'yan a matsayin 'ya'yansa wanda suke karkashin shari'a.
Allah ya aiko da Ruhun Dansa zuwa cikin zuciyar'ya'yansa.
Kafin mu san Allah, mu bayi ne ga ruhohin dake iko da duniya, wanda ba alloli ba ne ko kadan.
Bulus ya damu cewa Galatiyawan su na komawa kuma wa ruhohi masu iko na duniya.
Bulus na tsoron cewa Galatiyawan za su zama bayi kuma, da kuma wai ya yi wahala a banza.
A loƙacin da Bulus ya fara zuwa Galatiya, ya na da rashin lafiya.
Da damuwan Bulus, Galatiywan sun ƙarɓe shi kamar mala'ikan Allah, kamar Almasihu Yesu.
Mallaman karyan su na kokarin raba Galatiyawan daga Bulus.
Mallaman karyan na kokarin mayar da Galatiyawan zuwa karkashin shari'an.
Ibrahim na da 'ya'ya biyu, ɗaya daga baiwar kuma ɗaya 'yantaciyar mata.
Urushaliman a sama, 'yantaciyar mata, ita ce alamar mahaifiyar Bulus da Galatiyawa masu bi.
Masubi a Almasihu 'ya'ya ne na alkawari.
'Ya'yan da an haife su ta hanyar mutuntaka, su ne suke tsananta wa 'ya'yan alkawari.
'Ya'yan baiwar ba su gada tare da 'ya'yan 'yantaciyar matan ba.
Masubi a Almasihu 'ya'yan 'yantaciyar matan ne.
1 Saboda 'yanci ne Almasihu ya yantar da mu. Sai ku dage kada ku sake komawa cikin kangin bauta. 2 Duba, ni Bulus, ina gaya maku cewa idan an yi maku kaciya, Almasihu ba zai zama da amfani a gare ku ba a kowace hanya. 3 Haka kuma, na shaida ga ko wanda mutum wadda aka yi masa kaciya ya zama dole ya yi biyayya da dukan shari'a. 4 Kun rabu da Almasihu, dukanku wadanda aka "baratar" ta wurin shari'a. Kun fadi daga alheri. 5 Domin ta wurin Ruhu, cikin bangaskiya, muna jira gabagadi na adalci. 6 A cikin Almasihu kaciya ko rashin kaciya ba shi da ma'ana. Bangaskiya kadai mai aiki ta wurin kauna ita ce mafi muhimmanci. 7 Da kuna tsere da kyau, wanene ya tsayar da ku daga yin biyayya da gaskiya? 8 Rinjayarwa da ke sa yin wannan, ba daga wanda ya kira ku ba ne 9 Ai karamin yisti shi yake sa dukan kulli ya kumbura. 10 Ina da wannan gabagadin game da ku cikin Ubangiji cewa ba za ku yi tunani a wata hanya daban ba. Shi wanda ya rikita ku zai sha hukunci ko wanene shi. 11 'Yan'uwa, idan har yanzu wa'azin kaciya nake yi, don me har yanzu ake tsananta mani? Inda haka ne dutsen sanadin tuntube game da gicciye da ya ragargaje. 12 Ina fata wadanda suke badda ku su maida kansu babani. 13 'Yan'uwa, domin Allah ya kira ku zuwa ga yanci, kada dai ku mori yancin nan ya zama zarafi domin jiki. A maimakon haka ta wurin kauna ku yi wa juna hidima. 14 Saboda dukan shari'a ta cika ne a cikin doka guda daya; "Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka." 15 Amma idan kuna cizo da hadiye juna, ku lura kada ku hallakar da junanku. 16 Na ce, ku yi tafiya cikin Ruhu, ba za ku cika sha'awoyin jiki ba. 17 Domin jiki yana gaba mai karfi da Ruhu, Ruhu kuma yana gaba da jiki. Domin wadannan akasin juna suke. Sakamakon shine ba za ku iya yin abin da kuke so ba. 18 Amma idan Ruhu ne ke bishe ku, ba ku karkashin shari'a. 19 Yanzu ayyukan jiki a bayyane suke. Sune al'amuran lalata, rashin tsarki, sha'awoyi, 20 bautar gumaka, sihiri, yawan fada, jayayya, kishi, zafin fushi, gasa, tsattsaguwa, hamayya, 21 hassada, buguwa, buguwa da tarzoma, da dai sauran irin wadannan abubuwa. Na gargade ku, kamar yadda a da na gargade ku, cewa wadanda suke aikata wadannan abubuwa ba za su gaji mulkin Allah ba. 22 Amma 'ya'yan Ruhu kauna ne, farinciki, salama, hakuri, kirki, nagarta, bangaskiya, 23 tawali'u, da kamun kai. Babu wata shari'a da ke gaba da wadannan abubuwa. 24 Wadanda suke na Almasihu Yesu sun giciye halin jiki tare da marmarin sa da miyagun sha'awoyi. 25 Idan muna zaune cikin Ruhu, mu yi tafiya da Ruhu. 26 Kada mu zama masu girman kai, ko muna cakunar juna, ko muna kishin juna.
Bulus yayi amfani da misali ya tunashe masubi ga yin amfani 'yanci su cikin Almasihu domin a cika duka shari'a cikin kaunace maƙwabta kamar kanmu.
"saboda mu iya samun 'yanci ne shi yasa Almasihu ya 'yantar da mu." Ana ba da tabbacin cewa Almasihu ya 'yantar da masubi daga tsohon alkawari. Anan 'yanci daga tsohon alkawari na ma'anar kassance ba wajibi ne a yi biyaya da ita ba. AT: "Almasihu ya 'yantar da mu daga tsohon alkawari domin mu zama da yanci." ko "Almasihu ya 'yantar da mu domin mu iya rayuwa kamar 'yanttatun mutane"
tsayawa da karfi anan na wakilce ɗaukan kuduri ba za ka canja ba. ana iya bayyana yadda ba su canja ba a sarari haka. AT: " kada ku ba da kai ga jayayyan mutane da suke koyas da wani abu dabam" ko "kassance da kudurin zama a 'yanci"
Bulus na amfani da kaciya yana nufin Yahudanci. AT: "in kuka juya ga adinin yahudanci"
A nan kassancewa karkashin kangin bauta na wakilci kassance wajibi ne a biyayya da shari'a. AT: "kada ku yi rayuwa kamar wanda ke karkashin kangin bauta ga shari'a"
"Na furta" ko "Na zama kamar mashaiɗi"
Bulus na amfani da kaciya a nufin kassance Bayahude. AT: "ga duk wanda a zama Bayahude"
"dole ya yi biyayya"
A nan "yanke" na nufin rabuwa daga Almasihu. AT: ka ƙarar da dangantakar da Almasihu" ko "ba ka haɗe da Almasihu"
Bulus na magana cikin habaici anan. Zahiri ya koyas cewa ba wani da za a baratar ta wurin aikata aikin da shari'a ke buƙata. AT: "duk wanda ke tunani za a baratar da shi ta wurin aikata aikin da shari'a ke bukata" ko "wanda ke son baratarwa ta wurin shari'a"
Wanda alheri ya zo daga, ana iya bayyana a sarari. AT: " Allah ba zai yi mu ku alheri ba"
A nan kalman "mu" na nufin Bulus tare da wanda suke ƙoƙarin hana masubi yin kaciya. Ya yiwu ya haɗa har da Galatiyawa.
"Wannan haka ne domin ta wurin Ruhu"
Manufar na mai yiwuwa 1) "ta wurin bangaskiya muna jiran begen adalci" ko 2) muna jira begen adalci da ke zuwa ta wurin bangaskiya."
"muna hakuri da murnan jiran Allah ya daidaita mu da kansa har abada, da kuma tsammanin zai yi"
Wannan na bayyana kassancewa Bayahude ko wanda ba Bayahude ba. AT: "ba kassancewa Bayahude ko ba ka kassance Bayahude ba"
"a maimako, Allah ya damu da bangaskiyar mu a cikin sa, wanda ke ta wurin ƙauna da muke wa wasu"
mara kima
"kuna aikata abin da Yesu ya koyar"
"ba Allah wanda ya kira ku ne ya rinjaye ku wajen yin haka ba"
abinda ya kira su ga, ana iya bayyana a sarari haka. AT: "wanda ya kira ku ku zama mutane sa"
rinjayar wani shi ne sa mutum ya canja abin da ya gaskata zuwa aikata wani abu dadam.
"ba za ku gaskata ga wani abu dabam da abin da na ke gaya muku"
"Allah zai hukunta duk wanda ke matsa muku"
"ke sanadin rashin tabbacinku game da gaskiya" ko "zuga ta da hankili a tsakanin ku"
Mai yiwuwa ana nufin 1) Bulus bai san sunayen mutanen da suke gayawa Galatiyawa da cewa suna bukatar su yi biyayya da shari'ar Musa, ko 2) Bulus baya so Galatiyawa su damu ko ma su rikicer da su na da arziki ko talakawane, ko masu girma ko kanana, ko masu addini ko kuma marasa addini.
Bulus na bayyana wani yanayi ne da bai faruba ta wurin nanata cewa mutane na tsananta mishi domin baya wa'azin mutane na bukatan su zama Yahudawa. Ana iya bayyana wanan cikin sifar aiki. AT: " 'Yan'uwa, kun gani har yanzu bana shelar kiciyar domin Yahudawa suna tsananta mani."
dubi yadda ka fassara wannan cikin Galatiyawa 1:2.
Bulus na bayyana wani yanayi ne da bai faruba domin ya nanata cewa mutane na tsananta mishi domin yana wa'azi cewa Allah na yafe wa mutane domin aikin da Yesu yayi a bisa giciye.
"inda har yanzu ina cewa mutane na bukatan su zama Yahudawa"
Wannan za a iya bayyana cikin sifar aiki. AT: "koyas game da giciye bata da tsanandin tuntubɓe" ko kuma "ba wani abu da ke sa mutane tuntube a koyaswa game da giciye"
Mai yiwuwa ana nufin 1) ciren marainan namiji don su zama baban ya ko kuma 2) janyewa daga al'umman masubi gaba daya.
Bulus na bayar da dalilin rubutun da yayi a Galatiyawa 5:12.
ana iya bayyana wannan a sifar aiki. AT: "Almasihu ya kira ku ga 'yanci"
ana iya bayyana da kyau dangata tsakanin "dama" da "halin mutumta" a haka. AT: "kun samu wata damar nuna halin mutumtakar ku"
Mai yiwuwa ana nufin 1) "za ka in bayyana dukka shari'ar cikin umurni guda, wannan shi ne" ko kuma 2) "ta wurin yin biyayya da umurni guda, kun yi biyayya ga duk umurnai, wannan umurnin shi ne."
tafiya na nufin rayuwa. AT: "bi da rayuwarku cikin iƙon Ruhu Mai tsarki" ko kuma "ku yi rayuwarku cikin dogara ga Ruhu"
managan "biye wa sha'awarce sha'awarcen wani" karin magana ne da ke nufin "biye wa sha'awar wani." AT: "ba zu biye wa abin da halin mutumtakarku ke sha'awar ba"
an yi magana game da halin mutumtaka kamar wani mutum ne da ya ke so yayi zunubi. AT: "abin da ku so ku yi ta dalilin halin mutumtakar ku" ko kuma "abubuwan da ku ke so ku yi domin ku masu zunubi ne"
"ba wajibtar biyayya ga shari'ar Musa ba"
ana iya fassarar kalmar "ayuka" cikin sifar aiki "aikata." AT: "abin da halin mutumtaka ke aikata"
ana magana game da abinda Allah ya Alkawarta ga masubi kamar wani dukiya da ake mallaka a wurin ɗan iyali.
Anan " 'ya'ya' " na nufin "sakamako." AT: "abin da Ruhu ke haifa ita ce kauna ...kamunkai" ko kuma "Ruhun ya kan haifa a cikin mutanen Allah Kauna ... kamunkai"
Bulus na magana game da Masubi da ba su rayuwar mutumtaka kamar halin mutumtaka wani mutum ne da aka kashe a bisa giciye. AT: "rashin rayuwa ta halin mutumtaka da matsananciyar sha'awarta, kamar an kashe ta bisa giciye"
ana magana game da halin mutumtaka kamar wani mutum ne da ke da matsananciyar sha'awa. AT: "halin mutumtakar su, da kuma abubuwan da suke sa karfin bukatar yi game da ita"
"tun da Ruhun Allah ya rayar da mu"
"ya kamata mu"
Saboda 'yanci ne Almasihu ya yantar da mu.
Bulus faɗa cewa idan Galatiyawan sun yi kaciya, Almasihu ba zai zama da amfani a gare su ba a kowace hanya.
Bulus ya gargade duka Galatiyawan da za su so su yantu ta wurin bin shari'an da cewa, za a raba mutumin daga Almasihu kuma zai faɗi daga alheri.
A Almasihu, aikin bangaskiya ne kaɗai ta wurin ƙauna na nufin ko wane abu.
Bulus na da gabagadin cewa wanda ya rikita Galatiyawan game da bisharan zai sha hukuncin Allah.
Bulus ya faɗa cewa yin wa'azin kaciya, dutsen tuntube na giciyen, za a hallaka.
Masubi ba za su yi amfani da 'yancinsu ya zama zarafi domin jiki.
Masubi za su yi amfani da 'yancinsu ta wurin yin hidima wa juna cikin ƙauna.
Dukan shari'a ta cika a doka ɗaya, "Ka ƙaunaci makwabcinka kamar kanka."
Masubi za su iya yin tafiya cikin Ruhu, kuma ba za su cika sha'awoyin jiki ba.
Ruhu da jiki ke hamayya da juna a cikin mai bi.
Misalai uku na ayyukan jiki su ne , al'amuran lalata, rashin tsarki, sha'awoyi, 20bautar gumaka, sihiri, yawan fada, jayayya, kishi, zafin fushi, gasa, tsattsaguwa, hamayya, 21hassada, buguwa, buguwa da tarzoma.
Waɗanda suke yin ayyukan jiki ba za su gaji mulkin Allah ba.
'Ya'yan Ruhu ita ce ƙauna, farinciki, salama, hakuri, kirki, nagarta, bangaskiya, tawali'u, da kamun kai.
Waɗanda suke na Almasihu Yesu sun giciye jikin da sha'awowinsa.
1 'Yan'uwa, idan an kama mutum yana yin wani laifi, ku da kuke da ruhaniya sai ku dawo da mutumin a hanya cikin ruhun tawali'u, ka lura da kanka don kada kai ma ka fada a cikin gwaji. 2 Ku dauki damuwar juna, ta yin haka za ku cika shari'ar Almasihu. 3 Domin idan kowa ya zacci shi wani abu ne alhali shi ba komai ba ne rudin kansa yake yi. 4 Sai kowa ya auna aikin sa. Sa'annan zai sami abin da zai yi takama, ba sai ya kwatanta kansa da wani ba. 5 Domin kowa zai dauki nauyin kayansa. 6 Wanda aka koya masa maganar, wajibi ne ya ci amfanin abubuwansa masu kyau duka tare da malaminsa. 7 Kada fa a yaudare ku ba a yi wa Allah ba'a. Dukan abin da mutum ya dasa, shine abin da zai girba. 8 Domin shi wanda ya shuka wa kansa dabi'ar zunubi zai girbi hallaka, amma shi wanda ya shuka cikin Ruhu, zai girbi rai madawwami daga Ruhu. 9 Kada mu gaji da aikata nagarta, domin a lokacin da ya dace za mu yi girbi idan ba mu gaji ba. 10 Saboda haka, lokacin da muke da zarafi, sai mu yi nagarta ga kowa. Mu yi nagarta mussamman ga wadanda suke na iyalin bangaskiya. 11 Dubi yawan wasikun da na rubuta maku da hannuna. 12 Wadanda suke so su nuna hali mai kyau cikin jiki suke tilasta ku yin kaciya. Suna yin haka ne kadai saboda kada a tsananta masu saboda gicciyen Almasihu. 13 Domin ko su wadanda suke masu kaciya ba su kiyaye shari'a. Maimakon haka suna so ne a yi maku kaciya don su yi fahariya game jikinku. 14 Bari kada ya zama ina fahariya sai dai ta gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu. Ta wurinsa ne aka gicciye duniya a gare ni, ni kuma ga duniya. 15 Domin kaciya ko rashin kaciya ba komai ba ne. Maimakon haka, sabon halita ne ke da muhimmanci. 16 Ga dukan wadanda za su zauna cikin wannan ka'ida, bari salama da jinkai su kasance tare da su da kuma bisa Isra'ila na Allah. 17 Daga yanzu zuwa nan gaba kada wani ya dame ni, domin ina dauke da tabbai na Yesu a jikina. 18 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance da ruhun ku, 'yan'uwa. Amin.
Bulus na koyar da masubi yadda za su lura da 'yan'uwan masubi da kuma yadda Allah ke sakayya.
Dubi yadda kuka fassara wannan cikin Galatiyawa 1:2.
idan kowane a tsakanin ku"
Mai yiwuwa ana iya nufin 1) wani ne dabam ya tarar da wani mutum yana aikatawa. AT: "idan a gano wani na cikin aikata zunubi" ko kuma " 2) wancan mutum ya aikata zunubi ba da nufin yin mugunta ba. AT: "idan wani ya ba da kansa cikin zunubi"
"ku wanda Ruhu ne ke bi da ku" ko kuma "ku wanda kuke rayuwa cikin jagorar Ruhu"
"daidaita mutummin da yayi zunubi" ko kuma "gargadi mutummin da ya yi zunubi ya dawo zuwa ga ɗangantaka mai kyau da Allah"
Mai yiwuwa ana nufin 1) Ruhu ne ke jagoran mutummin da ke yin gargadi ko kuma 2) "da halin tawali'u" ko "cikin halin kirki."
Wannan kalmomin sun zama ga Galatiyawa kamar da mutum da a ke magana domin a nanata cewa da kowani mutum a cikin su ya ke magana da. AT: "ku zama da kula da junanku" ko kuma "ina magana da kowanen ku, kula da kanka"
ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "don kada wani abu ya gwada kai ma ga yin zunubi"
"domin in da." kalmomin da suka biyo suna ba da dalilin da zai sa Galatiyawa su 1) "dauki nauyin juna" (Galatiyawa 6:2] 9./01.md)) ko kuma 2) kuyi lura kada suma da kansu a gwada su (Galatiyawa 6:1) ko 3) "kada a zama da fahariya" ([Galatiyawa 5:26).
"shi muhimmin mutum ne" ko kuma "shi ya fi wasu"
"ba shi da muhimminci" ko kuma " shi bai fi wasu ba"
"dole kowanenku"
"za a yi wa kowa hukunci bisa ga aikin sa. ko kuma "kowanen ku zai ɗauki alhakin aikinsa ne kadai"
"kowani mutum zai"
"mutumin"
"sakon," duk abin da Allah ya ce ko kuma ya umurta
Shuƙi na nufin yin abubuwan da a karshe suna da wasu sakamako, tarawa kuma na wakilce zama da sakamakon abin da mutum ya yi. AT: "domin yadda manomi ke tara duk 'ya'yan irin da ya shuka ya haifa, haka kowa ke zama da sakamakon duk abin da ya yi"
ba maza ne kadai Bulus ke nufi anan ba. AT: "duk abin da mutum ya shuƙa" ko kuma "duk abin da wani ya shuƙa"
shuka iri na bayyana aikata halin da sakamako zai biyo baya. A wannan yanayin, mutum na aikata zunubi domin halin mutumtakarsa ne. AT: "shuƙa irin da yake so domin halin mutumtakarsa" ko kuma "aikata abin da yake so domin halin mutumtakarsa"
an bayyana yadda Allah na hukunta mutumin kamar yadda mutum na girbe amfanin gona. AT: "zai karɓi hukuncin abin da ya aikata"
shuka iri na bayyana aikata halin da sakamako zai biyo baya. A wannan yanayin, mutum na aikata hali mai kyau domin yana sauraron Ruhun Allah. AT: "aikata abubuwan da Ruhun Allah ke so"
"zai karɓi sakayya rai madawwami ta wurin Ruhun Allah"
"mu ci gaba da yin nagarta"
yin nagarta zuwa ga wasu domin zaman lafiyar su
"gama a lokacin da ya ɗace" ko kuma "domin a lokacin da Allah ya zaɓa"
"ta dalilin wannan" ko kuma "domin wannan"
"tun ba....waɗanda" ko kuma "musamman ... waɗanda"
"waɗanda suke gungiyar iyalin Allah ta wurin bangaskiya cikin Almasihu"
Wannan na iya nufin Bulus na so ya nanata 1) maganar da zai bi baya, ko kuma 2) cewa wannan wasikar daga gare shi ne.
Mai yiwuwa ana nufin 1) mai yiwuwa Bulus na da mataimaki wanda ke taye shi rubuta wannan wasika, shi Bulus yana gaya masa abin da zai rubuta, amma shi da kansa ne ya rubuta sashin karshi na wannan wasika, ko kuma 2) Bulus ne ya rubuta dukkan wasikar da kansa.
"sa wasu tunani mai kyau game da su" ko kuma "sa wasu tunanin cewa su mutane ne masu kirki"
"shaidar da ke bayyane a idanuwa" ko kuma " ta wurin himmar su"
"a sa dole" ko kuma " tasiri mai karfi"
" don kada Yuhadawa su tsanata musu domin sun yarda cewa a giciyen Almasihu ne kadai mutane ke samun ceto"
giciye anan na wakilci abin da Almasihu ya yi mana lokacin da ya mutu bisa giciye. AT: "aikin da Yesu ya yi bisa giciye" ko kuma "mutuwar Yesu da tashin sa"
"mutane da suke takarar ku ga yin kaciya"
"domin su iya fahari cewa sun ƙara ku cikin mutanen da suke ƙoƙarin kiyaye shari'a"
"bana taɓa son in yi fahariya da wani sai dai akan giciye" ko kuma "bari in yi fahariya a giciye ne kadai"
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "sha'anin duniya matacen a gare ni" ko kuma "ina kalon duniya kamar wani mai laifi ne da Allah ya riga ya kashe a bisa giciye"
an riga an fahimci wannan kalmomin "kassance giciyaye" a maganar baya. AT: "na kuma kassance giciyaye ga sha'anin duniya"
Mai yiwuwa ana nufin 1) mutane duniya wanda basu damu da Allah ba, ko kuma 2) abubuwan da wanda basu damu da Allah ba suke dauka ke da muhimmaci.
na da muhimmanci wajen Allah
Mai yiwuwa ana nufin 1) sabon tuba cikin Yesu Almasihu, ko kuma 2) sabon rayuwar mai bi.
Mai yiwuwa ana nufin 1) cewa masubi dukka sune Isra'ila na Allah, ko kuma 2) "bari salama da jinkai su kassnce bisa al'ummai masubi da kuma Isra'ila na Allah" ko kuma 3) bari salama ya kassance ga masu kiyaye doka, kuma jinkai ya kassance bisa Isra'ila na Allah."
Wannan na iya nufin "a karshe" ko kuma "a karshen wannan wasikar da na rubuta"
Mai yiwuwa ana nufin 1) Bulus na umurcen Galatiyawa kada su dame shi, "Na umurce ku: kada ku tayar mun da hankali," ko kuma 2)Bulus na gaya ma Galatiyawa cewa yana umurtan kowa da wannan: kada a tayar masa da hankali," ko 3) Bulus na faɗin marmarin zuciyarsa, "bana son wani ya tayar mun da hankali."
Mai yiwuwa ana nufin 1)"yi mun magana game da wannan ai'amari" ko kuma 2) "sa mun nauwaya" ko kuma "ba ni aiki mai nauyi."
waɗannan alamun taɓo ne daga muttanen da suka yi wa Bulus bulala domin basu son sa ya koyar game da Yesu. At: "gama taɓon jiki na sun nuna cewa ina bautan yesu"
"Ina addu'a kyaun zuciyar Ubangiji Yesu ya kassance da ruhun ku"
Waɗanda suke da ruhaniya sai su dawo da mutumin a hanya cikin ruhun tawali'u.
Waɗanda su na da ruhaniya su lura da kansu don kada su ma su fada a cikin gwaji.
Masubi su na cikin dokar Almasihu ta wurin ɗaukan damuwar juna.
Mutum na iya sami abin da zai yi takama, ba sai ya kwatanta kansa da wani ba.
Wanda aka koya masa maganar, wajibi ne ya raba duka ƙyauwawan abubuwansa tare da malaminsa.
Dukan abin da mutum ya shuka a ruhaniya, shine zai girba.
Mutumin da ya shuka cikin Ruhu, zai girbi rai madawwami daga Ruhu.
Mutumin da ya shuka jikinsa, na girba rashawa daga jikinsa.
Mai bi da ya cigaba da aikata nagarta zai yi girbi.
Masubi su yi nagarta mussamman ga waɗanda suke iyalin bangaskiya.
Waɗanda suke so su tilasta masubi su yi kaciya ba su so a tsananta masu saboda gicciyen Almasihu.
Bulus ya ce ya na takama da giciyen Ubangiji Yesu Almasihu.
Abu me muhimminci shi ne sabon hallita.
Bulus ya so salama da jinkai su kasance tare da waɗanda sun yi rayuwa bisa ga dokan sabon hallita, da kuma bisa Isra'ila na Allah.
Bulus ya ɗauka alamomin Yesu a jikinsa.
1 Bulus, manzon Yesu Almasihu ta wurin nufin Allah, zuwa ga kebabbu na Allah da ke a Afisa wanda suke aminci cikin Yesu. 2 Bari alheri ya kasance da ku, da salama daga wurin Allah Ubanmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu. 3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu. Shine ya albarkace mu da kowanne albarku na ruhaniya da ke cikin sammai cikin Almasihu. 4 Kafin halitar duniya, Allah ya zabe mu da muka ba da gaskiya cikin Yesu. Ya zabe mu domin mu yi zaman tsarki da rayuwar da babu aibu a gabansa. 5 Cikin kauna Allah ya kaddara ya dauke mu mu zama yayansa ta wurin Yesu almasihu. Ya yi wannan domin ya gamshe shi ya yi abin da ya ke so. 6 Sakamakon shine Allah ya karbi yabo domin daukakan alherinsa. Wannan shine abinda ya ba mu hannu sake ta wurin kaunataccensa. 7 Gama cikin kaunataccensa aka fanshe mu ta wurin jininsa, da gafarar zunubai ta wurin wadataccen alherinsa. 8 Ya ba da wannan alherin a yalwace cikin dukan hikima da fahimta. 9 Allah ya bayyana mana gaskiyar al'amarin da aka boye na shirinsa, ta wurin abin da yake so ya nuna cikin Almasihu. 10 Idan lokaci ya yi na kammala shirinsa, Allah zai kawo dukan abubuwan da ke sama da kasa cikin Yesu. 11 An zabe mu cikin Almasihu mu zama abin gado na Allah. Ya yi mana wannan shirin tun da cikin shirin sa, shi mai yin dukan abu ta dalilin nufinsa. 12 Allah ya yi haka saboda mu rayu domin yabon daukakarsa. Mune na farko da muka sami bege cikin Almasihu. 13 A cikin Almasihu ne kuma kuka samu jin maganar gaskiya, bisharan cetonku ta wurin Yesu. A cikinsa ne kuka bada gaskiya aka hatimce ku da Ruhu Mai Tsarki wanda aka alkawarta. 14 Ruhun shine tabbacin gadonmu kafin mu kai ga samunsa. Wannan don yabon daukakarsa ne. 15 Sabo da haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kaunar ku zuwa dukan wadanda aka kebe dominsa. 16 Ban fasa tunawa da ku ba ina addu'a saboda ku cikin addu'o'ina. 17 Ina addu'a da cewa Allah Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uban daraja, ya ba ku ruhun basira da wahayin saninsa. 18 Ina addu'a idanun zuciyarku su bude domin ku san tabacin kiranku. Ina addu'a dominku san arzikin mulkin gadonsa cikin wadanda aka kebe dominsa. 19 Ina addu'a ku san ikon nan nasa mai girma mara iyaka da ke cikin mu da muka ba da gaskiya. Wannan girman yana ta wurin aikin karfin ikonsa ne. 20 Wannan shine ikon da ya yi aiki cikin Almasihu lokacin da Allah ya tashe shi daga matattu ya sa shi a hannun damansa cikin sammai. 21 Ya sanya shi bisa birbishin dukan sarauta, iko, mulki, karfi, da kowanne irin suna. Ya sanya Almasihu ba a wannan zamanin kadai ba, amma da zamani mai zuwa. 22 Allah ya saka dukan abubuwa a karkashin kafafun Almasihu. Ya sa shi shugaban dukan abubuwa a cikin ikilisiya. 23 Ikilisiya jikinsa ne, cikarsa wanda ya cika dukan abubuwa cikin kowacce hanya.
Bulus ya sa sunansa a matsayin marubucin wannan wasikar wa masubi a ikilisiyar Afisus.
sai dai in an rubuta, dukan misalan "ku" da kuma "na ku" na nufin masubi na Afisus da kuma dukan masubi da haka suke suna.
Yaren ku na iya samun wani hanyar gabatar da mawallafi na wasika da kuma masu sauraro. AT: "Ni, Bulus, manzon ... rubuta wannan wasikar maku, Tsarkakun mutanen Allah Afisus"
"cikin Kristi Yesu" da magana kusan iri guda ne da ke baya nufin ainahin abun da ke faru sosai a cikin wasikun Sabon Alkawari. Su na magana akan irin karfin dangantaka mai yu'a tsakanin Kristi da waɗanda sun gaskanta da shi.
Wannan ne gaisuwa da kuma albarka da Bulus na yawan amfani da shi a cikin wasikar shi.
Bulus ya buɗe wasikar sa da magana akan matsayin masubi da lafiyarsu a gaban Allah.
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki: "mu yabe Allah Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu"
"domin Allah ya albarkace mu"
"da kowwane albarku dake zuwa daga Ruhu na Allah"
"cikin bisa halittar duniya." Kalmar "sama" na nufin wurin da Allah yake.
"cikin Kristi" da magana kusan iri guda ne da ke baya nufin ainahin abun da ke faru sosai a cikin wasikun Sabon Alkawari. Su na magana akan irin karfin ɗangantaka mai yu'a tsakanin Kristi da wa'anda sun gaskanta da shi.
Bulus ya yi amfani da kalmomi kusan iri guda domin ya nanata halin kirki mai kyau.
Kalmar "ya," "shi," da kuma "ya" na nufin Allah.
Kalmar "mu" na nufin Bulus, ikilisiyar Afisus, da dukan masubi a cikin Kristi. AT: "Allah ya shiria da daɗewa domin ya karɓe mu"
A nan "karɓa" na nufin a ajiye a gidan Allah.
Allah ya kawo masubi cikin gidan shi ta wurin aikin Yesu Kristi.
"waɗanda yake ƙauna, Yesu Kristi " ko "Ɗansa, wanda yake ƙauna"
Bulus ya yi magana akan alherin Allah kaman kayan dukiya. AT: "girman alherin Allah" ko"yawan alherin Allah"
"ya bamu wannan babban yawan alheri" ko "ya yi mana kirki na ƙwarai"
Wannan na iya nufin 1) "saboda ya na da dukan hikima da fahimta" 2) domin mu iya samun babban hikima da fahimta"
Wannan na iya nufin 1) "saboda ya so ya sa mu mu sani" ko 2) "wanda da ya so."
"kuma ya bayana wannan nufi a cikin Almasihu"
"ta hanyar Almasihui"
Ana iya fadan sabuwar jumla anan. AT: "Ya yi wannan da ni'yar yin shiri" ko "Ya yi wannan, yin tunani akan wani shiri"
"saboda idan lokaci ya kai" ko "saboda lokacin da ya sa"
Ana iya bayana wannan cikin sifar aiki. AT: "Allah ya zaɓe mu mu zama magaji"
"Allah ya zaɓe mu da wuri"
A nan kalmar "mu" na nufin Yahudawa masubi da su ka fara jin bishara, ba masubi a Afisus ba.
"saboda mu yi rayuwar yabonsa domin ɗaukakarsa"
An saka ruwan candle akan wasika an kuma hatimce da abun shaida da ke wakilin mutumin da ya rubuta wasikar. Bulus ya yi amfani da wannan al'ada a matsayin hoto don ya nuna yanda Allah ya yi amfani da Ruhu mai Tsarki domin ya tabbatar mana cewa mu nashi ne. AT: "Allah ya hatimce ku da Ruhu mai Tsarki da alkawarta"
An yi maganar karɖan abun da Allah ya yi alkawari kamar wani ya gaje kaya ko dukiya daga ɗan gida. AT: "an tabbata cewa za mu karɓa abun da Allah ya alkawarta"
Bulus ya yi adu'a ma masubi na Afisus da kuma yabon wa Allah domin ikon da masubi suke dashi ta wurin Almasihu.
Bulus ya yi anfani da "daina ba" saboda ya nanata cewa ya cigaba da gode wa Allah. AT: "na shigaba da gode wa Allah"
"ruhun basira don ganen wahayinsa"
Wannan zance "idanun zuciyarku" na nanata iyawan wani ya samu ganewa. AT: "Saboda ku samu ganewa da haskaka"
Ana iya bayana wannan cikin sifar aiki. AT: saboda Allah ya haskaka zuciyar ku" kokuwa "saboda Allah mai yuwa ya haskaka ganewan ku"
"an yi shi domin gani"
Ana maganar karɓan abin da Allah ya alkawarta wa masubi ne kamar wani ne na gadan kaya da kuma dukiya daga ɗan gidan.
Ana iya bayana wannan cikin sifar aiki. AT: "dukan wanda ya keɓe ma kansa" ko "dukan wanda sun zama cikakken nashi"
Iƙon Allah na fiye da dukan iƙo.
"sabuda anfanin mu" ko "cikin ɗangantaka wa mu"
"baban iƙon sa daku aiki ma mu"
"tashe shi daga matattu " ko "yi shi da rai kuma"
"Almasihu yana zaune a hannun damar Allah" ko "Almasihu yana zauna a wurin mai daraja a gefen Allah"
"duniyan da ya wuce iƙon ɗan Adam." Kalmar "sammai" na nufin wurin da Allah yake. Dubi yanda an fasara a cikin 1:3.
Wannan maganan dabam-dabam ne da na matsayin ya wuce iƙon ɗan Adam, duka biu mala'ika da aljani. AT: "fiye da dukan irin abun da ya wuce iƙon ɗan Adam"
A nan iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: Ma'ana na kamar 1) " kowane suna da mutum ya bayer" ko2) "kowane suna da Allah ya bayer"
Wannan na iya nufin 1) suna kokuwa 2) wurin izni.
"a wannan lokacin"
"a mai zuwa"
" Allah ya sami" ko " Allah ya saka" (UDB)
A nan "kafafun" na misali da Ubangijin Allah, izni, da kuma iko. AT: " dukan abubuwa a karkashin iƙon Almasihu"
Kawai yanda tare da jikin mutum, kai na mulki da dukan abu dake na jikinsa, haka Almasihu ne shugaban jikin ikilisiya.
A nan "shugaban" na nufin shugaba kokuwa wanda ke lura. AT: "sarkin dukan komai a cikin ikilisiya"
Ikilisiya na yawan nufin jikin Kristi.
"Almasihu ya cika ikilisiya da ransa da iƙo kamar da yake bayar da rai wa dukan abubuwa"
Bulus ya bayyana mutanen da ya ke rubuta masu kamar wanda Allah ya keɓe, kuma suna ba da gaskiya da dogara ga Yesu Almasihu.
Allah Uba ya albarkaci masubi da kowane albarka na ruhaniya a cikin sama na cikin Almasihu.
Allah Uba ya zaɓe waɗanda suka yi ĩmanĩ da Almasihu kafin a yi halittan duniya.
Allah Uba ya zabi masu bi saboda su zama masu tsarki kuma su zama marasa laifi a gabansa.
Allah ya ƙaddara masubi tun farko domin yă yarda da yin haka, kuma domin ayi masa yabo don alherinsa mai daraja.
Masubi suna samun fansa ta hanyar jinin Almasihu, da kuma gafarar zunubai.
Allah zai haɗa kome a sararin sama da kuma duniya a karkashin Almasihu.
Masubi za su samu hatimi na alkawarin Ruhu mai tsarki.
Ruhu na da tabbaci daga gadon masubi.
Bulus ya na addu'a cewa Afisawa su sami ilimin fahimtar amincewar kiransu.
Wannan ikon ya tăyar da Almasihu daga matattu ya kuma bashi wurin zama a hannun daman Allah a sama.
Allah ya sa dukan abubuwa a ƙarƙashin kafan Almasihu.
Almasihu shi ne kan kome a cikin ikklisiya.
Iklissiya ita ce jikin Almasihu.
1 Amma da ku matattu ne cikin zunubanku da laifofinku. 2 A cikinsu kuka yi rayuwa bisa ga al'amuran duniyan nan. Kuka biye wa mai sarautar ikokin sararin sama, wannan ruhun ne da ke aiki cikin kangararrun 'ya'ya. 3 Da can dukanmu muna cikin wadannan marasa bada gaskiya. Muka biye wa mugun burin jikinmu. Muna aikata halin mutuntaka da na tunaninmu. Bisa ga dabi'a 'ya'ya ne wadanda sun cancanci fushin Allah, kamar wadansu. 4 Amma Allah mai yalwar jinkai ne, sabili da matukar kauna da ya kaunace mu. 5 Sa'anda muke matattu cikin zunubai, ya kawo mu cikin sabon rai tare da Almasihu. Ta wurin alheri aka cece mu. 6 Allah ya tashe mu tare ya kuma sa muka zauna tare a matsayi guda cikin Almasihu Yesu. 7 Ya yi wannan domin a zamanai masu zuwa ya nuna mana matukar yalwar arzikin alherinsa ta wurin Yesu. Yana nuna mana wannan ta wurin alherinsa. 8 Domin ta wurin alheri aka cece ku ta wurin bangaskiya, wannan ba daga gare ku ba ne, kyauta ce ta Allah. 9 Ba daga ayyuka ba, Saboda wannan dalili kada kowa ya yi fahariya. 10 Gama mu aikin hannuwansa ne, halitattu cikin Almasihu Yesu domin mu yi kyawawan ayyuka, wadanda tun da Allah ya tanada, mu yi rayuwa a cikinsu. 11 Saboda haka ku tuna da ku al'ummai ne a dabi'ar jiki. Ana kiranku "marasa kaciya", abin da ake kira kaciya cikin jiki wadda hannayen mutane ke yi. 12 Gama a lokacin nan a rabe kuke da Almasihu. Ku bare ne ga mutanen Isra'ila. Ku baki ne ga wa'adodi na al'kawarai. Ba ku da tabbaci a kan gobe. Ba ku da Allah a cikin duniya. 13 Amma yanzu a cikin Almasihu Yesu ku da da kuke nesa da Allah, an kawo ku kusa da shi ta wurin jinin Almasihu. 14 Gama shine salamar mu. Domin ya mai da biyun daya. Cikin jikinsa ne ya rushe katangar gaba da ta raba mu da juna. 15 Wato ya kawar da shari'a mai umarnai da sharudda, domin ya halitta sabon mutum daya a cikinsa. Yin haka ya kawo salama. 16 Ya yi haka domin ya sulhunta mutum biyu cikin jiki daya ga Allah ta wurin gicciye. Ta wurin gicciye ya kashe gabar da ke tsakaninsu. 17 Yesu ya zo ya yi maku shelar salama ku da kuke nesa da ku na kusa. 18 Domin ta wurin Yesu dukanmu biyu cikin Ruhu daya muna da hanya zuwa wurin Uba. 19 Sabo da haka yanzu ku al'ummai, ko daya, ba bare ba ne. Maimakon haka ku abokai ne tare da kebabbun Allah, abokan aiki. 20 Wadanda an gina su bisa tushen manzanni da annabawa. Almasihu Yesu da kansa shine mafificin dutsen ginin. 21 A cikinsa dukan ginin ya hade tare, suna kuma girma kamar haikali cikin Ubangiji. 22 A cikinsa ne kuma ake gina ku gaba daya kun zama mazaunin Allah a cikin Ruhu.
Bulus ya tunashe masubi game da rayuwar su na da kuma yadda suke a gaban Allah yanzu.
Wannan ya nuna yadda mutane masu zunubi sun kasa yin biyaya ga Allah ta haka mutattcen mutum ba ya iya ji ta jiki.
Kalmar "laifofin" da kuma "zunuban" na da ma'ana kusan iri ɗaya. Bulus ya yi amfani da su ne domin ya nanata girman zunuban mutanen.
Manzanni sun kuma yi amfani da "duniya" don nufin halin son kai da daraja mari kirki na mutanen da su ke rayuwa a wannan duniya. AT: "bisa darajan mutane da ke rayuwa a wannan duniya" kokuwa "bin ƙa'idodi na wannan duniya"
Wannan na nufin ibilis ko kuwa shaiɗan.
"ruhun shaɗan, da ke aiki"
Kalmar "jiki" da kuma "zuciya" na misali da dukan mutum.
mutanen da Allah ke fushi da su
"Allah mai yawan jinkai ne" ko "Allah na da kirki domin mu"
"sabili da matuƙar ƙauna domin mu" ko "saboda ya na ƙaunar mu sosai"
Wannan ya nu yanda mutum mai zunubi ya kasa yin biyaya ga Allah sai an bashi sabuwan rai ta ruhaniya kamar mutatcen mutum da ba ya iya ji ta jiki sai dai an tashe shi daga mattatu.
"cikin Almasihu" da magana kusan iri guda ne da ke baya nufin ainahin abun da ke faru sosai a cikin wasikun Sabon Alkawari. Su na magana akan irin karfin ɗangantaka mai yiwuwa tsakanin Almasihu da waɗanda sun gaskanta da shi.
Ana iya bayana wannan cikin sifar aiki. AT: "Allah ya cece mu saboda yawan kirkin sa gare mu"
kaman yada ya tashe Almasihu, zai daga mu sama ma, kuma za mu kasance da Almasihu a sama.
"cikin bisa halittar duniya." Kalmar "sama" na nufin wurin da Allah yake. Dubi yadda an fasara a cikin 1:3.
"cikin Almasihu Yesu" da magana kusan iri guda ne da ke baya nufin ainahin abun da ke faru sosai a cikin wasikun Sabon Alkawari. Su na magana akan irin karfin ɗangantaka da ke tsakanin Almasihu da waɗanda sun gaskanta da shi.
"nan gaba"
Ƙaunar Allah gare mu ne dalilin da ya sa shi ya mun tsira daga hukunci idan mun gaskanta da Yesu. AT: "Allah ya cece ku ta alheri saboda bangaskiyar ku a cikinsa"
Kalmar "wannan" na nufin baya zuwa "wannan ceto bai zo saboda kyaun abubuwan da kun yi ba"ta alheri aka ceceku ta wurin bangaskiya."
"wannan ceto bai zo saboda kyaun abubuwan da kun yi ba"
"cikin Almasihu Yesu" da magana kusan iri guda ne da ke baya nufin ainahin abun da ke faru sosai a cikin wasikun Sabon Alkawari. Su na magana akan irin karfin ɗangantaka mai yu'a tsakanin Almasihu da waɗanda sun gaskanta da shi.
"bi" ko kuwa "yi" (UDB)
Bulus ya tunashar da waɗannan masubi cewa yanzu Allah ya yi Al'ummai da Yahudawa cikin jiki ɗaya ta wurin Almasihu da giciyan sa.
Wannan na nufin mutanen da ba haifafar Yahudawa ba.
Waɗanda ba mutanen Yahudawaba ba su yi kaciya kamar yara kuma don haka Yahudawa sun dauke su mutanen da ba sua bin dokokin Allah AT: "kafiri marasa kaciya"
Wannan wata ka'ida ne na mutanen Yahudawa saboda dukan jinjiraye maza ana yin masu kaciya lokacin da an haife su da kuwana 8. AT: "mutanen da an yi masu kaciya"
"marasabi"
Ma'anan na kamar 1) "Yahudawa, wanda an yi masu kaciya ta mutane" ko 2) "Yahudawa, wanda sun yi ma jikin jiki kaciya."
Ana iya bayana wannan a cikin aiki. AT: "ta abun da mutane ke kira" "ta waɗanda mutane ke kira"
Bulus ya yi wa Al'ummai masubi magana kamar su baki ne, an aje a wajen kasar wa'adodin Allah da kuma al'kawari.
Bulus ya sa alamar nuna bambanci tsakanin Afisawa kamin su yarda da Almasihu kuma bayan sun yarda da Yesu.
Saboda zunuban masubi, an raɓa su daga Allah. Ƙodashiƙe, yanzu Yesu ya kawo su kusa da Allah ta wurin jinin sa.
Jinin Almasihu na nuna mutuwar sa. AT: "ta mutuwar Almasihu" ko kuwa "lokacin da Almasihu ya mutu domin mu"
"Yesu ke bamu salama"
"ya mai da Yahudawa da Al'ummai ɗaya"
"Ta mutuwar jikin sa a kan giciye"
"katangar kiyayya" ko kuwa "katangar mugun nufi"
Kalmar "mu" na nufin Bulus da Afisawan. Su Al'umman an raɓa su daga Yahudawan. AT: "Wancan ya raɓa mu Yahudawa daga Al'ummai daga junan mu"
Jinin Yesu ya biya buƙatar shari'a na Musa saboda duka Yahudawa da Al'ummai su iya zaman salama a cikin Allah.
gudan saban mutane, mutanen ceton 'yan adam duka
Haɗuwa ne da Almasihu ya sa sulhu mai yiwuwa tsakanin Yahudawa da Al'ummai.
"Almasihu ya kawo Yahudawa da Al'ummai tare a cikin salama"
Gicciye anan na nuna mutuwar Almasihu a bisa gicciye. AT: "ta wurin mutuwar Almasihu a bisa gicciye"
An bayyana daina gabar su kamar ya kashe gabar su. Ta mutuwar sa a bisa gicciye Yesu ya cire dalilin da Yahudawa da Al'ummai za su yi gãba da juna. Ko yanzu ya kamata su yi rayuwa ta shari'a na Musa. AT: "hana su daga ƙiyayya da juna"
Bulus na faɗa wa masubi na Afisus cewa masubi na Al'ummai da ke nan sun zama ɗaya tare da manzanen Yahudawa da anabawa; su ne haikali na Allah a cikin Ruhu.
"sanar da bishara na salama" kokuwa "furta bishara na salama"
Wannan na nufin Al'ummai ko kuwa waɗanda ba Yahudawa ba.
Wannan na nufin Yahudawa.
Anan"mu biyu" na nufin Bulus, Yahudawa masubi, da masubi da ba Yahudawa ba.
Dukan masubi, da Yahudawa da Al'ummai, an basu yanci su zo gaban Allah Uba ta Ruhu mai Tsarkin nan ɗaya.
Bulus yana kuma magana game da yanayin ruhaniyar Al'ummain bayan sun zama masubi kaman yadda zai yi magana akan baƙi yadda za su zama 'yan gari na kasa dabam.
Bulus ya yi magana akan mutanen Allah kaman sun zama gini. Almasihu ne shi ne mafificin dutsen ginin, manzane ne tushe, kuma masubin ne abin da an kafa.
Ana iya bayana shi cikin sifar aiki. AT: "Allah ya riga ya gina ku" (Dubi:
Bulus ya cigaba da magana akan iyalin Almasihu kamar gini ce. Yanda mai gini na kafa dutse tare a yin gini, haka ne Almasihu yana kafa mu tare.
"a cikin Almasihu ... a cikin Almasihu Yesu ... a cikin Almasihu "Wannan zancen kwatanacin na nanata irin karfin ɗangantaka da ke tsakanin Almasihu da waɗanda sun gaskanta da shi.
Wannan na kwatanta yanda ana hada masubi tare don su zama wurin da Allah zai yi zaman dawama ta wurin iƙon Ruhu mai Tsarki.
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "Allah na kuma gina ku tare"
Dukkan marasa bi matattu ne a cikin laifofinsu da zunubansu.
Ruhun mai mulkin hukumomi na iska ya na aiki a cikin 'ya'yan marasa biyayya.
Dukkan marasa bi da ga halintansu 'ya'ya masu fushi ne.
Allah ya kawo wasu marasa bi zuwa ga sabon rai a cikin Almasihu domin yawan rahamansa da kuma kauna mai girma.
Masubi sun sami ceto ta alherin Allah.
Masubi suna zama a sama da Yesu Almasihu.
Allah ya ceta ya kuma tăyar da masubi, domin a shekaru masu zuwa idan ya yiwu ne ya nuna masu girman arzikin alherinsa.
Kada wani mai bi ya yi alfahari da aikin sa, domin yă sami ceto ta wurin alherin kyautar Allah.
Nufin Allah ne wa masubi a cikin Yesu Alamasihu su yi tafiya a cikin ayukka masu kyau.
Al'ummai marasa bi an raba su daga Almasihu, an rarraba su da ga Isra'ila, baƙi a wurin alkawari, marasa bege kuma marasa Allah.
Wasu al'ummai marasa bi sun sami kusanci da Allah ta wurin jinin Yesu.
Ta wurin jikin sa, Almasihu ya zamar da al'ummai da Yahudawa sun zama mutane daya, lalata rashin jituwa da ya raba su.
Almasihu ya warware shari'ar dokoki da kuma ka'idodi domin kawo salama tsakanin Yahudawa da Al'ummai.
Dukka masubi suna samun hanya zuwa Uba ta hanyar ruhu mai tsarki.
An gina Iyalin Allah a kan tushen manzanninsa, da annabawansa, Yesu Almasihu ne kuwa ginshiƙin.
Ikon Yesu yana harhada tare yana kuma kara dukkan ginin iyalinsa.
Ginin iyalin Allah haikali ne da aka keɓe wa Ubangiji.
Allah yana zaune a cikin ruhun mai bi.
1 Saboda haka, ni Bulus, dan sarka sabili da Almasihu dominku al'ummai. 2 Ina zaton kun ji a kan aiki mai girma na alherin Allah da ya ba ni dominku. 3 Ina rubuto maku bisa ga wahayin da aka sanashe ni. Wannan ita ce boyayyar gaskiya da na rubuta a takaice a cikin wata wasikar. 4 Sa'adda kuka karanta a kan wannan, za ku iya fahimtar basira ta cikin boyayyar gaskiya a kan Almasihu. 5 Wanda a zamanun da ba a bayyana wa mutane ba. Amma yanzu an bayyana shi ga manzanni da annabawa kebabbu a cikin Ruhu. 6 Wannan boyayyar bishara ita ce al'ummai ma abokan gado ne tare da mu, gabobi ne cikin jiki daya. Abokan tarayya ne kuma cikin alkawaran Almasihu Yesu ta wurin bishara. 7 Domin wannan na zama bawa ta wurin baiwar alherin Allah da ya bani ta wurin karfin ikonsa. 8 Allah ne ya ba ni wannan baiwa. Ko da shike nine mafi kankanta cikin kebabbun Allah, in yi shelar bishara ga al'ummai akan wadatar Almasihu marar matuka. 9 In kuma fahimtar da dukan mutane a kan shirin Allah, wannan boyayyar gaskiya wadda tun zamanai da suka wuce Allah ya boye, shi da ke mahallicin dukan abubuwa. 10 Saboda haka, ta wurin ikilisiya, masu iko da masu mulkin sararin sama za su san hikimar Allah ta fuskoki daban daban. 11 Wannan ya kasance bisa ga dawwamammen nufi da ya zartar cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu. 12 Gama a cikin Almasihu muna da gabagadi, da dama, da amincewa sabili da gaskiyar mu a cikinsa. 13 Saboda haka ina rokon ku kada ku karaya da wahalar da na sha domin ku wadda ta zama daukakar ku. 14 Saboda haka nake durkusawa da gwiwa ta a gaban Uba, 15 wanda ta wurinsa ake kiran kowanne iyali na sama da na kasa. 16 Ina addu'a ya amince maku bisa ga yalwar wadatar daukakarsa, ku karfafa matuka da iko ta wurin Ruhunsa, da yake cikinku. 17 Ina addu'a Almasihu ya zauna a cikin zuciyar ku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu'a ku kafu ku kuma ginu da zurfi kwarai cikin kaunarsa. 18 Ku kasance cikin kaunarsa domin ku gane, tare da dukan masu bi, menene zurfi, da fadi, da tsawon kaunar Almasihu. 19 Ina addu'a domin ku san mafificiyar kaunar Almasihu da ta wuce sani. Ku yi wannan domin a cika ku da dukan cikar Allah. 20 Yanzu ga wanda yake da ikon aikata dukan abu fiye da abin da muke roko ko tunani, bisa ga ikonsa da ke aiki a cikinmu, 21 daukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikilisiya ta wurin Almasihu Yesu har ya zuwa zamanun zamanai har abada abadin. Amin.
Domin a bayyana wa masubi boyayyen gaskiya game da ikilisiya, Bulus na nufin ɗayantaka na Yahudawa da Al'ummai da kuma haikali wanda yanzu masubi na ciki.
"Saboda alherin Allah gare ku"
"wanda Almasihu Yesu ya sa a sarka"
"alhakin da Allah ya bani na kawo alherin sa gare ku"
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "bisa ga abinn da Allah ya bayyana mani"
Bulus na nufin wani wasikar da ya rubuta wa waɗanan mutane.
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "Allah bai bayyana waɗannan abubuwan wa mutane a zamanin da ya wuce ba"
Ana iya bayyana wannan cikin sifar aiki. AT: "Amma yanzu Ruhu ya bayyana shi" ko "Amma yanzu Ruhu ya sa ya zama sananne"
"manzanni da annabawa wanda Allah ya keɓe su domin su yi wannan aiki"
Wannan ne boyayyen gaskiya da Bulus ya fara bayyanawa a cikin sura na baya. Al'ummai da su ka karɓi Almasihu sun kuma karɓi abu iri guda da Yahudawa masubi.
sau da yawa ikilisiya na nufin jikin Almasihu.
"cikin Almasihu Yesu" da makamanin waɗannan karin magana sun auku sau da dama a wasikun Sabon Alkawari. Sun yi magana ne ƙwarai akan ɗangantaka da ke yiwuwa tsakanin Almasihu da waɗanda suka yarda da shi.
suna iya nufin1) saboda bisharar da Al'ummai suna masu rabo a cikin alkawarin 2) saboda bishara da Al'ummai suna masu gãdo da gabobi na jiki da kuma masu rabo a cikin alkawarin.
"waɗanda Allah ya keɓe wa kansa"
wanda bai iya sani gabadaya ba
Bulus ya yi magana game da gaskiya akan Almasihu da kuma albarkun da yake kawo kamar kayan wadata.
Fahimtar da mutane na wakilin koyar da su. AT: "haskakka haske a kan boyayyen shirin Allah don dukan mutane su sani abun da yake" ko "koyar da dukan mutane abin da boyayyen shirin Allah yake"
Ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. "Allah da ya hallici dukan abubuwa, ya aje wannan boyayyar shirin tun da dadewa a zamanin da suka wuce"
hikimar Allah ta fuskoki daban daban-"Allah zai sa baban hikimar sa ya zama sananne ga dukan masu iƙo da mulkin sararin sama ta wurin ikilisiya"
Kalmomin nan na da ma'ana kusan iri ɗaya. Bulus ya yi amfani da su ne don ya nanata cewa kowane rai na ruhaniya zai san hikimar Allah.
"cikin duniyan da ta wuce na ɗan'adam." Kalmar "sararin" na nufin wurin da Allah yake. Dubi yanda an fasara a 1:3.
hikimar Allah ta fuskoki daban daban- hikimar Allah mai wuyan ganewa
"cikin riƙen dawwamammen nufin" ko kuwa "daidaitawar dawwamammen nufi"
Bulus ya yabe Allah a cikin wahaloli ya kuma yi adu'a domin wannan masubi na Afisus.
"bamu da tsoro" ko kuwa "muna da karfin zuciya"
"dama cikin gaban Allah da amincewa" kokuwa "yancin shiga cikin gaban Allah da amincewa"
yaƙini" kokuwa "tabbaci"
A nan "ɗaukaka" na kwatanta takama wanda za su ji ko za su ji a mulki mai zuwa. Masubi na Ephesus su yi takama akan abun da Bulus ke shan wahala a sarka. AT: "Saboda da anfanin ku" ko "yakamata ku yi takama akan wannan"
"Saboda Allah ya yi dukan wannan wa ni"
Durkusawar gwiwa hoto ne na dukan mutum a cikin halin adu'a. AT: "Ina durkusa a cikin adu'a wa Uba" ko "Ina addu'a da kasƙanta wa Uba"
Yin suna anan halamane kuma wakilin yin halicci. AT: "wanda ya yi halitta da kuma yin sunan kowane iyali a sama da kasa"
"Allah, domin shi mai girma da kuma mai iƙo, zai yarda maku ku zama da karfi da iƙonsa"
"zai baku"
Bulus ya cigaba da addu'ar da ya fara a cikin 3:14.
Wannan ne abu na biyu wanda Bulus ya yi addu'a cewa Allah zai "biya" su Afisawan "bisa ga bisa ga yalwar wadatar na iƙon sa"; na farko shi ne za su "karfafu" (3:14).
A nan "zuciya" na misali da cikin mutum, da kuma "ta wurin" na fada hanyar yadda Almasihu na rayuwa a cikin maibi. Almasihu na rayuwa a cikin zuciyar masubi saboda Allah ta alherinsa ya yarda su sumu bangaskiya.
Ma'anar na kamar 1) "bangaskiya. Ina adu'a ku kafu ku kuma ginu da zurfi ƙwarai cikin ƙaunarsa domin ku gane" kokuwa 2) "bangaskiya don ku ginu da zurfi kwarai cikin ƙaunarsa. Ina addu'a ku gane"
Bulus yana magana game da bangaskyar su kamar itace dake da saiwa mai zuifi ko kuwa gida da a ka gina ta a tushe mai kauri. AT: "saboda ku zama kamar itace da saiwar sa mai zuifi ne da karfi da kuma gini da aka gina a kan dutse"
Wannan ne na biu da Bulus ya durkusar da gwiwar sa a addu'a; na farko shi ne, saboda Almasihu ya biya da kuma su suma karfafawa (3:14) kuma Almasihu ya yi rayuwa a cikin zukatar su ta wurin bangaskiya (3:14). Kuma "gane" shi ne farkon abu da Bulus ya yi addu'a cewa Afisawan dakansu su iya yi.
"dukan masubi a cikin Almasihu" ko kuwa "dukan tsattsarka"
Ma'anar na kamar 1) Wannan kalma na kwatanta girman hikimar Allah, AT: "yadda kowane Allah mai wayo yake" ko 2) wannan kalma na kwatanta ƙauna mai tsanani da Almasihu ke da shi domin mu. AT: "nawa Almasihu yake ƙaunar mu"
Wannan ne abu na biyu da Bulus ya yi addu'a saboda Afisawa su iya yi; na farko shi ne su "gane." AT: " saboda ku san girman hikimar ƙaunar Almasihu domin mu"
Wannan ne abu na uku da Bulus ya durkusa da gwiwan sa ya yi addu'a (3:14); na farko shi ne su "karfafa" (3:14), kuma na biyu shi ne su "iya gane" (3:18).
Bulus ya gama addu'a sa da albarka.
Kalmar "muke" ko "mu" a cikin wannan littafin ya sa ciki dukan Bulus da dukan masubi.
"Yanzu ga Allah, wanda"
Allah na iya yin fiye da muke roƙo, ko tunani.
Allah ya bawa Bulus kyauta domin amfanin al'ummai.
Ɓoyayyen Gaskiya game da Almasihu ne ba a bayyana ba a wasu zamanai.
Allah ya bayyana ɓoyayyen gaskiya game da Almasihu zuwa ga manzanninsa da kuma anabawansa.
Ɓoyayyen gaskiyan da aka bayyana ita ce al'ummai da magadansu da kuma yan'uwansu na jiki, da kuma yan'uwansu na tărayya a cikin alkawarin Yesu Almasihu.
An ba wa Bulus kyautar alherin Allah.
An aika Bulus ya taimaka wa al'ummai su fahimci shirin Allah.
Ta hanyar ikklisiya haɗadɗun hikimar Allah za su zama sanannu.
Bulus ya ce masubi suna da gabagadi da hanya ta amincewa domin bangaskiya a cikin Almasihu.
An yi suna da halittar Kowace iyali a sama da kuma duniya bayan Uban.
Bulus yana addu'a masubi su samu karfafawa tare da iko ta hanyar ruhun Allah.
Bulus ya na addu'a masubi su iya fahimtar faɗi, da tsawo, da dogo, da kuma zurfin kaunar Almasihu.
Bulus ya na addu'a ce wa za a bada daukaka a cikin ikklisiya da kuma a cikin Yesu Almasihu wa Uban dukan zamani.
1 Saboda haka a matsayi na na dan sarka saboda Ubangiji; ina rokon ku ku yi zaman rayuwa da ta cancanci kiran da Allah ya kiraye ku. 2 Ku zamna da matukar tawali'u da sahihanci da hakuri. Ku karbi juna cikin kauna. 3 Ku yi kokarin zaman dayantaka cikin Ruhu kuna hade cikin salama. 4 Akwai jiki daya da kuma Ruhu daya, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan daya. 5 Ubangiji daya, bangaskiya daya, da kuma baftisma daya. 6 Allah daya ne da Uban duka. Shine bisa duka, ta wurin duka, da kuma cikin duka. 7 Ko wannenmu an ba shi baiwa bisa ga awon baiwar Almasihu. 8 Kamar yadda nassi ya ce, "Da ya haye zuwa cikin sama, ya bi da bayi cikin bauta. Ya kuma yi wa mutane baye baye. 9 Menene ma'anar, "Ya hau?" Ana cewa kenan ya sauka har cikin zurfin kasa. 10 Shi da ya sauka shine kuma wanda ya hau birbishin sammai. Ya yi wannan domin ya cika dukan abubuwa. 11 Almasihu ya ba da baye baye kamar haka: manzanni, annabawa, masu shelar bishara, makiyaya, da masu koyarwa. 12 Ya yi haka domin ya shiryar da masu bi saboda hidima, domin gina jikin Almasihu. 13 Ya yi haka har sai mun kai dayantakar bangaskiya da sanin Dan Allah. Ya yi haka har sai mun kai ga manyanta, kamar wadanda suka kai cikakken matsayin nan na falalar Almasihu. 14 Wannan ya zamanto haka domin kada mu kara zama kamar yara. Kada a yi ta juya mu. Wannan haka yake domin kada mu biye wa iskar kowacce koyarwa ta makirci da wayon mutane masu hikimar yin karya. 15 Maimakon haka za mu fadi gaskiya cikin kauna domin mu yi girma cikin dukan tafarkun da ke na sa, shi da yake shugaba, Almasihu. 16 Almsihu ya hada dukan jikin masu ba da gaskiya. Jikin yana hade ta wurin kowanne gaba, domin jikin ya yi girma ya gina kansa cikin kauna. 17 Saboda haka ina yi maku gargadi cikin Ubangiji cewa, kada ku sake yin rayuwa irin ta al'ummai da suke yi cikin azancin wofi marar amfani. 18 Sun duhunta cikin tunaninsu. Bare suke da rai irin na Allah, ta wurin jahilcin da ke cikinsu da ta wurin taurare zukatansu. 19 Basa jin kunya. Sun mika kansu ga mutumtaka ta yin kazamtattun ayyuka da kowacce zari. 20 Amma ba haka kuka koyi al'amuran Almasihu ba. 21 Ina zaton kun rigaya kun ji a kansa. Ina zaton an koyar da ku cikinsa, kamar yadda gaskiyar Yesu ta ke. 22 Dole ku yarda halin ku na da, wato tsohon mutum. Tsohon mutumin ne ya ke lalacewa ta wurin mugun buri. 23 Ku yarda tsohon mutum domin a sabonta ku cikin ruhun lamirinku. 24 Ku yi haka domin ku yafa sabon mutum, mai kamanin Allah. An hallitta shi cikin adalci da tsarki da gaskiya. 25 Saboda haka ku watsar da karya. "Fadi gaskiya ga makwabcin ka", domin mu gabobin juna ne. 26 "Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi." Kada ku bari rana ta fadi kuna kan fushi. 27 Kada ku ba shaidan wata kofa. 28 Duk mai yin sata, kada ya kara yin sata kuma. Maimakon haka, ya yi aiki. Ya yi aiki da hannuwan sa domin ya sami abin da zai taimaka wa gajiyayyu. 29 Kada rubabbun maganganu su fito daga cikin bakinku. Maimakon haka, sai ingantattu da za su ba da alheri ga masu ji. 30 Kada ku bata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai domin ta wurin sa ne aka hatimce ku domin ranar fansa. 31 Sai ku watsar da dukan dacin rai, da hasala, da fushi, da tankiya, da reni tare da dukan mugunta. 32 Ku yi wa juna kirki, ku zama da taushin zuciya. Ku yafe wa juna, kamar yadda Allah cikin Almasihu ya gafarta maku.
Saboda abin da Bulus ya yi ta rubuta wa Afisawa, ya fada wa masubi yadda za su yi zaman rayuwan su a matsayin masubi kuma ya nanata cewa masubi su yarda da junansu.
"kamar wani da yake sarka saboda zaɓin sa domin ya bauta wa Ubangiji"
Zama na kaman hayar da aka saba nanata ra'ayin na zaman rayuwa.
"ku zama masu tawali'u, masu hankali, da hakuri"
"ku biɗa zaman tare a cikin salama domin ku kula da ɗayantaka cikin Ruhu"
sau da yawa ikilisiya na nufin jikin Almasihu.
"Ruhu mai Tsarki ɗaya kadai" (UDB)
"Allah ya kira ku domin ku sami amincewa da bege a kiran ku" ko "akwai abu daya da Allah ya zaɓe ku ku amince a ciki kuma ku sa rai ya yi"
Kalmar "duka" anan na nufin "kome da kome."
Bulus na tunashe da masubi akan kyautar da Almasihu ya ba masubi domin su yi amfani da shi a cikin ikilisiya, wanda shi ne dukan jikin masubi.
Maganar anan na daga wakan da sarki Dauda ya rubuta.
Ana iya bayana a cikin aiki. AT: "Allah ya bayar da alheri ga kowanen mu" ko "Allah ya bayar da kyauta ga kowane maibi"
"lokacin da Almasihu ya je cikin sama"
"Almasihu ya je sama"
"Almasihu ya kuma wuce kasa"
su na iya nufin1) zurfin kasa na sashin kasa kokuwa 2) "zurfin sashen" wani hanya ne na nufin kasa." AT: "cikin zurfin sashen, kasan."
"domin ya kasance a ko ina a cikin iƙonsa"
"kammala" kokuwa "biya bukata"
ana iya bayana wanda Almasihu ya bayar da kyautan ba shakka. AT: "Almasihu ya bayar da waɗannan ofisoshin ga ikilisiya" ko "Ya ba mutane wannan alhakin ga ikilisiya
"ya shiryar mutanen da ya keɓe" ko kuwa "ya tanada wa masubi"
"domin su iya yi ma waɗansu hidima"
Bulus na maganar mutanen da suke girma a ruhania kamar suna motsa jiki don su kara karfin motsar jikin su.
"ƙarin kyau"
"jikin Almasihu" na nufin ga dukan mutumin membobi na ikilisiyar Kristi.
Ya kamata masubi su san Yesu a matsayin Ɗan Allah idan sun hadu a bangaskiya da girma a matsayin masubi.
"zama daidai da karfi a bangaskiya" ko "zama tare a cikin bangaskiya."
Wannan mahimmin suna ne wa Yesu.
"kai ga manyantar masubi"
"cikaken girma," "yi girma," ko "cikakke"
Bulus na nufin masubi wanda basu yi girma a cikin ruhaniya kamar su zama yaran da sun samu ji kadan a rayuwa. AT: "zama kaman yara"
Wannan na maganar mai bi da bai manyanta ba kuma na bin koyarwa da ba daidai ba kaman maibin ya zama kwalekwalen da iska ke bugawa a kowane waje a ruwa.
"ta mutane masu wayo da suke da dabara ga masubi da fasahar karya"
Bulus ya yi amfani da jikin mutum ya bayana yanda Almasihu ya sa masubi su yi aiki tare a cikin jituwa kaman yanda kan jiki yake sa gabobin jiki su yi aiki tare don su yi girma da kyau.
"jijiya" ɗauri ne mai karfi dake haɗa kasusuwa ko kuwa gabobin cikin wurin jikin.
"yanda membobin suna ƙaunan juna"
Bulus ya fada masu abun da kar su yi dashiƙe yanzu da su masubi an hatimce su da Ruhu mai Tsarki na Allah.
"Domin abun da na ce, zan fada wani abu mafi karfi don in karfafa ku domin mu duka na Yesu ne"
Tafiya na nuna yanda mutane suna rayuwar su. AT: "daina rayuwa kamar Al'ummai da banzan tunani"
Ba sua tsammani ko tunani da kyau. AT: "sun duhunta tunanin su" kokuwa "Ba su iya ganewa ba"
Ana iya bayana wanan cikin sifar aiki. AT: "Domin ba su san Allah ba, ba za su iya yin rayuwa yanda Allah yake son mutanen sa su yi rayuwa ba." ko "Sun cire kansu daga rai na Allah ta wurin jahilcinsu"
"yanke" ko kuwa "raɓa"
"rashin sani" kokuwa "rashin labari"
Sun ki su saurare Allah su kuma bi koyarwan sa.
Bulus na magana a kan mutanen nan kamar su abu ne da su da kansu aka ba waɗansu mutane, kuma ya yi magana game da yanda suke so su biya bukatar jikin su kaman mutumin ne wanda sun mika kansu. AT: "su na so su biya bukatan jikinsu kadai"
Kalmar "amma" na nufin yanda Al'umai su ke zama, kamar yanda an kwatanta a cikin 4:17. Wannan na nanata cewa abun da masubi suka koya akan Almasihu akasi ne. AT: "Amma abun da kun koya daga Almasihu ba haka bane"
Bulus ya sani cewa Afisawa sun ji kuma sun koya.
sunna iya nufin 1) "mutanin Yesu sun koya maku" ko 2) "wani ya koya maku domin ku mutanin' Yesu."
"yadda komai game Yesu gaskiya ne"
Bulus na magana game da kyauwawan hali kaman sun zama gutsuren tufafi. AT: "domin ku daina rayuwa yadda kuke rayuwa a da"
Bulus na magana game da kyauwawan hali kaman sun zama gutsuren tufafi. AT: "domin ku daina rayuwa ku ta da"
" tsohon mutumin" na nufin "tsohon hali" ko "hali na da."
Bulus ya yi magana akan tsohon halitar mutum kamar mutaccen jiki dake sokawa zawa cikin kabarin sa .
Ana iya bayana a cikin aikin. AT: "domin ku yarda Allah ya sake halin ku da tunanin ku" ko kuwa "domin ku yarda Allah ya baku sabon hali da tunani"
Bulus na magana game da taƙaitaccen darasi kaman su zama gutsuren tufafi. AT: "domin ku yi sabon rayuwa, da aka hallita bisa ga kamannin Allah" ko "domin ku fara rayuwa a cikin sabon hanya da saboda an hallice ku bisa ga kamannin Allah"
"gaskiyar adalci da tsarki"
"ku daina fadin karya"
"mun zama na junan" ko "mu yan gidan Allah ne"
"za ku iya yin fushi, ama kadda ku yi zunubi" ko kuwa "idan kun yi fushi, kadda ku yi zunubi"
"Dole ne ku daina yin fushi kafin dare" ko "Kadda fushin ku ya kai tsawon lokaci"
"Kada ku ba shaidan wata kofa ya kai ku ga zunubi"
Wannan na nufin magana da ke mara tausayi ko mara ladabi.
"domin karfafa juna" ko "domin karfawan juna"
"bukatar su. A haka kuwa za ku taimake waɗanda sun ji ku"
"kada ku tsananta" ko "kadda ku tar da hankalinku"
Ruhu ma Tsarki ya yi wa masubi alkawari cewa Allah zai fanshe su. Bulus na magana game da Ruhu mai Tsarki kamar shi ne alama da Allah ya sa wa masubi domin ya nuna cewa nashi ne. AT: "domin shi ne hatimi da ya tabatar da cewa Allah zai fanshe ku a ranar fansa" ko "domin shi ne ya tabatar cewa Allah ne zai fanshe ku a ranar fansa" ko
Bulus ya gama da umurnin sa game da abinda bai kamata masubi su yi ba ya kuma kare da abun da dole ne su yi.
sunna iya nufin 1) dole ne ku yi shi da kanka ko 2) "dole ne ku yadda Allah ya dauke"
"daina jin fushi akan mugun abubuwa da waɗansu su yi ma ku"
lokacin zafin fushi
taƙaitaccen darasin ajali na fushi
"maimako, dole ne ku yi kirki"
"ladabi" ko "cike da tausayi"
Bulus ya na gargadin ma su bi su yi zaman tawali'u, da hakuri, da kuma yarda da juna a cikin kauna.
Bulus ya ce akwai jiki guda, ruhu, fata gabagadi, Ubangiji, bangaskiya, baftisma, da kuma Allah Uba.
Almasihu ya bawa kowane mai bi kyauta bisa ga aunin kyautar Almasihu.
Almasihu ya ba wa jikin kyautar manzanninsa, annabawansa, ma su bishararsa, fastoci, da kuma malamai.
Kyauta biyar na jiki ya kamata su ba wa masubi wadata domin aiki, don gina jiki.
Masu bi zasu iya zama kamar yara ta wurin yawan jujjuyawa su da za a yi da kuma yadda ta wurin yaudarar mutane da kuma kuskuren yaudara.
Jikin masubi suna a harhaɗe, gaɓobinsu su kuwa na rike su a harhaɗe, kowane sashi kuma na aiki domin ƙarin girman jikin, domin gina kowane ɗaya a cikin ƙauna.
Al'ummai suna da tunani ma su duhu, sun rabu da Allah sun kuma koma wa ayukka marasa tsarki.
Masubi ya kammata su ƙauda tsohon mutum, su kuma ɗauki sabon mutum.
Mai bi yana iya ba wa shaiɗan zarafi ta wurin barin fushin sa ya kai fadiwar rana.
Ya zama tilas ma masubi su yi aiki domin su iya taimakon mai bukata.
Kada wata alfasha ta fita da ga bakin mai bi, amma a maimakon wadannan ya furta kalmomin da za su gina wasu.
Ya zama tilas kada mai bi ya yi baƙin cikin ruhu mai tsarki.
Ya zama tilas mai bi ya gafarta ma wasu domin Allah a cikin Almasihu ya gafarta masa.
1 Saboda haka ku zama masu koyi da Allah, kamar kaunatattun 'ya'yansa. 2 Ku yi zama cikin kauna kamar yadda Almasihu ya kaunace mu, ya kuma mika kansa sadaka da hadaya ga Allah dominmu, hadaya mai kanshi abin karba ga Allah. 3 Fasikanci ko kowacce irin kazamta, ko kazamar lalata kada a ambace su a tsakaninku, don haka ya dace ga masu bi. 4 Kada a ambaci batsa, maganar wauta ko alfasha wadanda ba su dace ba. Maimakon haka, mu zama masu godiya. 5 Domin wannan kun sani cewa ba fasiki, ko mara tsarki, ko mai hadama wato mai bautar gumaka zai sami gado cikin mulkin Almasihu da Allah. 6 Kada kowa ya rude ku da maganganun wofi. Saboda wadannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa kan kangararrun 'ya'ya. 7 Kada ku yi tarayya tare da su. 8 Domin da ku duhu ne, amma yanzu ku haske ne cikin Ubangiji. Sai ku yi tafiya kamar 'ya'yan haske. 9 Saboda amfanin haske shine dukan alheri, adalci da gaskiya. 10 Kuna bidar abin da Ubangiji ke murna da shi. 11 Kada ku sa hannu ga ayyuka marasa amfani da ayyukan duhu amma gara a tone su. 12 Don abubuwan da suke yi a boye abin kunya ne a bayyana su. 13 Dukan abu, idan haske ya bayyana su, za a gan su. 14 Domin duk abin da aka bayyana ya zama haske. Saboda haka aka ce, "Ka farka, kai mai barci, ka tashi daga cikin matattu; Almasihu kuwa zai haskaka bisanka". 15 Saboda haka, ku maida hankali yadda kuke rayuwar ku, ba kamar mutane marasa hikima ba amma kamar masu hikima. 16 Ku yi lura yadda kuke amfani da lokaci don kwanakin miyagu ne. 17 Kada ku zama wawaye. Maimakon haka, ku fahimci ko menene nufin Ubangiji. 18 Kuma Kada ku bugu da ruwan inabi, don yana iya lalata rayuwa. Maimakon haka, ku cika da Ruhu Mai Tsarki. 19 Kuna magana da junanku cikin zabura da wakoki da wakokin ruhaniya, kuna rairawa da yabo da zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum kuna ba da gaskiya domin dukan abubuwa cikin sunan Ubangiji Yesu ga Allah Uba. 21 Kuna sarayadda kanku ga juna cikin girmama Almasihu. 22 Mata, ku yi biyayya ga mazan ku kamar ga Ubangiji. 23 Domin miji shine shugaban matarsa kamar yadda Almasihu yake shugaban ikilisiya. Shine kuma mai ceton jiki. 24 Amma kamar yadda ikilisiya take biyayya ga Almasihu, haka kuma dole mata suyi ga mazajen su cikin kowanne abu. 25 Mazaje, ku kaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya har ya ba da kansa dominta, 26 Ya yi wannan domin ya tsarkake ta. Ya wanke mu da ruwan wanki ta wurin kalma. 27 Ya yi wannan domin ya mika ma kansa ikilisiya mai daraja, ba tare da tabo ko cikas ko wani abu kamar wadannan, amma ta zama da tsarki da kuma mara aibi. 28 Hakannan kuma, mazaje su kaunaci matansu kamar jikunnansu. Wanda yake kaunar matarsa yana kaunar kansa. 29 Ba wanda ya taba kin jikinsa. Amma, yakan ciyadda shi yana kaunarsa, kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikilisiya. 30 Domin mu gabobin jikinsa ne. 31 "Domin wannan mutum zai rabu da ubansa da uwarsa ya manne wa matarsa, su biyu su zama nama daya". 32 Wannan asirin gaskiyar, da girma yake, amma ina magana ne game da Almasihu da ikilisiyarsa. 33 Duk da haka, kowannenku dole ya kaunaci matarsa kamar kansa, matar kuma dole ta girmama mijinta.
Bulus ya cigaba da faɗa wa masubi yadda ya kamata su yi rayuwa da kuma yadda bai kamata su su yi rayuwa ba a matasyinsu na 'ya'yan Allah.
"Saboda haka ku yi abinda Allah ya yi." Saboda da haka na maida zuwa 4:31 wadda na magana akan dalilin da masubi su yi koyi da Allah, domin Almasihu ya yafe wa masubi.
Allah na so mu yi koyi ko mu bi shi da shiƙe mu 'ya'yansa ne. AT: "kamar 'yadda ƙaunatattu 'ya'ya suna ƙaunar ubanninsu" ko "domin ku 'ya'yan sa ne kuma yana ƙaunar ku sosai"
Wato yadda mutum ke rayuwa. AT: "yi zaman rayuwa na ƙauna"
"Bayaswa da hadaya kamar kamshi mai daɗi zuwa ga Allah"
"kada ku yi wani abu da mutane za su yi tunani kuna da zunubin faskanci ko wani kazanta ko hadama"
"wani halin kirki mara kazanta"
"maimako ku gode wa Allah"
Karɓan abinda Allah ya alkawatar wa masubi ne an yi maganasa kamar wata kayan gãdo da dukiya daga cikin iyali.
kalamai da ba gaskiya a cikin su
Kamar yanda mutum baya iya gani a duhu ba, haka ne mutanen da suke kaunan zunubi sun rasa fahimta na ruhaniya.
Kamar yadda mutum yake gani a haske, haka mutane da Allah ya cece su suke gani yadda za su gamshe Allah.
"yi rayuwa kamar mutane da suka fahimta abinda Allah yake so su yi"
Kamar yadda iche mai lafiya ke ba da 'ya'ya kyawawa, mai bi zai yi abinda ke da kyau, a yi abubuwan adalci da Allah ke so da shi yi yi, da yin kalmomin na gaskiya.
Bulus ya yi maganan rashin amfani, ababan zunubi da marabi ke aikatawa kamar aikin shaidan da mutane ke yi a duhu da ba ba wanda zai gan su. AT: "Kada ku yi ayuka mara amfani, ayukan zunubi da marasa bi"
ayukan da ba su yin abu mai kyau, mai amfani, ko mai riɓa
"a kawo su zuwa ga haske" ko kuwa "a tuɓe su" ko "a nuna a kuma gaya wa mutane yadda waɗanan ayukan mara kyau ne"
Yana a ɓoye idan wanan rubutu yana a haɗe da rubutu daga anabi Ishaya ko rubutu ne daga wakar da masubi sun yi.
"mutane na iya gani sarai dukan abinda ya zo wurin haske."Wannan na kwatanta yadda kalmar Allah na bayana yadda ayukan mutane ke da kyau ko mumuna, ku fasara shi a yanda yake.
Ma'anan su na kamar 1) Bulus na magana ne da marasabi wadda ya kamata su farka daga matattu na ruhaniya yadda dole ne mutum da ya mutu ya rayu kuma domin ya ji, kokuwa 2) Bulus yana magana da masubi na Afisus da ya yi amfani da mutuwa ya kwatanta raunanar ruhaniyarsu.
Wannan yanayin na "kai" na nufin "mai barci" kuma ɗaya ne.
Almasihu zai taimaka wa marabi ya fahimci yanda mugun ayukansa yake da yanda Almasihu zai yafe shi ya kuma bashi sabon rai, kaman yanda haske na bayana yanda abu yake a cikin duhu.
Marasa hikima ba sua yin lura da kansu game da zunubi ba. Ko dashiƙe masu hikima na iya gane zunubi su kuma gudu daga ita. AT: "A hakan dole ne ku yi hankali domin ku yi zama kamar mutum mai hikima ba kaman mara hikima ba"
"ku yi abu mafi muhiminci da lokacin ku," "yi amfani da lokaci da wayo," ko "Sa lokaci domin yin abinda ya fi"
Kalmar "kwanaki" na kwatancin abinda mutane ke yi a wancen kwanaki. AT: "domin mutane da na kewaye da ku na yin dukan mumunan abubuwa"
Bulus ya kare da ka'idodin sa a yadda dukan masubi za su yi rayuwa.
"Da kada ku bugu daga shan ruwan inabi"
"Maimakon Ruhu mai Tsarki ya bi da ku"
Ma'anar su kamar yanda 1) Bulus ya yi amfani da waɗanan kalamai kamar kwatanci ne na "dukan irin waƙoƙin yabon Allah" ko 2) Bulus yana lissafta yanayin waka ta masamman.
Ma'anar su kamar yanda 1) yanda aka rubuta a littafin Zabura ko 2) kowane wakar yabo.
waka da ya ke ɗaukaka Uban ko Ɗansa
Ma'anar su kamar yanda 1) wannan waƙoƙi ne game da Allah kokuwa 2) wannan waƙoƙi ne da Ruhu Mai Tsarki ya bayer kokuwa 3) wannan kalmar daya ne da "waƙoƙi" kuma ba ya neman bambanta kalma.
Bulus ya fara da bayana yadda masubi za su yi biyayya da juna (5:18). Ya fara da umurni wa mataye da mazaje akan yanda za su yi rayua da junan su.
Kalmar "shugaban" yana wakilcin shugaba.
A nan kalmar " kansa" da "Ya" na nufin Almasihui. Kalmar "ta" na nufin ikilisiya.
A nan "ƙauna" na nufin bauta mara son kai ko bayar da ƙauna wa mataye.
"yarda mutane su kashe shi"
sunna iya nufin 1) Bulus na nufin yadda Allah na sa mutanen Almasihu wankaku daga kalman Allah ta baftisma na ruwa a cikin Almasihu ko 2) Bulus ya na cewa Allah ya wanke ruhaniyar mu daga zunubanmu ta wurin kalmar Allah yadda muke wanke jikinmu ta wurin wankewa da ruwa.
Bulus ya na magana akan taron masubi kamar mace ce wadda Yesu zai aura. AT: " domin mu ... yi mu tsarki ... wanke mu"
Bulus ya yi magar ikkilisiya kamar tufafi da an wanke kuma na yanayi mai kyau. Ya yi anfani da wannan ra'ayin a wuri biu domin ya jaddada tsarkin ikkilisiyan.
Maganar "mara kuskure" na nufin asalin abu iri ɗaya kamar "tsarki." Bulus ya yi amfani da biu nan tare domin ya jaddada tsarkin ikklisiya.
Don mutane suna son jikinsu za iya bayana shi a bayyane. AT: "yadda mazaje sunna son jikinsu"
"amma ciyad da"
sunna iya nufin 1) "mu gabagadin jikinsa na masubi" ko 2) masubi sun dace tare su gina jikin Almasihu kamar yadda kashin jikin adam ya ɗace tare su gina mutum.
Ambatawannan na daga rubutun Musa a cikin tsohon alkawari.
Kalmar"ya" da "ya" na nufin namiji maibi wadda ya yi aure.
Ya kamata masubi su yi koyi da Allah Uba kamar 'ya'yansa.
Almasihu ya bada kansa hadaya ga Allah saboda ma su bi.
Lalata na jima'i, kazamta, da handama bai kamata a yi shawaransu a tsakanin masubi ba.
Masubi ya kamata su sami halin godiya.
Masu lalatan jima'i, masu kazamta, da kuma ma su handama ba su da gado a cikin mulkin Almasihu da kuma Allah.
Fushin Allah ya na zuwa kan 'ya'ya ma su rashin biyayya.
'ya'yan alheri, adalci, da gaskiya ne Ubangiji yake jin dadinsu.
Bai kamata masubi su sa hannu ba, amma su bankaɗa ayukkan duhu.
Haske yana bayyana kome.
Ya kamata masubi su fanshi lokacin nan tun da kwanakin mugunta ne.
Maye da ruwan inabi ya ke kai ga halakka.
Ya kammata ma su bi su yi magana da juna da kalmomin zabura, the wakokin yabo, da wakokin ruhu.
Mata su saukar da kansu ma mazajensu kamar zuwa ga Allah.
Miji shine kan matarsa, kuma Almasihu shine kan ikklisiya.
Almasihu ya kan tsarkake ikklisiya ta wurin wanke ta da ruwa da kalma.
Ya kamata mazaje su kaunace matan su kamar jikin su.
Mutum ya na ciyad da jikinsa ya kaunace jikinsa.
A lokacin da aka hada na miji da matarsa su kan zama jiki daya.
Ana nuna Ɓoyayyen gaskiya game da Almasihu da ikklisiyarsa a haɗuwan miji da matarsa.
1 'Ya'ya, ku yi biyayya ga iyayenku chikin Ubangiji, domin wannan daidai ne. 2 "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka" (Doka ta fari kenan da alkawari), 3 "ta haka za ku yi albarka, domin kwanakinku su yi tsawo a duniya". 4 Hakanan, ku ubanni kada ku cakuni 'ya'yan ku har su yi fushi, amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargadinsa. 5 Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya tare da girmamawa da tsoro da zuciya mai gaskiya. Ku yi masu biyayya kamar ga Almasihu. 6 Ku yi masu biyayya ba don lallai suna kallonku ba domin ku faranta masu rai. Maimakon haka, ku yi biyayya kamar bayi ga Almasihu. Ku yi nufin Allah daga zuciya. 7 Ku yi hidima da dukan zuciya, kamar kuna bautar Ubangiji ba mutane ba. 8 Sai ku sani cewa duk abinda mutum ya yi zai karbi sakamako daga wurin Ubangiji, ko shi bawa ne ko 'yantacce. 9 Ku kuma iyayengiji, ku yi irin wannan ga barorin ku. Kada ku razana su. Kun sani shi wanda ke Ubangijinsu da ku daya ne yana sama. Kun sani tare da shi baya nuna tara. 10 A karshe, ku karfafa cikin Ubangiji da cikin karfin ikonsa. 11 Ku dauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa gaba da dabarun shaidan. 12 Gama yakinmu ba da nama da jini bane. Amma, da ikoki da mulkoki da mahukuntan wannan zamani mai duhu da rundunai masu duhu na mugunta cikin sammai. 13 Don haka ku dauki dukan makamai na Allah, domin ku iya tsayawa da karfi cikin muguwar rana. Bayan kun yi komai za ku tsaya da karfi. 14 Saboda haka ku tsaya da karfi. Ku yi wannan bayan kun yi damara cikin gaskiya kuna yafa sulke na adalci. 15 Ku yi wannan bayan kun daure kafafunku da shirin kai bisharar salama. 16 Cikin dukan abu ku dauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku kashe dukan kibau masu wuta na mugun. 17 Ku dauki kwalkwalin ceto da takobin Ruhu, wanda shine maganar Allah. 18 Tare da kowacce irin addu'a da roko kuna addu'a kullum cikin Ruhu. Da wannan lamiri, kuna tsare wannan da iyakacin kula da dukan juriya da roko saboda dukan masu bi. 19 Ku yi mani addu'a, domin in karbi sako duk sa'adda na bude bakina. Ku yi addu'a in sami gabagadin bayyana boyayyar gaskiyar bishara. 20 Saboda bishara nake jakada cikin sarkoki, yadda a cikinta zan yi magana gabagadi yadda takamata. 21 Amma domin ku san rayuwa ta, da yadda nake, Tikikus, dan'uwa kaunatacce da amintaccen bawa cikin Ubangiji, zai sanar da ku dukan abu. 22 Saboda wannan dalili na aiko shi gare ku, domin ku san al'amuran mu, kuma domin ku sami ta'aziya a zukatan ku. 23 Bari salama ta kasance tare da 'yan'uwa, kauna da bangaskiya daga wurin Allah Uba da Ubangiji Yesu Almasihu. 24 Alheri ya kasance tare da wadannan da suke kaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu tare da kauna mara mutuwa.
Bulus ya ci gaba da bayana yanda Almasihu ya kamata su yi biyaya ga juna. Ya bayer da umurni wa 'ya'ya, Ubanni, ma'aikata, da kuma iyayengiji.
Kalmar farko "ku" na nufin abubuwa da yawa. Sai Bulus ya fadi abun da Musa ya ce. Musa na magana da mutanen kamar da mutum ɗaya, "ku" da "ku" na nufin abu ɗaya.
Bulus ya tunasher da 'ya'ya su yi biyaya ga iyayen su.
"kada ku sa 'ya'yan ku fushi" ko " kada ku zama dalilin ''ya'yan ku su yi fushi"
" ku taimakesu su yi girma a tarbiya da koyarwan Ubangiji"
"biyayya." Wannan umurni ne.
Maganar "girmamawa mai zurfi da tsoro " ya jaddada ra'ayin daraja da halin su da kuma ɗauki.
"kamar ka na girgiza da tsoro"
"za da gaskiya gaba ɗaya"
yi biyayya ga iyayengijinku na duniya kamar iyayengijinku na duniya ne Almasihu da kansa.
"yi aiki da farinciki, tun da ku na yin aiki wa Ubangiji ne ba domin mutane ba"
"kukuma ku yi wa bayin kirki" ko " kamar yadda bayi dole ne su yi kirki ga iyayengijinsu, ku kuma dole ne ku yi kirki ga bayin ku (Dubi: 6:5)
"Kun san cewa Almasihu ne shugaban ku barori da iyayengiji, kuma shi yana sama"
"yana shar'anta kowa ta hanya ɗaya"
Bulus ya ba da umurni domin ya sa masubi su dage daga yaƙi da muke ciki wa Allah.
"karfin iƙonsa." Dubi yadda "da cikin baban karfin shi" an fasara kusa da karshen 1:19.
Ya kamata Almasihu su yi amfani da abubuwan da Allah ya basu domin su tsaya da karfi daga ibilis kamar da soldier yake sa makamai domin su kare kansu daga harin makiya.
"dabarun sha'ani mai wuya"
Wannan maganan na nufin mutane ne, ba ruhohi wanda basu da jikunan mutum ba.
Ya kamata Almasihu su yi amfani da abubuwan tsaro da Allah ya basu domin fada da ibilis kamar da soldier yake sa makamai domin su kare kansu daga harin makiya.
Kalmar "tsaya da karfi" na tsaya a maɗaɗin kalmala kari'a ko fada da wani abu. AT: "domin ku iya dage wa ibilis"
Kalmar "tsaya" ya zama wakilin tsayaya ko kuwa fada da wani abu. Dubi yadda aka fasara "tsaya da karfi" a 6:12. "tsaya da ibilis"
Gaskiya na riƙe komai tare wa masubi kamar da damara ke riƙe kaya na soja tare.
Ya kamata mu san gaskiya mu kuma yi ayuka ta hanya da zai gamshi Allah.
sunna iya nufin 1) kyautar adalci na rufe zuciyar maibi kamar da sulke ke tsare ƙirjin soja kokuwa 2) rayuwarmu kamar yadda Allah ke so, ya ba mu warair lamiri domin ya tsare zuciyar mu yadda sulke yake tsare kirjin soja.
Kamar yad'da soja na sa takalma ya bashi karfin ƙafa,ya kamata maibi ya samu sani mai karfi na bishara na salama domin ya yi shelar.
Dole maibi ya yi amfani da bangaskiya da Allah ya bashi domin tsarewa daga harin ibilis, yadda soja yake anfani da sulke domin ya tsare shi daga harin.
Harin na ibilis akan maibi na kaman kibau masu wuta da ya harbi soja daga makiyi
Ceto da Allah ya bayar na kiyaye zuciyar maibi kamar yadda kwalkwali yake tsare kan soldier.
Kalmar Allah, hurarrun daga ruhun mai tsarki, ke kamata ayi anfani domin a yi yaƙi da kuma kare masubi daga ibilis kamar da soldier yake amfani da takobi domin ya yake da kuma kare harin maƙiyi.
"yi addu'a kullum a cikin ruhu yanda ku yi addu'a da yin roƙo musamman"
"domin ku iya yin addu'a haka." Wannan na nufin hali na ɗaukar makami na Allah.
"jurewa a zaman jijjiga, ku yi addu'a wa dukan tsarkaken mutanen Allah" ko "yi adua'a da jijjiga wa dukan masubi"
A karshe, Bulus ya roƙe su da su yi addu'a domin rashin fargaba a yin wa'azi yayin da ya ke cikin kurkuku da kuma cewa zai aiki Tikikus ya karfafa su.
AT: "domin Allah ya bani kalmar" ko kuwa "Allah ya bani sako"
"idan na yi magana. ku yi addu'a in bayana gabagadi"
"magana"
"A yanzu haka, ina cikin kurkuku domin ni mai shalar bashara ne.
Kalmar "addu'a" na iya ganewa daga sura 19.AT: " ku yi addu'a domin dukan lokacin da na yi wa'azin bishara, zan yi shi da gabagadi yan da ya kamata" ko " ku yi addu'a domin in yi wa'azin bishara da gabagadi yadda ya kamata"
Tikikus na ɗaya daga mutanen da sun yi aiki da Bulus.
Bulus ya rufe wasikar sa ga masubi na Afisawa tare da albarka na salama da alheri ga dukan masubi waɗanda suna kaunar Almasihu.
'ya'yan krista ya kammata su yi biyayya su kuma ba wa iyayensu daraja.
ya kammata iyaye maza da su ke krista su ta da 'ya'yansu da horo da umurci na Ubangiji.
Ya kammata bayin da suke krista su yi biyayya da masu gidansu a cikin kirkin zuciya , suna bauta da murmushi kamar zuwa ga ubangiji.
Ya kamata mai bi ya tuna ce wa duka ayukka masu kyau da ya yi, zai samu lada da ga wurin Ubangiji.
Ya kamata kowane mai gida ya tuna cewa da shi da bayinsa dukka mai gidan su na sama, shi kuwa ba ya zabe.
Ya kammata mai bi ya sa duka sulken Allah domin ya tsaya da karfi ya yi găbă da mugun shirin shaidan.
Mai bi ya na yaki da gwamnati, da kuma hukumomin ruhohi da masu mulkin mugayen duhu.
Ya zama tilas ma mai bi ya sa dukka sulken Allah don ya tsaya da karfi ya yi găbă da mugun shirin shaidan.
Ya zama tilas ma mai bi ya sa dukka sulken Allah don ya tsaya da karfi ya yi găbă da mugun shirin shaidan.
Garkuwan bangaskiya ita ce ta ke kau da kibiyoyi na harshen wutan mai mugunta?
Takobi na ruhu ita ce maganar Allah.
Ya zama tilas ma mai bi ya zama mai adu'a a kowace lokaci, ya na hakuri da lura don amsar Allah.
Bulus ya na fata ya sama a ba da kalmar nan da gabagadi a lokacin da ya ke maganar bishara.
Bulus ya na kurkuku ne a lokacin da ya ke rubuta wannan wasikan.
Bulus yana rokan Allah ya bada salama, kauna da bangaskiya da kuma alheri zuwa ga masubi.
1 Bulus da Timoti bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan wadan da aka kebe cikin Almasihu Yesu da ke a Filibi, tare da masu kula da ikilisiya da dikinoni. 2 Bari alheri ya kasance tare da ku da salama daga Allah Ubanmu da Ubagijinmu Yesu Almasihu. 3 Ina godiya ga Allahna duk lokacin da na tuna da ku. 4 Ko yaushe cikin addu'a ta dominku duka, da farin ciki na ke addu'a. 5 Ina godiya domin tarayyar ku a cikin bishara tun daga rana ta fari har ya zuwa yanzu. 6 Na tabbata game da wannan abu, shi wanda ya fara aiki mai kyau a cikinku zai ci gaba da shi har ya kai ga kammala zuwa ranar Yesu Almasihu. 7 Daidai ne in ji haka game da dukanku domin kuna zuciya ta. Dukanku abokan tarayya ta ne cikin alherin Allah wajen dauri na da kuma kariyar bishara, da tabbatar da bishara. 8 Domin Allah mashaidi na ne, a kan yadda ina da marmarin ku duka cikin zurfin kaunar Almasihu Yesu. 9 Ina yin wannan addu'a: kaunar ku ta habaka gaba gaba a cikin sani da dukan fahimta. 10 Ina addu'a a kan haka domin ku gwada ku zabi mafifitan abubuwa. Ina addu'a domin ku zama sahihai marasa abin zargi a ranar Almasihu. 11 Wannan kuma domin a cika ku da 'ya'yan adalci da ake samu ta wurin Yesu Almasihu, zuwa ga daukaka da yabon Allah. 12 Yanzu ina so ku sani, 'yan'uwa, cewa al'amuran da suka faru da ni sun zama dalilan cin gaban bishara kwarai da gaske. 13 Sakamakon haka, sarkokina cikin Almasihu sun zama sanannu ga dukan sojojin fada da kuma sauran jama'a, 14 har galibin 'yan'uwa cikin Ubangiji suka karfafa kwarai sabili da sarkokina, suka fito a fili suka yi shelar maganar Allah gabagadi. 15 Lalle wadansu suna shelar Almasihu cikin kishi da husuma, wadansu kuwa domin kyakyawar manufa. 16 Masu shelar Almasihu domin kauna sun sani cewa an ajiye ni nan domin in kare bishara. 17 Amma wadansu kuwa suna shelar Almasihu saboda sonkai da rashin gaskiya. A zaton su suna wahalar da ni cikin sarkokina. 18 Sai kuma me? Ta kowace hanya, ko da gangan ko da gaske, shelar Almasihu ake yi, ina kuma murna da wannan! I, zan yi murna. 19 Domin na sani wannan zai kai ga sanadiyar kubuta ta. Wannan zai faru sabili da addu'ar ku, da kuma taimakon Ruhun Yesu Almasihu. 20 Bisa ga abin da hakikance nake tsammani da tabbaci cewa ba zan kunyata ba. Maimakon haka, da dukan karfin hali kamar kullum, da yanzu kuma, ina da burin kawo daukaka ga Almasihu a cikin jikina. Ina da begen Almasihu ya sami daukaka a cikin jikina ko cikin rayuwa ko cikin mutuwa. 21 Domin ni a gare ni rai Almasihu ne, mutuwa kuwa riba ce. 22 Amma idan ya zamanto rayuwata cikin jiki za ta kawo amfanin hidima to, ban san wanda zan zaba ba. 23 Amma dukansu biyu suna jan hankali na. Ina da burin in bar nan in kasance tare da Almasihu, wannan ya fiye mani kwarai! 24 Duk da haka rayuwata cikin jiki wajibi ne sabili da ku. 25 Tunda shike ina da tabbas a kan wannan, na kuma sani zan rayu, in cigaba da kasancewa da ku duka domin cigaban ku, da farincikin ku, cikin bangaskiya. 26 Sakamakon haka, takamar ku cikin Almasihu Yesu za ta bunkasa sabili da dawowa ta a gare ku. 27 Ku tafiyar da al'amuran ku kamar yadda ya cancanci bisharar Almasihu, ku yi haka domin ko na zo in duba ku, ko bana nan inji yadda kuke tsaye daram cikin ruhu guda. Ina fatan in ji cewa da nufi daya kuke fama tare saboda bangaskiyar nan ta bishara. 28 Kada ku tsorata da kome da magabtanku za su yi. Alama ce a gare su ta hallakar su. Amma ku kuwa alama ce ta ceton ku, wannan kuwa daga Allah ne. 29 Gama an yi maku alheri, sabo da Almasihu, ba gaskantawa da Almasihu kawai ba, amma har ma shan wuya dominsa. 30 Kuna da shan wuya irin tawa wanda kuka gani, wanda kun ji nake sha har yanzu.
Bulus da Timoti ne suka rubuta wannan wasiƙa zuwa ga ikkilisiyar Filibi.
Idan Harshen ku na da wata hanya ta musamman na gabatar da marubucin wasiƙa, a yi amfani da shi a nan.
"Timoti. Mu bayin Yesu Almasihu ne"
"zuwa ga dukan masubi da ke cikin Yesu Almasihu"
"shugabanen ikilisiya"
Bulus yana bayyana godiyar sa ga Allah domin 'yan Filibi ma suna wa'azin bishara. AT: "Ina godiya ga Allah domin kuna shelar bishara" .
"na amince"
"Allah, wanda ya fara"
"yadace mani" ko kuma "ya mun kyau"
"ina kaunar ku sosai" .
"kasance maciyan alheri da ni" ko kuma" kasance masu tarayya da ni cikin alheri"
"Allah ya sani" ko kuma "Allah ya fahimta"
Ana iya fassara kalman "tausayi" da wannan kalman aiki "kauna." AT: "kuma ina ƙaunar ku kamar yadda Almasihu yake matukar ƙaunar mu duka"
Bulus ya yi addu'a ga masu bi a Fillibi, kuma yayi magana game da farin ciki da akwai a shan wahala domin Ubangiji.
Bulus na maganar kauna kamar wasu abubuwa ne da bayan samun su mutane za su iya ƙara samu. AT: "na iya kãra"
"fahimta" a nan na nufin game da Allah kuma za a iya ƙãra yin gamsashen bayyanin sa. AT: "sa'an da kun koya kun kuma ƙãra fahimtar abin da zaigamshi Allah"
Wannan na nufin bincika abubuwa sa'an nan a ɗauki masu kyau kawai. AT: "gwaji da zaɓi"
"abin da ya fi gamasar Allah"
kalmomin nan "sahihi" da "marasa abin zargi" na da ma'ana ɗaya. Bulus ya haɗa su ne domin ya nanata halin tsarki. AT: "marar laifi gabaki ɗaya" .
Ma'anoni masu yiwuwa na "'ya'yan adalci" su ne 1) kalma ne da ke nuna halin adalci. AT: "ku kuma za ku yi halin adalci domin Yesu Kiristi ya ba ku dama" ko 2) kalma ne da ke nuna ayuka masu kyau ta dalilin zaman adalci. AT: "ku kuma za ku yi halin ayuka masu kyau domin Yesu Kiristi ya maishe ku adalai
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "Sa'an nan sauran mutane zasu ga yadda kuke girmama Allah" (UDB) or 2) "Sa'an nan mutane za su yaba, su kuma ba wa Allah girma ta dalilin nagarin abubuwan da suka ga kuna yi." Waɗannan ma'anoni masu yiwuwa za su buƙaci sabuwan jumla.
An yi amfani da kalmar na "yanzu" an nan domin a sa alamar wata sabuwar sashin wasiƙar.
A nan wannan yana nufin 'yan'uwa Kirista, maza da mata, domin duk masu bi a cikin Almasihu 'yan iyali ɗaya ne cikin ruhu, da Allah a matsayin Ubansu na sama.
Bulus yana magana ne game da lokacin da ya ke a kurkuku. AT: "wannan abin da na sha wahala, saboda an sa ni kurkuku a kan wa'azin Yesu"
"ya sa mutane da yawa sun ji bishara"
"sarkokina cikin Almasihu" magana ce da ke nufin kasancewa a kurkuku saboda Almasihu. "zuwa ga haske" kalma ce da ke nufin "ya zama sananne." AT: "ya zama sananne cewa ina kurkuku ta dalilin Almasihu"
Ana iya bayana wannan da sifan aiki. AT: "sojojin fada da sauran mutane da yawa a Roma sun san cewa ina cikin sarkoki saboda Yesu."
Bulus ya yi amfani da mahaɗin kalma "cikin" mai ma'ana "saboda." AT: "sarƙoƙina saboda Almasihu" ko kuma "sarkokina saboda ina koyar wa mutane game da Almasihu"
kalmar "sarkoki" a nan na nufin kurkuku. AT: "ɗaurewa ne a kurkuku"
wannan sojoji ne da ke taimaka wa a kare Sarkin Roma.
"wasu mutane suna wa'azin bisharar Almasihu"
"domin basu son mutane su saurare ni, kuma su na so su kawo matsala
"amma sauran mutane suna yi ne saboda suna da kirki kuma suna so su yi taimako.
"Masu shelar Almasihu da kyakyawar manufa"
Ana iya bayana wannan da sifan aiki. AT: 1) "Allah ya zabe ni in kare bishara" ko kuma 2) "Ina kurkuku saboda ina kare bishara."
"in koyar da kowa cewa sakon Yesu gaskiya ne.
"Amma sauran" ko kuma "waɗanda suke shelar Almasihu cikin ƙishi da husuma"
maganan nan "cikin sarkoki" na nufin kurkuku. AT: "tun ina ɗaure a kurkuku" ko kuma"tun ina cikin kurkuku"
Bulus yana amfani ne da wannan tambayan ya faɗi yanda yake ji dangane da yanayin da ya rubuto a 1:15. Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) wannan na nufin "ba kome." ko kuma 2) kalmomin nan "zan yi tunani game da wannan" ana iya fahimtarsu a matsayin jikin tambayar. AT: "Sai kuma me zan yi tunani game da wannan?" ko kuma "Ga abin da nake tunani game da haka"
"muddin mutane suna yin wa'azin Almasihu, ba kome ko sun yi shi domin manufofi masu kyau ko da manufofi marasa kyau."
"ina murna domin mutane suna wa'azin Yesu"
"zan bayyana murna" ko kuma "zan yi farin ciki"
"domin mutane suna shelar Almasihu, Allah zai kubutar da ni"
Ainihin ma'anar "kuɓuci," bai fita fili ba ko daga menene Allah zai ceci Bulus. Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) Bulus yana nufin taimako daga wani mummunan yanayi, ko kuma 2) Bulus yana nufin samun 'yancin sa daga kurkuku.
"domin kuna yi mani addu'a kuma Ruhun Yesu Almasihu yana taimako na"
"Ruhu Mai Tsarki"
A nan maganan "haki na tunani" da "tabbacin bege" suna da ma'ana ɗaya. Bulus ya yi amfani da su duka ne domin ya nanata karfin sa ran sa. AT: "na tabbata sarai"
Wannan sahshi shi ne sa rai da begen Bulus. AT: "amma ina sa rai da kuma bege cewa da dukan karfi, yanzu kamar kullum, Almasihu zai sammu ɗaukaka"
"yanzu zan kasance da gabagaɗi, kamar yadda na ke ko da yaushe da"
wannan maganan "jikina" na nufin abin da Bulus ya ke yi da jikinsa. Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar kaha 1) "zan girmama Almasihu ta wurin abubuwan da nake yi" ko kuma 2) "mutane za su yabi Almasihu saboda abubuwan da nake yi"
"idan na ci gaba da rayuwa ko idan na mutu"
"Domin idan na ci gaba da rayuwa, zan rayu in gamshi Almasihu, kuma idan na mutu, shi zai ma fi alhẽri
Kalman nan "jiki" a nan magana ce da ke nufin kasancewa da rai. AT: "Amma idan zan zama mai rai a cikin jikina: ko kuma "Amma idan na cigaba da rayuwa"
Kalmar nan "ni'ima" a nan yana nufin sakamakon aikin Bulus mai kyau. AT: "wato zan iya in yi aiki kuma aiki na zai ba da kyakyawar sakamako" ko kuma "sa'an nan zan ƙara samun zarafi in ƙarfafa mutane su gaskata da Almasihu"
Bulus yana magana ne game da yadda yana masa wuya ya zaɓa tsakanin rai da mutuwa kamar abubuwa ne masu nauyi, irin su duwatsu ko kuma gungume, suna tura shi daga gefe biyu a lokaci guda. Wataƙila harshen ku zai fi dacewa da yin amfani da abubuwa da ke ja ko dai turi. "Ina cikin tashin hankali. Ban san ko in zaɓi rai ko mutuwa ba"
Bulus ya yi amfani da wannan maganar a nan domin ya nuna cewa ba ya tsoron mutuwa. AT: "Zan so in mutu domin zan je in kasance tare da Almasihu"
"Tun da shike ina da tabbaci cewa ya fi mini amfani in rayu"
"na san cewa zan cikigaba da rayuwa" ko kuma "na san cewa zan daɗa rayuwa"
"saboda ta dalilina" ko kuma "saboda ta wurin abubuwan da nake yi"
Wadannan jumloli biyu suna da ma'ana kusan ɗaya kuma suna nanata muhimmancin ɗayantaka.
"fama tare da zuciya daya." Anyi maganar yarda da juna kamar kasancewa ne da zuciya ɗaya. AT: "yarda da juna da fama tare"
"faman aiki tare"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "a yaɗa bangaskiyar da ke cikin bishara" ko kuma 2) "a gaskata a kuma yi rayuwar yadda bishara ke koya mana"
Wannan umurni ne zuwa ga masubi na Filibi. Idan harshen ku yana da wata hanya da ake ba da umurni ga mutane da yawa, a yi amfani da shi a nan
"ƙarfin halin ku zai nuna musu cewa Allah zai hallakas da su. Zai kuma nuna muku cewa Allah zai cece ku."
"Shi ya sa kuke shan wuya kamar yadda kuka ga na sha, kun kuma ji nake sha har yanzu"
Bulus ya rubuta wanan wasiƙar zuwa ga duka mutanen da aka keɓe a cikin Yesu almasihu a Filibi, tare da masu kula da ikkilisiya da kuma masu dattijan.
Bulus ya ba da godiya zuwa ga Allah domin Filibiyawa saboda tarayyarsu wajen yaɗa bishara tun daga ranar farko har zuwa yanzu.
Bulus ya amince cewa wanda ya fara kyakkyawan aiki a cikinsu zai ƙarasa shi.
A cikin ɗaurin kurkukun Bulus, da tsaro da kuma tabbatarwar bishara, Filibiyawa sun kasance abokan hulɗar shi.
Bulus ya yi addu'a ƙauna ya ƙaru a kai a kai a tsakanin Filibiyawa.
Bulus ya yi marmarin cewa Filibiyawa su cika da ya'yan adalci.
Ɗaurin kurkukun Bulus don Almasihu ya kawo yaɗuwar sani, kuma mafi yawan yan'uwan yanzu na magana tare da ƙarfin zuciya mai yawa.
Waɗansu suna wa'azin Almasihu soboda sonkai da muraɗi mara kirki suna tunani cewa suna ƙara wa Bulus baƙin ciki a kurkuku.
Bulus ya yi farin ciki cewa, ko dai yaya aka yi, ana shelar Almasihu.
Bulus yana marmarin ya kawo ɗaukaka ga Almasihu, ko da rai, ko a mutuwa.
Bulus ya ce ya rayu Almasihu ne, kuma ya mutu riba ne.
Zabin kasancewa tare da Almasihu a mutuwa, ko zama a cikin jiki don ya cigaba da aiki sune suke jan Bulus.
Bulus ya amince cewa idan ya tsaya da Filibiyawa domin cin gaba da farin ciki a cikin bangaskiya su ne.
Bulus ya so ya ji cewa Filibiyawa sun tsaya da tabbaci a ruhu daya, da rai daya suna jihadi tare don bangaskiyan bishara.
A lokacin da Filibiyawa basu jin tsoron, alamar halakan abokanen gabansu ne, amma na cetonsu.
An ba wa Filibiyawa cewa sun yi imani da Almasihu, amma kuma sun sha wahala a madadin shi.
1 Idan akwai wani abin karfafawa cikin Almasihu. Idan da wata ta'aziyya daga kaunarsa. Idan akwai zumunta a Ruhu. Idan da tatausan jinkai da tausayi. 2 Ku cika farin cikina don ku zama da tunani irin haka, kuna da kauna daya, kuna tarayya cikin Ruhu daya, ku kasance da manufa iri daya. 3 Kada ku yi komai cikin sonkai ko girman kai. A maimakon haka cikin zuciya mai tawali'u kowa na duban wadansu fiye da kansa. 4 Kada kowa ya dubi bukatun sa, amma yana lura da bukatun wadansu. 5 Ku yi tunani cikin hanya wadda ke cikin Almasihu Yesu. 6 Wanda ya yi zama cikin siffar Allah, bai mai da daidaitarsa da Allah wani abin da zai rike ba. 7 Maimakon haka, ya wofintar da kansa. Ya dauki siffar bawa. Ya bayyana cikin kamannin mutane. An same shi a bayyane kamar mutum. 8 Ya kaskantar da kansa, ya yi biyayya har ga mutuwa, mutuwa ta gicciye. 9 Saboda haka Allah ya ba shi mafificiyar daukaka. Ya ba shi suna wanda yafi kowanne suna. 10 Domin a cikin sunan Yesu kowace gwiwa za ta durkusa, gwiwoyin wadanda ke cikin sama da kuma duniya da kuma karkashin duniya. 11 Kuma kowanne harshe zai furta cewa Yesu Almasihu Ubangiji ne, zuwa daukakar Allah Uba. 12 Domin wannan kaunatattuna, kamar yadda kullum kuke biyayya ba sai ina nan kadai ba. Balle yanzu da bananan, ku yi aikin cetonku da tsoro da far gaba. 13 Gama Allah ne yake aiki a cikinku ku yi nufi duka da aikata abin da zai gamshe shi. 14 Ku yi kowanne abu ba tare da gunaguni da gardama ba. 15 Domin ku zama marasa abin zargi kuma masu gaskiya, 'ya'yan Allah marasa aibi. Ku yi haka domin ku haskaka kamar haske a cikin wannan duniya, a tsakiyar karkatacciyar da gurbatacciyar tsara. 16 Ku rike kalmar rai da karfi domin in sami dalilin daukaka Almasihu a ranarsa. Sa'annan zan san cewa ban yi tseren banza ba, ban kuma yi wahalar banza ba. 17 Ko da ana tsiyaye ni kamar sadaka a kan hadaya da kuma hidimar bangaskiyarku, na yi farin ciki, kuma na yi farin ciki tare da ku duka. 18 Kamar haka kuma sai ku yi farin ciki, ku yi farin ciki tare da ni. 19 Amma na yi niyya in aiko da Timoti wurin ku ba da dadewa ba, domin ni ma in sami karfafuwa idan na san al'amuran ku. 20 Gama bani da wani wanda halinmu yayi daidai da nasa, wanda yake juyayin ku da gaskiya. 21 Domin duka ribar kansu suke nema bata Yesu Almasihu ba. 22 Amma kun san darajar sa, kamar yadda da ke hidimar mahaifisa, haka ya bauta mani cikin bishara. 23 Shi nake sa zuciyar in aiko maku ba da dadewa ba idan naga yadda al'amura nake gudana. 24 Amma ina da gabagadi cikin Ubangiji cewa ni da kaina zan zo ba da dadewa ba. 25 Amma ina tunanin yakamata in sake aiko maku da Abafaroditus, shi dan'uwana ne, abokin aiki, da abokin yaki, manzon ku da kuma bawa domin bukatu na. 26 Da shike yana marmarin ku duka, ya damu kwarai da shike kun ji yayi rashin lafiya. 27 Da gaske yayi rashin lafiya har ya kusan mutuwa. Amma Allah ya ji tausayin sa, ba shi kadai ba, amma har da ni, domin kada in yi bakin ciki kan bakin ciki. 28 Domin haka na yi niyyar aiko shi, saboda idan kun sake ganinsa za ku yi farin ciki ni kuma in kubuta daga juyayi. 29 Ku karbi Abafaroditus da dukan murna cikin Ubangiji. Ku ga darajar mutane irin sa. 30 Domin saboda aikin Almasihu ne ya kusan mutuwa. Ya sadakar da ransa domin ya bauta mani domin ya cika hidimar da ya kamata ku yi mani.
Bulus yana shawartar masubi su kasance da haɗin kai da tawali'u, yana kuma tunashe su da misalin Alnasihu.
"Idan Almasihu ya ƙarfafa ku"
"idan kaunarsa ta baku wata ƙarfafawa"
"idan kuna da zumunci da Ruhu"
"idan kun taba jin jinƙai da tausayi na ayyukan Allah masu yawa"
Bulus yana maganar farin ciki a nan sai ka ce kamar ruwa ne da ke cika randa. AT: "sa ni in yi farin ciki ƙwarai"
"kada ku yi wa kanku hidima ko kuma ku aza kanku fiye da waɗansu"
"kada ku lura da bukatun ku kaɗai, amma har ma da bukatun waɗansu"
"Kasance da irin halin Almasihu Yesu" ko kuma "Yi tunanin abubuwa a hanyar da Almasihu Yesu yayi"
Bulus yana magana ne a nan game da daidaici da Allah Uba kamar wani abu ne da Almasihu zai iya kamawa da hannun sa. Kamar yadda UDB ya bayyana, a lokacin da Almasihu yake duniya, bai daina zama Allah ba; amma ya daina yin ayyuka a matsayin Allah.
"suna" anan kalma ce ke nufin matsayi ko kuma daraja. AT: "matsayi da yafi duk wani mastayi" ko kuma "daraja da yafi duk wani daraja"
Sunan mafi muhimmanci ne, wadda ya kai a yaba masa fiye da duk wani suna
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "a lokacin da kowa da kowa ya ji sunan Yesu" (UDB) ko kuma 2) "a cikin darajar Yesu"
"gwiwa" a nan yana nufin mutum gabaɗaya, kuma durƙusa gwiwa zuwa ƙasa na nufin yin sujada. AT: kowane mutum zai yi wa Allah sujada"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "wurin da mutane ke zuwa a lokacin da sun mutu" ko kuma 2) wurin da aljanu suke zama.
"harshe" a nan yana nufin mutum gabaɗaya. AT: "kowane mutum" ko kuma "kowane mai rai"
kalmar nan "zuwa" yana nuna sakamakon: "sakamakon shi ne za su ɗaukaka Allah Uba"
Bulus ya ƙarfafa masu bi na Filibi ya kuma nuna musu yanda za su yi rayuwa irin a Kirista a gaban mutane; ya kuma tuna musu gurbi da ya bar musu.
"masoya 'yan'uwanna masu bi"
"lokacin da ina can tare da ku"
"lokacin da bana can tare da ku"
"cikagaba da yi wa Allah biyayya"
Waɗannan kalmomin "tsõro" da "fargaba" suna da ma'ana ɗaya ne. Bulus ya yi amfani da su ne ya nanata girmama Allah. AT: "tsõro tare da fargaba" ko kuma "tare da matuƙa girma"
"Allah yana ayyukan sa domin ku yi marmarin yi masa biyayya ku kuma yi masa biyayya"
kalmomin nan "marasa abin zargi" da "masu gaskiya" suna kama sosai a ma'ana kuma an yi amfani da su don a ƙara ƙarfin zancen AT:"marasa abin zargi gaba ɗaya"
Haske misali ne na nagarta da gaskiya. "Haskaka kamar hasken duniya" na misalin zaman nagarta da adalci a hanyar da ta dace har mutanen da suke duniya su gane cewa Allah mai nagarta da gaskiya ne. AT: "saboda ku zama kamar hasken duniya"
A nan kalmar nan "duniya" na nufin mutanen duniya. Wannan kalmar "karkatacciyar" da " gurɓatacciyar" an yi amfani da su tare domin a yi nuni cewa mutanen sun yi zunubi sosai. AT: "a cikin duniya, a saƙanin mutane masu zunubi sosai"
"Ku riƙe da ƙarfi" na nufin gaskata wa da ƙarfi. AT: "cigaba da yarda da kalmar rai da ƙarfi"
"kalmar da ya ke bada rai" ko "kalmar yana nuna yadda zaka yi rayuwa yanda Allah yake so ka yi"
"zuwa ga farin ciki" ko kuma "zuwa ga murna"
wannan yana nufin zuwa lokacin da Yesu zai dawo ya kafa mulkin sa ya kuma yi mulkin duniya. AT: " A lokacin dawowar Almasihu.
Wannan maganan "tseren banza" da kuma "wahalar banza" suna da ma'anna ɗaya. Bulus ya yi amfani da su tare don ya nanata ƙoƙarin aiki da yayi domin ya taimaki mutane su gaskata da Almasihu." AT: "Ban yi ƙoƙarin aiki a banza ba"
Littafin ya na yawan amfani da hoton tafiya domin bayyana halin mutu. Gudu zaman rayuwa ne na mai da hankali.
Bulus yana manganar mutuwarsa kamar shi wani hadayar dabba ne wadda aka zuba masa ruwan inabi ko kuma man zaitun. Abinda Bulus yake nufin shi ne zai mutu da farin ciki saboda mutanen Filibi idan hakan zai sa su su ƙara gamsar da Allah. Kuma, ana iya bayana wannan a cikin sifar aiki. AT: "Amma, ko da 'yan Roma sun yanke shawara domin su kashe ni, zan yi murna ƙwarai idan mutuwa ta zai sa bangaskiyar ku da biyayyar ku ta ƙara gamsar Allah"
Wannan maganan tare suna nuna matuƙar farin ciki. "Ina so kuma ku yi matuƙar farin cikin tare da ni"
"Amma, idan Ubangiji Almasihu ya yarda, ina bege"
"Babu wani a nan da ke ƙaunarku kamar yadda shi yake"
kalmar "su" a nan yana nufin mutane da Bulus bai ji zai iya amince wa ya aika su zuwa Filibi ba. Bulus yana kuma nuna fushin sa da waɗannan mutane, waɗanda yakamata su iya zuwa, amma Bulus bai amince da su cewa za su iya cika manufansu ba.
Bulus yana magana game da Timoti, wanda ya bauta wa Almasihu tare da Bulus, kamar shi ɗa ne da ke bauta wa mahaifinsa. Bulus yana nanata dangantakar mahaifi da ɗa na kusa da yake da shi da Timoti a cikin bautar Almasihu.
"bisharan" a nan yana nufin aikin gaya wa mutane game da Yesu. AT: "a cikin faɗawa mutane game da bisharar"
"ina da tabbaci, idan Allah ya nufa, ni ma zan zo ba da daɗewa ba."
Wannan sunan wani mutum ne da ikilisiyar Filibi suka aika ya yi wa Bulus hidima a kurkuku
Bulus yana maganar Abafaroditus kamar shi soja ne. Yana nufin cewa Abafaroditus ya horu kuma yana da ƙwazo ga bautar Allah, duk da tsananin wahala da dole ne ya sha. AT: "dan'uwa mai bida yayi aiki da gwagwarmaya tare da mu"
"da kuma wanda ya kawo saƙonninku wurina ya kuma taimake ni a lokacin da nake da bukata."
"ya damu kwarai kuma yana so ya kasance tare da ku duka"
Za a iya ƙara bayyana dalilin baƙin cikin. AT: baƙin cikin rabuwa da shi ya ƙara mani baƙin cikin da nake da shi na zama a kurkuku"
"zan rage juyayi" ko kuma "ba zan damu da yawa kamar yadda da nake yi ba"
"ku karɓe shi da farin ciki"
a matsayin da'uwa mai bi a cikin Ubangiji da dukan farin ciki." ko kuma "da matuƙar farin ciki da muke da shi domin Almasihu Yesu yana ƙaunar mu. (UDB)
Bulus yana maganar mutuwa a nan kamar wani wuri ne da wani zai iya zuwa.
Bulus yana maganar bukatunsa sa kamar wasu gora ne da Abafaroditus ya cika su da abubuwa masu kyau wa Bulus."
Tilas ne Filibiyawa su zama yi zama da tunani iri ɗaya, zama da ƙauna iri ɗaya, kuma su zama da haɖɗe a ruhu da tunani.
Ya kamata Filibiyawa su sa juna fiye da kansu.
Bulus ya ce muna bukatar mu samu halin Yesu Almasihu.
Almasihu Yesu ya zama a siffan Allah.
Almasihu Yesu ya ɗauki siffan bawa, a bayyanuwansa na ɗan mutum.
Yesu ya kaskantar da kansa ta wurun biyayya, ta wurin biyayya da ta kai shi mutuwa a bisa giciye.
Allah ya ɗaukaka shi mafificiyar ɗaukaka, ya kuma ba shi suna da ke sama da kowane suna.
Kowane harshe zai furta cewa Yesu Almasihu Ubangiji ne.
'Filibiyawa za su yi aiki don cetonsu da tsoro da kuma rawar jiki.
Allah na aiki a masubi zuwa so ta da na aiki wa daɗinsa mai kyau.
Tilas ne a yi kome ba tare da gunaguni da gardama ba.
Bulus na zuba rayuwarsa a hadaya da hidima na bangaskiyar Filibiyawa.
Bulus ya yi farin ciki da babban murna.
Babu kamar Timoti domin ya kula da Filibiyawa kuma ba don ribar kansa ba.
I, Bulus yana tsammanin ganin Filibiyawa ba da daɗewa ba.
Abafaroditas ya kusa mutuwa yana yin aikin Almasihu, yin hidima wa Bulus da samar da buƙatun Bulus.
1 A karshe, 'yan'uwana, ku yi farin ciki cikin Ubangiji. In sake rubuta maku wadannan abubuwa ba wani abu mai nauyi ba ne a gare ni. Wadannan abubuwa zasu tsare ku. 2 Ku yi hankali da karnuka. Ku yi hankali da miyagun ma'aikata. Ku yi hankali da masu yanke-yanke. 3 Gama mune kaciyar. Don mune muke sujada ta wurin Ruhun Allah. Mune masu fahariya chikin Almasihu Yesu, kuma ba mu da gabagadi cikin jiki. 4 Ko da shike, ni kaina ina gabagadi ga jiki. Idan wani zai iya tunanin gabagadi ga jiki, ni na fi shi. 5 An yi mani kaciya a rana ta takwas, daga mutanen Israila, na kabilar Biliyaminu, Bayahuden Yahudawa; ga zancen shari'a Bafarisiye nake. 6 Wajen himma na tsanantawa ikilisiya. Ga zancen adalci cikin sharia, na zama mara abin zargi. 7 Amma duk wadannan abubuwan da suka zama riba a gare ni, na dauke su asara ne saboda Almasihu. 8 I, lallai ina lisafta dukan wadannan abubuwa asara saboda mafificin sanin Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shine na yi asarar dukan abubuwa. Na maishe su marasa amfani domin in ribato Almasihu, 9 a iske ni cikinsa. Ba ni da wani adalcin kaina ta wurin shari'a. Maimakon haka, ina da adalci ta wurin bangaskiya cikin Almasihu, adalcin dake daga wurin Allah ta wurin Bangaskiya. 10 Yanzu ina so in san shi da ikon tashinsa, da tarayya cikin shan wuyarsa. In kuma zama kamarsa wajen mutuwarsa, 11 domin ta ko kaka in kai ga tashi daga cikin matattu. 12 Ba wai na rigaya na sami wadannan abubuwa bane, ko kuma na riga na zama cikakke. Amma ina nace bi domin in cafki wannan da Almasihu Yesu ya cafko ni dominsa. 13 'Yan'uwa, ban dauka cewa na riga na cafka ba tukuna. Amma akwai abu daya da nake yi: ina mantawa da abin da ke baya, ina kutsawa zuwa ga abin da ke gaba. 14 Ina nacewa zuwa ga manufar nan in kai ga samun ladar nasara na madaukakin kiran Allah cikin Almasihu Yesu. 15 Dukan mu wadanda muke kammalallu, sai mu yi tunani ta wannan hanyar, idan kuwa kun yi tunanin wani abu daban, to Allah zai bayyana maku wannan kuma. 16 Sai dai, in da muka rigaya muka kai, bari mu rike shi haka. 17 Ku zama masu koyi da ni, 'yan'uwa. Ku duba da kyau wadannan da suke tafiya yadda muka zama abin koyi a gare ku. 18 Mutane da dama suna tafiya -sune wadanda na ba ku labarin su, yanzu kuma ina fada maku har da hawaye - kamar makiyan gicciyen Almasihu ne. 19 Karshen su hallaka ne. Domin allahn su ciki ne, fahariyar su kuma tana cikin kunyar su. Tunanin su na kan al'amuran duniya. 20 Amma mu 'yangarincin mu a sama yake, daga inda muke sauraron mai ceto, Ubangiji Yesu Almasihu. 21 Za ya sake jikinmu na kaskanci ya siffanta shi kamar jikin darajarsa, siffantacce ta karfin ikonsa inda ya sarayar da dukan abubuwa a gare shi.
Bulus yana ba da na sa shaida game da lokacin da yake tsananta wa masu bi domin ya gargaɗi yan'uwan sa masu bi game da Yahudawan da za su yi ƙoƙari sa su su bi dokoki na da.
"Yanzu muna ci gaba, 'yan'uwana" ko kuma "game da sauran al'amura, 'yan'uwana"
Juya wannan kamar yadda yake a 1:12.
"yi farin ciki saboda duk abinda Allah ya yi"
baƙin ciki
"waɗannan abubuwa" a nan na nufin koyaswar Bulus. Za'a iya ƙara wannan a ƙarshen jumla da ya gabata. AT: "domin waɗannan koyaswar za su kare ku daga masu koyaswar ƙarya"
"yi hattara" ko kuma "yi lura"
waɗannan hanyoyi ne daban-daban na bayana ƙungiya guda masu koyaswar ƙarya. Bulus yana amfani ne da magana mai ƙarfi domin ya kai/isad da yadda yake ji game da waɗannan malaman Yahudawa Kirista
Bulus yana magana ne game da yin kaciya don ya zagi masu koyaswar karya. Masu koyaswar karyan sun ce Allah zai ceci mutum mai kaciya ne kaɗai, wanda ya yanke loɓa. An bukaci wannan ne a dokar Musa ga dukan mazan Isra'ila.
Bulus ya yi amfani da "mu" domin ya yi magana game da kansa da dukan masu bi na gaskiya a cikin Almasihu, duk da masu bi na Filibi
Bulus ya yi amfani ne da wannan yana nufin masubi a cikin Almasihu waɗanda ba a yi masu kaciya ta jiki ba amma suna da kaciya ta ruhu, wato sun karɓi Ruhu Mai Tsarki ta wurin bangaskiya. "mutanen Allah na gaske"
"kada ku amince da cewa yanka jiki kawai zai gamshi Allah"
"duk da haka" ko kuma "amma dai"
A nan Bulus yana cewa in da yana yiwuwa ne Allah ya ceci mutane bisa ga abin da suka yi, da lallai Allah zai cece shi. AT: "Babu wani da zai iya yin abubuwan da yawansu za su kai ya gamshi Allah, amma idan akwai wani wanda zai iyan yin abubuwa da yawansu za su kai ya gamshi Allah, to ni zan yi fiye da haka in kuma ganshi allah sosai fiye da kowa"
Bulus ya yi amfani da "kaina" domin jaddadawa. "lallai ni"
Za'a iya sa wannan a sifan aiki. AT: "Wani Firist ya yi mani kaciya"
"bayan kwana bakwai da haifuwa ta" (UDB)
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "ɗan Bayahude mai iyaye Yahudawa" ko kuma 2) "Bayahude tsantsa"
Bayahude yana iya zama Bafarisiye ne idan mahaifinsa Bafarisiye ne. Amma wannan yana sa wa mutumin alhakin rayuwa a matsayin Bafarisiye, da ba da kai na musamman ga dokar Musa. "a matsayi na na Bafarisiye, na miƙa kai gaba ɗaya ga doka."
Bulus a nan yana cewa ya azabta mutane saboda bin Yesu. "na kudura ainun in ji wa masubi Kirista."
"na yi biyayya da doka gaba ɗaya"
Bulus yana komowa ne zuwa ga yabon da ya samu na zama bafarisiye na kwarai. Yana maganar wannan yabo kamar abin da ya wuce ne a matsayin ribar ɗan kasuwa. AT: "cikin duk abin da sauran Yahudawa suka yaba mini"
Bulus yana maganar wancan yabon kamar yana duban sa a matsayin asara ce na kasuwa maimakon riba. Abin da Bulus yake faɗi shi ne, dukan ayukansan na adalci banza ne a gaban Almasihu.
"haƙiƙa" ko kuma "da gaske"
Kalmar "yanzu" yana nanata yadda Bulus ya canja ne tun da ya bar zama bafarisi zuwa zama maibi cikin Almasihu. AT: "yanzu da na gaskata da Almasihu, ina lisafta" Dubi:
Bulus yana cigaba da moron hoton kasuwanci daga 3:6, da cewa banza ne a gaskata da kowane abu daban da Almasihu. "na ɗauki kowane abu banza"
"saboda sannin Almasihu Yesu Ubangijina ya fi daraja sosai"
"Saboda shi na yarda na jefar da dukan abubuwa"
Yi amfani da kalmar da aka saba sa wa abubuwan da ba a so kuma ana jefar da su nesa daga inda mutum yake.
Bulus yana maganr abubuwan da mutum zai iya gaskata da su kamar sharar zubar wa a waje ne. Yana nanata ainihin rashin darajarsu. AT: "Ina daukar su kamar tarkace ne"
"domin in samu Almasihu kadai"
maganar "a iske" salon magana ne da ke nanata "ya zama." AT: "a haƙiƙance tare da Almasihu da gaske"
"ba ina ƙoƙari in gamshi Allah da kaina ta wurin biyayya da doka ba ne.
"ikon sa da yabamu rai"
"shan wuya kamar yadda ya sha, sai ka ce muna shan wuyar abu ɗaya a wuri ɗaya a lokaci ɗaya"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) Bulus yana so Almasihu ya canja shi domin ya mutu kamar yadda Almasihu ya mutu. Ko kuma 2) yana so marmarin sa na zunubi ya zama matacce kamar yanda Yesu yake a mace kafin a tashe shi daga matattu.
Kalmar "ko ta ƙaƙa" yana nufin cewa Bulus bai san menene zai faru da shi a wannan rayuwa ba, amma ko da menen ya faru, zai kai ga rai na har abada. "saboda ko da menen ya rafu, zan sake rayuwa bayan mutuwa."
waɗannan sun haɗa da sanin Almasihu, sanin ikon tashinsa, da tarayya cikin shan wuyar Almasihu, da kasancewa ɗaya da Almasihu a cikin mutuwarsa da tashinsa (3:8).
"don haka ban riga na zama cikakke ba" ko kuma "don haka ban riga na gama girma ba"
"Amma ina ta ƙoƙari"
an yi maganar karbar abubuwan ruhu daga Allah kamar Bulus zai cafke su da hanun sa ne. Kuma Yesu yayi maganar cafke Bulus da hannayen sa AT: "ina iya samun waɗannan abubuwan"
An yi maganar karban abubuwan daga Allah kamar Bulus zai cafke su da hannun sa.AT: "Duk waɗannan abubuwa ba su zama nawa ba tukuna"
kamar yadda mai gudu a wasan tsere baya damuwa da fannin tsere da ya riga ya kammala amma yana mayar da hankali ne ga sauran tsere da ya rage, haka ma Bulus yana magana game da mantawa da ayyukan adinin sa na adalci yana kuma maida hankali a kan tseren rayuwa da Almasihu ya sa a gaban shi domin ya kammala" (Dubi:|Metaphor)
Kamar yadda mai wasan gudu yana nacewa domin nasara, Bulus yana nacewa cikin bauta da kuma rayuwar biyayya ga Almasihu. AT: "ina yin duk abin da na iya don in zama kamar Almasihu, kamar mai gudu da ke tsere zuwa ga karshen layi, domin in zama nashi, kuma Allah ya kira ni zuwa wurinsa bayan na mutu" (Dubi: |Metaphor)
Ma'anoni masu yiwuwa sune, Bulus yayi maganar zama har abada da Allah kamar Allah zai kira Bulus ya haura 1) zuwa sama kamar yadda Yesu yayi ko 2) hawa zuwa dandali inda masu nasara a wasan tsere suke karɓar sakamako a matsayin misalin saduwa da Allah fuska da fuska da kuma karɓar rai na har abada.
Bulus yana so 'yan'uwansa masubi su kasance da marmari ɗaya da ya ambata a 3:8. AT: "Na ƙarfafa dukan mu masubi da ke da ƙarfi a cikin bangaskiya mu yi tunani ɗaya"
"Allah kuma zai sa shi ya zama muku sarai" ko kuma "Allah zai tabbata kun san shi"
"barin dukan mu mu cigaba da biyayya da wannan gaskiya ɗaya da mun riga mun karɓa"
"yi abin da nake yi" ko kuma "yi rayuwa kamar yadda ina rayuwa"
"waɗannan da suna rayuwa kamar yadda nake rayuwa" ko kuma "waɗannan da suna yin abin da nake yi"
An yi maganar halin mutum kamar mutum yana tafiya a kan hanya. AT: "dayawa suna raye" ko "dayawa suna gudanar da rayuwarsu"
Bulus ya katse abinda yake faɗa da waɗannan kalmomi da suke bayyana "da dama." Za'a iya kai su zuwa forkon ko kuma karshen ayan idan akwai bukata.
"na gaya muku sau da dama"
"ina faɗa muku wannan da matukar baƙin ciki"
"giciyen Almasihu" a nan yana nufin "shan wahala da mutuwar Almasihu." Maƙiyan giciyen sune waɗanda suke cewa sun gaskata da Yesu amma basu yarda su sha wahala ko ma su mutu kamar yadda Yesu ya sha ba. AT: a wata hanya da ya nuna a zahiri cewa suna gaba da Yesu, wanda ya yarda ya sha wahala ya kuma mutu bisa giciye"
"wata rana Allah zai hallakar da su"
"ciki" a nan yana nufin marmarin annashuwar mutum ta jiki. Kiran sa allahn su a nan yana nufin cewa suna marmarin waɗannan annashuwan fiye da marmarin su yi wa Allah biyayya. AT: "sun fi marmarin abinci da sauran annashuwar jiki fiye da marmarin biyayya ga Allah.
"kunya" a nan yana madadin yadda ya kamata mutanen su ji kunya amma basu ji. AT: suna fahariya da abubuwan da ya kamata su jawo musu kunya" Dubi:
"duniya" a nan yana nufin dukan abubuwan da ke ba da annashuwar jiki kuma basu girmama Allah. AT: "Dukan tunanin su game da abinda zai gamshe su ne maimakon abin da zai gamshi Allah"
Bulus, ta wurin yin amfani da "na mu" da kuma "mu" a nan, ya shafe shi da masu bi da ke Filibi.
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "mu 'yan same ne" (UDB) ko kuma 2) "garinmu sama ne" ko kuma 3) "gidanmu na gaskiya a sama yake"
za ya canja jikunan mu zuwa masu daraja
"cikin jikuna kamar jikin darajarsa"
za a iya sa wannan a kalmar aiki. AT: "Jiki. Shi za ya canja jikunan mu da wannan ikon da yake amfani da shi ya kula da dukan abubuwa"
Bulus ya gargadi masubi su yi hankali da karnuka, mugayen ma'aikata, da masu yankan jiki.
Bulus ya ce masu kaciya na ainihi sune masu bauta ta wurin Ruhun Allah, masu taƙama da Almasihu Yesu, kuma basu amince a jiki ba.
Bulus ya bayyana gudanarwarsa na baya kamar mara laifi a darajar adalcin doka.
Bulus yanzu ya lisafta duka amincewarsa na baya a cikin jiki kamar a banza saboda Almasihu.
Bulus ya duba duka abubuwan baya kamar datti domin mai yuwa ya ci riban Almasihu.
Bulus yanzu yana da adalci daga Allah ta hanyar bangaskiya a Almasihu.
Bulus na da zumuncin wahalar Almasihu.
Bulus ya ci gaba da nacewa.
Bulus na nacewa ga manufar cin nasarar kyautar kiran Allah na Almasihu Yesu.
Bulus ya gaya wa Filibiyawa su hadu su kuma kwaikwayon misalin tafiyarsa.
Waɗanda allahnsu ne cikin su da waɗanda suke tunani a kan kayan duniya, an ƙaddara su ga hallaka.
Bulus ya ce yankasancin masu bi na a sama.
Almasihu zai fasala kaskantattun jikunan masu bi zuwa jikunan ya mai da shi kamar jikinsa mai daraja
1 Saboda haka, kaunatattu 'yan'uwana da nake marmari, farin ciki na da rawani na, a wannan hanya ku tsaya daram cikin Ubangiji, kaunatattun abokai. 2 Ina rokon Afodiya, ina rokon Sintiki, ku zama da ra'ayi daya cikin Ubangiji. 3 Babu shakka, ina sake rokon ku, abokan tarayyar takunkumina na gaske: ku taimaka wa matayen nan. Domin mun yi wahala tare a cikin yada bishara tare da Kilimas da sauran abokan aiki na, wanda sunayensu na rubuce cikin littafin rai. 4 Yi farin ciki cikin Ubangiji kullayomi. Ina sake cewa, yi farin ciki. 5 Bari dukan mutane su ga jimirin ku. Ubangiji ya yi kusa. 6 Kada ku damu da kowanne abu, maimakon haka, cikin komai tare da addu'a, da rokeroke, da godiya, bari rokeroken ku su sanu ga Allah. 7 Salamar Allah, da ta zarce dukan ganewa za ta tsare zuciyarku da tunaninku cikin Almasihu Yesu. 8 A karshe, 'yan'uwa, duk abin da ke mai gaskiya, duk abin da ya isa ban girma, duk abin da ke mai adalci, duk abin da ke mai tsabta, duk abin da ke karbabbe, duk abin da ke kawo kauna, duk abin da ke da kyakkyawan ambato, idan akwai yabo, yi tunani a kan wadannan abubuwan. 9 Wadannan abubuwan da kuka koya kuka karba kuka ji kuka gani a rayuwa ta, ku aikata wadannan abubuwan. Allah mai salama zai kasance tare da ku. 10 Na yi farin ciki sosai cikin Ubangiji domin yanzu a karshe kun sabunta kulawar ku game da ni. Kun kula da ni da gaske kwanakin baya, amma ba ku samu zarafin taimako ba. 11 Ba don bukata ta bane nake fada wannan. Domin na koyi dangana a kowanne irin yanayi. 12 Na san yadda zan zauna cikin bukata, na kuma san yadda zan samu a yalwace. A kowace hanya cikin kowanne abu na koyi asirin yadda zan ci da yawa da yadda zan zauna da yunwa, yadda zan zama a yalwace kuma in zama cikin bukata. 13 Zan iya yin komai ta wurinsa shi da yake karfafa ni. 14 Duk da haka, kun yi zumunta da ni cikin kunci na. 15 Kun kuma sani, ku Filibiyawa, cewa da farkon bishara, lokacin da na bar Makidoniya, babu ikilisiya da ta tallafe ni cikin batun bayarwa da karba sai ku kadai. 16 Ko lokacin da nake Tassalonika, kun aika da gudumawar biyan bukatu na fiye da sau daya. 17 Ba domin ina neman kyauta ba ne. A maimakon haka, ina neman amfani da zai kawo karuwa cikin ajiyar ku. 18 Na karbi dukan abubuwan, ina da shi a yalwace. An kosar da ni. Na karba ta hanun Abafroditus abubuwa daga wurinku. Shesheki na dadin kamshi mai dandanno, karbabbiyar hadaya mai gamsarwa ga Allah. 19 Allah na zai cika dukan bukatunku bisa ga yalwarsa da ke cikin daukaka cikin Almasihu Yesu. 20 Yanzu bari daukaka ta tabbata ga Allah da Ubanmu har abada abadin. Amin. 21 Gai da kowanne mai bi cikin Almasihu Yesu. Dukan 'yan'uwa da ke tare da ni suna gaisuwa. 22 Dukan masu bi a nan suna gaisuwa, musamman wadanda suke gidan Kaisar. 23 Bari alherin Ubangijin Yesu Almasihu ya zauna tare da ruhunku. Amin
Bulus ya cigaba da waɗansu umurnai ga masu bi na Filibi game da haɗin kai sa'an nan ya ba da umurnai don ya taimake su su yi rayuwa domin Almasihu.
Sa'ad da bulus ya ce, " abokin tarayyar takunkumina na gaske," kalmomin suna nufin mutum ɗaya ne. Bulus bai faɗi sunan mutumin ba. Ya kira shi haka ne domin ya nuna cewa ya yi aikin yaɗa bishara tare da shi.
"'Yan'uwana masubi, ina ƙaunar ku kuma ina matuƙar marmarin ganin ku"
Dubi yadda zaka juya wanna a cikin filibiyawa 1:12.
Bulus ya yi amfani da kalmomin nan "farin ciki" domin ya nun da cewa Ikilisiyar Filibi ne dalilin farincikinsa. Da ganyaye ne a ke yin "rawani," kuma mutum yakan sa shi a kai domin alamar darajantawa bayan ya yi nasara a wata gasa mai muhimmanci. "Rawani a nan yana nufin cewa Ikilisiyar Filibi ta kawo masa daraja a gaban Allah. AT: "Kun bani farin ciki domin kun gaskata da Yesu, kuma ku ne sakamakona da darajar aikin da na yi"
"Sai ku cigaba da rayuwa wa Ubangiji cikin hanyar da na koya muku, kaunatattun abokai"
Waƙannan mata ne masu bi da su ka taimake Bulus a Ikilisiyar Filibi. AT: "na roƙi Afodiya, kuma na roƙi Sintiki"
Maganar "zama da ra'ayi ɗaya" na nufin zama da hali ɗaya ko zaɓi daya. AT: "yarda da juna domin dukan ku kun gaskata da Ubangiji ɗaya ne"
"ka" a nan na nufin "abokin tarayyar takunkumi" ne.
Kilimas wani mutum ne maibi kuma ma'aikaci ne a Ikilisiyar Filibi.
"wanda Allah ya rubuta sunayen su cikin litafin rai"
Fasara wannan kamar yadda aka yi a 3:1.
Ma'anoni masu yiwuwa 1) Almasihu Yesu yana kusa da masubi cikin ruhu ko kuma 2) ranar da Yesu zai dawo duniya ya yi kusa.
"duk abin da ya faru da ku, ku tambayi All dukan abin da kuke bukata tare da addu'a da godiya"
"salamar da Ubangiji ke bayarwa"
"wanda ya fi abinda za mu iya ganewa"
A nan ana magana game da salamar Allah kamar soja ne da ke kare yadda muke ji da kuma tunanin mu daga damuwa. AT: "zai zama kamar soja ne yayi tsaron yadda kuke ji da kuma tunanin ku daga damuwa game da matsalolin rayuwa"
Yayin da Bulus yake kammala wannan wasiƙan, ya faɗin yadda ya kamata masubi su yi rayuwa domin su samu zaman lafiya da Allah.
"duk abuwuwan da ke kyawawa"
"duk abubuwan da mutane ke sha'awa" ko kuma "duk abin da mutane ke darajawa"
"idan suna da hali mai kyau"
kuma idan sune abubuwan da mutane suke yabo"
"da na koyar na kuma nuna muku"
"gamsu" ko kuma "murna"
"komen al'amari da nake ciki"
Bulus ya san yadda zai yi zama da murna ko babu dukiya ko da dukiya.
ƙoshi ko zama a cikin fama da yunwa, da kuma yadda ake samu a yalwace ko kuma zama cikin bukata- Waɗannan jumloli biyu suna nufin abu ɗaya ne. Bulus yana amfani da su ne domin ya nanata cewa ya koyi yadda za'a yi rayuwa da gamsuwa a kowane yanayi.
"zan iya yin kome domin Almasihu yana bani karfi"
Bulus yana maganar wahalu kamar wasu wurare ne da yake. AT: "Sa'ad da abubuwa sun zama da wuya"
Ma'anar bishara, a manufar Bulus a nan, ita ce wa'azin bisharar sa.
Za'a iya sanar da wannan cikin tabbaci. AT: "Ku ne kaɗai ikilisiyar da ta aika mini kuɗi ko kuma kuka tallefe ni"
Bulus yana maganar kyautar Filibi kamar ajiyar banki da ke daɗa ƙaruwa. A wannan yanayi, Allah ya san da kyawawan abubuwan da masubi na Filibi su ka yi. Bulus yana son masubi na Filibi su ba da kyautai domin su karɓi albarku na ruhu. AT: "In son Allah ya daɗ ƙara muku albarku na ruhu"
Wannan na iya nufin 1) Bulus ya karɓi komai da 'yan Filibi suka aika ko kuma 2) Bulus yana amfani da raha ta wurin cigaba da amfani da misalin kasuwanci daga 3:8 don faɗin cewa wannan sashin wasiƙar rasiti ne na kayan da Abafroditus ya isar.
Bulus yana nufin yalwar abubuwan da yake da bukata.
Bulus yayi maganar kyautar ikilisiyar Filibi kamar hadaya ce ga Allah a kan bagadi. Bulus ya nuna da cewa kyautar su karɓaɓɓiya ce ga Allah, kamar hadayar da firist ya ke konawa, wanda yake da kamshi da yake sa Allah ya ji daɗi. AT: "Na tabbatar maku cewa kyautar ku karɓaɓɓiya ce ga Allah, kamar karɓaɓɓiyar hadaya"
Wannan kalma ɗaya ne da wanda aka fassara "an cika" a aya 18. Salon zance ne da ke nufin "zai tanada dukan abuwbuwa da kuke bukata"
"daga ɗaukakar yalwarsa da yake bayarwa ta wurin Almasihu Yesu"
Kalmar nan "yanzu" na nuna addu'ar rufewa da kuma rufe wannan sashin wasiƙar.
Wannan yana nufin mutanen da ke aiki tare da Bulus ko kuma suna yi mishi hidima.
Wasu juyin sun juya wannan ta wurin amfani da "mutum mai tsarki" da "mutane masu tsarki."
Wannan yan nufin bayin da suka yni aiki a fadar Kaisar. "musamman 'yan'uwa masubi da ke aiki a fadar Kaisar"
Bulus yana magana game da masubi ta wurin amfani da wannan kalma "ruhu", wanda shine yake ba wa mutane daman yin dangantaka da Allah. AT: "tare da ku"
Bulus yana Filibiyawa su tsaya da karfi a Ubangiji.
Bulus yana so ya ga Afodiya da Sintiki sun same hankali daya a Ubangiji.
Bulus ya gaya masu su yi farin ciki a Ubangiji kulluyaumi.
Bulus ya ce maimakon damuwa, ku gaya wa Allah a addu'a abin da kuke bukata, ku kuma gode masa.
Idan mun yi wanan, salamar Allah zata tsare zukatan mu da kuma tunanin mu.
Bulus ya ce a yi tunani a kan abubuwa waɗanda ke da daraja, da adalci, tsarki, kyakkyawa, rahoto mai kyau, mafifici, da kuma yabo.
Filibiyawa yanzu sun iya sabunta damuwarsu game da Bulus.
Bulus ya koya asirin rayuwa wadatacciya a wadata da bukata duka.
Bulus na iya rayuwa wadatacciya ta wurin Almasihu wanda na karfafa shi.
Bulus na neman amfani ya ƙaru a kan ribar Filibiyawa
Allah ya ji dadi da sadaukarwar da Filibiyawa suka yi wa Bulus.
Bulus ya ce Allah zai wadata kowace bukatar Filibiyawa daga cikin yawar daukakarsa da take ga Almasihu Yesu.
Waɗanda suke iyalin Kaisar su gaida Filibiyawa.
1 Bulus manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah da Timoti dan'uwanmu, 2 zuwa ga masu bada gaskiya da amintattun 'yan'uwa cikin Almasihu da suke a Kolosi. Bari alheri da salama su kasance tare da ku daga wurin Allah Ubanmu. 3 Muna godiya ga Uban Ubangijinmu Yesu Kristi, kuma kullum muna addu'a dominku. 4 Mun ji bangaskiyar ku cikin Almasihu Yesu da kaunar da kuke da ita wa dukan kebabbu ga Allah. 5 Kuna da kaunar nan domin bege na hakika ga abin da aka tanadar maku a sama. Kun riga kun ji game da begen nan na hakika maganar gaskiya da bishara, 6 wanda ta zo maku. Wannan bishara tana ba da yaya tana kuma hayayyafa da kuma girma a cikin dukan duniya. Tana yin haka a cikinku kuma tun ranar da kuka ji ta kun kuma yi koyi game da alherin Allah cikin gaskiya. 7 Wannan itace bishara kamar yadda kuka koye ta a wurin Abafaras, kaunataccen abokin bautar mu, wanda ke amintacce mai hidimar Almasihu a madadin mu. 8 Abafaras ya bayyana mana kaunarku a Ruhu. 9 Saboda da wannan kauna, tun daga ranar da muka ji haka, ba mu fasa yi maku addu'a ba. Muna ta roko domin ku cika da sanin nufinsa cikin dukan hikima da fahimta ta ruhaniya. 10 Muna ta addu'a domin ku yi tafiya da ta cancanci Ubangiji a kowace hanya da za ta faranta masa rai. Muna ta addu'a cewa za ku ba da 'ya'ya cikin kowanne aikin nagari kuma za ku yi girma cikin sanin Allah. 11 Muna addu'a ku karfafa a cikin kowanne iyawa bisa ga ikon daukakarsa zuwa ga matukar jimrewa da hakuri. 12 Muna addu'a za ku yi godiyar farinciki ga Uban, wanda ya sa kuka samu rabo cikin gado na masu bangaskiya cikin haske. 13 Ya kwato mu daga mulkin duhu ya kuma maishe mu ga mulkin kaunataccen Dansa. 14 Ta wurin Dan ne muka sami fansa, gafarar zunubai. 15 Dan shine surar Allah mara ganuwa. Shine farkon dukan hallitta. 16 Domin ta wurinsa ne aka halicci dukan abubuwa, wadanda ke sama da wadanda ke duniya, masu ganuwa da marasa ganuwa. Ko kursiyai ko mulkoki ko sarautai ko ikoki, dukan abubuwa shi ya hallice su kuma dominsa. 17 Ya kasance kafin dukan abubuwa, a cikinsa ne kuma komai yake hade. 18 Kuma shine kan jikin, ikilisiya. Shine farko da kuma dan fari daga cikin matattu, don haka yana da wuri na fari a cikin dukan abubuwa. 19 Domin Allah ya yi farinciki cewa dukan cikarsa ta kasance a cikinsa, 20 kuma ya sulhunta kowanne abu zuwa gare shi ta wurin Dan. Allah ya kawo salama ta wurin jinin giciyensa. Allah ya sulhunta duka zuwa gare shi, ko abubuwan da ke duniya ko abubuwan da ke sama. 21 Domin a da ku baki ne ga Allah, kuma makiyansa ne cikin zuciya da cikin mugun ayyuka. 22 Amma yanzu, ya sulhunta ku ta wurin mutuwarsa ta jiki. Ya yi haka domin ya mika ku tsarkakaku, marasa aibu da marasa abin zargi a gabansa, 23 idan kuka ci gaba cikin bangaskiya, kafaffu da tsayayyu, marasa kaucewa daga begen ku na hakika na bishara da kuka ji. Wannan itace bishara da aka yi wa kowanne halitaccen taliki a karkashin sama. Wannan itace bishara wadda ni, Bulus, na zama bawa. 24 Yanzu ina murna da wahala ta domin ku. A jikina cika abin da ya rage cikin wahalar Almasihu domin jikinsa wadda itace ikilisiya. 25 Saboda wannan ikilisiya na zama bawa, bisa ga haki da Allah ya ba ni domin ku, domin cika sakon Allah. 26 Wannan shine asirin gaskiya da yake a boye shekara da shekaru da zamanai. Amma a yanzu an bayyana shi ga wadanda suka gaskanta da shi. 27 A gare su ne Allah ya so ya bayyana yalwar daukakar asirin gaskiyarsa a tsakanin al'ummai. Ya nuna Almasihu ne ke cikin ku, tabbacin daukaka mai zuwa. 28 Wannan shine wanda muke shella. Muna gargadar da kowanne mutum, muna kuma koyar da kowanne mutum tare da dukan hikima, don mu mika kowanne mutum cikakke cikin Almasihu. 29 Domin wannan nake aiki da himma bisa ga karfinsa da yake aiki a cikina da iko.
ko da shike wannan wasiƙa ya fito ne daga Bulus da Timoti zuwa ga masubi na Kolosi, wasiƙar ya tabbatar da cewa Bulus ne marubicin. Yana iya yiwuwa Timoti yana tare da shi kuma shi ne ya rubuta sa'an da Bulus ke magana.
"wadda Allah ya zaɓa ya zama manzon Almasihu Yesu"
Waɗannan kalamun basu haɗa da Kolosiyawa ba.
Bulus yana keɓe masu sauraronsa.
"Imanin ku a cikin Almasihu Yesu"
A nan "bege na haƙiƙa" ya tsaya a madadin abin da maibi zai sa rai da gaske, wa to, abubuwan da Allah ya alkawarta zai yi wa dukkan masubi. Ana maganan waɗannan abubuwan kamar wasu abubuwane da za a iya gani ko taɓawa da Allah ke ajiye wa a sama domin masu bi su mallaka nan gaba. AT: "domin kun haƙiƙance da cewa Allah na Sama zai yi abubuwa masu kyau da ya alkawartar muku.
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "saƙo game da gaskiyar, bisharar" ko kuma 2) "saƙon gaskiya, bisharar"
"'Ya'ya" a nan na nufin "sakamako". AT: "Wannan bisharar tana da sakamako mai kyau da yawa" ko kuma "Wannan bisharan tana samun ƙarin sakamako"
Wannan magnan na nufin yankin duniya da suka sani. AT: "ko ina a duniya"
"alherin Allah ta gaskiya"
Kalamunnan "na mu" da "mu" bai haɗa da Kolosiyawa ba
"bishara. Shi ne daidai da abin da kuka koya daga Abafaras, wanda shi ne ƙaunataccen abokin bautar mu kuma wanda" ko kuma "bishara. Shi ne daidai abin da Abafaras, ƙaunataccen abokin bautar mu, ya koya muku. Shi"
A nan "a madadin mu" yana nufin cewa Abafaras yana yi wa Almasihu aiki wadda Bulus kansa zai yi inda ba don yana kurkuku ba.
mutumin da ya yi wa'azin bishara wa mutanen da ke Kolosi
Bulus yana maganar Ruhu Mai Tsarki kamar wani wuri ne da masubi suke. AT: "yadda Ruhu Mai Tsarki ya sanya ku ku ƙaunaci masubi"
Domin Ruhu ya sanya su su ƙaunace wasu, Bulus ya yi musu addu'a ya kuma faɗa musu yadda yake addu'a domin su.
"Saboda Ruhu Mai Tsarki ya sanya ku ku ƙaunace sauran masubi"
Waɗanan Kalmomi basu haɗa da Kolosiyawa ba.
"daga ranar da Abafaras ya faɗa mana waɗannan abubuwan"
Bulus yana maganar masubi na Kolosi kamar su akwati ne. AT: "domin Allah ya cika ku da abinda kuke bukata ku sani domin ku iya aikata nufinsa"
"saboda Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu hikima ku kuma fahimci abinda Allah yake so ku yi"
Tafiya a nan na nuna halin rayuwa. AT: domin ku yi rayuwa yadda Allah yake sa rai ku yi
"a hanyoyin da za su gamshi Ubangiji"
Bulus yana maganar masubi na Kolosi kamar su bishiyoyi ne ko kuma shuke-shuke. Kamar yadda shuke-shuke sukan bada 'ya'ya, hakama masubi yakamata su cigaba da samun sanin Almasihu suna kuma yin kyawawan ayuka.
Kalmar nan "mu" yana nufin Bulus da Timoti amma ba Kolosiyawa ba.
Bulus yana maganar masubi na Kolosi kamar Allah zai matsar da su ne cikin wani wurin matuƙar jimrewa da hakuri. Yana addu'a ne domin kadda su daina dogara ga Allah kuma su zama da matuƙar hakuri yayin da suke girmama shi.
"ya bar ku ku samu rabo"
Bulus a nan yana maida da hankalin masu karatunsa a matsayin masu samun albarkun Allah ne. Amma ba wai yana nufin cewa shi kansa ba shi da rabo cikin waɗancan albarkun ba ne.
Karbar abin da Allah ya alkawarta wa masubi kamar cin gadon tarin dũkiya ne daga mallakar wani dangin iyali.
Wannan ra'ayin ya bambanta da ra'ayin mulkin duhu da ke aya na gaba. AT: "cikin darajar kasancewarsa"
"Allah Uba ya kwato"
"Duhu" a nan na nufin iko miyagu. AT: "ikon miyagu da suka bi da mu"
"ƙaunataccen Ɗan Allah Uba, Yesu Almasihu"
Bulus yakan yi magana kamar masubi suna "cikin" Yesu Almasihu ko kuma "cikin" Allah. AT: "ta wajen Ɗan mun sami fansa."
"fansa; Ɗansa ya gafarta zunuban mu" ko kuma "Uban ya gafarta mana ta wurin Ɗansa"
A nan "sura" baya nufin wakilcin wani abu da ake gani. Maimakon haka, "sura" a nan yana nufin cewa ta wurin sanin Ɗan, za mu iya koya yadda Allah Uban yake
Wannan wata suna ce ta Yesu mai muhimmanci, Ɗan Allah.
"Ɗan shine forƙon halitta duka." Furcin nan "Ɗan forƙon halita duka" ba nufin haifuwar Yesu a Baitalami yake ba. Maimakon haka, yanu nufin matsayin dawwawamar Allah Uban. A nan "forƙon halitta duka" na nufin "mafi muhimmanci". Yesu shine mafi muhimmanci da kuma "Ɗan" Allah na musamman. Shi Allah ne. Kalmar "Ɗa" a nan yana nuna dangantaka mafi kusa da Yesu ke da shi da Uban. Ba za'a iya fahimtar wannan dangartakar ba har sai kuma kun yi amfani da kalmomin "ɗa" da "uba" a harshenku.
AT: "Domin Ɗan ya halicci dukkan abubuwa" ko kuma "Allah ya sa Ɗan ya halicci dukkan abubuwa"
Ɗan ya halicci dukan abubuwa wa kansa, wanda sun haɗa da kursiyai, mulkoki ko sarautai, hukumomi, da ikoki
"shi ne ya rayu kafin dukkan abubuwa"
Bulus a nan yana maganar yadda Ɗan ke mulkin dukan abubuwa kamar yana rike da komai a wuri ɗaya. "ya rike komai wuri ɗaya"
"Yesu Almasihu, Ɗan Allah ne kan"
Bulus yana maganar matsayin Yesu a kan ikilisiya kamar kan da ke jikin mutum ne. Kamar yadda kai yana mulkin jiki, haka ma Yesu yana mulkin ikilisiya.
"tushen iko." shine shugaba na forko ko kuma wanda ya ƙirƙiro.
Yesu shi ne forkon mutum da ya mutu ya kuma tashi da rai, ba domin ya sãke mutuwa kuma ba.
"ta wurin jinin da Yesu ya zubar a bisa giciye"
A nan "jini" ya tsaya ne a madadin mutuwar Amasihu a bisa giciye.
"Akwai wani lokaci da ku masubi a Kolosi ma"
"kamar mutane ne da Allah bai san su ba" ko kuma "turo Allah gefe"
Bulus yana bayana Kolosiyawan kamar ana iya gani da ido yadda Yesu ya tsabtace su, ya saka musu tufafi masu tsabta, sa'an nan ya kawo su su tsaya a gabar Allah Uba.
Bulus yana amfani ne da waɗannan kalmomi biyun ya nanata ra'ayin magana ɗaya na zama kammalallu. AT: "kammalallu"
Wannan maganar yana tsaye ne a madaɗin "a fuskar Allah" ko kuma "a zuciyar Allah"
da masubin suka yi shela
"ga kowane mutum a duniya"
A zahiri dai Bulus bawan Allah ne. AT "bishara wadda ni, Bulus, na bauta wa Allah ta wurin yin shela"
Bulus yana magana ne game da shan wahala da ya cigaba da ɗanɗanawa. Yayiwu yana amincewa wa ne anan da cewa akwai wata shan wahala da shi da kuma duk sauran masubi zasu jure kafin Almasihu ya sake zuwa, da kuma cewa Yesu yana haɗakai tare da su cikin ɗanɗana waɗannan wahalu a cikin ruhu. Haƙiƙa ma'anar Bulus anan ba shine cewa wahalar Almasihu kaɗai bai isa tanaɗin ceto ga masubi ba.
Bulus yana magana game da jikinsa kamar wata randa ce da ke iya riƙe wahala.
Bulus yakan yi magana game da ikilisiya, kungiyar dukan masubi, kamar ita ce jikin Yesu.
Wannan na nufin domin cika manufan bisharar Allah, wadda shine a yi wa'azin ta a kuma gaskata. " maganar Allah" anan na nufin saƙo daga Allah. AT: "a yi biyayya da abinda Allah ya umurta"
AT: "Wannan shine asirin gaskiya da Allah ya ɓoye
kalmomin nan "shekara da shekaru" da kuma "zamanai" na nufin tsawon lokaci daga halitar duniya har zuwa lokacin da aka yi wa'azin bisharar.
AT: "a yanzu Allah ya bayyana ta"
Bulus yana maganar darajar wanan asirin gaskiya game da Allah kamar wata taskar dukiya ce mai daraja. "arziki"
Bulus yana maganar masubin kamar su wasu randuna ne da Yesu yake cikin su. Wannan shine wani hanayarsa na bayyana dayantakar masu bi da Almasihu.
"don haka za ku iya sa rai da gabagaɗin samun ɗaukakar Allah"
Waɗanan kalmomi basu haɗa da Kolosiyawa ba.
"muna bada ƙashedi ga kowa"
Zaku iya faɗin a wadda za a miƙa masa kowane mutum. AT: "don mu miƙa kowanne mutum ga Allah"
Zama cikakke na nufin kammalalle a ruhu. AT: "kammalalle a ruhu"
Bulus ya zama manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah.
Bulus ya rubuto wa waɗanda an keɓe wa Allah da kuma amintattun 'yan'uwa a Kolossia.
Kolossiyawan sun ji game da bege na hakika a kalmar gaskiya, bisharan.
Bulus ya ce bishara tana ba da 'ya'ya tana kuma girma a cikin dukan duniya.
Abafaras, amintaccen bawan Almasihu ne ya ba da bisharan ga Kolossiyawan.
Bulus ya yi addu'a cewa Kolossiyawan su cika da sanin nufin Allah a dukka hikima da fahimta na ruhaniya.
Bulus yayi addu'a cewa Kolossiyawan su yi tafiyan da ta cancanca ga Ubangiji, da ba da 'ya'ya da ƙyauwawan ayuka, kuma da girma cikin sanin Allah.
Waɗanda an keɓe wa Allah sun cancanci raɓo a gadon a cikin haske.
Ya cece su daga mulkin duhu ya kuma maishe su ga mulkin Ɗansa.
Cikin Almasihu, an fanshe mu, wanda shi ne gafarar zunubai.
Ɗan shine surar Allah mara ganuwa.
An halicci dukan abubuwa ta wurin Yesu Almasihu kuma domin shi.
Allah ya sulhunta dukka komai wa kansa a loƙacin da ya kawo salama ta wurin jinin Ɗansa.
Kafin gaskantawa da bisharan, Kolossiyawan baki ne daga Allah, kuma makiyansa ne.
Ɗole ne Kolossiyawan su cigaba cikin bangaskiya da amincewan bisharan.
Bulus na shan wahala ta dalilin ikilisiya, kuma ya na farin ciki da shi.
Asirin da aka ɓoye shekara da shekaru da zamanai amma a yanzu an bayyana shi, shi ne Almasihu a cikinku, amintatceyar ɗaukaka.
Maƙasudin Bulus shi ne ya mika kowanne mutum cikakke cikin Almasihu.
1 Ina so ku san yadda na sha faman gaske dominku, domin wadanda ke a Lawudikiya, da kuma wadansu da yawa da a jiki basu taba ganin fuska ta ba. 2 Na yi aiki saboda zuciyar su ta sami karfafawa ta wurin hada su cikin kauna zuwa dukan arziki na tabbaci da fahimtar asirin gaskiya na Allah, wato Almasihu. 3 A cikinsa dukan taskar hikima da sani ke boye. 4 Na fadi haka domin kada wani ya yaudare ku da jawabi mai jan hankali. 5 Ko da yake ba na tare da ku a jiki, duk da haka ina tare da ku a cikin Ruhu. Ina murnar ganin ku a yanayi mai kyau da kuma karfin bangaskiyar ku cikin Almasihu. 6 Kamar yadda kuka karbi Almasihu Ubangiji, ku yi tafiya cikinsa. 7 Ku kafu da karfi a cikinsa, ku ginu a kansa, ku kafu cikin bangaskiya kamar yadda aka koya maku, ku yawaita cikin yin godiya. 8 Ku lura kada wani ya rinjaye ku ta hanyar ilimi da yaudarar wofi bisa ga al'adun mutane, bisa ga bin abubuwan duniya, ba na Almasihu ba. 9 A cikinsa ne dukan Allahntaka ta bayyana ta jiki. 10 Ku kuwa kun cika a cikinsa. Shine gaban kowanne iko da sarauta. 11 A cikinsa ne aka yi maku kaciya, ba kaciya irin da yan adam suke yi ba, ta cire fatar jiki, amma ta kaciyar Almasihu. 12 An binne ku tare da shi ta wurin baftisma. Kuma a cikinsa ne aka ta da ku ta bangaskiya a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga mutattu. 13 A lokacin da kuke matattu cikin laifofinku, a cikin rashin kaciyar ku ta jiki, ya rayar da ku tare da shi kuma ya yafe maku dukan laifofinku. 14 Ya share rubutattun basussukanku da ka'idodin da suke gaba da mu. Ya cire su duka ya kafa su a kan giciye. 15 Ya cire ikoki da sarautu. A fili ya falasa su ya shugabance su zuwa ga bukin nasara ta wurin giciyensa. 16 Saboda haka, kada kowa ya shari'anta ku ta wurin ci ko sha, ko kuma sabon wata, ko game da ranakun Assabaci. 17 Wadannan sune inuwar abubuwan da ke zuwa nan gaba, amma ainihin shi ne Almasihu. 18 Kada kowa wanda ke son kaskanci da sujadar mala'iku ya sharantaku ku rasa sakamakonku. Irin wannan mutum yana shiga cikin abubuwan da ya gani ya zama mai girman kai a tunaninsa na jiki. 19 Ba ya hade da kai. Daga kan ne dukan jiki da gabobi da jijiyoyi ke amfani suna kuma hade tare; yana girma da girman da Allah yake bayarwa. 20 In kun mutu tare da Almasihu ga ala'muran duniya, don me kuke rayuwa kamar kuna karkashin duniya: 21 "Kada ku rike, ko ku dandana ko ku taba?" 22 Dukan wadannan abubuwa karshen su lalacewa ne in ana amfani da su, bisa ga kaidodi da koyarwar mutane. 23 Wadannan dokoki suna da hikima ta jiki irin ta addini da aka kago na kaskanci da kuma wahalar da jiki. Amma ba su da amfanin komai a kan abin da jiki ke so.
Bulus ya cigaba da ƙarfafa masubi da ke Kolosi da Lawudikiya don su gane cewa Almasihu Allah ne kuma yana nan cikin masubi, don haka su yi rayuwa kamar yadda sun karɓe shi.
Bulus yayi ƙoƙarin gaske da ganin cewa sun bunƙasa a zaman tsarkinsu da kuma fahimtar bishara.
Wannan wani birni ne da ke kusa da Kolosi wurin da akwai wata ikilisiya da Bulus ke yi masu addu'a.
A nan "ganin fuska" yana nufin mutumin da kansa. AT: "dukan waɗanda basu taɓa ganina da kai na ba" ko kuma "dukan waɗanda ban taba saduwa dasu fuska da fuska ba"
Bulus ya haɗa da Galatiyawa ko da shike ya yi amfani da wata wakilin suna dabam. AT: "saboda zukatansu da naku"
Wannan na nufin zuwan su kusa cikin dangantaka.
Bulus yana maganar mutum da ya gaskata da bisharar gaskiya ne kamar mutumin yana da arziki cikin abubuwan jiki
Allah ne kadai ke iya bayyana wannan sanin.
Yesu Almasihu shine asirin gaskiya da Allah ya bayyana.
Almasihu ne kaɗai ke iya bayyana gaskiyar hikimar Allah da kuma fahimita. AT: "Allah ya ɓoye dukan taskar hikima da kuma sani a cikin Almasihu"
Bulus yana magnar hikima da sanin Allah kamar su dukiyan kaya ne. AT: "matuƙar darajar hikima da sani"
Waɗannan kalmomi suna nufin abu ɗaya ne a nan. Bulus yana amfani da su tare ne domin ya nanata cewa dukan fahimta ta ruhu sun fito ne daga Almasihu.
Wannan yana nufin sa wani ya gaskata cewa wani abu ba gaskiya ba ne, sai yanayin mutumin ya canja har ma ya jawo wahalan sakamakon hakan.
jawabin da ke sa mutum yayi wani tunani dabam
Jikin mutum, na nufin mutumin. AT: "bana tare da ku fuska da fuska"
kasancewa da mutum a ruhu na nufin tunani game da mutumin ko da yaushe. AT: "Ina tunaninku ko da yaushe"
yin abubuwa yadda yakamata
"yadda babu wani ko wani abu da zai sa ku ku daina bada gaskiya"
Tafiya a cikin hanya na nufin yadda mutum ke rayuwarsa. Kalmar nan "a cikinsa" na nufin zama da dangantaka na kusa da Yesu da kuma aikata abubuwan ta ke faranta masa rai. AT: "yi rayuwanku yadda yake so ku yi" ko kuma "yi rayuwar da zai sa mutane su gani cewa ku nasa ne"
Waɗanan kalmomi suna bayyana abin da ake nufi da "tafiya a cikinsa."
Bulus yana maganar mutumin da ke da bangaskiya a cikin Almasihu kamar mutumin ya zama bishiya ne da ke girma da jijiyoyi masu zurfi a ƙasa
Bulus yana maganar mutumin da ke da bangaskiya na gaske a cikin Almasihu kamar wani gini ne da ke da tushe mai ƙarfi.
"ku dogara ga Yesu domin kowane abu"
Ya fi a bayyana wannan ba tare da ambata suna ko kuwa jan hankali zuwa ga mai koyarwar ba, wato Abafaras ((1:7). AT: "kamar yadda kuka koya" ko kuma "kamar yadda sun koya maku" ko kuma "kamar yadda ya koya maku"
Bulus yana maganar yin godiya kamar wani abu ne da mutum na iya daɗa samu. AT: "zama da godiya ga Allah sosai"
"Ku tabbatar cewa"
Bulus yana maganar yadda mutum ke iya gaskata koyaswar ƙarya
koyaswar addini da imanin da basu fito daga Allah ba amma tushen su daga tunanin mutum ne game da Allah da kuma rayuwa.
Bulus yana maganar ra'ayoyin ƙarya da basu kawo komi kuma basu da daraja kamar su randuna ne da babu komi a cikin su.
Duk imanin tsarin al'adun Yahudawa da al'ummai (Halinawa) banza ne. "Abubuwan duniya" na iya nufin ruhohi miyagu da ke cewa sune ke mulkin duniya kuma suna samun girmamawa daga mutane. Amma kima cikin masu fassara sun gano "abubuwan duniya" a matsayin takaitatcen koyaswar mutane game da duniya.
"Halin Allah gabaɗaya ya kasancewa ta siffar jiki a cikin Almasihu"
Bulus yana maganar mutane kamar su wani akwati ne da Allah ya ajiye Almasihu a ciki. AT: "ku kun zama cikakku a cikin Almasihu"
Almasihu ne mai mulki bisa kowane mai mulki
Bulus yana maganar waɗanda ke na Almasihu kamar suna cikin jikin Almasihu ne. AT: "A lokacin da kuka haɗu da ikilisiya ta wurin baftisma, Allah ya maku kaciya"
Da wannan maganan, Bulus yana cewa Allah ya sa masubi sun zama ƙarɓaɓɓu a gareshi ta wata hanya da ke tunashe shi da kaciya, bikin da Yahudawa ke yi domin shigar da 'ya'ya maza cikin al'umman Isra'ila.
Bulus yana maganar baftisma da kuma haɗin kai da taron masubi kamar binnewa ne tare da Almasihu. AT: "Allah ya binne ku da Almasihu a lokacin da kuka haɗa kai da ikilisiya ta wurin baftisma.
Da wannan maganan, Bulus yana maganar sabon rayuwar ruhaniya ta masubi da ke iya yiwuwa domin Allah ya sa Almasihu ya sake rayuwa kuma. AT: "domin kun haɗa kanku da Almasihu, Allah ya ta da ku"
A nan a tayar wata karin magana ne da ke sa mutum da ya mutu ya dawo da rai kuma. AT: "Allah ya tashe ku" ko kuma "Allah ya sa kun rayu kuma"
Bulus ya yi maganar rashin tuba zuwa ga Allah kamar mutuwa ce. AT: "A sa'ad da ku masubi ta Kolosi ba ku iya tuba ga Allah ba"
Da wannan maganan, Bulus yana maganar samun sabon rai na ruhaniya kamar sumun rai na jiki ne.
Dama ku matattu ne domin dalilai biyu: 1) ku matattu ne a ruhaniya, kuna rayuwar aikata zunubi ga Almasihu da kuma 2) ba a yi maku kaciya bisa ga shari'ar Musa ba.
"ya yafe mana, da mu Yahudawa da ku Helinawa, dukan laifofinmu"
Bulus yana maganar yadda Allah ke gafarta zunubanmu kamar yadda mutumin da yake bin mutane da yawa bashin kuɗi ko kayayyaki da yawa ya jante lissafin bashin yadda baza su biya kuma ba.
A lokacin Romawa, ba wuya sojojin Roma su yi fareti na nasara idan sun komo gida, suna nuna duk 'yan firsinan da kuma kayayyakin yaƙi da suka kwaso su sanadiyyar yaƙi. Allah na da nasara bisa ikoki da kuma hukumomin miyagu.
A nan "giciye" yana madadin mutuwar Almasihu a bisa giciye.
Shari'ar Musa ya shafi abinda mutum na iya ci da kuma sha. "gama abinda kuke ci ko abinda kuke sha"
Shari'ar Musa ya keɓe ranakun bukukuwa, sujada, da kuma miƙa hadaya. "don yadda kuke bikin ranakun ci da sha ko sabon wata ko kuma Asabar"
Inuwa bata ba da ainihin yadda abu yake ko kuma sifar abu. Hakannan kuma, al'adun addini kamar su shari'ar Musa na iya nuna zahirin Yesu Almasihu kaɗan ne kawai.
A nan wannan na nufin "gaskiyar," abinda ke bada "inuwar"
A nan Bulus yana maganar masu koyarwar ƙarya kamar su alƙalai ne masu cin hanci da rashawa a takaran wasan guje-guje da tsalle-tsalle da za su iya hana masubi samun kyautar nasaran da ya cancance su, kuma yana maganar Almasihu a matsayin mai ba da wannan kyautar ga mai nasara a irin wannan takara. AT: "kada kowa ... ya hana ku cin nasarar samun wannan kyautar"
Kalmar "ƙasƙanci" a nan na nufin yin abubuwa domin mutane su ga cewa mutum yana da ƙasƙanci. AT: "wanda ke so ku yi abubuwa domin ku nuna cewa kuna da ƙasƙanci"
A nan Bulus yana magana ne game da mutanen da suke ƙirari cewa suna da mafarkai da kuma wahayoyi daga Allah kuma suna magana game da su da nuna girman kai
A nan Bulus yana cewa tunani ta hanyar zunubi na sa mutum ya nuna cewa ya fi kowa sani. AT: "yana girman kai ta wurin tunaninsa na jiki"
A nan ana maganar mutum mai taƙama kamar wani abu ne da za a iya hura shi da iska ya yi girma fiye da yadda yakamata ya kasance
A nan kalman "jiki" yana nufin yanayin mutuntaka na zunubi. "tunanin zunubi da ya fi masa sauƙin yi"
Ana maganar wanda bai gaskanta da Yesu ba a matsayin wanda bai manne wa kan da tabbaci ba. Ana maganar Almasihu ne a matsayin kan jikin. AT: "Bai cafke Almasihu ba, wanda shi ne kamar kan jikin" ko kuma "Bai manne wa Almasihu ba, wadda shine kamar kan jikin"
Bulus yana maganar ikilisiya, da Yesu ne ke mulkin ta yana kuma inganta ta, kamar ita wata jikin mutum ne. AT: "Daga kan ne Allah ke biyan bukatar dukkan jiki ta wurin gaɓoɓi da jijiyoyi yana kuma haɗa su tare"
Da wannan maganan, Bulus yana magana game da maibi ne a matsayin wanda ke tare da Almasihu cikin ruhu: kamar yadda Almasihu ya mutu, hakama maibi ma ya mutu a cikin ruhu; kuma yadda Almasihu ya dawo da rai, hakama masubi zasu dawo da rain, wato maibin ya dawo da rai a ruhu zuwa tuba ga Allah.
Bulus yayi amfani da wannan tambaya ne domin ya tsauta wa Kolosiyawan saboda biye wa ra'ayoyin da ke duniya. AT: "ku daina biyayya da ra'ayoyin duniya! Ku daina gaskata su idan sun ce , 'ku ... taɓa!'"
"yi tunani lallai ne ku yi biyayya da sha'awace-sha'awacen duniya"
"tunanin, sha'awace-sha'awacen, da kuma ra'ayoyi masu yawa na mutanen duniya masu aikata zunubi
"Waɗannan dokokin sun zama kamar hikima ne ga marasabi domin sun sa waɗanda suke bin su su zama kamar masu ƙasƙanci ta wurin raunata jikunan su ne"
"basu hana ku biye wa sha'awace-sha'awacen mutuntakan ku"
Auke-auken Allah shi ne Almasihu.
Dukka taskar hikima da sani na ɓoye a cikin Almasihu.
Bulus ya damu cewa Kolossiyawan na iya samin yaudara daga jawabi mai jan hankali.
Bulus ya ce wa Kolossiyawan su yi tafiya cikin Almasihu Yesu kamar yadda sun ƙarbe shi.
Yaudarar wofin na bisa al'adun mutane da kuma bisa ga abubuwan zunubi na duniya.
Dukkan Allahntaka na zama cikin Almasihu.
Almasihu ne gaban kowanne iko da sarauta.
A na cire jiki na zunubi ta wurin kaciyar Almasihu.
A na binne mutum da Almasihu a baftisma.
Mutum matacce ne a zunubansa kafin Almasihu ya rayar da shi.
Almasihu ya share rubutattun basussukan ya kuma kafa su a kan giciye.
Almasihu ya cire ikokai da sarautun, a fili ya falasa su ya kuma shugabance su zuwa ga nasara.
Bulus ya ce abinci, abin sha, da kuma Assabar su ne inuwan abubuwa masu zuwa.
Inuwan su na nuna ainahin Almasihu.
A na tanada wa dukan jiki, suna kuma haɗe tare ta wurin kan, Almasihu.
Umurnin kada ku rike, dandana ko taba na cikin al'adun duniya.
Dokokin addinin mutane ba su da amfanin komai a kan abin da jiki ke so.
1 Idan dai Allah ya tashe ku tare da Almasihu, ku nemi abubuwan da ke sama, inda Almasihu ke zaune a hannun dama na Allah. 2 Yi tunanin a kan abubuwan da ke sama, ba a kan abubuwan da ke kasa ba. 3 Gama ku kun mutu, ranku kuma yana boye tare da Almasihu cikin Allah. 4 Sa'anda Almasihu ya bayyana, wanda shine ranku, sa'anan ku kuma zaku bayyana tare da shi cikin daukakarsa. 5 Ku kashe sha'awacce-sha'awaccen da suke a duniya - zina da fasikanci, rashin tsarki, muguwar sha'awa, mummunar buri, da kuma kwadayi, wadda shine bautar gumaka. 6 Saboda wandannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa a kan marasa biyayya. 7 A cikin wadannan abubuwa ne kuka yi rayuwa a da da kuke zauna a cikinsu. 8 Amma yanzu dole ku kawar da wadannan - zafin rai, fushi, mugayen manufofi, zage-zage, da kazamar magana daga bakinku. 9 Kada ku yi wa juna karya, domin kun tube tsohon mutumin da ayyukansa, 10 kun kuma yafa sabon mutum, wanda ake sabontawa cikin sani bisa ga surar wannan da ya hallice shi. 11 A nan ne inda babu Baheline da Bayahude, mai kaciya da marar kaciya, bare, baubawa, ko Basikitiye, bawa ko yantacce, amma Almasihu shine duka, yana kuma cikin duka. 12 A matsayin ku na zababbun Allah, masu tsarki da kaunatattu sai ku yafa jinkai, ayyukan kirki, saukin kai, kamewa da hakuri. 13 Yi hakuri da juna. Ku yi wa juna alheri. Idan wani na da damuwa da wani, ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku. 14 Fiye da wadanan abubuwa duka, ku kasance da kauna, wanda itace cikakkiyar kammalla. 15 Bari salamar Almasihu ta mallaki zukatanku. Sabili da wannan salama ce aka kiraye ku cikin jiki daya. Ku yi godiya. 16 Ku bar maganar Almasihu ta zauna a cikinku a yalwace. Da dukan hikima, ku koyar, ku kuma gargadi juna da zabura, wakoki, da wakokin yabo na ruhaniya. Kuna rairawa tare da godiya cikin zukatanku ga Allah. 17 Kuma duk abin da zaku yi cikin magana ko aiki ku yi duka cikin sunan Ubangiji Yesu. Kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa. 18 Mata, ku yi biyayya ga mazajenku, yadda yakamata a cikin Ubangiji. 19 Mazaje, ku kaunaci matayenku, kada ku muzguna masu. 20 Yaya, ku yi wa iyayen ku biyayya cikin dukan komai, domin wannan yana faranta wa Ubangiji rai. 21 Ku Ubanni, kada ku cakuni 'ya'yanku domin kada su karaya. 22 Bayi, ku yi wa iyayengijinku na jiki biyayya cikin kowane abu, ba tare da bautan ganin ido ba don faranta wa mutane rai, amma da sahihiyar zuciya. Ji tsoron Ubangiji. 23 Duk abin da kuke yi, ku yi aiki daga zuci domin Ubangiji ba domin mutane ba. 24 Kun san cewa, zaku karbi sakamako na gado daga wurin Ubangiji. Domin Ubangiji Almasihu kuke bauta wa. 25 Domin kowa ya yi rashin adalci zai karbi sakamakon rashin adalcin da ya yi, kuma babu son kai.
Bulus yana yi wa masubi gargaɗi cewa da shi ke su na Almasihu ne, lallai ne su kiyaye aikata wasu abubuwa.
Wannan karin magana ne da ke nufin "saboda"
Kamar yadda Allah ya tashi Almasihu zuwa sama, haka kuma Allah yana ganin masubi da ke Kolosi kamar su ma ya tashe su zuwa sama.
"abubuwan da ke cikin aljanna"
Zama "a hannun dama na Allah" alama ce ta karbar girma da iko daga wurin Allah. AT: "inda Almasihu ke zaune a wurin girma da iko a gefen Allah"
Kamar yadda Yesu ya mutu zahiri, haka ma Allah yana ganin masubi na Kilosi a matsayin waɗanda sun mutu tare da Almasihu.
Bulus yana maganar rayukan mutane kamar wasu abubuwa ne da ake iya ajiye su cikin akwati kuma yana magana kamar Allah shi ne wannan akwati. AT: Wannan na iya nufin 1) "yana kamar Allah ya dauki rayukan ku ya ɓoye tare da Almasihu a gaban Allah" ko 2) "Allah ne kaɗai masani ainihin abinda rayukanku suka ƙumsa, kuma shi zai bayyana shi a lokacin da ya bayyana Almasihu"
Almasihu ne ke ba da rai na ruhu ga maibi.
Bulus yana maganan sha'awacce-sha'awaccen zunubi kamar su gaɓoɓin jikin mutum ne da mutane ke amfani da su su gamsar da kan su.
"halin ƙazamta"
"sha'awar banza"
"da kuma kwaɗayi, wadda ke cikin bautar gumaka" ko "kuma kada ku zama da kwaɗayi domin shi ne bautar gumakai" (UDB)
Fushin Allah a kan waɗanda su ke aikata mugunta kamar yadda ya bayyana ta wurin hukunta su.
"mutane marasa biyayya" ko kuma "mutanen da sun ƙi yi masa biyayya"
Bulus yana maganar yadda mutum ke rayuwa kamar wata hanya ce da mutum ke tafiya a ciki. AT: Waɗanan ne abubuwan da kuke yi a da"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "da kuke yin waɗanan abubuwan" 2) "da kuke rayuwa cikin mutanen da ke rashin biyayya ga Allah"
"marmarin aikata mugunta"
maganar da ke ɓata wa mutane rai
kalmomi da basa nuna ladabi cikin hira
A nan "baki" yana nufin magana. "cikin maganar ku"
Bulus a nan yana maganar yadda mai bi ke kin tsohon halinsa na zunibi kamar wani tsohon tufafi da ake cirowa domin a yafa wani sabon tufafin. Kamar yandda Bulus yake magana, an saba moran tufafi wajen yin magana game da hali a cikin jama'ar Isra'ila.
Wannan na nufin Yesu Almasihu.
Waɗannan kalmomin misalai ne a sashin mutanen da Bulus ya ce ba kome bane ga Allah. Allah yana ganin kowane mutum iri ɗaya ne, babu zancen jinsi, addini, ƙasan da mutum ya fito, matsayin jama'a da mutum ya fito. AT: "jinsi, addini, al'ada, da kuma jama'ar da mutum ya fito ba kome bane"
baƙo wanda bai san al'adun inda yake zama ba
Mutumin da ya fito daga Sikitiya, da ba ya Daular Roma. Helinawa da Romawa kan yi amfani da wannan kalman wa mutumin da ya girma a wurin da ake aikata mugunta a kowane lokaci.
Babu abinda yake a ware ko a cire daga mulkin Almasihu. AT: "Almasihu na da muhimmanci kuma yana rayuwa a cikin duka mutanen sa"
AT: "A matsayin waɗanda Allah ya zaɓa wa kansa, wadda yake marmarin ganin cewa suna rayuwa dominsa kaɗai, kuma wadda yake ƙauna"
Aan maganar waɗannan halaye kamar wasu tufafi ne da ake iya sa wa. AT: "ku zama da jinƙai, halin kirki, sauƙin kai, kamewa, da zuciyar haƙuri" ko kuma "ku zama masu jinƙai, halin kirki, sauƙin kai, kamewa, da hakuri"
"Ku yi haƙuri da juna" ko kuma "Ku riƙe juna ko da kun ba wa juna kunya"
"ku bi da juna fiye da yanda sun cancanci ku bi da su"
AT: "na da wani dalilin da"
AT: "ku yi ƙaunar juna domin hakan zai haɗa ku tare"
Bulus yana maganan salamar da Almasihu ke bayarwa kamar wani mai mulki ne shi. Wannan na iya nufin 1) "Ku yi dukan kome domin ku sami salama a dangantakar ku da juna" ko kuma 2) "Ku bar Allah ya baku salama a cikin zuciyarku"
A nan "zukata" na nufin hankalin mutane. AT: "a cikin hankalin ku"
Bulus yana maganar Kalmar Almasihu kamar wani mutum ne da ke iya kasancewa a cikin sauran mutane. "Maganar Almasihu" na nufin koyaswar Almasihu. AT: "ku yi biyayya da koyaswar Almasihu" ko kuma "A ko da yaushe sai ku gaskata da Alkawarai na Almasihu"
"ku gargaɗas ku kuma ƙarfafa juna"
"da dukan ire-iren waƙoƙin yabo ga Allah"
A nan "zuciya" na nufin hankalin mutum. AT: " rairawa tare da godiya cikin zukatanku" ko "raira tare da godiya"
yin magana ko aikatawa
"domin girmama Almasihu Yesu" ko kuma "tare da ikon Ubangiji Yesu"
Ma'anoni masu yiwuwa sun akamar haka 1) domin girmama Ubangiji Yesu" ko kuma 2) "domin ya sa mutane su san cewa ku na Ubangiji Yesu ne su kuma yi tunani mai kyau game da shi" ko kuma "kamar Ubangiji Yesu ne da kansa yake yi"
Wannan na nufin 1) "domin ya yi manyan ayyuka" ko kuma 2) "domin ya sa mutane su iya magana da Allah suna masa godiya."
"Mata, ku yi biyayya"
"ya kamata" ko kuma "daidaine"
kada ku yi musu kaushi "kada ku yi fushi da"
"kada ku sa 'ya'yanku su yi fushi a banza"
"ku yi wa iyayengijinku na jiki biyayya"
"abubuwa. Kada ku yi biyayya a lokacin da Iyayengijinku ke kallo kaɗai, kamar kuna buƙatar gamsar mutane ne kawai"
"zuciya" anan na nufin tunani ko kuma manufa, AT: "da dukkan manufar gaskiya" ko kuma "da rashin munafinci"
"kamar yadda za ku yi wa Ubangiji aiki"
"gadon sakamakonku"
Anyi maganar karbar abin da Allah ya alkawarta wa masubi kamar gadan mallakar dukiya daga wani ɗan gida ne.
Jumlar nana "karbi sakamako" na nufin a hukunta. AT: za a hukunta dukan wanda ya yi rashin adalci" ko kuma "Allah zai hukunta duk wanda ya yi rashin adalci"
wanda ke kowane irin kuskure na ganganci
A nuna sonkai na nufin a ba wa wasu hukunci daban da na waɗanda suka aikata laifi iri ɗaya. AT: "Allah yana shar'anta kowa daidai" ko kuma "Allah yana shar'anta kowa bisa ga tsari ɗaya"
An tashe Almasihu don ya zauna a hannun daman Allah.
Masubi su nemi abubuwan da ke sama, ba abubuwan duniya ba.
Allah ya ɓoye ran masubin a cikin Almasihu.
A bayyanar Almasihu, masubi za su kuma bayyana da shi a cikin ɗaukaka.
Ɗole ne masubi su kashe sha'awacce-sha'awaccen zunubi na duniya.
Fushin Allah na zuwa kan waɗanda suke da rashin biyayya ga Allah.
Ɗole masubi su watsar da zafin rai, fushi, mugayen manufofi, zage-zage, da kazamar magana.
A na hallitar sabon ran mai bi a sifar Almasihu.
Ɗole ne masubin sa yafa jinkai, ayyukan kirki, saukin kai, kamewa da hakuri.
Mai bi ya yafe kamar yadda Ubangiji ya yafe masa.
Ƙauna ce cikakkiyar kammallan.
A halinsa, waka, kalma, da ayuka, ya kamata mai bi ya yi godiya wa Allah.
Ya kamata salamar Almasihu ya ɗau shugabanci a zuciyar mai bi.
Maganar Almasihu ta zauna a cikin mai bi a yalwace.
Mace ta yi biyayya ga mijinta.
Mai gida ya ƙaunaci matansa, kada ya muzguna ta.
Ɗa ya yi biyayya ga iyayensa cikin dukan komai.
Kada Uba ya cakuni 'ya'yansa.
Masubi su na yin aiki wa Ubangiji a kowane abubuwan da su na yi.
Wanda sun bauta wa Ubangiji a kowane abubuwan da su na yi, za su ƙarbi ladan gadon.
Waɗanda su na yin rashin adalci za su ƙarbi sakamakon abin da sun yi.
1 Ku iyayengiji, ku ba bayinku abin ke daidai ya kuma dace garesu. Kun sani cewa ku ma, kuna da Ubangiji a sama. 2 Ku cigaba da himmantuwa ga yin addu'a. Ku zauna a fadake cikin addu'a da godiya. 3 Ku yi addu'a tare domin mu kuma, domin Allah ya bude kofa domin kalmar, a fadi asirin gaskiyar Almasihu. Don wannan ne nake cikin sarka. 4 Ku yi addu'a domin in iya fadinsa daidai, yadda yakamata in fada. 5 Ku yi tafiya da hikima game da wadanda suke a waje, ku yi amfani da lokaci. 6 Bari maganarku ko yaushe ta zama ta alheri. Bari ta zama da dadin ji domin ku san yadda za ku amsa wa kowanne mutum. 7 Game da abubuwan da nake ciki, Tikikus zai sanar maku da su. Shi kaunataccen dan'uwa, amintaccen bawa, shi abokin barantaka na ne a cikin Ubangiji. 8 Na aike shi wurinku don wannan, domin ku iya sanin halin da muke ciki, don kuma ya karfafa zukatanku. 9 Na aike shi tare da Onisimus, amintacce da kuma kaunataccen dan'uwa, wanda daya ne daga cikin ku. Za su gaya maku duk abin da ya faru anan. 10 Aristarkus, abokin sarka na, yana gaishe ku da Markus, dan'uwan Barnaba (wanda a kansa ne kuka sami umarni; in yazo, ku karbe shi), 11 da kuma Yesu wanda ake kira Yustus. Wadannan ne kadai daga cikin masu kaciya abokan aiki na domin mulkin Allah. Sun zama ta'aziya a gare ni. 12 Abafaras na gaishe ku. Shi daya daga cikinku ne kuma bawan Almasihu Yesu ne. Kullum yana maku addu'a da himma, don ku tsaya cikakku da hakikancewa a cikin nufin Allah. 13 Gama ina shaidarsa a kan ya yi aiki da himma domin ku, domin wadanda ke Lawudikiya, da na Hirafolis. 14 Luka kaunataccen likita da Dimas suna gaishe ku. 15 Ku gai da 'yan'uwa dake a Lawudikiya, da Nimfa da ikilisiyar da ke cikin gidanta. 16 Lokacin da aka karanta wannan wasika a tsakanin ku, sai a karanta ta kuma a cikin ikilisiyar Lawudikiya, ku kuma tabbata kun karanta wasika daga Lawudikiya. 17 Ku gaya wa Arkibas, "Mai da hankali ga hidimar da ka karba cikin Ubangiji, don ka cika shi." 18 Wannan gaisuwa da hannu na ne - Bulus. Ku tuna da sarka na. Alheri ya tabbata a gare ku.
Bayan magana da iyayengiji, Bulus ya kammala umurnan sa na musamman ga masubi daban-daban a cikin ikilisiyar da ke Kolosi.
Waɗannan kalmomi mun suna da ma'ana kusan ɗaya kuma an yi amfani ne da su domin a nanata abubuwan da ke daidai masu kyau.
Allah yana so dangartakar da ke tsakanin maigida da baransa ya kasance da ƙauna kamar yadda Allah, Ubangijin mu na sama, yake ƙaunar bayinsa na duniya, haɗe da shugabanen barori na duniya.
Kalmar "mu" a nan na nufin Bulus da Timoti ba 'yan Kolosi ba.
"ku dinga yin addu'a da aminci" ko kuma "ku dinga yin addu'a ba fasawa"
Buɗe kofa a nan na nufin ba wa mutum zarafi ya yi wani abu. AT: "Allah zai tanadar da zarafi"
Wannan yana nufin bisharar Yesu Almasihu, wanda ba a gane ba kafin Yesu ya zo.
"sarƙa" a nan na nufin kasancewa a cikin kurkuku. AT: "Saboda shelar sakon Yesu Almasihu ne yanzu ina cikin kurkuku"
"Ku yi addu'a in iya faɗin sakon Yesu Almasihu daidai"
Akan yi amfani tafiya domin bayyana yadda mutum ke gudanar da rayuwarsa. AT: "Ku yi rayuwa a hanyar da zai sa waɗanda ba masubi ba su ga cewa kuna da hikima"
AT: "ku yi iyakar abubuwa masu kyau da zaku iya yi da lokacin ku" ko kuma "ku yi amfani da lokacinku da kyau"
Maganar alheri da kuma main daɗin ji da ke koya wa wasu ko wadda wasu ke jin daɗin ji. AT: "Bari taɗinku a ko yaushe ya zama na alheri da jan hankali"
"domin ku san yadda za ku amsa tambayoyi daga kowa game da Yesu Almasihu" ko kuma "domin ku iya bi da kowane mutum da kyau"
"dukkan abin da ya dinga faruwa da ni" (UDB)
"abokin bauta." Duk da yake Bulus mutum mai 'yanci ne, yana ganin kansa a masayin Bawan Almasihu ne kuma yana ganin Tikikus a masayin abokin bauta ne.
Waɗannan kalmomi basu haɗa da 'yan Kolosi ba
A kan ɗauka da cewa zuciya itace cibiyar shauƙi mai yawa. )
Bulus ya ce da Onisimus dan'uwa Kirista da bawan Almasihu.
"Tikikua da Onisimus za su gaya"
Za su gaya wa masubi a Kolosi duk abinda ke faruwa a wurin da Bulus ke zama a halin yanzu. Al'adu na cewa Bulus yana Roma a tsare a gida ko kuma a cikin kurkuku a wannan lokacin.
yana tare da Bulus a kurkuku a Afisa lokacin da Bulus ya rubuto wanan wasiƙar zuwa Kolosi.
"in Markus ya zo"
"Wannan wani mutum ne da yayi aiki tare da Bulus shi ma"
Bulus ya yi amfani da "kaciya" a nan da nufin Yahudawa domin, bisa ga shiri'ar Tsohon Alkawari, lalle ne a yi wa dukkan Yahudawa maza kaciya. AT: "Waɗannan mutane ukun ne kadai masubi Yahudawa da ke aiki tare da ni domin shelar Allah a matsayin sarki ta wurin Almasihu
"Waɗannan mutanen— Aristarkus, Markus, da Yustus kadai ne daga cikin masu kaciya"
Abafaras ne mutumin da ya yi wa'azin bishara ga mutanen da ke cikin Kolosi. (Dubi: 1:7)
"daga garinku" ko kuma "ɗan garinku"
"wani almajirin Almasihu Yesu mai himma"
"yana yi muku addu'a da naciya"
"ku tsaya kamalallu da gabagaɗi"
"na lura cewa ya yi aiki tukuru domin ku" (UDB)
Wannan wani abokin aiki ne tare da Bulus.
Wannan yanan nufin 'yan uwa masubi, a haɗe da maza da mata.
wata birni ce a kusa da Kolosi sosai da ke da wata ikilisiya
Wata mata mai suna Nimfa da ikilisiya da ke taruwa a gidanta domin sujada. AT: "Nimfa da taron masubi da ke haɗuwa a gidanta" (UDB)
Bulus yana tunashe da Arkibas game da hidimar da Allah ya ba shi kuma wanda wajabi ne ya yi. Kalmomin nan "mai da hankali," "ka karɓa" da kuma "ka cika" duka suna zuwa ga Arkibas ne shi kaɗai
Bulus yakan yi maganar sarƙa idan yana nufin ɗaurinsa a kurkuku. AT: "Ku tuna da ni ku yi mini addu'a yayin da ina kurkuku."
"Alheri" a nan yana a matsayin Allah, mai nuna alheri ko kuma ayyukan kirki ga masubi. AT: "Ina addu'a don Ubangiji Yesu Almasihunmu ya cigaba da nuna alherinsa a gareku duka" (UDB)
Bulus ya tuna wa iyayengijin duniya cewa su na da Ubangiji a sama.
Bulus na son Kolossiyawan su cigaba da himmantuwa a addu'a.
Bulus na son Kolossiyawan su yi addu'a don ya sami buduwar kofa don ya yi maganar kalman, asirin gaskiyar Almasihu.
Bulus ya umurce su su yi tafiya da hikima, su kuma yi magana da alheri ga waɗanda ke bare.
Bulus ya basu aikin sa komai sananne game da shi wa Kolossiyawan.
Bulus ya gaya wa Kolossiyawan cewa su ƙarbi Markus indan ya zo masu.
Ya na addu'a don Kolossiyawan su tsaya cikakku da hakikancewa a cikin dukka nufin Allah.
Sunan likitan Luka.
Ikilisiya a Lawudikiya na saduwa a gida.
Bulus ya rubuto wasika wa ikilisiya a Lawudikiya.
Bulus ya rubuta sunan shi a ƙarshen waskikan.
1 Bulus, Sila, da Timoti zuwa ga Ikilisiyar Tassalonikawa cikin Allah Uba da Ubangiji Yesu Almasihu. Alheri da Salama su kasance a gare ku. 2 Kullum muna bada godiya ga Allah domin ku dukka, kamar yadda muke ambaton ku a addu'o'in mu. 3 Muna tunawa da ku ba fasawa a gaban Allahn mu da Ubanmu kuma ayyukanku na bangaskiya, da kauna. Da hakurin bege na abinda ke gaba cikin Ubangijinmu Yesu Almasihu. 4 'Yan'uwa kaunatattu na Allah, Mun san kiran ku, 5 yadda bishararmu ta zo gare ku ba ta magana kadai ba, amma da iko, ta wurin Ruhu Mai Tsarki, haka kuma tawurin tabbatarwa. Ta haka kuma, kun san irin mutanen da muke acikin ku kuma domin ku. 6 Kun zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji, kamar yadda kuka karbi kalmar cikin tsanani mai yawa da murna tawurin Ruhu Mai Tsaki. 7 Sakamakon haka, kuka zama abin misali ga dukkan wadanda ke Makidoniya da na Akaya wadanda suka bada gaskiya. 8 Gama daga gare kune maganar Allah ta bazu ko ina, ba kuwa Makidoniya da Akaya kadai ba. A maimako, har ma zuwa ko ina bangaskiyarku cikin Allah ta kai. Don haka, bama bukatar muce maku komai. 9 Domin su da kansu suna bada labarin irin zuwan mu gare ku. Suna fadin yadda kuka juyo ga Allah daga bautar gumaka don ku bautawa Allah mai rai. 10 Suna bayyana cewa kuna jiran bayyanar Dansa daga sama, wanda ya tasar daga matattu. Wannan shine Yesu, wanda ya 'yantad da mu daga fushi mai zuwa.
Bulus ya bayyana kansa a matsayin marubucin wannan wasiƙa, ya kuma gaida Ikilisiya da ke Tasalonika
littafi ta nuna a sarari cewa Bulus ne marubucin wannan wasiƙar.
"Alheri" da "salama" kalmomi ne da ke bayyana halin kirki na zaman lafiya da mutum ke nuna wa zuwa ga mutane. AT: "Allah ya yi muku alheri ya kuma baku salama"
"Ku" na nufin masubi da ke Tasalonika.
"Kullum" a nan na ba da ra'ayin cewa a duk lokacin da Bulus ke addu'a, ba ya fasa miƙa Tasalonikawa ga Allah cikin addu'a.
"muke yi muku addu'a"
ayyuka da aka aikata domin gaskatawa da Allah
Bulus ya cigaba da godiya da yaba wa masubi da ke Tasalonika saboda bangaskiyarsu ga Allah.
A nan wannan na nufin Masubi maza da mata.
Kalman "mu" na nufin Bulus ne, Sila da Timoti, ba masubi na Tasalonika ba
"ba ta abin da mun faɗa kaɗai ba"
AT: 1) Ruhu mai Tsarki ya ba Bulus da abokansa ikon shelar bishara, ko kuma 2) Ruhu mai Tsarki ya sa wa'azin shelar bishara ta zama da iko a cikin masubi da ke Tasalonika, ko 3) Ruhu mai Tsarki ya nuna gaskiyar da ke cikin shelar bishara ta wurin mu'ujizai, al'ajabai da abin ban mamaki.
ana iya sa wannan haka. AT: "Allah ya sa kun tabbata cewa gaskiya ne"
"yadda muka bi da kanmu lokacin"
yin "koyi" na nufin "aikata kamar" ko kuma "kwaikwayon halin wani."
"marabci saƙon" ko kuma "karɓan abin da muka faɗa"
"a mawuyacin lokaci" ko kuma " cikin tsanani"
Wannan wata tsohowar lardi ce a cikin kasar Girka.
...
"magana" anan na nufin "saƙo." AT: "koyarwan Ubangiji"
A nan Bulus yayi magana game da shaidar Masubi da ke Tasalonika kamar wata ƙarar ƙararrawa ko kuma kayan kiɗa da aka buga
Bulus na nufin ikilisiyu da ke kewayen wancan yanki, da suka ji game da masubi na Tasalonika.
A nan "da kansu" na jaddada game da mutanen da suka ji game da masubi da ke Tassalonika.
A nan "zuwa" na nufin irin marabtan da Bulus da abokansa suka samu. AT: "yadda kuka marabce mu da kyau"
A nan "juyo ga...daga" na nufin kassance wa da biyayya ga wani mutum da kuma rashin biyayya ga wani. AT: "Suka faɗa yadda kuka daina bautar gumaka kuka fara bautawa Allah rayaye da gaskiya"
Wannan muhimmin suna ne na Yesu da ke bayyana dangantakarsa da Allah.
"Wanda Allah ya sa shi ya sake rayuwa kuma"
"domin ya zama ba mattace kuma ba." Wannan na nufin tayar da mutum daga cikin matattu, ya kuma kassance rayaye.
A nan Bulus ya haɗa har da masubi na Tasalonika.
Bulus ya na tunawa da ayyukansu na bangaskiya, da ƙauna, da hakurinsu na bege.
Bisharar ta zo wa Tessalonikawan ta magana, a iko, ta wurin Ruhu Mai Tsarki, haka kuma tawurin tabbatarwa.
Tessalonikawan sun ƙarba maganan da farin ciki a cikin Ruhu mai Tsarki.
Tessalonikawa suka ƙarbi maganan da tsoro.
Maganar Allah ta bazu ko a ina, bangaskiyarsu ta bayyana.
Tessalonikawan su na bautar gumakai kafin sun zama masubi na Allah na gaskiya?
Bulus da Tessalonikawan suna jiran Yesu ya zo daga sama.
Yesu ya 'yantad da mu daga fushi mai zuwa.
1 Domin ku da kanku kun sani, 'yan'uwa, cewa zuwan mu gareku, ba a banza yake ba. 2 Kun kuma san yadda aka wulakantar damu, aka kuma kunyatar damu a Filibi, kamar yadda kuka sani. Muna nan kuwa da karfin zuciya cikin Allahnmu domin yi maku bisharar Allah cikin fama da yawa. 3 Domin kuwa gargadinmu zuwa a gare ku ba gurbatacciya bace, ko cikin rashin tsarki, ba kuma ta yaudara bace. 4 A maimako, kamar yadda Allah ya amince damu, ya kuma damka mana amanar bishararsa, haka kuma muke yin magana. Muna maganar ba domin mu gamshi mutane ba, amma domin mu gamshi Allah. Domin shi ne yake gwada zuciyarmu. 5 Domin bamu taba yi maku dadin baki ba, ko sau daya, kamar yadda kuka sani, ko kwadayi a asirce, kamar yadda Allah shine shaidar mu. 6 Bamu kuma nemi daukaka daga mutane ko daga gare ku ko kuma wadansu ba. Da mun so da mun mori ikonmu a matsayin manzannin Almasihu. 7 A maimakon haka, mun kaskantar da kanmu a tsakanin ku kamar yadda uwa take ta'azantar da 'ya'yan ta. 8 Don haka muna da kauna domin ku, ba bisharar Allahnmu kadai muke jin dadin yi maku ba, amma harda bada rayukan mu domin ku. Domin kun zama kaunatattu ne a garemu, 9 Kufa tuna, 'yan'uwa, game da aikinmu da famarmu. Dare da rana muna aiki sosai domin kada mu nawaita wa kowane dayan ku. A lokacin da muke yi maku bisharar Allah. 10 Ku shaidu ne, haka ma Allah, yadda muka yi rayuwar tsarki da kuma adalci da rashin abin zargi a wajenku wadanda kuka bada gaskiya. 11 Don haka kun kuma sani yadda muka rika yi da kowannenku, kamar uba da 'ya'yansa, yadda muka yi ma ku garadi da kuma karfafa ku, mun kuma shaida. 12 Domin ku yi tafiya a hanyar da ta dace ga Allah, wanda ya kira ku zuwa ga mulkinsa da kuma daukakarsa. 13 Domin wannan dalili ne yasa muke yi wa Allah godiya a koyaushe. Domin a lokacin da kuka karbi maganar Allah daga wurinmu wadda kuka ji, kun karbeta da gaske ba kamar maganar mutum ba. A maimako, kuka karbeta da gaskiyarta, kamar yadda take, maganar Allah. Wannan kalma kuma ita ce ke aiki a cikin ku wadanda kuka yi bangaskiya. 14 Domin ku 'yan'uwa, kun zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah da ke Yahudiya cikin Almasihu Yesu. Domim kuma kun sha wahala irin tamu daga wurin mutanen kasarku kamar yadda suma suka sha a hannun Yahadawa. 15 Yahudawane suka kashe Ubangiji Yesu da sauran Annabawa, kuma Yahudawane suka koro mu, Basu gamshi Allah ba. A maimako, suna hamayya da dukkan mutane. 16 Sun kuma haramta mana yin magana da Al'ummai domin su sami ceto. Sakamakon haka kuwa kullum suna cika zunubansu. Fushi kuma ya afko kansu daga karshe. 17 Mu kuma, 'yan'uwa, mun rabu daku na karamin lokaci, a zahiri, ba a zuciya ba, mun kuma yi iyakar kokarinmu da marmarin ganin fuskarku. 18 Domin mun yi maramarin zuwa gareku. Ni, Bulus, ba sau daya ba, amma Shaidan ya hanamu. 19 To menene begenmu a gaba, ko murnarmu ko rawanin alfahari, a gaban Ubangijinmu Yesu a ranar zuwansa? Ko ba ku bane, da kuma sauran jama'a? 20 Don kuwa kune daukakarmu da kuma farin cikinmu.
Bulus na bayyana hidimar masubi da kuma ladar da ke biye.
"ku" da "kanku" na nufin masubi da ke Tasalonika.
A nan ana nufin 'yan'uwa masubi maza da mata.
kalmar "mu" na nufin Bulus, Sila, da Timoti ne, banda masubi na Tasalonika.
Ana iya faɗin wannan ta wata hanya kamar haka. AT: " ya kassance mai daraja"
"aka zalunce mu, aka kuma ci mana mutunci"
"yayin da ake gwagwarmaya cikin gãba"
"cikin gaskiya da tsarki"
Allah ya gwada Bulus ya kuma tabbatar da amincinsa.
Bulus na nufin shelar saƙon bisharar.
kalmar "zuciyar" na nufin tunani da sha'awace sha'awacen mutum. AT: "wanda ya san tunaninmu da sha'awace sha'awacenmu"
Bulus na gaya wa masubi na Tasalonika cewa ɗabi'arsa ba bisa ga lallaɓa, son kai, ko kuma ɗaukaka kai ba ne.
"bamu taɓa yi maku magana cikin yabon ƙarya ba"
A nan "asirce" na bayana cewa an ɓoye abu daga sanin mutane. AT: " ko kuma mun yi amfani da kalmomi domin mu ɓoye ƙwaɗayi" ko kuma "ba mu yi amfani da kalmomi domin ɓoye muguwar sha'awar kuɗin ku ba"
"da mun nace maku ku ba mu kuɗi"
kamar yadda uwa take ta'azantar da 'ya'yan ta cikin tawali'u, haka ma cikin tawali'u ne Bulus, Sila da Timoti suke magana da masubi da ke cikin Tasalonika.
"Wannan ita ce yadda muka nuna ƙaunarmu a gare ku"
"mun ƙaunace ku"
Bulus yayi magana game da saƙon bishara da rayuwarsa da na mutane da suke tare da shi kamar wasu kaya ne da za a iya raba wa da wasu. AT: "bai gamshe mu kaɗai ba mu faɗa maku bisharar Allah, amma mun kassance da ku mun kuma taimaka muku.
"mun kula da ku sosai"
kalamomin "aiki" da "fama" na nufin abu ɗaya ne. Bulus ya yi amfani da su domin ya nanata matuƙan aikin da suka yi. AT: "yadda muka yi aiki tuƙuru"
"Mun yi aiki tukuru don zaman rayuwarmu, domin haka ba zaku bukaci ku tallafa mana ba"
Bulus yayi amfani da kalmomin nan uku domin ya bayana kyaun halin da suka nuna ga masubi da suke Tassalonika.
Bulus ya kwatanta yadda ya ƙarfafa Tasalonikawa kamar yadda uba ke koyar da halin kirki ga 'ya'yansa.
Kalmomin nan "roƙo", "ƙarfafawa", da kuma "izawa" anyi amfani da su tare domin nuna yadda Bulus da tawagar sa suka ƙarfafa Tasalonikawa. AT: " Mun karfafa ku sosai"
kalma "ɗaukaka" na bayana kalma "mulki." At: "zuwa mulkinsa mai daraja"
A nan 'tafiya" na nufin "rayuwa." AT: "yin rayuwa domin mutane su yi tunani mai kyau game da Allah"
Bulus yakan gode wa Allah domin yadda suka ƙarbi saƙon bishara da ya kawo gare su.
"maganar mutum" na nufin duk saƙon da ke zuwa daga kowane mutum. AT: "ba saƙon da ke zuwa daga mutum ba"
"magana" a nan na nufin "saƙo." AT: "kuka ƙarbe ta kamar yadda gaskiyar take, wato saƙon da ta zo daga Allah"
Bulus na magana game da bisharar Allah kamar wani aiki ne da mutum ke yi. "Magana" na nufin "saƙo." AT: "wannan tsari ne na umarnin Allah wanda zai taimakawa waɗanda suka ba da gaskiya su yi aiki da kyau tare"
masubi a Tasalonika sun jimre tsanani kamar Yahudawa masubi. "zama kamar ikilisiyu"
"daga wasu Tasalonikawa"
"Sun yi ƙoƙarin hana mu magana"
Bulus na magana kamar mutum zai iya cika bokiti da zunubi kamar yadda ake cika wa da ruwa.
Wannan na nufin yadda a ƙarshe Allah na yin shari'a da kuma hukunta mutane domin zunubansu.
A nan "zuciya" na nufin tunani da shauƙi. Koda ya ke Bulus da abokan tafiyarsa basu nan a Tasalonika, basu daina tunani da kuma kula da masubi da suke wurin ba. AT: "a zahiri, amma mun cigaba da tunani game da ku"
A nan "fuskarku" na nufin gaba ɗaya mutumin. AT: "ganin ku" ko kuma "kassance da ku"
"Ni, Bulus, na yi ƙoƙarin zuwa gare ku sau da dama"
Bulus ya yi amfani da tambayoyi domin ya nanata dalilin marmarinsa na ganin masubi da ke Tasalonika. AT: "Domin ku da sauran masubi ne begenmu nan gaba, da murnarmu, da rawanin alfahari, a gaban Ubangijinmu Yesu a lokacin zuwansa."
Bulus yayi amfani da "bege" da nufin tabbacin cewa Allah zai saka masa domin aikin sa. Masubi na Tasalonika sune dalilin begensa.
Masubi na Tasalonika sune dalilin murnar sa.
A nan "rawani" na nufin lada ko sakayya da ake ba ƙwararren ɗan wasa da ya yi nasara. maganar "rawanin alfahari" na nufin ladan nasara, ko kuma yin aiki mai kyau.
Bitrus da waɗanda suke tare sun sha wahala aka kuma kunyatar dasu.
Bulus ya na so ya faranta wa Allah rai da wa'azinsa na bishara.
Bulus bai yi amfani da fadanci, ko ya nemi ɗaukaka daga wurin mutane ba.
Bulus ya kaskantar da kansa kamar uwa ko uba da 'ya'yan su.
Bulus da waɗanda suke tare sun yi aiki ɗare da rana don kadda su nawaita Tessalonikawan.
Bulus ya kaskantar da kansa kamar uwa ko uba da 'ya'yan su.
Bulus ya gaya wa Tessalonikawan cewa su yi tafiya a hanyar da ta dace ga Allah, wanda ya kira su zuwa ga mulkinsa da kuma ɗaukakarsa.
Tessalonikawa sun ƙarbi sakon kamar maganar Allah, ba kamar maganar mutum ba.
Yahudawan da basu bada ba sun tsananta wa ikilisiyoyi a Judea, sun kuma ƙashe Ubangiji Yesu da Annabawan, sun kuma koro Bulus, sun kuma hana Bulus ya yi magana da Al'ummai.
Bulus bai iya zuwa ba saboda Shaiɗan ya hana shi.
Tessaloniyawan za su zama begen Bulus, murna, da rawanin ɗaukaka a ranar zuwan Ubangiji.
1 Saboda haka, da bamu iya jimrewa ba, sai mukayi tunanin cewa ya dace mu dakata a Atina tukunna. 2 Sai muka aikaTimoti, dan'uwanmu dakuma bawan Allah a bisharar Almasihu, domin karfafaku ya kuma ta'azantar daku a fannin bangaskiya. 3 Mun yi haka ne saboda kada waninku ya raunana domin wadannan wahaloli. Domin ku da kanku kun sani cewa don haka aka kiraye mu. 4 Hakika, a lokacin da muke tare daku, mun gaya maku cewa muna daf da shan wahala, haka ya kuma kasance, kamar yadda kuka sani. 5 Domin haka, da ban iya jimrewa ba, sai na aiko domin in san yadda bangaskiyar ku take. Watakila ko magafci a wata hanya ya rinjaye ku, sai ya kasance wahalarmu ta zama a banza. 6 Amma Timoti da ya dawo daga gareku sai ya kawo mamu labari mai dadi akan bangaskiyarku da kuma kaunarku. Yako gaya mana cewa kuna kyakkyawan tunani a kanmu, kuma kuna marmarin ganinmu yadda muke marmarin ganinku. 7 Sabili da haka, 'yan'uwana, mun sami ta'aziyya tawurinku domin bangaskiyarku, a cikin dukkan bakin cikinmu da shan wuyamu. 8 Yanzu a raye muke, idan kun tsaya da karfi a cikin Ubangiji. 9 Gama wace irin godiya zamu ba Allah sabili da ku, domin dukan farin cikin da muke dashi a gaban Allah domin ku? 10 Dare da rana muke yi maku addu'a sosai domin muga fuskokinku kuma mu cika abin da kuka rasa cikin bangaskiyarku. 11 Bari Allah da kuma Ubanmu da kansa, da Ubangijinmu Yesu, ya bida sawayen mu zuwa gareku. 12 Bari Ubangiji yasa ku karu ku kuma ribambamya a kaunar 'yan'uwanku da dukan mutane, kamar yadda muke maku. 13 Bari yayi haka domin ya karfafa zukatanku marassa abin zargi a cikin tsarki a gaban Allah da Ubanmu a lokacin zuwan Ubangijinmu Yesu da dukan tsarkakansa.
Bulus na gaya wa masubi cewa ya aiki Timoti a gare su ya ƙarfafa bangaskiyarsu.
"bamu iya jimre damuwa game da ku ba"
"ya yi kyau ni da Sila mu dakata a Atina"
"ya dace" ko kuma "ya wajibta"
Wannan wata birni ce a yankin ƙasar Akaya wanda take garin Girka ayau.
Wannan maganganu biyun na bayana Timoti ne.
a raunana na nufin kassance wa da tsoro. AT: "kada wani ya razana daga amincewa da Almasihu"
Bulus na tsammanin kowa ya sani cewa Allah ne ya zaɓe su. AT: "Allah ya zaɓe mu"
Wannan na nuna cewa akwai sauran gaskiyan maganar fiye da abin da an gama faɗa.AT: " bugu da ƙari"
"shan wulakanci daga wasu mutane"
Bulus na bayana yadda yake ji ta wannan maganar. AT: " ban iya yin haƙurin jira ba"
Ana nuna cewa Bulus ne ya aiko Timoti. AT: "Na aiki Timoti"
"mun yi aiki tukuru a tsakaninku" ko kuma "koyarwanmu a cikinku"
"mara amfani"
"mu" na nufin Bulus ne da Sila.
A gane cewa wannan bangaskiyar a cikin Almasihu ne. AT: "labari mai kyau game da Bangaskiyarku"
a duk lokacin da suka yi tunanin Bulus, sukan samu tunani mai kyau game da shi.
"kuna so ku gan mu"
A nan " 'Yan'uwa" na nufin 'Yan'uwa masubi.
Wannan na nufin bangaskiya cikin Almasihu. AT: "domin bangaskiyarku a cikin Almasihu"
kalman "wuya" ya bayana dalilin "baƙin cikinmu." AT: "cikin dukkan baƙin cikinmu da ke zuwa daga shan wuyarmu"
Wannan maganar na nufin zaman gamsuwa da rayuwa. AT: "mun samu ƙarfafawa"
"tsaya da ƙarfi" na nufin kassancewa da aminci. AT: "idan kun cigaba da dõgara ga Ubangiji"
AT: "ba zamu iya ba Allah isashen godiya ba domin abubuwan da yayi maku! muna matuƙan farin ciki sabili da ku a duk lokacin da muke yin addu'a ga Allahnmu"
Bulus na magana kamar shi da abokansa na gaban Allah fuska da fuska. Mai yiwuya yana nufin ta wajen addu'a ne.
"duk ƙarfinsa"
kalman "fuska" na nufin ganin su gaba ɗaya. AT: "ziyarce ku"
A wannan ayoyin, kalman "mu" baya nufin ƙungiyar mutane ɗaya a kowane lokaci. A yi lura da fassara domin a gane ainihin ma'ana.
Bulus ya haɗa masubi na Tassalonika da abokan aikinsa.
"Muna addu'a cewa Allahnmu"
Bulus na magana kamar yana so Allah ya nuna masa da tawagarsa hanyar da zasu bi domin ziyarar masubi da ke Tasalonika. Yana nufin cewa, yana so Allah ya ba su zarafin yin haka.
A nan "kansa" na nufin Uban ne, an yi haka domin nanaci ne.
Bulus na magana game da ƙauna kamar wani abu ne da ake samuwa sannan a iya ƙarawa.
A nan "zuciya" na nufin abin da mutum ya yarda dashi, ya kuma amince da shi. AT: "ƙarfafa ku, domin ku zama"
"a lokacin da Yesu ya dawo duniya"
"tare da dukkan waɗanda suke nasa"
Bulus ya aikaTimoti domin ya karfafa ya kuma ta'azantar da masubi aTessalonika.
Bulus ya ce an kira shi ga shan azaba.
Bulus ya damu cewa watakila magafcin ya rinjaye su, kuma wahalarsa ta zama a banza.
Bulus ya karfafa a jin labari mai ƙyau na bangaskiya da kuma kaunar Tessaloniyawan, sun na kuma begen ganin shi.
Bulus ya ce a raye yake, idan Tessaloniyawan sun tsaya da ƙarfi a cikin Ubangiji.
Bulus na addu'a dare da rana domin ya iya ganin Tessaloniyawan ya kuma tanada abin da aka rasa a cikin bangaskiyarsu.
Bulus ya so Tessaloniyawan su karu su kuma ribambamya a kaunar juna da kuma dukan mutane.
Bulus ya so Tessaloniyawan su yi shiri don zuwan Ubangiji Yesu da dukan tsarkakansa.
1 A karshe, 'yan'uwa, muna karfafa ku kuma muna yi maku gargadi cikin Ubangiji Yesu. Yadda kuka karbi umarni a garemu game da yadda dole za kuyi tafiya kuma ku gamshi Allah, kuma a cikin wannan hanya ku tafi, ku kuma wuce haka. 2 Domin kun san umarnin da muka baku cikin Ubangiji Yesu. 3 Gama wannan ne nufin Allah: kebewar ku - cewa ku kauce wa zina da fasikanci, 4 Cewa kowannenku ya san yadda zai rike mata tasa cikin tsarki da girmamawa. 5 Kada kayi mata cikin zautuwar sha'awa (kamar al'ummai wadanda basu san Allah ba). 6 Kada wani ya kuskura yaci amanar dan'uwansa akan wannan al'amari. Gama Ubangiji mai ramuwa ne akan dukkan wadannan al'amura, Kamar yadda a baya muka yi maku kashedi kuma muka shaida. 7 Gama Allah bai kira mu ga rashin tsarki ba, amma ga rayuwar tsarki. 8 Domin haka, duk wanda yaki wannan ba mutane yaki ba, amma Allah, wanda ya bada Ruhunsa Mai Tsarki a gareku. 9 Game da kaunar 'yan'uwa, baku bukatar wani ya sake rubuta maku, gama ku da kanku Allah ya koyar da ku kaunar 'yan'uwa. 10 Ba shakka, kunayin haka ga dukkan 'yan'uwa wadanda ke cikin dukkan Makidoniya. Amma muna gargadin ku 'yan'uwa, kuyi haka bugu da kari. 11 Kuma muna gargadin ku 'yan'uwa kuyi kokari ku zauna a natse, ku kula da al'amuranku, kuyi aiki da hannuwanku, Yadda muka umarceku a baya. 12 Kuyi haka domin tafiyar ku ta zama dai dai a gaban wadanda basu bada gaskiya ba, kuma ya zama baku cikin bukatar komai. 13 Bamu so ku zama da rashin fahimta ba, 'yan'uwa, game da wadanda sukayi barci, domin kada kuyi bacin rai kamar sauran wadanda basu da tabbacin abinda ke gaba. 14 Domin idan mun bada gaskiya Yesu ya mutu kuma ya tashi, haka kuma tare da Yesu Allah zai maido da duk wadanda suka yi barci a cikinsa. 15 Gama muna fada maku wannan daga maganar Ubangiji, cewa mu da muke a raye, da aka bari har zuwan Ubangiji, babu shakka ba za mu riga wadanda suka yi barci ba. 16 Gama Ubangiji da kan sa zai sauko daga sama. Zai zo da muryar babban mala'ika, da karar kahon Allah, sai matattu cikin Almasihu su fara tashi. 17 Sai mu da muke a raye, wadanda aka bari, tare dasu za'a fyauce mu zuwa cikin gizagizai, mu hadu da Ubangiji cikin sararin sama. Haka zamu cigaba da kasancewa da Ubangiji. 18 Domin haka ku ta'azantar da juna da wadannan maganganu.
A nan "'yan'uwa" na nufin masubi.
Bulus na amfani da kalmar "ƙarfafa" da kuma "gargaɗi" domin ya nanata ƙarfin yadda suka ƙarfafa 'yan'uwa masubi AT: "mun ƙarfafa ku kwarai"
AT: "muka ƙoyar da ku"
A nan "tafiya" kalma ce da ke nufin yadda ya kamata mutum yayi rayuwa. AT: "ya kamata kuyi rayuwa"
Bulus na maganar umurninsa kamar Yesu ne da kansa ya bayar.
"ku yi nesa daga aikata zina da fasikanci"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "san yadda zai yi rayuwa da matarsa" 2) san yadda zai kula da jikin sa"
"da sha'awar zina da fasikanci mara kyau"
A nan "mutum" na nufin na miji ko ta mace. "ba wani"
Wannan jumlu biyu ne da ke nufin abu ɗaya domin nanata ƙarfin maganan. AT: "aikata abin da ba daidai ba"
AT: "Ubangiji zai hukunta wanda ya ƙetare doka, ya kuma yi kariyan ga wanda aka yi wa laifi"
"faɗa maku kafin lokacin da kuma ba da gargaɗi"
AT: "Allah ya kira mu ga tsabtacewa da rayuwan tsarki"
kalman "mu" na nufin duk masubi.
"duk wanda ya ƙi kula da wannan koyarwan" ko kuma "duk wanda ya yi watsi da wannan koyarwan"
Bulus na bayyana cewa wannan koyarwan daga Allah ne ba mutum ba.
"ƙaunar 'yan'uwa masubi"
"kuna nuna ƙauna zuwa ga dukkan masubi da suke Makidoniya"
"yi ƙoƙari"
Bulus yayi amfani da kalman "natse" da nufin zaman salama cikin al'umma ba tare da jayayya ba. AT: "zama cikin natsuwa da kuma yadda ya kamata"
"ku yi aikinku" ko " ku kula da abubuwan da ke alhakinku ku yi. Wannan na iya nufin da cewa kada mu dinga tsegumi da kuma tsoma baki a al'amuran wasu.
Wannan na nufin yin rayuwa mai ribatowa. AT: "yi na ku aikin domin samun abin da kuke bukata na zaman rayuwa"
A nan "tafiya" na nufin "rayuwa" ne ko kuma "nuna hali." AT: "nuna halin da ya dace"
ta hanyar nuna girmamawa ga wasu da kuma samun girmamawansu.
Bulus na magana game da waɗanda basu bada gaskiya a cikin Almasihu ba kamar suna wajen wani wuri ne da masubi ke ciki. AT: "a idanun waɗanda basu ba da gaskiya cikin Almasihu ba"
Bulus na magana game da masubi waɗanda sun riga sun mutu, da waɗanda suke raye, da kuma waɗanda zasu kassance a raye har lokacin dawowan Almasihu.
AT: "Muna so ku fahimta" ko "Muna so ku sani"
A nan "barci" na nufin mutuwa. AT: "waɗanda suka mutu"
"domin bamu so kuyi baƙin ciki kamar sauran"
makoki, fushi game da wani abu
"kamar mutane waɗanda basu da bege game da alkawari dake zuwa nan gaba." Ana iya bayyana abin da waɗanan mutanen basu da bege a kai. AT: "kamar mutane waɗanda basu da tabbacin cewa zasu tashi daga matattu"
A nan "mu" na nufin Bulus ne da masu sauraronsa.
"tashi domin a sake rayuwa"
A nan "yi barci" na nufin mutuwa ne.
"kalma" a nan na nufin "saƙo" ne. AT: "ta hanyar fahimtar koyarwan Ubangiji"
"a loƙacin da Ubangiji ya dawo"
"Ubangiji zai sauƙo da kasa"
"shugaban mala'ika"
"matattu cikin Almasihu" sune masubi waɗanda suka mutu. AT: "waɗanda suka badagaskiya a cikin Yesu Almasihu, amma sun riga sun mutu zasu zama farkon tashi"
A nan "mu" na nufin duk masubi da basu mutu ba.
kalman "su" na nufin masubi waɗanda suka mutu amma an sake rayar da su.
"hadu da Ubangiji Yesu a cikin sararin sama"
Bulus ya so Tessaloniyawan su yi tafiya su kuma gamshi Allah, su kuma yi fiye.
Bulus ya ce nufin Allah ga Tessaloniyawan shi ne tsarkakawarsu.
Ya kamata maza su bi da matansu a cikin tsarki da girmamawa.
Ubangiji zai zama mai ramuwa akan ɗan'uwan da ya yi zunubi a zancen zina.
Mutumin da ya ƙi ƙira zuwa ga zaman tsarki, ya ƙi Allah.
Bulus ya so Tessaloniyawan su ƙaunace juna sosai.
Tessaloniyawan za su natsu, su kula da al'amuransu, su kuma yi aiki da hannuwansu.
Mai yiwuwa Tessaloniyawan sun sami rashin fahimta game da abin da ya faru da waɗanda sun yi barci.
Allah zai kawo tare da Yesu waɗanda suka yi barci a cikin Almasihu.
Ubangiji zai sauko daga sama da babban murya da karar kahon Allah.
Matattu a cikin Almasihu za su fara tashi, sai waɗanda su na raye za su fyauce su sadu da su.
Wanda sun tashi za su sadu da Ubangiji a sarari, kuma za su kasance da Ubangiji kullum.
Bulus ya faɗa wa Tessaloniyawan cewa su karfafa juna da kalmominsa.
1 Yanzu fa game da zancen lokatai da zamanai 'yan'uwa, ba ku da bukatar a rubuta maku wani abu. 2 Domin ku da kanku kun sani kwarai cewa ranar zuwan Ubangiji kamar barawo take da dare. 3 Da suna zancen "zaman lafiya da kwanciyar rai," sai hallaka ta zo masu ba zato ba tsammani. Zai zama kamar nakudar haihuwa ce da ke kama mace mai ciki. Ba su kwa da wata hanyar kubuta. 4 Amma ku, 'yan'uwa, ai ba cikin duhu kuke ba har da wannan rana zata mamaye ku kamar barawo. 5 Domin dukkan ku 'ya'yan haske ne 'ya'yan rana kuwa. Mu ba 'ya'yan dare ba ne ko na duhu, 6 Don haka, kada muyi barci kamar yadda sauran ke yi. Maimakon haka, bari mu kasance muna zaman tsaro kuma muna a fadake. 7 Don masu yin barci da dare suke yin barci, haka kuma masu sha su bugu ma da dare suke yi. 8 Tunda shike mu 'ya'yan rana ne, bari mu zauna a natse. Bari musa sulke na bangaskiya da kauna, mu kuma sa kwalkwali don ceton mu dake gaba. 9 Domin Allah bai kaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijin mu Yesu Almasihu. 10 Shi ne wanda ya mutu domin mu, don ko da muna raye ko muna mace, mu iya rayuwa tare da shi, 11 Domin haka ku ta'azantar da juna ku kuma inganta juna, kamar yadda kuke yi. 12 Muna rokon ku, 'yan'uwa, ku bada daraja ga wadanda suke aiki a tsakaninku wadanda kuma suke shugabanci a kan ku cikin Ubangiji, wadanda kuma suke horonku. 13 Muna kuma rokon ku, da ku kula dasu ku kuma kaunacesu sabili da irin ayyukansu. Ku kuma yi zaman lafiya da junan ku. 14 Muna yi maku gargadi 'yan'uwa; ku jawa marassa ji kunne, ku karfafa marassa karfin zuciya, ku taimaki gajiyayyu, kuyi zaman hakuri da kowa. 15 Ku lura kada wani ya rama mugunta da mugunta, Maimakon haka ma, Ku cigaba da abinda ke mai kyau ga juna da kowa duka. 16 Kuyi farin ciki koyaushe. 17 Kuyi addu'a ba fasawa. 18 A cikin kome kuyi godiya. Domin wannan ne nufin Allah a cikin Yesu Almasihu game daku. 19 Kada ku hana Ruhun Allah aiki a cikin ku. 20 Kada ku raina anabce anabce. 21 Ku gwada komai. Ku rike abinda ke mai kyau. 22 Ku kaucewa duk wani abinda yayi kama da mugunta. 23 Bari Allah na salama ya mai da ku cikakun tsarkaka. Bari dukkan ruhun ku, da zuciyar ku, da jikin ku su zama adanannu marassa zargi domin zuwan Ubangijin mu Yesu Almasihu. 24 Wanda ya kira ku mai aminci ne, wanda kuma zai aikata. 25 Yan'uwa, kuyi addu'a domin mu. 26 Ku gaida dukkan yan'uwa da tsattsarkar sumba. 27 Ina rokon ku saboda Ubangiji ku karanta wasikar nan ga dukkan 'yan'uwa. 28 Bari alherin Ubangijin mu Yesu Almasihu shi kasance tareda ku.
Bulus ya cigaba da magana akan ranar da Yesu zai dawo.
A wannan surar, kalman nan "mu" na nufin Bulus, Sila da Timoti, sai dai ko in an ambata cewa ba haka ba ne. Kalman nan "ku" kuma na nufin masubi da ke ikilisiyar da take a Tassalonika.
Wannan na nufin abubuwan da za su auku kafin dawowan Yesu.
A nan "'yan'uwa" na nufin 'yan'uwa masubi.
"da kyau kwarai" ko "babu kuskure"
Kamar yadda ba wanda ya san a wane dare ne ɓarawo zai zo, hakannan kuma ba mu san sa'ad da ranar Ubangiji zai zo ba. AT: "ba tsammani"
"Sa'ad da mutane ke zance"
"sai hallaka ta zo ba zato ko tsammani"
Kamar yadda naƙudan mace take zuwa ba tsammani kuma ba za ta tsaya ba har sai ta haihu, hakannan hallakan za ta zo kuma mutane ba za su iya guje mata ba.
A nan " 'yan'uwa" na nufin 'yan'uwa masubi.
Bulus na magana game da mugunta da rashin sani game da Allah kamar sune duhu. AT: "ku ba jahilai ba ne kamar mutane waɗanda suke rayuwa a cikin duhu"
ranar da Ubandgiji zaya dawo kar ya zama da ban mamaki ba ga masubi.
Bulus na magana game da "gaskiyan" kamar wata haske ne da rana. AT: "Gama kun san gaskiyan, kamar mutane waɗanda suke rayuwa cikin haske, da kuma mutanen rana"
Bulus na magana game da mugunta da rashin sani game da Allah kamar sune duhu. AT: "Mu ba jahilai ba ne kamar mutane waɗanda suke rayuwa a cikin duhu"
Bulus na magana game da jahilcin ruhaniya kamar yin barci. AT: "kada mu zama kamar sauran waɗanda basu san cewa Yesu zai dawo ba"
kalmar "mu" na nufin dukkan masubi.
Bulus ya bayyana game da sani na ruhaniya a matsayin abin da ya sha bam-bam da barci da kuma maye.
kamar yadda mutane ke barci, ba su iya sanin abin da ke faruwa hakanan mutanen wannan duniyan basu san cewa Almasihu zai dawo ba.
Bulus na bayyana cewa da dare ne mutane ke sha su bugu, hakanan mutane da ke da rashin sani game da dawowan Almasihu, ba su rayuwa cikin kamun kai da natsuwa.
Bulus na magana akan sanin gaskiya game da Allah kamar 'ya'yan rana. AT: "mun san gaskiyan" ko "mu samu hasken gaskiyan"
Bulus na bayyana zama a faɗake kamar zama cikin natsuwa da kamun kai. AT: "mu yi rayuwa cikin natsuwa da kamun kai"
kamar yadda mayaƙi ke sa sulke domin tsaron jikin sa, haka maibi da ke rayuwa cikin bangaskiya da ƙauna ke samun tsaro. AT: " mu tsare kanmu da bangaskiya da ƙauna" ko "mu tsare kanmu ta wurin gaskatawa cikin Almasihu da ƙaunarsa"
kamar yadda kwalkwali ke tsare kan mayaki hakane tabaccin ceto ke tsare maibi. AT: " mu tsare kanmu ta wurin tabaccin cewa Almasihu zai cece mu"
A nan "gina" na nufin ƙarfafa. AT: "ƙarfafa juna"
"a girmama da kuma yaba wa waɗanda suke shugabanci"
Wannan na nufin mutanen da Allah ya maishe su shugabane a bisan masubi.
Bulus na gargadin masubi da su girmama kuma su ƙaunaci shugabanensu na ikilisiya.
Bulus yana yi wa masubi gargaɗi da cewa su cigaba da halin farin ciki cikin kowane abu, su yi zaman tsaro cikin addu'a, da kuma godiya cikin kowane abu.
cikin kowane yanayi
Bulus na nufin cewa halayen da ya ambata nufin Allah ne ga masubi.
"Kada ku hana Ruhu Mai Tsarki aiki a tsakanin ku"
"Kada ku raina annabci" ko "Kada ku ƙi kowane abu da Ruhu Mai Tsarki ya faɗa wa wani"
"Ku tabbata cewa kowace saƙon da kuna zaton ya zo daga Allah lallai daga shi ne"
Bulus ya yi magana game da saƙo daga Ruhu Mai Tsarki sai kace wani abu ne da wani ke iya riƙewa a hannayen sa.
Wannan na nufin cewa Allah yana sa mutum ya zama mara zuunubi da kuma mara aibi a gabansa.
A nan "ruhu, zuciya, da jiki" na nufin mutum gaba dayan sa. In har harshen ku ba shi da kalmomin nan guda uku, kuna iya bayyana kamar "dukan rayuwar ku" ko "ku." AT: "Bari Allah ya sa dukan rayuwar ku ta zama mara zunubi" ko "Bari Allah ya mai da ku marasa aibu sarai"
"mai amincin ne wanda ya kira ku"
"zai yi ta taimakon ku"
AT: "Ina zuga ku, kamar a ce Ubangiji ne ke magana da ku, ku karanta wasiƙar nan" ko "da ikon Ubangiji ina umurtar ku, ku karanta wannan wasiƙar"
Bulus ya ce ranar zuwan Ubangiji zai zo kamar barawo ne da dare.
Wasu mutane za su ce "Salama da kwanciyar rai".
Domin masubin ba sua cikin duhu, amma su 'ya'yan haske ne, kar ranar Ubangiji ya wuce su kamar barawo.
Bulus ya gaya wa masubin su yi zaman tsaro kuma da fadake.
Allah ya ƙaddara wa masubi ceto ta wurin Ubangiji Yesu Almasihu.
Bulus ya faɗa cewa su yarda su kuma ɗaukake su sosai cikin ƙauna.
Bulus ya ce kada kowa ya rama mugunta indan an yi masu mugunta.
Bulus ya ce masubi su yi godiya a cikin komai, domin wannan ne nufin Allah domin su.
Bulus ya umurce masubin cewa kada su raina anabce anabce, su gwada komai, su kuma rike abinda ke mai kyau
Bulus ya yi addu'a cewa Allah zai tsarkake masubi gabaɗaya a ruhu, da rai, da kuma jiki.
Bulus na addu'a cewa alherin Ubangiji Yesu Almasihu ya kasance da masubi.
1 Bulus da Silbanus da Timoti, zuwa ga ikilisiyar Tasolonika cikin Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Almasihu. 2 Bari alheri ya kasance tare da ku da salama daga Allah Ubanmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu. 3 Lallai ne mu godewa Allah kulluyaumin domin ku, yan'uwa. Domin hakan dai dai ne, saboda bangaskiyarku ta karu sosai, kuma kaunar junanku tana karuwa. 4 Mu da kanmu muna fahariya da ku a ikilisiyoyin Allah. Muna maganar hakurinku da bangaskiyarku a cikin dukkan tsananin da kuke fuskanta. Muna maganar kuncin da kuke jimrewa. 5 Wannan itace alamar shari'ar Allah ta adalci. Sakamakon haka shine za a dauke ku cancantattu na mulkin Allah wanda kuke wahala dominsa. 6 Adalci ne ga Allah ya mayar da kunci ga wadanda suke kuntata maku, 7 ya kuma baku hutu ku dake shan wuya tare da mu. Zai yi haka ne a bayyanar Ubangiji Yesu daga sama da Mala'ikun ikonsa. 8 A cikin wuta mai huruwa zai dau fansa bisa wadanda basu san Allah ba da wadanda basu karbi bisharar Ubangijinmu Yesu almasihu ba. 9 Za su sha azaba ta hallaka har abada daga fuskar Ubangiji da kuma daukakar ikonsa. 10 Zai yi wannan lokacin da yazo a wannan rana don jama'arsa su daukaka shi, kuma ya zama abin mamaki ga dukkan wadanda suka bada gaskiya. Domin kun gaskata shaidarmu a gare ku. 11 Saboda wannan muke addu'a kullum domin ku. Muna addu'a domin Allahnmu ya sa ku cancanci kiran ku. Muna addu'a ya biya ku muradin ku na yin nagarta da dukkan wani aikin bangaskiya da kuma iko. 12 Muna addu'a haka domin sunan Ubangijinmu Yesu ya sami daukaka daga gare ku. Addu'armu itace ya daukaka ku, saboda alherin Allahnmu da Ubangijinmu Yesu Almasihu.
Bulus ne marubucin wannan wasiƙar, amma ya sa Sila da Timoti a matsayin wanɗanda ya aike su da wasiƙar. Ya fara da gaisuwa zuwa Ikilisiyar da take a Tasalonika.
Wannan sunan "Sila" ne a Latanci. Mutum ɗaya ne da wanda aka ambata cikin littafin Ayyukan Manzanai a matsayin wanda ke abokin tafiyar Bulus.
Bulus ya cika amfani da wannan gaisuwar cikin wasiƙunsa.
Bulus ya yi amfani da "kulluyaumi" don ya nuna ma'anar cewa "sau da yawa" ko "a kai a kai". Jumlar nan ta na nanata yawan abubuwan da Allah ke yi a rayuwar Masubi na Tasalonika. AT: "Mu gode wa Allah kulluyaumi"
A nan "'yan'uwa" na nufin 'yan'uwa Masubi, maza da mata duka. AT: "'yan'uwa maza da mata"
"Domin abu mai kyau ne" ko "Don daidai ne"
"kuna ƙaunar juna da gaske"
A nan "juna" na nufin 'yan'uwa Masubi.
A nan "kanmu" an yi amfani da ita ne don nanata taƙamar Bulus.
AT: "Allah zai ɗauke ku cancantattun zama cikin mulkinsa"
Da Bulus ya cigaba, ya yi maganar cewa Allah mai adalci ne.
"Allah ya yi daidai" ko "Allah mai adalci ne"
A nan "a mayar" na nufin a sa wani ya ji daidai kamar yadda ya yi wa wani. AT: "Allah ya sanya wa waɗanda suka sanya muku bala'i, bala'i, ya kuma sassauta muku"
Ku na iya bayyana wa cewa Allah shine wanda ke kawo sauƙi. AT: "don Allah ya ba ku sauƙi"
"mala'ikunsa masu iko"
"shi zai hukunta waɗanda basu san Allah ba da wuta da kuma waɗanda" ko "Sa'an nan da wuta zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da waɗanda"
Anan "Su" na nufin mutane da sun yi rashin biyayya ga bisharar. AT: "Ubangiji zai hukunta su"
A nan "wannan rana" rana ce da Yesu zai dawo duniyan nan.
AT: "A Sa'ad da mutanensa za su ɗaukaka shi, duk waɗanda suka gaskanta za su yi mamakin sa"
Bulus ya nanata yadda ya ke addu'a saboda su. AT: "mu ma muna muku addu'a a koyaushe" ko "muna cigaba da yi muku addu'a"
A nan "kira" na nufin cewa Allah ya zaɓi mutane don su zama 'ya'yansa da bayinsa, don yin shelar saƙon cetonsa ta wurin Yesu.
"sa ku ku iya yin nagarta cikin kowace hanya da kuke so"
AT: Domin ku ɗaukaka sunan Ubangijinmu Yesu"
AT: "Yesu zai ɗaukaka ku"
"saboda alherin Allah"
Bulus yi godiya ga Allah domin girman bangaskiyansu da kuma ƙaunarsu ga juna.
Masubin su na jimre tsanani da azaba.
Za a ɗauke masubin cancantattu na mulkin Allah.
Allah zai azabantar da wanda sun azabantar da masubin, hukunta su da zafin wuta.
Masubi za su huta a loƙacin da Yesu Almasihu zai bayyana daga sama.
Hukuncin waɗanda basu san Allah ba zai zama har abada.
Ana keɓe waɗanda basu san Allah daga gaban Ubangiji kaman daga cikin hukuncinsu.
Masubin za su yi mamaki a loƙacin da Almasihu zai zo a ranarsa.
Sakamakon kyauwawan ayukansu shi ne a ɗaukaka sunan Ubangiji Yesu Almasihu.
1 Yanzu game da zuwan Ubangijinmu Yesu Almasihu da taruwarmu domin kasancewa tare da shi; muna rokonku yan'uwa, 2 kada kuyi saurin damuwa ko ku gigice saboda wani ruhu ko kuma sako ko kuma wasika da ta yi kamar daga wurin mu, da ke cewa ranar zuwan Ubangiji ta rigaya ta zo. 3 Kada wani ya yaudare ku ta kowace hanya. Domin wannan rana baza ta zo ba sai fandarewar nan ta zo kuma an bayyana mutumin tawayen nan wato dan hallaka. 4 Wannan shi ne wanda ya ke gaba, yana kuma daukaka kansa fiye da duk abin da ake kira Allah ko kuma ake bautawa. Sakamakon haka yana zama a kursiyin Allah har ma yana cewa shine Allah. 5 Baku tuna ba lokacin da nake tare daku na gaya maku wadannan abubuwa? 6 Yanzu kun san abinda ke tsaida shi, domin a bayyana shi a lokacin da ya dace. 7 Ko yanzu asirin take shari'a ya na aiki, sai dai a kwai wanda ke tsaida shi yanzu har sai an dauke shi. 8 Sa'anan za'a bayyana dan tawayen, wanda Ubangiji Yesu zai hallaka shi da numfashin bakinsa. Ubangiji zai mayar da shi ba kome ba ta wurin bayyanuwar zuwansa. 9 Mai tawayen nan kuwa, zai zo ne bisa ga aikin shaidan da dukan iko, alamu, da al'ajiban karya, 10 da kuma dukan yaudara ta rashin adalci. Wadannan abubuwa za su zama ga wadanda suke hallaka, saboda ba su karbi kaunar gaskiya ba domin su sami ceto. 11 Saboda wannan dalilin Allah ya aiko masu da sabani, saboda su yarda da karya. 12 Sakamakon shine dukkan su za'a yi masu shari'a, wato wadanda ba su yarda da gaskiya ba suna kuma jin dadin rashin adalci. 13 Amma muna masu godiya kulluyaumin ga Allah domin ku, yan'uwa wadanda Ubangiji yake kauna. Ubangiji ya zabe ku a matsayin yayan fari don ceto cikin tsarkakewar Ruhu da gaskatawa da gaskiya. 14 Wannan shine abinda ya kira ku gare shi ta wurin bishararmu domin ku sami daukakar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 15 Saboda haka yan'uwa, ku tsaya da gaske. Ku rike al'adun da aka koya maku, ko ta kalma ko kuma ta wasikarmu. 16 Yanzu bari Ubangiji Yesu Almasihu da kansa, da Allah Ubanmu wanda ya kaunace mu ya ba mu madawwamiyar ta'aziya da gabagadi mai kyau domin gaba ta wurin alheri, 17 ya ta'azantar da ku ya kuma gina zuciyarku cikin kowane aiki mai kyau da kalma.
Bulus ya gargaɗi masubi cewa kada su yarda a yaudare su game da ranar dawowan Yesu.
Kalman nan "yanzu" alama ce ta canjin kan magana cikin umurnin Bulus.
A nan "'yan'uwa" na nufin 'yan'uwa masubi, maza da mata duka. AT: "'ɗan'uwa da 'yar'uwa"
"kada ku yi saurin sa kanku cikin damuwa"
"ta wurin kalmomin baƙin ko ta wurin wasiƙar da ta yi kamar daga gare mu"
"cewa"
Wannan na nufin lokacin da Yesu zai dawo duniya saboda masubi.
"ranar Ubangiji ba zai zo ba"
Wannan na nufin lokacin da ke gaba a sa'ad da mutane dayawa za su juya wa Allah baya.
AT: "Allah ya bayyana mutum mai aikata mugunta"
Bulus ya yi magana a kan hallaka kamar mutum wanda ya haifi ɗa wanda manufar sa ita ce ya hallaka kowani abu gabaki ɗaya. AT: "wanda ya hallaka kowane abu da zai iya"
AT: "kowane abin da mutane ke duba a matsayin Allah ko kuma kowane abu da mutane ke bautawa"
"nuna kansa cewa shi Allah"
Bulus ya yi amfani da tambayar da ba lallai ne a bada amsa ba don ya tunashe su game da koyarwarsa a lokacin da ya ke tare da su a dã. Ana iya bayyana wannan cikin furci. AT: "Na tabbata kun tuna ... waɗannan abubuwan."
Wannan na nufin dawowar Yesu, ranar Ubangiji, da mutum mai aikata mugunta.
AT: "Allah zai bayyana mutum mai aikata mugunta a sa'ad da lokacin ya yi"
Wannan na nufin asirin mai tsarki da Allah ne kaɗai ya sani.
a tsaida wani ita ce a riƙe su ko kuwa a hana su yi abin da suna so su yi.
AT: "Sa'anan Allah zai bar ɗan tawayen nan ya bayyana kansa"
A nan "numfashi" na nufin ikon Allah. AT: "ta wurin ikon kalmomin bakinsa"
A Sa'ad da Yesu ya dawo duniya ya bayyana kansa, zai yi nasara kan wannan mai tawayen.
"da kowace irin iko, alamu, da al'ajiban ƙarya"
Wannan mutumin zai yi amfani da kowace irin mugunta ya yaudari mutane zuwa ga bada gaskiya gare shi a maimakon Allah.
Wannan mutumin da ya sami iko ta wurin Shaiɗan zai yaudari kowane mutum da bai gaskanta da Yesu ba.
A nan "hallaka" na nuna ra'ayin mara matuƙa ko madawamiyar hallaka.
"Domin mutanen basu ƙaunar gaskiyar"
Bulus na magana game da cewa Allah yana barin wani abu ya faru da mutane sai ka ce ya na aiko masu wani abu ne. AT: "Allah yana barin mutumin nan mai aikata mugunta ya yauɗare su"
AT: "Allah zai hukunta dukan su"
"waɗanda ke jin daɗin rashin adalci saboda basu gaskata da gaskiyar ba"
Bulus a yanzu ya canja kan magana.
Bulus ya yi amfani da wannan kalma anan don ya sa alamar cewa akwai canji cikin kan magana.
Kalman nan "kulluyaumi" na nufin kowane lokaci. AT: "mu cigaba da godiya"
A nan "mu" na nufin Bulus, Sila da Timoti.
AT: "Gama Ubangiji na ƙaunar ku, 'yan'uwa"
an yi magana game da zama cikin mutane na farko da aka cece su sai ka ce masubi da ke Tasalonika su "'ya'yan fari" ne. Ana iya bayyana wannan ta wurin fid da kalmomin nan "ceto", "tsarkakewar"
Bulus ya gargaɗi masubi su riƙe bangaskiyarsu cikin Yesu da ƙarfi.
A nan "al'adu' na nufin gaskiyar Alamasihu da Bulus da sauran manzanni suka koya. Bulus ya yi magana game da su sai ka ce masu karatunsa za su iya riƙesu da hannayen su. AT: tuna da "al'adun" ko "gaskata da "gaskiyar"
AT: "mun koya maku"
"ta wurin kalma" anan na nufin "ta wurin umurnin" ko "ta wurin koyarwa." ku na iya bayyana wannan a fili. AT: "ko ta wurin abin da muka koya muku da kanmu ko ta wurin wasiƙar da muka rubuto muku"
Kalman nan "mu" na nufin dukan masubi.
A nan "kansa" na ƙara bada nanaci ga maganan nan "Ubangiji Yesu Almasihu."
A nan "zuciya" na misalin inda shauƙin ta ke. AT: "ta'azantar da ku ya kuma ba ku ƙarfi don"
"kowane abu na gari da kuke yi kuke kuma faɗa"
Bulus ya ce yanzu zai rubuta game da zuwan Ubangiji Yesu Almasihu.
Bulus ya ce masu kada su gaskanta cewa ranar Ubangiji ya rigaya zo.
Ɗole ne faɗiwa da bayyanar mutumin tawaye ya zo kafin ranar Ubangiji.
Mutum mai tawaye na gaba, na kuma ɗaukakan kansa fiye da Allah, a zaune a cikin haikalin Allah na kuma nuna kansa kaman Allah.
Zai a bayyana mutumin tawayen idan loƙacin ya yi, a loƙacin da an ɗauke wanda ke tare shi.
Idan an bayyana Yesu, zai kashe mutumin tawayen.
Shaiɗan na aiki da mutumin tawaye don ya bashi iko, alamu, da kuma karyan abubuwan al'ajibi.
Ana ruɗin wasu domin basu ƙarbi ƙaunar gaskiya don su iya tsira ba.
Waɗanda an ruɗe su su na kuma hallaka, su na jin dadin rashin adalci.
Allah ya zaɓa wa Tessaloniyawan su samu ɗaukakan Ubangiji Yesu Almasihu ta wurin bisharan.
Bulus ya ce wa Tessaloniyawan su tsaya da ƙarfi su kuma kama al'adun da an koya masu.
Bulus na son Tessaloniyawa su kafu a cikin duk ƙyauwawan ayuka da magana.
1 Yanzu yan'uwa, ku yi mana addu'a saboda maganar Ubangiji tayi sauri ta sami daukaka, kamar yadda take tare da ku. 2 Ku yi addu'a domin mu kubuta daga mutane masu mugunta da keta, gama ba kowa ke da bangaskiya ba. 3 Amma Ubangiji mai aminci ne, shi wanda zai kafa ku ya tsare ku daga mugun. 4 Muna da gabagadi cikin Ubangiji a kan ku, cewa kuna yi, kuma za ku ci gaba da yin abubuwan da muka umurta. 5 Ubangiji ya bi da zuciyarku zuwa kaunar Allah da kuma jimrewar almasihu. 6 Yanzu muna umurtar ku, yan'uwa, a cikin sunan Ubangiji Yesu Almasihu, ku guji duk dan'uwa wanda yake zaman banza ba kuma akan al'adun da kuka karba daga wurin mu ba. 7 Saboda ku da kan ku kun sani yana da kyau kuyi koyi da mu. Ba mu yi zama a cikin ku kamar wadanda ba su da tarbiya ba. 8 Ba mu kuma ci abincin kowa ba tare da mun biya ba. Maimakon haka, mun yi aiki dare da rana cikin wahala da kunci domin kada mu dora wa kowa nauyi. 9 Mun yi haka ba don ba mu da iko ba. Maimakon haka, mun yi wannan ne saboda mu zama abin koyi a wurin ku, domin ku yi koyi da mu. 10 Lokacin da muke tare da ku, mun umurce ku, "Duk wanda ba ya son yin aiki, kada yaci abinci." 11 Saboda mun ji cewa wasun ku sun ki yin aiki. Ba su aiki sai dai shiga shirgin wasu. 12 Irin wadannan, muke umurta da kuma karfafa wa cikin Ubangiji Yesu Almasihu, da su yi aiki da natsuwa, suna cin abincin kan su. 13 Amma ku yan'uwa, kada ku rabu da yin abinda ke daidai. 14 In wani yaki biyayya da kalmominmu cikin wannan wasika, ku kula da shi kuma kada kuyi ma'amalar komai dashi, saboda ya ji kunya. 15 Kada ku dauke shi a matsayin makiyi, amma ku gargade shi a matsayin dan'uwa. 16 Bari Ubangijin salama da kansa ya ba ku salama kulluyaumin ta kowace hanya. Ubangiji ya kasance tare da ku duka. 17 Wannan ita ce gaisuwa ta, ni Bulus, da hannuna, wanda shine alama a kowace wasika ta. Haka nake rubutu. 18 Bari alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance tare da ku duka.
Bulus ya roƙi masubi su yi addu'a domin sa da kuma abokansa.
Bulus ya yi amfani da wannan kalma "yanzu" don nuna alamar canji ciki kan maganarsa.
A nan "'yan'uwa" na nufin 'yan'uwa masubi, duk tare da maza da mata. AT: "'ɗan'uwa da 'yar'uwa"
Bulus ya yi magana game da bazuwar maganar Allah sai ka ce ta na guduwa zuwa wurare dabam dabam. AT: "saboda jim kaɗan mutane da yawa za su ji saƙon mu game da Ubangijinmu Yesu su kuma daraja ta, kamar yadda ya faru da ku"
AT: "domin Allah ya cece mu" ko "domin Allah ya kubutar da mu"
"gama yawancin mutane ba su gaskanta da Yesu ba"
"wanda zai ba ku karfi"
"Shaiɗan"
"Mu na da bangaskiya" ko "Mun dogara"
A nan "zuciya" na nufin tunanin ko zuciyar mutum. AT: "sa ku ku fahimci"
Bulus ya yi magana game da ƙaunar Allah da jimrewar Almasihu sai kace masaukin da ke hanya. AT: "yawan yanda Allah ke ƙaunarku da kuma yawan yanda Almasihu ya jimre saboda ku"
"Suna" a nan na nufin Yesu Almasihu. AT: "kamar Ubangijinmu Yesu Almasihu kansa ne ke magana"
A nan "mu" na nufin dukan masubi.
"yi kamar yadda ni da abokan aiki na ke yi"
Bulus ya yi amfani da korau biyu don ya nanata mai yaƙinin na. AT: "mun yi rayuwa cikin ku kamar waɗanda sun sami tarbiya sosai"
"mun yi aiki cikin dare da rana." A nan "dare" da "rana" na nufin "kowane lokaci." AT" mun yi aiki kowane lokaci"
Bulus ya nanata yadda yanayinsa mai wuya yake. Aiki mai wuya na nufin aikin da ke bukatan himma sosai. Ƙunci na nufin sun jimre zafi da wahala. AT: "cikin kowane yanayi mai wuya"
Bulus ya yi amfani da korau biyu don ya nanata mai yaƙinin nan. AT: Haƙika mu na da ikon karban abinci daga gare ku, amma maimakon haka mun yi aiki don abincin mu"
AT: "Idan mutum na son ya ci abinci, to lallai ne ya yi aiki"
A nan "tafiya" na a madadin hali cikin rayuwa. AT: "wasu suna rayuwan zaman banza" ko "wasu suna da ƙiwuya"
Masu shiga shirgin wasu, mutane ne waɗanda ke shigan al'amuran sauran mutane tun ba a nema taimako daga gare su ba.
"cikin natsuwa, cikin kwanciyar rai, da kuma sassauci." Bulus ya gargaɗi masu shiga shirgin wasu su bar shiga cikin al'amuran wasu.
Bulus ya yi amfani da wannan kalman don ya bambata masubi wanda suke da ƙiwuya da kuma masubi da ke da kwazon aiki.
Kalman nan "ku" na nufin duk masubi da ke Tasalonika.
"In wani bai yi biyayya da umurnan mu ba"
Lura ko shi waye ne. AT: "a bayyana wannan mutum a idon jama'a"
Bulus ya umurci masubi da su fita daga sha'anin masubi da ke malalata a matsayin horo.
Za ku iya sa shi a bayyane cewa wannan addu'ar Bulus ne ga Tasalonikawa. AT: "Ina addu'a cewa Ubangijin salama kansa yã ba ku"
A nan "kansa" na nanata cewa Ubangiji zai bada salama ga masubi.
Ni Bulus na rubuta wannan gaisuwan da hannuna, shine na saba yi cikin kowace wasiƙa ta a matsayin alamar cewa wannan wasiƙar haƙiƙa daga ni ne"
Bulus ya bayyana a fili cewa wannan wasiƙar daga shine ba jabu ba ne.
Bulus na son Tessaloniyawan su yi addu'a don maganar Ubangiji ya bazu da sauri kuma ya samu ɗaukaka.
Bulus na son a cece shi daga mugu da mugayen mutane wanda basu da bangaskiya.
Bulus ya gaya wa Tessaloniyawan su cigaba da yin abubuwan da ya umurce su.
Ya kamata masubin su guje duk ɗan'uwa da ke zaman banza.
Bulus ya yi aiki dare da rana, da biyan abincinsa, bai kuma zama masu nauyi ba.
Bulus ya umurta cewa duk wanda ba ya son yin aiki kada ya ci abinci.
Bulus ya umurce ragayen su yi aiki da natsuwa, su ci abincin kan su.
Kada 'yan'uwan su yi ma'amalar da duk wanda bai yi biyayya da umurnin Bulus a wannan wasikin.
Bulus ya so Ubangiji ya ba Tessaloniyawan salama a ko wane loaƙci a kowaye hanyoyi.
Bulus ya rubuta gaisuwan da hannunsa don alaman cewa shi ne marubucin.
1 Bulus, manzon Almasihu Yesu bisa ga umarnin Allah Mai cetonmu, da Almasihu Yesu begenmu, 2 zuwa ga Timoti, dana na gaske cikin bangaskiya: Alheri, jinkai da salama daga wurin Allah da Almasihu Yesu Ubangijinmu. 3 Kamar yadda na nanata maka ka yi, da zan tafi Makidoniya cewa, ka dakata a Afisa domin ka umarci wadansu mutane kada su koyar da wata koyarwa dabam. 4 Kada su bata lokacinsu wajen sauraron tatsunniyoyi da kididdiga marar iyaka. Wannan yana haddasa gardandami, maimakon taimakawa shirin Allah, da ke ta wurin bangaskiya. 5 Manufar shari'a kuwa kauna ce daga tsabtacciyar zuciya, da tsatstsakan lamiri, da kuma sahihiyar bangaskiya. 6 Wadansu sun kauce daga tafarkin sun juya zuwa ga maganganun banza. 7 Suna so su zama malaman sha'ria, amma basu fahimci abin da suke fada ba ko abin da suka tsaya akai. 8 Amma mun sani shari'a tana da kyau idan an yi amfani da ita bisa ga ka'ida. 9 Gama mun san wannan, shari'a ba domin mai adalci take ba, amma domin marasa bin doka, mutane masu tawaye, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa Allah, da masu sabo. An bada shari'a domin masu kisan iyaye maza da iyaye mata, da masu kisan kai, 10 Domin fasikai da 'yan ludu, domin masu satar mutane su kai su bauta, domin makaryata, da masu shaidar zur, da kuma dukan abin da ke gaba da amintaccen umarni. 11 Wannan umarni bisa ga daukakkiyar bisharar Allah ne mai albarka, wadda aka bani amana. 12 Ina gode wa Almasihu Yesu Ubangijimu. wanda ya karfafa ni, gama ya karbe ni amintacce, ya sani cikin hidimarsa. 13 Dama can ni mai sabo ne, mai tsanantawa kuma dan ta'adda. Amma duk da haka aka yi mani jinkai domin na yi su cikin jahilci da rashin bangaskiya. 14 Amma alherin Ubangijinmu ya kwararo mani tare da bangaskiya, da kauna da ke cikin Almasihu Yesu. 15 Wannan bishara amintacciya ce, ta isa kowa ya karba, cewa Almasihu Yesu ya zo cikin duniya domin ceton masu zunubi, a cikinsu kuwa ni ne mafi lalacewa. 16 Saboda haka ne na sami jinkai, domin ta wurina ni na farko, a nuna hakurin Yesu Almasihu. Ya yi wannan domin in zama misali ga wadanda za su bada gaskiya zuwa rai madawwami. 17 Yanzu, ga Sarkin zamanai, marar mutuwa, boyayye, Allah makadaici girma, da daukaka su tabbata a gare shi har abada abadin. Amin. 18 Ina danka wannan umarni gareka, dana, Timoti. Ina haka ne bisa ga anabcin da aka yi a baya game da kai, domin ka shiga yaki mai kyau. 19 Ka yi wannan domin ka zama da bangaskiya da kyakkyawan lamiri. Wadansu mutane sun ki sauraron wannan suka yi barin bangaskiyarsu. 20 Kamar su Himinayus da Iskandari, wadanda na bada su ga shaidan domin su horu su koyi kin yi sabo.
A wannan littafi sai dai in an faɗa amma, kalma "mu" na nufin Bulus ne da Timoti
"Ni, Bulus manzo marubucin wannan wasiƙa." Ya yiwu akwai yadda ake gabatar da marubucin wasiƙa a harshe ku, toh ayi amfani dashi a nan. In ya zama lalle za a iya faɗa wanene ake rubutawa wasiƙan.
"daga dokan" ko "ta wurin ƙarfin ikon"
"Allah wanda ya cece mu"
A nan "begenmu" na nufin mutumin da muke da bege a kansa. AT: "Almasihu Yesu wanda a cikin shi ne muke da bege" ko "Almasihu Yesu wanda mun gaskata"
Bulus na magana game da dangantakarsa da Timoti kamar na wani Uba da ɗansa. Wannan ya nuna sahihiyar ƙauna da amincewa da Bulus ke dashi game da Timoti. Ya yiwu kuma ta hannun Bulus ne Timoti ya karɓi ceto shiya sa Bulus ya ɗauke shi a matsayin ɗansa. AT: "wanda yake kamar ɗa a wurina"
"Bari alheri, jinkai, da salama su kasance da kai," ko "Bari ka kasance da kyan zuciya, jinkai, da salama"
"Allah, wanda shine Ubanmu." A nan "Uba" muhimmin suna ne na Allah.
"Almasihu Yesu, wanda shine Ubangijimu"
Bulus na gargaɗi wa Timoti kada yayi amfani da koyarwarkarya amma yayi amfani da koyarwa mai kyau daga Allah.
"kamar yadda na roƙe ka" ko "kamar yadda na faɗa maka da karfi"
"jira ni a garin Afisa"
AT: "wani koyarwa dabam da abin da muka koyar"
AT: "kuma ina so ka umurce su kada su mai da hankali"
Wannan ya yiwu labaru game da kakaninsu ne.
Bulus yayi amfani da kalman "mara iyaka" domin ya nuna cewa kididdigan na da tsawo.
rubutacen tarihin asalin mutun daga iyaye har kakaninsa
"wannan yana sa mutane rashin amincewa cikin fushi." Mutanen suna muhawara game da labarin ƙididdiyar asali wanda ma basu san gaskiyarba.
AT: 1 "a maimakon taimaka mana fahimtar shirin Allah game da ceton mu wanda muka koyar wa ta wurin bangaskiya" 2 "maimakon taimaka mana cikin aikin Allah, wanda muke yi ta wurin bangaskiya."
An yi amfani da wannan kalman domin a dakatar da ainihin koyarwa da a ke yi. Anan Bulus ya bayyana manufar umurni da yake ba wa Timoti.
Anan wannan baya nufin Tsohon Alkawari ko dokoki goma amma umurni ne da Bulus ya bayar a 1Timoti 1:3-4.
AT: "ƙauna ce zuwa Allah" ko "a ƙaunaci mutane."
A nan "sahihiya" na nufi cewa mutum ba shi da wata muguwar manufa a ɓoye. "zuciya" kuma anan na nufin tunani da hankalin mutum. AT: "daga tunani mai kyau"
"lamiri da ya zaɓi abu mai kyau ba mumuna ba"
"bangaskiya na gaske" ko "bangaskiya ba tare da munafurci ba"
Bulus na magana game da bangaskiya cikin Almasihu kamar wata buri ne da a ke nufa. Bulus na nufin cewa waɗansu mutane basu cika manufar bangaskiyar su ba, wanda shine ƙauna, kamar yadda ya faɗa a 1:5.
A nan "juya zuwa" na nufin cewa sun daina yin abun da Allah ya umurta.
A nan "shariya" na nufin shari'ar Musa.
"ko da yake basu fahimta ba" ko "basu fahimta ba tukuna"
"abin da suka amince a kan gaskiya"
"mun fahimci cewa shariya tana da amfani"
"idan mutum yayi amfani da ita yadda ya kamata" ko "idan mutum yayi amfani da ita yadda Allah ke so"
"Gama mun fahimci wannan" ko "mun kuma san wannan"
AT: "ba domin adalin mutum bane Allah yayi shari'a"
A nan "mutum" na nufin namiji da mace. AT: "mutum na ƙwarai"
AT: "Allah yayi shari'a"
Wannan na nufin duk wanda ke jima'i da wanda basu yi aure tare ba.
maza da ke jima'i da junansu
"waɗanda suke satar mutane su kuma sayar da su ga bauta" ko "waɗanda suke ɗaukan mutane su sayar da su zuwa bauta"
"da kuma duk waɗanda suke yin wani abu dake gãba da gaskiyar koyarwar masubi"
"bishara mai ɗauke da daraga daga Allah mai albarka" ko kuma "bisharar ɗaukaka da albarkan Allah"
AT: "wadda Allah ya bani ya kuma amince mani"
ya dauke ni abin dogara
Bulus na magana game da hidimar Allah kamar wani wuri ne da ana iya sanya abu. AT: "ya sanya ni cikin hidimarsa" ko "ya naɗa ni bawansa"
"Dama na kassance mutum ne wanda ke maganar banza game da Almasihu." Bulus na magana game da halinsa kafin ya zama maibi.
"mutum wanda ke tsanantawa masubin Almasihu"
"mutum mai halin mugunta." Wannan mutum ne wanda ya saba da halin mugunta ga wasu.
"Amma domin ban gaskata da Yesu ba kuma ban san abin da nake yi ba, na sami jinkai daga wurin Yesu"
"Yesu ya nuna mani jinkai" ko "Yesu yayi mani jinkai"
"da kuma Alheri"
Bulus na magana game da alherin Allah kamar wani ruwa ne da cike a bokati har yana zuba. AT: "Allah ya nuna mani yalwar alheri"
Wannan ne sakamakon yadda Allah ya nuna Alherinsa zuwa Bulus. AT: "wannan shine sanadin bangaskiya da ƙaunar da nake wa Yesu"
Ana magana game da Yesu kamar shi wani bokati ne da ke rike da ruwa. Amma anan "cikin Almasihu" na nufin dangantaka ne da Yesu. AT: "wanda Almasihu Yesu ya sanya mani in ba wa Allah, domin ina tarayya da shi"
"Wannan maganan gaskiya ne"
"mu karɓa ba tare da shakka ba" ko "ya cancanci mu yarda da ita ƙwarai"
AT: "Allah ya nuna mani jinkai" ko "na sami jinkai daga wurin Allah"
'domin ta wurina, mafi zunubi"
An yin amfani da kalman "Yanzu" domin a canza daga asalin koyarwa ne. Anan Bulus na yabon Allah.
"madawwamin sarki" ko "shugaba na har abada"
AT: "Yanzu bari duk mutane su girmama, su kuma ɗaukaka sarkin zamanai har abada, wanda shine Allah makaɗaici, marar mutuwa, ɓoyayye"
Bulus na magana game da umurnin kamar wani abu ne da ya sa a gaban Timoti wanda ana iya gani. AT: "ina danƙa maka wannan umurnin" ko "wannan umurni ne nake ba ka"
Bulus na bayyana dangantakarsa da Timoti kamar na Uba da ɗansa. Ya yiwu ta hanun Bulus ne Timoti ya karɓi bishara shiya sa Bulus na ɗaukarsa a matsayin ɗa. AT: "wanda yake kamar ɗa na gaske"
AT: "bisa ga anabci game da kai daga sauran masubi"
Bulus na magana game da aikin da Timoti ke yi wa Ubangiji kamar yaƙi ne da soja ke yi. AT: "cigaba da matukar aiki wa Ubangiji"
"lamiri da ke zaɓan abu mai ƙyau ba mumuna ba." dubi yadda aka fasara a 1:5.
Bulus na magana game da bangaskiyar waɗanan mutane kamar wani jirgi ne da ya yi haɗari a tẽku.Yana nufi cewa sun illatar da bangaskiyarsu, wato basu gaskata cikin Yesu kuma ba.
Wannan sunayen maza ne.
Bulus na magana kamar ya danka mutanen wa Shaiɗan fuska da fuska. Ya yiwu Bulus ya ƙi amincewa da su a cikin al'umman masubi. Dashike sun bar iyalin masubi Shaiɗan na da iko akan su, kuma zai iya yi masu illa.
AT: "Allah ya koyar da su"
An zamar da Bulus manzon almasihu bisa ga umarnin Allah.
Timoti ɗa ne na gaskiya a wurin Bulus a cikin bangaskiya.
Ya kamata Timoti ya kasance a Afisa.
Ya kamata ya umarce su kada su koyar da wata koyaswa dabam.
Maunufarsa shine ya yi kauna da ga tsarkakkar zuciya, da ga lamiri mai kyau, da kuma sahihiyar bangaskiya.
Dokar domin marasa bin doka ne, ma su tawaye, mugayen mutane, da kuma ma su zunubi.
Suna aikata zunubin kisan kai, lalata na jiki, satar yara, da kuma ƙarya.
Bulus mai yin saɓo ne, mai tsananta wa masubi, kuma mai fushi.
Alherin Ubangijinmu ne ya zo ga Bulus.
Yesu Almasihu ya zo cikin duniyan nan domin ya cece ma su zunubi.
Bulus ya ce shi ne misalin rahaman Allah domin shine mafy zunubi, amma ya sami rahamar Allah a farko.
Bulus ya yarda da anabcin da aka yi a kan Timoti, game da yaƙi mai kyau da ya ke yi da bangaskiya da kuma lamiri mai kyau.
Bulus ya ba da su ga shaiɗan domin ya koya masu kada su yi saɓo.
1 Don haka da farko dai, Ina roko a yi roke-roke da addu'o'i, da yin roko domin jama, a dukka, da ba da godiya, a yi haka domin dukkan mutane, 2 domin sarakuna da dukkan masu mulki, domin mu yi zaman salama da rayuwa a natse cikin Allahntaka da daraja. 3 Wannan yana da kyau da karbuwa a gaban Allah mai cetonmu. 4 Yana so dukkan mutane su sami ceto, su kai ga sanin gaskiya. 5 Domin Allah daya ne, Matsakanci kuma daya ne, tsakanin Allah da mutum, wannan mutum Almasihu Yesu ne. 6 Ya bada kansa fansa domin kowa, domin shaida a daidaitaccen lokaci. 7 Sabo da wannan dalilin, aka sa ni kaina, na zama mai shelar bishara da manzo. Gaskiya nake fada. Ba karya nake yi ba. Ni mai koyarwa ne na al'ummai cikin gaskiya da kuma imani. 8 Saboda haka, ina so maza da ke a kowanne wuri suyi addu'a, kuma suna daga hannuwa masu tsarki a sama ba tare da fushi da gardama ba. 9 Kazalika, ina so mata su sa kayan da ya cancanta, da adon da ya dace da kamun kai. Kada su zama masu kitson gashi da zinariya da azurfa da tufafi masu tsada. 10 Ina so su sa tufafin da ya cancanci matan da ke rayuwar Allahntaka ta wurin kyawawan ayyuka. 11 Mace ta koya cikin natsuwa da saukin kai a cikin komai. 12 Ban ba da izini mace ta koyar ko ta nuna iko a kan namiji ba, amma ta zauna da natsuwa. 13 Adamu ne aka fara halitta, kafin Hauwa'u. 14 Ba Adamu ne aka yaudara ba, amma macen ce aka yaudara cikin laifi. 15 Duk da haka, zata sami ceto ta wurin haifuwar 'ya'ya, idan suka ci gaba cikin bangaskiya, da kauna da tsarki da sahihiyar zuciya.
Bulus ya ƙarfafa Timoti ya cigaba da yi wa dukkan mutane addu'a.
"mafi muhimmanci" ko "kafin wani abu dai"
AT: "Ina roƙon duk masubi su yi roƙe-roƙe, addu'o'i, cẽton wasu, da kuma godiya ga Allag"
"Na roƙa" ko "Na ce"
A nan "salama" da "natse" na nufin abu ɗaya ne. Bulus na biɗar masubi su iya rayuwa cikin kwanciyar hankali ba matsala da hukuma.
"da ke daraja Allah da kuma bangirma a wurin sauran mutane"
AT: " Allah na so ya ceci dukkan mutane, su kuma kai ga sanin gaskiyan"
Bulus na magana game da koyan gaskiyar Allah kamar wani wuri ne da a ke iya kawo mutane. AT: "cikin sani da karɓan abin da ke gaskiya"
matsakanci, mutum ne da ke taimako wajen shirya yarjejeniya cikin salama tsakanin ɓangarori biyu wanda suke da rashin amincewa tsakanin su. A nan Yesu na taimakawa masu zunubi domin su shiga dangantaka da Allah cikin salama.
"yarda ya mutum"
"a matsayin kuɗin 'yanci" ko "biyan kuɗi domin samun 'yanci"
Ana iya bayana cewa wannan shine shaidar da Allah ke so ya ceci dukkan mutane. AT: "abin shaida ne a daidai lokacin da Allah ke so ya cece dukkan mutane"
Wannan na nufin cewa, wannan ita ce lokacin da Allah ya zaɓa.
"domin wannan" ko "ta dalilin haka"
AT: "Almasihu ya maishe ni Bulus, mai bishara da kuma manzo"
"Ina koyar wa al'ummai saƙon gaskiya da imani." A nan mai yiwuwa Bulus na amfani da "gaskiya" da "imani" domin bayana ra'ayi ɗaya ne. AT: "Ina koyar da al'ummai game da tabatacciyar bangaskiya"
A nan "hannuwa masu tsarki" na nufin mutumin gaba ɗaya na da tsarki. AT: "Ina so maza masu tsarki dake kowanne wuri su ɗaga hannuwansu suna kuma addu'a"
"maza a dukka wurare" ko "maza a ko'ina." A nan kalman "maza" na nufin maza na musamman.
al'ada ne mutane su ɗaga hannuwansu lokacin addu'a
waɗannan kalmomin na nufin abu ɗaya ne. Bulus na jaddada muhimmanci sa kaya yadda ta dace ga mata ba tare da janyo hankalin maza ba.
a zamanin Bulus, matan Roma sukan yi kitso domin yanyo hankali ne. Kitso wata hanya ce da mace ke bada hankalin da bai kamata wa gashinta ta. Idan ba a san kitso ba sai a yi amfani da sanannen kalma. AT: " kada su ƙawata gyaran gashi" ko "kada su dinga shirya gashinsu domin janyo hankalin mutane"
waɗannan suna kama da duwatsu kuma suna da kyau da daraga har ma mutane kan yi amfani da su a matsayin kayan ado. Ana samun su ne a jikin wani irin ƙaramin dabba da ke rayuwa a tẽku.
"wanɗanda suke so su girmama Allah ta wurin ƙyawawan ayyukan da suke yi
"cikin kawaici"
"yi biyayya da abun da aka koyar"
"ban yarda mace"
AT: "Adamu ne na farko da Allah ya halitta" ko "Allah ya halicci Adamu ne da farko"
Ana iya rubuta wannan a fili kamar. AT: "sa'an nan Allah ya halicci Hauwa'u" ko "daga baya Allah ya halicce Hauwa'u"
AT: "kuma ba Adamu bane maciji ya yaudara"
AT: "amma macen ne ta yi rashin biyayya ga Allah a lokacin da macijin ya yaudareta."
A nan "ta" na nufin dukkan mata. Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) Allah zai tsare lafiyar mata a lokacin haifan 'ya'ya, ko 2) Allah zai ceci mata daga zunubansu ta wurin matsayinsu na masu haifan 'ya'ya.
AT: "Allah zai cece ta" ko "Allah zai ceci mata"
"idan sun kasance" ko "idan sun cigaba da zama." A nan "su" na nufin mata.
Ana iya fasarar waɗanan cikin fi'ilin magana. AT: "dogara cikin Yesu da ƙaunar mutane da kuma rayuwa cikin tsarki"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) da yanke shawara mai kyau, 2) da hali na ƙwarai 3) da kamunkai."
Idan an riga an fahimci wannan fasarar, to ana iya barin wannan siffar fasarar. AT: "sahihiyar zuciya"
Bulus yana roƙo a yi addu'a domin dukkan mutane, domin sarakuna da kuma dukka waɗanda suke mulki.
Bulus yana marmarin a yarda wa masubi su yi rayuwar zaman lafiya da kuma rayuwar shuru a cikin bin Allah da martaba.
Allah ya na marmarin dukkan mutane su sami ceto su kuma samu sani na gaskiya.
Yesu Almasihu shi ne matsakanci tsakanin Allah da mutum.
Almasihu Yesu ya ba da kansa domin fansar kowa.
Bulus malami ne na al'ummai.
Bulus ya na so maza su yi addu'a su kuma ɗaga hannayensu masu tsarki.
Bulus ya na so mata su sa tufafi da kuma kamunkai.
Bulus bai yarda mace ta yi koyarwa ba ko ta nuna yi iko a kan na miji ba.
Bulus ya na so mata su cigaba a cikin bangaskiya da kuma kauna da tsarkakewa tare da tunani mai kyau.
1 Wannan magana tabattaciya ce: Idan wani na da marmari ya zama shugaban Ikilisiya, ya na marmarin aiki mai kyau. 2 Don haka, wajibi ne shugaban Ikilisiya ya zama mara abin zargi. Ya zama mai mace daya. Wajibi ne ya zama mai kamewa, mai hankali, mai natsuwa mai karbar baki. Wajibi ne ya iya koyarwa. 3 Kada ya zama mashayin giya, da mai tankiya. A maimakon haka ya zama da natsuwa, mai salama. Ba mai son kudi ba. 4 Wajibi ne ya iya lura da gidansa da kyau, 'ya'yansa su zama masu yi masa biyayya da dukkan bangirma. 5 Gama idan mutum bai iya sarrafa gidansa ba, ta yaya zai iya lura da Ikkilisiyar Allah? 6 Bai kamata ya zama sabon tuba ba, domin kada ya kumbura da girman kai, kada ya fadi cikin irin hukunci da aka yi wa Ibilis. 7 Wajibi ne kuma ya kasance mai kyakyawar shaida a cikin wadanda ba masubi ba, domin kada ya fadi cikin kunya da kuma tarkon Ibilis. 8 Hakanan kuma Dikinoni su kasance da halin mutunci, ba masu magana biyu ba. Bai kamata su zama mashayan giya ko masu hadama ba. 9 Su zama masu rikon bayyananniyar gaskiyar bangaskiya da lamiri mai tsabta. 10 Daidai ne kuma a fara tabbatar da su, daga nan su fara hidima domin basu da abin zargi. 11 Hakanan ma mata su zama masu mutunci. Bai kamata su zama magulmanta ba, amma masu kamewa da aminci cikin komai. 12 Tilas Dikinoni su zama masu mata daya daya. Su iya kulawa da 'ya'yansu da gidajensu. 13 Gama wadanda suka yi hidima da kyau sun sami tsayawa mai kyau da gabagadi cikin bangaskiyar da ke cikin Almasihu Yesu. 14 Ina rubuta maka wadannan abubuwa, da sa zuciya zan zo wurin ka ba da jimawa ba. 15 Amma idan na yi jinkiri, ina rubuta maka ne domin ka san yadda za ka gudanar da al'amuranka a cikin gidan Allah, wato Ikklisiyar Allah rayyayiya, ginshiki da kuma mai tallafar gaskiya. 16 Babu musu an bayyana cewa ibadarmu ta gaskiya da girma take: "Ya bayyana kansa cikin jiki, Ruhu ya baratar da shi, mala'iku suka gan shi, aka yi shelarsa a cikin al'ummai, aka gaskanta shi a duniya, sa'an nan aka dauke shi sama cikin daukaka.
Bulus ya bayar da muhimman umurnai game da yadda rayuwa da halin masu kulla da ikilisiya ya kamata ya kasance.
"aiki mai daraja"
Dole shugaban Ikilisiya ya kasance mai mata ɗaya. Ba a bayana a fili ba ko wannan ya shafi wanda ya taɓa kasancewa gwauro ko wanda aurensa ya mutu, ko wanda bai taɓa aureba.
"kada ya zama mai aikata abubuwa fiye da yadda ake buƙata, mai aikata abu mai ma'ana, mai ɗa'a, ya kuma zamanto abokin baƙi"
"kada ya zama mashayin barasa ko mai son yin faɗa da gardama, maimakon haka ya kasance mai ɗa'a da salama"
"haɗamar kuɗi"
"ya shugabanci" ko "ya lura da abu"
Ma'anonni masu yiwuwa suna kamar haka 1) yaran shugaban su kasance masu biyayya da girmama mahaifinsu, ko 2) yaran shugaban su zama da bangirma ga kowa, ko 3) shugaban ya kasance mai daraja waɗanda suke iyalinsa, a sa'ad da yake shugabantar su.
"cika da girmamawa" ko "daraja mutane a kowane lokaci"
"Gama idan mutum bai iya lura ba"
Bulus ya yi amfani da tambaya ya koyar da Timoti. AT: "ba zai iya lura da Ikilisiyar Allah ba." ko "ba zai iya shugabantar Ikilisiyar Allah ba."
A nan "Ikilisiya" na nufin ƙungiyar jama'ar Allah. AT: "ƙungiyar jama'ar Allah" ko " Masubi da ke ƙarƙashin shugabancin sa"
"kada ya kasance sabon tuba" ko "dole ya kasance mai bi da ya girma"
Bulus na maganar kasancewa cikin hukunci domin laifi kamar wani rami ne da mutum zai iya faɗi a ciki. AT: "Allah ya hukunta shi kamar yadda ya hukunta Ibilis"
"waɗanda ba 'yan Ikilisiya ba." Bulus na magana game da Ikilisiya kamar wani wuri ne da ake shiga, sai kuma marasabi kamar suna wajen Ikilisiyar. AT: "waɗanda ba masubi ba"
Bulus na maganar wulakãnci da yadda Ibilis ke sa mutum ya yi zunubi kamar wani rami ne na tarko da mutun ke faɗi ciki. A nan "faɗi ciki" na nufin yanayin da mutum ya kasance. AT: "domin kada Ibilis ya sa shi zunubi"
"Dikinoni, kamar Shugabanen Ikilisiya"
Bulus na magana game da waɗanan mutanen kamar suna magana biyu ko suna faɗan abubuwa biyu a lokaci guda. Yana nufin cewa mutumin na faɗin abu amma yana nufin wani abu dabam. AT: " kasance da rayuwa mai kyau da kuma tabbatar da maganarsa"
"Dole su cigaba da gaskata gaskiyar saƙon Allah da ke a bayyane gare mu da kuma masubi." wannan na nufin gaskiyar da ke nan a da amma Allah ya nuna masu a wannan lokaci. Bulus na maganar gaskiyar koyarwa game da Allah kamar wani abu ne da mutum ke iya ajiye wa a wurinshi.
AT: "gaskiyar da Allah ya bayyanar"
Bulus na maganar sanin mutum cewa bai aikata wani laifi ba kamar wannan sanin ko lamirin na da tsabta. AT: bangaskiyar sanin cewa sun yi iyakar ƙoƙarinsu su aikata abun da ke daidai"
AT: "Dole ne sauran masubi su amince da su tukuna" ko "su nuna tabbacin kansu tukuna"
Wannan na nufin sauran masubi ma su kimanta waɗanda suke so su zama dikinoni, su kuma yanke shawara ko sun yi daidai su yi hidima a cikin Ikilisiya.
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "mata" na nufin matan dikinoni, ko 2) "mata" na nufin dikinoni da ke mata.
"hali mai kyau" ko "cancanci girmamawa"
"Bai kamata suna muguwar magana game da wasu ba"
"ba tare da aikata fiye da yadda ya kamata ba." dubi yadda aka fasara wannan cikin 1Timoti 3:2
Dole na miji ya kasance da mata ɗaya. Ba a bayana a fili ba ko wannan ya shafi wanda ya taɓa kasancewa gwauro ko wanda aurensa ya mutu, ko wanda bai taɓa aureba. Dubi yadda aka fasara wannan cikin 1 Timoti 3:2
"tafiyad da yaran da kyau da wasu da ke zama a gidajen su"
"ga dikinoni waɗanda" ko "ga waɗannan shugabanen Ikilisiya"
"sama wa kansu" ko "ribato wa kansu"
Ana iya nuna ainihin ma'anar wannan a fili. AT: "suna mai kyau a cikin sauran masubi"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) za su amince da Yesu sosai, ko 2) za su yi magana da gabagaɗi wa wasu mutuna game da bangaskiya a cikin Yesu.
"ammaidan ban iya zuwa wurin da sauri ba" ko "Amma idan wani abu ya riƙe ni ban samu zuwa da sauri ba"
Bulus na maganar kungiyar masubi kamar su iyali ɗaya ne. Ma'anoni masu yiwuwa sana kamar haka 1) Bulus na magana game da halin Timoti ne kadai a cikin Ikilisiya. AT: " domin ka san yadda za ka gudanar da rayuwarka a matsayin ɗan iyalin Allah" ko 2) Bulus na magana da masubi dukka. AT: "domin ku duka ku san yadda zaku gudanar da kanku a matsayinku na 'yan iyalin Allah"
Wannan maganar na ba da bayani game da "gidan Allah" ba wai yana nuna banbanci tsakanin gidan Allah wanda itace Ikilisiya da kuma wanda ba Ikilisiya ba. Ana iya sa wannan cikin sabuwar jumla. AT: "gidan Allah. Waɗanda suke na iyalin Allah suna jama'ar Allah rayayye"
Bulus na maganar yadda masubi sun zama shaidu na gaskiya game da Almasihu kamar sun zama ginshiḷƙi da tushen da ke tallafawa wani gini. Ana iya sa wannan cikin sabuwar jumla. AT: "wato Ikilisiyar Allah rayayye. Kuma tawurin kiyaye gaskiyar koyarwar Allah jama'ar Ikilisiya suna tallafawa gaskiya kamar yadda ginshiƙi da tushe ke tallafawa gini"
Wannan maganar anan na iya ba da ra'ayin cewa Allah ne wanda yake ba da rai ga kowa, kamar yadda yake a cikin UDB.
"ba wanda zai iya ƙaryatawa"
AT: "da cewa gaskiyar da Allah ya bayyana da girma take"
Mai yiwuwa wannan wata waƙa ce da Bulus ya ruwaito. Idan akwai yadda harshenku zai nuna cewa wannan waƙa ne, ku na iya amfani da shi. In kuma babu, to a fasara shi a yadda ya ke.
A nan kalman "ya" ba'a fili ya ke ba. Yana iya nufin "Allah" ne ko "Almasihu." Zai fi kyau a fasara wannan yadda yake "Ya." Idan yazama lallai a ba da takamammen fasara, a sa shi haka "Almasihu wanda shine Allah" ko "Almasihu."
A nan Bulus ya yi amfani da "jiki" da nufin mutum. AT: "a matsayin mutum na gaske"
AT: Ruhun Mai Tsarki ya tabbatar cewa shine wanda ya ce da kansa"
AT: "Mutane ƙasashe dayawa suka faɗa wa wasu game da shi"
AT: "Mutane a wurare dayawa cikin duniya suka gaskata da shi"
AT: "Allah Uban ya ɗauke shi zuwa sama cikin ɗaukaka"
wannan na nufin cewa ya samu iko daga Allah Uba kuma ya cancanci daraja.
Aikin mai kula aiki ne mai kyau.
Ya zama tilas wa mai kula ya iya koyaswa.
Ya zama tilas wa mai kula ya zama mara sabuwa da giya kuma kada ya ƙaunaci kuɗi.
Ya zama tilas wa 'ya'yan mai kula su yi masa biyayya su kuma ba shi daraja.
Ya zama da muhimmanci domin idan baya iya saraffa iyalinsa da kyau ba, mai yi yuwa ba zai kula da ikklisiya ba.
Hatsarin shine zai zama mai girman kai ya kuma faɗi cikin hukunci.
Ya zama tilas wa mai kula ya zama da suna mai kyau ga waɗanda ba su a cikin ikklisiya.
Kafin su yi hidima, ya kamata dattijan su sami amincewa.
Ana girmama Mata ma su ibada, ba masu ɓata suna ba, matsakaita, da kuma masu aminci a cikin dukan abubuwa.
Gidan Allah shi ne ikklisiya.
An yi shellar Yesu a tsakanin al'umma, aka bada gaskiya gareshi a cikin duniya, an kuma ɗauke shi sama a cikin daukaka.
1 To Ruhu ya fada a fili cewa, a zamanin karshe wadansu mutane za su kauce daga bangaskiya, su mai da hankalin su ga ruhohi masu rudi, da koyarwar aljannu, 2 cikin karya da munafunci. Lamirinsu zai yi kanta. 3 Za su haramta aure da karbar abincin da Allah ya halitta, domin su raba da godiya a cikin wadanda suka bada gaskiya suka kuma san gaskiyar. 4 Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau. Domin duk abin da muka karba da godiya, bai kamata mu ki shi ba. 5 Gama an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da addu'a. 6 Idan ka tuna wa 'yan'uwa wadannan abubuwa za ka zama bawan kirki na Almasihu. Domin ana gina ka ne ta wurin maganar bangaskiya da kuma kyakkyawar koyarwa wadda ka bi. 7 Amma ka guji labaran almara wadanda tsofaffin mata ke so. Maimakon haka sai ka hori kanka cikin bin Allah. 8 Domin horon jiki ya na da amfani kadan. Amma horon kai cikin bin Allah yana da amfani ga dukkan abubuwa. Gama a cikinsa akwai alkawari domin wannan rayuwar da kuma rayuwa mai zuwa. 9 Maganan nan amintacciyace ta isa a karbe ta dungum. 10 Dalilin da ya sa kenan mu ke aiki tukuru. Domin muna sa bege ga Allah mai rai, mai ceton dukkan mutane, musamman masu ba da gaskiya. 11 Ka yi shela ka kuma koyar da wadannan abubuwa. 12 Kada ka yarda kowa ya rena kuruciyarka. Maimakon haka, ka zama abin koyi ga dukkan masubi: a furci, hali, kauna, aminci da kuma tsarki. 13 Har sai na zo, ka himmatu da yin karatu, da wa'azi, da kuma koyarwa. 14 Kada ka yi sakaci da baiwar da ka ke da ita wadda aka baka ta wurin anabci sa'ad da dattawa suka dibiya maka hannayensu. 15 Ka kula da wadannan abubuwa. Ka himmatu a cikinsu. Domin ci gabanka ya zama sananne a idanun kowa. 16 Ka kula da kanka da kuma koyawarka. Ci gaba a cikinsu. Domin ta yin haka ne za ka ceci kanka da masu sauraronka.
Bulus na gaya wa Timoti abun da Ruhu ya faɗa cewa zai faru, ya kuma ƙarfafa shi cikin abun da zai koyar.
An yi amfani da wannan kalmar a nan domin a canja daga ainahin koyarwan. Bulus ya fara gabatar da sabuwar sashin koyarwan.
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) wannan na nufin zamanin da ke zuwa bayan Bulus ya mutu, ko 2) wannan zamani ne a karshen rayuwar Bulus.
Bulus na maganar yadda mutune ke daina gaskatawa cikin Almasihu kamar yadda mutum ke barin wani wuri ko wani abu. AT: "daina gaskatawa cikin Yesu"
"bayar da hankali" ko "domin suna bayar da hankalinsu"
"ruhohi masu yaudarar mutane da abubuwan da aljanu ke koyarda"
Ana iya faɗin wannan a wata sabuwar jumla. AT: "aljanu. Waɗannan mutane za su kasance munafukai da masu faɗin ƙarya"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) Bulus na maganar mutanen da basu iya ganewa ko sun aikata mumunar abu kamar tunaninsu na da illa da za a iya kwatantashi da fatar da wani ya ƙona da karfe mai zafi, ko 2) Bulus na magana game da waɗanan mutanen kamar Ibilis ya yi musu tabo da karfe mai zafi domin ya nuna cewa su nasa ne.
"waɗanan mutanen za su"
ya nuna cewa za su hana masubi aure. AT: "hana masubi aure"
ya nuna cewa za su hana wasu irin abinci. AT: "za su bukaci masubi su ƙauce wa wasu irin abinci" ko "ba za su yarda mutane su ci wasu irin abinci ba"
AT: "komai da Allah ya halitta yana da kyau"
AT: "kada mu ƙi karɓar duk abun da muka ba Allah godiya" ko "duk abun da muka ci da godiya karɓaɓɓe ne"
A nan "maganar Allah" da "addu'a" na nufin abu daya ne. Addu'ar na amincewa da gaskiyar da Allah ya bayyana. AT: " an keɓe domin aikin Allah ta wurin addu'a da amincewa da kalmarsa"
AT: "mun tsarkake shi" ko "mun keɓe shi"
A nan "kalma" na nufin saƙon Allah ko abun da ya bayyanar.
Bulus na maganar umurninsa kamar wani abu ne da ake iya gani da iddo ana miƙa wa masubi. A nan, a "miƙa wa" na nufin umurni ko a tunatar. AT: "idan kana taimakawa masubi ka tuna da waɗanan abubuwan"
wannan na nufin koyarwar da aka fara a cikin 1 Timoti 3:16.
wannan na nufin masubi maza ko mata.
Bulus na magana game da maganar Allah da koyarwarta kamar wani abu ne da ake gani da ido na ciyad da Timoti domin ya yi karfi. AT: "kalmar gaskiya da kyakyawar koyarwa da ka bi har ya sa ka amincewa da Almasihu da karfi sosai"
"maganar da ke sa mutane su gaskata"
"mummunar labarai da tatsuniyar tsofaffin mata." kalmar "tatsuniya" na nufin abu ɗaya ne da "labari" a cikin 1 Timoti 1:4, don haka a fasara shi haka a nan.
Wannan maganar na iya nufin "wauta" ko "abu mara ma'ana." Ba wai Bulus na da niyyar zagin tsofaffin mata bane. Amma shi Bulus da wanda yake rubuto musu sun fahimci cewa maza na mutuwa kafin mata, don haka an fi samun mata da tunaninsu bashi da zurfi domin shekaru fiye da maza.
horad da kanka ga daraja Allah" ko "horad da kanka ta wurin aikata abun da zai gamshi Allah"
"motsa jiki"
"na da amfani a wannan rayuwar"
"ta isa ka gaskata sosai" ko "ta isa ka amince sosai"
"Wannan ne dalilin"
kalmar "fama" da "aiki tukuru" na nufin abu daya ne. Bulus ya yi amfani da su tare domin ya nuna tsananin hidimar su ga Allah.
Mai yiwuwa a nan "Allah mai rai" na nufin "Allah da ya sa kowane abu ya rayu."
Ana iya ƙara bayyana wannan maganar a fili. AT: "shi mai ceto ne musamman ga wanda suka ba da gaskiya"
"ba da umurni da koyarwar waɗanan abubuwa" ko " ba da umurni da kuma koyar da waɗanan abubuwan kamar yadda na faɗa"
"kada ka yarda kowa ya kalle ka da rashin muhimmanci domin kai saurayi ne"
Ana iya sa kalmomin nan "karatu", "Wa'azi", da "koyarwa" ta wani sifar jumla. Ana iya saka wannan kuwa a cikin fasara. AT: "cigaba da karata wa mutane littafin, ka yi musu wa'azi, da kuma koyar da su"
Bulus na magana game da Timoti kamar shi wani abu ne da za a iya sa baiwar Allah a ciki. AT: "kada ka sake baiwar ka ta Ruhu Mai Tsarki"
AT: "ka tabbata ka yi amfani"
AT: "wadda ka samo sa'ad da shugabanen Ikilisiya suka yi shelar maganar Allah"
Wannan biki ne da dattawar Ikilisiya suka ɗore hannuwarsu bisa Timoti suka kuma yi addu'a Allah ya bashi ikon aikata abun da ya umurce shi ya yi.
Bulus na managa da Timoti game da baiwar Allah kamar wani abu ne da ake iya zama a ciki. AT: "Aikata dukka waɗannan abu ka kuma yi rayuwa bisa ka'idarsu"
Bulus na maganar cigaban Timoti a bautar Allah kamar wani abu ne da mutane ke iya kallo. AT: " domin mutane su gani cewa kana bautar Allah da kyau da kyau"
"ka gudanar da kanka cikin hankali, ka kuma mayar da hankalinka ga koyarwar" ko "lura da halinka, ka kuma sa hankali ga koyarwar"
"ka cigaba da aikata waɗannan abubuwa"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) Timoti zai ceci kansa da kuma waɗanda suke sauraronsa daga hukuncin Allah, ko 2) Timoti zai ceci kansa da kuma masu sauraronsa daga rinjayar mallaman ƙarya.
Wasu mutane za su bar bangaskiyar su kuma bada hankalin zuwa ga ruhohi masu yaudara.
Zasu haramta yin aure da kuma haramta cin wasu abinci.
Duk abubuwan da muke ci na tsarkake da kuma karɓuwa ta wurin kalmar Allah da kuma addu'a.
Bulus ya gaya wa Timoti ya horad da kansa a cikin bin Allah.
Horo a cikin bin Allah ya fi riba domin yana riƙe da alkawarin wannan rayuwar da rayuwa mai zuwa.
Bulus ya gargaɗi Timoti ya yi shella ya kuma koyar da waɗannan abubuwan zuwa wasu.
Ya kamata Timoti ya zama abun misali ta wurin kalma, gudanarwa, kauna, bangaskiya, da kuma tsarki.
An ba Timoti baiwar ta winur annabci tare da sa miƙa hannun dattawa.
Timoti zai cece kanshi da kuma waɗanda suke sauraronsa.
1 Kada ka tsauta wa dattijo. Sai dai ka gargade shi kamar mahaifi. Ka gargadi samari kamar 'yan'uwa. 2 Gargadi dattawa mata kamar iyaye mata, 'yan mata kamar 'yan'uwa mata cikin dukkan tsarki. 3 Ka girmama gwamraye, gwamraye na gaske. 4 Amma gwamruwar da take da 'ya'ya ko jikoki, bari su fara nuna bangirma cikin danginsu. Bari su sakawa iya-yensu, domin Allah yana jin dadin haka. 5 Amma gwamruwa ta gaske da ke ita kadai, ta kafa begenta ga Allah. Kullum tana tsananta yin roke-roke da addu'o'i dare da rana. 6 Amma, mace mai son zaman annashuwa ta riga ta mutu, ko da shike tana raye. 7 Kuma ka yi wa'azin wadannan al'amura donsu zama marasa abin zargi. 8 Amma idan mutum bai iya biyan bukatun 'yan'uwansa ba, musamman iyalin gidansa, ya musunci bangaskiya, kuma gara marar bi da shi. 9 Bari a lisafta mace gwamruwa idan ba ta kasa shekara sittin ba, matar miji daya. 10 A san ta da kyawawan ayyuka, ko ta kula da 'ya'yanta, ko tana mai karbar baki, ko mai wanke kafafun masubi, ko mai taimakon wadanda ake tsanantawa, mai naciya ga kowanne kyakkyawan aiki. 11 Amma game da gwamraye masu kuruciya, kada a sa su cikin lissafi. Domin idan suka fada cikin sha'awoyin jiki da ke gaba da Almasihu, sukan so su yi aure. 12 Ta wannan hanya ce sun tara wa kansu tsarguwa saboda sun tada alkawarinsu na fari. 13 Sun saba da halin ragwanci, suna yawo gida gida. Ba zama raggwaye kawai su ka yi ba. Amma sun zama magulmata, masu shishshigi, masu karambani. Suna fadin abin da bai dace ba. 14 Saboda haka ina so gwamraye masu kuruciya su yi aure, su haifi 'ya'ya, su kula da gida, domin kada a ba magabci zarafin zargin mu ga aikata mugunta. 15 Domin wadansu sun rigaya sun kauce zuwa ga bin shaidan. 16 Idan wata mace mai bada gaskiya tana da gwamraye, bari ta taimakesu, don kada a nawaita wa Ikilisiya, domin Ikilisiya ta iya taimakon gwamraye na gaske. 17 Dattawa wadanda suke mulki da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman wadanda suke aiki da kalma da kuma koyarwa. 18 Gama nassi ya ce, "Kada a sa takunkumi a bakin takarkari lokacin da yake sussukar hatsi," kuma "Ma'aikaci ya cancanci a biya shi hakinsa." 19 Kada ka karbi zargi game da dattijo sai shaidu sun kai biyu ko uku. 20 Ka tsauta wa masu zunubi gaban kowa domin sauran su ji tsoro. 21 Na umarce ka a gaban Allah, da Almasihu Yesu, da zababbun mala'iku ka kiyaye ka'idodin nan ban da hassada kuma kada ka yi komai da nuna bambanci. 22 Kada ka yi garajen dibiya wa kowa hannuwa. Kada ka yi tarayya cikin zunuban wani. Ka tsare kanka da tsabta. 23 Kada ka ci gaba da shan ruwa. Amma, maimakon haka ka sha ruwan inabi kadan saboda cikinka da yawan rashin lafiyarka. 24 Zunuban wadansu mutane a bayyane suke, sun yi gaba da su cikin hukunci. Amma wadansu zunubansu na bin baya. 25 Haka kuma, wadansu kyawawan ayyukansu a bayyane suke, amma wadan sun ma ba su boyuwa.
Bulus ya cigaba da gaya Timoti yadda zai bi da maza, mata, gwauruwaa, da kuma mata masu ƙuruciya a cikin Ikilisiya.
Bulus na ba da waɗannan umurnai ga mutum ɗaya ne, wato Timoti.
"kada ka faɗa wa dattijo baƙin magana"
"A maimako, ka ƙarfafa shi"
Bulus ya yi amfani da waɗannan kwatanci ya gaya wa Timoti cewa ya bi da 'yan'uwa masubi da sahihiyar ƙauna da girmamawa.
Za a iya bayyana wannan a fili, cewa. AT: "gargadi mata masu ƙurciya" ko "karfafa mata masu ƙuruciya"
"tunani da halin tsarki" ko "cikin hanyar tsarki"
"tanadi da girmama gwauraye"
"gwauraye da ba wanda zai yi masu tanadi"
"da farko su koyi" ko "bari su sa fifiko a koyon"
"wa danginsu" ko "ga waɗanda suke zama a gidansu"
"Bari su yi wa iyayensu alherin da suka yi musu"
"Amma wadda ta ke gwauruwar gaske ba ta da iyali"
"ta cigaba da miƙa roƙo da adduo'i"
dukka waɗannan kalmomi suna nufin abu ɗaya ne. Bulus ya yi amfani da su tare domin domin ya jaddad yadda waɗannan gwauraye ke addu'a.
An yi amfani da waɗannan kalmomi "dare" da "rana" da nufin "kowane lokaci." AT: "kowane lokaci"
Bulus na magana game da waɗanda ba sa ƙoƙari su gamshi Allah kamar su mattatu ne. AT: "kamar wadda ya mutu, ba ta jin Allah"
Wannan na nufi ba matacce ba.
"Umurci waɗannan abubuwa"
"domin kada wani ya same su da laifi." Mai yiwuwa "su" na nufi 1) "waɗannan gwaurayen da iyalinsu" 2) "masubi." Zai fi kyau a yi amfani da shi kalmar "su."
"baya taimakon daginsa da bukatu, tun ma ba 'yan iyali da suka kasance a gidansa ba"
"baya aikata bisa ka'idar bangaskiyarmu ba"
"ya fi wanda ba su ba da gaskiya ga Yesu ba muni." Bulus na nufi cewa wannan mutum ya fi marasa bi mugunta domin marasa bi ma suna lura da danginsu. Saboda haka, lalle ne mai bi ya kula da danginsa.
Ya yiwu akwai lisafin gwauraye, ko rubutacce ko ba a rubuce ba. 'Yan Ikilisiya ne ke biya wa waɗannan matan bukatun su na mafaka, tufafi, da abinci. Waɗannan mata kuwa ana sa rai za su duƙufa cikin bautar al'umman masubi.
Kamar yadda Bulus ya bayyana a 5:11-16, gwauraye wanɗanda ba su kai shekaru sittin ba na iya sa ke aure. Saboda haka, al'umman masubi su kula da gwauraye wanda su ka shige shekaru sittin.
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) tana da aminci ga mijin ta, ko 2) ba ta saki mijin ta zuwa auren wani ba.
AT: "Mutane sun shaida da kyawawan ayyukanta"
"ta marabci baƙi cikin iyalin ta"
Wanke kafafun wadda suka yi datti ko da taɓo hanyar biya wa wasu bukata ne, kuma sa su su ji daɗi. Wannan na iya nafin cewa tana da halin tawali'u. AT: "ta saba aikin taimakawa 'yan'uwa masubi"
Wasu juyi sun fasara kalmar cewa "masubi" ko "tsarkaka mutanen Allah." Abu mai muhimminci kawai shine ana nufi 'yan'uwa masubi.
AT: "ta taimaki waɗanda suke wahala"
"ta miƙa kai ga aikata kowane irin kyawawan ayyuka"
"Amma kada ka sa gwauraye masu ƙuruciya a lisafin." Lisafin na gwauraye ne wadda suka kai shekaru sittin zuwa sama da al'umma masubi zasu taimakawa.
"Domin a sa'ad da sun fi so su cika sha'awar su na son aure, to sai su kasa cika alkawarin bautar Almasihu na gwauraye"
"ba su kiyaye wa'adinsu na da ba" ko "ba su yi abun da suka yi alkawarin yi a baya ba"
Wa'adin gwauraye shi ne hidimar da za su yi wa al'aumma masubi muddin ransu, in al'ummar za su tanada musu bukatunsu.
"koyi halin zama ba abun yi"
Duk waɗannan na yiwuwa ana maganar abu ɗaya ne. Waɗannan mutane su daina shishigi, suna shiga harkokin wasu da bai shafe su ba, har ma suna faɗa wa wasu abin da ma ba taimako zai yi ba.
maganar da ba zai taimaki masu sauraro ba
"kula da kowa da kowa da ke cikin gidansu"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) Wannan na nufin Shaiɗan, ko 2) Wannan na nufin marasabi wanda suna gãba da masubi.
A nan "mu" na nufi dukan al'ummar masubi, har da Timoti.
Bulus na maganar amincewa da Almasihu kamar wani hanya ne da ake takawa a bi. Wannan na nufin matar da ta daina biyayya da Yesu, ta kuma fara biyayya da Shaiɗan. AT: "barin hanyar Almasihu zuwa bin Shaiɗan" ko "zaɓi yi wa Shaiɗan biyayya a maimakon yi wa Almasihu"
"kowace mace mai bi" ko "kowace mace wanda ta gaskanta da Almasihu"
"na da gwauruwa a cikin danginta"
Bulus na maganar yadda al'ummar masubi ke taimakon mutane fiye da yadda yakamata su yi kamar suna ɗaukan wani abu ne mai nauyi a bayansu. AT: "domin kada Ikilisiya ta yi ta hidima fiye da iyawanta" ko "domin kada al'ummar masubi su taimaki gwauraye wanda iyalinsu na iya tanada musu"
AT: "duk masubi su dubi dattawan da suke aiki mai kyau da daraja"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "girmamawa da biya" ko 2) "girmama fiye da yadda wasu ke samu"
Bulus na magana game da wa'azin kalmar kamar wani abu ne da mutum yake iya aiki da shi. AT: "waɗanda suke wa'azi da koyar da maganar Allah"
Wannan na nufin abun da wani ya rubuta a cikin nassi. AT: Domin mun karanta a cikin nassi cewa"
Bulus na kawo maganar nan da nufin cewa yakamata al'ummar masubi su biya shugabanen Ikilisiya domin aikinsu.
Wannan wani abu ne da ake sa wa a hanci da bakin dabba don a hana ta cin abinci sa'ad da take aiki
takarkari na "sussukar hatsi" a sa'ad da yake tafiya ko jan wani abu mai nauyi akan hatsin da aka yanke don a raba hatsin da kara. Ana barin takarkarin ya ci daga hatsin a lokacin da yake aiki.
"isa"
Bulus na maganar ƙara kamar wani abu ne da ake iya ɗauka a mika wa mutane su karɓa. AT: "Kada ka yarda da ƙarar da wani ya kawo"
"a kalla biyu" ko "biyu ko fiye"
Wannan na nufin duk wanda yake aikata rashin biyayya ko abu da baya fararta wa Allah rai, ko mutane sun san da abun ko basu sani ba.
"inda kowa da kowa na iya gani"
"domin sauran su ji tsoron aikata zunubi"
Wannan na nufi mala'ikun da Allah da Yesu suka zaɓa domin su yi hidima ta musamman.
Kalmar "son kai" da "gatanci" na nufin abu ɗaya ne. Bulus na jaddada cewa dole Timoti ya yi hukunci cikin adalci da sassauci ga kowa. AT: "kiyaye waɗannan dokoki ba tare da nuna gatanci ko son kai ba"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) dokokin da Bulus ya gaya wa Timoti, ko 2) dokokin da Bulus na shirin faɗa wa Timoti.
ɗora hannu biki ne da shugabanen Ikilisiya ko shugaban ikisiliya ke ɗora wa mutane hanu a kuma yi addu'a ga Allah ya ba su ikon yi wa ikilisiya hidimar da zai gamshi Allah. Yakamata Timoti ya jira sai mutumin ya nuna halin kirki na tsawon lokaci kafin ya keɓe wannan mutumin domin hidima wa jama'ar masubi.
Bulus na maganar zunubin wani kamar wani abu ne da a ke iya rabawa da wasu. AT: "kada ka yi taraya a zunubin wani" ko "kada ka sa hannu a sa'ad da wani na aikata zunubi"
Wannan na nuna cewa ba ruwa kaɗai Bulus ke ce wa Timoti ya sha ba. Yana ce wa Timoti yayi amfani da ruwan inabi a matsayin magani. Ruwar wurin na sa cuta.
AT: "Zunuban wasu mutane a sarari suke"
"zunuban waɗanan mutanen zasu bi su har hukunci." Bulus na maganar zunubai kamar suna motsi. Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) Zunuban su a fili suke wa kowa, ba sai wani ya ba da mumunar shaida akan su ba, 2) Zunubansu a fili suke, kuma yanzu Allah zai hukuntasu.
"Amma wasu zunuban daga baya mutane suke gani." Bulus na maganar zunubai kamar suna motsi. Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) Timoti da al'ummar masubi ba za su san da wasu zunubai ba sai nan gaba, ko 2) Allah ba za ya hukunta wasu zunubai ba sai a ranar shariya.
"a sarari wasu kyawawan ayyuka suke"
Ana duban ayyukan a matsayin "kyawawa" domin sun dace da halin Allah, da nufinsa.
Bulus na magana game da zunubi kamar wani abu ne da ake iya ɓoye wa. AT: "Amma nan gaba mutane zasu san da kyawawan ayyukan da ba a fili suke ba"
Bulus ya gaya wa Timoti ya bi da shi kamar Uba ne a wurinsa.
'Ya'ya da jikoki ya kamata su săka wa iyayensu su kuma kula da ita.
Ya yi musun bangaskiya kuma ya fi mara bi muni.
Ya kamata a san gwauruwa domin ayukka masu kyau.
Akwai hatsarin cewa za ta so ta sake yin wani aure a nan gaba, ta soke alkawarinta na da.
Bulus yana so mata masu ƙurciya su yi aure , su haifi 'ya'ya , su kuma sarrafa gida.
Dattawa waɗanda suka yi shugabanci da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu.
Ya zama tilas akwai shaidu kusan biyu ko uku kafin a karɓi zargi a kan wani dattijo.
Bulus ya umarce Timoti ya yi hankali ya ajiye waɗannan dokoki ba tare da nuna bambanci ba.
Ga wasu mutane, ba a sanin zunuban su sai lokacin shari'a.
1 Bari duk wadanda ke bayi a karkashin karkiya su ga iyayengijinsu sun cancanci dukan daraja. Su yi haka domin kada a sabawa sunan Allah da koyarwarsa. 2 Bayin da suke da iyayengiji da ke masu ba da gaskiya kada su rena su saboda su 'yan'uwa ne. A maimakon haka, su yi masu hidima da kwazo. Gama iyayengijin da suke cin ribar aikinsu masu bi ne, kaunattatu kuma. Ka koyar ka kuma bayyana wadannan abubuwa. 3 Idan ya kasance wani na koyar da wani abu dabam bai kuma yarda da amintaciyar koyarwa ba, wato maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu. Alal misali ba su amince da koyarwa da ke kai ga Allahntaka ba. 4 Wannan mutum mai girman kai ne, kuma bai san komai ba. A maimakon haka, yana da matukar jayayya da gardama game da kalmomi. Wadannan kalmomi na kawo kishi, da husuma, da zage-zage, da miyagun zace-zace, da 5 yawan rashin jituwa tsakanin mutane masu rubabbun hankula. Sun bijire wa gaskiya. Suna tunani cewa ibada hanya ce ta yin arziki." Ka zame daga wadannan abubuwa. 6 Yanzu bin Allah tare da dangana babbar riba ce. 7 Gama ba mu kawo komai a duniya ba, ba zamu iya fita cikinta da komai ba. 8 A maimakon haka, mu dangana da abinci da kuma sutura. 9 To wadanda ke son zama mawadata su kan fada cikin jaraba, cikin tarko. Suna fadawa cikin abubuwan wauta da sha'awoyi masu illa da kowanne abu da ke sa mutane su dulmaya cikin lallacewa da hallaka. 10 Gama son kudi shine tushen kowacce irin mugunta. Wadansu mutane garin neman kudi sun kauce daga bangaskiya, sun kuma jawowa kansu bakin ciki mai yawa. 11 Amma kai, mutumin Allah, ka guji wadannan abubuwa, ka bi adalci, ibada, aminci, kauna, jimiri, da tawali'u. 12 Ka yi fama, fama mai kyau na bangaskiya. Ka kama rai madawami da aka kira ka gare shi. A kan wannan ne ka ba da shaida a gaban shaidu masu yawa game da abin da ke da kyau. 13 Ina ba ka wannan umarni a gaban Allah wanda ke rayar da dukan abubuwa, da gaban Almasihu Yesu, wanda ya fadi abin da ke gaskiya ga Bilatus Babunti. 14 Ka bi doka daidai, babu abin zargi har bayanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 15 Allah zai nuna bayyanuwarsa a daidai lokaci- Allah, mai albarka, Makadaicin iko, Sarkin da ke sarauta, Ubangiji mai mulki. 16 Shine kadai marar mutuwa, mai zama cikin hasken da ba ya kusantuwa. Ba wanda ke ganinsa, ko ya iya hango shi. Girma ya tabbata a gare shi da kuma madawwamin iko. Amin. 17 Ka gaya wa masu dukiya a cikin wannan duniya kada su daga kai, kada su sa bege ga arziki mara dawwama. Maimamakon haka, su sa begensu ga Allah wanda ke ba mu wadatar gaske domin jin dadin mu. 18 Gaya masu su yi nagarta su arzurta a ayyuka nagari, su zama masu bayarwa hannu sake. 19 Ta haka za su ajiye wa kansu harsashi mai kyau kan abin da ke zuwa domin su amshi rayuwa ta kwarai. 20 Timoti, ka kare abin da aka ba ka. Ka nisanci maganar wauta da gardamomin da ke sabawa juna wanda ake kira ilimi a karyace. 21 Wadansu mutane suna shelar wadannan abubuwa, don haka sun kauce wa bangaskiyar. Bari alheri ya kasance tare da kai.
Bulus yana ba da umurnai musamman ga bayi da iyayengida, sannan ya cigaba da ba da umurnai game da zaman rayuwar da zai gamshi Allah.
Bulus na magana game da bayi kamar su takarkari ne da ke ɗauke da kaya. AT: "Bari duk wanda suke aiki a matsayin bayi"
Wannan na nuna cewa Bulus na magana game da masubi. AT: "Bari wanda suke masubi"
AT: "marasabi su girmama sunan Allah da koyarwar nan"
A nan "suna" na nufi yadda Allah yake ko ɗabi'unsa. AT: "ɗabi'un Allah" ko "Allah"
"bangaskiya" ko "bishara"
A nan " 'ya'uwa" na nufi " 'yan'uwa masubi."
AT: "Domin Iyayengidan da bayin ke taimakonsu da aikinsu"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) da kuma bayin da suke ƙaunar su" ko 2) "wanda Allah ke ƙauna"
A nan "Yana" na nufi duk wanda yake koyar da abun da ba daidai ba. Domin bayyana wannan a fili kana iya fasara "yana" kamar "su" a UDB.
"bai san komai game da gaskiyar Allah ba"
Bulus na magana game da mutane da ke jin cewa tilas ne su yi jayayya mara amfani kamar basu da lafiya. waɗannan mutane suna da matukar marmarin jayayya, kuma ba sa son amincewa. AT: "abun da ya ke so kadai shine jayayya" ko "yana neman jayayya"
"gardama da jayayya game da maganganu, da kuma gardama da jayayya masu jawo ƙishi"
"game da ma'anar kalmomi"
jayayya, faɗa
mutane suna faɗin munanan abubuwa game da juna da ba gaskiya
"mutane suna ji kamar wasu suna so su yi musu mugunta"
"muguwar tunani"
A nan kalmar "su" na nufi duk wanda yake koyar da abun da bai daidaita da koyarwa Yesu ba. kalmar "ƙaurace wa gaskiya" na nufin yin watsi ko mance wa da abu. AT: "Sun yi watsi da gaskiyar" ko "Sun mance da gaskiyar"
Wannan na nuna canji daga koyarwar. Bulus ya fara bambamta irin arzikin da mugayen mutane su ke nema ta bin Allah (1Timoti 6:5) da asalin riban da ake samu ta wurin bin Allah. AT: "haƙiƙa"
Kalmar nan "bin Allah" da kuma "wadar zuci" suna bayana yanayin mutum ne. AT: "Abu ne mai riba da yawa idan mutum na bin Allah, kuma yana dangana da abun da yake da shi"
"na da matukar amfani" ko "zai yi ma na abubuwa masu kyau"
"bamu kawo kome duniya ba lokacin da a ka haife mu"
"ba kuwa za mu iya fita da kome ba a sa'ad da mun mutum"
"sai mu"
Bulus na magana game da waɗanda suka yarda jarabar kuɗi ya sa su cikin zunubi, kamar su dabboni ne da suka faɗi a cikin tarkon rami da mafarauci ke yi. AT: "zama masu arziki na da jarabobi sosai da za su fuskanta kuma su yi tsayayya da ita. Za su zama kamar dabbar da ke a tarko
An cigaba da amfani da tarko domin bayani. Wannan na nufin cewa wauta da sha'awoyinsu zasu ka da su. AT: "Kuma kamar yadda dabba ke făɗowa a tarkon mafarauci haka ma zasu făɗa cikin wauta da sha'awoyi masu illatarwa da yawa"
Bulus na magana game da waɗanda suka yarda zunubi ya hallakar da su kamar su wani jirgin ruwa ne da ke nutsewa a ruwa. AT: "zuwa kowane irin muguwar lalata da ke hallakar da mutane kamar su jirgin ruwa ne da ke nutsewa a ruwa"
Bulus na maganar sanadin mugunta kamar wani tushen abun da aka shuka. AT: "Wannan na faruwa haka domin son kuɗi shi ke zama sanadin kowane irin mugunta"
"wanda ke sha'awar kuɗi"
Bulus na maganar muguwar sha'awa kamar su mugayen jagora ne da ke jagorar mutane ta mummunar hanya da gangan. AT: "suka bar sha'awoyinsu suka bauɗar da su daga gaskiya" ko "daina amincewa da gaskiyar"
Bulus na maganar baƙin ciki kamar wani takobi ne da mutum ke amfani da shi ya soki kansa. AT: "suka sa wa kansu baƙin ciki matuƙa"
A nan "kai" na nufi Timoti ne.
"bawan Allah" ko "mutum da ke na Allah"
Bulus na magana game da waɗannan jarabobi da zunubai kamar su abubuwa ne da mutum ke iya yin gudu daga wurin su. AT: "kauce wa waɗannan abubuwan gaba ɗaya"
Mai yiwuwa "waɗannan abubuwa" na nufi 1) "son kuɗi" ko 2) wani koyarwa dabam, girman kai, jayayya, da son kuɗi.
"bi da gudu" ko "bi"
A nan Bulus na maganar yadda mutum na cigaba a cikin bangaskiya kamar ɗan wasan guje-guje ne da ke fama domin nasara, ko mayaƙi ne da yake kan yaƙi. AT: "Yi iyakar ƙoƙarin biyayya da koyarwar Almasihu da yawan kuzari kamar ɗan wasan guje-guje"
An cigaba da bayani. Bulus na maganar yadda mutum yake samun rai madawwami kamar shi wani ɗan wasa ne ko mayaƙi da ke karbar ladar nasara"
AT: "wanda Allah ya ƙira ka sobada shi"
'Ka ba da kyakkyawar shaida" ko "ka shaida gaskiyar"
Bulus na magana a kan wuri domin ya ba da bayani a kan mutanen da Timoti ke magana. AT: "ga shaidu da yawa"
"Wannan ne abun da nake umurtar ka"
"a gaban Allah, wanda yake sa dukan abubuwa su rayu." Wannan na nuna cewa Bulus na biɗar Allah ya zama shaidar shi. AT: "da Allah wanda ya ke sa dukka abubuwa su rayu, ya shaida ni"
"a gaban Almasihu Yesu wanda ke shaida ... Bilatus." Yana nuna cewa Bulus na bidar Yesu ya zama shaidar shi. AT: "da Almasihu Yesu wanda ke shaida ... Bilatus, a matsayin shaida na"
Kalmar "aibi" na a nufin laifi. Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) Yesu ba zai sami Timoti da wani aibi ba ko ya zargi da wani laifi ba, ko 2) mutane ba za su sami Timoti da laifi ba ko su zarge shi domin aikata abun da ba daidai ba.
"har sai Ubangiji Yesu Almasihu ya sake zuwa"
Ya na nufin cewa Allah zai nuna bayyanuwar Yesu. AT: "Allah zai nuna bayyanuwar Yesu"
"a lokaci da yakamata"
"wanda ya isa yabo, mai mulkin duniya"
"Shi kaɗai yake da ikon rayuwa har abada"
"zama a babban haske da ba mai iya zuwa kusa"
A nan "dukiya" na bayana sunan abu ne. AT: gaya wa wanda suke da dukiya"
"a cikin abubuwa da suka mallaka da za su iya rasawa." Ana nufin kayayyakin da ake iya gani.
"dukka abubuwan da za su sa mun jin daɗi sosai." Wannan na nufi har ma da kayakin da ake iya gani, amma mai yiwuwa ana nufi kayayyakin duniya da mutane suke mallaka domin neman kasancewa cikin ƙauna, farin ciki, da salama.
Bulus na maganar albarkun ruhaniya kamar dukiyar duniya ne. AT: "yi hidima da taimakawa wasu a hanyoyi da yawa"
A nan Bulus na maganar albarkun Allah da yake bayarwa a sama kamar dukiya ne da mutum ke tara wa domin amfani nan gaba. kuma ana maganar tabbacin yadda ba za a rasa waɗannan albarkun ba kamar harsashin gini. AT: "zai kasance kamar suna tara wa kansu abubuwa masu yawa da Allah zai ba su"
Wannan na tunashewa da bayani wasanni da aka yi a 1 Timoti 6:12, wanda ladar abu ne da mai nasara ke karɓa a hannuwan sa. A nan "ladar" shi ne "rayuwa ta ƙwarai."
AT: "ka yi shelar saƙon gaskiya da aminci, wanda Yesu ya danƙa maka"
kada ka saurari maganganun banza"
AT: "game da abun da wasu mutane ke ƙaryar cewa da shi ilimi"
Bulus na maganar bangaskiya cikin Almasihu kamar wani abu ne da ake ƙoƙarin ci ma buri. AT: "basu fahimci ko gaskata da asalin bangaskiyar ba"
"Bari alherin Allah ya tabbata a gare ku duka." "Ku" na nufi dukan al'ummar masubi.
Bulus ya ce bayi su ga iyayengijinsu kamar waɗanda suka cancanci daraja.
Mutumin da ya ƙi kalmomi nagari da kuma koyaswar ibada nagari shi mai girman kai ne kuma bai san komai ba.
Bulus yace bin Allah da wadar zuciya babban riba ne.
Mu zama masu godiya domin ba mu zo duniyan nan da kome ba, kuma ba zamu iya tafiya da kome ba.
Waɗanda suke marmarin arziki suna faɗawa a cikin jaraba da kuma tarko.
Son kuɗi shine tushen dukan mugunta.
Wasu da suka so kuɗi a baya sun ɓata daga bangaskiya.
Bulus ya ce wa Timoti ya zama tilas ya yi faɗa mai kyau na bangaskiya.
Mai albarka duka ya na zama a hasken da ya ke boye wurin da ba wani mutum da zai iya ganin shi.
Ya kamat masu arziki su sa begen su a cikin Allah domin shine mai bada dukan arziki na gaskiya.
Wadanda suke da arziki a cikin ayuka masu kyau suna ajiye wa kansu tushe mai kyau, kuma sun riƙe rayuwa na gaskiye.
Bulus ya gaya wa Timoti ya kare abubuwan da aka ba shi.
1 Bulus, manzon Almasihu Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai da ke cikin Almasihu Yesu, 2 zuwa ga Timoti, kaunataccen da: Alheri, jinkai, da salama daga Allah Uba da Almasihu Yesu Ubangijinmu. 3 Na gode wa Allah, wanda na ke bautawa tun daga kakannina, da lamiri mai tsabta, sa'adda na ke tuna wa da kai cikin addu'o'ina koyaushe (dare da rana). 4 Sa'adda na tuna da hawayenka, na yi marmarin ganinka, saboda in cika da farin ciki. 5 An tunashshe ni game da sahihiyar bangaskiyarka, wadda ta samo asali daga kakarka Loyis da mahaifiyarka Afiniki. Na kuma tabbata ta na zaune a cikinka. 6 Wannan shine dalilin da ni ke tunashshe ka cewa ka sake rura baiwar Allah da ke cikinka wadda ka samu sa'adda na dibiya maka hannuwana. 7 Domin Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, amma na iko da kauna da kamun kai. 8 Saboda haka kada ka ji kunyar shaida ga me da Ubangijinmu, ko ni, Bulus, daurarrensa. Maimakon haka, ka zama a shirye ka sha wahala domin bishara bisa ga ikon Allah. 9 Allah ne ya cecemu kuma ya kira mu da kira mai tsarki. Ya yi wannan, ba ta wurin ayyukanmu ba, amma ta wurin shirinsa da alherinsa. Ya ba mu wadannan abubuwan a cikin Almasihu Yesu kafin farkon zamanai. 10 Amma yanzu an bayyana ceton Allah ta wurin bayyanuwar mai cetonmu Almasihu Yesu. Almasihu ne ya kawo karshen mutuwa ya kuma kawo rai marar karshe da ya bayyana ta wurin bishara. 11 Domin wannan, an zabe ni mai wa'azi, manzo da mallami zuwa ga al'ummai. 12 Domin wannan dalili na ke shan wahalar wadannan abubuwa. Amma ban ji kunya ba, domin na san shi, wanda na gaskanta. Na sakankance zai iya adana abinda na mika masa har zuwa ranan nan. 13 Ka adana misalin amintattun sakwanni da ka ji daga gare ni, ta wurin bangaskiya da kauna da ke cikin Almasihu Yesu. 14 Abu mai kyau da Allah ya danka maka, ka tsare shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki, da ke zaune a cikinmu. 15 Ka dai sani, dukkan wadanda su ke zama a Asiya sun juya mani baya. A cikin kungiyar akwai Fijalas da Harmajanas. 16 Bari Ubangiji ya yi wa iyalin Onisifaras jinkai, domin ya na yawan yi mani hidima, kuma ba ya jin kunyar sarkata. 17 Maimakon haka, sa'adda ya ke a Roma, ya neme ni da kokarin gaske, ya kuma same ni. 18 Bari Ubangiji ya sa, ya sami jinkai daga gare shi a wannan rana. Dukkan hanyoyin da ya taimake ni a kasar Afisa, kun sani sarai.
A wannan littafin, kalmar nan "mu" na nufin Bulus ne da Timoti, sai inda aka ce ba haka ba,
Mai yiwuwa harshen ku na da yadda ake gabatar da marubucin wasiƙa; yi amfani da shi. Haka kuma bayan gabatar da marubucin yana iya yiwuwa a ga bukatar gabatar da wanda ake rubuta wa wasiƙan.
"saboda nufin Allah" ko "domin Allah ya so haka." Bulus ya zama manzo domin haka Allah ya so ba domin zaɓen mutum ba.
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "domin manufar." Wannan na nufin cewa Allah ya zaɓi Bulus domin ya faɗa wa mutane game da alkawarin Allah na samun rai cikin Yesu, ko 2) "bisa dalilin." Wannan na nufin cewa kamar yadda Allah yayi alkawarin rai ta wurin Yesu, haka nan ya mayar da Bulus ya zama manzo.
Bulus na magana game da "rai" kamar wani abu ne da ake samu a cikin Yesu. Wannan na bayyana rai da mutane ke samu ta wurin zama na Almasihu Yesu"
"ɗa da nake so" ko "ɗan da nake ƙauna. Anan "ɗa" kalma ce na ƙauna mai muma girma da amincewa. Mai yiwuwa ta hannun Bulus ne Timoti ya karɓi Almasihu, shiyasa Bulus ya dauke shi a matsayin ɗansa. AT: "wanda ya ke a matsayin ƙaunataccen ɗa na"
"Bari alheri, jinkai, da salama sukasance a gare" ko "Bari ku kasance da alheri, jinkai, da salama a cikin ku daga"
"Allah, wanda shine Ubanmu, da." Wannan muhimmin suna ne na Allah.
"Almasihu Yesu, wanda shine Ubangijimu"
"wanda na bautawa kamar yadda kakannina suka yi"
Bulus na magana game da lamirisa kamar wani abu ne da ake iya wanke wa. Wannan na nufin cewa lamirin mutum da ke so ya aikata abun da ke daidai ba zai kasheshi ba. AT: "sannin cewa na yi iyakan ƙoƙarina in yi abin da ke daidai" ̇
"duk lokacin da nake tune da kai" ko "yayin da a kowane lokaci ina tune da kai"
A nan an yi amfani da "dare da rana" ana nufin " ko da yaushe." AT: "ko da yaushe" ko "kullum"
"Ina son ganin ka sosai"
Bulus na magana game da kanshi kamar shi bokati ne da wani ke iya cika wa. AT: "in cika da murna" ko "in iya samun cikakkiyar farin ciki"
A nan "hawaye" na nufin kuka. AT: "Ina tune da yadda ka yi kuka domina"
AT: "Na tuna da" ko "Na yi tunani game"
"bangaskiyar ka na gaske" ko "bangaskiyarka na gari"
Bulus na magana game da bangaskiyarsu kamar wani abu ne da ke a raye kuma na zaune cikinsu. Bulus na nufin suna da bangaskiya ɗaya. AT: "bangaskiya. Loyis kakarka da Afiniki mahaifiyar ka suna da sahihiyar bangaskiya tun farko, haka kuma na tabata cewa kaima kana da sahihiyar bangaskiya"
Waɗanan sunayen mata ne.
Bulus na karfafa Timoti yayi rayuwa cikin iko, ƙauna, horaswa da kuma ba na kunya ba, domin Bulus na shan wahala a cikin kurkuku sabili da bangaskiyarsa a cikin Almasihu.
"domin wannan dalilin" ko "domin sahihiyar bangaskiyarka a cikin Yesu"
Bulus na magana cewa yakamata Timoti ya fara amfani da baiwarsa kamar yana so ya sake kunna wuta. AT: "ya fara amfani da baiwarsa"
"baiwar Allah da ka samu lokacin da na dibiya maka hannuwana." Wannan na nufin bukin da aka yi inda Bulus ya sanya hannuwa wa Timoti da kuma addu'a ga Allah domin ya bashi ikon aikata abin da ya umurce shi ya yi.
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "ruhu" na nufin "Ruhu mai Tsarki." AT: "Ruhun Allah Mai Tsarki ba ya sa mu kasancewa da tsoro. Ya kan sa mu samu iko da ƙauna da kuma horaswa" 2) "ruhu" na nufin yanayin ɗabi'u. AT: "Allah baya sa mu kasancewa da tsoro amma mu samu iko da ƙauna da kuma horaswa"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) ikon mu iya kama kanmu, 2) ikon gyara wasu mutane wanda suke aikata laifi.
"na shaidawa" ko "na faɗa wa wasu"
"ɗaurarre saboda shi" ko "ɗaurarre domin ina shaida game da Ubangiji"
Bulus na magana game da wahala kamar wani abu ne da ake iya raba wa a tsakanin mutane. AT: "shan wahala tare da ni domin bishara"
"bishara, yanda Allah ya ba ka ƙarfi"
"da kira da ya kebe mu mun zama mutanensa" ko "kasance tsarkakan mutanensa"
"Ya cece mu ya kuma kira mu"
"ba domin mun yi wani abu da ya cancance shi ba"
"amma domin ya shirya ya nuna mana alherinsa"
"ta dalilin dangantakarmu da Almasihu Yesu"
"kafin farkon duniya" ko "kafin zamanai"
Bulus na magana game da ceto kamar wani abu ne wanda za a iya nuna wa mutane. AT: " Allah ya nuna yadda zai cecemu ta wurin aiko da mai cetonmu Almasihu Yesu"
Bulus na magana game da mutuwa kamar wani abu ne da ke zaman kanta ba mutuwa da mutane kan yi ba. AT: "wanda ya halakar da mutuwa" ko " wanda ya sa mutane ba za su zama mattatu na har abada ba"
Bulus na magana game da rai madawami kamar wani abu ne da a ka kawo daga duhu zuwa haske domin mutane su iya gani. AT: "koyar game da rayuwa mara ƙarewa ta wurin shelar bishara"
AT: "Allah ya zaɓe ni in zama mai bishara"
"Domin ni manzo ne"
Bulus na nufin kasancewa a kurkuku.
"Na kawar da shakka"
Bulus na amfani da wannan hoto da ke nuna mutum da aka ba ajiyan wani abu da ya kamata ya kare har lokacin da zai mayar. Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) Bulus na dogara da Yesu ya taimakeshi ya kasance da aminci, ko 2)Bulus na sa rai cewa Yesu zai tabbatar mutane sun cigaba da shelar sakon bishara .
Wannan na nufin ranar da Allah zai hukunta dukan mutane.
"cigaba da koyar da kyawawan koyarwa da na koyar da kai" ko "Yi amfani da yadda na saba koyar da kai domin abun da ya kamata ka koyar"
"kamar yadda ka amince da Yesu Almasihu ka kuma ƙaunaceshi"
Wannan na nufin aikin shelar bishara yadda ya kamata.
yakamata Timoti ya yi takatsantsan domin mutane zasu yi hamayya da aikinsa, da kokarin tsayar da shi, da kuma karkatar da maganar sa.
"tare da ikon Ruhu Mai Tsarki"
Wannan na nufin sun daina taimakawa Bulus. Suka ƙyale Bulus domin hukumomin sun jefar da shi cikin kurkuku. AT:"tsayad da taimakamun"
Wannan sunayen mazaje ne.
"ga iyali"
A nan "sarƙa" kalma ce da ke nufin kasancewa a kurkuku. Shi Onisifaras ba ya kunyar cewa Bulus na ɗaure a kurkuku amma ya kan ziyarce shi akai-akai. AT: "ba ya kunyar cewa ina kurkuku"
"Bari Onisifaras ya sami jinkai daga Ubangiji" ko "Bari Ubangiji ya nuna masa jinkai"
Bulus na magana game da jinkai kamar wani abu da ake iya samu.
Wannan na nufin ranar da Allah zai shar'anta dukan mutane.
Bulus ya zama manzon Almasihu ta wurin yardan Allah
Timoti ɗan bulus ne a ruhu.
Bulus ya na marmarin ya ga Timoti.
Kakarsa da mahaifiyarsa duka suna da sahihiyar bangaskiya.
Allah ya bawa Timoti ruhun iko da kauna da kuma horo.
Bulus ya gaya wa Timoti kada ya ji kunyan shaida game da Ubangiji.
Bulus ya gaya wa Timoti a maimakon haka ya zama mai shan wahala domin bishara.
An bamu Shirin Allah da kuma alherinsa kafin farawar lokaci.
An bayyana shirin Allah game da ceto ta hanyar bayyanuwar mai cetonmu Almasihu Yesu.
Yesu ya hallaka mutuwa, ya kuma Kawo rai da ba ya ƙarewa ta hanyar bishara.
Bulus ya na gabagadi cewa Allah na iya riƙe abubuwan da ya danƙa wa Allah har sai ranan nan.
Ya kamata Timoti ya tsare ta wurin ruhu mai tsarki abu mai kyau da Allah ya danƙa masa.
Dukka waɗanda suke Asiya sun juya wa Bulus baya.
Bulus ya na rokon Ubangiji ya kyauta rahama zuwa ga iyalin Onisifaras domin Onisifaras ya taimaki Bulus a cikin hanyoyi da yawa.
1 Domin wannan kai, dana, ka karfafa cikin alherin da ke cikin Almasihu Yesu. 2 Abubuwan da ka ji daga gare ni a bainar jama'a masu yawa, ka danka su ga mutane masu aminci da za su iya koya wa wadansu kuma. 3 Ka daure shan tsanani tare da ni, kamar amintaccen sojan Almasihu Yesu. 4 Ba bu sojan da zai yi bauta yayin da ya nannade kansa da al'amuran wannan rayuwar, domin ya gamshi shugabansa. 5 Hakanan, idan wani yana gasa a matsayin dan wasa, ba zai sami rawani ba tukuna har sai in ya karasa tseren bisa ga ka'idodin gasar. 6 Wajibi ne manomi mai kwazon aiki ya fara karbar amfanin gonarsa. 7 Ka yi tunani game da abin da na ke gaya maka, gama Ubangiji zai ba ka ganewa a cikin komai. 8 Ka tuna da Yesu Almasihu, daga zuriyar Dauda, wanda a ka tayar daga matattu. Bisa ga wa'azin bisharata, 9 wanda na ke shan wahala har ya kai ga dauri kamar mai laifi. Amma maganar Allah ba a daure ta ba. 10 Saboda haka na jure wa dukkan abubuwa domin wadanda aka zaba, saboda su ma su sami ceton da ke cikin Almasihu Yesu, da daukaka madawwamiya. 11 Wannan magana tabbatacciya ce: "Idan mun mutu tare da shi, za mu kuma rayu tare da shi. 12 Idan mun jure, zamu kuma yi mulki tare da shi. Idan mun yi musun sa, shi ma zai yi musun mu. 13 Idan mun zama marasa aminci, shi mai aminci ne koyaushe, domin shi ba zai yiwu ya musunta kansa ba." 14 Ka yi ta tuna masu da wadannan abubuwan. Ka yi masu kashedi a gaban Allah kada su yi ta dauki ba dadi game da kalmomi. Saboda wannan bai da wani amfani. Domin wannan zai halakar da ma su sauraro. 15 Ka yi iyakacin kokarika domin ka mika kanka ma'aikacin Allah wanda aka tabbatar, wanda babu dalilin kunya a gareshi. Wanda ya ke koyar da kalmar gaskiya daidai. 16 Ka guje wa masu maganar sabo, wanda ya kan kara kaiwa ga rashin bin Allah. 17 Maganarsu za ta yadu kamar ciwon daji. Daga cikinsu akwai Himinayus da Filitus. 18 Wadannan mutanen sun kauce wa gaskiya. Sun fadi cewa an rigaya an yi tashin matattu. Suka birkitar da bangaskiyar wadansu. 19 Duk da haka, ginshikin Allah ya tabbata. Ya na da wannan hatimi: "Ubangiji ya san wadanda ke nasa," Kuma "Duk mai kira bisa ga sunan Ubangiji dole ya rabu da rashin adalci." 20 A gida mai wadata, ba kayayyaki na zinariya da azurfa ba ne kawai. Haka kuma akwai kayayyaki na itace da yunbu. Wadansu domin aikin mai daraja, wadansu kuma ga aiki mara daraja. 21 Idan wani ya tsarkake kansa daga rashin daraja, shi kayan aiki ne mai daraja. An kebe shi, abin aiki domin mai gidan, kuma a shirye domin kowanne aiki mai kyau. 22 Ka guje wa sha'awoyi na kuruciya, ka nemi adalci, bangaskiya, kauna da salama da wadanda suke kira ga sunan Ubangiji daga zuciya mai tsabta. 23 Amma ka ki tambayoyi na wauta da jahilci. Ka sani sukan haifar da gardandami. 24 Tilas bawan Ubangiji ya guje wa jayayya. A maimakon haka dole ya zama mai tawali'u ga kowa, mai iya koyarwa, kuma mai hakuri. 25 Dole ne ya koyarwa mutane da su ke jayayya da shi a cikin tawali'u. Watakila Allah ya ba su ikon tuba domin sanin gaskiyar. 26 Suna iya sake dawowa cikin hankalinsu kuma su bar tarkon Ibilis, bayan da ya cafke su domin nufinsa.
Bulus na kallon rayuwan bi na Timoti kamar rayuwar soja, manomi, da kuma ɗan wasan guje-guje da tsalle-tsalle ne.
A nan kalmar "ɗa" na nuna matuƙar ƙauna da amincewa. Ya yiwu kuma ta hannun Bulus ne Timoti ya fara bin Almasihu, shi ya sa Bulus na kallon shi a matsayin ɗansa. AT: "wanda ya ke kamar ɗa na"
Bulus na magana game da ƙarfafawa da dagewa da alherin Allah kan sa masubi su samu. AT: "Bari Allah ya yi amfani da alherin da ya ba ka ta wurin dangantakar ka da Almasihu Yesu ya ba ka ƙarfi"
"da shaidu masu yawa a wurin domin su yarda cewa abin da na faɗa gaskiyane"
Bulus ya yi magana game da umurnin da ya ba Timoti kamar wasu abubuwa ne da Timoti zai iya ba wasu da ya yarda da su akan cewa zasu riƙe yanda ya kamata. AT: "danƙa masu" ko "koyar da su"
Ma'anoni masu yiwuwa 1) "jimre shan wuya kamar yadda nake" ko 2) "tarayya cikin shan wahalata"
Bulus na kamanta wahala saboda Almasihu Yesu da wahalar da amintaccen soja ke jimrewa.
babu sojan da zai yi bauta yayin da ya ke sa hannusa a ayyukan rayuwa ta kowace rana" ko "A lokacin da sojoji ke bauta, basu damuwa da abubuwan da mutane suke yi." kada bayin Almasihu su yarda al'amuran rayuwa na yau da kullum su hana su yin aikin Almasihu.
Bulus na magana game da janye hankali kamar wani raga ne da ke kokorin kada mutane yayin da suke tafiya.
"mai jagoransa" ko "wanda ke ba shi umurni"
Bulus na magana a fakaice game da bayin Almasihu kamar su 'yan wasa ne.
AT: "za a ba shi rawani a matsayin mai nasara amma sai dai in ya yi tseren bisa ka'ida"
"ba zai sami kyautar nasara ba."A zamanin Bulus akan yi wa 'yan wasa da suka yi nasara rawani da wasu irin ganyayyaki"
"yin gasa bisa ka'idodin" ko "biyayya da ka'idodin"
Wannan karin magana na uku kenan da Bulus ke yi wa Timoti. Yakamata mai karatu ya fahimci cewa wajibi ne mabiyan Almasihu su yi aiki da ƙwazo.
Bulus na ba Timoti hoton magana, amma bai bayyana masa manufar maganar ba. Yana sa ran cewa Timoti zai fahimci abin da yake faɗa game da bayin Almasihu.
"game da kowani abu"
Wannan karin magana ce da ke nufin Yesu daga zuriyar Dauda ne. AT: "wanda ke ɗan zuriyar Dauda"
a "tada daga" karin magana ce da ke nufin a sa wanda ya mutu ya kasance da rai kuma. AT: "wanda Allah ya sa ya rayu kuma" ko "wanda Allah ya tada daga matattu"
Bulus na magana game da saƙon bishara kamar na shi ne musamman. Yana nufin cewa wannan shi ne saƙon bishara da yake shela. AT: "bisa ga saƙon bisharar da na ke wa'azi"
A nan "ɗauri da sarƙa" na nufin kasance a kurkuku. AT: "har ya kai ga ɗauri da sarƙa kamar wani mai laifi a kurkuku"
A nan "ɗauri" na magana game da abin da ke faruwa da ɗan kurkuku, kuma wannan ƙarin magana ce da ke nufin cewa ba wanda zai iya tsayar da saƙon Allah. Ana iya fasarar wannan cikin sifar aiki, AT: "ba wanda zai iya sa maganar Allah a kurkuku" ko "ba wanda zai iya hana maganar Allah"
AT: "na mutanen da Allah ya zaɓa"
Bulus na magana game da ceto kamar wani abu ne da ake iya karɓa fuska da fuska. AT: "za a samun ceto daga Almasihu Yesu"
"za su kuma kasance da shi har abada cikin ɗaukakar wurin zaman sa"
"Wannan maganar abin amincewa ce"
Wannan mai yiwuwa kalmar waƙa ce Bulus ya ɗauko. Idan harshenku na da yadda za a sa wannan kamar waƙa to ana iya yin haka. In ba haka ba, za ku iya fasarar yadda ya ke.
Bulus ya yi amfani da wannan maganar da nufin cewa mutane na tarayya da mutuwar Almasihu yayin da sun amince da shi, suna musun kansu, suna kuma yi masa biyayya.
"ko da mun kasa a gaban Allah" ko "ko da ba mu yi abin da mun gaskata Allah na so mu yi ba"
"yana rayuwa bisa ga halinsa ko da yaushe" ko "ba zai aikata abin da ba asalin halinsa ba"
Kalmar "su" na iya nufin "malamai" ko "mutanen ikilisiyar"
Bulus na magana game da yadda Allah ya san shi kamar ya kasance tare da Allah fuska da fuska. Wannan na nuna cewa Allah zai zama mashaidin Timoti. AT: a gaban Allah" ko "da Allah a matsayin mashaidinka"
Ma'anoni masu yiwuwa 1) " ban da gardama akan abubuwan wauta da mutane suke faɗi" ko 2) ban da jayayya game da ma'anar kalmomi"
"Wannan ba ta ba wa kowa riba"
"miƙa kanka ga Allah a matsayin tabbatancen mutum wanda ya cancanta kuma ba dalili ya kunyata"
Bulus na magana da Timoti game da yadda yakamata ya bayyana maganar Allah kamar shi wani gwanin ma'aikaci ne. AT: "kamar ma'aikaci" ko "kamar mai aiki"
Ma'anoni masu yiwuwa 1)"bayyana saƙon daidai game da gaskiya" ko 2) "bayyana gaskiyar saƙon yadda yakamata."
Bulus na magana game irin wannan magana kamar wani abu da za'a iya kaishi zuwa wani sabon wuri, kuma yayi magana game da rashin bin Allah kamar shine wannan sabon wurin. AT: "wanda ya ke sa mutane su ƙara kasance da rashin bin Allah"
ciwon daji na yaɗuwa a jikin mutun da wuri har ya halakar da shi. Wannan ƙarin magana ce da ke nufin cewa maganganun waɗannan mutane zasu cigaba da yaɗuwa daga mutum zuwa mutum har ya kawo lahani ga bangaskiyar waɗanda suka ji. AT: "
Wannan sunayen maza ne.
A nan "ƙauce wa gaskiya" ƙarin magana ne da ke nufin daina gaskatawa ko koyar da abun da ke gaskiya. AT: "wanda suka fara faɗin abubuwan da ba gaskiya ba"
"Allah ya riga ya tashi masubi da suka mutu zuwa ga rai madawwami"
"sabili da su ne waɗansu mutane suka daina ba dagaskiya"
Mai yiwuwa ana nufin 1) "gaskiyar Allah na kamar ƙaƙƙarfan harsashin gini ne" ko 2) "Allah ya kafa mutanen sa kamar ƙaƙƙarfan harsashin gini" ko 3) Amincin Allah na kamar ƙaƙƙarfan harsashin gini." Bulus na bayana wannan kamar wata harsashin gini ne da aka sa a ƙasa.
"wanda ke kira bisa sunan Ubangiji." A nan "sunan Ubangiji" na nufin Ubangiji da kansa. AT: "wanda ke kira ga Ubangiji" ko "wanda ya ce ya gaskata da Almasihu"
Bulus na magana game da rashin adalci kamar wani wuri ne da mutum ke iya bari. AT: "daina kasancewa mai mugunta" ko "daina aikata abun da ba daidai ba"
A nan "kayayyaki" na nufin tasa, faranti, da tukwane, wanda mutane ke sa abinci ko ruwa a ciki. Idan ba kalma daya da ake iya kiran dukan wadanan abubuwan a harshen ku, ku yi amfani da "tasa" ko "tukwane." Bulus na amfani da wannan a matsayin karin magana ne da ke bayyana irin mutane daban-daban.
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "lokaci na musamman ... na kullum" ko 2)irin ayuka da mutuna ke yi a cikin jama'a... irin ayuka da mutane ke yi ba a cikin jama'a ba."
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) " raba kansa da mutanen banza" ko 2) "ya tsarkake kansa." Bulus na magana game da wannan yanayi kamar yadda mutum ke wanke kansa.
Bulus na magana game da wannan mutum kamar shi wani kayan aiki ne mai daraja. AT: "yana kamar kayan aiki mai amfani a lokaci na musamman" ko "yana kamar kayan aiki mai amfani don aikin da mutanen kirki ke yi a gaban jama'a"
AT: "Maigidan ya keɓe shi, kuma yana shirye domin maigidan yayi amfani da shi domin kowani aiki mai kyau"
ba'a keɓe shi ta wurin canja masa wuri ba, amma domin yin wani aiki na musamman. Wasu fasara sun yi amfani da kalmar "tsarkake," amma ayar na bayyana keɓewa.
Bulus na magana game da sha'awoyin kuruciya kamar wani mugun mutum ne ko dabba da Timoti zai guje wa. AT: "kauce wa sha'awoyin kuruciya" ko "ka ƙi aikata abubuwa marasa kyau da matasa ke son aikatawa"
A nan "nemi" na nufin kishiyar "gujewa." Bulus na magana game da adalci kamar wani abu ne da Timoti zai iya gudu zuwa gare shi, domin zai yi masa kyau. AT: " Yi ƙoƙari ka samu adalci" ko "biɗi adalci"
Ma'anoni masi yiwuwa suna kamar haka1) Bulus na so Timoti ya haɗu da sauran masubi cikin neman adalci, bangaskiya, ƙauna da salama, ko 2) Bulus na so Timoti ya kasance cikin salama da sauran masubi, ba tare da jayayya ba.
A nan "kira ga Ubangiji" karin magana ne da ke nufin amincewa da yi wa Ubangiji sujada. AT: "waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada"
A nan "tsabta" na nufin abu mara datti ko abu sahili. "Zuciya" kuma a nan na nufin "tunani" ko "jin tausayi." AT: "sahihiyar hankali" ko " ba tare da munafunci ba"
"ƙi amsa tambayoyin wauta da jahilci." Bulus na nufin cewa wanda suke irin wannan tambayoyin wawaye ne da jahilai. AT: daina amsa tambayoyin da wawayen mutane waɗanda ba su son su san gaskiyar ke tambaya"
Bulus na magana game da tambayoyin jahilci kamar matan da suke haifan yara. AT: "sukan kawo gardandami"
"mai tawali'u" ko "mai hankali"
"koyar da waɗanda" ko "daidaita waɗanda"
Bulus na magana game da tuba kamar wani abu ne da Allah ke ba wa mutane a hannu. AT: " watakila Allah ya ba su damar tuba"
"domin su san gaskiyar"
Bulus na magana game da yadda masu zunubi za su samu tunani mai kyau game da Allah kamar mutane da sun bugu su na dawowa hankalinsa. AT: "Watakila za su yi tunani da kyau kuma"
Bulus na magama game da yadda ibilis ke iya shawo kan masubi zuwa zunubi kamar tarko ne. AT: "daina aikata abin da ibilis ke so"
Ana magana game da shawo kan masubi zuwa aikata zunubi kamar ibilis ya kama su ne kamar bayi. AT: "bayan ya yaudare su zuwa ga yin biyyaya da nufinsa"
Timoti ɗa ne na ruhu a wurin Bulus.
Timoti ya kamata ya danƙa sakon ga mutane masu bangaskiya waɗanda za su iya koya wa wasu kuma.
Soja mai kyau ba ya ɗaure kansa a cikin harkokin wannan rayuwa.
Bulus ya na wahala ta hanyar sarƙokin da aka ɗaura shi kamar mai laifi.
Ba a ɗaure Kalmar Allah ba da sarƙoki.
Bulus yana jimre wa waɗannan abubuwa duka domin mutanen da Allah ya zaɓa, saboda su samu ceton da ya ke cikin Almasihu Yesu.
Waɗanda suka jimre za su yi mulki da Almasihu.
Waɗanda suke musun Almasihu, Almasihu zai yi musunsu.
Ya kamata Timoti ya gargadi mutane ka da su yi jayayya game da kalmomi, wanda ba ta da riban kome.
Suna koyarwa cewa an rigaya an yi tashin matattu?
Ya kamata masu bi su tsabtace kansu daga amfani mara daraja, su tsarkake kansu domin kowane aiki mai kyau.
Bulus zai gudu da ga sha'awõyi na ƙuruciya.
Ya zama tilas wa bawan Allah ya zama mai tawali'u, ya iya koyaswa, mai hakuri, a cikin tawali'u ya koyas da waɗanda suke hamayya da shi.
Shaiɗan ya kama a tarko ya kuma kama marasa bi domin aikin sa.
1 Amma ka san da wannan: a cikin kwanakin karshe za a yi lokuta masu matsananciyar wahala. 2 Gama mutane za su zama masu son kansu, masu son kudi, masu Kumburi, da girman kai, masu sabo, marasa biyayya ga iyaye, marasa godiya, da kuma marasa tsarki. 3 Za su kasance marasa dabi'a, wadanda basu son jituwa da kowa, masu tsegumi, marasa kamun kai, 'yan tawaye, marasa kaunar nagarta. 4 Za su zama masu zagon kasa, taurin kai, masu takama, da masu kaunar anishuwa fiye da kaunar Allah. 5 Za su kasance da siffar ibada amma za su musunci ikonta. Ka juya daga wadannan mutanen. 6 A cikinsu akwai wadanda suke shiga gidaje suna yaudarar mataye marasa hikima. Wadannan ne mataye wadanda suke cike da zunubi, kuma sun kauce hanya sabili da sha'awoyi dabam daban. 7 Wadannan matayen suna ta koyo, amma ba za su taba kai wa ga sanin gaskiya ba. 8 Kamar yadda Yannisu da Yambrisu suka yi jayayya da Musa. Haka nan wadannan malaman karya kuma suke yin tsayayya da gaskiya. Mutane ne lalatattu a zuciya, marasa sahihiyar bangaskiya. 9 Amma ba za su yi nisa ba. Domin wautarsu za ta bayyana a fili ga kowa, kamar wadannan mutane. 10 Amma kai, ka bi koyarwata, da dabi'ata, nufe nufena, da bangaskiyata, da jimriyata, da kaunata, da hakurina, 11 da yawan kuncina, da wahalolina, da duk abubuwan da suka faru da ni a Antakiya, da Ikoniya da kuma Listra. Na jure a cikin kuncina. Amma a cikinsu dukka, Ubangiji ya cece ni. 12 Duk wadanda su ke so su yi rayuwa ta ibada a cikin Almasihu Yesu za su sha tsanani. 13 Miyagun mutane da masu hila za su yi ta kara lalacewa. Za su badda wasu. Su da kansu ma sun bijire. 14 Amma kai, ka ci gaba da abubuwan da ka koya kuma ka gaskata da zuciya daya. Ka san daga wurin wanda ka koya. 15 Ka san da cewa, tun kana dan karamin yaro ka san wadannan littattafai masu tsarki. Wadannan suna iya mai da kai mai hikima domin ceto ta wurin bangaskiya a cikin Almasihu Yesu. 16 Dukkan Nassi hurarre ne daga Allah. Yana da amfani domin koyarwa, domin tsautawa, domin gyara, kuma domin horarwa cikin adalci. 17 Wannan domin mutumin Allah ya zama cikakke ne, shiryayye domin dukkan ayyukan nagarta.
Bulus ya sa Timoti ya sani cewa nan gaba mutane za su daina amincewa da gaskiyar, amma shi Timoti ya cigaba da gaskatawa cikin kalmar Allah ko a lokacin da ake tsananta masa.
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamr haka 1) wannan lokaci ne bayan zamanin Bulus. AT: "nan gaba kafin dawowar Yesu" ko 2)wannan na nufin zamanin masubi, har da zamanin Bulus. AT: "a wannan zamanin kafin ƙarshen"
Ya yiwu wannan zai zama 'yan kwanaki ne, watani, ko ma shekaru ne da masubi zasu jure wahala da haɗari.
A nan "so" na nufin kaunar 'yan uwa ko abokai ko 'yan iyali, kauna ce ta abokai da dangi da mtane ke nuna wa. wannan ba kauna ce da ke zuwa daga Allah ba. AT: "son kai"
"ba su ƙaunar iyalinsu"
"basu son jituwa da kowa" ko "ba su zaman salama da kowa"
AT: "makiyan abu mai kyau
aikata abu da rashin kula ko tunanin me zai biyo baya, ko da sun san mumunar abu da zai iya faruwa
suna takamar cewa sun fi kowa
Bulus na magana game da ibada, da halin girmama Allah kamar wani abu ne mai sifa da iko wanda ake iya gani. AT: "za su kasance da siffar girmama Allah, amma hallayensu na nuna cewa basu gaskata ga iko Allah ba"
"ana ganin su da siffar ibada" ko "kasance kamar ana girmama Allah"
"Juya" a nan karin magana ne da ke nufin kauce wa wani mutum. AT: "kauce wa wannan mutane"
"shiga cikin gidaje su rinjayi"
"raunanan mataye a ruhaniya." Mataye na iya kasance wa raunana a ruhu domin basu kokarin bin Alla ko domin suna zaman banza suna kuma cike da zunubi.
Bulus na magana game da yadda zunubi ke jan hankali kamar an cika zunubin a kan wannan matayen. Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "wanɗanda su ke zunubi a kai a kai" ko 2) wanɗanda basu jin daɗin yadda suke cigaba da aikata zunubi." Wannan na ba da ra'ayin cewa wannan mazajen na iya yaudarar matayen nan cikin sauki domin waɗannan matayen basu iya daina aikata zunubi ba.
Bulus na magana game da wannan sha'awoyin kamar suna iya janye mutum ya kauce. AT: "suna sha'awar aikata zunubi ta kowane hali fiye da biyayya ga Almasihu"
wannan sunayen maza ne.
Bulus na magana game da masu jayayya da wani kamar suna gãba ne. AT: "hămayyă"
"hămayyă da bisharar Yesu"
"tunaninsu ya lalace" ko "basu iya tunani mai kyau"
Aka gwada bangaskiyarsu ga biyayyya cikin Almasihu, amma sun gază. AT: "ba tare da sahihiyar bangaskiya ba" ko "sun nuna cewa bangaskiyarsu ba ta gaskiya bace"
Bulus na magana game da malaman ƙarya cewa ba za su yi nasara ba acikin masubi. AT: "ba za su yi nasara ba"
abun da mutane ke iya gani a fili
"na Yannisu da Yambrisu"
Bulus na magana game da maida hankali da waɗannan abubuwan kamar wani ne da ke bin su sa'ad da suna tafiya. AT: "ka lura da koyarwata" ko "ka ba da hankalinka ga koyarwata"
"abun da na koyar da kai ka yi"
"yadda mutum ke tafiyar da rayuwarsa"
yadda mutum na hakuri da waɗansu mutane waɗanda suke yin abubuwa da bai amince ba.
Bulus na magana game da yadda Allah ya cece shi daga wahala da waɗannan hatsarorin kamar Allah ya ɗauke shi daga wani wurin zama ne.
"yin rayuwa ta ibada a matsayin mabiyin Almasihu"
AT: "lailai ne ya jure tsanani"
mai hila mutum ne wanda yake so mutane suyi tunanin cewa shi wani muhimmin mutum ne fiye da yanda ya ke.
"kasance da ƙarin mugunta"
A nan, baɗda wasu, ƙarin magana ne na rinjayar wani zuwa ga amincewa da abun da ba gaskiya ba. AT: "yaudarar kansu da waɗansu" ko "amincewa da ƙarya da kuma koyar da ƙaryan"
Bulus na yi wa Timoti magana game da umarnin Littafi Mai Tsarki kamar wani wuri ne da zai zauna a ciki. AT: kar ka manta da abun da ka koya" ko "ci gaba da aikata abun da ka koya"
Bulus na magana game da Littattafai Masu Tsarki kamar su wani mutum ne wanda zai iya ba wa wani hikima. AT: "Idan ka karanta maganar Allah, za ka iya samun hikima domin cote daga Almasihu Yesu ta wurin bangaskiya"
wasu littattafai sun fasara wannan kamar haka " Dukan Nassi hurarre na Allah ne." Wannan na nufin Allah ne ya sarrafa Nassi ta wurin Ruhunsa ta hayar gaya wa mutane abun da zasu rubuta. AT: "Allah ya yi magana a cikin dukan Nassi ta Ruhunsa"
"Yana da amfani" ko "yana da muhimmanci"
"domin nuna kuskure
"domin magance kuskure"
"domin horar da mutane su kasance da adalci"
wannan na nufin kowane mai bin Allah, na miji ko ta mace. AT: "dukan masubi"
"kasance da shiri"
Bulus ya ce a kwanakin karshe mugayen lokaci za su zo.
A cikin kwanakin karshe, mutane za su yi ƙaunace kansu, za su yi ƙaunar kuɗi, da kuma ƙaunar daɗi a maimakon Allah.
Bulus ya gaya wa Timoti ya juye daga masu siffar ibada guda ɗaya.
Waɗansu mugayen mazan nan na shigan gidaje su kuma yaudari matan da ake saurin shawo kansu da kayan kwaɗayi.
Waɗannan mugayen mazan masu koyaswar ƙarya ne waɖanda suke gaba da gaskiya kamar Yannisu da Yambrisu.
Timoti ya bi Bulus.
Allah ya cece Bulus daga dukan tsanantawa.
Bulus ya ce duka waɗanda suke so su yi rayuwa a cikin ibada za a tsananta ma su.
mugayen mutane da masu shigan burtu za su ƙara muni a karshen kwanaki.
Timoti ya san rubuce rubuce ma su tsarki tun da ya ke yaro.
Dukan littafi mai tsarki da ga Allah ne.
Dukan Littafi mai tsarki hurarre ne daga Allah, Yana da riba domin koyarwa, domin tsautawa, domin gyara, kuma domin horarwa cikin adalci.
Ana koyar da mutum a cikin littafi mai tsarki saboda ya iya aiki kuma ya samu kayan aiki don aiki mai kyau.
1 Ina bada wannan umarni a gaban Allah da Yesu Almasihu, wanda zai yi wa rayayyu da matattu shari'a, kuma saboda bayyanuwarsa da mulkinsa: 2 Ka yi wa'azin Kalma. Ka himmantu a kai ko da zarafi ko ba zarafi. Ka tsautar, ka kwabar, ka gargadar, da dukan hakuri da koyarwa. 3 Gama lokaci na zuwa wanda mutane ba za su jure wa koyarwar kirki ba. Maimakon haka, zasu tattara wa kansu malamai bisa ga sha'awowin zuciyarsu. Za su rika fada masu abin da kunnuwansu ke so. 4 Za su juya kunnuwansu daga koyarwar gaskiya, za su koma wa tatsunniyoyi na banza. 5 Amma kai, sai ka natsu a cikin dukan abubuwa. Ka jure wa wahala; ka yi aikin mai bishara, ka cika hidimarka. 6 Gama ana-tsiyaye ni. Lokacin yin kaurata yayi. 7 Na yi tsere na gaskiya; na kuma kammala tseren; na rike bangaskiya. 8 An adana mani rawani na adalci, wanda Ubangiji, alkali mai adalci, zai ba ni a ranan nan. Ba ni kadai ba, amma kuma ga dukkan wadanda suke kaunar zuwansa. 9 Ka yi iyakacin kokarinka ka zo wurina da sauri. 10 Domin Dimas ya yashe ni. Ya kaunaci wannan duniyar, ya tafi Tassalonika, Kariskis ya tafi Galatiya, Titus kuma ya tafi Dalmatiya. 11 Luka ne kadai yake tare da ni. Ka nemo Markus ka zo tare da shi domin yana da amfani a gareni a cikin aikin. 12 Na aiki Tikikus zuwa Afisus. 13 Ka kawo mani mayafin da na bari a Taruwasa wurin Karbus, idan za ka zo ka taho da shi, duk da littatafan nan, musanman takardun nan. 14 Iskandari makerin dalma ya kulla mani makirci ba kadan ba. Ubangiji zai biya shi gwargwadon ayyukansa. 15 Kai ma ka yi hankali da shi, domin yana tsayyaya da maganganunmu sosai. 16 Da farkon kariyar kaina, babu wanda ya goyi bayana. Maimakon haka kowa ya guje ni. Bana so dai a lissafta wannan a kansu. 17 Amma Ubangiji ya kasance tare da ni, ya kuma karfafa ni, yadda ta wurina, shelar ta sami cika da kyau, domin dukan al'ummai su ji. An kwato ni daga bakin zaki. 18 Allah zai kubutar ni daga dukan ayyukan mugunta, ya kuma cece ni domin mulkinsa na sama. Daukaka ta tabatta a gareshi har abada abadin. Amin. 19 Ka gayar da Briskilla, da Akila, da gidan Onisifurus. 20 Arastus ya nan zaune a Korinti, amma na bar Turufimus ya na zazzabi a Militus. 21 Ka yi iyakar kokarinka, ka zo kamin hunturu. Yubulus yana gayar da kai, haka ma Budis da Linus da Kalafidiya da dukan 'yan'uwa. 22 Bari Ubangiji ya kasance tare da ruhunka. Bari Alheri ya kasance da kai.
Bulus ya cigaba da tunashe da Timoti ya kasance amintacce, da kuma cewa shi Bulus na shirye ya mutu.
ya yiwu cewa Allah da Almasihu Yesu ne shaidun Bulus. AT: "wannan muhimmin Umurni ne da ke a matsayin shaidu na ga Allah da Almasihu Yesu"
"umurni mai muhimmanci"
A nan "rayayyu" da "mattatu" na nufin dukan mutane. AT: "dukan mutane da suka taɓa rayuwa"
A nan "mulki" na a matsayin shugabancin Almasihu Sarki. AT: "matattu, a sa'ad da ya dawo ya yi mulki a matsayin Sarki"
"Kalma" a nan na nufin "saƙo." AT: "saƙo game da Almasihu"
an riga an gane kalmar "zarafi" anan. AT: "ko babu zarafi"
faɗa wa mutum cewa ya aikata abun da ba daidai ba
"gargadar, koyar da mutanen, da kuma haƙuri da su"
"Domin lokaci na zuwa nan gaba"
wannan aya na nuna cewa wannan mutanen za su zama daga al'umman masubi ne.
"ba za su so su saurari koyarwar kirki ba"
Wannan na nufin koyarwar gaskiyar, da ke daidai, bisa ga maganar Allah.
Bulus na magana game da tara malamai kamar an tara wani abu ne. AT: "za su saurari malamai da yawa wanda za su ba su tabbacin cewa babu wani laifi da sha'awowin zunubansu"
Bulus na magana game da yadda mutane ke marmarin jin wani abu kamar kunnuwarsu na ƙaiƙayi kuma sai malamai sun faɗa masu abin da suke so su ji. AT: "wanda suke faɗan iyakan abun da suke son ji sosai"
Bulus na magana game da yadda mutane ba su mayar da hankali kamar yadda ake juya baya domin kar a ji abu. AT: "Ba za su ƙara mayar da hankali da gaskiya ba"
Bulus na magana game da yadda mutane suka fara mayar da hankalinsu ga tatsunniyoyin ƙarya kamar yadda ake juya wa domin a ji magana da kyau. AT: "za su fara mayar da hankali ga koyarwar ƙarya"
Bulus na so masu karatu su samu tunani na kwarai game da kowane abu, yana magana game da wannan abubuwan kamar yana so su zama a natse, ba a buge da giya ba. AT: "yi tunani da kyau"
Wannan na nufin cewa a faɗa wa mutane game da wanene Yesu, abun da ya yi domin su, da kuma yadda za su yi rayuwa domin shi.
Bulus na magana game da shirin mutuwarsa kamar shi kofin ruwan inabi ne wanda ake shirye a zuba kamar hadaya zuwa Allah.
"ƙaura" a nan wata hanyar magana ce da ke nufin mutuwa. AT: "bada jimawa ba zan mutu in bar wannan duniya"
Bulus na maganar jure wahalolisa kamar shi dan wasan tsere ne domin lada. AT: "Na yi iyakan ƙoƙarina"
Bulus na maganar rayuwarsa na hidimar Allah kamar ya dinga wasan guje-guje ne. AT: "Na kammala abunda yakamata in yi"
Bulus na maganar amincewarsa da Almasihu da biyayya ga Allah kamar wani muhimmin dukiya mai daraje ne da yake riƙe da shi. Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "Na dinga yin aikina da imani" ko 2)"Na riƙe koyarwar abun da muka gaskata ba kuskure"
AT: "Allah ya keɓe rawanin adalci domina"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) rawanin shi ne ladar da Allah ke bayar wa mutanen da suka yi rayuwa mai kyau, ko 2) rawanin karin magana ne na adalci. Kamar yadda alkalin wasa ke ba da lada ga wanda ya yi nasara, haka ma idan Bulus ya kammala rayuwarsa, Allah zai bayyana shi adali.
wani irin kambi ne da ake yi da ganye domin a bayar ga wanda ya yi nasara a tsere.
"a ranar da Ubangiji ya sake dawowa" ko "a ranar da Allah zai shar'anta mutane"
Bulus na maganar wannan aukuwar kamar ya riga ya faru. Ana iya faɗin wannan kamar abun da zai faru nan gaba. AT: amma kuma zai bayar ga duk waɗanda suke jiran dawowarsa"
"zo ... bada jimawa ba"
Wannan sunayen maza ne.
A nan "duniya" na nufi kayan duniyar da ke kalubalantar abubuwan Allah. Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar hake 1) yana ƙauna da gamsuwar wannan duniya da ke na ɗan ƙanƙanin lokaci, ko 2) yana tsoro zai iya mutuwa idan ya kasance tare da Bulus.
waɗannan mutane biyun sun bar Bulus, amma ba wai Bulus na faɗin cewa su ma suna "ƙaunar wannan duniyan" kamar Dimas ba.
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "yana da taimako cikin hidimar Ubangiji" ko 2) "zai iya taimakona ta wurin yi mani hidima."
wani riga mai nauyi da ake sanya wa bayan a sa taguwa
wannan sunan na miji ne.
wannan wani irin lattafi ne da ake yi da fata. Bayan an yi rubuta ko karanta littafin, akan naɗe shi da sanduna da ke ƙarshen littafin
Wannan na iya nufin wani irin littafi na musamman. AT: "musamman wanda aka yi da fatan dabba"
"Iskandari, wanda yake aiki da dalma, ya nuna"
Wannan sunan na miji ne.
Bulus na maganar aikata mugunta kamar sau abubuwa ne da ake nunawa. AT: "ya yi mani mugunta sosai"
Bulus na maganar hukunci kamar biyan kuɗi ne. AT: "Ubangiji zai hukunta shi domin abun da ya aikata mani"
wanɗanan na nufin Iskandari.
A nan "maganganu" na nufin saƙo ko koyarwa. AT: "tsayyaya da saƙon da muke koyarwa"
"A farkon kasancewa na a kotu na bayyana ayyukana"
"babu kowa da ya tsaya da ni ya taimake ni"
AT: "Bana so Allah ya lissafta a kansu" ko "Ina addu'a kada Allah ya hukunta waɗanan masubi domin sun rabu da ni"
Bulus na magana kamar Ubangiji na tare da shi fuska da fuska. AT: "Ubangiji ya taimake ni"
AT: "Domin in iya faɗin dukan saƙon Ubangiji"
Bulus na maganar abu mai hatsari kamar yana hatsarin zaki. Wannan hatsarin na iya zama ta ruhaniya, ko ta jik, ko duka. AT: "An kuɓutar da ni daga baban hatsari"
A nan "gida" na nufin mutanen da suke wurin. AT: "Iyalin Onisifurus"
Wannan sunan namiji ne. dubi yadda aka fasara wannan cikin 2 Timoti 1:16.
Wannan sunayen maza ne.
Wannan sunan wani gari ne kudu daga Afisa.
"ka nemi hanyar zuwa"
"kafin lokacin sanyi"
Ana iya fasara wannan a wani sabuwar jumla. AT: "gai da kai. Budis, Linus, Kalafidiya da dukan 'yan'uwan suma suna gaishe ka"
Wannan sunan mace ce.
A nan " 'yan'uwa" na nufin duk masubi maza da mata. AT: "dukan masubi a nan"
"Ina addu'a cewa Ubangiji ya karfafa ruhunka." A nan "ka" na nufin Timoti ne.
"Ina addu'a Ubangiji ya nuna alherinsa a gareku duka." A nan "ku" na nufin dukan masubi da suke tare da Timoti.
Yesu Almasihu shine alkalin masu rai da matattu.
Bulus ya ba Timoti muhimmin umurni ya yi wa'azin kalmar.
Mutane ba sa su jimre koyarwa mai nagari ba, amma za su saurari koyarwar da ta yadda d muguwar sha'awar su.
An ba wa Timoti aiki da hidima ta mai bishara.
Bulus ya ce lokacin tafiyarsa ta zo.
Bulus ya ce duka waɗanda suke kaunar bayannar Almasihu za su samu rawanin adalci.
Dimas ya bar Bulus domin yana ƙaunar wannan duniya ta yanzu.
Luka ne kawai ya tsaya da Bulus.
Bulus ya ce duk mutumin da ya yi hamayya da shi zai sami sakamako bisa ga ayukansa.
A farkon tsaron Bulus, babu wanda ya tsaya tare da Bulus.
1 Bulus, bawan Allah, kuma manzon Yesu Almasihu, ta wurin bangaskiyar zababbun mutanen Allah da sanin gaskiya da ta yadda da allahntaka. 2 Wadannan na cikin begen rai marar matuka wanda Allah, wanda babu karya a cikinsa, ya alkawarta kafin dukkan lokatan zamanai. 3 A daidai lokaci, ya bayyana maganarsa ta wurin sakonsa da ya damka mani in shelar. Zan yi wannan ta wurin umarnin Allah mai ceton mu. 4 Zuwa ga Titus, da' na gaske a cikin bangaskiyarmu. Alheri, jinkai da salama daga wurin Allah Uba da Almasihu Yesu mai ceton mu. 5 Sabili da wannan ne na bar ka a Karita domin ka daidaita abubuwan da basu cika ba, ka kuma nada dattibai a dukan birane kamar yadda na umarceka. 6 Dole ne dattijo ya zama marar abin zargi, mijin mace daya, da amintattun 'ya'ya wadanda babu wani zargi na mugunta ko rashin kamun kai a kansu. 7 Wajibi ne shugaban Ikklisiya, a matsayin sa na mai kulla da haikalin Allah, ya zama marar aibi. Kada ya zama mai surutu ko rashin hakuri. Kada ya zama mai saurin fushi, ko mashayi, ko mai hayaniya, ko mai handama. 8 Maimakon haka, ya zama mai karbar baki, abokin abinda ke mai kyau. Dole ne ya zama mai hankali, adali, cike da allahntaka, da kuma kamun kai. 9 Ya zama mai rike amintaccen sakon da aka koyar da karfi, yadda zai iya karfafa wasu da koyarwa mai kyau ya kuma yi wa wadanda suke hamayya da shi gyara. 10 Domin akwai kangararrun mutane dayawa, musamman masu kaciya. Maganganunsu na banza ne. Suna yaudara kuma suna badda mutane. 11 Wajibi ne mu hana su. Suna koyar da abinda bai kamata su koyar ba saboda makunyaciyar riba suna kuma rusar da iyalai dungum. 12 Daya daga cikinsu, kuma mai hikima ne daga cikinsu, yace, "Kirawa manyan makaryata ne, lalatattu kuma miyagun dabbobi, masu kyiuya da zarin cin abinci." 13 Wannan magana gaskiya ne, ka yi masu gyara da tsanani yadda zasu kafu a cikin bangaskiya. 14 Kada ka mai da hankalin ka ga tatsunniyoyi na Yahudawa ko dokokin mutane wadanda sun sauya gaskiya. 15 Ga wadanda suke da tsarki, komai mai tsarki ne. Amma wadanda suke marasa tsarki da rashin bangaskiya, komai marar tsarki ne. Domin zuciyarsu da lamirinsu sun gurbata. 16 Suna cewa sun san Allah, amma sun musanta shi ta wurin ayyukansu. Sun zama abin kyama da marasa biyayya. Ba za a iya tabbaatar dasu ba akan wani aiki maikyau.
a ƙarfafa bangaskiyar
"ta yi daidai don girmama Allah"
"kafin loƙaci ta fara"
"A loƙacin da ya kamata"
Bulus ya yi magana game da maganar Allah kamar wani abu ne da za a iya nuna wa mutane su gani. AT: "Ya sa ni in fahimci saƙonsa"
"ya danƙa mani in kawo" ko "ya ba ni hakin yin wa'azi"
"Allah, wanda ya cece mu"
Kodashike Titus ba ɗan cikin Bulus ba ne, bangakiyarsu ɗaya ne cikin Almasihu. Cikin Almasihu kuwa, Bulus ya dubi Titus a matsayin ɗansa. AT: "kana kamar ɗa a gare ni"
Bulus ya bayyana ɗayantakar bangaskiya cikin Almasihu wanda dukansu ke da shi. AT: "koyarwar da duka mun gaskanta"
Wannan gaisuwa ce wanda Bulus ya saba amfani da ita. Za ka iya bayyana yanda za a fahimta a fili. AT: "Bari ka sami abin lirki da salama a cikin ka"
"Almasihu Yesu wanda shine mai cetonmu"
"Wannan ita ce dalilin"
"Na ce maka ka tsaya a Karita"
"don ka gama shirya abubuwan da ya kamata a yi"
"naɗa dattibai" ko "sanya dattibai"
Cikin Ikkilisiyoyin Masu bi na farko, dattiban masu bi na yin shugabanci ta ruhaniya ga taron masu bi.
Bayan ya gaya wa Titus ya keɓe dattibai a kowace birnin da ke tsibirin Karita, Bulus ya ba da halayen da ake buƙata ga dattibai.
Zama "mara abin zargi" ita ce a san mutum a matsayin wanda ba ya yin munanan abubuwa. AT: "Dole dattijo ya zama wanda ba shi da mummunan suna"
Wannan na nufin cewa yana da mata ɗaya, wato, ba shi da waɗansu mataye balle ƙwaraƙwarai. Zai iya zama cewa baya zina kuma bai saki matar sa ba. AT: "na miji mai mace daya" ko "na miji da ke amminci ga matar sa"
Mai yiwuwa wannan na nufin haka 1) 'ya'ya waɗanda sun gaskata da Yesu ko 2) amintattun 'ya'ya.
ba su da kamun kai, ba su iya kamun kan su ba
Wannan wata suna ce ɗaya da matsayin shugabancin ruhaniya da Bulus ke nufin "dattijo" a 1:6.
Bulus ya yi maganar ikkilisiya kamar iyalin Allah ne, kuma mai kula kamar shi wani bawa ne da ke sarrafa iyalin.
"ba bugagge ba" ko "ba wanda yake shan barasa da yawa ba"
"ba wanda ke sa tashin hankali ba" ko "ba mai son faɗa ba"
Bulus na canzan maganarsa daga abin da bai kamata dattijo ya zama ba zuwa abin da ya kamata dattijo ya zama.
"mutum wanda ke ƙaunar abin da ke da kyau"
Bulus ya yi magana game da duƙufa a cikin bangaskiyar masu bi kamar kãmun bangaskiya da hannu ne. AT: "duƙufa ga" ko "sani da kyau"
Dole ne ya koyar da abin da ke gaskiya game da Allah da kuma wasu al'amuran ruhaniya.
Waɗannan kangararrun mutanen ne da ba su goyi bayan sakon bisharar Bulus ba.
Wannan magana na bayyana kangararrun mutanen da aka ambata a baya. Anan "fanko" na nufin banza, kuma "masu fankon maganganu" su ne mutanen da ke maganganu banza da wofi. AT: "mutane waɗanda ke yin banzan maganganu su kuma yaudari waɗansu"
Wannan na nufin Yahudawan masubi waɗanda ke koyar da cewa dole ne mutane su yi kaciya don su bi Almasihu.
"Dole ne a hana su yaɗa koyarwar su" ko "Dole ne a hana ɓata wasu ta wurin kalmomin su"
Waɗannan abubuwa ne da ba daidai ne a koyar game da Almasihu ba da kuma shari'ar, domin, ba gaskiya ba ne.
Wannan na nufin riba da mutane ke samu ta wurin aikata abubuwan da ba na halal ba.
"suna ɓata iyalai ɗungum." Ainihin zancen ita ce su na rusar da iyalan ta wurin rushe bangaskiyarsu. Mai yiwuwa wannan ya sa 'yan iyalin yin musu da juna.
"Annabi daga Karita" ko "dan Karita wanda su kan su suna ɗauka a matsayin annabi"
"Karitawa suna ƙarya a kowace lokaci." Wannan zuguiguitawa ne da ke nufin cewa yawancin Karitawa suna ƙarya sosai.
Wannan na kwatanta Karitawa da mugun naman daji.
"Lallai ne ka yi amfani da harshen da Karitawa za su fahimta sa'anda ka ke yi musu gyara"
"don su sami bangaskiya mai lafiya" ko "don bangaskiyar su ta zama gaskiya"
Wannan na nufin koyarwar karya na Yahudawa.
Bulus ya yi magana game da gaskiyar kamar wani abu ne da wani ke iya juya mata baya ko kuwa kauce mata. AT: "ƙi gaskiyar"
"In mutane suna da tsarki a cikinsu, kowane abin da suka yi zai zama da tsarki"
"Ga waɗanda ke karɓaɓɓu a wurin Allah"
Bulus ya yi magana game da masu zunubi sai ka ce suna da datti a jikinsu. AT: "In mutane na da ƙazantatciyar hali kuma ba su gaskata ba, ba za su iya yin wani abu mai tsarki ba"
"Yanda suke rayuwa ya nuna cewa ba su san shi ba"
"Su abin ƙyama ne"
Manufansa shi ne ya kafa bangaskiyar zababbun Allah kuma ya kafa sanin gaskiya.
Ya yi alƙawarin nan tun kamin dukan shekaru daabn-daban na lokaci.
A'a.
Allah ya yi amfani da manzo Bulus.
Titus yaron Bulus na ne na gaskiya a cikin bangaskiyan su na kowa.
Ya zama tilas ne ya zama mijin mata ɗaya, tare da yara masu aminci waɗanda ke da horo.
Tilas ne kada ya zama mai ihu da rashin kangewa, ba mashayi ba, ba mai gardama ba, ba mai haɗama ba.
Shine mai sarrafa iyali.
Dattijo ya kamata ya zama mai yi ma baki alheri, mai son abu nagari, natsatse, mai kirki, tsarkakke, mai kamun kai.
Tilas ne ya rike su ƙam, ya kuma iya yin amfani da su ya ƙarfafa ya kuma tsauta ma wasu.
Suna yaudaran mutane da kuma raba iyalai.
Sun himmatuwa ne ta wurin kazamar riba.
Tilas ne ya gyara su da sauri domin su zama masu bamgaskya mai nagari.
Kada su ɓata lokaci a kan tatsuniyoyin Yahudawa, da kuma dokokin mutane.
Zuciyarsa da kuma lamirinsa sun ƙazantu.
Yana musun Allah ta hanyar ayyukan sa.
1 Amma kai, ka fadi abinda yayi daidai da amintaccen umarni. 2 Dole tsofaffin mazaje su zama masu kamun kai, masu daraja kansu, masu-hankali, masu aminci cikin bangaskiya, cikin kauna da jurewa. 3 Haka ma tsofaffin mataye su kame kansu da girma, ba magulmata ba. Kada su zama bayi wajen yawan shan ruwan inabi. Su koyar da abubuwa masu kyau 4 domin su koyar da kananan mataye da hikima su kaunaci mazajensu da 'ya'yansu. 5 Su horar dasu su zama masu hikima da tsabtar zuci, masu tsaron gidajensu, kuma masu biyayya da mazajensu. Suyi wadannan abubuwa saboda kada maganar Allah ta sami zargi. 6 Ta haka kuma, ka karfafa samari, su zama masu hankali. 7 A kowanne fanni, ka mayar da kan ka abin koyi a cikin kyawawan ayyuka; idan kayi koyarwa, ka nuna mutunci da martaba. 8 Ka bada sako lafiyayye marar abin zargi, yadda masu hamayya da maganar Allah zasu ji kunya, domin rashin samun mugun abin fadi akan mu. 9 Bayi suyi biyayya ga iyayengijin su a cikin komai. Su faranta masu rai, ba suyi gardama dasu ba. 10 Kada suyi sata. Maimakon haka, sai su nuna dukan bangaskiya mai kyau, domin suyi wa koyarwarmu game da Allah mai cetonmu kwalliya a cikin dukan komai. 11 Domin alherin Allah ya bayyana ga dukan mutane. 12 Yana koya mana mu musanci miyagun ayyuka, da sha'awoyin duniya. Yana horar damu muyi zama cikin hankali, da adalci a cikin hanyar allahntaka a wannan zamani 13 yayin da muke cigaba da jiran karba albarkataccen begenmu, wato bayyanuwar daukakar Ubangiji Allah da kuma mai cetonmu Yesu Almasihu. 14 Yesu ya bada kansa domin mu, domin ya cece mu daga rashin kiyaye doka ya mai damu masu tsarki, domin sa, mutane na musamman wadanda suke da marmarin aikata kyawawan ayyuka. 15 Ka yi magana da karfi ka karfafawa wadannan abubuwa. Ka yi gyara da dukan iko. Kada ka bar wani ya raina ka.
Bulus ya ci gaba da ba wa Titus dalilan yin wa'azin maganar Allah, ya kuma bayyana yanda tsofaffin mazaje, da tsofaffin mataye, samari, da bayi ko kuwa barori za su yi rayuwa kamar masu bi.
Bulus na nufin abin da ke da bambanci. AT: "Amma kai, Titus, cikin saɓani da masu koyarwar ƙaryar, ka tabbata ka faɗi abubuwan da ke daidai"
"da sahihiyar koyarwa" ko "da koyarwar da ke daidai"
"zama natsattsu" ko "zama masu kamun kai"
" ... sarrafa sha'awarsu"
A nan kalman nan "sahihiya" na nufin zama da ƙarfi kuma babu shakka. Ana iya bayyana "bangaskiya" "ƙauna," da kuma "jimiri" cikin aikatau. AT: "kuma dole ne su gaskata koyarwar gaskiya game da Allah da ƙarfi, su ƙaunaci wasu da gaske, su kuma ci gaba the bautar Allah ko a lokacin da abubuwa sun yi wuya"
"haka kuma, ka koyar da tsofaffin mataye" ko "ka kuma koyar da tsofaffin mataye"
Wannan kalma na nufin mutane masu faɗin abubuwa marasa kyau game da wasu mutane ko gakiya ne ko ba gakiya ba.
Ana magana game da mutumin da bai iya sarrafa kansa ba, na kuma shan barasa sosai sai kace mutumin bawa ne ga barasa. AT: "kuma kada a sha barasa sosai" ko " ba kuma shagala ga barasa"
"magana" a nan na nufin "saƙo" wanda ya na kuma nufin Allah da kansa. AT: "don kada wani ya zargi maganar Allah" ko "don kada wani ya zargi Allah ta wurin faɗin munanan abubuwa game da saƙonsa"
ya kamata Titus ya karfafa samarin kamar yanda ya kamata ya karfafa tsofaffin mutane.
"nuna kanka ka zama"
"gurbi wanda ke yin abin da ke daidai da kuma abubuwan da sun dace"
Wannan na nuna hoton yanayin da wani ya yi hamayya da Titus sai kuma ya kai ga kunya don ya yi haka. AT: "domin in wani ya yi hamayya da kai, zai iya jin kunya" ko "domin in mutane sun yi hamayya da kai, za su iya jin kunya"
"nasu iyayengijin"
"cikin kowane yanayi" ko "koyaushe"
"sa iyayengijinsu farin ciki" ko "gamsar da iyayengijinsu"
"nuna cewa sun cancanci iyayengijinsu su dogara a gare su"
"cikin kowanne abin da suke yi"
"su iya sa koyarwa game da Allah Mai Cetonmu ta jawo hankali" ko "su sa mutane su fahimci cewa koyarwa game da Allah Mai Cetonmu na da kyau"
"Allahn mu wanda ya cece mu"
Bulus ya yi maganar alherin Allah sai ka ce mutum ne wanda ke zuwa wurin mutane ya kuma koya masu zaman tsarki.
"koya mana kada mu yi rashin biyayya ga Allah"
"sha'awace-sha'awace masu ƙarfi don abubuwan wannan duniya" ko "sha'awace-sha'awace masu ƙarfi don jin daɗin zunubi"
"a yayinda muna rayuwa cikin wannan duniya" ko "a wannan lokacin"
"muna jira don mu marabci"
A nan "ɗaukaka" na nufin Yesu da kansa wanda zai bayyana cikin ɗaukaka. AT: "abu mai kyau da mu ke begen shi, wato, ɗaukakar bayyanuwar Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Almasihu"
Wannan na nufin Yesu ya mutu da son ransa. AT: "ya bada kansa don ya mutu donmin mu"
Bulus ya yi maganar Yesu kamar yana kuɓutar da bayi daga mugun ubangijinsu.
rukunan mutane da ke daraja a wurinsa.
"su na da marmari sosai"
Wannan magana ana iya sa ta a bayyane. AT: "da dukan iko ka yi wa waɗannan mutanen da basu aikata waɗannan abubuwan, gyara"
"Kada ka bar wani"
Wannan maganar ana iya sa ta a bayyane. AT: "ƙin jin maganar ka" ko "ƙin ba ka girma"
Ya kamata su nuna kamunkai, martaba, bangaskiya nagari, a kauna, da kuma jimiri.
Ya kamata su nuna girmamawa, ba tsegumi, su zama kamilai su kuma abinda ke da kyau.
Ya kamata su koya masu kaunace mazajensu, su kuma yi masu biyayya, su kaunace 'ya'yansu, su zama masu natsuwa, masu tsarki, su kuma zama masu kula da gida.
Ya kamata ya koya, yana nuna tsarki da martaba, da kuma yin amfani da kalmomin da basu buƙatar gyara.
Za su yi biyayya ga masu gidansu, ba wai suyisata daga wurinsu ba, kuma ya kamata su nuna bangaskiya mai kyau.
Zai sa koyaswar game da Allah mai ceto ya jawo hankalin wasu.
Alherin Allah zai iya ceton kowa da kowa.
Alherin Allah yana kowa mana mu muyi musun rashin bin Allah da kuma mugayen sha'awar duniya.
Masu bi suna duban gaba ma bayyanar daukakan Allah mai girma da ceton Yesu Almasihu.
Ya bada kansa domin ya fanshe mu daga dukan aikin mugunta, ya kuma sa tsarkakkun mutane hanzarin yin aiki mai kyau.
1 Ka tuna masu su zama masu sadaukar da kai ga masu mulki da masu iko, suyi masu biyayya, su zama a shirye domin kowane kyakkyawan aiki. 2 Ka tuna masu kada su zagi kowa, su gujiwa gardama, su bar mutane su bi hanyarsu, su kuma nuna tawali'u ga dukan mutane. 3 Domin a da, mu da kan mu marasa tunani ne kuma masu rashin biyayya. Mun kauce hanya muka zama bayi ga sha'awoyin duniya da annashuwa. Mun yi zama a cikin mugunta da kishi. Mu lalatattu ne kuma muna kiyyaya da junanmu. 4 Amma da jinkan Allah mai ceton mu da kaunarsa ga 'yan Adam ta bayyana, 5 ba saboda wani aikin adalci da muka yi ba, amma sabili da jinkan sa ne ya cece mu. Ya cece mu ta wurin wankewar sabuwar haihuwa da sabuntuwar Ruhu Mai Tsarki. 6 Allah ya zubo mana Ruhu Mai Tsarki a wadace ta wurin Yesu Almasihu mai cetonmu. 7 Ya yi wannan saboda, bayan mun samu 'yantarwa ta wurin alherinsa, za mu zama magada a cikin begen rai na har abada. 8 Wannan amintaccen sako ne. Ina son kayi magana gabagadi game da wadannan abubuwa, yadda dukan wadanda suka bada gaskiya ga Allah za suyi kudirin yin kyawawan ayyuka da Allah ya mika masu. Waddannan abubuwa masu kyau ne da kuma riba ga dukan mutane. 9 Amma ka guji gardandami na wofi, da lissafin asali, da husuma da jayayya game da dokoki. Wadannan abubuwa basu da amfani kuma marasa riba. 10 Ka ki duk wani dake kawo tsattsaguwa a tsakaninku, bayan ka tsauta masa sau daya ko biyu, 11 ka kuma sani cewa wannan mutumin ya kauce daga hanyar gaskiya, yana zunubi kuma ya kayar da kansa. 12 Sa'adda na aiki Artimas da Tikikus zuwa wurin ka, kayi hanzari ka same ni a Nikobolis, a can na yi shirin kasancewa a lokacin hunturu. 13 Kayi hanzari ka aiko Zinas wanda shi gwani ne a harkar shari'a, da Afolos ta yadda ba zasu rasa komai ba. 14 Ya kamata Jama'armu su koyi yadda zasu yi ayyuka masu kyau da zasu biya bukatu na gaggawa yadda ba za suyi zaman banza ba. 15 Dukan wadanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gai da masu kaunar mu a cikin bangaskiya. Alheri ya kasance tare da dukan ku.
Bulus ya cigaba da ba wa Titus umarni yanda zai koyar da dattibai da mutanen da ke ƙarƙashin kulawarsa a cikin Karita.
"Gayawa mutanenmu kuma abin nan da sun riga sun sani, su miƙa kai" ko "Ka cigaba da tunashe su su mika kai"
"yi kamar yanda masu mulki da masu ikon gwamnati sun faɗa ta wurin yi musu biyayya"
Waɗannan kalmomin biyu suna da ma'ana kusan iri ɗaya kuma an yi amfani da su tare don ya shafi duk waɗanda suna da iko a gwamnati.
"yi shirin yin kyakkyawan aiki a sa'anda kun sami zarafi"
"yi mugun magana game da"
"Domin mu kanmu ma a dã"
"a dã" ko " a wata lokaci" ko "a baya"
"ko mu ma" ko "mu kuma"
"dã wawaye ne" ko "dã marasa hikima"
Bulus ya yi maganar "sha'awoyin da annashuwa" kamar mutane ne wanɗanda za su iya kai wasu ga kaucewa ko kuma zama bayi. A nan "sa wani ya kauce" na nufin sa wani ya gaskata abin da ba gaskiya ba. A nan "bayi ga sha'awoyi iri iri da annashuwa" na nufin rashin iya kamun kai. AT: "mun ruɗi kanmu mun kuma aikata abin da ke daidai a gare mu"
"muguwar sha'awa" ko "sha'awace-sha'awace"
Anan "mugunta" da "ƙishi" kalmomi ne kusan iri ɗaya na zunubi. AT: "Mun cika yin mugayen abubuwa da kuma son abinda wasu na da shi"
"Mun sa wasu sun ƙi mu"
Bulus ya yi maganar alherin Allah da ƙaunar sa kamar su mutane ne da sun zo wurin mu.
"domin ya yi mana jinƙai"
Mai yiwuwa Bulus yana maganar yafewar Allah ga masu zunubi kamar yana wanke su ne a jiki. Ya kuma yi magana game da masu zunubi waɗanda sun yi na'am da Allah kamar an sãke haihuwarsu.
waɗanda suka rubuta Sabon Alkawari sun saba maganar Ruhu Mai Tsarki kamar ruwa-ruwa ne da Allah zai iya zuba wa dayawa. AT: "ba mu Ruhu Mai Tsarki a yalwace"
"sa'adda Yesu ya cece mu"
AT: "dashike Allah ya maishemu marasa zunubi"
An yi maganar mutane waɗanda Allah ya yi musu alkawarensa kamar za su gaji mallaka da dukiya daga wani daga cikin iyali.
Wannan na nufin Allah ya ba da Ruhu Mai Tsarki ga masu bi ta wurin Yesu cikin [Titus 3:7]
"ƙoƙarin yin kyawawan ayyuka"
"don haka ka guje" ko "Saboda haka, guji"
"gardama game da al'amura marasa amfani"
Wannan ita ce nazari a kan dangantakan dangin iyali.
gardama ko faɗa
"shari'ar Musa"
"Guje wa kowane mai"
"Bayan ka tsauta wa mutumin sau ɗaya ko biyu"
"mutum kamar wannan"
Bulus ya yi maganar wani wanda ya yi kuskure kamar ya bar hanyar da dã yake tafiya a kai.
"kawo shari'a a kansa"
"bayan da na aiki"
Waɗannan sunayen maza ne.
"zo da sauri"
"tsaya a loƙacin bazara"
"Kada kayi jinkirin aiko"
"ka kuma aiko Afolos"
Bulus na nufin masu bi a Karita.
"da ya taimake su su iya taimakon mutanen da ke bukatan abubuwa masu amfani nan da nan"
Bulus ya yi maganar kyawawan ayyukan mutane kamar bishiyoyi ne da ke bada 'ya'ya mai kyau. Wannan na nufin su ba da 'ya'ya ko kuwa su zama masu sarrafa 'ya'ya. AT: "bukatu, ta haka za su ba da 'ya'ya" ko "bukatu, ta haka kuma za su yi kyawawan ayuka"
Bulus ya ƙarasa wasiƙar sa zuwa ga Titus.
"Duk mutanen"
Ma'ana mai yiwuwa AT: 1) "masu bi waɗanda suke ƙaunar mu" ko 2) "masubi da ke ƙaunar mu domin bangaskiyar mu ɗaya ne."
Wannan gaisuwa ce da masubi sun saba yi. AT: "Bari Alherin Allah ta kasance a gare ku" ko "Ina roƙo cewa Allah ya yi muku dukkan Alheri"
Ya kamata mai bi ya yi ladabi da biyayya, suna zaune da shiri wa aiki mai kyau.
Mugayen sha'awarsu da annashuwa ke kai su ga ɓatawa.
Ya cece mu ta hanyar wankewar sabon haihuwa da sabuntawa ta Ruhu mai Tsarki.
Muna da ceto domin rahamar Allah kawai.
Allah ya maida mu magadansa.
Ya kamata masubi su sa zuciyarsu a kan ayyuka masu kyau wanda Allah ya sa gabaninsu su yi.
Ya kamata masu bi su kauce wa muhawarar wauta.
Duk wanda ke haddasa rabuwa a tsakanin masubi dole ne a ƙi shi bayan gargadi daya ko biyu.
Tilas ne masubi su shigar da kansu a aiki masu kyau da ke biyan buƙatun gaggawa?
1 Bulus, daurarren Yesu Almasihu, da kuma dan'uwa Timotawus zuwa ga Filimon, kaunataccen abokinmu da kuma abokin aikin mu, 2 da Afiya yar'uwanmu da Arkifus abokin aikin mu a filin daga, da kuma Ikilisiyar da take taruwa a gidan ka: 3 Alheri da salama su kasance gare ka daga wurin Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Almasihu. 4 Kowane lokaci ina gode wa Allah. Ina ambaton ku cikin addu'oi na. 5 Na ji labarin kauna da bangaskiya da ka ke da ita a cikin Ubangiji Yesu da dukkan yan'uwa masu bi. 6 Ina addu'a zumuntar bangaskiyarka ta inganta ga kawo sanin kowane kyakkyawan abu dake cikin mu a cikin Almasihu. 7 Na yi farinciki kwarai, na kuma ta'azantu saboda kaunarka, saboda zukatan masu bi sun kwanta ta wurin ka, dan'uwa. 8 Saboda haka, ko da ya ke ina da gabagadi a cikin Almasihu domin in ba ka umarni ka yi abinda ya kamata ka yi, 9 duk da haka sabo da kauna, na fi so in roke ka- Ni, Bulus, dattijo, a yanzu kuma ga ni dan kurkuku domin Almasihu Yesu. 10 Ina rokon ka saboda da na Onisimus, wanda na zama uba a gare shi sa'adda nake cikin sarkokina. 11 Domin a da kam, ba shi da amfani a wurin ka, amma yanzu yana da amfani a gare ka da kuma a gare ni. 12 Na kuma aike shi wurinka, shi wanda ya ke a cikin zuciyata kwarai. 13 Na so da na rike shi a wuri na, domin ya rika yi mini hidima a madadin ka, a lokacin da ni ke cikin sarkoki saboda bishara. 14 Amma ba na so in yi wani abu ba tare da sanin ka ba. Ba ni so nagarin aikinka ya zama na dole amma daga kyakkyawar nufi. 15 Watakila dalilin da yasa ya rabu da kai na dan lokaci ke nan, domin ka karbe shi kuma har abada. 16 Daga yanzu ba za ya zama bawa ba kuma, amma fiye da bawa, wato kaunataccen dan'uwa. Shi kaunatacce ne musamman a gare ni, har fiye da haka ma a gare ka, a cikin jiki da kuma cikin Ubangiji. 17 Idan ka maishe ni abokin hidima, ka karbe shi kamar yadda za ka karbe ni. 18 Idan kuwa ya yi maka abinda ba daidai ba ko kuwa kana bin sa wani abu, ka dauka yana wurina. 19 Ni, Bulus, na rubuta wannan da hannuna: zan biya ka. Ba kuwa cewa sai na gaya maka cewa ina bin ka bashin kanka ba. 20 I, dan'uwa, ka yi mani alheri cikin Ubangiji; ka ba zuciyata hutu a cikin Almasihu. 21 Saboda Ina da tabbaci game da biyayyarka, na rubuta maka. Na san za ka yi fiye da abinda na roka. 22 Harwayau, ka shirya mani masauki. Domin ina fata ta wurin adu'oinku, nan ba da dadewa ba za a maida ni wurin ku. 23 Efafaras, abokina cikin Almasihu Yesu a kurkuku yana gaishe ka, 24 haka ma Markus da Aristarkus, da Dimas, da Luka abokan aikina. 25 Bari Alherin Ubangiji Yesu Almasihu ya kasance da Ruhunka. Amin.
Sau uku Bulus ya nuna kansa a matsayin marubucin wannan wasiƙar. A fili yake cewa Timoti yana tare da Bulus lokacin rubuta wannan wasiƙar, kuma babu mamaki Timotawus ne ya rubuta wasiƙar lokacin da Bulus yake faɗin kalaman. Bulus ya miƙa gaisuwar sa ga wanɗanda ke ikilisiyar da ke taruwa a gidan Filimon.
Mai yiwuwa harshen ka na da wata hanyar ta da take gabatar da marubucin wasiƙa. AT: "Ni, Bulus, ɗan sarka saboda Almasihu Yesu, da kuma Timotawus, ɗan'uwan mu, na rubuta wannan wasiƙa zuwa ga Filimon"
"ɗan sarka saboda Almasihu Yesu." mutanen da suka yi tsayanya da wa'azin Bulus sun horas da shi ta wurin jefa shi a kurkuku.
A nan wannan na nufin abokin aiki mabiyin addinin kirista
wannan kalmar "mu" na nufin Bulus da wanda suke tare.
"wanda yake kamar mu, yake aikin shelar bishara"
A nan "'yar'uwa" na nufin ita daga zumuntar masubi ne. AT: "maibi ce abokiyar aikinmu Afiya" ko "Afiya yar'uwarmu ta ruhaniya ce"
Wannan sunar mutum ne da ke ikilisiya ɗaya da Filimon.
Bulus ya yi magana a nan game da Arkifus kamar su sojoji ne a filin daga. Yana nufin Arkifus mai kwazo ne kwarai, kamar yadda Bulus kansa mai kwazon shelar bishara ne. AT: "abokin aikin mu jarumin mayaƙi na ruhaniya" ko "jarumin mayaƙi wanda yayi faɗa na ruhaniya tare da mu"
"Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Almasihu shi ba ku alheri da salama." Wannan albarka ne.
A nan kalmarnan "mu" na nufin Bulus, da waɗanda suke tare, da masu karanta wasiƙar.
Wannan muhimmin sunan Allah ne.
"domin aikin ka tare da mu"
"ya kai ga sanin abin da ke mai kyau"
"saboda Almasihu"
"Zukata" a nan shine shauƙi ko can cikin mutum. Za a iya ambatarsa a fannoni daban-daban. AT: "ya kan ƙarfafa masu bi" ko "ya taimakawa masu bi"
"ɗan'uwa na ƙwarai," ko "aboki." Bulus ya kira Filimon "ɗan'uwa" domin su masu bi ne kuma domin ya ƙarfafa cewa su abokai ne.
Bulus ya fara da roko da bayyana dalilin wasiƙar sa.
AT: 1) "ƙarfin iko saboda Almasihu" ko 2) "ƙarfin hali saboda Almasihu." "Ƙarfin hali saboda Almasihu ya ba ni ƙarfin iko"
AT: 1) "soboda na san yanda kake ƙaunar mutanen Allah" 2) "saboda kana ƙauna ta" ko 3) "soboda ina ƙaunar ka"
"ɗana Onisimus." Bulus ya yi magana game da abokantakar su da Onisimus kamar yanda uba ya ke ƙaunar ɗansa. Ba wai Onisimus ɗan Bulus ne na asali ba, amma ya karbi koyarwa ta ruhaniya game da Yesu ta wurin Bulus ne, kuma Bulus ya ƙaunace shi. AT: "Onisimus ɗana na ruhaniya"
Wannan suna "Onisimus" na nufin "riba" ko "mai amfani"
A nan "uba" na nufin cewa Bulus ne ya canza Onisimus zuwa mataki na sannin Almasihu. AT: "wanda ya zama ɗa na ruhaniya a gare ni, na koyar da shi game da Almasihu ya kuma karɓi sabon rayuwa yayinda ina sarƙoƙina" ko "wanda ya zama kamar ɗa a gare ni yayinda ina cikin sarƙoƙina"
'Yan kurkuku kunlum na cikin sarƙoƙi. Bulus ya koyar da Onisimus sa'anda yana cikin kurkuku, a cikin kurkuku kuma ya rubuto wannan wasiƙa. AT: "... yayin da ina cikin kurkuku"
Ya yiwu Bulus ya aiki Onisimus tare da wani mai bi dauke da wannan wasiƙa.
A nan "zuciya" na nuna shauƙi na mutum. wannan jimla "wanda ya ke a cikin zuciyata kwarai" na nuna ƙauna da wani ke da shi ga wani. Bulus na faɗin wannan game da Onisimus. AT: "wanda nake ƙauna sosai"
"domin shi zai taimake ni, tun da bazaka kasance a nan ba" ko "domin shi zai iya taimako na a madadin ka"
Bulus ya shigga kurkuku sabo da ya yi shelar bishara a fili. AT: "sabo da na yi shelar bishara a fili"
Bulus ya ambaci abubuwa biyu domin ya sadar da akasin abin da ya ambato. AT: "Amma na so in rike shi a wurina tare da yardarka"
"Ba ni so ka yi nagarin aiki domin na sa ka tilas, saidai domin ka so aikata wa"
"amma domin ka zaɓa ka aikata abu mai kyau"
AT: "Watakila dalilin da ya sa Allah ya dauki Onisimus daga gare ka na ɗan lokaci domin kă"
"a wannan lokacin"
"mai muhimmanci fiye da bawa"
"ɗan'uwa na ƙwarai" ko "ɗan'uwa mai daraja cikin Almashihu"
"ya fi kasance wa da daraja a gareka"
" a matsayin mutum." Bulus na nufin Onisimus wanda ya kasance amintaccen bawa.
"kamar ɗan'uwa a cikin Ubangiji" ko "domin shi na Ubangiji ne"
"idan kayi tunanina a matsayin abokin aiki na Almasihu"
"ka faɗa cewa ni ke rike da basussukan ka"
"Ni, Bulus, na rubuta wannan da kaina." Bulus ne ya rubuto wannan sashi da hannun sa, saboda Filimon ya sa ni kalmomin daga Bulus ne. Da gaske Bulus zai biya shi.
"Ba sai na tunashe ka ba" ko "Ka riga ka sani." Ko da shike Bulus na faɗin cewa bai kamata ya faɗa wa Filimon wannan ba, amma ya cigaba da faɗin hakan. Faɗin hakan ya ƙarfafa gaskiyar abinda Bulus ke faɗa masa.
"ina bin ka bashin rayuwar ka." Bulus na faɗin cewa kada Filimon ya ga kamar yana bin Onisimus ko Bulus bashin wani abu domin Bulu na bin Filimon bashi mai yawa. Dalilin kuma shi ne Bulus na bin Filimon bashin ran sa. AT: "kana riƙe da bashi na mai yawa domin na ceci rayuwar ka" ko "abin da na faɗa maka ya ceci rayuwar ka, soboda haka ina bin ka bashin rayuwar ka"
A nan "hutu" na nufin ta'aziya ko karfafawa. A nan "zuciya" kuma na nufin yanda mutum ke ji, tunani, ko cikin jiki. Bulus ya so Filimon ya ba wa zuciyarsa hutu. AT: "ka karfafa ni a cikin Almasihu" ko "ka ta'azantar da ni a cikin Almasihu" ko "ka ba zuciyata hutu a cikin Almasihu ta wurin karɓar Onisimus"
"Saboda ina da tabbaci za ka iya yin abin da na roƙa"
"Kuma"
"ka shirya mini masauki a gidanka." Bulus ya roƙi Filimon ya masa wannan.
zan sami 'yanci na komowa wurin ku daga waɗanda suka ajiyeni a kurkuku.
Wannan mai bi ne da ke kurkuku tare da Bulus
"wanda yana kurkuku tare da ni saboda bautar Almasihu Yesu"
"Markus da Aristarkus, da Dimas, da Luka abokan aikina, suna gaisheku"
Waɗannan sunayen maza ne
"mazajen da suke aiki tare da ni" ko "dukan waɗanda suna aiki tare da ni."
Kalmar nan "ku" na nufin Filimon da dukan waɗanda suna tattaruwa a gidansa. Kalmar nan "ruhunku" yana nufin mutane da kansu. AT: "Bari Ubangijin mu Yesu Almasihu shi yi maku alheri"
Bulus ya na kurkuku a lokacin da ya rubuta wannan wasikar.
Wannan wasikar an rubuta ta zuwa ga Filimon ne , aminin Bulus da kuma abokin aikin sa.
Ikklisiyar na saduwa a gida ne.
Bulus ya ji labarin Kaunar Filimon, bangaskiyarsa a Ubangiji, da kuma amincinsa ga dukan tsarkaka.
Filimon ya wartsake zuciyar tsarkaka.
Bulus yana kurkuku a lokacin da rubuta wannan wasiƙar.
Bulus yana tambayar Filimon saboda kauna.
Bulus ya zama Uban Onisimus a lokacin da yake kurkuku.
Bulus ya aike Onisimus ya koma zuwa ga Philimon.
Bulus yana kurkuku ne a lokacin da ya rubuta wannan wasiƙar
Bulus zai so Unisimas ya iya taimakonsa.
Bulus zai so Filimon ya yantad da Unisimus, ya kuma yadda wa Unisimus ya koma wurin Bulus.
Bulus ya na so Filimon ya dubi Unisimas a matsayin ɗanuwarsa kaunatacce.
Bulus ya na so ya biya Filimon dukan basussukan da Unisimus yake riƙe masa.
Filimon yana rike wa Bulus bashin ransa ne.
I, Bulus na da tabbacin cewa Filimon zai aiko Onisimus zuwa wurinsa.
Bulus zai je ya kuma ziyarce Filimon idan an sake shi daga kurkuku.
1 A zamanin da, Allah ya yi wa kakanin kakanninmu magana ta hanyoyi ma su yawa iri iri, ta bakin annabawa. 2 Amma a zamanin nan na karshe, ya yi mana magana ta wurin Dansa, wanda ya sa magajin kome, wanda ta wurinsa ya halicci duniya. 3 Shi ne hasken daukakar Allah, ainihin kamanin zatinsa. Ya na rike da dukkan abubuwa ta ikon kalmarsa. Bayan da ya tsarkake zunubanmu, sai ya zauna a hannun dama na madaukaki a can sama. 4 Ta haka ya ke da fifiko a kan mala'iku, kamar yadda sunansa da ya gada yake da fifiko nesa a kan nasu. 5 Domin kuwa wanene a cikin mala'iku Allah ya taba cewa, "Kai Da na ne, yau na zama Uba a gare ka?" kuma, "Zan kasance Uba a gareshi, shi kuma, zai kasance Da a gare ni?" 6 Kuma, da Allah ya kawo magaji a duniya, sai ya ce, "Dukan mala'ikun Allah su yi masa sujada." 7 A game da mala'iku kuma sai ya ce, "yakan mai da mala'ikunsa ruhohi, masu hidimarsa kuma harsunan wuta. 8 A game da Dan, ya ce "kursiyinka, ya Allah, na har abada abadin ne. Sandar sarautarka sanda ce ta tsantsar gaskiya. 9 Ka kaunaci aikin adalci, ka ki aikin sabo. Saboda haka Allah, wato Allahnka, ya shafe ka da man farin ciki fiye da tsararrakinka." 10 "Tun farko, Ubangiji, kai ne ka hallici duniya. Sammai kuma aikin hannayenka ne. 11 Za su hallaka, amma kai madawwami ne. Duk za su tsufa kamar tufafi. 12 Za ka nade su kamar mayafi, za su kuma sauya, amma kai kana nan ba sakewa, Har abada shekarunka ba za su kare ba." 13 Amma wanene a cikin mala'ikun Allah ya taba cewa, "Zauna a hannun dama na, sai na sa makiyanka a karkashin kafafunka?" 14 Ashe, ba dukkan mala'iku bane ruhohi, wadanda Allah yakan aika, don su yi wa wadanda za su gaji ceto hidima?
Kodashike wannan wasiƙar bata ambaci masu karɓan ta ba waɗanda aka aika masu, marubucin dai ya rubuto wannan wasiƙar musamman zuwa ga Yahudawa, waɗanda sun fi fahimtar misalai da dama da ya bayar daga Tsohon Alkawari.
"a waɗannan kwanakin ƙarshen." Jmlar na nufin lokacin da Yesu ya fara hidimarsa, har zuwa sa'ada Allah zai ƙaddamad da cikakken mulkin sa a bisa halitarsa.
"Ɗa" a nan wata laƙabi ce mai muhimmanci na Yesu, Ɗan Allah.
Marubucin yana maganar Ɗan kamar zai gaji wata arziki ne ko dukiya daga Ubansa. AT: "yă mallaki dukan komai"
"Ta wurin Ɗan ne Allah ya halici dukkan komai"
"hasken ɗaukakarsa." A nan an haɗa ɗaukakar Allah ne da wuta mai haske kwarai. Marubucin yana cewa Ɗan yana ɗauke da hasken, yana kuma wakilcin ɗaukakar Allah.
"ɗaukaka, sifar Allah." "Ainihin kamaninsa" ya na da ma'ana kusan ɗaya ne da "hasken ɗaukakarsa." Ɗan yana ɗauke da hali da allahntakar Allah, yana kuma wakilcin dukkan koman da Allah yake. AT: "ɗaukaka yana kuma kamar Allah" ko kuma "ɗaukaka, kuma abinda ke gaskiya game da Allah, gaskiya ne game da Ɗan"
"kalmarsa mai iko." A nan "kalma" na nufin wata sako ko umurni. AT: "umurnin sa mai iko"
"tsarkakewa" AT: "bayan da ya gama tsarkakemu daga zunubanmu"
Marubucin yana maganar gafarar zunubai kamar tsarkake mutum ne. AT: "ya sa shi abu mai yiwuwa Allah yă gafarta zunubanmu"
Zama a "hannun damar Allah" alama ce na samun girma da iko daga wurin Allah. AT: "yana zaune a wurin girma da iko a gefen Zatinsa a can sama"
A nan "Zatinsa" na nufin Allah. AT: "Allah maɗaukaki"
"Ɗan ya zama"
A nan "suna" na nufin daraja da iko. AT: "yadda daraja da ikon da ya gãda ke da girma fiye da daraja da ikonsu"
Marubucin yana maganar samun girma da iko a wurin Allah kamar gãdan arziki ne da kuma dukiya mai yawa daga Ubansa. AT: "ya karɓa"
Wannan tambayan na nanata cewa Allah bai taɓa ce da wani mala'ika ɗansa ba. AT: "Domin Allah bai taɓa ce wa wani mala'ikansa 'kai ɗa ne ... ɗa a gare ni ba."
Waɗannan jumloli biyun na nufin abu ɗaya ne.
Wato Yesu kenan. Marubucin yana ce da shi "ɗan fãri" ne domin ya nanata muhimmanci da ikon Ɗan a bisa kowa. Wannan bai nuna cewa Yesu ya taɓa fara kasancewa a wani lokaci a baya ba ko kuma cewa Allah yana da wasu 'ya'ya kuma kamar Yesu ba. AT: "Ɗansa mai girma, tilonsa"
"Allah ya ce"
Wannan na iya nufin 1) "Allah ya sa mala'ikunsa su zama ruhohi, masu bauta masa da iko kamar harsunan wuta" ko kuma 2) Allah ya sa iska da harsunan wuta su zama ''yan aika da kuma masu hidimarsa. A ainihin harshen, kalmar nan "mala'ika" na da ma'ana ɗaya da "ɗan aika" sa'annan kalmar nan "ruhohi" na da ma'ana ɗaya da "iska." Ko ma ta yaya, kwayar maganar itace mala'ikun suna bauta wa Ɗan domin ya fi su girma.
"Amma Allah ya faɗa haka wa Ɗan"
Wannan wani laƙabi ne na Yesu mai muhimmanci, Ɗan Allah.
Kursiyin Ɗan na madadin mulkinsa. AT: "Kai Allah ne, kuma mulkinka zai cigaba har abada abadin"
A nan "sanda" na nufin mulkin Ɗan. AT: "Kuma za ka yi mulki a bisa mutanen ka da gaskiya"
A nan "man farin ciki" na nufin farin cikin da Ɗan yayi yayin da Allah ya girmama shi. AT: "ya girmama ka, ya kuma sa ka zama mai farinciki fiye da kowa"
Marubicin ya cigaba da bayani cewa Yesu ya fi mala'iku.
"kafin komai ma ya kasance"
Marubucin yana maganar yadda Allah ya halicci duniya ne kamar ya yi gini ne a bisa harsashi. AT: "kai ne ka halicci duniya"
A nan "hannaye" na nufin ikon aikin Allah. AT: "Kai ne ka hallici Sammai"
"Sammai da ƙasa duk za su shuɗe" ko kuma "Sammai da ƙasa za su daina kasancewa"
Marubucin na maganar sammai da ƙasa kamar su tufafi ne da za su tsufa har su zama marasa amfani.
Marubucin yana maganar sammai da kasa kamar wasu tufafi ne ko wasu irin riguna ne da ake iya yafa su a kan riguna.
Marubucin yana maganar sammai da kasa kamar su taguwa ne ko wata irin mayafi ne da ake iya sauyasu.
AT: "za ka sauya su"
Ana amfani da tsawon lokaci a madadin kasancewar Allah ta har abada. AT: "ranka ba za ta taɓa ƙarewa ba"
Marubucin yana amfani ne da wannan tambayan don ya nanata cewa Allah bai taɓa faɗin haka wa wani mala'ika ba. AT: "Amma Allah bai faɗa wa wani mala'ika ... ƙafafu"
A zauna a "hannun dama na Allah" wata alama ce ta samun babban girma da iko daga Allah. AT: "Zauna a wurin girma a gefe na"
Ana maganar maƙiyan Almasihu kamar za su zama wani abun taka wa ne da sarki ke taka wa da ƙafafunsa a fãda. Wannan sifar na nuna nasara da rashin daraja ga maƙiyansa.
Marubucin yana amfani ne da wannan tambayan domin ya tunashe da masu karanta wannan wasiƙar cewa mala'iku basu da iko kamar Almasihu, amma suna da nasu hidima dabam. AT: "Dukkan mala'iku ruhohi ne waɗanda ... gaji ceto"
Ana maganar samun abinda Allah ya alkawarta wa masubi kamar gadan dukiya ne ko kuma arziki daga wani ɗan iyali. AT: "ga dukkan waɗanda Allah zai ceta"
Allah ya yi magana a dã ta wurin annabawa a lokatai da yawa a ta hanya masu yawa.
Allah ya yi magana a waɗannan kwanaki ta wurin Ɗa.
An halici duniya ta wurin Ɗan Allah.
An riƙe dukkan abubuwa ta wurin kalmar ikon Ɗan Allah
Ɗan shine hasken ɗaukakar Allah da kuma ainihin halin Allah.
Ɗan Allah ya fi mala'ikun fifiko.
Allah ya ummurci mala'iku su yi wa Ɗan sujada sa'ad da ya shigo cikin duniya.
Ɗan zai yi mulki a matsayin sarki har abada abadin.
Ɗan na ƙaunar adalci, ya kuma ƙi jinin rashin bin doka.
Duniya da sammai za su shuɗe kamar yadda tufafi ke lalacewa.
Allah ya ce wa Ɗan ya zauna a hannun damansa har sai ya sa abokan gãbansa sun zama mazaunin kafan Ɗan.
Mala'ikun suna kula da waɗanda za su gãji ceto.
1 Saboda haka, lalle ne mu kara mai da hankali musamman da abubuwan da mu ka ji, don kada mu yi sakaci, su sullube mana. 2 Idan kuwa maganar nan da aka fada ta bakin mala'iku ta zama tabbatacciya, har kowanne keta umarni da rashin biyayya, suka gamu da sakamakonsu wanda ya kamace su, 3 ta kaka za mu tsira, in mun ki kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji da kansa, shi ne ya fara sanar da shi, wadanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi. 4 San'nan kuma Allah da kansa ya shaida ta wasu alamu, da abubuwan al'ajabai, da mu'ajizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa. 5 Ai ba ga mala'iku ba ne Allah ya sa mulkin duniyar nan da za a yi, wanda muke zance. 6 Amma wani ya shaida a wani wuri cewa, "Mutum ma menene, har da za ka tuna da shi? Ko dan mutum ma, har da za ka kula da shi? 7 Ka sa mutum ya gaza mala'iku; Ka nada shi da daukaka da girma. Bisa dukkan hallitta. 8 Ka dora shi a kan dukkan halittarka, ka kuma mallakar da kome a karkashin sawayensa. Domin Allah ya mallakar da dukkan abubuwa a karkashinsa. Bai bar kome a kebe ba. Amma kuwa har a yanzu ba mu ga yana sarrafa dukkan abubuwa ba tukuna. 9 Amma mun ga wani wanda dan lokaci aka sa shi ya gaza mala'iku, shine Yesu, an nada shi da daukaka da girma, saboda shan wuyarsa ta mutuwa, wanan kuwa duk ta wurin alherin Allah ne Yesu ya mutu saboda kowa. 10 Saboda haka, ya dace ga Allah, shi da dukkan abubuwa suka kasance domin sa, ta gare shi, domin ya kawo 'ya'ya masu yawa ga samun daukaka. Domin a kammala cetonsu ta wurin shan wuyarsa. 11 Domin da shi mai tsarkakewar da kuma wadanda aka tsarkaken, duk tushensu daya ne. Saboda wanan dalili ne shi ya sa ba ya jin kunyar kiran su 'ya'uwansa. 12 Da yace, "zan sanar da sunanka ga ya'uwana, a tsakiyar taronsu zan yabe ka da waka." 13 Har wa yau, yace, "Zan dogara a gare shi." Da kuma "Ga ni nan, ni da 'ya'yan da Allah ya ba ni." 14 Wato tun da yake 'ya'yan Allah duk suna da nama da jini, Yesu ma ya dauki kamannin haka, ta wurin mutuwa ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato Iblis. 15 Ya kuma 'yanta duk wadanda tun haihuwarsu suke zaman bauta sabo da tsoron mutuwa. 16 Don hakika ba mala'iku yake taimako ba, a'a, zuriyar Ibrahim ne yake taimako. 17 Saboda haka, lalle ne ya zama kamar yan'uwansa ta kowacce hanya, domin ya zama babban Firist, mai jinkai, mai aminci kuma na al'amarin Allah, ya kuma mika hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama'a. 18 Tun da yake Yesu ma da kansa ya sha wahala, sa'adda aka gwada shi, don haka, zai taimaki wadanda ake yi wa gwaji.
Wannan shi ne na farko cikin kashedi biyar da marubucin ya bayar.
A nan "mu" na nufin marubucin a haɗe da masu sauraro.
Wannan na iya nufin 1) ana maganar mutanen da sun daina gaskatawa da Allah ne kamar suna sulluɓewa, kamar yadda kwalekwale ke sulluɓewa daga wurin tsayawarsa a ruwa. AT: "domin kada mu daina gaskantawa da shi" ko kuma " 2) ana maganar mutanen da sun daina gaskantawa da maganar Allah kamar suna sulluɓewa ne, kamar yadda kwalekwale ke sulluɓewa daga wurin tsayawarsa a ruwa. AT: "domin kada mu daina biyayya da shi"
Yahudawa sun gaskanta da cewa Allah ya ba da shari'ar sa wa Musa ta wurin mala'iku. AT: "Idan kuwa maganar nan da Allah ya yi ta wurin mala'iku"
Marubucin na da tabbaci cewa waɗannan abubuwa gaskiya ne. AT: "Domin maganar"
A nan "keta" da "rashin biyayya" na tsaye ne a madadin mutanen da ke da laifin waɗannan zunuban. AT: "duk mutumin da ya yi zunubi ya kuma yi rashin biyayya zai gamu da sakamako"
Waɗannan kalmomi biyun a takaice na nufin abu ɗaya.
Marubucin na amfani ne da wannan tambaya domin ya nanata cewa mutanen za su gamu da hukunci idan sun ƙi ceton Allah ta wurin Almasihu. AT: "lallai ne Allah zai hukunta mu idan ba mu kasa kunne ga maganarsa game da yadda zai cece mu ba!"
"ƙi kasa kunne" ko kuma "ɗauke shi da rashin muhimmanci"
AT: "Ubangiji ne da kansa ya fara sanar da wannan sako game da yadda Allah zai cece mu, sa'annan waɗanda suka ji sun tabbatar mana da shi"
"yadda dai yake so ya yi"
Ambacin da ke nan daga littafin Zabura ne a Tsohon Alkawali. Ya cigaba har zuwa sashi na gaba.
"Allah bai sa mala'iku su yi mulki bisa"
A nan "duniya" na nufin mutanen da suke kasancewa a wurin. "za a yi" kuma na nufin duniya da za a yi bayan da Yesu ya dawo. AT: "mutanen da za su kasance a sabuwar duniya da za ayi"
Wannan tambayan ne da ke nanata cewa mutum ba komai ba ne, yana kuma nuna yadda ya zama abun mamaki yadda Allah ke sa hankalinsa a kansu. AT: "mutane ba komai bane, kuma duk da haka kana tunawa da su!"
Wannan karin maganar "ɗan mutum" na nufin 'yan adam. Wannan tambayar na da ma'ana ɗaya ne da na farkon. Yana nuna yadda ya zama abun mamaki yadda Allah ke kula da mutane, wadda ba komai ba ne. AT: "Muhimmancin mutane kaɗan ne, duk da haka kana kula da su!"
AT: "ko wanene ɗan mutum"
Marubucin yana maganar yadda mutane sun gaza a muhimmanci kamar suna tsaye ne a matsayi da ya gaza matsayin mala'iku. AT: "basu da muhimmanci kamar mala'iku"
Waɗannan duka na nufin mutane gabaɗaya, a haɗe da maza da mata. AT: "sa mutane ... ka naɗa su ... sawayensu ... gă su"
Ana maganar kyautar ɗaukaka da girma kamar wata rawani ce a kan ɗan wasan guje-guje da tsalle-tsalle. AT: "kã basu babban girma da ɗaukaka"
Marubucin yana maganar mulkin mutane bisa kowane abu kamar sun taka kowane abu da ƙafafunsu ne. AT: "ka basu mulki bisa kowane abu"
Wannan na nufin cewa dukkan abubuwa za su zama a ƙarƙashin Almasihu. AT: "Allah ya sa su suna mulki bisa dukkan komai"
"Mun san cewa har yanzu mutane basu mulkin dukkan komai"
"mun san akwai wani"
AT: "wadda Allah ya sa"
Duba yadda aka yi fassar wannan a [2:7]
AT: "yă ɗanɗana mutuwa"
AT: "ceci 'ya'ya masu yawa"
A nan wannan na nufin masubin Almasihu, maza da mata. AT: "masubi da yawa"
Wannan na iya nufin 1) wannan wata karin magana ce da marubucin yana zancen ceto kamar wani wuri ne na zuwa , kuma Yesu shi ne wadda ya je wannan wurin kafin jama'ar da ke hanya, yana kuma kai su ga samun ceto. AT: "mai kai jama'a ga samun ceto" ko kuma 2) kalmar da aka fassara a nan "shugaba" na iya nufin "mai kafa" kuma marubucin yana magana ne game da Yesu wanda shi ne ya kafa ceto, ko ya sa shi ya zama abu mai yiwuwa wa Allah ya ceci mutane. AT: "wadda ya sa samun ceto ya zama abu mai yiwuwa"
Ana maganar manyanta da kammalawa kamar mutum ya zama kammalalle ne, mai yiwuwa kammalalle a dukkan gabobin jikinsa.
"mai sa mutane su zama da tsarki" ko kuma "mai tsarkake mutane daga zunubi"
AT: "mutanen da ya tsarkake" ko kuma "mutanen da ya tsarkake daga zunubi"
Za a iya bayyana wannan tushen a fili. AT: "na da tushe ɗaya" ko kuma "na da Uba ɗaya"
"Yesu baya jin kunya"
Wannan na nufin ya ɗauke su a matsayin 'yan'uwansa. AT: "yana farin cikin kiransu 'yan'uwasa"
A nan wannan na nufin dukkan waɗanda suka ba da gaskiya ga Yesu, maza da mata.
A nan "suna" na nufin halin mutum da kuma abinda ya yi. AT: "zan sanar wa 'yan'uwana manyan abubuwan da ka yi"
"yayin da masubi sun taru su yi wa Allah sujada"
"Kuma wani annabi ya rubuto a wata nassi abinda Almasihu ya faɗa game da Allah:"
Wannan na maganar waɗanda suka gaskata da Almasihu kamar su 'ya'ya ne. AT: "waɗanda ke kamar 'ya'ya ... waɗanda ke kamar 'ya'ya a gaban Allah"
Wannan jumlar "nama da jini" na nufin ainihin mutuntakar mutane. AT: "su duk 'yan' adam ne"
"Yesu ya zama ɗan adam kamar su"
AT: "ta rasuwa"
AT: "na da ikon sa mutane su mutu"
Ana maganar tsoron mutuwa kama bauta ne. Ana kuma maganar 'yantar da mutum daga tsoro kamar 'yantar da mutum ne daga bauta. AT: "Wannan saboda ya 'yantar da dukkan mutane ne. Gama mun yi rayuwa kamar bayi domin muna tsoron mutuwa."
...
"ya zama lallai ne wa Yesu"
A nan "'yan'uwa" na nufin mutane gabaɗaya. AT: "kamar 'yan adam"
Mutuwar Almasihu a bisa giciye na nufin cewa Allah na iya gafarta zunubai. AT: "zai sa shi ya yiwu Allah ya gafarta zunuban jama'a"
AT: "Shaiɗan ya gwada shi"
AT: "wadda Shaiɗan ke yi wa gwaji"
Lallai ne masubi su kassa kunne ga abind a suka ji don kada su kauce da abin da suka ji.
Kowane laifi da rashin biyayya na kawo hukuncin adalci.
Allah ya shaida sakon ta wurin alamu da abubuwab ban mamaki da al'ajibi da kuma ta wurin kyautar Ruhu Mai Tsarki.
Mala'iku ba za su yi mulkin duniyan nan mai zuwa ba.
Mutum ne zai yi mulkin duniyan nan mai zuwa.
An sa wa Yesu rawani ta ɗaukak da daraja saboda wahalar da ya sha da mutuwarsa.
Yesu ya ɗanɗana mutuwa saboda kowane mutu.
Allah ya yi shirin kai 'ya'yansa ga ɗaukaka.
Da mutumin da ke tsarkakewa da waɗanda aka tsarkake duk daga wuri ɗaya ne, daga Allah.
An mashe da ibilis mara tasiri ta wurin mutuwar Yesu.
Ta zama da muhimmanci domin ya zama mai jinkai da kuma babbar firist mai adalci bisa abubuwan na Allah, domin kuma ya yafe zunuban mutanen.
Yesu ya yi taimakon waɗanda aka gwada su domin shi ma an gwada shi.
1 Don haka yanuwana tsarkaka, a bokan kira a samaniya. Yi la'akari da Yesu. wato Manzo da babban firist na shaidar bangaskiyarmu. 2 Shi amintacce ne na Allah, wanda ya bashi hidima, kamar yadda Musa ya kasance amintacce a gidan Allah. 3 Gama Yesu ya cancanci daukaka mafi girma fiye da ta Musa. Domin wanda ya gina gida, ya fi gidan nan daukaka. 4 Gama kowane gida, akwai wanda ya gina shi, amma mai ginin komai shine Allah. 5 Musa hakika amintaccen bawa ne a gidan Allah, yana ba da shaidar abubuwan da za su faru a nan gaba. 6 Amma Almasihu shi Da ne mai mulki a gidan Allah. Mu ne gidansa idan mun rike begenmu da dukkan zuciyarmu. 7 Saboda haka, kamar yadda Ruhu Mai Tsarki ya fadi: "Yau, Idan kun ji muryarsa, 8 kada ku taurare zuciyarku kamar yadda 'ya'yan isra'ila suka yi cikin tawaye a lokacin gwaji a jeji. 9 A lokacin nan ne kakanninku suka yi mani tawaye, ta wurin gwada ni, bayan shekara arba'in suna ganin ayyukana. 10 Saboda haka na yi bakin ciki da wannan tsarar, sai na ce,' Kullum suna yawan bijirewa a zukatansu. Basu san tafarkuna ba.' 11 Don haka na yi rantsuwa a cikin fushina, ba za su shiga cikin hutuna ba." 12 Ku yi hankali 'yan'uwa kada a tarar da mummunar zuciya marar bangaskiya a tsakaninku, zuciya wadda ke juyawa daga Allah mai rai. 13 Maimakon haka, ku karfafa juna a kowacce rana, muddun muna cikin wannan rana kada wani cikinku ya taurare zuciyarsa saboda yaudarar zunubi. 14 Gama mun zama abokan aiki da Almasihu, idan mun rike begenmu cikinsa da karfi, daga farko zuwa karshe. 15 Game da wannan, an fadi "Yau idan kun saurari muryarsa, kada ku taurare zuciyarku, kamar a kwanakin tawaye nan." 16 Su wanene suka ji muryar Allah suka yi tawaye? Ba wadanda Musa ya yi masu jagora daga Masar ba ne? 17 Kuma da su wa Allah ya yi fushi shekara arba'in? Ba da wadanda suka yi zunubi ba ne, wadanda gawawwakinsu suka warwatsu a jeji? 18 Da su wa Allah ya rantse ba za su shiga hutunsa ba? In ba wadanda suka yi masa rashin biyayya ba? 19 Mun kuma gani cewa basu iya shiga hutunsa ba saboda rashin bangaskiyarsu.
Kashedi na biyun ya fi tsawo, da kuma bayani, ya kuma haɗa da surori 3 da 4. Marubucin ya fara ta wurin nuna cewa Almasihu ya fi bawansa Musa.
A nan 'yan'uwa na nufin masubi kirista, maza da mata.
A nan "samaniya" na nufin Allah. AT: "Allah ya kiraye mu tare"
A nan kalmar nan "manzo" na nufin wanda aka aiko. A wannan nassi, ba ya nufin ko ɗaya daga cikin manzanni goma-sha-biyun. AT: "shi wadda Allah ya aiko kuma shi ne babban firist"
AT: "wadda muka furta" ko kuma "wadda muka ba da gaskiya
Ana maganar mutanen Yahudawa wadda Allah ya bayyana kansa masu kamar su gida ne. AT: "zuwa ga dukkan mutanen Allah"
AT: "Allah ya mai da Yesu mutumin da ya cancanci"
Ana maganar ayyukan hallitar duniya da Allah ya yi ne kamar ya gina gida ne.
kowane gida na da wanda ya gina shi
Ana maganar mutanen Yahudawa da Allah ya bayyana kansa a garesu kamar su zahirin gini ne. Dubi yadda kun fassara wannan a [3:2]
Wannan jumlar na maganar aikin Musa. AT: "Rayuwar Musa da aikinsa sun nuna waɗannan abubuwa"
AT: "Yesu zai faɗa nan gaba"
Wannan wata laƙabi ne mai muhimmanci na Yesu, Ɗan Allah.
AT: "wadda ke mulkin jama'ar Allah"
AT: "Mu ne jama'ar Allah"
AT: "idan mun cigaba da ƙarfin hali da farin cikin jira Allah ya cika alkwarinsa"
Ambacin da ke nan daga littafin Zabura ne a Tsohon Alkawari.
"muryar" Allah na nufin maganar sa. AT: "yayin da kun ji maganar Allah"
A nan "zuciya" na nufin hankalin mutum. Jumlar nan "taurare zuciya" na nufin zama gagararre. AT: "kada ku zama gagararru" ko kuma "kada ku ƙi ji
AT: "kamar yadda kakanninku suka yi wa Allah tawaye, suka gwada shi a jeji"
Wannan na nufin jama'ar Isra'ila.
A nan "ni" yana nufin Allah.
"shekara 40"
"na yi fushi" ko kuma "ban ji daɗi ba ko kaɗan"
A nan "bijerewa a zukatansu" na nufin rashin aminci ga Allah." A nan "zukata" na nufin hankalin mutum ko kuma marmarinsa. AT: "suka riƙa ƙi na" ko kuma "suka riƙa ƙi yi mani biyayya"
Wannan na maganar yanayin bi da rayuwar mutum ne kamar wata tafarki ne ko kuma hanya. AT: "Ba su fahimci yadda na ke so su bi da rayuwarsu ba"
An yi maganar salama da tsaron da Allah ke tanadawa kamar wata hutu ce da yake bayar wa, kuma kamar wata wuri ce da mutane ke iya zuwa. AT: "Ba za su taɓa shiga wurin hutu ba" ko kuma "Ba zan taɓa barin su su ɗanɗana albarkun hutuna ba"
Wannan na nufin masubi, maza da mata. AT: "'yan'uwa masubi"
A nan "zuciya" na nufin hankalin mutum ko kuma ra'ayi. An yi maganar rashin ba da gaskiya da rashin biyayya ga Allah kamar zuciyar da ta juya wa Allah ne a ganin idon mutane. AT: "kada a tarar da kowa a cikinku da ya ƙi gaskiya, ya kuma daina yi wa Allah mai rai biyayya"
"Allah na gaske da ke da rai"
"tun da sauran zarafi"
AT: "yaudarar zunubi ba zai taurare kowa daga cikinku ba"
A nan "mu" na nufin marubucin da masu karatu.
"idan mun cigaba da dogara gareshi da gabagaɗi"
"daga lokacin da muka fara gaskatawa da shi"
Wannan wata hanya ce ta maganar har lokacin mutuwar mutum. AT: "har zuwa mutuwarmu"
AT: "marubucin ya rubuta"
Duba yadda aka fassara wannan a [3:8]. AT: "kamar yadda kakanninku suka yi wa Allah tawaye"
Marubucin yana amfani ne da waɗannan tambayoyin ya koya wa masu karatun wannan wasiƙa. Ana iya haɗin waɗannan tambayoyin a jumla ɗaya, idan akwai bukatar yin haka. AT: "Dukkan waɗanda suka fito daga Masar tare da Musa sun saurari Allah, duk da haka sun yi tawaye."
Marubucin yana amfani ne da waɗannan tambayoyin ya koya wa masu karatun wannan wasiƙa. Ana iya haɗa waɗannan tambayoyin a jumla ɗaya, idan akwai bukatar yin haka. AT: "Har shekaru arba'in, Allah ya yi fushi da waɗanda sun yi zunubi, ya kuma sa suka mutu a jeji."
Marubucin ya yi amfani ne da wannan tambayar domin yă koya wa masu karatun wannan wasika. AT: "Kuma ga waɗanda suka yi rashin biyayya ne ya rantse cewa ba za su taɓa shi hutunsa ba."
An yi maganar salama da tsaron da Allah ke tanadawa kamar wata hutu ce da yake bayar wa, kuma kamar wata wuri ce da mutane ke iya zuwa. AT: "Ba za su taɓa shiga wurin hutu ba" ko kuma "Ba zan taɓa barin su su ɗanɗana albarkun hutuna ba" (Dubi: )
AT: "domin basu gaskata da shi ba"
Marubucin ya ba wa Yesu lakabin Manzani da kuma Babban Firist.
An dubi Yesu wa matsayin wanda ya cancanci ɗaukaka saboda sa'ad da Musa ya zama mai adalci a gidan Allah, Yesu kuwa shine wanda ya gina gidan.
Musa ya bada shaida game da abubuwan da za a yi magana game su nan gaba.
Musa bawa ne a gidan Allah.
Yesu shine wanda ke mulki a gidan Allah.
Masubi sune gidan Allah idan sun riƙe gabagaɗin sun da ƙarfin.
Isra'ilawan sun taurare zukatansu.
Allah ya rantse cewa ba za su shiga wurin hutunsa ba.
An gargaɗi 'yan'uwa su yi kula kada sun juya wa Allah rayayye baya ta wurin rashin bada gaskiya.
Ya kamata 'yan'uwan su karfafa juna kowace rana.
A matsayin abokan tarayyar Almasihu, lallai ne masubi su reƙe gabagaɗin da suke da shi cikin sa daga farko har zuwa ƙarshe da ƙarfi.
Allah ya yi fushi da waɗanda suka yi zunubi a jejin.
Gawakinsu sun bazu a jeji.
Ba su shiga wurin hutun Allah ba saboda rashin bada gaskiya.
1 Saboda haka, sai muyi lura kwarai don kada wani ya kasa kai ga shiga hutun da aka alkawarta maku na Allah. 2 Don mun ji albishir game da hutun Allah kamar yadda aka fada masu. Amma wancan sakon bai anfana ga wadanda suka ji ba tare da sun bada gaskiya ga sakon ba. 3 Ai mu, wadanda muka gaskata-mune zamu shiga wannan hutun, kamar yadda ya ce, "Yadda na yi rantsuwa cikin fushina, baza su shiga hutu na ba." Ya fadi hakan, ko da yake ya gama aikin hallittarsa tun daga farkon duniya. 4 Domin yayi fadi a wani wuri game da rana ta bakwai, "Allah ya huta a rana ta bakwai daga dukkan ayyukansa." 5 Ya sake cewa, "Baza su taba shiga hutu na ba." 6 Saboda haka, tun da hutun Allah na kebe domin masu su shiga, kuma tun da Isra'ilawa da yawa wadanda suka ji sakon nan mai kyau game da hutunsa ba su shiga ba saboda rashin biyayya, 7 Allah ya sake shirya wata rana da ake kira, "Yau." Ya sa wannan rana sa'adda yayi magana ta wurin Dauda, wanda ya ce tun da dadewa da aka fara fada, "Yau idan kun ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku." 8 Don idan Joshua ya ba su hutu, da Allah ba zai sake magana a kan wata rana ba. 9 Saboda haka, akwai hutun asabar kebabbe ga mutanen Allah. 10 Don shi wanda ya shiga hutun Allah shi kansa ma ya huta daga ayyukansa, kamar yadda Allah yayi da nasa. 11 Saboda haka muyi marmarin shiga wancan hutun, don kada kowa ya fadi ga irin rashin biyayyar da suka yi. 12 Maganar Allah kuwa rayayyiyace, kuma mai ci, fiye da takobi mai kaifi-biyu. Takan ratsa har tsakanin rai da ruhu, kuma tana kaiwa bargo. Takan iya bincika tunanin zuciya da manufarta. 13 Babu halittaccen abu da ke boye a idon Allah. Sai dai, kome a sarari yake, kuma a bayyane yake a idonsa wanda lallai ne zamu bada lissafin kanmu a gare shi. 14 Da yake muna da babban firist wanda ya ratsa sammai, Yesu Dan Allah, sai mu riki bangaskiyarmu da karfi. 15 Domin babban firist namu ba marar tausayi ga kasawarmu bane, amma wanda aka jarraba ne ta ko wanne hali irin yadda aka yi mana, sai dai ba'a same shi da zunubi ba. 16 Sai mu zo wurin kursiyin alheri gabagadi, domin a yi mana jinkai mu kuwa sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.
Sura huɗu ya cigaba da yi wa masubu kashedi da aka fara a [3:7]. Allah, ta wurin marubucin, ya ba wa masubi hutu wadda hutun Allah cikin hallitar duniya na ba da misali.
"Domin abinda na fito faɗa maku gaskiya ne" ko kuma "tunda lallai Allah zai hukunta masu rashin biyayya" ([3:19])
An yi maganar Alkawarin Allah kamar wata kyauta ce da Allah ke riƙe da ita yayin da ya ziyarci mutanen. AT: "Allah zai bar ku ku kai ga shiga hutu kamar yadda ya mana alkawari"
An yi maganar salama da tsaron da Allah ke tanadawa kamar wata hutu ne da yake bayar wa, kuma kamar wani wuri ne da mutane ke iya zuwa. AT: "su shiga gun hutu " ko kuma " su ɗanɗana albarkun hutu na Allah"
AT: "Gama mun ji albishirin kamar yadda su ma sun ji"
A nan "su" na nufin kakannin Yahudawa da suke da rai a lokacin Musa.
A nan farkon furcin, "yadda na yi rantsuwa ... hutu," daga Zabura ce. Furci na biyun, "Allah ya huta rana ta ... ayyukansa" daga rubuce-rubucen Musa ne. Furci na ukun, "Ba za su taɓa shiga ... hutu," har yanzu daga Zabura ne.
"mu da muka gaskanta"
An yi maganar salama da tsaron da Allah ke tanadawa kamar wata hutu ne da yake bayar wa, kuma kamar wani wuri ne da mutane ke iya zuwa. AT: "mu da muka gaskanta za mu shiga wannan wurin hutu" mu da muka gaskanta za mu ɗanɗana albarkun hutu na Allah"
"kamar yadda Allah ya ce"
"Yadda na rantse a lokacin matuƙar fushina"
An yi maganar salama da tsaron da Allah ke tanadawa kamar wata hutu ne da yake bayar wa, kuma kamar wani wuri ne da mutane ke iya zuwa. AT: "Ba za su taɓa shiga wurin hutu ba" ko kuma "Ba zan taɓa barin su su ɗanɗana albarkun hutuna ba"
AT: "ya gama hallita" ko kuma "ya gama aikinsa na hallita"
AT: "daga farkon farin duniya"
Wannan jerin lamba ta "bakwai" ce.
An yi maganar salama da tsaron da Allah ke tanadawa kamar wata hutu ne da yake bayar wa, kuma kamar wani wuri ne da mutane ke iya zuwa. AT: "Allah yana barin wasu su shiga wurin hutu ba" ko kuma "Allahn yana barin wasu su ɗanɗana albarkun hutuna ba"
Ana maganar umurnin Allah zuwa ga Isra'ilawa kamar ya basu umurnin da wata babban murya ce. Duba yadda aka fassara wannan a [3:7-8]. AT: "idan kun ji Allah yana magana"
A nan "zuciya" na nufin hankalin mutum. Jumlar nan "taurare zuciya" na nufin zama gagararre. AT: "kada ku zama gagararru" ko kuma "kada ku ƙi ji
An yi maganar salama da tsaron da Allah ke tanadawa kamar wata hutu ne da Joshua ke bayarwa AT: "idan Joshua ya kawo Isra'ilawa zuwa wurin da Allah zai basu hutu"ko kuma "idan Isra'ilawa a lokacin Joshua sun ɗanɗana Albarkun Allah na hutu"
AT: "akwai hutun asabar da Allah ya keɓe wa mutanensa"
An yi maganar salama na har abada da tsaro kamar su ne ranar asabar, ranar sujada na Yahudawa da kuma hutawa daga yin aiki. AT: "hutu na har abada"
An yi maganar salama da tsaron da Allah ke tanadawa kamar wata wuri ce da ake shiga. AT: "mutumin da ya shiga wurin hutun Allah" ko kuma "mutumin da ya ɗanɗana albarkun hutu na Allah"
An yi maganar salama da tsaron da Allah ke tanadawa kamar wata wuri ce da ake shiga. AT: "mu ma mu yi duk abinda muka iya yi don mu huta tare da Allah a wurin da yake"
Ana maganar rashin biyayya kamar wani rami ne da mutum na iya faɗị a ciki. AT: "yi rasahin biyayya kamar yadda suka yi"
A nan "su" na nufin kakannin Ibraniyawa lokacin Musa.
A nan "maganar Allah" na nufin dukkan abinda ya sadu da mutum ko ta wurin magana ko rubuce-rubuce. AT: "Kalmomin Allah kuwa rayayyune"
Ana maganar wannan kamar maganar Allah na da rai. Yana nufin cewa idan Allah ya yi magana, yana da iko da kuma inganci.
Takobi mai kaifi-biyu na iya yanka tsoka. Maganar Allah na ci sosai a nuna abinda ke zuciya da kuma tunanin mutum.
takobi mai kaifi-biyu da ke ci a gefe biyun
Wannan na cibaga da magana a kan maganar Allah kamar wata takobi ce. A nan takobin na ci sosai har ma yana iya yanka zuwa gabobin jikin mutun da ke da wuya ko kuma wadda ma basu yiwuwa a yanke. Wannan na nufin cewa babu abinda ke cikin mu da zamu iya ɓoye wa Allah.
Waɗannan sune bangaren jikin mutum daban daban da ido baya iya gani. "Rai" shi ne abinda ke sa mutum ya zama rayayye. "Ruhu" kuma shi ne bangaren jikin mutum da ke sa mutum ya iya sani ko kuma ya gastanta da Allah.
"bargo" itace tsakiyar kashin jiki.
Wannan na bayyana maganar Allah kamar wani mutum ne da ke iya sanin abu. AT: "Maganar Allah tana fallasa"
"Zuciya" a nan tana nufin tunanin zuciyar mutum AT: "abinda mutum ke tunani ko kuma niyyar yi"
AT: "Ba wani abinda Allah ya hallita da za a iya ɓoye masa"
...
Waɗannan kalmomi na nufin abu ɗaya ne, suna kuma nanata cewa babu abinda za a iya ɓuya wa Allah.
Ana maganar Allah ne kamar yana da idanu. AT: "ga Allah, wanda zai shar'anta yadda muka yi rayuwa"
"wanda ya shigo wurinda Allah yake"
Wannan wata laƙabi ne na Yesu.
Ana maganar bangaskiya da dogara kamar wasu abubuwa ne da mutum na iya cafke su da ƙarfi. AT: "bari mu cigabada da gaskatawa da shi da gabagaɗi"
Wannan na nufin cewa Yesu yana da tausayi ga mutane. AT: " muna da babban firist da ke iya jin tausayi ... haƙiƙa, wanda"
AT: "Wanda ya jimre kowace irin jarraba da muke da su" ko kuma "wadda shaiɗan ya jarrabta a kowace hali da yake jarrabtar mu"
"ba yi zunubi ba"
"wurin kursiyin Allah, wurin da akwai alheri." A nan "kursiyi" na nufin sarautar Allah a matsayin sarki. AT: "inda Allahn mu mai alheri ke zaune a kursiyinsa."
An yi maganar "jinƙai" da "alheri" a nan kamar wasu abubuwa ne da ake iya bayar wa ko samu. AT: "Allah na iya yi mana jinƙai da alheri, zai kuma iya taimakonmu a lokacin bukata"
Masubi da Isra'ilawan sun ji bishara game da wurin hutu na Allah.
Bisharar ba ta amfane Isra'ilawan ba domin ba su bada gakiya ba.
Allah ya gama aikin halita a farkon duniya sa'an nan ya huta a rana ta bakwai.
Waɗanda suka bada gaskiya sun shiga wurin huta na Allah.
Allah ya ce Isra'ilawan ba za su shiga wurin hutunsa ba.
Lallai ne mutum ya kassa kunne ga muryar Allah, kada kuma ya taurare zuciyarsa.
Allah ya shirya "yau" a matsayin ranar da mutane za su shiga wurin hutunsa.
An ajiye hutu na asabaci don mutanen Allah.
Mutumin da ya shiga hutun Allah ya huta daga ayyukansa.
Ya kyautu masubi su yi marmarin shiga hutun Allah don kada su faɗi kamar yadda Isra'ilawa suka yi.
Magana Allah ta fi kowane takobi mai kaifi biyu.
Maganar Allah za ta iya rarrabe tunanin da manufar zuciya.
Maganar Allah za ta iya raba rai da ruhu da kuma gabobi daga ɓarbo.
Babu wani halita da ke ɓoye a gaban Allah.
Yesu Ɗan Allah shine ke aiki a matsayin babbar firist na masubi?
Yesu ba shi da zunubi.
Yesu ya ji juyayi game da rashin ƙarfin masubi saboda shi ma an gwada shi ta kowace hanya.
Cikin lokacin bukata, ya kamata masubi su zo kursiyi ta alheri da gabagadi.
1 Kowanne babban firist, da yake an zabe shi ne daga cikin mutane, a kansa shi ya wakilci mutane ga al'amarin Allah, don ya mika sadakoki da kuma hadayu domin kawar da zunubai. 2 Yana kuma iya tafiyar da jahilai da sangartattu a cikin salihanci, tun da shi ke rarrauna ne shi ta ko'ina. 3 Saboda haka, wajibi ne ya mika hadayu, ba saboda kawar da zunuban jama'a kadai ba, har ma da na kansa. 4 Ba wanda zai kai kansa wannan matsayi mai girma, sai dai Allah ya yi kiransa ga haka, kamar yadda aka kirayi Haruna. 5 Haka kuma, Almasihu, ba shi ya daukaka kansa ya zama Babban firist ba, sai dai wannan ne ya sa shi, wanda ya ce da shi, "Kai Dana ne; Yau na zama Uba a gare ka." 6 Kamar dai yadda a wani wuri kuma ya ce, "Kai firist ne na har abada, bisa ga kwatancin Malkisadak." 7 Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roke-roke, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsannin mika kansa. 8 Ko da yake shi Da ne, ya koyi biyayya ta wurin wuyar da ya sha. 9 Har ya kai ga kammala, sai ya zama tushe madawwami, ceto ga dukkan wadanda suke masa biyayya. 10 Gama Allah yana kiransa Babban firist, bisa ga kwatancin Malkisadak. 11 Muna da abu da yawa da za mu fada a game da Yesu, amma zai yi wuyar bayani, da yake basirarku ta dushe. 12 Ko da yake yanzu kam, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sake koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba? har ya zamana sai an ba ku madara ba abinci mai tauri ba? 13 To, duk wanda yake madara ce abincinsa, bai kware da maganar adalci ba, kamar jariri yake. 14 Amma abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato wadanda hankalinsu ya horu yau da kullum, don su rarrabe nagarta da mugunta.
Marubucin yana bayyana zunubin firitocin Tsohon Alkawari, sa'an nan yana nuna cewa irin firist a kwatancin Almasihu, wanda shine mai kama da kwatancin Malkisadak, ya fi, ba irin firist a kwatancin Haruna ba.
AT: "wadda Allah ya zaɓa daga cikin mutane"
AT: "Allah yakan sa shi"
...
AT: waɗanda ... sun yaudaru" ko kuma "waɗanda ... sun gaskata da ƙarya"
"waɗanda sun gaskata da rashin gaskiya kuma suna mumunar rayuwa"
Ana maganar rarraunar babban firist kamar wani ne daban ke mulki a bisa shi. AT: "rarraune ne a ruhaniya" ko kuma "rarraune ne ga zunubi"
mamarin aikata zunubi
AT: "Allah ya sa ya zama wajibi ne"
Ambacin da ke nan daga littafin Zabura ne a Tsohon Alkawali.
Ana maganar girma a nan kamar wani wurin ne da ake iya zuwa ko kuma mutum ke iya kai kansa.
AT: "Allah ya yi kiransa ga haka, kamar yadda ya kirayi Haruna"
"Allah ya ce da shi"
Waɗannan jumloli suna nufin abu ɗaya ne. Dubi yadda aka fassara wannan a [1:5].
Waɗannan wasu laƙabi ne da ke bayyanin dangantakar da ke tsakanin Yesu da Allah Uba.
Ana iya fassarawa a fili wanda Allah ke magana a kai. AT: "kuma ya ce wa Almasihu"
"a wani wuri a cikin nassi"
Wannan na nufin cewa Almasihu, a matsayin firist, na da wasu halaye kamar Malkisadak a matsayin firist kenan. AT: "yadda Malkisadak firist da yake "
A nan "lokaci" na nufin tsawon lokacin zamansa a cikin "duniya" kuma na nufin rayuwar da Yesu yayi a duniya. AT: "Da yake rayuwa a duniya"
Waɗannan kalmomi biyun a takaice na da manufa guda.
Wannan na iya nufin 1) Allah na iya ceton Yesu don kada yă mutu. AT: "yă cece shi daga mutuwa" ko kuma 2) Allah na iya ceton Almasihu bayan mutuwa ta wurin rayar da shi kuma. In ya yiwu, a fassara wannan yadda zai ba da ma'ana biyun nan duka.
AT: "Allah kuwa ya ji shi"
Wannan wani laƙabi ne mai muhimmanci na Yesu, Ɗan Allah.
AT: "Har Allah ya kai shi ga kammala"
Wannan na nufin ya yi girma, zai iya girmama Allah a kowane fanin rayuwa.
AT: "yana ceton dukkan waɗanda suke masa biyayya har ma yana sa su rayu har abada"
AT: "Allah ya zaɓe shi"
Ko da shike marubucin ya yi amfani da wannan wakilin suna "mu", babu shakka yana nufin shi da kansa ne. AT: "Ina da abubuwa dayawa da zan faɗa"
Ana nufin basirar iya fahimata da aikatawa ko kuma biyayya. Ana kuma maganar basirar kamar wani gatari ne da ke iya dushe wa. AT: "kuna da matsalar fahimtar wannan"
Anan "jigajigan" na nufin jagora ko kuma ma'auni na ɗaukar ra'ayi. AT: "jigajigan gaskiyar"
Ana maganar koyar da maganar Allah da ke da sauƙin fahimta kamar shi wani madařa ne, abincin da jarirai ke iya ci. AT: "kun zama kamar jarirai, madařa ne kawai za ku iya sha"
Ana maganar koyar da maganar Allah da ke sa wuyar fahimta kamar abinci ne mai tauri, da ya dace ga manyan mutane. AT: madara, a maimakon abinci mai tauri da manya na iya ci
AT: "ke shan madara"
Ana kwatanta girmar ruhaniya da irin abincin da yaro mai girma ke ci. Abinci mai tauri ba na jariri ba ne, kuma wannan karin magana ne da ke bayyana sabon maibi da ke iya koyan wasu koyaswar gaskiya masu sauƙi; amma jim kaɗan, akan bashi abinci mai tauri, kamar yadda idan mutum ya manyanta yana iya koyan abubuwa masu ban wuya.
Ana maganar mutanen da sun horu su fahimci abu kamar sun horu ne su sami basirar fahimta. AT: "Waɗanda sun manyanta kuma suna iya bambamta nagarta da miyagu.
Kowane babbar firist ya kan miƙa kyauta da hadayu don zunubai saboda mutanen.
Babban firist kuma ya kan miƙa hadayu don zunubansa.
Lallai ne Allah ya ƙira shi don ya zama babbar firist na Allah.
Allah ya maishe Almasihu babbar.
Almasihu babbar firist ne na Allah bar abada.
Bisa ga matakin Malkisadik, Alamasihu ya zama babbar firist.
Allah ya ji Almasihu saboda Amasihu ya girmama Allah.
Alamasihu ya koyi yin biyayya daga abubuwan da ya sha wahala a kai.
Almasihu ya zama sanaɗin madawamiyar ceto domin duk wanda ya yi biyayya.
basirar nihin masu karatun ta dushe
Masubi kan yi girma a ruhuniya ta wurin bambanta abin da ke daidai da wanda ba daidai ba da kuma rarrabe nagarta da mugunta.
1 Saboda haka, sai mu ci gaba a kan ka'idodin farko na al'amarin Almasihu, har ya zuwa kammala, ba wai mu sake koyar da jigajigan nan na tuba da ibada marar tasiri ba, da na gaskatawa da Allah, 2 da kuma na koyarwa a kan wanke-wanke, da dora hannu, da tashin matattu, da dawwamammen hukuci. 3 Za mu kuwa ci gaba in Allah ya yarda. 4 Domin wadanda aka haskaka zukatansu sarai, har suka dandana baiwar nan Basamaniya, suka kuma sami rabo na Ruhu Mai Tsarki, 5 har su ka dandana dadin Maganar Allah, da ikon zamani mai zuwa, 6 sa'an nan kuma suka ridda--ba mai yiwuwa ba ne a sake jawo su ga tuba, tun da yake sake gicciye Dan Allah suke yi su da kansu, suka kuma wulakanta shi a sarari. 7 Kasa ma da take shanye ruwan da ake yi a kai a kai, take kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga wadanda ake nomanta dominsu, Allah yakan sa mata albarka. 8 Amma idan tsire-tsirenta kaya ne da kashin yawo, ba ta da amfani ke nan, tana kuma gab da la'antarwa, karshenta dai konewa ne. 9 Ko da yake mun fadi haka, a game da ku kam, ya kaunatattu mun tabbata kuna abubuwa mafiya kyau na zancen ceto. 10 Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ki kula da aikinku, da kuma kaunar sunansa da kuke yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi. 11 Muna dai bukata kwarai kowannanku ya nuna irin wannan himma ga yin cikkaken bege, tabbatacce, har ya zuwa karshe. 12 Don kada ku yi ragwanci, sai dai ku yi koyi da wadanda suka karbi cikar alkawaran nan, ta wurin bangaskiyarsu da hakurinsu. 13 Sa'adda Allah ya yi wa Ibrahim alkawari, da yake ba wani wanda ya fi shi girma da zai rantse da shi, sai ya rantse da kansa, 14 Ya ce, "Hakika zan yi maka albarka, in kuma ribambamya zuriyarka." 15 Ta haka, Ibrahim bayan da ya jure da hakuri, ya karbi cikar alkawarin. 16 Hakika mutane sukan rantse da abin da ya fi su. Rantsuwa kuma ita ce abar da take tabbatarwa da kowacce magana. 17 Don haka, sa'adda Allah yake son kara tabbatar wa magadan alkawarin nan dahir, cewa nufinsa ba mai sakewa ba ne sam, sai ya hada da rantsuwa, 18 Domin albarkacin abubuwa guda biyun nan marasa sakewa, masu nuna, cewa ba shi yiwuwa Allah ya yi karya, mu da muka gudu muka sami mafaka, mu karfafa kwarai mu riski abin da muka kafa bege a kai. 19 Muna da bege, kamar yadda yake ga rai, kafaffe, tabbatacce, shi ne kuma yake shiga har can ciki bayan labulen. 20 Inda saboda mu ne Yasu ya riga mu shiga, da yake ya zama Babban Firist na har abada, kwatancin Malkisadak.
Marubucin ya cigaba da abinda sabobin masubi ke bukata zuwa kammala a cikin bi. Ya masu tunin koyarwar farƙo.
AT: "mu daina tattauna abinda mun koya tun farko kurum, yan zu ma ƙara da fahimtar manya-manyan koyaswa"
AT: "Kada mu sake maimaita koyarwar farkon ... na gaskatawa da Allah"
Wato ayyukan zunubi.
...
Ana yin wannan domin a keɓe mutum domin wata hidima ko matsayi ta musamman.
Wato fahimta kenan. AT: "waɗanda sun taɓa fahimtar saƙon bisharar Almasihu"
Ana maganar ɗanɗana ceto ne kamar ɗanɗana daɗin abinci. AT: "waɗanda sun ɗanɗana ikon ceto na Allah"
Ana maganar Ruhu Mai Tsarki da ke saukowa ga masubi kamar wani abu ne da jama'a ke iya rabawa. AT: "wanda suka karɓi Ruhu Mai Tsarki"
Ana maganar koyar maganar Allah kamar ɗanɗana daɗin abinci ne. AT: "Wanda sun koyi daɗin maganar Allah"
Wato ikon Allah da zai zo yayin da mulkinsa zai kasance a duniya gabaƙiɗaya. Dan haka, "ikon" na nufin Allah da kansa, mai riƙe dukkan iko. AT: "sanin yadda Allah zai yi aiki da iko nan gaba"
AT: "wanda sun daina gaskata da Allah"
...
Idan mutane sun yi řidda, yana kamar sun sake giciye Yesu ne kuma. AT: "yana kamar sun sake giciye Ɗan Allah ne don kansu kuma"
Wannan wani laƙabi ne mai muhimmaci na Yesu da ke bayyana dangantakar shi da Allah.
Ana maganar gona da ke cin moriyar ruwan sama kamar mutum ne da ke shan ruwan sama. AT: "ƙasa da ke janye ruwan sama"
Ana maganar gona mai ba da amfani kamar yana haifar su ne. AT: "da ke ba da tsire-tsire"
AT: "ga waɗanda aka shirya masu gonar"
Ruwan sama da amfanin gona da muke gani suna tabbatar mana cewa Allah ya tallafi gonar. Ana maganar gona kamar mutum ne da ke iya karbar albarkun Allah.
A nan "albarka" na nufin tallafi da ga Allah, ba furcin kalmomi ba.
Ana maganar "la'antarwa" kamar wani wuri ne da mutum ke iya matsowa kusa da shi. AT: "yana hatsarin la'anta daga Allah"
Manomin zai ƙone kome da ke gonar"
Kodashike marubucin ya yi amfani da wannan wakilin suna "mu", yana maganar shi da kansa ne kurum. AT: "bani da shakka" ko kuma "ina da tabbaci"
Wannan na nufin cewa suna abubuwa fiye da waɗanda suka ƙi Allah, suka yi masa rashin biyayya, kuma ba za su sake iya tuba ba domin Allah ya gafarce su (Dubi: [6:4-6]) AT: "kuna yin abubuwa masu kyau fiye da abinda na ambata"
AT: "zancen ceton da Allah ke yi maku"
Wannan na iya nufin cewa Allah cikin ădalcinsa zai tuna da dukkan abubuwa masu kyau da jama'ar sa suka yi. AT: "Gama Allah mai ădalci haƙiƙa zai tuna"
"Sunar" Allah na nufin Allah da kansa. AT: "masa"
Kodashike marubucin ya yi amfani da wannan wakilin suna "mu", yana maganar shi da kansa ne kurum. AT: "ina da bukata ƙwarai"
kula, aiki tuƙuru
Za a iya karin bayanin ma'anar wannan a fili. AT: "zuwa ƙarshen rayuwarku"
"zuwa ga samun chikakken tabbaci na karɓan abinda Allah ya alkawarta maku"
Mai "koyi" mutum ne da ke kwaikawayon halayyar mutum.
Ana maganar karɓar alkwarin da Allah ya yi wa masubi kamar gadan dukiya ne ko kuma arziki na wani ɗan iyali. AT : "karɓi abinda Allah ya yi masu alkawari"
"Allah ya ce"
AT: "Zan baka zuriya masu yawa"
"alkwawrin da Allah ya yi masa"
Ana maganar mutanen da Allah ya masu alkwarai kamar za su gada dukiya ne ko kuma arziki ne na wani ɗan iyali. AT: "ga waɗanda za su karɓi abinda Allah ya alkawarta"
"cewa nufinsa ba zai ta taɓa sakewa ba" ko kuma "cewa zai riƙa yin abinda ya ce za yi a koda yaushe"
Wannan na nufin Alkawarin Allah da kuma rantsuwar Allah. Babu wanin su da zai iya sekewa.
Wannan na nufin cewa Allah ya faɗi gaskiya game da wannan yanayin. AT: "game da abinda Allah zai riƙa faɗin gaskiya a ko yaushe"
Ana maganar Masubi da ke dogara ga Allah domin ya ƙare su kamar guduwa ne zuwa wurin tsira. AT: "mu, da muke dogara gareshi"
Wato dogarar mu ga Allah kenan. AT: "za mu cigaba da dogara ga Allalh kamar yadda ya ƙarfafa mu mu yi"
AT: "da Allah ya sa a gabanmu"
Kamar yadda anka yake hana kwale kwale bijirewa a cikin ruwa, Haka Yesu yana kafe mu a gaban Allah. AT: "da ke sa mu rayu a kafe a gaban Allah"
Waɗannan kalmomi biyun a takaice suna da ma'ana guda, kuma suna nanata matuƙar tabbacin da ake da shi a kan anka. AT: "tabbaccen bege"
Ana maganar gabagaɗi ne a nan kamar wani mutum ne da ke iya shigo har cikin wurin mafi tsarki a haikali.
Wannan ne wurin mafi tsarki a cikin haikalin. Ana ɗaukan wannan wurin a matsayin wurin da Allah ya fi kasancewa a cikin jama'arsa. A wannan nassi, wannan na nufin sama, kursiyin Allah.
Wannan na nufin Almasihu a matsayin firist yana da halayya iri ɗaya da Malkisadak a matsyin firist. AT: "haka ma Malkizadak firist ne"
Marubucin yana so masubi su nace zuwa ga kammalawa.
Harshashi koyaswar sune tuba daga mataccen ayyuka, sa bangaskiya cikin Allah, baftisma, sanya hanuwa, tashin matattu, da kuma dawwammammen hukunci.
Ba shi yiwuwa ga waɗandan da suka ɗanɗana daga Ruhu Mai Tsarki, amma kuma sun fãɗi, ba mai yiwuwa ba ne a sãke jawo su ga tuba.
Sun ɗanɗan baiwan nan ta sama, maganar Allah, da kuma ikon zamani mai zuwa.
Ba za a iya sãke jawo ba domin, saboda kansu sun giciye Ɗan Allah.
ƙasar da ta sami ruwa amma ta bada ƙaya da kashin yawo, ƙarshen ta za a ƙona ta.
Marubucin na sammanin abubuwan mafikyau game da waɗanna masubin, abubuwa game da ceto.
Allah ba zai manta da aikinsu da ƙauna, da kuma hidimarsu zuwa ga zaɓaɓɓe.
Ya kyautu masubi su yi bisa ga bangasakiya da hakurin waɗannan sun gãji alkawaren Allah.
Ibrahim ya yi hakurin jira don ya samin abin da Allah ya alkawarta.
Allah ya tabbatar da alkawarinsa ta wurin ransuwa don ya bayana a fili nufinsa wanda ba ya canzawa.
Ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya.
Gabagadi da masubi suke da shi a gaban Allah shine kubuta da anka don ransa.
Yesu ya shiga cancan ciki a bayan labulen a matsayin wanda ya rigaye mu saboda masubi.
1 Wannan ne Malkisadak, sarkin Salem, firist na Allah Madaukaki, wanda ya gamu da Ibrahim na dawowa daga yaki da wasu sarakuna ya kuma albarkace shi. 2 Ibrahim ya ba shi ushirin dukkan ganimar da ya samu. Sunansa," Malkisadak," ma'anar itace, "Sarkin adalci," haka ma, "sarkin salem," ma'anar iitace," Sarkin salama," 3 Bashi da uwa bashi da uba, ba shi da lissafin asalin zuriya, ba shi da farkon rayuwa ba shi da karshen rai. Shi firist ne na har abada, kamar Dan Allah. 4 Yanzu fa dubi irin girman wannan mutum. Kakan kakanninmu Ibrahim ya bada ushira ta abubuwan da ya samo na ganimar yaki gare shi. 5 Kuma hakika, zuriyar Lawi da suka karbi aikin nan na firistanci suna da umarni daga shari'ar Allah cewa su karbi zakka a gun jama'a, wato, daga yan'uwan su Isra'ilawa, koda shike suma zuriyar Ibrahim ne. 6 Amma Malkisadak, shi da ba zuriyar Lawi ba ne, ya karbi zakka daga Ibrahim, ya kuma albarkace shi, shi wanda ya ke da alkawarai. 7 Ba jayayya, karami shi ke karban albarka daga babba wanda ya girme shi. 8 A wannan tsarin mutanen da ke karban zakka wata rana sai ka ga sun mutu, amma a wani kauli mutumin da ya karbi zakka a wurin Ibrahim, ance, wanzaje ne har yau. 9 Kuma bisa ka'ida Lawi, wanda ke karban zakka, shi ma ya bada zakka ga Ibrahim, 10 Saboda kuwa Lawi na cikin tsatson Ibrahim lokacin da Malkisadak ya gamu da Ibrahim. 11 Yanzu in da mai yiwuwa ne a sami kammala cikin aikin firistanci na Lawiyawa (domin ta wurin ta ne aka bada shari'a), to ina amfanin wani firist ya zo bisa ga ka'ida irin ta Malkisadak, ba'a kuma ambaci ka'idar Haruna ba? 12 Don kuwa lokacin da aka canza firistanci, shari'a kuma dole ne a sauya ta. 13 Domin mutumin da aka fadi wadannan abubuwa a kansa na wata kabila ne, wadda ba wani mutumin da ya taba yin aiki a kan bagadi. 14 Wannan a bayyane yake Ubangijinmu ya zo ne daga zuriyar Yahuza, kabilar da Musa bai taba anbatonsu game da zancen firistanci ba. 15 Abinda muke fadi a bayyane yake cewa, idan wani firist ya taso da kamanin Malkisadak. 16 Wannan sabon firist, ba firist ne da ya taso bisa ga ka'idar zuriya ta yan'adam ba, amma ya zama firist ne ta rayuwa mai iko marar shudewa. 17 Domin a rubuce yake cikin littafi ga me da shi; "Kai firist ne na har'abada bisa ga tsari irin na Malkisadak." 18 Domin doka ta fari an ajiye ta a gefe guda saboda rarrauna ce kuma marar amfani. 19 Don kuwa shari'a ba ta iya kamalta kome. Amma fa a kwai bege mai kyau a nan gaba wanda ta gare shi ne zamu sami iso a gun Allah. 20 Kuma wannan kyakkyawan bege baya faruwa ba tare da rantsuwa ba, don kuwa su wadancan firistocin ba su dauki wata rantsuwa ba. 21 Amma Allah yayi rantsuwa game da Yesu cewa, "Ubangiji ya rantse ba kuwa zai fasa tunaninsa ba; 'Kai firist ne har'abada.'" 22 Ta wurin haka Yesu ya bada tabbatacce da kuma ingataccen alkwari. 23 Hakika, mutuwa ta hana firistoci su yi aiki har'abada. Wannan shi ya sa akwai firistoci da yawa daya bayan daya. 24 Amma da shi ke Yesu na rayuwa ne har'abada, aikinsa na firist ba a musanya shi sam sam. 25 Domin haka kuma yana da cikakken ikon ceton wadanda ke gusowa ga Allah ta wurinsa, domin kullum a raye ya ke yana kuma roko dominsu 26 . Domin irin wannan babban firist shi ne ya dace da mu. Ba shi da zunubi, marar abin zargi, tsarkakakke, kebabbe daga masu zunubi, ya na sama da sammai dukka. 27 Ba shi da bukata, kamar manyan firistoci, da ke mika hadayu kullum, da farko don zunubin kansu, sa'annan don zunubin jama'a dukka. Amma Yesu yayi wannan sau daya tak ba kari don kowa da kowa, yayin da ya mika kansa. 28 Domin shari'a na nada mutane da ke da gazawa a matsayin firistoci, amma maganar rantsuwa, wadda ta zo a bayan shari'a, ta nada Dan, wanda ya ke cikakke har'abada.
Marubucin ya cigaba da kwatanta Yesu a matsayin firist da kuma Malkisadak a matsayin firist.
Wannan sunan wani gari ne.
Wannan na nufin lokacin da Ibrahim da mutanen sa suka je suka ci sojojin sarakuna huɗu da yaƙi domin su ceci danginsa Lutu, da iyalinsa
"ya ba wa Malkisadak"
"sarki mai adalci ... sarki mai salama"
Ana iya tunani daga wannan nassin cewa ba a taɓa haifan Malkisadak ba, balle ma a ce yă mutu. Amma, yana iya yiwuwa cewa marubucin na nufin cewa Littafi bai ba da wani bayani game da lissafin asalin sa, haifuwarsa, da mutuwarsa ba.
"Malkisadak"
Marubucin ya faɗa haka ne domin ba dukkan 'ya'yan Lawi ba ne sun zama firist. AT: "Zuriyar Lawi da suka zama firist"
"a gun mutanen Isra'ila"
Anan 'yan'uwansu" na nufin cewa dukkan su sun haɗa dangi ta wurin Ibrahim. AT: "daga danginsu"
...
...
Ana maganar abubuwan da Allah ya alkawarta zai yi wa Ibrahim kamar wasu abubuwa ne da ake iya mallaka. AT: "wadda Allah ya furta masa alkawaransa"
...
An yi amfani ne da waɗannan Jumaloli don a kwatanta Lawiyawa firistoci da Malkisadak. Harshen ku na iya samun wata hanyar nanata cewa marubucin yana kwatanci ne.
Ba a taɓa rubutawa a fili cewa Malkizadak ya taɓa mutuwa ba. Marubucin yana maganar rashin bayani game da rasuwar Malkizadak a littattafai kamar sanarwa ne cewa yana da rai har wa yau. AT: "littafi na nuna cewa yana da rai har wa yau"
Da shike ba a haifi Lawi ba tukuna, marubucin yana maganar sa ne kamar har yanzu yana cikin jikin Ibrahim. Ta haka ne marubucin yana bayar da hujja cewa Lawi ya ba da zakka ta wurin Ibrahim
Wannan ba ya nufin "a dai dai wannan lokacin", amma ana amfani ne da wannan a jawo hankali zuwa ga wata jawabinsa mai muhimmanci da ya biyo baya.
Wannan tambayan na nanata cewa ba a sa tsammanin cewa za a samu wani firist mai kama da Malkizadak ba. AT: "ba wanda zai bukaci samun firist da ke kamar Maikizadak, amma ba kamar Haruna ba, yă zo"
"yă bayyana"
Hakan na nufin cewa Almasihu a matsayin firist na da wasu halaye irin ta Malkizadak a matsayin firist. AT: "kamar yadda Malkizadak ma firist ne"
AT: "ba ka'idar Haruna kuma ba" ko kuma "wadda ba firist kamar Haruna ba"
...
Wato Yesu.
AT: "wadda nake magana a kai"
"Ubangijinmu" na nufin Yesu.
"daga kabilar Yahuza"
Amabacin da ke nan daga littafin Zabura ne na sarki Dauda.
"Muna iya fahimta har ma fiye sosai." Anan "mu" na nufin marubucin da masu sauraronsa.
"idan wani firist dabam ya bayyana"
Wannan na nufin cewa Almasihu a matsayin firist na da halaye iri ɗaya da Malkizadak a matsayin firist. AT: "kamar yadda Malkizadak ma dã firist ne"
"Zamar sa firist ba bisa ga ka'idar bane"
AT: "bisa ga ka'idan zuriyar 'yan'adam" ko kuma "ka'idar game da zaman firist daga zuriyar firstoci"
AT: "Domin an shaide shi ta wurin littattafai" ko kuma "Domin haka yake a rubuce game da shi a littattafai"
A nan "ajiye ta a gefe" karin magana ne da ake nufin marar amafani. AT: "Allah ya mayar da dokar ya zama marar amfani"
Ana maganar shari'a ne a nan kamar wani mutum ne da ke iya yin wani abu. AT: "ba wanda zai iya zama kamalalle ta wurin kiyaye doka"
AT: "Allah ya kawo bege mai kyau" ko kuma "Allah ya bamu dalilin kafa bege da gabagadi"
Ana maganar yi wa Allah ibada da kuma samun alherinsa cewa isowa gun sa ne. AT: "kuma saboda wannan bege ne muke zuwa gun Allah" ko kuma "kuma saboda wannan bege ne muke yi wa Allah sujada"
Kalmar nan "wannan" na nufin Yesu a matsayin firist na har abada abadin. Ana iya fassarawa a fillin mai rantsuwar. AT: "Kuma Allah bai zaɓi wannan sabon firist haka kurum ba ba tare da rantsuwa ba! ko kuma "Kuma domin Allah ya a ɗauki rantsuwa ne ya sa Ubangiji ya zama sabon firist ɗin!"
"ya faɗa mana cewa muna iya tabbatar da cewa za a samu wata ingantaccen alkawari"
Ana maganar aikin firist kamar wata kaya ce da Yesu ya mallaka. AT: "shi firist ne da dindindin"
Ana iya ƙarin bayani abinda "Don haka yana" ke nufi. AT: "Da shike Almasihu shi ne babban firist na mu da ke raye har abada, yana"
"waɗanda suka zo gun Allah ta dalilin abinda Yesu ya yi"
"Allah ya ɗaga shi zuwa saman sammai dukka. Marubucin na maganar mallakar girma da iko fiye da kowa ne kamar wani matsayi ne da ke sama da dukkan kome. AT : "Allah ya girmama shi, ya kuma bashi iko fiye da kowa"
A nan "shari'a" karin magana ce da ke nufin masu naɗa manyan firistoci bisa ga shari'ar Musa. Ba akan mutanen ake sa hankali ba, amma da tabbacin cewa sun yi haka bisa ga shari'a. AT: "bisa ga shar'a ne mutane sun naɗa mutane da ke da gazawa a matsayin manyan firistoci" ko kuma "gama bisa ga shari'a, mutane da ke gazawa ne aka naɗa a mastayin manyan firistoci"
"mutane da ke da gazawa a ruhaniya" ko kuma mutane raunana"
"maganar rantsuwa" na wakilcin cewa Allah wadda ya rantse. AT: "Allah ya naɗa Ɗan ta wurin rantsuwarsa, wadda ya yi bayan ya ba da shari'ar" ko kuma "bayan da ya bayar da shari'a, Allah ya ɗauki rantsuwa ya kuma naɗa Ɗansa"
AT: "wanda ya yi wa Allah biyayya gabaƙiɗaya ya kuma zama cikakke"
Malkisadik shine sarki salem shi kuma firistin Allah maɗaukaki.
Ibrahim ya ba wa Malkisadik ɗaya daga cikin goma na kowane abin da ya kama.
Sunan nan Malkisadik na nufin "sarkin adalcin" da kuma "sarkin salama."
Malkisadik ba shi da kakani, ba shi kuma da ƙarshen rayuwa.
Firistocin sun zo daga zuriyar Lewi ne da kuma Ibrahim.
Malkisadik shine mafi girma domin ya albarkaci Ibrahim.
Lewi kuma ya bada zakka ga Malkisadik saboda Lewi ya zo daga zuriyar Ibrahim sa'ad da Ibrahim ya ba da zakka ga Malkisadik.
Ana bukatan wani firist ya zo bayan Malkisadik saboda ba a iya samun kammalawa ta wurin firistoci na zuriyar Lawi.
Lallai ne a sauya shari'ar a sa'ad da an sauya matsayin firitanci?
Yesu ya zo da kabilar Yahuza, wanda ba su taɓa yin hidima a gaban bagadi a matsayin firist.
Yesu ya zama firist bayan ka'idar Malkisadik bisa ga ikon rai mara lalalcewa.
An soke Umurni na dã, wato shari'ar, saboda rashin ƙarfin da kuma rashin amfanin ta.
Allah ya rantse cewa Yesu zai zama firist na har abada
Yesu ya zama lamuni na alkawari mafi kyau.
Yesu ya cece waɗanda suka zo kusa da Allah ta wurin Yesu domin a koyaushe ya roƙo domunsu.
Yesu ba ya bukata ya yi hadaya saboda zunubinsa domin shi ba mai zunubi ba ne.
Yesu ba shi da zunubi, ba shi da aibu, tsarkakke da kuma ba ya tare da masu zunubi.
Yesu ya miƙa kansa a matsayin sau ɗaya domin zunuban mutane.
Firistocin da aka zaɓa ta wurin shari'ar ba su da ƙarfi, amma Yesu ya zama mara aibu har abada.
1 Yanzu abin da muke kokarin cewa shine: Muna da babban firist wanda ke zaune a hannun dama na kursiyi mai martaba dake sammai. 2 Shi kuwa bawa ne a wannan wuri mai tsarki, haikali na gaskiya wanda Allah ya shirya ba wani bil'adama ba. 3 Kowanne babban firist kuwa yana mika bayebaye da hadayu. Don haka ya kamata a sami abin hadaya. 4 Da a ce Almasihu yana duniya ba zai zama firist ba ko kadan. 5 Domin a kwai masu mika hadaya bisa ga shari'a. Suna hidimar misalin abubuwan da suke inuwar sama. Kamar yadda Allah ya yi wa Musa gargadi yayin da ya ke shirin gina Alfarwa: "Duba" Allah ya ce, "kayi komai bisa ga salon da aka koya maka a bisa dutse." 6 Amma yanzu hidimar da Almasihu ya karba ta dara tasu dukka, domin kuwa shine matsakancin muhimmin alkawari, wanda aka kammala a kan muhimman alkawura. 7 Domin kuwa idan alkawarin fari ba shi da laifi babu anfanin neman alkawari na biyu. 8 Da Allah ya sami laifi akan mutane, sai ya ce "Zan sake sabon alkawari da gidan Isra'ila da kuma gidan Yahuza. 9 kuma ba zai zama kamar yadda nayi da kakanninku ba, kamar yadda na rike su a hannu har Na fidda su daga kasar Masar. Basu kuma ci gaba da Alkawarina ba, ni kuwa na yi watsi da su," inji Ubangiji. 10 Gama wanna shine alkawarin da zan yi da gidan Isra'ila bayan wadannan kwanaki, Inji Ubangiji. Zan sa shari'a ta a bakinsu in kuma rubuta ta a zuciyarsu, Zan kuma zama Allah a garesu, su kuma su zama jama'ata. 11 Ba za su kuma koyar da makwabta ko yan'uwansu cewa, "ku san Ubangiji" gama dukkanin su za su san ni, daga karami har zuwa babba. 12 Zan kuma nuna tausayi ga ayyukan su na rashin adalci, ba kuma zan kara tunawa da zunubansu ba. 13 A kan fadin "sabo" ya mayar da alkawarin fari tsoho. Wannan kuma da aka ambata tsoho na shirin bacewa.
Bayan da murubucin ya unan cewa firistancin Almasihu ya fi firistancin duniya, ya kuma nuna cewa firistancin duniya yana kamanta salon na sama ne. Almasihu yana da babbar hidima, babbar alkawali.
Wannan bai nuna cewa "a daidain wannan lokacin ba", amma anyi amfani ne da shi domin a jawo hankalinmu zuwa wani bayani da ke biye.
Ko da shike marubucin yana amfani da wakilin suna da ke nuna mutum fiye da ɗaya, "mu," ba shakka yana magana game da shi kansa ne kawai. AT: "Ina cewa" ko kuma "Ina rubutawa"
Zai zauna a "hannun dama na Allah" alama ce na nuna samun wata babbar girma da iko daga Allah. Duba yadda aka fassara wannan a [1:3]. AT: "ke zaune a wurin girma da iko a gefen kurusiyi mai martaba"
Mutane sukan gina haikali daga patan dabbobi, sai su manna shi a jikin wani katako, sai su shirya shi kamar wani bukka. A nan "haikali na gaskiya" na nufin haikali na sama da Allah ya ƙirƙiro"
AT: "Gama Allah yanan sa kowane firist ne"
"yadda Allah ya umarta a cikin shari'a"
Ana amfani ne da waɗannan kalmomi masu ma'anna kusan ɗaya ne domin nanata cewa haikalin misali ne kawai na ainihin haikalin da ke cikin sama. AT: "sifa marar cikakken bayani"
Marubucin yana maganar haikali da ke duniya, wadda yake misalin haikalin da ke sama ne kamar, hakan inuwa ne.
AT: "Yana daidai kamar yadda Allah ya yi wa Musa gargaɗi ne yayin da Musa ya ke"
Ba Musa ne ya yi alfarwar da kansa ba. Ya umarci mutane ne su yi shi. AT: "shirin umartar mutane su yi alfarwar"
"Ku tabbatar cewa"
"gă zane"
AT: "da ni na nuna maka"
Za ku iya ƙarin bayani cewa "dutsen" na nufin dutsen Sina'i . AT: "a bisa dutsen Sina'i "
"Allah ya ba Alamsihu"
Wannan na nufin cewa Almasihu ya sa muhimmin alkawari tsakanin Allah da mutane domin su rayu.
AT: "alkawari. Wannan shi ne muhimmin alkawari da Allah ya yi akan muhimman alkawura" ko kuma "alkawari. Allah ya yi alkawarin muhimman abubuwa da ya yi wannan alkawari"
Waɗannan kalmomi "fari" da kuma "biyu" jerin lambobi ne. AT: "tsohon alkawari ... sabon alkawari"
"yana kammalalle"
A wannan ambacin annabi Irimiya ya yi anabcin sabon alkawari da Allah zai yi.
"akan jama'ar Isra'ila"
"Duba" ko kuma "ku ji" ko kuma "ku kassa kunne ga abinda zan faɗa maku"
Ana maganar abin nan gaba kamar yana nufan mai magana. AT: "za a kai wani lokaci"
Ana maganar jama'ar Isra'ila da na Yahuza kamar gidaje ne. AT: "jama'ar Isra'ila tare da jama'ar Yahuza"
Wannan karin maganar na nufin matuƙar ƙauna da kulawar Allah. AT: "na fidda su daga Masar kamar yadda uba yake bi da ɗan yaron sa"
Ana maganar jama'ar Isra'ila kamar su wani gida ne. AT: "jama'ar Isra'ila"
"bayan wannan lokaci"
Ana maganar umarnan Allah kamar wasu abubuwa ne da ake iya sa wa a wuri. Ana kuma maganar iya tunanin mutane kamar wani wuri ne. AT: Zan sa su iya fahimtar shari'una"
A nan "zuciya" na nufin tunanin mutum. Jumlar nan "rubuta shi a zuciyarsu" karin magana ne da ke nufin ba da ikon sa mutane su yi biyayya da shari'a. AT: "Zan kuma sa a zuciyarsu" ko kuma "Zan ba su ikon iya yin biyayya da shari'a"
"Zan kuma zama Allah da suke bauta wa"
"su kuma zama jama'ar da nake kula da su"
AT: "Ba lallai su koyar wa makwabtansu ko 'yan'uwansu su san ni ba"
Waɗannan duka suna nufin Isra'ilawa
"san" a nan na nufin tunawa.
Wannan na nufin mutane masu aikata miyagun ayyuka"
A nan "tunawa" na nufin "tunani a kai"
'ya kusa gama ɓacewa" ko kuma "zai ɓace nan ba da daɗewa ba"
Babban firist na masubi na zaune a hannun dama na kursiyin Mai iko dukka a cikin sama.
Alfarwa ta gaskiya yana sama.
Ya kamata kowane firist ya sami abin da zai miaƙ.
Firistocin da suka miƙa kyautai bisa ga shari'ar sun nan a duniya.
Firistoci a duniya sun bauta wa makamatan abubuwan sama da ishararsu.
An gina alfarwa ta duniya bisa ga tsarin da Allah ya nuna wa Musa a kan dutsen.
Almasihu na da hidimar firist mafi iko domin shi ne matsankancin alkawarin mafi kyauta da aka kafa bisa alkawari mai kyau.
Allah ya yi alkawari da cewa zai yi sabon alkawari da Isra'ila da kuma Yahuza.
Allah ya ce zai sa shari'ar sa cikin zukatan mutane, zai kuma rubuta shi a kan allon zukatansu.
Dukka mutanen za su san Ubangiji, bisa ga sabon alkawari, daga ƙarim har zuwa mafi girma.
Allah ya ce ba zai tuna da zunuban mutane ba kuma.
Ta wurin sanar da sabon alkawarin, Allah ya maishe da alkawarin na farko tsohon kuma na shirye ya shuɗe
1 To ko da alkawarin farko ma ya na da wurin sujada da kuma ka'idojin sujada a nan duniya. 2 Domin a cikin alfarwar akwai daki da aka shirya, daki na waje wanda ake kira wuri mai tsarki. A wannan wuri akwai kebabbun fitilu, akwai teburi da kuma gurasa. 3 Kuma bayan labule na biyun akwai wani daki, wanda ake kira wuri mafi tsarki. 4 Yana da bagadin zinariya domin turare. Yana kuma da akwatin alkawarin, wanda aka lailaye shi gaba daya da zinariya. A cikinsa a kwai kaskon zinariya dake dauke da manna, da sandar Haruna wadda tayi toho, da kuma allunan duwatsu na alkawarin. 5 A sama da akwatin alkawarin akwai siffofin kerubobi masu daukaka da suke wa marfin jinkai inuwa, wadanda yanzu ba zamu iya yin bayani akansu ba daki daki. 6 Bayan an shirya wadannan abubuwa, firistocin alfarwar sukan shiga daki na wajen alfarwar akai akai suna aikin hidimominsu. 7 Amma babban firist din ne kadai yake shiga daki na biyun, sau daya tak a shekara, kuma tilas sai tare da jinin hadaya domin kansa, da kuma domin laifuffukan mutane da a kayi ba dagangan ba. 8 Ruhu Mai Tsarki yana nuna cewar ba'a riga an bayyana hanyar zuwa wuri mafi Tsarki ba muddin alfarwar nan ta farko na a tsaye. 9 Wannan ya zama bayani ne game da lokacin yanzu. Da kyaututtuka da hadayu dukka da ake mikawa basu iya sun kammala lamirin mai yin sujadar ba. 10 Abinci ne da abin sha kawai wadanda aka hada da bukukuwan wanke wanke dabam dabam. Wadannan duka tsare tsare ne da aka shirya a dinga yi a zahiri har sai an shirya sabuwar ka'ida. 11 Almasihu yazo a matsayin babban firist na abubuwa masu kyau da suka zo, ta wurin alfarwa babba, kammalalla kuma mafi tsarki wadda ba hannuwan mutane suka gina ba, wadda ba ta wannan duniyar aka halicce ta ba. Amma almasihu ya zo a matsayin babban firist na abubuwa masu kyau da ke zuwa. 12 Ba ta jinin awaki da 'yan, maruka bane, amma Almasihu da jininsa ya shiga wuri mafi tsarki sau daya tak domin kowa dukka ya karbo mana fansa ta har abada. 13 To idan jinin awaki da na bajimai da yayyafa tokar karsana bisa wadanda suka bata tsarkinsu yana tsarkake su ya wanke jikkunansu. 14 To balle kuma jinin Almasihu, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya mika kansa hadaya marar aibi ga Allah, wanda yake wanke lamirinmu daga matattun ayyuka domin muyi bautar Allah mai rai? 15 Domin wannan dalili, Almasihu shine magamin sabon alkawari. Wannan kuwa ya kasance ne domin anyi mutuwar da ta 'yantar da wadanda ke karkashin tsohon alkawari daga sakamakon zunubansu, saboda wadanda Allah ya kira su karbi alkawarin gadonsu madawwami. 16 Gama duk inda wani ya rubuta wasiyya ya bari, dole ne a tabbatar da mutuwar wanda yayi wasiyyar nan. 17 Gama sai inda akayi mutuwa ake amfani da wasiyya, amma ba ta da amfani idan wanda ya rubuta ta yana nan da rai. 18 Ko alkawari na farko bai tabbata ba sai tare da jini. 19 Gama bayan Musa ya bada dukkan dokoki da ke cikin shari'ar ga dukkan mutanen, sai ya dauki jinin 'yan marukan da awakin, tare da ruwa, da jan yadi, da reshen itacen doddoya mai soso, ya yayyafa bisa mutanen da kuma littafin dokokin. 20 Daga nan yace, "Wannan ne jinin alkawarin da Allah ya bayar da dokoki gareku." 21 Ta haka kuma, ya yayyafa jinin bisa alfarwar da dukkan kayayyakin da ke cikinta wanda ake hidimar firistanci da su. 22 Kuma bisa ga shari'a, kusan komai da jini ake tsarkake shi. Idan babu zubar da jini to babu gafarar zunubi. 23 Saboda haka ya zama tilas wadannan kayayyaki na kwaikwayon abubuwan dake cikin sama a tsarkake su da hadayar dabbobi. Duk da haka abubuwa na sama dole a tsarkake su da hadaya mafi kyau. 24 Domin Almasihu bai shiga cikin wuri mafi tsarki da aka yi da hannuwa ba, wanda kwaikwayo ne kawai na abin da ke na gaske. Maimakon hakan, ya shiga cikin samaniya da kanta, sa'an nan yaje gaban Allah domin mu. 25 Bai je wurin don ya mika kansa sau da yawa, kamar yadda firist din alfarwa yake yi ba, wanda yake shiga wuri mafi tsarki kowacce shekara da jinin wata dabba. 26 Idan haka ne, to dole ke nan ya sha wahala akai akai tun farkon duniya. Amma yanzu sau daya ne tak aka bayyana shi a karshen zamanai domin ya kauda zunubi ta wurin mika hadayar kansa. 27 Kamar yadda aka kaddara wa kowa ya mutu sau daya tak, kuma bayan haka sai shari'a. 28 Haka kuma Almasihu, wanda aka mika shi sau daya tak domin ya dauke zunuban mutane da yawa, zai kuma bayyana karo na biyu, ba domin yin aikin kawar da zunubi ba, amma domin ceton wadanda suke jiran zuwansa da hakuri.
Marubucin yana ƙarin bayani ne ga Yahudawa masubi cewa shari'ar da alfarwar Tsohon Alkawari misali ne kawai na sabuwar alkawari wanda shi ne mafi kyau.
Wannan na nuna wata sabuwar fanni na koyaswar.
Dubi yadda aka fassara wannan a [8:7]
"yana da cikakken ka'idodi" ko kuma "yana da dokoki"
Marubucin yana cigaba ne da tattaunawar daga [8:7].
An yi alfarwar and kuma shirya shi domin amfani. AT: "Isra'ilawan sun shirya alfarwar"
Dukkan waɗannan kayayyakin hidimar suna nan ne na musamman shi ya sa an morin kalmar nan "da" domin marubicin yana tsammanin cewa masu karatunsa sun riga sun san da waɗannan abubuwa.
AT: "gurasa da aka ajiye gaban Allah" ko kuma "gurasa da firist sukan miƙa wa Allah"
Labule na farkon itace sashi na wajen alfarwar ne, don haka, "labule na biyun" ita ce labulen da ke tsakanin "wuri mai tsarki" da kuma "wuri mafi tsarki"
Wannan shine kalmar kirgen lamba ta biyu.
"a cikin akwatin alkawarin"
Wannan ne sandar da Haruna ke da shi lokacin da Allah ya tabbatar wa jama'ar Isra'ila cewa ya zaɓi Haruna ta wurin sa sandar Haruna ta yi toho.
"wadda ganyayenta da fure suka yi girma"
A nan "duwatsu" wasu shimfiɗaɗɗun duwatsu ne da ke da rubutu a kan su. Wannan na nufin allunan duwatsu ne da aka rubuta dokoki goma a kai.
Da Isra'ilawan suke yin akwatin alkawarin, Allah ya umarce su su ƙera kerubobi biyu da ke fuskantar juna, da fuka-fukansu suna taɓa marfin jinƙan akwatin alkawarin. Ana maganar su ne a nan kamar suna ba wa akwatin alkawarin inuwa. AT: "kerubobi masu ɗaukaka masu rufe marfin jinƙai da fukafukan su"
A nan "kerubobi" suna nufin kerubobi biyu.
Kodashike marubucin ya yi amfani da kalmar nan "mu" da ke nufin fiye da ɗaya, ya fi dacewa a ce yana maganar kansa ne shi ɗaya. AT: "ba zan iya"
AT: "Bayan da firistocin sun shiya waɗannan abubuwa"
AT: "yakan kawo jinin"
Wato jinin bijimi da akuya da babban firist ke miƙa hadaya a rana ta yin kafara.
Wannan na iya nufin 1) ɗaki na ciki da ke cikin alfarwar da ke duniya ko kuma 2) Kasancewar Allah a sama.
Wannan na iya nufin 1) "ɗaki da ke wajen alfarwar na a tsaye" 2) "alfawar da ke dumiya da kuma yanayin hadaya da ke akwai"
"Wannan hoto ne" ko kuma "Wannan alama ce"
"na yanzu"
AT: "da firist ke miƙawa yanzu"
Marubicin yana maganar lamirin mutum kamar wani abu ne da ake iya sa ta tă daɗa kyau har ta zama ba laifi. Lamirin mutum shi ne sanin sa na abinda ke daidai da rashin daidai. Shi ne sanin sa ko ya aikata daidai ko bai aikata daidai ba. Idan ya san cewa ya yi ba daidai ba, muna cewa yana da laifi. AT: "basu iya sa mai ibada ya zama da rashin laifi"
Marubucin ya yi kamar yana maganar mutum ɗaya ne kawai mai yin sujada, amma yana nufin dukkan waɗanda suka taho su yi wa Allah sujada a alfarwa ne.
"har sai Allah ya yi sabuwar ka'idar"
"sabuwar alkawari"
Wannan ba kayan duniya ba ne. Amma yana nufin abubuwa masu kyau da Allah ya alkawarta a sabuwar alkawarinsa.
Wato gida da ke sama ko kuma alfarwa, wadda ya fi muhimmanci, kammalalle kuma fiye ma da alfarwar da ke a duniya.
AT: "wadda ba mutane ne suka gina ta ba"
A nan "hannuwa" na nufin mutum gabaɗaya. AT: "'yan'adam"
Ana maganar kasancewar Allah a sama ne a matsayin wuri mafi tsarki, ɗaki na ciki sosai na cikin alfarwar.
Firist ɗin zai yafa toka kaɗan a bisa jama'ar da suka ɓata tsarkinsu.
...
Marubucin yana amfani ne da wannan tambayan domin ya nanata cewa hadayar Almasihu shi ne mafi iko. AT: "To lallai jinin Almasihu zai tsarkakke lamirin mu har ma fiye daga matattun ayyuka zuwa bautar Allah mai rai! Domin ta wurin ruhu madawwami ne ya miƙa kansa marar aibi ga Allah"
Wannan wani ƙaramin zunubi ne ko kuma kuskure da ake maganarsu a nan kamar ƙaramin ɗigo da ba a saba ganin shi ba ko wani lahani a jikin Almasihu.
A nan lamiri na nufin yadda mutum ke jin alhakin laifi. Bai kamata masubi su ji alhakin zunubin da sun aikata a baya har yanzu ba domin Yesu ya ba da kansa hadaya ya kuma gafarce su.
A nan "tsarkake" na nufin ɗaukan mataki a kan nauyin da lamirin mu ke ji domin zunuban da muka aikata
Ana maganar halayen zunubi ne kamar sun zama na duniyar mattatu.
"Hakan ne ya sa" ko kuma "Saboda haka ne"
Wato Almasihu ne ya sa sabon alkawari tsakanin Allah da 'yan'adam ya kasance.
"don ɗaukan zunuban waɗanda suke ƙarƙashin alkawari na farko." Wannan na iya nufin 1) a nan "zunubansu" karin magana ne da ke nufin alhakin zunubansu" AT: "don ɗaukan alhakin waɗanda ke ƙarƙashin alkawarin farko" ko kuma 2) a nan "zunubansu" karin magana ne da ke nufin hukuncin zunubansu. AT: "ɗaukan hukuncin waɗanda ke ƙarkashin alkawarin farko"
AT: "waɗanda Allah ya zaɓa su zama 'ya'yansa"
Ana maganar karɓan abinda Allah ya alkawarta ne kamar gãdan dukiya ne da kuma arzikin na wani ɗan iyali.
Wannan wata takarda ce bisa tsarin doka da mutum ke sanar da mai mallakar dukiyarsa bayan ya rasu. Ana yin wannan sanarwar a rubuce.
AT: "dole ne wani ya tabbatar cewa wanda ya rubuta wanna wasiyar ha mutu"
AT: "Saboda haka, Allah ya tabbatar da alkawari na farkon ma tare da jini ne"
Firist ɗin yakan tsoma reshen itachen doddoya mai soso a cikin jinin da kuma ruwa sa'an nan ya jijjiga reshen itachen doddoyan domin ya yafa jinin da ruwan su zuzzuba a bisa littattafansu da kuma mutanen. Yayyafawar alama ce na abinda firist ke yi wanda ke nuna cewa dukkan fa'idodin alkawarin ya shafi mutanen da kuma abubuwan su. A nan samun karɓa da littattafan da mutanen ke da shi a wurin Allah sun sabunta kenan.
wani irin ciyawa ne mai ƙarfi da akan same shi da damina , ana amfini ne da shi a bukukkuwan suka shafi yayyafawa
A nan "jini" na nufin dabbobin da aka miƙa su hadaya domin su cika umurnin alkawarin. AT: "jinin da da ya tabbatar da alkawarin
"Musa ya yayyafa"
Yayyafawa alama ce da firistoci ke yi, ta wurin haka suke nuna cewa fa'idodin alkawarin sun shafi mutanen da kuma abubuwansu. Duba yadda aka fassara wannan a [:19]
kayayyakin da ake iya ajiye abubuwa a ciki. A nan tana nufin ko ma wane irin kayan girke-girke ko aiki. AT: "dukkan kayan girke-girke da ake amfani da su a hidimar"
AT: "da firistocin ke amfani da su cikin aikinsu"
Wato ana maganar sa abu ya zama karɓaɓɓe ga Allah a matsayin tsarkakken abu. AT: "firistoci suna amfani ne da jini domin su tsarkake kusan komai"
A nan "zubar da jini" na nufin mutuwar wani abu a matsayin hadaya ga Allah. Wannan na iya nufin cewa dukkan gafarar zunubi na zuwa ne ta wurin zuɓar da jini. AT: "Ana samun gafara ne kaɗai idan wani ya mutu a matsayin hadaya" ko kuma "Allah yana yafe wa kaɗai idan wani ya mutu a matsayin hadaya"
Ana iya bayyana ma'anan wannan a fili. AT: "gafarar zunuban mutane"
AT: "firistocin za su yi amfani da waɗannan hadayun dabbobin su tsarkake abubuwan da ke kwaikwayon abubuwa na sama"
Wato, fiye ma da hadayun da ake amfani da su don a tsarkake kwaikwayon da suke duniya. AT: "amma abubuwan da ke na sama da kansu, Allah ya tsarkake su da hadayu mafi kyau"
A nan "da hannuwa" na nufin "ta wurin 'yan'adam." AT: "wuri mafi tsarki, wadda 'yan'adam suka yi, kuma wanda"
"da ke wuri mafi tsarki"
"Bai shiga sama"
"kowace shekara"
wato da jinin wata dabba wanda aka azabtar, ba da jininsa ba.
"idan da hakane yakan miƙa kansa akai-akai"
kauda zunubi na nufin samun gafarar Allah. AT: "domin yă sa Allah ya gafarta zunubai ta wurin sadaukar da kansa" ko kuma "yă sadaukar da kansa domin Allah ya gafarta zunubi"
AT: "Almasihu ya miƙa kansa sau ɗaya tak"
Ana maganar sa mu mu zama mararsa zunubi a maimakon masu zunubi kamar zunubanmu wasu abubuwa ne da Almasihu ke iya ɗauka wa daga gare mu. AT: "domin Allah ya gafarta zunuban"
Anan "zunubai" na nufin laifin da mutane ke da shi a gaban Allah saboda zunuban da suka aikata.
Wuri sujada na alkawarin na farko ita ce alfarwa ta duniya.
Cikin wuri mai tsarki na alfarwa ta duniya inda mazaunin fitila da tabur da kuma keɓaɓɓiyar gurasar.
Cikin wuri mai tsarki na alfarwa ta duniya inda mazaunin fitila da tabur da kuma keɓaɓɓiyar gurasar.
Babban firist ya kan shiga wuri mafi tsarki sau ɗaya a kowace shekara, bayan ya miƙa hadaya ta jini don kansa da mutanen.
Hadayar ta alfarwa ta sujada ta ƙãsa tsarkake lamirin mai sujada.
Alfarwa ta duniya da kyautai da kuma hadayun da aka miƙa sun zama kamar misalin ne a wannan zamani.
An ba da ƙa'idan alfarwa ta duniya har zuwa loƙacin da sabuwar ƙa'idar za ta kassance.
Alfarwa mai tsarki da Almasihu ya yi hidima alfarwa ce mara aibi, ba da hannun ɗan adam aka yi ta ba, ba kuma ta wannan duniya da aka halita ba.
Almasihu ya yi hadaya da jininsa, ta wurin wannan ya shiga cikin wuri mafi tsarki.
Hadayar Almasihu ta ba da madawwammiyar ceto ga kowa.
Jinin Almasihu ya wanke lamirin masubi daga mataccen ayyuka don yin wa Allah rayayya hidima.
Almasihu ya zama matsakancin sabon alkawari.
Ana bukatan mutuwa domin al'amari wasiyya ya tabbata.
Ana buƙatan 'yan maruƙa tare da awaki don alkawari na farko.
Idan ba a zub da jini ba, ba za a sami gafara zunubai ba.
Almasihu ya bayana a cikin sama, a gaban Allaha, a maimaƙon mu
Almasihu ya miƙan kansa loƙaci ɗaya a ƙarshen zamanai don gafara zunubi ta wurin hadayar kansa.
Bayan kowane mutum ya mutu, sun fuskanci shari'a.
Bayyanuwa Almasihu na biyu zai zama domin ceton waɗanda suka yi hakurin jiransa.
1 Domin shari'a hoto ce na kyawawan abubuwan da ke zuwa, ba ainihin siffar wadannan abubuwa ba. Wadanda ke gusowa kusa da Allah ba za su taba ingantuwa ta wurin hadayu da firistoci ke mikawa shekara da shekaru ba. 2 In ba haka ba, ba sai a dena mika hadayun ba? Bisa ga wannan al'amari, inda sun tsarkaka sau daya tak da masu sujada ba su san menene zunubi ba. 3 Amma wadannan hadayun sun zama matuni ne na zunubi shekara biye da shekara. 4 Domin ba shi yiwuwa jinin bijimai da awakai su kawar da zunubai. 5 Yayin da Almasihu ya zo duniya, ya ce, "Ba hadayu da sadakoki kake marmari ba. Maimakon haka, ka shirya mini jiki domin hadaya. 6 Baka murna domin sadakoki da hadayu na konawa domin zunubi. 7 Sai na ce, 'Duba, gani na zo in yi nufinka, kamar yadda aka rubuta akaina.'" 8 Da fari Yace "ba hadayu, ko sadakoki, ko kuma hadaya ta konawa domin zunubi kake bukata ba. Ba ka kuwa jin dadinsu." Wadannan sune hadayun da ake bayarwa bisa ga shari'a. 9 Sa'annan sai ya ce "gani na zo domin in aikata nufinka." Ya kawar da hidimar farko domin ya kafa hidima ta biyu. 10 A hidima ta biyu, an kebe mu ga Allah ta wurin nufinsa ta wurin hadayar jikin Yesu Almasihu bugu daya ba kari. 11 Haka, kowanne firist ya ke tsayawa kulliyomi domin ya yi hidima ga Allah. A kullum yana mika hadayu, iri daya, koda shike ba za su taba kawar da zunubai ba. 12 A ta wata hanya kuma, Almasihu ya mika hadaya sau daya tak domin zunubai har abada, ya zauna a hannun dama na Allah. 13 Yana jiran har a maida makiyansa matashin sawayensa. 14 Domin ta wurin hadaya guda dayan nan ya kammala har abada ga wadanda suka sadaukar da kansu ga Allah. 15 Kuma Ruhu mai Tsarki ya shaida mana. Abu na farko yace, 16 "Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su a bayan kwanakin nan,' inji Ubangiji Zan sa dokokina a cikin zukatansu, kuma zan rubuta su a lamirinsu. 17 Ba zan sake tunawa da zunubansu da kurakuransu ba." 18 Yanzu fa duk in da aka sami gafara domin wadannan abubuwa, babu wata hadaya domin zunubi. 19 Saboda haka, yan'uwa, ba mu da shakkar shigowa wurin nan mafi tsarki ta wurin jinin Yesu. 20 Wannan ita ce sabuwar rayayyar hanya da ya bude mana ta wurin labulen, wato ta wurin jikinsa. 21 Saboda muna da babban firist a gidan Allah. 22 Bari mu matso kusa da sahihiyar zuciya, da kuma cikakken gabagadi cikin bangaskiya, da zuciyarmu wadda aka tsarkake daga mummunan tunani, da kuma jikunanmu wankakku da ruwa mai tsabta. 23 Bari mu rike da karfi shaidar bangaskiyar begenmu, ba tare da raurawa ba, domin Allahn, da ya yi alkawari, mai aminci ne. 24 Bari mu kuma yi lura yadda za mu iza juna ga kauna da ayyuka masu dacewa. 25 Kada mu fasa zumunci da juna, kamar yadda wadansu sukan yi. A maimakon haka, bari mu karfafa juna a kulluyomin, kamar yada kuke ganin kusantowar ranan nan. 26 Saboda idan mun ci gaba da zunubin ganganci bayan mun rigaya mun sami wannan sanin gaskiyar, hadayar irin wannan zunubi bata samuwa. 27 Maimakon haka, sai fargabar babban tsoron hukunci, da kuma wuta mai zafi, da zata cinye makiyan Allah. 28 Dukkan wanda ya ki bin dokar Musa zai mutu ba tausayi ta wurin shaidu biyu ko uku. 29 Wanne irin hukunci kuke tsammani ya dace ga wadanda suka raina Dan Allah, duk wadanda suka maida jinin alkawarin nan kamar ba tsarkakakke ba, wanda ta wurin jinin nan ne aka kebe shi ga Allah- wadanda suka wulakantar da Ruhun alheri? 30 Domin mun san wanda yace, "Ramako nawa ne; Zan yi sakayya." Sa'annan kuma, "Ubangiji zai hukumta jama'arsa." 31 Abin tsoro ne a fada cikin hannuwan Allah mai rai! 32 Amma ku tuna da kwanakin baya, bayan da ku ka sami haske, yadda kuka jure babban fama cikin wahala. 33 Aka kunyatar da ku a gaban jama'a, ta wurin ba'a da cin mutunci, kuna kuma dandana irin azabar da wadansu suka shiga ciki. 34 Domin kuna da tausayi ga wadanda suke kurkuku, da farin ciki, kun amince da kwace na dukiyarku da aka yi, kun mallaki madauwamiyar mallaka mafi kyau. Dominn kun ji tausayina sa'adda na ke a kurkuku. 35 Don haka kada ku yarda gabagadinku, wanda ke da babban sakamako. 36 Domin kuna bukatar hakuri don ku sami abin da Allah ya alkawarta, bayan kun aikata nufinsa. 37 "Domin a dan karamin lokaci, mai zuwan nan zai zo ba zai yi jinkiri ba. 38 Adalina kuwa zai rayu ta wurin bangaskiya. In kuwa ya ja da baya, ba zan yi farin ciki dashi ba." 39 Amma mu bama cikin wadanda suka ja da baya zuwa hallaka. Maimakon haka, muna cikin wadanda suke da bangaskiya domin kula da rayukanmu.
Marubucin yana nuna gazawar shari'a da hadayu, dalilin da ya sa Allah ya ba da shari'a, da kuma kammalawar sabuwar firistanci da kama hadayar Almasihu.
Wannnan na maganar shari'a kamar ita wata hoto ce. Marubucin na nufin cewa ba shari'ar bane abu mai kyau da Allah ya alkawarta. Ya ɗan ambato kaɗan daga abubuwa masu kyaun da Allah zai yi.
"ba ainihin abubuwan da kansu ba"
"kowace shekara"
Marubucin yana amfani ne da wannan tambaya ya sanar cewa ƙarfin hadayun sun gaza. "da sun daina yin hadayun"
"tsayar da kasancewa"
A nan samun tsarkakewa nan nufin ba su kuma da wani hakin zunubi. AT: "da hadayun sun kau da zunuban su" ko kuma "Da Allah ya kawar masu da hakin zunubi"
"ba su san cewa suna da hakin zunubi ba" ko kuma "za su san cewa basu da wata hakin zunubi kuma"
Ana maganar zunubai ne kamar wasu abubuwa ne da jinin dabba ke iya kawar da su yayin da yake zubowa. AT "Gama ba shi yiwuwa jinin bijimai da awaki su sa Allah ya gafarta zunubai"
A nan "jini" na nufin mutuwar waɗannan dabbobi a matsayin hadayu ga Allah.
An faɗi maganar Almasihu alokacin da yake duniya a wata furucin da ke littafin Zabura da Dauda ya rubuta.
A nan "ka" na nufin Allah ne.
"ka shirya mini wata jiki"
Anan "na" na nufin Almasihu ne.
AT: "kamar yadda annabawa suka rubuta game da ni a Littafi"
Wato Littafin Masubi kenan ko kuma rubuce-rubuce masu tsarki.
Duba yadda aka juya waɗannan kalmomi a [10:5-6]
AT: "da firist ke bayarwa"
"Duba" ko "saurara" ko "Sa hankali ga abinda zan faɗa maka"
A nan "hidima" na nufin wata hanyar tuɓa daga zunubai. Ana maganar ƙin aikata shi kamar wani abu ne da ake iya kawar da shi. Ana maganar fara aikata shi na biyu kamar kafa wannan hidimar ne. AT: "Ya hana mutane miƙa hadayar zunubi a hanya ta farko domin ya miƙa hadayan zunuban a hanya ta biyun"
Kalmomin nan "farko" da "biyu" suna jerin kirge ne. AT: "tsohon hidima ... sabuwar hidimar"
AT: "Allah ya kaɓe mu" ko kuma "Allah ya miƙa mu ga kansa"
Ana iya bayyana kalmar nan "miƙa" da kalmomin nan "bayar" ko kuma "hadaya." AT: "domin Yesu Almasihu ya miƙa jikinsa hadaya" ko kuma "domin Yesu Almasihu ya yi hadaya da jikinsa"
"koda yaushe" ko kuma "kowace rana"
Wannan na maganar "zunubai" ne kamar su wasu abubuwa ne da ake iya kawar da su. AT: "ba za su taɓa iya sa Allah ya gafarta zunubai ba"
A zauna "a hannun dama na Allah" misali ne na samun matuƙar daraja da iko daga Allah. Duba yadda aka juya wannan jumlar a [1:3]. AT: "ya zauna a wurin daraja da iko a gefen Allah"
Ana maganar yadda Almasihu zai ƙasƙantar da maƙiyansa ne kamar za a mayar da su wuri ne da zai ajiye kafafunsa a kai. AT: "har sai Allah ya ƙasƙantar da maƙiyansa su zama kamar kujera da zai sa kafafunsa a kai"
AT: "waɗanda Allah yake tsarkekewa" ko kuma "waɗanda Allah ya miƙa su ga kansa"
"da jama'a ta" ko kuma "da mutane na"
"sa'anda lokacin alkawari na da mutane na ya kãre"
A nan "zukatan" na nufin hankalin mutum. Jumlar nan "sa su a cikin zuciyarsa" na nufin iza su su yi biyayya da dokokina. AT: "Zan iza su su yi biyayya da dokokina"
Wannan wata karin magana ne da ke nufin a sa mutane su fahimci doka. AT: "Zan iza su su fahimci dokokina"
"Ba zan tuna da zunubansu da kurakuran su kuma ba. To yanzu" ko kuma "Ba zan yi tunanin zunubansu da kurakuransu kuma ba. To yanzu" Ana iya ƙara bayanin sashin shaidar Ruhu Mai Tsarki na biyun [10:15-16] a fili a juyin ta wurin kammala furucin a karshen aya 16 da kuma fara wani sabuwar furuci a nan. AT: "Sa'annan ya ce, 'Zunubansu da kurakurasu ba zan tuna kuma ba.' To yanzu"
Kalmomin nan "zunubai" da "kurakuran" na da ma'ana ɗaya. Dukansu suna nanata yadda tsananin zunubin yake. AT: "An haramta abubuwan da suka aikata da kuma yadda suka ƙarya doka"
Wannan ba ya nufin "a daidai wannan lokaci", amma yana jan hankali ne zuwa ga wani abu mai muhimmanci da ke biye.
AT: "da Allah ya gafarta waɗannan abubuwan"
Ana iya canja fasalin wannan kalma "hadaya" zuwa "miƙa hadaya" AT: "mutane basu bukatar miƙa hadaya domin zunubi"
Wato dukkan masubin Almasihu kenan, maza da mata. AT: "maza da mata" ko kuma "'yan'uwa masubi"
Wato gaban Allah kenan, ba wai wuri mafi tsarki da ke tsohon alfarwar ba.
A nan "jinin Yesu" na nufin mutuwar Yesu kenan.
Wannan na iya nufin 1) sabuwar hanyar zuwa wurin Allah da Yesu ya zama sanadiyar sa masubi su rayu har abada. ko kuma 2) Yesu yana da rai, kuma ta wurinsa ne masubi ke zuwa gaban Allah.
Labulen da ke a haikalin duniya na wakilllcin maraban da ke tsakanin mutane da aihihin gaban Allah.
A nan "jikinsa" na nufin jikin Yesu kenan, jikinsa kuma yana nufin mutuwarsa. AT: "ta wurin mutuwansa"
Lallai ne a juya wannan a hanyar da zai bayyana a fili cewa Yesu ne wannan "babban firist."
"mai mulki a gidan"
Wannan na maganar jama'ar Allah kamar su ginannen gida ne. AT: "duk jama'ar Allah"
A nan "matso" na nufin yi wa Allah sujada, kamar yadda firist zai haura zuwa haikalin Allah ya miƙa masa hadayar dabbobi.
"da amintattciyar zuciya" ko kuma "da zuciya mai gaskiya." A nan "zuciya" na nufin manufa mai kyau da ƙarfafawar masubi. AT: "da gaskiya" ko kuma "a gaskiya"
"da kuma gabagaɗin bangaskiya" ko kuma "da matuƙar dogara ga Yesu"
AT: "kamar ya tsarkakke zuciyarmu da jininsa"
A nan "zuciya" na nufin lamiri, sanin abinda ke daidai da wanda ba daidai ba. Tsarkakewa na nufin samun gafara da kuma samun matsayin adalci.
...
AT: "kamar ya wake jikunanmu da ruwa mai tsabta"
Idan mau juyi ya fahimci wanna jumlar a matsayin baftismar Maibi, to ana nufin ainihin ruwa kenan, ba alama ba. Amma idan mai juyi na ɗauki ruwa a matsayin ainihin ruwa, to "tsabta" alama ce da ke nufin tsabta a ruhaniya da baftisma ke kawo wa. "Wankin" na nufin samun karɓa a gaban Allah na maibi.
A nan "riƙe da ƙarfi" karin magana ne da ke nufin ƙudiri da mutum ke yi na zuciya da yin abu ba tare da yarda yă bari ba. AT: "Bari mu ƙudura mu cigaba da faɗa wa mutane cewa muna da gabagaɗi domin mun gaskata Allah zai yi abin da ya alkawarta"
Ana maganar rashin tabbacin abu kamar shi wani abu ne dake kaɗawa daga wannan gefen zuwa wancan gefen. AT: "ba tare da rashin tabbaci ba" ko kuma "ba tare da shakka ba"
Ana iya bayyanawa a fili cewa jama'a sukan haɗu domin sujada. AT: "Kada mu daina tattaruwa domin yin sujada"
Anan maganar nan gaba kamar wani abu ne da ke matsowa kusa da mai magana. AT: "kamar yadda kun san cewa Allah zai dawo nan ba da jimawa ba" (Dubi: and
"mun san cewa muna yin zunubi amma duk da haka mun ci gaba da shi akai-kai"
Ana maganar sanin gaskiya kamar wani abu ne da wani ke ba wa wani. AT: "bayan mun san wannan gaskiya"
Gakiya game da Allah.
Babu wanda zai iya miƙa irin wannan sabuwar hadaya domin hadayar Almasihu ne kaɗai ke aiki. AT: "babu wanda zai iya miƙa irin hadaya da zai sa Allah yă gafarta zunubanmu"
A nan "hadayar irin wannan zunubi" na nufin "wata hanya mafi dacewa na miƙa hadayar dabbobi domin kawar da zunubai"
na hukuncin Allah, wato, cewa Allah zai hukunta.
Ana maganar fushin Allah kamar wata wuta ce da ke iya kona maƙiyansa.
Ana ɗaukan cewa wannan na nufin "ta wurin shaidu da basu ƙasa biyu ko uku ba"
Marubucin yanan nanata tsananin hukuncin waɗanda sun ƙi Almasihu ne. AT: "Wannan hukunci ne mai tsanani. Amma hukuncin ma zai fi tsanani ga duk ... alheri!"
AT: "suka ƙi Ɗan Allah"
Wannan wata laƙabi ne mai muhimmanci na Yesu.
Wannan na nuna yadda mutumin ya raina Ɗan Allah. AT: "ta wurin mai da jinin alkawali kamar ba tsarkakke be"
A nan "jini" na nufin mutuwar Almasihu, wadda ta wurinshi ne Allah ya kafa sabuwar alkawari.
AT: "jinin da ta wurin sa ne Allah ya keɓe shi"
"Ruhun Allah, mai tanadin alheri"
Ana maganar ramako kamar wani abu ne da ke na Allah, wanda yana da 'yancin yin yadda ya ga dama da abinda ke nashi. Allah yana da 'yancin ɗaukan ramako a kan maƙiyansa"
Ana maganar ɗaukar ramako kamar biyan wani abu mai hatsari ne da wani ya yi wa wasu.
Ana maganar gamuwa da horon Allah kamar mutum yă faɗa ne a hannun Allah. A nan "hannu"na nufin ikon hukunci na Allah. AT: "a gamu da hukuncin Allah"
"a lokacin da ya wuce"
Ana maganar samun gaskiya kamar Allah ya haska wata wuta ce ga mutum. AT: "bayan da kuka samu sanin gaskiya game da Amasihu"
"yawan wahala da kuka jure"
AT: "mutane suka kunyatar da ku, ta wurin yi maku ba'a da kuma cin mutuncin ku a gaban jama'a"
"kun haɗa kai da waɗansu"
Ana maganar madawamiyar albarkun Allah ne kamar wata "mallaka"
Ana maganar mutum marar gabagaɗi kamar dai mutumin zai yar da bangaskiyar ne, kamar yadda mutum yake yin banza da abin da ba shi da amfani. AT: "kada ku daina zama da gabagaɗi, domin za ku samu babban sakamako na zama da gabagaɗi" ko kuma "kada ku daina dogara ga Allah da gabagaɗi, wanda shi ne zai ba ku babbar lada"
Ana iya ƙara faɗin wannan a fili. AT: "Kamar yadda Allah ya faɗa a Littafi, 'Domin a ɗan karamin lokaci"
"nan da nan"
Wannan na nufin ko ma wanene daga cikin jama'ar Allah gabaɗaya. AT: "Mutane na masu aminci ... In kuwa ɗaya daga cikinsu ya ja da baya ... da mutumin" ko kuma "Mutane na ... in kuwa sun ja da baya ... da su"
A nan "na" da "zan" na nufin Allah kenan.
daina aikata abubuwan nagarta da yake yi
Ana maganar mutumin da ya rasa karfin ziciyar da bangaskiya kamar mutum ne da ke matsawa baya domin tsoron wani abu. Ana kuma maganar "hallaka" kamar wani wuri ne da ake iya zuwa. AT: "waɗanda sun daina dogara ga Allah, wanda zai sa shi ya hallaka mu"
Ana maganar rayuwa har abada da Allah kamar kula da ran mutun ne. A nan "rai" na nufin mutum gabaɗaya"
Shari'ar ishara ce kawai ba ainihin siffarsu ba indan an kwatanta shi da gaskiyar da ke cikin Almasihu.
Hadayun da aka saɓa yi ta wurin shari'ar na tunashe da masu sujada zunuban da suka yi shekara bayan shekar.
Ba shi yiwuwa jini bijimi da awaki su shafe zunubai.
Allah ya shirya wa Amasihu jiki.
Allah ya maishe da al'ada ta farko na hadayun da ake miƙawa bisa ga shari'ar.
Allah ya kafa al'ada ta biyu na miƙa jikin Yesu Almasihu sau ɗaya domin dukka.
Almasihu na jira har sai an ƙasƙantar da makiyinsa a kuma yi wa ƙafafunsa mazauni.
Almasihu ya kammala waɗanda an tsarkake ta wurin hadayar da ya yi sau ɗaya.
Ba a buƙatan wata hadaya kuma a inda akwai gafara zunubai.
Masubi za su iya shiga wurin mafi tsarki ta wurin jinin Yesu.
An wanke zuciyar maibi daga muguwar lamiri, an kuma wanke jikinsa da ruwa mai tsarki.
Lallai ne masubi su riƙe shaidar gabagadi game da abin da suke sammani.
Lallai ne masubi su ƙarfafa juna sa'ad da sun ga ranar tana gabatowa.
Abin sammani ga waɗanda sun cigaba da yin zunubi bayan sun sami sanin gaskiya shine hukunci da wuta da zata cinye maƙiyin Allah
Mutumin da ya maishe jinin Almasihu, wadda aka tsarkake shi, a matsayin abu mara tsarki ya cancanci hukunci batare da an yi masa jinkai fiye da hukuncin da aka bayar bisaga ga Shari'ar Musa ba.
Ramako na Ubangiji ne.
Masubin sun karɓi kwacen da aka yi musu na mallakarsu da farinciki, da sanin cewa suna da mallaka mafi kyau na har abada.
Mai bi na buƙatan gabagadi da kuma haƙuri don ya sami abin da Allah ya alkawarta.
Allah bai ji daɗin waɗanda suka juya baya ba.
Masu adalcin za su yi rayuwa ta wurin bangaskiya.
Marubucin na sa zuciyar cewa waɗanda suka sami wasikar sa za su sami bangaskiyar da zata ba su rai.
1 Bangaskiya ita ce tabbatawar al'muran da muke begensu. Ita ce tabbatawar al'amuran da idanu basu gani. 2 Domin ta wurin ta ne kakanninmu suka sami yardar Allah. 3 Ta wurin ta ne aka hallicci duniya da umarnin Allah, har ma abubuwan da ake gani ba'a yi su daga abubuwan da suka kasance ba. 4 Ta dalilin bangaskiya ne Habila ya mikawa Allah hadaya da ta fi dacewa fiye da ta Kayinu. Don haka ne kuma aka yaba masa akan cewa shi adali ne. Ya sami yardar Allah sabili da sadakarsa da ya bayar. Don haka kuma, harwayau Habila yana magana, ko da shike ya rigaya ya mutu. 5 Ta dalilin bangaskiya aka dauki Anuhu zuwa sama domin kar ya ga mutuwa. "Ba a same shi ba kuwa, domin Allah ya dauke shi." Kamin a dauke shi an shaida da cewa ya faranta wa Allah zuciya. 6 Zai yi wuya matuka a faranta wa Allah zuciya in ba tare da bangaskiya ba. Domin ya kamata dukkan wanda zai zo ga Allah, tilas ne ya bada gaskiya da kasancewar sa, kuma shi mai sakamako ne ga dukkan masu nemansa. 7 Ta dalilin bangaskiya Nuhu, ya karbi sako daga Allah akan al'amuran da ba'a gani ba, ta wurin girmamawa da rawar jiki. ya gina jirgin ruwa domin ya ceci iyalan sa. Dalilin haka kwa, Allah ya hallakar da duniya, Nuhu kwa ya gaji adalci wadda ke bisa ga bangaskiya. 8 Ta dalilin bangaskiya ne Ibrahim, sa'an da aka kira shi, ya yi biyayya sai ya tafi wurin da zai karba a matsayin gado. Ya kwa fita bai ma san inda za shi ba. 9 Ta dalilin bangaskiya kuma ya zauna bare a kasar alkawari. Ya yi zama cikin Alfarwa tare da Ishaku da Yakubu, magadan alkawari guda tare da shi. 10 Domin yana hangar birnin da ke da tushi, Birnin da mai zaiyanar sa da ginin sa shine Allah. 11 Ta dalilin bangaskiya, Ibrahim ya sami haihuwa ko da shike shi da matarsa Saratu sun yi nisa a cikin shekaru, kuma Saratu bakarariya ce, ta kuma wuce lokacin haihuwa. Tun da shike sun amince da wanda ya yi musu alkawari mai aminci ne. 12 Sabo da haka, ta wurin mutumin nan daya, wanda ya ke kamar matacce ne, aka haifi zuriya mai dimbin yawa, su ka yawaita kamar taurari a sama kamar yashi a bakin teku, wanda ba shi kidayuwa. 13 Dukkan su kuwa suka mutu a cikin bangaskiya ba tare da sun karbi alkawarin ba. Maimakon haka, sun hango, kuma sun marabcesu daga nesa, sai suka amince su baki ne kuma matafiya ne a duniya. 14 Gama wadanda suka yi furci haka sun nuna a fili cewa suna bidar kasa ta kansu. 15 Da kamar suna tunanin kasar da suka fita daga ciki, da sun sa mi damar komawa. 16 Amma kamar yadda yake, sun bukaci kasa mafi dacewa, wato, wadda take a sama. Saboda haka ne Allah bai ji kunyar a kira shi Allahnsu ba, da shike ya shirya birni dominsu. 17 Ta dalilin bangaskiya ne Ibrahim, sa'adda aka yi masa gwaji, akan ya mika Ishaku dansa hadaya. 18 Shi ne kuwa makadaicin dansa, wanda aka yi alkawari da cewa, "Ta wurinsa ne za a kira zuriyarka." 19 Ibrahim ya yi tunani da cewa Allah na da ikon tada Ishaku ko daga cikin matattu ma, haka kuwa yake a misalce, daga matattun ne ya sake karbarsa. 20 Ta dalilin bangaskiya ne kuma Ishaku ya albarkaci Yakubu da Isuwa game da abubuwan da ke zuwa a gaba. 21 Dalilin bangaskiya ne Yakubu, sa'adda yake bakin mutuwa, ya albarkaci 'ya'yan Yusufu dukkansu biyu. Yakubu ya yi ibada, yana tokare a kan sandarsa. 22 Ta dalilin bangaskiya Yusufu, sa'adda karshensa ya kusa, ya yi magana game da fitar 'ya'yan Isra'ila daga Masar har ya umarce su game da kasussuwansa. 23 Ta dalilin bangaskiya Musa, sa'adda aka haife shi, iyayensa suka 'boye shi kimanin watanni uku domin kyakkyawan yaro ne shi, kuma basu ji tsoron dokar sarki ba. 24 Ta dalilin bangaskiya ne kuma Musa, sa'adda ya girma, yaki a kira shi 'dan diyar Fir'auna. 25 A maimakon haka, ya amince ya sha azaba tare da jama'ar Allah, a kan shagali da annashuwar zunubi na karamin lokaci. 26 Ya fahimci cewa wulakanci domin bin Almasihu babbar wadata ce fiye da dukiyar Masar. Gama ya kafa idanunsa a kan sakamakon da ke gaba. 27 Ta dalilin bangaskiya Musa ya bar Masar. Bai ji tsoron fushin sarki ba, ya jure kamar yana ganin wannan da ba a iya ganinsa 28 Ta dalilin bangaskiya ya yi idin ketarewa da kuma yayyafa jini, domin kada mai hallaka 'ya'yan fari ya taba 'ya'yan fari na Isra'ila.` 29 Ta dalilin bangaskiya suka haye baharmaliya kamar bushashiyar kasa. Sa'adda Masarawa su ka yi kokarin hayewa, bahar din ta hadiye su. 30 Ta dalilin bangaskiya ganuwar Yeriko ta fadi, bayan sun kewaya ta har kwana bakwai. 31 Ta dalilin bangaskiya Rahab karuwan nan bata hallaka tare da marasa biyayya ba, don ta saukar da masu leken asirin kasa a gidanta, ta kuma sallame su lafiya. 32 Me kuma za mu ce? Gama lokaci zai kasa mini idan zan yi magana game da Gidiyon, Barak, Samson, Yefta, Dauda, Sama'ila, da annabawa. 33 Ta dalilin bangaskiya suka ci nasara kan kasashe, suka yi aikin adalci, sa'annan suka karbi alkawura. Suka rufe bakin zakuna, 34 suka kashe karfin wuta, suka tsira daga bakin takobi, suka sami warkaswa daga cutattuka, suka zama jarumawan yaki, sa'annan suka ci nasara akan rundunar sojojin al'ummai. 35 Mata kuwa suka karbi matattunsu da aka tayar daga mutuwa. Aka azabtar da wadansu, ba su nemi yancin kansu ba, domin suna begen tashi daga mattatu. 36 Wadansu kuwa suka sha ba'a da duka da bulala, har ma da sarka da kurkuku. 37 A ka jejjefe su. Aka tsaga su kashi biyu da zarto. A ka karkashe su da takobi. Su na yawo sanye da buzun tumakai da na awaki, suka yi hijira, suka takura, suka wulakantu. 38 Duniya ma ba ta dauke su a matsayin komai ba. Suka yi ta yawo a jazza, da duwatsu, da kogwanni, da kuma ramummuka. 39 Ko da yake mutanen nan amintattun Allah ne domin bangaskiyarsu, basu karbi cikar alkawarin ba tukunna. 40 Domin Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau ba kuwa za su kammala ba sai tare da mu.
Marubucin ya faɗi abubuwa uku game da bangaskiya a wanna taƙaitaccen gabatarwa.
Ana amfani ne da wannan kalmar a nan domin a nuna canji daga ainihin koyarwa da ake yi. A nan marubucin ya fara bayyana ma'anan "bangaskiya".
AT: "Idan muna da bangaskiya, muna da tabbacin abubuwan da muke begensu" ko kuma "Bangaskiya ita cene abinda ke barin mutum ya sa zuciya da gabagaɗi a kan wasu abubuwa na musamman"
A nan wannan na nufin tabbacin alkawarai na Allah, musamman ma tabbacin cewa dukkan masubin Yesu za su kasance da Allah a sama har abada.
AT: "da har yanzu ba mu iya gani ba" ko kuma "da har yanzu ba su faru ba"
"Domin suna da tabbaci game da abubuwan da basu faru ba tukuna"
AT: "Allah ya yarda da kakanninmu domin suna da bangaskiya ne"
Marubucin yana magana ne da Ibraniyawa akan kakanninsu.
AT: "Allah ya hallic duniya ta wurin ba ta umarni ta kasance"
AT: "Allah bai halita abubuwan da muke gani daga abubuwa da ake gani ba"
AT: "Allah ya ce da shi mai adalci" ko kuma "Allah ya ce da Habila ma adalci ne"
Ana maganar karatun Littafi da yin koyi da bangaskiyar Habila ne kamar Habila ne da kansa yana kan magana. AT: "Harwayau muna koyi da abinda Habila ya yi"
AT: "Ta wurin bangaskiya ne Anuhu bai mutu ba domin Allah ya ɗauke shi"
Ana maganar mutuwa kamar wani abu ne da ake iya gani da ido. Wato a ɗanɗana mutuwa kenan. AT: "mutu"
AT: "kafin Allah ya ɗauke shi"
Wannan na iya nufin 1) "Allah ya ce Anuhu ya gamshe shi" ko kuma 2) "Mutane sun ce Anuhu ya gamshi Allah."
A nan ana amfani ne da wannan kalmar "to" domin a jawo hankali zuwa ga wata darasi mai muhimmanci da ke biye.
AT: "mutum na iya faranta wa Allah zuciya idan yana da bangaskiya ga Allah"
Ana maganar son yi wa Allah ibada da kuma zama ɗaya daga cikin jama'arsa kamar mutum yana ainihin zuwa gun Allah ne. AT: "cewa dukkan wanda yana son yă zama na Allah ne"
"yana saka wa duk masu"
Ana maganar waɗanda suke da sanin Allah suna kuma ƙoƙarin yi masa biyayya kamar suna neman su same shi ne.
AT: "domin Allah ya faɗa masa"
AT: "akan abubuwan da ba wanda ya taɓa gani" ko kuma "game da abubuwan da basu auku ba tukuna"
An an "duniya" na nufin mutanen duniya. AT: "jama'ar da ke duniya a wannan lokaci"
Ana maganar Nuhu kamar ya gãji dukiya ne da arziki da wani ɗan iyali. AT: "ya samu adalcin Allah"
"wadda Allah ke ba wa waɗanda ke da bangaskiya gare shi"
AT: "sa'an da Allah ya kira shi"
"bar gida zuwa wurin"
Ana maganar ƙasa da Allah ya alkawarta zai ba wa Ibrahim ne kamar wata gãdo ce da zai karɓa. AT: "da Allah zai ba shi"
"Ya kuwa bar gidansa"
Ana iya amfani da wasu kalmomi da za su nuna cewa "alkawari" ɗin na nufin an "alkawarta." AT: "ya zauna bare a ƙasar da Allah ya alkawarta masa"
"magada tare." Wannan na magana game da Ibrahim, Ishaku, da Yakubu ne kamar su magada ne da za su karɓi gãdo daga gun ubansu.
"birini mai tushe." Mai tushe na nufin birni da ke dawamamme. AT: "birnin har abada"
"wadda Allah ne ya zanata ya kuma gina" ko kuma "wadda Allah ne zai zana ta yă kuma gina"
mutum mai zana gine gine da kuma birane
Ana iya juya kalmar nan "bangaskiya" zuwa "gaskata". Wannan na iya nufin 1) Ta dalilin bangaskyar Ibrahim ne" AT: "saboda Ibrahim ya gaskata da Allah ne" ko kuma 2) ta dalilin bangaskiyar Saratu ne. AT: "saboda Saratu ta gaskanta da Allah ne"
"ya iya samun ya zama uba" ko kuma "ya iya samun ɗa"
"domin ya gaskanta da Allah ne, wadda ya ba da wannan alkawari, amintacce ne"
"ya wuce shekarun samu 'ya'ya" ko kuma "tsoho ne ƙwarai"
Wannan na nufin cewa Ibrahim na da zuriya da yawa kenan.
Wannan na nufin cewa kamar yadda akwai yashi sosai a bakin teku, babu mai iya ƙidaya su duka, Ibrahim yana da zuriya da yawa da babu mai iya ƙirga su dukka.
Wannan na maganar alkawaran kamar wasu abubuwa ne da mutum ke karɓa. AT: "ba tare da karɓar abinda Allah ya alkawartar masu ba"
Anan maganar alkawarin da ke nan gaba ne kamar matafiya ne da ke zuwa daga nesa. AT: "bayan sanin abinda Allah zai yi masu nan gaba"
"sai suka amince" ko kuma "sai suka amsa"
A nan "baƙi" da "matafiya" na nufin abu ɗaya ne a takaice. Wannan na nanata cewa wannan duniya ba gidansu ta ainihi ba ce. Suna dai jiran gidansu ta ainihi da Allah zai gina masu.
"ƙasa da za ta zama ta su"
"wadda take ƙasar sama" ko kuma "ƙasa sa sama"
AT: "Allah yana jin daɗi su ce da shi Allahnsu" ko kuma "Allah yana fahariya su ce da shi Allahnsu"
AT: "sa'ad da Allah ya gwada shi"
AT: "wanda Allah ya faɗi"
A nan "kira" na nufin a sanya ko kuma naɗa. AT: "cewa ni zan naɗa zuriyarka"
"Allah na da iko ya sa Ishaku ya rayu kuma"
A wannan aya, "yă tada" na nufin ya sa masa rai. Kalmomin nan "daga matattu" na maganar dukkan matattu gabaɗaya a ƙarƙashin ƙasa.
"a wata yanayin magana." Wannan na nufin cewa a fahimci abinda marubucin zai faɗa kuma ba zahiri ba ne amma karin magana ne. Allah bai tada Ishaku daga matattu a zahiri ba. Amma domin daidai lokacin da Ibrahim zai miƙa hadayar Ishaku sai Allah ya hana shi, to wannan kamar Allah ya tada shi daga mattatu ne.
"daga matattun ne"
"Ibrahim ya sãke karɓar Ishaku"
"Yakubu ya yi wa Allah ibada"
A nan "ƙarshensa" wata hanya ce na maganar mutuwa. AT: "sa'ad da ya yi kusa da mutuwa"
"ya yi maganar lokacin da 'ya'yan Isra'ilawa za su bar ƙasar Masar"
"Isra'ilawa" ko kuma "zuriyar Isra'ila"
Yusufu ya mutu yayin da yake ƙasar Masar. Yana son mutanensa su ɗauki kasusuwansa tare da su a lokacin da za su bar ƙasar Masar domin su bizne ƙassusuwansa a ƙasar da Allah ya yi masu alkawari.
AT: "Musa, iyayensa sun ɓoye shi kimanin watani uku bayan haifuwarsa"
"ya zama babba"
AT: "ya ƙi mutuane su ce da shi"
Ana iya juya wannan kalma "wulakanci" zuwa "rashin bangirma." AT: "rashin samun girma da ga gun mutane domin ya aikata abinda Almasihu ke so"
Ana maganar biyayya da Almasihu kamar binsa ne zuwa wata hanya.
Ana maganar sa hankali gabaɗaya ga cimma burin samun wani abu kamar mutum yana zuba wa abun ido ne har ma ya ƙi yă kalli wani wuri.
Ana maganar Musa ne kamar ya ga Allah, wadda ba a iya gani.
"wanda ba mai iya gani"
Wannan itace Idin Ƙeterewa na farko. Musa ya yi wannan ta dalilin yin biyayya ne da umarnin Allalh game da Ƙeterewar da kuma umartar mutanen su riƙa yin haka a kowace shekara. AT: "ya umarce mutanen su yi biyayya da umarnin Allah game da ƙeterewar da kuma yayyafa jini a kofofinsu" ko kuma "ya kafa Ƙeterewar da kuma yayyafa jini"
Wannan na nufin umurnin Allah ga Isra'ilawa cewa su kashe ɗan tinkiya sai su yafa jininsa a bisa kofofin kowane gida da Isra'ilawan ke zama. Wannan zai hana mai hallakar da 'ya'yan su na fari. Wannan yana ɗaya daga cikin dokokin Ƙeterewar.
A nan "taɓa" yana nufin a yi rauni ko a yi kisan wani. AT: "ba zai jawo rauni ba" ko kuma "ba zai kai ga kisa ba"
A nan kalmar nan "su" na farko na nufin Isra'ilawa, "su" na biyun na nufin "Masarawa", "su" na ukun na nufin ganuwan Yerico.
"Isra'ilawa suka haye Bahar Maliya"
AT: "ruwan ta haɗiye Masarawan"
AT: "Isra'ilawan suka riƙa tafiya suna zagaya ta har kwana bakwai"
"kwana 7"
"da salama ta karɓi masu lekan asirin"
Marubucin yana amfani ne da wannan tambayan don ya nanata cewa akwai misalai da dama da zai iya ambatowa. AT: "Har yanzu akwai misalai da dama".
"ba ni da lokaci isasshe"
Wannan sunan wani mutum ne.
A nan "su" ba ya nufin kowane mutum da aka ambata a 11:32 ya yi dukkan abubuwan da marubucin zai ambato. Marubucin yana dai cewa ga irin abubuwa da waɗanda ke da bangaskiya suka iya yi. AT: "Ai ta dalilin bangaskiya ne mutane kamar haka"
A nan "masarautai" na nufin mutanen da ke zama a wurin. AT: "suka yi nasara da mutanen wasu masarautai"
Waɗanna wasu hanyoyi ne kullum da Allah ke cetas da masubi daga mutuwa. AT: "Zakuna basu cinye su ba, wuta bai ƙone su ba, abokan gabansu basu kashe su ba. Suka"
AT: "samu warkaswa daga gun Allah" (Dubi:
"sa'an nan suka zama jarumawan yaƙi suka kuma ci nasara"
Ana iya sanar da wannan ba tare da an ambaci "tayar" ba. AT: "Mata kuwa suka karɓi matattumsu da rai waɗanda sun mutu"
Ana ɗaukan cewa maƙiyan su na iya sake su daga kurkuku bisa ga wasu ka'idodi. AT: "Wasu sun gwammaci su sha azaba da a sake su daga kurkuku" ko kuma "Wasu sun bar maƙiyansu su sa su su sha azaba da su yi abinda maƙiyan ke so su yi don a sake su"
a sa mutum ya sha wahala da zafi ƙwarai da gaske a hankali da kuma a jiki
Wannan na iya nufin 1) Waɗannan mutane za su ɗanɗana rayuwa mafi kyau a Sama har ma fiye da wanda sun ɗanɗana a nan duniya, ko kuma 2) waɗannan mutanen za su sami tayarwa mafi kyan sosai fiye da waɗanda basu da bangaskiya. Masu bangaskiya za su yi rayuwa tare da Allah har abada. Waɗanda ba su da bangaskiya kuma za su yi rayuwa a raɓe nesa da Allah.
AT: "Mutane kuwa suka yi wa wasu ba'a suka bulalesu ... Mutane suka jefe wasu da duwatsu. Mutane suka tsaga wasu kashi biyu da zarto. Mutane suka karkashe wasu da takobi"
AT: "Allah ya gwada wasu ta wurin barin maƙiyansu su yi masu ba'a, su kuma bulale su, har ma su ɗaure su da sarƙoƙi su kuma jefa su a kurkuku"
"suna tafiya nan da can" ko kuma "rayu kowane lokaci"
"suna sanye da fatan tumaki da na awaki ne kurum"
"ba su da komai" ko kuma "cikin talauce ƙwarai"
A nan "duniya" na nufin mutane. AT: "Mutanen duniyan nan basu cancanci"
Ya zama haka ne domin sun rasa wurin zama ne.
"kogwanni, wasu kuma sun yi zama a ramummuka a cikin ƙasa"
AT: "Allah ya daraja dukkan waɗannan saboda bangaskiyarsu, amma su kansu basu karɓi abinda Allah ya alkawarta ba tukuna"
Wato "alkawarin da Allah ya yi masu"
AT: "domin Allah ya kammala mu tare da su gabakiɗaya"
Mutum mai bangaskiya na sammanin su da gabagadi, yana kuma da tabbaci game da alkawaren Allah da ba su cika ba.
Abubuwan da ana gani a wannan duniya ba a halice su daga abubuwan da ana iya gani ba.
Allah ya yabi Habila domin ta wurin bangaskya ya miƙa wa Allah hadayar da ta cancanta fiye da wanda Kayinu ya yi.
Duk wanda ya zo wurin Allah, lallai ne ya badaga gaskiya da cewa Allah na nan kuma yana sãka wa waɗanda suka ɓiɗe shi.
Nuhu ya nuna bangaskiyarsa ta wurin sassaka jirgi don ya cece iyalinsa bisa ga gargaɗin Allah.
Ibrahim da Saratu sun karɓa ikon yin ciki ta wurin bangaskiya kodashike sun tsufa.
Kakanin bangaskiya sun gani, sun kuma marabci alkawaren Allah tun daga nesa.
Kakaknin bangaskiya sun dubi kansu a matsayin baƙi da kuma bare a duniya.
Allah ya shirya birnin samma ga waɗanda suke da bangaskiya.
Ibrahim ya bada gaskiya Allah zai iya tashe Ishaku daga matattu.
Yusufu ya yi annabci game da tafiyar 'ya'yan Isra'ila daga Masar sa'ad da ya kusan mutuwa.
Musa, ta wurin bangaskiya ya gwammaci a wulakanta shi tare da mutanen Allah, saboda Almasihu wadata ce a gare shi.
Musa ya kiyaye Jibin Ƙetarewa da kuma yayyafa jinin ta wurin bangaskiya don ya cece 'ya'yan fari maza na Isra'ilawan
Ta wurin bangaskiya Rahab ta karɓi 'yan ganganiman kamar aminai
Ta wurin bangaskiya kakanin bangaskiya sun ci nasara kan mulkoki, sun tsere wa kaifin takobi, suka yi jaruntaka wajen yaƙi, sun kuma fatattaka rundunar waɗansu ƙasashe.
Wasu kakanin bangakiya sun sha azaba, da ba'a, da bulala, da ɗauri, da jefawa cikin kurkuku, da jajjefe da duwatsu, an raba su biyu da zarto, da mutuwa, matsiyacin yanayi.
Ba su sami abin da Allah ya alkawarta ba.
Za su karɓi alkawaren Allah zu kuma zama kammalallu tare da masubin Almasihu na sabon alkawari.
1 Da shike muna kewaye da wannan irin kasaitaccen taro na shaidu, sai mu watsar da dukkan abubuwan dake nawaita mana da kuma zunubin da zai saurin makale ma na. Bari a cikin hakuri mu yi tseren da ke gabanmu. 2 Bari mu kafa idonmu ga Yesu, wanda shine mafarin bangaskiyarmu da cikarta. Wanda sabili da murnar da a ka sa a gabansa ya jimre giciye, ya kuma yi watsi da kunyarsa, wanda kuma ya zauna a hannun dama na kursiyin Allah. 3 Ku dube shi wanda ya jimre irin wannan adawa daga masu zunubi, domin kada ku gaji ko ku karai. 4 Ba ku yi tsayayya ko jayayya da zunubi har ta kai ga zub da jininku ba tukunna. Kun kuma manta da gargadin da a ka yi maku a matsayin 'ya'ya: 5 "Dana, kada ka dauki horon Ubangiji da wasa, kadda kuma ka yi suwu lokacin da ka sami horonsa," 6 Domin kuwa Ubangiji yana horon dukkan wadanda yake kauna, yana kuma hukunta duk wadanda ya karba. 7 Ku daure wahala a matsayin horo. Allah yana yi da ku kamar 'ya'yansa, domin kuwa wanne da ne wanda ubansa bazai yi masa horo ba? 8 Amma idan baku da horo kamar yadda sauran mutane ke da shi, kun zama shegu kenan ba 'ya'ya ba. 9 Hakannan kuma kamar yadda muke da iyaye a duniya wadanda suke yi mana horo, kuma muna basu daraja. To ba sai mu yiwa Ubanmu na Ruhaniya biyayya don mu rayu ba? 10 Ta wani fanni kuwa iyayenmu suna yi mana horo na kwanaki kadan bisa ga yadda suka ga ya dace, Amma Allah kuwa yana yi mana horo domin anfanin kanmu, domin kuma mu sami rabo daga cikin tsarkinsa. 11 Ba horon da ke da dadi a lokacin yinsa, amma sai zafi. Sai dai kuma bayan haka yakan haifar da 'ya'ya na ruhaniya da kuma adalci ga dukkan wadanda aka yi rainonsu a ciki. 12 Don haka sai ku karfafa hannayenku da ke reto, da kuma guwawunku da ke kaduwa. 13 Ku bi hanyoyi mikakku domin abin da ya gurgunce kada ya karye amma ya warke. 14 Ku bidi salama da kowa, da kuma rayuwar tsarki wanda in ba tare da shi, babu wanda zai ga Allah. 15 Ku mai da hankali domin kada waninku ya rasa, alherin Allah, kuma kada wani tushe mai daci ya tsiro a cikinku har ya haifar da fitina, domin kada da dama daga cikinku su gurbata ta wurinsa. 16 Ku yi hankali kuma kada a sami mazinanci ko marar ibada a cikinku, kamar Isuwa, wanda sabili da abinci ya sayar da 'yancinsa na dan fari. 17 Kun kuwa san cewa sa'adda ya yi marmarin ya gaji albarka a gaba, an kishi, domin kuwa bai sami damar tuba ba, ko da shike ya nema har da hawaye. 18 Domin kuwa baku zo ga dusen da ake tabawa da hannu ba, dutse ne mai ci da wuta, da tukuki da bakin hayaki da hadari. 19 Ba Ku zo ga karar kaho mai ban razana da murya mai firgitarwa ba, da masu sauraro suka yi roko kar su sake jinta. 20 Don basu iya jimre abin da aka yi doka a kan saba: "koma dabba ce ta taba dutsen, sai a jejjefe ta." 21 Abin tsoro ne kuwa kwarai, har Musa yace, "A tsoroce nake kwarai har na firgita." 22 Maimakon haka kun zone ga Dutsen Sihiyona da kuma birni na Allah mai Rai, kuma na Urushalima ta Samniya, da kuma dubun dubban mala'iku cikin murna da farin ciki. 23 Kun zo taro na dukkan 'ya'yan fari, rubuttatu a sama, kuma kun zo ga Allah wanda shine alkalin dukka, hakannan kuma zuwa ga ruhu na adalai wanda a ka rigaya aka tsarkake. 24 Kun zo ga Yesu, wanda shine matsakancin sabon alkawari, kuma ga jinin yayyafawa da ke magana fiye da na jinin Habila. 25 Ku yi lura kada ku ki wannan da ke yi mu ku magana. Gama in har basu kubuta yayin da su ka yi jayayya da wanda ya yi mu su gargadi a duniya ba, balle ma mu ba za mu kubuta ba in mun ki wanda ke mana gargadi daga sama. 26 A wani karo, muryar sa ta girgiza duniya. Amma yanzu yayi alkawari da cewa, "Har'ila yau ba duniyar kadai zan girgiza ba, amma har da sammai." 27 Wannan kalma, "Harl'ila yau," ta bayyana cirewar abubuwan nan da za su girgizu, wato abubuwan da a ka halitta, domin abubuwan da ba zasu girgizu ba su kasance. 28 Don haka, samun mulkin da ba za ya girgizu ba, sai mu zama masu godiya, kuma a cikin wannan yanayi mu yi wa Allah sujada cikin daraja da tsaninin gimamawa. 29 Domin kuwa Allahnmu wuta ne mai konewa.
Saboda yawan masubi da ke Tsohon Alkawari, marubucin yana maganar rayuwar bangaskiya da masubi za su yi da Yesu a matsayin wanda za su bi gurbinsu.
Kalmar nan "mu" na nufin marbucin da masu karatunsa ne. Kalmar nan "ku" na nufin masu karatu.
Marubucin yana magana game da masubi na Tsohon Alkawari ne kamar su kasaitaccen taron shaidu ne da ke kewaye da masubi na yau. AT: "irin wannan kasaitaccen taron shaidu da ke kewaye da mu" ko kuma "akwai misalai da yawa na mutane masu aminci da muke iya yin koyi da su a Littafi"
A nan "shaidu na nufin masubi na Tsohon Alkawarii da ke sura 11 da suka yi rayuwa kafin tseren bangaskiya da masubi ke yi a yau.
A nan ana maganar "nawaita" da "zunubin da zai saurin maƙale" kamar mutum na iya cire su yă ajiye.
Ana maganar halaye ko kuma ra'ayoyin da ke iya hana masubi gaskata Allah ko yi masa biyayya ne kamar wasu kaya ne masu nauyi da za su sa yă zama da wuya mutum yă ɗauka yayin da yake tsere.
Ana maganar zunubi ne kamar wani taru ne ko wani abu daban da zai iya sa mutane su faɗi. AT: "zunubin da ke sa bin Allah yă zama da wuya"
Ana maganar bin Yesu kamar wasan tsere ne. AT: "Bari mu cigaba da biyayya da abin da Allah ya umarce mu, daidai kamar yadda mai tsere ke cigaba da gudu har sai wasan ya ƙare.
Yesu ne ke bamu bangaskiya, yana kuma cika bangaskiyarmu ta wurin kai mu ga cimma burinmu. AT: "mai ƙirƙiro da kammala bangaskiyarmu" ko kuma "wanda ke sa mu iya samun bangaskiya daga farko zuwa ƙarshe"
Ana maganar murnar da Yesu zai samu kamar Allah Uba ne ya sa a gabansa a matsayin burin cikawa.
Wannan na nufin cewa bai damu da kunyar mutuwa a bisa giciye ba.
Zama a "hannun damar Allah" alama ce ta samun girma da iko daga Allah. Dubi yadda aka fassara irin wannan jumlar a [1:3]. AT: "ya zauna a wurin girma da ikɔ a gefen kurusiyin Allah"
AT: "fid da zuciya"
A nan, ana maganar zunubi kamar wani mutum ne da ke faɗa a yaƙi. AT: "Ba ku riga kun jure hare haren masu zunubi ba tukuna"
Ana maganar ƙin abokan hamayya har mutuwa ne kamar mutum ya kai ga mutuwa.
A nan "jini" na nufin mutuwa. AT: "mutuwa"
Ana maganar littafin Tsohon Alkawari kamar wani mutum ne da ke iya ƙarfafa wasu. AT: "abinda Allah ya gargaɗe ku a Littafi yă ƙarfafaku"
Wato duk wanda ke na Allah ne maza da mata. AT: "a matsayin 'ya'ya ... Ɗana ... kowane ɗa"
A nan, marubucin yana ambacin wannan maganar ne daga littafin Karin Magana a Tsohon Alkawari.
AT: "ka ɗauke horon Ubangiji da muhimmanci, kuma kada ka gaza"
"kada kuma ka fid da zuciya"
AT: "yana horas da kai"
"duk wanda ya karɓa a matsayin ɗansa"
"kă sani cewa a lokacin wahala Allah yana horas da mu ne"
Wannan yana kwatanta yadda Allah ke horas da mutanensa da yadda uba ke horas da nasa 'ya'ya. Ana iya bayyana wannan a fili. AT: "Allah yana yi da ku kamar yadda uba ke yi da 'ya'yansa"
Dukkan inda aka mori waɗannan kalmomi suna nufin maza da mata. AT: "'ya'ya ... ɗa"
Marubucin ya isar da saƙo da wannan tambayar cewa duk uba na kirki yana horas da 'ya'yansa. AT: "kowane uba yana horas da 'ya'yansa!"
AT: "don haka idan Allah bai horas da ku ba kamar yadda yake horas da duk 'ya'yansa"
Ana maganar waɗanda Allah ba ya horas da su kamar su 'ya'ya ne waɗanda aka haife su ga uba da uwa da ba su yi aure ba.
Marubucin yana amfani ne da wannan maganar domin yă nanata cewa yakamata mu yi wa Allah Uba biyayya. AT: "Saboda haka, sosai ma, sai mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu rayu."
Wannan karin magana yana nuna bambancin "ubanni na jiki." AT: "Uban mu a ruhu" ko kuma "Ubanmu da ke cikin sama"
"domin mu rayu"
Ana maganar "tsarki" kamar wani abu ne da mutane ke iya raɓa, ko kuma ke iya samu. AT: "domin mu zama da tsarki kamar yadda Allah ke da tsarki"
"'ya'ya" a nan na nufin "sakamako" ko kuma "abinda yake kawowa". AT: "yakan haifar da kwanciyar hankali na adalci" ko kuma "yakan haifar da adalci, wadda ke kawo salama"
"waɗanda aka yi rainonmu ta wurin horaswa." Ana maganar horaswa ko kuma gyara da Allah ke yi kamar Allalh ne da kansa. AT: "waɗanda Allah ya yi rainonsu ta wurin horas da su"
Yana iya yiwuwa cewa wannan ya cigaba ne da maganar tseren da ke a [12:1]. Haka nan ne marubucin yake magana game da yin rayuwa a matsayin masubi da kuma taimakon juna.
Ana maganar rayuwa da ke girmama Allah da kuma gamsar Allah kamar wata miƙaƙƙiyar hanya ce da ake bi.
A wannan karin maganar tseren, "gurgu" na nufin mutumin da ke tseren da ya ji rauni kuma yana son yă bari. Wannan dai har yanzu na nufin masubi da kansu. AT: "duk wanda ya gaji kuma yana son yă bar tseren ba zai ƙarye idon kafansa ba"
Ana maganar mutumin da ya daina yi wa Allah biyayya kamar ya ji ciwo ne a kafar sa ko kuma a idon kafarsa a kan hanya. AT: "ba zai ƙarye idon kafarsa ba"
AT: "a maimakon haka, zai zama da ƙarfi" ko kuma "a maimakon haka, Allah zai warkar da shi"
Ana maganar "salama" kamar wani abu ne da sai mutum ya nema. AT: "Ku yi ƙoƙari ku zauna lafiya da kowa"
Ana iya bayyana wannan a matsayin karfafawa. AT: "kuma ku yi ƙoƙari ku yi rayuwar tsarki, domin masu tasrki ne kaƙai za su ga Allah"
Ana iya bayyana wannan a fili. AT: "kuma ku nemi zaman tsarki"
"ba wanda zai karɓi alherin Allah sa'an nan ya bar shi ko kuma "ba wanda ya ke ƙin alherin Allah bayan ya riga ya dogara gareshi"
Ana maganar halin ƙiyayya ko fushi kamar wata tushe ne mai ɗaci. AT: "kada wanin ko yă zama kamar jijiya mai ɗaci, wadda idan ta yi girma takan kawo damuwa tana kuma jawo wa mutane da yawa illa"
AT: "mahaifinsa, Ishaku, ya ƙi ya sa mashi albarka"
AT: "domin kuwa bashi da damar tuba" ko kuma "domin kuwa bashi yiwuwa yă canza ra'ayinshi"
A nan "ya" na nufin Isuwa ne.
AT: "Domin baku zo, kamar yadda mutanen Isra'ila suka zo, ga dutsen da ake iya taɓawa da hannu ba"
Wannan na nufin cewa masubin Almasihu ba su zo ga dutse kamar Dutsen Sina'i da mutum ke iya taɓawa ko gani ba. AT: "da mutum ke iya taɓawa" ko kuma "da mutane ke iya gani da hankalinsu"
"Ba ku riga kun kai gun da ke da ƙaran ƙaho mai ƙarfi ba"
A nan "murya" na nufin wani na magana. AT: "ko wurin da Allah na magana a wata hanya da waɗanda suka ji shi sun roƙe shi kada yă ƙara yin magana da su haka"
AT: "abinda Allah ya yi doka"
AT: "sai ku jejjefe ta"
Marubucin yana maganar Dutsen Sihiyona, dutsen haikalin da ke Urushalima, kamar sama kenan da kanta, wurin zaman Allah
"mala'ikun masu yawa da ba a iya ƙirgawa"
Wannan na maganar masubin Almasihu ne kamar su 'ya'yan fari ne. Wannan na nanata matsayin su na musamman na kasancewa jama'ar Allah.
"waɗanda sunayen su ke a rubuce a sama." AT: "waɗanda Allah ya rubuta sunayensu a sama"
Wannan na nufin cewa Yesu ne ya sa sabon alkawari tsakanin Allah da mutane ya kasance. Duba yadda aka fassara wannnan a [9:15]
AT: "waɗanda Allah ya kammala"
Ana maganar jinin Yesu da jinin Habila kamar mutane ne da ke magana. AT: "jinin yayyafawa na Yesu da ke faɗin abubuwa mafiya kyau fiye da jinin Habilla"
A nan "jini" na nufin mutuwar Yesu, kamar yadda jinin Habila na nufin mutuwarsa.
AT: "ku kasa kunne ga wanda ke yi maku magana"
AT: "idan kuwa mutanen Isra'ila basu kuɓuta da ga shari'a ba"
Wannan na iya nufin 1) "Musa, da ya masu gargaɗi a duniya" ko kuma 2) "Allah, da ya masu gargaɗi a Dutsen Sihiyona"
AT: "in mun yi rashin biyayya da wanda ke mana gargaɗi"
"da Allah ya yi magana, ƙarar muryarsa ta sa duniya ta girgiza"
Yi amfani da kalmoni abinda girgizar ƙasa ke yi yă motsa ƙasa. Wannan na mayar da mu zuwa ga [12:18-21] da abinda ya faru da mutanen suka ga dutse inda da Musa ya karɓi shari'a daga wurin Allah.
AT: na nufin cewa Allah zai cire abubuwan da zai iya girgiza, wato, abubuwan" Dubi: and
Yi amfani da kalmar abinda girgizar ƙasa ke yi yă motsa ƙasa. Wannan na mayar da mu zuwa [12:18-20] da abinda ya faru yayin da mutanen suka gan dutse inda Musa ya karɓi shari'a daga wurin Allah. [12:26]
AT: "da Allah ya halitta"
AT: "abubuwan da basu girgiza" ko kuma "abubuwan da ba za su iya girgiza ba"
Ana iya ƙarin waɗannan kalmomin "domin mu ne" don a ƙara bada bayani mai kyau tsakanin wannan maganar da wanda ke biye. AT: "domin muna samun wata mulki" ko kuma "domin Allah yana naɗa mu mu zama 'yan mulkinsa"
AT: "da ba ta iya girgiza"
"sai mu yi godiya"
Kalmomin nan "dara" da "tsananin girmamawa" na nufin abu ɗaya ne kuma suna nanata matuƙar girmamawa da ya cancanci Allah. AT: da matuƙar ban girma da tsoro"
Ana maganar Allah a nan kamar shi wani wuta ne da ke iya ƙane kowane abu.
Tun dashike yana kewaye da taron shaidu masu ɗumbun yawa, to, ya kamata maibi ya yar da zunubin da ya ɗafe shi.
Yesu ya ɗaure wa giciyen, bai kuma mai da shi abin kunya ba domin farin cikin da aka sanya a gabansa.
Ta wurin duban Yesu wanda ya ɗaure ba'a daga masu zunubi, mai bi zai iya guje wa gajiya ko kuwa karai a zuci?
Ubangiji yakan ba da horo ga waɗanda yake ƙauna kuma ya karɓe su.
Mutumin da Ubangiji bai yi masa horo ba, ba 'yan halal ba ne kuma ba 'yan Allah ba ne.
Allah ya kan yi wa 'ya'yansa horo don amfanin kansu ne domin su zama abokan tarayya cikin tsarkinsa.
Horo ya kan kawo kwanciyar rai da adalci ke kawowa.
Ya kamata masubi su biɗi salamar tare da dukka mutane.
Kada tushen ɗacin rai ta tabbata, da kuma haddasa ɓarna da kuma ƙazantar da mutane masu yawa.
An ƙi Isuwa a lokacin da ya so ya gãji albarka cikin hawaye bayan ya sayar da hakkinsa na ɗan fari.
Isra'ilawa sun roƙa kada a yi musu magana.
Masubin Almasihu za su zo Dutsen Sihiyona da kuma birnin Allah tayayye.
Masubin Almasihu za su zo taron dukkan 'yan fari da aka shirya a sama.
Masubin Almasihu za su zo wurin Allah wanda zai hukunta dukka, zuwa kuma ga ruhohin adalcin da kuma Yesu.
Waɗanda suka juya baya ba za su kuɓuce daga wurin Allah ba.
Allah ya yi alkawarin girgiza duniya da sama.
Masubi za su sami mulkin da ba shi jijiguwa.
Ya kamata masubi su yi wa Allah sujada da tsoro da sanin girmamawa.
Ya kamata masubi su yi sujada ga Allah a wannan hanya domin shi wuta ne mai cinyewa
1 Bari kaunar 'yan'uwa ta cigaba. 2 Kada ku manta da karrama baki, domin ta wurin yin haka, wasu suka marabci mala'iku ba tare da saninsu ba. 3 Ku tuna da wadanda ke cikin kurkuku, kamar dai kuna tare da su cikin wannan hali. Kuma ku tuna da masu shan azaba kamar tare kuke cikin wannan hali 4 Bari kowa ya girmama aure, bari kuma a tsarkake gadon aure, gama Allah zai shar'anta fasikai da mazinata. 5 Bari halinku ya kubuta daga kaunar kudi. Ku dangana da abubuwan da kuke dasu, domin Allah da kansa yace, "Bazan barku ba, ba kuma zan yashe ku ba." 6 Bari mu zama da dangana domin mu sami gabagadin cewa, "Ubangiji ne mai taimakona, ba zan ji tsoro ba. To me mutum zai iya yi mani?" 7 Ku fa lura da wadanda ke shugabanninku, wadanda suka horar da ku cikin maganar Allah, kuma ku lura da sakamakon rayuwarsu, ku yi koyi da bangaskiyarsu. 8 Yesu Almasihu daya ne a jiya, da yau, da har abada. 9 Kada ku kauce zuwa ga bakin koyarwa daban daban, domin yana da kyau zuciya ta ginu ta wurin alheri, amma ba da dokoki game da abinci ba, wadanda basu taimaki wadanda suka kiyayesu ba. 10 Muna da bagadin da wadanda ke hidima a cikin alfarwa basu da ikon su ci daga bisansa. 11 Babban firist na shiga wuri mai tsarki da jinin dabbobin da aka yanka, hadayar zunubai, amma namansu a kan kai bayan sansani a kone shi. 12 Domin haka Yesu shima ya sha wahala a bayan kofar birnin, domin ya tsarkake mutane ta wurin jininsa. 13 Domin haka bari mu tafi gare shi a bayan sansani dauke da kunyarsa. 14 Domin bamu da wani birni dawwamamme a nan. Maimako haka muna bidar birni dake zuwa. 15 Ta wurin sa kuma, bari kullum mu mika hadayu na yabo ga Allah, yabon kuwa shine kalmomin bakinmu da ke daukaka sunansa. 16 Kada kuma mu manta da yin nagarta da kuma taimakon juna, domin Allah na farin ciki sosai da irin wadannan hadayun. 17 Ku yi biyayya da sadaukarwa ga shugabanninku, domin suna aikin tsaro a kanku saboda rayukanku, kamar wadanda zasu bada lissafi. Kuyi biyayya gare su saboda su yi aikin lura daku cikin farin ciki, ba da bakin ciki ba, don in su yi da bakin ciki ba zai amfane ku ba. 18 Kuyi mana addu'a, domin mun tabbata muna da lamiri mai tsabta, kuma muna burin muyi rayuwar dake daidai cikin dukkan al'amura. 19 Kuma ina karfafa ku dukka kuyi haka, domin in sami dawowa gareku da sauri. 20 To bari Allahn salama, wanda ya tada babban makiyayin tumakin nan daga matattu, Ubangijinmu Yesu, ta wurin jinin madawwamin alkawari, 21 ya kammala ku da dukan abu mai kyau domin ku aikata nufinsa. Bari yayi aiki a cikinmu wanda zai gamshe shi sosai. Ta wurin Yesu Almasihu, bari daukaka ta tabbata gare shi har abada. Amin. 22 'Yan'uwa, yanzu dai ina karfafa ku, da ku jurewa takaitacciyar maganar karfafawar da na rubuto maku. 23 Ina so ku sani an saki dan'uwan mu Timoti, tare da shi zan zo in gan ku idan ya iso da sauri. 24 Ku gaida shugabanninku dukka da kuma dukkan masu bada gaskiya. 'Yan'uwa daga can Italiya suna gaishe ku. 25 Bari alheri ya kasance tare daku dukka.
A sashi na ƙarshe, marubucin yi wa masubi gargaɗi game da wasu fannoni na rayuwa a kan yadda yakamata su yi rayuwa.
"Ku cigaba da nuna ƙaunar ku ga sauran masubi kamar yadda za ku yi wa 'yan iyalinku"
AT: "Ku tabbatar cewa kun tuna"
"da karɓar baƙi da kuma nuna masu ƙauna"
AT: "kamar dai kuna ɗaure tare da su" ko kuma "kamar dai kuna tare da su a kurkuku"
AT: "waɗanda ake masu ba daɗi" ko kuma "waɗanda suke shan wahala"
Wannan jumlar tana ƙarfafa masubi su dinga yin tunan game da azabar sauran jama'a kamar yadda za su yi tunanin nasu azaba. AT: "kamar ku ne a cikin wahalar"
AT: "Lallai ne maza da mata da suka auri juna su girmama juna"
Wannan na nufin haɗuwa ta jima'i kenan kamar ita ce kaɗai gadon da ma'aurata ke da shi. AT: "Bari maza da mata su daraja dangartakar aurensu da juna, su kuma ƙi kwana da wasu dabam"
A nan "hali" na nufin halin mutum, ko kuma yadda mutumin ke rayuwa; "kubuta daga son kuɗi" na nufin ƙin marmarin ƙara tara kuɗi. Duk mai ƙaunar kuɗi baya dangana da iyakar kuɗin da yake da shi. AT: "kada ƙaunar kuɗi ya ɓata halinku" ko kuma "Kada ku yi marmarin ƙara tara kuɗi"
"Ku ƙoshi"
Wannan wata furci ne daga littafin Zabura a Tsaohon Alkawari.
Marubucin yana amfani ne da wannan tambayan don yă nanata cewa ba ya tsoro domin Allah ne mai taimakonsa. A nan "mutum" na nufin ko ma wanene a ko ina. AT: "ba zan ji tsoron abinda ko ma wanene zai iya yi mani ba"
"abinda Allah ya faɗa"
"ƙarshen yanayinsu"
A nan, ana maganar dogara ga Allah, da kuma yanayin rayuwa da shugabannin nan suka yi ne a matsayin "bangaskiyarsu." AT: "Ku dogara ga Allah, ku yi masa biyayya kuma kamar yadda suka yi"
A nan "jiya" na nufin dukkan lokatai na dã. AT: "ɗaya ne a dã, a yanzu, da kuma a nan gaba har abada"
Wannan sashin yana maganar hadayu na dabbobi da masubin Allah ke yi a lokacin Tsohon Alkawari, wadda ke rufe zunubai ba ƙaramin kafin isowar lokacin mutuwar Almasihu.
Ana maganar rinjaya na koyarwa dabam-dabam kamar mutum na bauɗe wa ne da ƙarfi. AT: "Kada ku bar wasu su rinjaye ku zuwa ga ba da gaskiya ga ire-iren baƙuwar koyarwarsu"
"ire-iren koyarwa da dama da ba bisharar da muka faɗa maku ba"
AT: "Muna ƙara samun ƙarfin yayin da muka yi tunanin yadda Allah ke yi mana alheri, amma ba mu samun ƙarfi ta wurin kiyaye dokoki game da abinci"
A nan "zuciya" wata karin magana ce da ke nufin "hankalin mutum". AT: "mu ginu a ciki"
A nan "su abinci" na nufin dokoki game da abinci. (Dubi:
AT: "waɗanda suke rayuwa ta wurin su" ko kuma waɗanda suka bi da rayuwarsu bisa ga ka'idarsu"
A nan "bagadi" na nufin wurin ibada. Yana kuma nufin dabbobin da firistoci na tsohon alkawari ke miƙa hadaya, wadda daga wurin ne suke samun abincinsu da na iyalensu.
AT: "babban firist ne ke kai, cikin wuri mafi tsarki, jinin dabbobi da firistoci suka yanka domin zunubai"
"yayin da firistoci suna ƙona naman dabobbin"
"nesa da wurin da mutane suke"
"Haka kuma" ko kuma "Domin an ƙona hadaya a bayan zango" [13:11]
Wato a "bayan garin"
Ana maganar biyayya da Yesu kamar mutum ya bar zango ne zuwa wurin da Yesu yake.
Ana maganar babbar kunya kamar wani abu ne da ake iya ɗauka da hannu ko kuma a bayan mutum. AT: "yayin da muka bar mutane su ci mutuncin mu kamar yadda suka ci mutuncinsa"
"muna jira"
Ana maganar yabo kamar wata hadaya ce da dabbobi ko kuma turare na hayaƙi.
AT: "yabo da ke fitowa daga baƙin waɗanda suke ɗaukaka sunansa"
A nan "baƙi" na nufin mutanen da ke magana. AT: "baƙin waɗanda ke ɗaukaka sunansa" ko kuma "waɗanda suke ɗaukaka sunansa"
Sunan mutum na ba da hoton mutumin. AT: "shi"
AT: "Bari mu riƙa tuna wa da aikata nagarta da kuma taimakon sauran mutane a koyaushe"
Ana maganar aikata nagarta da kuma taimakon mutane kamar hadaya ne a bisa bagadi.
Anyi maganar rayukan masu bi, wato ana lafiyar masubi a ruhaniya, kamar wasu abubuwa ne ko dabbobi da masu tsaro ke iya kula da su.
A nan "baƙin ciki" na nufin ɓacin zuciya ko gunaguni (Dubi:
A nan "mu" na nufin marubicin da abokan tafiyarsa, amma ba a haɗe da ma su karatun ba.
A nan "tsabta" na nufin marar laifi ko aibu. AT: "mu tabbata cewa bamu da laifi"
AT: "don Allah ya ɗauke abubuwan da suke hana ni zuwa gareku"
Wannan alama ce ta sabuwar sashe a wasiƙar. A nan, marubucin yana yaba wa Allah yana kuma yin addu'arsa na ƙarshe wa masu karatunsa.
"wanda ya tashi babban makiyayin tumakin, Ubangijinmu Yesu, zuwa ga rai"
Daga dukkan waɗanda sun mutu. Wannan furcin na bayani a kan dukkan mutanen da sun mutu da ke a ƙarƙashin ƙasa. Ta da mutum daga matattu na maganar sa mutumin yă sake zama da rai ne.
Ana maganar Almasihu a matsayinsa na shugaba da kuma mai tsaron dukkan waɗanda sun gaskata da shi ne kamar shi makiyayin tumaki ne.
A nan "jini" na nufin mutuwar Yesu wadna shi ne tushen alkawarin da zai kasance har abada tsakanin Allah da dukkan masubi a cikin Almasihu.
"yă baku kowane abu nagari da kuke bukata domin ku iya aikata nufinsa" ko kuma "ya sa ku iya aikata kowane nagarin abu bisa ga nufinsa"
Kalmar nan "mu" na nufin marubucin da masu karatun.
"wanda dukkan mutane za su yabeshi har abada"
Wannan na nufin dukkan masubi da yake rubuto masu ko maza ko mata. AT: "'yan'uwa masubi"
"da hakuri, ku yi tuanin abinda na rubuto maku domin in ƙarfafa ku"
A nan "magana" na nufin saƙo. AT: "saƙon ƙarfafawa"
AT: "ba ya kurkuku kuma"
Wannan na iya nufin 1) marubucin ba ya Italiya, amma akwai wata ƙungiyar masubi tare da shi da sun fito daga Italiya ko kuma 2) marubucin yana Italiya yayin da yake rubuto wannan wasiƙa.
Wannan shi ne sunan yankin a wannan lokacin. Roma a dã ita ce birnin tarayya na ƙasar Italiya.
Wasu sun marabci mala'iku cikin rashin sani.
Ya kamata masubi su tuna da su kamar su ma suna kurkuku, da kuma kamar an tsananta wa jikunansu su ma.
Lallai ne kowa ya girmama aure.
Allah zai hukunta fasikai da mazinata.
Maibi zai iya samun 'yanci daga ƙaunar kuɗi domin Allah ya ce ba zai bar shi ba ba kuma zai yashe shi ba.
Ya kamata masubi su yi koyi da bagaskiyar waɗanda suka shugabanci su da kuma waɗanda suka yi masu maganar Allah.
Marubucin ya gargaɗi masubi a kan baƙuwar koyarwa da ta ƙunshi dokoki game da abin ci.
Ana ƙona gawakin dabbobin a bayan gari.
Yesu ya sha wahala a waje bayan birnin.
Lallai ne masubi su je wurin Yesu a bayan zango, mu sha irin wulakancinsa.
Masubi suna biɗan birnin nan mai zuwa.
Masubi ba su da dawwammamen birni a nan duniya.
Ya kamata masubi su miƙa hadayu ta yabo ga Allah.
Ya kamata masubi su yi biyayya su kuma miƙa kai ga shugabanninsu.
Allah ya yi ayyuka masu faranta masa rai.
Marubucin zai zo tare da Timoti a lokacin da zai ziyarci masubi.
1 Yakubu, bawan Allah, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilun nan goma sha biyu da suke warwatse: ina gaishe ku. 2 Ku dauke su duka da farin ciki, 'yan'uwana, duk sa'adda kuke fuskantar jarabobi. 3 Ku sani cewa gwajin banskiyar ku ta kan haifi jimiri. 4 Bari jimiri ya cika aikin sa, domin ku kai ga cikakken girma kuma ku kammalu, domin kada ku rasa komai. 5 Amma idan waninku yana bukatar hikima, sai ya roki Allah, wanda yake bayarwa a yalwace, ba tare da gori ba ga duk wanda ya roke shi, zai kuwa ba shi. 6 Amma fa sai ya roka da banskiya ba tare da shakka ba, don mai shakka kamar rakumin ruwan teku yake, wanda iska take korarwa tana tunkudawa. 7 Tilas ne wannan mutum kada ya yi tunanin zai karbi wani abu a wurin Ubangiji. 8 Irin wannan mutumin mai zuciya biyu ne, mara tsai da hankali a dukan hanyoyin sa. 9 Bari dan'uwa matalauci ya yi takama da matsayin sa babba, 10 amma mutum mai arziki kuma a kaskantaccen matsayin sa, gama zai shude kamar furen ciyawa na jeji. 11 Domin rana na bullowa da zafi mai konarwa kuma ya busar da ciyawa. Furen ya fadi, kuma kyaun sa ya lalace. Haka ma, mai arziki zai bushe yana cikin tsakiyar tafiyarsa. 12 Albarka ta tabbata ga mutum mai jurewa da gwaji. Domin in ya jure gwajin, zai sami rawanin rai, wanda aka yi alkawarin sa ga wadanda ke kaunar Allah. 13 Kada wani ya ce idan aka gwada shi, "Wannan gwaji daga wurin Allah ne," domin ba a gwada Allah da mugunta, shi kan sa kuwa ba ya gwada kowa. 14 Amma kowanne mutum yakan sami gwaji daga muguwar sha'awar sa, wadda take janye shi kuma ta rinjaye shi. 15 Bayan da muguwar sha'awar ta dauki ciki, sai ta haifi zunubi. Kuma bayan da zunubi ya yi girma, yakan haifi mutuwa. 16 Kada fa ku yaudaru, 'yan'uwana kaunatattu. 17 Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar baiwa daga sama take. Ta sauko ne daga wurin Uban haskoki. Wanda babu sauyawa ko wata alamar sakewa kamar yadda inuwa ke yi. 18 Allah ya zabi ya haife mu ta wurin maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunar fari na dukan halittar sa. 19 Kun san wannan, 'yan'uwana kaunatattu: bari kowanne mutum ya yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi. 20 Domin fushin mutum ba ya aikata adalcin Allah. 21 Saboda haka, sai ku yar da kowanne irin aikin kazanta da yalwar mugunta. A cikin tawali'u ku karbi dassashiyar maganar, wadda ke iya ceton rayukan ku. 22 Ku zama masu aikata maganar, kada ku zama masu jin ta kawai, kuna yaudarar kanku. 23 Domin duk wanda ya ke mai jin maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba fuskarsa a madubi. 24 Yakan dubi kansa sai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya manta da kamannin sa. 25 Amma duk mai duba shari'ar da bin ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace biyayya da ita, ba zai zama kamar wanda zai ji ya manta ba, wannan mutum zai zama da albarka a cikin abin da yake yi. 26 Idan wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, yana yaudarar zuciyarsa ne, addinin mutumin nan na banza ne. 27 Addini sahihi kuma marar aibi a gaban Allahnmu da Ubanmu, shine a kula da gwauraye da marayu a cikin kuntatar su, kuma mutum ya kebe kansa ya zama marar aibi daga duniya.
Manzo Yakubu ya rubuta wannan wasika zuwa ga dukan masubi. Yanwancin su Yahudawa ne, kuma mazauna ne a wurare dabam-dabam.
Jimlar nan "wannan wasikar daga" ya tabbatar da. AT: "Wannan wasikar daga Yakubu ne, bawan Allah, da kuma Ubangiji Yesu Almasihu"
AT: 1) domin Yahudawa masubi, ko 2) domin dukan masubi. "ga mutanen Allah masu aminci"
Kalmar nan "warwatse" na nufin Yahudawan da suke a warwatse a wasu kasashe dake nesa da Isra'ila, kasarsu ta haihuwa. AT: "wanda suka bazu a duniya" ko "wanda suke zama a wasu kasashe"
asalin gaisuwa, kamar "Sannu" ko "Ina kwana"
"Yan'uwana masubi, ku dauke kowani irin jarabobi a masayin abun shagali"
Furcin nan "gwajin," "bangaskiyar ku," da kuma "jimiri." Allah ne ke gwajin, domin, ya sani ko masubi suna da yarda ko suna biyayya da shi. Masubi ("ku") sun yarda da shi kuma suna jimre wahala. AT: "Idan kuna shan wahaloli, Allah yana binciken yanda kuka yarda da shi. Ta dalilin wannan, zaku iya daure kowace irin wahaloli"
An yi maganar jimiri anan kamar mutun da yana aiki. AT: "Ka koyi jure kowani irin wahala"
a cikin kowani yanayi akwai damar yarda da Almashihu da kuma yi masa biyayya
An ambata wannan a bangare mai kyau AT: "samun abinda kake bukata" ko "kasance abinda kake so ka zama"
"roki Allah. shi ne wanda yake bayarwa"
"bayarwa a yalwace ba tare da tsautawa ba"
"Allah zai yi" ko "Allah zai amsa addu'ar ka"
Wannan za iya bayyana shi kamar haka. AT: "da cikakkeyar tabbacin cewa Allah zai amsa"
Duk wanda yayi shakkar Allah zai taimake shi yana kamar ruwan teku ko tafki ne, dake tafiya zuwa a wurare dabam-dabam.
Kalmar nan "zuciya biyu" yana nufin mutum da baya iya yanke shawara don kansa. AT: "ba ya iya yanke shawarar zai bi yesu ko babu"
Anan yana magana ne game da mutum da bai da masaya daya.
"mai bi mara kuɗi iya gwargwaɗo"
Ana magana game da wanda Allah ya ɗaukaka kamar yana tsaye a tudu
Wannan kalmar "muyi takama" an fahimce shi daga maganar baya. AT: "bari mai arziki kuma yă yi takama da kaskancinsa"
"amma mutum mai kuɗi sosai." AT: 1) mai bi dake da kuɗi, ko 2) mai kuɗi mara bi.
Mai bi da ke da kuɗi ya kasance da farin ciki idan Allah ya sa shi shan wahala. AT: "ya kasance da farin ciki domin Allah ya ba shi wuya"
Anyi maganar masu kuɗi kamar furenin jeji, wanda su na nan a raye na ɗan lokaci.
Anyi maganar furen mara kyaun gani kamar kyaun sa ya mutu. AT: "kuma ba sauran ban sha'awa"
Anan karin magana mai kwatanci da fure zai iya ci gaba. Kada ka mutu da sauri kamar furenin da yakan bushe a gajeren lokaci, mai yiwuwa masu arziki ba sukan mutu ba zato ba tsammani amma a maimakon hakan sukan dauki ƙanƙanin lokaci su bace.
Anyi maganar ayyukan mai kuɗi a rayuwar sa na yau da kullum kamar tafiya da yake yi. Wannan misalin ya nuna cewa baya tunanin zuwan mutuwan sa kuma zai dauke shi da mamaki.
Yakubu ya nuna wa masu wanda suka guji cewa Allah baya zama sanadin jaraba; ya gaya masu yadda za su kauce wa jaraba.
"mutumin da ya jurewa gwaji mai sa'a ne " ko "Mutumin da ya jurewa gwaji mai samu ne"
kasancewa da aminci ga Allah a lokacin wahala
Allah ya amince da shi
Anyi maganar rawanin rai kamar furannin ganye ne da aka tubka a kan ƙwararren ɗan wasa mai nasara. AT: "ya samu rawanin rai a masayi lada"
AT: "Allah ya yi alkawarta ga waɗanda suke kaunar sa"
"idan ya bukaci yin abinda ke mugu"
AT: "Allah na ko karin sa ni yin abinda ke na mugunta"
AT: "Ba wanda zai sa Allah yin marmarin mugunta"
"kuma Allah kansa ba ya rinjayar kowa ya aikata mugunta"
Anyi maganar abinda mutun ke sha'awar sa kamar wani mutum ne daban da ke sa shi zunubi
An ci gaba da magana game da muguwar sha'awar kamar wani mutum ne da zai iya jawo wani dabam
janyo hankali, rinjaye wani ya aikata mugunta
An ci gaba da maganar sha'awar kamar mutum, a wannan lokaci yana nan kamar mace mai ciki. An bayyana aihin yaron kamar zunubi. Zunubi wani yă ta mace ce da ta girma, zamanto da ciki, ta kuma haife mutuwa. Wannan karin maganan hoton wani mutum ne da yana mutuwa a ruhaniyance ko kuma a jiki domin muguwar sha'awar da kuma zunubin sa.
"Kada ku bari wani ya yaudare ku" ko "Dakata da yaudaran kanku" bari "
Wannan jimloli biyun na nufin abu iri guda. Yakubu ya yi amfani da wadɗannan domin ya jaddada da cewa ko mai yana da kyau kuma mutum ya fito daga Allah ne.
Allah, mahalici na dukanin hasken dake sararin sama
wannan na bayyana hotunan Allah kamar haske da ba ya canzawa, kamar rãna, wata, duniyoyi da taurari dake sararin sama. wannan ya sha bambam da inuwa da yakan canza kullum a wannan duniya. AT: "Allah baya canzawa. Yana nan daram kamar rãna, wata, da taurari dake sararin sama, yayi dabam da inuwa da yakan bayyana ya kuma bace a doron ƙasa"
wannan kalma "mu" na nufin Yakubu da masu sauraron sa.
Allah, da ya bamu rai madawami, anyi maganar sa kamar shi ya haife mu.
AT: 1) "saƙo game da gaskiya" ko 2) "gaskiyan saƙo."
Yakubu na morar ra'ayin al'adar Yahudanci game da nunar fari amasayin hanya na siffanta darajar masu bi mabiyan addinin kirista na Allah. AT: "domin mu zama kamar bayaswa na nunar fari"
AT: 1) "San wannan" umurni ne, ga mai hankali game da abun da nake kokarin rubutawa ko 2) "Kun san wannan" Zance ne, da ina kokarin tunatar da ku game da abin da kun riga ya kun san ni.
Wannan karin magana da farko na nufin ka yi sauraro da kyau, sa'anan kuma yin tunani akan abun da suka ce mai kyau. Anan "jinkirin yin magana" ba yana nufin yin magana a hankali ba ne.
"banda saurin fushi"
Idan mutum mai fushi ne koda yaushe, ba zai iya aikin Allah ba, wato aikin adalci.
Anyi maganar zunubi da kuma mugunta kamar rigar da zaka saka da iya cirewa. AT: "daina aikata aikin ƙazanta da kuma na mugunta mai yawan gaske"
Anan "ƙazanta," da ke nufin, datti, ya tsaya a matsayin zunubi da kuma mugunta.
"Ba tare da girman kai" ko "Ba tare da alfahari ba"
wannan tinani "dassashe" na nufin saka wani abu a cikin wani. Anan kalmar Allah ya yi magana kamar wanni dassashe itace da ya yi girma a cikin masu bi. AT: "yi biyayya da saƙon Allah da ya yi magana a gare ka"
mutumin da aka ceta da ga gare shi ya zama a bayyane. AT: "an ceto shi daga hukuncin Allah"
Anan kalmar nan "rayukan" na nufin mutane. AT: "kanku"
"Ku zama mutane masu bin umurnin Allah"
"yiwa kanku wauta"
"Domin duk wanda ke saurarar saƙon Allah a cikin nassosin"
Kalmar nan "ne" da kuma "na kalma" za a fahimce shi daga jimla na baya. wannan suna "aikatawa" za iya bayyana cikin aikatau "yi" ko "biyayya." AT: "ba mai aikata kalmar ba" ko "ba mai biyayya da kalmar ba"
mutun mai jin kalmar Allah yana kamar mutun mai duban kamannin sa a madubi.
Kalmar nan "yanayin" Yakubu ya mori wannan domin ya tãtacce ainihin ma'anar kalma "fuska." AT: "fuskarsa"
Ko da yake akwai tabbacin zai iya ganin bukatun yin wani abu, kamar wanke fuska ko gyaran gashin sa, ya kan wuce ya kuma mance da yin hakkan. Wannan yana kama da mutumin da bai yi biyayya da kalmar Allah ba. AT: "sai ya wuce kuma nandanan ya mance da yin abin da yake bukata ya yi"
wannan magana ya ci gaba da ganin siffan shari'ar kamar madubi.
Dangantaka sakanin shari'ar da kuma 'yanci za'a iya bayyana shi a fili. Anan "'yanci" yana iya nufin 'yanci daga zunubi. AT: "shari'ar da bin ka'idar da ke bada 'yanci" ko "shari'ar da bin ka'idar da ke sa mabiyanta su samu 'yanci"
AT: "Allah zai sanya albarka akan mutum da ya yi biyayya ga shari'a"
"zaton yana bautar Allah daidai"
Kamun bakina na matsayin iko akan faɗar magana na. AT: "abin da ya ce"
sa wani ya yarda da abin da ba gaskiya ba
Anan "zuciya" na nufin imanin sa ko tunanin. AT: "kansa"
ya na bautar Allah da wãsa
Yakubu ya yi magana game da addini, a yanda wani ke bautar Allah, kamar ya zama jiki sahihi kuma marar aibi. Wadannan hanyoyi a al'adar Yahudawa da sukan ce wani abu mai karbuwa ne ga Allah. AT: "Yana da karbuwa gabaki ɗaya"
kai tsaye ga Allah
"da marayu"
Marayu da gwauraye na shan wahala domin ubanninsu ko mazajensu sun rasu.
Anyi maganar zunubi kamar wani abu mai datti da zai iya bata mutun, AT: "kada ka bar mugunta na cikin duniya ya saka zunu"
Yakubu ya rubuta wannan wasiƙar zuwa ga ƙabila goma sha biyu da suke warwatse.
Yakubu ya ce a duba shi da duka murna sa'adda ana fuskantar matsala.
Gwajin bangaskiyar mu na samar da jimiri.
Ya kamat mu tambaye Allah hikima idan muna bukatan shi.
Ya kamata kada wanda yayi tambaya da shakka yayi tsammanin zai karɓi wani abu daga Ubangiji.
Dan'uwa mai arziki ya kamata ya zama mai tawali'u domin zai ȿhude kamar fure.
Waɗanda suka yi nasara da gwadawar bangaskiya zasu same rawani na rai.
Marmarinsa na mugunta ne ke sa shi ya jarabtu da mugunta.
Sakamakon zunubi mai cikakken girma shine mutuwa
Kowane kyakkyawar baiwa da kowane cikakkiyar kyauta yazo kasa ne daga Uban haske.
Allah ya zaɓi ya bamu rai ta kalmar gaskiya.
Yakubu ya gaya mana muyi saurin ji, jinkirin magana, da kuma jinkirin fushi.
Yakubu ya ce zamu iya yaudaran kanmu ta wurin sauraron kalma da rashin aikata wa.
Ya zama tilas ne mu sarrafa harshenmu domin mu zama masu addini na gaske
Addini sahihi kuma mara aibu a gaban Allah shi ne a ziyarce marayu da gwauraye, kuma mu kare kanmu daga rashawar duniya.
1 Ya ku 'yan'uwana, muddin kuna rike da bangaskiyar ku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijin daukaka, kada ku nuna bambanci ga wadansu mutane. 2 Idan wani mutum ya halarci taron ku da zobban zinariya da tufafi masu kyau, wani matalauci kuma ya shigo da tufafi marasa tsabta. 3 Sa'adda kuka kula da mai tufafi masu kyau nan, har kuka ce masa, "Idan ka yarda ka zauna a nan wuri mai kyau," mataulacin nan kuwa kuka ce masa, "Kai ka tsaya daga can," ko kuwa, "Zauna a nan kasa a gaba na," 4 Ashe ba kuna zartar da hukunci a tsakanin ku ba ke nan? Ba kun zama alkalai na mungayen tunani kenan ba? 5 Ku saurara, ya 'yan'uwana kaunatattu, ashe, Allah bai zabi matalautan duniyar nan su zama mawadata cikin bangaskiya ba, su kuma zama magada a cikin mulkin nan da ya yi wa masu kaunar sa alkawari ba? 6 Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa maku ba? Ba su ne kuwa suke jan ku zuwa gaban shari'a ba? 7 Ba kuma sune ke sabon sunan nan mai girma da ake kiran ku da shi ba? 8 Duk da haka, idan kuka cika muhimmiyar shari'ar da nassi ya ce, "Ka kaunaci makwabcin ka kamar kanka," to, madalla. 9 Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi kenan, shari'a ta same ku da laifin keta umarni. 10 Duk wanda yake kiyaye dukan shari'a, amma ya yi tuntube a hanya daya kadai, ya sabi shari'a gaba daya ke nan. 11 Domin wanda ya ce, "Kada ka yi zina," shi ne kuma ya ce, "Kada ka yi kisan kai." Idan ba ka yi zina ba amma ka yi kisan kai, ai, ka zama mai taka shari'a kenan. 12 Saboda haka, ku yi magana ku kuma yi aiki kamar wadanda za a hukunta ta wurin 'yantacciyar shari'a. 13 Gama hukunci yana zuwa ba tare da jinkai ba ga wadanda ba su nuna jinkai. Jinkai ya yi nasara a kan hukunci. 14 Ina amfanin haka, 'yan'uwana, idan wani ya ce yana da bangaskiya, kuma ba shi da ayyuka? Wannan bangaskiyar ba za ta cece shi ba, ko za ta iya? 15 Misali, idan wani dan'uwa ko 'yar'uwa ba su da tufa mai kyau ko suna rashin abincin yini. 16 Misali, idan waninku kuma ya ce masu, "Ku tafi cikin salama, ku kasance da dumi ku koshi." Idan baku ba su abubuwan da jiki ke bukata ba, ina amfanin wannnan? 17 Haka ma, bangaskiya ita kadai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, matacciya ce. 18 To, wani zai ce, "Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa ina da ayyuka." Nuna mani bangaskiyar ka ba tare da ayyuka ba, ni kuma in nuna maka bangaskiya ta ta wurin ayyuka na. 19 Ka gaskanta cewa Allah daya ne; ka yi daidai. Amma ko aljannu ma sun gaskata, kuma suna rawar jiki. 20 Kana so ka sani, kai marar azanci, cewa bangaskiya ba tare da ayyuka ba banza ce? 21 Ba an baratar da Ibrahim mahaifinmu ta wurin ayyuka ba, sa'adda ya mika Ishaku dansa a bisa bagadi? 22 Ka gani, ashe, bangaskiyar sa ta yi aiki da ayyukan sa, kuma da cewa ta wurin ayyuka bangaskiyar sa ta ginu sosai. 23 Nassi kuma ya cika da ya ce, "Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lisafta masa ita a matsayin adalci." Aka kuma kira shi abokin Allah. 24 Kun ga, ta wurin ayyuka ne mutum yake samu baratarwa ba ta wurin bangaskiya kadai ba. 25 Ta wannan hanyar kuma, ba Rahab karuwar nan ta samu baratarwa ta wurin ayyuka, da ta marabci masu leken asirin nan ta fitar da su ta wata hanya dabam ba? 26 Kamar yadda jiki idan ba tare da ruhu ba matacce ne, haka kuma, bangaskiya ba tare da ayyuka ba matacciya ce.
Yakubu ya cigaba da gaya was Yahudawa masubi da suke a warwase yanda zasu yi zaman kaunan juna kuma ya tunashe su akan kada su so masu arziki fiye da 'yan'uwa matalauta.
Yakubu yayi la'akari da masu sauraronsa wanda su Yahudawa ne masubi AT: "Yan'uwanmu masubi" ko "'Yan'uwanmu maza da mata a cikin Almasihu"
Anyi maganar yarda da Yesu Almasihu kamar wani abu da mutun zai iya rike wa.
Kalmar nan "mu" ya haɗa da Yakubu da sauran 'yan'uwa masubi.
son taimakawa waɗan su mutane fiye da sauran
Yakubu ya fara siffanta yanayin da masubi sun fara daraja masu arziki fiye da matalauta.
"ya yi ado kamar mai arziki"
zauna a wuri mafi girma
tafi wuri mafi kaskanci
tafi wuri mafi muhimmanci
Yakubu na morar tambayoyi da ba su damu da amsa ba domin ya koyar ya kuma yi wa masu karantawa tsawa. AT: "kuna hukunci a sakanin ku kuma kuna zama alkalai na mugayen tunani"
Yakubu ya tsawatawa wa masu sauraron sa kamar iyali. "Maida hankali, zuwa ga 'yan'uwanmu masubi"
Anan Yakubu ya mora tambayoyi da ba su damu da amsa ba domin ya koya wa masu karantawa kada su nuna son kai. Za iya bayyana shi a magana. AT: "Allah ya zaɓe ... kaunar sa"
Wannan na nufin gaba dayan matalautan mutane.AT: "matalautan mutane"
Anyi maganar samun bangaskiya kamar samun wadata ko arziki. Abun na bangaskiya ya kamata ya zama ƙayyadadde. AT: "zama da ciƙankiyar bangaskiya a cikin Alhasihu"
Anyi maganar mutanen da Allah yayi masu alkawarai kamar wadanda za su ci gadon mallaka da kuma dũkiya da daya daga cikin iyali.
Yakubu ya na magana akan dukan masu sauraron sa.
"kun kunyatar da matalautan mutane"
Anan Yakubu ya mora tambayoyi da ba su damu da amsa ba domin ya daidan ta masu sauraron sa. AT: "masu arzikin ne suke matsa maku."
wannan na nufin gaba dayan mutane masu arziki. AT: "mutane masu arziki"
"suke yi muku mugunta"
Anan Yakubu ya mora tambayoyi da ba su damu da amsa ba domin ya daidan ta masu sauraron sa. Za a iya bayyana shi a magana. AT: "Masu arziki suke ... zuwa gaban shari'a."
"a akan tilas ta ku zuwa gaban alkalai su tuhume ku su yi muku shari'a"
Anan Yakubu ya mora tambayoyi da ba su damu da amsa ba domin ya daidan ta ya kuma koya wa masu sauraron sa. Za a iya bayyana shi a magana. AT: "Mutane masu arziki ke saɓon ... ake kiran ku da shi."
Wannan na nufin sunan Almasihu ne. AT: "sunan Almasihu da ya kira ka"
Kalmar nan "ku" na nufin Yahudawa masubi.
"biyayya da shari'ar Allah." Allah ya ba wa Musa asalin dokoki, da an rubuta a cikin Littattafai na Tsohon Alkawari.
Yakubu ya ɗauko daga cikin faɗar Littafin Leviticus
"dukan mutane" ko "kowa da kowa"
"kana yi daidai" ko "kana yin abu mai kyau"
"bada cikanken kulawa ga" ko "bada girma ga"
"yin zunubi" wato, Karya doka.
Anan anyi maganar shari'a kamar mutum da ke hukunci. AT: "laifin rashin ketare dokan Allah"
"Duk wanda ya yi biyayya"
tuntuɓe fadowa ƙasa ne lokacin da mutum ke kokarin tafiya. Anyi maganar rashin biyayya a wani ɓangaren shari'a kamar tuntuɓe a na kan tafiya.
domin rashi biyayya na daya daga cikin abin da ake bukata a shari'a
Wannan na nufin Allah ne, wanda ya bawa Musa dokan.
"Ka yi" shine ka dau mataki.
Anan "kai" na nufin "kowane dayan ku." Kodayake Yakubu na rubutawa zuwa ga yanwacin Yahudawa masubi ne, a wannan magana, ya mora mufuradi kamar yana rubutawa kowane mutum daya.
"Saboda haka dole ku yi magana ku kuma yi biyayya." Yakubu ya umurce dukan mutanen da su yi wannan.
AT: "wa ya sani cewa Allah zai yi muku hukunci ta wurin 'yantacciyar shari'a"
Wannan nassi na nufin Allah zai yi hukunci bisa ga shari'a.
"shari'ar da takan bada ainihin 'yanci"
"Jinkai mafi inganci ne akan" ko "Jinkai ya yaƙi." Anan anyi magana akan jinkai da ãdalci kamar su mutane ne.
Yakubu ya mora tambayoyi da ba su damu da amsa ba domin ya koyar wa masu sauraron sa. AT: "Ba si da kyau ko kaɗan, 'yan'uwanmu masubi, idan wani ya ce yana da bangaskiya, kuma ba shi da ayyuka."
Za a iya sake maganar ta wurin cire ra'ayin sunaye "bangaskiya" da kuma "ayyuka." AT: "idan wani ya ce ya yi ĩmãni da Allah kuma bai yi abin da Allah ya umurce shi kada ya yi ba"
Yakubu ya mora tambayoyi da ba su damu da amsa ba domin ya koya wa masu sauraron sa. Za a iya sake maganar ta wurin cire ra'ayin suna "bangaskiya." AT: "Cewa bangaskiya ba zai iya ceton sa ba" ko "idan mutun bai yi abin da Allah ya umurce shi ba, to ya na cewa bai yi ĩmãni Allah zai iya ceton sa ba"
"an cece shi daga shari'an Allah"
Wannan na nufin "samun isashshen kayan sa wa" ko "samun magwanci"
Abin da ya koshas da su abinci ne. Za a iya bayyana baro-baro. AT: "ku koshi da abinci" ko "samu isasshe ku ci"
ku ci, ku sa, ku kuma rayu a tsanake
Yakubu ya mora tambayoyi da ba su damu da amsa ba domin ya koya wa masu sauraron sa. AT: "game da abin da bai da amfanin."
'Yan'uwanmu masubi cikin Almasihu, koda namiji ko ta mace
Yakubu ya yi magana game da bangaskiya kamar abu mai rai indan mutun ya yi aiki mai kyau, kuma bangaskiya kamar mataccen abu ne idan mutun bai yi ayuka masu kyau ba. Za a iya sake maganar ta wurin cire ra'ayin sunaye "bangaskiya" da kuma "ayyuka". AT: "idan mutum ya ce ya yi ĩmãni da Allah, san nan bai yi abin da Allah ya umurce shi ba, bai yi ĩmãni da Allah ba ke nan"
Yakubu ya bayyana yanayin da wani ke ganin koyarwan sa. Yakubu ya biɗa gyarar ganewar masu sauraron sa game da bangaskiya da kuma ayyuka.
Yakubu ya na bayyanin yanda wani zai iya yin jayayya da gaba da koyarwan sa da kuma yanda zai amsa masa. Za iya sake maganar ta wurin cire ra'ayin sunaye "bangaskiya" da kuma "ayyuka". AT: "'Mun yarda cewa ka yi ĩmãni da Allah kuma kana aikata abin da Allah ya umurta.' Tabbatar mini ĩmãnin ka da Allah da ba za ka iya yin abinda ya umurta ba, ni kuma sai in tabbatar maka da ĩmãni na da Allah ta wurin yin abin da Allah ya umurta"
"ko aljannu ma sun gaskata, amma suna rawar jiki don tsoro." Yakubu ya bambanta tsakanin aljannu da masu neman su nuna sun yi ĩmãni kuma basu da ayyuka masu kyau. Yakubu ya yi magana da cewa alajanun suna da hikima domin suna da tsoron Allah sa'annan wasu basu da shi
Yakubu ya mora tamabaya domin gabatar da koyarwar sa na gaba. AT: "Saurare ni, wawan mutum, zan kuma nuna maka cewa bangaskiya ba tare da ayyuka ba banza ce."
Za a iya sake maganar ta wurin cire ra'ayin sunaye "bangaskiya" da kuma "ayyuka". AT: "idan ba ka aikata abi da Allah ya umurta ba, ya zama banza ce a gare ka a ce ka yi ĩmãni da Allah"
Tun da yake waddannan Yahudawa masu bi ne, sun san labarin Ibrahim, game da abin da Allah ya faɗa musu tuntuni a cikin kalmarsa.
An mora wannan tambaya da ba ta damu da amsa ba domin sukar wawan mutumin mai haddama [2:18]
Yakubu ya yi maganar ayyuka kamar wasu ababai da wani ya manlaka. AT: "barata ta wurin yin aiki mai kyau"
Anan "mahaifi" an mora a bangarin "kakan kaka."
Kalmar nan "ka" ɗan tilo, na nufin mutum mai shiririta. Yakubu na yiwa dukkan masu sauraronsa jawabi kamar mutun guda.
Yakubu ya yi magana kamar "bangaskiya" da kuma "ayyuka" abubuwa ne da sukan yi aiki a wuri guda tawurin taimakon juna. AT: "saboda Ibrahim ya gaskata Allah, tawurin aikata abin da Allah ya umurta. kuma saboda Ibrahim ya aikata abin da Allah ya umurta, ya gaskanta da Allah gabaki ɗaya"
AT: "Wannan nassi kuma ya cika"
"Allah ya na kallon bangaskiyan sa a matsayin adalci." Bangaskiya da kuma adalcin Ibrahim an ɗauke shi tamkar kamar wani abu da za'a iya kirgawa kamar samun daraja.
"ayyuka da kuma bangaskiya baratar da mutum, kuma ba bangaskiya ka dai ba." Yakubu ya yi magana game da ayyuka kamar waddansu abubuwa da za ka iya samu.
Yakubu ya ce abin da ke gaskiya ce game da Ibrahim gaskiya ce kuma game da Rahab. Dukansu sun sami baratarwa ta wurin ayyaku.
Yakubu ya mora tambaya da bai damu da amsa ba domin ya umurce masu sauraron sa. AT: "abin da Rahab karuwar nan ta samu baratarwa ... ta wata hanya dabam."
Yakubu ya tsammanci masu sauraron sa su zama da masananciya game da labarin macen nan Rahab na Tsohon Alkawari.
Mutane masu kawo sakonni daga wani wuri
"sai sun sami taimako suka gudu suka kuma bar birnin"
Yakubu ya na maganan akan bangaskiya ba tare da ayyuka ya na kamar mataccen jikin da bata da ruhu.
Yakubu ya gaya musu kada su nuna ma wasu so saboda bayyanar su.
Yakubu ya ce Allah ya zabi matalauta su yi arziki a bangaskiya kuma su gaji mulkin.
Yakubu ya ce masu arziki suna ta zuluntar 'yan'uwa kuma suna saɓon sunan Allah.
Mahimmin dokan shine "Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka".
Duk wanda ya karya aya ɗaya na dokan Allah yayi laifin karya duka dokokin.
Hukunci ba tare da rahama ba na zuwa ga waɗanda basu nuna rahama ba.
Yakubu ya ce waɗanda suka ce suna da bangaskiya, amma ba su taimakawa ma su bukata ba su na da bangaskiyar da baza ta iya cetonsu ba.
Bangaskiya ita kan ta, idan ba ta da ayyuka, matacce ne.
Yakubu ya ce tilas ne mu nuna bangaskiyarmu ta wurin ayyukan mu.
Waɗanda suka ce suna da bangaskiya da kuma aljanu duka sun gaskanta akwai Allah daya.
Ibrahim ya nuna bangaskiyarsa ta wurin ayyukan lokacin da ya miƙa Ishaku a bagadin hadaya.
Litaffi Mai Tsarki da ya cika ya ce "Ibrahim ya gaskanta Allah, kuma aka yaba mashi kamar adalci"
Rahab ta nuna bangaskiyarta ta awurin yyukan ta a lokacin da ta marabce masu bada saƙo ta kuma sallame su ta wata hanya dabam.
Jiki a rabe daga ruhu matacce ne
1 Ba mutane dayawa za su zama masu koyarwa ba, 'yan'uwana. Mun san cewa za mu karbi hukunci mafi tsanani. 2 Domin mukan yi tuntube ta hanyoyi dayawa. Duk wanda bai yi tuntube ta hanyar kalmomi ba, shi mutum ne ginanne sosai, wanda ke iya kame dukan jikinsa. 3 Idan muka sa linzami a bakunan dawakai, domin su yi mana biyayya, za mu iya sarrafa jikunan su gaba daya. 4 Ku lura kuma da jiragen ruwa, ko da yake suna da girma sosai kuma iska mai karfi tana kora su, da karamin karfe ne matukin yake juya su inda ya so. 5 Haka kuma harshe dan karamin gaba ne a jiki, sai fahariyan manyan abubuwa. Ku lura yadda dan karamin wuta yake cinna wa babban jeji wuta. 6 Harshe ma wuta ne, a cikin dukan gabobin mu, duniyar zunubai da aka sa cikin fannonin jikunan mu. Yana gurbata dukan jiki, ya kuma sa al'amurar rayuwa su kama da wuta. Shi kuwa gidan wuta ne yake zuga shi. 7 Domin kowace irin dabbar jeji, tsunsu, da masu jan ciki, da hallittar teku, ana sarrafa su kuma dan Adam har ya sarrafa su ma. 8 Amma game da harshe, babu wani a cikin 'yan Adam da ya iya sarrafa shi. Mugunta ne mara hanuwa, cike da dafi mai kisa. 9 Da wannan harshe muke yabon Ubangiji da kuma Uba, da shi kuma muke la'antar mutane wandanda aka hallitta cikin kamanin Allah. 10 Bakin da ake sa albarka, da shi kuma ake la'antarwa. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba. 11 Mabulbulan ruwa ba zai iya bubbugowa da ruwan dadi da na zartsi tare ba, ko zai iya? 12 "Yan'uwana, itacen baure ba zai iya yin zaitun ba, zai iya? Ko kuwa gonar inabi ya yi baure? Haka kuma, ruwan zartsi ba zai iya bayar da ruwan dadi ba. 13 Ina mai hikima da fahimta a cikin ku? Bari wannan mutumin, ta kyakkyawan zaman sa ya nuna aikin da halin tawali'u da hikima ke sawa. 14 Amma in kuna da matsanancin kishi da kazamin buri a cikin zuciyar ku, kada ku yi fahariya da karya game da gaskiya. 15 Wannan hikima ba irin wadda take saukowa daga sama ba ce, a maimakon haka, ta duniya ce, mara ruhaniya, ta aljanu. 16 Domin duk inda kishi da kazamin buri suke, a nan ake samun hargitsi da kowanne irin aikin mugunta. 17 Amma hikiman nan ta sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, kamila ce, mai saukin kai, mai tsananin jinkai, mai yawan alheri, mara gajiya, sahihiya kuma. 18 Kuma 'ya'yan adalci wanda ake shukawa a cikin salama a tsakanin wadanda ke kulla zumunci.
Yakubu na yin magana na gabaki daya.
"'yan'uwanmu masubi"
Wannan nassi ya yi magana game da hukunci mafi tsanani da ke zuwa daga wurin Allah bisa kan masu koyarwa game da shi. AT: "Allah zai yi mana mu masu koyarwa shari'a mai tsanani don mun san kalmar sa sosai feye da wasu mutane da muka koyar"
Yakubu ya hada da kansa da kuma sauran masu koyarwa, amma banda masu karantawa, don haka kalmar nan "mu" na nan dabam.
Yakubu yayi magana game da kansa, wasu malamai, da masu karatu, wannan kalmar "mu" a haɗe ne.
Ana magana game da zunubi kamar tuntuɓe ne ayayin da ake tafiya. AT: "faɗi" ko "zunubi"
"baya zunube ta wurin faɗan abubuwa marasa amfani"
"ruhaniyarsa ginanne ne"
Yakubu na nufin zuciyar mutum, shauƙi, da kuma aikinsa. AT: "kame halinsa" ko " kame ayukansa"
Yakubu ya cigaba da wani bayani a kan wannan mahawara cewa kananan abubuwa na iya mulkin manyan abubuwa.
Yakubu yayi magana akan linzamin dawakai. Linzami wata karamar karfece wace ake sakawa a bakin doki domin ya jagorance inda zashi.
"Idan" ko "lokacin"
Doki babban dabbane wanda ake amfani da ita domin daukan abubuwa ko mutane.
jirgin ruwa an kamanta shi da babbar mota wace ke tafiya akan ruwa Matuki karamar karfi ce ko sanda wace ke bayan jirgin ruwa, wace ake amfani dashi don ya jagoranci inda zata. Kalman nan "matuki" za' a iya fassarata a matsayin "kayan aiki."
Za' a iya bayyana ta cikin tsifar aiki. AT: "iska mai ƙarfi na korarsu"
"nada karamin kayan aiki da matukin kan iya amfani dashi wajen juya jirgin duk inda zai je"
Wannan kalmar na harshe na kwatanci ne da linzamin doki da matukin jirgin ruwa yanda aka fada a surorin da suka gabata. AT: "ta haka kuma"
Anan "abubuwa" kalmace wacce ake mora don a nuna yadda waddannan mutane suke fahariya da komai.
"Yi tunani akan"
Domin a fahimtar da mutana hatsarin da harshe kan iya jawowa, Yakubu yayi magana akan barnan da karamin wuta ke iya kawowa. AT: "yadda ɗan karamin macinne yake cinna wa itatuwa wuta"
Harshe kalma ne wacce mutane ke morra. Yakubu ya kirata wuta saboda barnan da takan iya yi. AT: "Harshe na kamanni da wuta"
Ana maganane game da babban illan kalmomin zunubi kamar su duniyace da kansu.
Ana magana ne game da zunubin munanan kalmomi kamar magane ce wadda ke lalata jikin mutum. Yana kuma zama marar ƙarɓiya ga Ubangiji kamar kuma datti ne ga jikin dan adam.
Kalman nan "al'amurar rayuwa" na nufin rayuwar mutum gaba ɗaya. AT: "ta kan lalata rayuwar mutum gaba ɗaya" (Dubi:
Kalman nan "shi kansa" na nufin harshe ne. Anan kuma jahannama na nufin mumunar ikon ibilis. Wannan an iya bayanashe a sifar aiki. AT; "rayuwa saboda ibilis yakan ye aiki da she ta wurin hayyamara amfani.(Dubi:
Wannan sashen "kowace irin"
wannan ɗabbace wanda take rarrafe a kasa.
ɗabbace wanda take zama a cikin teku
Yakubu yayi magana game da harshe kamar wata ɗabban jeji ne. "harshe" wakilin mutum ne kuma yana son sa mutum yayi magana a kan kowace mugunta. Dubi: ko
Yakubu yayi magana akan illan da mutane zasu iya jawowa game da abun da suke faɗawa kamar harshe mugune ko ɗafi hallita wanda zai iya kashe mutum. AT: "Muguntatciyar hallita ne mara hanuwa, cike da dafi mai kisa" ko" halintatciyar mugunta ce mai geje-ama da zashe iya kashe mutum da kuma dafi" Dubi:)
"Muna amfani da harshe mu faɗa kalmomi da"
"Muna rokon Allah ya lahanta mutane
AT: "Wadda Allah ya hallita cikin kamanin sa"
" albarka" ko "la'antarwa" za' a iya juya ta a wata sashen magana. AT: "da baki ɗaya mutun zai sa wa mutane albraka ko ya la' anci mutane" Dubi:
"Waɗanan abubuwa ba daidai ba ne"
Bayyan da Yakubu yayi ta nanata magana cewa kada kalmomin masubi su zama masu sa albarka da la' ana, ya ba da misalai daga halitta domin ya koya wa masu karatu cewa mutane da suka ɗaukaka Allah ta wurin yi masa sujada su kuma zauna a hanyar da ta dace.
Yakubu yayi magana da tambaya da ba ta damu da amsa ba domin ya tunashe masubi da abun da yake faruwa a halitta. AT: "kun san da cewa mabulbulan ruwa ba zai iya bubbugowa da ruwan dadi da na zartsi tare ba."
yakubu yayi amfani da wata tambayan da bata damu da amsa ba kuma domin ya tunashe masubi a kan abubuwan da suke faruwa a halitta. AT: "dan'uwa ka sani da cewa mabulbulan ruwa ba zai iya bubbugowa da ruwan dadi da na zartsi tare ba."
wannan kalma "yi"an gane ta a sashen da ta wucce. Yakubu yayi magana da tambayan da ba ta da amsa domin ya tunashe masubi a kan abubuwan da suke faruwa a halitta. AT: "Ko kuwa gonar inabi ya yi baure? " ko " haka kuwa gonar inabi ba za ta haifi baure ba."
Yakubu yayi amfani da wannan tambayan domin ya koya wa jama' a hallaiya masu kyau. wanan kalman "hikkima" ko"ganewa" suna kama. AT: zan gaya maku yadda mutum mai hikkima da ganewa yi."
wanan za' a iya bayanawa a cire dahii "tawali'u" da "hikkima" AT: amin mutum yayi ayuka da rayuwa mai kyau na hallin kaskanci da hikkima"
Anan "zuciya"
wannan dahin "gaskiya"za a iya fadarta kaman "gaskiya." AT: kada ku yi fahariya da cewa kuna da hikkima, domin haka ba gaskiya bane"
Anan wannan yana nufin "ɗacin kishi da kokari" wadda aka bayyyana a sashen da ta wucce. wannan sashen maganar "daga sama" ana amfani da ita wurin kwatancin "sama" wadda take misalim Allah da kasa. AT:"wanan hikkiman ba irin wadda Allah ya koyar bane daga sama"
wanan kalma "basira" az' a iya fadan ta kamar "hikkima."- AT: duk wananda yayi kamar haka bashi da hikkima yadda Allah na sama ya koya mana. a maimakon haka, ta duniya ce, mara ruhaniya, ta aljanu"
wanan kalma "duniya" tana nufin daraja da ayuka na mutane wadda basu daukaka Allah ba. AT: "basu daraja Allah"
"ba daga ruhu mai sraki ba" ko "mai ruhaniya"
"daga a'ljanu"
wanan kalma "kishi" "kazamin buri" da "hargitsi." AT: "domin idan mutane suna kishi da son kai, wannan yakan sa suyi aikin mugunta a hanyoyin da be dace ba"
"akwai rashin shiri" ko " akwai rashin shiri kankat"
"ko wacce hallayen zunubi" ko "ko wacce aikin zunubi"
anan "daga bisa" ya na misalin "sama" wadda yake misalin Allah da kansa. wannan kalma "hikkima." AT; amma idan mutum yana da hikkima kamar yadda Allah na sama ya koyar, yayi aiki da a tsattsarkarkiyar hanya"
"mai tsarki tun farko"
Anan "kyauwawan ayuka" ta na nufin abubuwa da mutane suke yi masu kyau ta wurin samun hikkima da Allah. AT: "cike da tausayi da ayuka masu kyau"
"da mai gaskiya" ko "dagaskike"
Mutane sunan salama kamar suna sukin iri, adalci kuma ana maganar ta kamar 'ya 'ya ce wadda take grima ta dalilin salama. AT: "sakamakon salama shene adalci" ko "ko kuma wadda suke ayukan salama su temaki mutana a sami salama ya haifi adalci"
wannan kalma "salama"za' a iya fadin ta kamar "kwanciyar rai." AT: "sa mutane su zauna da "kwanciyar rai" ko a taimaki mutane kada su ɓata rai tsakanin juna"
Kada dayawa su zama malamai domin za su samu hukunci mafi tsanani.
Dukan mu munyi tuntuɓe a hanyoyi da yawa.
Mutumin da baya tuntuɓe a kalmominsa shine kuma ke iya sarrafa dukan jikinsa.
Yakubu yayi amfani da misalain ragaman doki da kuma radan jirgin ruwa.
Harshe mai zunubi zai iya ƙazantar da dukan jiki.
Babu wanda ya iya horar harshe a tsakanin mutane.
Albarka da la'ana ne duka ke fitowa daga baki ɗaya.
Mutum na nuna hikimar da fahimta ta wurin ayyukansa da ya yi a tawali'u.
Mutum da ke da haushin kishi da sonkai yana da hikimar ta duniya, da rashin ruhaniya, kuma ta shaiɗan.
Mutum de ke kaunar zaman lafiya, hankali, tsananin jinkai, mai yawan alheri da kaywawan 'yaya, ba tare da nuna gatanci, kuma sahihi ke da hikima daga sama.
1 Me ke kawo gaba da rashin jituwa a tsakanin ku? Ba yana tasowa ne daga muguwar sha'awa da ke yaki a cikin ku ba? 2 Kuna sha'awa, kuma ba ku da shi. Kuna kisa da kyashi, kuma ba za ku iya samu ba. Kuna danbe da fada. Har wa yau baku samu ba domin baku tambaya ba. 3 Kun roka kuma ba a baku ba saboda kuna roko ta hanya mara kyau, kuna so ku yi amfani da shi domin miyagun sha'awoyin ku. 4 Ku mazinata! Baku sani ba, abokantaka da duniya, tawaye ne ga Allah? Don haka duk wanda ya shiga abokantaka da duniya ya zama magabcin Allah. 5 Ko kuna zaton nassi ya fadi haka a banza ne, "Ruhun nan da ke a cikinmu yana da kishi matuka?" 6 Amma Allah ya bayar da karin alheri, shi ya sa nassi ya ce, "Allah yana gaba da mai girman kai, Amma yana ba da alheri ga mai tawaliu." 7 Saboda haka ku mika kan ku ga Allah. Ku yi tsayayya da shaidan, zai kuma guje maku. 8 Ku matso kusa da Allah, shi kuma za ya matsa kusa da ku. Wanke hannayen ku, ku masu zunubi, ku tsabtace zukatan ku, ku masu zuciya biyu. 9 Ku yi bakin ciki, makoki, da kuka! Ku mayar da dariyar ku ta koma bakin ciki, farin cikinku kuma zuwa ga bakin ciki. 10 Ku kaskantar da kanku a gaban Ubangiji, shi kuma za ya daukaka ku. 11 Kada ku rika zargin juna, 'yan'uwa. Wanda ya ke zargin dan'uwa ko shari'anta dan'uwansa, yana zargin shari'a kuma yana hukunta shari'a. Idan ka hukunta shari'a, ya nuna ba ka biyayya da shari'ar, amma mai hukunci. 12 Mai ba da shari'a da yin hukunci daya ne. Shine mai iya ceto kuma ya hallakar. Kai wanene, da ke hukunta makwafcin ka? 13 Saurara, ku da kuke cewa, "Yau ko gobe za mu tafi wancan birnin mu yi shekara guda a wurin, muna kasuwanci, mu kuma yi riba." 14 Wa ya san abin da zai faru gobe, kuma yaya rayuwan ka zai kasance? Kai kamar hazo ne mai bayyana bayan dan lokaci kadan ya bace. 15 Maimakon haka, sai ka ce, "Idan Ubangiji ya nufa, za mu rayu kuma mu yi wannan ko wancan." 16 Amma yanzu kana fahariya da shirye shiryen ka na takama. Irin wannan fahariya, mugunta ce. 17 Saboda haka ga wanda ya san abin da ya kamata ya aikata amma bai yi ba, ya zama zunubi a gare shi.
Yakubu ya kwubɓi masubi sabo da ayukan duniya da rasin kaskanci. ya kuma izasu su kula da yadda suki maganar da juna.
A wannan sashin kalmar da ake ce "kai da kanka," "naka," da "kai" jam'i ne kuma suna nufin masubi wadda Yakubu ya rubuta masu.
wannan kalma "gãba" da "rashin jituwa" a takaice na nufin abu ɗayane kuma za 'a iya fasarta su cikin aikatau. AT: "Don mai kuke da gãba da rashi jituwa a sakanin ƙu?" ko mai yasa kuke fada a sakanin ku?"
Yakubu yayi amfani da tambayan nan domin ya kwaɓi masu sauraro. za' a iya juya shi kamar bayani. AT; suna zuwa da muguwar sha'awar ku na abubuwa, sha'awar mugunta da yake a sakanin ku"
Ma'ana mai yuwa ne 1) akwai fada a sakanin masubi na wuri ɗaya, 2) faɗa wacce take, anafadin fada ,yana cikin ko wacce mai bi.
wannan kalma "ka ƙashe" wannan na iya faɗin yadda mutane suke yin abu mara kyau don su sami abin da suke so. za'a iya juya ta kamar "ka yi dukan ko wacce irin mugunta ka samu ama baza ka samu ba"
wannan kalma "faɗa" da "jayaya" suna nufin abu ɗaya na. Yakubu yayi amfani da su so nawa mutane suki musu a sakanin sa. AT: "ku fada kullum"
Ma'ana mai yuwa ne 1) "kuna tambaya da muraɗi mara kyau" ko "kuna tambaya da halin mara kyau" ko 2) " kuna tambayan abubuwa marasa kyau "
Yakubu yayi magana akan masubi kamar matayen da suke kwana da mazajen da ba nasu ba. AT: ba ku yin aminci ga Allah!" Dubi:
Yakubu yayi amfani da tambayan domin ya koya wa masu sauraronsa. Wannan za' a iya fasara shi kamar bayani. AT; ka sani ... Allah!"
wannan kalma na nufin ganawa da ko kasan cikin darajan ayukan duniya.
wadda yake aboki da duniya magabci na da Allah. Anan "abokantaka da duniya" ya tsaya ne a masayin abokantaka da duniya, da "gaba da Allah" ya tsaya a masayin gaba ne da Allah. AT; "abokan da duniya abokan gaba na Allah ne"
Yakubu yayi amfanin da tambayan nan domin ya gargaɗe masu sauraro. yin maga na a banza she na yin magana mara amfani. AT: "akwai dalilin da ya sa nassin ya fada"
wasu juyin, duk da ULB da UDB, sun fahimci wannan nassoshin zuwa ga ruhu mai tsarki. wasu juyin sun juya shi kamar "ruhun" kuma na nufin cewa ruhun yan adam wadda aka halita da shi. muna bada shawara cewa kuyi amfanin da ma'anar da aka bayar a wasu juyi da ake amfani da su.
wannan ayan na da dangataka da ayan da ya wuce. "amma ko da shike ruhun mu yakan so abin da baza mu samu ba, ya ba mu alheri da yawa, idan mun kaskantar da kan mu"
"Domin Allah ya bada alheri da yawa, nassin ... Domin Allah ya ba da alheri wa masu tawaliu, ku mika"
wannan na nufin mutane ma su girman kai a duka. AT: "mutane masu girman kai"
wannan na nufin mutane masu tawali'u a duka. AT: "mutane masu tawaliu"
"yi biyayya ga Allah"
yi gãba da shaiɗan" ko "kada ku yi abin da shaiɗan ya ka so"
"zai kuma gudu daga nan"
wannan kalman jam' i ne kuma yana nufin masu sauraro Yakubu.
Anan zuwa kusa na ba da ra'ayin zama mai gaskiya ga Allah.
Waɗan nan maganganu biyun na layi ɗaya da juna.
Wannan magana umurni na ga mutane suyi adalci rayuwa a maimakon rashin adalci. AT:" nuna hali a hanyan da za ta daukaka Allah"
Anan "zuciya" na nufin tunanin mutum da tausayi. AT: ku daidaita niyyar ku da tunanin ku"
Wannan kalman "zuciya biyu" na nufin mutum wadda ba zai iya yanke shawara mai karfi akan abu ba. AT: "mutane masu zuciya biyu" ko mutanen da ba za su iya yanke shawara idan suna so suyi ko karsu yi biyayya ga Allah"
Wannan kalman guda uku nada ma'a na kusan ɗaya. Yakubu yayi amfani da su domin ya jaddada mutane su zama masu rokon gafara da rashin yin biyayya ga Allah.
Wannan na faɗin abu ɗaya na a hanyoyi daban daban domin jaddadawa. wannan kalman "dariya," bakin ciki," "murna" da "bakin ciki" za'a iya juya su kamar fi'ili. AT: "dena dariya kayi bakin ciki. "dena yin murna ama kayi bakin ciki"
ku zama masu kaskanci zuwa ga Allah." An yi magana game da ayukan da aka yi da sanin Allah a zuciya kamar anyi ta ne a gaban Allah.
Yakubu ya nuna cewa Allah zai daraja mutum mai kaskanci ta wurin cewa Allah zai dauke wannan mutum a jiki daga kasan inda wannan mutumin ya mika kansa cikin kaskanci. AT: "zai daraja ka"
"munanan magana akan" or "hamayya"
Yakubu yayi magana akan masubi kaman su 'yan'uwan juna ne. ambatacce maganar sun haɗa da mata da kuma maza. AT: " 'yan'uwamu masubi"
"amma kana yi kamar mutum wadda ya bada dokan"
wannan na nufin Allah ne. "Allah ne kaɖai yake bada doka ya kuma sharanta mutane
wannan tambaya Yakubu yayi amfani da ita domin ya tsauta wa masu sauraron. wannan za'a iya baiyanata kamar sanarwa ne. AT: kai mutum ne kuma baza ka iya sharanta wani mutum ba."
Yakubu yayi magana akan bayar da lokaci kamar wani kuɗi ne. "zauna a chan na shekara"
Yakubu yayi amfani da wannan tambaya domin ya kwabɓi masu sauraron ya kuma koya masubi rayuwa ta jiki bashi da amfani.za a iya bayana sa kamar sanarwa. AT: "ba wadda ya san gabe, kuma rayuwan ka ba zai dawama harabada ba"
Yakubu yayi magana akan mutane kamar hazo ne wadda yaki bayyana bayan dan lokaci kuma ya bace. AT: "kana zama na dan lokaci ne sai kuma ka mutu"
"Maimakon haka, halin ka ya zama"
"zamu jima sosai muyi abin da muka shirya. "kalmanan "mu"baya nufin Yakubu ko masu sauraron amma misaline ga masu sauraron Yakubu su duba yadda ya kamata rayuwa ya zama.
duk wadda ya san ya kamata yayi abu mai kyau amma baiye ba zunubi ne gareshi
Mafarin shine sha'awar mugunta da na yaki shakanin su
Sun kasa samu domin sun tambaya ma mumunan abubuwa su kashe akan sha'awar muguntan su.
Mutum da ya yanke shawara ya yi abuntaka da duniya ya mai da kansha makiyi da Allah.
Allah na tsayayya da girman kai, amma yana ba da alheri ma masu tawali'u.
Iblis zai gudu.
Allah zai kusance wadanda suka kusance shi.
Yakubu ya gaiya ma masu bi kada su yi magana kushewa ma juna
Yakubu ya gaya wa masubi su fadi cewa idan Almasihu ya yadda, za mu rayu kuma mu yi wannan ko wancan.
Yakubu ya faɗi cewa waɗanda ke yin alfahari da shirinsu suna yin mugunta.
Zunubi ne idan wani ya san yin abu mai kyau, amma bai yi ba.
1 Ku zo yanzu, ku da kuke masu arziki, ku yi ta kuka da kururuwa domin bakin ciki iri-iri da ke zuwa gare ku. 2 Arzikin ku ya rube, tufafinku kuma duk cin asu ne. 3 Zinariya da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsar su kuwa zai zama shaida a kanku. Zai cinye naman ku kamar wuta. Kun yi ajiyar dukiyarku domin ranakun karshe. 4 Duba, hakin ma'aikata yana kuka - hakin da kuka hana wa wadanda suka girbe maku gonaki. Kuma kukan masu girbin ya tafi ya kai ga kunnuwan Ubangiji mai Runduna. 5 Kun yi zama cikin annashuwa a duniya kuma kun tsunduma kanku. Kun sa zukatan ku sun yi kiba domin ranar yanka. 6 Kun hukunta kuma kun kashe adalin mutum. Bai kuwa yi tsayayya da ku ba. 7 Saboda haka ku yi hakuri, 'yan'uwa, har sai zuwan Ubangiji. Duba, yadda manomi ya kan jira kaka mai amfani daga gona. Da hakuri yake jiran ta har sai ta karbi ruwa na fari da na karshe. 8 Ku, ma, ku yi hakuri. Ku karfafa zukatan ku, domin zuwan Ubangiji ya yi kusa. 9 Kada ku yi gunaguni, 'Yan'uwana, game da juna, don kada a hukunta ku. Duba, mai shari'a na tsaye a bakin kofa. 10 Dauki misali, 'yan'uwa, daga shan wuya da hakurin annabawa, wadanda suka yi magana a cikin sunan Ubangiji. 11 Duba, mukan kira wadanda suka jimre masu albarka. Kun dai ji irin jimiri da Ayuba ya yi, kun kuma san nufin Ubangiji, yadda yake mai yawan tausayi da jinkai. 12 Fiye da komai duka, 'yan'uwana, kada ku yi rantsuwa, ko da sama, ko da kasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. A maimakon haka bari "I" ya zama "I", in kuwa kun ce "A'a", ya zama "A'a", don kada ku fada a cikin hukunci. 13 Akwai wanda ke fama a tsakanin ku? Sai ya yi addu'a, akwai wanda yake murna? Sai ya raira wakar yabo. 14 Akwai mara lafiya a tsakanin ku? Sai ya kira dattawan ikilisiya, sai su yi masa addu'a. Suna shafa masa mai a cikin sunan Ubangiji. 15 Addu'ar bangaskiya zai warkar da mara lafiyan, Ubangiji zai tashe shi. Idan ma ya yi zunubi, Allah zai gafarta masa. 16 Soboda haka, ku furta zunuban ku ga juna, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da karfin aiki kwarai da gaske. 17 Iliya dan Adam ne kamar mu. Amma da ya nace da addu'a kada a yi ruwa, ba kuma yi ruwa a kasar ba har shekara uku da wata shida. 18 Sai Iliya ya sake yin addu'a. Sammai suka ba da ruwa, kasa kuma ta ba da amfanin ta. 19 Ya ku 'yan'uwana, idan wanin ku ya baude wa gaskiya, wani kuma ya dawo da shi, 20 wannan mutum ya sani cewa, duk wanda ya dawo da mai zunubi a hanya daga baudewar sa, zai cece shi daga mutuwa, kuma zai rufe dunbin zunubai.
Yakubu ya gargaɗe masu kuɗi game da maida hankali ga rayuwan nishaɗi da kuɗi .
AT: 1) Yakubu na bada gargaɗi mai karfi game da masubi da ke da arziki, ko 2) Yakubu na magana ne akan masu arziki marasabi. AT: " ku da kuke da kuɗi kuma kun ce kuna grimama Allah"
Yakubu ya ambata cewa mutanen za su sha wahala mai tsanani nan gaba, kuma ya rubuta game da wahalar kamar wani abu ne da take zuwa garesu. wannan kalman "bakin ciki"za 'a iya juyata kamar aikatau. AT: domin zaku sha tsananin wahala nan gaba "
Arzikin duniya bata jimawa ko kuma wata madowwamiyar daraja. Yakubu yayi magana akan waddannan abubuwa kamar sun rega sun faru. AT: "arzikin ku zai ruba, asu kuma zasu ci tufafinku. zinariyar ku da azurfarku zasu yi tsatsa"
waddannan abubuwan da aka ambata misalin abubuwa ne masu daraja ga mutane masu arziki.
An yi amfani da kalmomin nan domin a siffanta yadda zinariya da azurfa suke hasara. AT: "ke hasara ... yana yin hasara" ko " ke lalacewa ... sun lalace"
Yakubu ya rubuta akan darajan abubuwan yadda suke da hasara kamar mutum ne wadda aka masa zargi a gidan shari'a. AT: "idan Allah yayi maka shari'a hasaran dukiyan ka zai zama kamar wadda aka zargi shi a gidan shari'a. lalacewa su" (Dubi: da )
Anan ana maganar lalacewar kamar wuta ne da zai kona masushi.
Wuta anan na tunashe mutane game da hukuncin Allah mai zuwa akan dukan mugaye.
Wannan na nufin dab da lokacin da Allah zai zo ya shara'anta dukan mutane. mugaye na tunanin cewa suna ajiyan arziki domin lokaci mai zuwa, amma ba su sani da cewa suna ajiye wa kansu shari'a bane. AT: "domin idan Allah zai yi maka shari'a"
Kuɗin da yakamata ayi biya ana maganar sa kamar mutun wadda yake ihu domin rashin gaskiya da aka yi masa. AT: " hakika domin kaki ka biya wadda kayi hayar su suyi maka aiki a ganarka yanuna cewa baka yi daidai ba"
Ana maganar ihun masu girbin kamar za'a jisu a sama. AT: "Ubangiji mai runduna yaji kukan masu gribin"
Ana maganar Ubangiji kaman yana da kunnuwa kamar na mutane.
anan an kalla mutane kamar shanu, dasuke marmari suci abinci suyi kiɓa domin ayanka su abiki. koda shike ba wadda zai yi biki a lokacin shari'a. AT: "haɗamar ku ya shirya ku domin masanancin madowamiyar shari'a"
"zuciyar " an duba ya zama sakiyar begen mutane, yana kuma nufin mutum gaba ɗaya.
Wannan ba halamar "hukunci" cikin azancin shari'a wadda akan sharanta mai laifi zuwa ga mutuwa. maimakon, kokuma na nufin zuwa ga masu karfi kokuma magayen mutane wadda suke wahalar da talakoki har ga mutuwa.
" mutane da suka yi abin da ke da kyau. ba suyi" ana "adalin mutun" na nufin adallen mutane ba a gaya kuwa mutun ɗaya ba . AT: adallen mutane. ba suyi"
"yi hamayyan ku"
akarshe Yakubu ya tunashe masubi game da zuwan Ubangiji ya kuma bada wasu kananan darasi game da yadda za'a zauna wa Ubangiji
"Domin wannan ku jira da hankali"
wannan kalmar na nufin zawan yesu, lokacin da zai fara mulkinsa anan duniya ya kuma sheranta mutane. AT: "har ga zuwan Ubangiji"
Yakubu yayi misali da manomi da masubi domin ya koya masu hakuri.
Yakubu na shirya zuciyar masubi ga sa ziciya. AT: "sa zuciya" ko "sa ajiye bangaskiyar su da karfi"
"Ubangiji yayi kusan dawowa"
Yakubu na rubutawa dukan Yahudawa masubi da ke warwatse.
"akan juna"
AT: Almasihu ba zai yi maku shari'a ba
"ku saurara domin abin da zan faɗa gaskiya na kuma nada amfani: mai shari'a"
Yakubu ya kwatanta Allah, mai shari'a, kamar mutum wadda yake so ya shiga ta kofa yayi nauyin akan zuwan Allah ya yi kusa domin ya sharanta duniya. AT: "mai shari'an yayi kusan zuwa" Dubi:
" yaya annabawan dasu kayi magana acikin sunar Ubangij suka jimre wuya da zalunci"
"Suna" wannan ya tsaya a masayin mutumin Allah. AT: "da ikon Ubangiji" ko "yi maganar Ubangijiwa mutane"
"ku saurara, domin abunda inaso in faɗa gaskiyane kuma nada amfani: mun duba"
"wadda suka cigaba da bin ummurnin Allah ko da shan wuya"
wannan na da amfani 'yan'uwana:" ko "musamman' 'yan'uwana"
wannan na nufin masubi harda mata. AT: 'yan'uwa masubi"
yin "ransuwa" shene kace zaka yi abu, kokuma abu gaskiyane, kokuma manyan ikoki su rike ka ga tambayoyi. AT: kada kayi rantsuwa" ko "kada kayi alkawali"
wannan kalman "sama" da "kasa" na nufin ikoki na jiki ko na ruhu wadda ke sama ko kasa.
"kayi abin da kace zaka yi, ko kace abu gaskiyane, basai kayi rantsuwa ba"
Anan maganar yin hukunci kamar wani ya fadi,rugurguji da nauyin wani abu. AT: "Allah kuma ba zai horas da shiba"
Yakubu yayi amfani da tambayannan domin ya sa mai karatu yayi tunani akan damuwar sa. za'a iya juya ta kamar labari. AT: idan akwai wadda yake jure wa damuwa, sai yayi addu'a"
Yakubu yayi amfani da tambayan nan domin ya sa mai karatu yayi tunani akan albarkan sa. za'a iya juya wannan kamar labari' AT: idan wani yana murna,sai ya raira wakar yabo
Yakubu yayi amfani da tambayan nan domin ya sa mai karatu yayi tunani akan damuwanr sa. za'a iya juya ta kamar labari. AT: "idan Akwai mara lafiya, Sai ya kira"
"Suna" wannan ya tsaya a masayin mutumin Yesu Almasihu. AT: da ikon Ubangiji" ko "da ikon da Ubangiji ya ba su"
Marubucin ya yi magana akan Allah ya na jin addu'a marasa lafiya ya kuma warkar da su kamar addu'a da kansa ya na warkar da mutane. AT: "Ubangiji zai ji addu'ar mai bangaskiya kuma zai warkar da mara lafiya"
"Addu'ar da masu bi suke yi" ko "Addu'ar da mutane ke yi suna bada gaskiya cewa Allah zai yi yadda suka tambaya"
"Ubangiji zai warkar dashi" ko "Ubangiji zai taimakeshi ya koma ayukan sa daidai"
Ku yarda da abin da kuka yi da ba kyau wa sauran masubi domin a yafe maku.
"ga kowan ne dayan ku"
Wannan za'a iya bayyana a wata siffa. AT: "domin Allah ya warkar da kai"
An hallarar da addu'a kamar wani abu mai karfi. AT: "idan mutumin da yake biyyaya ga Allah ya yi addu'a, Allah zai yi abubuwa mai girma"
"3 ... 6"
"addu'a mai ƙosawa" ko "addu'a na ƙwarai"
"Saman" mai yuwa na nufin sararin sama, wanda ya zama shine tushin ruwa. AT: "Ruwa yana fadowa daga sararin sama"
Anan ƙasa ya hallara kamar tushin baroro.
Anan " 'ya'ya" ta tsaya a masayin dukan baroron manomi.
Wannan kalma anan zai iya nufin maza da kuma mata. AT: "'yan'uwanmu masu bi"
Anyi magana game da mai bi da ya bar dogara da kuma yiwa Allah biyayya kamar yanda tumaki kan bace daga cikin garke. Ana kuma yi magana game da mutum da ya lallashe shi kamar makiyayi da ya je neman tumakin da ya bace. AT: "duk lokacin da wani ya bar yiwa Allah biyayya, kuma wani mutum ya taimake shi ya cigaba da yin biyayyan kuma"
Yakubu na nufin Allah zai more kuzarin mutum mai zunubin ya tuba ya kuma tsira. Amma Yakubu yayi magana kamar wani mutun daban da ya ceci ran mai zunubin daga mutuwa.
Anan "mutuwa" na nufin mutuwa na ruhaniya, rabuwa da Allah na har'abada. AT: "zai cece shi daga mutuwan na ruhaniya, kuma Allah zai yafe wa mai zunubin dukan zunuban sa"
AT: 1) mutumin da ya dawo da ɗan'uwa mara biyayya, za'a yafe masa zunubansa ko 2) ɗan'uwa mara biyayya, in ya koma ga Ubangiji, zai yafe zunuban sa. Anyi maganar zunubi kamar wani abu da Allah ya rufe da ba zai gansu ba, domin ya yafe masu.
Masu arziki sun tsibanta taskansu.
Waɗannan masu arziki basu biya ma'aikatansu ba.
Waɗannan masu arziƙin sun kushe suka kuma salihin mutumin.
Ya kamata masubi su jira da hakuri domin zuwan Ubangiji.
Annabawan tsofon alƙawari sun nuna hakuri da jurewa a wahala.
"I" na mai dole ne ya zama "I" kuma "A'an" shi kuma dole ya zama "A'a".
Ya kamata waɗanda ba su da lafiya su kira dattawa don su yi masa adu'a su kuma shafa masa mai.
Ya kamata masubi su furtawa juna laifofinsu su kuima yi wa juna addu'a.
Misalin Iliya ya nuna mana cewa addu'an mutum salihi na samar da babban sakamako.
Mutumin da ya jagoranci mai zunubi ya fita daga kuskuren hanyarsa ya cece rai daga mutuwa ya kuma rufe taron zunubai.
1 Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zababbu wadanda suke baki, a warwatse cikin Buntus, Galatiya, kappadokiya, Asiya, da Bitiniya. 2 Bisa ga rigasanin Allah Uba, Ta wurin tsarkakewar Ruhu, zuwa biyayya da yayyafar jinin Yesu Almasihu. Alheri da salama su yawaita a gareku. 3 Albarka ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu. Ta wurin jinkansa mai girma, ya maya haihuwarmu zuwa bege mai rai ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu. 4 Zuwa gado marar lalacewa, marar baci, ba kuma zai kode ba. Wanda aka kebe a sama dominku. 5 Ku da ikon Allah ya kiyaye ta wurin bangaskiya domin ceto wanda za'a bayyana a karshen zamanai. 6 Cikin wannan kuna murna da yawa, duk da ya ke ya zama wajibi gare ku yanzu ku yi bakin ciki, a cikin jarabobi iri iri. 7 Wannan kuwa da nufin a iske aunawar bangaskiyarku ne, bangaskiyar da tafi zinariya daraja, wadda takan lalace ko da an gwada ta da wuta. Wannan ya faru domin bangaskiyan nan taku ta jawo maku yabo da girma da daukaka a bayyanuwar Yesu Almasihu. 8 Wanda kuke kauna, ko da yake baku ganshi ba. Ko da yake baku ganinsa yanzu, duk da haka kun bada gaskiya gare shi murnar da ku ke yi kwarai da farin ciki wanda tafi gaban a fadi cike da daukaka. 9 Kuna karbar sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku. 10 Annabawan da su ka yi annabcin ceton da ya zama naku su ka yi bidassa suka bincike kuma da himma. 11 Sun nemi su san ko wanene da kuma kowanne lokaci ne Ruhun Almasihu da ke cikinsu yake bayyana ma su. Wannan ya faru ne sa'adda yake gaya ma su tun da wuri game da shan wahalar Almasihu da kuma daukakar da zata biyo baya. 12 An kuwa bayyana wa annabawan cewa ba kansu suke hidimtawa ba, amma ku suke yi wa hidima. Wannan shine abin da suke yi game da abin da aka rigaya aka gaya maku, ta wurin wadanda da Ruhu mai Tsarki ya bishe su. Wanda aka aiko daga sama. Wadannan sune abubuwan da mala'iku ma suka yi marmarin a bayyana masu. 13 Domin wannan fa ku natsu. Ku yi dammara a hankalinku. Ku kafa begenku sarai akan alherin da za'a kawo maku a lokacin bayyanuwar Yesu Almasihu. 14 Kamar 'ya'ya masu biyyaya, kada ku biyewa sha'awoyinku na da a zamanin jahilcinku. 15 Amma yadda shi wanda ya kira ku mai tsarki ne, kuma ku zama da tsarki cikin dukkan al'amuranku. 16 Domin a rubuce yake, "Ku zama da tsarki, gama ni mai tsarki ne." 17 Idan ku na kira bisa gare shi "Uba" shi wanda yake hukuntawa ba da tara ba, amma gwar-gwadon aikin kowane mutum, sai kuyi zaman bakuncinku da tsoro da bangirma. 18 Kun san cewa ba da azurfa ko zinariya mai lalacewa aka fanshe ku ba, daga halinn wauta da kuka gada daga wurin iyayenku. 19 Maimakon haka an fanshe ku da jinin Almasihu mai daraja, marar aibu kamar na dan rago. 20 An zabi Almasihu tun kafin kafawar duniya, amma a karshen zamanu ya bayyanu a gare ku. 21 Ku da kuka bada gaskiya ga Allah ta wurinsa, wanda ya tashe shi daga matattu ya kuma bashi daukaka domin bangaskiyarku da begenku su kasance cikin Allah. 22 Da shike kun tsarkake rayukanku cikin biyayyar ku ga gaskiya zuwa ga sahihiyar kauna ta 'yan'uwa, sai ku kaunaci junanku da zuciya mai gaskiya. 23 da shike an sake hai'huwarku ba daga iri mai lalacewa ba amma daga iri marar rubewa, ta wurin maganar Allah wadda take rayuwa ta kuma dawwama. 24 Gama "dukkan jiki kamar ciyawa yake, dukkan darajarsa kuwa kamar furen ciyawa take. Ciyawa takan yi yaushi, furenta ya kan yankwane ya fadi, 25 amma maganar Ubangiji tabbatacciya ce har abada. "Wannan ita ce maganar bishara wadda akayi maku wa'azinta."
Bitrus ya nuna kansa a matsayin marubucin, ya kuma gaishe da masubi waɗanda yake rubuta musu.
Bitrus ya yi magana game da masu karanta wasiƙarsa kamar mutane da ke zama nesa da gidajensu cikin ƙasashe dabam-dabam.
Da sauran wuraren da Bitrus ya ambata, "Kaffadokiya" da "Bitiniya" yankin Roma ne da ake kira a yau kasar Toki.
"zaɓaɓɓu waɗanda Allah Uban ya zaɓa ... bisa ga rigasaninsa." Allah ya zaɓe su bisa ga rigasaninsa.
"rigasanin" ana iya juya shi cikin magana. Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) Allah ya shirya abin da zai yi a kan lokaci. AT: "abin da Allah Uban ya shirya a da" ko 2) Allah ya san abin da zai faru a kan lokaci. AT: "abin da Allah Uban ya sani tun da wuri"
A nan "jinin" na nufin mutuwar Yesu. kamar yadda Musa ya yayyafa jini a kan mutanen Isra'ila don nuna alamar alkawarinsu da Allah, haka masubi suna cikin alkawari da Allah saboda mutuwar Yesu.
Wannan nassin na maganar alheri kamar wani abu ne da masubi za su iya samu, da kuma salama kamar wani abu ne da zata iya ƙãruwa. Alheri wata hanya ce ta kirki da Allah ke yin dangantaka da masubi, salama kuma ita ce yadda masubi suke rayuwa cikin kwanciyar rai da murna tare da Allah.
Kalman nan "mu" na nufin Bitrus ne da kuma waɗanda ya rubuta musu wasiƙar.
"ya sa an săke haihuwarmu"
Kuna iya yin amfani da aikatau ku juya wannan. AT: "da gabagaɗi muna sa rai za mu samu gădo"
An yi maganar samun abin da Allah ya alkawarta wa masubi kamar wata kayar gădo ce da kuma arziki daga wani ɗan iyali.
Bitrus ya yi amfani da waɗannan jimloli don ya bayyana cewa gădon wani abu ne mara aibi kuma madawwami ne.
AT: "Allah yana keɓe shi a sama domin ku"
AT: "Allah yana kiyaye ku"
A nan "iko" wata hanya ce ta cewa Allah yana da ƙarfi kuma shi mai iya tsare masubi ne.
A nan "bangaskiya" na nufin cewa masubi sun dogara ga Almasihu. AT: "saboda bangaskiyar ku"
AT: "cewa Allah yana shirye ya bayyana"
Kalman nan "wannan" na nufin dukan albarkun da Bitrus ya ambata a ayoyin da ke baya.
kamar yadda wuta tana sabunta zinariya, wahala tana gwada yadda dogarar masubi ga Almasihu take.
Allah yana so ya gwada yadda dogarar masubi take a cikin Almasihu.
Bangaskiya ta fi zinariya daraja, domin zinariya bata dawwamma ko an sake sabunta ta da wuta.
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) cewa "Allah zai ɗaukaka ku sosai" saboda bangaskiyar ku ko 2) cewa "bangaskiyar ku zata jawo yabo, girma da ɗaukaka" ga Allah.
"a sa'ad da Yesu Almasihu zai bayyana." Wannan na nufin dawowar Almasihu. AT: "a sa'ad da Yesu Almasihu ya bayyana ga dukan mutane"
"farin ciki mai ban mamaki da kalmomi ba za su iya bayyana ta ba"
Anan kalman nan "rayuka" na nufin mutum. Kalman nan "ceto" ana iya juya ta da aikatau. AT: "ceton ku" ko " Allah ya cece ku"
Kalmomin nan na ba da ra'ayoyi biyu kamar waɗansu al'amurra ne ko kuma abubuwa. "Ceto" na nufin abin da Allah ya yi don ya cece mu, ko kuma abin da ya faru ta dalilin sa. "Alheri" na nufin yadda Allah ke yin dangantaka da masubi cikin kirki.
kalmomin nan "bin diddigi" na nufin abu daya ne da "bincike." waɗannan kalmomin na nanata wuyar da annabawa suka sha don ƙoƙarin fahimtar wannan ceton." AT: "matsanaciyar dubawa da kula"
Bitrus ya cigaba da magana game da binciken annabawan game da ceto.
"Sun yi ƙoƙarin neman gaskiyar"
Wannan na nufin Ruhu Mai Tsarki.
AT: "Allah ya bayyana wa annabawan"
"cewa mala'iku ma suna so su fahimta"
"domin wannan, yi ɗammara." Bitrus ya yi amfani da wadannan kalmomi "don haka" don ya koma baya zuwa ga dukkan abin da ya faɗa game da ceto, bangaskiyar su, da kuma yadda Ruhun Almasihu yake bada wahayin ga annabawan.
Yin ɗammara a hankalinku na nufin shirin aiki ƙwarai da gaskiye. Wannan na samuwa ne daga al'adar shigar da ƙasar riga karkashin ɗamarar dake kewaye da ƙugu domin iya tafiya cikin sauƙi. AT: "ku shirya zukatanku"
A nan kalmar nan "natsu" na nufin hankali mai tsabta da kuma shiri. AT: "Kula da tunaninku" ko "yi kula da abinda ku ke tunani"
AT: "Alherin da Allah zai kawo maku"
Wannan na nufin dawowar Yesu Almasihu. Dubi yadda kuka juya wannan cikin [1 Bitrus 1:7]. AT: "a sa'ad da Yesu Almasihu ya bayyana ga dukan mutane"
"kada ku yi sha'awan abin nan kuma" AT: "kada ku yi rayuwar biye wa sha'awace-sha'awacen"
Wannan na nufin saƙon Allah cikin Littafi Mai Tsarki. AT: "Gama kamar yadda Allah ya faɗa"
Anan kalman nan "Ni" na nufin Allah.
Bitrus ya yi magana game da masu kara wasiƙar kamar su mutane ne da ke zama cikin kasar da ba tasu ba wadda take nesa da gida. AT: "ku yi amfani da lokacin da kuke zama inda ba gidan ku ba"
AT: "Allah ya fanshe ku"
A nan "jini" na madadin mutawar Almasihu bisa giciye.
Yesu ya mutu a madadin hadaya don Allay ya yafe wa mutane zunubansu. AT: "kamar dan rago mara aibu ko tabo da firistocin yahudawa ke yin hadaya" Dubi:
Bitrus ya bayyana ma'ana ɗaya ta hanyoyi dabam-dabam guda biyu don nanata tsarkin Almasihu. AT: "babu lahani"
AT: "Allah ya zaɓi Almasihu"
Ku na iya juya wannan da jumla ta aikatau. AT: "Kafin Allah ya halici duniya"
AT: "Allah ya bayyana shi a gare ku"
A nan "tashe shi," na nufin sa wadda ya mutu ya sake yaruwa kuma. AT: "wadda ya sa shi ya rayu, hakannan kuwa ba ya cikin matattu"
"kuma ɗaukaka shi" ko "kuma nuna cewa shi maɗaukaki ne"
A nan kalmar nan "rayuka" na nufin mutum. AT: "kun tsarkake kan ku"
A nan "tsabta" na nufin samun karbuwa ga Allah.
Kuna iya juya wannan ta wurin yin amfani da jumla ta aikatau. AT: "ta wurin yin biyayya ga gaskiyar"
Wannan na nufin ƙauna tsakanin masubi.
A nan "zuciya" na nufin tunani da kuma shauƙin mutum. A ƙaunaci wani "daga zuciya" na nufin a ƙaunaci wani sasai da dukan miƙa kai. AT: "ƙaunaci junanku da himma da kuma miƙa kai"
Ma'anoni masu yiwuwa su ne cewa Bitrus ya yi magana game da maganar Allah ko dai 1) kamar iri dake girma ya kuma haifi sabon rayuwa cikin masubi ko 2) kamar wata ƙanƙanin ƙwai na jiki miji ko mace dake sa yaro ya yi girma cikin mace.
iri da ba zai ruɓa ba, ko ya bushe, ko kuma ya mutu
Bitrus ya yi magana a kan maganar Allah kamar tana raye har abada. Allah ne ke raye har abada, kuma dokokin sa da alkawuran sa sun dawwama har abada.
Kalmar nan "jiki" na nufin dukan 'yan Adam. annabi Ishaya ya kwatanta 'yan adam duka kamar ciyawa ne da ke girma da kuma mutuwa da sauri. AT: "Dukan mutane za su mutu kamar yadda ciyawa ke mutuwa"
A nan kalmar nan "daraja" na nufin kyakkyawa ko nagarta. Ishaya ya kwatanta abubuwan da mutane ke duba a matsayin abu mai kyau game da 'yan adam da fure dake mutuwa da sauri. AT: "nagartar 'yan adam na tsayawa, kamar yadda fure ke mutuwa nan da nan"
"sakon da ke zuwa daga wurin Ubangiji"
A nan kalmar nan "wannan" na nufin "maganar Ubangiji"
AT: "bisharar da mun sanar da ku"
Bitrus annabin Yesu Almasihu ne.
Bitrus ya rubuta wa bakin da suke watsuwa, zababbun, cikin Pontus, Galatia, Kappadocia, Asia, da kuma Bitynia.
Baƙin sun zama zaɓabɓu bisa ga sannin Allah Uba, kuma ta tsarkakar Ruhu mai Tsarki.
Bitrus ya so su samu alheri da ƙaruwar salama.
Bitrus ya so a albarkace Allah da Uban Ubangijinsu Yesu Almasihu.
Allah ya ba su sabon haifuwa a cikin babban rahamarsa.
Domin an ƙebe masu gadon a sama.
An kare su ta wurin bangaskiya don ceton da an shirya a bayyana a karshen loƙaci.
Wajibi ne don a gwada bangaskiyarsu, kuma domin sakamakon bangaskiyarsu ya kawo yabo, girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Almasihu.
Bangaskiya tafi zinariya daraja.
Sun ƙaunace shi, sun gaskanta da shi, sun kuma yi farin ciki da murna kwarai da ya cika da ɗaukaka.
Sun samu ceton ransu.
Annabawan sun yi bincike game da ceton da masubin su ke samu, game da alherin da zai zama nasu.
Ya na gaya masu game da azaban Almasihu da kuma ɗaukakan da zai bi shi.
Su na yin hidima wa masubi.
Har mala'ikun sun so a bayyana sakamakon.
Ya umurce su su shirya zuciyarsu don su gaskanta da Allah, su zama da natsuwa a tunaninsu da cikakken aminci a alherin da za a kawo masu, kuma kada su bi sha'awarsu na da.
Domin wanda ya kira su mai tsarki ne.
Domin su na ƙiran "Uba" wanda ya ke hukunci ba tare da nuna bambanci bisa aiƙin kowa ba.
Ba a fanshe su da zinariya ka azurfa ba, amma da ɗaukakar jinin Almasihu, kamar na Ragon da bai da aibi ko tabo.
Sun koya halin wautan daga Ubannensu.
An zaɓe shi kafin kafawar duniya; an bayyana shi wa baki, zababbun, wato a loƙacin nan na karshe.
Ta wurin Almasihu, wanda Allah ya ta da daga matattu da wanda Allah ya ba da ɗaukaka.
Sun tsarkake kansu ta biyayya ga gaskiyan don ƙauna na yan'uwa.
An sake hai'huwarsu daga iri mara lalacewa, ta wurin sauran rayayyen maganar Allah, ba daga iri mai lalacewa ba.
Jiki kamar ciyawa ne, darajarsa kuwa kamar furen ciyawa.
Maganar Ubangiji tabbatacciya ce har abada.
1 Saboda haka sai ku tube dukkan keta, rikici, da riya, kishi, da dukkan mugun zance. 2 Kammar jarirai, sababbin haihuwa, ku yi marmarin madara mai ruhaniya wadda take sahihiya, domin ta wurinta kuyi girma zuwa ceto, 3 idan kun dandana Ubangiji mai-alheri ne. 4 Kuzo gareshi rayayyen dutse wanda mutane suka ki, amma zababbe ne mai-daraja wurin Allah. 5 Ku kuma kamar rayayyun duwatsu ana gina ku gida mai ruhaniya, domin ku zama tsarka-kan fristoci, domin ku mika hadayu masu ruhaniya abin karba ga Allah ta wurin Yesu Almasihu. 6 Gama nassi ya ce, "Ga shi na sanya dutse na kan kusurwa, zababe, mai daraja a cikin Sihiyona. Duk wanda ya bada gaskiya gareshi ba zaya kunyata ba." 7 Daraja a gareku take ku da kun bada gaskiya. Amma, ga wadanda suka ki bada gaskiya, "Dutsen da magina suka ki shine aka mai she shi kan kusurwa". 8 kuma, "Dutsen sa tuntube da fa na sa tuntube. "Sun yi tuntube, da shike sun ki biyayya da maganar, an kuwa kaddara su ga wannan. 9 Amma ku zababben jinsi ne, kungiyar fristoci ba-sarauci, al'umma mai-tsarki, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wanda ya kiraye ku daga chikin duhu zuwa cikin haskensa mai'ban al'ajibi. 10 Ku da ba jama'a ba ne a da, amma yanzu jama'ar Allah ne. Da baku sami jinkai ba, amma yanzu kun sami jinkai. 11 Kaunatattu, ina rokon ku misalin baki da masu-tafiya kuma, ku guje wa sha'awoyin jiki wadanda ke yaki da rai. 12 Ku kasance da kyakkyawan hali a cikin al'ummai, domin, sa'adda suke kushen ku kamar masu aikata mugunta, sai su lura da nagargarun ayyukanku su kuma daukaka Allah a ranar zuwansa. 13 Kuyi biyayya ga kowacce hukuma ta mutane sabili da Ubangiji, ko ga sarki domin shi ne shugaba. 14 Ko kuwa ga masu mulki aikakkunsa ne domin su hori masu aikata mugunta da yabawa masu aikata nagarta. 15 Gama wannan nufin Allah ne, ta wurin aikin kirki ku, kwabi jahilcin mutane marassa hikima. 16 Kamar 'yan'tattu kada ku mori 'yan'cinku kamar mayafin mugunta, amma ku zama kamar bayin Allah. 17 Ku girmama dukkan mutane. Ku kaunaci 'yan'uwa, kuji tsoron Allah. Ku girmama sarki. 18 Ku barori, kuyi biyayya ga iyayen gidanku da dukkan bangirma, ba ga nagargaru da masu saukin kai ba, amma har ga miskilai. 19 Gama abin yaba wa ne idan sabili da lamiri zuwa ga Allah in wani ya jimre da shan zalunci. 20 Gama wacce riba ke nan idan kun yi zunubi ana horonku kuna jimrewa da hukuncin? amma idan kunyi aikin kirki kuka sha wuya a kansa kuka yi hakuri, wannan abin karba ne wurin Allah. 21 Gama akan haka aka kiraye ku, gama Almasihu ma yasha azaba saboda ku, ya bar maku gurbi kubi sawunsa. 22 Bai taba yin zunubi ba, ba'a taba jin yaudara a bakinsa ba. 23 Da'a ka zage shi bai mai da zagi ba. Da ya sha azaba, bai yi kashedi ba, amma ya mika kansa ga wanda yake yin shari'ar adalci. 24 Shi da kansa ya dauki zunubanmu a cikin jiki nasa ya kai su bisa itace, domin kada a iske mu cikin zunubi, amma muyi rayuwa ga adalci. Ta wurin raunukansa ne kuka warke. 25 Dukkanku da kun bata kuna yawo kamar batattun tumaki, amma yanzu kun dawo wurin makiyayi da mai tsaron rayukanku.
Bitrus ya cigaba da koyar da masu karanta wasiƙar sa game da tsarki da kuma biyayya.
An yi maganar waɗannan ayukan zunubi kamar waɗansu abubuwa ne da mutane ke iya wurgawa. Kalman nan "Soboda haka" na nufin komawa zuwa ga abinda Bitrus ya faɗa game da zaman tsarki da biyayya a baya. AT: "don haka, ku tuɓe kowane mugun abu, da riya, da ƙishi, da kowane mugun zance" ko "don haka, ku bar aikata mugunta, ko ruɗu, ko riya, ko ƙishi ko mugayen zance"
Bitrus ya yi magana da masu karanta wasiƙar sa kamar jarirai. Jarirai suna bukatar tsantsan abinci wanda za su iya narkewa da sauki. haka kuma masubi suna bukatar tsantsan koyarwar daga maganar Allah. AT: Kamar yadda jarirai suna marmarin mama daga uwarsu, haka kuma lallai ne ku yi marmarin tsantsan madaran ruhaniya"
"matuƙar marmari" ko "yi begen"
Bitrus ya yi magana game da maganar Allah kamar wata madaran ruhaniya ce da ke da amfani sosai ga 'ya'ya
A nan kalmar nan "ceto" na nufin a sa'ad da Allah ya kammala ceton mutanensa a lokacin da Yesu ya dawo (Dubi 1 Bitrus 1:5).
Bitrus ya yi maganar karuwa cikin sanin Allah da kuma amincin masubi ga Allah kamar su 'ya'ya ne da ke girma.
A nan ɗanɗana na nufin mutum ya jin abu da kansa. AT: "In ka ji alherin Ubangiji zuwa gare ka"
Bitrus ya fara faɗin misalin Yesu da masubi a matsayin rayayyun duwatsu.
Bitrus ya yi magana game da Yesu kamar shi dutse ne cikin gini. AT: "Zo gare shi, wanda shi kamar dutsen gini, amma rayayye, ba mataccen dutse ba"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "wanda shi rayayyen dutse ne" ko 2) "wanda shine dutsen da ke bada rai."
AT: "wanda mutane suka ƙi"
AT: "amma wanda Allah ya zaɓa"
Kamar yadda mutane ke gina haikali a Tsohon Alkawari, masubi kayan da Allah ke amfani da shi ya gina gidan wanda zai yi rayuwa a cikin ta ne.
Bitrus ya kwatanta masu karatunsa da duwatsun da ke raye.
AT: "da Allah ke ginawa zuwa ga gidan ruhaniya"
Anan matsayin firist na nufin frist wanda ke cika aikin sa na wajib
An yi maganar nassin kamar wata akwati. Wannan na nufin kalmomin da mutum ke karantawa cikin nassin. AT: "Wannan ita ce abin da annabin ya rubuta cikin nassosin tun dã.
A nan "ga shi" na jan hankalin mu da mu yi kula da labari mai ban mamaki da ke zuwa.
Allah ne wanda ya zaɓi dutsen. AT: "dutsen kusurwa mai muhimmanci, wanda na zaɓa"
Annabin ya yi magana game da Almasihu cewa shi dutse ne mai muhimmanci na gini.
Wannan na nufin mutane, kamar masu gini,sun ƙi Yesu, amma Allah ya maishe shi dutse mafi muhimanci na gini.
AT: "dutsen da maginan suka ƙi"
Wannan na nufin dutse mafi muhimanci a gini kuma na nufin abu ɗaya da "dutsen kusurwa" cikin [1 Bitrus 2:6].
Waɗannan batutuwa guda biyu na da ma'ana kusan iri ɗaya. Tare, su na nanata cewa mutane za su yi fushi da wannan "dutsen" wanda na nufin Yesu. AT: "dutse wanda mutane za su yi tuntuɓe a kai"
A nan "maganar" na nufin saƙon bishara. Yin rashin biyayya na nufin ba su gaskata ba. "tuntuɓe don ba su gaskanta da saƙo game da Yesu ba"
AT: "abin da Allah ya ƙaddara gare su"
za ku iya bayyana cewa Allah ne ya zaɓe su. AT: "mutane wanda Allah ya zaɓa"
ma'anoni masu yiwuwa 1) "kungiyar sarakuna da kungiyar firistoci" ko 2) "kungiyan firistoci wanda ke yi wa sarki hidima."
"mutanen Allah"
"wanda ya kira ku ku fita"
A nan "duhu" na nufin yanayin mutane masu zunubi wanɗanda ba su san Allah ba; "haske" na nufin yanayin mutane wanɗanda sun san Allah suna kuma aikata adalci. AT: "daga rayuwar zunubi da rashin sanin Allah zuwa ga rayuwa ta sanin sa da kuma faranta masa rai"
wanɗannan kalmomin na nufin abu ɗaya ne. Bitrus ya yi magana game da masu karatunsa a matsayin mutane da ke rayuwa a kasar da ba nasu ba, nesa da gidan. Dubi yadda kuka juya "baƙi" cikin [Bitrus 1:1]
A nan jiki na nufin halin mutuntaka ta 'yan adam cikin wannan duniya mai shuɗewa. AT: "don kada mu bada zarafi ma sha'awace-sha'awacen zunubi"
A nan kalmar nan "zuciya" na nufin rayuwar ruhaniyar mutumin. Bitrus ya yi magana game da sha'awace-sha'awacen zunubi kamar sojoji ne da ke ƙoƙarin rushe ruhaniyar masubi. AT: "biɗan rushe rayuwar ruhaniyar ku"
Ana iya juya "hali" da aikatau. AT: "ku nuna halin kirki" ko "ku nuna halin kirki ta hanya mai kyau"
"in sun zarge ku da"
Ana iya juya "ayyuka" cikin aikatau. AT: "za su lura da nagargarun abubuwan da ku ke yi"
"a ranar da ya zo." Wannan na nufin ranar da Allah zai shar'anta dukkan mutane. AT: "sa'ad da ya zo don ya shar'anta kowa"
Ma'anoni masu yiwuwa 1) cewa tawurin biyayya ga hukumomi, su na biyayya ga Ubangiji wanda ya kafa waɗannan hukumomin ko 2) ta wurin biyayya ga hukumomin, za su girmama Yesu wanda kansa ma ya yi biyayya ga hukumomi.
"sarki wanda shine mafi girma ciki hukumar mutane"
AT: "wanda sarkin ya aika su hori"
"ta wurin aikin nagarta, za ku kwaɓi mutane marasa hikima daga faɗin abubuwan da ba su sani ba"
Bitrus ya yi maganar yanayinsu a matsayin 'yantattun mutane kamar wani abu ne da bai kamata su yi amfani da shi don ɓoye halin zunubi ba. AT: "hujjar yin mugayen abubuwa"
Wannan na nufin dukan masubi.
A nan kalmomin nan "nagari" da "saukin kai" na da ma'ana kusan iri ɗaya na kuma nanata cewa iyayen gidan nan na yi wa bayin su alheri. AT: waɗannan iyayen giji masu alheri"
"marasa tausayi" ko "marasa ladabi ga mutane"
"ta cancanci yabo" ko "ta faranta wa Allah rai"
Ma'anoni masu yiwuwa na asalin wannan nassi suna kamar haka 1) cewa wannan mutum ya karɓi wahala saboda ya san cewa yana biyayya ga Allah ko 2) cewa wannan mutum ya iya jumre hukunci mara adalci saboda ya san cewa Allah ya san yadda yake shan wahala.
Bitrus ya yi wannan tambaya don ya nanata cewa babu wani abin yabo game da shan wahala don yin abin da ba daidai ba. AT: Gama babu wata riba ... in an sha hukunci."
AT: "sa'annan wani ya hukunta ku"
AT: "kun sha wuya sa'ad da wani ya hukunta ku"
A nan kalmar nan "wannan" na nufin jumrewar masubi a sa'ad da suke shan wahala don aikata nagarta, kamar yadda Bitrus ya bayyana. AT: " Allah ya kiraye ku ga wannan"
"don ku bi sawunsa." Bitrus ya yi magana game da bin gurbin Yesu ta hanyar shan wuya kamar wani na tafiya a tafarkin Yesu. AT: "don ku kwaikwayi halin sa"
AT: "babu wani kuwa wanda ya sami yaudara a bakin sa"
A nan "zagi" shi ne a yi maganar ashar ga mutum. AT: " Da mutane suka zage shi, ba mai da zagin ba"
"ya danƙa kansa ga wanda ke shari'ar adalci." Wannan na nufin ya dogara ga Allah ya dauke kunyar da aka sa a kansa daga waɗanda suka tsananta masa.
Tare da nanaci, wannan na nufin Yesu ne.
Anan "ɗauke zunubanmu" na nufin ya sha wahalar hukunci saboda zunubanmu. AT: "sha wahalar hukunci saboda zunubanmu a cikin jikin sa bisa itace"
Wannan na nufin giciye wanda Yesu ya mutu a kai, wanda aka yi ta da itace.
AT: "Allah ya warkar da ku don mutane sun yi masa rauni"
Bitrus ya yi magana game da masu karatunsa kafin su gaskata da Almasihu kamar su na kama da tumakin da ke yawo ba manufa.
Bitrus ya yi magana game da Yesu kamar shi makiyayi ne. Kamar yadda makiyayi ke tsaron tumakin sa, Yesu yana tsaron waɗanda sun dogara a gare shi.
An gaya masu su sa a gefe dukkan ketan rikici, da riya, kishi, da dukkan mugun zance.
Ya kamata su yi marmarin madara mai ruhaniya don su iya girma a cikin ceto.
Yesu Almasihu ne rayayyen dutsen.
Suna nan kamar rayayyun duwatsu saboda an gina su domin su zama gida na ruhaniya.
Maginan sun yi tuntuɓ don an sa su su yi haka.
An zaɓe su don su iya sanar da ayyukan al'ajibi na Allah.
Ya ce masu su guje don waɗanda za su iya ce sun yi mugun abu, za su iya gani kyauwawan ayyukansu su kuma girmama Allah.
Zasu yi biyayya da kowane hukuma ta mutum domin Allah ya na so ya yi amfani da biyayyar su don ya rufe maganar rashin sanin wautan mutane.
Za su yi amfani da yancinsu don su zama bayin Allah.
Ya kamata barori su yi biyayya har da miskilan iyayen gidansu domin yin ƙyauwawan abubuwa sai kuma wahala, hukunci, ɗaukaka ne da Allah.
Domin Almasihu ya sha azaba saboda ku, ya bar masu gurbi, ya kuma ba da kansa wa wanda ke yin hukunci da adalci.
Ya ɗauke zunubansu don kada su kasance da zunubi su kuma yi rayuwa na adalci, kuma domin an warkad da su ta wurin hudansa.
Sun dawo wurin makiyayin da kuma mai tsaron rayukansu.
1 Haka ku kuma da kuke matan aure, kuyi biyayya da na ku mazajen, domin in har wadansunsu basa biyayya da maganar Allah, halin matansu ya shawo kansu ba tare da magana ba, 2 Domin sun ga tsattsakan halinku da ladabinku. 3 Haka ma adonku kar ya zama na kwalliyar waje kitson kai, kayan zinariya ko tufafi masu kawa. 4 Amma bari adon ya zama na mutum na cikin zuciya, kuma adon ya zama kyan nan marar dushewa, na kamun kai da natsatsen ruhu, wanda yake da daraja a gaban Allah. 5 Haka tsarkakan mata su ka yi ado kamar haka. Suka dogara ga Allah suka yi biyayya ga mazajensu. 6 Ta haka Saratu ta yi biyayya ga Ibrahim ta kira shi "ubangiji". Yanzu ku 'ya'yantane in dai kun yi aiki nagari, idan kuma ba ku ji tsoron wahala ba. 7 Kamar yadda na fada wa matan aure haka ma mazaje, ku zauna da mata da sanin su raunana ne abokan tarayya ne na karbar baiwar rayuwa. Ku dinga yin haka domin a rika jin addu'oinku. 8 Daga karshe, dukanku ku hada hankulanku, ku zama masu juyayi, masu kauna kamar 'yan'uwa, masu taushin zuciya, masu tawali'u. 9 Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi. A maimakon haka ku cigaba da sa albarka, gama sabili da haka ne musamman aka kiraye ku, domin ku gaji albarka. 10 "Wanda duk yake so ya more a rayuwarsa ya kuma ga kwanaki masu alheri, to fa, ya kame harshen sa daga mugunta da lebensa daga maganganun yaudara. 11 Ya rabu da mugunta ya aikata abin da ke nagari. Bari ya nemi zaman salama ya kuma dimanceta. 12 Idanun Ubangiji suna duban adalai, kunnuwansa kuma suna sauraron roke rokensu. Amma fuskar Ubangiji tana gaba da masu aikata mugunta." 13 Wanene ya isa ya cuce ku idan kun himmatu ga yin abin da ke nagari? 14 Amma idan kuna shan wuya saboda adalci, ku masu albarka ne. Kada ku ji tsoron abin da su ke tsoro. Kada ku damu. 15 Maimakon haka, ku kebe Ubangiji a cikin zukatanku cewa shi mai tsarki ne. Kullum ku zauna da shiri domin ku amsa wa mai tambayar ku dalilin sa begenku ga Allah. Amma fa kuyi haka tare da tawali'u da bangirma. 16 Ku zama da tsatsakan lamiri domin mutanen da ke zargin rayuwarku mai kyau cikin Almasihu, su ji kunya domin suna maganar gaba da ku kamar ku mugaye ne. 17 Ya fi kyau, a sha wuya akan aiki nagari, idan nufin Allah ne, da a sha wuya sabili da mugun aiki. 18 Almasihu ya sha wahala sau daya tak sabili da zunubai. Shi da ya ke mai adalci ya sha wahala domin mu marasa adalci, domin ya kawo mu ga Allah. Aka kashe shi cikin jiki, amma aka rayar da shi cikin Ruhu. 19 A Ruhu ne, ya je ya yi wa'azi ga ruhohin da ke a yanzu cikin kurkuku. 20 Sun yi rashin biyayya ne sa'adda hakurin Allah yake jiransu a lokacin Nuhu a zamanin sassaka jirgin ruwa, sai Allah ya tsirar da mutane kalilan wato rayuka takwas daga cikin ruwa. 21 Wannan kwatancin baftismar da take cetonmu yanzu ne, ba kamar ta wanke Dauda daga jiki ba, sai dai ta rokon Allah da lamiri mai kyau ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu. 22 Ya hau sama. Yana dama ga Allah. Mala'iku, da mulkoki da masu iko dole su yi masa biyayya.
Bitrus ya fara magana da matan aure.
Daidai kamar yadda masubi za su yi "biyayya ga kowane hukuma ta mutane" [1 Bitrus 2:13] da kuma bayi su "yi biyayya" ga iyayen gijinsu [1 Bitrus 2:18], matan aure su yi biyayya ga mazajen su. Kalmomin nan "biyayyay", "bin" da kuma "mika kai" ana iya juya su ta wurin yin amfani da kalma ɗaya.
A nan "maganar" na nufin saƙon bishara. Rashin biyayya na nufin basu gaskata ba. Dubi yadda ku ka juya magana makamancin haka cikin [ 1 Bitrus 2:8]. AT: "Waɗansu mazaje basu gaskata da saƙo game da Yesu ba"
"mai yiwuwa a rinjaye su su gaskata da Almasihu." Wannan na nufin cewa mazajensu da ba su gaskata ba za su zama masubi. AT: "za su iya zama masubi"
"ba tare da matan ta yi wani magana ba." A nan "magana" na nufin wani abin da matan za ta iya faɗa game da Yesu.
Wannan kalmar "halinku" ana iya juya ta cikin aikatau. AT: "za su gani cewa kuna da tsattsarkan hali da ladabi"
Ma'anoni masu yiwuwa 1) "tsattsarkan halinku gare su da kuma yadda kuke girmama su" ko 2) "tsantsan halinku gare su da kuma yadda kuke girmama Allah."
Bitrus ya cigaba da magana da matan aure.
Wannan kalmar "ta" na nufin biyayyar matan auren da kuma halin su ga mazajen su.
A nan kalmomin nan "mutum na cikin zuciya" da "ziciya" na nufin ɗabi'a na ciki da kuma halayya na mutum. AT: "yadda ka ke a ciki" )
"kamun kai da halin zaman lafiya." A nan kalmar nan "natsatse" na nufin "zaman lafiya" ko "natsuwa." Kalmar nan "ruhu" na nufin halin mutum ko hali.
Bitrus ya yi maganar ra'ayin Allah game da mutum kamar mutumin na tsaye a gabansa. AT: "Wanda Allah ya duba cewa yana da daraja"
cewa shi ubangijinta, wato, maigidanta
Bitrus ya ce mata masubi waɗanda sun yi kamar yadda Saratu ta yi ana iya ce da su kamar su ainihin 'ya'yan ta ne.
Wannan na nufin yadda Saratu da waɗansu matan auren ma da suke tsoron Allah suka yi biyayya ga mazajensu cikin [1 Bitrus 3:5-6].
Bitrus ya yi magana game da mataye kamar su akwati ne, kamar yadda maza wani lokaci a kan yi magana a kansu haka. Ana iya juya kalman nan "fahimta" cikin aikatau. AT: "matan aure, tare da fahimtar cewa mace raunanar abokiyar tarayya ce"
ku na iya juya wannan ta wurin yin amfani da fi'ilin magana. AT: "girmama su don ta wurin alheri za su karbi rai madawami wanda Allah ke bayarwa"
An cika maganar "rai madawami" kamar wani abu ne da mutane ke gada.
A nan "wannan" na nufin yadda mazajen aure za su bi da matayen su. AT: "Ku yi rayuwa da matayen ku a wannan hanya"
A "hana" ita ce sa wani abu kada ya faru. AT: "don kada wani abu ya hana addu'o'inku ga karɓuwa" ko "don kada wani abu ya hana ku addu'a kamar yadda ya kama"
"ku zama masu ra'ayi ɗaya ku kuma" ko "zama masu hali iri ɗaya ku kuma"
zama masu hankali da tausayi ga waɗansu
Bitrus ya yi magana a kan daukan mataki game da halin wani mutum kamar biyan bashin waɗannan halayyan. AT: "Kada ku yi mugunta ga wani wanda ya yi muku mugunta ko kuwa zagi ga wanda ya zage ku"
Kuna iya bayyanawa a fili wanda da za a sa masa albarka. AT: "ku cigaba da sa wa waɗanda suka yi muku mugunta ko sun zage ku, albarka"
AT: "sabili da wannan ne Allah ya kiraye ku"
Bitrus ya yi maganar samun albarkan Allah kamar karɓar gado ce. AT: "don ku karɓi albarkar Allah a matsayin dauwamammen mallaka"
Waɗannan maganganu biyun na nufin abu ɗaya ne kuma na nanata sha'awar samun rayuwa mai kyau.
A nan an yi maganar samun abubuwa masu kyau kamar ganin abubuwa masu kyau. Kalmar nan "kwanaki" na nufin dukan rayuwar mutum. AT: "samun abubuwa masu kyau cikin rayuwa"
Kalmomin nan "harshe" da "leɓe" na nufin mutumin da ke magana. Waɗannan na nufin abu ɗaya na kuma nanata dokan cewa kada ka yi karya. AT: "daina faɗin mugayen abubuwa da kuma abubuwa yaudara"
A nan "juyo" na nufin a bar yin wani abu. AT: "ya bar aikata abu mara kyau"
Kalman nan "idanu" na nufin iyawar Ubangiji na sanin abubuwa. An yi maganar cewa Ubangiji ya yarda da adalai kamar yana ganin su. AT: "Ubangiji na ganin adalan" ko "Ubangiji ya yarda da adalai"
Kalman nan "kunnuwa" na nufin cewa Ubangiji ya na sane da abin da mutane ke faɗi. Cewar Allah na jin maganar roƙe-roƙensu na nufin cewa yana kuwa amsa su. AT: "yana jin roƙe-roƙensu" ko "yana amsa roƙe-roƙensu"
Kalmar nan "fuska" na nufin nufin Ubangiji ya yi gaba da maƙiyansa. An yi maganar gaba da wani kamar a ce an sa fuskar wani gaba da mutumin. AT: "Ubangiji na gaba"
Bitrus ya yi wannan tambaya don ya nanata cewa ba mai yiwuwa bane wani ya cuce su in sun yi abubuwan da ke nagari. AT: "Babu wani da zai cuce ku in kun yi abin da ke nagari."
Ku na iya juya wanna da fi'ilin magana. AT: "shan wuya saboda kun yi abin da ke daidai"
AT: "Allah zai albarkace ku"
Waɗannan maganganun na da ma'ana kusan iri ɗaya, na kuma nanata cewa kada masubi su ji tsoron waɗanda ke tsananta masu. AT: "Kada ku ji tsoron abin da mutane za su yi muku:
A nan kalman nan "su" na nufin duk wanda mai yiwuwa ke ƙoƙarin cutan waɗanda Bitrus ke rubuta masu.
"Maimakon zama cikin damuwa, keɓe"
Kalmomin nan "keɓe Ubangiji Almasihu ... mai tsarki ne" na nufin yarda da tsarkin Almasihu. A nan "zuciya" na nufin "cikin mutum." AT: "Yarda a tsakanin ku cewa Ubangiji Almasihu mai tsarki ne" ko "a tsakanin ku, ku girmama Ubangiji Almasihu don shi mai tsarki ne"
Kalmar nan "mu" ya shafi mutanen da Bitrus ke rubuta musu. (Dubi:"
Ya na iya yiwuwa Bitrus na nufin cewa Almasihu ya mutu don ya haɗa dangantaka tsakanin mu da Allah
A nan "jiki" na nufin jikin Almasihu; bisa ga jiki, an kashe Almasihu. AT: "Mutane sun kashe Almasihu cikin jiki"
AT: "ruhun ya rayar da shi"
Ma'anoni masu yiwuwa 1) ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki 2) kasancewa cikin ruhu.
Ma'anoni masu yiwuwa 1) "Ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki, ya tafi" ko 2) "cikin ruhu ya tafi."
Ma'anoni masu yiwuwa na kalmar nan "ruhohi" 1) "mugayen ruhohi" ko 2) "ruhohin mattattun mutane."
Kalman nan "hakkuri" na nufin Allah kansa. Bitrus ya rubuta game da hakkurin Allah sai ka ce mutum ne. AT: "sa'ad da Allah yana jira cikin haƙuri"
AT: "a lokacin Nuhu, sa'ad da yake sassaƙar jirgin ruwa"
A nan kalmar nan "rayuka" na nufin mutane. AT: "mutane takwas"
Bitrus ya ce baftisma ta yi daidai da hanyar da Allah ya ceci Nuhu da iyalinsa cikin jirgin daga ruwan tsufana.
Baftisma hanya ce da Allah ke ceton mutane. AT: "ta wurin baftismar da Allah ya cece ku yanzu"
Ma'anoni masu yiwuwa 1) "roƙon mutum ga Allah ya bashi lamiri mai kyau" ko 2) "alkawarin mutum ga Allah wadda aka yi da lamiri mai kyau, wato, da gaske."
"saboda tashin Yesu Almasihu daga mattattu." Wannan maganar ta kammala bayanin cewa "Wannan alama ce ta baftismar da ta cece ku yanzu."
Zama a "hanun daman Allah" alama ce da ke nufin cewa Allah ya ba wa Yesu babbar daraja da iko bisa kowa. AT: "Almasihu na gefen Allah cikin wurin ɗaukaka da iko"
"yi wa Yesu biyayya"
Ya kamata mata suyi biyayya don a ci nasara da waɗannan maza da suke da rashin biyayya.
Ya kamata mataye su ci nasara da mutum na cikin zuciya, ba na kwalliyar waje.
Bitrus ya ambaci Saratu kamar misalin.
Maza sun zauna da matayensu bisa sani domin a ji addu'oinsu.
Domin an kira su duka su yi haka, don su iya gaji albarka.
Domin idanun Ubangiji suna ganin adalai.
Waɗanda suka sha wuya saboda adalci, aka sa masu albarka.
Za su amsa kullum da tawali'u da kuma bangirma
An ce masu su ƙebe Ubangiji Almasihu da daraja a zuciyarsu.
Almasihu ya sha wahala domin domin ya kawo Bitrus da masu bi ga Allah.
Ruhohin da a yanzu suke cikin kurkuku sun yi rashin biyayya ne sa'adda hakurin Allah yake jira a lokacin Nuhu.
Yana nuna baftismar da take ceton mai bi yanzu.
Ɗole ne su yi masa biyayya.
1 Saboda haka, tunda yake Almasihu ya sha wuya a jiki, muma mu sha damara da wannan ra'ayi. Duk wanda ya sha wuya a jiki ya daina aikata zunubi. 2 Wannan mutum kuma baya kara zaman biye wa muguwar sha'awar mutumtaka, amma sai dai nufin Allah dukkan sauran kwanakinsa a duniya. 3 Gama lokaci ya wuce da zamu yi abin da al'ummai suke son yi, wato fajirci, mugayen sha'awace-sha'awace, da buguwa da shashanci da shaye-shaye da bautar gumaku da abubuwan kyama. 4 Suna tunanin bakon abu ku ke yi da ba kwa hada kai tare da su yanzu a yin wadannan abubuwa, sai suna zarginku. 5 Za su bada lissafi ga wanda yake a shirye ya shari'anta masu rai da matattu. 6 Shi yasa aka yi wa matattu wa'azin bishara, cewa ko da shike anyi masu shari'a cikin jikunan mutane, su rayu bisa ga Allah a ruhu. 7 Karshen dukkan abubuwa yana gabatowa. Saboda haka, ku zama natsatsu, ku natsu cikin tunaninku domin yin addu'oi. 8 Gaba da kome, ku himmatu wajen kaunar juna, domin kauna bata neman tona zunuban wadansu. 9 Ku yi wa juna bakunta da abubuwa nagari ba tare da gunaguni ba. 10 Yadda kowanne dayanku ya sami baiwa, kuyi amfani da su domin ku kyautata wa juna, kamar masu rikon amanar bayebaye na Allah, wanda ya ba mu hannu sake. 11 Idan wani yana yin wa'azi, ya zamana fadar Allah ya ke fadi, idan wani yana hidima, ya yi da karfin da Allah ya ba shi, domin cikin dukkan abubuwa a daukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Daukaka da iko nasa ne har abada abadin. Amin. 12 Ya kaunatattu, kada ku zaci cewa matsananciyar wahalar da ta zo ta gwada ku bakon abu ne, ko kuma wani bakon abu ne yake faruwa a gareku. 13 Amma muddin kuna tarayya da Almasihu cikin wahalarsa, ku yi murna, domin kuyi farin ciki da murna sa'adda za a bayyana daukakarsa. 14 Idan ana zargin ku sabili da sunan Almasihu, ku masu albarka ne, domin Ruhun daukaka da Ruhun Allah ya tabbata a kanku. 15 Amma kada kowannen ku ya sha wahala sabo da horon shi mai kisan kai ne, ko barawo, ko mamugunci, ko mai shisshigi. 16 Amma in wani yana shan wahala sabili da shi na Almasihu ne, kada ya ji kunya, amma ya daukaka Allah a wannan sunan. 17 Domin lokaci ya yi da shari'a za ta fara daga gidan iyalin Allah. Idan kuwa za a fara da mu, menene karshen wadanda suka ki biyayya da bisharar Allah? 18 Idan mutum, "mai adalci ya tsira da kyar, to, me zai faru da marar bin Allah da mai zunubi kuma?" 19 Sabo da haka bari wadanda suke shan wuya bisa ga nufin Allah, su mika rayukansu ga amintaccen Mahalicci suna kuma yin ayyuka nagari.
Bitrus ya cigaba da koyar da masubi game da rayuwar masubi. Ya fara da bayar da karshen maganar sa game da wahalar Almasihu a suran da ke kafin wannan.
"cikin jikinsa"
Maganar nan "ku yi ɗamara" na sa masu karatu su yi tunanin soja wanda ke shirya makamansa don yaƙi. Ya kuma bada hoton "ra'ayi" kamar makamai ko kuma kamar wani makami. A nan wannan na nufin cewa masubi su ɗau kudurin shan wuya cikin zuciyar su kamar yadda Yesu ya yi. AT: "ku shirya kanku da irin tunani da Alamasihu ke da shi"
"ya bar yin zunubi kenan"
abubuwan da mutane masu zunubi ke sha'awan ta
Waɗannan kalmomin na nufin taruwan mutane don a sha barasa fiye da haka kuma sai su yi halin ban kyama.
Wannan misalin masu halin hauka da matuƙar zunubi ne; an yi maganar su sai kace wata ambaliyan ce da ke shafe mutane.
yi kowanne abu da za su iya yi don su biya bukatan sha'awace-sha'awacen jikunan su
Ma'anoni masu yiwuwa 1) "Allah, wanda ke shirye ya shar'anta" ko 2) "Almasihu, wanda ke shirye ya sharanta"
Wannan na nufin dukan mutane, ko suna raye har wa yau ko kuwa sun mutu. AT: "kowane mutum"
Ma'anoni masu yiwuwa 1) "har ma an yi wa mutanen da suka mutu wa'azin bishara" ko 2) "har ma an yi wa waɗanda a dă suna raye amma a yanzu mattattu ne"
Ma'anoni masu yiwuwa 1) Almasihu ya yi wa'azi. AT: "Almasihu ya yi wa'azin bisharar" ko 2) mutane sun yi wa'azi. AT: "mutane sun yi wa'azin bisharar"
Ma'anoni masu yiwuwa 1) Allah ya shar'anta su a wannan rayuwa ta duniya. AT: "Allah ya shar'anta su cikin jikunan su a matsayin 'yan adam" ko 2) mutane sun shar'anta su bisa ga ma'aunin 'yan adam. AT: "mutane sun shar'anta su cikin jikunan su a matsayin 'yan adam"
Wannan batun mutuwa ne a matsayin sifar shari'a na ƙarshe.
Ma'anoni masu yiwuwa 1) "rayuwar ruhaniya kamar yadda Allah ke rayuwa, domin Ruhu Mai Tsarki zai iza su su yi haka" ko 2) rayu bisa ga ma'aunin Allah ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki"
Wannan na nufin ƙarshen duniya loƙacin zuwan Almasihu ta biyu.
An yi magana game da ƙarshen da zai zo ba jimawa sai kace ya na zuwa kurkusa daga nesa. AT: "zai faru ba da jimawa ba"
Waɗannan maganganu biyun na nufin abu ɗaya ne. Bitrus ya yi amfani da su don ya nanata bukatar yin tunani game da rayuwa da shike ƙarsehn duniya ta kusa.
A nan kalman nan "natsu" na nufin ba shakka cikin hankali da kuma zaman shiri. Dubi yadda ku ka jiya wannan cikin [1 Bitrus 1:13]. AT: "ku sarrafa tunanin ku" ko " ku yi hankali da abin da kuke tunaninsu"
"Mafi muhimmanci duka"
Bitrus ya bayyana "ƙauna" sai ka ce wai mutum ne wanda ke sa murfi kan laifofin wasu. Ma'anoni masu yiwuwa 1) "gama mutumin da ke ƙauna kuwa ba zai taɓa yi ƙoƙarin neman sanin ko wani ya yi zunubi ba" ko 2) "gama mutumin da ke ƙauna zai yafe laifofin sauran mutane, ko su na da yawa"
Ku yi wa juna kirki ku kuma marabci baƙi da matafiye
Wannan na nufin iyawa ta ruhu na musamman wanda Allah ya ba wa masubi. AT: "Domin kowane ɗayanku ya karbi iyawa ta ruhu na musamman a matsayin kyauta daga wurin Allah"
AT: "don ta kowace hanya za ku daukaka Allah"
yabo, girmamawa
kamar yadda wuta ke fid da ainihin kyaun zinariya, hakanan gwaje gwage ke fid da ainihin kyaun bangaskiyar mutumin.
Wannan maganganun na nufin abu ɗaya ne kuma na nanata ƙarfin farin cikin. AT: "ku yi murna sosai" ko "ku yi farin ciki ainun"
"sa'ad da Allah ya bayyana daukakar Almasihu"
A nan kalman nan "suna" na nufin Almasihu kansa. AT: "in mutane sun zarge ku don kun gaskata da Almasihu"
Dukan waɗannan na nufin Ruhu Mai Tsarki. AT: "Ruhun ɗaukaka wanda shine Ruhun Allah" ko "Ruhun ɗaukaka na Allah"
na tare da ku
Wannan na nufin mutumin da ke sa kansa cikin ayyukan mutane wanda ba shi da izinin yin haka.
"saboda ya na ɗauke da sunan nan maibi" ko "saboda mutane sun gane cewa shi maibi ne." Kalmomin nan "wannan suna" na nufin kalman nan "maibi."
Wannan na nufin masubi wadda Bitrus ya yi magana game da su cewa su iyalin Allah ne.
Bitrus ya yi amfani da wannan tambaya don ya nanata cewa shari'a Allah zai fi tsanani ga mutane da suka ƙi bishara na masubi. AT: "Idan kuwa an fara da mu, lailai abin da zai zama ga waɗanda sun yi rashin biyayya ga bisharar Allah zai zama da muni."
"me zai faru da waɗanda"
"waɗanda ba su gaskata da bisharar Allah ba." A nan kalman nan "biyayya" na nufin gaskatawa.
Bitrus ya yi amfani da wannan tambaya don ya nanata cewa masu zunubi za su sha wahala fiye da masubi. AT: "mutum mai adalci ... abin da zai haifar wa mara bin Allah da masu zunubi zai fi muni."
me zai faru da marasa bin Allah da masu zunubi"
A nan kalman nan "tsira" na nufin ceto na ƙarshe a sa'ad da Alamasihu ya dawo. AT: "In har mutum mai adalci ya sha wuya kafin Allah ya cece shi"
Kalmomin nan "mara bin Allah" da "mai zunubi na nufin abu ɗaya, su na kuma nanata muguntar waɗannan mutanen. AT: marasa bin Allah, masu zunubi"
A nan kalman nan "rayuka" na nufin mutum gabadayansa. AT: "miƙa kansu" ko "miƙa ransu"
Ana iya juya "yin ayuka nagari" cikin fi'ilin magana. AT: "sa'and da suke nagargarun ayuka" ko "sa'and da suke rayuwa da ta cancanta"
Ya umurce su su sha damara da irin niya da Almasihu yake da shi a loƙacin da ya sha wahala a cikin jiki.
Sun yi mugayen maganganu game da bakin, zababbun, don ba su yi fajirci, mugayen sha'awace-sha'awace, da buguwa da shashanci da shaye-shaye da bautar gumaku da abubuwan kyama kamar al'umman ba.
Allah ya na a shirye ya sharanta masu rai da matattu.
Ya kamata su yi waɗannan abubuwa domin karshen dukka komai na zuwa, kuma don dalilin addu'oinsu.
Za su yi amfani da baiwansu domin Allah ya samu ɗaukaka cikin dukkan abubuwa ta wurin Yesu Almasihu.
Domin su masu albarka ne idan an zarge su.
Ba kamata masubi su sha wahala kaman masu kisan kai, ko barawo, ko masu mugunci, ko masu shisshigi.
Domin ko mutum mai adalci na tsira da kyar.
Za su ɗanka rayukansu ga amintacceyar mai Halitta sa'adda su na yin kyauwawan ayuka.
1 Ina yiwa dattawan da ke cikinku gargadi, ni da nike dan'uwanku dattijo, mashaidin shan wuyar Almasihu, ni kuma mai samun rabo ne daga cikin daukakar daza a bayyana. 2 Saboda haka na gargade ku dattawa, kuyi kiwon garken Allah dake tare da ku. Ku kula da su, ba a kan dole ba, amma domin kuna son yin haka, bisa ga yin Allah. Ku kula da su, ba don cin ribar banza ba amma sabo da yardar rai. 3 Kada ku zama kamar masu iko akan mutanen dake hannunku, amma ku zama abin koyi ga garken. 4 Sa'adda za a bayyana Sarkin Makiyaya zaku karbi rawanin da darajarsa bata dushewa. 5 Hakannan, ku kuma samari kuyi biyayya ga dattawa. Dukanku kuyi damara da tawali'u, kuna bauta wa juna, domin Allah ya na tsayayya da mai girman kai, amma yana yiwa masu tawali'u alheri. 6 Saboda haka ku kaskantar da kanku karkashin hannuwan Allah mai iko duka domin ya daukaka ku a madaidecin lokaci. 7 Ku jibga masa duk taraddadin zuciyarku, domin yana kula da ku. 8 Ku natsu, ku zauna a fadake. Magabcinku, ibilis, kamar zaki mai ruri yana zazzagawa, yana neman wanda zai cinye. 9 Ku yi tsayayyiyar gaba da shi. Ku yi karfi cikin bangaskiyarku. Ku sani fa abokan tarayyarku da suke cikin duniya suna jimrewa da shan wuyan nan irin taku. 10 Bayan shan wuyarku na dan lokaci kadan, Allah mai alheri mara iyaka, wanda ya kiraye ku zuwa ga madawwamiyar daukakarsa cikin Almasihu, zai kammalaku, ya kafa ku, ya kuma karfafa ku. 11 Mulki ya tabbata a gare shi har abada abadin. Amin. 12 Na amince da Sila amintaccen dan'uwa ne, kuma na rubuto maku a takaice ta hannunsa. Ina yi maku gargadi ina kuma shaida maku cewa abin da na rubuto alherin Allah ne na hakika. Ku kafu a cikinsa. 13 Ita matar da ta ke a Babila zababbiya tare da ku, ta na gaisheku, da Markus, dana, yana gaisheku. 14 Ku gai da juna da sumbar kauna. Salama ta tabbata a gare ku dukanku da ke cikin Almasihu.
Bitrus ya yi magana game da mazajen da ke dattawa.
Wannan na nuna dawowar Almasihu ta. AT: "ɗaukakar Almasihu da Allah zai bayyana"
Bitrus ya yi magana game da masubi kamar garken tumaki da kuma dattawa kamar makiyaya da suke lura da su.
Ma'anoni masu yiwuwa 1) "mai kula da" wani ma'aikaci ne wadda ke kula da mutanen Allah, ko 2) marubucin na bayyana abin da makiyayi ke yi ("zama makiyayin tumakin Allah"), "kulawa da su."
Dattawa su yi shugabanci ta wurin zama abin koyi ga mutane kada kuma su zama kamar ubangida mara tausayi ga bayinsa.
Kuna iya juya wannan cikin fi'ilin magana. AT: "waɗanda Allah ya sa ƙarƙashin kulawar ku"
Bitrus ya yi magana game da Yesu sai ka ce shi makiyayi ne mai iko kan duk sauran makiyayan. AT: "sa'ad da Yesu, sarkin makiyayin ya bayyana" ko "sa'ad da Allah ya bayyana Yesu, Sarkin makiyayin"
A nan kalmar nan "rawani" na a madadin sakamako da wani ya karɓa a matsayin alamar nasara. Kalmomin nan "bata dusashewa" na nufin cewa madawwamiya ce. AT: "kyauta mai daraja wadda zai dawama"
daraja
Wannan na kai mu baya ga yadda dattawan sun mika kan su ga Shugaban Makiyaya cikin 1 Bitrus 5: 1-4.
Wannan na nufin dukan masubi, ba masu ƙuruciya kawai ba.
Bitrus ya yi maganar samun ingantacciyar halin tawali'u a matsayin sa tufa. AT: "zaman tawali'u ga juna" ko "zama da tawali'u"
A nan kalmar nan "hannu" na nufin ikon Allah don ceton masu tawali'u da kuma hukunta masu girman kai. AT: "ƙarƙashin girman ikon Allah" ko "gaban Allah tare da sanin cewa yana da iko mai girma"
Bitrus ya yi magana game da taraddadi sai ka ce wata kaya mai nauyi ce da mutum ya sa kan Allah a maimakon ɗauka da kansa. AT: "Dogara a gare shi da dukan abubuwan da ke damun ku" ko "ku bar shi ya kula da dukan abubuwan da suke damun ku"
A nan kalmar nan "natsu" na nufin hankali mai tsabta da kuma shiri. AT: "Kula da tunaninku" ko "yi kula da abinda ku ke tunani"
Bitrus ya kamanta ibili da zaki mai ruri. Daidai kamar yadda zaki mai jin yunwa ke cinye abin da ya yi farautar sa, hakanan ibili na neman ya rushe bangaskiyar masubi.
"yawo" ko "yawo na kuma farauta"
tsayayya na nufin yaƙi. AT: "yaƙi da shi"
Bitrus ya yi magana game da 'yan'uwa masubi a matsayin 'yan'uwa ɗaya. AT: "'yan'uwan ku masubi"
"cikin wurare dabam-daban a ko'ina a duniya"
"na guntun lokaci"
a nan kalmar nan "alheri" mai yiwuwa na nufin abubuwan da Allah ya bayar ko kuwa halin Allah. Ma'anoni masu yiwuwa 1) "Allahn da a kulliyomi yana ba mu abin da muke bukata" ko 2) "Allah mai alheri a koyaushe."
"wanda ya zaɓe ku ku sami rabo zuwa ga madawamiyar ɗaukakarsa cikin sama saboda an haɗa ku da Almasihu"
"sa ku zama kammalallu" ko "mayar da ku" ko "sa ku ku zama lafiyayyu"
Waɗannan maganganu biyu suna da ma'an kusan iri ɗaya, wato, Allah zai sa masubi su dogara a gare shi su kuma yi masa biyayya komin wahalar da suke sha.
Sila ne ya rubuto abin da Bitrus ya faɗa masa ya rubuta cikin wasiƙar.
"Na rubuta game da gaskiyar alherin Allah." A nan kalmar nan "alheri" na nufin saƙon bishara wadda ta faɗi irin abubuwan da Allah ya yi wa masubi.
Kalmar nan "ta" na nufin "gaskiyar alherin Allah." An yi maganar miƙa kai ga wannan alherin kamar tsayawa a wuri ɗaya ba matsawa. AT: "Tsaya da ƙarfi da kuma mika kai cikin ta"
A nan "ita matar" mai yiwuwa na nufin kungiyar masubi da ke zama a "Babila." Ma'anoni masu yiwuwa na "Babila" 1) sananniyar alama ce ta birnin Roma, 2) sananniyar alama ce ta duk inda masubi ke shan wahala, ko 3) na nufin birnin Babila. mai yiwuwa ta na nufin birnin Roma.
AT: "wanda Allah ya zaɓa kamar yadda ya zaɓe ku"
Bitrus ya yi magana game da Markus sai ka ce ɗansa ne a ruhaniya. AT: "ɗana cikin ruhaniya" ko "wadda ke kamar ɗa a gare ni"
"sumbar ƙauna" ko "sumbar nuna ƙauna ga juna"
Bitrus ɗan'uwa dattijo, mashaidin shan wuyar Almasihu, kuma mai samun rabo ne daga cikin ɗaukakar daza a bayyana.
Ya gargaɗe su su kiyaye garken Allah su kuma lura da su.
Za su yi biyayya ga dattawa.
Don Allah na ba da alheri ga masu tawali'u, kuma don Allah ya ɗaukake su a madaidecin lokaci.
An umurce su su natsu, su zauna a faɗake, su yi tsayayyiyar gaba da shi, su kuma yi karfi cikin bangaskiyarsu.
Allah zai kammalasu, ya kafa su, ya kuma karfafa su.
Ya ce abin da ya rubuta na gaskiyar alherin Allah.
Bitrus ya amince da Sila amintaccen ɗan'uwa.
Ita wanda take a Babila zababbiya tare da ku, ta na gaisheku, ɗan Markus, ya gaishesu; za su gai da juna da sumbar ƙauna.
1 Siman Bitrus, bawa da manzon Almasihu Yesu, zuwa ga wadanda suka karbi bangaskiya mai daraja kamar yadda muka karba, bangaskiya cikin adalcin Allahnmu da Yesu Almasihu. 2 Bari alheri ya kasance tare da ku; bari salama ta karu ta wurin sanin Allah da na Yesu Ubangijinmu. 3 Dukkan abubuwan ikon Allah na rayuwa da Allahntaka an bamu su ta wurin sanin Allah, wanda ya kira mu ta wurin daukakarsa da nagarta. 4 Ta wurin wanan, ya bamu babban alkawari mai daraja. Yayi wanan ne saboda ku zama masu rabo cikin Allahntaka, yayin da ku ka kubuta daga lalacewa da ke cikin duniya saboda mugayen sha'awace sha, awace. 5 Saboda wanan dalilin kuyi iyakacin kokarinku ku kara nagarta ta wurin bangaskiyarku, kuma ta wurin adalci, sani. 6 Ta wurin sani ku kara da kamun kai, kuma ta wurin kamun kanku, ku kara da jimrewa, ta wurin jimrewarku, ku kara da bin Allah. 7 Ta wurin bin Allah, ku kara da kauna irin ta 'yan'uwa, ta wurin kauna irin ta 'yan'uwa, ku kara kauna. 8 Idan wadannan abubuwan suna cikinku, kuma suka yi girma a cikinku, baza a sami bakarare ko rashin 'ya'ya cikin sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu ba. 9 Amma duk wanda ya rasa wadannan abubuwan yana kallon abin da ke kusa ne kawai; ya makance. Ya manta da cewa an wake shi daga tsofaffin zunubansa. 10 Saboda haka, 'yan'uwa, kuyi iyakacin kokari ku tabbatar da kiranku da zabenku. Idan kun yi wadannan abubuwan, baza ku yi tuntube ba. 11 Ta haka zaku sami shiga cikin mulki na har'abada na Ubangijinmu da Maicetonmu Yesu Almasihu. 12 Saboda haka a shirye nake kulayomi in tunashe ku game da wadannan abubuwan, ko da yake kun san su, kuma kun yi karfi cikin gaskiya yanzu. 13 Ina tunani daidai ne in zuga ku da tuni game da wadannan abubuwan, tun ina cikin wannan jiki. 14 Domin na sani jim kadan zan bar wannan jiki, kamar yadda Yesu Almasihu ya nuna mani. 15 Zan yi iyakancin kokarina kulayomi domin ku rika tunawa da abubuwan, bayan kaurata. 16 Domin bamu bi labaru da aka kago na nuna wayo cikinsu ba, da muka fada maku game da iko da bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Almasihu, amma mu shaidu ne na ikonsa. 17 Gama ya karbi daukaka da daraja daga wurin Allah Uba lokacin da murya ta zo daga ikon mai daukaka cewa, "Wannan shine dana, kaunataccena, wanda nake jin dadinsa kwarai." 18 Mun ji muryar nan da ta zo daga sama, lokacin da mu ke tare da shi a dutse mai tsarki. 19 Muna da wannan kalmar annabci wanda akwai tabbaci sosai, kun yi daidai idan kun mayar da hankali a kansu. Yana nan kamar fitillar da take walkiya a wuri mai duhu kafin asubahi ya zo, kuma tauraron asubahi ya tashi cikin zukatanku. 20 Ku san da wannan tun da farko, cewa babu annabci da ke bisa ga fasarar mutum. 21 Domin babu annabcin da ya taba zuwa ta wurin nufin mutum. Maimakon haka, Ruhu Mai Tsarki ne ke iza su, su fadi maganar Allah.
Bitrus ya bayyana kansa a matsayin marubucin, sa'an nan ya gaishe da masubi da ya ke rubuta masu.
Bitrus yana maganan zama bawan Yesu Almasihu. An kuma ba shi matsayi da ikon zama manzon Almasihu.
Cewar mutanen nan sun karɓi bangaskiya na nufin Allah ya ba su irin bangaskiyarmu. AT: "ga waɗanda Allah ya ba su bangaskiya iri ɗaya da tamu mai daraja"
"zuwa ga ku da ku ka karɓi." Bitrus ya na magana da dukkan masubi waɗanda mai yiwuwa za su karanta wannnan wasiƙar.
A nan kalman nan "mu" na nufin Bitrus ne da sauran manzanni, amma banda waɗanda ya ke rubuta masu wasiƙar. AT: "mu manzanni mun karɓa"
Allah ne wanda zai ba wa masubi alheri da salama. AT: "Bari Allah ya ƙara alheri da salamar ku"
Bitrus ya yi maganar salama kamar wani abu ne da zai iya karuwa a girma ko kuwa ƙirge.
Kuna iya juya "sani" ta wurin yin amfani da jumla ta aikatau. AT: "Ta wurin sanin Allah da kuke da shi da kuma Yesu Ubangijinmu"
A nan "bin Allah" na bayanin kalmar nan "rayuwa". AT: "don rayuwar bin Allah"
A nan kalmar nan "mu" na nufin Bitrus da masu sauraron sa.
A nan "waɗannan" na nufin "ɗaukakarsa da kuma kirkin sa."
"ku sami rabo"
yadda Allah yake
Bitrus ya yi magana game da rashin shan wahalar mutane saboda lalacewar da ake samu ta wurin mugayen sha'awace-sha'awacen sai ka ce sun tsere ne daga lalacewa. Kalman nan "lalacewa" ana iya juya ta cikin kalmar aikatau. AT: "kuma don mugayen sha'awace-sha'awace da ke cikin wannan duniya ba zata ƙara lalata ku kuma ba"
Wannan na nufin abinda Bitrus ya faɗa a ayoyin da ke baya. AT: "saboda abin da Allah ya yi"
Wannan na nufin ƙaunar abokai ko kuwa ƙauna tsakanin 'yan iyali, yana kuma iya nufin ƙaunar cikin iyalin ruhu.
Wannan na nufin bangaskiya, kirki, sanin ya kamata, kamunkai, jimiri, bin Allah, son 'yan'uwa, da ƙauna, da Bitrus ya ambato cikin ayoyin da ke a baya.
Bitrus ya yi magana game da mutumin da ba shi da waɗannan ingancin sai ka ce wata gonar da ba ta bada amfani. Ana iya bayanin wannan a cikin kalmomi masu nuna iganci. AT: "za ku bada 'ya'ya" ko "za ku zama da amfani"
Waɗannan kalmomin na nufin abu ɗaya, kuma na nanata cewa wannan mutum ba zai yi amfani ba ko kuwa ya sami wata amfani daga sanin Almasihu. AT: "rashin bada 'ya'ya"
Ana iya juya "sani" ta wurin yin amfani da jumla aikatau. AT: "Ta wurin sanin Allah da kuke da shi da kuma Yesu Ubangijinmu"
duk mutumin da ya rasa waɗannan abubuwa
Bitrus ya yi magana game da mutumin da ba shi da waɗannan ingacin sai ka ce mutum ne da ke ganin abubuwan da ke kusa ne kaɗai ko kuwa mutumin ne da ya makance domin bai fahimci darajar su ba. AT: "shi kamar mutum ne da ba ya iya hangen nesa, wanda ba ya iya ganin muhimmancin su."
Ku na iya amfani da aikatau don juya wannan. AT: "cewa Allah ya tsarkake shi daga zunubansa na dã"
Kalmomin nan "ƙira" da "zaɓe" su na da ma'ana kusan iri ɗaya kuma su na nufin cewa Allah ya zaɓe su don su zama nasa. AT: "ku tabbatar cewa lallai Allahne ya zaɓe ku don ku zama nasa"
A nan kalman nan "tuntuɓe" na nufin 1) aikata zunubi. AT: " ba za ku aikata halin zunubi ba" ko kuwa 2) zama da rashin amininci ga Almasihu ba. AT: "ba za ku zama da rashin aminci ga Almasihu ba"
AT: "Allah zai yi muku cikakkiyar tanadi a mashigar madawwamin mulkinsa"
damar shiga
Bitrus ya yi wa masubi magana game da hakkinsa ta cigaba da tunasashe su da kuma koyas da su.
A nan kalmomin nan "waɗannan abubuwa" na nufin dukkan abubuwan da Bitrus ya faɗa a ayoyin da ke a baya.
"da gaske ku ka gaskata gaskiyar waɗannan abubuwa"
A nan kalmar nan "zuga" na nufin a tashi wani daga barci. Bitrus yana magana game da sa masu karatun sa da su yi tunani game da waɗannan abubuwa sai ka ce ya na tashin su ne daga barci. AT: "a tunashe ku game da waɗannan abubuwa don ku yi tunani game da su"
Bitrus yana magana game da jikinsa sai ka ce wata tanti da yana sa wa kuma zai cire ta. Zama cikin jikinsa na nufin zaman da rai, cire ta kuma na nufin mutuwa.
Bitrus yana magana game da mutuwarsa sai ka ce zai bar wani wuri zuwa wani wuri. AT: "bayan mutuwa ta" ko "bayan na mutu"
A nan kalmar nan "mu" na nufin Bitrus da sauran manzannin, amma banda masu karantun. AT: "don mu manzannin ba mu bi labarin da aka ƙirƙiro ba"
Waɗannan maganganu biyun mai yiwuwa na nufin abu ɗaya ne kuma ana iya juya su kamar magana guda. AT: "ikon zuwan"
Wannan na iya nufin 1) zuwan Ubangijin Yesu na biyu nan gaba ko kuwa 2) farkon zuwan Ubangiji Yesu.
A nan kalman nan "mu" na nufin dukkan masubi.
AT: "sa'ad da ya ji murya na zuwa daga Mabuwãyin Ɗaukaka" ko kuwa "sa'ad da ya ji muryar Mabuwãyin Ɗaukaka ta yi magana da shi" ko kuwa "sa'adda Mabuwãyin Ɗaukaka ya yi magana da shi"
Bitrus yana nufin Allah a cikin ɗaukakarsa. Wannan wata yanayin magana ce da ke ƙoƙarin gujewa amfani da sunan Allah, don girmansa. AT: "Allah, mai madaukakin ɗaukaka, cewa"
Da kalmar nan "Mu," Bitrus yana nufin kansa ne da kuma almajire, wato Yakubu da kuma Yahaya, wanda suka ji muryar Allah. AT: "Mu kanmu mun ji wannan muryar da ta zo daga sama"
"ji muryar shi wanda ya yi magana daga sama"
"mu na tare da Yesu"
Abubuwan da Bitrus da sauran manzannin suka gani, wanda ya bayyana a ayoyin da ke a baya, sun tabbatar da abin da annabawan sun faɗa. AT: "Gama abubuwan da muka gani sun tabbatar da wannan saƙon annabcin"
A nan kalmar nan "mu" na nufin dukkan masubi, duk da Bitrus da masu karatunsa.
Wannan na nufin Tsohon Alkawari. AT: "nassosin da annabawa suka yi magana, ta sa"
Bitrus ya umurci masubi cewa su kasa kunne ga saƙon annabci.
Bitrus yana kwatanta kalmar annabci da fitila da ke bada haske cikin duhu har lokacin da haske za ta zo da safiya. Zuwan safiya na nufin zuwan Almasihu.
Bitrus ya yi magana game Almasihu a matsayin "tauraruwar safiya" wanda ke nuna cewa safiya ta yi kuma ƙarshen duhu ta kusa. Almasihu zai kawo haske ga zukantan masubi, zai kawo ƙarshen shakka da kuma cikakken fahimta game da ko wanene shi. A nan "zukatan" na nufin hankalin mutane. AT: " Almasihu na haskaka hasken sa cikin zukatanku kamar yadda tauraruwar safiya na haskaka duniya"
"Tauraruwar safiya" na nufin tauraro mai kewaye rana, wanda ke fitowa wani lokaci daidai kafin rana na kuma nuna cewa safiya ta kusa.
"Mafi Muhimanci, lallai ne ku fahimci"
Wannan na iya nufin 1) annabawan ba su yi annabcinsu da kansu ba ko kuwa 2) dole mutane su dõgara ga Ruhu Mai Tsarki don su fahimci annabce-annabcen ko kuwa 3) dole mutane su fasara annabce-annabace tare da taimakon jama'a masubi ga baki ɗaya.
Bitrus yana magana game da Ruhu Mai Tsarki na taimakon annabawan da su rubuta abin da Allah ke so su rubuta sai ka ce Ruhu Mai Tsarki yana ɗaukan su daga wani wuri zuwa wani wuri. AT: "mutane sun yi magana daga Allah kamar yadda Ruhu Mai Tsarkin ya shugabace su"
Siman Bitrus, bawa da manzon Almasihu Yesu.
Bitrus ya rubuta wa waɗanda suka karɓi irin bangaskiya mai daraja.
An basu ta wurin sanin Allah.
Ya yi haka domin su zama masu rabo cikin Allahntaka.
A takaice ya kamata su sami ƙauna ta wurin bangaskiyarsu.
Ya manta da wankewarsa sa daga tsofaffin zunubansa.
Baza su yi tuntuɓe ba,ta haka zaku sami shiga cikin mulkin Ubangiji da Maiceto Yesu Almasihu.
Domin Yesu Almasihu ya nu na mashi cewa ya yi kusan cire wannan jiki.
Sun ga cewa ya karɓi ɗaukaka da daraja daga Allah Uba.
Domin annabcin da an rubuta bai zo daga nufin annabin ba, ko wani annabci daga nufin mutum, amma ta wurin mutane da Ruhu Mai Tsarki ke iza su, wanda sun yi magana daga Allah.
1 Annabawan karya sun zo ga mutane, hakannan kuma malaman karya suma sun zo. A asirce za su zo maku da karkatacciyar koyarwa mai hallakarwa, su kuma yi musun sanin Ubangiji da ya fanshe su. Su na jawowa kansu hallaka da sauri. 2 Da yawa za su bi gurbinsu, kuma ta wurinsu za a sabawa sahihiyar gaskiya. 3 Ta wurin hadama za su ribace ku ta wurin maganganunsu na yaudara. Hallakarsu ba za ta yi jinkiri ba; hukuncinsu na nan tafe. 4 Allah bai kebe mala'ikkun da suka yi zunubi ba. Maimakon haka ya tura su a cikin bakin duhun jahannama daure da sarkoki, har ya zuwa ranar shari'a. 5 Hakan nan kuma bai kebe duniya ta zamanin da ba. Maimakon haka, ya kebe Nuhu, wanda yake wa'azin adalci, tare da mutane bakwai, lokacin da ya kawo ambaliyar ruwan Tsufana a fuskar duniyar marasa bin Allah. 6 Sa'annan Allah ya kone biranen Sadoma da Gomrata da wuta ya maishe su toka, wannan ya zama misalin abin da zai faru da marasa ibada. 7 Amma ga adalinnan Lutu, wanda ya zaku a ransa ta wurin miyagun halayen mutanen, Ubangiji kuwa ya cece shi. 8 Ga wannan mutum mai adalci, wanda yayi zama a cikinsu kowace rana ransa na baci, domin abin da yake gani yake kuma ji. 9 Saboda haka Allah ya san yadda zai ceci masu adalci daga gwaji, da yadda kuma zai kama masu rashin adalci da hukunci a ranar shari'a. 10 Wannan kuwa musamman gaskiya ce ga wadanda suka ci gaba da ayyuka na jiki suka kuma raina masu mulki. Suna da taurin kai da kuma yin ganin dama. Ba sa tsoron sabo ga wadanda aka daukaka. 11 Ko da shike mala'iku suna da karfi da iko fiye da su, amma basu kawo karar batanci a kansu a gaban Ubangiji ba. 12 Amma wadannan dabbobi marassa tunani an yi su ne musamman domin a kama a yanka. Suna sabawa abin da ba su sani ba. Zasu halaka. 13 Za su sami sakamakon mugun aikinsu. Suna tunanin yin nishadi da rana abin annashuwa ne. Su kan su tababbu ne. Suna jin dadin ayyukansu na yaudara yayin da suke liyafa tare da ku. 14 Suna da idanun sha'awace sha'awacen mata mazinata; ba sa koshi da aikata zunubi. Suna rinjayar wandanda ba su da tsayayyan hankali zuwa ga munanan ayyuka, kuma sun kafa zukatansu ga hadama, su 'ya'yan la'ana ne! 15 Sun bar bin hanyar gaskiya. Sun bijire kuma sun bi hanyar Bal'amu dan Be'or wanda yake kaunar ribar rashin adalci. 16 Amma ya karbi tsautawa domin zunubinsa. Jaki ma da baya magana ya tsauta wa haukan annabin da muryar dan adam. 17 Wadannan mutane suna kamar mabulbullai da babu ruwa. suna nan kamar gizagizai da iska ke korawa. Duhu mai tsanani yana jiransu. 18 Su masu babatu ne da girman kai. suna yadaurar mutane ta wurin sha'awowin jiki. Suna yaudarar mutane da suke kokarin su tsere daga wadanda suke rayuwa cikin kuskure. 19 Suna masu alkawarin yanci, amma su da kan su bayi ne ga zunubi. Domin mutum bawa ne ga duk abinda ya rinjaye shi. 20 Duk wanda ya kubuta daga shashanci na duniya ta wurin sanin Ubangiji da mai Ceto Yesu Almasihu, sa'annan ya koma cikin shashaci, yanayinsu na karshe ya zama da muni fiye da na farkon. 21 Da ma zai fi masu kada su san hanyar adalci da su san ta amma sa'annan su juya daga ka'ida mai tsarki wanda aka damka masu. 22 Wannan karin magana ya zama gaskiya a kan su: "Kare ya dawo yana lashe amansa. Aladen da akayi masa wanka ya koma cikin tabo."
Bitrus ya fara yi wa masubi kashedi game da masu koyarwar ƙarya.
Kamar yadda masu koyarwar ƙarya sun zo suna yauɗaran Isra'ila da kalmomin su, haka kuma masu koyarwar ƙarya za su zo suna koyarwar da karya game da Almasihu.
kalmomin nan "karkatacciyar koyarwa" na nufi ra'ayoyin da ke dabam da koyarwar Almasihu da kuma manzannni. Wannan karkatacciyar koyarwar na rushe bangaskiyar wanɗanda suka gaskanta da ita.
Kalman "ubangidan" a nan na nufin mutumin da ke da bayi. Bitrus yana magana game da Yesu a matsayin mamallakin mutane da ya saya, mutuwarsa ita ce farashin.
haramtaccen hali ta jima'i
Maganan nan "hanyar gaskiya" na nufin bangaskiyar masubi a matsayin hanya ta gaskiya zuwa ga Allah. AT: "marasa bi za su yi saɓo ga hanyar gaskiya"
"shawo kan ku ga bada kuɗi ta wurin yi muku karya"
Bitrus yana magana game da "hallaka" da "hukunci" sai ka ce su mutane ne da za su iya yin abu. Maganganun nan biyu a takaice abu ɗaya ne su na nanata yadda masu koyarwar karya za su hallaka jim kaɗan.
Bitrus yana bada misalan mutanen da ke gãbã da Allah da kuma wanda Allah ya hukunta saboda abinda suka yi.
"bai dena hukunci" ko "ya hukunta"
Kalmomin nan "bakin duhu ta jahannama" kalmomi ne a addinin Helenawa dake nufin wurin da aka hukunta mugayen ruhohi da kuma mugayen mutanen da suka mutu. AT: "ya jefa su cikin jahannama"
AT: "inda zai sa su cikin sarƙar baƙin duhu"
Wannan na iya nufin 1) "a sarƙa cikin wurin da ke da matuƙar duhu" ko kuwa 2) "cikin matuƙar duhun da ta sa su cikin kurkuku kamar sarƙoƙi."
Wannan na nufin ranar shari'a a sa'ad da Allah zai shar'anta kowane mutum.
A nan kalman nan "duniya" na nufin mutanen da ke cikin ta. AT: "bai rangwata wa mutane da sun yi rayuwa cikin duniya ta dã ba"
Allah bai halaka Nuhu da mutane bakwai ba a sa'ad da ya halaka sauran mutane wanda sun yi rayuwa a duniya ta dã.
"kona biranen Saduma da Gwamrata da wuta har suka zama toka"
A nan kalman "su" na nufin Saduma da Gwamrata da kuma mutanen da sun yi rayuwa cikin su.
Saduma da Gwamrata sun zama misalai ne da kuma kashedi na abin da zai faru da waɗanda sun yi wa Allah rashin biyayya.
"haramtacciyar halayen mutanen da ke karya shari'ar Allah"
Wannan na nufi Lutu.
A nan "rai" na nufin tunani da kuma shauƙin Lutu. Haramtacciyar halayen 'yan Saduma da Gwamrata ta dame shi kwarai. AT: "ya damu kwarai da gaske"
Kalmar nan "wannan" na nufin cewa Allah ya sa mutane marasa Adalci cikin kurkuku har ya zuwa ranar shari'a bisa ga 2 Peter 2:9.
A nan "sha'awace sha'awace na jiki" na nufin sha'awace-sha'awace ta halin zunubi na mutuntaka. AT: "waɗanda sun cigaba da dulmuya cikin sha'awace-sha'awace ta zunubi"
"sun ƙi biyayya da mulkin Allah." Anan kalmar nan "mulki" mai yiwuwa na nufin ikon Allah.
A nan "mulki" na a madaddin Allah wanda ke da ikon bada umurni da kuma hukunta rashin biyayya.
"aikata kowane abinda suke so su yi"
Wannan na nufin halitattun ruhohi kamar mala'iku ko kuwa aljannu.
"ƙarfi da iko fiye da masu koyarwar ƙarya"
Kalman nan "su" na nufin mala'iku. Ma'anoni masu yiwuwa na kalmar nan "su" na kamar haka 1) masu ɗaukaka ko kuwa 2) masu koyarwar ƙarya.
Ra'ayin cewa mala'iku na iya zargin waɗannan mugayen mutane na kamar za su iya kai masu hari ta wurin amfani da zargi a matsayin makamai.
Daidai kamar yadda dabbobi ba su da tunani, waɗannan mutane ba za a iya muhawara da su ba. AT: "waɗannan masu koyaswar karya suna kamar dabbobin da ba sa tunani wanda aka kama su domin hallaka"
Suna miyagun maganganu game da abin da ba su sani ko fahimta ba.
AT: "Allah zai halaka su"
Bitrus yana magana game da hukuncin da masu koyaswar ƙarya za su samu kamar wata sakamako ne. AT: "Za su karɓi abinda ya cancance su saboda miyagun ayyukansu"
A nan kalmar nan "nishaɗi" na nufin ɗabi'u marasa kyau duk da handama, shaye- shaye da kuma haramtattun ayyuka. Yin waɗannan abubuwan da rana na nuna cewa waɗannan mutane ba sa kunyan wannan hali.
Kalmomin nan "datti" da "lahani" suna da ma'ana kusan iri ɗaya. Bitrus ya yi magana game da malaman karya sai ka ce su datti ne a tufa, wadda ke sa kunya ga waɗanda suka sa ta. AT: "Su kamar datti ne da kuma lahani a kan tufafi, wadda ke sa kunya"
A nan "idanu" na nufin sha'awace-sha'awace kuma "idanu cike" na nufin cewa sun cika son abu. AT: "Koda yaushe su na son aikata zina"
Kodashike sun yi zunubi don su samu gamsuwa cikin sha'awar su, zunubin da suka yi bai taɓa gamshe su ba.
A nan kalman nan "ran" na nufin mutanen. AT: "Sun rinjayi mutanen da ba sa tsayawa a guri ɗaya"
A nan kalmar nan "zukata" na nufin tunani da shauƙin mutumin. Saboda halayen da suka saba yi, sun hori kansu ga yin tunani da kuma yin ayyuka bisa ga haɗama.
"Waɗannan malaman ƙaryan sun bar bin hanyar gaskiya sun kuma bijire ga bin." Malaman karyan sun ki yin biyayya ga Allah domin su guje wa abin da ke daidai.
An yi magana game da halayen da ke girmama Allah sai ka ce wata hanya ce da za a bi.
Za ku iya yin cikakken bayani cewa Allah ne ya tsauta wa Bala'am. AT: "Allah ya tsauta masa"
Jaki, bisa ga halittar sa ba ya magana, ya yi magana da murya kamar ta ɗan adam.
Allah ya yi amfani da jaki don ya hana munanan ayyukan annabi.
Maɓulɓullai da ke da ruwan sha ga mutane masu jin ƙishi, amma "maɓulɓullai da ba su da ruwa" za su sa masu jin ƙishi cikin kunya. Haka nan kuma, malaman ƙarya, kodashike sun yi alkawaran abubuwa dayawa, ba su iya cika abin da su ka alkawarta ba.
Sa'ad da mutane sun ga hadari, suna stammanin cewa ruwa zai sauko. Sa'ad da guguwa mai karfi ta fura hadarin kamin ruwa ta faɗi mutane za su ji ba daɗi a ran su. Haka nan kuwa malaman ƙarya, kodashike sun yi alkawarin abubuwa da yawa, basu iya cika wa ba.
Kalmar nan "su" na nufin malaman ƙarya. AT: "Allah ya shirya masu duhu mai tsanani"
Suna amfani da kalmomi masu burgewa amma marasa ma'ana.
Tawurin halin zunubi su kan sa mutane su yi haramtaccen ayyuka da kuma ayyuka na zunubi.
Bitrus yana magana game da mutane da ke rayuwa ta zunubi sai ka ce su bayin zunubi ne da ke bukatan 'yanci daga zaman talala.
Wannan magana na nufin mutanen da suka zama sabobbin tuba. Jumlar nan "waɗanda ke rayuwa cikin kuskure" na nufin marasabi wanɗanda ke rayuwa cikin zunubi. AT: "mutanen da ke son su yi rayuwar da ke daidai, maimakon yin rayuwa ta zunubi kamar yadda suka saɓa kuma kamar yadda sauran mutane suke yi"
" 'Yanci" a nan na nufin rayuwa daidai yadda mutum ke so. AT: "Sun yi masu alkawarin cewa za su ba su irin rayuwar da suke so, amma su da kansu bayin zunubi ne"
Bitrus yana magana game da mutum a matsayin bawa ne a sa'ad da wani abu ya mulke shi da kuma wannan abin da ke mulki a matsayin ubangijin mutumin. AT: "Gama in wani abu na mulki a bisa mutum, wannan mutum ya zama kamar bawa ne ga wancan abin"
Kalmar nan "lalacewa" na nufin halin zunubi da ke sa wani ya zama mara tsabta. "Duniya" na nufin al'umma. AT: "Ayyukan da ke kazantar da al'umma"
Ku na iya juya "sani" ta wurin yin amfani da fi'ilin magana. Dubi yadda ku ka juya magana makamancin haka cikin [2 Bitrus 1:2] AT: "ta wurin sanin Ubangiji da Almasihu Yesu Mai ceto"
"yanayinsu ya yi muni fiye da na dã"
Bitrus yana magana game da rayuwa kamar "hanya" ko tafarki. Wannan magana na nufin yin rayuwar da ke daidai bisa ga nufin Allah.
A nan "juyawa daga" na nufin mutum ya bar yin wani abun. AT: "bar yin biyayya ga ka'ida mai tsarki"
AT: "Ka'ida mai tsarki da Allah ya danƙa masu" ko kuwa "ka'idan nan mai tsarki da Allah ya tabbata cewa sun karɓa"
"Wannan karin magana ya shafe su" ko kuwa "Wannan karin magana ta bayyana su"
Bitrus ya yi amfani da karin magana biyu don ya yi misalin yadda malaman ƙarya waɗanda, kodashike sun san "hanyar adalci", suka juya baya zuwa ga abubuwan da ke kazantar da su cikin ruhaniya da kuma ɗabi'u marasa kyau.
Malaman karya su na handamar yin riba da 'yan'uwa.
Hallaka da hukunci da sauri zai zo kan malaman karya.
Malaman karya za su zo maku da karkatacciyar koyarwa mai hallakarwa, su kuma yi musun sanin Ubangijin da ya fanshe su.
Allah bai bar mala'ikun da suka yi zunubi, duniya ta zamanin da, da kuma biranen Sadoma da Gomrata
ya keɓe Nuhu, wanda yake wa'azin adalci, tare da wasu bakwai.
Matakin Allah ya nuna cewa Ubangiji ya san yadda zai ceci masu bi da kuma yadda za a kare masu adalci.
Mala'iku ne waɗanda aka ɗaukaka, wanda basu kawo karar batanci a kan mutane a gaban Ubangiji ba.
Malaman karyan suna rinjayar wanɗanda ba su da tsayayyan hankali.
Jakin da baya magana ya tsauta wa Balaam da muryar mutum.
Domin mutum bawa ne ga duk abin da ya rinjaye shi.
Abin da zai fi masu shi ne da ba su san hanyar adalci da su sani ba.
1 Yanzu, ina rubata maku, kaunatattu, wannan wasika ta biyu domin in tunashe ku, in kuma zuga tunaninku na gaskiya, 2 don ku tuna da kalmomin da annabawa tsarkaka suka fada a da, kuma da umurnin Ubangijinmu da mai ceto da aka bayar ta wurin manzaninku. 3 Ku san wannan da farko, cewa masu ba'a za su zo a kwanakin karshe. Za su yi ba'a kuma su ci gaba bisa ga sha'awowinsu. 4 Za su ce, "Ina alkawarin dawowarsa? Tun lokacin da kakaninmu suka mutu, dukkan abubuwa sun kasance yadda suke, tun farkon halitta." 5 Da gangan suka manta cewa sama da kasa sun kasance daga ruwa, kuma ta wurin ruwa, da dadewa ta wurin umarnin Allah, 6 kuma cewa ta wurin wadannan abubuwa duniyar wancan zamani ta halaka, da ambaliyar ruwan tsufana. 7 Amma sama da kasa na yanzu, an tanada su domin wuta ta wurin wannan umarnin. An tanada su domin ranar shari'a da halakar marassa ibada. 8 Kada ku manta da wanan, kaunatattu, cewa rana daya a gun Allah kamar shekaru dubu ne, kuma shekaru dubu kamar rana daya suke. 9 Ubangiji baya jinkiri game da alkawaransa kamar yadda wadansu ke ganin jinkiri. Maimakon haka, yana hakuri da ku. Ba ya so ko dayanku ya hallaka, amma kowanenku ya kai ga tuba. 10 Duk da haka, ranar Ubangiji za ta zo kamar barawo. Sammai za su shude da kara mai karfi. Wuta zata kone komai da komai, kuma duniya da dukkan ayyukan da ke cikinta zasu bayyanu. 11 Da shike dukkan wadanan abubuwa za a hallaka su haka, wadanne irin mutane yakamata ku zama? Ya kamata kuyi rayuwar tsarki da ta ibada. 12 Ku zauna cikin bege da kuma hanzarta zuwan ranar Allah. A ranan nan, za a hallaka sammai da wuta, kuma dukkan komai da komai zai narke cikin zafi mai tsanani. 13 Amma bisa ga alkawarinsa, muna jiran sabuwar sama da sabuwar duniya, inda adalci zai kasance. 14 Saboda haka, kaunatattu, tun da kuna da begen wadannan abubuwa, ku yi iyakacin kokarinku a same ku marassa tabo da marasa aibu a gabansa, cikin salama. 15 Kuma, ku dauki hakurin Ubangiji domin ceto ne, kamar yadda kaunataccen danuwanmu Bulus ya rubuta maku bisa ga hikima da aka ba shi. 16 Bulus yayi magana akan wadanan abubuwa cikin dukkan wasikunsa, a ciki akwai abubuwa da suke da wuyar ganewa. Jahilai da mutane marassa natsuwa sukan juya ma'anarsu, kamar yadda suke yi wa sauran nassoshi, don hallakar kansu. 17 Saboda haka, kaunatattu, tun da kun san wadannan abubuwa, ku kula da kanku kada a badda ku ta wurin rudun mutanen da ba su bin doka, har ku rasa amincinku. 18 Amma ku yi girma a cikin alheri da sanin Ubangijinmu da mai ceto Yesu Almasihu. Bari daukaka ta tabbata a gare shi yanzu da har abada. Amin.
Bitrus ya fara magana game da ƙarshen zamani.
Bitrus yana magana game da sa masu karantun sa su yi tunani game da waɗannan abubuwa sai ka ce ya tashe su ne daga barci. AT: "in sa ku ku yi tunani masu tsabta"
AT: "Kalmomin da annabawa masu tsarki suka faɗa a dã"
AT: "umurnin Ubangijinmu da Mai Cetonmu, wanda manzannin ku suka ba ku"
"Ku san wannan a matsayin abu mafi muhimmanci." Dubi yadda ku ka juya wannan cikin [2 Bitrus 1:20]
A nan kalman nan "sha'awowi" na nufin sha'awace-sha'awacen zunubi da ke gãbã da nufin Allah. AT: "rayuwa bisa ga sha'awowinsu ta zunubi"
yi, nuna hali
Masu ba'an sun yi wannan tambaya don su nanata cewa su ba su gaskata Yesu zai dawo ba. Kalmar nan "alkawari" na nufin cikan alkawarin cewa Yesu zai dawo. AT: "Alkawarin cewa Yesu zai dawo ba gaskiya ba ne! Ba Zai dawo ba!"
A nan "ubanni" na nufin kakani waɗanda sun yi rayuwa tun da jimawa. Yin barci na nufin mutuwa. AT: "kakaninmu sun mutu"
Masu ba'a sun yi amfani da kalmar nan "dukan" sosai, kuma suna cewa dashike babu wani abu da ya canza a duniya, lallai ba zai zama gaskiya ba ce Yesu zai dawo.
AT: "tun lokacin da Allah ya halici duniya"
AT: "Allah ya kafa sammai da duniya ... tun dã ta wurin kalmarsa"
Wannan na nufin cewa Allah ya sa ƙasa ta kasance daga ruwa, ya tattara ruwa a wuri ɗaya don ƙasa ta kassance.
A nan "waɗannan abubuwa" na nufin kalmar Allah da kuma ruwa.
AT: "Da ambaliyan ruwa, Allah ya hallaka duniya a zamanin dã "
AT: Ta wurin wannan kalma ɗayan, Allah ya keɓe sammai da duniya don wuta"
A nan "umurni" na a madaddin Allah wanda zai bada umurnin: AT "Allah, wanda zai ba da umurni iri ɗaya"
za a iya fara wannan da wata sabuwar jumla. AT: "Yana keɓe su don ranar shari'a"
AT: "domin ranar da zai hukunta da kuma hallakar da mutane marasa bin Allah"
"kada ku kãsa fahimtar wannan" ko "kada ku yi watsi da wannan"
"cewa bisa ga duban Ubangiji, rana ɗaya kamar shekaru dubu ne"
"Ubangiji baya jinkirin cikata alkawarensa"
Wasu mutane na tunanin cewa Ubangiji na jinkirin cikata alkawarensa saboda yadda suke duban lokaci dabam ne da yadda Allah ke duba.
Koda shike Ubangiji na hakuri kuma ya na so mutane su tuba, haiƙƙa zai dawo ya yi shari'a
Bitrus yana magana game da ranar da Allah zai hukunta kowa sai ka ce ɓarawo ne wanda zai zo babu stammani da mamaki kuma zai ɗauki mutane.
"Sammai za su ɓace"
AT: "da wuta Allah zai ƙone komai da komai"
Wannan na iya nufin 1) abubuwan da ke samaniya kamar rana, wata, da taurari ko kuwa 2) abubuwan da ke kunshe a sama da duniya kamar kasa, iska, wuta, da ruwa.
Allah zai ga dukan duniya da kuma ayyukan kowa, zai kuma hukunta kowane abu. AT: "Allah zai bayyana duniya da duk abubuwan da mutane suka aikata a cikin ta"
Bitrus ya fara gaya wa masubi yadda ya kamata su yi rayuwa a yayin da su na jiran ranar Ubangiji.
AT: "Tunda shike Allah zai hallaka duk waɗannan abubuwan ta wannan hanya"
Bitrus ya yi amfani da wannan tambayar don ya nanata abin da zai faɗa nan gaba, cewa su "yi rayuwar tsarki da kuma bin Allah." AT: "kun san irin mutanen da ya kamata ku zama."
AT: Allah zai hallaka sama da wuta, zai kuma narke komai da komai cikin zafi"
Bitrus yana magana game da "adalci" sai ka ce mutum. Wannan na nufin mutane masu adalci. AT: "inda mutane masu adalci za su dawwama" ko kuwa "inda mutanen za su yi rayuwar adalci"
AT: "ku yi iyakacin ƙoƙarin ku ku yi rayuwa a hanyar da ta dace saboda Allah ya same ku marasa tabo da marasa aibu, ku kuma zama da salama tare da shi da kuma juna"
Kalmomin nan "marasa tabo" da "marasa aibu" na nufin abu ɗaya ne na kuma nanata halin tsarki. AT: "tsarki gaba ɗaya"
A nan wannan na nufin "marasa laifi."
Domin Ubangiji mai haƙuri ne, shi ya sa ranar shari'a ba ta zo ba tukuna. Wannan ya ba wa mutane zarafin tuba da kuma ceto, kamar yadda ya bayana cikin [2 Bitrus 3:9] AT: "Kuma, ku yi tunani game da hakkurin Ubangijinmu a matsayin zarafin tuba da kuma ceto aka ba ku"
AT: "bisa ga hikimar da Allah ya ba shi"
"Bulus ya yi magana game da haƙurin Allah da ke kai ga samun ceto a cikin duk wasiƙunsa"
A kwai abubuwan cikin wasiƙun Bulus da ke da wuyar fahimta.
Jahilai da mutane marasa natsuwa sukan yi fasarar da ba daidai ba na abubuwan da ke da wuyar fahimta cikin wasiƙun Bulus.
"wanda ba a koyar da su ba da marasa natsuwa." Ba a koya wa mutanen nan yadda za su fasara nassin da kyau ba kuma ba su kafu cikin gaskiyar bisharar ba.
"kai ga hallakarsu"
"Waɗannan abubuwa" na nufin gaskiya game da haƙurin Allah da kuma koyaswar malaman ƙaryan nan.
"tsare kanku"
A nan "ɓadda" na nufin a rinjayi wani ya yi wani abin da ba daidai ba. AT: "don kada mutanen da ba sa bin doka su yaudare ku su kuma sa ku ku yi abin da ba daidai ba"
An yi magana game da aminci sai ka ce wata mallaka ne da masubi za su iya rasa wa. AT: "ku bar aikata adalci"
A nan girma cikin Alheri da sanin Ubangiji na nufin ƙara samun alherinsa da saninsa. Ana iya bayyana "alheri" da "yi kirki." AT: "ƙara samun alherin Ubangijinmu da Mai cetonmu Yesu Almasihu, da kuma ƙara saninsa" ko kuwa "ku ƙara sanin yadda Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Almasihu ya yi mana kirki, ku san shi yadda ya kamata"
Ya rubuta domin ya tunashe su da kalmomin da annabawa suka fada a da, kuma game da umurnin Ubangijinsu da mai cetonsu.
Masu ba'a za su tuhunta alkawarin dawowar Yesu, sun kuma ce dukkan abubuwa sun kasance yadda suke, tun farkon halitta.
An kafasu da kuma keɓe su ta wurin kalmar Allah.
Domin ba ya so su hallaka, amma kowa ya kai ga tuba.
Ranar Ubangiji zai zo kamar barawo.
Domin za a hallaka sammai da duniya, kuma don sun yi begen adalci ya kasance a sabon sammai da sabon duniya.
Ayukansu zai kai ga hallakar kansu.
Ya umurce su su yi girma a cikin alheri da kuma sanin Ubangijinsu da mai ceto Yesu Almasihu.
1 Abin nan da yake tun daga farko, wanda muka ji, wanda muka gani da idanunmu, wanda muka gani hannuwanmu suka kama, a wajen maganar rai. 2 Ran kuwa aka baiyyana shi, muka gani, muka bada shaida, muka gaya maku labarin rai na har abada, wanda da yake a wurin Uba, aka kuma sanar da mu. 3 Wannan da muka gani muka ji muka baku labari, domin kuyi zumunci da mu, zumuncinmu kuwa tare da Uba yake da Dansa Yesu Almasihu. 4 Haka nan, muna rubuta maku wadannan abubuwa domin farin cikinmu ya cika. 5 Wannan shi ne sakon da muka ji daga wurinsa mu kuwa muka sanar da ku: Allah haske ne a wurinsa kuwa babu duhu ko kadan. 6 Idan mun ce muna zumunci da shi kuma muna tafiya cikin duhu, muna yin karya kuma bama aikata gaskiya. 7 Amma idan muna tafiya cikin haske kamar yadda yake cikin haske, muna zumunci da juna, jinin Yesu Dansa ya wankemu daga dukka zunubi. 8 Idan mun ce bamu da zunubi, muna rudin kanmu kenan, ba kuma gaskiya a cikinmu. 9 Amma idan mun fadi zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci da zai gafarta mana zunubanmu, ya kuma wankemu daga dukkan rashin adalci. 10 Idan mun ce bamu yi zunubi ba, mun mai da shi makaryaci kenan, maganarsa kuma bata cikinmu.
Yahaya ya cigaba da rubutu game da zumunci sa'anan ya nuna cewa yana iya yiwuwa domin Yesu yana tsakanin masubi da Uban.
Jumlar nan na nufin Yesu, wadda ya kasance kafin a halice kome. AT: "Muna rubuta maku game da shi wanda ya kasance kafin halitar dukan kome"
"forkon dukan kome" ko kuma "halitar duniya"
"wadda muka ji shi ya koyar"
An maimaita wannan ne domin nanaci. AT: "wadda mu da kan mu mun gani"
"Yesu, mai sa mutane su rayu hara abada"
Kalmar nan "rai" a wannan litafin gaba ɗaya na nufin fiye da rai na jiki. A nan yana madadin Yesu, rai na har abada.
AT: "Allah ya sa wannan Rai na har abadan ya zama sananne a gare mu" ko kuma "Allah ya sa mun iya sanin sa, shi Rai na har abadan"
"muka gan shi"
"mun yi alƙawarin gaya wa sauran mutane game da shi"
A nan "Rai na har abada" na nufin shi mai ba da rai, Yesu. AT: "shi wanda ya iza mu mu rayu har abada"
"da ke tare da Allah Uban"
Wato lokacin da yake rayuwa a duniya kenan. AT: "kuma ya zo ya kasance a tsakanin mu"
"muna faɗa muku abin da mu ma muka gani muka ji"
"ku zama abokan mu na kusa. Mu abokai ne da Allah Uban"
Bai fita a fili ko maganar Yahaya ya shafi masu karantun wasiƙar sa ko bai shafe su ba. Za ku iya fasara wannan ko ta wane hanya.
Waɗannan sunaye ne masu muhimmamci da ke bayyana dangartakar da ke tsakanin Allah da Yesu.
"domin ya cika farincikinmu" ko kuma "domin mu sa kanmu mu yi murna sosai"
Daga nan zuwa sura na gaba, Yohaya na rubutu game da zumunci--dangartakarmu da Allah da kuma sauran masubi.
Wannan wata magana ce da ke nufin cewa Allah mai tsarki ne gabaki ɗaya. Al'adun da ke kwatanta abu mai kyau da haske na iya barin wannan haka ba tare da fasara ba. AT: "Allah zallan adalci ne kamar zallan haske"
Wannan na nufin cewa Allah baya taɓa aikata zunubi kuma baya taɓa mugunta. Al'adun da ke kwatanta mugunta da duhu na iya barin duhu ba tare da fasara ba. AT: a cikinsa babu wani mugunta"
A nan "tafiya" na nufin yadda mutum ke rayuwa ko nuna hali. A nan "duhu" na nufin "mugunta" AT: "aikata mugunta"
A nan "tafiya" na nufin yadda mutum ke rayuwa ko nuna hali. A nan "haske" na nufin "mai kyau" ko "daidai." AT: ko "aikata abubuwa masu kyau kamar yadda Allah na da cikakken kyau" ko "ko aikata abin da ke daidai kamar yadda Allah ke daidai cikin komai.
Wannan na nufin mutuwar Yesu
Wannan wata suna ce mai muhimmanci sosai na Yesu, Ɗan Allah.
"ba mu taɓa zunubi ba"
"na yaudaran" ko kuma "na ƙarya"
An yi maganar gaskiya a nan kamar wani abu ne da ake iya samun sa cikin masubi da za a iya gani da ido ko a taɓa da hannu. AT: "bamu gaskata cewa abin da Allah ya faɗa gaskiya bane"
Jumloli biyun nan na nufin abu ɗaya ne. Yahaya ya yi amfani ne da su domin ya nanata cewa ba shakka Allah zai gafarta zunubanmu. AT: "kuma zai gafarta mana dukan inda mun yi kuskure
An ɗauki cewa mutumin da ya ce bashi da zunubi zai ce Allah maƙaryaci ne tunda Allah ya ce kowa mai zunubi ne. AT: "daidai ne da kiransa maƙaryaci, domin ya ce mun yi zunubi"
"Maganarsa" a nan na nufin "saƙo." AT: "bamu fahimci Maganar Allah ba balle ma mu yi biyayya da shi"
Yahaya ya ce Kalmar Rai ya fara ne daga farko.
Yahaya ya ji, ya gani, ya dudduba, ya kuma riƙe Kalmar Rai.
Kalmar Rai na tare da Uba kafin a bayyana wa Yahaya.
Yahaya na shellar abubuwan da ya gani ya kuma ji ne domin in ya yiwu wasu ma su yi zumunci da shi.
Yahaya ya rigaya yayi zumunci da Uba da kuma Ɗansa, Yesu Almasihu.
Yahaya na sanad da saƙo cewa Allah shine haske, a cikin sa kuma babu duhu ko kaɗan.
Yahaya ya ce wannan irin mutum maƙaryaci ne kuma baya aikata ayukkan gaskiya.
Jinin yesu shi ya ke wanke su daga dukan zunubi.
Yahaya ya ce irin wannan mutumin ya na yaudarar kansa ne kuma gaskiya bata cikinsa.
Domin waɗanda suke furta zunubansu, Allah zai yafe masu zunubansu ya kuma wanke su da ga dukan rashin adalci.
1 'Ya'yana, na rubuta ma ku wadannan abubuwa domin kada kuyi zunubi. Amma idan wani yayi zunubi muna da matsakanci a wurin Uba, Yesu Almasihu, mai adalci. 2 Shine fansar zunubanmu, ba ma namu kadai ba amma na duniya dukka. 3 Ta haka muka san cewa mun san shi, idan mun kiyaye dokokinsa. 4 Duk wanda yace, "Na san Allah" amma bai kiyaye dokokinsa ba, makaryaci ne gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5 Amma duk wanda ya kiyaye maganarsa, hakika kaunar Allah ta kammala a cikin wannan mutum. Ta wurin haka muka sani muna cikinsa. 6 Duk wanda yace yana cikin Allah dole ne shi da kansa yayi tafiya kamar yadda Yesu Almasihu yayi. 7 Kaunatattu, ba sabuwar doka nike rubuta maku ba, amma tsohuwar doka ce wadda kuka ji tun farko. Tsohuwar dokar kuwa itace maganar da kuka ji tun farko. 8 Amma yanzu ina rubuta maku sabuwar doka wadda gaskiya ce a cikin Almasihu da cikinku, saboda duhu yana wucewa, haske na gaskiya yana haskakawa. 9 Duk wanda yace yana cikin haske amma yana kin dan'uwansa, yana cikin duhu har yanzu. 10 kuma wanda yake kaunar dan'uwansa yana cikin haske babu dalilin tuntube a wurinsa. 11 Amma duk wanda yake kin dan'uwansa yana cikin duhu, yana kuma tafiya cikin duhu, bai san ma inda ya nufa ba, domin duhu ya makantar da shi. 12 Na rubuta maku, ya ku kaunatun 'ya'yana, saboda an gafarta zunubanku domin sunansa. 13 Na rubuta maku, ubanni, saboda kun san shi wanda yake tun daga farko. Na rubuta maku matasa saboda kun yi nasara da mugun. Na rubuta maku, yara kanana, saboda kun san Uban. 14 Na rubuta maku, Ubanni, saboda kun san shi wanda yake tun daga farko. Na rubuta maku, matasa, saboda kuna da karfi, kuma maganar Allah tana zaune cikinku. Kuma kun yi nasara da mugun. 15 Kada kuyi kaunar duniya ko abubuwan da suke cikin duniya. Idan wani yayi kaunar duniya, kaunar Uban bata cikinsa. 16 Domin dukkan abubuwan da suke a cikin duniya, kwadayi na jiki, abin da idanu suke sha'wa, da rayuwar girman kai ta wofi, ba na Uban bane amma na duniya ne. 17 Duniya tana wucewa tare da sha'awarta. Amma dukkan wanda ya aikata nufin Allah zaya kasance har abada. 18 Yara kanana, sa'a ta karshe ce. Kamar dai yadda kuka ji magafcin Almasihu yana zuwa, ko yanzu ma magaftan Almasihu da yawa sun rigaya sun zo, ta haka muka san sa'a ta karshe ce. 19 Sun fita daga cikinmu, dama su bana cikinmu bane. Gama idan da su namu ne da sun ci gaba tare damu. Amma da yake sun fita, ya nuna su ba na cikinmu bane. 20 Amma ku kun karbi shafewa daga wurin Mai Tsarki, kuma dukkanku kun san gaskiya. 21 Bana rubuta maku bane domin baku san gaskiya ba, amma saboda kun santa, kuma ba wata karya da ta fito daga gaskiya. 22 Wanene makaryaci shine wanda yayi musu cewa Yesu ba Almasihu bane? Wannan mutumin shi ne magafcin Almasihu, tun da yayi musun Uba yayi musun Dan. 23 Ba wanda yayi musun Dan kuma yake da Uban. Dukkan wanda ya amince da Dan yana da Uban ma. 24 A game daku kuma, sai ku bari abinda kuka ji daga farko ya zauna a cikinku. Idan abin da kuka ji daga farko ya zauna a cikinku, kuma zaku kasance a cikin Dan da kuma Uban. 25 Alkawarin da ya bamu kenan, rai na har abada. 26 Na rubuta maku wadannan abubuwa ne game da wadanda zasu baudar daku. 27 Game daku, shafewar daku ka samu daga wurinsa tana nan a cikinku, baku bukatar wani ya koyar daku. Amma kamar yadda shafewar da kuka karba a wurinsa ta koya maku dukkan abu, kuma gaskiya ne ba karya bane, tana nan a cikinku kamar yadda a ka koya maku, ku kasance a cikinsa. 28 Yanzu fa, 'ya'ya na kaunatattu, ku kasance a cikinsa domin sa'adda zai baiyyana mu zama da gabagadi ba tare da kunya ba a gabansa sa'adda zai zo. 29 Idan kun sani shi mai adalci ne, kun sani dukkan wanda ke aikata adalci haifaffe ne daga wurinsa.
Yahaya ya cigaba da rubutu game da zumunci sa'anan ya nuna cewa yana iya yiwuwa domin Yesu yana tsakanin masubI da Uban
Anan kalmar nan "mu" na nufin Yahaya da dukkan masubi kuma "na shi" na nufin na Allah Uban, ko kuma na Yesu.
Yahaya tsohon mutum ne kuma shi ne shugabansu. Yayi amfani ne da wannan furci domin ya nuna yadda yake ƙaunansu. AT: "Ƙaunatattun 'ya'yana a cikin Almasihu" ko kuma "Ku da kuke ƙaunattatu a gare ni kamar 'ya'yan kaina"
"Ina rubuta mu ku wannan wasiƙa"
"Amma sa'and da wani yayi zunubi." Wannan abu ne da ke iya faruwa.
Kalmar nan "matsakanci" a nan na nufin Yesu. AT: "muna da Yesu Almasihu, mai adalci, mai magana da Uban mai kuma roƙa a gafarta mana"
"Allah baya fushi da mu kuma domin Yesu ya sadaukar da ransa saboda zunubanmu" ko kuma "Yesu shi ne wanda ya sadaukar da ransa saboda zunubanmu, don haka, Allah baya fushi da mu kuma a kan zunubanmu.
"mun sani da cewa mun san shi" ko kuma "mun san muna da dangantaka mai kyau da shi"
"idan mun yi biyayya da dokokinsa"
"Duk wanda ya ce" ko "Mutumin da ya ce"
"Ina da dangantaka mai kyau da Allah"
"baya biyayya" ko "rashin biyayya"
"abinda Allah ya ce mishi ya yi"
An yi maganar gaskiya a nan kamar wata abu ce da ake iya samu cikin masubi da za a iya gani da ido ko a taɓa da hannu. AT: "bai gaskata cewa abin da Allah ya faɗa gaskiya bane"
A kiyaye maganar mutum na nufin biyayya. AT: "yana yin abin da Allah ya ce mishi ya yi"
Wannan na iya nufin 1) "ƙaunar Allah" na nufin zuwa ga mutumin da ke ƙaunar Allah, kuma "kammala" na matsayin gabaki ɗaya ko a cike. AT: "mutumin da ke ƙaunar Allah gabaki ɗaya kenan" ko kuma 2) "ƙaunar Allah" na nufin ƙaunar da Allah na yi wa mutane, kuma "kammala" na masatayin cika nufinsa. AT: "ƙaunar Allah na cinma burin sa a cikin rayuwar wannan mutum"
Jumlar nan "muna cikinsa" na nufin maibin da na da dangantaka da Allah. AT: idan mun yi biyayya da abinda Allah ya faɗi, za mu iya tabbatar da cewa muna zumunci da shi" ko kuma "ta haka muka san cewa mun haɗe da Allah"
kasancewa a cikin Allah na nufin a cigaba da zumunta da shi. AT: cigaba da zumunta da Allah" ko kuma "zama a haɗe da Allah"
An yi maganar bi da rayuwa kamar tafiya ne a wata hanya. AT: "lallai ne ya yi rayuwa kamar yadda Yesu Almasihu ya yi" ko kuma "yakamata su yi biyayya da Allah kamar yadda Yesu Almasihu ya yi"
"ku mutane wadda na ke ƙauna, Ina" ko kuma "Ƙaunattun abokai, Ina"
"Na rubuta muku cewa ku ƙaunaci juna, wannan ba wata sabuwar abin yi bane amma tsohuwar dokar da kun taba ji." Yahaya na nufin umurnin Yesu mai cewa a ƙaunaci juna.
A nan "forƙo" na nufin lokacin da sun yanke shawara su bi Yesu. AT: daga forkon lokacin da kun gaskata da Almasihu"
"Tsohuwar dokar itace sakon da kuka ji"
"Amma a wata hanya dokar da na rubuta maku sabuwar doka ce"
"wadda gaskiya ce, kamar yadda ta bayyana a cikin halayen Almasihu da halayen ku"
A nan "duhu" na nufin "mugunta" kuma "haske" na nufin abu "mai kyau." AT: "domin kuna barin yin mugunta kuna kara yin abu mai kyau"
A nan zama "a cikin haske" na nufin yin abinda ke daidai. AT: "yana yin abin da ke daidai"
A nan zama "a cikin duhu" na nufin yin mugunta. AT: "na yin mugunta"
"babu abinda zai sa shi tuntuɓe." Kalmar nan "tuntuɓe" na nufin mutum ya kasa a ruhaniya ko a halin kirki. AT: "babu abinda zai sa shi zunubi" ko kuma "ba zai kasa yin abinda zai gamshi Allah ba"
A nan "tafiya" na nufin yadda mutum na rayuwa ko nuna hali. A nan zama "a cikin duhu" da kuma "tafiya a cikin duhun" na nufin abu ɗaya ne. Wannan na jan hankali ne cewa mugunta ne mutum ya ƙi ɗan'uwansa maibi. AT: ke yin mugunta"
wannan na maganar maibi da baya rayuwa yadda yakamata mai bi ya yi rayuwa. AT: "bai san ma abinda yakamata ya yi ba"
"duhu ya sa shi ba ya iya gani." Duhu na nufin zunubi ko mugunta. AT: "zunubi ya sa ba ya iya fahimtar gaskiya"
Yahaya tsohon mutum ne kuma shi ne shugabansu. Yayi amfani ne da wannan furci domin ya nuna yadda yake ƙaunansu. Duba yadda kun fasara wannan a [1 Yahaya 2:1] AT: "Ƙaunatattun 'ya'yana a cikin Almasihu" ko kuma "Ku da kuke ƙaunattatu a gare ni kamar 'ya'yan kaina"
AT: "Allah ya gafarta zunubanku"
"sunansa" na nufin Almasihu da kuma ko shi wanene. AT: "domin abin da Almasihu ya yi maku"
Kalmar nan "ubanni" a nan na nufin masubi kamilai. AT: "Ina rubuta maku, kamilai masubi"
"wanda yana rayuwa ko da yaushe" ko kuma "wanda yana nan koda yaushe." Yana nufin "Yesu" ko kuma "Allah Uba"
Wannan na iya nufin waɗanda ba sabobbin masubi ba amma suna girma a cikin ruhaniya. AT: "matasa a bi"
A nan "ƙarfi" na maibi ba na jiki bane, amma aminci ga Almasihu.
"maganar Allah" a nan na nufin saƙo daga Allah. Marubucin ya ambaci ƙarin amincin masubi ga Almasihu da kuma sanin sa kamar yana maganar kalmar Allah na nan a cikinsu. AT: "Sakon Allah na cigaba da koyar maku" ko kuma "kun san maganar Allah"
Marubucin na maganar kin yardar da masubi ke yi na bin shaiɗan da kuma lalata shirye-shiryen sa a matsayin wani abun nasara ne.
A 2:15-17 Kalmar nan "duniya" na nufin dukan abubuwan da mutane ke so su yi da ba su girmama Allah. AT: Kada halin ku ya zama kamar na mutanen da suke cikin duniya da basu girmama Allah, kuma basu ƙauna"
"abubuwan da waɗanda basu girmama Allah suke so"
Mutum ba zai iya ƙaunar duniya da kuma dukan abubuwan da basu darajanta Allah ya kuma ƙaunaci Uban a lokaci ɗaya ba.
"baya ƙaunar Uban"
Waɗannan sune jerin wasu abubuwan da ke cikin duniya. Sun bayyana abin da ake nufi da "kome da ke cikin duniya"
"samun ƙaƙƙarfan marmarin aikata zunubi"
"Ƙaƙƙarfan marmarin samun abubuwan da muke iya gani"
Wannan na iya nufin a mallaka da kuma halayya. AT: "yin alfahari da abinda mutum ke yi ko ke da shi" ko kuma "girman kai da mutane ke yi domin abubuwan da suke da shi da abubuwan da suke yi"
"basu zo daga Uban ba ne" ko kuma "ba yadda Uban ya koya mana mu yi rayuwa bane"
"wucewa" ko kuma "watarana ba za a same ta a nan ba"
"masubi da ke girma" Dubi yadda kun fasara wannan a [2:1]
Jumlar "sa'a ta ƙarshe" na nufin kafin Yesu ya dawo. AT: "Yesu zai dawo ba da daɗewa ba"
"akwai mutane da yawa da ke gaba da Almasihu"
"ya zo, kuma saboda haka mun sani" ko kuma "magabtan Almasihu sun zo, yanzu mun sani"
"Sun bar mu"
"amma a gaskiya su ba namu ba ne" ko kuma "a gaskiya su ba namu bane tun farko" Abinda ya sa su ba namu bane da gaske shine domin su ba masubin Yesu bane.
"Mun san wannan domin da basu barmu ba inda su ainihi masubi ne.
"Mun san haka ne domin inda su masubi ne da gaske da basu barmu ba"
Yahaya yana maganar Ruhu Mai Tsarki kamar shi "shafewa ne" da mutane sun karɓa daga wurin Yesu. AT: "Amma Mai Tsarkin ya shafe ku" ko kuma "Amma Yesu, Mai Tsarkin ya ba ku Ruhunsa"
Wannan na nufin Yesu. AT: Yesu, Mai Tsarkin"
AT: Abinda ke gaskiya ... ba wata ƙarya da ta fito daga abinda ke gaskiya"
Wanane maƙaryacin? Duk wanda ya yi musun cewa Yesu ba Almasihu ba ne. Yahaya yayi amfani da wannan tambayan ne don ya nanata su wanene masu ƙarya.
"na ƙin cewa Yesu ne Almasihu" ko kuma "na cewa ba Yesu ne Almasihu ba"
"na ƙin faɗin gaskiya game da Uban da Ɗan" ko kuma "na ƙin Uban da Ɗan."
Waɗannan wasu sunaye ne masu muhimmanci da ke bayyana dangantakar da ke tsakanin Allah da Yesu.
"ke na Uban"
"faɗin gaskiya game da Ɗan"
Wannan yana nuna yadda Yahaya ke gaya musu yadda yakamata su yi rayuwa a mastsayin masu bin Yesu a maimakon yadda masu gãba da Almasihu ke rayuwa.
"ku tuna ku kuma gaskata da abinda kuka ji tun farƙo". Za a iya ƙarin bayyanin yadda suka ji shi, abinda suka ji, da kuma abinda "forƙon" ke nufi: AT: "ku cigaba da gaskata abinda muka koya maku game da Yesu kamar yadda kun gaskata tun da kuka zama masubi"
"abinda mun koya maku game da Yesu lokacin da kuka zama masubi"
Wannan shine alkawarin da ya bamu--rai na har abada" ko kuma "Ya alkawarta mu mu rayu har abada"
A nan "bauɗar da ku" na nufin rinjayar mutum ya gaskata cewa abu ba gaskiya bane. AT: waɗanda suke so su yaudare ku" ko kuma "waɗanda suke so su sa ku ku yarda da ƙarya game da Yesu Almasihu"
Wannan na nufin "Ruhun Allah". Duba rubutun da aka yi game da "shafewa" a [2:20]
AT: "domin shafewarsa yana koya maku dukan abubuwan da kuke buƙata ku sani"
A kasance a cikin mutum na nufin a cigaba da zumunci da shi. Dubi yadda kun fasara "kasance a cikin Allah" a [2:5-6]. AT: "cigaba da zumunci da shi" ko kuma "zama a haɗe da shi"
An yi amfani ne da wannan kalmar don a nuna wata sabuwar bangaren wasiƙar.
Yahaya tsohon mutum ne kuma shi ne shugabansu. Yayi amfani ne da wannan furci domin ya nuna yadda yake ƙaunarsu. AT: "Ƙaunatattu 'ya'yana a cikin Almasihu" ko kuma "Ku da kuke ƙaunatattu a gare ne kamar 'ya'yan kaina"
"mun ganshi"
"rashin tsoro"
...
"yayin da Ya sãke zuwa kuma"
"haifaffe ne na Allah" ko kuma "Ɗan Allah ne"
Yesu Almasihu haday ne domin zunuban dukan duniya.
Za mu iya sanin mun san Yesu Almasihu idan muna riƙe dokokinsa.
Wanda ya ce ya san Allah amma ba ya ajiye dokokinsa, maƙaryaci ne.
Mai bi ya kamata ya yi tafiyarsa kamar yadda Yesu Almasihu ya yi tafiya.
Wanda ya ke cewa ya na haske, amma yana gaba da ɗan'uwansa, ya na cikin duhu.
Allah ya na găfarta zunuban ma su bi saboda sunan Ɗansa Almasihu.
Ya ce dole ne mai bi ya zama wanda ba ya kaunar duniya da kayan duniya.
Ya yi lissafa sunayen muguwar sha'awa na jiki, the muguwar sha'awa na idanu, da kuma banzar daukakar rayuwa wanda ke a duniya kuma ba da ga Allah ba.
Ya ce ya san cewa wannan karshen sa'a ne domin maƙiyan Kristi da yawa sun rigaya sun zo.
Ya ce maƙiyin kristi ya na zuwa.
Maƙiyin kristi na musun Uba da kuma Ɗan.
A'a, ba zai yiwu wanda yayi musun Ɗan ya sami Uban ba.
Yahaya ya gaya wa masu bi su kasance a cikin abubuwan da su ka ji da ga farko.
Allah ya ba wa masubi alkawarin Rai na har abada.
Wadanda suka kasance a cikin Ɗan za su sami ƙarfin hali kuma ba za su ji kunya ba a lokacin da Almasihu zai bayyana a zuwansa.
1 Dubi irin kaunar da Allah ya bamu, har da za a kira mu 'ya'yan Allah, haka muke kuwa. Saboda wannan dalili ne duniya bata san muba, saboda bata san shi ba. 2 Kaunatattu, yanzu mu 'ya'yan Allahne, kuma ba a bayyana mana yadda zamu zama ba tukuna, mun sani sa'adda Almasihu zai bayyana, zamu zama kamarsa, domin zamu ganshi kamar yadda yake. 3 Dukkan wanda yake da wannan bege game da gidan gobe ya kan tsarkake kansa, kamar yadda shima yake da tsarki. 4 Dukkan wanda yaci gaba da yin zunubi yana ketare shari'a kenan. Gama zunubi ketare shari'a ne. 5 Kun sani Almasihu ya bayyana domin ya dauke zunubai ne. Kuma a cikinsa babu zunubi. 6 Ba wanda zai kasance a cikinsa da zai cigaba da yin zunubi. Ba wanda zai ci gaba da aikata zunubi da zai ce ya sanshi, ko kuma ya ganshi. 7 'Ya'yana kaunatattu, kada ku bari kowa ya baudar da ku, wanda yake aikata adalci shi adali ne, kamar yadda Almasihu yake adali. 8 Wanda yake aikata zunubi na ibilis ne, gama ibilis yayi zunubi tun daga farko. Dalilin haka ne Dan Allah ya bayyana, domin ya rushe ayyukan ibilis. 9 Duk wanda aka haife shi daga Allah ba ya yin zunubi, saboda irin Allah na cikinsa. Ba zaya iya ci gaba da yin zunubi ba domin an haife shi daga wurin Allah. 10 Ta haka ne ake bambanta 'ya'yan Allah da 'ya'yan ibilis. Dukkan wanda baya aikata adalci ba na Allah bane; haka kuma wanda ba ya kaunar dan'uwansa. 11 Domin wannan shine sakon da kuka ji tun daga farko: cewa mu kaunaci junanmu, 12 ba kamar Kayinu ba wanda yake na shaidan kuma ya kashe dan'uwansa. Me yasa ya kashe shi? Saboda ayyukansa miyagu ne, na dan'uwansa kuma masu adalci ne. 13 Kada kuyi mamaki 'yan'uwana, idan duniya ta ki ku. 14 Mun sani mun ratsa mutuwa zuwa cikin rai, saboda muna kaunar 'yan'uwa. Dukkan wanda ba ya yin kauna, shi matacce ne. 15 Dukkan wanda yake kin dan'uwansa, mai kisan kai ne. Kun kuma sani babu rai na har abada a cikin mai kisankai. 16 Ta wurin haka muka san kauna, da ya ke Almasihu ya bayar da ransa saboda mu. Mu ma ya kamata mu bada ranmu saboda 'yan'uwamu. 17 Amma duk wanda yake da kayan duniya, ya ga dan'uwansa cikin bukata, kuma bai ji tausayinsa ba, ta yaya kaunar Allah ke cikinsa? 18 'Ya'yana kaunatattu, kada muyi kauna ta fatar baki kawai, amma muyi aikin kauna da gaskiya. 19 Ta wurin haka mun sani mu masu gaskiya ne kuma mun tabbatar da zuciyarmu a gabansa. 20 Gama idan zuciyarmu bata kayar damu ba, Allah ya fi zuciyarmu girma, kuma yana sane da kome. 21 Kaunatattu, idan zuciyarmu bata kashe mu ba, muna da gabagadi a gaban Allah. 22 Kuma duk abin da muka nema zamu samu a wurinsa, saboda muna kiyaye dokokinsa, muna yin abubuwan da suka gamshe shi. 23 Kuma ummurninsa kenan: mu bada gaskiya ga sunan Dansa Yesu Almasihu, mu yi kaunar juna kuma kamar yanda ya bamu wannan doka. 24 Duk wanda yake kiyaye umarnin Allah, yana cikinsa, Allah kuma yana cikin mutumin. Ta haka muka gane cewa yana cikinmu, Ta wurin Ruhu, wanda ya bamu.
A wannan sashin, Yahaya yana faɗi wa masubi game da sabuwar halittarsu, wadda ba ya iya zunubi.
"Yi tunanin yadda Ubanmu yana matuƙar ƙaunarmu"
"Uban ya kira mu 'ya'yansa"
A nan wannan na nufin mutanen da sun zama na Allah ta wurin bangaskiya cikin Yesu.
Wannan na iya nufin 1) "Saboda mu 'ya'yan Allah ne kuma saboda duniya bata san Allah ba, bata san mu ba." Ko kuma 2) Saboda duniya bata san Allah ba, bata san mu ba."
A nan "duniyan" na nufin mutanen da basu girmama Allah. Ana iya ƙarin bayyanin abinda duniya bata sani ba. AT: "waɗanda basu girmama Allah basu san cewa mu na Allah ba ne, saboda basu san Allah ba"
"Ku mutane da nake ƙauna, mu" ko kuma "Ƙaunattatun abokai, mu, " Dubi yadda aka fasara wannan a [2:7]
AT: "Allah bai riga ya bayyana ba"
Wannan na iya nufin "faɗi" ko "nuna"
Dukan wanda yana sa rai da gabagaɗi a kan ganin Almasihu yadda yake zai tsarkake kansa saboda Almasihu yana da tsarki"
"Almasihu ya bayyana" ko kuma "Uban ya bayyana Almasihu"
"kasance da dangantaka da Allah" Duba yadda kun fasara wannan a [2:2-6]
Yahaya yana amfani da "gani" da "sani" ne domin ya ce mutumin mai yin zunubi bai sadu da Almasihu a ruhu ba. Mutumin da yake rayuwa bisa ga halin zunubi ba zai iya sanin Almasihu ba. AT: "Ba wanda ... bai gaskatawa da shi da gaske ba"
Yahaya tsohon mutum ne kuma shi ne shugabansu. Yayi amfani ne da wannan furci domin ya nuna yadda yake ƙaunarsu. AT: "Ƙaunatattun 'ya'yana a cikin Almasihu" ko kuma "Ku da kuke ƙaunatattu a gare ne kamar 'ya'yan kaina"
A nan "ɓaudar da ku" na nufin a rinjayi mutum har ma ya yarda da abinda ba gaskiya ba ne. AT: "kada ku bar kowa ya mayar da ku wawaye" ko kuma "kada ku bar kowa ya ruɗe ku"
"Shi mai aikata abinda ke daidai yana faranta wa Allah rai kamar yadda Almasihu yana farantawa Allah rai."
"ya zama na ibilis" ko kuma "yana kamar ibilis ne"
Wannan na nufin ainihin forkon haliita kafin mutum ya aikata zunubi na forƙo.AT: "tun ainihin forkon lokacin halita"
AT: "Allah ya bayyana Ɗansa"
Wannan wata suna ce mai muhimmanci sosai na Yesu da ke bayyana dangantakar sa da Allah.
AT: "Duk wanda Allah ya mayar da shi ɗansa"
Wannan na maganar Ruhu Mai Tsarki ne, wanda Allah ke ba wa masubi wanda kuma yake sa su iya gãba da zunubi, su kuma aikata abinda kan gamshi Allah kamar shi wani irin hatsi ne da ake shukawa cikin ƙasa har yayi girma. Wani lokaci, a kan ce da wanna sabuwar halitta. AT: "Ruhu Mai Tsarki"
AT: "Allah ya bashi sabuwar rai na ruhaniya" ko kuma "shi ɗan Allah ne"
AT: "Ta haka ne mu ke sanin 'ya'yan Allah da kuma 'ya'yan ibilis"
Ana iya fahimtar waɗannan kalmomin "na Allah" a fuskoki biyu a jumlar. AT: Dukan wanda bai aikata adalci ba ba daga Allah ba ne; dukan wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa shi ma ba daga Allah ba ne" ko kuma "waɗanda suke aikata adalci na Allah ne, kuma waɗanda suke ƙaunar 'yan'uwansu na Allah ne su"
A nan "ɗan'uwa" na nufin 'yan'uwa masubi.
Kayinu da Habila ne 'ya'yan Adamu da Hauwa'u, na miji da macen forƙo.
"kada mu yi yadda Kayinu ya yi"
Wannan na nufin Kayinu ɗan'uwan Habila.
Yahaya yana amfani ne da wannan tambayar don ya koya wa masu sauraronsa. AT: "Ya kashe shi ne saboda"
Ana iya fahimtar kalmar nan "ayyuka" ta fuskoki biyu. AT: "Ayyukan Kayinu miyagu ne, ayyukan ɗan'uwansa kuma masu adalci ne" ko kuma "Kayinu ya aikata mugunta, ɗan'uwansa kuma ya yi abinda ke daidai.
"'yan'uwana masubi." Masu karatun wasiƙar Yahaya maza da mata ne.
A nan kalmar nan "duniya" na nufin mutanen da ba su girmama Allah. AT: "idan waɗanda ba su girmama Allah sun ƙi ku masu girmama Allah"
An yi maganar sharaɗin rayuwa da na mutuwa kamar wasu wurare ne da mutum zai iya bari ko zuwa. AT: "Mu ba matattu bane a ruhaniya har yanzu amma muna da rai a ruhu"
Kalmar nan "rai" a wannan wasiƙar gaba ɗaya ya wuci rai na jiki kawai. A nan ya tsaya ne madadin Yesu, rai na har abada. Duba yadda kun fasara wannan a [1:1-2]
"yana mace a ruhaniya har yanza"
Yahaya yana maganar mutumin da ke ƙin ɗan'uwansa maibi a matsayin mai kisankai ne. Tunda mutanen da ke kisan kai su na yin haka ne don sun ƙi sauran mutanen, Allah yana ɗaukan duk wanda ke ƙin wani a matsayin mai laifi kamar wanda ya kashe mutum ne. AT: Dukan wanda ya na ƙin ɗan'uwansa mai laifi ne daidai da wanda ya ƙashe mutum"
"Rai na har abada" wani abu ne da Allah ke ba masubi bayan sun mutu, amma shi ma wani iko ne da Allah ke ba wa masubi a wannan rai don ya taimake su su daina yin zunubi kuma su fara aikata abinda kan gamshe shi. An yi maganar rai na har abada kamar wani mutum ne da na iya zama a cikin mutum. AT: "mai kisan kai ba shi da ikon rayuwa na ruhaniya"
Wannan furcin na nufin "Almasihu ya yarda ya ba da ransa domin mu" ko kuma "Almasihu ya yarda ya mutu domin mu"
mallaka kamar kuɗi, abinci, ko sutura
"ya lura cewa ɗan'uwansa na bukatan taimako"
Anan Bai ji tausayinsa ba na nufin bai nuna masa ƙauna ba. AT: "bai nuna masa ƙauna ba" ko kuma "bai yarda ya taimake shi ba"
Yahaya yana amfani ne da wannan tambayan ya koyar wa masu sauraronsa. AT: "ƙaunar Allah bata cikinsa"
Yahaya tsohon mutum ne kuma shi ne shugabansu. Yayi amfani ne da wannan furci domin ya nuna yadda yake ƙaunarsu. AT: "Ƙaunatattun 'ya'yana a cikin Almasihu" ko kuma "Ku da kuke ƙaunatattu a gare ni kamar 'ya'yan kaina"
Wannan jumlar "ta fatar bãki" na nufin abinda mutum ke faɗi. An bayyana kalmar "ƙaunar" a bangare na biyu na jimlar. AT: "kada ku ce kuna ƙaunar mutane kawai, amma ku nuna cewa kuna matukar ƙaunar mutane ta wurin taimakonsu"
"mun zama masu gaskiya" AT: "muna rayuwa bisa yadda Yesu ya koya mana kenan"
Kalmar nan "zuciya" a nan na nufin yadda mutum ke ji. AT: "ba a zargin mu da laifi"
A nan "zuciya" na nufin tunani ko lamiri. A nan "zuciya na kayar da mu" na nufin zargi" AT" "idan mun san cewa mun yi zunubi kuma hakan ya jawo mana zargi"
A nan "zuciyar" na nufin tunani ko lamiri. "Allah ya fi zuciyarmu" na nufin Allah ya san fiye da mutum. Saboda haka, zai iya shar'anta abubuwa fiye da yadda mutum zai iya. Sakamakon wannan gaskiyar na iya nufin cewa Allah na da yawan jin ƙai fiye da yadda lamirinmu ke ɗauka. AT: "Allah ya sani fiye da mu"
"ku da nake ƙauna, idan" ko kuma "Ƙaunatattun abokai, idan". Duba yadda ku ka fasara wannan a aya [2:7]
Ana maganar ra'ayin Allah kamar ya danganta ne ga abinda yake gani na faruwa a gabansa. AT: "kuma muna yin abinda ya gamshi shi"
"umurni" da "doka" anan na nufin abu ɗaya ne. AT: "Wannan shi ne abinda Allah ya umurce mu mu yi." "Ba da gaskiya ... kamar yadda ya dokacemu muyi"
Wannan wata suna ce mai muhimmanci sosai na Yesu da ke bayyana dangartakansa da Allah.
A nan an bayyana dangantaka ta kusa da ke tsakanin masubi ta wurin amfani da "cikinsa." Dubi yanda aka fasara a [2:-6]
Uba ya ba su sunan 'ya'yan Allah.
A lokacin da Almasihu zai bayyana, ma su bi za su zama kamar Almasihu, kuma za su gan shi kamar yadda ya ke.
kowane mai bi da ya ke begen Almasihu ya tsarkake kansa.
Almasihu bashi da zunubi a cikinsa.
Duk wani mutum da ya cigaba a cikin zunubi bai taba ganin Almasihu ko san shi ba.
An bayyana Ɗan Allah domin a rushe ayukkan shaidan.
Ana bayyana 'ya'yan Allah ta wurin ayukkan adalci, kuma ana bayanna 'ya'yan shaidan ta wurin zunuban su.
Halin kauna zuwa ga masu bi ya na nuna cewa mutum ɗan Allah ne.
Kayinu ya nuna cewa shi ɗan mai mugunta ne a lokacin da ya kashe ɗan'uwansa.
Yahaya ya ce wa masubi kada su yi mamaki cewa duniya ta ƙi su.
Halin kauna zuwa ga masubi ya na nuna cewa mutum ɗan Allah ne.
Mun san menene kauna domin Almasihu ya ba da ransa domin mu.
A lokacin da akwai ɗan'uwa mai bukata, mai bi zai nuna kaunar Allah ta wurin taimakon sa da abubuwa na duniya.
A lokacin da mai bi ya nuna kaunar Allah a cikin aiki da gaskiya, ya na samun wa kansa tabbatarwa da amincewa zuwa ga Allah.
Yahaya yana tuna wa masubi game da umarnin Allah na yin ĩmanĩ da sunan Ɗansa Yesu Almasihu da kuma su kaunace juna.
Allah ya ba wa masubi Ruhu don su sani Allah na kasancewa a cikin su.
1 Kaunatattu, kada ku amince da kowanne ruhu. Amma ku gwada ruhohi ku gani ko na Allah ne, gama annabawan karya masu yawa sun fito zuwa cikin duniya. 2 Ta haka zaku gane Ruhun Allah, dukkan ruhun da ya amince Yesu Almasihu ya zo cikin jiki na Allah ne, 3 kuma dukkan ruhun da bai amince da Yesu ba, ba na Allah bane. Wannan ruhun magafcin Almasihu ne, wanda kuka ji cewa yana zuwa, ya kuwa rigaya yazo cikin duniya. 4 'Ya'yana kaunatattu, daga Allah ke, kuma kun rigaya kun yi nasara da su da yake wanda ke cikinku ya fi wanda ke cikin duniya girma. 5 Su na duniya ne, saboda haka abin da suke fadi na duniya ne, duniya kuma tana sauraronsu. 6 Mu na Allah ne, duk wanda ya san Allah yana saurarenmu. Wanda ba na Allah bane, ba ya sauraronmu. Ta haka muka gane ruhun gaskiya da ruhun karya. 7 Kaunatattu, mu yi kaunar juna, gama kauna ta Allah ce, wanda yake kauna an haife shi daga wurin Allah, kuma ya san Allah. 8 Mutumin da baya kauna ba na Allah ba ne, kuma bai san Allah ba, gama Allah kauna ne. 9 A cikn haka aka bayyana kaunar Allah a garemu, Allah ya aiko tilon Dansa cikin duniya domin mu rayu ta wurinsa. 10 A cikin wannan akwai kauna, ba mune muka kaunaci Allah ba, amma shi ya kaunace mu ya aiko da Dansa ya zama mai gafarta zunubanmu. 11 Kaunatattu, da yake Allah ya kaunace mu haka, ya kamata mu kaunaci junanmu. 12 Ba wanda ya taba ganin Allah. Idan muna kaunar juna, Allah yana zaune cikinmu, kuma kaunarsa tana zaune a cikinmu. 13 Ta haka mun sani muna zaune a cikinsa shi kuma a cikinmu, saboda ya bamu Ruhunsa. 14 Mun gani mun shaida, cewa Allah ya aiko Dan, domin ya zama mai ceton duniya. 15 Duk wanda ya amince Yesu Dan Allah ne, Allah na zaune cikinsa, shi kuma a cikin Allah. 16 Mun sani kuma mun gaskata da kaunar da Allah yake da ita dominmu, Allah kauna ne wanda yake zama cikin kauna yana zaune cikin Allah, Allah kuma a cikinsa. 17 Dalilin wannan kauna ta kammala a cikinmu, domin mu kasance da gabagadi a ranar shari'a, domin kamar yanda ya ke haka muma muke a cikin duniyan nan. 18 Babu tsoro a cikin kauna. Amma cikkakiyar kauna takan kawar da tsoro, domin kuwa tsoro na tafi tare da hukunci. Amma wanda yake da tsoro ba shi da cikkakiyar kauna. 19 Muna kauna domin Allah ne ya fara kaunarmu. 20 Idan wani ya ce,"Ina kaunar Allah", amma yana kin dan'uwansa, makaryaci ne. Domin wanda baya kaunar dan'uwansa da yake gani, ba zai iya kaunar Allah da bai taba gani ba. 21 Wannan ne umarnin da muke da shi daga wurinsa: Duk wanda yake kaunar Allah dole ne ya kaunaci dan'uwansa.
Yahaya yana bada kashedi wa malaman ƙarya wadda suke musun cewa Yesu yana da jikin mutum da malaman da ke magana kamar yadda waɗanda ke ƙaunar duniya ke yi.
"ku mutanen da nake ƙauna, kada ku amince da" ko kuma "Ƙaunatattu abokai, kada ku amince da." Duba yadda kun fasara wannan a [2:7].
A nan, Kalmar nan "ruhu" na nufin ikokin ruhu ko kuma wani halitta da ke ba mutum wata sako ko anabci. AT: "kada ku amince da kowane annabi da ke cewa ya karɓi sako daga wani ruhu"
A nan, kalmar nan "ruhohi" na nufin ikokin ruhaniya ko kuma wani halittada ke ba mutum wani sako ko anabci. AT: "yi tunani a hankali game da abinda annabin ke faɗi"
A nan "jiki" na nufin jikin mutum. AT: "ya zo a matsayin rayayyen mutum" ko kuma "ya zo a wannan jiki da muke iya gani"
Waɗannan ne annabawan da ke gãba da Almasihu, wadda kuka ji cewa suna zuwa, sun kuwa zo cikin duniya"
Yahaya tsohon mutum ne kuma shi ne shugabansu. Yayi amfani ne da wannan furci domin ya nuna yadda yake ƙaunarsu . AT: "ƙaunatattu 'ya'yana a cikin Almasihu" ko kuma "ku da kuke ƙaunatattu a gare ni kamar 'ya'yan kaina"
"baku amince da malaman ƙaryan ba"
"Allah, wanda ke cikinku ya"
Wannan na iya nufin 1) shaiɗan AT: "Shaiɗan, da ke duniya" ko kuma "Shaiɗan, da ke amfani da waɗanda ba su biyayya da Allah" ko kuma 2) masu koyas da abubuwan duniya AT: "masu koyas da abubuwan duniya" (Dubi: )
Wannan na nufin cewa suna samun ikonsu daga duniya ne. "duniya" kuma na nufin "wanda ke cikin duniyan", Shaiɗan. Ko da shike yana kuma iya nufin masu aikata zunubi waɗanda suke jin su suna kuma basu ƙarfi.
"duniya" a nan na nufin "shi wanda ke cikin duniya," Shaiɗan. Ko da shike yana kuma iya nufin masu aikata zunubi waɗanda suke jin su suna kuma basu ƙarfi. AT: "saboda haka suna koyar da abin da suka koya daga mutane masu aikata zunubi"
Kalmar nan "duniya" na nufin mutanen da basu biyayya da Allah. AT: "don haka mutanen da basu biyayya da Allah suna sauraronsu"
"ku mutanen da nake ƙauna, kada ku amince da" ko kuma "Ƙaunatattu abokai, kada ku amince da." Duba yadda kun fasara wannan a [2:7].
"yakamata masubi su ƙaunace sauran masubi"
"kuma domin waɗanda suke ƙaunar 'yan'uwansu masubi sun zama 'ya'yan Allah sun kuma san shi"
"domin Allah ne yakan sa mu mu ƙaunace juna"
Wannan na nufin mutumin da ke da dangantaka da Allah kamar yadda ɗa yake da ubansa.
Jimlar nan "Allah ƙauna ne" na nufin "halin Allah ƙauna ne." AT: "Waɗanda ba su ƙaunar 'yan'uwansu masubi basu san Allah ba domin halin Allah shi ne a ƙaunace mutane.
A cikin haka ... a garemu: Allah ya aiko tilon Ɗansa." Jumlar "A cikin haka" na nufin jumlar nan "Allah ya aiko da tilon Ɗansa."
Ana iya fasara "ƙauna" zuwa kalmar aiki. AT: "Allah ya nuna cewa yana ƙaunar mu"
"domin ya sa mu rayu har abada saboda abinda Yesu yayi"
"Allah ya nuna mana abinda ake nufi da sahihiyar ƙauna"
A nan "gafartawa" na nufin mutuwar Yesu a bisa giciye ya kwantar wa Allah da fushinsa saboda zunubi. AT: "ya aiko Ɗansa ya zama hadayar da ya kwantar wa Allah zuciya saboda zunubanmu"
"ku mutanen da nake ƙauna, kada ku amince da" ko kuma "Ƙaunatattu abokai, kada ku amince da." Duba yadda ku ka fasara wannan a [2:7].
"tunda Allah ya ƙaunace mu haka"
"ya kamata masubi su ƙaunaci sauran masubi"
Zama a cikin mutum na nufin cigaba da zumunta da shi. Dubi yadda ku ka fasara wannan a [2:5-6] AT: "Allah yana cigaba da zumunta da mu ... mu cigaba da zumunta da Allah shi kuma zai cigaba da zumunta da mu" ko kuma "Allah yana haɗe da mu ... mu kuma muna a haɗe da Allah shi kuma yana haɗe da mu"
AT: "shi kuma yana zaune da mu"
"ƙaunar Allah ta cikă a cikinmu"
Fasarar ku na iya fin ba da haske idan kun cire ko "ta haka" ko kuma "saboda" AT: "mun sani ... mu saboda ya bayar" ko kuma "Ta haka mun sani ... mu: ya bayar"
"kuma mu manzannin mun ga Ɗan Allah mun kuma faɗa wa kowa cewa Allah Uban ya aiko Ɗansa ya ceci mutanen da ke wannan duniyan"
Waɗannan wasu sunaye ne da ke bayyana dangantakar da ke tsakanin Allah da Yesu
"Duk wanda ya faɗi gaskiya game da Yesu, cewa shi Ɗan Allah ne"
Wannan wata suna ce mai muhimmanci na Yesu wadda ke bayyana dangantakasa da Allah.
A zauna a cikin mutum yana nufin a cigaba da dangantaka da shi. Dubi yadda ku ka fasara wannan a [2:5-6]. AT: "Allah yana cigaba da zumunta da shi kuma yana cigaba da dangantaka da Allah" ko kuma "Allah yana haɗe da shi shi kuma yana haɗe da Allah"
AT: "shi kuma yana zaune a cikin Allah" (Dubi: Ellipsis)
Wannan na nufin cewa halin Allah ƙauna ne." Dubi yadda kuka fasara wannan a [4:8]
"waɗanda sun cigaba da ƙaunan wasu"
A zauna a cikin mutum na nufin a cigaba da dangantaka da shi. Dubi yadda ku ka fasara wannan a [2:5-6]. AT: "na cigaba da dangantaka da Allah, kuma Allah na cigaba da dangantaka da shi" ko kuma "yana haɗe da Allah, Allah kuma yana haɗe da shi"
Wannan na iya nufin 1) "Dalilin wannan" na maida tunanin mu baya zuwa [4:16]. AT: Domin duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna yana cikin Allah, Allah kuma yana cikinsa. Allah ya cika ƙaunar da yake da shi domin mu saboda haka muna da cikakken gabagaɗi" ko kuma 2)"Saboda haka" na nufin "za mu iya samun gabagaɗi". AT: Muna da gabagaɗi cewa Allah zain karɓe mu a ranar da zai shari'anta kowa, don haka mun san irin ƙaunar da yake da shi domin mu"
AT: Allah ya sa ƙaunarsa domin mu yă zama cikakke"
"domin dangantakar da Yesu ke da shi da Allah ɗaya ne da dangantakar da muke da shi da Allah a duniyan nan"
A nan an fasara "ƙauna" kamar wani mutum ne da ke da ikon cire tsoro. Ƙaunar Allah kamalalle ne. AT: "Amma sa'and da ƙaunar mu ta cika, ba za mu ji tsoro kuma ba"
"domin za mu ji tsoro ne kaɗai idan mun san cewa zai hukunta mu"
AT: "Amma idan mutum yana da tsoron cewa Allah zai hukunta shi, ƙaunarsa bai cika ba"
"yana ƙin ɗan'uwansa mai bi"
Idan maganganun biyu a jeri ɗaya na kawo rikecewa, ana iya fasara su dabamdabam. AT: "wanda yake kin ɗan'uwansa, wadda yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah ba, wadda bai taɓa gani ba"
Yahaya ya gargadin masubi domin akwai annabawan ƙarya da suka shiga duniya.
Kowane ruhu da ya ke shaidan Yesu Almasihu ya zo a naman jiki na Allah ne.
Ruhun makiyin kristi ba ya shaidan cewa Yesu Almasihu ya zo a naman jiki.
Ruhu mafi girma shine wanda ke cikin masubi, yafi ruhohin da ke a duniya.
Masubi suna kaunar juna, wanda ke nuna sun san Allah, domin Allah shine Kauna.
Allah ya bayyana kaunarsa ta wurin aiko da Ɗansa haifaffe shi kadai cikin duniya.
Uban ya aiko Ɗansa domin idan yiwu mu yi rayuwa ta wurin sa.
Masubi na gaskiya suna shaidar Yesu shine Ɗan Allah.
Waɗanda suka kasance cikin kauna da kuma cikin Allah za su sami amincewa a ranar shari'a.
Muna kauna domin Allah ya kaunace mu a farko.
Wanda ya ki ɗan'uwansa ba zai iya kaunar Allah ba.
Waɗanda suke kaunar Allah ya zama tilas su kuma kaunace ɗan'uwansu.
1 Duk Wanda ya gaskata Yesu shine Almasihu haifaffe na Allah ne. Kuma duk wanda ya kaunaci uba ya kaunaci dan da uban ya haifa. 2 Haka muka sani muna kaunar 'ya'yan Allah: yayin da muka kaunaci Allah, kuma muka aikata umarninsa. 3 Wannan itace kaunar Allah, cewa mu kiyaye umarninsa. Domin umarninsa ba masu nawaitawa bane. 4 Duk wanda yake haifaffe na Allah yakan yi nasara da duniya. Wannan itace nasarar da ta rinjayi duniya, wato bangaskiyarmu. 5 Wanene wannan mai nasara da duniya? Sai dai wanda ya gaskata Yesu Dan Allah ne. 6 Wannan shine wanda yazo ta wurin ruwa da jini: Yesu Almasihu. Ya zo ba ta wurin ruwa kadai ba, amma ta wurin ruwa da jini. 7 Domin akwai uku wadanda suke bada shaida: 8 Ruhu, da ruwa, da kuma jini. Wadannan ukun kuwa manufarsu daya ce. 9 Idan mun karbi shaidar mutane, shaidar Allah ta fi girma. Wannan ita ce shaidar Allah, wato ya bada shaida akan Dansa. 10 Wanda ya gaskata da Dan Allah shaidar tana nan tare da shi. Duk wanda bai bada gaskiya ga Allah ba, ya mai da shi makaryaci kenan, domin bai gaskata da shaidar da Allah ya bayar game da Dansa ba. 11 Wannan ita ce shaida: Allah ya bamu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Dansa. 12 Duk wanda yake da Dan, yana da rai. Duk wanda ba shida Dan Allah kuwa bashi da rai. 13 Na rubuto maku wannan ne don ku tabbata kuna da rai madawwami--a gare ku wadanda suka gaskata da sunan Dan Allah. 14 Wannan shine gabagadin da muke da shi a gabansa, wato, in mun roki kome bisa ga nufinsa, zai ji mu. 15 Haka kuma, in mun san yana jinmu--Duk abin da mu ka rokeshi--mun sani muna da duk abin da muka roka daga gare shi. 16 Idan wani ya ga dan'uwansa ya yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yayi masa addu'a, Allah kuwa zai ba shi rai. Ina nufin wadanda suka yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yake kai wa ga mutuwa: Ban ce a yi addu'a domin wannan ba. 17 Dukkan rashin adalci, zunubi ne, amma akwai zunubin da bai kai ga mutuwa ba. 18 Mun sani kowanne haiffafe daga wurin Allah ba ya yin zunubi. Amma wanda ke haifaffe daga wurin Allah, ya kan kare shi, mugun nan kuwa ba zai iya yi masa illa ba. 19 Mun sani mu na Allah ne, mun kuma sani dukkan duniya tana hannun mugun nan. 20 Amma mun sani Dan Allah yazo, kuma ya bamu fahimta, domin mu san wanda yake shi ne mai gaskiya. Haka kuma muna cikin wannan wanda shine gaiskiya, kuma cikin Dansa Yesu Almasihu. Shine Allah na gaskiya, da kuma rai na har abada. 21 'Ya'ya, ku tsare kanku daga bautar gumaka.
Yahaya yana cigaba da koyaswa masu karatun wasiƙarsa game da ƙaunar Allah da kuma ƙaunar da yakamata masubi su kasance da ita domin sun samu wata sabuwan halitta daga Allah.
"ɗan Allah ne"
"Yayin da mun ƙaunaci Allah mun kuma kiyaye umarninsa, toh mun san cewa muna ƙaunar 'ya'yansa"
"Domin yayin da mun kiyaye umarninsa, shi ne ƙaunar Allah ta gaskiya"
"Umarninsa ba masu wuya bane"
"nauyi" ko "murkushewa" ko "wuya"
"duk 'ya'yan Allah sukan yi nasara"
"na da nasara a kan duniya" ko kuma "suna kin aikata miyagun abubuwan da marasabi ke yi"
A nan "duniya" na nufin dukan mutane masu aikata zunubi da kuma sha'anin miyagu da ke duniya. AT: "dukan abin duniya da ke gãba da Allah"
"Wannan itace abinda ke bamu ikon tsayayya da duk abinda zai kai mu ga yi wa Allah zunubi: bangaskiyar mu" ko kuma "Bangaskiyar mu ne ke bamu ikon tsayayya da duk abinda zai kai mu ga yi wa Allah zunubu"
Yahaya ya yi amfani ne da wannan tambayan ya gabatar da wata sabuwan abu da yake so ya koyar. AT: "Ni zan gaya maku wanda ke mai nasara da duniya"
Wannan na nufin ko ma wa, duk dai wanda ya gaskata da haka. AT: "Duk wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne"
Wannan wata suna ce mai muhimmanci na Yesu wadda ke bayyana dangantakarsa da Allah.
Yahaya yana koyarwa a kan Yesu Almasihu da kuma abinda Allah ya faɗi game da shi.
Yesu Almasihu shi ne wanda ya zo ta wurin ruwa da jini. A nan "ruwa" na iya nufin baftismar Yesu, "jini" kuma na iya zama alama ce ta mutuwar Yesu a bisa giciye. AT: "Allah ya nuna cewa Yesu Almasihu Ɗansa ne ta wurin baftismar Yesu da mutuwarsa a bisa giciye"
A nan "ruwa" na nufin baftismar Yesu, "jini" kuma na iya zama alama ce ta mutuwar Yesu a bisa giciye. AT: "Ba ta baftisma ne kawai Allah ya nuna mana cewa Yesu Ɗansa ba ne, amma ta wurin baftismarsa da mutuwarsa a bisa giciye"
Mai fasara na iya ƙarin bayani game da dalilin ya sa yakamata mu gastata da abinda Allah ke faɗi: AT: "idan mun gaskata da abinda mutane ke faɗi, toh sai mu gaskata da abinda Allah ke faɗi domin shi mai faɗin gaskiya ne a ko da yaushe"
Wannan, wato "karɓi shaidar", na nufin a gaskata da abinda wani ke faɗi game da wani abinda ya gani. AT: "gaskata da abinda mutane sun shaida" ko kuma "gaskata abinda mutane ke faɗi game da abinda suka gani"
shaidar Allah ta fi muhimmanci da abin dogaro
Wannan wata suna ce ta Yesu, Ɗan Allah
"Duk mai gaskata da Yesu ya sani da tabbaci cewa Yesu Ɗan Allah ne"
"ya ce da Allah maƙaryaci"
"domin bai gaskata cewa Allah ya faɗi gaskiya game da Ɗansa ba"
"Ga abinda Allah ke faɗi"
A nan "rai" na madaɗin yancin rayuwa har abada ta wurin Alheri da ƙaunar Allah. Dubi yadda ku ka fasara wannan a [1:1-2]
"wannan rai ta wurin Ɗansa ne" ko kuma "Zamu rayu har abada idan muna manne da Ɗansa" ko kuma "Zamu rayu har abada indan mun haɗa kai da Ɗansa"
An yi maganar samun dangantaka na kusa da Ɗan kamar shi ne samun Ɗan. AT: "Shi wanda ke gaskata da Ɗan Allah na da rai. Shi wanda bai gaskata da Ɗan ba ba shi da rai na har abada"
"wannan wasiƙa"
A nan "suna" na nufin Ɗan Allah. AT: "ku da kuka gaskata da Ɗan Allah"
AT: "Muna da gabagaɗi a gaban Allah don mun san cewa"
"idan mun roƙi abubuwan da Allah ke so"
"mun san cewa zamu samu abinda muka roƙa daga Allah"
"ɗan'uwansa maibi"
Wannan na nufin mutuwa na har abada, wato rayuwa na har abada da ba ayi a gaban Allah.
Wannan jumlar "mugun nan" na nufin Shaiɗan, ibilis.
kasancewa a hannun mutum na nufin bishewarsa ko kuma mulkinsa. AT: "mugun ne ke bi da duniya"
A nan "duniya" wata hanya ce da marubutan Littafi ke nufin mazauna cikin duniya da ke tawaye da Allah da kuma tsarin duniya da ke lalace saboda ikon zunibi.
"ya iza mu mu fahimci gaskiyar"
kansancewa a "cikin" mutum na nufin samun dangantaka ta kusa da shi, wato a haɗe da shi ko kuma ku zama nashi. Wannan jumlar "shi ne gaskiya" na nufin Allah mai gaskiya, sa'annan jumlar nan "a cikin Ɗansa Yesu Almasihu" na bayyana yadda muke a cikinsa mai gaskiya. AT: "muna haɗe da shi mai gaskiya ta wurin haɗa kai da Ɗansa Yesu Almasihu"
"mai gaskiya" ko "Allah na asali"
"shi ne" na nufin Yesu Almasihu
Ana ce da shi "rai na har abada" domin shi ne ke ba mu rai na har abada. AT: "da kuma wadda ke ba da rai na har abada"
Yahaya tsohon mutum ne kuma shi ne shugabansu. Yayi amfani ne da wannan furci domin ya nuna yadda yake ƙaunarsu . AT: "ƙaunatattun 'ya'yana a cikin Almasihu" ko kuma "ku da kuke ƙaunatattu a gare ni kamar 'ya'yan kaina"
"ku yi nesa da gumakai" ko "kada ku bauta wa gumaka"
Muna nuna mu na kaunar Allah a lokacin da muka ajiye dokokinsa.
Nasaran da ya shawo kan duniya shine bangaskiyar mu.
Yesu Almasihu ya zo ta ruwa da jini.
Ruhu, ruwa, da kuma jini duka suke shaidar Yesu Almasihu.
Duk wanda bai yi ĩmanĩ da kuma shaidar da Allah game da Ɗansa ba, ya na zamar da Allah makaryaci.
Allah ya bamu rai na har abada a cikin Ɗansa.
Masubi suna amincewa idan suka tambayi kowane bisa ga nufin Allah, yana sauraron su.
Ya zama tilas ma mai bi wanda ya gan ɗan'uwansa ya na zunubi wanda ba na zuwa ga mutuwa ba ya yi masa adu'a don Allah ya ba wa ɗan'uwansa rai.
Duka rashin adalci shine zunubi.
Dukkan duniya tayi ƙarya a cikin mai mugunta.
Allah na gskiya shine Uban Yesu Almasihu.
Ya zama tilas ne Masubi su ajiye kansu daga gumaka.
1 Daga dattijon zuwa ga uwar gida zababbiya da yayanta, wadanda nake kauna da gaskiya, ba ni kadai ba, amma da dukan wadanda sun san gaskiya - 2 domin gaskiya da take cikinmu za ta kuma kasance tare da mu har abada. 3 Alheri da jinkai da salama za su kasance tare da mu, daga Allah Uba da kuma daga Yesu Almasihu Dan Uba, a cikin gaskiya da kauna. 4 Na yi murna sosai sa'anda na sami wadansu yayanki suna tafiya cikin gaskiya, kamar yadda muka karbi wannan umarni daga Uba. 5 Yanzu ina rokon ki, uwar gida, ba kamar ina rubuta maki sabon umarni ba, amma wannan da muka samu tun da can, cewa mu kaunaci junanmu. 6 Wannan kuma itace kauna, cewa mu yi tafiya bisa ga umarnin sa. Wannan shine umarnin, daidai kamar yadda kuka ji da fari, da cewa ku yi tafiya a cikinsa. 7 Gama masu yaudara sun fito a duniya, wadanda ba su yarda cewa Yesu ya zo cikin jiki ba. Wannan ne mayaudari da kuma magabcin Almasihu. 8 Ku dubi kanku, domin kada ku rasa abubuwan da mu duka muka yi aiki a kansu, amma domin ku karba dukan sakamon ku. 9 Duk wanda ya ci gaba da tafiya ba cikin koyarwa Almasihu ba, ba shi da Allah. Wanda ya zauna cikin koyarwar kwa yana tare da Uban da kuma Dan. 10 Duk wanda ya zo wurinku, ba tare da wannan koyarwar ba, kar ku karbe shi cikin gidanku, kada ma ku gaishe shi. 11 Domin duk wanda ya gaishe shi ya yi tarayya da shi kenan cikin miyagun ayyukan sa. 12 Ina da abubuwa dayawa da nake so in rubuta maki amma al'kalami tawada da takarda baza su iya daukar su duka ba. Amma duk da haka ina begen zuwa gare ki domin mu yi magana fuska da fuska, domin farin cikn mu ya zama cikakke. 13 Yayan yar'uwarki zababbiya suna gaishe ki.
Bisa ga al'ada, Yahaya manzo ne marubucin wannan wasiƙar. Kodashike yana iya yiwuwa ya rubuta zuwa ga wata mace ce, amma domin ya rubuta cewa su "ƙaunaci juna", mai yiwuwa wannan zuwa ga wata ikilisiya ce.
Haka ake fara rubuta wasiƙa. Ana iya bayyana sunan marubucin. AT: "Ni, dattijo Yahaya, ina rubuta wannan wasiƙar zuwa ga uwar gida zaɓaɓɓiya da 'ya'yanta"
Wannan na nufin Yahaya ne, manzo da kuma almajirin Yesu. Ya kira kansa "dattijo" domin tsufansa ne ko kuma domin shi shugaba ne na ikilisiya.
Mai yiwuwa wannan na nufin taron jama'a da kuma masubi da suke a wurin.
"ku, mutanen da nake ƙauna da gaske"
waɗanda suka san gaskiya game da Allah da kuma Yesu
Waɗannan muhimman sunaye ne da ke bayyana dangantaka tsakanin Allah da kuma Yesu.
Kalmar nan "gaskiya" ta na bayyana "ƙauna." Mai yiwuwa ana nufin "cikin kauna ta gaskiya."
"kamar yadda Allah Uba ya umurce mu"
"ba kamar ina umurtar ki yin wani sobon abu ba ne"
A nan "farko" na nufin "tun lokacin da muka gaskata." AT: "amma ina rubuta maku abin da Almasihu ya umurce mu tun lokacin farko da muka gaskata."
Ana iya fasarar wannan kamar sabon magana. AT: "afarko. Ya umurce mu cewa mu ƙaunaci junanmu"
Anyi magana game da gudanar da rayuwar mu bisa ga umurnin Allah kamar muna tafiya cikinsu ne. Kalmar nan "shi" na nufin ƙauna. "Kuma ya umurce ku, tun farko da kuka gaskanta, ku yi ƙaunar juna"
Yahaya ya gargaɗe su game da masu yaudara, ya tunashe su domin su cigaba cikin koyaswar Almasihu, kuma ya gargaɗesu da su guje wa waɗanda ba su tsaya cikin koyaswa na Almasihu ba.
"Gama malaman ƙarya dayawa sun bar cikin taron" ko "Gama masu yaudara dayawa suna cikin duniya"
"malamen ƙarya dayawa" ko "masu ruɗi dayawa"
Zuwa cikin jiki kalmomi ne da aka mora domin nuna ainihin mutum. AT: "Yesu Almasihu ya zo ne a matsayin ainihin ɗan Adam"
"Su ne waɗanda suka yaudari wasu suka kuma ki goyon bayan Almasihu kansa"
"Yi la'akari" ko "Maida hankali"
"rasa lada mai zuwa a sama"
"cikakken sakamako a sama"
Wannan na nufin mutumin da yake nuna sani game da Allah da kuma gaskiya fiye da kowa. AT: "Duk wanda ya ce yana da sani mafi yawa game da Allah" ko "Duk wanda yayi rashin biyayya ga gaskiya"
" shi ba na Allah bane"
"Wanda yake bin koyaswar Almasihu yana tare da Uban da kuma Ɗan"
Waɗannan muhimman sunaye ne da ke bayyana dangantaka tsakanin Allah da kuma Yesu.
A nan wannan na nufin marabtarsa da kuma martaba shi domin gina dangantaka da shi.
"ya goyi bayan shi cikin miyagun ayyukan sa" ko "ya taimake shi cikin miyagun ayyukan sa"
Yahaya bai so ya rubuta sauran waɗannan abubuwan ba, amma zai so ya zo ya faɗa masu. Bai faɗa masu cewa zai rubuta masu da wani abu dabam da alƙalami, tawada da kuma takarda ba.
"Fuska da fuska" a nan na nufin yin magana a gabansu. AT: "yi magana a gabanku" ko "yi magana da ku"
A nan, Yahaya na magana game da ikilisiyar da ke tare da shi kamar 'yar'uwar wanda take karanta watsiƙar shi, da kuma masubi da ke tare da ita kamar 'ya'yan ta ne. Wannan na nanata cewa dukan masubi 'ya'yan iyali ɗaya ne cikin ruhu .
Yahaya ya gabatar da kansa kamar babba duka.
An rubuta wannan wasiƙar zuwa ga zaɓabɓiyar budurwa da kuma 'yayan ta
Yahaya ya ce alheri, rahama, kuma salama su kasance daga Allah Ubba da kuma Yesu Almasihu ɗansa.
Yahaya na farin ciki ne soboda ya samu wasu 'yayan budurwar na tafiya a gaskiya.
Yahaya ya ce suna da dokoki na kaunar ma juna daga farko.
Yahaya ya ce Kauna shine a yi tafiya bisa ga dokokin Allah.
Yahaya ya kira waɗanda basu furta cewa Yesu Almasihu ya zo a cikin jiki ba mayaudara da kuma maƙiyan Kristi.
Yahaya ya gaya wa masu bi su yi hankali kada su rasa abubuwan da suka aikata.
Yahaya ya gaya wa masu bi kada su karbi kowa wanda bai kawo koyarwa na gaskiya ba game da Almasihu.
Yahaya ya gaya wa masubi kada su karɓi duk wanda bai kawo gaskiyar koyi game da Kristi ba.
Yahaya na fatan ya zo ya kuma yi magana fuska da fuska da zaɓabɓiyar budurwar.
1 Daga dattijon zuwa ga Gayus, wanda nake kauna da gaske. 2 Ya kaunatace na, ina addu'a domin ka samu albarka cikin kowanne al'amari, da kuma koshin lafiya, kamar yadda ruhun ka yake lafiya. 3 Na yi farin ciki kwarai sa'adda wadansu 'yan'uwa suka zo suka ba da shaida a kan bangaskiyar ka, kamar yadda ka ke bin gaskiya. 4 Ba abin da ya fi faranta mani rai kamar in ji yayana suna tafiya cikin gaskiya. 5 Ya kaunatace na, kana aiki da aminci zuwa ga 'yan'uwa da baki, 6 wadanda suka shaida kaunar ka a gaban ikilisiya. Zai yi kyau ka yi masu taimako da kyakkyawar salama, ta hanyar da ta dace da masu ibada, 7 domin sabili da sunan nan ne suka fito, ba su kuma karbar kome a hannun al'ummai. 8 Don haka ya kamata mu karbi irin wadannan mutane, domin mu zama abokan aiki tare da su a kan gaskiya. 9 Na rubuta wasika zuwa ga ikilisiya, amma Diyotariffis, wanda ya fi kowa son girma a cikinsu, bai karbe mu ba. 10 Saboda haka, idan na zo, zan tuna masa da irin ayukkan sa, da kuma yadda yake babbata sunayen mu a wurin jama'a da miyagun kalmomi. Wannan ma bai ishe shi ba, har ma yana kin karbar 'yan'uwa. Ya kuma hana wadanda suke son su yin hakan, harma ya kan kore su daga ikilisiya. 11 Ya kaunatace na, kada ka yi koyi da mugun abu, sai dai abu mai kyau. Dukan wanda yake yin abu mai kyau na Allah ne; mai aikata mugunta kuma bai san Allah ba. 12 Dimitiriyas yana da kyakkyawar shaida a gun kowa har a wurin gaskiyar da kanta. Mu ma mun shaida shi, ka kuma san shaidar mu gaskiya ce. 13 Ina da abubuwa dayawa da zan rubuta maka, amma ban so in rubuta maka su da alkalami da tawada ba. 14 Ina sa zuciya mu sadu ba da dadewa ba, sa'annan mu yi magana ido da ido. 15 Bari salama ta kasance tare da kai. Abokanmu suna gaishe ka, kuma ka isadda sakon gaisuwar mu ga sauran abokai da sunayen su.
Wannan wasiƙa ce daga Yahaya zuwa ga Gayus. Dukan inda aka mori "ka" ana nufin Gayus ne.
Wannan ya na nufin Yahaya, manzo da kuma almajirin Yesu. Watakila ya kira kansa "dattijo" saboda shekarunsa ko kuma domin shi shugaba ne a ikillisiya. Ana iya sa sunan marubucin a bayyane. "Ni, Yahaya dattijo, ina rubutu."
Wannan ɗan'uwa mai bi ne wadda Yahaya ya rubuto masa wannan wasiƙan.
"wadda na ke ƙauna ta gaskiya"
"ku kasance da nasara cikin kowanne al'amari, ka kuma kasance da ƙoshin lafiya"
"kamar yadda kake lafiya a ruha"
"yan'uwa masubi sun zo." Da alama waɗannan mutanen maza ne duka.
Tafiya a hanya, na nufin yadda mutum yake rayuwarsa. AT: "Ku na rayuwar ku a bisa gaskiyar Allah"
Yahaya yana magana game da wadda ya koyar da su game da bangaskiya cikin Yesu kamar su 'ya'yansa ne. Wannan ya na nanata ƙaunarsa garesu da kulawa da yake da shi dominsu. Yana kuma iya zama cewa shi ne ya kai su ga sanin Ubangiji. AT: " 'ya'yana na ruhu"
Yahaya ya rubuta wannan wasiƙa ne domin ya yaba wa Gayus da yadda ya riƙe mallamai na Littafi masu tafiye tafiye; sai ya yi magana game da mutane biyu , ɗaya mai halin kirki da kuma ɗaya mai hali marar kirki.
A nan ana amfani da kalmar ƙauna domin yan'uwa masubi.
"kana aiki da aminci ga Allah" ko kuma "ka na biyayya da Allah"
"taimaki 'yan'uwa masubi da waɗanda ba ku sansu ba"
"baƙi waɗanda suka faɗa wa masubi a cikin ikilisiya game da yadda ka ƙaunace su"
Yahaya ya na gode wa Gayus domin taimako da ya saba yi wa waɗannan masubi.
A nan "sunan" na nufin Yesu. AT: "saboda sun fita domin su gayawa mutane game da Yesu"
babu karɓar kyauta ko kuma taimako
A nan "Al'umman" ba yana nufin mutane da ba Yahudawa kaɗai ba. Ya na nufin mutane da ba su dogara da Yesu ba.
"domin mu hada kai da su a sanar da gaskiyar Allah ga mutane"
Wannan ya na nufin Gayus da kungiyar masubi waɗanda sukan haɗu domin su bauta wa Allah.
Shi ɗan taron ne.
"wanda ya fi son kasancewa da muhimminci a tsakaninsu" ko kuma "wanda ya na son yi kamar shi ne shugabansu"
"da kuma yadda ya ke faɗin mugayen abubuwa game da mu da ba gaskiya ba"
"bai karɓi 'yan'uwa masubi ba"
"hana waɗanda suke so su karɓi masubi"
"ya tilasa masu su bar taron"
"kada ka yi koyi da mugayen abubuwa da mutane suke yi"
AT: "Amma ka yi koyi da abubuwa masu kyau da mutane su ke yi"
"ya zama na Allah ne"
"ba na Allah ba ne" ko kuma "bai gaskata da Allah ba"
AT: "Dukan waɗanda sun san Dimitiriyas suna shaida shi" ko kuma "Kowane mai bi da ya san Dimitiriyas ya na magana mai kyau game da shi"
Mai yiwuwa wannan mutumin ne Yahaya ya ke so Gayus tare da taron masubi su marabce shi a lokacin da zai ziyarce su.
"gaskiya da kanta tana shaidar shi." A nan an kwatanta "gaskiya" kamar mutum ne da ke magana. AT: "Dukan wadda ya san gaskiyan ya san cewa shi mutumin kirki ne"
Wannan ya na tabbatar da abin da Yahaya yake nufi a nan. AT: "Mun kuma yi magana da kyau game da Dimitiriyas"
Yahaya ba ya so ya rubuta waɗannan abubuwa ko kaɗan. Ba wai ya na ce wa zai rubuta masu wasiƙa da wani abu dabam da alƙalami da kuma tawada ba.
"ido da ido" na nufin "da kansa." AT: "da kansa"
"Bari Allah ya ba ku salama"
"Abokai a nan suna gaishe ka"
"ka isadda sakon gaisuwa na ga masubi a can"
Yahaya ya gabatar da kansa a sunan datijjo.
Yahaya ya na kaunar Gayus a cikin gaskiya.
Yahaya yayi adu'a cewa Gayus ya ɓunkasa a cikin kowane abu ya kuma zama da lafiya, kamar yadda ruhunsa ya ke ɓunkasa.
Babban farin cikin Yahaya shine y ji cewa yaranshi suna tafiya cikin gaskiya.
Gayus ya yi marabci ya kuma aika su a tafiyarsu wasu waɗanda ke fita saboda Sunan.
Yahaya ya ce masubi su marabce so domin su zama yan'uwa ma'aikata domin gaskiya.
Diyotarifis ya na kaunar ya zama shine farko a cikin ikklisiya.
Diyotarifis bai karɓi Yahaya ba.
Idan Yahaya ya zo zai yi tuna da mugun halayen Diyotarifis
Diyotarifis ba ya karɓan yan'uwan.
Diyotarifis ya na hana su karɓan yan'uwan, ya na kuma korar su da ga ikkklisiya.
Yahaya ya gaya wa Gayus ya kwaikwayi mai kyau.
Yahaya na begen zuwa ya kuma yi magana tare da Gayus fuska da fuska.
1 Yahuza, bawan Yesu Almasihu kuma dan'uwan Yakubu, zuwa ga kirayayyu, kaunatattu a cikin Allah Uba, kebabbu domin Yesu Kristi: 2 bari jinkai da salama da kauna su ribabanya a gare ku. 3 Kaunatattu, ina iyakar kokari in rubuta maku game da ceton mu duka, ya zama dole in gargade ku sosai game da bangaskiya wadda aka mika wa masu bi sau daya tak ba kari. 4 Don wasu mutane sun sadado sun shigo da sanda a asirce wadanda an rubuta game da hukuncin su tun da dadewa-mutane marasa imani, wanda suka canza alherin Allah zuwa lalata, kuma sun karyata makadaicin Shugaba da Ubangijinmu, Yesu Almasihu. 5 Ina so in tunashe ku-ko da shike kun rigaya kun san abin, da cewa Allah ya ceci wasu mutane daga kasar masar, amma daga baya ya hallaka wadanda basu ba da gaskiya ba. 6 Kuma mala'iku wadanda ba su rike matsayin ikon su ba, amma suka bar wurin zaman su na ainihi-Allah ya tsare su a sarka na har'abada a cikin bakin duhu domin babban ranar shari'a. 7 Suna nan kamar Saduma da Gwamrata da kuma biranen da ke kewaye da su, wadanda suka ba da kansu ga fasikanci suna bin sha'awoyi wanda ba na dabi'a ba. Aka mai da su abin misalin wadanda suka sha wuta mara matuka. 8 Haka kuma, wadannan masu mafarkan suna lalatar da jikinsu. Suna raina masu mulki, kuma suna fadar miyagun abubuwa a kan masu daukaka. 9 Amma ko Mika'ilu babban mala'ika, a lokacin da yake jayyaya da muhawara da shaidan a kan gawar Musa, bai kuskura ya fadi wata kalmar hukunci a kansa ba. Maimakon haka ya ce, "Bari Ubangiji ya tsauta maka!" 10 Amma waddannan mutane suna kawo batanci game da dukan abin da ba su gane ba. Wadannan mutane masu halin dabbobi ne, suna kwa jawo wa kansu hallaka kenan. 11 Kaiton su! Domin sun bi hanyar Kayinu, kuma sun tsunduma cikin kuskuren Bal'amu domin samun riba. Suka hallaka cikin husuma irin ta Kora. 12 Wadannan hatsari ne a boye cikin bukukuwan ku na kauna. Suna shagali ba kunya ba tsoro, suna ciyar da kansu kadai. Su holokon hadari ne marar ruwa, wanda iska ke korar sa. Su itatuwa ne shirim ba yaya, mattatu ribi biyu, tumbukakku tun daga saiwa. 13 Su rakuman teku ne masu hauka, suna fahariya cikin kumfar kunyar su. Su kamar taurari ne masu tartsatsi. Wadanda aka tanada wa duhu baki kirin na har abada. 14 Ahnuhu, mutum na bakwai daga Adamu, ya yi anabci game da su cewa, "Duba, Ubangiji zai zo da tsarkakan sa dubun dubbai. 15 Domin ya zartar da hukunci a kan dukan kowa, ya kuma cakune dukan marasa da'a a cikin dukan ayyukan su na rashin da'a wanda suka aikata a hanyar da bata cancanta ba, da kuma kalmomi masu kaifi da masu zunubi suka fada game da shi." 16 Wadannan masu cecekuce ne, masu gunaguni, wadanda ke bin sha'awar su ta mugunta, masu tinkaho da fahariya, masu bambadanci domin ribar kansu. 17 Amma ku, kaunatattu, ku tuna da kalmomin da manzannin Yesu Almasihunmu suka gaya maku tun da. 18 Sun ce maku, "A cikin kwanaki na karshe, za a samu masu ba'a, wadanda ke bin sha'awoyin su na rashin ibada," 19 Wadannan mutane masu haddasa tsatsaguwa ne, kuma su yan duniya ne, ba su kuma da Ruhu. 20 Amma ku, kaunatattu, ku gina kanku a cikin mafificiyar bangaskiyar ku mai daraja, kuma kuna addu'a a cikin Ruhu Mai Tsarki. 21 Ku rike kanku a cikin kaunar Allah, kuna kuma jiran jinkan Ubangijinmu Yesu Almasihu wanda ke kawo rai na har abada. 22 Ku nuna jinkai ga masu shakku. Ceci wadansu ta wurin fizge su daga wuta. 23 Ga wadansu kuma ku nuna jinkai da rawar jiki, kuyi kyamar koda tufafin jikinsu ma. 24 Yanzu, zuwa ga wanda yake da iko ya hana ku tuntube, ya kuma sa ku tsaya a gaban madaukakiyar kasancewarsa, marasa abin zargi da kuma murna mai yawa, 25 zuwa ga Allah makadaici mai ceton mu ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu, daukaka, da girma, da mulki, da iko su kasance, kamin dukan lokuta, yanzu, da har abada. Amin.
Yahuza ya gabatar da kansa a matsayin marubucin wannan wasiƙar, ya kuma gaishe da masu karanta ta. Mai yiwuwa shi ɗan'uwan Yesu ne. Akwai kuma masu suna Yahuza guda biyu a Sabon Alkawali.
Yahuza ɗan'uwan Yakubu ne. AT: "Ni ne Yahuza, bawan"
Yakubu da Yahuza 'yan'uwan Yesu ne.
"bari jinkai, salama, da ƙauna su yawaita sosai a gare ku. "Ana maganan waɗannan abubuwan kamar suna ƙaruwa ne ta wurin lamba ko girma. AT: "Bari Allah ya cigaba da yi maku jinkai domin ku yi rayuwar salama, ku kuma kara yin ƙaunar junanku
Yahuza ya gaya wa masubi dalilinsa na rubuta wannan wasiƙar.
"ceton mu da naku"
"Na ji buƙata kwarai in rubuta " ko "Na ji ya kamata in yi rubutu da hanzari"
"domin in karfafa ku, ku tsaya wa koyaswar gaskiya"
"a karshe gaba ɗaya"
"Domin wasu mutane da basu son su jawo hankula a gare su sun shigo cikin masubi a asirce"
AT: "mutane waɗanda Allah ya zaɓa ya hukunta"
Ana magana game da alherin Allah kamar abu ne da za'a iya canza ta zuwa mummunan abu. AT: "wanɗanda sun koyas da cewa alherin Allah ya ba da izini a cigaba da yin rayuwar zunubin lalata"
Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka AT:1) sun koyas da cewa shi ba Allah bane ko 2) waɗannan mutane basu biyayya da Yesu Almasihu.
"Ina son ku tuna"
"ko da shike kun rigaya kun san wannan abin gaba ɗaya"
"Tun da daɗewa Ubangiji ya ceci Isra'ila daga Masar"
Wasu rubutun na nuna "Yesu ne."
"rikon amana da Allah ya basu"
"bar ainihin wurin da aka zaɓa masu"
"Allah ya saka waɗannan mala'ikun a cikin baƙin kurkuku inda baza su iya gudu ba"
A nan "duhu" kalma ce da take nuna wurin da matattu suke ko jahannama. AT: "cikin duhu mai tsanani a jahannama"
rana ta karshe da Allah zai yanke shari'a wa kowa
A nan "biranai" na nufin mutanen da suka yi rayuwa a cikin ta.
Sakamakon zunubin zina da Saduma da Gwamrata su ka yi iri ɗaya ne da mummunan tawaye da mala'ikun nan suka yi.
Hallakar mutanen Saduma da Gwamrata ya zama misali ne ga duk waɗanda suka ƙi Allah.
mutane da suka yi rashin biyyaya ga Allah, mai yiwuwa domin sun ce wahayi ne da suka gani ya basu ikon yin haka
Wannan magana ta bayyana cewa zunubin su ne ya sa jikunansu, wato ayukansu, suka zama mara ƙarɓuwa kamar yadda datti da ke ă cikin ruwa na hana shan ta.
"faɗin zagi"
Wannan na nufin ruhohi, kamar mala'iku.
"bai faɗi wani abu" ko "ba ya so ya faɗi wani abu"
"mummunar kalmar hukunci" ko "mummunar hukunci"
mutane marasa tsoron Allah
"faɗi mummunar abu marar gaskiya game da"
"kowane abu da ba su san ma'anar ba." AT: "duk abubuwa masu kyau da basu gane ba" ko "abubuwa masu ɗaukaka da basu gane ba" (1:8)
"bi hanyar" kalma ce da ke nufi "yi rayuwa iri ɗaya da." AT: "yi rayuwa iri ɗaya da wanda Kayinu ya yi"
Kalman nan "Waɗannan" na nufin "marasa tsoron Allah" na [1:4]
Waɗannan manyan duwatsu ne da ake samu a cikin ruwa na teku. Suna da hatsari sosai domin ma'aikatan jirgin ruwa basu iya gannin su. Jiragen ruwa na iya rushewa nan take idan sun bugi irin waɗanan duwatsun.
AT: 1) waɗannan mutane suna nan kamar itace ne da mutane na begen girbar 'ya'yan ta, amma bata da ko guda, ko 2) itacen da bata taba haifar 'ya'ya ba.
Wannan kalma ce ta rayuwa da ta gamshi Allah, tana kuma taimakon mutane.
Itace da wani ya tumbuke ta, kalma ce da ake amfani wa mutuwa.
Kamar itatuwa da aka tumbuke tushensu daga kasa, haka ne an raba mutanen da basu da tsoron Allah daga Allah wanda shine tushen rayuwa.
Kamar yadda iska mai ƙarfi ke hura rakuman ruwa, hakannanne mutanen da basu da tsoron Allah zasu yi tafiya a hanyoyi dabam-dabam.
Kamar yadda iska ke saka rakuman ruwa hauka domin ya kaɗa kumfa mai datti, haka mutanen nan, ta wurin koyaswan karya da kuma ayukansu, zasu kunyata. AT: "kamar yadda rakuman ruwa ke kawo kumfa da datti, waɗannan mutanen na kazamtar da sauran jama'a da kunyar su.
Waɗanda suka yi karatu game da taurari a zamanin da sun kula da cewa abin da muke kira taurari masu kewaye rana basu tafiya kamar yadda tauraro yake yi. AT: "Suna kama da tauraro da ke tafiya"
A nan "duhu" kalma ce da ke wakilcin inda mattatu suke ko jahannama. A nan "matsanancin duhu" kalma ce da take nufin "duhu baƙi ƙirin." Kalmomin nan " an tanadasu" ana iya bayyana su cikin aiki. AT: "kuma Allah zai saka su cikin baƙin duhu na harabada a jahannama"
Idan aka kidaya Adamu a mastayin mutum na farko, Anuhu ne zai zama na bakwan. Idan ɗan Adamu ne kuma na farkon, Anuhu ne zai zama na shida.
"Ji" ko "Kasa kunne ga abu mai muhinminci da zan fada"
"ya yanke hukunci a kan" ko "ya hukunta"
Mutanen da basu so su yi biyyaya suna kuma kushe mulki na tsoron Allah. "Masu gunaguni" suna magana a asirce, masu "ƙunƙuni" kuma suna magana a fili.
Mutane da suke yabon kansu domin sauran jama'a suji.
"suna yabon karya ga sauran jama'a"
Ana magana game da waɗannan mutane kamar sha'awar su sarakuna ne da suke mulki a kansu. AT: "ba za su taba iya daina rashin biyayya ga Allah ba ta wurin mugayen halayen da suke so su yi"
"Waɗannan ne masu ba'a" ko "Masu ba'an nan ne"
suna tunani kamar yadda marasa tsoron Allah suke yi, suna daraja abubuwan da marasa bi suke daraja wa
Ana magana game da Ruhu mai Tsarki kamar abu ne da mutane ke iya mallaka. AT: "Ruhun baya tare da su"
"kada ku zama kamar su, ƙaunatattuna. A maimakon haka"
Ana magana da su saka bege ga Ubangiji su kuma yi biyayya da shi kamar hanya ce da ake shirin gini.
A nan ana maganar cigaba da iya karɓar ƙaunar Allah kamar wanda yake ajiye kansa ne a wani wuri.
"marmarin saka zuciya domin ganin"
A nan "jinƙai" na tsayawa á madadin Yesu Almasihu ne da kansa, wanda zai nuna jinƙansa wa masubi ta wurin sa su yi rayuwa har abada tare da shi.
"waɗanda har yanzu basu yarda da cewa Yesu Allah bane"
Bayanin nan na nuna yadda ake jawo mutane daga wuta kafin su fara ƙonewa. AT: "ana yi masu duk abin da yakamata domin a tserar da su daga mutuwa da rashin sannin Almasihu. Wannan na kama da ana jawosu ne daga cikin wuta"
"Ku nuna jinƙai ga jama'a, amma ku yi tsoron zunubi kamar yadda suka yi"
Yahuza yana zuguiguita al'amarin don ya gargaɗi masu karatun cewa zasu iya zama kamar waɗannan masu zunubi. AT: "Ku yi da su kamar kuma zaku iya zama masu laifin zunubi tawurin taɓa tufafinsu"
Ɗaukakarsa haske ne sosai da ke nuna girmansa. AT: "ă kuma barku ku ji daɗi ku kuma ɗaukaka ikonsa"
A nan ana magana game da zunubi kamar datti ne ko illa da ke jikin mutum. AT: "inda za a kasance babu zunubi"
"zuwa ga Allah makadaici, wanda ya cece mu tawurin abin da Yesu Almasihu yayi." Wannan na nanata cewa Allah Uba, da Ɗan, mai ceto ne.
Ɗaukaka, da dukan shugabanci, da cikakken mulki akan komai na Allah ne a da, da yanzu da har abada.
Yahuda bawan Yesu Almasihu ne.
Yahuda dan'uwan Yakubu ne
Ya rubuta wa waɗanda an kira, ƙaunatattun Allah Ubba, da kuma riƙe domin Yesu Almasihu.
Yahuda ya so a yawaita masu rahama, zaman lafiya, da kuma kauna.
Yahuda da farko ya so ya rubuta game da ceto na kowa.
A zahiri, Yahuda ya rubuta game da bukatan gwagwarmaya domin bangaskiyar tsarkaka
Wasu da aka hukunta da rashin bin Allah sun zo a sirri
Sun canza alherin Allah zuwa jima'in lalata da karyata Yesu Almasihu.
Ubangiji ya cece su daga ƙasar Masar
Ubangiji ya hallaka mutanen da ba su yi imani ba.
Ubangiji ya sa su a sarƙa a cikin duhu domin hukunci.
Suka yi zina da bin sha'awa ta jiki da ba halarta ba.
Sun kazantad da jikin su a mafarkan su, suka ƙi hukuma. da kuma faɗin abubuwan mugunta.
Mala'ikan Mika'ilu ya ce, "Bari Ubangiji ya tsauta maka."
Suna kula da kansu ne kawai ba tare da wata kunya ba.
Anuhu ne na bakwai a layin Adamu.
Ubangiji zai zartar da hukunci bisa ga dukan mutane.
Masu gunaguni, masu ƙorafi, masu bin muguwar sha'awar su, alfahari da ƙarfi, da kuma masu yi wa mutane yabo domin ribar kai sune mugayen mutanen da za a ɗaure.
Manzannin Ubangiji Yesu Almasihu suka fada a da akan izgilai.
Ba su da ruhu mai tsarki
ƙaunatattun suna gina kansu a cikin bangaskiyar su mafi tsarki, da yin adu'a a cikin Ruhu mai Tsarki.
Kaunatatun za su ajiye kansu a ciki, su kuma nemi kaunar Allah, da kuma jinkan Ubangiji Yesu Almasihu.
Ya kamata ƙaunatattun su yi rahama a, su kuma cece waɗanda suke shakka ko tare da rigar da ke da tabon naman jiki, da kuma waɗanda ke a cikin wuta.
Allah ya iya ya riƙe su daga yin tuntuɓe da kuma ajiye su a ɗaukakarsa mara aibi.
Allah ya zama da ɗaukaka kafin dukan lokaci, yanzu, da har abada abadin.
1 Wannan shine wahayin Yesu Almasihu da Allah ya bashi ya nuna wa bayinsa abinda zai faru ba da dadewa ba. Ya bayyana wannan ta wurin aiko da mala'ikansa ga bawansa Yahaya. 2 Yahaya yayi shaida akan abinda ya gani game da maganar Allah da kuma shaidar da aka bayar game da Yesu Almasihu. 3 Mai albarka ne wanda ke karanta littafin nan da murya mai karfi, da kuma wadanda ke sauraron kalmomin wannan annabci kuma suke biyayya da abinda aka rubuta a ciki, domin kuwa lokaci ya kusato. 4 Ni Yahaya, zuwa ga ikilisiyoyi bakwai na kasar Asiya: alheri zuwa gare ku da salama daga wanda ke yanzu, wanda ya kuma kasance a da, shi ne kuma mai zuwa nan gaba, kuma daga ruhohin nan bakwai da ke gaban kursiyinsa, 5 kuma daga Yesu Almasihu, wanda ke amintaccen mashaidi, dan fari na tashi daga cikin matattu, kuma mai mulkin sarakunan duniya. Ga wanda ya ke kaunar mu ya kuma kwance mu daga daurin zunubanmu ta wurin jininsa, 6 ya maishe mu masu mulki, firistoci na Allahnsa da Ubansa - daukaka da iko su tabbata gare shi har abada abadin, Amin. 7 Duba yana zuwa tare da gizagizai, kowane ido zai gan shi, har ma da wadanda suka soke shi. Haka kuma dukkan kabilun duniya za su yi makoki saboda da shi. I, Amin. 8 "Nine na farko da na karshe", in ji Ubangiji Allah, "Wanda yake shine a yanzu, shine wanda ya kasance a da, kuma shi ne mai zuwa nan gaba, Mai iko duka." 9 Ni, Yahaya- dan'uwan ku da wanda ke tarayya daku cikin shan wahala, da mulki da tsawon jimrewa wadanda ke cikin Yesu - ina tsibirin da ake kira Batmusa saboda maganar Allah da kuma shaida game da Yesu. 10 Ina cikin Ruhu a ranar Ubangiji. Sai naji wata murya mai karfi a baya na kamar ta kaho. 11 Ta ce, "Rubuta abinda ka gani a cikin littafi, ka kuma aika wa ikilisiyoyin nan bakwai - ga Afisus, ga Simirna, ga Birgamas, ga Tayatira, ga Sardisu, ga Filadalfiya, da kuma ga Laudikiya." 12 Na juya don in ga wanda muryarsa ke magana da ni, da na juya sai na ga fitilu bakwai akan madorin su 13 A tsakiyar fitilun akwai wani mai kama da dan mutum, yana sanye da doguwar tufa har tafin sawunsa, da damara ta zinariya kewaye a kirjinsa. 14 Kansa da gashinsa fari fat kamar auduga - kamar dusar kankara, kuma idanun sa kamar harshen wuta. 15 Kafaffunsa kamar gogaggiyar tagulla, kamar tagullar da aka tace da wutar makera, muryar sa kuma kamar kugin ambaliyar ruwan teku ne. 16 A hannunsa na dama yana rike da taurari bakwai, daga bakinsa kuma kakkaifan takobi mai kaifi biyu ke fitowa. Fuskarsa tana haskakawa kamar sa'adda rana ke haskakawa kwarai. 17 Lokacin da na gan shi, na fadi kamar mataccen mutum a kafaffunsa. Ya dora hannunsa na dama a kaina ya ce, "Kada ka ji tsoro. Nine na farko da na karshe, 18 da kuma wanda ke raye. Na mutu, amma duba ina raye har abada! Kuma ina da mabudin mutuwa da na hades. 19 Domin haka ka rubuta abinda ka gani, abin da ke yanzu, da abin da zai faru bayan wanan. 20 Akan boyayyar ma'ana game da taurari bakwai da ka gani a hannun dama na, da madorin fitilu bakwai na zinariya: Taurarin nan bakwai mala'iku ne na ikilisiyoyi bakwai, kuma madorin fitilun nan bakwai ikilisiyoyi ne bakwai.
Wannan ne gabatarwa na littafin Wahayin Yahaya. Ya bayyana cewa wahayi ne daga Yesu Almasihu yana kuma ba da albarka ga duk waɗanda suka karanta.
Wannan na nufin mutanen da sun gaskata da Almasihu.
"waɗannan ababai zasu faru ba da daɗewa ba"
"Ya sanar da wannan"
Yahaya ne ya rubuto wannan littafi yana kuma nufin kansa ne. AT: "ga ni, Yahaya, bawansa"
"sakon da Allah ya faɗa"
Wannan na iya nufin 1) shaidar da Yahaya ya bayar game da Yesu Almasihu. AT: "ya kuma bayar da shaida game da Yesu Almasihu" ko 2) "shaida da Yesu Almasihu ya faɗa game da kansa"
Yana nufin ga duk wanda ke karanta littafin da murya mai ƙarfi. AT: "duk wanda ke karanta littafin da karfi"
AT: "biyayya da abin da Yahaya ya rubuta a ciki" ko "biyayya da abinda suka karanta a ciki"
"abubuwan da zasu faru, zasu faru ba da daɗewa ba"
Wannan fata ne ko kuma albarka. Yahaya ya yi magana game da waɗannan abubuwa kamar su ne Allah na iya bayarwa, kodashike ya na bege ne Allah ya yi aiki wa mutanen sa ta wurin waɗannan hanyoyin. AT: "1:4-6"
"daga Allah, wanda ke"
Kasancewan nan gaba na nufin zuwa ne.
Lamba ta bakwai ɗin alama ce dake nuna kammalawar aikin gabaɗaya. "ruhohin nan bakawai" na nufin Ruhun Allah ko ruhohi bakwai wanda ke bauta wa Allah.
"mutum na fari da a ka tayar daga mattatu"
Daga cikin dukkan waɗanda suka mutu.
"kuma bamu yanci"
"an shirya mu keɓaɓɓu an kuma fara mulki akan mu kuma ya mayad da mu firistoci"
Wannan na nufin mutum ɗaya ne. AT: "Allah, Ubansa"
Wannan suna ne mai muhinminci na Allah da yake bayanin dangartaka tsakanin Allah da kuma Yesu.
Wannan fata ne ko kuma addu'a. AT: 1) "Bari mutane su daraja ɗaukakarsa da kuma ikon sa" 2) "Bari ya samu ɗaukaka da kuma iko." [ 1:4-6].
Mai yiwuwa wannan na nufin ikonsa a matsayin sarki.
Dashike mutane suna gani da idanuwan su ne, kalman nan "ido" na nufin mutane ne. AT: "kowane mutum" ko "kowa da kowa"
"har da waɗanda suka soke shi zasu gan shi"
An soke hannuwar Yesu da kuma kaffafunsa a lokacin da aka kafa masa ƙusa akan giciye. Wannan na nufin mutanen da suka kashe shi ne. AT: "kashe shi"
yi rami cikin
Wannan shine farko da kuma karshen rubutun baƙaƙe na Girka. AT: 1) "wanda shi ne ya fara komai, ya kuma kai komai ga ƙarshe" ko 2) "wanda tun farko yana raye zai kuma rayu har abada." Idan akwai rashin fahimta ga masu karatu, zaku iya yin tunanin amfani da farko da kuma karshen rubutun baƙaƙen ku. AT: "na farko da kuma karshe"
Wata harshe na iya saka "Ubangiji Allah ya ce" a farko ko kuma karshen dukkan magana.
Waɗannan na nufin masubi na cikin ikilisiyu bakwai.
... AT: [ 1:9]
"saboda na gaya wa wasu maganar Allah"
"shaidar da Allah ya bayar game da Yesu." Fassara kamar [1:2]
Yahaya ya yi magana akan bishewar Ruhun Allah kamar yana cikin Ruhu ne. AT: "Na samu izawa ta wurin Ruhu" ko "Ruhu ya iza ni"
ranar sujadar masubi cikin Almasihu
Muryan na da ƙarfi kamar na ƙaho.
Wannan na nufin kayan kiɗe-kiɗe na waƙa ko domin tara mutane tare a wuri ɗaya domin sanarwai ko taro.
Waɗannan sunaye ne na biranai a yammacin Asiya da a yau ana kira Turkiya.
Yahaya ya fara bayyana abin da ya gani a wahayinsa.
Wannan na nufin wanda ke magana ne. AT: "wanda"
Wanda ke da kamanin mutum.
mayafi da ake sakawa kewaye da ƙirji. Mai yiwuwa ta na da zare mai zinariya cikinta.
Auduga da dusar ƙanƙara misali ne na abubuwan da farare ne sosai. Maimaitawar "fari fat kamar" na nanatawa cewa farare ne sosai.
Wannan gashin rago ne ko akuya. An san da ita fari fat ce sosai.
Ana yi bayanin idanunsa na cike da haske kamar harshen wuta. AT: "idanunsa sun yi haske kamar harshen wuta"
Ana goge tagulla domin ta yi ƙyalli ta kuma nuna haske. AT: "Kafaffunsa sun yi haske sosai kamar gogaggiyar tagulla"
Ana iya fara tace tagullar sa'annan a goge ta. AT: "kamar tagulla da aka tsarkake ta a cikin wutar makera mai zafi aka kuma goge ta"
gongoni mai ƙarfi domin rike wuta mai zafi sosai. Mutane suna saka karfe cikin ta, kuma wuta mai zafin zai kone kowace abu mara kyau da ke a cikin karfen.
Wannan kara ce sosai, kamar karar babban ruwa da ke wucewa na mafaɗar ruwa, ko na rukunin ruwa mai ƙarfi a teku.
Bakin takobi na fitowa daga bakinsa. Takobin da kanta ba ta motsi.
Wannan na nufin takobi mai baki biyu wanda aka wasa duka gefensa domin ya ci a kowane gefe.
Yahaya ya kwanta, ya fuskanci ƙasa. Mai yiwuwa ya firgita sosai kuma ya nuna bangirma wa Yesu.
"Ya taɓa ni da hannunsa na dama"
Wannan na nufin sifar Yesu na har abada. (Dubi: )
Anyi magana game da samun iko akan abubuwa kamar samun mabuɗin sa ne. Nufin bayanin nan shine, yana iya ba da rai ga waɗanda suka mutu ya kuma fitad da su daga Hades. AT: "Ina da iko akan mutuwa da kuma Hades" ko "Ina da iko in ba da rai ga mutanen da suka mutu in kuma fitad da su daga Hades"
Waɗannan taurarin alama ce da ke nufin mala'iku bakwai na ikilisiyoyi bakwain ne.
Maɗorin fitilun alama ce da na nufin ikilisiyoyin nan bakwai. AT: [1:2]
AT:1) mala'iku na sama da suke tsare ikilisiyoyin nan bakwai ko 2) mutum mai ba da saƙo ga ikilisiyoyin nan bakwai.
Wannan na nufin ikilisiyoyi bakwai da su ka kasance a Asia Ƙarama a wancan lokaci. AT: [1:11]
Wahayin Yesu Almasihu ya zo daga Allah ne, kuma wa bayinsa ne aka nuna wa.
Abubuwan wahayin nan zasu faru ne ba da daɗewa ba.
Waɗanda suka ƙaranta ta, suka ji, suka kuma yi biyayya ga littafin nan ne zasu samu albarka.
Yahaya ne ya rubuta wannan littafin, kuma ya rubuta wa ikilisiyoyi bakwan da ke Asiya ne....
Yahaya ya ba wa Yesu Almasihu laƙani na shaida aminci, ɗan fari ga mutuwa, da kuma mai mulkin sarakan duniya.
Yesu ya yi wa masu bi ƙasan sarauta da kuma firistocin Allah Uɓa
Idan Yesu ya dawo dukkan idanuwa zasu gan shi, har ma da waddanda suka soke shi.
Ubangiji Allah ya bayyana kansa a matsayin Farko da kuma Karshe, wanda shi a yanzu, shi yake tun, shi kuma ya ke zuwa, mafi girma. ...
Yahaya yana tsibirin Batmusa domin kalman Allah da kuma shaida game da Yesu.
Murya mai ƙarfin nan ya gaya wa Yahaya cewa ya yi rubutu a littafi game da abin da ya gani ya kuma tura su zuwa ikkilisiyoyin nan bakwai.
Mutumin da Yahaya ya gani na da gashi fara kamar audiga, idanuwarsa kuma ja kamar wuta.
Mutumin nan yana da taurari bakwai a hannun damarsa, kakkaifan takobi mai kaifi biyu kuma na fitowa daga bakin sa.
Yahaya ya faɗi a kafaffun mutumin kamar mattacen mutum.
Mutumin ya ce yana da mabuɗin Mutuwa da kuma na Hades.
Taurari bakwan nan su ne mala'ikun ikkilisiyoyi bakwan nan, madorin fitilu bakwan nan kuma su ne ikkilisiyoyi bakwan.
1 "Zuwa ga mala'ikan dake ikilisiyar Afisus, ka rubuta: 'Wadannan sune kalmomin wanda ke rike da taurari bakwai a cikin hannun damarsa. wanda yake tafiya a tsakanin zankayen fitilun zinari bakwai, 2 "Na san abubuwan da ka yi, da famar ka, da hakurinka da jimirinka. Na sani ba ka jimrewa miyagun mutane, na sani ka gwada wadanda suka ce da kansu, su manzanni ne, amma ba haka ba, ka tarar da su makaryata. 3 Na san kana da tsawon jimrewa, kuma ka sha wahala sosai sabili da sunana, kuma baka gaji ba. 4 Amma ga rashin jin dadi na da kai, ka bar kaunar ka ta fari. 5 Domin haka ka tuna daga inda ka fadi. Ka tuba ka yi abubuwan da ka yi da fari. Sai fa ka tuba, zan zo maka in kuma cire fitilar ka daga mazauninta. 6 Amma kana da wannan: Ka tsani abubuwan da Nikolatawa suka yi, wanda nima na tsana. 7 wanda yake da kunnen ji ya saurari abinda Ruhu yake fada wa ikilisiyoyi. Ga wanda yayi nasara zan bashi dama ya ci daga itacen rai, wanda ke cikin firdausin Allah."" 8 Zuwa ga mala'ikan da ke Ikilisiliyar Samirna rubuta: 'Wadannan su ne kalmomin wanda yake shine farko shine karshe, wanda ya mutu ya sake rayuwa kuma. 9 "Na san wahalun ka da talaucin ka amma kana da arziki. Nasan masu bata suna wadanda suke cewa su Yahudawa ne, amma ba haka suke ba. Su majami'ar Shaidan ne. 10 Kada ka ji tsoron wahalar da zaka fuskanta nan gaba. Duba! Shaidan yana gab da jefa wadansun ku cikin kurkuku, domin a gwada ku, kuma zaku sha wahala ta kwana goma. Kuyi aminci har ga mutuwa zan baku rawanin rai. 11 wanda yake da kunne ya saurari abinda Ruhu yake fada wa ikilisiyoyi. Shi wanda yayi nasara ba zai cutu a mutuwa ta biyu ba."" 12 "Zuwa ga mala'ikan dake ikilisiyar Burgamas rubuta: 'Wadannan ne kalmomin wanda ya ke da takobi mai kaifi biyu; 13 "Na san inda kake zama can inda kursiyin shaidan yake. Duk da haka ka rike sunana da karfi, na sani baka yi musun bangaskiyar ka da ni ba, ko a lokacin Antifas mashaidina, amintaccena, wanda aka kashe a tsakaninku, can inda shaidan yake zama. 14 Amma ga rashin jin dadi na kadan da kai: Kana da wadansu da suke rike da koyarwar Bil'amu kamkam, wanda ya koya wa Balak ya sa abin tuntubi gaban 'ya'yan Isra'ila, domin su ci abincin da aka mika wa gumaka kuma suyi fasikanci. 15 Hakannan kuma wasunku sun rike koyarwar Nikolatawa kamkam. 16 Sabili da haka ka tuba! Idan ka ki zan zo gare ka da sauri, kuma in yi yaki gaba da su da takobi dake cikin bakina. 17 Bari wanda yake da kunne ya sauriri abin da Ruhu yake fadawa ikilisiyoyi. Ga wanda yayi nasara zan bada wata boyayyar manna, kuma zan bashi farin dutse da sabon suna a rubuce a kan dutsen, suna wanda ba wanda ya sani, sai shi wanda ya karbe shi."" 18 Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar Tiyatira rubuta: 'Wadannan sune kalamomin Dan Allah, wanda yake da idanu kamar harshen wuta; sawayen kamar gogaggiyar tagulla: 19 "Na san abin da ka yi, kaunar ka, da bangaskiya da hidima da tsawon jimrewar ka. Na san abinda ka yi bada dadewa ba ya fi abinda ka yi da fari. 20 Amma ga rashin jin dadi na da kai: Kana hakurce wa matar nan Yezebel, wadda take kiran kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta, ta rudi bayina suyi fasikanci kuma su ci abincin da aka mika wa gumaka sadaka. 21 Na bata lokaci domin ta tuba amma bata so ta tuba da fasikancin ta. 22 Duba! zan jefa ta a kan gadon jinya, wadanda kuma suka yi zina da ita za su shiga babbar wahala, sai dai in sun tuba daga ayukan ta. 23 Zan buga 'ya'yanta da mutuwa, kuma dukan ikilisiyoyi zasu san cewa nine wanda nake bincike tunani da zukata. Zan ba kowanen ku bisa ga ayyukansa. 24 Amma ga sauran ku dake cikin Tayatira, ga kowanen ku wanda bai rike wannan koyarwar ba, kuma bai san abinda wadansu suke kira zurfafan abubuwan Shaidan ba--ga ku na ce ban sa muku wata nawaya ba.' 25 Duk da haka dole ku tsaya da karfi har in zo. 26 Wanda yayi nasara da wanda ya yi abin da na yi har karshe, a gareshi zan bada iko akan al'ummai 27 Zai yi mulkin su da sandar karfe, zai farfasa su kamar randunan yumbu." 28 Kamar yadda na karba daga wurin Ubana, ni kuma zan bashi tauraron asubahi. 29 Bari wanda yake da kunne ya saurari abinda Ruhu yake fadawa ikilisiyioyi.""
Wannan ne farkon sakon Ɗan Mutum zuwa ga mala'ikan ikilisiyar Afisa.
AT: 1) mala'iku na sama da yake tsare ikilisiyoyin nan bakwai ko 2) mutum mai ba da saƙo ga ikilisiyoyin nan bakwai. [1:20]
AT: Waɗannan taurarin alama ne. Suna a madadin mala'iku na ikilisiyoyi bakwen ne [1:16]
AT: Fitilun alama ne da ke nufin ikilisiyoyi bakwai.[1:12].
"Fama" da kuma "jimiri" irin magana ne da za'a iya bayyana su da aiki "aiki" da kuma "jimriya" AT: "Na san ... cewa kayi ta famar aiki sosai, kuma ka jimre da hakuri"
"amma ba manzanni ba ne"
"ka iya gane wa cewa waɗancan mutane manzanni na ƙarya ne"
"Suna" a nan kalma ce da yana nuna Yesu Almasihu. AT: "domin na" ko "domin kun gaskata da suna na" ko "domin kun gaskanta da ni"
An yi magana game da fid da zuciya kamar gajiya ne. AT: "baka zama mai fid da zuciya ba" ko "baka bari ba"
"Ban yarda maka ba domin" ko "Ina fushi da kai domin"
Anyi magana game da daina yin abu kamar barin shi a baya ne, ƙauna kuma kamar abu ne da ana iya bari a baya. AT: "ka daina ƙauna ta kamar yadda kayi a farko"
Anyi magana game da yanke ƙauna kamar yadda suka saba kamar faɗiwa daga sama ne. AT: "yawan yadda ka canja" ko "yawan ƙauna da ka saba mani"
"Idan baka tuba ba"
AT: Fitilun alama ne da ke nufin ikilisiyoyi bakwai [1:12]
Mutane waɗanda suka bi koyaswar wani mutum wanda ake kira Nikolaus
Anyi magana game da mai son ji kamar samun kunne ne. AT: "Bari wanda yake so ya ji, ya ji" ko "Idan kana so ka ji, ka ji"
Wannan na nufin wanda yayi nasara ne. AT: "duk wadda ya ƙi mugunta" ko "waɗanda suka ƙi yarda da mugunta"
"gonar Allah." Wannan alama na nufin sama ne.
AT: Wannan suna ne na birni a yammacin Asiya da a yau ake ƙira Turkiya [1:11]
AT: Wannan na nufin kasancewar Yesu na har abada [1:17]
"Wahallu" da kuma "talauci" ana iya fasara su kaman aiki ne. AT: "Na san yadda ka sha wahala ka kuma talauce"
"Ɓata suna;" ana iya fasarar wannan kamar aiki. AT: "Na san yadda mutane sun ɓata maka suna-waɗanda suka ce su Yahudawa ne" ko "Na san yadda mutane sun faɗi munanan abubuwa game da kai-waɗanda suka ce su Yahudawa ne"
"amma su ba asalin Yahudawa bane"
Ana magana game da mutanen da suka taru domin su yi biyaya ko ɗaukaka Shaiɗan kamar su majami'a ne, wurin sujada da kuma koyaswan domin Yahudawa.
"A kwanakin nan, Shaiɗan zai saka wasun ku cikin kurkuku"
"Kuyi mani aminci ko za'a kashe ku." AT: "har ga" ba ya nufin cewa ku daina yin aminci a lokacin mutuwa.
"rawanin mai nasara." Wannan ganye ne daga itace zaitun ko ganyayen laurel, shi ake sa wa a kan wanda yayi nassara a wasan guje guje.
AT: 1)"rawani da yake nuna cewa na riga na baku madauwamiyar rai" ko 2) "rayuwa na ƙwarai kamar kyautar mai zasara"
Anyi magana game da mai son ji kamar samun kunne ne. AT: "Bari wanda yake so ya ji, ya ji" ko "Idan kana so ka ji, ka ji [2:7]
"ba zai ga mutuwa ta biyu ba" ko "ba zai mutu so biyu ba"
AT: Wannan sunan wani birni ne a yammacin Asiya da ayau ake ƙira Turkiya. [1:11]
AT: Wannan na nufin takobi mai baki biyu wanda aka wasa duka gefensa domin ya ci ta kowace gefe [1:16]
AT: 1) Ikon Shaiɗan da kuma mugun ra'ayi akan mutane, ko 2) inda Shaiɗan yake mulki.
"Suna" a nan kalma ce da ake amfani wa mutum. Anyi magana game da gaskantawa sosai kamar abu ne da ake riƙewa da ƙarfi. AT: "ka gaskanta da ni sosai"
"Bangaskiya" za'a iya bayyana shi kamar aiki "gaskata." AT: "ka cigaba da gaya wa mutane cewa ka gaskata da ni"
Wannan sunan mutum ne.
"Ban yarda maka ba domin kiman abubuwan da ka yi" ko "Ina fushi da kai domin kiman abubuwa da ka yi." AT: [Revelation 2:4]
AT: "waɗanda suka koyar da abin da Bil'aminu ya koyas; zai" ko "wanda zai yi abin da Bil'aminu ya koyas; zai."
Wannan sunan sarki ne.
Ana magana game da abin da yake jan ra'ayin mutane zuwa yin zunubi kamar ɗutse ne akan hanya da yake saka mutane tuntuɓe. AT: "wanda ya nuna wa Balak yadda zai saka mutanen Isra'ila suyi Zunubi"
"zunubin fasikanci" ko "yin zunubin fasikanci"
"tuba"
AT: "Idan ka ƙi tuba, zan"
"faɗa da su"
Wannan na nufin takobi da ke [Revelation 1:16] AT: "da takobi dake cikin bakina, wanda itace kalmar Allah"
AT: Wannan na nufin duk wanda yayi nassara [2:7] AT: "duk wanda ya ƙi mugunta" ko "waɗanda basu yarda da mugunta ba"
AT: Wannan suna ne na birni yammacin Asiya da a yau ake ƙira Turkiya. [1:11]
Wannan sune mai muhinminci ne naYesu.
AT: "wanda idanun sa na da haske kamar harshen wuta" [Revelation 1:14]
AT: [Wahayin Yahaya 1:15]
Kalmomin nan "ƙauna," "bangaskiya," "hidima," da kuma "jimriya" ana iya bayyana su da kalmar aiki. AT: "Yanda ka ƙaunace ni, ka amince da ni, ka yi mani hidima, ka kuma jimre cikin haƙuri"
AT: "Amman ba yarda da wasu abubuwan da kake yi ba" ko "Amma ina fushi da kai domin wani abun da kake yi" [2:4]
Yesu yayi magana akan wata mata a ikilisiyar su kaman ita ce Sarauniya Yezebel, domin ta yi ayukan zunubi iri ɗaya da wadda Sarauniya Yezebel tayi tun kafin lokacin su. AT: "matar da tayi kamar yadda Yezebel ta yi, da kuma"
"Na bata zarafi domin ta tuba" ko "Na yi zaman jira domin ta tuba"
Kwanciyar ta akan gado zai zama sakamakon ciwo mai tsanani ne da Yesu ya saka mata. AT: [Revelation 2:22]
Yesu, yayi magana game da saka mutane su shiga wahala kamar wurgasu ne cikin wahala. AT: "Zan wurga waɗanda suke yin zina tare da ita su shiga wahala mai tsanani"
"aikata zina"
Wannan na nufin cewa suma sun yi mugayen halayen ta tare da ita. Ta wurin tuba daga ayukan ta, su ma sun tuba daga yin ayukan ta. AT: "idan basu tuba daga aikata mugunta da suna yi ba" ko "idan basu tuba da aikata ayuka tare da ita ba"
"Zan kashe 'ya'yanta"
Yesu yayi magana game da masu bin ta kamar 'ya'yan ta ne. AT: "masu bin ta" ko "Mutane da suke yin abin da ta koyas"
"Zukata" kalma ce da ke nuna yadda ake ji ko sha'awa. AT: "abin da mutane na tunani da kuma so"
Wannan magana ne game da hukunci da kuma sakamako. AT "Zan hukunta ko saka wa kowanen ku"
Ana magana game da yarda da koyaswa kamar riƙe koyaswa ne. AT: "duk wanda bai yarda da koyaswar nan ba"
Kalman na "koyarwa" ana iya bayyana shi kamar aiki. AT: "baka riƙe abin da take koyaswa ba" ko "baka yarda da abin da take koyaswa ba"
AT: "waɗanda suka ƙira su zurfafan abubuwa sun gane cewa daga Shaiɗan ne" ko "waɗansu mutane na ƙiran su zurfafan abubuwa, amma Yesu na cewa waɗancan abubuwan daga Shaiɗan ne.
"abubuwa masu zurfi da Shaiɗan ke koyaswa"
Ana magana game da abubuwan da ake yi a boye kamar suna da zurfi ne. AT: "ɓoyayyun abubuwa"
Wannan annabci ne daga Tsohon Alkawali game da Sarkin Isra'ila, amma Yesu ya yi amfani da shi a nan domin waɗanda ya ba su iko a kan al'umai.
Ana magana game da matsanacin mulki kamar mulki ne da sandar karfe. AT: "Zai yi mulkin su da tsanani kamar yana buga su ne da sandar ƙarfe"
Farfasa su zuwa 'yan gutsure hoton ne da yake nufin 1) hallakar da masu aikata miyagun abubuwa ko 2) yin nasara da abokan gaba. AT: "Zai yi nasara a kan abokan gabansa kamar yana farfasa randunan yumbu ne"
AT: 1) "Kamar yadda na karɓi iko daga wurin Ubana" ko 2) "Kamar yadda na karɓi tauraron asubahi daga wurin Ubana"
Wannan suna mai muhinminci ne na Allah da yake bayyana dangantaka tsakanin Allah da kuma Yesu.
"shi" a nan na nufin wanda yayi nasara.
Wannan tauraro ne mai haske da ke bayyana da asuba kafin gari ya waye. Alama ce tanasara.
A rubuta ɗayan sashi na littafin nan ga mala'ikan ikkisiyan Afisus.
Ikkilisiyar Afisus sun raɓu da mugayen mutanen nan kuma sun gwada annabawan ƙaryan nan.
Rashin jin daɗin Almasihu da ikkilisiyar Afisus shine sun bar matsoyin su na farko.
Almasihu ya ce zai zo ya cire madorin fitilar su daga in da yake idan basu tuba ba.
Almasihu ya yi alkawali cewa waddanda suka yi nassara za su ci daga itacen rai a aljannan Allah
Sashi na littafin da ke zuwa nan gaban nan an rubuto wa mala'ikar ikkilisiyar Samirna ne.
Ikkilisiyar da take Samirna ta shigo cikin shan wuya, ta talauce, an kuma ɓata mata suma.
Almasihu ya yi alkawali cewa waddanda su ka yi aminci har ga mutuwa, suka kuma yi nassara za su sami rawanin rai kuma ba za su sha azabar mutuwa ta biyu ba.
Sashi na littafin da ke zuwa nan gaban nan an rubuto wa mala'ikar ikkilisiyar Burgamas ne.
Ikkilisiyar da ke Burgamas ya na inda kursiyin Shaiɗan yake.
Ikkilisiyar da ke Bargamas sun rike sunan Almasihu gam-gam, ba su kuma yi mutsun bangaskiyar su ba a lokacin da aka kashe Antifas.
Wasu da suke ikkilisiyar Bargamus sun rike koyaswar Bil'amu da kuma koyarwar Nikolatawa.
Almasihu ya jawo masu kunne cewa zai zo ya yi yaƙi da waddanda suka rike waddanan koyaswa na ƙaryan.
Almasihu yayi alkawali cewa waddanda suka yi nassara za su ci boyayyar manna kuma su sami farar dutse mai sabuwar suna.
Sashi na littafin da ke zuwa nan gaban nan an rubuto wa mala'ikar ikkilisiyarTiyatira ne.
Almasihu ya sani cewa ikkilisiyar Tiyatira ta nuna ƙauna, bangaskiya, hidima, da tsawon jimrewar.
Rashin jin daɗin Almasihu game da ikkilisiyar Tiyatira shine, sun haƙurce da Yezebel annabiyar ƙarya mai fasikanci.
Almasihu ya ce zai jefa ta a kan gadon jinya, ya kuma buga 'ya'yanta har ga mutuwa idan bata tuba ba.
Almasihu ya ce masu su tsaya da ƙarfi har zuwan sa.
Almasihu ya yi alkawali wa waddanda suka yi nassara cewa zai basu iko akan al'ummai da kuma tauraron asubahi.
Almasihu ya ce wa mai karanta wannan littafi cewa ya kasa kunnen sa ga abin da Ruhu ke faɗa wa ikkilisiyoyin nan.
1 "Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar Sardisu rubuta: 'Wadannan ne kalmomin wanda yake rike da ruhohi bakwai na Allah da taurari bakwai. "Na san abin da ka aikata. Ka yi suna cewa kana raye amma kai mattacce ne. 2 Ka farka ka karfafa abin da ya rage amma ya kusan mutuwa, domin ban sami ayyukanka cikakku a gaban Allahna ba. 3 Domin haka sai ka tuna, da abubuwan da ka karba kuma kaji. Ka yi biyayya da su, ka kuma tuba. Amma idan baka farka ba, zan zo maka kamar barawo, kuma ba zaka farga da sa'ar da zan zo gaba da kai ba. 4 Amma akwai sunayen mutane kadan a Sardisu wadanda basu kazantar da tufafinsu ba. Za su yi tafiya tare da ni sanye da fararen tufafi domin sun cancanta. 5 Wanda ya yi nasara za a sanya mashi fararen tufafi, kuma ba zan taba share sunansa ba daga Littafin Rai, kuma zan fadi sunansa a gaban Ubana, da kuma gaban mala'ikunsa. 6 Bari wanda yake da kunne ya saurari abin da Ruhu ke fadawa ikilisiyoyi."'" 7 Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar cikin Filadelfiya rubuta: kalmomin wanda yake maitsarki ne kuma mai gaskiya - yana rike da mabudin Dauda, yana budewa babu mai rufewa, kuma inda ya rufe ba mai budewa. 8 Na san abin da ka aikata. Duba, na sa budaddiyar kofa a gabanka wanda ba mai iya rufewa. Na san kana da karamin karfi, duk da haka ka yi biyayya da maganata kuma baka yi musun sunana ba. 9 Duba! Wadanda ke na majami'ar Shaidan, wadanda suke cewa su Yahudawa ne; amma maimakon haka karya suke yi. Zan sa su zo su rusuna a kafafunka, kuma za su san cewa ina kaunarka. 10 Tun da ka jure cikin hakuri ka kiyaye dokoki na, ni ma zan kiyaye ka daga sa'a ta gwaji da zata sauko kan dukan duniya, domin a gwada mazauna duniya. 11 Ina zuwa da sauri. Ka rike abin da kake da shi kamkam domin kada wani ya dauke maka rawani. 12 Zan sa wanda ya yi nasara ya zama ginshiki a haikalin Allahna, kuma ba zai taba fita daga cikin sa ba. Zan rubuta sunan Allahna a kansa, sunan birnin Allahna (sabuwar Urushalima, mai saukowa daga sama daga wurin Allahna), da kuma sabon sunana. 13 Bari wanda yake da kunne ya ji abin da Ruhu ke gayawa ikilisiyoyi." 14 "Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar da ke Lawudikiya rubuta: 'Wadannan sune kalmomin Amin, madogara da mai shaidar gaskiya, mai mulki bisa hallittar Allah. 15 Na san abin da ka aikata, ba ka sanyi ko zafi. Naso ko da kana sanyi ko zafi! 16 Amma saboda kai tsaka-tsaka ne - ba zafi ba sanyi - na kusa tofar da kai daga bakina. 17 Domin ka ce, "Ni mai arziki ne, na mallaki kadarori da yawa, ba na bukatar komai." Amma ba ka sani ba kana cike da takaici ne, abin tausayi, matalauci, makaho kuma tsirara kake. 18 Saurari shawara ta: Ka sayi zinariya a wuri na wadda aka goge da wuta domin ka zama mai arziki, domin ka suturta kanka da fararen tufafi masu kyalli domin kada ka nuna kunyar tsiraicin ka, da mai domin ka shafa wa idanunka ka sami gani. 19 Ina horar da duk wanda nake kauna, ina kuma koya masu yadda za su yi rayuwa. Saboda haka, ka himmatu ka tuba. 20 Duba, ina tsaye a bakin kofa ina kwankwasawa. Idan wani ya ji muryata ya bude kofar, zan shigo cikin gidansa, in ci tare da shi, shi kuma tare da ni. 21 Wanda ya ci nasara, zan bashi dama ya zauna tare da ni bisa kursiyina, kamar yadda nima na ci nasara kuma na zauna da Ubana a kan kursiyinsa. 22 Bari wanda yake da kunne ya saurari abin da Ruhu yake fadawa wa ikilisiyoyi."
Wannan ne farkon wasiƙar Ɗan Mutum zuwa ga mala'ikan ikilisiyar dake Sardisu.
AT: [ Wahayi Yahaya 1:11]
AT: [Wahayin Yahaya 1:4]
AT: [Wahayin Yahaya1 16]
Biyayya da kuma girmama Allah na nufin zama a raye ne; rashin biyaya kuma, da rashin girmama shi na nufin mutuwa ne.
Ana magana kuma game da ayuka masu kyau da masubi da ke Sardisu suka yi kamar suna raye ne, amma, suna cikin haɗarin mutuwa. AT: "Ka tashi, ka kuma kammala aikin da ya rage, ko kuma abin da ka yi zai zama a banza" ko "Ka tashi. Idan baka gama abin da ka rigaya ka fara ba, aikin ka na baya zai zama mara amfani"
Zama a shirye ga haɗari na nufin ka farka ne. AT: "Zama shiryaye" ko "Ka yi lura"
Wannan na nufin maganan Allah ne, wanda suka gaskanta. AT: "Maganar Allah da ka ji da kuma gaskiyar da ka gaskanta"
AT: "ka farka" [Wahayin Yahaya 3:2]
Yesu zai zo a lokacin da mutane basu tsamanci zuwan shi ba, kamar yadda barawo ke zuwa alokacin da ba a tsamance shi ba.
"sunaye" kalma ne da mutane na amfani domin kansu. AT: "mutane kaɗan"
Yesu yayi magana akan zunubi a rayuwar mutum kamar ƙazantatccen tufafi ne. AT: "basu ƙazantar da rayuwarsu kaman ƙazantatccen tufafi ba"
Mutane sun cika magana game da rayuwa a masayin "tafiya" AT: "zai yi rayuwa tare da ni"
Fararen tufafi na nuna rayuwa mai tsabta, mara datti. AT: "kuma za'a saka musu fararen tufafi, wanda zai nuna cewa suna da tsabta"
AT: [Wahayin Yahaya 2:7]
AT: "zai sanya fararen tufafi" ko "Zan ba shi fararen tufafi"
Ba zai faɗi sunan mutumin kawai ba, amma zai sanar cewa mutumin nan, nashi ne"
"a gaban Ubana"
Wannan lakaɓi mai muhinminci ne na Allah dake bayyana dangantaka tsakanin Allah da kuma Yesu.
AT: [Wahayin Yahaya 2:7]
AT: [Wahayin Yahaya 1:11]
Yesu yayi magana game da ikon yanke shari'ar wanda zai iya shiga ƙasar sa kamar mabuɗin Sarki Dauda ne.
"yana buɗe kofar shiga ƙasar kuma, ba mai iya rufewa"
"yana kulle kofar kuma, ba mai buɗewa"
"Na riga na buɗe maka kofa"
AT: "ka yi bisa ga koyaswa" ko "ka yi biyayya ga umurnina"
"suna" a nan kalmace da ake amfani wa mutumin da yake da suna. AT: "ni"
AT: [Wahayin Yahaya 2:9]
Wannan alama ce ta miƙa kai, ba sujada ba. AT: "suka rusuna domin miƙa kai"
A nan kalman "ƙafafu" na nuna wanda muntanen nan na rusunawa a gaban shi. AT: "a gaban ka" ko "maka"
"zasu koya" ko "zasu amince"
"zan kuma tsare abin da zai faru da kai daga sa'a ta gwaji" ko "zan tsare ka domin kada ka shiga sa'a ta gwaji"
"lokacin gwaji." Mai yiwuwa wannan na nufin "lokacin da mutane na ƙoƙarin sa ka yi mini rashin biyayya."
Ana magana game da kasancewa nan gaba kamar zuwa ne.
yana zuwa domin yayi sheri'a. AT: "Ina zuwa da sauri domin in yi sheri'a"
Ana magana game da cigaba da gaskantawa sosai cikin Almasihu kamar riƙe abu kamkam ne. AT: "ka cigaba da gaskantawa sosai"
A nan "rawani" na nufin sakamako. AT: [Wahayin Yahaya 2:10]
A nan "Wanda yayi nasara" na nufin duk wanda yayi nasara ne. "ginshikin" na nuna muhinmin madauwamiyar guri ne na mulkin Allah. AT: [Revelation 2:7]
AT: [Wahayin Yahaya 2:7]
AT: [Wahayin Yahaya 1:11]
A nan "Amin" suna ne domin Yesu Almasihu. Ya bamu tabbacin alkawuran Allah ta wurin cewa, amin.
AT: 1) "wanda yake mulkin kowane abu da Allah ya halitta" ko 2) "ta wurin wanda Allah ya hallici komai."
Marubucin yayi magana game da Lawudikiyawan kamar su ruwa ne. Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) "sanyi" da "zafi" na nufin ƙurewan abubuwa dake jawo hankalin mutum ga ƙaunan Allah AT: "kana nan kaman ruwan da bai yi sanyi ko zafi ba"
"ka na da ɗumi kanɗan ." Marubucin yayi magana game da mutanen Lawudikiya kamar su ruwa ne da babu sanyi sosai ya rage ƙishi ga waɗanda suke shan ta, kuma babu ɗumi sosai ya dafa abu ko ya warkas da waɗanda suke yin wanka cikin ta. AT: 1) wannan na bayanin mutane da suke da ƙanƙanin tabbaci na ruhaniya ko 2) wannan na bayanin mutanen da Allah bashi da amfani a gare su.
Ana magana game da kin su kamar tofar da su ne daga baki. AT: Zan ƙi ka kamar yadda zan tofar da ruwan da ke tsaka-tsaka ne.
Yesu yayi magana game da ruhaniya mai kyau kamar halli na jiki mai kyau ne. AT: "Kuna nan kamar mutane masu takaici dayawa, abin tausayi, matalauta, makafi kuma tsirara kuke"
A nan "saya" na nufin karɓan abu daga Yesu ne da yake da muhinminci na gaske ga ruhaniyar mutane. AT: "Zo gare ni ka sami arziki na ruhaniya, wanda yana da daraja fiye da zinariyan da aka tace a wuta. Karɓi adalci daga gareni, wadda yake kama da fararen tufafi masu kyalli, domin kar ka sha kunya. Kuma ka karɓi hikima daga wuri na, wanda na nan kamar ceto ne wa idanu, domin ka iya gane abubuwan ruhaniya"
"ka himmatu ka tuba"
Yesu na magana game da yadda yake so mutane suyi dangantaka da shi kamar yana so su gayyace shi cikin gidajen su ne AT: "Ina nan kamar wanda ke tsaye a bakin kofa ina kwankwasawa"
Idan mutane na son wani ya marabce su cikin gidajen su, zasu kwankwasa a bakin kofa. AT: "Ina son ku bar ni in shiga ciki"
Kalman nan "murya ta" na nufin cewa Yesu ne ke magana. AT: "ji ni ina magana" ko "ji ƙira ta"
Wasu harsunan su fi son kalman aikaton nan "shigo" AT: "Zan shigo cikin gidan sa"
Wannan na nufin zaman su tare a matsayin abokane.
Wannan ne ƙarshen sakon Ɗan Mutum ga mala'iku na ikilisiyoyi bakwain
A zauna akan kursiyi na nufin ayi mulki ne. AT: "yi mulki tare da ni" ko "ya zauna a kursiyi na ya kuma yi mulki tare da ni"
Sashi na littafin da ke zuwa nan gaba an rubuto wa mala'ikar ikkilisiyar Sardisu ne.
Sunar da ikkilisiyar Sardisu ta yi shine cewa suna raye, amma gaskiyar kuma ita ce mattace ce.
Almasihu ya jawo masu kunne cewa su tashi su kuma abin da ya rage.
Za a sanya wa wadanda suka yi nassara fararen tufafi, za a kuma bar su cikin littafin rai, za a kuma yi maganar su a gaban Allah Uba.
Sashi na littafin da ke zuwa nan gaba an rubuto wa mala'ikar ikkilisiyar Filadelfiya ne.
Ikkilisiyar da take Filadelfiya ta yi biyayya ga maganar Almasihu kuma bata yi mutsun sanin sa ba.
Almasihu zai saka waddanda suna zuwa majami'ar shaiɗan su durkusa a kaffafun tsarkakku.
Almasihu ya gaya masu cewa su rike kam-kam abin da suke da shi saboda kada wani ya kwace masu rawanin.
Wadanda za su yi nassara za su zama ginshiki a haikalin Allah, za su samu sunan Allah, za a kuma rubuta sabon sunnan Almasihu a kan su.
Sashi na littafin da ke zuwa nan gaba an rubuto wa mala'ikar ikkilisiyar Lawudikiya ne.
Almasihu ya yi fatan cewa da ikkilisiyar Lawudikiya tana da sanyi ko zafi.
Almasihu ya na so ya amayar da ikkilisiyar da take Lawudikiya daga bakin sa domin suna nan kamar tsaka-tsaka.
Almasihu ya ce ikkilisiyar Lawudikiya tada cike da takaici, abin tausayi ce, matalauta, makaho kuma tsirara take.
Ikkilisiyar Lawudikiya ta ce ta na da arziki kuma ba ta neman komai.
Almasihu na horaswa ya kuma koyas wa waddanda yake ƙauna.
Waddanda suka yi nassara za su zauna a kursiyin Almasihu.
Almasihu ya ce wa mai karatun ya ƙassa kunnen sa ga abin da Ruhu ke faɗa wa ikkilisiyoyin.
1 Bayan wadannan abubuwa na duba, sai ga budaddiyar kofa a sama. Muryar fari da na ji kamar kakaki, na cewa hauro in nuna maka abubuwan da dole za su faru bayan wadannan al'amura." 2 Nan da nan ina cikin Ruhu, sai na ga wani kursiyin da aka ajiye shi a sama, da wani zaune bisansa. 3 Shi da ke zaune a kan tana da kamanin yasfa da yakutu. Akwai Bakangizo kewaye da kursiyin kamanin bakangizon kuwa zumurudu. 4 A kewaye da kursiyin kuwa akwai kursiyoyi ashirin da hudu, masu zama bisa kursiyoyin nan kuwa dattawa ne ashirin da hudu, sanye da fararen tufafi, da kambunan zinariya bisa kawunansu. 5 Daga kursiyin walkiya na ta fitowa, cida, da karar aradu. Fitilu bakwai na ci a gaban kursiyin, fitilun sune ruhohin Allah guda bakwai. 6 Gaban kursiyin akwai tekun gilashi, mai haske kamar karau. A tsakiyar kursiyin da kewayen kursiyin akwai rayayyun hallitu guda hudu cike da idanu gaba da baya. 7 Rayayyen hallitta na farko na da kamanin zaki, rayayyen hallitta na biyun kamanin dan maraki ne, rayayyen hailitta na uku fuskar sa kamar dan adam, kuma rayayyen hallitta ta hudu na da kamanin gaggafa mai tashi. 8 Dukan rayayyun hallittan nan hudu na da fukafukai shida shida, cike da idanu a bisa da karkashin fukafukan. Dare da rana ba sa daina cewa, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki ne Ubangiji Allah, mai iko duka, shine da shine yanzu shine mai zuwa." 9 A dukan lokacin da rayayyun hallittun nan suke ba da girma, daukaka, da godiya ga shi da ke zaune bisa kursiyin, wanda ke raye har abada abadin, 10 sai dattawan nan ashirin da hudu suka fadi da fuskokinsu a kasa gaban shi da ke zaune bisa kursiyin. Suka yi sujada ga shi da ke rayuwa har abada abadin, suna jefar da kambinsu a gaban kursiyin, suna cewa, 11 "Ka cancanta, ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka karbi yabo da daukaka da iko. Domin kai ka hallicci dukan komai, da kuma nufinka ne, suka kasance aka kuma hallicce su.
Yahaya ya fara bayanin wahayin sa akan kursiyin Allah.
"Bayan da na gan wanɗannan abubuwa kenan" ([Wahayin Yahaya 2:1-3:22])
Wannan magana na nufin zarafin da Allah ya ba wa Yahaya ya ga cikin sama, ko da shike, ta wurin wahayi.
Za a iya bayyana yadda muryar nan kamar ƙaho a fili. AT: "na magana da ni da ƙarfi kamar ƙarar ƙaho"
AT: [Wahayin Yahaya 1:10]
Yahaya yayi maganar bishewar Ruhun Allah kamar yana cikin Ruhu ne. AT: [1:10]
Duwatsu masu daraja. Mai yiwuwa yasfa na da haske irin na gilashi ko dutse mai kama da madubi, yukutu kuma jawur ne.
Dutse mai kalar kore kuma mai daraja
"kursiyoyi 24"
Wannan na kama ne da furen da ke fita a itacen zaitun ko ganyen laurel, da aka yi shi da zinariya. Irin waɗannan ganyayen ne ake ba wa masu guje-guje da suka yi nassara su saka a kawunansu.
Yi amfani da harshen ka ta wurin yin bayanin yadda walkiyar take a duk lokacin da ta bayyana.
Haka ne aradu ke yin ƙara da ƙarfi. Yi amfani da harshen ka ta wuring yin bayanin yadda ƙarar tsawa take.
AT: [ 1:4]
AT: 1) Ana magana game da teku kamar ita gilashi ne. "teku da take nan sumul kamar gilashi" ko 2) gilashi kuma kamar teku ce. "gilashi da ta bazu kamar teku"
AT: "mai haske kamar ƙarau"
"Kewaye da kursiyin nan da nan" ko "Kusa da kursiyin da kuma kewaye da shi"
"Mutune rayayyu guda hudu" ko "abubuwa rayayyu guda huɗu"
Yadda kan kowane rayyayen hallita ya bayyana wa Yahaya kwatanci ne da za a fi ganewa da sauri.
"rayayyen mutum" ko "abu mai rai." AT: [4:6]
A bisa da kuma karkashin kowane fukafuki na cike da idanu.
Ana maganar kasancewar shi nan gaba kamar zuwan ne.
Wannan mutum ɗaya ne. Wanda ke zaune a kursiyin na rayuwa har abada abadin.
Kalmomi biyun nan na ma'anar abu guda ne kuma ana sake faɗan sune domin a nanata magana. AT: "na har abada"
Da dalili suka kwanta da kawunansu ƙasa domin su nuna cewa suna sujada ne.
Wannan na kama ne da furen da ke fita a itacen zaitun ko ganyen laurel, wanda aka yi shi da zinariya. Dattatan nan sun ajiye rawanin su a ƙasa da biyayya; wannan ya nuna cewa suna miƙa kai ga ikon Allah ya yi mulkin su." AT: "suka ajiye rawanin su a gaban Allah domin su nuna cewa suna miƙa kai ga shi"
AT: 1) a ajiye abu, ko 2) a yer da abu na dole, kamar mara amfani ne. ("wurgar," [Wahayin Yahaya 2:22])
"Ubangijinmu da Allahnmu." Wannan mutum guda ne, wanda ke zaune a bisa kursiyin.
Waɗannan abubuwan ne Allah yake da su kullum. An yi maganan yabon shi domin yana da su kamar karɓan su ne yake yi. AT: "ka karɓi yabo domin ɗaukakar ka, girma, da kuma iko" ko "saboda kowa ya baka yabo domin kai mai ɗaukaka ne, mai girma ne, kuma mai iko ne"
Yahaya ya ga budaddiyar kofa a sama.
Muryan ya ce zai nuna wa Yahaha abubuwan da dole ne sun faru bayan wadannan abubuwan.
Wani na zaune a bisa kursiyi a sama.
A kewaye da kursiyin kuwa akwai kursiyoyi ashirin da huɗu tare da dattawa ashirin da huɗu da suke zaune a kan su.
Fitilu ukun sune Ruhohi bakwai na Allah.
Rayyayun hallitu guda huɗu ne suke kewaye da kursiyin.
Dare da rana hallitu guda huɗun nan basu daina waka ba, "Mai tsarki, mai tsarki, mai tsarki."
Dattawa ashirin da huɗun nan sun shirya kansu a gaban kursiyin suka kuma durkusa da fuskokin su a kasa.
Dattawan nan suka ce Allah ne ya hallice dukkan komai kuma nufin sa ne komai ya kasance.
1 Sa'annan na ga a cikin hannun daman wanda ke zaune a kan kursiyin, na ga littafi wanda ke da rubutu ciki da waje, an kuma hatimce shi da hatimai bakwai. 2 Na kuma ga wani kakkarfan mala'ika na shela da murya mai karfi, "Wa ya isa ya bude littafin ya kuma bambare hatimin?" 3 Ba wani a sama ko a kasa ko karkashin kasa da ya iya ya bude littafin ko ya karanta abin da ke cikinsa. 4 Na yi kuka mai zafi saboda ba wani da ya cancanta da zai bude littafin ko ya karanta abin da ke cikinsa. 5 Amma daya daga cikin dattawan nan ya ce mani, "Kada ka yi kuka. Duba! Zaki na kabilar Yahuza, Tushen Dauda, ya yi nasara. Ya cancanci bude littafin da kuma hatimansa bakwai." 6 Na ga Dan Rago yana tsaye tsakanin kursiyin da rayayyun halittun nan guda hudu a cikin dattawa. Yana kama da wanda aka kashe. Yana da kafonni bakwai da idanuwa bakwai; wadannan sune ruhohin Allah bakwai da aka aiko zuwa dukan duniya. 7 Ya tafi ya karbi littafin daga hannun daman wanda ke zaune bisa kursiyin. 8 Lokacin da Dan Ragon ya dauki littafin, rayayyun halittun nan hudu da dattawan nan ashirin da hudu suka fadi har kasa a gaban Dan ragon. Kowannen su na dauke da molo da tasar zinariya cike da kayan kamshi, wadanda kuwa sune addu'o'in masu ba da gaskiya. 9 Suka raira sabuwar waka: "Ka cancanta ka dauki littafinka kuma bude hatimansa. Domin an yanka ka, da jininka ka saya wa Allah mutane daga kowacce kabila, harshe, jama'a da al'umma. 10 Ka maishe su mulki da firistoci su bauta wa Allanmu, kuma za su yi mulki a duniya." 11 Da na duba sai na ji karar mala'iku masu yawa kewaye da kursiyin da rayayyun halitu da kuma dattawa. Jimillarsu ya kai dubbai goma, sau dubbai goma, da dubun dubbai. 12 Suka tada murya da karfi suka ce, "Macancanci ne Dan Ragon da aka yanka ya karbi iko, wadata, hikima, karfi, girma, daukaka da yabo." 13 Na ji kowanne halittaccen abu da ke cikin sama da kasa da karkashin kasa da cikin teku - dukan abubuwan da ke cikinsu - na cewa, "Ga shi wanda ke zaune a kan kursiyin da kuma Dan Ragon, yabo, girma, daraja, da kuma ikon yin mulki, har abada abadin. 14 Sai rayayyun halittun nan hudu suka ce, "Amin!" dattawan nan kuma suka fadi da fuskokinsu suka yi sujada.
Yahaya ya cigaba da bayanin abin da ya gani a wahayin sa game da kursiyin Allah.
"Bayan da na ga waɗancan abubuwa, na ga"
Wannan abu iri "ɗaya ne" da na [Revelation 2:3-4]
"littafi wanda ke da rubutu ciki da waje"
"yana kuma da hatimi bakwai da ya kulle"
Mutum zai ɓamɓare hatimin kafin nan ya iya buɗe littafin. AT: "Wa ya cancanci ya ɓamɓare hatimin ya kuma buɗe littafin?"
Wannan na nufin kowane wuri: wurin rayuwar Allah da mala'ikunsa, wurin rayuwar mutane da kuma dabbobi, da kuma inda mattatu suke. AT: "ko'ina a sama ko kasa ko ƙarƙashin ƙasa"
"Ka ji" ko "Kasa kunne ga abin da nake shiri in faɗa maka"
Wannan laƙabi ne da Allah yayi wa mutum daga kabilar Yahuza, zai zama babban sarki. AT: "Wanda ake kira Zaki na kabilar Yahuza" ko "Sarki da ake kira Zaki na kabilar Yahuza"
Ana magana game da wannan sarki kamar shi zaki ne domin zaki na da ƙarfi kwarai.
Wannan laƙabi ne na wanda da Allah ya yi wa zuriyar Dauda alkawali cewa zai zama babban sarki. AT: "wanda ake ce da shi Tushen Dauda"
Ɗan Ragon, ya bayyana a cikin kursiyin.
"ɗan rago" ƙaramar tunkiya ce na miji. A nan kuma na nufin Almasihu ne.
AT: [Wahayin Yahaya 1:4]
AT: "wanda Allah ya aiko cikin dukan duniya"
Ya kusanci kursiyin. Wasu harsunan sun yi amfani da wannan aikatau "zo." AT: "Ya zo"
Wannan ƙaramar tunkiya ce na miji. A nan kuma na nufin Almasihu ne. AT: [Wahayin Yahaya 5:6]
"dattawa ashirin da huɗu
"kwanta a kasa." fuskokinsu na fuskantar ƙasa domin su nuna cewa suna bautan Ɗan Ragon ne. Sun yi haka da dalili; ba cikin kusrkure ko hatsari ne suka yi ba.
AT: 1) "kowane dattijo da rayayyun hallitan" ko 2) "kowane dattijon."
Kayan ƙamshin alamar addu'a ce na masubi ga Allah.
AT: "Domin sun yanka ka" ko "Domin mutane sun kashe ka"
Idan yaren ka ya na da wata kalma na kashe dabba domin yin haɗaya, za ka iya yin amfani da shi a nan.
Da shike jini na nufin rai na mutum ne, rashin jini kuma na nufin mutuwa ne. Mai yiwuwa wannan na nufin "ta wurin mutuwar ka" ko "tawurin mutuwa."
"ka sayi mutane domin su zama na Allah" ko "ka biya farashin domin mutane su zama na Allah"
Wannan na nufin ya shafi kowane mutane na kabilu dabam-dabam.
Yi amfani da kalma na harshen ka domin nuna cewa wannan lambar na da yawa. AT: "zambar dubu ne" ko "ƙirgen dubbai masu yawa ne"
"Ɗan Ragon da aka yanka ya cancanta"
Ɗan Rago na da dukkan waɗannan abubuwa. Ana maganar yabo zama da waɗannan ababai kamar karɓan su ne. AT: [Wahayin Yahaya 4:11] AT: "domin kowa ya girmama shi, ya ɗaukaka shi, ya kuma yabe shi domin shi mai iko ne, mai wadata ne, mai hikima ne, kuma shi mai ƙarfi ne.
Wannan na nufin ko'ina ne. AT: [Wahayin Yahaya 5:3]
"Bari shi wanda ke zaune a kan kursiyin da kuma Ɗan Ragon ya samu"
Yahaya ya ga littafi da aka hatimce ta da hatimai bakwai.
Ba wanda ya cancanta ya buɗe littafin nan ko ya karanta ta.
Zaki na kabilar Yahuza, Tushen Dauda ne ya iya buɗe littafin.
Ɗan rago, da ya yi kamar a kashe shi ne, ke tsaye a sakanin dattawan a gaban kursiyin.
Ƙahohi bakwai da kuma idanuwa bakwan su ne Ruhohi bakwan da aka aiko zuwa dukkan duniya.
Tasar zinarian cike da kayan ƙamshin su ne adu'o'in tsarkakkun.
Ɗan ragon nan ya cancanta ne domin ya tsaya wa Allah mutane daga kowace kabila, harshe, da kuma al'umma da jinin sa.
Firistocin Allah za su yi mulki a duniya ne.
Mala'ikun sun ce Ɗan ragon ya cancanta ya karbi iko, wadata, hikima, ƙarfi, girma, ɗaukaka da yabo.
Dukkan abubuwan da aka hallita suka ce shi wanda ke kan kursiyin da kumaƊan Ragon nan a yabe su harabada abadin.
Dattawan sun kwanta a kasa suka kuma masa sujada.
1 Na duba lokacin da Dan Ragon ya bude daya daga cikin hatiman bakwai, sai na ji daya daga cikin rayayyun halittattun hudu ya fada da murya kamar tsawa, "Zo!" 2 Sai Na duba sai ga wani farin doki, mahayinsa na rike da baka, kuma an bashi rawani. Ya fito a matsayin mai nasara domin ya yi nasara. 3 Sa'anda Dan Ragon ya bude hatimi na biyu, sai na ji rayayyen halitta na biyu ya ce, "Zo!" 4 Sai wani doki ya fito waje - jawur. Ga mahayin aka bashi dama ya dauke salama daga duniya, domin mutanen ta su karkashe juna. Wannan mahayin an bashi babbar takobi. 5 Sa'anda Dan Ragon ya bude hatimi na uku, sai na ji rayayyen halita na uku ya ce, "Zo!" Na ga bakin doki, mai hawanta na rike da ma'auni a cikin hannunsa. 6 Sai na ji kamar wata murya daga cikin rayayyun halittattun nan hudu ta ce, "Mudun alkama guda a kan albashin yini, kuma mudun sha'ir uku. Amma kar ka bata mai da kuma ruwan inabi." 7 Da Dan Ragon ya bude hatimi na hudu, na ji muryar rayayyen halitta na hudu ya ce, "Zo!" 8 Sai na ga wani doki ruwan toka. Mai hawansa an bashi suna mutuwa, hades kuma tana biye da shi. An basu iko bisa kashi hudu na duniya su kashe da takobi, yunwa, cututtuka, da kuma namomin jeji na duniya. 9 Da Dan Ragon ya bude hatimi na biyar, a karkashin bagadi sai na ga rayukan wadanda aka kashe saboda maganar Allah, da kuma shaidar da suka rike. 10 Suka yi kuka da babban murya, "Sai yaushe ya mai iko duka, Mai Tsarki da gaskiya, zaka shari'anta mazaunan duniya, ka kuma dauki fansar jininmu? 11 Sai kowanne dayan su aka bashi farar tufa aka kuma fada masu su kara jira na lokaci kadan har sai adadin abokan bautar su da kuma 'yan'uwansu maza da mata wadanda aka kashe ya cika, kamar yadda aka kashe su. 12 Da Dan Ragon ya bude hatimi na shidan, ina kallo sai ga babbar girgizar kasa. Rana ta zama baki kirin kamar bakar tufa, wata kuma ya zama kamar jini. 13 Taurarin sama suka fado kasa, kamar yadda itacen baure ke karkade 'ya'yansa da basu nuna ba, yayin da babbar iska ta kada. 14 Sama kuma ta bace kamar takardar da aka nannade. Kowanne dutse da tsibiri aka kau da shi daga wurinsa. 15 Sai sarakan duniya da muhimman mutane da sarakunan yaki, attajirai, da masu iko, tare da kowanne mutum, bawa da 'yantacce suka boye cikin duwatsu da tsaunuka. 16 Suka ce wa tsaunuka da duwatsu, "Ku fado bisan mu! Ku boye mu daga fuskar wanda yake zaune bisa kursiyin da kuma fushin Dan Ragon. 17 Domin babban ranar fushin sa ta zo. Wa zai iya tsayawa?"
Yahaya ya cigaba da bayanin abubuwan suka faru a gaban kursiyin Allah. Ɗan Ragon ya fara buɗe hatimin kan littafin.
Wannan umurni ne ga mutum, mai yiwuwa mahayin farin dokin ne da aka yi maganarsa a aya ta 2.
Wannan na kama ne da furen da ke fita a itacen zaitun ko ganyen laurel, wanda aka yi da zinariya. Irin waɗannan ganyayen ne ake ba wa masu guje-guje da suka yi nassara su saka a kawunansu. AT: "ya karɓi rawani" ko "Allah ya ba shi rawani"
Wannan fure ne da ke fita a itacen zaitun ko ganyen laurel, wanda ake ba wa masu nasara a wasan guje-guje a zamanin Yahaya.
"hatimi na gaba" ko "hatimi lamba ta biyu"
"rayayyen halitta na gaba" ko "rayayyen hallita lamba ta biyu"
AT: "fito waje. Ga ta jawur kamar wuta" ko "fito waje. Ga ta da haske kamar wuta"
AT: "Allah ya ba wa mahayin izini" ko "aka ba wa mahayin mutum"
AT: "aka ba wa wannan mahayi babbar takobi" ko "Allah ya ba wa mahayin nan babbar takobi"
"takobi mai girma sosai" ko "takobi na ƙwarai"
"hatimi na gaba" ko "hattimi lamba ta uku"
"rayayyen halitta na gaba" ko "rayayyen hallita lamba ta uku"
kayan aiki da ake gwada nauyin abu.
Wasu harsuna sun fi so su yi amfani da waɗaṇnan aikatau ă maganar su "kimmanin kuɗi" ko "saya". Akwai alkama kaɗan domin dukan mutane, saboda haka kuɗin yayi tsada sosai. AT: "Yanzu mudun alkama na kimmanin kuɗi dinari guda" ko "Sayan mudun alkama da dinari guda"
"mudu" ma'auni ne na musanman iri ɗaya da na ruwa. AT: "Mudu ɗaya na alkama ... mudu uku na sha'ir" ko "kwano ɗaya na alkama ... kwano uku na sha'ir"
Wannan kuɗi na kai albashin kwana guda. AT: "azurfa ɗaya na kuɗi" ko "albashin aikin kwana guda"
Idan an ɓata mai da ruwan inabi, ba za'a samu dayawa domin mutane su saya ba, kuma farashin zai haura.
Mai yiwuwa waɗannan kalmomi na nufin girbin mai na zaitun da kuma girbin inabi.
"hattimi na gaba" ko "hattimi lamba ta huɗu"
"rayayyen halitta na gaba" ko "rayayyen halitta lamba ta huɗu"
"doki ruwan toka." Wannan kalar mataccen jiki ne, kalar kuma alamar mutuwa ne.
A nan "duniya" na nufin mutanen duniya ne. AT: "kashi huɗu na mutanen duniya"
Takobi makami ne, a nan kuma na nufin yaƙi ne.
Wannan na nufin cewa Mutuwa da Hades zasu zama sanaɗin da namomin jaji zasu yi faɗa wa mutane su kuma kashe mutanen.
"hatimi na gaba" ko "hatimi lamba ta biyar"
Mai yiwuwa wannan a "ƙarƙashin bagadin ne."
AT: "waɗanda wasu suka kashe"
A nan "maganar Allah" magana ce na saƙo daga Allah. Game da "riƙe," ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka: 1) riƙe shaida na nufin ba da gaskiya ga maganar Allah da kuma shaida. AT: "saboda koyaswa na littafin da kuma abun da suka koyas game da Almasihu" ko "Saboda sun ba da gaskiya ga maganar Allah, wanda shi ne shaida" ko 2 riƙe shaida kuma, na nufin ba da shaida game da maganar Allah. AT: "domin sun yi shaida game da maganar Allah"
Kalmar jini anan na nufin mutuwar su ne. AT: "hikunta waɗanda suka kashe mu"
Wannan na nufin cewa Allah ya riga ya shirya mutanen da abokan gaban su za su kashe su.
Wannan kungiyan mutane guda ne, wanda aka yi bayani a hanyoyi biyu: a matsayin masu bauta, da maza da mata. AT: "'yan'uwan su maza da mata waɗanda suke bauta wa Allah tare" ko "abokan su masubi waɗanda suke bauta wa Allah tare"
Akan yi magana game da masubi maza da mata kamar 'yan'uwane ne . AT: " 'yan'uwa masubi"
"hatimi na gaba" ko "hatimi lamba ta shida"
Wasu lokatai, ana yin tufa da bakar gashi ne. Mutane na saka tufa yayin da suke makoki. An yi amfani da wannan ne domin ya saka mutane tunani akan mutuwa da kuma makoki. AT: "baƙa kamar kayan makoki"
An yi amfani da "jini" domin ya jawo hankalin mutane su yi tunani a kan mutuwa. Za a iya bayyana wa mutane a fili, yadda take nan kamar jini. AT: "jawur kamar jini"
AT: "kamar yadda babbar iska take kaɗa itacen ɓaure ta saukar da ɗanyun 'ya'ya"
An cika yin tunanin sama kamar tana da ƙarfi kamar ƙarfe, amma yanzu kamar takarda mara ƙarfi ce aka yi maganarn ta wanda nan da nan akan yaga a kuma naɗe.
Wannan na nufin jarumai ne waɗanda suke ba da umurni a fillin daga.
manyan ramukai na gefen tudai
A nan "fuska" na nufin "gaba ne." AT: "a gaban wanda" ko "wanda"
Ranar fushinsu na nufin lokacin da zasu hukunta mugayen mutane, AT: " wannan lokaci ne na ban tsoro kwarai da za a hukunta mutane"
Ana maganar kasancewan yanzu kamar ya rigaya ya zo ne.
"Su" na nufin Ɗan Ragon da kuma wanda yake kan kursiyin.
An yi maganan yin rai kamar tsayawa ne. An yi wannan tambayan, saboda a bayyana ƙurewar fushinsu da tsoron cewa ba wanda zai iya rayuwa alokacin da Allah zai hukunta shi AT: "Ba wanda zai iya rayuwa"
Ɗan Ragon ya buɗe ɗaya daga cikin hatiman nan bakwai na littafin.
Yahaya ya ga farar doki, da mahayinsa wanda ya fito domin ya yi nasara.
Yahaya ya ga doki jawur, wanda mai hawansa ya ɗauki salama daga duniya.
Yahaya ya ga baƙar doki, wanda mai hawansa ya rike ma'auni a cikin hannunsa
Yahaya ya ga doki ruwan toka, wanda mai hawansa an bashi suna mutuwa.
Yahaya ya ga rayukan mutane waddanda aka kashe domin maganar Allah.
Rayukan suna so su san ko yaushe ne Allah zai ɗauki fansar jininsu.
An gaya wa rayukan cewa su kara jira na lokaci kadan har sai adadin abokan bautar su sun mutu.
Yahaya ya ga babbar girgizar kasa, rana ta zama baka, wata ta zama kamar jini, taurari kuma suna fãɗiwa zuwa duniya.
Yahaya ya gan su suna boyewa a cikin kogo suna kuma ce wa duwatsun su faɗo a kan su domin su boye su.
Suna so su boye daga wanda ke zaune a bisa kursiyin daga kuma fushin Ɗan Ragon.
Babban ranar fushin wanda ke zaune a kan kursiyin da kuma Ɗan Ragon ya zo.
1 Bayan wannan sai na ga mala'iku hudu suna tsaye bisa kusurwoyi hudu na duniya, suka rike iskoki hudu na duniya kamkam domin kada iska ta hura a kan duniya, a kan teku, ko wani itace. 2 Sai na ga wani mala'ika na zuwa daga gabas, wanda yake da hatimin Allah mai rai. Ya yi kira da babbar murya da mala'ikun nan hudu da aka basu dama su azabtar da duniya da teku: 3 "Kada ku azabtar da duniya, da teku, da itatuwa har sai mun sa hatimi bisa goshin bayin Allahnmu." 4 Sai naji yawan wadanda aka hatimce: 144, 000, wadanda aka hatimce daga kowacce kabilar mutanen Isra'ila: 5 dubu goma sha biyu aka hatimce daga kabilar Yahuza, dubu goma sha biyu daga kabilar Ra'ubainu, dubu goma sha biyu daga kabilar Gad, 6 dubu goma sha biyu daga kabilar Ashiru, dubu goma sha biyu daga kabilar Naftali, dubu goma sha biyu daga kabilar Manassa. 7 Dubu goma sha biyu daga kabilar Saminu, dubu goma sha biyu daga kabilar Lawi, dubu goma sha biyu daga kabilar Issaka, 8 dubu goma sha biyu daga kabilar zabaluna, dubu goma sha biyu daga kabilar Yusufu, sai kuma dubu goma sha biyu daga kabilar Bilyaminu aka hatimce. 9 Bayan wadannan abubuwa na duba, sai ga wani babban taro wanda ba mai iya kirgawa daga kowacce al'umma, kabila, mutane da harsuna tsaye a gaban kursiyin da gaban Dan Ragon. Suna sanye da fararen tufafi da ganyen dabino a hannuwansu, 10 kuma suna kira da murya mai karfi: "Ceto ya tabbata ga Allahnmu wanda ke zaune bisa kursiyi, da kuma Dan Ragon!" 11 Dukan mala'iku suna tsaitsaye kewaye da kursiyin kuma kewaye da dattawan nan da kuma rayayyun halittun nan hudu, suka kwanta rib da ciki da fuskokinsu a gaban kursiyin. Suka yi sujada ga Allah, 12 suna cewa, "Amin! yabo, daukaka, hikima, godiya, girma, iko, da karfi su zama na Allahnmu har abada abadin! Amin!" 13 Sai daya daga cikin dattawan ya tambaye ni, "Su wanene wadannan, da suke sanye da fararen tufafi, kuma daga ina suka fito?" 14 Sai nace masa, "Ya shugaba, "Ka sani," sai ya ce mani, "Wadannan sune suka fito daga babban tsanani. Sun wanke tufafin su sun maida su farare cikin jinin Dan Ragon. 15 Domin wannan dalili, suke gaban kursiyin Allah, kuma suna masa sujada dare da rana cikin haikalinsa. Shi wanda ke zaune bisa kursiyin zai zama runfa a bisan su. 16 Ba za su kara jin yunwa ba, ko kishin ruwa ba. Rana ba zata buge su ba, ko kowanne zafi mai kuna. 17 Domin Dan Ragon dake tsakiyar kursiyin zai zama makiyayin su, kuma zai bishe su zuwa mabulbulan ruwan rai, kuma Allah zai share dukan hawaye daga idanuwansu."
Yahaya ya fara yin bayani a kan wahayinsa na bayin Allah guda 144,000 waɗanda aka saka musu hatimai. Wannan ya fara bayan da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na shida, wato kafin ya buɗe hatimi na bakwain.
Ana magana game da duniya cewa shimfiɗaɗɗiyar fili ce da ke kamar littafi. Kalman nan "kusurwa huɗu" ya shafi arewa, kudu, gabas, da kuma yamma.
Kalman nan "hatimi" a nan na nufin kayan aiki da ake amfani domin saka alama ta wurin buga shi a kan wani abu mai kama da kakin zuma. A wannan yanayi, za a mori wannan kayan aiki domin saka alama a kan mutanen Allah. AT: "abin saka alama" ko "abin buga hatimi"
Kalman nan "hatimi" ya shafi alama. Wannan alama na nuna cewa mutane na Allah ne, kuma zai tsare su. AT: "saka alama a goshin su"
Goshi na saman fuska ne, bisa idanu.
AT: "Waɗandan mala'ikun Allah suka yi wa alama"
"mutane dubu ɗari da arba'in da huɗu"
"mutane 12,000 daga kabilar"
Wannan sunayen mutanen Isra'ila ne waɗanda aka hatimce.
"babban taro" ko "gaggarumin taron jama'a"
Kalan nan "fari" na nufin tsarki.
"Ceto ya zo daga"
Suna ɗaukaka Allah da kuma Ɗan Ragon. Kalman nan "ceto" za a iya bayyana shi da kalmar aiki "cece." AT: "Allahn mu, wanda ke zaune a bisa kursiyi, kuma da Ɗan Ragon da ya cece mu!"
Waɗanan rayayyun halitattu huɗun ne aka ambato a [Wahayin Yahaya 4:6-8]
A nan "kwanta da fuskoki" karin magana ne da yake nufin a kwanta da ciki a ƙasa. AT: "Shirya kansu" a [Wahayin Yahaya 4:10]. AT: "suka durƙusa a ƙasa"
"Allahnmu ne ya isa ya karɓi yabo, ɗaukaka, hikima, godiya, girma, iko da ƙarfi"
Aikatau ɗin nan "bayar" za a iya yin amfani da kalmomi domin nuna yadda za a ba da yabo, ɗaukaka, da kuma girma "ga" Allah, AT: "Sai mun ba da yabo, ɗaukaka, godiya, da kuma girma ga Allahnmu"
Kalmomi biyun nan na nufin abu ɗaya ne kuma na sake nanata cewa yabo mara ƙarewa ne.
Waɗannan fararen tufafin na nuna cewa su masu adalci ne.
"suka rayu cikin babban tsanani"
"lokacin wahala mai ban tsoro" ko "lokacin da mutane zasu sha mugun wuya"
Ana magana game da zama masu adalci tawurin jinin Ɗan Ragon nan kamar wanke tufafinsu ne a jininsa. AT: " An mayar da su masu adalci tawurin wanke tufafinsu fari cikin jininsa"
Kalman nan "jini" na nufin mutuwar Ɗan Ragon.
Waɗannan duka na nufin mutane waɗanda suka fita daga cikin Babban Tsanani,
Ana amfani da kalmomin biyun nan dare da rana domin nuna yadda suke aiki "kowane lokaci" ko "ba tsayawa"
"zai zama runfa a bisan su." Ana magana game da tsare su kamar yana basu wurin fakewa ne domin su zauna. AT: "basu gun fakewa" ko "zan tsare su"
Ana kwatanta zafin rana da hukunci da ke saka mutane shan wahala. AT: "Rana ba zai kone su ba" ko "Rana ba zai sa su zama marasa ƙarfi ba"
"Ɗan Rago, wanda ke tsaye a tsakiyar kewayen kursiyin"
Dattijon yayi magana akan kula da Ɗan Ragon na nuwa wa mutanen sa kamar kula ne da makiyayi na nuna wa tumakinsa. AT: "Gama Ɗan Ragon ... zai zama kamar makiyayi ne a gare su" ko "Gama Ɗan Ragon ... zai kula da su kamar yadda makiyayi na kula da tumakinsa"
Dattijon yayi magana akan abu da ke ba da rai kamar mabulbula sabon ruwa ne. AT: "zai jagorance su kamar makiyayi ne ke jagorantar tumakinsa zuwa sabon ruwa" ko "zai jagorance su zuwa rai kamar yadda makiyayi na jagorantar tumakinsa zuwa ruwan rai"
Hawaye na nufin ɓacin rai. AT: "Allah zai cire masu ɓacin rai, kamar yadda ake share hawaye" ko "Allah ba zai sa su, su zama masu ɓacin rai kuma ba"
Mala'iku huɗun nan suna rike da iskoki huɗu na duniya.
Mala'ikan ya ce sai an saka hatimin goshin bawowin Allah kafin nan a hallakar da duniya.
Lambar mutane da aka hatimce guda 144,000 daga kowace ƙabila na mutanen Isra'ila ne.
Yahaya ya ga babban taro daga kowace al'umma, ƙabila, jama'a, da kuma harshe a gaban kursiyin.
Waddanda suke gaban kursiyin suka ce ceto ya tabbata ga Allah da kuma Ɗan Ragon.
Sun kwanta, suka saka fuskokin su a kasa da suke yi wa Allah sujada.
Sun mayar da tufafin su fari ta wurin wanke su da jinin Ɗan Ragon ne.
Dattawan sun ce waddanda suka fito daga cikin babban tsanani ne.
Allah zai shimfida alfarwa a bisan su domin kada su kuma sha wahala.
Ɗan Ragon zai zama makiyayin su, zai kuma bishe su zuwa mabulbulan ruwan rai.
1 Lokacin da Dan Ragon nan ya bude hatimi na bakwai, sai aka yi shiru a sama na kimanin rabin sa'a. 2 Sa'anan na ga mala'iku bakwai wadanda ke tsaye a gaban Allah, aka kuma basu kahonni bakwai 3 Wani mala'ika ya zo, rike da tasar turaren konawa na zinariya, a tsaye gaban bagadi. Turaren konawa mai yawa aka bashi saboda ya mika su tare da adu'o'in dukan masu bada gaskiya akan bagadin kona turare na zinariya a gaban kursiyin. 4 Hayakin turaren konawa, da adu'o'in masu bada gaskiya, suka tashi sama a gaban Allah daga hanun mala'ikar. 5 Mala'ikan ya dauki tasar turaren konawa ya cika ta da wuta daga bagadin. Sa'annan ya wurgo ta kasa zuwa duniya, sai ga tsawar aradu, da cida, da walkiya mai haske, da kuma girgizar kasa. 6 Mala'ikun nan bakwai wadanda suke da kahonni bakwai suka yi shirin busa su. 7 Mala'ika na fari ya hura kahonsa, sai ga kankara da wuta a garwaye da jini. Aka jeho shi kasa zuwa duniya sai kashi daya cikin uku na duniya ya kone, daya cikin uku na itatuwa suka kone, da duk danyar ciyawa suka kone kaf. 8 Mala'ika na biyu ya busa kahonsa, sai wani abu mai kama da babban dutse mai cin wuta aka jefo shi cikin teku. Kashi daya cikin uku na tekun ya zama jini, 9 daya cikin uku na rayayyun halittu da ke cikin ruwa suka mutu, sai daya bisa uku na jiragen ruwa aka hallaka. 10 Mala'ika na uku ya busa kahonsa, sai gagarumin tauraro ya fado daga sama, yana ci kamar cocila, bisa kashi daya cikin uku na koguna da mabulbulan ruwa. 11 Sunan tauraron Daci. Kashi daya cikin uku na ruwaye suka yi daci, sai jama'a da yawa suka mutu domin ruwayen sun yi daci. 12 Mala'ika na hudu ya busa kahonsa, sai daya cikin kashi uku na rana ya harbu, da daya cikin kashi uku na wata da kuma daya cikin kashi uku na taurari. Sai daya cikin kashi uku nasu duka suka duhunce; daya cikin kashi uku na yini da daya cikin uku na dare suka rasa hasken su. 13 Da na duba sai na ji gaggafa da take shawagi a tsakiyar sararin sama tana kira da babban murya, "Kaito, kaito, kaito, ga mazaunan duniya sabili da sauran karar kahonni na mala'ikun nan uku da za su busa."
Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na bakwai.
Wannan ne ƙarshen hatimi guda bakwai na kan takardan. AT: "hatimi na gaba" ko "hatimi na ƙarshe" ko "hatimi na bakwai"
Aka ba kowannen su ƙaho guda ɗaya. AT: 1) "Allah ya ba su ƙahonni guda bakwai ko 2) "Ɗan Ragon ya ba su kahonni bakwai"
"zai miƙa turaren wa Allah tawurin konawa"
Wannan na nufin kwanon da ke a hannun mala'ikan. AT: "kwanon da ke a hannun mala'ikan"
Mai yiwuwa kalman nan "wuta" na nufin garwashi ne. AT: "cike da garwashi" ko "cike da wuta na garwashi"
Mala'iku guda bakwan suka busa ƙahonin a lokaci ɗaya.
AT: "Mala'ikan ya wurga ƙanƙara da wuta zuwa ƙasa a duniya garwaye da jini"
AT: "ya ƙona kashi ɗaya cikin duniya, kashi ɗaya cikin uku na itatuwa, da duk danyar ciyawa"
"Mala'ika na gaba" ko "Mala'ika na biyun"
AT: "mala'ikan ya jefa wani abu mai kama da babban dutsen da ke chi da wuta"
Za a iya bayyana kashi "Na ukun" cikin fasarar. AT: "kamar an raba tekun zuwa kashi uku ne, kuma ɗaya daga cikin ya zama jini"
AT: 1) "ya zama jawur kamar jini" ko 2) ya zama ainihin jini.
"rayyayun abubuwa na cikin teku" ko "da kifaye da kuma sauran rayyayun dabbobi na cikin teku"
"gagarumin tauraro da ke chi kamar tocila ya faɗo daga sama." Wutar gagarumin tauraro na nan da kamanin wutan tocila.
wuta da ake sa wa a sanda ya ci ta gefe daya domin ya nuna haske.
Wannan ƙaramar itace ne da yake da ɗaci. Mutane na yin magani da itacen, sun kuma yadda cewa itacen na da dafi. AT: "Sunan tauraron Daci" ko "Sunan tauraron Maganin Ɗaci"
Ana magana game da ruwa mai ɗaci kamar ita ce ɗaci. AT: "ta zama ɗaci"
"suka mutu domin su sha ruwan ɗacin"
Ana magana a kan saka mummunan abu ya faru da rana kamar za a buga shi ne. AT: "ɗaya cikin kashi uku na rana ya canja" ko "Allah ya canja ɗaya cikin kashi uku na rana"
AT: 1) "ɗaya cikin kashi uku na lokacin ya duhunce" ko 2) "ɗaya cikin kashi uku na rana, ɗaya cikin kashi uku na wata, ɗaya cikin kashi uku na tauraron ya zama da duhu"
"babu haske a lokacin ɗaya cikin uku na rana da ɗaya cikin kashi uku na dare" ko "basu yi haske a alokacin ɗaya cikin ukun rana da kuma ɗaya ciki ukun dare"
AT: "domin mala'iku uku da basu riga sun busa ƙahon su ba suna gaf ga busawa"
A lokacin da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na bakwan, sai aka yi shiru a sama.
Ƙaho guda bakwai ne aka ba wa mala'iku bakwan nan da suka tsaya a gaban Allah.
Hayakin turaren konawa tare da adu'o'in tsarkakku ne suka tashi a gaban Allah.
Da mala'ikan ya wurgo wutan, sai ga tsawar aradu, da cida, da walkiya mai haske, da kuma girgizar kasa.
Da aka busa ƙaho na farkon, sai kashi daya cikin uku na duniya ta ƙone, daya cikin uku na itatuwa suka ƙone, da duk ciyawowi.
Da aka busa ƙaho na biyu, sai Kashi daya cikin uku na tekun ya zama jini, ɗaya cikin uku na rayayyun halittu da ke cikin ruwa suka mutu, sai daya bisa uku na jiragen ruwa aka hallaka.
Da aka busa ƙaho na uku, sai Kashi daya cikin uku na ruwaye suka yi daci, sai jama'a da yawa suka mutu.
Da aka busa ƙaho na huɗu, sai daya cikin kashi uku na yini da daya cikin uku na dare suka rasa hasken su.
Gaggafan ta ce "Kaito, kaito, kaito" ga waddanda suke a duniya saboda sauran karar kahonni.
1 Sa'annan mala'ika na biyar ya busa kahonsa. Na ga tauraro daga sama da ya fado zuwa duniya. An ba tauraron nan mabudin hanyar rami marar iyaka. 2 Ya bude hanyar rami marar iyaka, sai hayaki ya fito daga kofar kamar hayaki daga babban ramin wuta. Rana da iska suka juya duhu, sabili da hayakin da ke fitowa daga kofar ramin. 3 Daga cikin hayakin kuwa sai ga fari sun fito zuwa duniya, aka ba su iko kamar na kunamai cikin duniya. 4 Aka gaya masu kada su yi wa ciyayi da kowanne koren ganye ko itace illa, sai dai mutanen da basu da hatimin Allah a goshinsu. 5 Ba a basu izini su kashe wadannan mutane ba, sai dai su azabtar da su na watani biyar. Zafinsu kuwa zai zama kamar na cizon kunama idan ta harbi mutum. 6 A kwanakin nan mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su same ta ba. Za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za ta guje su. 7 Farin kuwa suna kama da dawakai da aka shirya domin yaki. A bisa kansu akwai wani abu kamar rawanan zinariya, fuskokinsu kuma kamar na 'yan adam. 8 Gashinsu kuma kamar na mata yake, hakoransu kamar hakoran zaki. 9 Sulkunansu kuma kamar na karfe, karar fikafikansu kuma kamar karar kekunan dawakin yaki masu yawa da dawakai da aka shirya domin zuwa yaki. 10 Suna da wutsiya da kari kamar kunamai; A wutsiyar su kuma suna da ikon da zai azabtar da mutane na tsawon wata biyar. 11 Suna da wani kamar sarki a kansu, mala'ikan rami marar iyaka. Sunansa da Ibraniyanci Abadon, da Helenanci kuma Afoliyon. 12 Bala'i na fari ya wuce. Duba! Bayan wannan akwai masifu guda biyu masu zuwa. 13 Mala'ika na shida ya busa kahonsa, sai na ji murya daga kahonin bagadin zinariya da ke gaban Allah. 14 Muryar ta ce wa mala'ika na shida da ke rike da kahon, "Kwance mala'ikun nan hudu da ke daure a babban kogin Yufiretis," 15 Mala'iku hudun da aka shirya domin wannan sa'a, da wannan rana, da wannan wata, da kuma wannan shekara, aka sake su su kashe daya bisa uku na 'yan adam. 16 Yawan sojoji da ke kan dawakai shine 200, 000, 000. Na ji adadin su. 17 Haka na ga dawakan a cikin wahayina da mahayansu: Sulkunansu jawur kamar wuta, bakin shudi, da kuma ruwan doruwa. Kawunan dawakan suna kama da na zakuna, daga bakunansu kuma wuta, da hayaki da farar wuta suka fito. 18 Aka kashe daya bisa uku na mutane ta annoban nan uku: wuta, hayaki da farar wuta da suka fito daka bakunansu. 19 Domin iko na dawakan na bakunansu da wutsiyoyinsu - domin wutsiyoyinsu suna kama da macizai, kuma suna da kawuna wadanda dasu suke ji wa mutane rauni. 20 Sauran 'yan adam, da ba a kashe su ta wannan annoba ba, basu tuba daga ayyukan da suka yi ba. Basu kuma daina bautar aljanu da gumakan zinariya, da azurfa, da tagulla, da dutse, da itace ba - abubuwan da ba su gani, ji, ko tafiya. 21 Basu kuma tuba ba daga kisan kai, sihiri, fasikanci, ko kuma ayyukansu na sata ba.
Na biyar cikin mala'ikun ya fara busa ƙahon sa.
Yahaya ya ga tauraron bayan da ya faɗi. Bai ga faɗiwan sa ba.
"mabuɗin da ke buɗe rami mara iyakan"
AT:1) "hanyar rami" wata hanya ce ta bayyana ramin a matsayin doguwa da ƙarama, ko2) "hanyar rami" na nufin buɗewar ramin.
Wannan karamar rami ne mai zurfi sosai. AT:1) ramin ba karshe; ya cigaba da gangara kasa kuma ba iyaka, ko 2) zurfin ramin yayi kaman bashi da karshe ne.
Babban ramin wuta na bada babban hayaƙi, baƙar hayaƙi. AT: "kamar babban hayaƙi dake fitowa daga ramin wuta"
"zama duhu"
taron ƙwari da suke yawo tare a sama. Mutane na tsoron su domin su kan ci duk ganyaye na lambu ko na kan itace.
kunamai suna da gwanin harbi, kuma dafi ne ga sauran dabbobi da kuma mutane. AT: "gwanin harbin mutane kamar kunamai"
ƙananan ƙwari masu dafi suna harbi ne da wutsiyar su. Harbin su na da zafi sosai har ma ya kan kai tsawon lokaci.
Fara da ake gani kullum mugun hatsari ne ga mutane domin idan suka taru, su kan ci duk ciyayi ko ganyaye da aka shuka da kuma na itace. An gaya ma faran kada su yi haka.
An iya gane kalmomin nan "yin ɓarna" ko "yin illa". AT: "sai dai su yi wa mutanen illa"
Kalmar nan "hatimi" a nan na nufin kayan aiki da ake amfani domin saka alama ta wurin buga shi a kan wani abu mai kama da kakin zuma. A wannan yanayi, za a mori wannan kayan aiki domin saka alama a kan mutanen Allah. AT: "hatimi" [Wahayn Yahaya 7:3] "abin saka alamar Allah" ko "abin buga hatimin Allah"
Goshin na bisa fuskan ne, a saman idanu.
"Su" na nufin fara ne. ([Wahayin Yahaya 9:3])
mutanen da faran na harbin su
An iya gane kalmomin nan "bayar da izini" AT: "aka basu izini su azabtar da su kwarai"
Za a ba wa faran nan dama suyi har na watanni biyar.
"saka su cikin tsananin wuya"
Kunama karamar ƙwaro ne dake harbi, mai dafi a karshen doguwar wutsiyar sa. Wannan harbin kan saka zafi mai tsanani har ma ya kai ga mutuwa.
Za a iya sake faɗin wannan domin a cire kalmomi mara amfani. AT: "mutane zasu yi kokarin samun hanyar mutuwa, amma ba za su same ta ba" ko "mutane zasu yi kokarin kashe kansu, amma ba zasu samu hanyar mutuwa ba" (Dubi:
"za su bukaci mutuwa kwarai" ko "za suyi fatan cewa, da sun mutu"
Yahaya ya yi magana game da mutuwa kamar mutum ne, ko dabba da zai iya guduwa. AT: "ba zasu iya mutuwa ba" ko "ba zasu mutu ba"
Waɗannan faran, basu yi kamar faran da muke gani kullum ba. Yahaya ya bayyana su ta wurin faɗin yadda waɗansun su na kama da abubuwa da bam.
Wannan na kama ne da furen da ke fita a itacen zaitun ko ganyen laurel, kuma an yi shi ne da zinariya. Irin waɗannan ganyayen ne ake ba wa masu guje guje da suka yi nassara su saka a kawunansu.
Kalman nan "Su" na nufin fara ne.
AT: [Wahayin Yahaya 9:6] "dake da abin harbi kamar na kunama" ko "da abin harbi irin na kunama da ke saka zafi mai tsanani"
AT:1) suna da ikon yin illa wa mutane har na tsawon watanni biyar, ko 2) zasu harbi mutane har ma su sa su cikin zafi na watanni biyar.
Dukkan sunayen na nufin "Mai lalatar da abu ne"
Ana magana game da kasancewa nan gaba kamar zuwan ne.
Muryan na nufin wanda ke maganan ne. Yahaya bai faɗa wanda yake maganan ba, amma zai iya yiwuwa Allah ne. AT: "na ji wani na magana"
Waɗannan ƙaho ne da aka ƙera su da tsawo a kowace kusurwa guda huɗu na kan bagadin.
Muryan na nufin mai maganan ne. AT: Mai maganan ya ce"
AT: "Mala'ikan ya saƙe mala'iku huɗun da aka shirya su domin ... a wannan shekaran"
AT: "Mala'iku huɗun da Allah ya shirya su"
An yi amfani da kalmomin nan domin nuna cewa akwai wani lokaci na musamman, amma ba kowane lokaci kawai ba. AT: "ainihin wannan lokacin"
Wasu hanyoyin da zaka iya bayyana wannan na kamar haka: "zambar dubu ɗari biyu" ko "dubu ɗari biyu" ko "dubu ashirin sui dubu goma." Idan harshen ka tana da wata kalma na musanman domin yin haka, ka yi amfani da ita. AT: [Wahayi Yahaya 5:11]
"jawur kamar wuta" ko " da haske jawur" AT: [Wahayin Yahaya 6:3]
"rawaya kamar farar wuta" ko "rawaya da haske kamar farar wuta"
"wuta, hayaƙi, da kuma farar hayaƙi ya fito daga bakinsu"
"ɗaya cikin uku na mutanen." AT: "Na uku" [Wahayin Yahaya 8:7]
Kalman nan "iko" za a iya fasarar shi da kalmar siffa. AT: "Domin bakuna, da wutsiyoyin dawakan ne na da iko sosai" ko "gama bakuna, da wutsiyoyin dawakan ne suka yi wa mutane rauni"
AT: "waɗanda annoban nan bai kashe ba"
Waɗannan kalmomin na tunashe mu cewa gunki basu da rai kuma basu cancanta a ɗaukaka su ba. Amma mutane basu daina ɗaukaka su ba. AT: "duk da yake gunki baya gani, ji ko tafiya"
Da aka busa ƙaho na biyar din, sai Yahaya ya ga tauraro daga sama da ya faɗo zuwa duniya.
Tauraron ta buɗe hanyar rami mara iyaka.
An gaya wa farãn cewa kada su yi wa duniya illa, amma mutane waddanda ba su da hatimin Allah kadai.
Mutanen da aka azabtar da su da wannan farãn za su nema mutuwa amma ba za su samu ba.
Ƙarar fikafikin farãn kamar ƙarar ce na dawankan yaki da kuma dokuna da suke gudu zuwa wurin yaki.
Sarkin farãn shine Abadon, ko da Helenanci kuma Afoliyon, mala'ikan rami.
Bala'i na fari ya wuce bayan da aka busa ƙaho na biyar.
Da aka busa ƙaho na shida, Yahaya ya ji murya daga bagadin zinariya da ke gaban Allah.
Da suka ju muryar, sai aka kwance mala'iku huɗun nan domin su kashe kashi ɗaya bisa uku na 'yan adam.
Yahaya ya ga sojoji 200,000,000 a kan dawakai.
Annobar wuta ne, da hayaƙi, da farar wuta da suka fito daga bakunan dokunan ne suka kashe kashi ɗaya bisa uku na mutanen.
Mutanen da annoban nan bata kashe su ba, ba su tuba daga ayukan suka yi ba, basu kuma daina bautar aljanun ba.
1 Sa'anan na ga wani babban mala'ika yana zuwa daga sama. Yana lullube cikin girgije, a bisa kansa akwai bakangizo. Fuskarsa kamar rana, kafafunsa kamar ginshikan wuta. 2 Yana rike da karamin littafi a hannunsa, da aka bude, sai ya sa kafarsa ta dama a bisa teku, kafarsa ta hagu kuma a kan kasa. 3 Sai yayi ihu da babbar murya kamar zaki mai ruri. Lokacin da ya yi ihu, tsawan nan bakwai suka yi magana da karar su. 4 Da tsawan nan bakwai suka yi magana, ina dab da rubutu, amma na ji wata murya daga sama cewa, "Ka rike asirin abin da tsawan nan bakwai suka fada. Kada ka rubuta shi." 5 Sai mala'ikan da na gani tsaye bisa teku da kasa, ya daga hannun damarsa sama. 6 Sai ya rantse da wannan da ke raye har abada abadin - wanda ya halicci sama da duk abinda ke cikinsa, da duniya da duk abin da ke a kanta, da teku da dukan abin da ke cikinsa, sai mala'ikan ya ce, "Babu sauran jinkiri. 7 Amma a ranar da mala'ika na bakwai yana dab da busa kahonsa, a lokacin ne asirin Allah zai cika, daidai da yadda ya sanar wa bayinsa annabawa." 8 Muryar da na ji daga sama ta sake magana da ni: "Tafi, ka dauki budadden littafin da ke hannun mala'ikan da ke tsaye bisa teku da kan kasa." 9 Sai na tafi wurin mala'ikan na ce da shi ka bani karamin littafin. Yace dani, "Dauki littafin ka ci. Zai sa cikinka ya yi daci, amma a bakinka zai yi zaki kamar zuma." 10 Na dauki karamin littafin daga hannun mala'ikan na ci. Ya yi zaki sosai a bakina kamar zuma, amma da na ci, sai cikina ya zama da daci. 11 Wani yace mani, "Dole ka sake yin annabci kuma game da mutane masu yawa, da al'ummai, da harsuna da sarakuna."
Yahaya ya fara bayanin wahayin babban mala'ika da yake riƙe da littafin. A wahayin Yahaya, yana kallon abin da ke faruwa a duniya. Haka ya faru ne a tsakanin busa ƙaho na shida da na bakwan.
Yahaya ya yi magana game da mala'ikan kaman ya saka gajimare ne a matsayin kayan sa. Ana iya gane wannan bayanin ta wurin magana ne. Ko da shike, domin ba kullum bane ake ganin abubuwan a cikin wahayi, za a iya gane wannan cikin yanayin rubutu.
Yahaya ya kwatanta hasken fuskarsa da hasken rana. AT: "Fuskarsa da haske kamar rana"
AT: "Kafafunsa suna kamar ginshiƙan wuta"
"Ya tsaya da ƙafar shi na dama a bisa teku, ƙafar shi na hagu kuma a kan kasa"
"Sai mala'ikan yayi ihu"
An bayyana tsawan nan kamar mutum ne wanda ya iya magana. AT: " tsawan nan bakwai suka yi magana da babban murya" ko "tsawan yayi ƙara da ƙarfi sau bakwai"
Ana magane akan tsawan da zai auko sau bakwai kamar "tsawa" bakwai ne dabam dabam.
Kalman nan "murya" na nufin kalmar da ke fitowa daga wani wanda ke fiye da mala'ikan. AT: "amma na ji muryar wani na magana daga sama"
Yayi haka domin ya nuna cewa yana rantsuwa da Allah.
"Ya yi roƙo cewa abin da zai faɗa ya zama tabbatatce ta wurin wanda ke raye har abada abadin"
A nan "wanda" na nufin Allah ne.
"Babu sauran jira" ko "Allah ba zai yi jinkiri ba"
AT: "asirin Allah zai cika" ko "Allah zai kammala shirin da yayi a sirance"
Yahaya ya ji murya daga sama, wanda ya ji a 10:3 ya sake mishi magana. [Wahayin Yahaya 10:4]
Kalman nan "murya" na nufin mai maganan ne. AT: "Wanda na ji ke magana daga sama" ko "Wanda ya mini magana daga sama"
Yahaya ya ji
"Mala'ika ya ce mini"
"sa ... tsami" ko "sa ... guba." wannan na nufin mumunan ɗanɗono daga ciki, bayan da aka ci wani abu mara kyau.
Wannan na nufin mutane ne da suke magana da harshen. AT: "harsuna dayawa dabam-dabam" ko "taron mutane dayawa waɗanda suke magana da nasu harshen"
Mala'ikan na da fuska kamar rana da kuma kafafu kamar ginshikan wuta.
Mala'ikan ya tsaya da kafar sa na dama a kan teku sai kuma kafarsa na hagu a kasa.
An gaya wa Yahaya cewa kada ya yi rubuta game da abin da tsawan nan guda bakwai suka faɗa.
Babban mala'ikan nan ya yi rantsuwa da wanda ke raye na harabada abadin, wanda ya halici sama da kasa, da kuma teku.
Mala'ikan ya ce, idan aka busa ƙaho na bakwan, babu sauran jinkiri ba, amma a lokacin ne asirin Allah zai cika.
An gaya wa Yahaya cewa ya ɗauki buɗaɗɗen littafin daga hannun mala'ikan.
Mala'ikan ya faɗi cewa littafin zai yi daɗi a bakin Yahaya, amma daci kuma a cikinsa.
An gaya wa Yahaya cewa ya yi anabci game da jama'a, al'ummai, harshuna, da kuma sarakai.
1 Aka bani sanda in yi amfani da ita kamar sandar awo. Aka ce mani, "Tashi ka auna haikalin Allah da bagadi, da wadanda ke sujada a cikinsa. 2 Amma kada ka auna harabar haikalin, domin an ba da shi ga Al'ummai. Za su tattake birnin mai tsarki har wata arba'in da biyu. 3 Zan ba shaidu na biyu iko su yi anabci na kwanaki dubu daya da dari biyu da sittin, sanye da tsummoki. 4 Wadannan shaidu sune itatuwan zaitun biyu da kuma fitilu biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya. 5 Idan wani ya yi niyyar cutar da su, wuta na fitowa daga bakinsu ta lashe makiyansu. Duk mai son cutar da su, dole a kashe shi ta wannan hanya. 6 Wadannan shaidu suna da iko su kulle sama domin kada a yi ruwa a lokacin da suke anabci. Suna da iko su juya ruwaye su zama jini, su kuma bugi duniya da kowacce irin annoba duk lokacin da suka ga dama. 7 Sa'adda suka gama shaidarsu, dabban da ke fitowa daga rami marar iyaka zai yi yaki da su. Zai ci nasara da su ya kashe su. 8 Gawawwakinsu zasu kwanta kan hanyar babban birnin nan (wanda ma'anar sa ake kira Saduma da Masar) inda aka gicciye Ubangijinsu. 9 Wajen kwana uku da rabi wadansu daga dukan mutane, da kabila, da harshe, da al'umma za su yi kallon gawawwakinsu. Za su ki yarda a sa su cikin kabari. 10 Mazaunan duniya zasu yi murna da biki a kansu. Har za su aika wa juna kyautai saboda annabawan nan biyu da suka azabtar da mazaunan duniya. 11 Amma bayan kwana uku da rabi, numfanshin rai daga wurin Allah zai shiga cikinsu sa'annan za su tsaya a kan kafafunsu. Matsanancin tsoro zata fado kan wadanda za su gansu. 12 Sa'annan zasu ji murya mai kara daga sama tana ce masu, "Ku hauro nan!" Sa'annan za su tafi sama cikin gajimarai, makiyansu suna kallo. 13 A waccan sa'a za a yi babbar girgizar kasa, sai kashi daya cikin goma na garin ya fadi. Mutane dubu bakwai za su mutu a girgizar kasar, wadanda suka tsira kuwa za su tsorata su ba da daukaka ga Allah na sama. 14 Annoba ta biyu ta wuce. Duba! Annoba ta uku tana zuwa nan da nan. 15 Sa'annan mala'ika na bakwai ya busa kahonsa, sai muryoyi masu kara suka yi magana cikin sama cewa, "Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa. Zai yi mulki har abada abadin." 16 Sa'annan dattawan nan ashirin da hudu da ke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fadi fuskokinsu na kasa. Suka yi wa Allah sujada. 17 Suka ce, "Mun yi maka godiya, Ubangiji Allah, Madaukaki, wanda yake yanzu da wanda yake a da, saboda ka dauki ikonka mai girma ka fara mulki. 18 Al'ummai suka fusata, amma hasalar ka ta zo. Lokaci ya zo da za a yi wa mattatu sharia, da zaka ba da sakamako ga bayinka annabawa, da masu ba da gaskiya, da wadanda suka ji tsoron sunanka, karami da babba. Lokaci kuma ya yi da za ka hallaka wadanda ke hallakar da duniya." 19 Sa'annan aka bude haikalin Allah da ke sama, sai aka ga akwatin alkawarinsa a cikin haikalinsa. Sai ga hasken walkiya, da rugugi, da aradu, da girgizar kasa, da manyan duwatsun kankara.
Yahaya ya fara yin bayani wahayi da ya gani game da karɓan sandar awu da kuma shaidu guda biyu da Allah ya zaɓa. Wannan wahayin ya faru ne bayan da aka busa ƙaho na shida da na bakwan.
AT: "Wani ya bani sanda"
Wannan kalma "mini" ko "ni" na nufin Yahaya ne.
"ƙirga waɗanda suke sujada cikin haikalin"
a yi da abu kamar mara amfani ne, ko a yi tafiya akan sa
"wata 42"
Allah ya cigaba da magana da Yahaya.
"na kwanaki dubu daya da ɗari biyu da sittin" ko "na kwanaki ɗari goma sha biyu da sittin"
Za a iya bayyana dallilin da zasu sanye tsummokin. AT: "kwanankin, suna sa mummunan kaya na makoki" ko "kwanakin: zasu saka kaya mai kaikayi su nuna cewa suna cikin mugun ɓacin rai"
Itatuwan zaitun biyu da fitili biyu alama ne na waɗannan mutanen. AT: "Itatuwa zaitun biyu da fitili biyu da suka tsaya a gaban Ubangijin duniya na madadin waɗannan shaidun ne"
Yahaya na son masu karatun su samu sani game da su domin sheƙaru da suka wuce da dama wani annabi ya yi rubutu akan su. AT: "itatuwan zaitun biyu da kuma fitilu biyu, da aka yi magana a cikin littafin, cewa"
Domin wannan game da abin da zasu faru nan gaba ne, za a iya a faɗan su a kalmomi na gaba. AT: "wuta na fitowa daga bakinsu ta lashe makiyansu"
Ana magana game da ƙonewar wuta kamar dabba ne da zai iya cinye su. AT: "wuta ... ta lashe makiyansu" ko "wuta ... zai ƙone dukkan makiyansu"
Yahaya yayi maganar sama kamar yana da ƙofa ne da ake buɗewa domin a sa ruwa faɗowa ko a kulle domin a hana ruwa. AT: "a hana ruwa faɗowa daga sama"
"su canja"
Yahaya ya yi magana game da annoban nan kamar sanda ce da wani zai iya ya bugi duniya da ita. AT: "ya auko da kowace irin damuwa a duniya"
Wannan siririn rami ne mai zurfi sosai. AT:1) ramin da ba karshe; ya cigaba da gangara ƙasa kuma ba iyaka, ko 2) zurfin ramin yayi kamar bashi da karshe ne. AT: [9:1]
Wannan na nufin jikunan shaidu guda biyun nan.
Birnin na da hanyoni fiye da ɗaya. Wannan fili ne inda jama'a zasu iya ganin su. AT: "a wata hanyar babban birnin" ko "a ainihin hanyar babban birnin"
"kwana 3 da rabin kwana guda" ko "kwana 3.5" "kwana 3,1/2"
Wannan alaman rashin biyayya ne.
"zasu yi murna cewa shaidu guda biyun sun mutu"
Wannan yana nuna yadda mutanen suka yi murna.
Domin wannan dalilin ne mutane zasu yi murna saboda shaidun sun mutu.
Ana maganan samun dama domin yin nufashi kamar wani abu ne da zai iya zuwa cikin mutane. AT: "Allah zai saka shaidu guda biyun nan suyi nunfashi, kuma su zama rayayyu"
Ana maganan tsoro kamar abu ne da zai iya faɗi a kan mutane. AT: "Waɗanda suka gan su zasu ji matsananciyar tsoro"
Mai yiwuwa wannan yana nufin 1) shaidu biyun nan zasu ji, ko 2) mutanen zasu ji abin da ake faɗa wa shaidu biyun nan.
Kalman nan "murya" na nufin wanda yake maganan ne. AT: "wani ya masu magana da ƙarfi daga sama"
"yace wa shaidu biyun nan"
"mutane 7,000"
"wanda basu mutu ba" ko "waɗanda suke kuma yin rayuwa"
"suka faɗa cewa Allah na sama mai dauƙaƙa ne"
"Aka gama abu na biyu mai ban tsoro." AT: Dubi yadda aka juya "Annoba ta fari ta wuce" [Wahayin Yahaya 9:12]
Zuwan na nufin kasancewa nan gaba ne. AT: "Annoba na ukun zai faru ne a kwanakin nan"
Wannan shine mala'ika na bakwai na karshe. "na bakwai" [Wahayin Yahaya 8:1] AT: "mala'ika na karshe"
Kalmomin nan "muryoyi masu ƙara" na nufin wanɗanda suka yi magana da ƙarfi suka ce"
A nan "mulki" na nufin ikon yin mulki a duniya ne. AT: "Ikon yin mulki a duniya ... iko da ya zama na Ubangiji da Almasihunsa
Wannan na nufin kowa ne a duniya. AT: "kowa a cikin duniya"
"Ubangijin mu da Almasihunsa masu mulki ne yanzu a duniya"
"dattawa 24." AT: [Wahayin Yahaya 4:4]
Wannan ƙarin magana ce da take nufin sun faɗi rub da cikinsu a ƙasa. AT: "suka durƙusa" [Wahayin Yahaya 4:10]
AT: kai, Ubangiji Allah, mai mulki bisan kowa. Kai ne wanda yake a yanzu, da wanda yake a da"
"wanda ya kasance" ko "wanda ya rayu"
"wanda ya dinga kasancewa" ko "wanda ya dinga rayuwa"
Za a iya yin bayanin abun da Allah ya yi da ikon sa mai girma. AT: "ka yi nassara da ikon ka kan duk wanda yayi tawaye da kai"
"suka yi fushi sosai"
Ana maganan kasancewan abu a yanzu kamar abun ya riga ya zo ne. AT: "ka yi shirin nuna fushin ka"
Ana maganan kasancewan abu a yanzu kamar abun ya riga ya zo ne. AT: "Lokaci ya kai" ko "Yanzu ne lokacin"
Waɗannan sun yi bayanin abin da "bayin ka" na nufi. Babu bambanci a tsakanin waɗannan kungiyan mutane ukun gaba ɗaya. Anbawan suma masu ba da gaskiya ne kuma suna jin tsoron sunan Allah. "Suna" a nan magana ce da ke nuna Yesu Almasihu ne. AT: "annabawa, da masu ba da gaskiya, da waɗanda suka ji tsoron ka" ko "da annabawa da kuma su waɗanda suka ba da gaskiya suka kuma ji tsoron sunan ka"
AT: "Sai wani ya buɗe haikalin Allah da ke sama"
AT: "Na ga akawatin alkawarinsa a cikin haikalinsa"
Yi amfani da harshen ka ta wurin yin bayanin yadda walkiyar take a duk lokacin da ta bayyana. [4:5]
Haka ne haradu ke yin ƙara da ƙarfi. Yi amfani da harshen ka ta wuring yin bayanin yadda ƙarar aradun take. [4:5]
An gaya wa Yahaya cewa ya auna haikalin Allah da kuma bagaden sa, da kuma waddanda suke sujada a cikin ta.
Al'umman za su tattake birni mai tsarkin har wata arba'in da biyu.
An ba wa shaidu biyun nan iku su kashe maƙiyansu da wuta.
Za a bar gawawwakin su a titin birnin da ake kira Saduma da Masar, inda aka giciye Ubangijin su.
Mutanen da ke duniya za su yi murna da farin ciki idan aka kashe shaidu biyun nan.
Bayan kwana uku da rabi, shaidu guda biyun nan za su tsaya da kafafunsu su kuma tafi sama.
Bayan shaidu da kuma girgizar ƙasar, bala'i na biyun ta wuce.
Da aka nusa ƙaho na bakwan, an faɗi cewa mulkin duniya ta zama mulkin Ubangiji da na kuma Almasihun sa.
Dattawan suka faɗi cewa Ubangiji Allah ya fara mulki.
Lokaci ta kai da za a sharanta matattu, domin a ba da sakamako wa bawowin Allah, da kuma Allah ya hallaka waddanda suke hallakar da duniya.
Haikalin Allah ne aka buɗe a sama.
1 Aka ga wata babbar alama a sama: wata mace ta yi lullubi da rana, kuma wata na karkashin kafafunta; rawanin taurari goma sha biyu na bisa kanta. 2 Tana da ciki, tana kuma kuka don zafin nakuda - a cikin azabar haihuwa. 3 Sai aka ga wata alama cikin sama: Duba! Akwai wani katon jan maciji mai kawuna bakwai da kahonni goma, sai kuma ga kambi guda bakwai bisa kawunansa. 4 Wutsiyarsa ta share daya bisa uku na taurari a sama ta zubo su kasa. Diragon nan ya tsaya a gaban matar da ta kusan haihuwa, domin lokacin da ta haihu ya lankwame yaronta. 5 Sai ta haifi da, namiji, wanda zai yi mulkin dukan al'ummai da sandar karfe. Aka fizge yaron ta zuwa ga Allah da kursiyinsa, 6 matar kuwa ta gudu zuwa jeji inda Allah ya shirya mata domin a iya lura da ita kwanaki 1, 260. 7 A lokacin sai yaki ya tashi a sama. Mika'ilu da mala'ikunsa suka yi yaki da diragon, sai diragon da nasa mala'iku suka yake su su ma. 8 Amma diragon ba shi da isashen karfin da zai ci nasara. Don haka, shi da mala'ikunsa ba su kara samun wuri a sama ba. 9 Sai aka jefa katon diragon nan tare da mala'ikunsa kasa, wato tsohon macijin nan da ake kira Iblis ko Shaidan wanda ke yaudarar dukan duniya. 10 Sai na ji wata murya mai kara a sama: "Yanzu ceto ya zo, karfi, da mulkin Allahnmu, da iko na Almasihunsa. Gama an jefar da mai sarar 'yan'uwanmu a kasa - shi da yake sarar su a gaban Allah dare da rana. 11 Suka ci nasara da shi ta wurin jinin Dan Ragon da kuma shaidar maganarsu, gama ba su kaunaci ransu ba, har ga mutuwa. 12 Don haka, yi farinciki, ya ku sammai da duk mazauna da ke cikinsu. Amma kaito ga duniya da teku saboda iblis ya sauko gare ku. Yana cike da mummunan fushi, domin ya san lokacin sa ya rage kadan. 13 Da diragon ya ga an jefar da shi kasa, sai ya fafari matar nan da ta haifi da namiji. 14 Amma aka ba matar nan fukafukai biyu na babbar gaggafa domin ta gudu zuwa inda aka shirya mata a jeji. A wannan wuri ne za a lura da ita na dan lokaci, da lokatai, da rabin lokaci - a lokacin da babu macijin. 15 Macijin ya kwararo ruwa daga bakin sa kamar kogi, don ya kawo ambaliyar da zai kwashe ta. 16 Amma kasa ta taimaki matar. Kasa ta bude bakinta ta hadiye kogin da diragon ya kwararo daga bakinsa. 17 Sai diragon ya fusata da matar, sai ya tafi ya yi yaki da sauran zuriyarta, wadanda suka yi biyayya da umarnan Allah suna kuma rike da shaida game da Yesu. 18 Sai diragon ya tsaya a kan yashi, a gaban teku.
Yahaya ya fara kwatanta macen da ta bayyana a cikin wahayinsa.
AT: "babbar alama ta bayyana a cikin sama" ko "Ni, Yahaya, na gan babban alama a cikin sama"
AT: "macen da ta yi lulluɓi da rana da ta ke da kuma wata a ƙarƙashin ƙafafunta"
Wannan atakaice makamancin rawani ne da aka yi shi daga ganyen laurel ko reshen zaitun, amma tare da taurari goma sha biyu a haɗe a ciki.
"taurari goma sha biyu"
Yahaya ya kwatanta macijin da ya gani a cikin wahayinsa.
Wannan babban, halitta ne mai rarrafe mai kuma ban tsoro, kamar kadangare. Alamar masifa ne da bala'i ga mutanen Yahudawa.
"Da wutsiyarsa ne ya share ɗaya bisa uku na taurari"
"daya bisa uku." Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 8:7.
An yi maganar yin mulki da tsanani kamar yin mulki da sandar ƙarfe ne. Dubi yanda kun fasara magana makamanci sa a 2:27.
AT: "Allah ya ɗauki yaron ta da sauri wa kansa"
"na kwanaki dubu ɗaya da dari biyu da sittin" ko "na kwanaki dari goma sha biyu da sittin"
Yahaya ya yi amfani da wannan kalma domin ya sa dabara a labarinsa don ya gabatar da wani abin da ke faruwa a cikin wahayinsa.
"Don haka diragon da mala'ikunsa ba su iya zama a cikin sama ba"
Ana iya ba da labari game da ibilis a cikin jumla dabam bayan maganar cewa an jefa shi zuwa duniya. AT: "an jefa diragon zuwa duniya, kuma an jefa mala'ikunsa tare da shi. Shi ne tsohon Ibilis wadda yake yaudaran duniya kuma ana kiran sa Ibilis ko Shaiɗan"
AT: "Allah ya jefa babban diragon ... da mala'ikunsa daga sama ya kuma turo su zuwa duniya"
Kalmar "Ni" na nufin Yahaya.
Kalmar "murya" ya na nufin wanin da ya ke magana. AT: "Na ji wani ya na magana da ƙarfi daga sama"
An yi maganar ceton mutane da Allah ya na yi ta wurin ikonsa kamar cetonsa da ikonsa abubuwa ne da sun zo. An yi maganar mulkin Allah da ikonsa kamar sun zo ne. AT: "Yanzu Allah ya ceci mutanensa da ikonsa, Allah ya na mulki kamar sarki, kuma Almasihunsa ya na da dukka iko"
"ya soma kasancewa" ko "ya bayyana" ko "ya zama gaskiya." Allah ya na bayyana waɗannan abubuwa domin lokacin da zai faru ya "zo." Ba wai ba su kasance tun farko ba ne.
Wannan ne diragon da an jefa a cikin 12:0.
An yi maganar 'yan'uwa masubi kamar su 'yan'uwa ne. AT: "'yan'uwanmu masubi"
An yi amfani da waɗannan sashen ranaku domin a nuna "dukka lokaci" ko "da rashin dainawa"
"Suka ci nasara da mai kushewa"
Jinin na nufin mutuwarsa. AT: "domin ragon ya zub da jininsa ya kuma mutu domin su"
Ana iya bayyana kalmar "shaida." Ana iya sa a bayyane wanda su ke shaida akai. AT: "ta wurin abin da suka ce a lokacin da sun shaida wa waɗansu game da Yesu"
Masubi sun faɗi gaskiya game da Yesu, ko da shike sun san cewa maƙiyansu za su iya kashe su domin haka. AT: "amma sun cigaba da shaida ko da shike sun san cewa mai yiwuwa za su mutu don haka"
An yi maganar Ibilis kamar abu ne, kuma an yi maganar fushi kamar ruwa ne da ke iya kasance wa a cikinsa. AT: "yana mummunan fushi"
AT: "Diragon ya gane cewa Allah ya jefar da shi da ga sama ya kuma turo shi zuwa duniya"
"ya fafari matan"
"shekaru uku da rabi"
Wannan wata hanya ce na kiran diragon.
Wannan abu ɗaya ne da diragon wanda an ambata da farko a cikin 12:9.
Ruwan ya gudu daga bakinsa kamar gudun kogi. AT: "dayawa"
"ya wanke ta"
An yi maganar duniya kamar abu mai rai ne, kuma an yi maganar rami a cikin duniya kamar baki ne da na iya shanye ruwa. AT: "Rami a kasa ya bude sai kuma ruwa ya tafi cikin ramin"
Ana iya fasara kalmar "shaida." AT: "cigaba da shaida game da Yesu"
A sama an gan wata mace ta yi lullubi da rana, da wata kuma a karkashin kafafunta, da rawanin taurari goma sha biyu a bisa kanta, tana kuma kuka don zafin nakuda.
A sama an gan wata jan maciji mai kawuna bakwai da kahonni goma, da kambi guda bakwai bisa kawunansa.
Macijin ta share daya bisa uku na taurari a sama da wutsiyarta ta zubo su ƙasa.
Macijin ta na so ta cinye ɗan matan.
Allah ya dauki ɗa na mijin zuwa kursiyin sa a sama.
ɗa na mijin zai je ya yi mulkin al''ummai da sandan ƙarfe.
Matar kuwa ta gudu zuwa jeji.
Mika'ilu da mala'ikunsa suka yi yaki da macijin da mala'ikunsa.
An jefa macijin da mala'ikunsa ƙasa.
Macijin shi ne tsohon iblis ko shaiɗan.
Yan'uwan sun ci nasara da shi ta wurin jinin Dan Ragon da kuma shaidar maganarsu.
Macijin ya san ni lokaci kaɗan ya rage masa.
An bawa matar nan fukafukai biyu domin ta gudu zuwa inda aka shirya mata a wuri ne za a lura da ita.
sai macijin ya tafi ya yi yaki da sauran zuriyarta, wadanda suka yi biyayya da umarnan Allah suna kuma rike da shaida game da Yesu.
1 Sai na ga wani dabba yana fitowa daga teku. Yana da kahonni goma da kawuna bakwai. A kan kahonninsa akwai kambi goma, a kan kowanne kansa akwai suna na sabo. 2 Wannan dabban da na gani yana kama da damisa, kafafunsa kuma kamar na beyar, bakinsa kuma kamar na zaki. Wannan diragon ya ba shi karfinsa, da kursiyinsa da ikonsa mai girma na sarauta. 3 Daya daga cikin kawunan dabban ya yi kamar an kashe shi, amma rauninsa mai tsanani ya warke. Sai dukan duniya ta yi mamaki a yayin da suke bin dabban. 4 Su ma suka yi wa diragon sujada, domin ya ba dabban ikonsa. Suka yi wa dabban sujada suna ta cewa, "Wanene kamar dabban? Wa kuma zai iya yin fada da shi?" 5 Aka ba dabban baki da zai iya fadin kalmomin fahariya da sabo. Ya sami izini na zartar da iko har wata arba'in da biyu. 6 Sai dabban ya bude bakinsa yana maganganun sabo ga Allah: yana sabon sunansa, da mazauninsa, da kuma wadanda ke zaune a sama. 7 Aka yarje wa dabbar ya yi yaki da masu bi ya kuma yi nasara da su. An kuma ba shi iko bisa kowacce kabila, da jama'a, da harshe, da al'umma. 8 Dukan wadanda ke zaune a duniya za su yi masa sujada, dukan wadanda tun hallitar duniya ba a rubuta sunayensu a littafin rai na Dan Rago ba, wanda aka yanka. 9 Idan wani yana da kunne, bari ya ji. Duk wanda za a dauke shi zuwa bauta, ga bauta zai tafi. 10 Duk wanda za a kashe da takobi, da takobi za a kashe shi. Wannan kira ne na dauriya, hakuri da bangaskiya ga wadanda suke da tsarki. 11 Sai na ga wani dabban na fitowa daga cikin kasa. Yana da kahonni biyu kamar na dan rago, ya kuma yi magana kamar maciji. 12 Ya zartar da dukan ikon dabban na farko a gabansa, ya kuma sa duniya da duk mazaunanta su yi wa dabban nan na farko sujada, wanda aka warkar masa da rauni mai kamar na ajali. 13 Ya yi manyan al'ajibai. Har ya sa wuta ta sauko kasa daga sama a gaban mutane. 14 Ta wurin alamu da aka yarje masa ya yi, ya yaudari mazaunan duniya. Ya ce masu su yi wata siffa don girmama dabban da yake da raunin takobi, amma duk da haka ya rayu. 15 Aka yarje masa ya ba da numfashi ga siffar dabban domin siffar ta yi magana, ta kuma sa a kashe duk wadanda suka ki yin sujada ga dabban. 16 Ya kuma tilasta kowa, kanana da manya, mawadata da matalauta, masu yanci da bayi, su karbi alama a hannun dama ko kuma a goshi. 17 Ba shi yiwuwa wani ya saya ko ya sayar sai dai yana da alamar dabban, wato lambar nan da ke wakiltar sunansa. 18 Wannan na bukatar hikima. Idan wani yana da hikima, sai ya kididdige lambar dabban nan. Gama lambar ta mutum ce. Lambarta itace 666.
Yahaya ya fara kwatanta dabba da ya bayyana a gare shi cikin wahayinsa. Kalmar "Ni" a nan ya na nufin Yahaya.
Wannan babban, halitta ne mai rarrafe mai kuma ban tsoro, kamar kadangare. Alamar masifa da bala'i ne ga mutanen Yahudawa. Ana ƙiran whi wannan diragon Shaiɗan da kuma Ibilis." Dubi yanda an fasara wannan a cikin 12:3.
Diragon ya sa dabban ya yi karfi kamar yadda yake. Bai rasa karfinsa ba, ko da shike ya ba wa dabban.
Waɗannan kalmomi ne da ke nufin ikonsa, kuma an nanata su ne domin a nuna cewa ikon babba ne.
A nan kalmar "kursiyi" ya na nufin ikon mulkin diragon kamar sarki. AT: "girman ikonsa" ko kuma "ikonsa na yin mulki kamar saiki"
AT: "amma rauninsa mai tsanani ya warke"
"mugun rauni." Wannan irin ciwo ne da ya isa ya sa mutum ya mutu.
Kalmar "duniya" ya na nufin mutanen da ke cikin duniya. AT: "Dukkan mutanen da ke cikin duniya"
"yi biyayya da dabban"
"ya sa dabban ya samu yawan iko kamar yanda yake da shi"
Wannan tambaya ya nuna irin mamakin da sun ji game da dabban. AT: "Babu wadda ya ke da iko kamar dabban!"
Wannan tambaya ya nuna irin tsoron ikon dabban da mutanen su ji. AT: "Ba bu wanda zai iya yin faɗa da dabban ya kuma yi nasara!"
AT: "Allah ya ba dabban ... Allah ya ba dabban izini"
Ba da baki, na nufin iya magana. AT: "An bar dabban ya yi magana"
"watanni arba'in da biyu"
"faɗin abubuwan rashin ladabi game da Allah"
Waɗannan su na faɗan yadda dabban ya yi maganan saɓo ga Allah.
AT: "Allah ya ba wa dabban iko"
Wannan ya na nufin cewa mutane daga kowane harshuna su na a haɗe. Dubi yadda kun fasara irin wannan tsarin sunaye a cikin 5:9.
"yi wa dabban sujada"
Wannan jumla ya bayyana waɗanda ke duniya da za su yi wa dabban sujada. AT: "waɗanda Ragon bai rubuta sunayensu ba ... a cikin Littafin rai" ko kuma "waɗanda sunayensu babu ... a cikin Littafin rai"
"a lokacin da an hallice duniya"
"Rago" karamin tunkiya ne. An yi amfani da shi don a kwatanta Almasihu ne. Dubi yanda kun fasara wannan a cikin 5:6.
AT: "wanda mutanen sun yanka"
An yi maganar niya a ji kamar kasancewa da kunne. Dubi yadda kun fasara irin jumlan nan a cikin 2:7. AT: "Bari wanda ya na da niyar ji, ya ji" ko "Idan ku na da niya, ku ji"
Wannan ya na nufin cewa wani ya faɗi wanda za a ɗauka. Idan a na so, masu juyi su na iya faɗin wanda ya yi maganan. AT: "Idan Allah ya faɗa cewa a ɗauki wani" ko "Idan nufin Allah ne cewa a ɗauki wani"
Ana iya bayyana kalmar "bauta" da kalmar "kama." AT: "Idan nufin Allah ne maƙiya su kama wani mutum"
Ana iya bayyana kalmar "bauta" da kalmar "kama." AT: "za a kama shi" ko "makiya za su kama shi"
AT: "Idan nufin Allah ne maƙiya su kashe wani mutum da takobi"
Takobi na wakilcin yaƙi. AT: "a cikin yaƙi"
AT: "makiyan za su kashe shi"
"Dole ne tsarkaka mutanen Allah su yi hanƙuri su kuma zama amintattu"
Yahaya ya fara kwatanta wani dabba wanda ya bayyana a cikin wahayinsa.
An yi maganan zance mara daɗi kamar ƙugin diragon. AT: "ya yi magana da tsawa kamar yanda diragon na magana"
"kowane mutum a duniya"
AT: "wanda ya ke da rauni mai kamar na ajali da ya warke"
"mugun rauni." Wannan irin ciwo ne da ya isa ya sa shi ya mutu.
"Dabban daga duniya ya yi"
AT: "Allah ya yarda wa dabban daga duniya"
A nan kalmar "numfashi" na wakilcin rai. AT: "ba da rai wa siffar dabban"
Wannan siffar dabba na farko ne da an ambata.
"kashe kowane mutum da ya ƙi yin sujada ga dabba na farko"
"Dabban daga duniya ya kuma tilasta kowa"
"Mutane na iya saya ko sayad da abubuwa idan su na da alama na dabban ne kawai." Ana iya bayyana umurni da dabba wanda yake daga duniya ya bayar. AT: "Ya umurta cewa mutane na iya saya ko sayad da abubuwa idan su na da alamar dabban ne kawai"
Wannan alama ce da ya nuna cewa mutumin da ya karba shi ne na yi wa dabban sujada.
"Ana bukatar hikima" ko "ya kamata ku yi wayo game da wannan"
Ana iya juya kalmar "hikima" da "fahimta." AT: "Idan wani ya iya fahimtan abubuwa"
"ya gane abin da lambar dabban ke nufin" ko "ya fahimci abin da lambar dabban ke nufin"
AT: 1) lambar ya na wakilcin mutum ɗaya ko 2) lambar ya na wakilcin dukkan 'yan Adam.
dabba yana fitowa daga teku.
Diragon ya bawa dabbar ikon sa, kursiyin da iko ya yi mulki.
Dukan duniya ta yi mamaki a yayin da suke bin dabban domin yana da ciwo mai ɗafi wanda aka warkar.
Sai dabban ya bude bakinsa yana maganganun sabo ga Allah: yana sabon sunansa, da mazauninsa, da kuma wadanda ke zaune a sama.
An yarda wa dabban ya yi yaki da tsakakan mutane ya kuma ci nasara.
Duk wadanda sunan su yana cikin littafin rai baza su bautawa dabbar ba.
Wadanda su tsarkakku ne an kira su da hakuri, jumriya da bangaskiya.
Sauran dabbar suna da ƙaho kamar Ɗan Ragon suna kuma magana kamar diragon.
Sauran dabban sun fito daga ƙasa.
sauran dabban su sa mazaunin duniya su bautawa dabba na farko.
Wadanda suka ƙi su bautawa dabban an kashe su.
kowa ya karɓi maki a hanun damar sa ko kuwa goshin sa.
lambar dabban shi ne 666.
1 Sai na duba na ga Dan Ragon yana tsaye a kan Dutsen Sihiyona. Tare da shi akwai mutum dubu dari da arba'in da hudu wadanda aka rubuta sunansa da sunan Ubansa a goshinsu. 2 Na ji wata murya daga sama mai kara kamar kogin ruwa mai gudu da kuma aradu mai kara. Muryar da na ji ta yi kama da masu molo suna kada molonsu. 3 Suka raira sabuwar waka a gaban kursiyin da kuma gaban rayayyun halittun nan hudu, da kuma dattawan. Ba mai iya koyon wakar nan sai dai mutum 144, 000 nan wadanda aka fanso daga duniya. 4 Wadannan sune wadanda basu kazantar da kansu da mata ba, gama sun kebe kansu da tsarki daga halin jima'i. Wadannan ne ke bin Dan Ragon duk inda ya tafi. Aka fanso su daga cikin mutane domin su zama nunan fari domin Allah da Dan Ragon. 5 Ba a iske karya a bakinsu ba; ba su da aibi. 6 Na ga wani mala'ika na firiya a tsakiyar sararin sama, wanda yake da madawwamin sako na labari mai dadi domin a sanar da ita ga mazaunan duniya - ga kowacce al'umma, da kabila, da harshe, da kuma jama'a. 7 Yayi kira da babbar murya, "Ku ji tsoron Allah, ku daukaka shi. Gama sa'arsa ta hukunci ta yi. Yi masa sujada, shi wanda ya yi sama da kasa, da teku, da kuma mabulbular ruwa." 8 Sai wani malai'ka, malaika na biyu, ya biyo yana cewa, "Ta fadi, Babila mai girma ta fadi, wadda ta rinjayi dukan al'ummai su sha ruwan inabin fasikancinta." 9 Wani mala'ika - na uku - ya biyo su da murya mai karfi yana cewa, "Duk wanda ya yi sujada ga dabban da kuma siffarsa, ya karbi alama a goshinsa ko a hannunsa, 10 shi ma zai sha daga ruwan inabin fushin Allah, ruwan inabi da aka zuba tsantsa cikin kokon fushinsa. Wanda ya sha shi za a azabtar da shi da wuta, da farar wuta, a gaban tsarkakan mala'ikun Allah da kuma Dan Ragon. 11 Hayaki daga azabarsu yana tashi sama har abada abadin, kuma ba su da hutu dare ko rana - wadannan masu sujada ga dabban da siffarsa da kuma dukan wadanda suka karbi alamar sunansa. 12 Wannan shine kira domin hakurin jimrewa na wadanda ke da tsarki, wadanda suke biyayya ga dokokin Allah da bangaskiya cikin Yesu." 13 Na ji murya daga sama cewa, "Rubuta wannan: Masu albarka ne matattu da suka mutu cikin Ubangiji." Ruhu yace, 'I' domin sun huta daga wahalarsu, gama ayyukansu na biye da su." 14 Na duba sai ga farin gajimare. Zaune a kan gajimaren akwai wani kamar Dan Mutum. Yana da kambin zinariya a kansa da lauje mai kaifi a hannunsa. 15 Sai wani malaika ya fito daga haikalin, ya yi kira da murya mai karfi ga wanda ke zaune kan gajimare: "Dauki laujenka ka fara girbi, domin lokacin girbin duniya ya yi." 16 Sai wanda ke zaune a kan gajimaren ya wurga laujensa bisa kan duniya, aka kuma girbe duniya. 17 Wani mala'ika ya fito daga haikali a sama, shi ma yana da kakkaifan lauje. 18 Sai wani mala'ika ya fito daga bagadin kona turare, wanda yake da iko kan wutar. Ya yi kira da murya mai karfi ga wanda yake rike da kakkaifan lauje, "Ka dauki kakkaifan laujenka ka tattara nonnan innabi daga itacen inabin na duniya, gama inabin ya nuna." 19 Mala'ikan ya jefa laujensa duniya ya tattara girbin inabin duniya. Ya zuba shi a cikin babbar taskar wurin matsar ruwan inabi na fushin Allah. 20 Aka tattake wurin matsar inabin a bayan birni, jini ya yi ta gudu daga wurin matsar inabin, ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, har mil dari biyu.
Yahaya ya fara kwatanta ɗayan sashin wahayinsa. Akwai masubi dubu ɗari da arba'in da hudu a tsaye a gaban Ragon.
Kalmar "Ni" ya na nufin Yahaya.
"Rago" karamin tunkiya ne. An yi amfani da shi a nan domin kwatancin Almasihu. Dubi yanda kun juya wannan a cikin 5: 6.
"dubu ɗari da arba'in da hudu." Dubi yanda kun juya wannan a cikin 7:4.
AT: "wanda Ragon da Ubansa sun rubuto sunayensu a goshinsu"
Wannan muhimmin laƙabi ne wa Allah wadda ya na kwatanta dangantaka tsakanin Allah da Yesu.
"ƙara daga sama"
"mutane 144,000 su ka raira sabuwar waƙa." Wannan ya bayyana irin ƙaran da Yahaya ya ji. AT: "Ƙaran nan sabuwar waƙa ne da suka raira"
"rayayyen mutum" ko "abu mai rai." Dubi yanda kun juya "rayayyun halittu" a cikin 4:6
Wannan ya na nufin dattawa ashirin da hudu a kewaye da kursiyin. Dubi yanda kun juya "dattawa" a cikin 4:4.
AT: 1) "basu taɓa yin fasikanci da mace ba" ko 2) "basu taɓa yin jima'i da mace ba." Yin abun ƙazanta da mace na iya zama alama ne na bautar gumakai.
AT: 1) "basu yi jima'i da macen da ba matar su ba" ko kuma 2) " basu san mace ba."
An yi maganar aikata abin da Ɗan Ragon na yi kamar bin shi. AT: "su na yin duk abin da Ɗan Ragon na yi" ko "su na biyayya da Ɗan Ragon"
"Nunan fari" na nufin farkon bayaswa da za a yi wa Allah a bikin girbi. AT: "aka saya daga cikin sauran mutane kamar biki na musamman na ceto"
"Bakinsu" na nufin abin da sun faɗa. AT: "Basu taba yin ƙarya ba a lokacin da suke magana"
Wannan ya na nufin cewa mutane daga kowane harshe su na a haɗe. Dubi yadda kun fasara wannan irin tsarin sunaye a cikin 5:9.
A nan "sa'a" na wakilcin lokacin da an zaɓa don wani abu, kuma "zuwan" sa'a magana ne na lokacin da an zaɓa. Ana iya bayyana maganar "hukunci." AT: "yanzu ne lokacin da Allah ya zaɓa don hukunci" ko "yanzu ne lokacin da Allah zai hukunta mutane"
Mala'ika ya yi maganar hallakar Babila kamar ta faɗi. AT: "Babila mai girma ta faɗi"
"Babila babban gari" ko "muhimmin garin Babila." Mai yiwuwa wannan alama ce na garin Roma, wadda ke da girma, arziki, da kuma zunubi.
An yi maganar Babila kamar mutum ne, a maimakon gari da ke cike da mutane.
Wannan alama ne na kasancewa a cikin fasikancinta. AT: "zama da fasikanci kamar ita" ko "bugu kamar ta na cikin zunubin zina"
An yi maganar Babila kamar karuwa ce wanda ta sa mutane yin zunubi tare da ita. Wannan na iya zama da ma'ana biyu: fasikanci a zahiri ko kuma bautar alolin ƙarya.
"da ƙarfi"
Shan ruwan inabin fushin Allah alama ce ta hukunci daga Allah. AT: "zai kuma sha daga ruwan inabin dake wakilcin fushin Allah"
AT: "da Allah ya zuba da cikakken ƙarfi"
Wannan kokon, wanda yake a madadin alama ne, ya riƙe ruwan inabi wanda ke wakilcin fushin Allah.
"azabarsu" ya na nufin wutan da ya na azabtar da su. AT: "Hayaƙi daga wutan da ya na azabtar da su"
"babu sauƙi" ko "azaban ba ya tsayawa"
An yi amfani da waɗannan sashi biyu don a bayyana dukka lokaci. AT: "abada abadin"
"Dole ne tsarkaka mutanen Allah su yi jimriyan haƙuri da amincewa." Dubi yanda kun juya irin wannan jumla a cikin 13:10.
"waɗanda suka mutu"
"waɗanda suka mutu suke kuma haɗe da Ubangiji." Wannan na iya nufin mutane da makiyansu suka kashe su. AT: "waɗanda sun mutu domin su na a haɗe da Ubangiji"
wuya da azaba
An yi maganar waɗannan ayyuka kamar su na da rai kuma su na iya bin waɗanda sun aikata su. AT: 1) "waɗansu za su san kyawawan ayyukan da waɗannan mutanen suka yi" ko kuma 2) "Allah zai albarkace su don ayyukansu"
Wannan magana ya na kwatanta mutum, wani da ya yi kama da mutum. Dubi yanda kun juya wannan a cikin 1:13.
Wannan kamar reshen zaitun ko ganyen laurel ne, da an yi shi da zinariya. Ana ba da misalai da rawani da an yi daga ganye wanda ake ba wa masu nasara a wasan guje-guje don su sa a kawunansu.
kayan aiki ne da yake a lanƙwashe wanda ake yin amfani da shi don yankar ciyawa, hatsi da itacen inabi
"fito daga haikalin sama"
An yi maganar kasancewa a lokacin kamar ya zo.
AT: "ya girbe duniyan"
A nan "iko a kan" na nufin alhakin kula da wuta.
Wannan na nufin abu ɗaya ne.
" babbar taskar wurin matsa ruwan inabi inda Allah zai nuna fushinsa"
"kamar tsawon linzami a bakin doki"
dabara ne da an yi shi daga siririn fata wadda yake kewaye kan doki kuma a na amfani da shi don bi da doki
"stadia dubu ɗaya da ɗari shida" ko kuma "stadia ɗari goma sha shida." "filin wasanni" mita 185 ne. Wannan na iya zama kamar "kilomita 300" ko "mil 200" a awun na zamani.
Yahaya ya ga Ɗan Ragon tsaye a gaban sa a dutsen siyona.
144,000 kawai wanda aka cice su daga duniya suka iya koyin wakar.
144,000 marasa laifi aka cece su a masayin 'yaya Allah na fari da kuma Ɗan Ragon.
Mala'ikan ya bada madowamiyar sako mai kyau ga kowane al'ummai, kabila, harshe, da mutanen duniya.
mala'ikan ya ce lokacin sari'an Allah ya zo.
Mala'ikan ya gaya masu su ji tsoro Allah su kuma bashi daukaka
Mala'ika na biyu ya furta Babilan nan mai grima ta faɗi.
Wadanda suka karba alamar dabban za su sha azabtar da wuta, da farar wuta.
Tsarkakku ana kiran su ga jumirin hakuri.
Yahaya ya gan wani kamar Ɗan Mutun ya na zaune a kan gajimare.
Wanda ya zauna akan gajimaren ya waina laujen sa domin ya yi girɓin duniya.
Mala'ika mai laujen ya tara girḅin duniya ya jefa su a cikin mammatsar inabi ta fushin Allah.
An tattake mammatsar inabisai jini ya fito daga ciki.
1 Sai na ga wata alama cikin sama, babba mai ban mamaki: Akwai mala'iku bakwai rike da annobai bakwai, wadanda sune annobai na karshe domin da su ne fushin Allah zai cika. 2 Na ga wani abin da da ya bayyana mai kama da tekun gilashi mai haske garwaye da wuta. Tsaye a gefen tekun sune wadanda suka ci nasara a kan dabban da siffarsa, da kuma lambar da ke wakiltar sunansa. Suna rike da molayen da Allah ya ba su. 3 Suna rera wakar Musa, bawan Allah, da wakar Dan Rago: "Ayyukan ka manya ne da ban mamaki, Ubangiji Allah, Mai iko duka. Adalci da gaskiya hanyoyinka ne, Sarkin al'ummai. 4 Wanene ba zai ji tsoron ka ba, Ubangiji, ya kuma daukaka sunanka? Domin kai kadai ne mai tsarki. Dukan al'ummai za su zo su yi sujada a gabanka domin an bayyana ayyukan ka na adalci." 5 Bayan wadannan abubuwa na duba, kuma aka bude haikalin alfarwar shaida a cikin sama. 6 Daga wuri mafi tsarki mala'iku bakwai masu rike da annobai bakwai suka zo. Suna sanye da tufafi masu tsabta, da lallausar linin mai haske, suna kuma da damarar zinariya a kirjinsu. 7 Daya daga cikin rayyayun halitu hudu ya ba mala'iku bakwai tasoshin zinariya bakwai cike da fushin Allah wanda yake raye har abada abadin. 8 Haikalin ya cika da hayaki daga daukakar Allah da kuma ikonsa. Ba wanda ya iya shigarsa har sai da annoban nan bakwai na mala'ikun nan bakwai suka cika.
Wannan aya ya taƙaita abinda zai faru a ciki 15:16-16:21.
Waɗannan kalmomi suna da ma'ana kusan iri ɗaya kuma ana amfani da su don nanaci. AT: "wani abu da ya na ba ni mamaki sosai"
"mala'iku bakwai da su na da ikon aika annobai bakwai a duniya"
"kuma bayan su, ba za a sake wani annoba ba"
AT: "domin waɗannan annobai ne za su cika fushin Allah"
Ana iya bayyana yadda ya na nan kamar gilashi ko teku. Ma'anoni masu yiwuwa suna kamar haka 1) an yi maganar teku kamar gilashi. AT: "tekun da ya yi sumul kamar gilashi" ko 2) gilashi idan an yi maganar sa kamar teku ne. Dubi yadda an juya wannan a cikin 4:6. AT: "gilashi da an baza kamar teku"
Ana iya bayyana yanda suka ci nasara a kan lambar. AT: "waɗanda suka ci nasara a kan dabban da siffarsa ta wurin rashin bauta masu"
Ana iya sa wa a bayyane yanda sun ci nasara a kan lamban. AT: "a kan lamba da na wakilcin sunansa ta wurin rashin sa alama da wannan lambar"
Wannan na nufin lamba da an kwatanta a cikin 13:18.
"Waɗanda sun ci nasara a kan dabban su na rera waƙa"
An yi amfani da wannan tambaya domin a nuna mamakinsu a kan ɗaukaka da girman Ubangiji. Ana iya bayyana shi kamar magana mai shauki. AT: "Ubangiji, kowa zai ji tsoronka ya kuma ɗaukaka sunanka!"
"sunanka" na nufin Allah. AT: "ɗaukaka ka"
AT: "ka sa kowa ya san game da ayyukan adalcinka"
Mala'iku bakwai masu rike da annobai bakwai sun fito daga tsarkakken wuri. An riga an yi maganarsu a cikin 15:1.
Ana ganin waɗannan mala'iku rike da annobai bakwai domin a cikin 15: 7 an ba su tasoshi bakwai a cike da fushin Allah.
kaya mai kyau, da kuma tsada da ana yinsa daga abu mai siffar ganye.
Damara wani kaya mai ado ne wanda a na sa wa a jiki.
"rayayyen mutum" ko "abu mai rai." Dubi yanda kun juya "rayayyun halittu" a cikin 4:6
Ana iya bayyana kamanin ruwan inabin a cikin tasoshin. A nan kalmar "fushi" ya na nufin hukunci. Ruwan inabi alama ne na hukunci. AT: "tasoshin zinariya bakwai cike da ruwan inabi wadda ya na wakilcin fushin Allah"
"sai da mala'ikun nan bakwai su ka gama turo da annoban nan bakwai a duniya"
Mala'ika na bakwai suna da bala'i bakwai wanda sune bala'i na karshe.
Wadanda suka ci nasara akan dabban sai ga gunƙi tsaye a bakin tekun.
Wadan da suke a bakin tekun suna raira wakar Musa da na Ɗan Ragon.
An kwatanta hanyoyin Allah daidai da gaskiya.
Dukan al'ummai za su zo su yi wa Allah sujada.
sai mala'ika bakwai masu bala'i bakwai suka fito daga cikin wuri mafi tsarƙi.
An bawa mala'ikun nan bakwai tasa cike da fushin Allah.
Har sai bala'in nan bakwai sun cika, ba wanda zai shiga wuri mafi tsaƙi.
1 Na ji babban murya na kira daga cikin haikali tana ce wa malai'iku bakwai, "Ku je ku zuba tasoshi bakwai na fushin Allah a kan duniya." 2 Mala'ika na fari ya je ya zuba tasarsa a kan duniya; munanan gyambuna masu zafi suka fito wa mutane wadanda suke da alamar dabbar, wadanda suka bauta wa siffarsa. 3 Mala'ika na biyu ya zuba tasarsa cikin teku. Ya zama jini, kamar jinin wanda ya mutu, kuma kowane abu mai rai da ke cikin tekun ya mutu.' 4 Malaika na uku ya zuba tasarsa a cikin rafuffuka da mabulbulan ruwa, sai suka zama jini. 5 Na ji mala'ikan ruwaye ya ce, "Kai mai adalci ne - wanda ya ke yanzu wanda yake kuma a da, Mai Tsarkin nan, domin ka shari'anta wadannan abubuwa. 6 Domin sun zubar da jinin masu ba da gaskiya da annabawa, ka basu jini su sha; shine abinda da ya dace da su. 7 Na ji bagadi ya amsa, "I, Ubangiji Allah Mai iko duka, shari'un ka gaskiya ne da adalci." 8 Mala'ika na hudu ya zuba tasarsa a kan rana, kuma aka ba shi izini ya kone jama'a da wuta. 9 Suka kone da zafi mai tsanani, kuma suka sabi sunan Allah, wanda ke da iko akan annobai. Ba su tuba ba ko su daukaka shi. 10 Sai malaika na biyar ya zuba tasarsa a kan kursiyin dabban, sai duhu ya rufe mulkinsa. Suka cicciji harsunansu saboda zafi. 11 Suka yi sabon Allah na sama domin zafi da gyambunansu, suka kuma ki su tuba daga abin da suka yi. 12 Mala'ika na shida ya zuba tasarsa cikin babban rafi, Yufiretis. Ruwansa ya bushe domin a shirya hanya da sarakuna za su zo daga gabas. 13 Na ga kazamun ruhohi uku suna kama da kwadin da ke fitowa daga bakin diragon, da makaryacin annabi. 14 Gama su ruhohin aljanu ne masu aikata alamun ban mamaki. Sun fita za su wurin sarakunan dukan duniya domin su tattaro su wuri daya saboda yaki a babbar ranar Allah Mai iko duka. 15 ("Duba! Ina zuwa kamar barawo! Mai albarka ne wanda ke zaune a fadake, wanda ke sanye da tufafinsa domin ba zai fita tsirara a ga tsiraicin sa ba.") 16 Aka kawo su tare a wurin da ake kira Armagiddon da Ibraniyanci. 17 Mala'ika na bakwai ya zuba tasarsa cikin iska. Sa'annan babbar murya ta fito daga cikin haikali da kuma kursiyin, cewa, "An gama!" 18 Aka yi walkiya, da kararraki masu tsanani, da aradu da babbar girgizar kasa - girgizar da ta fi kowacce da aka taba yi tun da 'yan adam suke a duniya, girgizar da girma ta ke. 19 Babban birnin ya rabu kashi uku, kuma biranen al'ummai suka fadi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, sai ya ba wancan birnin koko cike da ruwan innabi wanda aka yi daga fushinsa mai tsanani. 20 Kowanne tsibiri ya bace, sai ba a kara ganin duwatsun ba. 21 Manyan duwatsun kankara, masu nauyin talanti, suka fado daga sama kan mutane. Suka zagi Allah domin annobar kankarar saboda annobar ta yi tsanani.
Yahaya ya cigaba da bayyana sashin wahayi game da mala'iku bakwai da annobai bakwai. Annobai bakwan ne tasoshi bakwai na fushin Allah.
Kalmar "Ni" ya na nufin Yahaya.
Ana iya bayyana siffar ruwan inabi a cikin tasoshin. Kalmar "fushi" a nan na nufin hukunci. Ruwan inabi alama ce ta hukunci. Dubi yanda kun juya jumla makamanci haka a cikin 15:7. AT: "tasoshi cike da ruwan inabi da ke wakilcin fushin Allah"
Kalmar "tasa" ya na nufin abin da ke cikinsa. AT: "zubo ruwan inabi daga tasarsa" ko "zuba fushin Allah daga tasarsa"
"ciwo masu zafi." Waɗannan na iya zama harbi ne daga cututuka ko lahani da bai riga ya warke ba.
Wannan alama ce da ya nuna cewa mutumin da ya karɓa ya na bauta wa dabban ne. Dubi yanda kun juya wannan a cikin 13:17.
Wannan ya na nufin dukka rafin ruwan gishiri da kuma babban teku.
Wannan ya na nufin dukka ruwa mai kyau.
AT: 1) Wannan na nufin mala'ika na uku wanda shi ne mai zuba fushin Allah a rafuffuka da mabulbulan ruwa ko 2) wannan wani mala'ika ne wanda ke lura da dukka ruwayen.
"Kai" ya na nufin Allah ne.
"Allah wanda yake, wanda yake kuma." Dubi yanda kun juya jumla makamanci haka a cikin 1:4.
A nan "zubar da jinin" na nufin kisa. AT: "sun kashe tsarkaka mutanen Allah da annabawa"
Allah zai sa mugayen mutanen su sha ruwayen da ya juya zuwa jini.
Mai yiwuwa kalmar "bagadi" a nan na nufin wani a bagadi. "Ni ji wani a bagadin ya amsa"
Yahaya ya yi maganar rana kamar mutum ne. AT: "aka kuma sa rana ya kone mutanen sosai"
AT: "tsananin zafin ya kone su sosai"
Sunan Allah a nan ya na wakilcin Allah. AT: "sun saɓa wa Allah"
Wannan jumla ya tuna wa masu karatu abin da sun riga sun sani game da Allah. Ya na taimako a wurin bayyana dalilin da mutane suke saɓa wa Allah. "Allah domin ya na da iko a kan waɗannan annobai"
Wannan ya na nufin iko sa akan waɗannan annobai da ke kan mutane, kuma da ikon hana annoban.
Wannan wurin ne da dabban ya na mulki. Ya na iya nufin hedkwatar ƙasarsa.
An yi maganar "duhu" a nan kamar wani abu ne mai kama da bargo. AT: "Ya zama duhu a duk mulkinsa" ko "dukka mulkinsa ya zama duhu"
Wannan ya na nufin mutane a cikin mulkin dabban.
AT: "Yufiretis. Ruwansa ya bushe" ko "Yufiretis, ya kuma sa ruwansa ya bushe"
Kwaɗo karamin dabba ne da na zama kusa da ruwa. Yahudawa sun ɗauke su a matsayin dabbobin mara tsarki.
Wannan babban, halitta ne mai rarrafe mai kuma ban tsoro, kamar kadangare. Alamar masifa dabala'i ne ga mutanen Yahudawa. An nuna diragon a cikin aya 9 a matsayin "Shaidan da kuma Ibilis." Dubi yanda an fasara wannan a cikin 12:3.
A aya 15, an je hutu daga ainahin labarin wahayin Yahaya. Waɗannan kalmomi ne da Yesu ya faɗa. Labarin ya cigaba a cikin aya 16.
Wannan ya na nuna cewa ba ya cikin sashin wahayin. Sai dai, wannan wani abu ne da Ubangiji Yesu ya faɗa. Ana iya bayyana wa da kyau cewa Ubangiji Yesu ya ce, kamar na cikin UDB.
Yesu zai zo a lokacin da ba wanda ke zato, kamar yadda ɓarawo na zuwa a lokacin da ba a zata ba. Dubi yanda kun juya jumla makamanci haka a 3:3.
An yi maganar yin rayuwa mai kyau kamar sanya tufafi. AT: "yin abin da ya kamata, kamar sanya tufafinsa"
Kalmar "su" a nan na nufin waɗansu mutane.
"ruhoyin aljanu su ka kawo sarakuna da sojojinsu tare"
AT: "wurin da mutane ke kira"
Wannan sunan wuri ne.
Wannan ya na nufin wani da na zaune a kan kursiyin ko wanin da ya na tsaye kusa da kursiyin ya yi magana da karfi. Ba a gane wanda na magana ba.
Ku yi amfani da yanda harshenku ke kwatanta yadda walƙiya yake a duk lokacin da ya bayyana. Dubi yanda kun juya wannan a cikin 4:5.
Waɗannan babban ƙara ne da aradu na yi. ku yi amfani da yanda harshenku ke kwatanta ƙaran aradu. Dubi yanda kun juya wannan a cikin 4:5.
AT: "Girgizan kasan ta raba babban birnin"
"Sai Allah ya tuna" ko "Sai Allah ya yi tunanin" ko "Sai Allah ya fara maida hankali a kan." Wannan ba ya nufin cewa Allah ya tuna wani abu da ya manta.
Ruwan inabi alama ce ta fushinsa. Sa mutane su sha, alama ce ta hukunta su. AT: "ya sa mutanen garin su sha ruwan inabi da ke wakilcin fushinsa"
Rashin iya ganin duwatsu magana ne wanda ke bayyana zancen cewa babu duwatsu. AT: "babu wasu duwatsu
Za ku iya sa wannan a awu na zamani. AT: "kilo 34"
An gaya wa mala'ikun nan bakwai suje su zuba a duniya tasan nan na fushin Allah.
Mumunar miki suka fito a jikin mutanen wanda suke da alamar dabban.
Yeku ya zama kamar jinin mutumin da aka kashe
Rafi da mabulbulan ruwa suka zama jini.
Ta zama daidai da gaskiya domin wadan mutane sun zubar da jinin tsakakan allah a annabawa.
Rana ya babbaka mutanen da wuta.
Wadannan basu tuba ba ko su ba wa Allah daukaka.
Duhu ya rufe mulkin dabban.
Ruwan rafin Yufiratis ya bushe domin ya gyara hanya wa sarki daga gabas.
Ruhohi marasa tsarkin nan uku sun fito su tara saraƙen duniya domin yakin a wannan babban rana ta Allah.
Sunar wurin Armagedon.
Babban murya ta ce, "an gama!" sa'annan ga walkiya, aradu, da rawar ƙasa.
A wannan lokacin, Allah ya kira ya mai da hankali akak Babila mai girma, sai ya bawa Babila kwafi cike da fushin sa.
Mutanen su zagi Allah.
1 Daya daga cikin mala'ikun nan bakwai wanda ke rike da tasoshi bakwai ya zo ya ce mani, "Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwarnan da ke zaune a kan ruwaye masu yawa. 2 Da ita ce sarakunan duniya suka yi fasikanci. Da ruwan inabinta na fasikanci marar dacewa ta sa mazaunan duniya suka bugu." 3 Sai mala'ikan ya dauke ni cikin Ruhu ya tafi da ni jeji, sai na ga mace zaune bisa jan dabba cike da sunayen sabo. Dabbar tana da kawuna bakwai da kahonni goma. 4 Matar kuwa tana sanye da tufafi na shunayya da kuma jar garura, ta kuma ci ado da kayan zinariya da duwatsu masu tamani da lu'u-lu'ai. Tana rike da kokon zinariya a hannunta cike da abubuwan kyama da na kazantar fasikancinta marar dacewa. 5 Bisa goshinta an rubuta wani suna mai boyayyar ma'ana: "Babila mai girma, uwar karuwai da na kazamtattun abubuwan duniya." 6 Sai na ga matar a buge da jinin masu ba da gaskiya da kuma jinin wadanda aka kashe su domin Yesu. Da na gan ta, na yi mamaki kwarai da gaske. 7 Amma mala'ikan ya ce mani, "Don me kake mamaki? Zan bayyana maka ma'anar matar da kuma na dabbar da ke dauke da ita, dabban nan da ke da kawuna bakwai da kahonni goma. 8 Dabban da ka gani da, yanzu ba ta, amma ta na kusan hawowa daga rami marar iyaka. Sa'annan za ta je hallaka. Wadanda ke zaune a duniya, wadanda ba a rubuta sunayensu cikin littafin rai ba tun kafuwar duniya - za su yi mamaki idan suka ga dabbar da da ta kasance, ba ta nan yanzu, amma ta kusa zuwa. 9 Wannan al'amari na bukatar hikima. Kawunnan bakwai, tuddai ne bakwai da macen ke zaune a kai. 10 Su kuma sarakuna ne bakwai. Sarakuna biyar sun fadi, daya na nan, amma dayan bai zo ba tukuna; sa'anda ya zo zai kasance na dan lokaci kadan. 11 Dabban da ya kasance a da, amma yanzu ba shi, shi ma sarki ne na takwas; amma shi daya ne cikin sarakunan nan bakwai, kuma zai tafi hallaka. 12 Kahonnin nan goma da ka gani sarakuna goma ne wadanda ba a nada su ba tukuna, amma za su karbi iko kamar na sarakai na sa'a daya tare da dabban. 13 Ra'ayinsu daya ne, za su ba da sarautarsu da ikon su ga dabban. 14 Za su yi yaki da Dan Rago. Dan Ragon zai ci nasara a kansu domin shi Ubangijin iyayengiji ne da Sarkin sarakuna - kuma tare da shi sune kirayayyun, zababbun, amintattun." 15 Mala'ikan ya ce mani, "Ruwayen da ka gani, inda karuwar ke zaune, jama'a ce, da taro masu dumbin yawa, da al'ummai da harsuna. 16 Kahonnin nan goma da ka gani - su da dabban za su ki karuwar. Za su washe ta su tsiranceta, za su lankwame namanta, za su kone ta gaba daya da wuta. 17 Gama Allah ya sa a zukantansu su yi nufinsa ta wurin amincewarsa, su sadaukar da ikonsu na yin mulki ga dabban har sai maganar Allah ta cika. 18 Matar da ka gani ita ce babban birnin nan da ke mulki bisa sarakunan duniya."
Yahaya ya fara bayyana sashin wahayinsa game da babbar karuwan.
Ana iya bayyana kalmar "hukunci." AT: "yadda Allah zai hukunta babbar karuwarnan"
"babbar karuwan nan da kowa ya sani." Ta na wakilcin wani birni mai zunubi.
Idan ku na so, za ku iya amfani da takamaiman kalma na irin ruwan. AT: "a kan rafuna dayawa"
Ruwan inabin ya na wakilcin fasikanci. AT: "Mutanen duniya sun bugu ta wurin shan ruwan inabinta,
Wannan na iya samun ma'ana biyu: fasikanci a tsakanin mutane da kuma bautar alolin ƙarya.
Wurin ya canja daga kasancewar Yahaya a sama zuwa kasancewa sa a jeji.
farin dutsen wuya. Ana samun su a cikin kwasfan wani ƙaramin dabba da na zama a cikin teku.
AT: "Wani ya rubuta suna a goshinta"
Idan ana so a bayyana cewa sunan na nufin macen ne, ana iya sa wa a jumla. AT: "Ni ne Babila, mai iko"
"ta bugu domin ta riga ta sha jinin ... ta kuma sha jinin"
"masubi waɗanda sun mutu saboda sun gaya wa waɗansu game da Yesu"
mamaki
Mala'ikan ya yi amfani da wannan tambaya domin ya tsawatawa Yahaya a hankali. AT: "Kada ka yi mamaki!"
Wani siririn rami ne mai tsananin zurfin. AT: 1) ramin wanda ba shi da ƙarshe; ya cigaba da yin ƙasa har abada ko 2) ramin ya na da zurfi sosai kamar ba shi da ƙarshe. Dubi yanda kun juya wannan a 9:1.
Ana iya juya kalmar "hallaka" da kalmar aikatau AT: "Sa'an nan za a hallaka shi" ko "Sa'annan Allah zai hallaka shi"
An yi maganar tabbacin abin da zai faru a gaba kamar dabban zai tafi wurin.
AT: "waɗanda Allah bai rubuta sunayensu ba"
Mala'ikan ya yi maganar halittar duniya da Allah ya yi kamar ya kafa tushen duniya kamar yanda wani na kafa tushen gini. AT: "kafin Allah ya halicci duniya"
Mala'ikan ya cigaba da magana. Ya bayyana ma'anar kawuna bakwai na dabban da matan ta ke kai.
Ana iya bayyana "hankali" da "hikima" tare da "tunani" da "dabara." Ana iya bayyana dalilin da ake bukatar hankali mai hikima. AT: "Ana bukatar hankali mai hikima domin a iya fahimtar wannan" ko Ya kamata ka yi tunani da dabara don ka iya fahimtar wannan"
"Wannan ya sa dole ne a sami"
A nan "ne" ya na nufin "wakilci."
Mala'ika ya yi maganar mutuwa kamar faɗiwa ne. AT: "Sarakuna biyar sun mutu"
"ɗaya sarki yanzu" ko "wani sarki na da rai yanzu"
An yi maganar rashin kasancewa kamar rashin zuwo. AT: "wani bai riga ya zama sarki ba, lokacin da zai zama sarki"
Mala'ikan ya yi maganar wani da ya cigaba da zama sarki kamar ya na kasance a wani wuri. AT: "zai iya zama sarki na ɗan loƙaci kadan"
AT: "1) dabban ya yi mulki sau biyu: na farko shi ne ɗaya daga cikin sarakuna bakwai, sai kuma sarki na takwas ko 2) dabban na ƙungiyar sarakuna bakwai ne domin ya na nan kamarsu.
An yi maganar tabbacin abin da zai faru a gaba kamar dabban zai tafi wurin. AT: " "Sa'an nan za a hallaka shi" ko "haƙiƙa Allah zai hallaka shi"
Idan harshenku ba ya raba rana zuwa sa'a ashirin da huɗu, za ku iya amfani da yanayin magana da aka saba yi. AT: "na ɗan lokaci" ko "na ɗan karamin sashin rana"
"Duka waɗannan su na tunanin abu ɗaya" ko "Duka waɗannan sun yarda su yi abu iri ɗaya"
"Rago" karamin tunkiya ne. An yi amfani da alamar a nan don a bayyana Almasihu. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 5:6.
Wannan na nufin taron mutane. Ana iya bayyana kalmomin "kira" da "zabi" a cikin siffar aiki. AT: "kirayayyun, zababbu, amintattun" ko "waɗanda Allah ya kira ya kuma zaɓa, waɗanda sun amince da shi"
A nan "ne" na matsayin "wakilci."
Idan ku na so, za ku iya yin amfani da takamamman kalma na irin ruwan. Dubi yanda kun juya "ruwaye dayawa" a cikin 17:1. AT: "rafuffuka"
babban taron mutane
Wannan ya na nufin mutane da su na da harshe ɗaya. Dubi yadda aka juya wannan a cikin 10:11.
"sace komai da ta ke da shi a kuma bar ta babu komai"
An yi maganar lankwame ta dukka kamar cin dukkan namanta. "za su hallaka ta dukka"
Za su yarda su ba da ƙarfinsu ga dabban, amma ba zai zama cewa su na so su yi biyayya da Allah ba. AT: "Gama Allah ya sa a zukantansu su yarda su bayar ... sai maganar Allah ta cika, kuma ta yin haka, za su yi nufin Allah"
A nan "zuciya" na nufin sha'awa. An yi maganar sa su su yi wani abu kamar sa wa a zuciyarsu su yi shi. AT: "Allah ya sa su su so"
"ikon sarauta"
AT: "sai Allah ya cika abin da ya ce zai faru"
A nan "ne" na matsayin "wakilci."
A lokacin da aka ce birnin na mulki, ana nufin cewa shugaban birnin ya na mulki. AT: "
Mala'ikan ya ce zai nuna wa Yahaya hallakar babban karuwan.
Matan tana zaune akan dabban da kawuna bakwai da kahonni goma.
Kwafin tana cike da abubuwan kyama dakazanta da fasikancinta.
Sunar matan shine, "Babila mai girma, uwar karuwai da abubuwan ban kyama na duniya".
Matar ta bugu da jinin tsakaku da kuma asirin Yesu.
Dabban ya fito daga can cikin karkashin rami.
Dabban zata tafi zuwa hallaka.
Kawunan bakwai sune kawunan tuddai da matar take zama a kai, kuma sarakai bakwai ne.
Dabban zata tafi zuwa hallaka.
kahonnen goma sarakai goma ne.
idan hankalin su ta zama ɗaya, za su yi yaki da Ɗan Ragon.
Ruwan mutane ne, dayawa al'ummai da harshe.
za su ki matan su washe ta,tsiraita ta,su ci naman ta su kuma kone ta da wuta.
matar da Yahaya ya gani itace brini mai girma da ta yi mulki bisa sarakan duniya.
1 Bayan wadannan abubuwa sai na ga wani mala'ika yana saukowa daga sama. Yana da babban iko sosai, duniya kuwa ta haskaka da daukakarsa. 2 Ya yi kira da kakkarfar murya cewa, "Ta fadi, Babila mai girma ta fadi! Ta zama mazaunin aljannu, da matattarar kowanne kazamin ruhu da kuma mazaunin kowanne kazami da kyamataccen tsuntsu. 3 Gama dukan al'ummai sun sha ruwan innabin fasikancinta. Sarakunan duniya sun aikata fasikanci da ita. Attajiran duniya sun arzuta da ikon rayuwar annashuwarta." 4 Sai na ji wata murya daga sama ta ce, "Ku fito daga cikinta, mutanena, domin kada kuyi zunubi irin na ta, domin kuma kada bala'inta ya auko maku. 5 Zunubanta sun taru sun yi tsayi har sama. Allah kuma ya tuna da miyagun ayyukanta. 6 Ku saka mata gwargwadon yadda ta saka wa wadansu, ku biya ta ninki biyu na abin da ta yi; a cikin kokon da ta dama, ku dama mata ninki biyu. 7 Kamar yadda ta daukaka kanta ta yi ta annashuwa, ku wahalsheta da azaba da bakin ciki haka. Domin ta ce a zuciyarta, 'Ina zaune kamar sarauniya; ni ba gwauruwa ba ce, kuma ba zan taba yin makoki ba,' 8 Saboda haka a rana daya bala'inta zai auko mata; mutuwa, makoki da kuma yunwa. Wuta za ta kona ta kurmus, domin Ubangiji Allah mai iko ne, kuma shine mai hukuntata." 9 Sarakunan duniya da suka yi fasikanci, har suka baude tare da ita, za su yi kuka da kururuwa domin ta sa'adda suka ga hayakin kunarta. 10 Za su tsaya can nesa suna tsoron azabarta, suna cewa, "Kaito, kaiton babban birni, Babila, birni mai iko! Domin cikin sa'a guda hukuncinta ya zo." 11 Manyan 'yan kasuwan duniya za su yi kuka da bakin ciki dominta, da shike ba wanda ke sayan kayanta kuma - 12 kayan zinariya, azurfa, da duwatsun alfarma, da lu'u-lu'u, da lilin mai laushi, da hajja mai ruwan jar garura, da siliki, da jar alharini da itacen kamshi iri iri, da kayan da aka sassaka da itace mai tsada, da na tagulla, da na bakin karfe, da na dutse mai sheki, 13 da kirfa, da kayan yaji, da turaren wuta, da mur da lubban, da ruwan innabi, da mai, da garin alkama, da alkama, da shanu, da tumaki, da dawakai, da kekunan doki, da bayi, da rayukan 'yan adam. 14 Amfanin da kika kwallafa rai da duk karfinki sun fice daga gareki. Duk annashuwarki da darajarki sun bace, ba za a kara samunsu ba kuma. 15 Manyan 'yan kasuwa na wadannan kaya da suka azurta ta wurinta, za su tsaya can nesa da ita, sabili da tsoron azabarta, kuka da kururuwar bakin ciki. 16 Za su ce, "Kaito, kaito ga babban birni da take sanye da lilin mai laushi da tufafi masu jar garura da kuma jan alharini, da ta ci ado da kayan zinariya, da duwatsu masu daraja da lu'u-lu'u! 17 A cikin sa'a guda duk dukiyan nan ta lallace. Kowanne matukin jirgin ruwa, da fasinjoji, da masu tuki da duk wadanda suke samun biyan bukatun rayuwarsu daga ruwa, suka tsaya can nesa. 18 Suka yi kuka sa'anda suka ga hayakin kunarta. Suka ce, "Wanne birni ne ya yi kama da babban birnin?" 19 Suka watsa kura a kawunansu, suka yi kuka da karfi, da kururuwa da bakin ciki, "Kaito, kaiton babban birnin nan inda duk masu jiragen ruwa suka azurta daga dukiyarta. Domin a sa'a guda an hallakar da ita." 20 "Ku yi murna a kanta, sama, ku masu ba da gaskiya, manzanni, da annabawa, domin Allah ya kawo hukuncinku a kanta!" 21 Wani kakkarfan mala'ika ya dauki wani dutse mai kama da dutsen nika, ya jefa shi cikin teku yana cewa, "Ta wannan hanya, Babila, babban birnin, za a jefar da ita kasa da karfi, ba za a kara ganinsa ba. 22 Muryar masu kidar molaye, mawaka, masu busa sarewa, da na masu busa algaita, ba za a kara ji a cikinta ba. Babu wani mai kowanne irin sana'a da za a samu a cikinta. Ba za a kara jin karar nika a cikinta ba. 23 Hasken fitila ba za ya kara haskakawa a cikin ki ba. Ba za a kara jin muryoyin ango da na amarya a cikinki ba, domin attajiranki sune 'ya'yan masu mulki a duniya, kuma ta wurin sihirinki kika yaudari al'ummai. 24 A cikinta aka sami jinin annabawa da na masu ba da gaskiya, da jinin duk wadanda aka kashe a duniya."
Wani mala'ika ya sauƙo daga sama ya kuma yi magana. Wannan mala'ikan dabam ne da wanda yake a aya da ta wuce, wanda ya yi magana game da karuwa da kuma dabban.
Kalmar "ita" na nufin birnin Babila, wadda aka yi maganar ta kamar karuwace.
Mala'ikan ya yi maganar halakar Babila kamar ta faɗi. Dubi yanda kun juya wannan a cikin 14:8.
"kyamataccen tsuntsu"
Al'ummai na nufin mutanen waɗannan al'ummai. AT: "mutanen dukkan al'ummai"
Wannan alama ne na shiga cikin aikata fasikancinta. AT: "sun zama masu fasikanci kamar ita" ko " sun bugu kamar ita a cikin zunubin fasikancinta"
An yi maganar Babila kamar karuwace wanda ta sa waɗansu mutane yin zunubi tare da ita. Wannan na iya zama da ma'ana biyu: fasikanci a zahiri da kuma bautar allolin karya.
Attajiri mutum ne mai sayar da abubuwa.
"domin ta na kashe kuɗi dayawa akan fasikanci"
Kalmar "murya" ta na nufin mai magana, wadda mai yiwuwa Yesu ne ko Uban. AT: "wani dabam"
Muryar ta yi maganar zunuban Babila kamar abubuwa ne da na iya zama taro. AT: "zunuban ta sun yi yawa, su na nan kamar taro da sun kai sama"
"ya yi tunanin" ko "ya fara maida hankali a kan." Wannan ba ya nufin cewa Allah ya tuna wani abu da ya manta. Dubi yadda kun juya "tunawa" a 16: 19.
Muryar ta yi maganar hukunci kamar biya ce. AT: "hukunta ta kamar yanda ta hukunta waɗansu"
Muryar ta yi maganar hukunci kamar biya ce. AT: "hukunta ta so biyu fiye da"
Muryan ya yi maganar sa waɗansu su sha wuya kamar shirya ruwan inabi mai ƙarfi don su sha. AT: "shirya mata ruwan inabi na wuya da ke da ƙarfi ninki biyu kamar yanda ta yi wa waɗansu" ko "sa ta sha wuya so biyu fiye da yanda ta sa waɗansu su sha wuya"
AT: "shirya so biyu" ko 2) "sa shi ya yi ƙarfi so biyu"
"mutanen Babila sun ɗaukaka kansu"
A nan "zuciya" na nufin hankali da tunanin mutum. AT: "Domin ta ce wa kanta"
Ta na nuna cewa ita mai mulki ce, da ikonta.
Ta na nufin cewa ba za ta taɓa dogara da waɗansu mutane ba.
An yi maganar yin makoki kamar ganin makoki. AT: "Ba zan taɓa yin makoki ba"
An yi maganar kasancewa a gaba kamar zuwa.
An yi maganar konewa da wuta kamar wutar ya cinye ta. AT: "Wuta zai kone ta gaba ɗaya"
"yi zunubin lalata sun kuma yi abin da sun so kamar yanda mutanen Babila su ka yi"
Ana iya juya "azaba" a matsayin aikatau AT: "jin tsoro cewa za a azabtar da su kamar yanda Babila ta ke" ko "jin tsoro cewa Allah zai azabtar da su kamar yanda ya azabtar da Babila"
An nanata wannan don jaddadawa.
An yi maganar kasancewa yanzu kamar ya riga ya zo.
"yi makoki don mutanen Babila"
"duwatsu masu tsada dayawa." Dubi yadda kun juya wannan a cikin 17:4.
kaya mai tsada da an yi daga wani irin tsiro. Dubi yadda kun juya "linin" a cikin 15:6.
hajja mai ruwan jar galura ƙyalle ne mai jan kala da ke da tsada. Siliki ƙyalle ne mai laushi, da karfi da a ka yi shi daga kirtani.
"kowane kayayyaki da an yi shi daga haure"
farin kyakkyawan abu mai karfi da mutane ke samu daga haure ko hakorin katon dabba kamar giwa. AT: "haure" ko "hakorin dabba mai amfani"
dutse mai kyau da ake amfani da shi a gini
abin da ke da kamshi mai daɗi kuma ana samun sa daga bayan wani irin itace
wani abu ne da ana amfani da shi don ya ƙara daɗi ko kamshi mai daɗi a mai
Sun yi magana game da abubuwa masu kyau kamar 'ya'yan itace ko amfanin gona ne. AT: "Abubuwa masu kyau"
"so dayawa sosai"
Rashin samuwa na wakilcin rashin kasancewa. AT: "ɓace; ba za ku taɓa samun su kuma ba"
Ana iya sake bayyana "tsoro" da "azaba." AT: "domin za su ji tsoron azabar da Allah zai yi masu kamar yanda ya yi mata" ko kuma "domin za su ji tsoron jin wahala kamar yanda ta na shan wahala"
Wannan ne abin da attajiran za su yi. AT: "kuma su yi kuka da kururuwar baƙin ciki"
Gaba ɗaya a cikin wannan aya, an yi maganar Babila kamar mace ce. Attajirai sun yi maganar Babila kamar tana sanye da lilin mai laushi domin mutanen ta suna sanye da lilin mai laushi. AT: "babbar birni, wanda yake kamar mace da take sanye da lilin mai laushi" ko kuma "babbar birni, wanda matayensu suna sanye da lilin mai laushi"
AT: "da tana sanye da lili mai laushi"
AT: "yi adon kanta da zinariya" ko kuma "yi adon kansu da zinariya" ko "sa zinariya"
"dutse mai tsada"
farin dutsen wuya mai tsada. Ana samun su daga ciki kwasfar wani karamin dabba da na zama a cikin teku. Dubi yanda an juya wannan a cikin 17:4.
Jumlar "daga teku" ya na nufin abin da su ke yi akan tekun. AT: "wadda na tafiya a kan teku don bukatun rayuwarsu" ko kuma "wadda na tafiya a kan teku zuwa wurare dabam dabam domin sayar da abubuwa"
Wannan tambaya ya na nuna wa mutane muhimmincin birnin Babila. AT: "Babu wani birni da na nan kamar babban birnin, Babila!"
Ana iya bayyana kalmar "hukunci" cikin aikatau. AT: "Allah ya riga ya hukunta ta domin ku" ko kuma "Allah ya hukunta ta domin mugayen abubuwa da ta yi maku"
babban mulmulallen dutse da ake nika hatsi
Allah zai halakar da birnin gaba ɗaya. AT: "Allah zai jefar da birnin Babila da ƙarfi, babban birni, kuma ba zai sake kasancewa ba"
"babu wani da zai sake ganinta kuma." Rashin ƙara ganinta a nan na nufin cewa ba za ta sake kasancewa kuma ba"
AT: "Babu wani a birninki da zai ƙara kuma jin ƙarar da masu kiɗar molaye, mawaƙa, masu busa sarewa, da na masu busa algaita ke yi"
Mala'ikan ya na magana kamar Babila ta na jinshi a wurin. AT: "a cikin Babila"
"babu wani da zai sake jin su a cikinki." Rashin samuwa a wurin na nufin cewa ba za a same su a wurin ba. AT: "ba za su kasance a birnin ki kuma ba"
Rashin samuwa a wurin na nufin cewa ba za a same su a wurin ba. AT: "Babu wani mai sana'a na kowanne iri da za a samu a cikinki"
Rashin jin ƙaran wani abu na nufin cewa babu wani da zai yi wannan ƙaran. AT: "Babu wani da zai yi niƙa a cikinki"
AT: "Babu wani da zai sake ji a Babila muryoyin murna na amarya da na ango "
Rashin ji a nan na nufin cewa ba za su kasance a wurin ba. AT: "ba za su kasance a birninki ba"
Mala'ikan ya yi maganar mutane masu muhimmanci da iko kamar sun zama 'ya'yan sarki. AT: "attajiranki suna kamar 'ya'yan sarki a duniya" ko "attajiranki sune mutane masu muhimminci a cikin duniya"
AT: "kika ruɗi mutanen duniya da sihirinki"
Samun jini a wurin ya na nufn cewa mutanen sun yi laifin kashen mutane. AT: "Babila ta na da laifin kashen annabawa da masubi da kuma dukkan sauran mutanen duniya da an kashe su"
Mala'ika ya yi sanarwa cewa babilan nan mai girma ta faɗi.
Muryan ya gaya wa mutanen Allah su fito daga Babila kada zunubin ta ya shafe su.
Allah ya biya Babila ninki biyu na abin da ta yi.
Mutuwa, bakinciki da yunwa ta dauƙi babila a kwana ɗaya kuma ta kone da wuta.
Sun tsaya da nesa saboda suna tsoron azabar ta.
sa'anda sarakuna da masu ciniki suka gan shari'an Babila, sun yi kuka da ihu bisan ta.
Babila ta jima da zama abu mai daɗi da daraja, wanda ta ɓace a cikin sa'a ɗaya.
Sun tsaya da nesa saboda suna tsoron azabar ta.
hafsosin jiragen sun yi tambaya, "wace birni ne kamar birne mai girm?"
An gaya wa tsakakun, annabawa, da manzanai su yi murna sa'anda Allah ya yi wa babila shari'a.
Bayan shari'an ta, ba za a sake ganin Babila kuma ba.
Jinin manzanai da annabawa, tsakaku, da dukkan wanda aka kashe a duniya an same ta.
1 Bayan wadannan abubuwa na ji wata karar da ta yi kamar muryar mutane masu yawa a sama suna cewa, "Halleluya. Ceto, daukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu. 2 Hukunce - hukuncensa gaskiya ne da adalci, domin ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta kazamtar da duniya da fasikancinta. Ya dauki fansar jinin bayinsa, wadda ita da kanta ta zubar." 3 Suka yi magana a karo na biyu: "Halleluya! Hayaki na tasowa daga wurinta har abada abadin." 4 Dattawan nan ashirin da hudu da rayayyun halittun nan hudu, suka fadi suka yi wa Allah sujada shi da yake zaune a kan kursiyin. Suna cewa, "Amin. Halleluya!" 5 Sai wata murya ta fito daga kursiyin tana cewa, "Ku yabi Allahnmu, dukanku bayinsa, ku da kuke tsoronsa, da duk marasa iko da masu iko." 6 Sai na ji murya kamar na kasaitaccen taron mutane, kamar rurin kogi na ruwaye masu yawa, kuma kamar tsawar aradu, cewa, "Halleluya! Gama Ubangiji yana mulki, Allah mai iko duka. 7 Bari mu yi murna, mu yi farinciki matuka mu kuma ba shi daukaka domin bikin auren Dan Ragon ya zo, amaryarsa kuma ta shirya kanta. 8 An yardar mata ta sa kaya masu haske da tsabta na lilin mai laushi" (domin lilin mai laushi shine ayyukan adalci na tsarkaka). 9 Mala'ika ya ce mani, "Rubuta wannan: Masu albarka ne wadanda aka gayyace su zuwa bikin auren Dan Ragon." Ya kuma ce mani, "Wadannan kalmomin Allah na gaskiya ne." 10 Na fadi a gaban kafafunsa domin in yi masa sujada, amma ya ce mani, "Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne tare da kai da 'yan'uwanka wadanda ke rike da shaida game da Yesu. Yi wa Allah sujada, domin shaida game da Yesu shine ruhun annabci." 11 Sai na ga sama a bude, na kuma duba sai ga wani farin doki. Mahayinsa ana kiransa amintacce da gaskiya. Yana shari'a da adalci yana yaki. 12 Idanunsa kamar harshen wuta suke, a kansa akwai kambuna da yawa. Yana da suna a rubuce a jikinsa wanda ba wani da ya sani sai dai shi da kansa. 13 Yana sanye da riga da aka tsoma a cikin jini, kuma ana kiran sunansa Kalmar Allah. 14 Rundunonin sama suna biye da shi a kan fararen dawakai, suna sanye da lilin mai laushi, fari mai tsabta. 15 Daga cikin bakinsa takobi mai kaifi na fitowa, da ita yake sarar al'ummai, zai kuma mulke su da sandar karfe. Yana tattake wurin matsar ruwan inabi da matsananciyar fushin Allah Mai iko duka. 16 Yana da suna a rubuce a rigarsa da cinyarsa: "Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji." 17 Na ga mala'ika tsaye a rana. Yayi kira da murya mai karfi ga dukan tsuntsaye da ke firiya a sama. 18 "Ku zo, ku tattaru saboda babban bukin Allah. Ku zo ku ci naman sarakuna, da naman sarakunan yaki, da naman manyan mutane, da naman dawakai, da na mahayansu, da naman dukan mutane, yantattu da bayi, marasa iko da masu iko." 19 Na ga dabban da sarakunan duniya da rundunoninsu. Suna tattaruwa domin su yi yaki da wanda ke bisa doki da rundunarsa. 20 Aka kama dabban tare da makaryatan annabawa da suka yi ayyukan al'ajibai a gabansa. Da wadannan alamu ya yaudari wadanda suka karbi alamar dabbar da wadanda suka yi wa siffarta sujada. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin farar wuta mai ci. 21 Sauran aka karkashe su da takobin da ke fitowa daga bakin mahayin dokin. Dukan tsuntsaye suka ci gawarwakinsu.
Wannan sashin na gaba ne a wahayin Yahaya. A nan ya kwatanta farin ciki a sama akan faɗiwar babbar karuwan, wadda ita ce birnin Babila.
A nan "na" na nufin Yahaya.
Wannan kalma na nufin "Yabi Allah" ko "Bari mu yabi Allah."
A nan, Yahaya ya na nufin birnin Babila wanda mugayen mutanenta suke mulki a kan dukkan mutanen duniya kuma suna sa su su bauta wa allolin ƙarya. Ya na maganar mugayen mutanen Babila kamar su babbar karuwace.
A nan "duniya" na nufin mazauna. AT: "wadda ta kazamtar da mutanen duniya"
A nan "jini" na wakilcin kisa. AT: "yin kisar bayinsa"
Wannan na nufin Babila. An yi amfani da "kanta" domin ƙarin bayani.
A nan "su" na nufin taron mutane a sama.
Kalmar "ita" ya na nufin birnin Babila, wadda a na maganarsa kamar karuwace. Hayakin daga wutar da ke halaka birnin. AT: "Hayaki na tasowa daga birnin"
"Dattawa ashirin da huɗu." Dubi yanda kun juya wannan a 4: 4.
"rayayyun halittu huɗu" ko "rayayyun abubuwan nan huɗu" Dubi yanda kun juya wannan a 4:6
AT: "wadda ya zauna a kan kursiyin"
A nan Yahaya na maganar "murya" kamar mutum ne. AT: "wani ya yi magana daga kursiyin"
A nan "mu" na nufin mai magana da dukka bayin Allah.
A nan "tsoro" ba ya nufin jin tsoron Allah, amma a girmama shi. AT: "dukkan ku da ku na girmama shi"
Mai magana ya yi amfani da waɗannan kalmomi don ya na nufin dukka mutanen Allah.
Yahaya na maganar abin da ya na ji kamar ƙara ne da aka yi daga babban taron mutane, babbar ruwa mai gudu, da kuma babbar aradu.
"Domin Ubangiji"
Muryan taron da aka yi magana a baya.
A nan "mu" na nufin dukka bayin Allah.
"ba Allah ɗaukaka" ko "girmama Allah"
A nan Yahaya na maganar haduwan Yesu tare da mutanensa har abada kamar bikin aure.
Wannan ɗan rago ne. A nan na nufin Almasihu. Dubi yanda kun juya wannan a cikin 5:6.
An yi maganar kasancewa yanzu kamar ya riga ya zo.
Yahaya ya yi maganar mutanen Allah kamar sun zama amarya da ta yi shirin aurenta.
A nan "ta" na nufin mutanen Allah. Yahaya ya na maganar ayyukan adalcin mutanen Allah kamar sun zama kaya mai haske da tsabta da amarya na sa wa a ranar aurenta. AT: "Allah ya bar ta ta sa kayan haske da tsabta na lilin mai laushi"
AT: "mutanen da Allah ya gayyata"
A nan mala'ikan ya yi maganar haɗuwar Yesu tare da mutanensa har abada kamar bikin aure ne.
Wannan ya na nufin cewa Yahaya ya kwanta a ƙasa ya kuma miƙa kansa don girmama ko biyaya. Waɗannan muhimman ayyuka ne a sashin sujada, don nuna biyaya ko bauta. Dubi rubutu a cikin 19:3.
Kalmar "'yan'uwa" anan na nufin dukkan masubi, maza da mata.
A nan "riƙe" na matsayin gaskatawa ko sanarwa. AT: "waɗanda ke faɗan gaskiya game da Yesu"
A nan "ruhun annabci" ya na nufin Ruhu mai Tsarki na Allah. AT: "don Ruhun Allah ne na ba mutane ikon faɗan gaskiya game da Yesu"
An yi amfani da wannan magana don a nuna farkon sabon wani wahayi. Dubi yadda kun juya wannan magana a cikin 11:19 da 15:5.
Yesu ne mahayin.
A nan "adalci" ya na nufin abin da ke daidai. AT: "Ya na shar'anta dukkan mutane, ya na kuma yin yaƙi bisa abin da ke daidai"
Yahaya ya yi maganar idanun mahayin kamar sun haskaka kamar harshen wuta.
AT: "Wani ya rubuta suna a kanshi"
"a kanshi, kuma shi kaɗai ne ya san ma'anar sunan nan"
AT: "jini ya rufe rigarsa"
Ku na iya bayyana wannan a cikin siffar aiki. "Kalmar Allah" a nan na nufin Yesu Almasihu. AT: "ana kiran sunansa Sakon Allah" ko kuma "sunansa kuma Kalmar Allah ne"
Ruwan takobin ya na tsabga daga bakinsa. Takobin da kansa ba ya motsi. Dubi yanda kun juya irin wannan jumla a cikin 1:16.
"halaka al'ummai" ko "kawo al'ummai a ƙarkashin ikonsa"
Yahaya ya yi maganar ikon mahayin kamar ya na mulki da sandar karfe. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 12:5.
Yahaya ya yi maganar hallaka maƙiyan mahayin kamar su inabi ne da mutum ya ke takawa a cikin inda ake matse ruwan inabi. A nan "fushi" ya na nufin hukuncin Allah a kan mugayen mutane. AT: "Ya take makiyansa bisa hukuncin Allah, kamar yadda mutum ke taka inabi a wurin matse shi."
AT: "Wani ya rubuto suna a rigarsa da cinyarsa:"
A nan "rana" na nufin hasken rana. AT: "Sai na ga mala'ika a tsaye a cikin hasken rana"
Mala'ikan ya na nufin dukka mutane ne da ya yi amfani da waɗannan akasin kalmomi tare.
AT: "mahayin farin dokin ya kama dabban da kuma annabin ƙarya"
Wannan alama ne da ke nuna cewa mutumin da ya karɓi alamar ya bauta wa dabban. Dubi yanda kun juya wannan a cikin 13:17.
AT: "Allah ya jefa dabban da annabin ƙarya da rai"
"tafkin wuta da ke konewa da farar wuta" ko "wuri cike da wuta da ke konewa da farar wuta"
AT: "Mahayin dokin ne ya ƙashe sauran sojojin dabban da takobi da ya fito daga bakinsa"
Ruwan takobin ya na tsabga daga bakinsa. Takobin da kansa ba ya motsi. Dubi yanda kun juya irin wannan jumla a cikin 1:16.
Murya mai karfin daga sama ya ce shari'an Allah gaskiya ne kuma daidai ne.
Allah ya yi wa babban karuwan nan shari'a domin ta ƙazantar da duniya da fasikanci ta kuma zub da jinin bayin Allah.
Hayaki zata tashi daga babban karuwan har abada abadin.
An gaya wa bayin Allah su yi masa yaba.
An gaya wa bayin Allah su yi murna domin bikin auren Ɗan Ragon ya zo.
An yi wa amaryan shiri da lilin mai kyau, wanda shine aikin adalcin tsarkaka na mutanen Allah
Mala'ikan ya ce shaida game da Yesu shine ruhun anabci.
Yahaya ya ga kalmar Allah ta na tuƙa farar dokin.
Daga bakin kalmar Allah wani kakkaifan tokobi ke fitowa wanda zai sare al'ummai.
Akan regan sa da cinyar sa an rubuta, "sarkin sarakuna da Allahn alloli".
An kira tsuntsaye su zo su ci naman sarakuna, shugabanai, manyan mutane, dokuna damatukin su da dukkan mutane.
Suna shiri su yi yaƙi da kalmar Allah da sojojin sa.
Dukka dabban da annabawan aƙarya an jefa su a cikin tafkin farar wuta mai ci.
Sauran a kashe su da tokabi da yake fitowa da ga bakin Allah
1 Sai na ga mala'ika na saukowa daga sama. Yana da makullin rami marar iyaka, yana kuma da babar sarka a hannunsa. 2 Sai ya dauki tsohon macijin, wanda shine iblis, ko shaidan, ya daure shi shekaru dubu. 3 Ya jefa shi cikin rami marar iyaka, ya rufe shi ya kuma sa hatimi a bisansa. Hakan ya faru ne domin kada ya kara yaudarar al'ummai har sai bayan shekaru dubu. Bayan wannan, dole a sake shi na dan lokaci. 4 Sa'annan na ga kursiyoyi. Wadanda ke zaune a bisansu sune wadanda aka ba ikon hukunci. Na kuma ga rayukan wadanda aka fille wa kai saboda shaidar Yesu da maganar Allah. Ba su yi wa dabban sujada ba ko siffarsa, suka ki su karbi alamar a goshinsu ko a hannu. Sun sake rayuwa, suka yi mulki tare da Kristi shekaru dubu. 5 Sauran matattun basu sake dawowa da rai ba har sai da shekaru dubu din suka cika. Wannan shine tashin matattu na fari. 6 Mai albarka ne mai tsarki ne kuma wanda yake da rabo cikin tashin matattu na fari! Mutuwa ta biyu ba ta da iko akan wadannan. Za su zama firistocin Allah da na Almasihu za su kuma yi mulki tare da shi shekaru dubu. 7 Sa'adda shekaru dubu suka zo ga karshe, za a saki shaidan daga kurkukunsa. 8 Za ya fito domin ya yaudari al'ummai da ke kursuyoyi hudu na duniya, Gog da Magog ya tattara su domin yaki. Yawan su zai zama kamar yashin teku. 9 Suka bazu a fuskar duniya suka kuma kewaye sansanin masu ba da gaskiya, kaunataccen birni. Amma wuta ta sauko daga sama ta lankwame su. 10 Shaidan, wanda ya yaudare su, aka jefa shi cikin korama ta farin wuta mai ci, inda aka jefa dabban da makaryacin annabin. Za su sha azaba dare da rana har abada abadin. 11 Sai na ga babban kursiyi da wanda ke zaune a kansa. Duniya da sama suka guje wa fuskarsa, amma babu wurin da za su tafi. 12 Na ga matattu manya da kanana- suna tsaye gaban kursiyin, aka bude litattafai. Sai aka bude wani littafi - Littafin rai. Aka yi wa matattu shari'a bisa ga abinda aka rubuta cikin litattafan, gwargwadon ayyukansu. 13 Teku ta ba da matattun dake cikinta. Mutuwa da hades suka ba da matattun da ke cikinsu, aka yi masu shari'a gwargwadon abin da suka yi. 14 Aka jefa mutuwa da hades cikin tafkin wuta. Wannan shine mutuwa ta biyu - tafkin wuta. 15 Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce cikin littafin rai ba, aka jefar da shi cikin tafkin wuta.
Yahaya ya fara kwatanta wahayin mala'ika da ke jefa Ibilis a cikin rami mara iyaka.
A nan "na" na nufin Yahaya.
Wannan rami ne mai tsananin zurfi. AT: 1) ramin bashi da ƙarshe; ya cigaba da tafiya ƙasa har abada ko 2) ramin na da zurfin da na nan kamar bashi da ƙarshe. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 9: 1.
Wannan babban, halitta ne mai rarrafe mai kuma ban tsoro kamar kadangare. Alamar masifa da bala'i ne ga mutanen Yahudawa.
Mala'ikar ya hatimci ramin don ya hana kowa buɗewa. AT: "hatimce shi don ya hana kowa buɗewa"
A nan "alummai" na nufin mutanen duniya. AT: "yaudarar taron mutane"
" shekaru dubu ɗaya"
AT: "Allah zai umurci mala'ikar ya sake shi"
AT: "waɗanda Allah ya ba su ikon hukunci"
AT: "waɗanda waɗansu ne sun yanke kawunansu"
"domin sun faɗi gaskiya game da Yesu da kuma game da maganar Allah"
Waɗannan na nufin saƙo daga Allah. AT: "don abin da sun koyar game da nassi"
" Sun sake rayuwa"
"Dukka sauran matattun mutane"
"karshen shekaru dubu ɗaya"
A nan Yahaya ya kwatanta "mutuwa" kamar mutum ne mai iko. AT: "Waɗannan mutanen ba za su ga mutuwa ta biyu ba"
"Mutuwa ta biyu." An kwatanta wannan kamar hukunci na har abada a cikin tafkin wuta a 20:14 da kuma 21:8. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 2: 11. AT: "mutuwa na ƙarshe a cikin tafkin wuta"
AT: "Allah zai saki shaiɗan daga kurkukunsa"
Wannan karin magana ne da na nufin "dukka yankin duniya." Dubi yadda kun juya wannan a cikin 7: 1.
Waɗannan sunaye ne da annabi Ezekiel ya yi amfani don ya wakilci kasashe masu nisa.
Wannan ya na nanata tsananin yawan lambar rundunar sojojin Shaiɗan.
"Sojojin Shaiɗan suka tafi"
Wannan na nufin Urushalima.
Yahaya ya yi maganar wuta a nan kamar na da rai. AT: "Allah ya aiko wuta daga sama don ta kone su dukka"
AT: "Allah ya jefa Ibilis, wanda ya yaudare su, cikin" ko "Mala'ikar Allah ya jefa Ibilis, wanda ya yaudare su, cikin"
"tafkin wuta da ke konewa da farin wuta" ko kuma "wuri cike da wuta da na konewa da farin wuta." Dubi yadda kun juya wannan a cikin 19: 20.
AT: "inda ya kuma jefa dabban da kuma maƙaryacin annabin"
AT: "Allah zai azabtar da su"
Yahaya ya yi kwatancin sama da duniya kamar mutane ne da suke ƙoƙarin gudu daga hukuncin Allah. Wannan ya na nufin cewa Allah ya hallakar da tsohon sama da kuma duniya gaba ɗaya.
Yahaya ya haɗi waɗannan kalmomi masu akasin ma'ana don ya nuna cewa ya na nufin dukkan matattun mutane.
AT: "wani ya bude litattafai"
AT: "Allah ya hukunta mutanen da sun mutu, waɗanda suke kuma raye yanzu"
AT: "bisa abin da ya rubuto"
A nan Yahaya ya yi maganar teku, matattu, da kuma Hades kamar rayyayun mutane ne.
AT: "Allah ya jefa Mutuwa da Hades" ko "Mala'ikar Allah ya jefa Mutuwa da Hades"
A nan "Hades" magana ne da na wakilcin wurin da marasa bi su ke zuwa a lokacin da sun mutu, don su jira hukuncin Allah.
AT: "Idan mala'ikan Allah bai sami sunan mutum ba"
AT: "mala'ikan ya jefa shi cikin tafkin wuta" ko "mala'ikan ya jefa shi cikin wuta da ke ƙonewa har abada"
Mala'ikan yana da makullin rami mara matuka da baban tsarka a hanunsa.
Za'a daure shaiɗan har zuwa shekaru dubai.
Mala'ikan ya jefa shaiɗan a cikin rami mara matuka .
Shaiɗan ba zai iya yaudaran al'ummai ba bayan an daure shi.
Wadan da su ka ƙi su karba alamar dabban sun kuma rayu suna mulki da Yesu Almasihu shekaru dubai.
Sauran matattu zasu dawo a raye bayan da aka gama shekaru duban nan.
Wadan da aka fyauce su da farko zasu zama firistoci na Allah da Almasihu kuma zasu yi mulki da shi har shekaru dubai.
bayan shekaru dubai za a sake shaiɗan ya je ya yaudare al'ummai.
Sa'anda aka kewaye taron tsarkaku, wuta ya sauko daga sama ya cinye God da Magog.
An jefa shaiɗan a cikin wata mai zafi ya sha azaba har abada.
An yi wa mattatu shari'a da abin da aka rehotu da ke rubu ce a cikin littatafai, sakamakon abin da sun yi.
mutuwa na biyu tafkin wuta.
Duk wadan da babu sunayen su a cikin littafi rai an jefa su a cikin tafkin wata.
1 Sai na ga sabuwar sama da sabuwar duniya, domin sama ta fari da duniya ta fari sun shude, ba kuma teku. 2 Na ga birni mai tsarki, sabuwar Urushalima, wadda ta sauko kasa daga sama wurin Allah, shiryayya kamar amaryar da aka yi wa ado domin mijinta. 3 Na ji babbar murya daga kursiyinta na cewa, "Duba! Mazaunin Allah yana tare da 'yan adam, zai zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kuma da kansa zai kasance tare da su ya kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu, kuma babu sauran mutuwa, ko bakinciki, ko kuka, ko azaba. Abubuwan da sun shude. 5 Shi wanda yake zaune a kan kursiyin ya ce, "Duba! Na maida kome ya zama sabo." Ya ce, "Ka rubuta wannan domin wadannan kalmomi amintattu ne da gaskiya". 6 Ya ce mani, "Wadannan abubuwan an gama! Ni ne Alpha da Omega, farko da karshe. Ga mai jin kishi, zan bashi kyauta daga mabulbular ruwan rai. 7 Wanda ya ci nasara, zai gaji wadannan abubuwa, ni kuma zan zama Allahnsa, shi kuma ya zama da na. 8 Amma ga matsorata, da marasa bangaskiya, da masu kazanta, da masu kisan kai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da dukan makaryata, mazaunin su zai kasance cikin tafki mai ci da farar wuta. Mutuwa ta biyu kenan." 9 Daya daga cikin mala'ikun bakwai ya zo wurina, wanda yake dauke da tasoshi bakwai cike da annobai bakwai na karshe, yace, "Zo nan. Zan nuna maka amarya, matar Dan Rago". 10 Sai ya dauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsawo ya nuna mani birni mai-tsarki, Urushalima, tana saukowa daga cikin sama daga wurin Allah. 11 Urushalima tana da daukakar Allah, shekinta yana kama da dutse mai tamani, sai kace dutsen yasfa, garau kamar karau. 12 Tana da babban garu mai tsawo, da kofofi goma sha biyu, da mala'iku goma sha biyu a kofofin. Akan kofofin an rubuta sunayen kabilu sha biyu na 'ya'yan Isra'ila. 13 A gabas akwai kofofi uku, a arewa kofofi uku, a kudu kofofi uku, da kuma yamma kofofi uku. 14 Garun birnin yana da harsashin gini goma sha biyu, a bisansu akwai sunaye goma sha biyu na manzanni goma sha biyu na Dan Rago. 15 Shi wanda yayi magana dani yana da sandan awo na zinariya domin ya auna birnin, da kofofinsa, da garunsa. 16 Birnin; da tsawonsa da fadinsa iri daya ne. Ya gwada birnin da sandar awo, mil dubu sha biyu a tsaye (fadinsa, da tsawonsa, da tsayinsa duka daya ne) 17 Ya kuma gwada garunsa, kamu 144, bisa ga gwajin 'yan adam (wanda shine ma'aunin mala'ika). 18 An gina garun da Yasfa birnin kuma da sahihiyar zinariya, mai kama da madubi mai kyalli. 19 An kawata harsashin garun da kowanne irin dutse mai tamani. Na fari yasfa, na biyu saffir, na uku agat, na hudu emerald, 20 na biyar Onis, na shida sardiyus, na bakwai kirisolat, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofaras, na sha daya yakinta, na sha biyu kuma ametis. 21 Kofofi goma sha biyu lu'u-lu'ai ne goma sha biyu; kowacce daya a cikin kofofin daga lu'u-lu'u daya aka yi shi. Titunan birnin kuwa zinariya ce sahihiya, sai kace madubi garau. 22 Ban ga haikali a cikin birnin ba, gama Ubangiji Allah Mai iko duka da Dan Ragon su ne haikalinsa. 23 Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi gama daukakar Allah ta haskaka shi, kuma fitilarsa Dan Rago ne. 24 Al'ummai za su yi tafiya cikin hasken birnin. Sarakunan duniya kuma za su kawo daukakarsu cikinsa. 25 Kofofinsu kuma ba za a rufe su da rana ba, babu dare kuma a can. 26 Za su kawo daukaka da darajar al'ummai a cikinsa, 27 babu wani abu mai kazanta da zai taba shiga cikinsa. Ko wanda yake aikata abin kunya da karya, sai wadanda an rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Dan Rago kadai.
Yahaya ya fara kwatanta wahayinsa na sabon Urushalima.
A nan "na" na nufin Yahaya.
Wannan na kwatanta sabon Urushalima da amaryar da ta shirya kanta da kyau domin angon ta.
Kalmar "murya" na nufin wanda ke magana. AT: "wani ya yi magana da ƙarfi daga kursiyin da cewa"
Kalmar "duba" a nan yana sa mu mu saurare bayani mai ban mamaki da ke biye.
Waɗannan jumloli biyu na nufin abu ɗaya ne kuma ya na nanata cewa haƙiƙa, Allah zai, yi rayuwa tare da mutane.
Hawaye a nan na wakilcin baƙin ciki. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 7:17. AT: "Allah zai share baƙin cikinsu, kamar share hawaye" ko "Allah zai sa su kada su yi baƙin ciki kuma"
A nan "kalmomi" ya na nufin sakon da sun yi. AT: "wannan sakon amintattu ne da gaskiya"
Waɗannan jumloli biyu atakaice na nufin abu ɗaya ne kuma ya na nanata kasancewar Allah na matuƙa.
Waɗannan baƙaƙe ne na farko da ƙarshe na haruffar Greek. Ga ma'anoni masu yiwuwa 1) "wanda ya fara dukkan komai da wanda ya gama komai" ko kuma 2) "wanda ya ke rayuwa koda yaushe da kuma wanda zai yi rayuwa kullum." Idan masu karatun ba za su gane waɗannan ba, za ku iya amfani da baƙaƙe na farko da ƙarshe na harshenku. Dubi yanda kun juya wannan a cikin 1:18. AT: "A da Z" ko "na farko da ƙarshe"
AT: 1) "wanda ya fara dukkan komai ne zai sa dukka komai ya ƙare" ko 2) "wanda ya kasance kafin dukkan komai da kuma wanda zai kasance bayan dukkan komai."
Allah ya yi maganar begen mutum na rai na madawami kamar kishi kuma na mutumin da ke karɓan rai madawami kamar ya na shan ruwa mai ba da rai.
Wanda ya ke zaune a kan kursiyin ya cigaba da yi wa Yahaya magana.
"waɗanda suke tsoron yin abin da ke daidai"
"waɗanda su ke yin mugun abubu"
tafkin wuta da ke konewa da farin wuta" ko kuma "wuri cike da wuta da ke konewa da farin wuta." Dubi yadda kun juya wannan a cikin 19: 20.
"mutuwa ta biyu." An kwatanta wannan kamar hukunci na har abada a cikin tafkin wuta a 21:8. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 2:11. AT: "mutuwa na ƙarshe a cikin tafkin wuta"
Mala'ikan ya yi maganar Urushalima kamar mace ne da ta yi kusa ta auri mijinta, Ragon. Urushalima na nufin waɗanda sun gaskata, waɗanda za su zauna a ciki.
Wannan karamin tunkiya ne. Alama ne anan da ke nufin Almasihu. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 5: 6.
Wrin nuna wahayin ya canja sa'ad da aka ɗauki Yahaya zuwa babbar dutse inda zai iya ganin birnin Urushalima. Dubi yadda kun juya wannan jumla a cikin 17: 3.
Wannan ya na nufin "Urushalima mai zuwa daga sama" da ya kwatanta a aya da ya wuce kuma ba Urushalima da aka sani ba.
Waɗannan jumloli biyun na nufin abu ɗaya. Na biyun na nanata hasken Urushalima ta wurin ambatar abu mai tamani.
"garau sosai"
Wannan dutse ne mai daraja. Mai yiwuwa yasfa ya yi haske kamar gilas ko ƙarau. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 4:3.
" kofofi goma sha biyu"
AT: "wani ya rubuto"
Wannan na nufin Yesu. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 5:6.
"mil dubu ɗaya da ɗari huɗu." Za ku iya juya wannan zuwa awu na zamani. AT: "mita dubu biyu da ɗari biyu"
"kamu dari ɗaya da arba'in da huɗu." Za ku iya juya wannan zuwa awu na zamani. AT: "mita sittin da shida"
AT: "Wani ya gina garun da yasfa da kuma birnin da sahihiyar zinariya"
Zinariyan ya yi haske da har an yi maganar sa kamar gilas.
AT: "Wani ya kawata harsashin garun"
Waɗannan duwatsu ne masu daraja. Mai yiwuwa yasfa ya yi haske kamar gilas ko ƙarau, kuma mai yiwuwa sardiyus ja ne. Emerald kore ne. Dubi yadda kun juya waɗannan a cikin 4:3.
Waɗannan dukka duwatsu masu daraja ne.
kyakkyawan farin dutsen wuya mai kuma daraja. Ana samun su daga cikin kwasfan wani irin ƙaramin dabba da ke zama a cikin teku. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 17:4.
AT: "wani ya yi kowacce ƙofa daga lu'u-lu'u ɗaya"
Zinariyan ta yi sarai sosai har an yi maganarsa kamar ya zama gilas. Dubi yadda kun juya jumla irin wannan a cikin 21:18.
Haikalin ya wakilci gaban Allah. Wannan ya na nufin cewa sabon Urushalima ba ya neman haikali domin Allah da Ragon za su zauna a wurin.
An yi maganar ɗaukakar Yesu, Ragon, a nan kamar fitilace da na ba da haske a birnin.
"Al'ummai" na nufin mutane. "Tafiya" a nan na nufin rayuwa. AT: "Mutane daga dukka Al'umma dabam-dabam za su rayu"
AT: "Babu wanda zai rufe ƙofofin"
"Sarakunan duniya za su kawo"
AT: "abu mai tsabta ne kadai zai shiga, kuma babu wani"
AT: "amma sai waɗanda Ragon ya rubuta sunayensu kaɗai a cikin littafinsa na rai"
Sabuwar sama da ƙasa ya cika gurbin sama na farko da ƙasa.
Yahaya ya ga sabuwar sama da ƙasa ya shuɗe.
ƙasa mai tsarki, sabuwar Urushalima, ya sauko daga sama.
Muryan ya ce yanzu Allah zai zauna da yan adam.
Mutuwa, makoki, kuƙa, da zafi yanzu ya wuce.
wanda ya zauna a kan kursiyin ya kira kansa Alpha da Omega, farko da karshe.
Marasa bangaskiya, masu fasikanci da masu bautar gumaka suna da wurin su a cikin tafkin wuta.
Amaryan, matan Ɗan Ragon,ita ce tsarkaƙiyan brinin nan Urushalima, yana fitowa daga sama gun Allah.
Sunayen harshen 'yayan Isa'ilawa gama sha biyu aka rubuta a kofar sabuwar Urushalima.
Sunayen manzanni gama sha biyu na Ɗan Ragon aka rubuta akan harsashin sabuwar Urushalima.
Tsawon sa da fadin sa dukka ɗayane.
an gina birnin da zinariya tsansa, kamar gilas.
haikali a sabuwar Urushalima she ne Ubangiji Allah da Ɗan Ragon.
Tushin haske a sabuwar Urushalima shi ne ɗaukakar Allah da na Ɗan Ragon.
Babu wani abu mara tsarki da zai shiga sabuwar Urushalima.
1 Sai mala'ika ya nuna mani kogin ruwan rai, ruwa mai tsabta. Yana fitowa daga cikin kursiyin Allah da na Dan-Rago 2 ta tsakiyar titin birnin. A kowanne gefen kogin akwai itacen rai, mai ba da 'ya'ya iri goma sha biyu, kowanne wata. Ganyayen itacen kuma domin warkar da al'ummai ne. 3 Babu sauran la'ana nan gaba. Kursiyin Allah da na Dan Rago za su kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa bauta. 4 Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu. 5 Babu sauran dare; ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba gama Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su yi mulki har abada abadin. 6 Mala'ika ya ce mani, "Wadannan kalmomi amintattu ne da gaskiya. Ubangiji, Allah na ruhohin annabawa, ya aiki mala'ikansa ya nuna wa bayinsa abin da lallai zai faru ba da dadewa ba". 7 "Duba! Ina zuwa ba da dadewa ba! Mai albarka ne wanda ya yi biyayya da kalmomin littafin nan." 8 Ni, Yahaya, nine na ji na kuma ga wadannan abubuwa. Sa'adda na ji na gan su, sai na fadi gaban kafaffun mala'ikan da ya nuna mani wadannan abubuwa domin in yi masa sujada. 9 Ya ce mani, "Kada ka yi haka! Ni abokin bauta ne tare da kai, tare da 'yan'uwanka annabawa, da wadanda ke biyayya da kalmomin littafin nan. Yi sujada ga Allah!" 10 Ya ce mani, "Kada ka rufe kalmomin anabcin littafin nan, gama lokaci ya kusa. 11 Wanda yake mara adalci, bari ya cigaba da yin rashin adalci. Wanda yake mai kazanta bari ya cigaba da kazantar da kansa. Wanda yake mai adalci bari ya cigaba da yin adalci. Wanda yake mai-tsarki, bari yaci gaba da tsarki." 12 "Duba! Ina zuwa ba da dadewa ba. Sakamakona na tare da ni, zan saka wa kowa gwargwadon aikin da ya yi. 13 Nine Alpha da Omega, farko da karshe, mafarin abu da karshensa. 14 Masu albarka ne wadanda suka wanke rigunansu domin su sami izini su ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta kofofinsa. 15 A waje akwai karnuka, masu sihiri, masu bautar gumaka, fasikai, masu kisan kai, da duk wanda yake kaunar aikata rashin gaskiya. 16 Ni, Yesu na aiko mala'ikana ya shaida maku wadannan abubuwa saboda ikilisiyoyi. Nine tushe da zuriyar Dauda, tauraron asubahi mai-haske." 17 Ruhu da Amarya suka ce, "Zo!" Bari wanda ya ji ya ce, "Zo!" Kowanne mai jin kishi, da kowanne mai bukatar ta, bari ya sami ruwan rai kyauta. 18 Ina shaida wa duk mai jin kalmomin anabcin wannan littafi: Idan wani ya kara a kansu, Allah zai kara masa annoban da ke rubuce a cikin littafin. 19 Idan wani ya rage daga kalmomin wannan littafin anabci, Allah zai rage rabonsa daga cikin itacen rai daga cikin birni mai-tsarki, wadanda aka rubuta cikin wannan littafi. 20 Shi wanda ya shaida wadannan abubuwa ya ce, "I! Ina zuwa ba da dadewa ba." Amin! Zo, Ubangiji Yesu! 21 Alherin Ubangiji Yesu ya kasance tare da kowanne dayanku. Amin.
Yahaya ya cigaba da kwatanta sabon Urushalima kamar yadda mala'ikan ya nuna masa.
Anan "ni" na nufin Yahaya.
"rafin da ke gudu da ruwan bada rai"
An yi maganar rai madawami kamar an tanada shi ta wurin ruwa mai bada rai. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 21:6.
Wannan ƙaramin tunkiya ne. Alama ne a nan da ke nufin Almasihu. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 5: 6.
A nan "al'ummai" na nufin mutane da su ke zama a cikin kowane al'umma. AT: "mutanen dukka al'ummai"
AT: 1) "Ba za a sami wani da Allah zai la'hanta ba" ko 2) "Ba za a sami wani a wurin da na ƙarƙashin la'anar Allah ba"
Ma'anoni masu yiwuwa na "sa" 1) "Duk kalmomin na nufin Allah Uba, ko 2) Duk kalmomin na nufin Allah da Ragon, wanda na mulki tare.
Wannan ƙarin magana ne, da na nufin kasancewa a gaban Allah. AT: "Za su kasance a gaban Allah"
Wannan ne mafarin ƙarshen wahayin Yahaya. Mala'ikan ya na magana da Yahaya a aya 6. A aya 7, Yesu na magana kamar yanda aka bayyana a UDB.
A nan "kalmomi" na nufin sakon da sun yi. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 21:5. AT: "Wannan kalmomi amintattu ne da gaskiya"
Ma'anoni masu yiwuwa 1) kalmar "ruhohi" na nufin tunanin annabawa kuma ya na nuna cewa Allah ya sa su. AT: "Allah da ya sa annabawan" ko 1) kalmar "ruhohi" na nufin Ruhu Mai Tsarki da ya sa annabawan. AT: "Allah da ya ba da Ruhunsa ga annabawan"
A nan Yesu ya fara magana. Kalmar "Duba" na jan hankali ne a kan abinda na biye.
Ana nufin ya na zuwa domin ya yi hukunci. Dubi yadda kuka juya wannan a cikin 3:11. AT: "Ina zuwa in yi hukunci ba da daɗewa ba!"
Wannan na nufin cewa Yahaya ya ƙwanta a ƙasa ya kuma miƙe a kansa don girmamawa ko biyyaya. Wannan muhimmin abu ne a sujada, don nuna biyyaya da bauta. Dubi yadda kun juya irin wannan jumla a cikin 19:10.
Liƙe littafi, rufe littafi ne da wani abu da zai hana wani ya iya karanta abin da ke ciki sai ya yage liƙen. Mala'ika ya na gaya wa Yahaya cewa kada ya ajiye saƙon a ɓoye. AT: "Kada ka ɓoye ... wannan littafin"
A nan "kalmomi" na nufin saƙon da sun yi. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 22:7. AT: "Wannan saƙon anabcin wannan littafi"
Waɗannan jumloli na nufin abu ɗaya ne kuma su na nanata cewa Yesu ya na raye kuma zai kasance a dukkan lokaci.
Waɗannan baƙaƙe ne na farko da ƙarshe na haruffar Greek. Ga ma'anoni masu yiwuwa 1) "wanda ya fara dukka komai da wanda ya gama komai" ko kuma 2) "wanda ya ke rayuwa koda yaushe da kuma wanda zai yi rayuwa kullum." Idan masu karatun ba za su gane waɗannan ba, za ku iya amfani da baƙaƙe na farko da ƙarshe na harshensu. Dubi yanda kun juya wannan a cikin 1:18. AT: "A da Z" ko "na farko da ƙarshe"
Wannan ya na nufin kassancewar Yesu har abada. Dubi yadda kun juya wannan a cikin 1:17.
AT: 1) "wanda ya fara dukkan komai da wanda zai sa dukkan komai su ƙare" ko 2) "wanda ya kasance kafin dukkan komai da kuma wanda zai kasance bayan dukkan komai."
An yi maganar zaman adalci kamar wanke riguna. Dubi yadda kun juya jumla irin wannan a cikin 7:14. AT: "waɗanda su na da adalci, kamar sun wanke rigunansu"
Wannan na nufin cewa su na wajen garin ne kuma ba a yarda su shiga ba.
Kare a wannan al'ada dabba ne mai ƙazanta da ana kuma raina wa. A nan kalmar "karnuka" na ƙasƙantarwa ne kuma na nufin mugayen mutane.
Kalmomin nan "tushe" da "zuriya" na nufin abu ɗaya ne. Yesu ya yi maganar zama "zuriya" kamar ya zama "tushe" ne da ya fito daga Dauda. Kalmomin na nanata cewa Yesu ɗan iyalin Dauda ne.
Yesu ya yi maganar kansa kamar shi ne hasken tauraro da na bayyana a wani lokaci da asubahi kuma ya na nuna cewa gari ya yi kusan wayewa. Dubi yadda kun juya "tauraron asubahi" a cikin 2:28.
An yi maganar masubi kamar sun zama amaryan da za a ɗaura mata aure da angonta, Yesu.
Ma'anoni masu yiwuwa 1) wannan gayyata ne ga mutane don su zo su sha ruwan rai. AT: "Zo ku sha!" ko 2) wannan roƙo ne na ladabi don Yesu ya dawo. AT: "Zo!"
An yi maganar begen mutum don rai madawami kamar ƙishi ne da kuma mutum mai karɓan rai madawami kamar ya na shan ruwa mai ba da rai ne.
A nan "Ina" na nufin Yahaya.
Wannan gargaɗi ne mai ƙarfi na kada a canja komai game da wannan annabci.
AT: "waɗanda na rubuta game da su a cikin wannan littafi"
"Yesu, wanda ya shaida"
"kowanne ɗayanku"
Yahaya ya gan rafi ruwan rai yana zubowa daga kursiyin Allah.
ganyen itace na rai shine warkasuwa na al'ummai.
kursiyin Allah da na Ɗan Ragon zai zauna a cikin birnin.
Ba za a sake samun wani zagi ba, kuma ba za a sake yin dare ba.
Sai mutum ya yi biya ya da anabci wannan litafin kamin ya sami albarka.
Mala'ikan ya gaya wa Yahaya ya yi wa Allah sujada.
An gaya wa Yahaya kada ya kulle kalmar wannan anabcin domin lokacin ya yi kusa.
Ubangiji ya ce zai kawu ladar sa sa'anda ya dawo
Wadan da suke so su sami dama ci daga 'yayan itacen rai sai sun wanke rigunar su.
Yesu ya ce shi tushin da zuriyar sarki Dauda ne.
Dukka wanda ya ƙara akan anabcin wannan littafin zai karɓi bala'i da aka rubuta a wannan littafin.
Duk wanda ya rage daga anabcin wannan littafin za a dauke daga cikin ladar sa na itacen rai.
Maganar Yesu na karshe shi ne, "I! na yi kusan zuwa".
maganar karshe a wannan littafin shi ne "Amin"
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.
Shawarwarin Fassara
(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar "'ya'yan Allah" kalma ce da aka yi ta amfani da ita tana kuma da ma'anoni da yawa.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: mala'ika, aljani, ɗa, Ɗan Allah, mai mulki, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar "'ya'yan Allah" kalma ce da aka yi ta amfani da ita tana kuma da ma'anoni da yawa.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: mala'ika, aljani, ɗa, Ɗan Allah, mai mulki, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar "'ya'yan Allah" kalma ce da aka yi ta amfani da ita tana kuma da ma'anoni da yawa.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: mala'ika, aljani, ɗa, Ɗan Allah, mai mulki, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar "'ya'yan Allah" kalma ce da aka yi ta amfani da ita tana kuma da ma'anoni da yawa.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: mala'ika, aljani, ɗa, Ɗan Allah, mai mulki, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar "'ya'yan Allah" kalma ce da aka yi ta amfani da ita tana kuma da ma'anoni da yawa.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: mala'ika, aljani, ɗa, Ɗan Allah, mai mulki, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar "'ya'yan Allah" kalma ce da aka yi ta amfani da ita tana kuma da ma'anoni da yawa.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: mala'ika, aljani, ɗa, Ɗan Allah, mai mulki, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar "'ya'yan Allah" kalma ce da aka yi ta amfani da ita tana kuma da ma'anoni da yawa.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: mala'ika, aljani, ɗa, Ɗan Allah, mai mulki, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar "'ya'yan Allah" kalma ce da aka yi ta amfani da ita tana kuma da ma'anoni da yawa.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: mala'ika, aljani, ɗa, Ɗan Allah, mai mulki, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar "'ya'yan Allah" kalma ce da aka yi ta amfani da ita tana kuma da ma'anoni da yawa.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: mala'ika, aljani, ɗa, Ɗan Allah, mai mulki, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "'yanci" ko "'yancin kai" tana nufin hali na rashin kasancewa a ƙangin bauta, ko duk wani abu da kan tauye 'yanci. wata kalma da ake mora a memakon "'yanci" ita ce "dama."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hani, bautarwa, bawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "'yanci" ko "'yancin kai" tana nufin hali na rashin kasancewa a ƙangin bauta, ko duk wani abu da kan tauye 'yanci. wata kalma da ake mora a memakon "'yanci" ita ce "dama."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hani, bautarwa, bawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "'yanci" ko "'yancin kai" tana nufin hali na rashin kasancewa a ƙangin bauta, ko duk wani abu da kan tauye 'yanci. wata kalma da ake mora a memakon "'yanci" ita ce "dama."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hani, bautarwa, bawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "'yanci" ko "'yancin kai" tana nufin hali na rashin kasancewa a ƙangin bauta, ko duk wani abu da kan tauye 'yanci. wata kalma da ake mora a memakon "'yanci" ita ce "dama."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hani, bautarwa, bawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "'yanci" ko "'yancin kai" tana nufin hali na rashin kasancewa a ƙangin bauta, ko duk wani abu da kan tauye 'yanci. wata kalma da ake mora a memakon "'yanci" ita ce "dama."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hani, bautarwa, bawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "'yanci" ko "'yancin kai" tana nufin hali na rashin kasancewa a ƙangin bauta, ko duk wani abu da kan tauye 'yanci. wata kalma da ake mora a memakon "'yanci" ita ce "dama."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hani, bautarwa, bawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "'yanci" ko "'yancin kai" tana nufin hali na rashin kasancewa a ƙangin bauta, ko duk wani abu da kan tauye 'yanci. wata kalma da ake mora a memakon "'yanci" ita ce "dama."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hani, bautarwa, bawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ma'anar "'yantarwa" shi ne furtawa a fili cewa wannan mutum bashi da laifi game da taka shari'a ko halin da bai dace ba wanda ake ƙarar sa akai.
(Hakanan duba: gafartawa, laifi, zunubi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ma'anar "'yantarwa" shi ne furtawa a fili cewa wannan mutum bashi da laifi game da taka shari'a ko halin da bai dace ba wanda ake ƙarar sa akai.
(Hakanan duba: gafartawa, laifi, zunubi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
'Yar'uwa talika ce mace wadda a ƙalla suka haɗa ɗaya daga cikin iyaye da wani. A na ce mata 'yar'uwa ga wannan mutumin ko shi ya zama ɗan'uwan ta.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: ɗan'uwa cikin Almasihu, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
'Yar'uwa talika ce mace wadda a ƙalla suka haɗa ɗaya daga cikin iyaye da wani. A na ce mata 'yar'uwa ga wannan mutumin ko shi ya zama ɗan'uwan ta.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: ɗan'uwa cikin Almasihu, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
'Yar'uwa talika ce mace wadda a ƙalla suka haɗa ɗaya daga cikin iyaye da wani. A na ce mata 'yar'uwa ga wannan mutumin ko shi ya zama ɗan'uwan ta.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: ɗan'uwa cikin Almasihu, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
'Yar'uwa talika ce mace wadda a ƙalla suka haɗa ɗaya daga cikin iyaye da wani. A na ce mata 'yar'uwa ga wannan mutumin ko shi ya zama ɗan'uwan ta.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: ɗan'uwa cikin Almasihu, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
'Yar'uwa talika ce mace wadda a ƙalla suka haɗa ɗaya daga cikin iyaye da wani. A na ce mata 'yar'uwa ga wannan mutumin ko shi ya zama ɗan'uwan ta.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: ɗan'uwa cikin Almasihu, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
'Yar'uwa talika ce mace wadda a ƙalla suka haɗa ɗaya daga cikin iyaye da wani. A na ce mata 'yar'uwa ga wannan mutumin ko shi ya zama ɗan'uwan ta.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: ɗan'uwa cikin Almasihu, ruhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Abiya sunan wani sarki ne na Yahuda wanda ya yi mulki daga 915-913 BC. Ɗan Sarki Rehobowam ne. Akwai wasu mutane kuma da dama da ake kiran su Abiya a cikin Tsohon Alƙawari.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Abiya sunan wani sarki ne na Yahuda wanda ya yi mulki daga 915-913 BC. Ɗan Sarki Rehobowam ne. Akwai wasu mutane kuma da dama da ake kiran su Abiya a cikin Tsohon Alƙawari.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Abiyata babban firist ne domin al'ummar Isra'ila a zamanin Sarki Dauda.
(Hakanan duba: Zadok, Saul (Tsohon Alƙawari), Dauda, Suleman, Adoniya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Adamu mutum ne na fari da Allah ya hallita. Da shi da matarsa Hauwa'u an yi su cikin surar Allah.
(Hakanan duba: mutuwa, zuriya, Hauwa, siffar Allah, rayuwa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Adamu mutum ne na fari da Allah ya hallita. Da shi da matarsa Hauwa'u an yi su cikin surar Allah.
(Hakanan duba: mutuwa, zuriya, Hauwa, siffar Allah, rayuwa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Adamu mutum ne na fari da Allah ya hallita. Da shi da matarsa Hauwa'u an yi su cikin surar Allah.
(Hakanan duba: mutuwa, zuriya, Hauwa, siffar Allah, rayuwa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Adamu mutum ne na fari da Allah ya hallita. Da shi da matarsa Hauwa'u an yi su cikin surar Allah.
(Hakanan duba: mutuwa, zuriya, Hauwa, siffar Allah, rayuwa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Adamu mutum ne na fari da Allah ya hallita. Da shi da matarsa Hauwa'u an yi su cikin surar Allah.
(Hakanan duba: mutuwa, zuriya, Hauwa, siffar Allah, rayuwa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Afolos Bayahude ne daga birnin Alezandariya a Masar wanda yake da baiwar koyar da mutane musamman akan Yesu.
(Hakanan duba: Akuila, Afisawa, Firissila, maganar Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Afolos Bayahude ne daga birnin Alezandariya a Masar wanda yake da baiwar koyar da mutane musamman akan Yesu.
(Hakanan duba: Akuila, Afisawa, Firissila, maganar Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Afolos Bayahude ne daga birnin Alezandariya a Masar wanda yake da baiwar koyar da mutane musamman akan Yesu.
(Hakanan duba: Akuila, Afisawa, Firissila, maganar Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ahaz mugun sarki ne wanda ya yi mulki bisa masarautar Yahuda daga 732 zuwa 716 BC. Wannan kimamin shekaru 140 ne kafin lokacin da aka kwashe mutane da yawa daga Isra'ila da Yahuda zuwa bautar talala a Babila.
(Hakanan duba: Babila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokatanTsohon Alƙawari, Ai sunan wani garin Kan'aniyawa ne kudu da Betel ratan kilo mita 8 arewa maso yamma da Yeriko.
(Hakanan duba: Betel, Yeriko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokatanTsohon Alƙawari, Ai sunan wani garin Kan'aniyawa ne kudu da Betel ratan kilo mita 8 arewa maso yamma da Yeriko.
(Hakanan duba: Betel, Yeriko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokatanTsohon Alƙawari, Ai sunan wani garin Kan'aniyawa ne kudu da Betel ratan kilo mita 8 arewa maso yamma da Yeriko.
(Hakanan duba: Betel, Yeriko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokatanTsohon Alƙawari, Ai sunan wani garin Kan'aniyawa ne kudu da Betel ratan kilo mita 8 arewa maso yamma da Yeriko.
(Hakanan duba: Betel, Yeriko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokatanTsohon Alƙawari, Ai sunan wani garin Kan'aniyawa ne kudu da Betel ratan kilo mita 8 arewa maso yamma da Yeriko.
(Hakanan duba: Betel, Yeriko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokatanTsohon Alƙawari, Ai sunan wani garin Kan'aniyawa ne kudu da Betel ratan kilo mita 8 arewa maso yamma da Yeriko.
(Hakanan duba: Betel, Yeriko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokatanTsohon Alƙawari, Ai sunan wani garin Kan'aniyawa ne kudu da Betel ratan kilo mita 8 arewa maso yamma da Yeriko.
(Hakanan duba: Betel, Yeriko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokatanTsohon Alƙawari, Ai sunan wani garin Kan'aniyawa ne kudu da Betel ratan kilo mita 8 arewa maso yamma da Yeriko.
(Hakanan duba: Betel, Yeriko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokatanTsohon Alƙawari, Ai sunan wani garin Kan'aniyawa ne kudu da Betel ratan kilo mita 8 arewa maso yamma da Yeriko.
(Hakanan duba: Betel, Yeriko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokatanTsohon Alƙawari, Ai sunan wani garin Kan'aniyawa ne kudu da Betel ratan kilo mita 8 arewa maso yamma da Yeriko.
(Hakanan duba: Betel, Yeriko)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Akila Ba-yahuden Kirista ne daga lardin Fontus, wata yankin ƙasa kudancin gaɓas da BaƙinTekun.
(Hakanan duba: Afolos, Korint, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Akila Ba-yahuden Kirista ne daga lardin Fontus, wata yankin ƙasa kudancin gaɓas da BaƙinTekun.
(Hakanan duba: Afolos, Korint, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Akila Ba-yahuden Kirista ne daga lardin Fontus, wata yankin ƙasa kudancin gaɓas da BaƙinTekun.
(Hakanan duba: Afolos, Korint, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Akila Ba-yahuden Kirista ne daga lardin Fontus, wata yankin ƙasa kudancin gaɓas da BaƙinTekun.
(Hakanan duba: Afolos, Korint, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
"Mutanen Amon" ko Amoniyawa wasu jinsin mutane ne a Kan'ana. Sun fito ne daga zuriyar Ben-ami, wanda yake ɗan Lot ta wurin karamar ɗiyarsa.
(Hakanan duba: la'ana, Kogin Yodan, Lot)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Amos annabin Isra'ilawa ne wanda ya yi zamani da Sarki Uziya na Yahuda.
(Hakanan duba: ɓaure, Yahuda, masarautar Isra'ila, makiyayi, Uziya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Anas babban firist ne na Yahudawa a Yerusalem na tsawon shekara 10, daga AD 6 zuwa AD 15. Sa'an nan gwamnatin Romawa ta cire shi daga matsayin manyan firistoci, koda shi ke ya ci gaba da zama tsayayyen shugaba a cikin Yahudawa.
(Hakanan duba: babban firist, firist)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Andarawus yana ɗaya daga cikin mutum goma sha biyu da Yesu ya zaɓa su zama almajiransa na kurkusa da shi {daga baya an kira su manzanni}.
(Hakanan duba: manzo, almajiri, sha biyun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Andarawus yana ɗaya daga cikin mutum goma sha biyu da Yesu ya zaɓa su zama almajiransa na kurkusa da shi {daga baya an kira su manzanni}.
(Hakanan duba: manzo, almajiri, sha biyun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Andarawus yana ɗaya daga cikin mutum goma sha biyu da Yesu ya zaɓa su zama almajiransa na kurkusa da shi {daga baya an kira su manzanni}.
(Hakanan duba: manzo, almajiri, sha biyun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Aram sunan mutum biyu ne a Tsohon Alƙawari. kuma sunan wata yankin ƙasa ce arewa maso gabas da Kan'ana, inda Siriya take a yau.
(Hakanan duba: Mesofotamiya, Fadan Aram, Rebeka, Shem, Siriya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Aram sunan mutum biyu ne a Tsohon Alƙawari. kuma sunan wata yankin ƙasa ce arewa maso gabas da Kan'ana, inda Siriya take a yau.
(Hakanan duba: Mesofotamiya, Fadan Aram, Rebeka, Shem, Siriya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Arebiya ita ce babbar ƙasa duk duniya wadda ruwa ya kusan kewaye ta, kusan 3,000,000 kilomitas zagayen ta. Tana kudu maso gabas da Isra'ila, tana iyaka da Jan Teku, da Teku Arebiya da kuma Gacin Fasiya.
(Hakanan duba: Isuwa, Galatiyawa, Isma'ila, Shem, Sinai)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Asa sarki ne da ya yi mulki bisa sarautar Yahuda shekara arba'in, daga 913 - 873 BC.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Asa sarki ne da ya yi mulki bisa sarautar Yahuda shekara arba'in, daga 913 - 873 BC.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Asa sarki ne da ya yi mulki bisa sarautar Yahuda shekara arba'in, daga 913 - 873 BC.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Asa sarki ne da ya yi mulki bisa sarautar Yahuda shekara arba'in, daga 913 - 873 BC.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Asa sarki ne da ya yi mulki bisa sarautar Yahuda shekara arba'in, daga 913 - 873 BC.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Asa sarki ne da ya yi mulki bisa sarautar Yahuda shekara arba'in, daga 913 - 873 BC.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar "Asabaci" na nufin rana ta bakwai cikin mako, wadda Allah ya dokaci Isra'ilawa da su keɓe ta ranar hutu kada a yi wani aiki.
Shawarwarin Fassara:
(Duba kuma: hutu)
Wurarenda ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar "Asabaci" na nufin rana ta bakwai cikin mako, wadda Allah ya dokaci Isra'ilawa da su keɓe ta ranar hutu kada a yi wani aiki.
Shawarwarin Fassara:
(Duba kuma: hutu)
Wurarenda ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar "Asabaci" na nufin rana ta bakwai cikin mako, wadda Allah ya dokaci Isra'ilawa da su keɓe ta ranar hutu kada a yi wani aiki.
Shawarwarin Fassara:
(Duba kuma: hutu)
Wurarenda ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokacin LIttafi Mai Tsarki, "Asiya" sunan wani lardi ne na mulkin Roma. Wurin yana yamma da ƙasar da yanzu ake ce da ita Toki ko Turkaniya.
(Hakanan duba: Roma, Bulus, Afisawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokacin LIttafi Mai Tsarki, "Asiya" sunan wani lardi ne na mulkin Roma. Wurin yana yamma da ƙasar da yanzu ake ce da ita Toki ko Turkaniya.
(Hakanan duba: Roma, Bulus, Afisawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokacin LIttafi Mai Tsarki, "Asiya" sunan wani lardi ne na mulkin Roma. Wurin yana yamma da ƙasar da yanzu ake ce da ita Toki ko Turkaniya.
(Hakanan duba: Roma, Bulus, Afisawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokacin LIttafi Mai Tsarki, "Asiya" sunan wani lardi ne na mulkin Roma. Wurin yana yamma da ƙasar da yanzu ake ce da ita Toki ko Turkaniya.
(Hakanan duba: Roma, Bulus, Afisawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokacin LIttafi Mai Tsarki, "Asiya" sunan wani lardi ne na mulkin Roma. Wurin yana yamma da ƙasar da yanzu ake ce da ita Toki ko Turkaniya.
(Hakanan duba: Roma, Bulus, Afisawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokacin LIttafi Mai Tsarki, "Asiya" sunan wani lardi ne na mulkin Roma. Wurin yana yamma da ƙasar da yanzu ake ce da ita Toki ko Turkaniya.
(Hakanan duba: Roma, Bulus, Afisawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A lokacin LIttafi Mai Tsarki, "Asiya" sunan wani lardi ne na mulkin Roma. Wurin yana yamma da ƙasar da yanzu ake ce da ita Toki ko Turkaniya.
(Hakanan duba: Roma, Bulus, Afisawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ayuba mutum ne da aka yi bayaninsa a Littafi Mai tsarki a matsayin marar aibi mai adalci ne kuma a gaban Allah. Anfi saninsa domin jurewarsa a cikin bangaskiyarsa ga Allah a cikin lokuttan wahala mai tsanani.
(Hakanan duba: Ibrahim, Isuwa, ruwan ambaliya wato tsufana, Yakubu, Nuhu, ƙungiyar mutane)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ma'anar "Ba'al" shi ne "ubangiji" ko "maigida" kuma sunan babban gunkin da Kan'aniyawa suke bautawa ne.
(Hakanan duba: Ahab, Ashera, Iliya, allahn ƙarya, karuwa, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ma'anar "Ba'al" shi ne "ubangiji" ko "maigida" kuma sunan babban gunkin da Kan'aniyawa suke bautawa ne.
(Hakanan duba: Ahab, Ashera, Iliya, allahn ƙarya, karuwa, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ma'anar "Ba'al" shi ne "ubangiji" ko "maigida" kuma sunan babban gunkin da Kan'aniyawa suke bautawa ne.
(Hakanan duba: Ahab, Ashera, Iliya, allahn ƙarya, karuwa, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ma'anar "Ba'al" shi ne "ubangiji" ko "maigida" kuma sunan babban gunkin da Kan'aniyawa suke bautawa ne.
(Hakanan duba: Ahab, Ashera, Iliya, allahn ƙarya, karuwa, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Birnin Babila shi ne babban birnin ƙasar Babila ta dã, wanda shima ɓangaren Mulkin Babila ne.
(Hakanan duba: Babel, Kaldiya, Yahuda, Nebukadnezza)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Birnin Babila shi ne babban birnin ƙasar Babila ta dã, wanda shima ɓangaren Mulkin Babila ne.
(Hakanan duba: Babel, Kaldiya, Yahuda, Nebukadnezza)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Birnin Babila shi ne babban birnin ƙasar Babila ta dã, wanda shima ɓangaren Mulkin Babila ne.
(Hakanan duba: Babel, Kaldiya, Yahuda, Nebukadnezza)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Birnin Babila shi ne babban birnin ƙasar Babila ta dã, wanda shima ɓangaren Mulkin Babila ne.
(Hakanan duba: Babel, Kaldiya, Yahuda, Nebukadnezza)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Farisawa mahimman mutane ne ƙungiya kuma mai iko na shugabanin addinin Yahudawa a zamanin Yesu.
(Hakanan duba: majalisa, shugabannin Yahudawa, shari'a, Sadusiyawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bal'amu wani ba'al'ummen annabi ne wanda Sarki Balek ya yi hayarsa ya la'anta Isra'ila sa'ad da suka kafa zango a Kogin Yordan a arewacin Mowab, sa'ad da suke shirin shiga ƙasar Kan'ana.
(Hakanan duba : albarka, Kan'ana, la'ana, jaki, Kogin Yufiretis, Kogin Yodan, Midiyan, Mowab, Feyo)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bal'amu wani ba'al'ummen annabi ne wanda Sarki Balek ya yi hayarsa ya la'anta Isra'ila sa'ad da suka kafa zango a Kogin Yordan a arewacin Mowab, sa'ad da suke shirin shiga ƙasar Kan'ana.
(Hakanan duba : albarka, Kan'ana, la'ana, jaki, Kogin Yufiretis, Kogin Yodan, Midiyan, Mowab, Feyo)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Barnabas ɗaya ne daga cikin Kiristoci na farko da suka kasance tare da manzanni.
(Hakanan duba: Kirista, Saifuros, labari mai daɗi, Lebi, Bulus)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Barnabas ɗaya ne daga cikin Kiristoci na farko da suka kasance tare da manzanni.
(Hakanan duba: Kirista, Saifuros, labari mai daɗi, Lebi, Bulus)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yahudawa mutane ne zuriyar Yakubu jikan Ibrahim. Kalmar "Bayahude" ta fito daga kalmar "Yahuda."
(Hakanan duba: Ibrahim, Yakubu, Isra'ila, Babila, shugabannin Yahudanci)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yahudawa mutane ne zuriyar Yakubu jikan Ibrahim. Kalmar "Bayahude" ta fito daga kalmar "Yahuda."
(Hakanan duba: Ibrahim, Yakubu, Isra'ila, Babila, shugabannin Yahudanci)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yahudawa mutane ne zuriyar Yakubu jikan Ibrahim. Kalmar "Bayahude" ta fito daga kalmar "Yahuda."
(Hakanan duba: Ibrahim, Yakubu, Isra'ila, Babila, shugabannin Yahudanci)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yahudawa mutane ne zuriyar Yakubu jikan Ibrahim. Kalmar "Bayahude" ta fito daga kalmar "Yahuda."
(Hakanan duba: Ibrahim, Yakubu, Isra'ila, Babila, shugabannin Yahudanci)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yahudawa mutane ne zuriyar Yakubu jikan Ibrahim. Kalmar "Bayahude" ta fito daga kalmar "Yahuda."
(Hakanan duba: Ibrahim, Yakubu, Isra'ila, Babila, shugabannin Yahudanci)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yahudawa mutane ne zuriyar Yakubu jikan Ibrahim. Kalmar "Bayahude" ta fito daga kalmar "Yahuda."
(Hakanan duba: Ibrahim, Yakubu, Isra'ila, Babila, shugabannin Yahudanci)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Garin Betani yana gabashin gangaren Tsaunin Zaitun, misalin mil 2 gabas da Yerusalem.
(Hakanan duba: Yeriko, Yerusalem, La'azaru, Marta, Maryamu ('yar'uwar Marta), Tsaunin Zaitun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bilatus gwamnan lardin Yudiya ta Roma ne wanda ya zartar wa Yesu hukuncin mutuwa.
(Hakanan duba: gicciye, gwamna, laifi, Yudiya, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bilatus gwamnan lardin Yudiya ta Roma ne wanda ya zartar wa Yesu hukuncin mutuwa.
(Hakanan duba: gicciye, gwamna, laifi, Yudiya, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bilatus gwamnan lardin Yudiya ta Roma ne wanda ya zartar wa Yesu hukuncin mutuwa.
(Hakanan duba: gicciye, gwamna, laifi, Yudiya, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bilatus gwamnan lardin Yudiya ta Roma ne wanda ya zartar wa Yesu hukuncin mutuwa.
(Hakanan duba: gicciye, gwamna, laifi, Yudiya, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bilatus gwamnan lardin Yudiya ta Roma ne wanda ya zartar wa Yesu hukuncin mutuwa.
(Hakanan duba: gicciye, gwamna, laifi, Yudiya, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bilatus gwamnan lardin Yudiya ta Roma ne wanda ya zartar wa Yesu hukuncin mutuwa.
(Hakanan duba: gicciye, gwamna, laifi, Yudiya, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bitrus yana ɗaya daga cikin manzannin Yesu guda goma sha biyu. Shi shugaba ne mai mahimmanci a ikilisiya ta farko,
(Hakanan duba: almajiri, manzanni)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bitrus yana ɗaya daga cikin manzannin Yesu guda goma sha biyu. Shi shugaba ne mai mahimmanci a ikilisiya ta farko,
(Hakanan duba: almajiri, manzanni)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bitrus yana ɗaya daga cikin manzannin Yesu guda goma sha biyu. Shi shugaba ne mai mahimmanci a ikilisiya ta farko,
(Hakanan duba: almajiri, manzanni)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bitrus yana ɗaya daga cikin manzannin Yesu guda goma sha biyu. Shi shugaba ne mai mahimmanci a ikilisiya ta farko,
(Hakanan duba: almajiri, manzanni)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bitrus yana ɗaya daga cikin manzannin Yesu guda goma sha biyu. Shi shugaba ne mai mahimmanci a ikilisiya ta farko,
(Hakanan duba: almajiri, manzanni)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bitrus yana ɗaya daga cikin manzannin Yesu guda goma sha biyu. Shi shugaba ne mai mahimmanci a ikilisiya ta farko,
(Hakanan duba: almajiri, manzanni)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bitrus yana ɗaya daga cikin manzannin Yesu guda goma sha biyu. Shi shugaba ne mai mahimmanci a ikilisiya ta farko,
(Hakanan duba: almajiri, manzanni)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bitrus yana ɗaya daga cikin manzannin Yesu guda goma sha biyu. Shi shugaba ne mai mahimmanci a ikilisiya ta farko,
(Hakanan duba: almajiri, manzanni)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bo'aza Ba'isra'ile ne shi ne kuma mijin Rut, mahaifin kakan Sarki Dauda, da kuma zuriyar Yesu Almasihu.
(Hakanan duba: Mowab, fansa, Rut)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.
(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Daniyel annabi ne Bais'ile ne wanda a matsayinsa na matashi aka kwashe su zuwa bauta har tsawon shekaru 70 ta wurin sarkin Babila mai suna Nebubkadnezar a wajejen shekaru 600 kafin zuwan Almasihu.
Wuraren da ake samuunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dauda shi ne sarki na biyu a Isra'ila ya kuma ƙaunaci Allah. Shi ne babban marubucin littafin Zabura.
(Hakanan duba: Goliyat, Filistiyawa, Saul (Tsohon Alƙawari))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dauda shi ne sarki na biyu a Isra'ila ya kuma ƙaunaci Allah. Shi ne babban marubucin littafin Zabura.
(Hakanan duba: Goliyat, Filistiyawa, Saul (Tsohon Alƙawari))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dauda shi ne sarki na biyu a Isra'ila ya kuma ƙaunaci Allah. Shi ne babban marubucin littafin Zabura.
(Hakanan duba: Goliyat, Filistiyawa, Saul (Tsohon Alƙawari))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dauda shi ne sarki na biyu a Isra'ila ya kuma ƙaunaci Allah. Shi ne babban marubucin littafin Zabura.
(Hakanan duba: Goliyat, Filistiyawa, Saul (Tsohon Alƙawari))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dauda shi ne sarki na biyu a Isra'ila ya kuma ƙaunaci Allah. Shi ne babban marubucin littafin Zabura.
(Hakanan duba: Goliyat, Filistiyawa, Saul (Tsohon Alƙawari))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dauda shi ne sarki na biyu a Isra'ila ya kuma ƙaunaci Allah. Shi ne babban marubucin littafin Zabura.
(Hakanan duba: Goliyat, Filistiyawa, Saul (Tsohon Alƙawari))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dauda shi ne sarki na biyu a Isra'ila ya kuma ƙaunaci Allah. Shi ne babban marubucin littafin Zabura.
(Hakanan duba: Goliyat, Filistiyawa, Saul (Tsohon Alƙawari))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dauda shi ne sarki na biyu a Isra'ila ya kuma ƙaunaci Allah. Shi ne babban marubucin littafin Zabura.
(Hakanan duba: Goliyat, Filistiyawa, Saul (Tsohon Alƙawari))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dauda shi ne sarki na biyu a Isra'ila ya kuma ƙaunaci Allah. Shi ne babban marubucin littafin Zabura.
(Hakanan duba: Goliyat, Filistiyawa, Saul (Tsohon Alƙawari))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Dauda shi ne sarki na biyu a Isra'ila ya kuma ƙaunaci Allah. Shi ne babban marubucin littafin Zabura.
(Hakanan duba: Goliyat, Filistiyawa, Saul (Tsohon Alƙawari))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "duhu" tana nufin rashin kasancewar haske. Akwai kuma waɗansu ƙarin bayanai game da yadda aka baiyana kalmar nan duhu:
Shawarwarin Fassara:
(Hakanan duba: mazambaci, mallaka, daula, haske, fansa, mai adalci)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Elisha annabi ne a Isra'ila a lokutan sarakuna da yawa na Isra'ila: Ahab, Ahaziya, Yehoram, Yehu, Yehoahaz, da Yehoash.
(Hakanan duba: Iliya, Na'aman, annabi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Eliyakim sunan mutane biyu ne a cikin Tsohon Alƙawari.
(Hakanan duba: Hezikiya, Yehoaikim, Yosiya, Fira'auna)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
"Idin Makonni" bukin Yahudawa ne da ake yi bayan kwana hamsin da wucewar Idin Ƙetarewa. Daga baya ne aka kira shi "Fentikos."
(Hakanan duba: buki, nunar fãri, girbi, Ruhu Mai Tsarki, tashi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
"Idin Makonni" bukin Yahudawa ne da ake yi bayan kwana hamsin da wucewar Idin Ƙetarewa. Daga baya ne aka kira shi "Fentikos."
(Hakanan duba: buki, nunar fãri, girbi, Ruhu Mai Tsarki, tashi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A Ikilisiyar Kirista ta farko a Yerusalem, Filib yana ɗaya daga cikin shugabanni bakwai da aka zaɓa su lura da matalauta Kiristoci masu buƙatu musamman gwauraye.
(Hakanan duba: Filib (manzo))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A Ikilisiyar Kirista ta farko a Yerusalem, Filib yana ɗaya daga cikin shugabanni bakwai da aka zaɓa su lura da matalauta Kiristoci masu buƙatu musamman gwauraye.
(Hakanan duba: Filib (manzo))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A Ikilisiyar Kirista ta farko a Yerusalem, Filib yana ɗaya daga cikin shugabanni bakwai da aka zaɓa su lura da matalauta Kiristoci masu buƙatu musamman gwauraye.
(Hakanan duba: Filib (manzo))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A Ikilisiyar Kirista ta farko a Yerusalem, Filib yana ɗaya daga cikin shugabanni bakwai da aka zaɓa su lura da matalauta Kiristoci masu buƙatu musamman gwauraye.
(Hakanan duba: Filib (manzo))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A Ikilisiyar Kirista ta farko a Yerusalem, Filib yana ɗaya daga cikin shugabanni bakwai da aka zaɓa su lura da matalauta Kiristoci masu buƙatu musamman gwauraye.
(Hakanan duba: Filib (manzo))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A Ikilisiyar Kirista ta farko a Yerusalem, Filib yana ɗaya daga cikin shugabanni bakwai da aka zaɓa su lura da matalauta Kiristoci masu buƙatu musamman gwauraye.
(Hakanan duba: Filib (manzo))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A Ikilisiyar Kirista ta farko a Yerusalem, Filib yana ɗaya daga cikin shugabanni bakwai da aka zaɓa su lura da matalauta Kiristoci masu buƙatu musamman gwauraye.
(Hakanan duba: Filib (manzo))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Manzo Filib yana ɗaya daga cikin asalin almajiran Yesu guda goma sha biyu. Shi ɗan garin Betsaida ne.
(Hakanan duba: Filib (mai bishara))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Manzo Filib yana ɗaya daga cikin asalin almajiran Yesu guda goma sha biyu. Shi ɗan garin Betsaida ne.
(Hakanan duba: Filib (mai bishara))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Manzo Filib yana ɗaya daga cikin asalin almajiran Yesu guda goma sha biyu. Shi ɗan garin Betsaida ne.
(Hakanan duba: Filib (mai bishara))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Manzo Filib yana ɗaya daga cikin asalin almajiran Yesu guda goma sha biyu. Shi ɗan garin Betsaida ne.
(Hakanan duba: Filib (mai bishara))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Manzo Filib yana ɗaya daga cikin asalin almajiran Yesu guda goma sha biyu. Shi ɗan garin Betsaida ne.
(Hakanan duba: Filib (mai bishara))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Manzo Filib yana ɗaya daga cikin asalin almajiran Yesu guda goma sha biyu. Shi ɗan garin Betsaida ne.
(Hakanan duba: Filib (mai bishara))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Manzo Filib yana ɗaya daga cikin asalin almajiran Yesu guda goma sha biyu. Shi ɗan garin Betsaida ne.
(Hakanan duba: Filib (mai bishara))
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A zamanin dã, sarakunan da suka yi mulki a Masar ana ce da su Fir'aunnoni.
(Hakanan duba: Masar, sarki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A zamanin dã, sarakunan da suka yi mulki a Masar ana ce da su Fir'aunnoni.
(Hakanan duba: Masar, sarki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A zamanin dã, sarakunan da suka yi mulki a Masar ana ce da su Fir'aunnoni.
(Hakanan duba: Masar, sarki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A zamanin dã, Fonishiya al'umma ce mai wadata tana kafe a Kan'ana a gaɓar Tekun Baharmaliya arewa da Isra'ila.
(Hakanan duba: sida, shunayya, Sidon, Tyre)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Fontus wani lardin Roma ne a lokacin mulkin Roma da Ikilisiya ta farko. An kafa ta ne a kudancin gaɓar Baƙin Teku, a arewacin yankin da yanzu ita ce ƙasar Turkaniya ko Toki.
(Hakanan duba: Akila, Fentikos)
Wuraren da za ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Gad na ɗaya daga cikin 'ya'yan Yakubu. Hakanan ana kiran Yakubu Isra'ila.
(Hakanan duba: ƙirga, annabi, kabilu sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin lokacin Sabon Alƙawari Galatiya ta zama babban lardin Roma a yankin tsakiyar ɓangaren da yanzu ake kira ƙasar Turkiyya.
(Hakanan duba: Asiya, imani, Silisiya, labari mai daɗi, Bulus, ayuka)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin lokacin Sabon Alƙawari Galatiya ta zama babban lardin Roma a yankin tsakiyar ɓangaren da yanzu ake kira ƙasar Turkiyya.
(Hakanan duba: Asiya, imani, Silisiya, labari mai daɗi, Bulus, ayuka)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin lokacin Sabon Alƙawari Galatiya ta zama babban lardin Roma a yankin tsakiyar ɓangaren da yanzu ake kira ƙasar Turkiyya.
(Hakanan duba: Asiya, imani, Silisiya, labari mai daɗi, Bulus, ayuka)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin lokacin Sabon Alƙawari Galatiya ta zama babban lardin Roma a yankin tsakiyar ɓangaren da yanzu ake kira ƙasar Turkiyya.
(Hakanan duba: Asiya, imani, Silisiya, labari mai daɗi, Bulus, ayuka)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A cikin lokacin Sabon Alƙawari Galatiya ta zama babban lardin Roma a yankin tsakiyar ɓangaren da yanzu ake kira ƙasar Turkiyya.
(Hakanan duba: Asiya, imani, Silisiya, labari mai daɗi, Bulus, ayuka)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Galili shi ne yanki mafi yawa a arewacin Isra'ila, yana kudu da Samariya. "Bagalile" shi ne mutumin da ke zama a Galili ko mazaunin Galili.
(Hakanan duba: Nazaret, Samariya, Tekun Galili)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Galili shi ne yanki mafi yawa a arewacin Isra'ila, yana kudu da Samariya. "Bagalile" shi ne mutumin da ke zama a Galili ko mazaunin Galili.
(Hakanan duba: Nazaret, Samariya, Tekun Galili)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Galili shi ne yanki mafi yawa a arewacin Isra'ila, yana kudu da Samariya. "Bagalile" shi ne mutumin da ke zama a Galili ko mazaunin Galili.
(Hakanan duba: Nazaret, Samariya, Tekun Galili)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Galili shi ne yanki mafi yawa a arewacin Isra'ila, yana kudu da Samariya. "Bagalile" shi ne mutumin da ke zama a Galili ko mazaunin Galili.
(Hakanan duba: Nazaret, Samariya, Tekun Galili)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Galili shi ne yanki mafi yawa a arewacin Isra'ila, yana kudu da Samariya. "Bagalile" shi ne mutumin da ke zama a Galili ko mazaunin Galili.
(Hakanan duba: Nazaret, Samariya, Tekun Galili)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A kwanakin littafi Mai Tsarki, Gaza ita ce wuri mafi wadata a biranen Filistiyawa garin na gaɓar Tekun Baharmaliya kusa mil 38 a kudancin Ashdod. Yana ɗaya daga cikin manyan biranen Filistiyawa biyar.
(Hakanan duba: Ashdod, Filibus, Filistiyawa, Habasha, Gat)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Gidiyon mutumin Isra'ila ne wanda aka yi renonsa domin ya ceci Isra'ilawa daga maƙiyansu.
(Hakanan duba: Ba'al, Ashera, kuɓutarwa, Midiyan, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Girkanci" tana nufin harshen da ake magana da shi a ƙasar Girka. Girka, hakaka nan kalmar zata iya zama da ma'anar mutuminda ya zo daga Girka. Hakanan ana magana da harshen Girkanci a dukkan Daular Roma. Kalmar nan "Girkanci" tana nufin "magana da harshen Girkanci."
(Hakanan duba: Aram, Al'ummai, Girka, Ibraniyawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Girkanci" tana nufin harshen da ake magana da shi a ƙasar Girka. Girka, hakaka nan kalmar zata iya zama da ma'anar mutuminda ya zo daga Girka. Hakanan ana magana da harshen Girkanci a dukkan Daular Roma. Kalmar nan "Girkanci" tana nufin "magana da harshen Girkanci."
(Hakanan duba: Aram, Al'ummai, Girka, Ibraniyawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A kwanakin Sabon Alƙawari, Girka wani lardi ne na daular Roma.
(Hakanan duba: Korint, Al'ummai, Girkawa, Ibraniyawa, Filifiya, Tassalonika)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
A kwanakin Sabon Alƙawari, Girka wani lardi ne na daular Roma.
(Hakanan duba: Korint, Al'ummai, Girkawa, Ibraniyawa, Filifiya, Tassalonika)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
"Golgota" sunan wani wuri ne inda aka gicciye Yesu. Sunansa ya zo ne daga kalmar Aremiyanci wadda ke nufin "Wurin Ƙoƙon Kai."
(Hakanan duba: Aram, Tsaunin Zaitun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
"Golgota" sunan wani wuri ne inda aka gicciye Yesu. Sunansa ya zo ne daga kalmar Aremiyanci wadda ke nufin "Wurin Ƙoƙon Kai."
(Hakanan duba: Aram, Tsaunin Zaitun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Habila ɗa na biyu ne ga Adamu da Hauwa'u. Shi ƙanen Kayinu ne.
(Hakanan duba: Kayinu, hadaya, makiyayi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Habila ɗa na biyu ne ga Adamu da Hauwa'u. Shi ƙanen Kayinu ne.
(Hakanan duba: Kayinu, hadaya, makiyayi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Habila ɗa na biyu ne ga Adamu da Hauwa'u. Shi ƙanen Kayinu ne.
(Hakanan duba: Kayinu, hadaya, makiyayi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Hajara Bamasariya ce wadda ta zama baiwa ga Saratu.
(Hakanan duba: Ibrahim, zuriya, Isma'ila, Saratu, baiwa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ham shi ne ɗa na biyu a cikin 'ya'yan Nuhu guda uku.
(Hakanan duba: jirgi, Kan'ana, rashin girmamawa, Nuhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ham shi ne ɗa na biyu a cikin 'ya'yan Nuhu guda uku.
(Hakanan duba: jirgi, Kan'ana, rashin girmamawa, Nuhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Hamor mutumin Kan'ana ne da zama a birnin Shekem a lokacin da Yakubu da iyalinsa ke zama kusa da Sukkot. Shi mutumin Hibitiye ne.
(Hakanan duba: Kan'ana, Hibitiye, Yakubu, Shekem, Sukkot)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Hananiya suna ne na mutane mabambanta da yawa a cikin Tsohon Alƙawari.
(Hakanan duba: Azariya, Babila, Daniyel, annabin ƙarya, Irmiya, Mishayel)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Haran ƙanen Ibram ne, mahaifin Lotu kuma.
(Hakanan duba: Ibrahim. Kalib, Kan'ana, Lebiyawa, Lotu, Tera, Ur)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Haruna wan Musa ne. Allah ya zaɓi Haruna ya zama babban firist na farko domin mutanen Isra'ila.
(Hakanan duba: firist, Musa, Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Haruna wan Musa ne. Allah ya zaɓi Haruna ya zama babban firist na farko domin mutanen Isra'ila.
(Hakanan duba: firist, Musa, Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Haruna wan Musa ne. Allah ya zaɓi Haruna ya zama babban firist na farko domin mutanen Isra'ila.
(Hakanan duba: firist, Musa, Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Wanan ita ce mace ta farko. Ma'anar sunanta shi ne "rai" ko "rayuwa."
(Hakanan duba: Adamu, rai, Shaiɗan)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Wanan ita ce mace ta farko. Ma'anar sunanta shi ne "rai" ko "rayuwa."
(Hakanan duba: Adamu, rai, Shaiɗan)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Hezekiya shi ne sarki na sha uku a cikin sarautar Yahuda. Shi sarki ne da yada dogara da kuma kuma yi wa Allah biyayya.
(Hakanan duba: Ahaz, Asiriya, allahn ƙarya, Yahuda, Sennakerib)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ibram mutumin Kaldiya ne daga birnin Ur wanda Allah ya zaɓe shi ya zama kakan Isra'ilawa. Allah ya sauya sunansa zuwa "Ibrahim."
(Hakanan duba: Kan'ana, Kaldiya, Saratu, Ishaku)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ibram mutumin Kaldiya ne daga birnin Ur wanda Allah ya zaɓe shi ya zama kakan Isra'ilawa. Allah ya sauya sunansa zuwa "Ibrahim."
(Hakanan duba: Kan'ana, Kaldiya, Saratu, Ishaku)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ibram mutumin Kaldiya ne daga birnin Ur wanda Allah ya zaɓe shi ya zama kakan Isra'ilawa. Allah ya sauya sunansa zuwa "Ibrahim."
(Hakanan duba: Kan'ana, Kaldiya, Saratu, Ishaku)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ibram mutumin Kaldiya ne daga birnin Ur wanda Allah ya zaɓe shi ya zama kakan Isra'ilawa. Allah ya sauya sunansa zuwa "Ibrahim."
(Hakanan duba: Kan'ana, Kaldiya, Saratu, Ishaku)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ibram mutumin Kaldiya ne daga birnin Ur wanda Allah ya zaɓe shi ya zama kakan Isra'ilawa. Allah ya sauya sunansa zuwa "Ibrahim."
(Hakanan duba: Kan'ana, Kaldiya, Saratu, Ishaku)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ibram mutumin Kaldiya ne daga birnin Ur wanda Allah ya zaɓe shi ya zama kakan Isra'ilawa. Allah ya sauya sunansa zuwa "Ibrahim."
(Hakanan duba: Kan'ana, Kaldiya, Saratu, Ishaku)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ibram mutumin Kaldiya ne daga birnin Ur wanda Allah ya zaɓe shi ya zama kakan Isra'ilawa. Allah ya sauya sunansa zuwa "Ibrahim."
(Hakanan duba: Kan'ana, Kaldiya, Saratu, Ishaku)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ibram mutumin Kaldiya ne daga birnin Ur wanda Allah ya zaɓe shi ya zama kakan Isra'ilawa. Allah ya sauya sunansa zuwa "Ibrahim."
(Hakanan duba: Kan'ana, Kaldiya, Saratu, Ishaku)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ibram mutumin Kaldiya ne daga birnin Ur wanda Allah ya zaɓe shi ya zama kakan Isra'ilawa. Allah ya sauya sunansa zuwa "Ibrahim."
(Hakanan duba: Kan'ana, Kaldiya, Saratu, Ishaku)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ibram mutumin Kaldiya ne daga birnin Ur wanda Allah ya zaɓe shi ya zama kakan Isra'ilawa. Allah ya sauya sunansa zuwa "Ibrahim."
(Hakanan duba: Kan'ana, Kaldiya, Saratu, Ishaku)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ibram mutumin Kaldiya ne daga birnin Ur wanda Allah ya zaɓe shi ya zama kakan Isra'ilawa. Allah ya sauya sunansa zuwa "Ibrahim."
(Hakanan duba: Kan'ana, Kaldiya, Saratu, Ishaku)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
"Ibraniyawa" mutane ne da suka zama zuriyarsu daga Ibrahim ta layin Ishaku da Yakubu. A cikin Littafi Mai Tsarki Ibrahim ne aka fara kira "Ba'Ibrane."
(Hakanan duba: Isra'ila, Yahudu, shugabannin Yahudawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
"Ibraniyawa" mutane ne da suka zama zuriyarsu daga Ibrahim ta layin Ishaku da Yakubu. A cikin Littafi Mai Tsarki Ibrahim ne aka fara kira "Ba'Ibrane."
(Hakanan duba: Isra'ila, Yahudu, shugabannin Yahudawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
"Ibraniyawa" mutane ne da suka zama zuriyarsu daga Ibrahim ta layin Ishaku da Yakubu. A cikin Littafi Mai Tsarki Ibrahim ne aka fara kira "Ba'Ibrane."
(Hakanan duba: Isra'ila, Yahudu, shugabannin Yahudawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ifraim shi ne ɗa biyu ga Yosef. Zuriyarsa ita ake kira Ifraimiyawa, suna ɗaya daga cikin kabilan Isra'ila sha biyu.
(Hakanan duba: mulkin Isra'ila, kabilun Isra;ila goma sha biyu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Iliya ɗaya ne daga cikin mafiya muhimmaci a cikin annabawan Yahweh. Iliya ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakunan Isra'ila da na Yahuda masu Yawa tare da sarki Ahab.
(Hakanan duba: mu'ujuza, annabi, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Iliya ɗaya ne daga cikin mafiya muhimmaci a cikin annabawan Yahweh. Iliya ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakunan Isra'ila da na Yahuda masu Yawa tare da sarki Ahab.
(Hakanan duba: mu'ujuza, annabi, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Iliya ɗaya ne daga cikin mafiya muhimmaci a cikin annabawan Yahweh. Iliya ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakunan Isra'ila da na Yahuda masu Yawa tare da sarki Ahab.
(Hakanan duba: mu'ujuza, annabi, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Iliya ɗaya ne daga cikin mafiya muhimmaci a cikin annabawan Yahweh. Iliya ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakunan Isra'ila da na Yahuda masu Yawa tare da sarki Ahab.
(Hakanan duba: mu'ujuza, annabi, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Iliya ɗaya ne daga cikin mafiya muhimmaci a cikin annabawan Yahweh. Iliya ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakunan Isra'ila da na Yahuda masu Yawa tare da sarki Ahab.
(Hakanan duba: mu'ujuza, annabi, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Iliya ɗaya ne daga cikin mafiya muhimmaci a cikin annabawan Yahweh. Iliya ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakunan Isra'ila da na Yahuda masu Yawa tare da sarki Ahab.
(Hakanan duba: mu'ujuza, annabi, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Irmiya annabin Allah ne a masarautar Yahuda. Littafin Irmiya a Tsohon Alƙawari yana ɗauke da anabce-anabcensa.
(Hakanan duba: Babila, Yahuda, annabi, kangara, rijiya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ishaku shi ne tilon ɗa ga Ibrahim da kuma Saratu. Allah ya yi alƙawari zai ba su ɗa duk da yake sun tsufa sosai.
(Hakanan duba: Ibrahim, zuriya, har abada, cika, Yakubu, Saratu, kabilu sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ishaku shi ne tilon ɗa ga Ibrahim da kuma Saratu. Allah ya yi alƙawari zai ba su ɗa duk da yake sun tsufa sosai.
(Hakanan duba: Ibrahim, zuriya, har abada, cika, Yakubu, Saratu, kabilu sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ishaku shi ne tilon ɗa ga Ibrahim da kuma Saratu. Allah ya yi alƙawari zai ba su ɗa duk da yake sun tsufa sosai.
(Hakanan duba: Ibrahim, zuriya, har abada, cika, Yakubu, Saratu, kabilu sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ishaku shi ne tilon ɗa ga Ibrahim da kuma Saratu. Allah ya yi alƙawari zai ba su ɗa duk da yake sun tsufa sosai.
(Hakanan duba: Ibrahim, zuriya, har abada, cika, Yakubu, Saratu, kabilu sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ishaku shi ne tilon ɗa ga Ibrahim da kuma Saratu. Allah ya yi alƙawari zai ba su ɗa duk da yake sun tsufa sosai.
(Hakanan duba: Ibrahim, zuriya, har abada, cika, Yakubu, Saratu, kabilu sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ishaku shi ne tilon ɗa ga Ibrahim da kuma Saratu. Allah ya yi alƙawari zai ba su ɗa duk da yake sun tsufa sosai.
(Hakanan duba: Ibrahim, zuriya, har abada, cika, Yakubu, Saratu, kabilu sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ishaku shi ne tilon ɗa ga Ibrahim da kuma Saratu. Allah ya yi alƙawari zai ba su ɗa duk da yake sun tsufa sosai.
(Hakanan duba: Ibrahim, zuriya, har abada, cika, Yakubu, Saratu, kabilu sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ishaya annabin Allah ne da ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakuna huɗu na Yahuda, wato Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya.
(Hakanan duba: Ahaz, Asiriya, Kristi, Hezekiya, Yotam, Yahuda, annabi, Uzziya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ishaya annabin Allah ne da ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakuna huɗu na Yahuda, wato Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya.
(Hakanan duba: Ahaz, Asiriya, Kristi, Hezekiya, Yotam, Yahuda, annabi, Uzziya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ishaya annabin Allah ne da ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakuna huɗu na Yahuda, wato Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya.
(Hakanan duba: Ahaz, Asiriya, Kristi, Hezekiya, Yotam, Yahuda, annabi, Uzziya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ishaya annabin Allah ne da ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakuna huɗu na Yahuda, wato Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya.
(Hakanan duba: Ahaz, Asiriya, Kristi, Hezekiya, Yotam, Yahuda, annabi, Uzziya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ishaya annabin Allah ne da ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakuna huɗu na Yahuda, wato Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya.
(Hakanan duba: Ahaz, Asiriya, Kristi, Hezekiya, Yotam, Yahuda, annabi, Uzziya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Ishaya annabin Allah ne da ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakuna huɗu na Yahuda, wato Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya.
(Hakanan duba: Ahaz, Asiriya, Kristi, Hezekiya, Yotam, Yahuda, annabi, Uzziya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Isra'ila" ita ce kalmar da Allah ya ba Yakubu. Ma'anarta ita ce "Ya sha gwagwarmaya da da Allah."
(Hakanan duba: Yakubu, mulkin Isra'ila, Yahuda, banin, kabila goma sha biyu ta Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Isra'ila" ita ce kalmar da Allah ya ba Yakubu. Ma'anarta ita ce "Ya sha gwagwarmaya da da Allah."
(Hakanan duba: Yakubu, mulkin Isra'ila, Yahuda, banin, kabila goma sha biyu ta Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Isra'ila" ita ce kalmar da Allah ya ba Yakubu. Ma'anarta ita ce "Ya sha gwagwarmaya da da Allah."
(Hakanan duba: Yakubu, mulkin Isra'ila, Yahuda, banin, kabila goma sha biyu ta Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Isra'ila" ita ce kalmar da Allah ya ba Yakubu. Ma'anarta ita ce "Ya sha gwagwarmaya da da Allah."
(Hakanan duba: Yakubu, mulkin Isra'ila, Yahuda, banin, kabila goma sha biyu ta Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Isra'ila" ita ce kalmar da Allah ya ba Yakubu. Ma'anarta ita ce "Ya sha gwagwarmaya da da Allah."
(Hakanan duba: Yakubu, mulkin Isra'ila, Yahuda, banin, kabila goma sha biyu ta Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Isra'ila" ita ce kalmar da Allah ya ba Yakubu. Ma'anarta ita ce "Ya sha gwagwarmaya da da Allah."
(Hakanan duba: Yakubu, mulkin Isra'ila, Yahuda, banin, kabila goma sha biyu ta Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Isra'ila" ita ce kalmar da Allah ya ba Yakubu. Ma'anarta ita ce "Ya sha gwagwarmaya da da Allah."
(Hakanan duba: Yakubu, mulkin Isra'ila, Yahuda, banin, kabila goma sha biyu ta Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Isra'ila" ita ce kalmar da Allah ya ba Yakubu. Ma'anarta ita ce "Ya sha gwagwarmaya da da Allah."
(Hakanan duba: Yakubu, mulkin Isra'ila, Yahuda, banin, kabila goma sha biyu ta Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Isra'ila" ita ce kalmar da Allah ya ba Yakubu. Ma'anarta ita ce "Ya sha gwagwarmaya da da Allah."
(Hakanan duba: Yakubu, mulkin Isra'ila, Yahuda, banin, kabila goma sha biyu ta Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Isra'ila" ita ce kalmar da Allah ya ba Yakubu. Ma'anarta ita ce "Ya sha gwagwarmaya da da Allah."
(Hakanan duba: Yakubu, mulkin Isra'ila, Yahuda, banin, kabila goma sha biyu ta Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Isra'ila" ita ce kalmar da Allah ya ba Yakubu. Ma'anarta ita ce "Ya sha gwagwarmaya da da Allah."
(Hakanan duba: Yakubu, mulkin Isra'ila, Yahuda, banin, kabila goma sha biyu ta Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kalmar nan "Isra'ila" ita ce kalmar da Allah ya ba Yakubu. Ma'anarta ita ce "Ya sha gwagwarmaya da da Allah."
(Hakanan duba: Yakubu, mulkin Isra'ila, Yahuda, banin, kabila goma sha biyu ta Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yakubu shi ne ƙaramin ɗan tagwai na Ishaku da Rebeka.
(Hakanan duba: Kan'ana, ruɗa, Isuwa, Ishaku, Rebeka, kabilar sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yakubu shi ne ƙaramin ɗan tagwai na Ishaku da Rebeka.
(Hakanan duba: Kan'ana, ruɗa, Isuwa, Ishaku, Rebeka, kabilar sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yakubu shi ne ƙaramin ɗan tagwai na Ishaku da Rebeka.
(Hakanan duba: Kan'ana, ruɗa, Isuwa, Ishaku, Rebeka, kabilar sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yakubu shi ne ƙaramin ɗan tagwai na Ishaku da Rebeka.
(Hakanan duba: Kan'ana, ruɗa, Isuwa, Ishaku, Rebeka, kabilar sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yakubu shi ne ƙaramin ɗan tagwai na Ishaku da Rebeka.
(Hakanan duba: Kan'ana, ruɗa, Isuwa, Ishaku, Rebeka, kabilar sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yakubu shi ne ƙaramin ɗan tagwai na Ishaku da Rebeka.
(Hakanan duba: Kan'ana, ruɗa, Isuwa, Ishaku, Rebeka, kabilar sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yakubu shi ne ƙaramin ɗan tagwai na Ishaku da Rebeka.
(Hakanan duba: Kan'ana, ruɗa, Isuwa, Ishaku, Rebeka, kabilar sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yakubu shi ne ƙaramin ɗan tagwai na Ishaku da Rebeka.
(Hakanan duba: Kan'ana, ruɗa, Isuwa, Ishaku, Rebeka, kabilar sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yakubu shi ne ƙaramin ɗan tagwai na Ishaku da Rebeka.
(Hakanan duba: Kan'ana, ruɗa, Isuwa, Ishaku, Rebeka, kabilar sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yakubu shi ne ƙaramin ɗan tagwai na Ishaku da Rebeka.
(Hakanan duba: Kan'ana, ruɗa, Isuwa, Ishaku, Rebeka, kabilar sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yakubu shi ne ƙaramin ɗan tagwai na Ishaku da Rebeka.
(Hakanan duba: Kan'ana, ruɗa, Isuwa, Ishaku, Rebeka, kabilar sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Yakubu shi ne ƙaramin ɗan tagwai na Ishaku da Rebeka.
(Hakanan duba: Kan'ana, ruɗa, Isuwa, Ishaku, Rebeka, kabilar sha biyu na Isra'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Issaka shi ne ɗa na biyar ga Yakubu. Mahaifiyarsa ita ce Liya.
(Hakanan duba: Gad, Manasse, Naftali, kabilar Isra'ila sha biyu, Zebulun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Akan tuna da Istifanus domin shi ne mutum na farko da aka fara kashewa a masu bi na farko, wato shi ne na farko da aka kashe saboda bangaskiyar Almasihu. zahirin rayuwarsa da mutuwarsa an rubuta shi a littafin Ayyukan manzanni.
(Hakanan duba: zaɓa, dikin, Yerusalem, Bulus, dutse, gaskiya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Isuwa ɗaya ne daga cikin tagwan 'ya'yan Ishaku da Rebeka. Shi ne aka fara haifa musu. Ɗan'uwansa shi ne Yakubu.
(Hakanan duba: Idom, Ishaku, Yakubu, Rebeka)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Isuwa ɗaya ne daga cikin tagwan 'ya'yan Ishaku da Rebeka. Shi ne aka fara haifa musu. Ɗan'uwansa shi ne Yakubu.
(Hakanan duba: Idom, Ishaku, Yakubu, Rebeka)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kaldiya wani yanki ne a kudancin Mesafotamiya ko Babiloniya. Mazaunan wannan yanki ana kiransu Kaldiyawa.
(Hakanan duba: Ibrahim, Babila, Shina, Ur)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kan'ana ɗan Ham ne, ɗaya daga cikin 'ya'yan Nuhu. Kan'aniyawa sune zuriyar Kan'ana.
(Hakanan duba: Ham, Ƙasar Alƙawari)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kana ƙauye ne ko kuma gari a lardin Galili, wajen mil tara yamma da Nazaret.
(Hakanan duba: Kafarnihum, Galili, sha biyun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kana ƙauye ne ko kuma gari a lardin Galili, wajen mil tara yamma da Nazaret.
(Hakanan duba: Kafarnihum, Galili, sha biyun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kana ƙauye ne ko kuma gari a lardin Galili, wajen mil tara yamma da Nazaret.
(Hakanan duba: Kafarnihum, Galili, sha biyun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kana ƙauye ne ko kuma gari a lardin Galili, wajen mil tara yamma da Nazaret.
(Hakanan duba: Kafarnihum, Galili, sha biyun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kana ƙauye ne ko kuma gari a lardin Galili, wajen mil tara yamma da Nazaret.
(Hakanan duba: Kafarnihum, Galili, sha biyun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
Kana ƙauye ne ko kuma gari a lardin Galili, wajen mil tara yamma da Nazaret.